TARAYYYA 7-8
Page 7
Abokansa mafi yawansu turawa
ne sai 'Dan uwansa kuma
abokinsa dasuka taso tare khaleefa duk da kasancewar
basa guri 'daya shi khaleefa yana turkey ne amma suna yawan kasancewa tare idan
zasuzo gida kokuma idan sun tafi wata qasar Hutu,
Shiru shiru ne baida doguwar
hayaniya bare son dogon zance amma ahaka so silent dashi Allah yayisa mai
tsananin son rayuwar hutawa da shaqatawa batareda takurawa ba sam shi mutum ne
maison life shiyasa kana ganinsa zakaga wayayyyan mutum da ilimi ya kustsa
sosai tareda Hutu da naira.
SUHAILAT BOUKAR itace gidanta
yake kusadana maheer 'yar asalin Mali karatun masters dinta takeyi anan qasar
Sosai take shiri da maheer
kasancewar sunfara sanin junane sanadin abokinsa bell dayake itama friend
dinta.
Sunfara gaisawa ahankali
harsuka saba kasancewarsu wayayyu masu ilimi yasa suke jin dadin zama da juna
sbd kowa yasan abinda yakeyi kuma kowannansu is living a free life.
Itadai suhailat tana tsananin
son maheer amma ganin babu wannan ataredashi yasa tayi amfani da iliminta ta
danne tareda 6oyewa koda wasa babu wanda zaice yaga alamar sonsa atareda ita
sbd sanin ita mace ce meye amfanin iliminta ta wannan fannin idan bazata iya
danne soyyayyar wanda baimasan tanayiba.
TAKE NOTE 'yan mata pls mu
koyi boye soyayyar wanda baisanma kanayiba ki daraja kanki na zamantowarki
mace. 3
Sultana ma ba laifi sundan
saba da suhailat harkiranta tanayi ta gaidata.
Duk lokacinda yazo gida
maganar sultan 'dayace wato yayi aure asamu 'da namiji sbd dukkanin hope dinsu
yanxu akansa yake
Shi alamarin na matuqar basa
ciwon kai da mamaki idan ana cewa yayi aure ya haifi 'da namiji
He is man of his own now
baiga dalilin dazaisa ace anason dole yayi aureba duk lokacinda yaji yafara
buqatar kasancewa da mace zaiyi auren amma ba haka kawaiba yanxu yayi aure.
Ammynsa nason yayi auren amma
ita lalla6asa takeyi bakamar sultan dake son nuna masa qarfin iko ba kuma tasan
tunda sultan yace maheer 'din yayi aure to kobai tashiba sai yayi masa koyasan
matar kobai santaba.
Hakan yasa sultana take kaiwa
maheer 'din ziyara idan aka 'danja lokaci tana rarrashinsa amma dai still babu
alamar zai takura kansa yayi yanda sukeso 'din shiyasa ta hakura lalla6a sultan
akan abi maheer din ahankali abarsa har zuwa lokacinda zaiji ra'ayin yin auren.
Wani shu'umin murmushi sultan
yasaki lokacinda tagama fadar zancen wanda yasa gaban faduwa sbd tasan itama
fada kawai tayi ko za'a dace yaji shawarar tata amma tasan sultan Sam baya
'daga qafa ga wanda ke masa garaje.
Washe gari tun agurin sallar
asuba aka bada shelar saqon sarki na bayan sallar juma'ar satin nan za'a
'daurawa yarima aure.
Koda labarin ya iso kunnen
sultana ajiyar zuciya kawai tayi ahankali batareda tace komaiba Dan tasan dole
haka zata faru tayi magana asata kullen shekara.
Haka dai cikin dauriya
sultana ta daure tagabatarwa da sultan SUHAILAT amatsayin wadda yarima yake
kulawa acan inda yake.
Tsaf tabasa bayanin komai
akan suhailat babu bata lokaci akai aike ba laifi 'yar manyan mutane ce ita da
yayanta kadai iyayensu suka haifa rayuwarsu ba takura suna yin rayuwarda duk
sukeso amma sbd wadatar ilimi yasa Sam basa iskanci amma rayuwa tajin dadi da
Hutu babu wadda basayi musamman arziki da Allah yahorewa iyayensu.
Sanin waye maheer da mugun
ra'ayi akan abinda baiyi niyaba yasa sultan cewa sultana Zaarah ta koma
masarautar mahaifinta batareda bawa ko 'dayaba harsai ranarda matar maheer zata
shigo masarautar sushigo tare.
Rintse idanuwa tayi cikin
ciwon rai da tausayin maheer sbd daga ita har maheer da kowa yasan abinda sarki
ke nufi da hakan
Wato tayi gidansu harsai
maheer ya aminta da zaiyi aure bayan yasan hakan zai ta6a tarihi da sunan
masarautar mahaifinta.
Kwana biyu tayi tana hada
kayanta sbd tuni akayi mata booking ticket 'din jirgi.
Lokacinda labari ya iso
gurinsa rintse idanuwa yayi cikin daci da radadin zuciya sbd yasan me sultan ke
nufi da hakan,
Duk lokacinda yakeson wani
Abu daga garesa da ammynsa yake yaqarsa.
Bude jajayen idanuwansa yayi
yakalli wayarsa ya dauka babu bata lokaci yakira sarkin isarda saqo yana 'dauka
da wata irin murya mai nuna 6acin rai dayake ciki kai tsaye yace,
A isarwa da sultan saqon abar
ammynah ta tarbi matata ranar dayakeso.
Angama sarkin saqo yafada
cikin matuqar girmamawa kafin ya garzaya da hanxarinsa ya isarda saqon.
Murmushin manya sultan yayi
yace,
Kasanar masa ranar juma'a ne
saiya shirya dawowa idan kuma baidawoba ranar asabar sultana zata kawo masa
matarsa har inda yake.
Koda aka sake Isar masa da
wannan saqon datse wayar yayi tareda rintse ido ya budesu jajir sbd baqin cikin
yanda idan sultan nason quntata masa yakeyi ta hanyar ammynsa
Banda son a xafafa zuciyarsa
ace idan baijeba mahaifiyarsa za'asa takawo masa mata har wata qasa sbd anraina
masa ita....
Wurgi yayi da tumbler din
hannunsa a qule yace,
Wat did he think of himself
sultan dayake masa haka bayan yasan he can't tolerate seeing his ammy being
disrespected.
Baigama shan haushi da
mamakiba saida yakoma yatararda lbarin suhailat ce amaryarsa
Duk inda ransa yake saida ya
sake 6aci sbd rashin tunanin dama tun farko ita 'din yagabar tun kafin aci zarafin
ammynsa sbd yasan idan ya auri suhailat kowa zaiyi rayuwarda yakesone babu
takura sbd dukkaninsu sunada ilimi da wayewar bawa junansu freedom batareda
damuwar komaiba.
Hakan yasa ba laifi ya tsaya
akayi duk wani biki daza'ayi aka daura aure aka kawo amarya.
Abu 'daya daya sani shine
haihuwar da'akeson yayi rututu kamar ta awaki bazai yitaba sbd atsarinsa 'yaya
uku zuwa hudu sun ishesa sbd gidansa da familynsa suxamto yanda yakeso baya
sha'awar yara da yawa bare ayi zancen mata biyu Wanda shi yana ganin Sam bazai
iya ya kwana da wancan yazo yakwana da wannan ba koba komai baya tunanin zaiso
mata biyu dole 'daya zaiso so babu mgnar adalci agurin Dan haka Sam babu tsari
bare mafarkin auren mata biyu arayuwarsa koba komai shi mutumne mai tsananin
qyanqyami haka Allah yayisa.
A ranarda aka kawo suhailat
aranar yayiwa sultan yanda yakeso yayi kwanan aureda ita
Satinsu biyu suka tattara
suka koma Georgia shida suhailat.
Suhailat tasan Sam babu so
atsakaninta dashi saidai wayewarta da iliminta tareda zamantowarta free yasa
yakejin dadin zama da ita kuma shima sbd yanada wadataccen ilimi da wayewa yasa
Sam babu ma alamar datake nuna baya sonta as far as suna respecting juna dakuma
respecting ra'ayoyin junansu ya ishesu zaman aure sabanin wasu mazan dake nuna
qiyayyar mace qarara Wanda hakan ba halin namiji mai ilimi bane so pls marubuta
mu gyara Sam duk namijin dayakeda ilimi da wayewa baikamata ariqa sashi yana
nunawa mace tsana afiliba da kyararta,idan yanada ilimi to yayi amfani dashi. 2
Wata uku da komawarsu ciki ya
6ullo nan saqo ya isa masarauta farin ciki da murna suka kama koina sai sadakar
maqudan kudade akeyi da kyaututtuka baga masarautar ba kawai duk 'yan mineelik
duk wani mai arziki kyauta da sadaka yakeyi
na farin cikin insha Allah za'a samu magaji amasarautar dazata hanasu
zamantowa qarqashin wata azzalumar masarautar.
Lokacinda cikin ya isa
haihuwa suka dawo gida ranar haihuwa kaf koina ba wani hayaniya ko 'yan
kasuwanni basu firfitoba hakadai ake zaune zaman jira baga sultanba baga 'yan
fadaba baga 'yan gariba,
Masarautun dasuke abokantaka
datasu masarautarma yau duk cikin jiran haihuwar suke suna adduar samun namiji.
Bayi kuwa sunsan yau qaddara
tasasu yin laifi saidai wani kan badai nakaba shiyasa kowa ya nutsu anata
addua.
Sultan dai yau yasan 'yancin
masarautarsa ya dangana ne da abinda za'a haifa shiyasa yau tsit yake yana
lazimi cikin ransa.
Sultana zaarah nacan sashen
da ake kar6ar haihuwar sbd haihuwar tazo da gardama
Su jakadiya sai shar6e zufa
akeyi ga kuyangi da bayi ajere kofar sassan haihuwar sai gumin wahala da
fargaba sukeyi sbd sunsan yau duk aka haifi mace 'daya daga cikinsu ne zaije
isarda mummunan saqonda qila abakin lafiyarsa ko ransa shiyasa gabaki 'daya a
tsure suke da fargaba tareda adduar samun namiji.
#mamuhgee.
Page 8
Haske writers association💡
Yini guda cur masarautar tayi
cikin zaman jiran haihuwar suhailat,
Maheer kuwa duk yanda kowa ya
'daga hankalinsa bai 'daga nasaba sbd yasan dukkaninsu damuwarsu ba akan
lafiyar matarsa yakeba sai akan abinda za'a haifane yazamo namiji,
Shi tausayinsa akan suhailat
din ne duk da yasan tanada dauriya sbd zama da ita yanxu yasa yasake sanin
halayyarta tanada juriyar danne abu ta 6oyesa acikin ranta duk qwaqwarka yanada
wuya ka gano abunda ke ranta shiyasa take matuqar basa tausayi sbd shikuma
mutum ne da idan bayason Abu baya iya tsayawa basa kulawarda yakamata,
Tasani babu sonta aransa amma
baya nuna mata wasu halayansa ke nuna mata saidai son rayuwarsa yasa dukkaninsu
jin dadin rayuwar aurensu sbd sunayintane very romantic sbd maheer romantic
life is one of the best abinda yafiso arayuwarsa.
Zaune yake a lafiyyan palonsa
dake sashensa idanuwansa a lumshe kwata kwata bayan hot coffee dayasha dasafe
har lokacin baici komaiba duk da ankawo abinci daga kicin din sashen ammynsa
anjere masa dama kaidarsane bayacin abincin kowane kicin saina sashen
mahaifiyarsa.
Lokacinda limamin masarautar
yakammala kiran sallar magriba daidai lokacin suhailat tayi wani yunquri tareda
wahalallen nishi cikin tsananin azaba baby yafado.
Su sultana da sarauniya adama
tareda sauran 'yaya mata na zuriar gidan dake kusa duk sunzo suka miqe kusan
atare kowa na kallon quryar 'dakinda suhailat din take ciki.
Bayi da kuyangi tuni suka
sake gyara tsayuwa suna hadiye yawun fargabar meza a fito ace anhaifa.
'Daga jaririyar mai karbar
haihuwar tayi tareda kallonta taga mace ce aka haifa
Ta 'dago takalli jakadiya
tana ha'do sabon gumi ta miqa mata jaririyar.
Karbar jaririyar jakadiya
tayi tana kallonta yanda take canyara
kuka ta qura mata ido tareda sauke nannauyar ajiyar zuciya tamiqawa masu
gyarata ta fita tana tattaro kuzari ta iso gabansu sultana ta tsaya tareda
sunkuyardakai tace,
Allah yaqaramiki hkr da
lafiya uwar 'dakina Allah ya albarkaci yarima da samun 'YA MACE.
Wata irin 6oyayyar ajiyar
zuciya sarauniya adama tasauke zuciyarta na cika da wani irin farin ciki amma
afili kallon dakinda suhailat take ciki tayi tace,
Akimtsa uwar da 'yar amaidasu
sashensu
Jaririyar akawomin ita nizan
kaiwa sultan.
Sultana ganin adama tayi mgn
yasa ta 'dagawa jakadiya kai tareda cewa jakadiya akula sosai da suhailat ta
juya ta fice kuyanginta na bayanta.
Lokacinda labarin haihuwar
yagama isa koina sultan baice komaiba yace akaiwa maheer 'yarsa yayi mata
huduba.
Bayan maheer yayi mata huduba
aka maidawa sultan 'yar yasa mata suna AMATULLAH.
Ba laifi anyi shagalin suna
duk wani gata anunuawa suhailat da 'yarta duk da dai tana saneda ba wani farin
ciki kowa keyi da haihuwar ba.
Adama kuwa sbd jin dadin
ansamu mace ba namiji ba har wani soyayya take nunawa amatullah.
Watansu 'daya maheer yakoma
itakuma ta tafi Mali ganin gida kafin daga can takoma Georgia tasamu maheer.
Bayan komawarsu suka cigaba
da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali kuma sosai maheer keson amah 'dinsa sbd
yarinyar babu abinda tabaro nasa na kamanni shiyasa koyaushe take sake shiga
ransa.
Baca Juga
Ta bangaren suhailat kuwa
saidai tacigaba da sawa kanta dangana da hkr saidai tunda yanason 'yarta hakan
naqara saka mata nutsuwa da kwanciyar hankali.
Tunda suka koma cikin dubaru
sultana ke 'Dan lurarda suhailat akan kada tayi family planning.
Tunda suka dawo yamaida
hankali ga rayuwarsa yamanta da wani batun samun magaji da sultan keso.
STORY CONTINUES BELOW
Shekarar amah 'daya da sati
biyu aka sake tabbatarda ciki jikin suhailat nan aka sake shiga 'doki da duqufa
addua da sadakoki akan Allah yabiya buqata.
Wannan karon saida cikin ya
tsufa sultan yasa suka dawo akaro na biyu ranar naquda akayi jigum jigum jiran
tsammani
Allah mai yanda yaso tasake
haihuwar 'ya mace. 1
Ita kanta suhailat tayita adduar
Allah yabada 'da namijin sbd tafara hangowa kanta da 'yayanta kyara nan gaba.
Kai tsaye sultan yace kar
akawo masa jaririyar akaiwa maheer yayi mata huduba da suna gabaki daya.
Yarima yayiwa 'yarsa huduba
yasaka mata suna fammah.
Wannan karon babu wani
shagali ganin haka yasa yarima ya tattarasu suka komawarsu.
Shekarar fammah daya da wata
uku suhailat tasake samun ciki wannan karon ma sultan bai cire raiba yace
sudawo
Satinsu biyu da dawowa ta
haifi mace amma 'yar kwana biyu da haihuwa ta rasu ganin haka suka komawarsu
sbd wannan karon Sam ita suhailat yanxu ta rage jin dadin masarautar sosai sbd
sultana ce kawai ke qaunar 'yayanta sai adama dake yimusu soyayyar dole.
Ayanxuma tana 'daukeda ciki
tsoho sultan yace suyi zamansu harsai ta haihu anji me ta haifa saigashi ankuma
samun mace shine sultana taje tafada masa.
Ganin wankin hula na Neman
kaisa dare yasa ya yanke hukuncin yarima zaidawo gida atara masa barori koda
za'asamu qaruwar ta hanyarsu.
Basu dawo Ethiopia ba Mali
suka wuce acan gidansu suhailat sukai hutunsu na kusan sati biyu cikin jin dadi
sbd gidansu gidan wayayyin mutane ne masu ilimi gasu amah ma sunason nan 'din
sbd suna sakewa sosai ga qaunarsu da Granny's
dinsu suke musu.
Daga Mali komawarsu sukayi
Georgia tareda yaransu sukaci gaba da rayuwarsu.
Maheer duk cikin yaransa uku
babu kamar amah acikin ransa yana tsananin qaunarta Wanda suhailat ke adduar
Allah yasa ko kwatankwacin rabin qaunar dayakewa amah tasamu daga garesa.
Maheer da family dinsa wata
irin rayuwar turawa ta jin dadi sukeyi babu damuwa babu takura.
Yaransa sun taso cikin turawa
da yanayin rayuwar turawa dasuka ga iyayansu aciki
yanayin fatarsu dakeda sirkin
yellow da brown kawai zaka zaka kalla kace musu black Americans batareda kasan
asalinsu ba.
Baby AMNAH Nada shekara biyu
tasake samun ciki wannan karon yazo mata da laulayi da nauyin jiki sosai
shiyasa ta rage fita aiki sosai dakuma kula da gidan ta 6angare 'daya ga amnah
babu lafiya yarinyar tun tana jaririya take fama da pneumonia Wanda idan ya
tashi yana wahalarda yarinyar sosai hakan yasa iyayenta ke tsananin qaunarta.
Yau tun safe jikin nata
yatashi sosai sbd kwana tayi yau bada sweater da socks ajikintaba.
Koda Carolina ta shirya amah
da fammah shirin zuwa school sukai breakfast
Amah ta nufi hanyar palon
dadynsu da gudu tana cewa,
Dady we're running late pls
come out.
Fitowarsa daga wanka kenan
'daureda White towel yajiyo muryar amah 'din ya lumshe ido ya bude yakalli
agogo yana cewa,
Amah will kill me today for
this.
Kallon suhailat yayi data fito
daga dressing room 'dinsa daukeda kayanda sabon towels guda uku zata kai toilet
yace,
Ki taremin ita na shirya zata
cikamin kunne ne da surutu nakasa shiryawa.
Aje towels din tayi bakin
king size bed din dake cikin qaton hadadden bedroom din nasa ta nufi qofa tana
cewa,
Amah nima wlh bazan iya da
surutunki ba.
Tana fitowa amah na kama
handle din dakin.
Kamo hannunta tayi tana cewa,
Let's go and check on amnah
before your dad comes out....
Tsayawa tayi tareda 6ata
fuska zatayi kuka
Suhailat tayi saurin janta
suka nufi room 'din yaran dake tsare dakomai na yara.
Saurin isa tayi gurin amnah
dake kwance agadonta tana fusgar numfashi daqyar.
Daukarta tayi da sauri tareda
dubata taga ciwontane yatashi cikin karaji ta qwalawa Carolina kira jikinta na
rawa.
Da hanzari Carolina ta iso
tana cewa,
Yes ma'am.
Cikin daga murya rai amatuqar
6ace tace,
Are you trying to kill my
poor baby by letting her sleeps without any sweater and socks?
Arikice takalli suhailat
cikin rudewa tace,
I'm sorry ma'am but I.......
Just shut up I don't want to
hear your stupid silly excuses
Hw can you be so careless
and.....
Keep quite suhailat'''''
sukaji daga bakin qofar dakin ta juyo takallesa cikin takaici tace,
Baby pls.....
I said keep quite
suhailat"" yasake fada yana kallon yanda Carolina ke sheshekar kukan
fadanda suhailat tayi mata yace,
Why do you always wants to
make things worst? Yanxu kinxo kinsamu halinda amnah take ciki instead kiyi
saurin bata taimakon gaggawa kintsaya hayaniya and you seriously know hw much I
hate that,
Ga yara basu wuce school ba
kinanan kina fada kinkasa tsayawa kiji wat was trying to say.
Hawaye ne yaciko idon
suhailat takallesa lokacinda ya juya yafice yana zuwa palo su amah suka bisa
mota suka shiga ya wuce yafara ajesu school ya nufi gurin aikinsa.
Bayan fitarsa share hawayenta
tayi ta miqawa Carolina amnah tace,
Quickly remove her pampy and
dress let me go and change we're taking her to the hospital.
Lokacinda suka fito tuni
jikinta yaqara rikicewa tun a mota takirasa.
Tsaye suke ya zuba dukkanin
hannuwansa a aljihun trousers dinsa fuskarsa sai wani irin kwarjini da glowing
takeyi sbd kyan fata da hutu yana sauraron bayanan wasu new doctors da aka kawo
asibitin wayarsa tayi ringin yakalli nurse din dake tsaye riqe da kayansa na
theatre da wayarsa tareda wasu folders din patients din dazaiyiwa aiki ya miqa
mata hannu ta miqo masa wayar yana ganin suhailat ce ya rufe idanu ya bude
tareda dauka yana komawa office dinsa na qurya.
Sanin bayason hayaniya da
tashin hankali yasa ta daidaita nutsuwarta tareda share hawayenta tana 6oye
kukanta tace,
Baby my amnah is leaving me
wlh I can feel it....
Rufe ido yayi ya bude Wanda
yazamo 'dabi'arsace yin hakan duk zaiyi mgn sbd tattaro maganar kasancewar
baifiyason dogowar magana.
Jikin ne?
Eh baby kwata kwata she's not
breathing she's loosing it....
Bring her to hospital
yanxunan.
Muna hanya already.
Kashe wayar yayi tareda mayar
da hannuwansa aljihu ya rufe ido.
Suna isowa akayi gaggawar
fara bata taimakon gaggawa ta hanyar saka mata oxygen saidai tariga tayi nisa
sosai mintuna talatin da zuwansu Allah yakarbi ranta.
Cikin jinjina alamarin
doctors din dake kanta suka gama rubuce rubucensu tareda kallon maheer da
suhailat ke jikinsa tana kuka sukace,
Sorry doctor maheer we lost
her.
Wani irin kuka suhailat
tasaki tana qanqamesa
Rintse idanuwansa yayi ya
rungumeta yana bubbuga bayanta batareda yace komaiba.
#mamuhgee
Post a Comment for "TARAYYYA 7-8"