Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

TARAYYA 9-10


Page 9
 Haske writers association💡

Bayan rasuwar amnah sosai suhailat tashiga damuwa shikuma gashi bai iya ya ake lallashi ba bare
Iyakacinsa idan zai fita yanasaka
yin breakfast idan yadawo suyi dinner sbd bai cika lunch agidaba.
Hakadai ta dangana tacigaba da rainon sabon cikinta.

Sultan yayi yayi yaqara aure yamaqi dawowa qasar shiyasa yadauki mataki kaitsaye akansa.

Sultana tashiga damuwa matuqa jin amnah ta rasu batareda sun ta6a ganinba saidai a hoto kawai gashi tanason zuwa amma sultan yasa doka.

Jakadiya kuwa sosai tafara shirya shiryen na kullum tana sashe sashe duddubawa cikin dubara sbd sotake saita ringa fahimtar halayyarka sbd kar asamu magaji ta macenda batada nutsuwa ko ma'ana.

Kullum cikin kwantarwada suhailat hankali sultana take hardai taga ta warware itama hanakalinta ya kwanta.

Lurada jakadiya sultana tayi ta kalleta bayan ta kori dukkanin bayinta dake sashen sbd maganar datakesonyi da jakadiyar.

Rumanah ce kawai a bedroom din ammyn tana aikinta hankali kwance.

Cikin muryar bada umarni tace,

Inason sanin hukuncin da sultan ya yanke akan maheer sbd nasan me shirunsa yake nufi.

Sunkuyar dakai jakadiya tayi wani zufa ya tsatsafo mata cikin sanyin jiki da sanyin murya tace,

Sultan yabada umarnin atanadarwa yarima sa dakoki har biyar akillacesu zai dawo bazai komaba yanxu sai ansamu qaruwa daga garesu.

Tashi zaune sultana tayi cikin wani irin yanayi na tsananin damuwa da takaici taringa maimaita innalillahi.

Kallon jakadiya tayi tana qoqarin ganin damuwarta bata rinjayetaba murya amatuqar sanyaye tace,

Har kin tanadesu 'din?

Tukunadai ranki ya Dade saidai nima ina cikin tsananin fargaba da tsoron yanda zata kaya sbd aurensa ma ta yaya akasamu yayi bare yanxu mata har biyar.

Rintse idanu sultana tayi tareda budesu jajir tace,

Idan kin zabesu kafin ki gabatarwada sultan su ki gabatarmin dasu inason naga matanda wasu daga cikin jikokina zasu fito ajikinsu.

Jakadiya na fita ta bada umarnin abuga qararrawa atara mata dukkanin wata kuyanga dake masarautar.
Nan tafara dubasu cikin layi harbasa qirguwa sbd yawansu amma takasa samun 'daya dazata ware duk wadda takalla saitaga komai gyara da kulawar daza'ayi mata batakai matsayinda yarima zai hada shimfida da itaba.

Da haka ta sallamesu tace gobe kowanne yayo wanka su sake zuwa subi layi.

Tana gama gyaran bedroom din tafito tazo gaban sultana ta durqusa cikin girmamawa tace,

Ammy nagama kinada buqatar wani abu?

Kallonta sultana tayi da idanuwanta dasukai jajir sbd baqin ciki ta girgiza mata kai.

Ganin halinda ammyn take ciki yabata tsoro ta miqe hartakai qofa ta waiwayo cikin damuwa murya asanyaye tace,

Saida safe ammy.

Asanyaye ta isa dakinsu ta tararda daga mamani har nuratu basu dawoba ta tube taso watsa ruwa amma jin batada gajiya kuma batai wani aikin wahalaba tayi kwanta.

Tana qoqarin juyawa nuratu tashigo amatuqar gajiye ta zauna bakin 'yar katifarta tana cewa,

Rumanah wlh tsufa da wuri zai kamani sbd wahala.

Murmushi rumanah tasaki ahankali kafin ta tashi zaune tace,

Me kike gudu da tsufa da wuri?

Harararta nuratu tayi tana zame kayanta tace,

Ke kuma mekike yiwa sauri da tsufa?
Nifa rumanah banason tsufa da wuri sbd bazan ta6a cire rai daga hangowa kaina wata irin kyakkyawar rayuwa,
Ke nifa har mafarki nakeyi nazama wadda tafi kusanci ga Wanda wai zai mulki masarautarnan anan gaba,
Kuma kinsan menene?
Mace nake gani amafarkina koda yaushe saidai adon zinarai dake jikinta tana hanani ganin fuskarta....

Mamani dake shigowa tayi saurin qarasowa ta riqota tana washe dukkanin haqoranta tace,

'Yarda zaki haifawa yarima ce......

Fusgewa nuratu tayi da qarfi tana cewa,

Barni da zancenki mamani koyaushe bakinki baya tsayawa mmatsayinsa..

Sake washe baki mamani tayi tace,

Nuratuna dama nasan tuntuni jikina nabani kece zaki fitardani cikin wannan qasqantacciyar rayuwar,
Jikina nabani kece za'a zaba amatsayin sa 'dakar yarima.....

Dariyace taxowa rumanah tayi saurin rufe baki sbd gudun masifa da balain mamani dazata iya kwana tana surfa mata.

Cikin takaicin halin mahaifiyarta nuratu takalleta tace,

Lallai mamani bakya sona tunda harkike fatar nazama baiwarda za'a riqa kwana dani ina haihuwa ana karbe 'yayan.

Cikin saurin mamani tace,

Kibar maganar baiwa daga ranarda kika hada shimfida dashi kintashi daga baiwa sbd duk Wadda ta haifo magaji sultan ya 'yantata daga ranar kuma ita za'a miqawa matsayi dakuma kujerar zaman uwar sarki sbd tariga ta haifo sarki,
Duk Wanda taso nadawa yayiwa danta riqon qwarya shi zata nada har 'danta ya girma abasa kujerarsa,
Idan kika haifi namiji nuratu babu Wanda zaki bawa riqon kwarya kece zakiyi mulkin da kanki,
Kece zaki hau kujerar sarauta da kanki,
Kece zaki mulki dubban 'daruruwan sarakuna da daulolinsu,
Kece zaki zama mace ta farko dazatayi mulkin wannan masarauta da aka tsani haihuwar mata.....

Kasa riqe dariya rumanah tayi tasaketa tana kallon mamani data watso mata mugun kallo tayi saurin hadiye dariyar.

Nuratu ma dariyar tasaki tana kallon mamani kafin takalli rumanah suka saki wata dariyar.

Mamani tayi mugun hasala tayo kan rumanah nuratu tayi saurin riqota tana cewa,

Haba mamani nah kece fa uwar sarauniya nuratu kuma kakar magajin sarautar dariyafa kawai mukeyi ta farin cikin wannan mafarkin naki mai dadin gaske kokuwa 'dayar mamar magajin sarauta.

Dariya suka qunshe suna kallon juna suna kallonta.

Ganin sun maidata mahaukaciya yasa qyaci ta fice ahasale.
#Mamuhgee







Page 10

Haske writers association💡 +

Bayan fitarta rumanah taja abun lullubewarta tana murmushi tace,

Nuratu kinfa karyawa mamani gwiwa daga kawai tana mana fatar samun jin dadi da 'yanci idan kika zama sarauniya.... 1

Kallonta nuratu tayi cikin tsananin sanyin jiki tace,

Rumanah ke kinamin fatar nazama baiwarda za'a riqa kwana da ita tana haihuwa Ana karbe yayan idan nazama haka me naqaru dashi arayuwata bayandai ta tabbata naza baiwa tahar mutuwa...

Qarasowa da sauri rumanah tayi ta rungumeta ganin hawaye na zubo mata tace,

Nuratu bana miki fatar wannan rayuwar ko amafarki bare afili,
Keda mamani kune 'yan uwana kullum fatana da adduana musamu kubuta atare mukoma ga asalinmu domin kuwa saimun koma asalinmu zangano nawa asalin.

Cikin sanyin murya nuratu tace,

Rumanah bawa baida ra'ayin kansa ko abinda yakeso sai Wanda uwayen gidansa suka yanke akansa,
Shin kina tunanin qaddara zata iya zuwa kaina aza6eni cikin masu zuwa shimfidar yarima?

Girgiza mata kai rumanah tayi cikin son qarfafata tace,

Insha Allah bazamu ta6a wannan rayuwarba nuratu.

Rumanah ammy bazata ta6a bari kiyi wannan rayuwarba saidai ni banada tabbaci saidai Allah ya dubi rashin gatana.

Jiki sanyaye zuciya fal da tunani da zullumi suka kwanta har mamani tadawo cikin dare ta kwanta babu Wanda yayi bacci acikinsu sbd tunani.

Washe gari fuska 'daure mamani ta tashi babu Wanda ta amsa gaisuwarsa acikinsu qarshema kan rumanah taso sauke haushinta Dan har marinta tayi daga gaisuwa.

Cikin sanyin jiki ta share hawayenta tareda girgizawa nuratu data bude baki zataiwa mamani magana kai tareda sakin murmushin dole mai ciwo kafin ta kammala shirinta ta fice tana cewa,

Natafi'"""cikin sanyin murya.

Kodata isa sashen part ammy cikin sanyin jiki tafara aikinta har qarfe goma tabuga lokacin ammy ta tashi
Kanta qasa tagaida kafin tahau gyaran dakin cikin rashin walwala da rashin kuzari sbd duk lokacinda mamani tayi mata Abu abin na taba zuciyarta ganin batada wasu 'yan uwa kamarsu tunda sukadaine nata.

Ammy sosai ta lurada rashin walwalarta ta danne tata damuwar cikin kulawa takira sunanta.

Amsawa tayi tareda barin gyaran gadon datakeyi tazo gabanta ta durqusa kanta na qasa. 1

Qare mata kallo tayi taga yanda jikinta ke 'Dan rawa tace,

Rumanah meya faru dake?

Mayarda hawayenta tayi cikin qarfafa muryarta tace,

Bakomai ammy.

Sam batason takurawa rumanah shiyasa ta kyaleta kawai.

Tundaga lokacin sabuwar tsangwana da muguwar tsana tashiga tsakaninta da mamani sbd gani takeyi itace take zugewa nuratu kunne akan tadaina wanka da tsafta sbd kar azabeta.

Duk yanda take daurewa kasawa takeyi saita kwana tana kuka sbd wani irin zagi da gori data sakota gaba dashi akan iyayenta dasuka rasu.

Tun tana boyewa tuni damuwa tabayyana ajikinta sbd ramar datayi.

Sultana duk datana cikin damuwar dawowar maheer dakuma hukuncin sultan Saida damuwar ganin halinda rumanah take ciki tadameta musamman ganin tana ramewa ta daina walwala kwata kwata ta mayarda kanta cikin bayi 'yan uwanta duk wani aikin wahala tanayi Wanda yaqara hargitsata.

Duk yanda sultana tayi da ita tafada meke damunta ta nuna mata ba komai sbd idan tafada tasan azabardasu mamani zasusha zai iya sanadin rayuwarsu kuma bazai tsaya akantaba harda nuratu.

Jakadiya itace ta bincikowa sultana tsaf abinda ke faruwa da rumanah sosai ranta ya 6aci hartayiwa sultan Aiken abinda ke faruwa da rayuwar 'yar amintaccen bawansa daya rasu saikuma ta dakatar sbd tasan hukuncinsa bazaiyi dadiba Dan rayuwarsuce ke lilo a sama kuma barinsu duniya tamkar barin asalin rumanah ne sbd mamani kadaice tasani.


*
Qarfe biyar na yamma jirginsu ya sauka a qasar
Kasancewar ansan bayason rawar jiki da yawa yasa motoci uku kawai sukazo daukarsa da iyalinsa sai khaleefa dasuka zo tare bayan yazo gurinsu daga zuwa weekend yabiyosu suka dawo tare.

Tunda yafito ake zubewa ana gaishesa so daya kawai yadaga kai alamar amsawa hannunsa daya na aljihun wandonsa sai shades dinsa daya gyara.

Suhailat na gefensa ta saci kallonsa zuciyarta na nauyi sbd ganin tsantsar kyawu da kwarjininsa taji kishinsa na taso mata tayi saurin dauke kai tana gyara riqon handbag dinta.

Itada shine a mota 'daya 'dayar motar khaleefa dasu amah sai 'dayar ta guards.

Koda suka isa masarautar tuni duk wani guard da manyan masarautar suka fito tarbonsa.

Cikin girmamawa ake zubewa ana gaidasa harya isa gaban mahaifinsa a hankali yasaki murmushin da iyakacinsa fuskarsata ya gaidasa sultana cikeda girmamawa da kewarsa.

Lokacinda isawarsu maheer ta isowa sultana sakin murmushi tayi cikin tsananin farin ciki kafin tayiwa wanda ya isoda saqon babbar kyautar yana ficewa suhailat dasu amma suka shigo part 'din jakadiya na gaba.

Cikeda girmamawa suhailat taqaraso gaban sultana ta durqusa duk da cikinta daya fara girma ta gaidata.

Cikeda kulawa sultana ta amsa tana kallonsu amah dasuka zauna jikin mahaifiyarsu sbd rashin sabo dasu.

Tana kallon yaran tace,

Jakadiya aje asake dubowa part dinsu idan gyaran ya kammala sbd yaran sun gaji suna buqatar hutawa.

Washe baki Jakadiya tayi cikin girmamawa tace,

Allah yataimaki sarauniyar sarki kuma kakar sark ai tun asubar fari baiwa rumanah ta kammala duk wani gyara da'akasata a part 'din daga part 'din na yarima har part din gimbiya suhailat kuma kuyangi biyar nacan najiransu domin hidimarta data yara kuma anyi musu gargadin ko kallon part din yarima karsuyi bare tunanin shiga koda dasunan wanine ya aikesu.

Murmushi sultana tasaki tareda kallon suhailat tace,

Suhailat kuje kuhuta da yaran sun gaji sosai.

Miqewa tayi daidai fitowar rumanah daga bedroom din ammyn fuskokinsu suka sauka akan na juna daidai kuma shigowar yarima a palon na qurya Wanda qamshinsa yasasu juyawa qofar atare.

Saurin durqusawa rumanah tayi tareda sunkuyar dakanta ta gaidasu atare batareda ta bambamtaba.

Suhailat ce kawai ta amsa cikin wani mugun sanyin jiki daya saukar mata lokaci 'daya.

Ammynsa ya nufa da wani irin murmushi da duk duniya itakadai yakewashi
Cikeda farin ciki da murmushin daya kasa 6oye farin cikinta ta miqe tsaye yana zuwa ya rungumeta.

Cikin rawar jiki rumanah ta fice sbd wani kallo da Jakadiya ta watso mata.

Itama jakadiyar ficewa tayi hakama suhailat sbd tasan qaidane idan zai gana da mahaifiyarsa kowa ficewa yakeyi sbd itakadaice takejin doguwar maganarsa bayan ita ko suhailat datake matarsa baya doguwar magana da ita,su bayi ma ko masu hidimarsa tun tashinsa bayajin yata6a yiwa bawa magana.

Bayan fitarsu Jakadiya takalli rumanah data nufi qofar fita babban palon farko tana qoqarin barin part din gabadaya takira sunanta.

Dawowa tayi tana sunkuyar dakai sbd ko iya dagowa takalli suhailat bata iyayi sbd faduwar gaban datake ji.

Ki kama yaran ki rakasu part dinsu ta huta akula da yaran kar abari su dameta sbd yanayinta.

Jinjina kai tayi cikeda ladabi ta miqe ta 'dauki fammah tareda riqe hannun amah kuma ta 'dauki handbag din suhailat din tabi bayanta.
#Mamuhgee

Post a Comment for "TARAYYA 9-10"