TARAYYA 13-14
page 13
JAN HANKALI
'Yan uwa masu zantuka akan
wannan littafi masu dadi da marasa dadi tareda cin fuska duk inason Ku luradafa
akowane
lokaci mai rubutu idan zai isarda wani saqo na halin rayuwa tofa dolene
saiya fara kawo 6atancinsa da 6arnarsa kafin yazo ga darasin ciki tareda
gyaransa Dan haka please muriqa bari muna ganin inda aka dosa kafin muriqa
fadar ea'ayoyinmu. 5
Komai bakinta baida kuzarin
furtawa koda yanadashi 'din baida ikon furtawa sbd hakan na nufin ruwan sama
zai wanke jininta bayan anraba jijiyoyin dasuka riqe kanta da wuyanta
Saidai bazata iya hana
zuciyarta qunci da radadin zuciya ba sbd sai ayaune ta sake tabbatarda ita
baiwace Mara 'yanci gaba da baya.
Kai tsaye part din gyara taga
sun nufa nan shakkunta da wasi wasinta ya tabbata kenan itace zata zama.....
Kasa qarasawa tayi ta rufe
idanuwanta da qarfi hawaye na 6alle mata.
Daganan kasa daga kafafunta
tayi haka suka jata kamar makauniya suka shiga da ita.
Zaunarda ita sukayi tareda
fara zame mata kayan jikinta har lokacin bata iya 'daga koda Dan yatsanta bare
ta iya 'dago fuskarta.
Shigowa Jakadiya tayi kallo
daya tayi mata tagano tsananin dukan da firgici yayiwa zuciyarta tayi saurin
dauke kai cikin bada umarni tace,
Ku shiryata shirinda har
abada yarima zai riqa tuna qamshi da kyawunta kuma Ku kwantarda hankali kuyishi
anatse.
'Dagowa tayi ahankali takalli
jakadiya daidai lokacin hawayenta suka samu tsinkewa.
Cikin zafi da daure fuska
jakadiya tace,
Karkiyi mana kuka sbd ke
baiwace da akeda ikon kwana dake aduk lokacinda akaso kuma akeda ikon yin yanda
akeso dake Dan haka ki saurara da kyau
Idan kikayi mana garaje anan
wlh abincin kaji za'ayi da jininki. 2
Kalaman Jakadiya sundaki
zuciyarta matuqa ta rufe idano ahankali ta budesu jajir sbd quncin zuciya amma
tabbas babu yanda zatayi ita baiwace kuma yar bayi kamar yanda Jakadiya ta fada
Hannu tasa tashare hawayenta
bata qara motsiba suka fara aikinsu ganin ta zame rigarta tashiga cikin ruwan
madara da lalle dake cikeda bathtub suna zuba qamshi.
Jakadiya Juyawa tayi tafice
takoma part dinda aka warewa baiwarda duk aka zaba akusadana suhailat yake
Saidai baiyi girman nataba.
Duk wani abin jin dadi da
hutawa da more rayuwa ansaka sbd so ake jikinta yariqa murmurewa fatarta tasamu
isashen Hutu da kulawa ta yanda yarima zaiji dadin mu'amala da ita.
A cikin bedroom dinda ke part
din wardrobe din dakin cike take tab da wasu irin kayan barci marasa kyawun
gani basa qirguwa,
Hakama braziers masu daukar
hankali dakuma panties,
STORY CONTINUES BELOW
6angaren turaruka kuwa duk
wani turare mai tsada da qamshi ansiya har gaban mirror bai daukesuba aka zuba
wasu a wardrobe.
Suhailat Jakadiya ta tambaya
duk wani Abu da yarima yafiso ta 6angaren tayar masa da sha'awa zuwaga
auratayya bisaga umarnin sultan,
Cikeda damuwa ta zayyanowa
Jakadiya shinefa aka nemi turaruka masu matuqar tsada da kayan barci.
Saidata tabbatarda gyaran
komai yakammala takoma gurinda ake shirin rumanah din ta tarar sungama shiryata
cikin wata irin doguwar riga maroon colour dataji wasu irin tsadaddun adon
sequence stones sai rawa take tana qyalli.
Mayarda kallonta tayi zuwaga
fuskarta cikin tsananin mamaki da fargabar zallar kyawunda sultanace kawai take
gani da kwatankwacinsa zuciyarta tayi mugun bugawa cikin zuciyarta tace,
Ya Allah kabar wannan fuskar
mai tsananin kyawu da kwarjini ta dauwama ahaka karka wanke kyawun fuskarnan da
jinin bayinka.
Cikeda umarni tace,
Ku rufeta mutafi daga yau
rana bazata qara ta6a fatartaba harsai yarima yagama da ita idan ya gundura da
ita,
Hakama daga yau idan tafara
kwana barayar yarima duk bawa namiji yabari tsautsayi yasashi kallonta anyiwa
zakunan fita yaqi alqawarin namansa.
Sam bata jinsu sbd damuwa da
qunci dayayiwa zuciyarta yawa
Haka aka rufeta aka kamo
hannunta suka jata.
Part din da'aka ware mata aka
kaita har cikin bedroom Jakadiya ta kaita ta janye lullubinta tareda kallonta
fuskar tamke da kakkausar murya tace,
Daga yanxu kinshigo kenan
bazaki sake fitaba sai ranarda kika haihu,
Daga yanxu dokace mai tsanani
babu Wanda yakeda ikon ganinki sai yarima kawai,
Akwai komai na buqata kullum
dare zanxo narakaki barayar yarima harsai ranarda kika samu ciki saiki fara
shiri daga yanxu
Zanje bayan sallar ishai
zandawo nakaiki yarima baya jira Saidai ajirasa.
Ficewa tayi tabi bayanta da
kallo idanuwanta na qoqarin cikowa,
Kukan datake dannewane
tuntuni ya kufce mata ta zame qasa tafara wani irin kuka tana shidewa,
Kuka takeyi sosai tana
qanqame jikinta cikeda tsoro,fargaba da baqin cikin rayuwardata tsinci kanta
dakuma wadda zata fara daga yau bayan anfara kwanciya da ita duk lokacinda
akeso.
Sbd kuka muryarta shaqewa
tayi tashare hawayenta tareda miqewa ta nufi toilet din bedroom din tayo alwala
daqyar take gani sbd kumburin idanuwanta da fuskart.
4 hours later.
Kasa kallon kanta tayi ta
rintse ido jiki amatuqar sanyaye sbd kayanda ke jikinta,
Riqar baccice kalar black
Wanda babu wani sashe na jikinta da rigar ta suturta,
Bra da pant dinda aka sata
sakawa duka suma black ne aka daure dogon gashinta dashima aka gyara hatta
turaren hayaqi mai wani irin qamshi anyiwa gashinta bare jikinta aka daure
tsakiyar kai tareda 'dora mata wata doguwar tiga mai hula data rufe koina
ajikinta aka rufe fuskarta da hular tareda bata wasu takalmi masu laushi ta zufa
anatse Jakadiya tace,
Mutafi,Allah yadatar dake da
samun ciki acikin daren yau.
Jakadiya ce agaba sai ita
abaya bayi kusan guda biyar sun zagayeta suna kama rigarta dake Jan qasa.
Duk takunta 'daya kamar
zuciyarta zata fadone ta buga sbd bugawa da tsananin tsoro da baqin cikin
datake ciki,
Akaro na farko arayuwarta
zata kwana da namiji ba mijintaba kuma duniya da kowa zasusan ana kwana da ita
harta haihu,
Tabbas da ubangiji bai
halastawa uwayen gijiyoyi bayinsuba da ayau tafison a raba kanta da wuyanta
abawa dabbobi jininta data cika wannan umarnin amma sa6a musu da bijire musu
tamkar ta bijirewa ma'aikintane sbd shine ya halasta hakan.
Wani irin tsaro ne na
musamman a part din yarima ga wasu irin hasken fitilu masu kyau da burgewa haka
duk fadin masarautar idan kacire uban gayya sultan part dinsane ne kawai mai
palo hudu kafin akai master bedroom dinsa.
Cak suka tsaya bakin qofar
shiga Jakadiya tajuyo ahankali tayiwa
bayinda ke bayansu kallo daya
Suka ja baya suka tsaya
tareda sunkuyar dakai kafin tajuyo takalli guards din bakin qofar cikin
girmamawa suka wangale qofar ta saka qafa tashiga.
Wani irin numfashi rumanah
tasake sbd kukama yanxu yagaji yagudu yabarta zuciyarta da idanuwanta sun bushe
sauke numfashi kawai take yi akai akai sai jikinta dayake wata irin rawa ko Abu
bazai iya tsayawa ahannuntaba.
Numfashi tasauke ahankali
tareda 'daga qafarta tashiga ahankali tareda rufe ido tabude sbd rayuwarta ta
canxane daga yanxu data sako qafar palon yarima maheer ibn abdulshams abdallah.
Har lokacin fuskarta rufe
takeda hular rigar dake jikinta ahankali take takawa faduwar gabanta da rawar
jikinta na tsananta harsuka isa palon qarshe Wanda dagashi sai bedroom dinsa.
Abakin qofa Jakadiya ta tsaya
tareda juyowa tayi mata kallon mintuna uku kafin tazagaya bayanta ahankali
tasaka hannu ta zame doguwar rigar mai hula
Tasaka hannu ta zare ribbon
dinda aka 'daure gashinta
Gashin ya zubo kan kafadunta
ta juya mata baya cikin sanyin murya tace,
Kishiga ki kwanta a gadon
dake dakin kijira isowarsa.
Shiru tayi tareda Jan
numfashi ahankali tasauke sbd barazanar barin qirjinta dayakeyi.,
Daqyar ta iya daga qafafunta
dake rawa
Rawa hannunta keyi sosai
takasa bude qofar bedroom din
Ganin haka Jakadiya ta matso
tareda dafata cikin kulawa tace,
Karkiyi gardama da qaddara ki
nutsu kibi umarni kiyi biyayya Allah ne kawai yasan dalilin komai dake faruwa.
Bude mata qofar tayi tareda
juyawa sbd batada dama da iko tareda hurumin ganin makwancin yarima.
Akaro na farko da wani yayi
mata magana da sigar lallashi tun bayan data zamto za6abbiya.
Ajiyar zuciya tasauke tareda
saka qafarta cikin dakin Jakadiya ta jawo qofar ta rufe ahankali kafin ta juya
ta fice da doguwar rigar ahannunta.
Baca Juga
Komai na 'dakin white and
golden ne,
Sanyin AC da qamshin dakin da
mai dakin tareda nata data shigo dashi suka taru suka sauyawa dakin yanayin
qamshi mai dadi kasancewar turarukan arabian oud akayi mata amfani dasu sabanin
nasa dasuke designers na turawa.
Daqyar qafafunta suka kaita
bakin couch dake bedroom din ta sulale qasa ta jingina kanta jikin kejerar
tareda rufe idanuwanta.
Qarfe goma da rabi yafito
part din sultana ya nufi part dinsa guards biyu ba bayansa yana isa masu tsaron
qofar sukai saurin budewa yashige.
#mamuhgee
Page 14
Gyara tsayuwa suhailat tayi
daga bakin tafkeken windon bedroom dinta iska na daga curtains suna ta6o har
fuskarta sbd sosai take buqatar iskar sanyin AC bazai mata ba she's feeling
suffocated already. +
Gyara tsayuwarta tayi akaro
na ba adadi tana tsananin buqatar Wanda zai bata kulawa ayanxu sbd wani irin
kishin mijinta dakecin duk wani jini dake yawo acikin jijiyoyin jikinta,
Tana tsananin so da qaunar
maheer,
Maheer na respecting
relationship dinsu sbd 'yaya dakuma zaman fahimta dasukeyi Saidai maheer na
buqatar macen dazaiji dadin yin rayuwarda yakesonyi da ita Wanda bata fatar
yasamu hakan daga wata macen bayan ita,
Yanda labari yazo mata baiwa
rumanah ce aka za6a
Tsoronta na qaruwa aduk
lokacinda ta tuno kamanni da tsarin rumanah din Saidai kuma bata tunanin tafi
bata tausayi sbd sanin waye maheer bazai ta6a iya kwana da wata mace ba
musamman wadda ba matarsaba.
Girgiza kai tayi tana mayarda
dogon gashinta daya barbaje baya ta zauna bakin lafiyyan gadonta tana cewa,
Ya Allah ka yayamin wannan
azabar danakeji cikin raina
Hawayen datake dannewa tun
lokacinda zancen yazo mata suka 6alle ahankali tafara fitarda sautin kuka tana
rufe fuskarta.
Kallo daya yayiwa gefenda
take ya nufi bedroom yashiga ya tube yashiga cikin bathtub yakwanta tareda rufe
ido yana qoqarin samun nutsuwa azuciyarsa har tsawon lokaci kafin yayi wanka
yafito 'daureda towel milk colour yanufi closet yadauki kaya yashirya cikin
kayan bacci ya fesa turare mai sanyin qamshi ya nufi gadonsa ya kwanta hankali
kwance cikin nutsuwa tareda shigewa lallausan duvet ya zira hannu yakashe wuta
ya lumshe ido sbd shi baimasan ta yaya zai saka zancen sultan aransaba bare
harya cika kwata kwata shi ba mutumne mai yawan maganaba idanuwansa da kallonsa
suke bada magana ko umarnin abinda za'ayi kuma shima mutumne dazai iya 6ata
lokacinsa gun abinda baima shafesaba kokuma abinda baidauka da mahimmanciba
shiyasa ko kallo baiwar bata ishesaba idan sungaji da kawota zasu daina Dan
Kansu ko yanxu yabartane aringa kawota sbd abinda sultan yafada akan ammynsa if
not baisan yama za'ai yaringa kwana daki daya da wata macenba bayan ko matarsa
basa kwana daki daya.
Tunda yashigo ta lafe jikin
kujerar tareda tsayarda duk wani motsinta ta sunkuyar dakai numfashinta na
tsananta fita
Tana rabe kanta sunkuye yayi
duk abinda yakeyi ya kwanta tana ji tana jiran taji ya tunkarota amma ko kallon
inda take baiyiba harya kwanta.
Ajiyar zuciya tasauke
ahankali hawaye masu sanyi suka gangaro fararen idanuwanta bada damu data
sharesuba sbd duhune adakin ta kwantarda kanta kan gwiwoyinta hawayenta
nacigaba da gangarowa.
Asubar farko Jakadiya tazo ta
tsaya palon qarshe riqeda doguwar rigar dazata rufe kayan barcin dake jikinta.
Miqewa tsaye tayi jikinta ba
qwari sbd kuka da rashin bacci ta nufi qofa.
Alarm din gefen gadonsa dake
tadashi sallah sbd ba'a shigowa ko palonsa na biyu bare atadashi sallah yasa
yakeda alarm na tadashi sallar asuba kawai.
Ringing alarm din yasa ya
cira hannunsa daqyar cikin bacci ya danna hasken wutar dakin
Tayi saurin juyowa afirgice
sbd takai tsakiyar dakin takusa isa qofa daidai shikuma ya bude oily eyes dake
cikeda bacci suka sauka akanta,
Dishi dishi yake ganinta ya
lumshe idanun yabudesu itakuma hartayi saurin ficewa.
Tana ganin Jakadiya tsaye
wani irin tsoro da mamakinta suka kamata amma saita sunkuyar dakai jakadiya ta
miqa mata rigar ta sanya tareda janyo hular rigar ta rufe fuskarta suka fice.
Kallo daya Jakadiya tayi mata
tasan babu abinda yafaru tsakaninsu tasaki numfashi tana cigaba da tafiya.
Suna fitowa qofar part din
bayinda aka bari da Daren still sunan suka Mara musu baya suka kaita sabon
gurinta suka wuce batareda Jakadiya tace da ita qalaba.
Zamewa tayi qasa bakin gado
ta ta qurawa window ido ta fada dogon tunani fuskarta cikeda damuwarda tayiwa
rayuwarta dabaibayi.
Tadauki lokaci kafin tamiqe
tashiga makeken bathroom din dake dakin tayo alwala ta zame kayan jikinta
tareda mayar musu da kayansu cikin wardrobe tasaka doguwar Riga tayi sallah.
Koda gari ya waye ankawo mata
abinci bata iyacin komaiba hakama da rana ankawo amma takasa koda kallon
abincin.
Arayuwa yanxu batada wani
sauran buri ko mafarki sbd yanxu ta yarda mafarki baya zama gaskia,
Ita ayanxu tamkar wata
dabbace da duk yanda akaso ayi da ita haka za'ayi ta yarda da qaddara tabarwa
Allah alamuranta.
Sultana bawani doguwar
nutsuwa bace acikin zuciyarta sbd har lokacin zuciyarta da gangar jikinta
sunkasa nutsuwa da alamarin tsoro take ciki sosai sbd tana tsoron abinda zai
iya juyewa gaba.
Koda gari ya waye Jakadiya
tasanarda ita babu abinda yafaru tsakaninsu hakanan tasamu kanta da ajiyar
zuciyarta tayi shuru tsawon lokaci kafin takalli jakadiya cikin wata irin murya
tace,
Jakadiya zansa acirewa
rumanah mahaifa sbd fargabata tana yawa Wanda hakan nabani cewar zata iya
haihuwar namiji Wanda nibana mata fatar zamowa MINEELIK-ASSULTANAH kuma kinfi
kowa sanin me hakan ke nufi,
Tayi yarinya da riqe wannan
matsayin sbd bala'i da masifar dake ciki yafi qarfin shekarunta Dan haka abin
zaifi ta6ata.
Shiru Jakadiya tayi kafin
tagyara zama cikin son gyara zancen tace,
Allah yataimaki sultana cire
mata mahaifa tamkar mun qarasa nakasta rayuwartane,
Ke tamkar uwa kike agareta
muyi mata fatar samun 'ya mace ta yanda idan tasamu yantawa akorata nesa da nan
taje tayi aure tafara gina wata sabuwar rayuwar.
Ajiyar zuciya sultana tasaki
tareda lumshe ido tana fatar Allah karya bawa rumanah cikinma kwata kwata ana
dakatarda ita daga zuwa gurinsa ta 'yantata ta turata nesa da nan.
Mamani duk wani baqin ciki da
quncin duniya yataru axuciyarta tun lokacinda aka tafi da rumanah ko ruwa ta
kasa sawa cikinta jitakeyi kamar zuciyar naci da wutane saidai tana addua da
fatar Allah yasa ko cikin 'ya mace karta samu bare na namiji. 1
Sarauniya adama kuwa komawa
tayi tamkar zata mutu sbd baqin ciki acikin dakinta laifi qalilan zakayi tasa
arabaka da lafiyarka sbd ta daura damarar yaqi da duk Wanda zaishiga tsakaninta
da abinda take buri tun tana qanqanuwarta. 1
Kamar jiya qarfe goma aka zo
tafiya da ita bayan anshiryata cikin rigar da gwara ta jiya da ita suka tafi.
Yauma a qofar shiga bedroom
dinsa ta zame rigar sama da ribbon gashinta ya zubo dakanta yau ta bude tashiga
batada kuzari ko kadan ta nufi inda ta ra6e jiya tazauna tareda kwantarda kanta
kan gwiwoyinta ta rufe idanuwanta ahankali.
Kwance yake duk yau ko ina
bai fitaba iyakacinsa palonsa na biyu inda nan yake cin abinci sbd nan ne
dining room dinsa,
Ko suhailat ma so 'daya
takirasa awaya tana qoqarin boye damuwarta da kishinsa tagaidasa tabasa su amah
sukayi masa 'Dan surutunsu Wanda duk sukeyin abinsu iyakacinsa sauraransu suka
gama.
Ammynsa ma yau awaya
yagaidata koina bai fitaba yayi kwanciyarsa.
Tun lokacinda tashigo yaganta
ya rufe idanuwansa ahankali tareda gyara kwanciya sai alokacin ta fahimci yana
'daki sbd duhu bata luraba amma ko motsawa batayiba tayi Shiru ko tunanin bata
iyayi yanxu
Ahaka asuba tayi ta miqe
jikinta amatuqar sake ta fice.
Ahankali kwanakin suka ja
kusan sati biyu ana kaita amma baitaba ko kallon inda takeba. 1
Abu 'dayane daya fara canzawa
shine qamshinta daya kama koina acikin dakinsa har toilet dinsa Wanda hakan ne
kesakashi 6acin rai wani lokacin.
Itakuma ayanxu tarigada tasan
bazai ta6a yin komai da itaba shiyasa kowane irin kaya aka bata bata damuwa
sawa takeyi.
#mamuhgee
Post a Comment for "TARAYYA 13-14"