TARAYYA 5-6
Page 5
Haske writers association💡
+
Saida gari yayi haske sosai
yayi tsit su kutti sukaji tsit suka fito daga ma6oyarsu cikeda tsoro da tashin
hankalin rashin ganin mamani dasu bulama.
Dakatarda sauran yayi ya
ringa bin cikin hakukuwa batareda yana dogon motsiba yaje ya leqo qauyen.
Tsit sai koke koken dake
tashi gawarwaki kuwa gasunan kwance
Jini kuwa tuni yake gudana a
qauyen dabbobinsuma ba'a bariba shiyasa gawarwakin bana mutumba bana dabba ba.
Saki jikinsa yayi sosai
zuciyarsa tayi nauyi yasan tunda su bulama basa taredasu to kuwa sun mutu ko
antafi dasu tafiyarda bar abada ba dawowa,
Tafiyarda gwara mutuwa da ita
sbd a qasqantaccen bawa zaka qare wasuma kafin akai wahala da azaba tareda
yunwa takashesu.
Komawa yayi yana daga qafa da
qyar jiri na dibarsa yakirawo sauran suka shigo qauyen babu Mai nutsuwa nansuka
fara tsallake gawarwaki suna birkito wainda ke kife suna duba sauran iyalan
gidan dabaa ganiba.
Tuni suma wasu daga cikinsu
suka fara ihun kuka sbd ganin mazansu wasu kuwa sauran matansu Dan duka iyalan
gidan baabah din mazansu da matansu tareda 'yayansu su talatin da takwas ne
amma su ashirin da 'daya suka tsira ankashe sha hudu antafi da uku.
Lokacinda suka arba da gawar
baabah nan suka qara saddaqarwa nandai akayi kukan daza'ayi aka dangana
Mazan dasuka saura haka aka
hada gawarwakin sukaje nesa da qauyen suka rufesu suka dawo kowa yacigaba da
rayuwarsa amma kullum cikin fargaba duk da sunsan mutanen bazasu dawo yanxuba
sai zuwa nanda shekaru masu Dan tsawo sun kwatanci qauyen yasake cika sosai an
hayayyafa yara sungirma sunxama samari da yanmata saisu sake dawowa su kwashe.
Tunda dai suna tsoro haka
suka sake sakewa suka cigaba da rayuwa aka nada kutti amatsayin sabon shigaba
Wanda wannan karon shi akan hada mugayen makamai na itace da dafin macizai da
kunamu yamaida hankali sbd yadauki alqawarin angama satarsu ana siyardasu
amatsayin bayi yaqi zasu shirya daga yanxu har ranarda mutanen zasu dawo.
*
Abincin dake cikin jirgin
nasu ne iya sukadai suci su qoshi su kama wainda suka kamo suyita duka ba
ruwansu da namiji ba ruwansu da mace ga yunwa sunbarsu da ita ga qishirwa tuni
wasu daga cikinsu suka fara macewa sbd muguwar tafiyace mai nisa dazata kaisu
nahiyar da
MENEELIK PALACE take
Duk Wanda ya mutu ruwa kawai
suke jefasa ahaka mutanen suka rage da damansu.
Kwanansu goma sha bakwai
ajirgin ruwar kafin suka isa da sassafe.
Cikin mutane sittin da 'yan
kai dasuka kamo mutane arba'in kawai suka iso dasu daga qauyensu bulama sauran
duk sun mutu ahanya.
Bayan 'yan qauyensu bulama dama
sunsato wasu daga gurare da dama.
Kamar kayan wanki haka aka
gargadosu dukkaninsu hannuwansu a 'daure kusan da igiya 'daya sbd ajere suke.
Babu Wanda zaka kalla kaga
kamar baikusa mutuwaba sbd babu Wanda yake iya tsayuwa daidai sbd wahala da
yunwa ga dau'da data canza musu kamanni mamani tuni kuka ya qare zuciya ta qafe
banda tsanarsu asma'u ba abinda takeji sbd ganin sune sanadin zuwanta nan ga
cikin jikinta haryafi na asma'u fitowa.
Bulama duk wuya da azaba
asma'u yakeji itada mamani sbd ganin dukkaninsu juna biyune dasu gasu mata.
Kukansa da fargabarsa karsu
mutu kafin a iso
Basu mutuba amma dai suna
kusa sbd babu mai iya jan qwaqwaran numfashi acikinsu.
A inda suke baza hajar
siyarda bayinsu suka xubesu nansuka rarrabu cikin mutanen dake cikeda kasuwar
Dan kar agansu da yawa dakuma kalar marasa imani agane satosu sukayi ba bayi
bane babbansu tareda manyan yaransa uku
suka isa gurin wani mai siyarda 'yayan itatuwa suka zauna sunacin abinci cikin
farin ciki da nutsuwa.
Asma'u ce ta yanke jiki ta
fadi da 'dayansu ya lura yamiqe da sauri tareda yiwa ogan nuni da sauri shima
ya miqe suka isa gurinta
Bulama tuni yafashe da wani
irin kuka sbd yasan mutuwa tayi.
STORY CONTINUES BELOW
Ta6ata sukayi arikice 'dayan
cikin wani yare mara dadin ji yace,
Tanada rai yunwa da wahalace
muyi saurin bata abinci karta mutu kasan dokace anan duk mai siyarwa da
masarauta bayi yazo dasu suka mutu aka gano wahalace kashesa shima akeyi
musamman mu da satosu mukayi idan sultan dinsu yaji yankamu za'ayi abawa
zakunansa namanmu.
Yawun tsoro ogan ya hadiye
sbd yasan atarihin sarkin fiyedama hakan zai iyayi musu ba abin suqarasa
kashetaba basuda gurin 6oye gawarta ko yarwa batareda angansuba sbd tsantsar
tsaro da qa'idojin da sultan din nahiyar yake bayarwa.
Da ido yayiwa yaran alama
suka kwanceta tareda fakar idanun mutane suka koma can baya da ita suka siyo
mata abinci da ruwa kafin suka kelaya mata ruwa ta bude ido daqyar tanajan
numfashin wahala.
Miqa mata abincin sukayi
hannu na rawa ta kar6a daqyar take saita hannunta yashiga bakinta
Nan take ta cinye abincin
tanashan ruwa sai amai.
Amai tayi sosai wainda yasata
matuqar galabaita nantake zazzabi mai qarfi yafarasa jikinta karkarwa.
Damqo gashinta ogan yayi
6acin rai da takaicin sbd ita rayuwarsu na cikin ha'dari ya bude jajayen
idanuwansa sosai yace,
Idan baki saki jiki kin nuna
lafiyarki kalauba zan yanka mijinki agabanki na qona namansa nazuba tokarsa a
takarda Nayi sigari dashi.
Marinta yayi da qarfi saidata
kifa cikin qasa qasa da murya yace,
Kingane?
Bakinta dake jini ta goge
hannu na rawa ta 'daga kai idanuwanta na qara rinewa da Jan axaba.
Ingiza qeyarta yayi ta fadi
ta lalaba ta miqe da qyar suka koma gurin sauran bayin.
Bulama na hangota gabansa
yayi mummunan faduwa ya sunkuyar dakai tareda sakin sabbin hawayen baqin ciki
sbd hango jini abakinta duk da tana gogewa
Tafiyarma sai ha'da hanya
takeyi a wahalce amma haka take daurewa sbd bin umarninsu karsu kashe bulama.
Sai da rana ta fadi suna aje
cikin rana baci hargwara ruwa yau anbasu ganin mutane akasuwar gashi suna
tsoron akwai 'yan rahoton sultan
yamma tayi sosai
suntabbatarda lokacin sultan ke shaqatawa tareda 'dansa namiji qwaya 'daya tal
a gurin shan iskansa dake cikin masarautarsa kuma alokacin ake bada damar kai
bayi sbd kullum masarautar bata gajiya da siyan bayi sbd girma da ikonta.
Isarsu masarautar yayi daidai
da fitowar yarima MAHEER IBN ABDULSHAMS tareda abokinsa KHALEEFA ABDALLAH 'Dan
wazirin sultan 'yan kimanin shekaru goma sha biyu biyu sun fito daga sassan
hutawar sultan fadawan hudu na bayansu zasu gurin baturen malaminsu dayazo koyardasu karatu.
Kallo 'daya yarima yayiwa
sashen daduke ana gargadasu zuwa sashen koyarda bayi aiki ya 'dauke kai
Khaleefa kuwa tsayawa yayi
yana kallonsu yace,
Idan nagirma zansiyawa ummyna
bayinda harsu mutu suna kularmin da ita.
Tsayawa yarima yayi cak
tareda juyowa jin abinda khaleefa yace yasa yatuno da alqawarin dayayiwa
ammynsa yauda safe cewar zai mata kyautarda mutuwace kawai zata rabata da ita
sai kawai yace atsayar masa sa bayin.
Cikin hanxari aka tsayar dasu
batareda ya kalli gefensuba yace abashi namijin qarshe da macen qarshe ya siya
amafi tsadar farashi.
Jiki na rawa aka janyo bulama
da asma'u dake baya aka kawosu gabansa amma daga nesa sbd warin dau'da.
Still basu yake kalloba sbd
iko da mulki na jinin mahaifinsa dake yawo jikinsa yace,
Akaisu ke6antaccen guri a
tsaftacesu abasu abinci da suturu kyautace zanyiwa mahaifina da ammynah akaro
na farko.
Yana fada ta wuce khaleefa
yabisa yana tunanin siyawa nasa iyayen amma zaibari sai ansake kawo wasu bayin.
Sukuwa dasuka kawo bayin
maqudan kudaden qasar akabasu cikeda jaka suka karbe abinsu suka juya suna isa
kasuwa suka siya guzurin abinci mai yawanda zai ishesu suyi wata qasar safaro
wasu sudawo su sake siyarwa.
Lokacinda aka ke6esu bulama
aka tsaftacesu tsaf aka basu watadaccen abinci mai kyau sukaci nantake suka
'Dan murmure sukai fasali aka fito dasu aka nufi Sashen da sultan da iyalensa
kowa keda part.
Kallonta bulama yayi
idanuwansa taf da halayen tausayin gararinda rayuwarsu da abinda zasu haifa sbd
tasake shiga,
Tasu qaddarar ahaka take daga
'yaya masu gata da dukiya sunkoma wasu mutane masu wani yaren dabam agarinsu
baabah yanxu kuwa zasu zamo wasu bayi masu bauta kuma iyayenda zasu haihu su
haifarwa iyayen gidansu wani bawan ko
wata baiwar.
Itama kallonsa take da ido
jajir sbd sanin daganan rayuwarsu amatsayin ma'aurata ta tsaya takuma wargaje
sbd ikon ganin junaba basudashi yanxu bare kebewa kosunga juna iyakarsu satar
kallo ko ikon magana basudashi.
Ahankali aka jasa aka shige
dashi babban palon sultan cikin tsananin biyayya 'Dan Aiken yarima ya zube
yace,
Allah yaqarawa sultan yawan
rai da lafiya tareda qarfin mulki,
Ga babbar kyauta ta musamman
daga yarima.
Kallon bawan yayi tareda
sakin wani kyakkyawan qasaitaccen murmushi kafin yakalli 'dan aiken yakalli
saikin gida yace,
Sarkin gida gobe tundaga
6ullowar rana aje abudewa wanda yakawo saqonnan na yarima ma'ajiyar abincin
masarautar meenelik yaringa dibar duk abinda yakeso yana kaiwa gidansa harsai
rana ta fadi sanann yanxu yacire rigarsa ya shimfida acika masa itada sutura
mai tsananin tsada kalolo ba iyaka wanda saiya 'dauka daqyar sbd wannan ce
kyautar yarima ta farko agareni Dan haka wannan itace kyauta mafi soyuwa araina
kyautarda mutuwace zata rabani da ita
Aje asanarda yarima kyautarsa
ta faranta ran mahaifinsa ayimasa albishirda zuwa qasarda yakeson bin baturen
malaminsa karatu.
Jin haka Dan aike ya zube
jikinsa ba inda baya rawa sbd farin ciki yadinga rero kirari da godia kafin
yafice daukeda kayanda sarki yace yana nishi daqyar sbd yawansu da nauyinsu.
Kallon bulama sarki yayi
kafin yakalli su waziri cikin farin cikinsa dabai 6oyuba yace,
Wannan kyautace daga yarima
bazaiyi bautaba bawan dazai riqa kula da hutawatane daga yau anadasa.
#mamuhgee
Page 6
Haske writers association💡
+
Sashen sultana zaarah aka
nufa da Asma'u dake waiwayen qofar sashen da aka baro bulama tanaji ajikinta
shikenan sungama rayuwarsa atare saidai jiran lokaci kuma.
Lokacinda aka kaita gaban
sultana aka gabatarda ita amatsayin kyauta daga yarima.
'Dagowa tayi cikin wani irin
farin ciki da murmushi takalli asma'u cikin sanyin lafazi tace,
Allah yayiwa yarima albarka
bisaga wannan kyauta.
Sake kallon asma'u tayi dake
durqushe gabanta tasaki murmushin farin ciki murya a tausashe tacewa
jakadiyarta.,
Akaita abata 'daki sashen
bayi abarta tayi kwana biyu ana koyarda ita aiki kafin tadawo nan tafara
aikinta.
Baca Juga
Angama sultana.
Daki aka bawa asma'u kuma
cikin sa'a aka basu daki daya da mamani suka zauna jigum jigum kowa babu da'din
zuciya kafin aka sake zuwa aka tafi dasu bayin bayi kowannensu yayi wanka aka
rarraba musu uniform dinsu sukabi layi aka basu abinci kowa da 'yar tasarsa
Anan ne asma'u suka hadu da
bulama saidai iyakacinsu kallon juna sbd Layin maza dabam na mata dabam hakama
ga dukkanin alamar tsaro da dokokinda suka lura dasu agurin babu bawanda ya isa
ko yakeda ikon yiwa baiwa magana sbd tsaro dakuma gudun 6arna irinta zina.
Duk wanda aka bawa samun guri
yake a babban filin ya zauna yafara cin abincinsa.
Daga ita harshi ba wanda ya
iyacin abincin sai kallon juna suke daga nesa ba ikon magana har aka gama aka
gargadasu aka rarrabasu zuwa sassan dazasu riqa aiki kullum.
Kwanansu biyu da zuwa jikinsu
ya'dan murmure daga yunwa sbd issashe kuma lafiyayyan abincinda ake basu sbd
Sam babu yunwa ga bayin masarautar.
Asma'u da bulama iyakacinsu
da ganin junansu idan suka hadu gurin cin abinci.
Ganin basuda yunwa kuma babu
azabtarwa a masarautar yasa hankalinsu yadan kwanta suka fara maida hankali ga
ayyukansu damuwar bulama 'dayace cikin jikin asma'u da mamani.
Sosai asma'u ta dangana ta
rungumi rayuwar dasuka tsinci kansu ayanxu tabi uwargijiyarta sbd ganin tana
sake mata ba laifi.
Aiki da bauta takeyiwa
sultana tuquru babu kyuya ga tsafta da tsananin ladabi.
Tunda sultana zaarah ta
lurada cikin jikin asma'u tayi mamaki sosai ziciyarta tashiga wasu wasi takasa
hkr ta tsare asma'un ta tambayeta cikin ladabi kanta na qasa tabata labarinsu
kaf saidai ta boye mata asalinsu da dalilin barowarsu gida.
Cikin tsananin tausayawa
sultana tace,
Karki damu asma'u Allah baya
bacci kuma insha Allah za'a dauki mataki akan masu kamo bayin koba yanxu ba
nasan zasu dawo.
Sosai sultana tasa jakadiya
sassautawa asma'u ayukanta sbd yanayin cikinta daya tsufa kuma sosai sultana
keyiwa asma'u kyautar fresh fruits masu yawa sbd anason mai ciki ta yawaita
cinsu.
Kasancewarsu kusan sa'anni
yasa sosai sultana tasa asma'u tasaki jiki da ita tun tana noqewa harta 'Dan
sake idan tagama ayyukanta zata zauna gaban sultana suna 'Dan ta6a fira wani
zubin harda jakadiya.
Cikinta na isa haihuwa cikin
ikon Allah suka haihu rana 'daya da mamani dake aiki sassan sarauniya adama.
Dukkaninsu 'yaya mata suka
Haifa sultana dakanta tasa akai mata iso ga sarki tasanar dashi matar mafi
soyuwar bawansa ta haihu tasamu mace.
Shiru yayi cikin jinjina
alamarin bayi kuma da haihuwa amma saiya share sbd bayason sanin komai yanxu
tunda anriga anyi haihuwar yabawa bulama dama yaje yaga yarsa yayi mata huduba.
Koda bulama yaga 'yarsa
hawaye 6alle masa sukayi sbd tarigada tafado daga bayi irinsu shikenan ita
rayuwarda Allah yaxabarmata kenan.
Huduba yayi mata kafin ya
'durqusa har qasa yamiqawa sultana cikin girmamawa yace,
STORY CONTINUES BELOW
Kece kika cancanta daki za6a
mata suna.
Yarima daya fito sashen
sultan yaqaraso sashen sultana yana shigowa yaji zancensu kai tsaye yakalli
yarinyar yakalli sultana yace,
Asaka mata UMMU-RUMANA..
Kallonsa sultana zaarah tayi
fuskarta daukeda murmushi tace,
Mahaifiya kayiwa takwara
maheer.
Mayar mata da murmushin kawai
yayi tareda jinjina kai ahankali ya shafo fuskar jaririyar yace,
Allah ya raya ummu-rumanah.
Yana gama fadar haka ya
wucewarsa sultana takalli bulama tace,
Allah yaraya ummu-rumanah.
Amin sukace cikin farin ciki
da godiya harda jakadiya.
Yarinyar mamani ma shine yayi
mata huduba mamani tasawa 'yarta suna NURATU.
Tunda asma'u ta haihu
hankalinsu yasake kwantawa itada bulama tuni suka maida hankali ga bautarsu
Idan zatazo sashen sultana
adaki suke barin 'yayansu itada mamani daga baya sultana tace tariqa zuwa da
ummu-rumanah
Sosai lokaci yaja tuni
ummu-rumanah ta fara girma
Daga ummanta sai sultana da
jakadiya tafi sabo dasu sai nuratu dasuke wasa tare a can sashen bayi
mahaifinta ta saba dashi sbd ana 'Dan basa damar zuwa ganinta itada ummanta
wasu lokutan da haka rayuwa tayi nisa sosai.
Sultan an wayi gari baida
amintaccen bawa kamar bulama sbd takai ko fita za'ayi wata qasar da amintaccen
bawansa bulama yake zuwa gashi da tsananin biyayya da taka tsantsan sbd sultan
nada qarfin mulki da iko sosai da wasu irin dokoki.
Ummu-rumanah nada shekara
goma sha hudu cif aduniya Allah yayiwa bulama rasuwa sanadiyar ciwon ciki.
Anji mutuwarsa duk da
kasancewarsa bawa hakadai asma'u da rumanah suka dangana da rashinsa saidai
rasuwar ta ta6a asma'u sosai,
Ta rasa lafiya da nutsuwar
zuciya tun tana daurewa tuni ciwo ya kwantarda ita hakan tasa rumanah karbar
ragamar aikinta a sashen sultana.
Kwanciyar hankali tuni ta
qauracewa rumanah ganin babu uba ga uwarta na jinya sosai
Sultana ma tana cikin damuwar
ciwon asma'un Dana matuqar tausayin rumanah sbd jin asma'u takeyi tamkar 'yar
uwarta ta jini rumanah kuwa dama amatsayin 'ya take agareta sbd tun tana shan
nono tayi sabo da yarinyar.
Anyi maganin har andanga
anbarwa Allah ikonsa amma jikin yaqi sauqi ganin haka sultana ta 'yantata nanda
nan aka shelar an 'yanta baiwa asma'u.
Rumanah ga abin farin ciki
amma Sam batajinsa ita kadai tasan yanda takejin zuciyarta ganin mahaifiyarta
sai qarayin nisa takeyi.
Cikin dare Allah yakarbi
rayuwar asma'u tabar 'yarta cikin wannan duniya mai ababen tsoro. 1
Rumanah kam zuciyarta bushewa
tayi sosai tabawa kowa mamakin rashin kukanta har aka kai asma'un aka dawo.
Sultana zaarah lokacinda ta
aika kiran rumanah tana zuwa ta durqusa gabanta kallon rumanar tayi batasan
lokacinda hawaye suka taru a idonta ba tayi sauri shigewa qurya sai alokacin
rumanah tasaki wani kuka daya tokare qirjinta ta zube agurin tanayinsa jakadiya
tayi saurin jawota jikinta tana lallashinta.
Andauki tsayin lokaci kafin
rumanah tasaba da rayuwa ba iyayenta ga 6angare guda mamani Sam bata qaunarta
bare ta rage maraicin rashin uwa sbd da mamani da nuratu take kallo amatsayin
jininta.
Sultana zaarah kuwa sosai
take nuna qaunarta rumanah wanda itama rumanah tana qaunarta sbd ita take gani
tana rage kewar ummanta.
Da haka rayuwa taja harsuka
qara zama 'yan mata ta maida hankali sosai ga bautawa ummy kamar yanda take
kiran sultana zaarah.
********
ABDULSHAMS IBN ABDALLAH MUHD
shine sultan na yanxu dake mulki a meneelik wani yanki na babban birnin ethopia
kamar yanda kakanni da iyaye suka bar masa, 6
Mulkinsu wani irin tsauri da
zafi dashi ga wani irin qabilanci dasukedashi sbd Sam basa bayi ko borori da
'yan qasarsu saida akawo musu na wata qasar su siya shiyasa yawanci bayin
masarautar daga qasashe dabam dabam suke mafi yawansu Nigeria sbd rashin tsaro
na zama Dan qasa da 'yan Nigeria sukedashi.
Tun lokacin mulkin kakanni a
wannan zuriar ta ABDALLAH muhd basuda yawan 'yaya maza saidai mata wanda hakan
yayita kawo barazana ga barin sarauta da mulki daga zuriar.
Duk wani kalar arziki na
duniya Allah ya hore musu shi kobana sarautataba amma banda yaya maza daqyar
cikin yardar Allah suka samu namiji 'daya cikin 'yaya mata goma sha biyu da
sarkin yakedasu daga matansa uku.
ABDULSHAMS shine yazamto
namiji daya kuma ya gadi sarautar bayan rasuwar mahaifinsa ABDALLAH. 1
Tun yana yaro qanqani
mahaifinsa yake cusa masa qaidoji da hukunce hukunce masu zafi sbd karsuyi sake
sarauta tabar gidansu matuqar ba magaji sbd arubuce yaje a aje duk ranarda suka
wayi gari sarki ya mutu ba magani to masarautar da duk wanda ke cikinta zasu
zamo qarqashin ikon masarautar kilaimee tamkar bayi dundaga kan matan sarki da
'yayansa har bayinsu sbd wata tsohuwar muguwar gabace atsakanin masarautun.
Hakan yasa duk wanda yayi
mulki basa tsayawa kan matansu da qwarqwarori suke qarawa amma duk da haka
sunada qarancin maza sosai sai arzikin 'yaya mata.
Yanxu lokacin mulkin sultan
abdulshams yanada matuqar zafi da tsanani amma duk da haka baiyi na iyayensa da
sauran sarukan dasuka gabata.
Zafinsa yasa dukkanin fadin
qasar da zagayen ake tsoron hukuncinsa shiyasa kowa a ankare yake ba'a take
dokar sultan ko acikin matansa bare 'yaya kafinma akai ga 'yan qasa da bayi.
Matansa biyu sultana zaarah
'yar sultan jalaludden sarkin Libya.
'Sai sarauniya adama 'yar tsohon
wazirin mahaifinsa. 3
'Yayansa goma cif duka mata
sai yarima tak shine namiji.
Sultana zaarah keda yara hudu
Amatullah,hindu dakuma
maryamah duk suna aure,
Amatullah da maryamah a Libya
qasar mahaifiyarsu suke aure sai Hindu dake aure Kuwait,yarima shine qaraminsu.
'Yayan sarauniya adama shida
dukkaninsu mata kuma duka sunyi aure sai autarta najwah.
Duk qwarqwarori da sultan
yake kwana dasu Allah baiba ko 'daya daga cikinsu cikiba bare tahaifi 'da
namiji
Hakan yake tsananin 'daga
hankalinsa ga tsufa yafara kamasa yarima yafito fili yafada bayada ra'ayin
mulki ko wani Abu daya danganci sarauta
Kwata kwata rayuwarsa bata
yanayi damai sarauta sbd tunda yagama primary aka kawosa Greece karatu harya
gama yacigaba da degree dinsa a los Angeles kafin yayi masters duk akan
doctoring shiyasa rayuwarsa kwata kwata ta turawa ce,
Daga nan yadawo da rayuwarsa
a Georgia inda Yayi settling yafara aikinsa anan.
Sam bai cika zuwa gidaba sbd
yanayin aikinsa dakuma rashin son rayuwar masarautarsu koina mutane,koina bayi
Sam shi bayason gurunda zai kasance da mutane sosai yanason free life bayason
takura shiyasa yake ganin zama acan gida is a punishment.
#mamuhgee.
Post a Comment for "TARAYYA 5-6"