TARAYYA 11-12
Page 11
Haske writers association💡
Suna isa part din na suhailat
dake kallon na yarima itace tayi saurin matsawa ta bude mata qofar tashiga.
Babban parlour ne daya tsaru
sosai da uwayen nairorin da aka zuba masa gurin tsarasa,
Royal cushions ne purple and
golden komai na palon qyallin adon kalar golden din.
Duk haduwa da tsaruwar part
din sultana saidataga wannan ma na suhailat yayi kyau sbd ita atunaninta
baza'ataba samun part dinda yakai na sultana tsaruwa da kyauba saigashi na
suhailat dinma ya tsaru kamarna sultana duk da tanajin labarin haduwa da
tsaruwar part din adama kasancewarta itama 'yar adoce sosai.
Kuyanginda aka turowa
suhailat 'din sukayi saurin shiga taitayinsu suna mata barka da shigowa.
Hannu kawai ta 'daga musu
tareda kallon rumanah tana nuna mata 'dakinsu amah tace,
Kije kiyi musu wanka da ruwa
marasa sanyi kuma bamasu zafi sosaiba ki shiryasu sai abarsu su huta kafin
anjima suci abinci.
Tana gama fadar haka tamiqa
mata hannu ta bata handbag dinta ta shige bedroom dinta.
Dakinsu ta nufa dasu tayi
musu wanka ta shiryasu harzata fito suka maqale mata takaisu gurin mum dinsu.
Bata saba da yaraba batama
ta6a zama da yaraba tun tasowarta
Daqyar tasamu ta lallabasu ta
fito.
Tana fitowa part din tasaki
ajiyar zuciya sbd gabadaya a takure take sbd tsoro da gudun aikata laifi.
Kodata koma part din sultana
a palon farko ta ra6e sbd ganin alamun har lokacin yarima naciki.
Gab da magrib yafito tayi
saurin zubewa amma ko lurada akwai mutum shibaiyiba ya wuce yabar part din da
qamshinsa.
Sum sum ta nufi palon ciki ta
tararda ammyn zaune har lokacin ta durqusa cikin girmamawa tace,
Ammy a table za'a jera abinci
kokuwa anan?
Murmushi tayi cikeda farin
ciki tace,
Ajera a table kuma ayiwa
maheer honey pancakes da sugarless drink sbd bayacin abinci mai nauyi musamman
yanxu da daddare
And kihada masa fruitsalad
with less apple sai kikai masa part dinsa kisaka a fridge din Palo nasan idan
yafito sallar magrib bazai komaba sai dare.
Wani irin yawu ta hadiye na
muguwar faduwar data sameta jin inda aka aiketa itadai batason tayi laifi komai
qanqantarsa.
Ficewa tayi tafara kawo
abinci a second palo tana jerawa a dining jikinta amatuqar sanyaye.
Honey Pancakes din tayi
tareda kawowa dining daidai lokacin aka shiga sallar isha takoma tahado fruit
salad ta zuba a glassbowl ta 'daura a tray ta nufi part 'dinsa qafafuwanta har
wani hardewa sukeyi sbd yanda jikinta ke rawa.
Tana isa kallo 'daya tayiwa
guards din qofar ta juya tayi part din suhailat ta saka cikin fridge tareda
sanarda kuyangin palon su sanarda suhailat ankawo fruit salad din yarima.
Kodata koma sallah taje tayo
tareda komawa part din sultana tana saka kai da sallama dashi idanuwanta suka
faracin karo yana cin pancakes din yana yiwa mahaifiyarsa murmushi.
Juyawa tayi da sauri sultana
ta lurada ita amma sanin bayi basa zuwa idan yana guri musamman idan abinci
yakeci kozaici yasa tabarta takomawarta.
Sai qarfe tara yabar part din
sultana yanufi nasa
Yana zuwa ya tu6e yashiga
bathroom dinsa da aka cika masa bathtub da ruwa masu matuqar qamshi da 'dumi ya
lumshe fararen oily eyes dinsa tareda kwantawa yana sake jin nutsuwa.
Allah yayisa mutum mai
tsananin son rayuwa musamman tajin dadi saidai suhailat bata cika son irin
wannan rayuwarba itakuma sbd sunada abubuwan dasuka banbanta ra'ayoyinsu saidai
suna qoqarin ganin hakan baitaba rayuwar aurensuba.
STORY CONTINUES BELOW
Sam bayason wanka a shower
saidai a bathtub sbd yafison koyaushe yakwanta cikin ruwa tsawon mintuna goma
sha biyar zuwa ashirin kafin yayi wanka,
Itakuma suhailat Sam batason
wanka a bathtub saidai shower shiyasa haryau baisamu irin rayuwarda yakesoba
sbd basu ta6a wanka atareba
Kwata kwata batama shiga
toilet din bedroom 'dinsa sbd 'duk girma da fadin toilet dinsa bayason ganin
ruwa ko yayane a qasan toilet dinsa itakuma idan tashiga toilet saita gama jiqa
koina take fitowa.
A bangaren rayuwar aurensu
kuwa Sam bata iya kwana a 'dakinsa sbd komai dare idan suka gama abinda sukeyi
a bedroom dinta take kwana sbd daga ita harshi kowa yafison ya kwana shikadai
akan gado shiyasa yawanci zata raba dare a bedroom dinsa susha love dinsu kafin
tayo dakinta.
Bayan sun jima da aure yazo
yasaba baya iya kwana sai ajikinta amma itakuma dukkanin cikin datakeyi bayason
kwanciya dashi hakadai yama cirewa ransa kota haihu basa kwana tare saidai su
raba dare tare.
Bude idanuwansa yayi ahankali
tareda kallon ruwan sbd qamshin dasuke fitarwa yakalli gaban mirror din cikin
toilet din yagansu kaloli kusan guda goma masu kalar qamshi dabam dabam.
Saidayayi mintuna kwance
cikin ruwan kafin yayi wanka ya fito daureda brown towel sabo qal ya tsaya
gaban mirror tareda goge jikinsa ya fesa Hugo black men's spray tareda gyara
sumarsa da lafiyayyar qasumbar dake kwance a farar fatarsa fuskarsa ya fesa
mouth spray mint flavour ya nufi closet ya dauko kayan bacci white colour
yasaka tareda nufar makeken lafiyayyan royal bed dinsa dayake gyare da komai
white da kusan eight pillows masu laushi.
Wayoyinsa ya kashe tareda
ajesu a bedside drawer ya kashe wuta yabar bedside lamps masu duhun haske.
Kwashe komai tayi tasake
gyare palon tayiwa ammy Saida safe ta nufi gefensu na bayi anatse.
Tana zuwa babu kowa a dakin
ta kwanta bayan tacire uniform dinta tasaka tsohon uniform dinta sbd sune
tamayar na bacci dama idan akaga uniform dinka sun mutu ana baka wani.
Kodasu mamani suka shigo
idonta biyu amma ta lafe tanaji mamani nata fada tana zaginta
Ta share hawayenta tareda
rufe ido tana danne kukanta.
Tundaga ranar kusan itace
take wahala da suhailat da 'yaranta sbd kullum ita sultana ke aikawa tana yiwa
yaran wanka takuma kaimusu abinci ta Jere a dining safe rana dare saiya zamto
ayyuka sunmata yawa danma babu laifi suhailat na sakar mata fuska sosai hakama
yaran ba laifi suna yarda da ita ba kamar kowaba sbd kullum ita ake sawa ta
daukosu takawo gurin sultana su yini kokuma gurin sarauniya adama.
*
Sati 'daya da zuwansu yarima
yana zaune gaban sultan sbd kiransa dayayi cikeda girmamawa yake sauraren
mahaifin nasa.
Cikin iko da umarni sultan
yace,
Aure zaka qara maheer ibn
abdulshams.
Shiru yarima yayi cikin
tsananin mamaki tsawon lokaci harsaida mataimakin sultan yasake maimaita masa
kafin ya 'dago manyan oily eyes dinsa yakalli haris abdallah mahaifin khaleefa
kuma mataimakin sultan yace,
Ina bawa sultan da
mataimakinsa hkr sbd babu sha'awa ko burin qara aure arayuwata.
Wani shu'umin murmushi sultan
yasaki tareda sake maimaita zancensa.
Shima maheer cikin girmamawa
yasake maimaita amsarsa.
Kallonsa sultan yayi yasan
sarai waye maheer saidai bazai barsaba zaiyi amfani da qarfin ikon mulkinsa
dakuma ikonsa na mahaifinsa akansa.
Batareda yakallesaba yace,
Maheer ibn abdulshams zabin
farkone nabaka na qarin aurenka.
Rufe idanuwansa yayi ahankali
yana danne 6acin ransa yace,
Ina qara bawa sultan hakuri
akan wannan buqatar tasa sbd idan nayi auren bansan yaya zan iya kwatanta
adalcin kulada mata biyu ba.
Murmushi sultan yasake saki
tareda kallon sarkin gida dake tsaye da sauri yafice ya nufi hanyar part din
sultana.
Mintuna qalilan akayiwa
Jakadiya iso tashigo tareda zubewa qasa tana gaisuwa.
Cikin mulki da nuna ikonsa
yace,
Jakadiya aje yau awanke masa
baiwar datafi kowace kyau 'daya cikin biyar 'din danace agyara akai masa daga
yau aringa kaita kowane dare harsaitayi ciki,
Kuma daga yau an dakatarda
matarsa zuwa gurinsa sai baiwarsa tayi ciki
Idan ya kaucewa umarnina
Jakadiya ki sanarda sultana zaarah na sauketa daga matsayinta na sultana kiyiwa
adama albishir da samun sabon matsayi. 1
Yana fada ya miqe nan
dukkanin su haris abdallah suka miqe yashigewarsa palonsa na musamman.
Cikeda girmamawa Jakadiya
tace,
Angama sarki mai adalci.
Miqewa tayi da sauri ta fice
sbd ganin halinda yarima yashiga sbd tsananin 6acin ransa da baqin cikinsa daya
kasa 6oyuwa.
Miqewa yayi yafice kai tsaye
part dinsa ya nufa tareda bawa guards din qofar part dinsa gargadin duk Wanda
yayi motsi mai qarfinda harzai shigo part dinsa yadamesa arufesa tsawon shekara
guda.
Jin haka yasa akayi sanarwa
tuni kowa ya nutsu yashiga taitayinsa.
Jakadiya kuwa cikin qanqanin
lokaci tasa aka tara dukkanin wata baiwa dake masarautar mai shakatun dabasu
wuce sha takwas,sha tara zuwa ashirin da uku da hudu.
Koda aka kira duk suka
halarta banda rumanah dake bedroom din sultana tana jera kaya acikin closet.
Duk iya damuwa da rashin
mafita sultana naciki sbd tun binciken farko Jakadiya tace bataga wadda ta
daceba gashi sultan yace yau.
Zaune kawai take amma
hankalinta nakan halinda maheer yake ciki yanxu.
#mamuhgee
Page 12
Akan nuratu jakadiya ta
tsayarda idanuwanta tana nazarinta sbd zama da rumanah yasa itama takeda
nutsuwa daidai gwargwado...... +
Tsaya to idan zama da rumanah
yasa takeda nutsuwa ba kamar mahaifiyarba me zai hana su dauki Mai nutsuwar
gabaki daya.
RUMANAH"""shine
sunan dayazo ranta atake tasaki murmushi cikin farin ciki sbd tasan sultana
idan taji ta inda jikokinta zasu fito bazataji damuwaba.
Sallamarsu tayi tareda juyawa
kar tsaye ta nufi hanyar zuwa gurin sultan.
Tana zuwa akai mata iso
cikeda girmamawa ta zube gabansa cikin bayyanarda farin cikinta tace,
Allah yataimakeka ansamu
baiwa mafi nutsuwa da kyawu acikin bayin masarautar mineelik,
Baiwa ummu-rumanah 'yar
tsohon aminyaccen bawanka bulama.
Shima wani irin murmushi
yasaki tareda kallon Jakadiya yace,
Allah yayi saina hada zuria
da bawa mafi soyuwa agareni
Aje ashiryata yau za'a fara
rakata turakar yarima
Bulama Allah yaji qanka da
rahamarsa,
Baca Juga
Jakadiya kije idan ta haifi
namiji ina miki albishir da akwatin dalolin amurka. 9
Miqewa tayi tana zuba godia
da farin ciki tareda adduar asamu biyan buqata.
Lokacinda ta isa gurin
sultana ta zube gabanta ta zauna cikin farin ciki tace,
Allah yataimakeki Ansamu
wadda nasan zakifi kowa farin cikin fitowar jikokinki ta tsatsonta.
Kallon rashin fahimta sultana
tayi mata cikin qoqarin Kore damuwarta sbd jin ansamu mafita.
Baiwa ummu-rumanah ta wajenki
itace nakega tafi cancanta da'a za6a sbd ganin nutsuwa dakuma shakuwar dake
tsakani.
Wani irin kallo sultana ta
jefi Jakadiya dashi cikin mamaki da takaici.
Datasan rainon datakewa
rumanah na idan tasamu sanin asalintane daga mamani ta 'yantata danta koma gida
cikin yan uwanta ne.
Dauke kai tayi cikin bada
umarni tace,
Kije kinema masa wata banda
rumanah.
Kallonta Jakadiya tayi da
sauri cikin mamaki tace,
Allah yataimaki sultana naga
tafi kowace baiwa cancanta tazamo uwar jikinki koba komai tunda 'danki ne ba
wani akace akaiwaba.
Girgiza kai tayi tareda
juyawa takalli qofar bedroom dinta da rumanah ta fito cikin nutsuwa daukeda
zanin gadon data cire ta fice tana mamakin kallonda suka biyota dashi kamar ta
canza.
Laundry din masarauta ta nufa
takai kayan ta karbo wasu sabbin zannuwan gado masu laushi farare qal tana
fitowa mamani ta shigo part din laundry din daukeda kayan wankin adama itama
takawo.
Saurin matsawa tayi tana
cewa,
Mamani sannu da aiki.
Tsayawa mamanin tayi tareda
kasa danne baqin cikinta da takaicinta akan rumanah din sbd ko yauma dai ba'a
zabi nuratu ba sbd ko wanka batayiba.
Cikin takaici tace,
Rumanah tunda kika zuga
nuratu Dan karmu samu farin ciki kema bazaki ta6a farin cikiba arayuwa,
Keda iyayenki kunzamarmin
muguwar qaddara sun mutu sunbarmana masifa gashinan kin shiga tsakanina da yata
kin shiga tsakaninmu da farin cikinmu....
Rintse idanuwanta dasukai
jajir tayi Cikin dannewa tace,
Kiyi hkr mamani bawa baya
wuce qaddararsa ko.......
Shaqota tayi cikin tsananin
baqin ciki jitakeyi kamar ta cire takaicin iyayenta na shekara da shekaru
akanta ta huta.
Hawayen wahala rumanah ke
fitarwa sosai batareda tayi yunqurin kwatar kantaba.
STORY CONTINUES BELOW
Motsi yasa mamani sakinta ta
kwashi kayanta ta wuce zuciyarta na tafarfasa.
Kukan datake riqewa tana
shiga bedroom din sultana tasakesa zuciyarta na quna,
Sosai take kuka tana shesheka
sbd yanxune take 'dandana maraici da quncin dake cikinsa,
Wannan karon harcikin ranta
takejin qunci da radadin abinda mamani ke mata shiyasa takasa danne kukanta duk
yanda taso.
Sheshekar kukane yadauki
hankalin sultana da jakadiya cikin sanyin jiki suka dubi qofar cikeda tausayawa
Jakadiya tace,
Sultana amincewa kibada
rumanah shine zai sanyaya mata qunci da damuwar datake ciki na uwar riqonta sbd natabbarda shine zai
nesantata daga uquba da tsangwamarta.,
Koba komai wannan itace iya
mafi girman soyayyar dazakiyi mata ta amince mata ta zama mai kawarwa da 'danki
sha'awarsa.,
Har abada rumanah bazata ta6a
wulaqantaba idan ta hada shimfida da yarima koda kuwa bata haihuba,
Ki qara dubawa sultana.
Shiru tayi tareda rintse
idanuwanta cikin rashin madafa da shawara sbd bata fatar rumanah tazama
baiwarda za'a riqa kwana da ita tana haihuwa ana kar6e 'yayan daga qarshe kuma
asallameta tayi nesa da qasar bazata qara kusanto 'yayantaba.
Wani 6angaren kuma batada
wata mafita ko ba6in daya wuce rumanah din Dan itace taga tafi cancanta da
jikokinta su fito daga gareta koba namiji bane itadai gwara ace rumanah 'dince
ta haifar matasu ba wata baiwarba
Saidai zuciyarta na ganin
kamar bata yiwa asma'unta adalcin zaman amincin dasukayiba
Hakama zuciyarta na hango
mata wani irin rikici da tashin hankali agaba akan hakan.
Miqewa tayi cikeda damuwa da
fargabar rashin madafa,
Masarautarsu has been cursed
tun shekara da shekarun dasuka shude,
Duk wani abin alkhairi baya
'dorewa a masarautar,
Sarakunansu hankalinsu da
tausayinsu tareda imaninsu yana gushewa daga lokacinda suka hau kujerar mulkin
basa da hukunci saina yankewa duk Wanda yayi laifi kisa,
Hannuwa da qafafun
sarakunansu na jiqene da jinin mutane,
Sarakunansu are posses,
Duk Wanda ya alaqantu da
kujerar mulkin mineelik sai cursed din yashafesa sbd mugun abin daga kujerar
yake.,
Jakadiya kinsan me zamantowa
uwa ga magajin masarautar nan yake nufi,
Maheer yaqi karbar sunan
magajin sarkine sbd kubutardani daga zamtowa cikin makusanta kujerar mulkin,
Yaqi karbar sunan ne sbd
kubutarda kansa daga jiqa likkafaninsa da kabarinsa da jinin bayin Allah, 5
Kinfi kowa sanin tarihin
masarautar nan da abinda ke bibiyarta shine zamu 'dauko yarinyar da batada
hakkin komai musakata da abinda zata Haifa?
Rumanah kwaqwalwarta bazata
iya daukar masifun dazasu biyo bayan zamtowarta mahaifiyar magajin masarautar
nanba,
Idan muka sakata cikin wannan
masifar muka jiqa hannuwanta da jinin mutane bamuyi mata adalciba,
'Dana yakubatardani da kansa
daga wannan masifar shine zamu saka yarinya aciki bayan batasan me hakan ke
nufiba.,
Sultan alamarin yariga ya
dade shigarsa ayanxu koda 'Dan cikinsa baya tunani biyu kafin ya yanke musu
hukuncin kisa,
Masifar tariga tashiga
jikinsa bayaji baya gani rashin bin kowane irin umarninsa daidai yakeda fitar
ranka....
Cikeda sanyin jiki Jakadiya
tace,
Hakan zaki tuna kiyi hkr
kibada rumanah idan ta haihu mu tseratarda ita ta hanyar turata nesa inda har
abada bazata sake kawo kanta nanba wannan shixai mata Katanga daga zamowa MINEELIK-ASSULTANAH
TA BIYU.
Shiru sultana tayi cikeda
tsananin tsoro da fargabar abinda suke shirin yi,.
Fitowar rumanah daga bedroom
dinta yasasu juyawa qofar.
Sunkuyar dakanta tayi sbd
fuskarta datayi jajir sbd kukandatayi.
Wani irin mugun sabon
tausayinta yashiga sultana batasan lokacinda tajawota jikinta ta rumgumeba
cikin wata irin sanyin murya tace,
Asma'u ki yafemin.
Rumanah kema karki qullaceni.
Batamaji abinda ammyn
kefadaba sbd kukanta daya dawo sabo tuntuni take Neman Wanda zai rarrasheta
koda tsuntsune sbd mawuyacin halinda take ciki.
Jakadiya ma cikin tsananin
tausayin rumanah din can qasan maqoshi tace,
Ki gafarceni rumanah amma
rayuwarki ta birkice daga lokacinda kika haifi 'da namiji sbd qaunar danake
yimiki ina miki fatar samun 'ya mace sbd kubuta daga muguwar tsinuwar dakebin
makusanta kujerar masarautar mineelik.
Saida rumanah tayi kuka sosai
Wanda hakanan yake zuwa takasa tsaidasa saidatayisa sosai kafin sultana ta
'dagota tareda kallon fuskarta tana maida hawayenta takalli jakadiya tareda
'daga mata kai ahankali.
Tasaki rumanah tayi bedroom
dinta tanaji ajikinta haqqin rumanah bazai taba barinsuba.
Jiki amatuqar sanyaye ta juya
ta fice Jakadiya tabita da kallon tausayi.
Tana zuwa dakinsu ta zauna
bakin katifarta tareda rafka tagumi ta fada tunani.
Nuratu ce tashigo dakin tayi
saurin isa gurin rumanah din kawai ta rungumeta Tana cewa,
Rumanah karki karaya kisake
jajircewa kina haquri da mamani zata daina wata rana ko ance tayi bazatayiba. 1
Murmushi mai ciwo tasaki
tareda kallon nuratu tace,
Mamani uwace banta6a riqeta
arainaba.
Zuciyarki nada kyau rumanah
Allah yabarki ahaka.
Murmushi tayi tace,
Ummana,abbanah da ammy
bayansu kece mutum 'daya dana sani mai zuciya mai kyau Dan haka keda ammy Allah
kuma yabarku ahaka.
Dariya sukayi suna qoqarin
manta damuwar abinda yafaru.
Ahankali nuratu takalleta
tace,
Rumanah kintuna lokacinda
muke wasar riqe riqen gudu da ruwa a cup a dakin nan?
Murmushi tayi tareda kallon
nuratu sbd wannan wasar itace abinda bazata ta6a mantawaba a quriciyarta,
Itace abinda nuratu ke tuna
mata tasakata nishadi amma yau saitaji jikinta yayi sanyi tace,
Meyasa kika tuna wannan
yanxu?
Haka kawai na tuna sbd
bansaniba kobazamu sake samun damar tunawaba irin haka cikin jindadi.
Qurawa nuratu ido tayi zatayi
magana aka shigo dakin.
Kallon qofa sukayi sukaga
bayi kusan biyar atsaye saiga Jakadiya tashigo fuskarta a tamke babu alamar
wasa takalli rumanah ta 'dauke kai ta juya Tana cewa,
Ku taho da ita zuwa part din
gyara yanxunan.
Tana fada ta fice sbd kar tausayin
rumanah yashigeta.
Kallon juna sukayi itada
nuratu irin kallon da nuratu ke mata na tsananin tausayi yasa tayi saurin
kallon qofar da jakadiya ta fita tayi kafin tasake kallon nuratu da tuni
hawayen rabuwarsu ya gangaro mata.
Matsowa sukayi suka kama
hannunta ko qwaqwaran motsi bata iyayi suka fice da ita.
#mamuhgee
Post a Comment for "TARAYYA 11-12"