TARAYYA 39-40
TARAYYA
39
not edited
Kallonta
yayi da idanuwansa dasukai laushi sbd damuwa
Ahankali ya
qarasa bakin gadon
Negasi ya
bude baki zai
dakatarda dashi ya daga masa hannu ahankali cikin mulki da bada
umarni ya bude baki yace,
Ina buqatar
ganawa da ita.
Cikin
girmamawa suka fara ficewa ammy dake kallon rumanah kamar idanuwanta zasu fado
zuciyarta na bugawa da sauri gabaki daya bata cikin nutsuwa so take taji
rumanah tayi magana tasan halinda take ciki saidai rumanar idanuwanta a rintse
suke
Kowa ya fice
sai ammy da suhailat dake bayanta tsaye rungume da abeel zuciyarta na rauni.
Ahankali ya
zauna kusada ita bakin gadon ya riqo hannunta ya damqe cikin nasa tareda qurawa
fuskarta ido
Ahankali ta
bude idanuwanta dasukai jajir ta kallesa zuciyarta na harbawa da sauri,
Zuciyarta
qoqarin kallonsa takeyi a matsayin a iyayensa sukayiwa nata iyayen kisar
ganganci da rashin imanin abinda ke cikin mahaifiyarta saidai kuma Sam
zuciyarta takasa jin sauyi ko tsanarsa dan kuwa itama tana masa wani irin so ne
Wanda bazata iya ganin laifinsa akan abinda maifinsa ya aikataba saida kuma
batajin zatabar jinin duk Wanda ya zuba ya zube a banza sultan abdulshams zai
dandani kalar nata rashin imanin.
Juyar da
idanuwanta tayi kan ammy dake tsaye tana kallonta da idanuwanta dake bayyanarda
tsananin damuwa da tashin hankalinda take ciki.
Ajiyar
zuciya tasauke ahankali idanuwanta na cikowa da hawaye sbd itace ta rasa
iyayenta,itace baiwa a dah,itace uwar da aka kashewa 'da tun kafin tafita daga
radadin naqudarsa data wuni tana saidai ba itace abin tausayiba sune abin
tausayin sbd yanda take jin zuciyarta dakuma sanin abinda ya samarda karagar
mineelik batada tabbaci akanta da abinda zata iya yi sbd wani irin fushi,xafin
zuciya, qunci,rashin tausayi da bushewa takeji a zuciyarta dan ita kanta ayanxu
tasan tanada hadari sbd yanda takejin tamkar mineelik na cikin jikinta saidai
soyayyar wainda take so da qauna tananan daram cikin ranta musamman shi daya
zamo tamkar shine fitar numfashinta.
Ahankali ta
miqawa ammy hannu.
Cikin
tsananin farin ciki da 'doki ammyn ta qaraso ta zauna gefenta 'daya tareda kama
hannunta cikin tsananin sanyin jiki tace,
Rumanah
ki.......
Girgiza mata
kai tayi ahankali ta bude baki tace,
Ke uwace
agareni kuma zaki cigaba da zama uwata ko wane irin mataki na taka,kome nazama
bazan ta6a iya cutatardake ba laifin da aka sakaki kikayi koda badason
rankibane wannan tsakaninki ne da ubangijinki bazanso wannan maganar tashiga
tsakaninmuba.
Kasa riqe
hawayenta ammy tayi sbd kunyar rumanah ta miqe da sauri ta fice hawaye nabin
fuskarta.
Qoqarin
maida kukanta takeyi saidai takasa sbd radadin datake ji mai zafi na mutuwar da
iyayenta sukayi
Da sauri ya
rungumeta yanajin zafin ganin yanayinta tasaki wani irin kuka mai ciwo tana
qanqamesa.
Suhailat
dake tsaye tanason yimata sannu da jiki ta juya ta nufi qofa jikinta amatuqar
sanyaye zuciyarta na qoqarin jin zafi saidai tayi saurin kawar da hakan sbd
ganin rumanar batada lafiya tana buqatar kulawarsa saidai duk yanda taso
dannewa saida idanuwanta suka ciko da hawaye ta qanqame abeel ajikinta tana
qara sauri dan isa gefenta.
Baice mata
komaiba saida tayi kukan iya yanda zuciyarta keso kafin tayi shiru tana sakin
ajiyar zuciya ahankali.
Dago
fuskarta yayi yana kallonta ahankali ya shafota cikin sanyin murya yace,
I love you
ummu-rumanah bulama maheer abdulshams.
Kallon cikin
idanuwansa tayi akaro na farko dataji Kalmar na bata tsoro saidai tasan maheer
'dinta har abada bazai ta6a iya cutatar da itaba.
Lumshe ido
tayi ahankali ta bude tace,
Ummu-rumanah
nasonka tun kafin kace kanasonta saidai inason kayi min alqawarin zaka soni a
duk halinda nashiga,
Bazaka
gujeniba,
Kaine farin
cikina soyayyarka itace qwarin gwiwata karka.......
Hannunsa ya
dora a bakinta yana mata wani irin kallo yace,
Shihhhhhh
get some rest now sbd gangar jiki da ruhi tare suke rayuwa tare suke barin
duniya.
Kallonsa
tasakeyi tasaki wani irin numfashi mai sanyi tareda sake komawa jikinsa ta
kwanta.
Da kansa
yakaita toilet tayi wanka ta fito tana duba closet dinta taga sabbin royal
gowns 'dinda aka kawo mata ba adadi kowacce da kalar sarqoqinta nakai dana
qafafu da hannuwa tareda wuya.
Doguwar
English gown tasaka har qasa mara hannu takallesa lokacinda yasake shigowa
dakin ya riqo hannunta suka fito palonta na farko har zuwa dining inda aka jera
abinci fiyeda kala biyar da mamaki take kallon dining din sbd ganin duk
girmansa ancikasa da kalolin abinci da fruits ga masu tsaronta mata da aka kawo
tun daga palonta na farkon shigowa har wannan din sai wasu irin samudawan guards
da aka zuba tun daga qofar part din dazagayensa har zuwa hanyar dazata rinqa
kaita zuwa fada.
Kallonsa
tayi yasakar mata wani murmushi ahankali tareda jawo mata kujera ta zauna tana
kallonsa fuskarta daukeda qaramin murmushin qarfin hali sbd har lokacin
zuciyarta cike takeda radadi sosai takejin kamar ana babbaka jinintane ana
qunarsa mai laifi kadan take nema ta dau mataki akansa saidai kasancewarsa
tareda ita yasa take iya control din yanda takeji saidai kamar abin nason
yafara mata yawa.
Cikin
nutsuwa sukaci abincin duk da kadan taci tasha maganinda aka aje kan dining din
daga negasi.
Harsuka gama
cin abincin idonsa nakanta sbd sosai ya lurada sauyi atareda ita saidai
zuciyarsa naqara jaddadawa kanta arayuwa babu abinda zai rabata sonta.
Kasancewar
bata fara sallah ba yasa yakaita daki yasake kwantar da ita ya zauna tareda
riqo hannunta cikin nutsuwa yace,
Inason sanin
abinda yafaru tsakaninki da ammy.
Kallonsa
tayi kafin ta dauke kai tana sake sawa zuciyarta qin ganin laifin ammyn kai tsaye
tace,
Sultan ya
kashe iyayena da taimakon ammy da jakadiya.
Cikin wani
irin mugun yanayi na mamaki yake kallonta
Ta zame ta
sauka gadon ta nufi bakin window ta tsaya.
Gabanta ya
zagayo ya tsaya yana kallon cikin idonta ta rintse idon tana dauke kai.
Ahankali ya
bude baki zaiyi magana ta bude idanuwanta dasukai ja ta katsesa cikin sanyin
murya da cewa,
Bana maka
wani kallo na daban a zuciyata bayan Wanda nake maka na mahadinta ko Allah baya
kama wani da laifin wani....
Shiru tayi
tana tauna Kalmar dazata fada cikin qarfin hali tace,
Na yafewa
ammy sbd Allah da soyayyarta gareni da kasancewarta mahaifiya kuma kaka ga
mutane biyu danafiso ayanxu fiyeda rayuwata dakomai,kai YARIMA MAHEER
ABDULSHAMS da ABEEL HASSAN......
Cikin sanyin
murya dake nuna baqin cikin dayake ciki ya furta,
Sultan f....
Bai qarasaba
tace,
Kayi hakuri.
Ta juya masa
baya cikin wani irin zafi datakeji a zuciyarta ta rintse ido tasake cewa,
Kayi hakuri.
Kasa motsi
yayi sai idanuwansa dasukai jajir yana jujuya kalmarta ta yayi hakuri....zata
dauki mataki akan mahaifinsa kenan.... No not possible...tokuma ko Ba itace
akan mulkiba tana buqatar justice.....
Ficewa yayi
sbd jin kamar numfashi na masa wuyar ja ko gani sosai bayayi sbd tashin
hankalin dayake ciki.
Suhailat
dake tsaye gaban windonta taga fitowarsa daga sashen na rumanah ta 'dauke kai
tareda barin jikin windon sbd gujewa ganin damuwa.
Yana fita ta
zauna bakin gado tareda dafe kanta ta rintse idanuwanta kanta na mata wani irin
ciwo.
Koda dare
yayi duk yanda taso bacci kasawa tayi sbd kewar iyayenta da 'yayanta.
Koda gari ya
waye qarfe goma wata zungureriyar takardar saqo daga alqalamin sauraniyar
mineelik ummu-rumanah bulama ta isa hannun sarkin fada haroun inda saqon yake
cewa ayau angama karbar duk wani bayani akan asalin sarauniya ummu-rumanah daga
baiwa mamani dan haka ayau za'a yanke mata hukunci.
Atake aka
buga sanarwa koina ya dauka qarfe goma sha daya jama'a suka taru ana jiran
isowar assultana.
Cikin wata
irin royal gown tafito red mai adon golden gashinta koina rufe da adon sarqar
farin zinari wasu irin samudawan guards ne maza da mata taredasu Jakadiya a
bayanta ta fito suka nufi fada.
Cikin
nutsuwa na wani irin miskilanci ya yasha gabanta yana kallonta guards din
bayanta suka nufosa ta 'daga musu hannu tareda juyowa cikin nutsuwa ta kalli
Jakadiya tace,
Duk Wanda
yasake gangancin tare mijina aduk lokacinda yakeda buqatar magana dani yana
ganganci da rayuwarsane a sanarda kowa.
Cikin
tsananin ladabi dukkaninsu suka sauke kai suna tuba.
Ta juyo ta
kallesa cikin nutsuwa tace,
Ina kwana?
Kallonta
yayi kafin ya watsawa su jakadiya wani mugun kallo atake suka ja baya sukai
'dan nesa kadan dasu.
Ya kalleta
cikin ido yace,
Bazaki
yankewa mamani hukuncin kisaba that's an order amatsayin na mijinki
Ba mamaniba
har kowama bazaki yankewa hukuncin kisaba nin......
Sultan ne
bakason a kashe ba mamani ba"""ta fada tana kallonsa cikeda
fargabar abinda zaice.
#mamuhgee
TARAYYA
wattpad@mamuhgee
Haske writers association💡
40
Not edited
Kallonta
yayi yana sake kafeta da manyan idanuwansa ransa na qoqarin 6aci da zancenta
zuciyarsa na qoqarin hana faruwar hakan ya bude baki zaiyi magana ya fasa ya
kama hannunta da qarfi ya jata part din ammy dake kusa
Tsakiyar
palon ya saketa tareda kallonta cikin sautin dake nuna bacin ransa yace,
Me kika fada
yanxu?
'Dauke kai
tayi kai tsaye tace,
Kana qoqarin
kare sultan ne akan laifukanda yariga ya aikatasu ne cikin son rai da ganganci saidai
kuma nariga nayi alqawarin duk Wanda ya cutatar da wani sai anbi masa haqqinsa
sbd wannan shine adalcin assultana,wannan shine banbancin mulkin son rai da
adalci....duk Wanda ya kashe a kashesa wannan shine hukuncin a musulunce.....
Riqota yayi
da qarfi ransa na qarasa 6aci yace,
Kina tunanin
na hanaki hakane sbd sultan yana nahaifina?
Kisa dai
matuqar ina raye kuma da aurena akanki bazan ta6a bari kiyiba ko adama kin
kashetane a lokacinda bana kusa da bazan taba bari ki kashetaba and da.....
Qwacewa tayi
tana kallonsa tace,
Nice na
kashe adama kana qoqarin cemin mai kisa ne????
Bayan kasan
mutanen nan sun cancanci kisa tako wane sashe na sharia,
Anyiwa
iyayena kisan wulaqanci da son rai,
Anyiwa 'dana
kisar son rai da ganin dama duk basune masu laifiba nice danake shirin qaddamar
da adalci wa kaina amma y.......
Idan kina
maganar abeel Hussain ne ni mahaifinsa nabarwa Allah duk Wanda keda saka hannu
nabarsa shida ubangijinsa maganar iyayenki kuma amatsayina na mijinki nake baki
umarnin kibarwa Allah bazaki qara yankewa kowa kisar wulaqanciba ki tabbatarda
idan kika sake hakan ni maheer abdulshams mungama zama tare abakin aurenki
gabak......
Cikin tashin
hankali suhailat dake palon basusan da itaba tayi saurin katsesa da cewa,
Abu abeel
ka.....
Shut up and
stay out of this suhailat"""""yafada ransa a matuqar
6ace.
Baca Juga
Rumanah
datai mutuwar tsaye tana kallonsa idanuwanta sun kada jajir suna zubo hawaye
zuciyarta takai qololuwa gurin tashin hankali da baqin ciki ta bude baki cikin
baqin ciki tace,
Basaika
datse alaqar dake tsakaninmuba nasan bana ranka ko gabanka kayi qoqarin barina
da aurenka har zuwa yanzu da baka sallameni bayan haihuwataba sbd itace
amfanina daman shiyasa kace haka sbd sanin sirrin zuciyata saidai........
Fixgoto yayi
da qarfi zaiyi magana ta fixge jikinta tana sakin wani irin kuka mai qarfi da
ciwo sbd zancensa ya girgiza duniyarta gabaki 'daya ya kasheta jitake zuciyarta
kamar zata babbake ta kama da wuta sbd masifar dake ci mata zuciya.
Cikin
tsananin damuwa suhailat ta dauki abeel ta nufi palon qurya tafadawa ammy dake
zaune cikin tunani abinda yake faruwa.
Da sauri ta
taso tana shigowa palon ya juya zai fice ammy tayi saurin riqo rumanah dake
kuka kamar ranta zai fita takira sunansa ya tsaya cak batareda ya juyowa sbd
qaran kukan dake sake hargitsa nutsuwarsa da tafasa zuciyarsa.
Rungume
rumanah tayi tana qoqarin rarrashinta saidai kukane takeyi sosai Wanda ke nuna
tsananin ciwo da baqin cikin da zuciyarta ke ciki.
Kasa tsayawa
yayi ya rintse ido da qarfi ya fice yanajin baqin cikin kukanta da
maganganunta.
Suhailat
dake tsaye ji tayi jikinta ya qara wani irin sanyi da kukan da rumanah keyi
ahankali ta fice daga sashen sbd ganin suna buqatar tattaunawa tsakanin 'ya da
uwa dan jin tayi tazama baquwa acikinsu su duka din har maheer 'din.
Shiru ammy
tayi da ita rungume a jikinta batareda tace mata komaiba sbd halinda take ciki
tana buqatar tayi kukan ko dan ta rage nauyin dake zuciyarta,
Maganar
gskia ko ita bazataso rumanah ta zubar da jiniba sbd sauyi suke fatar samu daga
gareta...
Itace
sarauniya ta farko a tarihin qasar gabaki 'daya data hau sarauta batareda jinin
sarauta a jininta ba bama 'yar qasarba baquwar haure daga wata qasar,
Qaddara ta
koro iyayenta daga gida suka fada wani gari inda daganan Allah yasake jefasu
hannun masu kamun bayi aka kamosu zuwa nan qasar aka haifeta amatsayin baiwa
Wata qaddarar
tasa ta auri yariman masarautar,
duk wannan qaddarar data koro iyayenta ta
zamtowarta cikin lissafin masu mulkin qasar ne wannan kawai ya tabbatarda akwai
abinda Allah ke nufi da hakan Wanda suke fatar sauyine na alkhairi mezaisa suso
ganinta tana aikata abinda sauran sarakunan suka aikata.
Tasan tabbas
maheer yayi hakan ne dan bazai iya bari ya rasataba dan idan ta cigaba da zubarda jinin karagar
mineelik zata shiga jikintane sosai ta yanda zasu rasata har abada.
Dakinta
tashigarda ita ta kwantarda ita kan gadonta ta rufeta tareda shafa kanta ta
fice taje palo ta zauna tareda kallon Jakadiya data shigo duba assultana jin
shiru dan tuni aka zagaye sashen ammyn da tsaro kasancewar tana cikin.
Dafe goshi
ammy tayi cikin tsananin damuwa da rashin sanin mafita tace,
Kije
kisanarda sarkin fada haroun assultana ta 'daga hukuncin zuwa wani lokaci
batajin dadi yanxu.
Cikin
girmamawa da jimami tace,
To""ta
fice taje ta sanar atake akai sanarwar aka watse tareda tsananta tsaro sashen
ammy.
Har dare
tana sashen ammy kwance ko motsi bata yi
tayi wani irin sanyi idanuwanta sunyi jajir.
Shigowa ammy
tayi cikin nutsuwa ta zauna bakin gadon tareda sauke numfashi ahankali cikin
kulawa da sanyin murya takira sunanta.
Bata motsaba
ta bude idanuwanta dasuka kumbura batareda ta amsaba.
Duk wani 'da
na halak bazai iya kallon makasan mahaifansa ya qyalesuba matuqar yanada halin
daukar mataki ko fansa akansuba..
Saidai kuma
dangana da bariga Allah ta wata hanyar shine sasanci da kawo qarshe ga kashe kashen.,
Ummu-rumanah
har abada haqqin asma'u da bulama bazai bar ko 'dayanmuba koda kin yafe mana
saidai kuma ina sake roqon yafiyarki a maimakon mu duka 'din,
Wlh rumanah
ina kallonki amatsayin 'yar dana haifa,
Ina qaunarki
da sonki har cikin zuciyata fiyeda wasu daga cikin 'yayan dana haifa shiyasa
bazan iya bari naganki cikin wata muguwar rayuwa.
Kisan
bashine mafitaba bashine zaisa kiji sanyi a mutuwarsuba saima lalata rayuwarki
dazakiyi ta hakan sbd har abada bazaki yafewa kanki abinda kikayiba zaki tsinci
kanki cikin baqin ciki da damuwar da muma muke ciki ayanxu,
Mijinki yana
miki sonda bazai iya bari ki fada wani mummunan haliba bawai yanayi ne dan
karki kashe mahaifinsa saidan yana tsoron hakan zai qarasa gusarda imaninki ne.
Amatsayina
na uwa ba sultana matar sultan mahaifiyar maheer ba nake baki shawarar karki
kashe mahaifin mijinki ki bar iyayensa da haqqin ran iyayenki wlh Allah zai
kamasu sbd baya taba barin haqqin wani akan wani dan haka kiyiwa magana nazari.
Miqewa tayi
jiki asanyaye tabar dakin tana fatar rumanar tayiwa zancenta kyakkyawan
fahimta.
Qofar da
ammy ta fita ta qurawa ido idanuwanta nasake kadawa sbd zancen ya shigeta
saidai fadanta da maheer ya kasa barin zuciyarta ta nutsu da daga bakinsa
wainnan kalaman suka fito tabbas zuciyarta bazata tsaya wasi wasin daukarsu
ba,,
Meyasa zai
fada mata kalaman dasukafi dalma zafi gurin tarwatsa kunnuwanta da
zuciyarta?????
Meyasa zaiyi
fushi ya iya furta mata kalaman rabuwa da ita bayan alqawarin dayayi mata badan
mutuwaba dashi da ita bazasu rabeba????
Wasu irin
hawaye masu radadi suka gangaro mata ta rintse ido tana qoqarin danne kukan
dake qoqarin zuwar mata.
A cikin
daren takoma sashenta tareda guards inda ta bada gargadi mai qarfi akan batason
ganin kowa.
Kwana biyu
tayi bata fito ko qofar part dinta ba..
Abincin safe
rana dare haka ake kwashesa bata fitowa saidai ammy tazo dakanta har bedroom
tasata cin abinci dole.
Duk iya
yanda take jin kewa da soyayyarsa na cin zuciyarta dannewa tayi sbd har lokacin
zuciyarta cike takeda zafi da radadin kalamansa shima kwana biyun bai nemeta ba
hakan yaqara quntata yanayinta.
Nuratu data
rungumi qaddara da hannu bibbiyu akan mahaifiyarta still itace ke kulada
rumanar amintacciyar baiwarta duk da da farko anso hanata ko kusantar inda
rumanah take saidai rumanar ta hana sbd tasan suna tsananin buqatar juna sbd
sukadai suke ganin junansu amatsayin jininsu tunda mamani sunanta matacciya.
Sultan kuwa
a rubuce ta aikawa harooun da takardar a tsananta tsaro a sashensa kowama yanxu
ta hana yashiga gurinsa
Hakan kuwa
akayi nan take aka cika umarninta tareda bada gargadi ga duk Wanda yaje kar
abari yashiga.
Kwance take
kan doguwar royal chair 'din shaqatawa dake qaramin palonta dakeda manyan
qofofi guda biyar dasuke ta bayan garden din shashaqatawarta,
A rufe
idanuwanta suke saidai Sam ba baccin takeba iskar gurin mai sanyi take kado
mata ta shara sharen labulayen winduna da qofofin palon dan ragewa kanta zafi
da quncin datake ciki.
Ahankali ta
jiyo kukan jariri na shiga kunnenta ta bude idanuwanta a hankali sbd tasan
kukan abeel ne tunda kaf masarautar babu jariri bayanshi.
Tashi zaune
tayi cikeda kewar 'danta da tausayinsa na rashin 'dan uwansa dakuma 'dumin
jikin mahaifiyarsa
Miqewa tayi
ta nufi qofar bakin window ta tsaya tana hango cikin bedroom din suhailat da
itama ta iska ke daga farin labulenta....
Rungume take
dashi a tsaye tana jijjigasa cikin tsananin kulawa da damuwar kukan nasa
Ta 'dagosa
tafa duba fuskarsa cikin qaunarsa tayi kissing kumatunsa tana cewa,
Abeel please
kayi hakuri mummy bazata sake baka maganin zazzabi ba kaji pls my little prince
forgive mummy......
Hawayen
datake ruqewane suka gangaro mata na tsananin soyayyar 'danta da qaunarsa
saidai kuma bazata iya karbarsa daga suhailat na....
Tunda ta
shigo rayuwarta ta sanadinta ta rasa komai,
Ta rasa jin
dadi,kwanciyar hankali da soyayyar mijinta sbd ita,
Ta rasa
babynta sbd jin mijinta ya aureta,
A yanxuma ta
rasa jemal ne sbd ita Dan 'yayanta akaso kashewa duka tsautsayi yasa aka kashe
mata jemal kuma gashi ta rasa mahaifarta har abada...
Gashi ta
riqe 'dan kishiyar datai sanadin rabata da komai da zuciya 'daya tana qaunarsa
tamkar itace ta haifesa,,,
Wace irin
soyayyace takewa maheer??sbd tasan tana tsananin qaunar abeel ne sbd shi 'din
tsotson maheer ne.
Idan
suhailat ce a matsayinta na yanxu zata iya kashe mahaifin maheer?
Duk wainnan
abubuwan da suhailat ta rasa ta dangana bata riqe kowa araiba gashi tana
rayuwarta gwargwadon iyawarta batareda tasaka damuwar duk Wanda ya cucetaba
koya tauyeta.....meyasa ita takasa hakan?
Suhailat
tafita son maheer ne???
Girgiza kai
tayi tareda durqusawa a gurin tana zubarda sabbin hawaye masu radadi da ciwo
gabaki 'daya ta rasa nutsuwarta da sukuninta rashinsa atareda ita jitake
tanason zubarda jinin duk Wanda ya cutatar da ita da iyayenta da 'yayanta SBD
kalamansa dasuke yawo cikin kanta suna qona zuciyarta...
Cikin kuka
tace,
Bakasan
rashinka taredaniba ha'darine dan zan iya aikata abinda bakason dan Allah
kadawo gareni maheer.
Suhailat
data shigo palon dan kawo mata abeel tagansa sbd ta hangota lokacinda take
kallonsu tayi saurin tsayawa cak jin
abinda rumanar tace.
Numfashinta
taji yaqara gudu tayi saurin juyawa dan ficewa tun kafin rumanar taganta
Saidai tana
juyowa tagansa tsaye bayanta idanuwansa sunyi wani irin zurfi ya qureta da ido.
Tsawon
kwanaki kenan itama bata sakashi a idoba 6acin ran rumanah duk yashafesu saidai
Sam bata damu sosai da rashin ganinsaba sbd tasan irin radadi da zafi da
zuciyarsa ke ciki na fada da abinda kafiso fiyeda komai.
Rabasa tayi
zata fice sbd ahankali ya kira sunanta ta tsaya cak
Rumanah kuwa
tun shigowarsa taji qamshinsa saidai bata juyoba sbd wani irin bugawa da
zuciyarta keyi.
Hannu ya
miqa ya dawo da suhailat gabansa cikin murya mai bada umarni yace,
Miqa mata
'danta.
Arikice
takallesa itama rumanah a firgicen ta juyo takallesa.
Fuskarsa a
matuqar 'daure yace,
Kibata
'danta.
Wasu irin
hawayen soyayyar abeel da qaunarsa suka gangarowa suhailat takalli abeel din
takalli fuskar maheer din taga babu sakewa ko kadan ta juya tana tsiyayar
hawaye qafafunta na rawa ta nufi rumanah datai mutuwar tsaye cikeda mamakinsa.
Siririn kuka
suhailat tasaki tareda 'daga hannuwanta ta miqawa rumanah abeel.
Cikin rawar
murya rumanah ta bude baki daqyar tace,
Nabar miki
shi.
Girgiza mata
kai suhailat tayi tana wani irin kuka mai ciwo da qaramin sauti.
A firgice
tasake cewa,
Wlh na
barmiki shi....
Girgiza mata
kai suhailat tasakeyi tareda ajiye mata shi kan kujera ta nufi qofa da gudu
tana toshe bakinta sbd kukan dayaci qarfinta.
Dawo ki
daukesa.
Cak ta tsaya
tareda juyowa takallesa da sauri
Ki daukesa
nabakishi bar abada 'dankine.
Da sauri
tadawo ta daukesa ta rungume tareda dawowa gaban maheer din ta rungumesa cikin
tsananin farin ciki tace,
For a moment
I thought na rabu da abeel har abada..nagode.
Kallon
rumanah data zuba masa ido yayi cikin kulawa yace,
Suhailat
idan babu so biyayya na jawo soyayya fiyeda komai,
Idan akwai
so rashin biyayya na rusashi komai qarfinsa..
Har abada
suhailat matsayinki daban yake cikin zuciyata bazan ta6a daina ganin girma da
qimarkiba.
Sanyi
jikinta yayi masifar yi sbd gane amfani yayi da ita gurin isarda saqo ga
rumanah...
Wani irin
ciwo da radadi taji yana tasowa a zuciyarta akaro na farko data kasa riqe abinda
yake zuciyarta tasaki wani irin kuka mai ciwo tareda ficewa tana dafe qirjinta
dayake mata zafi sosai.
Gabanta ya
qaraso ya tsaya yana kallon cikin idanuwanta dake zubard hawayen abinda yayi
yanxu dan ta tabbarda ita yake fadawa magana bada suhailat din yake.
#mamuhgee.
Post a Comment for " TARAYYA 39-40"