TARAYYA 41-42
TARAYYA
41
Not edited
Marubucin
gskia baya rubuta abu acikin labarinsa batareda yayi bincike ko tambaya ba
yayiwa abin cikakken sani kusani marubuci ba jahili bane sbd wata
tambayar ko
comment din tamkar wanka da jirwayene akewa marubuci dan haka kusani ni bana
rubuta abinda banida sani akansa.
Juyawa tayi
tabasa baya zuciyarta na wani irin bugu sbd zafin maganar daya gama fada mata,
Kobai fadaba
tasani yafi ganin girma da qimar suhailat sbd ko babu komai itace uwar 'yayansa
kuma macen data girmama dukkanin abinda zaizo mata dashi saidai tasan itama
baza'ace bata masa biyayyaba,,,,
Rintse
idanuwanta tayi zuciyarta na sake jiyo mata zafin abin,
Da
kishiyarta yake gaya mata maganar bata masa biyayya...sabon ciwon hakan taji ta
rintse ido da qarfi tareda girgiza kai ta juya ta nufi qofa tana qoqarin maida
kukanta.
Riqo
hannunta yayi daidai lokacinda tazo wucesa ya dawo da ita gabansa yana kallon
fuskarta data qi kallonsa saidai yanayinta ya nuna jin zafinsa ne cikin ranta.
Kujera ya
nufa ya zaunar da ita ahankali kafin shima ya zauna tareda riqo hannunta cikin
nutsuwa da kulawa yace,
Kina tunanin
wannan itace mafita???
Kina tunanin
a halinda muke ciki yanxune lokacinda yakamata mu ringa samun matsala akan
abinda nake buqata nakuma baki umarni?....
Kina tunanin
sbd kare mahaifina nakeson dakatar dake daga abinda kike shirin aikatawa???
A musulince
duk Wanda ya kashe a kashesa amma idan kashewar zata kawo kashe kashen bayin
Allah da basujiba basu ganiba to an yarda abar Wanda yayi kisar sai ayi masa
wani hukuncin kwatan kwacin zafin abinda ya aikata.
Kina tunanin
sultan mahaifanki kawai ya kashe?
Sultan ya
bada umarni ankashe mutanen da sukafi mahaifanki abin tausayi,
Ya maida
yara qanana marayu babu adadi,
Ya saka mata
zaman takaba babu adadi,
Duk kina
tunanin yin kansa ne kokuma ra'ayin kansa ne???
Dana barki
da tun a shrkaran jiyar kinzama abinda yafi sultan ha'dari dan kuwa da yanxu
jinin mutanen da kika zubar yafara ta6a qwaqwalwarki...
Kinga abinda
mu bamu ganiba labari kawai mukeji na asalin abinda ya faru har aka samu karagar
kuma kinsan duk wata masifa dake bibiyar masarauta nan har yau ankasa samun
Wanda zaiyi amfani da tunani da baairarsa domin kawo sauyi domin kuwa tun farko
kisar cin amana ce ta samarda karagar kuma har yanxu kisar ce akeyi kina
tunanin hakan shine mafita da sauyi tareda jin qan da talakawan qasar ke buqata
bayan sune ake kashewa wainda basujiba basu ganiba.,
Kinason
yankewa sultan hukuncin kisa bawai dan fadar musulunci ba saidan daukar fansar
kisar iyayenka Wanda hukuncinki kwata kwata baiyiba a musulunce sbd kai tsaye
fansa ne kika dauka,,
Kafin sultan
anyi kashe kashe da dama wainda ma sukafi nasa dan haka...
Ina sonki
bazan iya bari kibi hanyar da sauran sukabiba,
Bazan iya
bari rayuwarmu ta lalace ba sbd rayuwata zata lalace ne daga lokacinda taki ta
lalace dan haka bazan iya bariba,
mahaifina tun tuni naso na kubutardashi daga
hakan amma yayi aiki da qarfinsa na zama mahaifi agareni ya nesantani da kansa
dan haka bazan sake aikata wannan kuskuren ba sbd ke din ikona ce.
Na auri
suhailat shekaru shida zuwa bakwai yanxu...,
A cikin
shekaru bakwai dinnan bantaba fada suhailat ta fadaba sbd soyayyarta gareni mai
girma ce irin girmanda yake sakata shanye duk wani tauyewa dazai fito daga
gareni.,
Kece
rayuwata,kece abinda zuciyata tafiso fiyeda komai saidai gaskiyar maganar shine
suhailat itace nutsuwata......itace mace mafi girma da qima a idanuwa na bayan
mahaifiyata...
Rintse
idanuwanta tayi da qarfi zuciyarta na tsananta bugawa jikinta na daukar rawa
hawayenta na tsananta.
Kallon
yanayinta yayi cikin damuwa yace,
I can't lie
to you amma steps dinda kika fara son dauka sun fara ankarar dani babban
kuskuren danake shirin aikatawa na barin suhailat ta fita daga rayuwata and
idan kika cigaba da qoqarin binsa to tabbas zaki rasani......
Wani irin
kuka ta fashe dashi mai qarfi da shiga zuciya tareda zamewa qasa ta zauna ta
cusa kanta cikin qafafunta tana jin sabon nauyi cikin zuciyarta sbd dukkanin
rayuwarta ta hargitse ta juya ta zama wani abu na daban,
Tana tunanin
zatayi rayuwar aure mai dadai saidai gabaki dayama rayuwar auren data kowama ta
lalace tun haihuwarsu masarautar ta hargitse takoma gidan baqin ciki sbd kowa
yarasa gane inda aka dosa.
Dafata yayi
ahankali tareda furta,
I love you
queen ummu-rumanah bulama,
Ina sonki
zanci gaba da sonki har numfashina na qarshe.
Miqewa yayi
ahankali yabar dakin idanuwansa na qara kadawa zuwa jajir.
Sabon kuka
tasaki bayan fitarsa tanajin maraici da baqin cikin wainda sukayi sanadin
barowar iyayenta da gida har sukazo nan aka haifeta..wace irin rayuwa tasamu
kanta ne aciki..
Tabbas
tanason yankewa sultan hukuncin kisa ne badan ya cancanta ba sai dan daukar
fansar kisar dayasa akayiwa iyayenta,
kwata kwata
zuciyarta takasa yarda tayi masa hukunci akan dukkanin abubuwan dayayiwa bayin
Allah kanta kawai da iyayenta take gani Wanda idan tayi masa kisa akan hakan
sun zamo daya babu banbanci a tsakaninsu.
Kuka takeyi
sosai tanason ko nauyin dake danne da zuciyarta ya sauka amma saima wani sabon
qunci dake qara mata nauyi.
Kuka takeyi
sosai tareda dafe zuciyarta dake mata tsananin radadi da ciwo,
Kukan
datakeyi ayau yafi na ko yaushe sbd duk wani hope datake dashi akan zai sota
wata rana ya rusashi dan kuwa ta tabbarda zuciyarsa ba ita takesoba kuma bazata
ta6a sontaba.
Taso ta
zauna dashi har qarshen rayuwarta sbd qaunarta garesa mai girma da tsafta ce
saidai kuma hakan bamai yiyuwa bace sbd tasa zuciyar takai qololuwa gurin son
wata
Saisai
Bazataga laifin rumanah ba sbd tun kafin aurenta tasan babu soyayyarta a
zuciyarsa saidai qauna da girmamawa zuciyarta ta dauki wannan sbd babu wata a
zuciyarsa tana fatar tashiga wata rana saidai yanzu dayakeda wadda yakeso
rayuwarsu su duka na neman lalacewa sbd soyayyarsa dan haka yau duk wani abinda
takeson tabbatarwa ta tabbatar dan kuwa har abada bazai ta6a sonta tunda bai
sota sbd 'yayanta da shekarun dasuka diba ba.
Ahankali ta
tsaida kukanta saidai hawayenta dasuka kasa tsayuwa cikin muryar kuka da tsananin
karaya tace,
Ka tarwatsa
duk wata soyayyarka dake raina maheer.
Kallon abeel
dake kwance tayi tabbas tana qaunarsa saidai bazata rayu dashiba dan kuwa zama
a tsakanin iyayensa ya qare mata har abada.
Hawayenta
dasuka kasa tsayuwa ta share tareda miqewa ahankali ta nufi wardrobe dinta ta
bude.
Ahankali ta
fidda dukkanin kayanta ta hada na abeel tareda duk wani abinsa dake gurinta.
Acikin daren
babu Wanda yayi bacci acikinsu sbd babu Wanda yake cikin nutsuwa kowannensu
tunanin step 'din dazai dauka dan kawo sauyi arayuwarsa mai kyau yakeyi.
Suhailat
tagama yanke shawarar rabuwa dasu takoma qasarta sbd tabbas kota cigaba da zama
zaman takurawa juna zasucigaba dayi musamman yanzu dayake buqatar lokacinda zai
daidaita komai na masarautar ta hanyar matarsa dan haka tafiyarta shine mafita
ga dukkaninsu gabaki 'daya.
Tsaye yake
bakin windon palon sama na gidan khaleefa ya qurawa waje idanuwansa dake cikeda
rashin bacci da damuwa..
Khaleefa
dake zaune yana kallonsa cikin tsananin kulawa yace,
Kaine
shugaba kuma kaine haqqin kawo gyara acikin zamanka da matanka ya rataya
akanka.,
Tun farko
kaso kawo gyara batareda ka hau ba Allah bai nufa ba sbd lokacin yanke ijabar
baiyiba amma yanzu lokaci yayi sbd Allah yabaka dama da ikon kawo sauyi ta hanyar
matarka dake qarqashin ikonka itace sarauniya....
Saidai kuma
saikayi taka tsantsan gurin gyaran sbd zai iya kawo rashin fahimta da matsaloli
ga rayuwar aurenku musamman suhailat......
Juyowa yayi
ya zauna ahankali tareda rintse ido damuwarsa na ninkuwa sbd sanin rayuwace
zasuyi sarqaqqiya sbd har abada bazai hada soyayyar dayakewa rumanah da wadda
yakewa suhailat ba sbd soyayyar rumanah a jininsa take tun haihuwarta..
Yanayin iya
qoqarinsa gurin ganin bai tauye haqqin suhailat da 'yayansa ba saidai zuciya
batada shamaki akan abinda takeso wani lokacin Wanda hakan yafara jawo masa
tsana daga suhailat abinda bazai taba fatar yakasanceba.
Dafasa
khaleefa yayi cikin sanyin murya yace,
Musulunci ya
yardar maka da kasaki matarka idan har babu sonta a zuciyarka sbd gudun shiga
haqqi dan haka zaka iya duba hakan sbd a yanxu bazata iya jure abinda ta jureba
lokacinda take ita kadai....
Rintse ido
yayi da qarfi jin wani irin zafi daya soki zuciyarsa da khaleefa yayi maganar
rabuwarsa da suhailat.
Miqewa tsaye
yayi tareda nufar qofa ya fice batareda yace komaiba.
Kai tsaye
part dinsa ya nufa harya kai qofa ya tsaya cak.
Juyowa yayi
ahankali ya kalli qofar sashen suhailat da ake fita da akwatinanta.
Ya saki
numfashi ahankali cikin wani irin yanayi na damuwa sbd yasan za'ai hakan.
Tabbas yana
qaunar suhailat har cikin ransa kuma a shirye yakeda yin rayuwa da ita har
mutuwarsa sbd abinda bata ganeba shine tanada wani matsayi mai girma a
zuciyarsa na qima Wanda ko rumanah dayake so batadashi sbd ita zai iya rufe ido
yayi mata wani abin amma bazai iya yiwa suhailat ba sbd akwai kunyarta mai
girma a idanuwansa saidai bazai tilas ta mata ba ga duk abinda ta zaba akansa
sbd ta cancanci abarta da abinda take raayi ayanxu.
Juyowa yayi
ya nufi sashenta a karo na biyu duk tsawon zamansu Wanda hakan na yasakasa jin
wata sabuwar gagarumar kunyarta.
Carolina ce
a palo tana qoqarin fitowa da akwatinan qarshe wainda suke na abeel ne tana
fitowa ta nufi sashen assultana dasu.
Bedroom
dinta ya shiga alokacinda ta dauki handbag dinta da abeel zata fito.
Kallon juna
sukayi dakyau
Ganin yana
qureta da kallo yasata sauke kanta ahankali tareda kwantarda abeel ta 'dago ta
qura masa ido ganin yanda duk ya rame lokaci 'daya yayi wani irin canzawa
saidai kuma abin tausayin shine yana cikin wannan halin ne sbd halinda rumanah
take ciki.
Gangarowa
hawayenta sukayi ta sauke kai ahankali cikin sanyin murya da nutsuwa tace,
Ranar farko
dana fara ganinka aranar nafara Sonka maheer ibn abdulshams abdallah,,
Kaine namiji
'daya da zuciyata ke so saidai babban kuskuren danayi shine na nacewa na aureka
a tunanina zaka soni wata rana saidai ashe babban kuskure da shishigi nayiwa
qaddarar datake jirana..
Kallon cikin
idanuwansa dasukai jajir tayi tasaki murmushi mai ciwo tace,
Haryanxu ina
sonka maheer abdulshams saidai bazan iya cigaba da zama dakaiba maheer sbd
girman soyayyar danake maka bazanso zuciyata ta tsanekaba.
Ayau ina
roqonka sbd darajar 'Yayana da soyayyata ka sauwaqemin na samu rayuwar data
cancanta dani wannan rayuwar ta gidanka ba tawa bace na tabbatarda tawa tana
wani guri tana jirana.
Rintse ido
yayi akaro na farko dayaji ruwa sun ciko idanuwansa sbd ita ya girgiza kai
yanason magana amma yakasa.
Ta riqo
hannunsa tana qoqarin maida hawayenta tace,
Wlh idan
nacigaba da zama dukkaninmu zamu cutu qarshe dukkaninmu zamu fada hanyoyinda
bazasu amfanemu ba sbd zan iya canzawa na zama wata daban,
Canzawata
zatasa ka tsaneni
Tsanata
dazakayi zaisa matarka ta canza sbd zata riqa ganin itace abar so nikuma zata
riqamin kallon mahaukaciya qarshe dukkaninmu zamu zama abinda bama fatar
kasancewa...
Na yarda da
aurenka shine qaddarata kuma na karbeta da hannu bibbiyu kuma ina fatar Allah
yasa na cinye wannan jarabawar zuwa yanxu sbd zuciyata tafara gazawa dan haka
nake roqon alfarma ta qarshe daga gareka dan Allah free me from this
relationship
Wlh I'm in
so much pain zuciyata zata iya bugawa kowane lokaci please free me maheer.
Girgiza kai
yayi yana kallonta da idanuwansa dasuka canza daqyar ya iya furta,
Suhailat I
need you in my life please don't.....
Girgiza kai
itama tayi kukanta na qoqarin qwacewa tace,
Wlh bazan
iyaba maheer,
Wlh mutuwa
zanyi I've endured enough,
Duk abinda
kamin na yafe maka ina fatar kaima ka yafemin
goodbye
yarima maheer abdulshams.
'Daukar
abeel tayi ta rungume wani irin ciwo mai zafi nacin zuciyarta ta rintse ido
hawaye masu zafi suka gangaro mata tasaka hannu ta goge fice dakin.
Kodata fita
palo Carolina da sauran masu hidamarta duk suna tsaye kowanne idanuwansa cikeda
hawayen rabuwa da ita.
Kallonsu
tayi tareda sakin murmushin qarfin hali ta fice sbd bazata iya cewa komaiba ta
nufi sashen rumanah.
Zaune take a
palonta tayi lamo ko motsi batayi ta qurawa gefe 'daya idanuwanta dasukai jajir
suka bushe dukkanin wani abincin karyawa an Jere mata a gabanta saidai ko motsi
batayiba bare takalli abincin gashi har rana tafarayi,
Ganin
halinda take ciki yasa dukkanin masu hidimarta da masu tsaronta yau jikinsu
asanyaye yake ko babban motsi ba'ayi a sashen tsit kakeji.
Da
shaqaqqiyar muryarta datasha kuka tai sallama tashigo palon taganta zaune da
alama agurin ta kwana tun jiyan sabd ganin kayan jikinta.
Ahankali
taqaraso gabanta ta durqusa ahankali ta dora mata abeel ajikinta.
'Dago
idanuwanta tayi a wahalce ta kalleta takalli abeel ta tashi zaune daidai tareda
qurawa abeel 'din ido ta 'dago takalli suhailat ahankali ta iya bude baki sbd
tsananin nauyi da ciwon kan datakeji tace,
Shine da
kansa yace yabaki bayan nima nace nabar miki sh......
Nagode sbd
kema kinyi abinda bakowace uwace zata iyaba ciki hardani kuwa sbd bazan ta6a
iya bawa kowa 'dana dana haifaba,
Ina qaunar
abeel qauna mai tsafta sbd shi 'din 'dan maheer ne kuma ina kallonsa amatsayin
jemal dina dana rasa saidai zamansa hannuna bamai yiyuwa bane Allah ya
albarkaci rayuwarsa.
Juyawa tayi
ta nufi qofa ta fita batareda tasake cewa komaiba sbd batason bayyanarda
hawayenta gaban rumanah tabarta da jin cewar kamar itace silar rabuwarsu.
#mamuhgee
TARAYYA
wattpad@muhgee
Haske writers association💡
42
Not edited
Baca Juga
Kasa motsi
tayi tabi bayanta da kallo harta fice ta jima tana kallon qofar kafin ta maido
kallonta kan abeel daya farka yana kallon fuskarta ta rintse ido tareda
rungumesa tana jin wata sabuwar damuwar sbd rashin sanin abinda yafaru yanxun.
Ahankali ta
lumshe idanuwanta mafarkin abbanta datai yau yana dawo mata.
"Ummu-rumanah
kibi mijinki a dukkanin umarninsa matuqar basu saba addininki ba sbd shine
gatanki kadai yanxu aduniya,
Ki gujewa
mulki sbd haqqoqin dubban mutane da bazaki iya daukaba sbd rauninki na zamowa
'ya mace kibarwa Allah komai ki gyara aljannarki."""
Kalaman da
mahaifinta ya sanarda ita a mafarki kenan saidai abinda takasa ganewa shine ta
yaya zata sauka mulkin batareda ta kawo sauyi da zaman lafiya a qasar ba.
Bude ido
tayi tareda jinjina shawararda zuciyarta ke bata dan kawo qarshen komai saidai
hakan wani abune mai girma dayakeda matuqar hadari saidai dole zata aikata
hakan koda hakan shine ajalinta zatayi dan kawo qarshen rayuwar da alummar
qasar suka samu kansu.
Tabbas
qaddararta itace ta koro iyayenta daga gida ta kawosu nan sbd gashi abinda
yafaru tun qarnikanda ko kakanninta ba'a haifa Ashe tana cikin qaddarar gashi
itace zata kawo qarshen abin.
Hawayen
tausayin mijinta da 'danta tareda ammy ne suka gangaro mata ta sauke kanta
tareda sakin kuka ahankali sbd tasan sune zasufi kowa kukan rashinta arayuwa
sbd sune wainda takeda matuqar mahimmanci arayuwarsa ta yanda rashinta zai
matuqar ta6a rayuwarsu.
Sunansa ta
furta ahankali cikin zuciyarta sbd tasan mutuwarta zata tarwatsa zuciyarsa
zatabarsa cikin mawuyacin hali saidai tasan suhailat na nan zata kula dashi.
Miqewa tayi
ta nufi dakinta ta kwantarda abeel ta zauna gabansa ta qura masa ido tana fidda
sautin kuka ahankali sbd kukane takeyi sosai.
Tana fitowa
sashen rumanah kai tsaye shashen ammy ta nufa bata nuna mata komaiba tasanarda
ita zataje Mali.
Ammy dake
fama da ciwon kai mai tsanani takalleta da idanuwanta ahankali tace,
Allah ya
kiyayeki ya hadaki da alkairin dake cikin tafiyar.
Amin ta
furta ahankali tareda juyawa ta fice dan dama su amah suna Mali tuntuni da aka
fara wainan rudanin.
Motocin
dazasu kaita airport na fitowa daga masarautar tasaki wani irin kuka ahankali
tareda rintse idanuwanta tana furta Allah yabani juriya da danganar rabuwa
dakai maheer.
Suna isa
airport basuyi minti ashirin ba suka tashi daga qasar Ethiopia zuwa mali.
Lokacinda ta
wuce tabarsa daqyar ya iya fita yabar dakin ya nufi part dinsa yana qoqarin
danne halinda zuciyarsa ke ciki amma yakasa saida jiri ya zaunar dashi kan
kujera da qarfi ya rintse ido ga mamakinsa saiyaji kamar hawaye na neman zubo
masa yayi saurin dafe kansa da hannu bibbiyu jin kamar zai rabe masa sbd yasan
bazai ta6a iya cireta aransa ba.
Ahankali ta
qaraso bayansa ta tsaya tareda zuba masa ido tana sake danne hawayenta..
Bude idanuwa
yayi ahankali sbd he can feel her presence.
Juyowa yayi
suka hada ido atake takasa riqe kukanta tafara girgiza kai tareda sakin kukan
Ya ware
hannunsa 'daya alamar tahowa garesa da gudu ta qarasa ta fada jikinsa ya
rungumeta sbd shikansa yana buqatarta kusa ayanxu.
Kukan
datakene yafara bashi mamaki ya 'dago fuskarta ya kalleta atake yaji kwanyarsa
ta qarasa hargitsewa ya bude baki zaiyi magana tayi saurin 'dora bakinta cikin
nasa tana tsiyar hawaye.
Ahankali
tasaki bakinsa tana kallon fuskarsa dake bayyane da damuwa cikin tsananin
sanyin muryar kuka tace,
Ina sonka
yarima maheer abdulshams,
Kaine farin
ciki da rayuwar ummu-rumanah bulama,
Kaine abinda
zuciyata bazata iya jure rashinsa ba,
Ina maka
qauna mai girma a tun ranardana fara ganinka agabana.,
Wlh bazan
taba iya aikata kuskurenda zai nesantani dakaiba bare kwatanta rayuwa babukai..
Kasan
mutuwane kawai banyiba a daren ranar daka furta rabuwa dani maheer abdulshams,
Ummu-rumanah
bazata iya rayuwa babu kaiba sbd kaine jigonta kuma jagorarta..
Share
hawayenta tayi tareda jan numfashi kukanta na rage sauti tace,
Wlh haryanxu
zuciyata zafi da takeyi da zancen daka fadamin kana tunanin zan iya rayuwane
wlh mutu.....
Maidata yayi
jikinsa da sauri ya rungumeta yana girgiza mata kai dan bazai iya ko maganaba.
Qanqamesa
tayi tana cewa,
Na tuba ka
yafemin.
Dora hannu
yayi abakinta yana sake rungumeta ahankali ya furta,
Maheer
abdulshams loves you ummu-rumanah bulama.,
Ummu-rumanah
bulama kece mahadin rayuwar maheer abdulshams.
Murmushin
qarfin hali tasaki ahankali tareda sake kwanciya ajikinsa.
Shiru sukayi
dukkaninsu ajiyar zuciyarta kawai ke fita akai akai
Sai kuma shi
dahar lokacin tunani da damuwar tafiyar suhailat ne kawai cikin ransa,
Tana buqatar
shan iska zai barta tasamu sarari idan yagama da matsalar mineelik ya
tabbatarda rumanah ta fita daga cikin wannan masifar zaije yadauketa su koma
Georgia gabaki 'dayansu.
A daren
ranar nan ta kwana gurinsa tareda abeel saidai kusan dukkaninsu babu mai
nutsuwar yin bacci saidai shiru sukayi a kwance kowannen da abinda yake damun
zuciyarsa.
Washe gari
koda aka tashi aka tararda Allah yayiwa mamani rasuwa
Koda aka
dudduba dan tabbatarda meya kasheta aka gano saran maciji ne har guri biyu a
wuyanta da gefen hannunta sbd wani irin canzawa da fatarta tayi takoma Kore
Kore alamar qarfin dafin macijin mai ha'darine.
Lokacinda
Jakadiya ta kawo mata saqon mutuwar suna zaune kan dining maheer na tilasta
mata cin abinci.
Kallon
Nuratu dake jera musu sauran abincin breakfast din tayi da sauri tareda miqewa
tsaye sbd ganin halinda tashiga lokacinda Jakadiya tagama fadar saqon da sauri
suka rungume juna nuratu na sakin wani irin kuka ahankali tareda rintse ido
tana girgiza kai.
Hawayen
tausayin nuratun ne itama suka ciko idanuwanta ta bubbuga bayanta cikin son
daure kukanta dake zuwa na tausayin kansu sbd sun tabbata marayu iyayensu
dasukazo nan suka haifesu sun rasu sun barsu ayanxu sune kadai 'yan uwan kansu.
Cikeda
tausayawa Jakadiya takallesu cikin sanyin murya tace,
Allah ya
gafarta mata laifukanta ya sadata da rahamarsa ina miqo ta'aziya ga assultana
da 'yar uwarta nuratu akan wannan rashi.
Ganin tana
neman rikicewa da kuka yasashi yiwa Jakadiya wani kallo
Atake tayi
gyaran murya tana cewa,
Nuratu kizo
muje kiyiwa mahaifiyarki addua kafin a fice da ita.
Sakinta
rumanah tayi tareda kallon fuskarta tana hawaye tace,
Allah yabaki
haqurin rashinta yasakamiki dauriyar yimata addua.
Kallon
rumanar tayi sbd jin bata ambatarwa mamanin rahamar ubangiji ba ahankali ta
bude baki cikin tsananin sanyin murya tace,
Ina roqorwa
mahaifiyata yafiya ki yafe mata sbd qauna da amincin dake tsakanina dake
dan......
Kije na yafe
sbd qauna da amincin dake tsakaninmu saidai haqqin ran 'yayana data dauka
wannan tsakanintane da ubangijinsu shida ya haliccesu.
Ahankali ta
furta,
ina fatar
Ubangiji ya yafe mata.
Juyawa tayi
ta fice rumanah ta juya ta zauna tana qoqarin saita nutsuwarta kartayi kuka
saidai Sam takasa sbd duk yanda mamani taqita takashe mata 'dah ita din tatace.
Ta bayanta
ya rungumeta jikinsa ahankali yana cewa,
Sorry luv.
Shigewa
jikinsa tayi tana daina kukan dan tana buqatar rarrashin gabaki daya ta rasa
ina ta dosa da rayuwarta.
Jin tayi
shiru yasashi shafa kanta cikin sanyin murya yace,
Allah baya
barin haqqin wani akan wani gashinan kin gani.
Shiru tayi
tana sauke ajiyar zuciya sbd tunowa da abinda zatai dan kawowa kowa sauqi da
qarshen masifar sbd a yanxu abeel dintane kawai ake jira ya gia yahau dan haka
bazata taba bari 'danta yahau wannan karagar ba sbd ajikinta tanajin masifa da
balain dake cikinta yana yawo cikin jininta ita kadai tasan yaya takeji take
daurewa sbd shirye take da yaqar komai akan qarfin soyayyar datakewa mijinta.
Abu taji na
fitowa ta hancinta ta taba ahankali tashafo taga jinine da sauri ta goge sbd
kar Maheer yagani.
Shigowar
ammy yasashi sakinta suka miqe gaba dayansu murya a tausashe suka gaidata ta
amsa tana kallon rumanah dataga tayi wani irin fayau kamar ba jini a jikinta ta
tsaya gabanta tareda riqo hannunta suka koma kan royal cushions dake palon suka
zauna tana kallonta cikeda mamaki tace,
Rumanah ki
fadamin gskia lafiyarki kalau?
Gefen Maheer
daya kafeta da ido ta kalla ta sauke kai cikin sanyin jiki tace,
Lafiyata
kalau.
Girgiza kai
ammy tayi tace,
Rumanah wlh
bakida lafiya wannan abun na cin jininki duba kiga kina canzawa rumanah karki
rufeni kifadamin gskiar abinda kikeji.
Dawowa yayi
kusada ita ya zauna yana zuba mata ido cikin tuhuma ya riqo hannunta zai duba
tafin hannunta ta zame hannun tareda girgiza kai tace,
Lafiyata
klau banajin komai....
Hancinta ya
qurawa ido cikin daukewar numfashi yakai hannunsa ya shafo jinin dake gangarowa
daga hancin ya kalla jikinsa na rawa ammy ma cikin tsananin tashin hankali take
kallon jinin...
Ganin suna
kallonta tayi saurin shafowa taga jini sosai ta miqe tsaye wani irin jiri ya
dibeta ta yanke jiki gurin ta fadi idanuwanta rufe jinin na sake ballewa daga
hancinta.
Cikin
masifaffen tashin hankali sukayi kanta ammy tuni tafara kuka tana kiran sunanta
Shikuwa
daukarta yayi hankali amatuqar tashe yayi bedroom dinta da ita ya kwantar ya
fidda waya atake yakira khaleefa dasu dr abeena tareda sauran manyan doctors
nasu.
Tissue yasa
yana goge mata hanci saidai Sam jinin yaqi tsayawa gashi tafara wani irin
jijjiga a rikice ya qanqameta jikinsa yana kiran sunayen Allah ahankali
muryarsa na rawa dan yasan bazai iya kwatanto rayuwa babu itaba.
A gigice
dukkaninsu suka iso tareda nurses da duk wasu kayan aikinsu atake suka fara
qoqarin tsaida jinin dan maqala mata oxygen sbd numfashinta daya fara mata
wuyar ja.
Dafasa
khaleefa yayi tareda kallon yanda duk jikinsa ya 6aci da jini cikin kulawa yace,
Kaje daga
palo gurin ammy zakafi samun nutsuwar bari mu dubata.
Palo
khaleefa ya rakosa ya zauna kusada ammy yakoma ciki shi.
Riqo
hannunsa ammy tayi cikin tsananin damuwa da tausayinsa dana abeel dake rungume
ajikinta tace,
Zataji sauqi
insha Allah.
Jinjina mata
kai kawai yayi sbd ko bude baki bazai iyaba bare magana.
Atake rashin
lafiyar assultana ya yada koina nan koina gari yafara 'daukar tsit sbd rufe
shaguna da kasuwanni.
Acikin
masarautar kuwa Sam ba wani dogon motsi tako wane bangare sbd jiran tsammanin
farfadowarta.
Daqyar suka
samu suka tsayar mata da jinin aka maqala mata oxygen tareda ruwa da sauran
abubuwan da suka kamata amma har lokacin bata farfado ba.
Bayan duk
sungama abinda zasuyi aka bar nurses uku dan kulada ita suka fice.
Lokacinda
yashiga yaga yanda takoma lokaci daya
Ya zauna
bakin gadon tareda 'dora hannunsa kan nata ya rufe ido
Shikadai
yasan radadi da ciwon da zuciyarsa ke ciki ganinta ahaka.
Ahankali
yace,
Tana
farfadowa zamu wuce bazan iya zama anan ba kuma.
Dafasa ammy
tayi tareda yarda da abinda yafada dan itama tagaji da nan 'din tana buqatar
nutsuwar rayuwa kota maida hankali gurin istighfar ga ubangijinta.
Sai tsakiyar
dare ta farka tareda bude idanuwanta ahankali ta qurawa masa ido yana zaune
bakin gadon hannunsa cikin nata a damke idanuwansa a lumshe saidai tasan ba
bacci yakeyiba.
Ahankali ta
bude baki da siririyar murya ta furta,
Abu abeel..
Bude
idanuwansa yayi da sauri tareda tashi zaune daidai yana kallonta fuskarsa na
bayyanarda tsananin farin cikin daya shiga na ganinta.
#mamuhgee.
Post a Comment for " TARAYYA 41-42"