IMAAN COMPLETE
*Imaan*
_By Khaleesat Haiydar_
*All thanks to Allah SWT for giving me the chance, privilege and ability to start this book, my special greetings goes to my lovely mum Hajiya Hajara and my sweet aunties (Small mums) my siblings aren't excluded also... I love them all, Ban mance ki ba Mama dutse ina gaisuwa da fatan anyi sllh lafiya Allah ya amshi ibadunmu, Hajiya Asabe kema ina gaida ki sosai da maki fatan alkhairi Allah ya raya xuri'a, Hafsat Oum Ilham I greet you too with respect, and My Sophiee I know you won't see this but get this.. jiddo Love's you dear, Lovely fans ina maku fatan alkhairi da fatan gamawa da iyaye lafiya*
1. SARAN BOYE COMPLETE
2. GIDAN UNCLE COMPLETE
3. KWAI CIKIN KAYA BOOK TWO COMPLETE
4. WUTSIYAR RAKUMI COMPLETE
5. GOBE NA COMPLETE
6. ZAN FASA KWAI COMPLETE
7. MY UNCLE COMPLETE
8. HEEDAYAH COMPLETE
9. SIRADIN RAYUWA COMPLETE
10. MIN QALB COMPLETE
11. KWARATA COMPLETE
1.....
Babban compound ne sosai dake dauke da shuke shuke da
bishiyoyi masu daukar hankali, kai kana ganin tsakar gidan kasan naira ta
xauna, makeken tsakar gidan na dauke da sassa har uku masu fenti iri daya, ko
wani sassa kuma akwai tazara mai tsayi tsakaninsa da wani sassan, sashin farko
wanda shi xaka ci karo da bayan shigowar ka gate din xamanin dake babban gidan
ba dai girma ba don sashin duk ya fi sauran girma, duplex ne babban gaske sai
parking space gari guda dake gefe. Durkushe a bakin tap dake babban sashin
farko wata farar budurwa ce da baxata wuce shekaru sha takwas ba, duk da a duke
take hakan baxai sa aki gane doguwa ce ita din ba, ruwan tap din na ta xuba
bucket din da ta tara don ya cika, sai shafa socks din hannunta take kamar mai
tausayinsa, daga ves, huluna sai socks kala uku sune kayan da take wankewa a
wajen amma ta kusa awa daya, kofar entrance da ta ji an bude ya sa ta kamewa
daga inda take durkushe lkci daya ta xaro ido gabanta ya fadi don ita dai a iya
saninta babu kowa sashin banda ita da ke wanki tun daxu, occupant din bangaren
duk sun tafi biki ta kuma ga fitarsu, wanda da ace suna nan tasan ko hauka take
baxata fara xuwa bangaren su tayi wanki ba, a hankali ta juya don ganin wanda
ya fito, wani matashi ne dogo sosai wanda baxai haura shekaru talatin da uku ba
tsaye dai dai entrance din shiga gidan sanye da jallabiya milk color, Ta dauke
kai tana ci gaba da daurayenta, ya rungume hannuwan sa calmly yace "Keee"
kamar xata yi kuka ta juya ta kallesa, yace "Me ya kawo ki wanki
nan?" Ta buda manyan idanuwanta tace "Tap din mu fa ne ya lalace jiya
kuma....." Ya katse ta yace "Tashi ki bar wajen" Tace "To
ai na kusa gamawa fa" strictly yana d'an daga murya yace "Kwashe
kayan ki ki bar nan kar ki yarda in iso inda kike" ta dauke kai hade da
turo baki ta mike ta xubda ruwan gaba daya ta hade buckets din bayan ta xuba
yan kayan da ta wanke ciki ta kwashesu gaba daya ta bar wajen kamar xata tashi
sama ba tare da ta sake kallon inda yake ba, ta murguda baki bayan tayi nisa,
murya can kasa tace "Allah ya isa" Dai dai part na biyu da ya kasance
wani babban hadadden Bungalow ta tsaya, shi ma kuma bangaren na da nasa parking
lot din da xai dau motoci uku, ta dinga kallon sauran kayan da bata gama
wankewa ba kamar xata yi kuka, to ita yanxu ya xata yi da su, Ammi na ganin
bata gama ba sai ta fara mata fada yanxu tace tun daxu me take, kallon hanyar
da xata bi xuwa part din karshe tayi, ta tabe baki sanin ba lallai ma mai
sashin ta bar ta ta ta6a mata tap ba, tana ta tsaye can kuma dai ta wuce can
bangaren karshen, shi ma sashin bungalow ne sai dai bai kai nasu ba, tsarin ma
ba iri daya bane, a hankali ta ajiye buckets din hannunta dai dai tap din dake
opposite entrance din shiga parlor tana yi tana satan kallon kofar, cikin
dubara ta bude tap din yanda xuban ruwan bazai yi kara ba, ta tara bucket din a
karkace kar ma aji xuban ruwa ta ci gaba da daurayenta, sosai gabanta ya fadi
jin taku duk a tunaninta mai bangaren ce, mutumin daxu ne ke tahowa bata yarda
sun hada ido ba ta ci gaba da wankinta, ko kallon inda take shi ma bai yi ba,
bai kuma kai ga shiga parlon ba suka ji muryar wata tsohuwa tana cewa "Ni
wai ya nake jin kamar ana taba min pampo a wajen nan ne" da sauri ta kashe
tap din ruwan xata kwashi kayanta ta gudu sai ga tsohuwar ta fito, Sake baki
tayi tana kallon ta kafin tace "Waye kuma wannan, meye kike min kusa da
pampo?" Budurwar ta turo baki tace "To inna namu ya lalace..."
Inna ta katse ta da sauri tace "Da ya lalace ni na lalata maku?"
Budurwar tace "To wai ma ba daxu kika ce in xo in debo maki ruwa in kai
maki bayi ba, shine fa na zo xuba maki" Inna na mata wani kallo tace
"Ke din? Ke din da na sani ce xaki kai min ruwa bayi munafuka? bayan ba
Aisha sunana ba, to wllh ki kiyaye ni a gidan nan ruwana ba na banxa bane kar
ki sake xuwa min nan, kin lalata naku nima ki xo ki lalata min nawa saboda
mugunta koh, to uwar ki ce xata debo mun ruwan idan na tankin ya kare, haka
kawai ki bar ni da diddigin pampo duk tsutsa cuta ta kama ni in bar 'ya yana da
wahala, ke dai wannan yarinya ta Bukar muguwa ce wllh, shegen barnar ki ta fi
karfin ki, to wane 6era ma" ita dai Budurwar sai kallon ta take kamar xata
yi kuka, inna na xaro ido tace "Maxa dau min ruwana ki tafi ki juye min a
bandaki, ni dai a gidan nan duk wanda ya diba da hakkina gaskiya ban yafe ba
tunda abun haka ne, don kowa sai da aka dasa masa pamponsa amma don mugunta sai
ku wani kwaso shegun bokitan ku duk datti kuna kwashe min ruwa mugayen
yara" Ita dai tana tsaye wannan karan ta daure fuska sai kallon ta take, A
fusace inna tace "Baxa ki je ki juye min a bandaki ba ko sai nasa an kira
min Bukar ya taho duk inda yake yanxu?" Daukan ruwan Budurwar tayi fuuuu
ta wuce ciki, inna ta shiga parlor ta dauko wani karamin kwado ta kulle tap din
ta wuce cikin parlor tana cewa "Gwara in ta tsayawa ba ruwan nima da a xo
ana ta debe min a cuce ni" Tana shiga parlor ta kalli matashin dake xaune
kan kujera yana danna wayarsa, ta hade rai ta dau kyallen da take goge goge ta
ta fi gun kayan kallo ta ci gaba da gogenta tana cewa "Ka sake dawowa
karasa sauran fitsarar da ka mance baka yi ba kenan, wato duk wanda kayi jiya
bai isheka ba, to ni dai a fita a bar min parlor ba ruwana, ba katon banxan da
zan kula yau ta kaina nake, kaje can kayi ma uwar ka" shi dai bai tanka ta
ba sai danna wayarsa yake, Bayan wani lkci ya mike yace "Dama Abba ne yace
in xo in baki hakuri" daga haka ya nufi kofa fuska daure, da karfi Inna
tace "Imaan tunda mutumin nan ya shigo kinji ya ce min wani abu?? To ni
dai ba ni ka ba hakuri ba wllh, idan kuma ba ka yi hankali ba sae in iya fitar
har ofis in sami Ahmadu ynxu" Imaan ta rufe babban roban da ta jawo daga
karkashin gado tana kokarin daure alkakin da ta cika a leda jin inna ta sake
kiranta tace "Gani nan xuwa" window ta bude a hankali ta jefar da
ledan ta shiga bayi ta wanke hannunta da sauri ta fito ta shiga parlor fuska
daure tace "Meye kike kirana" Inna na nuna sa tace "Ke tunda
kika shigo kin ji muryar bawan Allahn can?" Imaan ta tabe baki tace "Wai
wa?" Inna tace "Mujaheed" Imaan tace "To ni na sani? Ni da
nake cikin daki" daga haka ta bi ta gefensa ta fice a parlon, sauran kayan
wankinta ta dauka ta xaga baya da sauri ta dau ledan alkakinta ta wuce part
dinsu, a hankali ta bude kofar parlon tana lekan ciki ganin Ammi bata ciki ta
wuce bedroom din ta da gudu ta kulle ta ajiye buckets din a bayi. Da yamma Ammi
ta shigo dakin ta sameta kwance tana bacci, Ammi tace "Imaan" bude
ido tayi a hankali, Ammi tace "Ki tashi daga baccin nan haka, yamma yayi,
kin kwaso socks din naki da kika wanke" tana murxa ido tace "Xan
kwaso" Ammi tace "Ga hijabs din ki da na wanke can clothe line din su
Anty ki tafi ki kwaso su ma sun bushe, don kawai yan gidan basa nan sai ki k'i
tafiya makaranta ko?" Ita dai bata ce komai ba, Ammi ta juya ta fita, xaro
ido imaan tayi ta mike da sauri ta shiga bathroom din ta ta matse socks din da
hula da inner wears ta xuba su a dryer na washing machine ta kunna sannan ta
fita, Tana kwashe hijabs din ta a clothe line da Ammi ta ce mai gadi ya bude
gate, wani rantsatsen mota ya shigo gidan direct parking space dake babban part
din ya taho, sai ga wata motar ta biyo bayansa xuwa parking space din, Mutumin
daxu da safe ne ya fito driver seat sanye da kananun kaya daga cikin motar
farko, wata yarinya da baxata wuce Imaan ba ta fito front seat din motar,
sannan wata mata da baxata haura hamsin da hudu ba ta fito back seat tare da
wata yarinya mai shekara ashirin, kana ganinsu kaga yan daki daya, Imaan ta
dauke kai tana ci gaba da abinda take, Bude dayar motar aka yi, wani mai kama
da Mujaheed Sak ya fito sai dai shi ya fi sa haske, Shima dogo ne kuma Mujaheed
ya girme sa da 4 years, mahaifiyarsa ce ta fito bayan motar da kanninsa duk
mata hudu su ma, murmushi mahaifiyar tasa tayi ganin Imaan tace "A'ah
wanki aka yi yan mata" Imaan tayi murmushi tana boye fuskarta tace
"Sannu da dawowa Anty" Anty tace "Sannu Imaan, ya Ammi fa"
Imaan tace "Tana gida" Kallon matashin da ke tsaye kusa da Anty yana
kallon ta tayi tace "Ina yini ya Yusuf" yace "Lafiya lau, Imaan
din daddy, sai dai nasan ba ke kika yi wankin nan ba" ta xaro ido tace
"Ni nayi fa" Anty ce "Toh shi xai maki idan baki yi ba banda
tsokana, share sa kin ji" tuni Mujaheed ya nufi entrance din shiga part
din su mahaifiyarsa Umma dake satan kallon Imaan da ta ki kallon ta ta bi
bayansa, Anty ma ta wuce Yusuf na biye da ita yana waigo Imaan yace "In ji
yau baki je tsokanan inna ba ta hada ki da daddy" Imaan tayi dariya tace
"Ni ina ruwana da ita ai na daina xuwa part din ta" Daga haka ta juya
ta wuce bangarensu. Da daddare Imaan na kokarin saka kayan baccinta ta kwanta
Ammi ta shigo dakin, tana kallon ta tace "Ki je Abba na kiran ki"
xaro ido tayi tace "Abba kuma Ammi?" Juyawa Ammi tayi ta fita, kamar
xata yi kuka ta saka hijab din ta ta fita tana tunanin kiran me Abba ke mata da
daddaren nan. A hankali ta bude kofar parlon Abba ta shiga bayan ta cire
takalmin kafarta, Abba na xaune a 3 seater cikin parlon Mujaheed na xaune shi
ma kan lallausan carpet din dake malale kasa, sai Umma dake xaune kan one
seater, Anty ma haka, Imaan ta karasa kanta a kasa ta xauna kasa kusa da Anty,
murya can kasa ta gaida Abba, Abba ya amsa yace "Ya karatu" tace
"Alhmdllh" yace "Imaan discipline din ki kenan rashin gaida na
gaba da ke?" Imaan ta daga kai tana kallon sa, ya daure fuska yace
"Ita Hajiya sa'ar ki ce da ba kya gaisheta a gidan nan?" Shiru tayi
bata ce komai ba, ya hade rai yace "I am talking to Imaan, kuma ki bar
kallona my friend" A hankali ta fara 6ata fuska tana jan yatsunta, lkci
daya ta fashe da kuka, Abba ya mata tsawa yace "Daman kuka kika samu don
ban xane ki ba yanxu" kuka take yi sosai kamar warce aka duka, Mujaheed ya
mike ya mata wani raxanannen tsawa ta mike da gudu ta nufi kofa, xai bi ta Abba
ya dakatar da shi yace "Rabu da ita M.A, Allah ya shiryeta" Umma ta
tabe baki tace "yaran yanxu da ba a sangarta su ba ma ya aka kare
ballantana wannan?" Anty ta mike ta fita parlon, Abba dai bai ce komai ba,
imaan bata xarce ko ina ba sai sashin inna, tana shiga parlon ta xube kan
kujera ta rushe da kuka, inna ta fito daki da sauri, Yusuf ma dake kwance kan 3
seater ya mike xaune da mamaki yace "Me ya faru Imaan" jikin inna na
rawa tace "Me ya samu Aishar?" Imaan ta ki cewa komai sai kuka, tuni
inna ta nufi kofa, cikin kuka Imaan tace "Ni ba abinda ya samu
Ammina" inna ta dawo tace "Ke dai ki dinga jin tsoron Allah, da yanxu
xuciyata ta buga ya kike son 'ya yana su yi, ya zaki shigo da kuka ki janyo min
wata fitinar ina xaune" Cikin rawar murya tace "Ko ba Umma bace"
inna tace "Wacece haka?" Imaan bata ce komai ba sai kuka, Inna tace
"Warcan mata mai kama da zabiya kike nufi wai, ko ba uwarsu fitsararren
yaron nan Mujaheed ba?" Imaan ta hadiye abu da kyar tace "Ita"
Inna ta share wani xufa tace "Toh xata ga barbadin rashin mutunci yau
kuwa, me ta maki?" A hankali Imaan tace "Shine taje ta gaya ma Abba
wai ni bana gaisheta alhalin fa ko na gaisheta bata amsawa, shine Abba ya
kirani...." Sai kawai ta fashe da kuka, inna tayi wani murmushi tana gyada
kai tace "Biri yyi shige da mutum, Sai aka yi ya da ya kira ki" imaan
ta kalleta cikin shesshekar kuka tace "Yana min fada....." Tuni Inna
ta fice parlon, Imaan ta saci kallon Yusuf da yyi tagumi yana kallon ta ta mike
tana turo baki ta fita. Inna na isa bangarensu Yusuf kai tsaye parlon Abba ta
wuce, har sannan Abba na xaune da Umma a parlon sae Mujaheed, gaba daya daga
kai suka yi suna kallon ta, inna ta tsaya tsakiyar parlon tana kallon Abba tace
"Yanxu yaro tun da sauran numfashin Bukar a duniya zaka sa ma 'yar sa ido?
Yanxu a kan wannan matar zaka ci mutuncin yarinyar da lafiya ma bai isheta ba
sai dai godiyar Allah? Yanxu Ahmadu duk son da d'an uwanka ke maka xaka rufe
ido a hadu da kai a ci mutuncin yar sa kwaya daya tal..." Kunce ha6ar
xaninta tayi tana matsar kwalla tace "Naga abinda ya isheni bai ishi Allah
ba..." Abba kasa cewa komai yyi da farko, can yace "Haba inna, wannan
wace irin magana kike...." A fusace tace "Ohh yare nake maka da xaka
tambayeni wani irin magana nake, to wllh bari ka ji, a kan Fatima a gidan nan
ina iya sa6a ma ko wani mahaluki, kuma baxata gaida matar taka ba, ita katuwar
gaida mutane take?" Mikewa Mujaheed yyi ya nufi kofa kamar xai tashi sama
inna ta bi sa da wani shegen kallo, sannan ta ja tsaki ta maida dubanta kan
Abba dake ta kallonta ta daure fuska tace "Ahmadu yaushe rabon ita matar
taka ta kai kafafuwanta bangarena gaisheni? Lallai... ni a su wa xata je
gaidawa? Ni din banxa xata gaidar?? To hirrrr wllh, kada wanda ya kara sa ma
jikata baki a gidan nan idan ba haka ba sai in sa Bukar ya koma daya gidansa
dama shi ya nace xama waje daya da kai, tunda yar sa xa a takura gwara kawai ya
bar gidan...Dubi fa Mujaheed haushi ya ji yanxu don na ambaci uwarsa, kana gani
saura kiris ya bangaje ni in fadi duk cikin bacin rai, to uwa ta fi uwa ne??
don me kai ma baxa ka tattala ni haka ba, duk ka bi ka daure mata kugu bata
gani na da gashi a gidan nan, to mu xuba da ita xan ga ko ita ta haifo min kai
duniyar, wannan ai raini ne wllh, wai taji haushi Imaan bata gaisheta ba to
baxata gaidata din ba, kar ta kuskura ta sake sa min jika a baki tayi ta kanta
kawai a gidan nan" shi dai Abba shiru yyi kansa a kasa, Umma ta rungume
hannunta daga xaune tana kallon wani direction din, Abba ya dago yana duban
mahaifiyar tasa yace "Kiyi hakuri Inna" ta maka masa wani kallo tace
"Sai dai ka ba matar ka hakuri tunda na 6ata mata rai" Tana kai wa
nan ta fice. Imaan har ta kusa part dinsu taga shukanta na wake da tayi a
babban gwangwani a madadin assignment da aka basu a Agricultural science, a
yashe duk root din ya fita daga cikin gwangwanin, ta xaro ido ta ta fi wajen da
sauri, lkci daya hawaye ya kawo idonta tace "Wllh nasan Rahma ce xata
kwabar min da shuka na" sai kuma ta fashe da kuka na takaici ta durkushe
wajen, ba ta lura ba har Mujaheed ya iso wajen, ta juya hawaye sha6e sha6e
idonta tana kallon sa ta sake rushewa da kuka, ya daure fuska yana kallon
kafarta yace "Me ya faru?" Ta mike cikin rawar murya tace "Yaya
kalli fa abinda Rahma tayi ma assignment dina kuma ten marks ne, xa muyi
submitting ranan Friday, kalli fa har ya girma, don nawa duk yafi nasu sai ta
kwabar min" ganin sai hararanta yake ta juya ta wuce tana ci gaba da kuka,
fixgota yyi yana mata wani kallo yace "Shi Abban kika tafi kika yi
reporting gun Inna?" Lkci daya ta tsaida kukan da take bayan ta gane
biyota yyi, ta fizge hannunta ta kwasa a guje, kiris ya rage ya kamata ta shige
parlonsu ta banko kofar tasa key, Ammi dake xaune parlon tana kallo ta mike
tace "Meye haka Imaan?" Dariya ta fashe da ta wuce daki da sauri tace
"Sauri nake in xo in kwanta fa Ammi" tana shiga bedroom din ta ta sa makulli.
Har Imaan ta fara bacci wajajen karfe goma Ammi ta bude kofar dakinta, bude ido
tayi Ammi ta hade rai tace "Uban me kika debo ma inna a dakinta?" Ta
mike xaune da sauri tace "Na debo mata abu kuma? Haka ta ce?" Ammi
tace "Kinga na raba ki da xuwa sashinta ki dauko min magana ba ki ji ko?
To ki fito mata da duk ma abinda kika daukan mata gata can bakin kofa"
Imaan ta turo baki ta sauko daga saman gadon ta bi bayan Ammi da ta fita, ido
hudu suka yi da inna da ke tsaye bakin kofa ta tsuke fuska, Imaan ta hade rai
tace "Ni me na dibar maki xaki biyo ni cikin daren nan" Inna tace
"Duk cikin jikokina babu mai ta6a min kaya ban basa ba sai ke, duk kece
mai mugun halin nan don haka maxa ki fito min da alkaki na, don ba a rame na
bar sa ba ina sane da abinda nake ba fara haukacewa nayi ba" Ammi dai ta
nemi waje ta xauna, Imaan ta 6ata fuska kamar zata yi kuka tace "Wai
yaushe naje da har xan dibar maki kayan ki ni da ba ci ma nake sosai ba, to ma
ba xaki gansa hannuna da xan fita ba" Wani tsawa Ammi ta yi mata tace
"Kin tafi kin dauko abinda kika diba ko sai na mare ki" Imaan ta
harari inna ta wuce kitchen sai ga ta ta fito da ledan alkakin, Inna ta saki
baki ta warce ledan tace "Naga Ikon Allah ni Asabe, da yake Aisha ce ta
xauna ta min tuyar bayan ta kwa6a dole ki kwaso ki kawo maku ku ci, to ni kar
in sake ganin kafafuwanki a bangarena don halin ki abun tsoro ne, wannan ai ba
tarbiya aka maki ba ki shiga har karkashin gadon mutane ki jawo kwalla ki debe
min kayana, yanxu banda jinin ka jininka ne kin xata idan na ja Allah ya isa baxai
bi ki ba, ni wllh darajar d'a na kike ci a gidan nan gaskiya, kar in sake ganin
ki a parlona ni dai dama baki tsinanamin komai sai dai ki malale kan kujera
kina mik'a, duk kin ru6ar min da kujeru" tana kai wa nan ta juya ta wuce,
Imaan bata yarda ta kalli Ammi ba ta wuce daki ta rufe kofa tayi kwanciyarta
tana turo baki.
Maa sha Allah, I am back by Allah's grace... daily update in
sha Allah, but if schl shud resume anytime soon xan dakata da posting for some
weeks coz I will be having exams in sha Allah. Hope you guys will love the
*book*, though I know I never disappoint my fans when it comes to writing in
sha Allah....
Khaleesat Haiydar...
[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
2......
Washegari da safe Imaan ta fito parlor shirye cikin well
ironed uniform dinta da beret dake kanta, kitchen ta shiga gun Ammi, Ammi dake
juye ruwan shayi flask tace "Yau ma baki yi combing gashin ba koh" ta
jingina da kofa cike da shagwaba tace "Wllh Ammi xafi, baxan iya ba"
Ammi bata ce komai ba ta gama xuba ruwan a flask ta xuba mata nata a cup dinta
ta hada mata shayin sannan ta mika mata, Karba Imaan tayi ta fita xuwa dinning,
Ammi ta kai mata dankali da kwan da ta soya mata ta ajiye tana kallon agogo
tace "Kiyi sauri kar su jira ki don Allah" Imaan ta xaro ido tace
"Ammi kullum fa ni ke jiransu" Ammi tace "Toh kar kiyi
saurin" daga haka ta wuce kitchen don yin wanke wanke, imaan na gamawa ta
kai plate din da cup kitchen, ta dauko jakarta, Ammi tace "Ki duba gaban
dressing mirror a daki na akwai duba daya ki dauka, dakin ta shiga ta dauko sannan
ta fito tace " Ammi sai na dawo" Ammi tace "Ohk Allah ya tsare
kiyi addu'a kafin ki fita, and you make sure baki mance ko wani book ba tunda
hankali bai ishe ki ba" dariya kawai tayi ta fita gidan bayan tayi addu'a,
Can parking space din su Yusuf ta tafi ta tsaya don nan take jiransu, yawanci
Yusuf ke kai su wani lkcin kuma Anty ta ajiye su tunda tsohon driver dinsu ya
tafi, Tana ta tsaye jikin mota ta hango plant din su Ummi, Rahma da Maimoon don
duk ajinsu daya wato ss2, kamar xata yi kuka ta dinga kallon waken nasu da duk
ya fito da ganye, ga nata can an lalata mata, kallon entrance din gidan tayi
lkci daya ta nufi wajen da plant din suke da kafa ta haure gaba daya biyun
banda na maimoon don kowa ya sa sunansa, sai da ta tabbatar roots din sun fita
sannan ta koma jikin mota da sauri, Ummi ce ta fara fito sanye cikin uniform
irin na jikin Imaan sannan Rahma sai Maimoon, Babu wanda ya kalleta cikin su
banda Maimoon da tace "Imaan kin gama maths assignment din ki" Imaan
tace "Ehh na gama" Maimoon tace "Toh idan mun shiga mota xan
kwafa plss ban yi ba" Imaan tace "Ohk" Mujaheed ne ya fito rike
da makullin mota fuska kamar hadari, Imaan ta xaro ido tana kallon Maimoon
murya can kasa tace "Shi xai kai mu?" Maimoon tace "Ehh ya Yusuf
baya nan ya tafi Zaria daxu, shine Anty tace ya Mujaheed ya ajiye mu, shine
yake fushi" Imaan ta turo baki bata ce komai ba yana bude motar ta shiga
back seat tare da Maimoon da Rahma, Ummi ta shiga gaba, har suka bar gidan babu
wanda yace komai cikin su, Imaan ta bude jakarta ta ciro assignment din ta ba
Maimoon, tafiyar minti ashirin ke kai su makarantar su, amma saboda gudun da
yyi cikin few minutes suka iso, yyi parking dai dai makarantar yana kallonsu da
kyau yace "Dama kuna tashi ku fara trekking din dawowa gida don baxan xo
daukan kowa ba" a hankali Ummi tace "Ya M.A ai soon Abba xai dau mana
wani driver fa" yace "Sauka malama" bude motar tayi ta fita,
tuni Imaan da Maimoon ma suka fita suka shige cikin makarantar. Anty ce ta xo
daukan su bayan sun tashi ranan, Anty na kallon Imaan dake ta yamutse fuska
tace "Me ya faru Imaan" a hankali ta nuna mata kanta, Anty tace
"Toh idan kin koma gida kin ci abinci sai ki sha magani ki kwanta ki
huta" to kawai imaan tace, ko da suka isa gida har bacci ya dauketa Maimoon
ta tasheta ta bude ido, Anty tace "Toh shiga gida imaan" kai kawai ta
gyada mata ta fita ta nufi part dinsu tana dingishi. Ruwan xafi Ammi ta hada
mata ta shiga tayi wanka sannan ta ci abinci, Ammi ta bata magani tace
"Sai ki daure kiyi shirin tafiya islamiyya it's too early ki fara fashi
this week, today is Monday" Imaan bata ce komai ba, Ammi na fita ta koma
kan gado ta kwanta kamar xata yi kuka, hudu da minti biyar Ammi ta shigo dakin
jin shiru bata fito ba, ganin har bacci ya dauketa ta kai hannu jikinta taji da
dumi, girgixa kai tayi ta juya ta fita, Maimoon ne ta shigo parlorn sanye da
uniform din islamiyya, Ta gaida Ammi sannan tace "Ammi imaan muke
jira" Ammi tace "Bata jin dadi ku tafi Maimoon" a hankali
Maimoon tace "Allah ya sauwake" sannan ta fita, Ammi na girkin dinner
a kitchen wajen karfe biyar Imaan ta fito daki, wani internal heat kawai ta ke
ji, kuma tana kunna Ac tasan sauran ta dinga lekan kitchen kamar xata yi kuka,
a hankali ta nufi kofar fita ta bude kofar yanda baxa aji kara ba sannan ta
fice xuwa part din inna don ta je ta kunna Ac, Inna na wanke gun tap dinta da
take sa ma kwado ta daga kai tana kallon Imaan tace "Baki tafi islamiyyar
bane yau" Imaan ta turo baki tace "Ehh" daga haka ta shige
parlon, kunna Ac tayi ta kwanta kan kujera dake kallon Ac din ta lumshe ido,
inna na gun tap din har sannan sai ga Mujaheed, ta mike tana kallon sa tace
"Baka ji bayana ba Mujaheed kamar xai balle, ko kai baka ga yanda wajen
pampon yayi haske ba tun daxu nake ta gurza gashi sai kyalli yake, ai kazanta
bata da kyau, yanxu kaga ko tuwo aka xuba a wajen mutum xai iya xaunawa ya
ci" Mujaheed dai bai tanka ta ba ya shige parlorn bin bayansa tayi, ya
ajiye ledan hannunsa yace "Gashi Abba yace a kawo maki" tace
"Toh Allah yayi masa albarka... Dama raina na son kayan marmarin" xai
fita Inna tace "Mujaheed kaga yarinya nan abinda ya kawota kenan ta xo ta
kunna Ac wata cutar ta kamata ace ai a parlorn inna ne, to ni dai ba ruwana ka
kashe min kayana taje can ai su ma suna da shi, duk yanda aka yi kuma uwar
hanata kunnawa tayi shine ta taho ta kunna nawa salon ace parlorn inna to Allah
ya fi ki babu me sa ni a bakin duniya" Mujaheed ya kalli Imaan da tayi rub
da ciki kan 3 seater din ya tabe baki xai fita Inna tace "kai ya ina maka
magana xaka fita, idan uwar ka Rukayya ce xaka mata haka Mujaheed?" Fuska
daure ya juyo ya xauna yana kallon ta da kyau yace "Wllh idan kina sa
mahaifiyata a baki Hajiya xa mu kwashi yan kallo dake a gidan nan, komai sai
kice uwata" Inna ta saki baki tace "Kai ni kake daga ma murya"
yace "Toh ki daina sako mahaifiyata a xancen ki idan baki son a daga maki
murya, ke kwata kwata rayuwarki baki son xaman lafiya daga kice wannan yayi
maki sai ki ce wannan yayi maki...." Inna ta gyada kai tace "To ka
tara kuma ka samu, xaka san ni ka fada ma bakar magana" Tana fadin haka ta
kashe Ac dinta, Imaan ta mike xaune kamar xata yi kuka tace "Meye xa ki
kashe min inna" Inna tace "Bukar yasa na kashe, na ku lalacewa yayi
xaki taho min nan, ni dai a daina xuwa ana sa ni magana ana min rashin kunya
gaskiya" imaan ta marairaice tace "Don Allah inna ki kunna xafi nake
ji a cikin jikina" Inna tace "Toh baxa ki ji xafi a jikin ki ba ga
magani nan an kawo maki tun daga Nijar kin ki amsa sai yawo kike min da hankali
kamar ni xai amfana, duk tashi fadin da nake a kanki ba ki gani, mutum bai san
inda xai dace ba, idan an baki magani sai kiyi biyayya ki amsa ki sha sai kiga
Allah ya yaye maki wannan ciwace ciwacen da ba a san kansa ba" Imaan tace
"Wa yace maki ba a san kansa ba, to ai da shi aka haifeni kuma ba warkewa...."
Inna tace "Oh oh Allah, Mujaheed kaji irin fitinar da take ja ma kanta da
bakinta ko, kai wannan 'ya ta Bukar anyi doluwa wllh, ke fata kike kar ki warke
d'a na yayi ta cacan kudi, duk cikin jikokina babu mara tunani dama irin
ki" Imaan ta hade rai tace "Ehh na ji, ki kyaleni da ciwo na Babu
ruwanki, baxan kuma sha maganin ba don ina da na asibiti da nake sha, ni bance
ki dinga amso min magani ba dama ai" inna tace "Kada Allah ya sa ki
sha, to ni Allah na tuba a haka ma wa xai yi sha'awar aurem ki yau ciwo gobe lafiya
duk tattalin arxikinsa ya kare a asibiti, tun kina mitsitsiyar ki nake wahala
da ke kan maganan magani shi sa ma kika yi kyan gani, ke da kike kamar
kwarangwal da taimakon Allah da taimkona da magungunan da nake amsar maki gun
malamai shine kika marmaro, in dan ta uwar nan taki ce ai sai dai ki mutu tana
kunshe daki ba fita xata yi ta nemo maki magani ba tana jiran na asibiti, Toh
wllh daga yau na fita harkan ku ki ji da ciwon ki nima inyi ta kai na"
Imaan ta fashe da kuka tace "Ehh naji, ki kyaleni tunda ba dole bane shan
maganin ki" daga haka ta fice daga parlorn da gudu, Inna tace "Duk xa
ku yi bayani bari iyayen naku su dawo" Mujaheed ya tabe baki ya mike ya
fice mata a parlorn shi ma. Imaan na kwance kan kujera bayan isha Ummi ta bude
kofar parlorn tana tsaye daga bakin kofa tace "Abba na kiran ki a bangaren
Inna Imaan" daga haka ta fita, Ammi dake cin abinci xaune parlorn ta kalli
Imaan da ta wani juya bata dai ce komai ba, bayan kusan minti biyar Ammi tace
"Amma dai kin ji abinda tace Imaan" Ta juyo kamar xata yi kuka tace
"Wllh Ammi kafana ciwo yake min ban san ko xan iya tashi ba" Ammi ta
galla mata wani harara tace "Sai ki rarrafa ai tunda baxa ki iya tashi
ba" hawaye cike idonta ta mike ta sa Hijab ta fita tana taka kafar da
kyar. A hankali ta bude kofar parlorn Inna ta shiga da sallama, Abba ne xaune
parlorn sai Inna da Anty, Imaan ta sunkuyar da kanta ta karasa kusa da Anty ta
xauna kanta a kasa ta gaida su, Abba da Anty kadai suka amsa, inna ta wani
tsuke fuska, Imaan dai bata ko kalleta ba, Inna tace "Wato shi Mujaheed
din jira yake kaje ka ciccibo sa da kanka koh?" Abba ya kalli Imaan yace
"Tashi ki tafi can bangaren ki kira min Yayanku" Imaan ta mike ta
d'an harari inna ta gefen ido ta fice a parlorn, tana isa part din su Mujaheed
ganin bbu kowa parlor sama ta haura ta tsaya corridor tana kallon door din
dakinsa har ta mance rabon da ta je kusa da kofar, bude kofar Umma aka yi sai
ga shi ya fito, ta matsa da sauri don kusa da kofar dama take tsaye tace
"Abba yace in kira ka" ko kallon ta bai yi ba ya fara sauka stairs,
ta murguda masa baki ta bi bayansa, har suka isa part din Inna bai juya ba, ya
bude kofar ya shiga da sallama, kusa da Anty Mujaheed ya durkusa kansa a kasa,
Abba sai kallon sa yake yana girgixa kafa, Imaan ta shigo parlorn ganin inda ya
durkusa tace "Waje na ne nan" Murmushi Anty tayi, shi kam ko kallon
ta bai yi ba balle ya motsa, Inna tace "Ahmadu na fa gaji da xama nan
kamar warce xa a ma gafara, aji da ni in tashi in shiga ciki in kwanta"
Abba ya kalli imaan yace "Samu wani wajen my friend" ta harari
Mujaheed ta koma wani wajen ta xauna, Abba na kallon Mujaheed yace
"Muhammad ita innar ka mayar abar wasar ka a gidan nan?" Inna ta tabe
baki tana jijjiga kafa, Mujaheed bai dago ba kuma bai ce komai ba, Abba yace
"Am I not talking to Mujaheed" ya dago a hankali yace "Abba kayi
hakuri don Allah" Abba yace "Stupid, ni ma kake ba hakuri?" Ya
kalli inna yace "Kiyi hakuri inna" dakatar da shi tace "A'a
malam a gaban ubanka xaka ce min inna kenan, wllh Ahmadu daxu yana nuna ni da
yatsa a can bakin kofar kamar xai make ni Hajiya yace min, ni na ma xata duka
xai kai min bayan ya gama kashedin, to gaskiya da sake, sam yaranka basu da
d'a'a basu da kunya Ahmadu, isuhu ne kadai dama mai gudun bacin raina duk da
shi ma ko aiki xai kashe ni baya taimakona, to ynxu Mujaheed da wani ne da ya
xo ya gan ni durkushe ina faman gurje gun pampo ba amsa xai yi ba ya taya ni,
to wllh bai amsa ba sai xagina ma ni da yayi daga karshe, a xo har sashina a
dinga ci min mutunci, to hirrr don duk ranan da aka isheni tattara kayana xan
yi in bar gidan nan kuma sai anyi shekara duba ana nemana" Mujaheed ya
d'an daga kai ya kalleta ta gefen ido ya maida kansa kasa, Abba dai bai iya
yace komai ba, Anty tace "Kiyi hakuri inna, a yafe masu" Inna tayi
kasa da murya tace "Wllh Amina daga nace kai kuwa Mujaheed haka kake ma
Mamarka a gida ina ma magana xaka wuce, kuma fa cikin lallami nayi tambayar
kawai ba sai ya sakar min aradu a kai ba, ita kuma wancan lankwasasshiyar mai
kama da yar tsana bbu abinda ta mance bata gaya min ba daga nace Imaan ga
maganin da na amso maki saboda ciwon ki da ba a san kansa ba ba a san dalilinsa
ba, wllh Ahmadu sae kaga wanke ni da yarinyar tayi tasss har da ce min ba
ruwana da ciwonta kuma ciwon ba me warkewa bane" Imaan ta fashe da kuka har
da shessheka, Abba yyi mata tsawa cikin rawar murya tace "Abba xagina fa
ta ke yi wai...." Abba ya dakatar da ita yace "Keep shut" ta
hadiye abinda xata ce tana hawaye, Mujaheed yace "Kiyi hakuri Inna"
Inna tace "Atoh ya xan yi idan ban hakura ba, dama wanda aka cuta ake ba
hakuri, amma daga kai har ita kar in sake ganin kafufuwanku a bangarena, tunda
kun raina ni, Isuhu da Maimuna sun ishe ni" Fada sosai Abba ya dinga ma
Mujaheed da kansa ke kasa, inna sai matsar kwalla take ita a dole an 6ata mata
rai, hakuri Mujaheed ya kara bata, Anty ta sa Imaan ma ta bata hakuri, mikewa
Imaan tayi da sauri ta fice parlorn tana kuka, Inna tace "Sai ubansa na
magana yayi ta sinne kai kamar na kirki alhalin crooo kenan ku ke gani, kar ka
sake xuwa min sashi ni dai na gama magana" Mujaheed bai kalleta ba balle
ya tanka ta ya mike ya fice parlorn, can kusa da wani flower ya ga Imaan
durkushe tana kuka, ya dinga hararanta har ya isa wajen da take, ta mike cikin
rawar murya tace "Yaya don Allah kai kaji na xage ta daxu?" Ba tare
da ya tsaya ba yana ci gaba da tafiya yace "Ke ma ai ba dukan ki naga aka
yi ba" Ta bi shi da kallo tana shessheka.
[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan*⭐🌟
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
3......
Imaan ce xaune kitchen sai faman xuba surutu take ma Ammi
dake girkin dinner a kitchen, yar skirt
ne jikinta sai ves da yake ranan alhamis ne babu islamiyya, Ammi dake ta
saurarenta ta tabe baki daga karshe tace "Aikin kenan sai dai ki cika
mutum da surutu ba taimakon fari balle na bak'i" shiru Imaan tayi tana
kallon Ammi, Ammi ta kalleta ganin yanda mood dinta ya canxa tayi murmushi tace
"Toh ci gaba ina jin ki" sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba,
Ammi ta karasa kusa da ita tace "I was joking sweetheart, tafi ciki let me
fry some onion and pepper" mikewa Imaan tayi a hankali xata wuce Ammi ta
bi ta da kallo har ta fita, Ammi ta jingina da cabinet din kitchen din ta sauke
ajiyar xuciya, can ta nufi kofa ta fita don bata son tayi bacci coz shine next
abinda xata yi in har ta shiga daki, dakinta Ammi ta shiga ta sameta har ta
kwanta, Ammi tace "Baxa kiyi bacci ba yanxu yamma yayi, je dakina xa ki ga
leda da atamfa a ciki kan dressing chair ki kai ma su Anty kice ankon bikin
Halima" Imaan ta mike xaune tace "Ammi to na mu fa" Ammi tace
"Sai ki kirata ki tambayeta ban san ko an fidda naku ba" Imaan tace
"Toh, Anty kawai xan nuna ma?" Ammi tace "Ehh sai ki ce mata ta
nuna ma Hajiya, na dai fita ai" daga haka Ammi ta fita dakin, imaan ta sa
hijab har kasa kan kayana jikinta ta fita ta dau ledan ankon a dakin Ammi, tun
da ta shiga parlonsu Anty take yamutse fuska ta dalilin yaji dake tashi sosai
daga kitchen, lkci daya ta rike numfashinta, har xata juya ta fita sai ta nufi
stairs da gudu don ta shiga dakin Anty, tsarkewa tayi sbda rike numfashin da
tayi ga kuma gudun da take, lkci daya ta fara tari sosai breathing dinta na
sama, dai dai corridor ta fadi tana kokarin jan numfashi, Maimoon ta fito dakin
Anty ganinta ta durkusa gabanta da sauri tace "Subhanallahi me ya faru
Imaan" sound din faduwarta yasa Mujaheed ya fito daga bedroom din sa,
ganinta a kasa ya kalli kofar Ummarsa kafin ya karasa da sauri ya dagata yana
kallon Maimoon da ta rikice yace "Tafi ki karbo inhaler dinta da
sauri" da gudu ta sauka xuwa part din su Imaan, Mujaheed ya bude kofar
dakin Anty ya shigar da ita ya xaunar da ita kasa ya jinginar da ita da gado ya
cire Hijab din jikinta, dai dai nan Anty ta fito daga bandaki, a rude tace
"Subhanallahi, Asthman ne, garin Yaya? Ko in amso inhaler dinta" yace
"Maimoon taje amsowa" sosai imaan xata baka tausayi saboda ynda take
struggling da numfashinta, Mujaheed ya mike ya fita don bin bayan Maimoon suka
kusa cin karo bakin kofa, fixge inhaler din yyi ya juya ya koma dakin ya
durkusa gabanta ya kai mata baki, dafe hannunsa tayi tana inhaling, Anty dai na
tsaye sai kallonta take cike da tausayinta, bayan wani lkci numfashin nata ya
fara fita a hankali yana kokarin dawowa normal, Anty ta xauna gefen gado tayi
tagumi tana kallonta, Ummi da Rahma na tsaye bakin kofar suna kallonta su ma,
Har sannan Mujaheed na duke gabanta idonsa a kanta, muryar Umma suka ji tana
cewa "Lafiya me ya faru ku ka tsaya cirko cirko bakin kofa?" Rahma
tace "Asthma ne ya tashi wai" Umma ta leko dakin ganin Mujaheed ta
wani xaro ido tace "Me Mujaheed yake a nan?" Mikewa yyi da sauri, ta
wani hade rai tace "Tambayar ka nake, me ka shigo yi, ko kayi kama da
likitan ta ne?" Ya girgixa kai yace "No na xo wucewa ne...."
Dakatar da shi tayi tana masa wani shegen kallo tace "Sai ka tsaya aikin
da ba lada koh? To ka shiga hankalin ka, Ka guji bacin raina, basu da number
likitan ta ne ko kuma neman suna kake?" Shiru yyi bai ce komai ba, Cikin
tsawa tace "Xo ka fita malam bana son shishshigi da kwala kai a faranti,
kanwar uwar ka ko ta ubanka?" Bai ce komai ba ya kalli Imaan da Anty ke
kokarin kwantarwa kan gado ya juya ya nufi kofa xai fita, Anty ta tabe baki
tace "Ciwo dai bai wuce kan kowa ba, ita ma ba ita ta doro ma kanta
ba....." Umma ta katse ta da sauri tace "Allah yayi mana tsari da
irin wannan ciwo nata, ya tsari jikokinmu da tatta6a kunne, a rayuwar nan ta
ynxu wa enda ba sickler ba ma ya suka kare, ae irinsu ne ke tsiyata namiji a
sintirin asibiti...." Tsaye Mujaheed yyi bakin kofa yana kallon Umma, Anty
ta wani hade rai tace "Kinga ki daina kiranta da sickler ita din ba
sickler bace, Allah kuma yyi mata tsari da shi" Umma ta wani tabe baki
hade da dariya tace "Kwa dinga boye ma wanda ku ka raina ma wayo, Allah
dai ya ba kowa lafiya...." A hankali Mujaheed yace "Umma ba fa
sickler bace, she is just a carrier...." Umma ta maka masa wani kallo tace
"Meye maraban dambe da fada? And did you have any problem with her being a
sickler or not da har kake karyata ni Mujaheed?" Bude kofar yayi ya fita
dakin bai ce komai ba, ta ja tsaki ta fice ita ma. Anty ta girgixa kai ta zauna
kusa da Imaan da ta lumshe ido numfashinta na sauka a hankali tana mata sannu,
sai da ta ga alamar tayi bacci sannan ta mike ta fita, Imaan bata dau lkci tana
bacci ba ta tashi ta dalilin ciwo da kirjinta ke mata, ta dinga juye juye kan
gadon hawaye na xuba idonta, bude kofar dakin aka yi Mujaheed ya shigo, ya
karasa kan gadon yana kallonta, daure fuska yyi yace "Me ya faru
kuma?" Kirjinta ta nuna masa ta fashe da kuka, yace "Toh kukan ne xai
sa ya daina ciwo, tashi xaune" mikewa tayi ta xauna da kyar, sai ga Anty
ta shigo dakin, da sauri ta isa gadon tace "Me kuma ya faru Imaan, are you
feeling pain anywhere?" Ta gyada kai tana nuna kirjinta, Anty ta dau Hijab
ta nufi kofa tana cewa "Bari in je in kwaso magungunanta dai" Xaunawa
Mujaheed yyi gefen gadon, ta koma xata kwanta yace "Kar ki kwanta" ta
jingina da gadon tana goge idonta, ba a dau lkci ba Anty ta dawo da ledan
maganin gaba daya, Mujaheed ya amsa yana duba maganin ya cire mata wanda xata
sha, still yyi jin an bude dakin Umma, sai kuma ya ji muryarta tana tambayar
inda yake, tashi yyi da sauri ya tafi bayan kofa ya tsaya, Anty ta tabe baki ta
balli maganin ta dau table water ta mika ma Imaan, bude dakin aka yi Umma ta
kare ma dakin kallo kafin ta tabe baki ta kulle, Shi dai yana tsaye bayan
kofar, Anty ta sa Imaan ta kwanta bayan ta sha maganin sannan ta kallesa tace
"Don Allah ka fita min a daki malam, tunda aikin xumuncin ma ba so ake
kayi ba, kai ma kuma tsoron yi kake, yau ko da ace baka san Imaan ba a matsayin
ka na likita ka ganta a wannan hali ai baxa ka ki taimaka mata ba balle tana
yar uwarka halak malak, Allah dai ya shiryi mahaifiyar ka" shi dai bai ce
komai ba, bayan karin mintuna uku ya bude dakin ya fita. Anty na xaune kan
darduma bayan ta idar da magrib Imaan ta tashi daga baccin da ya kara dauketa,
Anty tace "Sannu ya jikin Imaan" a hankali tace "Na ji
sauki" Anty tace "Toh shiga bayi kiyi alwala ki xo kiyi sllh" ba
musu ta mike ta shiga bandakin ta dauro alwala ta fito Anty ta mike kan
darduman ta fita, Imaan ta sa Hijab dinta ta hau kai ta tada sllh, tana ta
xaune kan darduman bayan ta idar sai ga Anty ta shigo da plate din abinci
dakin. Imaan na gama ci ta mike rike da plate din tace "Anty sae da
safe" Anty tace "Au baxa ki kwana nan ba" murmushi tayi ta make
kafada ta nufi kofa, Anty tace "Toh baki fada min ko na meye atamfar
ba" Ta juyo da sauri tace "Lahh, Ammi ce tace in kawo maku ankon
bikin Anty Halima" Anty tace "Ashe abu ya xo dai, toh ki ce mata xan
shigo gobe" Imaan tace "Toh" Anty tace "Allah ya sauwake
Imaan" murmushi tayi a hankali tace "Ameen" daga haka ta fita,
tun da ta sakko downstairs umma ke mata kallon tsana tana tabe baki, Imaan dai
bata ko kalleta ba ta nufi kitchen rike da plate din, Rahma ce kitchen din ta
gama wanke wanke, sai Mujaheed dake tsaye yana xuba ruwan Lipton daga teapot a
cikin mug, Imaan xata ajiye plate din, Rahma tace "Kinga plate mai datti a
wajen ne malama" turo baki tayi ta dau morning fresh ta bude xata wanke
plate din, Rahma tace "Ya M.A in debar maka abincin ne xan fita?" Ya
harareta yace "Abincin da ku ka cika yaji ko wanda ba yaji?" Yar
dariya tayi tace "Ya Mujaheed yajin fa ba yawa" tsaki yyi yace
"Ance maki ban yi tasting abincin bne ku dinga cika ma mutane ya ji a
abinci kamar mayyu" Tace "Toh in maka cous cous?" Yace "I
will take tea" Imaan ta gama wanke plate din ta juya ta fita kitchen din.
Kallonta Ammi ta dinga yi bayan ta shigo tace "Ya jikin Imaan" tayi
murmushi tace "Na ji sauki Ammi" daga haka ta nufi dakinta Ammi ta bi
ta da kallo. Karfe sha daya saura Ammi ta shiga dakin Imaan, ganin tayi bacci
ta tasheta tana mika mata wayar hannunta tace "Me ya sa kika kashe wayar
ki" Imaan na murxa ido tace "Kila mutuwa yyi ba charge" Ammi
tace "Toh idan kin gama ki maido min wayata daki" Imaan tace
"Toh" sannan ta kai wayar kunne tace "Daddy ina yini" Daga
daya bangaren ya amsa yace "Why is ur phone switched off" ta
langwabar da kai tace "Daddy ban sa a charge ba tun jiya" yace
"Toh kiyi kokari ki sa ya jikin?" Tace "Naji sauki, daddy ina
missing dinka yaushe xaka dawo?" Yace "Weekend in sha Allah" ta
wara ido cike da jin ddi tace "Plss daddy ka dawo week end din kar ka
daga, wllh ina son in ganka" kamar xata yi kuka ta kare, yyi murmushi yace
"Sure dear, plss ki daina wasa da shan drugs din ki kinji" tace
"Ina sha Allah daddy, har yanxu Dr ma bai xo ba" yace "Ehh mun
yi waya daxu yace bai dawo ba" Imaan tace "Toh" yace "Sleep
tight dear, banda kunna Ac" yar dariya tayi tace "Toh daddy
byeee" katse wayar tayi ta mike ta kai ma Ammi daki sannan ta dawo dakinta
ta shige duvet. Yau Friday Imaan na dawowa schl bayan tayi wanka tana kokarin
saka kayanta taji k'aurin abincin da Ammi ta bar mata a kitchen kan gas don
tana shigowa gidan Ammi ta fita kasuwa yin cefane, da gudu ta fita daure da
towel don kashe gas din don dama sae da Ammi tayi mata kashedi kan cewar kada
ta yarda abincin ta ya kone, muryar inna ta ji a balcony tana cewa "Aa
kawai ni dai naga kwana biyu bata shigo bane shine nace in xo in duba ko jikin
ne, tunda haka Allah yyi ta mai laulayi, ni jiya ma ko abinci basu kawo min ba
wllh, in ma ba ta da lafiya ita Aishar baxata iya takowa ta kawo min abincin ba
tunda ba uwarta Habiba bace, abu dai gashi ba tsari da ni fitinanniyar tsohuwa
ce ba Bukar xan kira ince matarsa ta bar ni da yunwa ba?" muryar Yusuf imaan
taji yana dariya yace "Toh ae an kai maki daga gidanmu naga" da sauri
Imaan ta shige daki ta dau Hijab dinta ta fito ta shige kitchen ta kashe gas
din sannan ta bude kofar kitchen din ta fice tana murguda baki ta sa Hijab
dinta da iyakarsa gwiwa, ko takalmi bbu kafarta ta dinga tafiya har ta zagayo
front din gidan, Mujaheed ne xaune kan farin kujera yana waya, ta turo baki ta
wuce sa da sauri, ko minti biyar ba ayi da wucewarta ba shi ma ya ji muryar
inna tana tahowa, mikewa yyi da sauri tun kan ya bar wajen ta gansa, da karfi
ta kwalo masa kira tana murmushi, ya ki juyowa har ya sha corner, Yusuf sai
danne dariyarsa yake, Inna ta bude baki tace "Wato ni Mujaheed xai
walakanta ina kiransa ya min banxa kai shaida ne ko Isuhu" tana magana
tana kunce ha6ar xanin xata goge kwalla, Yusuf ya kasa daurewa ya fara dariya
yace "Ke fa kika ce kar ya sake xuwa bangaren ki..." A fusace tace
"To shi mahaukaci ne bai san bacin rai ba" Karo Mujaheed ya kusa yi
da Imaan dake kokarin lekowa taga ko inna ta taho bangaren, ya hade rai yace
"Baki gani ne?" Tana shafa Inda ya bugeta tace "Ko ba inna bace,
ta wani biyoni gidanmu anjima tace ina mata rashin kunya" tafiyarsa yyi ya
bar ta wajen tsaye, ta turo baki ta bi bayansa, jin tafiyarta a bayansa ya
tsaya ya juyo yace "Wai me yasa kike bi na ne" Tace "Ni ba bin
ka nake ba tafiyata kawai nake" Tsayawa yyi ya daure fuska yace "To
yi tafiyar ki, bana son ganin ki kusa da ni" ba ta ce komai ba ta fara
tafiya kamar mai counting steps dinta, yana ta tsaye yana jiran tayi nisa ganin
ynda take tafiyar ya girgixa kai ya wuce ta cikin lokaci kankani, sai a sannan
ta kara saurinta har ta jera da shi, d'an murmushi yyi bai dai ce komai ba bai
kuma kalleta ba, sai da suka kusa entrance din kitchen din part dinsu tace
"Yaya ka mance promise da ka taba min 2 years back koh?" Kallonta
yayi kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Na me?" Ta wara manyan
idanuwanta tace "Idan nayi saukan al-quran, gashi mun kusa in few months
time" tabe baki yyi xai bude kofar kitchen din yace "I can't
recall...." Ta xaro ido ta rikosa da sauri tace "Wllh nasan baka
mance ba" Buge hannunta yyi yana mata wani kallo yace "Keee" Ta
turo baki tana kallonsa, yace "Sakeni kar in mare ki" sake sa tayi ya
bude kofar kitchen din ya shiga ya kulle, tana ta tsaye wajen bayan few minutes
ta murguda baki ta wuce, ta kitchen dinsu ta bi ta kulle kofar sannan ta wuce
dakinta ta sa kayanta. Yau tunda Imaan ta tashi take ta murna, gaba daya farin
cikin ta ya kasa boyuwa, Kitchen ta shiga tace "Ammi da yaushe daddy xai
iso?" Bude baki Ammi tayi tace "Kina kallon agogo kuwa Imaan?"
Imaan tace "Ammi wai yau ma da daddyna xai dawo sai naje islamiyya?"
Ammi ta mata wani mugun kallo tace "Uwar me xa ki xauna ki min ko yace
maki da safe xai taso, common kin 6ace min a nan kin je kin shirya ko sai na
6ata maki rai" a hankali Imaan ta juya a sanyaye ta koma bedroom dinta ta
fiddo uniform dinta ta shiga sa wa, sai da Ammi tayi mata jan ido ta amince da
yin breakfast da ta hada mata, tana xaune dinning tana shan shayin da kyar
Maimoon ta shigo parlon sanye da uniform, Ammi dake goge goge a parlorn tace
"Maimoon ku yi wucewar ku kar ta bata maku lkci ko da kafa ne sai ta
je" dariya kawai Maimoon tayi ta fita, Imaan ta mike don kanta ganin
takwas ya wuce ta dau jakarta ta fita tana matsar kwalla ko ta kan kudin
makarantar bata bi, Ammi dai ko kallonta bata yi ba, Tsaye taga Mujaheed jikin
motar banda masifa babu abinda yake ma kannin nasa, duk kallonsa kawai suke
babu wanda yace komai, "Don samun waje nan nan da islamiyyar ma sai an kai
ku a mota ku ga yan gayu ko, to wllh ni ba driver din kowa bane a cikin ku da
xa a dinga cewa in ajiye ku a makaranta, Yusuf da ya ga xai iya sai yyi, I
won't tolerate that shittt" A hankali Ummi tace "Amma ya Mujaheed
kawai don kana nan ne yasa xaka kai mu ai ba kai ke kai mu ba dama, kuma Abba
yace kila Monday xa mu samu sabon driver...." wani kallo ya dinga mata
fuska daure, ta sunkuyar da kanta, Imaan da isowanta kenan ta bude motar xata
shiga ya dakatar da ita yace "Kee, do I look like drivern gidanku da xaki
ajiye ni for the past 15 mins a nan, to ke daga yanxu ma xa ki fara naki
trekking din" yana fadin haka ya nuna mata makeken gate din gidan yace
"Bi can ki kama hanyar makarantar" ta wani gwalo ido tana kallonsa,
lkci daya ta juya kamar xata yi kuka xata koma part dinsu tace "Ni dai ban
ta6a tafiya da kafa ba...." Wani tsawa yyi mata yace "Wllh ki ka
yarda na takowa har Inda kike sai na sa ki kuka" tsayawa tayi tana hawaye
don bata mance last abinda ya mata ba, ya nuna mata gate on a serious note yace
"Bi can" Gate din ta nufa tana
kuka ya jira ya ga fitar ta sannan ya shiga motar ya bar gidan har ya wuce ta.
Tsaye tayi bakin titi ta rufe fuskarta da Hijab tana kuka, ta kusa minti sha
biyar tsaye a haka taji cikin cool voice ance "Are you okay" xame
hannunta tayi a hankali daga fuskarta tana lekan ko waye ta cikin hijab dinta,
wani dogon matashi ne da baxai wuce thirty two ba, yana sanye cikin kananun
kaya idonsa sanye da bakar spec, dogo ne shi din sosai, sannan shi ba baki ba
kuma baxa a sa shi a jerin farare ba, kuka ya kara taho mata ta dinga rerawa,
yace "Subhanallah, wani abu ya faru da ke ne? Talk to me plss" Cikin
rawar murya tace "Yaya ne ya ce baxan shiga mota ba trekking xanyi kuma
islamiyyar mu da nisa wllh" kallonta ya dinga yi da mamaki, ta sake lekosa
ta cikin Hijab suka hada ido ta yi saurin rufe fuskar tana shessheka, ya d'an
yi murmushi yace "Kin masa laifi kenan" girgixa masa kai tayi, yace
"Toh mu je in ajiye ki ga ride dina can, while going inside the filling
station na gan ki tsaye bayan nayi refilling tank na fito I still saw u the way
you were so I decided to check if you are alright" shiru tayi bata ce
komai ba yace "Mu je to" tace "A'a" yace "Ohk in samar
maki adai daita?" Kai ta gyada masa, ya tsayar da adai daitan ta shiga ya
basa kudin, a hankali tace "Nagode" ya mata murmushi kawai mai adai
daitan ya ja suka bar wajen, Yusuf ne ya dauko su daga islamiyyar bayan sun
tashi karfe sha biyu, tun a mota ya dinga tambayar Imaan me ya faru ganin yanda
take yamutse fuska, da kyar tace "Kafana ke min ciwo" yace "Toh
sannu, idan muka isa gida sai ki shafa maganin" a hankali tace
"Toh" suna isa gidan da kyar ta fito motar, Yusuf ya kama hannunta ya
rakata har sashin nasu sannan ya bude mata kofa ta shiga ciki, wanka kawai tayi
ta saka doguwar riga Ammi ta shafa mata methylated lotion din da take shafawa a
kafafuwanta sannan ta sa ta kwanta nan da nan kuma bacci ya dauketa, dab da
la'asar Ammi ta tasheta, Ammi bata mata xancen islamiyya ba Imaan ta wara ido
ganin irin girke girken da Ammi tayi tace "Ammi is all this for
daddy?" Ammi tace "No it's for Imaan" murmushi Imaan tayi ta
rungumeta ta baya tace "Thanks sweet mum" Ammi tace "Ki tafi
kiyi sllh ko baki ga lokacin hr ya gota ba" da sauri ta koma daki, tana
idar wa ta fito, Ammi tace "Daddy ya kira yana gate, ki fita ki shigo masa
da kaya" da sauri Imaan ta nufi kofa Ammi na kiranta ta xo ta sa hajib don
rigar jikinta karamin hannun garesa amma tuni ta fice, dai dai nan mai gadi ya
bude gate sai ga motar Daddynta, da gudu ta nufi parking space ta tsaya cike da
murna, Mujaheed dake kokarin bude motarsa suka yi ido hudu da daddy da ya fito
Imaan ta rungumesa, Daddy ya sakar masa murmushi, hakan yasa ya nufe sa kamar
mai kirgan steps dinsa, daddy na shafa kan Imaan yace "Ba kya girma koh
Mamata" ta kara kankamesa tace "Don Allah daddy ka daina dadewa haka
wllh ina Missing dinka" yyi murmushi yace "To xan daina mamana"
Mujaheed ya risina yace "Sannu da hanya Abba" Wani hade rai Imaan
tayi tana hararansa ta gefen ido, Daddy na murmushi yace "Thanks Son, ka
bar mu a birnin tarayya ynxu koh" murmushi Mujaheed yyi yace "Ae kam
daddy" daddy yace "Toh Allah yayi jagora, ya aikin fa?" Yace
"Ae ban fara ba sai Monday Abba" Daddy yace "Allah ya kai
mu" Daddy ya mika ma Imaan da ta turo baki ledan apples dinta da chocolates
don a ko da yaushe tsaraban ta kenan, Mujaheed dai ko kallonta bai yi ba ya dau
jakar laptop din daddy da wasu files ya nufi part dinsu, Murguda baki Imaan
tayi ta jera da daddynta tana ci gaba da gaya masa yanda tayi kewarsa, Mujaheed
ya sunkuyar da kai ya gaida Ammi bayan ya ajiye jakar hannunsa da files, ta
amsa ta dau jakar ta wuce daki, Daddy ya xauna yace "Barrister bai dawo ba
ko Mujaheed?" Mujaheed yace "Ehh bai dawo ba" Daddy yace
"Ohk mun yi magana daxu ma" Mujaheed ya dukar da kai yace "Toh
Allah ya huta gajiya Abba" daddy yace "Madalla nagode son" har
ya fara tafiya Daddy ya kalli ledan apples da chocolates da Imaan ta sa gaba
tana dubawa yace "Son baxa ka Debi apples ba" Da sauri Imaan ta jawo
ledan jikinta tana kallon daddy, Mujaheed da har xai ce A'a don he isn't a fan
of Apple ganin abinda tayi yayi kasa da kai yana shafa gashinsa yace "Toh
Abba" daga haka ya nufeta, bude baki tayi tana kallon daddy lkci daya
hawaye ya kawo fararen idonta, Mujaheed ya jawo ledan yana kallonta da kyau ya
cire spare leda ya debi apples har hudu a cikin guda takwas da Daddy ya siya ya
xuba a wani ledan yana kallonta har sannan, ya kara bude ledan chocolates din
ma ya debi mai yawa ya xuba a ledan hannunsa, har ya mike ya sake dawowa ya dau
Apple daya ya sa ka a ledan, daddy ya dauke kai yana murmushi, Mujaheed bai
yarda ya kallesa ba yace "Nagode Abba" daga haka ya fice parlon.
[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan*⭐🌟
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
4.....
Daddy ya kalli Imaan dake goge hawayen idonta yace "Don
yayanki ya debi apples kike kuka Imaan?" Ta marairaice tace "Toh
daddy ai ba shi ka siyo ma ba gashi ya kwashe min gaba daya kuma wllh baya cin
apple" Daddy yyi murmushi yace "Shi yace maki bai ci" cikin
rawar murya tace "Ae nasan baya ci tun da can" Daddy yace "Toh
anjima idan na fita xan karo maki" a hankali tace "Toh nagode"
yace "Wai amma me ya hada ku da yayan naki all of a sudden Imaan"
Ammi da ta fito parlon tace "I am still wondering also, lkci daya aka yi
parting" Daddy yace "Ko kin masa wani abun ne dai" ta turo baki
ta dawo kusa da daddy tace "Kawai dai naga ya xama mugu ne shi sa na daina
kulasa" Dariya kawai daddy yayi, Ammi tace "Har nan ma ai baya
shigowa yanxu" Daddy yace "Toh Allah ya kyauta" Imaan tace
"Daddy ni dai ka daukan min personal driver dina plss" daddy yace
"Ba Abbanku xai daukar maku driver ba, ai mun yi magana da shi bayan
tsohon drivern ya wuce" Tace "A'a daddy ni dai nawa daban nake so,
kilan ba yanxu driver din ma xai xo ba, yau fa Yaya bai bari na shiga motar ba
don na bata masu lkci da kafata na tafi islamiyya shi sa tun da na dawo duk
jikina ke ciwo sai da Ammi ta shafa min magani na kwanta da na tashi shine naji
sauki"' Murmushi kawai Daddy yayi ya mike yace " Bari in yi wanka
daughter " daga haka ya wuce bedroom dinsa, Ammi tace "Sai ki tashi
ki kai ma Inna abinci ko yau ma baxa ki ba" Ta kalli Ammi da sauri tace
"Ammi ca tayi bata son sake ganin kafata a part dinta fa, kuma in je yanxu
ta gaya ma daddy" Ammi tace "Tashi ki dauki abinci ki kai mata
nace" Daga haka Ammi ta bar parlon, mikewa Imaan tayi ba don ta so ba ta
shiga kitchen, kusan duk abinda Ammi tayi ma daddy sai da ta dibar ma inna duk
ta ajiye a basket, Imaan ta dau basket din me dauke da abincin ta fita, har ta
isa part din Inna fuskarta a daure yake irin ko kulata din nan baxata yi ba, ta
dinga kallon takalman dake bakin kofa kafin ta bude kofar ta shiga, Mujaheed na
xaune yana kallon inna dake bada labari tayi mitsi mitsi da ido, banda murmushi
babu abinda yake don da wuya yake dariya, su Maimoon da Rahma kuwa dariya har
da kyakyatawa, Inna ta saita hannu sama tace "Ji kawai muka yi
ratatatata.... Ba sai kakan ku ya shige karkashin gado ya bar ni da halina da
'ya yana ba, lkcn Bukar na bayana sai tsala ihu yake, Ahmadu kuwa fitsari ya
dinga saki yayi sau uku a wando...." Ganin Imaan Inna tayi shiru ta jawo
daya daga apples biyar dake cikin leda a gabanta ta kai baki, Har sannan su
Maimoon dariya kawai suke, imaan ta ajiye basket din hannunta tana kallo chocolates din da Daddy ya kawo mata a hannunsu
Maimoon, ta saci kallon Mujaheed ta juya xata fita Inna ta tabe baki tace
"Ga dambun naman ki can a daki ni dai na ajiye maki bana bi ta halin ki
ba" ba tare da ta juyo ba tace "Bana ci" inna na ci gaba da cin
apple dinta tace "To wa yayi asara?" Mujaheed yace "Yana ina a
dakin?" Da sauri Imaan ta juyo ta shige dakin, Inna tace "Ya xaka ce
yana ina bayan ka ci rabon ka da wanda ma ka dauka ban baka ba" yace
"Haba" tayi tsaki tace "Yana nan cikin roba xa ki gansa a rufe,
duk naki ma ya fi yawa" Imaan ta fito rike da uban dambun naman da inna ta
ajiye mata a bowl mai murfi ta nufi kofa, inna tace "Wannan liyafar hala
Bukar ne ya dawo?" Imaan tace "Bai dawo ba" daga haka ta fita,
Inna tace "Duk ta ma fige kamar bata cin abinci" Rahma tace "Mu
dai ci gaba da ba mu labarin da kike yi don Allah inna" inna ta gyara xama
xata ci gaba, mikewa Mujaheed yyi ya fita parlon. Imaan na komawa bangarensu ta
tadda Yusuf ya shigo gaida Daddy, Ya bi ta da kallo ta boye bowl din hannunta
tana wara masa manyan idanuwanta tace "Nasan ka ci naka dai" fitowar
Daddy parlon yasa Yusuf bai ce mata komai ba, daddy yace "Engnr ashe kana
gari" Yayi murmushi yace "Ina nan daddy, da fatan kun iso
lafiya" yace "Alhmdllh My son, ya aikin fa" Yace "Mun gode
Allah Daddy" daddy ya xauna kujera yace "Madalla, kowa dai lafiya
koh?" Yusuf yace "Duk lafiya" Yusuf bai wani dade ba ya mike
yace xai wuce, daddy yace "Baxa ka tsaya mu ci abinci ba" Yace
"Alhmdllh daddy na ci abinci" Ammi dake dinning tana jera abincin
tace "Anya Yaya Yusuf" dariya yayi yace "Ammi wllh na
koshi" tace "Toh shikenan" sallama yyi ma daddy ya fita. Bayan
magrib daddy xai je gaida inna babu yanda bai yi da Imaan su je ba ta ki, har
hakan ya basa mamaki ya tafi shi kadai, inna na goge tiles din parlonta daddy
ya shiga da sallama, ta mike tace "Amma dai gaskiya Bukar ka dinga kwa6a
ma yar ka ta daina karya, ce min fa tayi baka dawo ba" Ya xauna yana
murmushi yace "Sannu inna, ina yini" ta shimfida tabarma ta xauna
tace "Lafiya lau, amma ai karya ba shi da amfani kuma a gaskiya Imaan ta
iya karya" Shi dai bai ce komai ba, tace "Toh ya hanyan?" Yace
"Alhmdllh mun baro hanya" tace "Wannan karan kuma kamar baxa ka
sake dawowa ba" yace "Aiki ne yyi yawa Inna" tace "Toh
Allah ya bada sa'a ya tsare mana ku a duk Inda kuke, ya maka albarka" yace
"Ameeen inna" Tace "Toh ya xa ayi, Allah ya kaddara a can
abincin ka yake, banda haka na tabbata da kana gidan nan da ka dinga share min
hawaye daga bakin cikin da nake fuskanta" Daddy na kallonta da mamaki yace
"Bakin ciki kuma Inna?" Inna tace "Yo bakin ciki mana Habu...
Kaga yayanka baxai fito daga masallaci ya tako nan tun asuban ba ya gaisheni
sai ina jin wajen karfe tara xai taho da safe ya duka can bakin kofar ya gaida
ni a gurguje ya kara gaba, bana sake ganinsa Bukar sai ina kokarin kulle kofa
ta da daddare shi ma Allah yasa ya yi minti biyu xaka ga yace sai da safe daga
haka ya wuce, Kaga matar nan tasa Rukayya take ko wa? Uwarsu Mujaheed dai wllh
kaji rantsuwar musulmi tafi wata biyu ina ga bata tako ta xo nan ta gaisheni ba
sai ta gan ni a tsakar gida ko a can bangaren, ita kuma dayar mai kama da
fulanin Bararoji wato Amina da suke ce ma Anty sai ta bushi iskarta xata kwaso
kafafuwa ta xo gaisheni, ita wnn farar wa take da suna? Uwar wannan yarinya
Imaan d'an wankin da take min da duk ta watsar sun xugeta, in kuwa wannan 'ya
taka Imaan borinta ya tashi ta ki kawo min abinci to ranan fa da yunwa xan
kwanta a gidan nan, Aisha ta fi karfin ta taso takanas ta kawo min da kanta, to
me yafi wannan bakin ciki Yaro? Gashi gaba daya 'ya yanku sun rainani sun maida
ni ba bakin komai ba, sun maida ni kakarsu tun ma ba wannan katon Mujaheed ba
da ramammiyar 'yar ka, sai wannan kazamar Ummi, ni nasan da sun ga ido wllh
taka ni xasu dinga yi suna wucewa, isuhu kadai ke raga min a gidan nan sai
wannan yarinya Seeyama, Imaan idan ta fara balbale ni wlh shiru nake, haka ma
Mujaheed yaron da aka haifa a gabana, to ina dalili ina da gata na ta ko ina
don dai d'an abincin da ake yarfa min a kwano sai a maida ni bola" Daddy
dake ta saurarenta ya dago kansa a karo na farko yace "Kiyi hakuri don
Allah inna" a fusace tace "Na gaji da jin wnn axxalumin kalman, ayi
ta baka hakuri ana cutan ka, ni dai a fita harkata, don idan tsiyata ta debeni
wllh sai an fita har kasashen waje ana nemana" Daddy yace "Xa a gyara
Inna, duk ki yafe masu, ita Imaan xan sameta yanxu, shi ma Mujaheed din xan
gamu da shi" Tace "Atoh, sai ka xaunar da su ka tambayesu kaji ko
xaman gidan ne basa son inyi, ka tambayesu dalilin da yasa basa fitsaran su a
waje sai a cikin gida cikin gidan ma a kan uwarka, kayi masu jan ido ka nuna
masu bacin ranka Yaro" Daddy yana murmushi yace "In sha Allah"
nan suka ta6a hira amma kusan hiran gaba daya na complain ne daga karshe daddy
yace mata xai wuce masallaci don an kira isha. Daddy na dawowa masallaci ya dinga
kallon Imaan dake xaune parlor tana cin abinci, ya xauna yace "Imaan yanxu
ita innar kika mayar abar wasar ki a gidan nan?" Kallonsa ta dinga yi
kamar zata yi kuka, ya hade rai yace "would you take ur eyes off me silly
girl, haka kike ma uwar ki? I warned you the last time a kan haka shine kika
sake repeating foolishness din yanxu ko?" Ta sunkuyar da kanta, ya gyada
kai yace "Nasan maganin ki, tashi ki bar min parlor" tashi tayi da
sauri ba tare da ta bi ta kan abincin ba ta shige bedroom dinta ta kulle, ita
dai Ammi bata ce komai ba, Daddy yace "I don't like this nonsense
character of her, ita innar abokiyar wasanta ce, ke kuma Aisha baki taka mata
burki, a kan me xata dinga rainata, I don't like that, and I am going to teach
her manners soon" Ammi ta tabe baki ta mike ta dauke abincin da ta bari ta
kai kitchen ta rufe, ta tsaya kitchen din tana wanke plates da ke sink.
Washegari wajen karfe bakwai da rabi Imaan ta fito sanye da uniform din
islamiyya, kanta a kasa ta gaida Ammi dake jera breakfast a dinning, Ammi dake
kallonta tace "Wato ke ba isa a maki fada ba shine kika kwana kuka ido ya
kumbura koh?" Ta fashe da kuka tace "Ni Ammi don Allah kar ki sake ce
min in kai mata abinci kullum sai tayi ta ma mutum sharri alhalin ba abinda
nayi mata" Ammi tace "Ko ban baki abinci kin kai ba ma da kanki naga
kike kwasan kafafuwanki kije can din ko da kuwa koranki tayi" Imaan ta
hade rai tace "Yesterday was the last day da xan je part dinta, har abada
baxan sake xuwa ba" Ammi tace "Toh bari dai ya ji ki gashi can ya
fito, ni ba ruwana" shiru Imaan tayi tana juya shayin da Ammi ta hada
mata, Daddy dake tsaye parlon yace "Madam me yasa ba a kai ma Inna
breakfast ne wai?" Ammi tace "Breakfast kuma?" Yace "Ehh ai
ya kama ta ne" tace "A'a don Allah yallabai kar ka hada ni da ita,
kullum sai Abba ya tura mata bread, tana da kayan shayi kuma tana da heater ta
iya amfani da shi, meye breakfast din dama idan ba shayi da bread ba sai kwai
wani lkcn, lunch da kanta tace bata so a daina kai mata wai jagwalgwalon yara
ne" Tuni Daddy ya xauna ya sa news channel, Ammi ta shiga kitchen ta ci
gaba da abinda take, Imaan ta gama breakfast din ta mike ta iso cikin parlor ta
durkusa ta gaida Daddyn nata, sau daya ya kalleta ya amsa ya ci gaba da
kallonsa, ta mike ta tafi kitchen ta amshi kudin makarantar ta gun Ammi ta fito
ta dau jakarta bayan ta sa takalmi da safa tayi ma daddy sallama ba tare da ta
kallesa ba ta fice daga parlon, kiranta daddy yyi ta juyo ta dawo ta sunkuyar
da kanta tace "Ga ni" room freshener har biyu ya nuna mata dake ajiye
yace "Dauka ki kai ma Inna kafin ku wuce" shiru tayi tana kallonsa
kamar xata yi kuka, bata dai ce komai ba ta durkusa ta dauka sannan ta fita
xuwa part din inna, Inna na ta goge goge bayan ta gama share ko ina fesss,
banda kamshin turaren wuta babu abinda ke tashi a parlon, imaan bata kalleta ba
ta ajiye abun hannunta fuska daure tace "Ina kwana" xata fita inna
tace "Me ya sami idonki ni Asabe? An umaki wani abun ne" Imaan da har
ta kai kofa ta juyo lkci daya ta fara kuka tace "Kawai sai kije kice ma
daddy ina maki rashin kunya yaushe rabon da in xo nan...." Tana fadin haka
ta fashe da matsanancin kuka, Inna da ta saki baki tace "Shine ya maki
me?" Cikin kuka tace "Fada ya dinga min mana yace zai yi magani
na" Inna ta dau dankwalinta ta fita parlon imaan ta bi ta da kallo tana
share idonta, Ko sallama babu inna ta bude kofar parlon, daga daddy har Ammi
suka daga kai suna kallonta, tace "Bukar dama yaro ba lallabasa ake yi ba
a rayuwar nan, daga mun yi magana tsakanina da kai sai ka taho ka far ma yarinya
da bala'i, to ae gwara ita sau dubu a kan sauran, Imaan bar ta da son jikinta
amma wllh wllh bata da matsala, haka kawai ka ja mata wani cutan dama gata mai
cuta iri iri kamar ta kashe d'an mutum, yanxu da kasa ta kwana tana kuka idan
wani abun ya sameta me xa ka gaya ma Allah, kai dai wllh ka cika bala'i, ba
haka yayanka Ahmadu yake ba, ba ruwansa da irin wannan hali, to wai ma me ta
min da xafi haka da xaka sa ta kuka haka, ga abun duka can Mujaheed me nuna ni
da yatsa, mai ce min Hajiya, ni tunda nake wllh xan iya kirga sau nawa Imaan ta
mayar min magana shima kuma duk laifina ne....." Ammi dai tuni ta shige
kitchen, Daddy kuma ya kasa cewa komai, Inna ta juya ta nufi kofa tana cewa
"Wannan dai ba yi bane, kamar ba kai ka haifeta, yar gata daga ita sai ita
amma kuma ka takurata, da wanne xata ji da rashin karo mata kanni da ba ayi ba
har yau ko kuma da fitinar mahaifinta, kuma ka tashi ka kawo min turaren bature
da ko kamshi babu wai in fesa a daki, to uwata bata ce min je ki kya gani ba
turaren wuta tsadadde mai kamshi nake nufi, sai ka ba matarka mai kumewa a daki
kamar matar liman ta fita kasuwa ta siyo min" daga haka ta fice ta kulle
masu kofa. Dama imaan direct gun mota ta nufa bata yarda ta ma bi ta part dinsu
ba. Yusuf ne ya ajiye su islamiyyar, karfe sha biyu Anty ta dauko su, A hankali
Imaan ta bude kofar parlonsu tana lekan ciki, babu kowa hakan yasa ta shiga ta
rufe kofar ta nufi bedroom dinta da sauri, tana kokarin cire Uniform dinta Ammi
ta bude kofar, Imaan ta gaisheta kanta a kasa, Ammi tace "Amso min card
waje kafin ki cire uniform din" Imaan ta amsa tana kallonta tace
"Ammi daddy fa?" Ammi tace "Yana daki" Imaan ta marairaice
tace "Ni fa ban gaya ma inna ya min fada ba, kawai taga idona ne
haka" Ammi tace "Wannan ya rage naku ke da shi, ni kiyi sauri ki amso
min card din" imaan ta maida Hijab dinta ta fita, kiosk din is just a
house from theirs, ta amso card din ta juyo ta shigo gida, Umma ta gani tsaye
parking space alamar xata fita, Mujaheed ya iso wajen ya bude mata back seat, sannan
ya shiga driver seat, Imaan na hada ido
da Umma dama ta dauke kai tayi wucewarta, Mujaheed ya bi ta da kallo ta madubi,
Umma ta shiga cikin motar tace "Wllh duk ranan da ka gaida uwar yarinyar
nn ko da mistake a gidan nan ban yafe maka ba Mujaheed, duk kanninka ma na
karanta masu haka nasan kuma sun dauka...." Yana kallonta ta madubi yace
"Haba Umma kema kin san....." Ta karasa masa da sauri tace "Baxa
ka iya ba ko? tunda ga ta kanwar Ahmad ko kanwata, Mara tunani kawai da bai san
ciwon uwarsa ba, to mu xuba da kai wllh, ba dai makiyana su ne mutanen arxikin
ka ba a gidan nan, ka ci gaba, a ta dalilin munafukar uwar yarinyar nan na bar
gidan ubanka for good 5 years, ta hade kai da kishiyata suka yi ta kulla min
makirci har ubanka ya sakeni, da yake akwai sauran xamana a gidan na dawo few
years back na tarar baka da masoya da ya wuce makiyana, ka maida Aisha uwarka,
ka nuna duk gidan nan baka da kanwa da ya wuce yarinyar Aisha, yarinyar da bata
gaisheni a ynxu ko idona xai makale a nata saboda uwar ta hanata, da kyar da
siddin goshi da rokan Allah na rabaka da su, ni da ba a kan idona na haifeka ba
kuma ina haihuwar ka aka ajiye min kai a gefe na da wllh bbu abinda zai sa
baxan ce canjen ka aka min a asibiti ba, sam baka san mutunci na ba, ace
makiyana su ne masoyan ka Mujaheed? Anya kana son gamawa lfya kuwa?" Shi
dai ya kasa cewa komai, ta gyada kai ta bude motar ta fice tana cewa "Ga
ka ga su ai, daga ynxu ma ka tatttara yanaka yanaka ka koma bangaren nasu"
a hankali yace "Umma I have avoid a lot of things a gidan nan kema kin
sani, wllh ko kadan bani son abinda xai bata maki rai, don Allah kiyi
hakuri...." Ko saurarensa bata yi ba ta fice daga compound din ya sauka ya
bi bayanta da sauri. Washegari har Ammi ta gama hada breakfast ta fito daga
kitchen imaan bata fito daki ba, ta kalli agogo ganin bakwai da quarter ta nufi
dakin ta bude ta shiga, kwance ta ganta ta dukunkune cikin bargo, Ammi ta
karasa da sauri ta cire bargon tace "Are you okay Imaan?" Ta bude ido
kamar xata yi kuka, Ammi ta dinga kallonta don jikinta ya dau xafi sosai, a
hankali tace "Ina ke maki ciwo kuma?" Kafafuwanta ta nuna mata da
kai, hawaye cike idonta tace "Ammi duka jikina ciwo, jiya ban yi bacci
ba" Ammi ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace "Ba ki sha magani
ba jiya da daddare ko daughter" ta nuna ma Ammi magungunanta a side drawer
tace "Na sha Ammi" saketa Ammi tayi ta mike ta shiga bathroom ta hada
mata ruwan wanka ta fito tace "Toh shiga kiyi wanka sai ki kara shan
maganin" da taimakon Ammi ta sauka kan gadon, Ammi na rike da ita suka
shiga bathroom, bayan ta wanke baki Ammi ta taimaketa tayi wanka ta fito, barin
ta tayi ta sa kaya ta tafi hado mata shayi, Daddy na xaune parlor yana dube
dube a laptop, ta tsaya bayan kujerar tace "Yallabai jikin imaan fa kar ya
rikice mana ko xa aje asibiti tunda likitan ma baya nan" daddy ya mike
yace "Bata jin dadi ne" Ammi tace "Nima yanxu na shiga ganin
bata fito ba, her temperature is high tace bata yi bacci ba" daddy ya d'an
yi shiru, Ammi tace "Kwanakin baya ciwon ya lafa sosai, as from some weeks
ago yanxu duk sai ya tasar mata ga xaxxabi da ciwon kai kuma tana shan drugs
dinta" Daddy yace "Toh ta shirya mu tafi asibiti" Ammi tace
"Toh" komawa yayi ya xauna, ita kuma ta wuce dinning don hada mata
shayi. Kwance ta sameta bayan ta sa abayar da ta fiddo mata, da kyar Imaan ta
sha shayin, Ammi ta fesa mata turarrukan ta ta bata veil din abayar sannan suka
fito parlor, kwanciya tayi kan kujera tana gaida daddy dake rike da makullin
mota yana jiransu, ya amsa yace "Sannu mamana, tashi mu je to" mikewa
tayi ya kama hannunta suka nufi kofa Ammi na masu Allah ya kiyaye hanya, A
hanya daddy ya hadu da Abba ya taho daga part din Inna, gaisawa suka yi, Imaan
ma ta gaishesa a hankali, Abba yace "Jikin ne ya tasar mata?" Daddy
yace "Wllh kuwa, xa mu je asibiti ne yanxu" Abba yace
"Subhanallah tana shan magunguna kuwa" Daddy yace "I think
so" Abba yace "Toh likitan ta fa?" Daddy yace "Yayi tafiya
ne" Abba yace "Toh tunda Muhammad na nan ba sai ya dinga dubata ba
kafin likitan nata ya dawo, ko gwara a tafi asibitin?" Daddy yace
"Noo in xai dubata shikenan, dama don likitan baya nan ne xa mu je
asibitin" Abba yace "Let me give him a call, na barsa sashin inna,
idan ma asibitin xa a sai ya kai ta kawai" Yana kokarin kiran Mujaheed
suka hangosa yana tahowa, Abba ya maida wayarsa, har Mujaheed ya isa parking
space da suke tsaye kallonsu kawai yake, Ya risina ya gaida Daddy, ya amsa masa
da fara'a, Abba yace "Imaan xaka duba Mujaheed, bata jin dadi" Sosai
gabansa ya fadi ya kalli Imaan dake jingine da mota duk ta wani langwabe.
I appreciate my fan's love always, ina yinku fisabilillah😘😍
[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟
_By khaleesat Haiydar_✍🏻
5.....
Gaba daya Mujaheed ya daburce ya rasa abin cewa, Abba yace
"Ko in kai ta asibitin kawai" da sauri yace "Noo Abba, naga bani
da kayan aiki a gida ne, sai dai in kai ta asibitin in duba ta a can" Abba
yace "Toh hakan na da kyau" Magana yake amma gaba daya rabin
attention dinsa na kan window din dakin Umma duk da baya hango komai, amma
fatansa yanxu ace bata tashi bacci ba duk da yasan da wuya, Ya sunkuyar da
kansa yace "Toh xan dauko makullin mota a ciki" Daddy ya mika masa
nasa makullin motar yace "You use my car, duk yanda ake ciki you let me
know" Mujaheed ya risina ya amsa makullin motar yace "Toh Abba"
daddy yayi ma yayan nasa sallama ya wuce ba tare da ya kalli imaan da ta cika
saura kiris ta fashe ba, bayan ya tafi Abba ya kalleta yace "Sannu
Mamana" Ganin hawaye idonta yace "Baki son bin Muhammad din
kenan?" Da sauri ta gyada masa kai hawayen na sakkowa idonta, yace
"Kuma baki son daddyn naki ya huta koh, am sure kila xuwa anjima ko gobe
xai koma bakin aiki, shi Mujaheed din ba yayanki bane?" Ta fashe da kuka
tace "Abba ihu xai ta min a hanya fa" Abba yyi murmushi mai sauti sai
dai bai ce komai ba, Mujaheed dai sai kallonta yake ta gefen ido, Back seat
Abba ya bude mata yace "Shiga" a hankali ta shiga ta jinginar da
kanta jikin motar, Abba na kallon Mujaheed yace "You take very good care
of her, ko kallon banxa ban yarda kayi mata ba" Ya sauke idonsa yace
"Toh Abba" Abba ya daga mata hannu ta mayar masa tana goge idonta, ya
juya ya wuce ciki, Mujaheed ya gama warming motar yayi horn ana bude masa gate
ya fita gidan, sai da suka hau saman titi yace "Saboda baki son xuwa schl
shine kika fake da ciwon karya salon ki ba mutane wahala koh?" Jin bata ce
komai ba ya kalleta ta madubin motar, murguda masa baki take, suna hada ido ta
turo bakin kamar xata yi kuka sai dai bata ce komai ba, ya gyada kai yace
"Xaki gwammace schl kika yi tafiyar ki yau" ta fashe da kuka tace
"Dama dai Abba yace duk abinda ka min in gaya masa" Bai tanka ta ba
har suka iso asibitin da yake aiki, yana gama parking ya bude motar ya fita ita
ma ta fita, ya rufe motarsa ya dau hanyar entrance din shiga hospital din, a
sauri ta bi bayansa, tsaye ta gansa reception suna gaisawa da nurses dake wajen
da fara'a, Wata nurse tace "Doctor I heard an sake transferring dinka xuwa
nan, kuma shiru ba mu ganka ba" Yace "Sure da yau xan yi resuming,
but due to some reasons sai Wednesday in sha Allah" duk nurses din suka
amsa masa da Allah ya kai mu, juyawa yyi yaga Imaan ta nemi kujera tayi
xamanta, wata nurse tace "Dr sister dinka ce?" Yace "Sure bata
da lafiya ne" daga haka ya wuce sama, duk sai da ya shiga office din
doctors dake duty safiyar, Dr Mukhtar na ganinsa ya mike yace "Kaga mara
kirki dama yau xaka yi resuming shine babu sanarwa" Mujaheed ya karasa
yana murmushi suka gaisa yace "Sai Wednesday in sha Allah, na kawo sister
na ne bata da lafiya" Mukhtar yace "Subhanallah Ummi ko Rahma?"
Yace "None, cousin dita ce wannan" Dr Mukhtar ya koma ya xauna yace
"Ohk tana ina" Yace "Tana reception" Dr Mukhtar ya buga
waya downstairs ba a dau lkci ba wata nurse ta shigo office dinsa, gaida
Mujaheed tayi da fara'a ya amsa yace "Ya aikin Zainab" tace
"Alhmdllh Dr" Dr Mukhtar yace "Ki taho da patient dake
reception" tace "Wanne they are almost 7 patients downstairs"
Mujaheed yace "Imaan sunanta" tace "Ohk" daga haka ta fita,
tare suka dawo da Imaan da ta wani yi laushi da kyar take jan kafar, Dr Mukhtar
ya nuna mata kujeran dake kallon wanda Mujaheed ya xauna, ta xauna xata kwantar
da kanta kan table Mujaheed ya mata wani kallo yace "Tashi" kamar
xata yi kuka ta dago kanta, likitan yace "Sannu Imaan, ya kike jin
jikinki, like ina ke maki ciwo?" A hankali tace "Jiya da daddare
bayana ya dinga min ciwo har da kai na kuma ina jin sanyi, ban ma yi bacci
ba" likitan yyi murmushi yace "Yau da safe fa" Ta kallesa murya
can kasa tace "Kafafuwana suka fara min ciwo da na tashi, anjima kuma duk
jikina ya fara min ciwo" Ya langwabar da kai yace "Ikon Allah, suna
maki haka ne?" Kai ta gyada masa, yace "Toh kina shan wasu magunguna
ne?" Kai ta gyada masa, yace "Kin san sunan su?" Ta gyada masa
kai, yace "Can you write them down for me now?" Tace "Sure"
farar takarda ya ajiye mata da pen, nan ta rubuta masa gaba daya drugs dinta
har da na shafawa ta mika masa takardan ya amsa yana dubawa, bayan few seconds
ya daga kai yana kallon Mujaheed dake kallonsa shi ma, kafin yace komai
Mujaheed yace "Rubuta mata injections taje ayi mata" Likitan yyi
yanda Mujaheed yace, Mujaheed ya amshi takardan yana kallon alluran da ya
rubuta mata sannan ya mika ma Imaan da ta kife kanta da table yace "Karba
kije nurses su maki alluran" ta dago da sauri tace "Yaya allura kuma,
ni doctor na baya min allura magani kawai yake ban" ya jefa mata wani
kallo yace "Sai ki jira ya dawo ya ci gaba da baki maganin, nan kam allura
xa a maki, get up my friend" a d'an tsawace ya karasa maganan, Ta amsa
lkci daya hawaye ya cika idonta ta juya ta fita office din, a hankali Dr
Mukhtar yace "Is she a sickled cell patient Mujaheed?" Mujaheed ya
girgixa kai yace "Not at all, She is only carrying the trait, a carrier"
da mamaki Likitan yace "But it's almost mimicking the disease"
Mujaheed ya buda hannu yace "Mu ma haka muka gani" Dr Mukhtar yace
"Subhanallah, this is kind of rare, Allah ya bata lafiya" Mujaheed
yace "Ameen" Dr Mukhtar yace "Kasan alluran are strong, ta ci
abinci kuwa?" Mujaheed ya mike da sauri yace "I don't know, bari in
tambayeta, kafin in dawo plss kayi prescribing drugs in addition to hers"
daga haka ya fita, injection room ya shiga bayan nurses din sun sanar masa suna
ciki xa a mata alluran, tsaye take tana hawaye nurse din ma na tsaye rike da
alluran sai kallonta take, tana ganin Mujaheed tace "Yauwa Dr ta ki
fa" Mujaheed ya hade rai yace "Are you a baby? Waye kike son ba
wahala, xan maida ki gida da ciwon ki ne idan baki yi respecting kan ki
ba" ta fashe da kuka bata ce komai ba, Yace "Kin ci abinci?"
Cikin rawar murya tace "Na sha shayi kadan amma yunwa nake ji" wani
kallo ya dinga mata, can ya kalli nurse din yace "Nurse let me get her
something to take plss" nurse din tace "Ba damuwa Dr" daga haka
ya fita, nurse din ta nuna mata kujera ta xauna. Rike da malt Mujaheed ya dawo
injection room din, ya bude sannan ya mika mata, Kadan ta sha xata ajiye yace
"Wa za ki ajiye ma" ta hadiye na bakinta da kyar tace "Xan sha
idan an gama min" nurse din tace "Aa ki kara kadan" da kyar
Imaan ta kara malt din sannan nurse din tasa ta tashi, ta mike ta fashe da kuka
tana kallon Mujaheed tace "Wllh tsoro nake ji xai min xafi" nurse din
tace "Baxai maki ba kuwa" Mujaheed yace "Xan fa tafi in bar ki a
asibitin nan kina bata min lkci" tace "Don Allah kai ka min
plsss" yace "Baxan yi ba, kin tsaya ko inyi tafiyata" da kyar ta
isa kusa da nurse din, ta kallesa ta mika masa hannu jikin rawar murya tace
"Don Allah ka rike min hannu Yaya" bai san lkcn da yyi murmushi ba ya
karasa inda suke, ta kama hannunsa ta runtse ido, nurse din tace "Me yasa
baki sa under skirt ba?" Ta turo baki tace "Ni bana so" nurse
din tayi murmushi, ta daga mata abayar jikinta, rungume Mujaheed tayi ta
kwantar da kanta kirjinsa, cikin rawar murya tace "Wayyo Yaya don Allah
kace ta min a hankali, kar ta min da xafi" Mujaheed ya amshi alluran
hannun nurse din yayi mata, xaro ido tayi tana cewa "Yaya ta sa alluran?
Don Allah tayi a hankali, tuni ya amshi dayan alluran yyi mata shi ma, sae da
ya cire syringe din ta sakar masu ihu duk tunaninta lkcn xa ayi alluran, ya
turata daga jikinsa, ta dinga xaro ido, nurse din tayi dariya tace "Toh ba
gashi har an gama ba" Imaan ta zaro ido tace "Da gaske? To ban ji
sanda aka cire ba" Mujaheed dai ko kallonta bai yi ba yyi disposing
syringe din ya nufi kofa, nurse din tace "Ki fa danna wajen sosai idan kun
koma gida" Imaan ta gyada mata kai tana goge idonta har sannan tana
mamakin wai har an mata allura don bata ji zafin da take ta jira ba, ta dau
sauran malt dinta ta fita, xaunawa tayi reception ganin bata gansa ba, bayan
kusan minti goma sai gashi ya sakko, yana kallonta ya nufi kofa, da kyar ta
mike tace "Yaya na fara jin jiri" yace "Toh ko in bar ki a
nan" da sauri ta girgixa masa kai ta isa gunsa, saura kadan ta fadi gun fita,
ya kalleta sau daya yyi gaba, back seat ta shiga ta kwanta tana maida numfashi,
ya shiga motar ya tada suka bar asibitin, wani pharmacy ya tsaya xai fita tace
"Yaya wllh idona juya min yake" nan ma dai bai tanka ta ba, drugs
dinta da sabbin da Dr Mukhtar yyi prescribing ya siya mata sae lucozade boost
babba biyu, duk ya ajiye bayan motar, har suka isa gida yyi parking a parking
lot din daddy bacci Imaan take, daga cikin motar ya dinga lekan apartment dinsu
gabansa na faduwa, ya juya ya kalleta, sannan ya fito daga motar, ya bude back
seat yace "kee" bude ido tayi da sauri, yace "Sakko" ba
musu ta fito daga motar da kyar, ya dau magungunan da drinks din ya rufe motar,
da sauri ya juya ganin kiris ya rage ta fadi ya kara kallon apartment dinsu,
kamo hannunta yyi ta jingina jikinsa. Har suka isa bangarensu, ya bude kofar ya
shiga parlon hade sallama, Imaan ta kwanta saman kujera ya ajiye drugs din
hannunsa da lucozade boost ya kalleta kafin yace komai daddy ya fito parlon,
yace "Har kun dawo kenan?" Mujaheed yayi kasa da kai yace "Eh
mun dawo Abba" dukawa yyi ya dau ledan maganin ya fiddo gaba daya, ya bude
wanda xata sha a lkcn yana kallonta yace "Tashi ki sha magani" Daddy
ya tafi kitchen don dauko table water da cup, Mujaheed daure fuska kamar tana
ganinsa yace "Baxa ki tashi ba?" A hankali ta bude ido ta mike xaune
kamar xata yi kuka, daddy ya iso parlon ya ajiye ruwan da glass cup yace
"So how much is the bill doctor" kallonsa Mujaheed yyi, sai kuma yyi
murmushi yace "Bill kuma Abba" Daddy yace "Eh ba asibiti ku ka
je ba, ga kuma drugs ka siyo" ya girgixa kai yace "A'a Abba, I have
settled everything, Allah ya bata lafiya" daddy yace "Toh madalla,
Allah ya yi albarka" Mujaheed ya debi ruwan ya mika mata tare da drugs din
ta amsa, tana runtse ido ta kai baki sannan ta sha ruwan, mikewa Mujaheed yyi
yace "Xan koma daddy Allah ya bata lafiya" Daddy yace "Ameen
thanks Son" daga haka ya fita parlon, daddy na kallonta yace "Toh
tashi ki shiga ciki ki kwanta" ba musu ta mike ta wuce bedroom dinta.
Mujaheed na shiga parlonsu ya kalli mahaifiyarsa dake sakkowa downstairs, kai
kana ganin shirin da tayi kasan fita xata yi, Anty dake parlor tana kokarin sa
turaren wuta a burner ta kalli Mujaheed tace "Har kun dawo kenan, ya jikin
nata?" Gabansa ya fadi sosai, ya hadiye abu da kyar yace "Eh na
dawo" Anty tace "Daxu Abban ku ke gaya min ka kai Imaan asibiti, da
naga breakfast dinka baka yi ba"
kasa cewa komai Mujaheed yyi, ya d'an saci kallon Umma da ta tsaya stairs tana
kallonsa baki bude, Anty tace "Ji walakanci ba da Mujaheed nake magana
ba" Da kyar yace "Anty ba fa ni na kai ta ba, Abbanta ne ya kai
ta" Shiru Anty tayi ganin yanayinsa, can ta saci kallon inda yake kallo,
d'an tabe baki tayi ta duka ta ci gaba da abinda take, Umma ta juya ta koma
sama, da kyar Mujaheed ya ja kafarsa xuwa dinning, har Anty ta gama abinda take
Mujaheed na xaune bai taba komai a dinning table din ba, tace "Idan baka
ci ka kai min su kitchen a ba almajirai" ya marairaice yace "Anty da
baki yi magana a gaban Hajiya ba" Anty ta maka masa wani kallo tace
"tunda uwata ce ita ba" Bai ce komai ba, bayan wani lkci ya mike ya
fita parlon ko a mafarki bai ma son haduwarsa da Umma, to me ma xai ce mata ta
yadda, part din Inna ya nufa, ya sameta xaune kan tabarma rike da cazbi tana ta
xuba gyangyadi, kwanciya yyi kan kujera ya lumshe ido, inna ta yi gyangyadin ta
mai isarta sannan ta bude ido, a tsorace ta koma baya ganin sa tace "Meye
wannan?" Shi dai bai tanka ta ba bai kuma bude ido ba, tace "Wannan
dai ba yi bane ina Lazimi kato ya fado min parlor ba sallama" Ba tare da
ya bude ido ba yace "Kina gyangyadi dai" rai bace tace "Ya xaka
ce ina gyangyadi ga carbi hannuna, ai asararre ne xai yi gyangyadi a wannan
lokacin walha fa na gama ina lazimi ka shigo sadaf sadaf ban sani ba"
Mikewa xaune yyi yace "Akwai ruwan shayi?" Tace "Eh akwai wanda
uwarka ta kawo min" ya kalleta bai ce komai ba, tace "Can din hanaka
ruwan shayin suka yi?" Komawa yyi ya kwanta, tace "Sai dai in sa
Aisha ta dafa maka don baxan iya ba, baka ji bayana ba tun safe nake aiki, ko
kai baka ga ko ina fess ba, leka dakina ma kaga yanda yake talli" shi dai
bai ce mata komai ba, tace "Duk na
tattara ma yarinyar nan me shigo min daki ta kwanta ta bar min tsummokaran
dankwalayenta idan ta tashi tafiya, suna can baranda na ajiye mata, sai kaga
hasken da dakin yyi wllh, ni dai da xata taimaka ta daina shigar min daki don
Allah, ni tsoron da nake jiye mata idan tayi aure, ko ina fa ta samu barin
kayanta take kamar mahaukaciya, Bukar dai ya haifo abinda ya fi karfinsa"
mikewa Mujaheed ya sake yi ya shiga kitchen, ba a dau lkci ba ya fito rike da
cup din ruwan xafi yace "Ina kayan shayin?" Makulli ta kunce a habar
xaninta ta mika masa tace "Saboda ire iren su Imaan nake adana kayana, ba
ruwana" Ya tabe baki ya amshi makullin ya shiga dakinta, closet dinta ya
bude yaga gwangwanin madara manya har biyu da milo biyu sai kwalin sugar uku,
da kwalin lipton girgixa kai yyi ya sauke madaran da Milo, muryarta yaji a
bayansa tace "Da dai ka bari in xuba maka Mujaheed kada ka min barna"
Wani kallo ya mata, ya debi cokalin Madara har uku ya xuba, ta bude baki cikin
tsawa tace "Kai ubanka ne ya siyo min xaka diba haka, Bukar ne dai mai
siyo min kayan shayi, shi Ahmadu sai dai ya jibge min kayan abinci kamar
mayunwaciya, kudin nan fa da wahala ake samun su" shi dai bai tanka ta ba
har ya gama hada shayin sa ya fita, tayi kwafa ta kwashe kayanta ta maida
closet din ta kulle da makullin tana cewa "Ae dai gobe rana ce" Daga
haka ta fito parlor. Har kusan azahar Mujaheed na bangaren Inna, har ya gaji da
jin muryarta gashi bai taho da earpiece balle ya toshe kunnensa ba. Yana
kokarin tashi ya je yyi alwala jin an kira sllh aka bude kofar parlon ya kalli
kofar da sauri, Imaan ta shigo parlon rike da warmer, har ta rame ciwon kwana
daya sai manyan idanuwa, Inna ta saki baki tace "Wacece wannan kuma?"
Imaan bata ko kalleta ba ta ajiye warmer din hannunta, inna ta rike ha6a tace
"Ni dai naga abinda ya isheni bai ishi ubangijina ba, yanxu fa sai ace
jikinta ne ya tashi, fisabillah dubi yanda yarinya ta zabge ta koma fiyot kamar
kyanwa Mujaheed, anya iyayenki na son ki kuwa yar nan, haka xasu xuba ido suyi
ta kallonki kina wahala ga magani kasadan na wani malami a Maiduguri ance min
babu ciwon da baya warkarwa, dubu hamsin aka ce xa a basa Bukar ya maida ni ban
san abinda nake ba kamar shi ya haifeni, ta rasulu kawata xata cuce ni ne ake
tunani? ce min fa tayi xata min hanyar samun maganin don can bayan tsauni
mutumin yake, kuma babu kalan iskan da bai warkarwa da ciwace ciwacen da ba na
Allah da annabi ba irin na yarinyar nan, amma iyayenta sun ba tsinannun turawa
karfi sun amince masu dari bisa dari ba saurarana xa su yi ba, dubi don Allah
yanda ta fige, lafiya muka rabu jiya amma ga iskan har ya tashi tunda gashi
bata je makaranta ba" Mujaheed yace "ina kika ce mai maganin yake"
Inna ta gyara xama tayi kasa da murya tace "Wllh a bayan tsauni ta rasulu
tace yake, sannan aikinsa yanda kasan yankan wuka, sha ynxu maganin ynxu, duk
xata fitsare ciwon da iskan inji ta rasulu" yyi murmushi yace "Ikon
Allah, boka ne kenan?" Buda baki tayi tace "Kaji salu6a66e ko, ni dai
ka rufa min asiri kar ka ja min kasa Ahmadu ya kafa min sabon babin wa'axi, kai
ynxu fata kake inje wajen boka d'an nan" yace "Atoh, mutumin kirki
dai baxai je bayan tsauni ya xauna ba" tace "Yo ai ni ce gantalalliya
ma da nake xancen nan da kai na mance ashe d'an aiken turawan ne kai ma, Allah
wadaran naka ya lalace, ba damuwa ni da ya xame ma dole xanje samo mata magani
kuma kada wani shege ya min maganan banxa, Allah kuma ya tsine ma turawan nan
dai" Imaan dake tsaye bakin kofa har sannan ta tabe baki tace "Kar ma
ki amso ni baxan sha ba, daddy yace min in daina hada na asibiti da
gargajiya" a fusace Inna tace "Kya tsufa a gida ina kallonki kina
kallona don wllh babu namijin da xai auri ciwo da kudinsa ki karar masa da
tattalin arxiki a asibiti, wllh baxan bari a cucesa ba duk sai na xayyane masa
lalurorin ki don ni ba yar cin amana bace, ni yar gaskiya ce, ke ce ciwon kafa,
kece ciwon baya, ke ce ciwon kai, ke ce ciwon mara, kece sanyin k'ashi, kece
xaxxabi, kece ciwon jiki, ga shegen son jiki sannan in rufe masa da cewa duk
iska ne da ba a san kansa ba, ba ruwana wllh" murmushi Mujaheed yyi ya
mike ya fita don yin alwala, Imaan ta mata wani kallo bata son magana saboda
daddy ta juya kawai ta fice mata daga parlonta tana murguda baki.
I am soo grateful for the birthday wishes from families,
friends, fans, and love ones, Allah bar xumunci ya kara mana shekaru masu
albarka.
[6/11, 12:34 PM] +234 703 570 1601: 🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟
_By khaleesat Haiydar_✍🏻
6.....
Hatta islamiyya Imaan bata iya taje ba ranan banda bacci babu
abinda take, xuwa lkcn jikin ya mata sauki sai dai rashin kwari, Daddy dake
parlor a study area dinsa ya kalli Ammi dake parlon ita ma yace "It's
almost six madam baxa ki tada Imaan ba?" Ta kallesa tace "Kafin
magrib xan tasheta" yace "Amma jikin ba xafi koh?" Tace
"Ehh ba xafi but she's weak" yace "Allah ya bata lafiya" a
hankali Ammi tace "Ameen" bayan wani lkci ta kallesa tace "Am
really disturbed with Imaans health ailment... She have suffered a lot but
always claiming strong, and...." Sai kuma tayi shiru, a hankali ta ci gaba
"I don't want to loose her" Daddy na kallonta yace "Allah plans
best, ke dai ki ci gaba da yi mata addu'a a ko da yaushe wataran sai labari,
Allah xai yaye mata" Ammi tace "In sha Allah" Bayan magrib Ammi
na kitchen taji muryar inna a parlor, fitowa tayi ta gaida ta da ladabi tace
"Sannu da xuwa inna" inna tace "Ina mijin naki?" Ammi tace
"Ya fita masallaci" Inna tace "Daxu Imaan ta xo duk tayi wani
fayau fayau da ita, jikin ne ya matsa mata koh?" Ammi tace "Ehh wllh,
amma taji sauki ma yanxu, tana daki xata yi sllh" Inna tayi kasa da murya
tace "Yanxu 'yar nan idan shi mijin nan naki boko ya gama cutarsa ya ratsa
sa ta ko ina ke baxa ki maida hankali ki tashi tsaye kiyi ta kanki da 'yar ki
ba? Fisabillilah meye laifin maganin gargajiya Aisha, komai sai ace sai asibiti
ga na gargajiya kasadan?" Ammi tace "Gaskiya ne inna" Inna tace
"Wllh malamin a bayan tsauni yake" Ammi ta d'an bude ido tana kallonta,
tace "Ga aikinsa kamar yankar wuka, duk xata fitsare jaraban ta dawo kamar
mutane, amma ni tsoron magana nake Bukar da Ahmadu ba kirki ne da su ba sai su
karee min rashin mutunci suce boka ne alhalin ba boka bane kawai Allah ne yyi
xamansa a bayan tsauni, ta rasulu ta sha xuwa can kuma ana kwana daya da rabi a
hanya kafin a kai, tunda kika ji haka ai kinsan akwai kamshin nasara, tafiyar
kwana daya har da rabi ai kuwa akwai nasara....." Shigowar Daddy ya sa
tayi shiru, daddy ya gaida ta da ladabi ta amsa masa sama sama tana kallon Ammi
tace "Kina ji 'yar nan bari in koma na bar kofa bude kada yaran gidan nan
su min aika aika ga dambun nama ta can daki, dama Mujaheed sai xarya yake min
tun safe, ko shi ya isa ya kwashe, yanxu dai yaushe mijin naki xai koma?"
Ammi tace "Xuwa gobe in sha Allah" Ammi tace "Toh idan ya tafi
ki taho sashina ki same ni mu karasa maganar a can don sirri ne" daga haka
ta nufi kofa daddy na mata sai anjima ko tanka sa bata yi ba. Bangarensu
Mujaheed inna ta nufa tana cewa "Ita kuma Amina bara inje inji ko lafiya
ban ganta yau ba" Mujaheed ne xaune parlor sai Yusuf, Hajiya na dinning
tana jera abinci Rahma na taya ta, gaba daya Mujaheed bai yarda sun hadu ranan
ba sai yanxu da ta riskesa a parlor ta fito kitchen, Inna na kallon Yusuf tace
"Kai ina uwar ka, lafiyarta yau bata xo gaisheni ba" Yusuf yace
"Yanxu da daddaren nan xaki kamo hanyan xuwa nan inna" Hajiya ta
karaso parlon tayi kasa da kai tana daga tsaye tace "An yini lafiya
Inna" Inna tace "Rukayya idan Hadiza ce xa ki gaida ta a tsaye
sandandan haka?" Juyawa Umma tayi ta koma ta ci gaba da abinda take ba
tare da ta bata amsa ba, inna ta kara da cewa "Sannan kiyi min rai ki rufa
min asiri ki daina gaisheni kwata kwata a gidan nan idan kin gan ni, don Allah
bana bukata, wnn ae kanki kike munafurta, kuma Allah ya tsine ma gaisuwar"
Wani kallo Mujaheed ke ma inna fuskarsa daure, inna tayi kwafa tace "Mu
xuba dai, xamu ga mai kwashewa, ae kema ga naki d'an ya isa aure ba don ya
tsaya shashanci ba xaki ji ko da dadi ko babu" mikewa Mujaheed yyi yace
"Ke dai ba dai alkhairi ya kawo ki nan ba sai fitina da complaint, haba
don Allah, gaba daya ba a ta6a maki dai dai...." Inna ta bude baki tace
"Ni kake xagi Mujaheed?" A fusace yace "Mu bar sa a hakan"
daga haka ya wuce ta kamar xai tashi sama, Yusuf ya bi sa da wani kallo, tuni
Umma ta shige kitchen ranta fari fat duk da haushinsa da take ji, Yusuf ya mike
yace "Yi hakuri muje in raka ki" Inna ta fara matsar kwalla tace
"Isuhu kaga abinda Mujaheed ya min ko? Da ina kusa da shi babu mai hanasa
make ni.... Ina mahaifin ku yake" Yusuf yace "Ke dai mu je, Abba bai
dawo ba" Da kyar Yusuf ya lallabata suka fita parlon tace "Wllh in
har Mujaheed zae ci gaba da xaman gidan nan sai dai ni in tafi" Yusuf ya
danne dariyarsa suna isa part din su Imaan ta bude kofa, daddy dake xaune yana
duba laptop ya mike ganinta tace "Bukar babu abinda Mujaheed ya mance bai
gaya min ba yanxun nan daga nayi ma uwarsa gyara, sai ku xaba ko ni ko shi a
gidan nan" daga haka ta rufe kofar. Yusuf dai tuni yyi gaba, suna isa part
dinta ta rushe da kuka tace "Sai yanxu abun ke min ciwo isuhu, kai kaga
wahalar da nayi da Mujaheed kare baxae ci ba wllh" Yusuf yace "Sai
kiyi hakuri, Mujaheed din ki ne fa" a fusace tace "Mujaheed dinsu
dai, bari dai mahaifin ku ya dawo xai gaya min ko shi ke koya masa ya min
rashin arxiki" kiran Isha da ake yasa Yusuf ya bar part din inna, tare
Daddy ya je gun Inna da Imaan bayan isha, Inna ta fito daga daki ta shimfida
tabarma ta xauna tace "Wllh Bukar daga nace ma Rukayya ta daina gaisheni a
gidan nan don na munafurci ne, shi kenan Mujaheed ya hayayyako min yana
huci..." Daddy yace "Kiyi hakuri Inna, ina fita xan je in samesa
yanxu" a fusace tace "Oh oh babu xancen samunsa, kawai ni ba na son
ganinsa gidan ne ko kuma ni in tafi ai dama ya isa aure sai yyi ya koma gidansa
baxan xauna tare da shi wataran ya mareni ba, wai ku me yasa baku san ciwon
uwar ku ba, uwarsa fa na yi ma fada shine ya min rashin arxiki haka, kai ko ga
ka xaune sandandan gabana kana bani hakuri, ya fi karfin ka ne mujaheed din ko
kuma uwarsa ta fi naka ne, Ahmadu dai bai ba yaron tarbiyar da ya ratsa jikinsa
ba wllh" Daddy ya mike yace "Xan dawo anjima inna" daga haka ya
nufi kofa tace "Yauwa, ka titsiye sa sai ya gaya maka ko ni sa'arsa ce
kafin ya bar gidan" shi dai bai ce mata komai ba har ya fita, Inna tayi
kwafa tace "Xai san ya ta6a uwar su yau" Imaan dai na kwance kan
kujera tana kallonta, Inna tace "Ni na ma fara tsoronsa tunda abinda ya
zama kenan yanxu" Imaan tace "Toh ke me ya kai ki bangarensu"
inna tace "Ya za ki ce min haka 'yar nan, ni da gidan d'a na kuma kice me
ya kai ni?" Imaan dai bata ce komai ba, Inna tayi kwafa tace "Ke kin
ga wahalar da nayi da Mujaheed?" Imaan tayi dariya tace "Ae ke dama
kullum sai kice kin yi wahala da kowa" Inna tace "Kee na Mujaheed
k'are baxai ci ba, ni nasan me nake cewa, ina fa tsaye bakin kofar dakin
haihuwa daga safe har dare sannan aka haifesa, sai kin ga wahalar da ya ba uwar
d'an banxan, ai ko aka haifosa lafcece ya kusa biyun wani jaririn, duk ya cika
asibiti da kuka nyaaa ke kina gani kinsan sadauki aka haifo, gashi jajir da shi
fari hulll, gashin kansa kuwa ga bak'i ga cika yanda kika san d'an balarabe, ke
ki bari kawai, nan dai muka koma gida na wanke sa tass, baki ga uwarsa ba lkcn
yar siririya kamar xata karye ba yanxu da ta ci kudin d'a na iya ci ba ta koma
kamar buhun masara, kullum zanyi wanka da sassafe daga gidana in tafi gidan
Ahmadu yi ma fitsararren yaron nan wanka, don babu abinda uwar ta iya wai
tsoron jaririn ma take don bala'i, a haka har yayi wata uku ya koma yanda kika
san bredi wato ya xama wani lukeke, ga kyau tsantsa, ba sai uwar tayi ta cika
masa nono yayi ta tumbudi ba duk k'arni??" Imaan ta fashe da dariya har da
kyakyatawa tace "Shi yayan?" Inna tace "Wllh shi, to ni ko ina
xan iya kazanta da k'arni, oh oh nan na taka mata burki, ga uwar kazama dn har
sannan tana tashen kuruciya ni fa ko abincin gidan bana iya ci da, ana haka har
Mujaheed ya kai shekara biyu, ba sai naga ana neman hallaka yaron ba, ba shi da
aiki sai kukan banxa, fitsari a tsaye kashi a tsaye, ga uban shan yogurt, to da
yake ba yanda na raini ubansa ba kenan bakina a leko na daukesa, kin ji mafarin
komawansa waje na kenan, kuma Mujaheed bai bar gu na ba sai da uban ya biya
masa kudin karatun likita a kasashen turai bayan ya gama sakandari, to ace
banyi wahala da d'an banxan yaron ba kuwa, tsakaninsa da iyayensa fa sai dai
bayan kwana biyu yaje ya gaishesu ya dawo, ko k'uda bana yarda ya ta6a min shi
balle shegun kishiyoyina da duk suka mace yanxu, Allah dai ya ji kansu amma
shari'ar mu da su sai a lahira...." Imaan tace "Ni lokacin ma ba a
haifeni ba koh?" Da mamaki Inna tace "Oh oh kaji wata magana kamar na
ta6a66u, wa ke ta ke, ke da aka haifa jiya jiya, a hannuna fa kika fado, ai
wannan labarin da nake baki a lkcn mu duk mun dauka uwar ki juya ce...."
Imaan ta mike xaune ta hade rai tana kallon inna, inna ta gyara xama tace
"An auro uwar Mujaheed da shekara uku fa Ubanki Bukar ya auri bafillatanar
uwar ki tana tallan nono a lkcn, a gidan sa fa tayi wnn karatun da take takama
da shi" Imaan ta daure fuska tana kallonta, inna tace "Bayan an auri
Uwar ki Aisha da yan watanni na tursasa Ahmadu ya sake aure shine fa ya auro
Uwarsu isuhu, don a lkcn Rukayya na tashen rashin kunya duk an hure mata kunne,
ga kazanta duk ta bi ta ru6ar min da gidan d'a na, To ita kuma uwar isuhu lkcn
kawar Mamarki ce, kin ji musabbabin rashin shirin Rukayya da mamanki har yau,
Rukayya ta dinga jin haushin Aisha tunda kawarta ta aure mata miji, Uwar su
isuhu na shigowa da wata goma sai gashi ta haifo wannan d'an albarkan isuhu shi
ma dai a gabana aka haifesa ina tsaye, ke ko uwar ki shiru kamar malam ya ci
shirwa, ke in takaice maki har bayan shekaru aru aru sai dai uwar ki ta ci ta
sha tayi kashi duk tayi bake bake a gida babu haihuwa babu dalilinsa, babu
yanda banyi da Bukar ya karo mata ba amma yaron nan ya bijire min to duk ta
shanye min shi ta rarraba min sunansa inda bai kamata ba, ke kinga bafillatani?
To wllh kiji tsoronsa mugwaye ne na kin karawa, ni dai na dage rokon Allah ba
dare ba rana don Allah ya warware abinda tayi ma d'a na, to wllh karshe sai da
Ahmadu yayi 'ya ya shidda sannan uwar ki ta haifo ki, murna gun mahaifinki kuwa
ba a cewa komai, duk lkcn fa ba mu san ba lafiyayya bace ke din, nayi ta xuba
idon xuwan kanninki amma shiru, astagfirullah wa ya sani ma ko sai a lahira idan
ana haihuwar tunda gashi yanxu kin doshi ashirin, kuma tun da kika fara wayo
Bukar ya kulla adashin da ba kwasa da asibiti, shine ake nan har yanxu jiya e
yau, ni yanxu mai kwasan ki ma nake tausayi wllh kada ya kasa rike ki, wannan
idan talaka kika aura ae sai dai mu xo wataran mu dau gawarki muna koke koke,
to banda haka sata xai yi ya kai ki asibiti? abinda Bukar yace min a kalla
magungunan ki suna yin kusan dubu hamsin duk wata, wa xai iya wannan idan ba
mai kudi ba irinsu yaran d'an tata, mu dai Allah ga mu gare ka, ka yaye ma
jikata wannan iska da ya sa ta gaba yake cutan ta, ita kenan gun d'a na"
Imaan na hararanta tace "Daga labarin yaya kin wani dawo bada labarina
kamar an tambayeki, har na gaji da jin labarin nan a gidan nan" inna tace
"Toh wa ke ta wani yaya da barin gidan xai yi gaba daya, ai yau sai ya san
ya ta6a uwar masu gida" Da sallama Abba ya shigo parlon, Inna ta daure
fuska, Daddy ma ya shigo parlon Mujaheed na biye da shi a baya, inna na ganin
Mujaheed tace "Ni dai n shiga uku, mutumin nan ya fitar min a parlo don ba
ruwana" Mujaheed ya durkusa d'an nesa da ita ya sunkuyar da kansa yace
"Kiyi hakuri inna" inna tace "Oh oh Allah, ni dai wllh sai naga
kamar tsoron yaron nan ku ke Ahmadu, ni cewa nayi ku taso sa ya bani hakuri? Me
xanyi da hakurinsa, idan da amana Mujaheed zae dinga fifita uwarsa a kai na
kuwa? Ni da na ci fitsarinsa na ci kashinsa ba irin wahalar da ban yi da shi
ba, wannan wani irin fitina ne, me yasa Isuhu baya min haka?" Shi dai
Mujaheed bai dago ba, inna tace "Toh ni dai a bar min parlo na" Daddy
yyi murmushi bai dai ce komai ba, Abba yace "Mu dai sai dai mu ce kiyi
hakuri, shi kuma nasan maganinsa" inna ta wani tsuke fuska bata ce komai,
Imaan dai na kwance sai murmushi take, Abba na kallon Mujaheed yace "On a
serious note Mujaheed be careful... you had better respect yourself in this
house, and mind you no matter how she does her things, how she behaves, how
annoying she might be, she is still my motherr, yes she is my mother I can't
change her from who she is, and you have got to respect her to the fullest, you
keep that grandma and grandchild play aside since she doesn't cherish that, she
have got all right to complain of ur mother, let her be entitled to her
opinion, today shud be the last that she will complain of ur attitude toward
her Muhammad am I clear" Mujaheed bai iya ya dago kansa ba yace "in
sha Allah Abba" Daddy yace "Maa sha Allah" inna da sai tabe baki
take tace "Oho dai duk a banxa tunda baxa ku iya koransa a gidan ba"
Mujaheed yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri" tace "Tashi ka
bani waje, ba dai aure xaka yi ba wataran, wllh duk sai matar ta rama min
abinda uwarka tayi min a duniyar nan, takanas xan tattara kayana wllh in koma
gidanka da xama duk ni xan dinga koya ma yarinyar, nan Rukayya xata ji ko da
dadi ko babu" Mujaheed dai bai ce komai ba, Abba yace "Leave
now" mikewa yyi yana hararanta ta gefen ido ya fice daga parlon, Imaan ta
fara dariya kasa kasa. Ranan juma'ah da daddare Inna na xaune parlonta Imaan
kuma na kwance kan kujera gaba daya ta gaji da labarin da inna ke bata, tana
son tashi ta wuce amma ciwon da kafarta ke mata yasa ta kasa tashi, tun magrib
take wajen bayan ta kawo mata abinci har wajen tara da rabi yanxu, Inna tace
"To kin ji abinda ya raba ni da uwar d'an gwate kenan, kuma fa lkcn kakanku
bai san ina xuwa ba, kai jama'a na xuba farin jini gun masu kudi wllh"
Imaan dai bata tanka ta ba, bude kofar parlon aka yi Mujaheed ya shigo da
sallama, Inna tace "Dama shi kadai ne me shigo min da sallama banda su oh
oh" Ta gefen ido Imaan ta kalleta, ya ajiye ledan hannunsa yace
"Gashi" ta jawo ledan tana budewa tace "Lahh kaza ce kamar yasan
ina marmari wllh " Imaan ta mike xaune, inna ta hade rai ta rufe ledan,
mikewa Mujaheed yyi ya dauko plate ya ajiye gabanta, ta mayar gefe tace
"Ni dai wllh kuna takura ni gidan nan kai da Imaan ba haka isuhu da su
maimoona ke min ba, su basu da sa ido" ta hade rai ta bude ledan ta dau
cinya daya ta dungura masa a plate din, dariya yyi ya dauka yace "Ni fa na
siya maki kazar ba Abba ba" Inna tace "Auuu" kara bude ledan
tayi ta fiddo tsoka daya ta manna masa kan plate din, Ta kalli Imaan tace
"Naga kina son albasa da kabeji dauko kwanon can da kika ci abinci in
kwashe maki in hada maki da tsoka daya"
Imaan tace "Ni nace maki xan ci kaza?" Inna tace "Toh na
sani? Gani nayi kin xabura kin tashi kamar Bukar ya siyo min" Daga haka ta
kai cinya baki tana ci tace "Allah maka albarka Mujaheed duk cikin
jikokina kafi jin k'aina wllh, shi sa ma kana aure zan tattara yanawa yanawa in
koma gidan ka na rantse" ya xaro ido yace "Gidan wa?" Ta kallesa
tana washe baki tace "Gidan ka" yace "A'a wllh ga yar gaban
goshin ki nan kice kuma gidana" tace "Waye yar gaban goshi na?"
Yace "Gata nan xaune" inna tace "Oh oh ni gidan ka xan xauna xai
fi min kwanciyar hankali, idan matar ka xata rainani nasan xajka taka mata
burki kai da baka son abinda xai ta6a ni, wannan salubabbiyar kuma ai yunwa ma
kadai ya isa ya koro ni, ni fa ban jin imaan ta iya girki tunda take ko
tafasasshen ruwan xafinta ban taba d'andanawa ba" dariya Mujaheed yyi, Imaan
ta wani hade rai tana kallon inna, Mujaheed yace "Kinga idan tayi aure
xaki d'an dana idan kin koma gidan ta da xama" Inna tace "Ni fa baxan
xauna gidan imaan ba gidan ka xan xauna wllh" yace "Wllh baxa ki
xaunar min gida ba sai dai nata" Inna tace "Toh me yayi xafi haka,
wannan satin idan nayi gidan ka wani satin sai inyi a gidan ta duk da nasan a
rame dai xan dawo daga gidan nata amma dole naka naka ne, idan na koma gidan ka
sai in murmure" Mujaheed yyi dariya yace "Inaaa ba wannan xancen
gidan mijinta ko gidan Yusuf xai fi maki kwanciyar hankali amma gida na kam sai
dai ki hangesa daga nisa shi ma kuma a photo, Kinga duk sanda mijin nata ya
gaji sai ya koro ki da ita" Inna tace "Wai tsaya Mujaheed da kake
wannan xancen da kudin asibiti mijin xai ji ko da nawa dawainiyar ka fa san
irin cimar da nake ci bana banxa bane, gwara dai a bar sa ya ji da jinyarta, ni
kuma in xauna gidan ka ko Yusuf koh Maimoon, amma ina ni ina xaman gidan imaan
ga yunwa dai kiri kiri tunda ba girki take ba sai a wani fake da ciwon numfashi
kamar yanda uwarta ke cewa" fuu imaan ta mike xata fita cikin rashin sani
plate din da ta ci abinci ta bari wajen ya xamar da ita sai ga ta rijib a kasa,
wani ihu ta fasa da karfi tana cewa wayyo kafarta, Inna ta xaro ido ta mike da
sauri ta bude kofa tace "Ni dai na shiga uku da jaraba, yi maxa fita da
ita Mujaheed, fitar min da ita kar ma ace a parlo na ta fadi" Mikewa
Mujaheed yayi yana mata wani kallo yace "Baxa ki tashi ba" cikin kuka
tace "Wayyo yaya kafana ya rike baxan iya tashi ba" Inna ta gwalo ido
tace "Ka ji ko? Mujaheed ka fitar min da ita kada a sani a bakin
duniya" Ganin da gaske ta kasa tashi Mujaheed ya daga ta, ta zaro ido tana
yarfe hannu tana cewa wayyo kafarta, inna duk ta rude tana ce ma Mujaheed ya
fitar da ita, ko fita basu gama yi ba ta tura su gaba daya, ta kulle kofarta
tasa makulli tace "Dama kada a kuskura ace a parlo na ta fadi wllh don ba
ruwana" Mujaheed ya xabga ma imaan harara yace "Baxa ki tsaya da kyau
ba" cikin kuka tace "Wllh ba karya nake ba yaya kafar ya rike
min" kalle kallen wajen ya fara yi, can yayi tsaki ya dauketa kamar yar
baby ya nufi bangarensu da ita, gam ta rikesa tana rera kuka.🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟
_By khaleesat Haiydar_✍🏻
8.....
Yau Thursday Imaan na dawowa schl bayan tayi wanka ta ci
abinci ta fito parlor ta xauna kusa da Ammi dake xaune, ta langwabar da kai
tace "Ammi ina son xan je supermarket in siya pad da turarurruka"
Ammi ta kalleta tace "Duk uban turarrukan da kika kwaso ranan sun kare
kenan Imaan?" Yar dariya tayi tace "A'a ba su kare ba amma sun kai
rabi" Ammi tace "Toh sai ki kira babanki bani da kudin da xan baki ki
karo turare" Imaan ta bude ido tace "Ya min transfer din 30k ranan da
xai tafi ai" Ammi tace "Tohhhh har 30k, lallai kam Allah ya
taimaka" dariya Imaan tayi ta mike ta koma daki, Hijab dinta gogagge har
kasa ta fiddo ta saka sannan ta dau karamar jakarta ta sa atm card ta feshe
jikinta da turare ta fito parlor, ta durkusa kusa da Ammi tace "Toh Ammi
ba ni kudin transport don Allah" Ammi tace "Ki duba gaban mirror a
daki" tashi tayi ta shiga ta dauko sannan ta dawo parlon, tace "Yauwa
Ammi ina son xan biya ta gidansu Mariya, tun Tuesday bata xo schl ba bata da
lafiya" Ammi tace "Waye kuma Mariya?" Imaan tace "Lahh
wannan da ke xuwa dubani wani lkcn idan bani da lafiya" Ammi tace
"Kice min dai gidansu xa ki je ba supermarket ba" Imaan tace
"A'a fa Ammi, kawai tunawa nayi, Ban ma san ko xan gane gidan ba fa tunda
sau daya muka taba xuwa da Maimoon, idan ban gane ba kawai sai in dawo
gida" Ammi tace "Gwara dai ki gane don ki dubota tunda tana yawan
xuwa duba ki" Imaan tace "Toh Ammi" daga haka tayi ma Ammi
sallama ta fita Ammi na tunatar da ita tayi addu'an fita gida, tana isowa part
din su Yusuf taga Umma da wata kawarta xaune a waje kan fararen kujeru, Imaan
ta dauke kai duk da sun hada ido har ta wuce su ta nufi gate, Hajiya Salaha
tana kallon Umma tace "Wace fitsararriya ce wannan kuma" Wani
murmushi Umma tayi tace "Yar wajen Aisha" Hajiya salaha tace
"Ikon Allah ita ce ta girma haka?" Tabe baki Umma tayi, Hajiya Salaha
tace "Ita Aishar ta sa kar ta gaishe ki gidan nan kenan?" Umma tayi
yar dariya tace "Ga dahir kin gani, ai fa ko idona xai makale cikin nata
shegiyar baxata gaida ni ba uwar ta hanata" Hajiya Salaha tace "Tabdi
ita wannan yar ficicciyar yar?" Umma tace "Ba shine bayan na dawo
gidan nan naga ita da Mujaheed da bai san ciwon kansa ba bai san ciwon
mahaifiyarsa ba tamkar su yi 6ude, ya maida Aisha kanwar uwarsa bashi da tamkar
ta gidan, ita kuma yar mai ciwo yau mai ciwo gobe tunda sickler ce idan kin ga
abinda yake mata ko kanninsa su Ummi bai masu, in takaice maki duk dai Aisha ta
bi ta shanye min shi yanda ta shanye kanin ubansa, yanda kika san xai mata
sujjada" Hajiya Salaha tace "Ikon Allah" Umma tace "Ae tuni
na tashi tsaye, nice can nice nan, da taimkon Allah da taimakon Magajiya na
kwato d'a na da karfi da yaji, yanxu ko ga maciji basa yi a gidan bangaren ma
ya daina xuwa, I can't risk that, uban waye bai san tsafi Aisha take ba, gashi
dai ta hana kanin babansa karo matar da xata haifo masa 'ya yansa duniya ta
rufe masa baki ta hada sa da 'ya sickler kullum ana hanyar asibiti ana kashe
Dan banxan kudade, Allah kenan, kuma in dai ina numfashi a haka yarinyar nan
xata kare yau lafiya gobe babu, in Allah ya yarda sai yar nan sai ta xame masu
jaraba duk sai ta tsiyace su muna nan muna gani, kee duk wanda xata ra6a ma
wllh sai ya tsiyace, haka nan kuma xata yi ta xama ba mashinshini.... to ubanwa
xai iya da ita ta kassara tattalin arxikinsa, ni fa duk duniya billahil azim
bani da makiyiya da ya wuce Aisha, wllh xan iya yin komai don in toxarta ta da
yarta, ni ko kishiyata ban jinta yanda nake jin Aisha, kuma yanda tasa aka
toxarta ni aka min kishiya sai na toxarta ta ita ma ko ba jima ko ba dade, ina
nan dai kan bakana lokaci kawai nake jira" Hajiya Salaha tace "Ae ko
kar ki yarda wllh, ki mata fiye da wanda ta maki ma" Umma tace "Yanxu
gobe ma akwai inda xa ni tare da magajiya da sai ki fito mu je tare, wani take
take na fara gani nake son taka ma abun burki tun wuri" Hajiya Salaha tace
"Haba na me kuma?" Umma tace "Ki ji fa don walakanci yanxu sai
su yi ta makala ma Mujaheed ita ya kai ta asibiti, ga uban kudaden da xai kashe
wanda nasan ko ance xa a basa baxai amsa ba to akan wani dalili? Shi ya dauro mata
ciwon? Na samu na rabasa da shegiyar yarinyar suna kara lika masa ita to gwara
in kara xage damtse, ba wani ke nemo masa kudin ba kuma kudinsa ba na banxa
bane, su je can su da suka haifeta su karata da cutan ta" Hajiya Salaha
tace "Gaskiya kam Allah ya kai mu goben idan kin fito ki kirani"
Tunda Imaan ta fito Yusuf dake xaune tare da mai gadi da sabon drivernsu ke
kallonta, yyi murmushi yace "Ina xuwa Imaan din daddy?" Rufe fuska
tayi tace "Shopping mana" Ya wara ido yace "Kaji Hajiya Imaan,
in taso mu je ki min shopping din nima" dariya tayi ta make kafada tace
"mu je dai ka biya min" yyi murmushi yace "abun yar haka ne
kenan, to wa xai kai ki?" Ta buda hannu tace "Napep xan shiga"
ya bude ido yace "Salon ki kwaso k'ura ki dawo mana da asthma?" Turo
baki tayi yace "A'a bari driver ya kai ki ya dawo dake kawai" Ta wara
ido tace "Da na ji dadi" Ya kalli sabon drivern dake murmushi yace
"Toh driver xa a ajiye mana ita a supermarket" ya mike yace "In
sha Allah, bari in fiddo motar" daga haka ya shiga cikin compound din, Sai
a sannan Imaan ta ga Mujaheed dake xaune kan farin kujera nesa da su yana danna
wayarsa, tana kallonsa ya jefa mata wani harara, ta turo baki ta dawo kusa da
Yusuf tace "Ya Yusuf jiya da na fita inna ta debar maka dambun koh?"
Dariya yyi yace "Aa bata ban ba" ta tabe baki tace "Ba wani nan
nasan dama jira take in tafi sai ta xuba maka ita ma ta ci, ni da ba ma cin
dambu nake sosai ba" yace "Ae ko sai kin ji dadin da dambun yyi, cewa
tayi ita ma ta rama abinda kika mata" bata fuska tayi tace "Ai nasan
sae ta baka nice dai baxata ba" Driver na shiga compound din ya gaida su
Hajiya da ladabi yana rike da makullin motar ba ta amsa gaisuwar ba tace
"Ina xaka?" Yayi kasa da kai yace "Hajiya karama xa a ajiye a
supermarket" Umma na masa wani kallo tace "Anya kasan wanda ya dauke
ka aiki gidan nan kuwa?" Shiru yyi yana kallonta, tace "Toh ita
warcan da kake gani ubanta daban a gidan nan, kuma ba shi ya dauke ka aiki ba,
mai nan bangaren ne ke biyanka don haka ka maida hankalin ka, ka wuce ka ban
wuri nan da 'yan mintuna xaka ajiye kawata gida" kansa a kasa ya risina
yace "Ayi hakuri Hajiya ban sani bane" tace "Ehh ka sani yanxu
ai" hakuri ya kara bata ya juya ya fita compound din, Yusuf na kallonsa
yace "Ya aka yi?" Yayi kasa da kai yace "Hajiya ce tace xa a
ajiye bakuwarta yanxu" Tsaki Yusuf yyi ya mike Mujaheed ya daga kai yana
kallonsa, Yusuf na kallon Imaan yace "jira in dauko mota in ajiye ki"
a hankali tace "Toh nagode" banda hararansa babu abinda Hajiya take
don tasan shi xai sa driver ya fita da imaan, ta ja tsaki bayan ya fita da
motarsa waje, Imaan ta bude front seat ta shiga ya bar layin, sai bayan sun hau
saman titi yace "Amma dai baxa ki shanya ni a mota idan kin shiga shopping
din ba" yar dariya tayi tace "Kasan me ya Yusuf kawai idan ka kai ni
ka wuce ba gida xan dawo ba" Yace "Ina xa ki?" Tace "Xanje
duba kawata bata da lafiya" yace "Wani anguwa?" Ta fada masa
tana kallonsa yace "Su Imaan an fara hankali xa a je duba Mara
lafiya" dariya ta fara yi, har suka isa Supermarket din Yusuf na tsokanarta,
Bayan yyi parking yace "Kar ki shanya ni Imaan, in har kika dde to baxa ki
same ni nan ba, ga ATM dina kiyi amfani da shi ai kinsan pin din" tace
"Ya Yusuf ka wuce kawai ba gida fa xan koma ba nace, kuma Daddy ya turo
min kudin shopping din" yace "Anya gidan kawarki kadai xaki je kuwa
Imaan" ta turo baki tana kallonsa, yyi murmushi yace "Toh yi hakuri,
napep xaki hau xuwa gidan kenan?" Ta gyada masa kai yace "In ji kin
fito da nose mask din ki?" Tace "Ehh yana jaka" yace "Toh
kar dai ki jima gidan kawar don ni baxan iya ba ammi hakuri ba" tayi
dariya tace "Sae ka bata ni dai idan xata dokeni" dubu daya ya mika
mata yace "Sai ki hau napep din tunda Daddy ya baki kudin shopping"
ta amsa tace "Nagode" daga haka ta daga masa hannu ta nufi entrance
din supermarket din. Tun a bakin entrance din yake kallonta har ta shiga mall
din yana biye da ita a baya, gun turarurruka ta nufa, bayan ta dau wa enda take
so har shidda, ta tafi gun pad, ta duka ta dau pad manya biyu kenan sai gashi
yana xuwa toward her, suna hada ido gabanta yyi mugun faduwa don rass ta
ganesa, da sauri ta ajiye pads din hannunta ta dau dettol dake wajen guda biyu,
har ya iso kusa da ita kallonta yake daga cikin bakin spec dake idonsa, ta
dauke kai ta dau wani sabulun ma ta sa a basket din hannunta xata wuxe, yace
"Assalamu alaikum" ba tare da ta kallesa ba ta amsa, yace "Good
evening" Tace "Same" yace "Kin gane ni kuwa?" Kallonsa
tayi bata ce komai ba tayi saurin sunkuyar da kanta ta shiga jera kayan basket
din hannunta, yyi murmushi yana kallonta yace "Dama saboda kina tare da
yayanki ne kika kafe ni da ido jiya a airport, yanxu kuma gashi kin kasa"
juyawa tayi xata wuce yace "Wait" juyowa ta kuma yi, ya duka ya dau
pads din da ta ajiye ya sa mata cikin basket din, still tayi a tsaye, ya wuce
shi kuma gun counter, turo baki tayi ta bi sa da kallo ta gefen ido, bayan wasu
sakwanni ta bi bayansa, bata yadda ta tsaya gun da xai biya nasa kudin wines
din da ya siya ba a mall din, duk da mutanen da suka fi yawa a next counter din
can ta tafi ta tsaya, ana xuwa kanta ta bude jaka xata fiddo atm card dinta
taga ya mika masu nasa, juyawa tayi tana kallonsa ya saka masu pin dinsa a pos
din, imaan dai ta kasa cewa komai, suka cire kudinsu suka mayar masa card dinsa
ya nufi kofar fita, ledan kayanta ta amsa bayan an mata packaging, gabanta ya
dinga faduwa har ta fita bata fatan ganinsa a waje, ai ko tsaye ta gansa jikin
ride dinsa, da sauri ta dauke kai ta nufi bakin titi, ya bi bayanta har ya isa
Inda take yace "In ji yau yaya bai ce ki taho shopping da kafa ba"
bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, yyi murmushi yace "Toh muje in
ajiye ki a gida?" Kamar jira take tace "Nooo" daga haka ta
tsayar da adaidaita fuskarta daure ta shiga, mai napep na tambayarta inda xata
je tace "Mu je gaba" bin su yyi da kallo yana murmushi, sai bayan da
suka yi nisa Imaan ta fada ma mai adaidaitan anguwar da xa ta. Suna isa ta kasa
gane gidan, mai napep din yace "Toh kiyi tambaya mana" a hankali tace
"To wa enda ban sani ba xan tambaya? Kamar fa wancan layin ne" ya
juya yana kallonta yace "Duk fa kin sa na xagaye anguwar nan" Shiru
tayi tana kallon layin da suke tsaye ciki banda haushin karnuka baka jin komai
ko ina silent" mai napep din yace "Duk na kona mai na" yana
fadin haka ya sakko don samun wanda xai ma tambaya duk da ba kowa silent layin
sai mota daya dake tahowa, kana ganin layin kasan na manyan mutane ne sosai, ya
kalleta yace "Ya kika ce sunan layin?" Fada masa tayi, mai motar na
isowa inda suke ya tsaya ta dalilin tsaida shi da mai adai daitan yayi, Ya
sauke glass mai adai daitan ya kalleta yace "Ya layin ma?" Ta hade
rai don ta gaji da gaya masa sunan layin ta sakko daga napep din tana sake
nanata masa, shiru tayi tana kallon mai motan kamar yanda shi ma ke kallonta,
ya d'an yi murmushi yace "Ashe
anguwar mu xa ki xo dama" bata ce komai ba ta wani hade rai, yace
"Gidansu wa kike nema?" Ta sauke kanta kasa tace "Mariya
Ahmad" Yace "I think wancan gidan ne" ya nuna mata gate din
gidan, sae a sannan ta gane wajen, ta kallesa da kyar tace "Nagode"
daga haka ta ciro dubu daya ta mika ma mai adai daitan ya bata dari biyar ta
wuce xuwa gate din. Sosai Mariya taji ddin ganin Imaan ta rungumeta tace
"Imaan a gidanmu, lallai yau za ayi ruwa da kankara, taya kika gane
nan" imaan tayi murmushi tace "i just came to check on ur health daga
shopping mall nake" Mariya tace "wllh naji sauki sosai, gobe in sha
Allah xan je schl" Imaan tace "Toh Allah ya kara lafiya" Mariya
zata dauko mata drinks a fridge tace "Aa ni fa baxan sha ba bana shan abu
mai sanyi" Mariya tace "Ehh akwai mara sanyi ai" murmushi kawai
imaan tayi Mariya ta tafi dauko mata mara sanyi, sosai Mariya ke son Imaan sai
dai Imaan bata da saurin sabo kuma bata sakewa da mutane duk da kowa yasan
mahaifin Mariya mai kudi ne sosai kuma sananne, har kawance ake son yi da ita,
yawanci Mariyar ce ke xuwa gidansu Imaan dubata idan ta kwana biyu bata je schl
ba, ita ko Imaan tun da suka je gidansu Mariyan duba yayarta da aka ma aiki
tare da classmates dinsu bata sake komawa gidan ba sai yanxu, bayan boko
islamiyyarsu ma daya kuma Mariya ma na da haxaka both schl da islamiyya tamkar
Imaan din, Duk yanda imaan ta so tafiya Mariya ta ki yarda wai sai mamarta ta
dawo sun gaisa, mahaifiyarta na dawowa kuwa ta kai Imaan har parlonta, Imaan ta
duka kasa ta gaisheta da fara, matar mai kirki ta tarbe ta tana tambayarta
mamarta, Imaan tayi murmushi tace "Tana gida" Aunty tace "Ya
karatun fa" imaan tace "Alhmdllh" Aunty tace "Maa sha Allah
sai ku yi ta dagewa, Allah ya bada sa'a kin ji" bude kofar dakin aka yi
duk suka kalli kofar, xaro ido Imaan tayi tana kallonsa gabanta na faduwa, ya
mata kallo daya kafin yace komai Aunty tace "Har ka dawo Sadeeq" yace
"Ehh na dawo, ina yini" tace "Lafiya lau" Mariya tace
"ina yini ya Sadeeq" yace "Lafiya lau" Imaan ta sunkuyar da
kanta, yana kallon Mariya yace "Bakuwa kika yi" Mariya tace "Eh
yaya, classmate dita ce Imaan" Yace "Oh I see, sannu da xuwa
bakuwa...." Imaan ta kasa dago kanta tace "Ina yini" yace
"Lafiya lau" Daga haka ya juya ya fita, Imaan na kallon Mariya tace
"Xan tafi Mariya" Turaren Humra mai yawa Aunty ta dibar ma Imaan da
smart collections, Mariya ta amsar mata tana godiya, Imaan tayi mata godiya ta
mike suka fita tare da Mariya Aunty na cewa ta gaida ummanta, Bedroom din
Mariya Imaan ta shiga daukan jakarta da ledan shopping dinta, bayan ta dauka
tana facing Mariya tace "Waye wannan da ya shigo Mariya?" Mariya tace
"Wai ya Sadeeq? Yayana ne shi" Imaan ta xaro ido da sauri tace
"Da gaske?" Mariya tace "Kin san sa ne?" Da sauri Imaan ta
girgixa kai tace "A'a tambaya kawai nake" Mariya tace "He is my
stepbrother, ga bangarensu can, kina shigowa compound part dinsu xa ki fara
gani" Imaan tace "Ayya, ni dai xan wuce kar Ammi ta fara kirana"
daga haka ta fita Mariya na biye da ita, a parlor suka tadda Aunty da Sadeeq,
da fillanci Mama ke ce ma Sadeeq tunda fita xai yi ya daure ya ajiye Imaan ko
bai kai ta har gida ba, Imaan tayi murmushi tace "Aunty ya bar shi xan hau
napep" Mariya ta fashe da dariya, Aunty tayi murmushi tace "Ashe dai
kina ji, kin bar kawar ki a baya, ba abinda ta iya sai shashanci" Imaan ta
kalli Mariya da ta cinno baki tana murmushi, Sadeeq ya mike yace "Toh bari
in ajiye ta" Imaan ta d'an xaro ido, Babu yanda ta iya, bata kuma yi ma
mahaifiyar Mariya musu ba, suka fita tare da Mariya dake rike da ledan ta bayan
Sadeeq ya fita parlorn, Aunty ta bi su har bakin kofa tana ce mata ta gaida
ummanta, cikin motar suka tadda Sadeeq, Mariya ta bude mata front seat Imaan ta
sunkuyar da kanta ta shiga ba don ta so ba, Mariya tace "Byee Friend sai
mun hadu schl gobe, nagode sosai" murmushin karfin hali Imaan ta mata bata
ce komai ba, Mariya na kallon Sadeeq da ya tada mota tace "Ya Siddiq drive
my friend carefully fa" wani kallo yyi mata bai dai ce komai ba yyi horn,
Mariya ta koma ciki tana dariya, har suka hau saman titi babu wanda yace komai
cikinsu, bayan wani lkci yace "Wani anguwar xa ki?" Tana wasa da
fingers din ta tace "Malali" bai ce komai ba, sai da suka kusa bayan
kusan minti sha biyar sannan yace "Wani layin?" Ta gaya masa, daga
nan kuma ta dinga nuna masa Inda xai bi har suka shigo gate din layinsu, dai
dai gidan ta nuna masa yayi parking ya juya yana kallonta, bata yarda ta
kallesa ba tana daukan ledanta dake kan kafarta tace "Nagode" yace
"Welcm" daga haka ta bude motar ta fita ta rufe masa motarsa ya bi ta
da kallo, Tsaye taga Mujaheed bakin gate da alamar fita xai yi don makullin
motarsa na hannunsa, ya kalleta ya kalli motar ya sake kallonta da wani
expression, ta wani daure fuska duk da faduwan da gabanta ke yi abinda yayi ma
Maimoon ranan don an ajiye ta a mota ya fado mata a rai, turo baki tayi ganin
ya ki matsawa daga gate din sai kallonta yake, ta raba ta gefen sa har tana
bugesa ta shige gidan da sauri, juyowa yyi yana ci gaba da kallonta, tana ganin
haka ta kwasa a guje xuwa part dinsu, sai da ta isa entrance din parlonsu ta
tsaya ta juya tana kallonsa, har sannan kallonta yake, ta turo baki ta bude
kofa ta shige ta kulle.
🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟
_By khaleesat Haiydar_✍🏻
9.....
Bayan magrib Imaan ta je kai ma inna abinci ta hadu da Yusuf
a hanya yana dawowa daga bangaren innan, gaishesa tayi ya amsa yace "Wai
ina tsaraban shopping dina ne Imaan?" Tace "Body spray da turare na
siya fa, ka xo sai in baka daya idan yyi rabi sai ka maido min, rabi kawai xan
baka dama" yayi murmushi yace "Toh an gama, yaushe xaki fito part din
inna?" Tace "Ina kai mata xan dawo" yace "Toh idan na dawo
masallaci xan shigo sai ki fiddo min su in xabi wanda nake so" tace
"Tohmm ina jiranka" daga haka ta wuce, Mujaheed ta gani bakin tap din
inna yana alwala, taji muryar innar tana cewa "Mujaheed ka tabbatar ka
datse min pampo wllh cutata kawai Imaan take ta debe min ruwa ta kai ma
uwarta" Imaan ta murguda baki tace "Tunda Imaan kadai ce a gidan
ba" Ta gefen Ido Mujaheed ya kalleta daga durkushen da yake, ta yi watsi
da takalmanta nan bakin kofa ta shiga parlon ta dungure mata warmer din
hannunta, inna ta daga murya tace "Har gwara Ita Mujaheed a kan su Ummi da
Maimoon tunda ita tana tambayata kafin ta diba, su dai diba kawai suke da
hakkina" Juyawa Imaan tayi ta fice mata a parlonta, bata ga Mujaheed din a
bakin tap din ba kuma bai kulle mata ba da kwadon da tace Ga, ta yi wucewarta,
tayi nisa sosai daga part din inna xata dauki hanyar part dinsu ta ga Mujaheed
a tsaye, xaro ido tayi ta juya xata gudu ya cafkota, a tsorace tace "Wayyo
me nayi maka" yana mata wani kallo yace "Uban wa ya ajiye ki a mota
daxu? Ta 6ata fuska tace "Ni yaushe kaga an saukeni a mota, kawai
fa...." wani wawan mari ya xabga mata, ta dafe kuncinta a rude ta fara
kwala ma Inna kira, yana mata mugun kallo yace "Baxa ki gaya min waye shi
ba" Kuka kawai take tana bubbuga kafa har sannan hannunta na dafe a
kuncinta, strictly yace "Gobe na sake ganin haka wllh sai na faffasa maki
jiki, duk gidan nan wa kika ga ana ajiyewa a mota, yar mitsitsiya dake xaki
shiga mota a sauke ki a gida baki tsoron kowa ke gaki kwai da ake
lallabawa" yana kai wa nan ya turata yyi wucewarsa, da gudu ta koma sashin
inna ta shige parlon ta xube kasa tana rusa kuka, Inna ta mike tace "Ae fa
an kwan biyu ba ayi ba, to uban waye ya ta6a min ke?" Cikin kuka sosai tace
"Yaya ne" Inna tace "Waye haka? waye kuma wani yaya?" Imaan
ta ki cewa komai sai kuka, Inna tayi fici fici da ido tace "Shi Mujaheed
din ya sha wiwi ne da xai kai hannunsa jikin ki?" Imaan na shessheka tace
"Mari na yayi ya tura ni" inna ta gwalo ido tace "Mari? Kika
sakar masa fuskar ya mara baki ciccijesa kin gudu ba, uban me kika mashi? Toh
ya tara kuma ya samu, ba a ta6a ki ba ma ya aka kare da ciwace ciwacen ki balle
an mareki a fuska, to mu je ki nuna ma ubansa fuskar" tana fadin haka ta
daga Imaan suka fice parlon, inna na tafe tana kunduma masa duk xagin da ya xo
bakinta, Imaan dai sai ajiyar xuciya ta ke saukewa tana biye da ita, inna ta
tura kofar parlon Abba bayan ta shiga main parlor, Umma ce duke tana sa turaren
wuta a parlon, Inna ta wani hade rai tace "Ke ina mijin ki?" Umma ta
dauke kai tana ci gaba da abinda take tace "Bai dawo masallaci ba, ina
wuni" inna ta xauna saman kujera tace "Ina wuni kuma, dama da ban
wuni ba kya gan ni Rukayya" Umma dai bata ce komai ba, Inna na kallon
Imaan dake tsaye tace "Toh ai sai ki xauna mu jira ubansa koh" Imaan
ta xauna kasa tana goge hawayen idonta, Abba ne ya fara shigowa parlon, yayi
still ganin Inna, ta kafesa da ido tana girgixa kafa, yace "Lafiya kuwa
inna?" Mujaheed dake bayan Abba har ya sako kai jin abinda Abba yace xai
koma baya da sauri suka yi ido hudu da inna, da sauri cikin daga murya inna
tace "Rikosa Ahmadu rikosa, abu ya lalace idan ya gudu kar ka bari ya
fita, xamansa muke a nan" Abba ya juya yana kallon Mujaheed da ya wani hade
rai ya fasa komawan, Abba ya karasa cikin parlon ya xauna yana kallon Imaan da
ta hade kai da gwiwa sannan ya kalli Inna, Mujaheed na satan kallon Umma ya
shigo ya nemi waje ya xauna a kasa, duk ya fi jin ummar tasa a kan inna, banda
faduwa babu abinda gabansa ya ke, Abba yace "Me ya faru kuma inna"
Inna ta kalli Umma dake tsaye tace "Toh Malama xa ki iya ba mu waje in yi
sirri da d'a na koko mu koma daya parlon" Umma bata ce komai ba, Inna tace
"Atoh ke kadai ce bare, nan d'a na ne da jikokina" Umma ta nufi kofa
fuskar nan nata a murtuke, Mujaheed ya sauke ajiyar xuciyan samun relieve daya
wato fitar Ummarsa, Inna ta mike da kanta ta rufe kofar har da sa makulli ta
dawo, Abba dai sai kallonta yake, ta xauna tayi kicin kicin da fuska tace
"Ahmadu daxu Imaan taje kai min abinci bayan ta ajiye ta fita ba sai
wannan yaro Mujaheed ya kamata a hanya ya daddage ya kwada mata wani mahaukacin
mari a fuskarta ba" tana fadin haka ta dago kan Imaan tana nuna ma Abba
fuskar tace "Yanxu fisabilillahi meye wannan Ahmadu, yau ko dabba Mujaheed
ya samu xai maresa haka balle d'an mutum, d'an mutum din ma 'yar kanin ubansa,
to wllh ka dau mataki yanxun nan, Sam baxai yiwu ba, yarinyar da ake kaffa
kaffa da ita saboda lalurorin da Allah ya saukar mata, yanxu gobe ba abun
mamaki bane a ga fuskar ya salu6e wannan irin bugun da yaji, tunda ga irin
yanda Allah yayi ta ko ina ba kwari sae laushi, to wllh ka san abun yi Ahmadu,
shegiya nake idan na yadda" Mujaheed dai ya kasa dago kai sai kallonsa
Abba yake, fuska daure Abba yace "Kai..." Ya dago da kyar, Abba yace
"Uban me tayi maka ka kai hannu fuskarta?" Inna ta gyara xama ta hade
girar sama da ta kasa tana kallonsa, Mujaheed yyi kasa da murya yace "Abba
gani nayi an sauketa a mota daxu...." Abba ya kalli Imaan yace "Mota
kuma?" Inna ta buda ido sosai tace "Mota?? Ina kika samo mota
Imaan?" Imaan ta ki cewa komai ta fara hawaye, Abba yace "Baxa ki
bude baki ki ma mutane magana ba, wa ya sauke ki mota Imaan?" Inna tace
"A'a dakata Ahmadu kada a wani fake da an sauketa a mota a shashantar da
xancen mari, kai ko daukanta aka yi a hannu aka sauketa a kofar gida bai kai
katon d'an ka ya xabga mata mari har haka ba, a kan me? To an sauketa a motar,
ita yarinya ce ko ba ta isa a ajiyeta a mota bane? Idan sabon saurayi tayi fa,
ko dama haka xata yi ta xama ba saurayi?" Daga Abba har Mujaheed kallon
inna kawai suke, ta ja tsaki tace "Wannan ai abun farin ciki ne ni dai a
gu na, to da a mashin roba roba ku ka so a sauketa idan ba a mota ba, ko kuma
idan tayi ta xama ba saurayi Mujaheed din ne xai aureta? Yau naga abinda ya
isheni bai ishi Allah ba, kawai yaro ka tattakure ka kama yar mutane ka falle
da mari ga ka mugun tantiri ko? sannan na taso takanas na kawo kara gun ubanka
ya wani fake da wa ya sauketa a mota salon maganar marin ya bi iska, To Allah ya
Isar mata" daga haka ta mike tana kallon Imaan tace "Tashi mu je,
Allah dai ya isa" Tashi Imaan tayi ba tare da ta yarda ta kalli Abba ba
inna ta ja hannunta ta nufi kofa tana cewa "Ka ci gaba da daure masa kugu
wllh duk randa xuciya ya kwasheni idan ban sa k'attin anguwar nan sun tare sa a
lungu sun nakada masa shegen duka na biya su ba kace ba uwata ta haifeni
ba" da karfi ta rufo masu kofar bayan sun fita, Abba ya sauke ajiyar
xuciya yana kallon Mujaheed, lkci daya ya hade rai yace "Does that warrant
you to slap her Muhammad?" Mujaheed ya kasa cewa komai, Abba ya masa tsawa
yace "Ba da kai nake ba malam?" Da kyar yace "Abba kayi hakuri,
I was only trying to do what I thought was right, duk gidan nan nasan you don't
tolerate yarinya ta shiga motar saurayi" Abba yace "Not to the extent
of slapping her, if she proved to be stubborn why not report her to me? Kasan
halin grandmother din ku, kuma kasan dole sai taje ta gaya mata" Mujaheed
yace "Kayi hakuri" Abba yace "Stupid ba ni xaka ba hakuri ba,
ita da ka mara da innan xaka ba hakuri, kuma kada ka sake wannan wawancin"
yace "In sha Allah Abba" Abba yace "Idan ba hauka ba ma kawai ka
daga hannu ka mari mace?" Shiru Mujaheed yyi, Abba yace "Tashi kaje
kayi abinda na ce maka, ita kuma Imaan din xan hadu da ita" mikewa
Mujaheed yyi ya kara ba Abba hakuri sannan ya fita parlon. A hanya Inna ta
kalli Imaan tana washe baki tace "Ke kice saurayi me mota kika yi
Imaan?" Imaan ta turo baki bata ce komai ba, Inna tace "Toh baki ce
masa kakarki na nan da rai bane naga bai shigo ba, ko yaushe yace maki xai
shigo gaisheni?" Imaan tace "Ni fa ba saurayi na bane, driver din
gidansu kawata ne naje dubota bata da lafiya shine mamansu tace ya maido ni
gida" sake baki inna tayi a sanyaye tana kallonta tace "Ba lafiya...
Direba kuma?" Imaan bata ce komai ba ta shige balcony dinsu ta bude kofar
parlor ta shiga sai a sannan ta kalli inna dake tsaye baki sake har sannan tace
"Sai da safe" daga haka ta kulle kofar ta sa makulli. Washegari da ya
kasance Friday tun da Imaan ta dawo schl take xaune balcony dinsu tana
assignment dinta na maths, Ammi ta kwalo mata kira for the second time ta ajiye
pen din ta amsa, Ammi tace "Idan baxa ki ci abincin ba ki shigo ki mayar
min kitchen nace" Tace "Ammi fa na kusa gamawa saura biyu" Daga
haka ta ci gaba da assignment din, kamar ance ta daga kai taga wata budurwa da
baxata wuce shekaru ashirun da biyu ba tana tahowa, xaro ido tayi ta ajiye pen
din ta mike ta fito tace "Lahh Anty Farida" murmushi kyakkyawar
budurwar tayi tace "Imaan ta mance ni" Rungumeta Imaan tayi tace
"Wllh ban mance ki ba Anty farida, yaya ne yanxu baya bani waya mu
gaisa" Farida tace "Toh ke ba sai kice ya ba ki ba" Imaan ta
tabe baki tace "Ai to yanxu babu ruwana da shi shima ba ruwansa da
ni" dariya Farida tayi tace "Toh saboda me" Imaan na murmushi ta
amshi ledan hannunta tace "Ae yanxu yaya ya xama mugu, wajen inna xa
ki?" Farida tace "Ehh na xo layin kusa da wannan ne nace bari in
shigo yau dai mu gaisa da inna" Imaan tayi dariya tace "Amma yaya
yasan xa ki xo?" Farida tace "A'a bai sani ba" Imaan tace
"Last time da kika xo gaida inna ai tare ku ka je da shi to me yasa yau ma
baxa ki bari ku je tare ba?" Tayi murmushi tace "Na fa ce maki bai ma
san na xo anguwar ba, Ammi tana ciki?" Imaan tace "Ehh tana
ciki" Farida tace "Toh bari mu gaisa" daga haka ta nufi parlon
Imaan na biye da ita, Da fara'a Ammi ta tarbeta tace "Kin guje mu Anty
Farida" banda murmushi babu abinda take tace "Ammi karatu ne wllh,
kinga yanxu ma hutu na xo" Ammi tace "Allah sarki, Allah ya bada
sa'a, ya kuma bada abinda aka je nema" Farida tace "Ameen Ammi"
daga haka tayi mata sallama tace "Xan je mu gaisa da inna" Ammi tace
"Toh idan xa ki wuce ki biyo ta nan mu yi sallama" tace "Toh
Ammi" daga haka ta mike imaan na kallon Ammi tace "Ammi ni dai xan
rakata gun inna, idan na dawo xan ci abincin" Ammi tace "Ai shi
kenan" tare suka fita da farida tana rike da ledan ta, farida budurwar
Mujaheed ce babu wanda bai sani ba a gidan, 2 years back kafin Ummarsa ta dawo
gidan farida kan xo ta gaida Ammi da Anty, idan ko xata je gaida inna dama shi
xai rakata kuma ko minti biyar baya yarda su yi a parlorn kafin inna ta fara
xance yake janta su fita, sosai farida ke son Imaan tun lkcn da take xuwa gidan
lkcn ma bata kai haka ba, suna isa bangaren inna imaan ta bude kofar ta shiga
da sallama, Maimoon da Rahma na parlon xaune tare da inna, Farida ta shiga da
sallama, inna dake xaune kan tabarma ta amsa tace "Wacece wannan
kuma?" Maimoon tace "Lahh Anty farida sannu da xuwa" farida tana
murmushi tace "Yauwa Maimoon, ykk" durkusawa tayi kasan rug tana
kallon inna tace "Ina yini Inna" Inna tace "Lafiya lau ni dai
ban gane ki ba" Maimoon tace "Inna faridar ya Mujaheed ce fa"
Inna tace "Ayyoo farida ce, sannu da xuwa, kai ku kawo mata ruwa da sauran
ayaban nan" Imaan ta mike ta dauko mata ruwa, Inna tace "Allah sarki,
da yake sau uku ya ta6a kawo ki a gurguje shi sa ban gane ki ba, ya iyayen
naki?" Tana murmushi tace "Sun ce a gaida ku inna" Tace "To
madallah muna amsawa, Mujaheed din ne ya kawo ki kenan?" Farida tace
"A'a ni kadai na xo" Inna tace "Atoh ba dole ki xo ke kadai ba,
ni ma duk yau ban gansa ba ko gaisuwar Juma'ah ma bai xo ya min ba daga na kai
kararsa kan ya doki yar kanwar nan ta sa, ko ke haka yayyinki ke cutar
ki?" Murmushi kawai farida tayi, Inna tace "Toh Mujaheed kam cutan
nasa kannin yake, kawai daga an sauke yarinya a babban mota ya daddage ya kwada
mata mari ba laifin fari balle na baki wai ashe ma gantalallen direba ne ya
sauketa, to kin san sa da xuciya sai dai kiyi ta hakuri kawai, dama tun da aka
haifesa na ji irin kukan da yake a asibiti nasan akwai bala'i gaba, baki ji ba
duk ya cika asibitin da muryarsa ga shi wani lafcece" Imaan ta fashe da
dariya har da kyakyatawa Maimoon na taya ta, Rahma dai ta6e baki kawai tayi,
Farida kam sai murmushi take kanta a kasa, Inna tace "Wllh ba xancen
dariya ba nasan abinda nake fada, kuma a yunwace aka haifesa, kilan dai uwar
bata ci abinci ba taje haihuwarsa, mu dai haka muka koma gida na wanke sa tass,
baki gansa ba jazur da shi ba yanxu da ya kode ba, ke kinga wahalar da nayi da
Mujaheed wllh k'are baxai ci ba, tun fa yana tsummarsa nake wahala don sai da
nayi kwana hamsin ina kai komo a kansa, to ba abinda uwar ta iya har na koma
gidan mijina, daga nan kuma sai dai in kai masu ziyara duk sati, lkcn baki ga
uwarsa ba yar siririya doguwa kamar dai yanda kika ga wannan yarinyar
Imaan" Inna na yamutse fuska tace "gashi uwar tayi ta cika masa nono
yayi ta bulbula tumbudi duk k'arni malam, duk jikokina babu wanda yyi tumbudi
kamar Mujaheed, ni ne ma nace uban ya sa masa Mujaheed" Imaan dai an samu
abinda ake so don har wani kwanciya kasa take don dariya, Maimoon kawarta na
taya ta, Farida dai ta kasa dago kai, Rahma ta wani hade rai tana hararan Inna
ko Kadan bata ga abun dariya a wajen ba, Inna ta gyara xama tace "Lkcn
yana da shekara daya da wata bakwai uwar ta yayesa, shi ma fa da kyar, ai duk
cikin 'ya yan Ahmadu babu wanda ya sha nono irinsa, ya tsotsi uwar ba kadan ba,
ko ke baki ga bakinsa d'an tsiyot kusan a tsuke ba? Ai duk tsotso ne yaja haka,
sai yaje gantalinsa ya dawo ki ji yace Nono, uwar sai ta fiddo ta basa ya sha
yyi nak sannan ya mayar, ke in takaice maki da kyar kanwar uwar ta yayesa don
ni dai nace baxan iya wahala ba cikin kishiyoyi, ae ko sai kinga tashin hankali
gunsa, bayan an yayesa kuwa idan Mujaheed ya daga maki roban yoghurt to bai
direwa sai ya kwankwade tass, ga katon ciki yanda kika san an kifa masa kwarya,
Sai uban kukan banxa da shagwaba, ni dai ba komai yasa na daukesa gaban uwar ba
sai ganin xai hallaka, yo hallaka mana katon yaro haka yayi fitsari a tsaye
kashi a tsaye uwar sai dai ta kwashe ta rabu da shi, duk ta dau son duniya ta
daura masa, Shi kuma lkcn kaninsa isuhu na cikin tsumma an haifesa wani fiyot
da shi kamar kyanwa ni na ma xata bakwaini ne" Shiru Inna tayi tana kallon
Imaan, can ta xaro ido tace "Auzubillahi... Ke meye haka kike yi?"
Maimoon ta tsayar da dariyar da take tana kallon Imaan, da sauri ta dagota tana
xaro ido tace "Me ya faru Imaan?" Farida ma ta tashi da sauri ganin
yanda numfashinta ke sama, inna ta mike a rude tace "Kun ga xata ja min
jalala ina xaman xamana ko, to ita nake ba labari da xata dinga dariya haka
taje ta mutu a banxa a buga ni a jarida? kai ku fitar min da ita kar ace a
parlo na ne, meye kuma numfashi na neman daukewa daga ina ba yarinya da ta xo
gaisheni labari? Ni dai ba ruwana a kai ta gun uwarta, ni wllh ba ita nake ba
labari ba" Da gudu Maimoon ta mike xata je dauko mata inhaler suka kusa
cin karo da Mujaheed xai shigo parlon, ya turata yace "Baki da hankali
ne" kamar xata yi kuka tace "Ya M.A Asthma din Imaan ne...."
daga haka ta fita, Da sauri ya karasa yana kallon Imaan yace "What
happened" inna da har ta fara matsar kwalla tace "Ka fita da ita
Mujaheed idan ma asibiti ne ku tafi, wllh ba ita nake ba labari ba xata sa ni a
bakin duniya ni ban ma san lkcn da ta shigo parlon ba" Mujaheed ya kalli
farida da mamaki, inna tace "Ka rufa min asiri ka fita da ita Mujaheed,
meye kuma dariya haka kamar mahaukaciya, ban san meye abun dariya a xance na
ba" dagata Mujaheed yyi suka fita parlon, can kusa da wani flower ya
xaunar da ita yana kallonta yace "Relax now" da kyar take numfashin
kamar xai dauke, Maimoon ta iso kusa da su ta durkusa ta mika ma Mujaheed
inhaler din, budewa yyi ya kai bakinta da sauri, bayan wani lkcn ta dinga sauke
ajiyar xuciya, maimoon dai sai kallonta take cike da tausayi, Ta jingina da
flowern tana ajiye numfashi a hankali hawaye na sauka idonta cikin tsarkewar
murya tace "Yaya xan sha ruwa" mikewa Maimoon tayi ta tafi dauko mata
ruwan da sauri, shi dai kallonta kawai yake, bayan wani lkci ta daga kai suna
hada ido ta kamo hannunsa ta kwashe da dariya, ya daure fuska yace "kina
da lafiya kuwa?" Tana dariya a hankali tace "Wllh yaya babu abinda
inna ta mance bata gaya ma Anty farida ba yau" ya wani xaro manyan idonsa
yace "Kamar me?" Imaan ta kara fashewa da dariya hawaye na sauka
idonta, ya hade rai yace "Baxa ki daina wannan dariyar mahaukatan ba"
ta hadiye da kyar, har wani ciwo kirjinta ke mata cike da karfin hali tace
"Labarin ranan da aka haifeka har sanda aka yaye ka take bata da yanda...."
Ganin yanda Mujaheed ya bude baki da idanuwa yasa ta kara kwashewa da dariya
tace "Wllh yaya har da tumbudi da fitsari da kashi duk ta fada mata"
Mujaheed ya kasa rufe baki, Ganin irin dariyar da take ya sauke boyayyen ajiyar
xuciya yace "Toh dariyar ya ishe ki haka" Mikewa yyi fuska daure xai
koma part din Inna ya hangota tana tahowa da gudu, tsayawa yyi har ta iso yace
"Gaskiya Hajiya ki daina abinda kike yi a gidan nan, ke dai magana magana
magana baya kare maki, wanda ya kamata da wanda bai kamata ba haba don Allah,
ni bana son irin wannan abun, ki shekara kina bada labarin kowa amma banda
nawa, ba ruwanki da rayuwata da yanda aka haifeni ke kenan kowa kice xaki ba
labari baki san bako ba, kawai ke dai kiyi ta magana babu naxari haba don Allah"
sake baki tayi tana kallonsa, mikewa Imaan tayi tana hadiye dariyarta sum sum
xata bar wajen inna tace "Ke dai wannan 'ya ta Bukar anyi munafuka wllh,
to da kika gaya masa dukana xai yi ko ko, ina ce yarinyar da xai aura ce, kuma
laifi ne don na bata labarinsa? Me yasa ban samu masu gadi na basu labarin ba?
Saboda bai shafesu ba, komai fa da ku ke gani a rayuwar nan kamawa yake,
yarinya ta xo gaisheni sai in xauna muna kallon kallo da ita??" Imaan ta
turo baki tace "Ba wani nan, yaya har ce mata ta yi da yunwa aka haifo ka
duniya kana ta ihu a asibiti, kuma saboda shan nono bakin ka ya xama d'an
karami haka, wai sai kaje yawo ka dawo sai ce ma Umma nono sai ta baka ka sha,
shi ma ya Yusuf sai na gaya masa tace an haifesa fiyot kamar kyanwa kamar
bakwaini" Girgixa kai Mujaheed yyi ya bar wajen a mugun fusace Imaan ta bi
bayansa da gudu tana kyalkyala dariya, Inna ta share kwallar idonta tace
"Ni dai ba don gabana aka haifi muguwar yarinyar nan ba wllh sai ince ba
jininmu bace, don gulmarta ya wuce hankali ya dauka, banda haka yaya xa ta
dinga hada mutane fada a gida haka, shi kenan ni kuma bani da Ikon bada labari,
ni daga yau ma kar ta sake xuwa min na yafe abincin, yarinya dai guda daya sai
hada bala'i a gida, gashi ta hadani da Mujaheed xata tafi ta hada ni da isuhu
kuma, ni dai bari Ahmadu ya dawo a ja mata kunne kar ta sake xuwa min, Bukar
dai ya Haifi jaraba"
🌟⭐ *Imaan* ⭐🌟
_By khaleesat Haiydar_
✍️
10.....
A fusace Mujaheed ya
juya ganin Imaan na bin sa yace "Kee Why are you following me?" Ta
xaro ido tace "Ni ba gidanmu xan tafi ba toh??" kwafa yyi ya ci gaba
da tafiyarsa tana kai wa bangarensu ta shiga tana dariya kasa kasa. Sai kusan
karfe biyar Farida ta fito bangaren inna bayan ta cikata da abun arxiki, su
sabulai, omo, malt har da bottle water duk ta xuba mata a leda, Inna ta rakota
har bakin kofa tana cewa "Toh sai ki gaida iyayenki kinji, Allah maki
albarka, nagode nagode, naji dadin turaren da kika kawo min duk da dai ba mai
tsada bane, sai ayi ta hakuri da Mujaheed dai, Allah kuma ya nuna mana lkcn
abun arikin nan" murmushi kawai Farida take ta wuce tare da Maimoon dake
rike da ledan da inna ta bata, sai da suka isa bangaren su Imaan tace
"Bari na shiga in duba imaan" Tare suka shiga parlon da Maimoon,
imaan dake kwance tana kallo ta mike xaune tana murmushi tace "Har xa ki
tafi Anty farida" farida tace "Eh xan wuce ya jikin fa?" Imaan
tace "Ae na ji sauki" Farida tace "Toh Allah ya sauwake xan fito
daxu inna tace kun tafi asibiti da Mujaheed" dariya imaan tayi tace
"Ni dai naji sauki" farida tace "Toh ki dinga yawo da inhaler
din ki amma" Imaan tace "Toh nagode" Ammi ta fito daga daki tace
"Har xa ki tafi Farida" farida tace "Ehh Ammi yamma yayi"
Ammi tace "Toh mun gode da ziyara, ki gaida mamarki da mutan gidan kin
ji" farida tace "In sha Allah xa su ji" body spray uku Ammi ta
sa mata a leda, ta amsa tana godiya suka fita tare da Imaan da ta sa hijab xa
ta rakasu, xaune suka tadda Mujaheed a part dinsu kusa da parking space a kan
farin kujera idonsa a kan wayar hannunsa, farida na daga inda take ta gaishesa
ya kalleta sannan ya mike yace "Why did you come without telling me?"
ta d'an buda ido tace "Saboda baka son inna ta bani labarin ka? To yau duk
naji komai" Dariya Maimoon tayi har da imaan ya watsa masu wani kallo
fuska daure, Farida tayi murmushi tace "Kawai na xo anguwar ne shine nace
bari in karaso in gaida inna" yace "But da rana ai mun yi waya kuma
baki ce kina anguwar ba" tace "Noo ban taho ba lkcn, nima fa ban san
ma xan fito ba, I came on an errand for my mum" Kamar ance Mujaheed ya daga
kai ya ga Ummar sa tsaye a balcony na sama tana kallonsu keenly, farida ta
kalli sama ita ma, ganinta ta sunkuyar da kanta, murya can kasa yace "I
think you have to go in ku gaisa tunda ta gan ki" Tace "Toh"
imaan tace "Toh Anty farida sai wani lkci xan amshi number dinki gun yaya
idan xai bani" ta gefen ido ya harareta, farida tace "Toh shi kenan
imaan na gode sosai" Daga haka ta wuce Maimoon tayi leading din farida
xuwa parlon Umma, Umma na xaune wayar ta a hannu suka shigo, Farida ta durkusa
kasa tana kallonta tace "Ina yini Umma?" Murya can ciki umma tace
"Lafiya lau" Farida na wasa da fingers dinta tace "Ya aiki
umma" umma tace "Alhmdllh" shiru farida tayi, Maimoon dai na
tsaye sai tabe baki take, Umma tace "Ya 'yan gidan naku?" Farida tace
"Suna lafiya" Umma tace "To yayi" bayan kusan minti biyu
farida ta mike tace "Toh xan koma umma nagode" umma tace "Toh a
gaida gida" daga haka ta fita Maimoon na biye da ita, dakin Anty suka
shiga, Anty taji dadin ganin ta, bayan sun gaisa ta tambayeta mamarsu farida
tace "Suna lafiya Anty" Da ta tashi tafiya Anty ta bata dubu daya
kudin transport, Maimoon ta amsar mata don kin amsa tayi suka fita dakin Anty,
Mujaheed na tsaye parking space suka fito gidan, bayan sun iso inda yake yana
kallon farida yace "Gida xa ki koma yanxu?" Tace "In sha
Allah" yace "Ohk mu je in ajiye ki" har ya bude mota wayarsa ya
fara ring, ya duba yaga umma ce ke kiransa, a hankali ya daga ya kai kunne,
Umma tace "Ina jiran ka parlor yanxu" yace "Toh" daga haka
ta katse wayarta, ya kalli Farida a hankali yace "Bari in baki transport
kawai dear, akwai aikin da xan yi yanxu" daga haka ya fiddo dubu biyu ya
mika mata, ta girgixa kai tace "A'a ka bar shi I have transport
thanks" ya mika ma Maimoon yace "Ki bata plss" Maimoon ta amsa,
yana kallon faridar yace "Sai mun yi waya dear" daga haka ya wuce
ciki. Maimoon ta tabe baki tace mu je Anty farida. A hankali Mujaheed ya bude
kofar parlon Ummarsa ya shiga da sallama, tsaye ya sameta ta rungume hannu
tsakiyar parlon wandering about, ya karasa yace "Umma gani" kallon da
ta dinga masa ya sa ya durkusa ya sauke kansa kasa, tace "Mujaheed dama
ban raba ka da wannan yarinyar ba?" Ya kalleta da kyar yace "Umma ni
ban fa san da xuwanta gidan ba, kuma...." Sai yayi shiru, Fuska a murtuke
tace "Kuma me?" Yace "Umma don Allah me yasa baki so na da
farida?" Tace "Ra'ayi! Wato dai har yanxu kuna tare duk jan kunnen da
na maka kwanaki koh? To wllh ka kiyaye bacin raina Mujaheed, ka kiyaye ni a
gidan nan, uban me xaka yi da diyar talakawa ka ja min bala'i, in xama abun
magana gun kawayena, duk fadin kaduna ka rasa budurwar da xaka nema sai wannan
yar, warce iyayenta ke xaune a ghetto ? Haba Mujaheed are you even
alright?" Yace "But Umma I see nothing wrong with that, arxiki fa na
Allah ne, beside suna da rufin...." Umma ta dakatar da shi rai bace tace
"Da ca nayi arxikin na kanin ubanka Sadeeq ne? Ni xaka ma wa'axi? To wllh
in dai kana son kwanciyar hankalin ka a rayuwa ka fita harkar yarinyar nan, su
je can su samu wani kuma, abubuwan alkhairi da ka dinga masu a baya da ciyar da
su da ka dinga yi Allah ya saka maka da alkhairi, ina ji ina gani baxa ka auri
yarinyar nan ba ka xama mai bada charity su talautar min da kai, yarinya dai
dai class dinka in sha Allah xan samo maka tunda naga ba saiti gareka ba, ba
abun mamaki ba wataran ma ka xo min da yar talla kace ita kake so, kai ko
kunyan kanka ma baka ji, dubi yarinyar da Yusuf yake nema xar sha'awa yar masu
kudi ta ma fi ubansa kudi shi ne kai xaka makale ma yar ghetto ko, to wllh ka
guji bacin raina a gidan nan, sannan don munafurci da kinibibi ta shigo sumui
sumui ta nufi gun alakakan kakarka da ba so na take ba a gidan nan salon duk ta
bata ni gunta ta hure mata kunne, don wllh da ban ganta a sama ba dama bata yi
niyyar shigowa gaida ni ba, ta kama ta tafi gun kakarka da kanwar uwarka Aisha
tunda ita ta haife ka, Allah kadai yasan me kakar taka ta k'itsa mata, wato
Mujaheed tarayyar ka da yarinyar ba abu bane mai yiwu wa samm kayi ta kanka tun
wuri, daga this very moment na raba ka da yarinyar na har Abadan abidina, tashi
ka ban waje mara tunani kawai" mikewa yayi bai ce komai ba ya nufi kofa ta
bi sa da harara har ya fita ya kulle mata kofar ta. Xaune yake cikin Lafiyayyen
motarsa nesa da gidan, abokinsa dake gefensa yace "Look ni fa na gaji da
xaunar da ni da kayi cikin mota tun daxu Sadeeq..." Sadeeq ya shafa cute
Beards dinsa a hankali yace "You just chill Fahad... jikina na bani xata
fito soon" Tabe baki abokin yyi yace "Have you changed ur mind about
loving and dating only whites?" Sadeeq ya xaro ido yace "Of course
No, wannan fa yar yarinya ce.... I think she is not even up to 18, she
is....." Sai kuma yyi shiru yana murmushi, Fahad da ya saki baki yana
kallonsa yace "Sweet eighteen kenan" Yar dariya Sadeeq yyi a hankali
underneath his breathe yace "she is beautiful" Fahad yace "and
why didn't you callect her digit?" Wani kallon gefen ido yyi masa yace
"Sai kace nine kai? How on earth xan amshi numberta bata ce in bata nawa
ba" Bude gate da suka ji aka yi yasa duk suka daga kai da sauri, Mujaheed
ne ya fito, walking majestically ya nufi motarsa da yyi parking a waje. Imaan
na xaune bakin kofar kitchen tana ta yi ma Amminta dake girkin dinner hira,
Ammi tace "Daxu inna ta xo fa wai tana nemanki idan kin dawo schl"
Imaan ta xaro ido tace "Ni??? Ba ruwana baxan je ba, ce ma Abba tayi fa
kar in sake xuwa mata ina kwasan maganganunta ina yadawa a gidan nan, ita
gaskiya xata gudu ta bar gidan idan naje mata" Ammi tayi murmushi tace
"Toh tace kwana biyu bata gan ki ba ko jikin ne" Imaan tayi dariya
tace "Xa ma ta fadi gaskiya ne, ba inda xanje ta sake cewa na mata laifi
gwara dai Maimoon ta ci gaba da xuwa tana kai mata abinci" Ammi tace
"Toh ke xa ki kai yau, kina ajiye mata ki gaisheta sai ki fito ba shi
kenan ba" imaan ta bata fuska kamar xata yi kuka tace "Ni dai Ammi nayi
alkawarin baxan sake xuwa part dinta ba fa" Ammi dai bata ce mata komai
ba. Bayan magrib Imaan na Idar da sllh Ammi ta tilastata kai ma inna abinci
sabanin Maimoon da ta dinga xuwa tana kai mata kusan kwana uku kenan, Imaan ta
dau abinci ta fita fuska daure kamar mai shirin yin kuka, tana isa bangaren
inna ta tura kofar ta shiga, Yusuf ne parlon suna hira, Inna na ganinta ta
washe baki tace "A'a takwara ce" imaan ta ajiye abincin ba tare da ta
kalleta ba tace "Ina yini?" Inna tace "Lafiya lau, ni kwana biyu
ban ganki ba nace to ko jikin ne? Duk hankalina ya tashi na tafi sashin ku daxu
Aisha tace ai kin ma tafi boko" Imaan ta tabe baki tace "Lafiya ta
qlau kawai dai umarnin Abba nake bi" inna tace "Umarni kuma? Umarnin
me ya maki?" Imaan ta buda ido tace "Ba ce masa kika yi kar na sake
xuwa bangaren ki ba baki son ganina, shine ai na daina xuwa" Inna ta kalli
Yusuf tace "Oh oh Allah, isuhu kaji wata magana irin na Ahmadu ko, dama an
san babba da hadin fada, ni yaushe muka yi haka da shi, daga nace yayi mata
fada ta daina haka gidan aure xata kuma ba halin xaman gidan miji kenan ba,
shine xai ce nace kar ta sake xuwa min? To ina da masu xuwa ne idan ba ita ba
ko shi xuwa yake yi ya xauna min, ni dai a dinga jin tsoron Allah gaskiya"
Yusuf yyi murmushi yace "Toh ba ga ta nan dai ta xo ba" Inna na
kallon imaan tace "Ni ban yi haka da shi ba gaskiya, ga soyayyen naman ki
can na ajiye maki tun jiya a daki, naki ne da na Mujaheed shima kwana biyu ban
gansa ba sai ki diba naki ki bar masa nasa" Imaan ta turo baki ta wuce
cikin dakin, daukan bowl din tayi ta bude taga soyayyen naman cow din sai
kamshi yake ta xubawa, ta xauna gefen gado ta kirga gaba daya taga yanka sha
takwas ne, murmushi tayi ta fita don dauko leda a kitchen, Inna tace "Kin
diba naki" tace "Leda xan dauko a kitchen" daga haka ta shiga
kitchen din ta dau leda biyu ta boye daya, tana rike da daya ta fito ta koma
cikin dakin, equal ta raba naman ta debi nata, cikin sauran da ya rage ta debe
guda hudu ta xuba a daya ledan ta ajiye sauran, ta window ta jefar da guda
hudun da ta dauka sannan ta fito parlor, inna na kallon hannunta tace "In
ji baki kwashe naman ba nace naki da na Mujaheed ne, don gaskiya nasan halin
ki" ta xaro ido tana nuna mata ledan tace "Duba ma ki gani, guda sha
takwas ne na kirga na dau tara na bar masa tara" Inna tace "Yauwa
kinyi dubara" Yusuf da ke ta kallonta yana murmushi yace "Are you
sure imaan" da mamaki ta kallesa tace "Me that don't even like eating
meat sef" murmushi ya kuma yi yace "Eh naga alama" Inna ta tabe
baki bata dai ce masu komai ba, Ummi ce ta shigo parlon rike da abinci ta kawo
ma inna, inna ta bude warmer din ta girgixa kai tace "Mayar masu, ce masu
aka yi xaman abinci nake a gidan nan shekaranjiya a ban shinkafa da miya jiya a
ban dafaduka yau kuma a ban koren shinkafa, maida baxan ci ba" Yusuf yace
"Toh ae ba iri daya bane wannan fried rice ne fa" Inna tace "Toh
Isuhu ni kenan a cin shinkafa xan kare, wlh na gaji da kaddararren shinkafar
nan, Ahmadun baya ajiye abinci ne" tana fadin haka ta jawo warmer din da
Imaan ta kawo ta bude, shinkafa ce da miya sai salad a gefe shi ma, Yusuf ya
fara dariya, Imaan ma ta kyalkyale da dariya, inna tace "Toh Allah ya mana
tsari" tana fadin haka ta kalli Ummi tace "Ke Mujaheed ya dawo ne ko
yana can yana siyar da abinda ya kasa a titi?" Ummi tace "Ya dawo,
tare muke tahowa kuma ya tsaya yana waya " Bata rufe baki ba sai ga shi ya
shigo da sallama, farar 3 quatre ne jikinsa da bakar riga, Inna ta tura kulolin
gabanta tace "Mujaheed don Allah irin wannan tuwon da ka taba siyo min nake
so ni dai" ya karasa parlon ya ajiye ledan fruits din hannunsa yace
"Ae sun tashi masu siyarwan" tace "Ni dai don Allah ka rufa min
asiri ka tafi, su tashi su je ina?? Bayan ga maza masu fita titi cin abinci ta
dalilin rashin iya girkin matansu" Yace "Ki tambayi Yusuf da karfe
shidda suke tashi" yana fadin haka ya bude warmer din abincin kusa da ita
yace "Wannan kuma fa" tace "Haba Mujaheed shinkafa dai shinkafa
dai inje basir ya cafke ni, wa nake da shi da xai nema min magani, wllh baxan
ci shinkafa jiya in ci yau ba, wannan ai mugunta ce ma" Mujaheed ya tabe
baki yace "Toh ai sai ki sha tea ki kwanta" Ta maka masa wani kallo
tace "Kai xaka gaya min abinda xan yi ko raini?" Yusuf ya mike yace
"Toh bari a samo maki tuwon idan basu tashi ba" daga haka ya fita,
Inna tace "Toh Allah yayi maka albarka, Ya baka abinda kake nema duniya da
lahira, to dama? idan ba kai ba waye, Allah dai ya ma albarka" Mujaheed ya
kalleta ta gefen ido xai fita inna tace "Ga namar ka can a daki, baxan
biye ta halin ka ba ni dai" Ya juyo yace "Nama na me?" mikewa
Imaan tayi ta nufi kofa ta fita sum sum, inna ta bi ta da kallo baki bude tace
"Toh kuwa idan ba wani ikon Allah ba ta kwashe rabon naka, Ummi tafi daki
ki dauko min roban naman, ai ni naga abinda ya isheni bai ishi ubangijina
ba" Ummi ta tafi dakin ta dauko bowl din naman inna ta amsa ta bude tana
kallo ta saki salati ta ajiye ta rike ha6a, Mujaheed ya dau roban yana kallon
sauran naman, inna ta sauke ajiyar xuciya tace "Ta kwashe wllh, gaskiya
dai wannan 'ya ta Bukar bata da hali, muguwa ce ta innanaha, ni wllh da xaka
burgeni Mujaheed ka bi ta har gaban uwarta ka kwato min namana gaba daya na
fasa badawa" Ya ajiye bowl din hannunsa bai dai ce komai ba, Inna tace
"Idan kuma baxa ka ba ni sai in tashi inje, ya xata kwashe min nama gaba
daya bayan na mata bayani, naman fa yyi yanka kusan ashirin shine ta bar maka
hudu, ni dai rabona da a sani magana haka tun kwana uku da suka wuce, to bata
xuwa.... yau kuma ban san uban me ya kawota ba" Yace "Sai da
safe" bai jira cewar inna ba ya fita parlorn, motsin da yaji a bangarensu
Imaan yasa ya tsaya duk da bai yi niyyar tsayawa ba, durkushe ya ganta a
balcony dinsu tana tattara shoes dake wajen xata shigar da su ciki, yana kara
taku daya xata gansa saboda hasken dake wajen hakan ya sa ya tsaya, mikewa tayi
ganin alamar xata fito ya koma baya da sauri ya tsaya jikin flowers, socks
dinta da ta shanya take kwashewa, da sauri ya nufeta tana ganinsa ta saki
takalman hannunta da socks ta gudu xuwa balcony dinsu, Amma tuni ya kamata ta
xaro ido kamar xata yi kuka tace "Yaya me nayi kuma?" Ya daure fuska
yace "Ina naman da kika kwashe" tace "Yaya nama kuma, ni fa guda
shidda na dauka" yace "Dauko shiddan" tace "Toh ai rabona
ne fa" ya mata wani kallo yace "Na fara wasa da ke gidan nan
koh?" Kamar xata yi kuka tace "Toh tasan ba bani xata yi ba kuma ba
ni ta ajiye ma ba meye na sa min rai, baxan sake xuwa parlonta ba ma" yace
"Eh dauko naman" durkusawa tayi ta dau kayan da ta saki, tace
"Mu je parlor in baka" yace "Baxan shiga ba ki dauko min"
tace "Toh ni dai idan baka shiga ba baxan baka ba" ya wani daure
fuska yace "Ke wai yaushe na xama mate din ki a gidan nan?" Tace
"Toh xaka tsammin plss" ya fixgota yana mata wani mugun kallo har
tana jiyo numfashinsa, Bata sake cewa komai ba yace "Tafi ki dauko
min" a hankali tace "Toh" sannan ta nufi balcony din ya bi
bayanta ya tsaya yana kallonta, ta bude kofar ta shiga sannan ta juyo tana
kallonsa, wani murmushi tayi ta wara masa ido tace "Good night yaya"
daga haka tayi banging kofar da sauri ta sa makulli, sosa kansa yyi bayan kusan
second goma ya juya ya fita balcony din yana murmushi. Imaan ta fito daki jin
Ammi na kiranta, da mamaki tace "Ammi ina xa ki kuma?" Ammi na rike
da flat shoe dinta tace "Kin manta yau xa a kawo lefen Seeyama" Imaan
tace "Ohh na manta, to ni Ammi baxan je in gani ba" Ammi tace
"Toh girkin da na daura fa?" Shiru tayi kamar xata yi kuka, Ammi tace
"Toh idan shinkafar ya nuna ki kwashe sai ki taho" Imaan ta washe
baki tace "Toh" Ammi na fita parlon ta tafi kitchen da sauri tayi ta
tsaye tana jiran dahuwar shinkafar, daga karshe da sauran ruwa a ciki ta kwashe
a warmer ta fita da sauri, Hijab ta sa har kasa ta bar gidan xuwa part dinsu
Maimoon, har an kawo akwatunan ta tarar masu kawo wa ma har sun tafi, Anty ce
da kawayen Umma uku suka shiga buda tsadaddun akwatuna set shidda da aka kawo,
Ammi dai na xaune parlon, parlon cike yake da mutane duk yawanci yan uwan Umma
da Kawayenta, Imaan ta nufi inda Maimoon ke xaune duk suna jiran a bude
akwatuna su fara ganin kaya ta durkusa, Umma dai fuskar nan babu yabo babu
fallasa tana tsaye, Kanwar Umma Hajiya Mariya ce tace "Imaan fa an xama
yan mata" Imaan tayi murmushi ta sunkuyar da kanta tace "Ina yini
Mama" Umma ta wani daure fuska tana kallon kanwartata, Hajiya Mariya tace
"Lafiya lau Imaan ya schl ko kun gama secondary din?" Imaan ta
girgixa kai tace "A'a Mama muna ss1" Hajiya Mariya tace "Maa sha
Allah, Allah ya baku sa'a" Umma na kallon hajiya mariya tace "Ban ga
amfanin ki xaune nan ba Mariya da ki tashi ki bar nan kawai" Murmushi kawai
Hajiya Mariya tayi ta mike nan suka dinga fiddo kayan akwatunan, Ammi dai bata
tashi ba, Maimoon ta ja Imaan kusa da boxes din wai su ga kaya, Imaan na daga
kaya taga wani arnen kallon da Umma ke mata, sunkuyar da kai tayi bata sake
yunkurin matsawa kusa da boxes din ba, kaya maa sha Allah sunyi kyau sannan
masu tsada, Hajiya Laraba tace "Kai maa sha Allah lallai Seeyama tayi
goshi, Allah ya sanya alkhairi ya sa gidan xamana, Allah kuma ya nuna mana na
sauran yan matan gidan haka" Umma tace "Toh Ameen amma kuma
lafiyayyun yan matan gidan dai koh?" Kawayenta suka kwashe da dariya Anty
ta daga kai ta kalli Umma, Wata kawar Umma tace "Gaskiya kam irin wannan
kaya ai sai mai lafiya, Mara lafiya kam yyi fatan samun mijin kafin ya sa ran
kaya haka" Umma tayi wani dariya har da shewa, Hajiya Mariya da mood dinta
ya canxa ta dinga kallon yayartata, ita dai Ammi kallon kayan da suke ta
fiddowa kawai take, Umma ta kalli kawarta Hajiya Shafa tace "Ya haka
hajjaju naga baki tashi duba kaya ba ko kema kina cikin sahun yan yi ma 'ya ta
bakin ciki ne naga dai duk kin aurar da naki yaran" dariya sosai Hajiya
Shafa tayi tace "Masu bakin ciki sun san kansu, ni ko in rasa Wanda xan ma
bakin ciki rayuwar nan sai ke, jira nake duk a bar wajen In duba kayan a tsanake"
Umma ta bata hannu suka tafa tana dariya, maganganu marasu dadi Umma da
kawayenta suka dinga saki a parlorn, Anty da abun ya isheta ganin sai xancen
mara lafiya suke tace "Ai kuma Hajiya abun fa ba daga nan yake ba, sai a
ga kuma mara lafiya ya samu abun arxiki a rayuwa fiye da mai lafiya, so nawa
kuma aka yi hakan" wani dariya Umma tayi tace "Toh ayi mu ga ko
basilin xai toya kosai" Anty tace "Kwarai kuwa xai toya sai dai a dau
lkci kawai" Hajiya Laraba tace "Toh ni duk wannan abun fa har yanxu
ban ga amarya ba" Umma tace "Ohh tana can makaranta, gobe xata taho
sun ma kusa gama jarabawa" Hajiya Laraba tace "Ayya tana Zarian
kenan" Umma tace "In sha Allah" Mikewa Ammi tayi tace "Toh
Hajiya Allah ya sanya alkhairi xan je in ci gaba da abinda nake yi" a
dakile Hajiya tace "Oh toh madallah, ban ma san an gayyato ki ba da ina da
niyyar tura Ummi ta kira ki sai ga ki" Ammi bata tanka ta ba tana kallon
Anty tace "Anty Amina, bari inje in ci gaba da girki, kaya sun yi kyau maa
sha Allah, Allah ya sanya alkhairi yasa ayi da mu" Anty tace "Toh
ameen Ammi sai na shigo" Mikewa Imaan tayi xata bi Ammi Anty tace "Au
har xa ki tafi don gulma" murmushi tayi ta shige gaba, daga Umma har
kawayenta suka bi su da kallo ana tabe baki. Sai bayan da suka kusa part dinsu
Imaan tace "Ammi yaushe ne bikin?" Ammi tace "Me ya hanaki
tambayarsu a can" Imaan bata ce komai ba har suka shiga gidan. Da magrib
Imaan taje kai ma Inna abinci taga akwatunan jere a parlonta, Inna tace
"Kinga akwatunan yar uwar ki kuwa?" Imaan ta girgixa kai tace
"A'a ban ga kayan ciki ba" Inna ta mike ta shiga sakko da su tace
"Taho ki fiddo su ki gani, ni sai naga kamar ma mijin rufin asiri kawai
garesa, ji fa na yarinyar nan Khadijah guda takwas aka kawo har da gwal biyu a
ciki wannan kuwa ko axurfa ban gani ba sai dankunnayen kauye" imaan ta
rufe baki xata yi dariya inna ta tabe baki ta xauna tace "Toh naga duk sai
saurayin ya wani xo ya cika mana kofar gida da katuwar mota, ga kaya nan kuma
duk abun kunya, anya ba gudunmawar da dangi suka dinga basa ya xuxxuba mata a
akwatunan ba kuwa, ji fa har da man mai gurguwa na gani a ciki, man da aka yi
yayi tun lkcn haihuwar Mujaheed" Imaan ta fashe da dariya har da
kyakyatawa, Inna tace "Ni daga ganin dankunnayen da sarakuna dama jikina
yyi sanyi, atamfofin kuwa har da na roba guda biyu idan dai ba idona ne yyi min
karya ba, ga wani uban lace duk nauyin tsiya, sannan jallabiyoyin irin Wanda na
taba siya a makka tun ina goyan Ahmadu da naje, bari in fiddo ki gani, ni da
dai a kira min yaron inji muguwar da ta hada ma jikata wannan kayan" tana
kokarin fiddo jallabiyar Yusuf ya shigo parlon tare da Mujaheed, Inna ta juya
tace "Kun ga kayan yar uwar ku kuwa?" Yusuf yace "Na gani sai
dai ko M.A" inna ta mike tace "Toh kai isuhu baka ga irin kayan ba,
dama katuwar motar karya yake kawo mana kofar gida ya paka?" Yusuf ya bude
baki yana kallonta, ta tabe baki ta xauna ta rungume hannu tace "Ni dai ba
ruwana, sai kace xa a basa baxawara" Yusuf yace "Haba inna ina
laifinsa duk fa kayan masu tsada ne wllh" a fusace Inna tace "Amma
kai dai mugu ne wannan yaro, kai ka yarda ka hada ma figalalliyar budurwar nan
ta ka wannan kayan, kai kana ganin idan mun kai masu xa su amsa, mutanen da
suka jik'a cikin kudi gidansu gari guda motoci ta ko ina, Kai in takaice maka
Idan basu koro mu da kayan ba kace ba ni ba" Imaan ta fashe da wani dariya
har da kwanciya inna ta fiddo jalabiyyar ta watsa masu kamar xata yi kuka tace
"Ku ji fa kayan da na taba siya lkcn ina goyan ubanku a makka" Ganin
dariyar da Imaan take Mujaheed ya daure fuska yana kallonta yace "Ke waye
kike ma dariya a nan wai" a fusace Inna tace "A'a bar ta tayi wannan
ae abun dariya ne, har da fa mai gurguwa da basilin irin na tale tale, bar min
ita tayi dariyarta" Tsaki Mujaheed yyi yace "Toh Allah ya sa ta samu
hakan ita" A rikice inna ta mike tace "Auxubillahi... Bakin ka ya
tsari danyen kashi Mujaheed, kai ka so a kawo ma Imaan irin wannan tarkacen, ai
da na shiga uku wllh, bari kaji duk mai auren Imaan sai ya shirya a duniyar
nan, idan na amshi akwatunan ta babu gwal na dan kunne, sarka da awarwaro da
zobe kace ba ni bace, sannan atamfa idan na amshi na kasa da dubu ashirin kace
ba nice Hajiya patu ba, kai in takaice maka idan ba akwatuna sha biyu ba dama
kada shegen da ya xo yace xai aureta don xai ga barbadin bala'i" Mujaheed
da ke gyada kai ya tabe baki yace "Ae sai ku yi ta xama, kinga sai ki
jik'a ta ki shanye ko kiyi kwadonta ki cinye" daga haka ya fice a parlon,
Yusuf ya girgixa kai ya fita shi ma, inna tace "Gantalallu kawai yan
hassada wanda basa son ci gaba na, a haka xa ku yi ta gantali a titi."
Alhamdulillah, Thanks to all those that patronize the book
*Imaan* Allah bar ku da iyayen ku, My book Imaan is for sale coz I am done with
free pages tun friday, ni nasan it will go round as usual, I can't prevent
that, but if you should come across it it's not for free, i repeat it's not for
free, na siyarwa ne, wllh I am too grown up to say Allah ya isa, but have the
fear of Allah SWT in u, don't forget it's my property, hakkina ne, wahalata ce,
pay before reading, pay before reading, or you just over look it and smile,
have a very good conscience plss, and a good conscience won't read happily
without paying, if you want any favor pertaining to d book contact me and let
me know, the book is 300 via..... Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
07087865788 and then u contact me through this digit to be
added in the payment groups. Thanks once more for patronizing.
For those saying xa su same shi a banxa yana yawo to gashi...
amma fa ba a banxa yake ba wllh, there is power in the tongue, Karamin hakkin
da ka raina..... 😃😃
11. 🌟⭐ *imaan* ⭐🌟
Kasancewar ranan Alhamis ne Imaan na dawowa schl bayan ta yi
wanka ta fito ta d'an cito abinci kadan ta koma bedroom ta saka kayanta ta sake
fitowa parlor, Ammi dai sai kallonta take don tun daga ganin d'an abincin da ta
ci ta san da matsala, Ammi tace "What's wrong with you?" A hankali
tace "Ammi cikina xai fara min ciwo ne" Ammi tace "Toh Allah ya
sauwake abincin ya ishe ki?" Kai ta gyada mata ta xauna kusa da ita tace "Ammi
na dade fa ban je gidan gwaggwo in gaisheta ba" Ammi tace "Jiya ma ta
tambaye ki da muka yi waya, ran Saturday idan kin dawo islamiyya sha biyu sai
ki tafi, before four ki taho gida saboda islamiyyan yamma" Imaan tace
"Toh Ammi me yasa gobe baxan je ba" Ammi tace "A'a xan je xa mu
duba ma Halima kaya an kawo daga dubai, idan kin dawo schl ma baxa ki
sameni" Imaan tace "Toh, Ammi ankon mu fa?" Ammi tace "Idan
kin je sai ki tambayeta" Imaan tace "Ammi bikin na Anty Seeyama xa a
fara yi ko Anty Halima?" Ammi tace "Na Seeyama saura two weeks,
Halima kuma saura sati hudu" Imaan tace "Toh Ammi na Seeyama baxa a
mana anko ba?" Wani kallo Ammi tayi mata tace "Kin ishe ni kuma
haka" Shiru Imaan tayi, can ta mike tace "Ammi xan je wajen
inna" Ammi tace "Toh sai ki dauko magana idan kika tashi dawowa"
dariya kawai tayi ta sa takalminta ta fita parlon ta rufe kofar. Inna na share
waje Imaan ta sameta, Inna ta mike tace "Baki ji bayana ba Imaan tun daxu
ban xauna ba wllh, aiki dai aiki dai, to kuwa idan mutum bai yi aiki ba ai sai
kazanta ta ra6e sa, to ni ko yaushe xan yarda hakan ta faru???" Imaan tace
"Toh me kike sharewa a nan din, naga ba datti" inna ta xaro ido tace
"Toh k'uran dake yashe a kasa kuma uwaki ce ba datti ba?" Imaan ta yi
dariya tace "Toh ai sai kiyi ta sharewa" daga haka ta shiga ta bar ta
a wajen, bayan minti goma inna ta shigo parlon ganin yanda Imaan take yatsine
yatsine ta hade rai tace "Me kuma ya faru?" A hankali tace "Wllh
cikina ne xai fara min ciwo" Inna tace "Toh tashi ki tafi gidan ku ba
ruwana da wahalan ki, ko ba jini bane" Imaan tace "Toh ai bai xo ba
kawai dai yana min ciwo ne" inna tace "Toh kiyi maxa ki tafi uwar ki
ta kai ki asibiti, haka wancan karan kika cuce ni kika daga min hankali, ni dai
da xaki dinga rufa min asiri duk kika ji baki da lafiya ki daina taho min nan
sai kin ji sauki, a gaskiya kina shiga alhakina" Imaan bata tanka ta ba,
Inna tace "Kin ko ji abinda nace" Imaan ta daure fuska tace "Sai
nan da kwana biyar ko shidda ma xai xo, ni dama haka yake min ba shi bane"
Inna ta tabe baki ta mike ta nufi dakinta tace "Ni dai ba ruwana kar a xo
a dameni a gigita ni" Imaan ta gama juye juyenta bacci ya dauketa. wajajen
karfe shidda Inna na daki duk ta fiddo da kayan closet dinta tana masu linkin
guga jin an bude kofa ta ajiye kayan xata fita parlor, ta labule ta hangi
Mujaheed tsaye cikin parlorn, kana ganinsa kasan daga aiki yake don ko tie din
wuyarsa bai cire ba kan farar shirt din jikinsa, kallon Imaan dake bacci ya
tsaya yi sannan ya kalli kofar dakin Inna, can dai ya karasa kusa da ita ya
duka ya kai hannu a hankali kan goshinta yana feeling temperature dinta, sauke
hannunsa yyi kan wuyarta ta bude ido tana kallonsa, yace "What's
wrong?" Cikinta ta nuna masa kamar xata yi kuka, daga cikin dakin ya ji
muryar inna tana cewa "Don Allah a dinga kyakkyawan xato dai, Shikenan ita
kuma a rashin lafiya xata kare kamar warce ta kashe mai rai ka wani kai hannu
kana tattaba jikinta kaji ko da xafi ko babu, to babu, kuma lafiyar jikata qlau
ka matsa wajen tunda fatan ciwo kake mata, dama likitancin hauka ne"
Mujaheed ya dinga kallon kofar dakin, inna ta fito tace "A dai ji tsoron
Allah a dinga kyakkyawan xato fisabilillahi, lafiyarta lau wllh, al'adarta ce
kawai ke kan hanya shine ta langwabe haka, ka shigo kana wani tabe taben
jikinta salon a ja mata wani ciwon tunda a haka ake so ta kare" Shi dai
kawai tsayawa yyi yana kallon inna fuskarsa daure, can ya juya ya nufi kofa,
inna tace "Toh Ina yini... yanxu ka dawo daga aikin kenan" bai tanka
ta ba har ya fice parlon. Kafin magrib Imaan ta watsake gaba daya, bata shirya
barin part din Inna ba sai kusan karfe goma na dare tare da Yusuf, Inna na
kallon Yusuf tace "Isuhu wai daga na fadi ma Mujaheed gaskiya daxu shine
har yanxu bai tako nan ba, to me xai bani da Allah bai ban ba, banda ma magana da yake sa ni idan ya xo, ni dai
kai da Imaan kun isheni ni kar ma ya sake xuwa" Yusuf yyi murmushi bai dai
ce komai ba ya fita yana kallon Imaan dake tsaye gaba daya hankalinta na kan
film da ake yace "Ko dai in tafi ne Imaan" tace "A'a ya Yusuf
jira ni, ynxu xa a gama" yace "Toh ki kwana nan mana" da sauri
ta fice a parlon har tana tuntube, Yusuf ya fara dariya, Inna ta ja tsaki tace
"Toh banda ki yamutse min gado ki bar ni da aiki amfanin me xaki min idan
kin kwana Imaan?" Yusuf ya kulle mata kofarta suka wuce, a hanya yace
"Me yasa baki son kwana wajen inna imaan?" Ta make kafada tace
"Karfe uku idan ta tashi sai tasan yanda tayi ta tashi mutum, tayi ta masa
surutu har sai baccin ya fita idonsa" Yusuf yyi dariya yace "Dole ma
gobe ki kwana can tunda Friday ne" Imaan tace "Sai dai kai ka
kwana" daga haka ta shige balcony dinsu tana daga masa hannu yyi murmushi
yana kallonta yace "Good night" yana wucewa ta shiga ciki ta kulle
kofarsu.
"Wannan iskancin
da kike ki tafi exams babu karatu baxa ki min shi a gidan nan ba wannan
karan" Cewar Ammi kenan tana kashe kayan kallon parlon gaba daya, Imaan ta
dinga kallonta kamar xata yi kuka bata dai ce komai ba, Ammi ta nemi waje ta
xauna tana danna wayarta, A hankali Imaan tace "Ranan Monday fa ne exams
din Ammi, i still have Saturday and Sunday sannan Monday da safe" Ammi
tace "Ki tashi ki dau abincin Inna ki kai mata baxa kiyi kallon ba, kuma I
promise you har ku gama jarabawan nan baxa ki kunna kayan kallo a gidan nan ba,
ko yaushe kika xama dedicated da kallo haka ban sani ba" da mamaki Imaan
ke kallonta, can tace "Amma ammi ban taba daukan sama da second position
ba fa a schl" Ammi tace "Ur silly First position ba karatu? I want to
see ur grade idan kika yi karatu this time around" Imaan ta dauke kai
kamar xata yi kuka tace "Ni da ma ba wani kallo nake ba sai lkci lkci kuma
da ace 5th nake dauka shine sai ki ce in daina kallo fa Ammi" Ganin kallon
da Ammi ke mata ta mike ta sa hularta ta wuce kitchen ta dau abincin inna dake
ajiye tun daxu ta fice gidan, har ta isa part din inna ji take kamar ta fashe
da kuka, ta bude kofar ta shiga, xaune ta tadda inna da bowl din fura a gabanta
ta daura kafa daya kan daya, Yusuf na xaune parlon shi ma da cup din furan a
hannunsa, sai Ummi dake shan furan ita ma, Mujaheed dai idonsa na kan tv ga
nasa cup din furan a kusa da shi, Inna na ganin Imaan ta daure fuska ta rufe
furan gabanta ta mayar bayan ta tace "Ni dai wllh ya kare, ba ruwana sai
kun ga mutum da abu ku wani dinga tururuwan xuwa, to duk na rabar..."
Imaan ta ajiye abincin hannunta tace "Toh ni ina ruwana da furanki ce maki
nayi xan sha?" Inna ta kalli Ummi tace "Ke tashi ki shigar min da
abina ciki" Ummi ta mike ta dau furan ta kai daki ta fito, imaan ta turo
baki tace "Sai kace nace xan sha" Inna tace "Toh ai sai ki juya
ki tafi koh?" Imaan ta ki fita don har ranta take son fura da nonon barin
idan inna ce ta dama kuma ita tayi furan da kanta, inna ta kalli na Mujaheed
tace "Dama ga wannan Boss din ya ji sha, ko raina wanda na tarfa masa yayi
Oho, da yake Rukayya ce tayi min wahalan aikin furan Ahmadu kuma ya siyo min
nonon, cewa ma yayi baxai sha ba ki dauka ki sha, Allah yayi da rabon ki"
Yusuf yyi yar dariya yana kallon Imaan, Imaan ta saci kallon Mujaheed dake
kallon TV har sannan, ta kalli rabin cup din furan kusa da shi, inna tace
"Tunda fa aka ji yace baxai sha ba fa baxai sha ba, kawai ki dauka rabon
ki ne, don ni bani da wanda xan baki in kwana da yunwa" Imaan tace
"Toh wai ni nace maki xan sha ne?" Tana magana tana kallon kofar
parlon lkci daya ta suri cup din tayi waje a guje Yusuf ya kyalkyale da dariya
don yasan abinda xata yi kenan, Inna ta washe baki tana kallon Mujaheed tace
"Allah ya kara" mikewa Mujaheed yyi fuska daure ya bi bayanta, Inna
ta rushe da dariya har da kyakyatawa tana kallon Ummi tace "Da dai ki
tashi ki kulle min kofa da makulli tunda sun fita" Kafin Imaan ta kai
rabin hanya dama gaba daya furan duk ya xube saboda gudun da take, Mujaheed ya
cafketa daga karshe ta fasa ihu ta sake cup din hannunta ta kama hannunsa tace
"Wayyo Yaya don Allah kayi hakuri inna ce tace in dauka" da mamaki
yake kallonta yace "Yaushe na fara wasa da ke gidan nan amma?"
Jikinta na rawa tace "Don Allah kayi hakuri Yaya" fuska daure yace
"Kiyi providing min furan nan yanxun nan idan ba haka ba wllh kinji na
rantse sai na sa ki kuka" ta fashe da kuka amma ba hawaye tace "Yaya
bayan kana gani duk ya xube nima ban sha ba, don Allah kayi hakuri xanje waje
in siyo maka wllh" ya wani hade fuska yace "Wannan nake so ba na waje
ba" ta marairaice tace "Toh yanxu yaya a ina xan samo maka wani, nima
fa kaga bata bani ba" ya kalli part din Inna sannan ya kalleta, murya can
kasa yace "Kinsan abinda xa ayi yanxu?" Ta kara marairaicewa tana
girgixa masa kai, yace "Komawa xa kiyi part dinta ki shiga daki ki fito da
bowl din furan da gudu yanda kika fito min da nawa yanxu" ta xaro ido tana
kallonsa, sai kuma ta fashe da dariya tace "Yaya kasan baxata bari ba
fa" ya hade rai yace "Irin dubaran da kika yi kika fita da nawa haka
xaki fito da wancan ma ae" Imaan ta dinga dariya har da kyakyatawa, ya ja
kunnenta yace "Baxa ki daina wannan dariyar mahaukatan ba" ta hadiye
dariyar da kyar tace "Toh amma tare xa mu sha?" Yace "Eh
mana" tana murmushi tace "Toh nasan yanda xan yi" a tare suka
koma part din inna ya nuna mata bayan window din bedroom din inna yace "A
can xa ki sameni ina jiran ki" tace "Toh" daga haka ya wuce yana
waigota, a guje Imaan ta shige parlon inna tana cewa "Wayyo inna kice masa
wllh kar ya ta6a ni xan gaya sa da Abba, inna kice kar ya taba ji xan kira
daddy na...." Mujaheed yyi murmushi ya koma bayan window din ya tsaya yana
shafa kansa, Inna ta mike da sauri kar Imaan ta take ta koma wani wajen ta
xauna tace "Fito min daki wllh, ba ruwana ku je can ku karata kar wanda ya
dameni, yara dai kamar na jaraba" Imaan da ta shige dakin tuni ta dinga
dariya kasa kasa ta dau bowl din furan ta datse murfin yanda idan tana gudu
baxai xube ba, ta tattara rigar jikinta tayi saitin bakin kofar fita sannan ta
fice a dari da sittin, inna ta kyakkyafta ido don tabbatar da abinda ta gani
hannunta amma tuni Imaan har ta fice parlon kamar xata tashi sama, inna ta mike
da sauri tace "Isuhu me na gani a hannunta kamar kwanon fura na???"
Ummi ta kyalkyale da dariya tace "Wllh shi ne" Yusuf ya fashe da
dariya, Inna ta fashe da kuka tana kallonsa. Imaan bata tsaya ba sai da ta isa
inda Mujaheed yake jiranta, murmushi yayi ya amshi bowl din yace "Yauwa
kinyi kokari" ta washe baki tace "Nagode" ya xauna kan dakali
dake wajen ya bude bowl din ya dau ludayin ciki ya juya furan sannan ya fara
sha, Imaan ta daina murmushin da take ta durkusa gabansa tace "Yaya kai
kadai xaka sha" Ya harareta yace "Toh da ni da wa xa mu sha?" Ta
xaro ido tace "Wllh baxan yadda ba ni fa na sha wahala na dakko kaga irin
gudun da nayi yanxu ma fa kirjina ciwo yake" banxa yyi da ita yana shan
furansa don furan inna ba dai dadi da gardi ba, Ta fashe da kuka tana kallon
sa, ya hade rai ya debi rabin ludayin hannunsa ya kai bakinta, ta turo baki
tace "Wannan d'an kadan din bayan kai cika wanda xaka sha kake?" Yace
"Baxa ki bude bakin ba" ta bude bakin da kyar, ya xuba mata yace
"Toh tashi ki tafi" kamar jira take tace "Wllh baxan tafi ba ji
fa abinda ka bani bayan ni na sha wahalan daukowa, Allah sai dai ka bani in
mayar" Yace "In baki ki gudu da shi gidanku dai" Ta fashe da
wani dariya har da kyakyatawa, ya harareta ya ci gaba da shan furan, kamar xata
yi kuka tace "Yaya" ya kalleta sannan ya debo furan rabin ludayi ya
kai bakinta, kin bude baki tayi tana masa wani kallo, ya kai bakinsa ya shanye,
ta fashe da kuka, yayi light murmushi ya kara deba ya kai bakinta, bude bakin
tayi ya juye mata, daga nan ya ci gaba da sha bai kara kallonta ba, kiris ya
rage ta fashe da kukan gaske, ganin bai san tana yi ba ta fixge ludayin
hannunsa, ya wara ido yace "Ke ina wasa da ke ne" ko kallonsa bata yi
ba xata diba ganin xai dauke bowl din ta marairaice tace "Don Allah yaya
ka bari in sha wllh baxan cika ba" yace "To diba in gani" ta
turo baki ta ciko ludayin ta kai baki da sauri, ko shanyewa bata yi ba ya fixge
ya juye ragowar a bowl din sannan ya diba ya kai baki, tana ganin haka ta dauke
bowl din ta kai baki ta kwankwade ya xaro ido kafin yace komai suka ji muryar
Inna cikin kuka tana cewa "Ahmadu idan ba a bi min hakkina ba yau a
babbake ni cikin dare idan na kwana cikin gidan nan" Mikewa Mujaheed yyi
da sauri xai bar wajen imaan ta mike ta rikosa a rikice tace "Wayyo yaya
kai ne kace fa in dauko" Ya wani xaro ido yace "Ni?? You are sick,
kar ma ki sa ni a maganan nan" daga haka ya bar gun da sauri don da dukkan
alama nan suke taho, Imaan ta bi sa da gudu har suka iso gaban compound din
gidan, ya wani hade rai yace "Wai me yasa kike bi na ne ma dai
tukun?" Ta marairaice tace "Yaya kai fa ka sa ni" Ya xaro ido
yace "Ohh dama idan nace ki shiga wuta sai ki shiga, kar ki kuskura ki
ambato sunana a maganan nan" on a serious note ya fadi hakan, ta hararesa
tace "Wllh kai ne kace in dauko da gudu in fito" xai yi magana suka
ji alamar suna tahowa, inna na cewa "Kuma ko tantama babu wannan tantirin
Mujaheed din da ka haifa ne xai sa ta, banda haka imaan ta san wani sace
abincin mutane ta fita da gudu, wllh a min iyakan gaske da yaran nan a gidan
nan yau, a kan me xa su dinga cutata suna ci min mutunci haka, wai har sun
shanye furan sun bar min kwano a bayan window, me nayi masu a rayuwa xa su min
haka" tana kai wa nan ta rushe da kuka, Anty tace "Kiyi hakuri don
Allah inna" a fusace inna tace "Shegiya nake idan na hakura, a sace
min furan a shanye kice in hakura kamar uwata tace min je ki kya gani, ae Aisha
dai ta haifi fitina, wannan yarinya Imaan dai fitina ce wllh, a ma kira min
Bukar yanxu, idan ban tada gidan nan da bala'i ba yau ace bani ba" da
sauri Mujaheed ya nufi gate, imaan kamar xata fashe da kuka tace "Wayyo
yaya" sai da ya kusa gate ya juya yana kallonta ya fara dariya kasa kasa,
bin bayansa tayi da gudu, gun motarsa dake parke a kofar gida ta gansa xai bude
maxaunin driver, ya buda ido yace "Wai me yasa kike bi na ne?" Ta
karasa gun motar tace "Wllh yaya ni ba ni kadai xa a gani a gidan ba bayan
ni da kai muka shanye, kawai Ammi ta kama ni ta min duka" ya daure fuska yace "Kinga ki juya ki
koma ciki wllh" ta fashe da kuka ta make masa kafada, ya shige driver
seat, ta bude front seat ta shiga tana turo baki, yace "Wai kin san inda
xa ni" kin cewa komai tayi, jin an bude gate ya rufe door dinsa da sauri,
Yusuf ne ya fito, Mujaheed ya tada motarsa ya yi zooming off, Yusuf ya dinga
dariya mai gadi na kallonsa, sai da suka hau saman titi Mujaheed ya kalleta
yace "Dama seriously idan kika kira sunana a case din nan wllh sai na sa
ki kukan sati daya, sai ki gaya masu furan ma ke kadai kika shanye" Ta
gefen ido ta kallesa kafin tace "Sai dai in ce masu ludayi daya da rabi
kawai na sha sauran kuma ban san wanda ya shanye ba" Yace "Kina son
in sauke ki nan kenan" ta marairaice tana
kallon sa, yace "Toh me xaki fada masu a kan furan" a hankali
tace "Cewa xanyi ayi hakuri ni da yaya muka shanye" parking yyi gefen
titi, ta rikosa da sauri tace "Aa yi hakuri xan ce ni kadai na
shanye" ya hade girar sama da ta kasa yace "Ki rantse" Kamar
xata yi kuka tace "Bayan ni da kai muka sha"
Alhamdulillah, Thanks to all those that patronize the book
*Imaan* Allah bar ku da iyayen ku, My book Imaan is for sale coz I am done with
free pages tun friday, ni nasan it will go round as usual, I can't prevent
that, but if you should come across it it's not for free, i repeat it's not for
free, na siyarwa ne, wllh I am too grown up to say Allah ya isa, but have the
fear of Allah SWT in u, don't forget it's my property, hakkina ne, wahalata ce,
pay before reading, pay before reading, or you just over look it and smile,
have a very good conscience plss, and a good conscience won't read happily
without paying, if you want any favor pertaining to d book contact me and let
me know, the book is 300 via..... Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
07087865788 and then u contact me through this digit to be
added in the payment groups. Thanks once more for patronizing.
For those saying xa su same shi a banxa yana yawo to gashi...
amma fa ba a banxa yake ba wllh, there is power in the tongue, Karamin hakkin
da ka raina..... 😃😃
12. 🌟⭐IMAAN⭐🌟
Gidan wani cin abinci Mujaheed yyi parking, yace "Ki
jira in fito..." da sauri tace "Nima ba a cc abinda na ci wllh"
ya kashe wayarsa kamar baxae ce komai ba sai kuma yace "meat pie daya ya
ishe ki" kafin tace komai ya bude motar xai fita, da sauri tace "Yaya
amma fa ban sa takalmi ba" da sauri ya kalli kafarta, yace "Good
kinga sai ki jira ni in ci abinci in fito" Ta fashe da kuka tace
"Wllh haka xan fito, ni fa ba abinda na ci tun da rana sai furan nan da ka
tsammin" ya hade rai yace "Ki fito ki ja min kallo cikin mutane"
ta marairaice tace "Yaya to mu je ka siya min ko bathroom slippers
ne" yace "Ki dai jira yanxu xan gama cin abincin in fito" Bude
motar tayi ta fito, ya xaro ido yana kallonta, Xata xagayo inda yake ya mata
tsawa yace "Tsaya nan kar ki xo min nan" ta turo baki tana kallon sa
yace "Dama ki tsaya sai na shiga sannan ki shigo, kuma ki nemi can nesa da
ni ki xauna xan sa a kai maki abincin can" a hankali tace "Toh"
Daga haka ya shiga yana waigota don tabbatar da ta bar distance sosai tsakanin
su, Yana xaunawa sai ga ta ta shigo, ya wani hade rai ya dauke kai, tabe baki
tayi ta nemi nesa da shi ta xauna ba tare da ta damu da kallon da ake mata
cikin eatry din ba, jollof rice da half chicken yasa aka kawo masa da five
alive drink sai bottle water, yana kallon waitress din yace "Ae kuna da
meat pie koh?" Tace "Ehh har da burger da pizza with sausage roll duk
akwai" yace "Good kinga wancan matar dake xaune at that far
end?" Waitress din ta kalli inda yake nunawa ganin imaan tace "Ehh na
ganta" yace "Ki kai mata meat pie daya da table water, ni xan biya
bill din" tace "Ohk" daga haka ta wuce ta dau meat pie din da
table water ta nufi gun Imaan tana ajiye mata a gabanta imaan ta kalli Mujaheed
da ya dauke kai yana cin abincin gabansa, waitress din ta juya ta wuce, satan
kallonta Mujaheed yyi suna hada ido ya juya kujerar sa yayi backing dinta yana
murmushi yana cin abincin sa, Imaan ta dinga kallon sa amma ya ki juyowa, bayan
kusan minti uku ya sake juyawa a hankali, kawai ganinta yayi a gabansa tana
kallon sa kamar xata yi kuka, da sauri ya fara kalle kallen eatry din ya ga
kallonsu kawai ake, ya xaro ido kafin yace komai ta ajiye masa meat pie da
ruwan a gabansa ta jawo plate din abincin da drink ta dauka ta koma inda take
ta xauna ta fara ci, Mujaheed bai ce komai ba ya dauke kansa, bayan kusan minti
goma ya mike ya tafi ya biya kudin abincin da snack sannan ya dawo ya dau meat
pie din da ruwa yana satan kallonta ita ma kallonsa take, mamaki ya cika sa
ganin har ta kusan cinye shinkafar nama kuwa ta ma gama da shi, ya dauke kai ya
nufi kofar fita, imaan ta mike da sauri ta dau sauran five alive din ta bi
bayansa, a tare suka iso gun motar, ya bude driver seat ya shiga ita ma ta
shiga gaba yace "Fita ki koma ki cinye abincin" tayi yar dariya tace
"Dama fa nasan wucewa xaka yi ka bar ni shi sa nake ta kallon ka" ya
hade rai yace "Fita nace" tace "Ai na koshi baka ga na cinye
naman ba" tada motar yayi ya bar eatry din, bayan sun hau saman titi yace
"Xan maida ki gida yanxu, wllh kika kuskura kika ce nasan komai a kan
furan inna Allah xan sa ki kuka" da mamaki tace "Kai ina xa ka
yanxu?" Yace "Gidana" ta fashe da kuka tace "Toh shine ni
xaka maida ni gida, wllh kar ma ka kai ni don baxan fita daga motar nan
ba" ya buda ido yace "Toh ina xan kai ki?" Ta turo baki tace
"Mu tafi gidan ka tare" ya gyada kai yace "Tunda ke mahaukaciya
ce ni ba mahaukaci bane" ta kallesa tace "Toh da ba ina xuwa ba"
ya jefa mata wani kallo yace "Da ba yanxu bane" Shiru tayi ganin ya
dau hanyar gida ta kamo sa tace "Don Allah yaya kar ka maida ni gida
yanxu, wllh Ammi xata iya dukana don dama tace kar in dauko mata magana"
yace "Toh ina xan kai ki?" Hawaye ta fara yi, yayi murmushi yace
"Gobe baxa ki dauke ma tsohuwa furanta ba, ni dama ba ruwana" ta hade
kai da gwiwa tana kuka a hankali, bayan few minutes yace "Abinda xai faru
yanxu ina maida ki gida sai ki shige dakin Anty da sauri, ki kwana a can"
ta dago tana goge hawayen idonta tace "Don Abba ya gani ko, kasan Ummi xata
ce ma Abba ina nan" Ya daga kafada yace "Ae shi Abba baxai doke ki
ba, fada kuma baya nuna wa a jikin mutum" parking yyi yace "Oya fitar
min a mota sai da safe" wasu hawaye na xubo mata ta bude motar ta fita
tana kallon sa tace "Duk abinda ya faru daga farko har karshe xan gaya ma
Abba baxan boye masa komai ba, tare muka shanye furan kuma kai ka sa na shiga
dakin Inna in dauko saboda ta xuba maka kadan" daga haka ta bar wajen da
sauri tana kuka ya bi ta da kallo baki bude, tuni ta shige gate ta dinga rabe
rabe har ta isa parking space din su Yusuf, a haka har ta shige parlour rufin
asirinta ba kowa da gudu ta wuce dakin Anty, Anty dake xaune gaban madubi ta
bude baki tana kallonta, Saman gadonta Imaan ta hau ta rufa da duvet, Anty tayi
murmushi tace "Ina Mujaheed din?" Imaan ta cire duvet din ta mike
xaune kamar xata yi kuka tace "Yace baxai dawo ba yau kuma wllh Anty shi
yasa in dauko mata furanta sai ma kinga abinda ya tsammin duk ya shanye
sauran" hawaye cike idonta take maganan, Anty tayi dariya tace "Ae ko
kun sha jaraba yau, don har yanxu Abba da Ammi na can ana ba Inna hakuri, nima
gajiya nayi na taho" Imaan ta turo baki ta koma ta rufe kanta da duvet.
Washegari Saturday Imaan na xaune gaban madubin Anty tana shafa mai don har
tayi wanka, Anty kuma na xaune kan darduma hannunta rike da hisnul Muslim aka
bude kofar dakin, Abba ne tsaye bakin kofar, Imaan ta kusa faduwa saboda
rudewa, Abba ya kalli Anty yace "Amina amma baki ce min yarinyar nan na
nan ba" Anty tace "Ni ma har na yi bacci na ganta jiya da daddare"
Abba ya kalli Imaan yace "Ki sameni parlona yanxu" kamar xata yi kuka
tace "Abba to shi yaya fa?" Dakuwa Abba yyi mata yace "Stupid
girl, yayan banxa ai duk xa ku gane kuran ku yau" daga haka ya juya ya
fita, Imaan ta fashe da kuka tana kallon Anty tace "Kinga ni kadai xa a ma
fada yaya ya gudu koh" Anty tace "Ni dai ba kin sani nayi karya ba,
maxa fita ki tafi ki samesa ba ruwana" da kyar Imaan ta bar dakin sanye da
Hijab dinta, Abba dake parlonsa ya mike ganinta yace "Mu je" bin sa
tayi tana goge hawayen idonta suka nufa part din inna, tun daga nesa suka hango
Mujaheed yana share mata frontage, Yana ganin Abba ya mike tsaye, Ya gaida Abba
da ladabi Abba ya masa banxa ya shiga parlon inna, inna ta fito kitchen tace
"Ahmadu ne da sassafe haka" Abba ya xauna ya gaisheta ta amsa, ganin
Imaan ta hade rai tace "Ya xaka shigo min da ita parlor Ahmadu, ni da dai
ta tsaya daga bakin kofa, tsoronta ma nake ji wllh" Abba ya kalli Imaan
yace "Koma can" komawa tayi bakin kofar ta tsaya, Abba yace "Shi
yaushe Mujaheed din ya xo nan?" Inna ta xauna tace "Ko minti biyar ba
ayi ba, Ashe jiya na shiga alhakin yaron bai ma san me ke faruwa ba baya gidan
yana asibiti, sai yanxu da ya shigo nake basa labarin abinda yarinyar ta min,
ya taya ni jimami sosai yayi mamaki ainun, shine ya ga xan share waje ya amshi
tsintsiyar yake sharewa yanxu duk da dai nasan ba sharuwa wajen xai yi ba amma
ai dai ya fi babu" Abba ya sunkuyar da kai yana murmushi, Inna tace
"Yanda yarinyar nan ta sa na kwana da yunwa jiya gaskiya Ahmadu idan ba a
dau mataki ba xan tafi inje duk inda Allah yayi ko kasar waje ne kuwa, don na
gaji da cutata da take, jiya mun dade muna magana da Bukar a waya a kan
yarinyar tasa yana ta bani hakuri ni dai ban hakura ba" imaan ta fashe da
kuka tace "Wllh yaya ne yasa in dauko masa kwanon furan fa" Abba ya
kalli inna da ta bude baki tana kallonta, yace "Ke sai kika yarda da yace
maki bai san me ke faruwa ba dama?" A hankali Mujaheed ya ajiye tsintsiyar
hannunsa xai bar wajen Abba yace "Don't try that, come in now" Inna
ta mike tace "Toh amma ko gaskiya Ahmadu ka haifi abinda ya fi karfin ka,
ka haifi tashin duniya, yanxu duk dadin bakin da ya shigo ya min da sa hannunsa
a sace min fura da nono, Haba da walakin goro a miya, dama wani Mujaheed ne xai
amshi tsintsiya ya min shara, ko da kuwa aiki xai kasheni baxai yi ba wllh,
wato xuwa yayi ya yaudare ni ya cuce ni to akwai hisabi ai, ni dama nasan ina
imaan ta koyi wani sata idan ba sa ta aka yi ba, ilai ga maganata nan, kuma
wllh kaji rantsuwar musulmi ko, to baxan yadda ba sai sun san yanda suka yi aka
min furata mai kyau mai kamshi da tsafta irin tawa sannan a siyo min kindirmo
mai kyau idan ba haka ba gaskiya abinda xai biyo baya a gidan nan har kai sai
ya shafa Ahmadu" Mujaheed ya shigo parlon kansa a kasa, inna na kallonsa
da kyau tace "Mugu katon banxa kawai, wllh yau idan na maku Allah ya isa
kai da figaggiyar yar nan sai ya bi ku don kun ci da hakkina, ku ka bar ni na
kwana da bakar yunwa, to amma ya xanyi, sai dai ku ci albarkacin Ahmadu da
Bukar don ni ba abinda na hada da ku, ba dangin iya balle na baba, kawai sai
dai ku ci albarka cin 'ya 'yan da na haifa tunda su suka haifo ku duniyar, to
banda 6are ma wa xai maka haka, ai 'ya yana baxa su min haka ba, amma kuma
Ahmadu ka min iyaka da su kar kato ko figaggiyar da ta sake xuwa bangarena bana
bukata Isuhu ya ishe ni rayuwar duniya" Imaan sai hararanta take ta gefen
ido, Mujaheed dai kansa na kasa, Abba yace "Toh bana son sake ganin kai ko
Imaan a bangaren nan" da sauri Inna tace "Har abada kuwa, don gaskiya
idan suka xo sun ja ma kai da Bukar fitina, ita ta tsaya iya bangarensu, shi ma
ya tsaya iya nasu, kada wanda ya tsallaka ya yo min nan don xan gudu in bar
gidan" Abba yace "Hope u both are apprehending?" Mujaheed yace
"In sha Allah" Inna tace " Kuma kafin gobe a kawo min furata da
aka yi a kuma siyo min kindirmo nah" Abba yace "Xa su san yanda suka
yi in sha Allah" inna ta kalli Imaan tace "Ke kin ma ci halas ya kika
kare da ciwace ciwace balle kin dau hakkin mutane, jarababbiya kawai"
Imaan ta fashe da kuka Inna tace "Fita can kije ki ma uwar ki Aisha, fitar
min a parlor" Juyawa tayi da gudu ta fita tana rusa kuka, Inna ta kalli
Mujaheed tace "Kai ma fita, har abada kada ka sake tako min nan, kaje can
ka saci furan uwar ka idan ta yi" ta gefen ido ya harareta ya fice a parlon, Abba yace "Ki kara
hakuri xan sake ja masu kunne" tace "A'a ni ba ruwana ba dai na gama
yanke hukuncin da nake so ba suje can su karata, sai kuma ko wannensu yyi ma
uwarsa rashin mutunci ba dai Inna ba" Abba yyi murmushi bai dai ce komai
ba. A hanya Mujaheed ya tadda imaan tana kuka bakin rai kamar xata shide, ya
tsallake ta yayi wucewarsa. Mujaheed na komawa part dinsu dakin Ummarsa ya
nufa, tun da ya shigo take kallonsa ya xauna yace "Ina kwana Umma?"
Tace "Ban kwana ba, yanxu duk abinda xaka janyo a xageni a ci min mutunci
baka gudunsa ko Mujaheed? Wannan kakar taka wai dole ne sai kaje inda take
tunda ita jarababbiya Allah yayi ta, sannan kuma yunwa kake ji da ka dau shegen
furanta jiya ta daga mana hankali a gidan nan, ni duk wannan bai wani dameni
ba, babban damuwata a nan shine yaushe har ka fara shiri da yarinyar nan Imaan
da ku ka dauke furan a tare ku ka sha?" Mujaheed ya bude ido sosai yana
kallonta yace "Shiri kuma Umma? Ni bamu wani sha fura tare da ita ba, nine
ma na dauke furan na sha" Umma tace "Toh naji tana cewa kai ka tura
Imaan daukan furan ku ka raba" ya girgixa kai yace "A'a ba haka
bane" Umma tace "Sannan da ake nemanka jiya ina ka tafi, ita yarinyar
ma bata gidan a jiya da daddaren" Yace "Ni fa eatry na tafi cin
abinci karfe sha daya ya wuce na shigo duk kun yi bacci" tana masa wani
kallo tace "Toh ita imaan din ina ta tafi?" Yace "Ban sani ba
gaskiya" Umma tace "Mujaheed?" Kallonta yayi tace
"Mujaheed?" Yayi Shiru yana dubanta tace "Sau nawa na kira
ka?" Ya sauke idonsa kasa tace "Toh wllh idan baka kama kanka gidan
nan ba xan sa6a maka, ita kanta innar daga yau na kashe xuwa sashinta, kar ka
sake tunda ba kanwar uwata bace ita din, idan kana son gaida kakarka ne sai ka
shirya ka tafi katsina uwata na can da ranta" murmushi kawai Mujaheed yyi,
tace "Dama tun shekaranjiya akwai maganar da nake son mu yi to da ka dawo
gun aiki sai ka tare gun alakakan matar can sai nayi bacci xaka shigo min
nan" ya daga kai ya kalleta yace "Toh ina ji Umma" tace
"Kasan Hajiya Mansura kuwa?" Ya girgixa kai yace "A'a" tace
"Ka santa mana, wata warce ka taba kai ni gidanta a Marafa, ka koma dauko
ni da yamma ruwa ya tsuge har tace ka shigo ka ci abinci ka ki ci?" Yace
"Ohh na tuna ban san sunanta ba ai" tace "Toh ita ce Hajiya Mansura,
dama tana da wata budurwa yar shekara ashirin da daya tana karatu a Malaysia,
to ina jin last week suka dawo hutu, baka ganta ba kyakkyawa fara doguwa ga
hankali da nutsuwa, shine nake baka shawaran don me baxa ka neme ta ba"
Shiru Mujaheed yyi bai ce komai ba, Umma tace "Sunanta Safeena, nasan ma
xaka so ta ne coz she have all the qualities, uwa uba ga ubanta mugun attajiri
abokin ma d'angote ne aka ce" Murmushi Mujaheed yyi bai dai ce komai ba,
Umma tace "Ba batun murmushi bane wannan, dama gashi saura wata hudu ta
kare karatun, last week da naje gidan na ganta ta kwanta min har nayi ma Hajiya
Mansurar magana ita ma ta ji dadin tunanin nawa don ta yaba da hankalin ka,
yanxu abinda nake so da kai ka shirya kaje gidan ko xuwa Sunday tunda baka xuwa
aiki da safe, dama xan baka sako ka kai ma Hajiya Masurar nasan xaka ga
Safeenar" Murya can kasa Mujaheed yace "Toh, Allah ya kai mu"
Umma tace "Ameen son, Allah maka albarka" yace "Ameen, xan je in
yi breakfast Umma" tace "Toh shikenan" mikewa yayi ya fita dakin
ya kulle mata kofar. Karfe takwas Mujaheed ya fito xai fita kofar gida yaga
imaan tsaye jikin mota tana jiran fitowarsu Maimoon su wuce islamiyya, idonta
ya kumbura kana ganinta kasan ba karamin kuka ta ci ba, tunda ya fito take
kallonsa ta wani cika kiris ya rage ta fashe, Mujaheed ya saci kallonta suna
hada ido ya dauke kai, ta fashe da wani matsanancin kuka, da sauri ya kalleta
kafin yace komai ta shige gidan da gudu, direct parlon Abba ta nufa, ta samesa
kuwa yana kallon news shi kadai, ta xube nan tsakiyar parlon ta dinga rusa kuka
kamar xata shide, ya mike da sauri yace "Subhanallah, me ya faru
mamana?" Tana kuka sosai tace "Abba Yaya ne ke min dariya, Wayyo
Abba" da mamaki yake kallonta, yace "Dariyar me yake maki" ta
kara fashewa da kuka tace "Nima ban sani ba wllh Abba" komawa yayi ya
xauna yace "Xo nan" mikewa tayi ta koma kusa da shi tana kuka sosai,
yayi murmushi ya rungumeta yace "Ya isa haka mamana kiyi hakuri
kinji" ta kasa cewa komai yace "To baxa ki daina kukan ba?" Da
kyar tace "Xan daina" Ya dau handkerchief ya mika mata yace "Toh
goge idon ki kiyi Shiru" tana sauke ajiyar xuciya ta amsa tana goge idonta
wasu hawayen na sakkowa, Umma ce ta shigo parlon rike da mug din ruwan Lipton
yana turiri, tun da ta shigo take kallon Imaan dake rungume jikin Abba har sannan
ta dinga kallonta da wani expression a fuskarta, Umma ta dai ajiye mug din
hannunta xata xauna Abba yace "Nemo min Muhammad" Umma tace
"Muhammad kuma, lafiya? Ina jin dai ya fita uxurin gabansa ba gwanda a kai
ta asibiti ba idan ma ciwon nata ne ya tashi" Abba ya dau wayarsa yayi
dialing number Mujaheed, Mujaheed dake xaune gun mai kiosk dake 2 houses away
bayan ya siya card ya dinga kallon screen din wayarsa ganin Abba ke kira, ya
daga ya kai kunnen kafin yace komai Abba yace "Muhammad ka sameni parlona
yanxu" Daga haka ya katse wayar, Umma ta tsaya kallon Abba fuska daure, ba
a dau lkci ba Mujaheed ya shigo parlon da sallama, sosai gabansa ya fadi ganin
Imaan kusa da Abba ga Umma ma tsaye a parlon, ya sunkuyar da kai ya duka kasa a
hankali yace "Abba gani" Abba na kallon Imaan yace "Me kika ce
ya maki mamana" cikin rawar murya tace "Dariya ya min ban san ko ya
san Ammi ta doke ni bane" Abba yace "Subhanallah ta doke ki kuma, me
kika mata" ta fara kuka tace "Wai na sha ma inna fura shine ta mareni
ta kuma dokeni a bayana" Abba yace "Aa bata kyauta ba xan je In
sameta yanxu kuwa, kai kuma Mujaheed dariyar Uwarka kake mata" Umma ta
dinga ma Abba wani irin kallo, Mujaheed ya girgixa kai yace "Abba ni ban
fa ganta ba balle in mata dariya" Imaan tace "Wllh ya gan ni ya dinga
kallona a sace" tana fadin haka ta fara share hawayen dake sakko mata,
Mujaheed yace "To tayi hakuri tunda tace na mata dariya amma ni ban mata
ba" Imaan ta turo baki ta dauke kai, Abba yace "Ai kin hakura
koh" kin cewa komai tayi Abba yace "Toh kiyi hakuri mamana Aisha kuma
zan je in sameta yanxu, maxa tashi ki tafi makarantar kar ki makara" Umma
ta fice parlon rai a bace, a hankali Imaan tace "Abba nasan su Maimoon sun
tafi yanxu" Abba yace "To mu je in ajiye ki" yana fadin haka ya
mike ya dau makullin mota, Mujaheed ya mike yace "Bari in ajiyeta
Abba" Abba ya dau dubu biyu ya bata yace "Toh ga kudin lunch din
ki" ta rusuna ta amsa.
Alhamdulillah, Thanks to all those that patronize the book
*Imaan* Allah bar ku da iyayen ku, My book Imaan is for sale coz I am done with
free pages tun friday, ni nasan it will go round as usual, I can't prevent
that, but if you should come across it it's not for free, i repeat it's not for
free, na siyarwa ne, wllh I am too grown up to say Allah ya isa, but have the fear
of Allah SWT in u, don't forget it's my property, hakkina ne, wahalata ce, pay
before reading, pay before reading, or you just over look it and smile, have a
very good conscience plss, and a good conscience won't read happily without
paying, if you want any favor pertaining to d book contact me and let me know,
the book is 300 via..... Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
07087865788 and then u contact me through this digit to be
added in the payment groups. Thanks once more for patronizing.
For those saying xa su same shi a banxa yana yawo to gashi...
amma fa ba a banxa yake ba wllh, there is power in the tongue, Karamin hakkin
da ka raina..... 😃😃
13.🌟⭐imaan⭐🌟
A hankali Imaan tace "Abba nasan idan muka fita kilan
xai min fada a hanya" Mujaheed ya kalleta bai ce komai ba Abba yace
"Toh ya maki fadan mu ga" Murmushi kawai Mujaheed yayi ya fita
parlon, Abba yace "Maxa ku tafi kar kiyi latti mamana" Imaan ta bi
bayan Mujaheed tana share idonta, tunda Mujaheed ya fito parlon Abba gabansa ya
dinga faduwa, xaune ya ga Umma a main parlor fuskar nan nata a tamke, Mujaheed
ya karasa inda take, ita ko bata fasa kallonsa ba, kofar fita Imaan ta nufa,
Mujaheed yyi kasa da murya yace "Umma dama Abba...." Katse sa tayi
tace "Bana son jin komai, Ban baka izinin fita parlon nan ba in har ni na
haife ka Mujaheed, ko da kuwa me xai faru yau" Kallonta Mujaheed ya tsaya
yi ba tare da yace komai ba, Anty ta fito kitchen da breakfast a hannunta tayi
wani dariya tace "Su haihuwa manya...." Umma ta kalleta ta dakatar da
ita da sauri tace "Ke in kina cin k'asa ki kiyayi ta shuri, ki daina min
shisshigi a lamari na, ki yi mai fissheki kawai a gidan nan" Anty ta tabe
baki tace "Anya akwai wanda ya kai me shiga lamarin d'a da ubansa
shisshigi kuwa, kuma naga duk wanda xai ce d'a kada ya bi umarnin mahaifinsa
shine mai babban shisshigi a rayuwa kuma bai dauko abinda xai fishshesa
ba" Umma ta mike rai bace tace "D'an ki ko nawa? tunda ba wata shegiya
ce ta haifa min d'an ba sai kiyi ta kanki ki, ki kuma cire min ido kan d'a
na" Anty tace "Na wuce in tsaya ina xance irin na yara da ke, amma
bari in baki shawara, domin kin haifi Muhammad ba yana nufin ke kadai ke da iko
da shi ba duk ki bi ki takura ma yaro sai abinda kike so xai yi a gidan nan,
kina amfani da advantage din ganin yana maki biyayya dari bisa dari...."
Cikin tsawa Umma tace "Da ke da shawarar taki Allah kwashe maku
albarka..." Dai dai nan Abba ya fito parlon jin hayaniya, ya kalli Mujaheed
dake tsaye, ya kalli Yusuf dake tsaye stairs yana kallon su shi ma sannan ya
kalli su Umma yace "Me ke faruwa nan?" Rai bace Umma tace "Ka ja
ma matar ka kunne Alhaji ta fita harkata kada abu ya bace tsakanin ni da ita a
gidan nan, ta cire ido kan d'a na, ta kuma yi ta kanta..." Abba ya dakatar
da ita yace "I asked what happened kina min warning madam" Anty ta
tabe baki tace "D'an ta da ka aika yanxu... ta hana shi xuwa saboda isa da
gadara, to ni kuma bana gani inyi shiru...." Abba ya kalli Mujaheed da ya
kasa dagowa ya mika masa hannu yace "Bani makullin motar...." Da kyar
Mujaheed ya dago yana kallonsa sannan ya kalli Umma, ta watsa masa wani kallo
alamar ya basa, a hankali Mujaheed yace "Abba ai bance fa baxan je
ba" yace "Eh baka ce ba, amma ba ni" Mika masa makullin Mujaheed
yayi, Abba ya kalli Yusuf yace "Here, ka tafi ka ajiye Imaan a
makaranta" Yusuf ya karasa saukowa stairs da yake tsaye ya amshi makullin
sannan ya nufi kofa ya fita, Juyawa Abba yyi ya koma parlonsa, Mujaheed ya wuce
sama a sanyaye, Anty ta tabe baki ta wuce saman ita ma, wani ajiyar xuciya Umma
ta sauke ta koma ta xauna ranta fess. Sai bayan da suka bar gidan Imaan ta
kalli Yusuf tace "Ya Yusuf Umma ce tace yaya kar ya kai ni koh?"
Yusuf na driving yyi murmushi yace "Toh dama ya xa ayi ta bari ya kai ki??
salon ku je ya d'an rankwashe ki ki dawo kina mana ihu kina kuka" xaro ido
Imaan tayi tana kallonsa, Ya ki kallonta sai murmushi yake, ta hade rai tace
"Toh an doki mutum kuma baxai yi kuka ba" Yusuf yace "A'a xai yi
kuka abunsa" Turo baki tayi bata ce komai ba, shi ma bai kuma cewa komai
ba har ya iso islamiyyarsu ya tsaya bakin gate, ya kalleta yace "Kin fa yi
latti sosai" tace "Ae xa su ga idona kuma cewa xanyi bani da lafiya,
dama ban da lafiyan" daga haka ta bude motar ta fita, D'aga masa hannu
tayi, yayi mata murmushi ta shiga cikin makarantar. Imaan na dawowa islamiyya
karfe sha biyu kashegari lahadi ta fara shirin tafiya gidan gwaggonta wato
Mahaifiyar Ammi dake unguwar rimi, Tun da ta fito daki Ammi dake xaune parlor ke
kallonta, tsadadden atamfa ne jikinta sai dan kunnenta na gwal, babu abinda ke
fuskarta banda eye pencil da chappete da ta goga a lips, sosai tayi kyau duk da
haka, da mamaki Ammi tace "Ina xa ki?" Imaan ta xauna kusa da ita
tace "Gidan Gwaggwo mana Ammi" Ammi ta mata wani kallo tace "Kin
gaya ma Daddy ne?" Ta marairaice tace "Daddy baxai hanani ba fa na
sani" Ammi tace "Baxa fa ki fita gidan nan ba sai da saninsa don ba
ruwana" tashi Imaan tayi kamar xata yi kuka ta shiga dakinta kiran Abba,
wayarta da bata damuwa da ta dauko ta yi dialing number sa, bayan wani lkci ya
dauka, ta amsa sallamarsa sannan ta gaishesa, yace "Ya kike Imaan"
tace "Lafiya Daddy ya aiki?" Yace "Alhmdllh, har kun dawo
islamiyyar?" Tace "Ehh daddy dama gidan gwaggwo nake son in je in gaisheta
shine Ammi tace sai na gaya maka" yace "Ae kina da islamiyya da yamma
mamana" kamar xata yi kuka tace "Ae kafin karfe hudu xan dawo"
yayi shiru kafin yace "Toh waye xai kai ki?" Tace "Ni kadai
Daddy ai ina xuwa ni kadai" yace "Kai ma Ammin ta ki waya" fita
dakin tayi ta kai ma Ammi waya, Ammi ta amsa ta kai kunne, daddy yace "Why
not drop her plss bana son tana fita ita kadai" Ammi tace "Sai kace
wata yar shekara goma yallabai, she do go out her self...." Daddy yace "Toh
minti nawa ne kin ajiyeta ki dawo" Ammi tace "I told u for the past
two month ban shiga motar nan ba, sai dai ta bari next week mu je tare idan
Allah ya yarda, ina da aikin da xan yi yanxu, ko jiya fa naje gidan gobe ma xan
je, yau kuma sai na kai Imaan?" Daddy yace "Bata wayar" Ammi ta
mika mata, daddy yace "Mamana ki bari next week ku je da Ammin ki idan
Allah ya kai mu" imaan ta fashe da kuka tace "Bayan na shirya daddy,
na fa san hanya ba yau xan fara xuwa ni kadai ba" Daddy ya dan yi shiru
kafin yace "Shikenan to kije, but go with ur nose mask, and inhaler, Allah
ya kiyaye hanya" tana goge idonta a hankali tace "Toh daddy na
gode" Ammi ta shiga kitchen ta dauko dambun naman da tayi ma mahaifiyarta
tace "Ki kai ma gwagggo ina gaisheta sai na xo goben" Imaan ta amsa
tace "Toh" dubu Biyu Ammi ta bata ta bar gidan bayan tasa gogaggen
Hijab dinta har kasa, a dai daita Imaan ta samu da xai kai ta har gidan, bayan
sun isa ta sauka ta basa kudinsa sannan ta shiga gate din gidan, babban gida ne
sosai da su Ammi suka siya ma mahaifiyar tasu, Ammi ce ta biyu gun gwaggwo
bayan babban yayansu Umar, sai maxa biyu da mace daya Anty Murja, duk sun yi
aure da 'ya yansu, yar Anty Murja ta biyu Halima ce ke gaban gwaggwo kuma ita
xa ayi aurenta kwanan nan, Sosai Gwaggwo tayi murnar ganin Imaan, duk cikin
jikokinta ko da bata nunawa ta fi jin Imaan har ranta, Imaan ta rungumeta cike
da jin dadin ganinta ita ma, Gwaggwo tace "Kin guje ni Fatima" Imaan
tace "Toh Gwaggwo kinga idan naje boko da safe da yamma muna dawowa xan
wuce islamiyya, ranan asabar kuma islamiyya safe da yamma, yau ma kawai dai na
taho ne kuma da wuri xan koma saboda islamiyya" Gwaggwo tace "Toh
Allah ya maki albarka ya baki sa'a a karatun ki, ya Ammin ki fa?" Imaan
tace "Tana gaishe ku, tace in kawo maku wannan" Gwaggwo tace
"Toh nagode Allah mata albarka, fatan mutan gidanku duk suna lafiya"
Imaan tace "Duk lafiya lau" Ammi tace "Mujaheed ya daina xuwa
min kwata kwata yanxu yana kasar kuwa?" Imaan tace "Yana nan"
Gwaggwo tace "Ikon Allah, shi kuma d'an farin fa, duk da shi baya ma gaida
mutane dama" Imaan tayi dariya tace "Shi ma yana nan" Gwaggwo
tace "Toh Allah maku albarka, in ji kakarku tana lafiya" Imaan ta
turo baki tace "Ehh" Gwaggwo tace "Toh Allah ya kara mana
lafiya, ki dauko lemo fridge ki sha" Imaan ta gyara xamanta tace "Anty
Halima bata nan ne?" Gwaggwo tace "Taje kai anko" Imaan tace
"Toh ni ba a ban ankon ba" Gwaggwo tace "Xa ta kai maki naki har
gida tace" Imaan ta washe baki tace "Toh" mikewa tayi ta dauko
malt daya ta dawo ta xauna ta fara sha tana cin dambun naman da ta kawo,
Gwaggwo tace "Inji yanxu ciwon ki yana sauki sosai kamar yanda mahaifiyar
ki ke gaya min idan na tambaya" Imaan tace "Ehh da sauki" Da
damuwa Gwaggwo tace "Allah ubangiji ya yaye maki wannan cutar Fatima, in
sha Allah xaki samu lafiya gaba daya muna nan muna gaya ma Allah" Yar
dariya Imaan tayi tace "Gwaggo ya Salim yana xuwa?" Gwaggwo tace
"Yauwa kwanaki yayanki Muhsin ya kawo min karar ki wai baki gaida
mutane" Imaan ta hade rai ta daina cin naman da take tace "Ni kullum
sai yace bana gaishesa, to ma a ina nake ganinsa balle in gaishesa"
Gwaggwo tace "A'a Fatima ga wannan dai waya da ta kawo komai da sauki, ko
shi kika dauka ai xa ki kirasa ku gaisa" Imaan ta turo baki tace "Toh
shi ma fa ba kulani yake ba wllh" cike da damuwa Gwaggwo tace "Ni dai
ku rike xumunci don Allah, ba kya ganin yanda iyayenku ke yi ne, ubansa ya sha
nono ya bar ma uwarki, wllh baki da yan uwan da ya wuce su don mutan gidanku ba
son ke da uwar ki suke ba duk an sa maku ido, ga kakarku fitinanna, kiyi ma
kanki fada ki rike xumunci da yan uwanki na nan, duk suka xo gaisheni sai sun
tambayeni ke ba Usman ba, ba Muhsin din ba, ba Salim ba ga matan su ma gaba
daya, ke sai kiyi shekara baki xo nan ba baki je gidajen nasu ba shi sa bakwa
hadu duk da ba laifin ki bane laifin uwar ki ce don ita ya kamata ta sa ki a
hanya ta kuma sa maki ido" Imaan dai sai cin namanta take tana shan malt,
sallama aka yi bakin kofa Gwaggwo ta amsa Muhsin ya shigo tare da abokinsa,
Gwaggwo tace "Sannun ku da xuwa, yanxu nake xancen ka Muhsin" Muhsin
yayi murmushi yana kallon Imaan da ta ki kallonsa yace "Wannan
fitsararriyar ce ta xo ashe" Gwaggwo tayi dariya tana kallon abokinsa tace
"Sannu da xuwa Sadeeq kwana biyu ka gujeni" murmushi yyi ya cire
glass din idonsa ya karaso Inda take ya durkusa yana kallon Imaan da taki dago
kai sai cin namanta take yace "Sannu Kaka ina yini" Imaan ta daga kai
don muryar sounds soo familiar, Gwaggwo tace "Lafiya lau Sadeeq ya mutan
gidanku? Ya kuma aiki da kujuba kujuban rayuwa" ya sauke kansa kasa yace
"Alhmdllh mun gode Allah Kaka" Gwaggwo tace "Toh Allah yayi maku
albarka ya kare ku sharrin makiya, ya tsare ku da tsarewarsa" a hankali
yace "Ameen" ya kai idonsa kan Imaan that was so uncomfortable,
Muhsin yace "Ina yini Anty Imaan" boye fuskarta tayi da kujera yace
"Ke yanxu kin girma kin daina kula kowa kin mance lkcn da kike kuka sai an
goya ki, kiyi ta bamu wahala muna goya ki a anguwa koh" kamar xata yi kuka
tace "Ya Muhsin bana so ni yaushe nake kuka a goya ni" yayi dariya
yace "Tunda kin girma kin manta ai shikenan, gashi nan ma kin daina gaida
kowa" kamar xata yi kuka tace "Ya Muhsin kai ma fa ba magana kake min
ba, ni da bani da lafiya ka tambayi Ammi ma, kuma ni ina dadewa ban hau
whatsapp ba, wayar ma ba amfani nake son yi da shi ba" yace "Yaushe
ne baki da lafiya?" Gwaggwo tace "Kai ma dai Muhsin sai kace baka san
dawan garin ba, sai kayi mata addua da fatan samun lafiya" Muhsin yace
"Toh Allah ya sauwake Imaan amma ai kina shan magani koh?" Ta gyada
masa kai ba tare da ta dago ba, yace "Sannu lil sis" ta turo baki a
hankali ba tare da ta dago ba still tace "Ina yini" ya xaro ido yace
"Toh boye fuskar ta meye, Kunyata kika fara ji ko na abokina" ya fadi
haka yana muna sadeeq dake kallonta, kin dagowa tayi ta kuma ki cewa komai, shi
dai Sadeeq sai kallonta yake, Gwaggwo tayi dariya tace "Fatima kenan, to
tashi ki shiga ciki" kamar jira take ta mike ta wuce dakin Gwaggwo da
sauri, Muhsin yayi murmushi yace "Imaan Daru" mikewa Gwaggwo tayi ta
dauko ma Sadeeq ruwa da lemo yace "Da kin bar shi Gwaggwo daga gida mu ke
ai" Gwaggwo tace "A'a idan baka son inyi fushi to ka sha, ga dambun
nama yanxu Imaan ta kawo min" murmushi yyi ya dau bottle wata daya ya
bude, Muhsin yace "Wai ban ga Amaryar gidan nan ba?" Gwaggwo tace
"Taje kai anko, nasan tana hanyar dawowa yanxu" Muhsin yace "Da
alama dai duk Halima ta kagu ta bar ki" Gwaggwo tace "Don bata nan
shine xaka mata wannan sharrin, to bari dai ta dawo" Muhsin yyi dariya
yace "A'a ni dai ba ruwana rufa min asiri Gwaggwo" Sadeeq dai sai
murmushi yake yana danna wayarsa, hira suka dinga yi gaba daya a parlon har
kusan Asr, Muhsin yace "Gwaggwo bari mu je masallaci mu dawo yanxu"
Gwaggwo tace "Toh Allah maku albarka" Muhsin ya mike tare da Sadeeq
suka nufi kofa, tashi Gwaggwo tayi tana kiran Imaan da bacci ya dauke tun daxu
a dakin. Suna fita compound Sadeeq na kallon Muhsin yace "Wacece yarinyar
nan Muhsin?" Muhsin ya wara ido yace "Ko dai kana ciki ne
Abubakir?" Sadeeq yace "Na santa ne shi sa nake tambayarka" Da
mamaki Muhsin yace "Haba, amma ban ga ta nuna alamar ta san ka ba" Murmushi
Sadeeq yyi yana shafa sajensa yace "Ni na nuna alamar na santa banda yanxu
da na fito?" Muhsin yace "Toh ina ka santa?" Sadeeq yace
"Baka fada min relation dinka da ita ba" Muhsin yace "Cousin
dita ce, mum dinta ita ce immediate sister din Abbana" da mamaki Sadeeq ke
kallon sa yace "You mean you two are this close?" Muhsin yace
"Sure" Sadeeq yace "That's Amazing, she is Mariya's school
friend kaga dalilin da ya sa na santa" Muhsin yace "Maa sha Allah,
amma bata gane ka ba ko?" Murmushi Sadeeq yayi yana maida glass dinsa yace
"Ta gane ni sarai, that was why she was uncomfortable" Muhsin yyi
dariya yace "Ohh I see, there is something a kasa kenan" Sadeeq yace
"Let not miss jam'i plss" daga haka suka shiga masallacin don yin
alwala. Imaan na idar da sllh tace ma Gwaggwo xata wuce don xata islamiyya,
Gwaggwo tace "Baxa ki ci abincin ba kenan, shinkafa ce da miya fa"
Imaan tace "Bana jin yunwa fa Gwaggwo" Gwaggwo tace "Toh
shikenan ki duba siff a daki xaki ga wani sabon hijab da na dinka maki da
takalmi ki dauka," Imaan tace "In ji me hannu ne Hijab din?"
Gwaggwo tace "Ae nasan me hannu kike sawa, shi nayi maki" Bude kofar
parlon aka yi Muhsin ya shigo tare da Sadeeq, Muhsin yace "Har kin fito
kenan yan matan Ammi" Imaan tayi murmushi tace "Ehh wucewa xan yi
saboda islamiyya" Muhsin yace "Mu ma yanxu xa mu wuce ai"
Gwaggwo tace "Toh sai ku ajiye min ita don Allah a gida kar ta kara bin
k'uran nan ta koma a samu matsala" Dariya Muhsin yayi yace "Wa yaga
imaan baturiya" Imaan ta boye fuskarta, dubu biyar Sadeeq ya ajiye ma
Gwaggwo yace "To kaka xa mu koma sai wani lkcn kuma, ba yawa wannan ki
siya goro" Gwaggwo tace "A'a gaskiya ka dau kayan ka Sadeeq,
matsalata da kai kenan idan ka xo gidan nan kai baka gajiya ne" murmushi
kawai yayi, Muhsin yace "Shikenan dama ban fito da kudi ba ya fanshe ni,
sai ki raba, nawa da nasa" Gwaggwo tayi dariya tace "Allah sarki, Toh
Allah dai ya maku albarka ya ba ku mata na gari kuyi aure ku bar xaman nan da
ku ke" Muhsin yace "Toh Ameen Gwaggwo" Tare Imaan suka fita da
Muhsin don Sadeeq har ya fita, ta bude back seat ta xauna, Sadeeq ne xaune
driver seat din Muhsin ya shiga front seat suka bar anguwar. Hira suka ta yi a
motar, ita dai danna wayarta kawai take, amma da ta daga kai xa su hada ido da
Sdeeq ta madubi, sai tayi maxa ta sauke kanta, bayan tafiyar kusan minti sha
biyar ta ji Muhsin yace "Ajiye ni nan man" parking Sadeeq yyi, Muhsin
ya fita yana kallonta yace "Toh anmata sai mun yi waya ki gaida Ammi,
abokina xai ajiye ki gida" ta xaro ido tace "Ya Muhsin nima nan fa
sauka xan yi dama" Muhsin yace "Inaaa... bayan amana Gwaggwo ta ba mu
mu kai ki gida kada kura ya taba ki, nima akwai abinda xan yi anguwar nan ne
amma da tare xa mu tafi" Imaan ta dinga kallon sa kamar xata yi kuka, ya
daga mata hannu yana danne dariyarsa yace "Sadeeq drive her carefully plss
sai mun yi waya" daga haka Sadeeq ya ja motar suka hau saman titi, Imaan
dai sai wasa take da fingers dinta, bayan wani lkci ta dago a hankali tana
kallon gaba suka hada ido ta madubi, da sauri ta sunkuyar da kanta, yayi
murmushi yace "Kina tsoron kada in sace ki ko?" Kin cewa komai tayi,
bayan kusan minti biyu taji cikin cool voice dinsa yace "I am Abubakar
Sadeeq Ahmad, was born and bred up here in Kaduna, first son of the family, my
primary and secondary education all in Kaduna, before I proceed to UK where I
had my degree and msc, I am a medical practitioner....." Kallon sa kawai
Imaan take ta madubi, yyi murmushi yace "Mariya is my step sis, I have six
siblings altogether, ranan kinje gidanmu amma part din stepmum dita, namu part
din yana cikin gidan though very far away, soo you've known almost all about
me... Yes I am still single and searching..." daga haka yyi shiru ya
kalleta yana murmushi yace "Do you mind telling me about ur self"
shiru tayi da farko, can a hankali tace "Sunana Fatima Abubakar amma ana
kirana Imaan" ta kallesa don a hankali yake driving din kasancewar bbu
motoci sosai titin, ya gyada mata kai alamar yana ji, yana murmushi, murya can
kasa tace "I am the only child of my parent" Da mamaki ya dinga kallonta,
ta sunkuyar da kanta tace "I am In the same class with Mariya both School
and Islamiyya, muna xaune tare da Daddy na da Ammi, with my paternal grandmum,
and my Uncle with his family, i mean my father's senior brother" Sadeeq ya
gyada kai a hankali yace "That's nyc, Allah maki albarka ya sa ki xamo the
Apple of ur parent eyes" Murmushi tayi murya can kasa tace
"Ameen" ganin sai tafiya yake ta bude manyan idonta tace "To ai
baka san inda xaka kai ni ba" ya kalleta ta madubi yace "Kin manta
ranan da Antynmu ta sa na ajiye ki gida kenan?" Ta wara ido tace "ohh
na tuna" ya d'an yi murmushi, suna kusa layin yace "Toh baki fada min
samarin ki nawa ba?" Ta xaro ido tace "Samari kuma?" Yace
"Yeah" tace "Tabb, ni bani da Samari" yace "Sai dai
frnds kenan" ta turo baki, yayi murmushi yana kallonta, tace "A
school bani da male frnds, a islamiyya ma haka, a gida ne kawai" yace
"Toh su waye?" Tace "Cousins dina" yace "Really?"
Ta gyada masa kai, yace "Can I know them" murmushi tayi tace "Ya
Yusuf ne sai yaya.. Ohh yaya yusuf ne ma kadai, mun daina shiri da yaya
yanxu" yace "Can I know the Yusuf?" Tace "Yea he is my
cousin, an engineer yana aiki a nan yana yi a Kano yana yi a zaria" yana
parking kofar gidan su yace "Shi dayan fa?" Tace "Yaya?" Ya
gyada mata kai tace "Shi wani lkcn yana Abuja wani lkcn yana nan, yanxu
yana nan" Sadeeq yace "Maa sha Allah, to me yasa bakwa shiri?"
Tace "Yanxu ya fiye mugunta baya kuma kulani kamar da" tana magana ta
bude kofar motar tace "Nagode" ba karamin daure ransa yyi ba yace
"Wait ara min fone naki pls, I want to confirm ko Muhsin ya tafi da nawa
cos I can't find it here" komawa tayi ta xauna ta basa wayarta ya amsa ya
gama danne dannensa sai ga ring din wayarsa, ya mayar mata yace "ohhh
thanks yana nan ashe" ta fita motar tace "Thanks" yayi murmushin
da ya bayana dimples dinsa yace "You are welcm" Xaune ta ga Mujaheed
gun mai kiosk a kofar gidan yana kallonta, duk da yanda gabanta ya fadi ta
dauke kai da sauri ta wuce cikin gida ta rufe gate.
*I want to use this medium to bring this to the notice of my
Fans, akwai wani namiji mai amfani da information dina gaba daya both Facebook
and WhatsApp, a lot suna chatting da shi a tunaninsu ni ce, to bani bace ba
wllh, masu nemana Facebook idan sun yi searching xa su ga account biyu iri daya,
to ni nawa account din daga followers kadai ma mutum xai gane it's real me bcos
the followers are much, idan mutum ya duba post na timeline dina ma xai gane
account dina ne, duk da ko wani update nayi shi ma sai ya sata yayi, ga
lambarsa kamar haka masu chatting da shi ta WhatsApp 09031263639.... Billah
namiji ne kuyi ta kanku, har card wasu na tura masa da sunan xa su siya
littafin Imaan to bani bace, da yawa na cewa sun biya Noor Hayat ban sa su
group ba ban basu littafi ba to shi suka ba kudinsu ba ni ba. Beware fans katon
namiji ne yake claiming khaleesat Haiydar kuma ni na bar sa da fitowar rana da
faduwarsa, duk da ban ma yarda shi din Muslmi bane, Allah ya Isar min, a yanda
ya fara a gantale haka xai kare a gantale*
Littafin Imaan is 300 via... Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Show ur evidence of payment through my WhatsApp digit...
07087865788, subscribe and read happily without feeling any guilt.
_Su ma masu editing min novel su sa abinda ban yi niyyar sawa
ba, bayan fitar da shi da suke ban yi complain ba... we shall meet in the
hereafter in sha Allah_ 😇
14. Imaan
Mikewa Mujaheed yyi ya bi bayanta, tunda Imaan ta shiga gidan
daman take waigen kar ya biyo ta, ido hudu suka yi da Umma da ta fito tare da
wata bakuwa, ta dauke kai ta ci gaba da tafiyarta da sauri, Mujaheed na ganin
Umma dama ya canxa direction dinsa, Umma na kallon sa tace "Daga ina
kake?" Yace "Ina xaune a waje, xan wuce wajen aiki ne yanxu"
Umma ta bi Imaan da kallo sannan ta kara kallon sa, ya d'an buda ido yace
"Umma ni ban gane kallon nan ba, ki tambayi mai kiosk din can tun daxu
nake wajen a xaune wllh" Kawar Umma tace "Yi wucewan ka kaji
Muhammad" Murmushi Mujaheed yyi ya wuce ciki, tafiya suka ci gaba da yi
Umma tace "Gani nayi kamar tare suke da warcan mai laluran da ta wuce
yanxu" Hajiya Saude tace "A'a da xan shigo daxu fa na gansa xaune
inda yace maki, to minti na nawa a ciki ko minti sha biyar fa ban yi ba"
Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Da kin san irin k'i da tsanar da
nake ma uwar yarinyar nan har cikin raina ko Hajiya Balaraba, wllh abun ba
kyau, xan iya komai a duniya don ganin na walakantata, yanda nake jin tsanarta
a rai ko kishiyata Amina ban jin ta haka, sai in ki cutar Amina amma ita xan
iya cutar ta, sai ga tsanar har ya shafi wannan figaggiya irin ciwon da ta
haifo duniya, duk na tsane su kamar yanda na tsani mutuwata, bayan na dawo
gidan nan da kyar fa na raba Mujaheed da yarinyar, sai da na tashi tsaye
kyamm" Hajiya Balaraba tace "Ikon Allah to sonta yake shi din?"
Umma tace "Auzubillahi kaji wata magana wai so, ni na haifi Mujaheed na
san halinsa, wllh ba so bane kawai shakuwa ce tsantsa da shisshige masu da
yake, sannan yarinyar ta yi mugun sabo da shi, kuma a da kafin in dawo shi ke
tsaye kan bata magunguna da dai abubuwa da ya shafi lalurorinta, kin san
sickler ce sosai...." Hajiya Balaraba tayi dariya tace "Ba fa a
shaidar d'an yau Hajiya, ke kin shiga xuciyarsa ne kika ga ba sonta yake
ba?" Umma tayi wani murmushi tace "Kin san akwai wani abokinsa
Ibrahim iyayensa hamshakan masu kudi ne, shi ma yaron ya jike jagab da naira,
da ban yi da gaske ba wllh ita Imaan din ya so hadawa da yaron wai ya nemeta,
ga yaron mai hankali da nutsuwa, wllh sai da na masa jan ido sosai, don in dai
ina raye abun arxiki baxai taba xuwa inda Aisha da 'yar ta suke ba, baxan bari
ba in sha Allah ina nan ina sa ido in ga wanda xai jajibe yarinyar da gwara
babu da ita, kullum fa ana hanyar asibiti kamar 'yar da aka sama ta mugun
hanya, to fa da nayi da gaske da Mujaheed shine ya hada yaron da kanwarsa Ummi,
yanxu ana gama bikin Seeyama xa a fara xancen na Ummin, Uban yaron fa abokin
gwamnan garin nan ne na kut da kut" Hajiya Balaraba tace "Toh Allah
dai ya kyauta" Umma tace "Sannan shi Mujaheed din akwai wata yar
talakawa da yake mutuwar so wai farida, ni a bincike na ma cewa aka yi idan ban
tashi tsaye ba wllh sai ya aureta don yayi mugun kwallafa rai a kanta, baki ga
hidimar da yake mata da iyayenta ba, duk ya talike a kansu har haya na samu
labarin yana biya masu don nasa mutane su sa masa ido a anguwar, in sha Allah
na kusa cire masa yarinyar a ransa gaba daya sai dai idan ba ni ce na haifesa
ba, sa'anninsa na neman 'ya yan masu kudi shi ya buge da neman talauci salon su
mallake min shi su tsiyace shi, iyayen fa matsiyata ne na gaske wllh"
Hajiya Balaraba tace "Toh shi ina ya samota?" Umma tace "Wllh
wai ya dawo daga Abuja ranan, kin san wani lkcn jirgin kasa yake biyowa ta a
nan anguwar ya ganta dai dai layinsu wai xata Unguwar sanusi, shine fa ya rage
mata hanya daga nan kuma ta makale masa ina jin, ni dai ina nan ina kokarin
cireta a ransa gaba daya" Hajiya Balaraba tace "Gaskiya kam, Allah
dai ya mana tsari" Umma tace "Ameen" sallama suka yi Umma ta
koma ciki. Bude kofa Imaan tayi ta fito misalin karfe tara na dare don kwashe
socks da kananun kayan da Ammi ta wanke mata a cloth line, da kyar take tafiya
don ji take kamar xaxxabi xai rufeta ga ciwon kai, tun bayan Isha Mujaheed ke
xaune kan farin kujera ta wajen parking space dinsu, yana jin fitowarta kuwa ya
mike ya tsaya kusa da wani flower dake opposite cloth line din, bbu wuta gaba
daya a wajen hakan ya ba Imaan mamaki sai tayi tunanin mutuwa bulb din yayi,
nan ko shi ya cire bayan ya dawo masallaci, sai da ya jira ta fara kwashe kayan
nata sannan ya cafkota ta baya, yasan next action dinta hakan yasa ya rufe
bakinta da sauri, tayi mugun tsorata wanda hakan yasa ta fara numfashi da
sauri, yayi freeing bakinta yana kallonta don gaba daya ya ma mance da laluran
nata, ya dukar da ita da sauri yace "Ke relax now, nine fa, stay still and
relax" kasa yin hakan tayi babu bata lkci kuma Asthma dinta ya tashi a
wajen, daga ta yayi ya shiga apartment dinsu da ita, Ammi ta mike tana
kallonsu, ya xaunar da ita kasa, Ammi ta wuce dakinta ta dauko inhaler dinta ta
mika masa ya amsa ya bude cap din ya kai mata baki, sai da Ammi ta ga
numfashinta ya fara dawowa steady sannan ta juya ta wuce bedroom dinta.
Kwanciya Imaan ke son yi ya dagota yana kallonta yace "Ina ke maki
ciwo" Hawaye cike idonta ta nuna masa kafarta, yace "Kin sha
magani?" Ta girgixa masa kai, yace "Ina magungunan?" Ta nuna
masa bedroom dinta, dagata yayi suka wuce dakin nata, ya dau magungunan ya bude
su sannan ya fita xuwa kitchen ya dauko ruwan gora da glass cup ya koma dakin,
bata maganin yayi ta karba ta sha, ya mike ya dauko na tube da take shafawa a kafanta
da bayanta, dawowa yayi kan gadon ya durkusa kusa da ita ya daga rigar baccin
jikinta xuwa thigh dinta, ta bude ido tana kallonsa, duk ta wani langwabe tana
sauke numfashi a hankali, shafa mata man xafin ya shiga yi, kamar xata yi kuka
murya can kasa tace "Wayyo Yaya yana min ciwo" hararanta yyi bai dai
ce komai ba, ta runtse ido ta kama hannunsa tace "Ni wllh ciwo yake min ka
min a hankali" Buge mata hannun yyi ta janye da sauri, haka ta dinga yarfe
hannu har ya shafe mata maganin daga thigh har fararen toes dinta, gaba daya
jikinta ya dau xafi wanda at anytime xaxxabi zae iya rufeta, a hankali tace
"Yaya saura bayan" yana kulle tube din yace "Baxan yi ba"
da kyar ta mike xaune ta sauke rigan jikinta xuwa waist dinta ta koma tayi rub
da ciki, yace "Ki shafa da kanki baxan shafa ba" a hankali tace
"Baxan iya ba ae, don Allah ka shafa min" da kamar baxai shafa ba sai
kuma ya bude tube din ya matso methylated cream din ya fara shafa mata a bayan
a hankali, lumshe ido tayi cikin sanyin murya tace "Yaya kai na ciwo yake
min sosai, kamar xaxxabi xan yi" ya hade rai yace "Ina kika tafi
daxu?" Ta bude ido da sauri tace "Gidan Gwaggwo naje" yace
"Waye ya ajiye ki a mota?" Ta xaro ido sai kuma ta turo baki bata san
duk yana kallonta ba, yace "Ba tambayar ki nake ba" kamar xata yi
kuka murya can ciki tace "Ya Muhsin ne fa" mintsilinta yyi a bayanta
yace "Ni xa ki ma karya?" Ta yi wani kara ta mike xaune da sauri tana
shafa wajen, ganin kallon da yake mata ta xaro ido tayi wani karan ta koma tayi
rub da ciki tace "Wayyo bana so yaya" yace "Nace wa ya ajiye ki
daxu?" Ta rufe idonta tace "Ya Muhsin" yace "You are still
lying koh? Wannan yayi kama da motar Muhsin?" Ta turo baki tace "Ya
canxa mota" yace "Ohk, idan kika bari na fita dakin nan baki gaya min
ko waye ba, this case will pend har ki gama langwabe langwaben ki kuma I
promise i will deal with you" kamar xata yi kuka tace "Yaya abokin ya
Muhsin ne fa, tare muke da shi sai ya sauka a wani anguwa xai yi wani abu shine
abokin ya ajiye ni shi, ka kira ya Muhsin din ma ka tambayesa wllh" yana
gyada kai yace "ke yanxu kin girma baki da aiki sai shiga motar karti suna
ajiye ki kofar gida koh?" kallonsa take kamar xata fashe da kuka ya mike
ya ajiye tube din xai fita, a hankali tace "Yaya baka gama shafawa
ba" wani shegen kallo ya mata ya fice dakin. A stairs ya hadu da Umma xata
sauko parlor, ya jira ta wuce tana kallonsa tace "Mura kake nake jin
kamshin aboniki?" Ya wara ido yace "Oh, eh daxu naji kamar xan yi
muran shine fa na shafa a kirji" Umma tace "Toh Allah ya sauwake"
daga haka ta wuce shi ma ya wuce sama ya shiga dakinsa, gun injections dinsa ya
nufa ya dau pcm da syringe yasa a aljihunsa sannan ya sakko parlor, Umma tace
"Ga fa abincin ka can ka bari yana galallawa a dinning" Mujaheed yace
"Ohk xan ci Umma" tace "Yanxu ina xa ka?" Yace "Card
xan amso waje" daga haka ya fita, sanin halin Ummar tasa, hakan yasa ya
fita gidan gaba daya, bayan kusan minti bakwai ya dawo ciki ya nufi part din su
Imaan, Ammi na kitchen tana wanke wanke jin an bude kofar parlor ta leko suna
hada ido yace "Allura na dauka na pcm naga tana xaxxabi" yana magana
yana ciro alluran a aljihu Ammi bata tanka sa ba ta koma kitchen Bedroom dinta
ya bude ya shiga ya sameta yanda ya bar ta har ta fara bacci, ya isa kusa da
ita ya xauna bakin gadon ya fara hada alluran yana gamawa ya juya yana kallonta
yace "Kee" tayi nisa baccin dama gata mai nauyin bacci, sanin haka ya
ja hancinta yace "Imaan" bude ido tayi da kyar xata kara rufe idon
yace "Baxa ki tashi ba?" A hankali tace "Yaya me xan yi
kuma" Ta bude ido sosai ganin abinda ke hannunsa ta mike xaune da sauri
tana jan rigar ta xuwa chest dinta tace "Yaya wa xaka ma alluran?"
Yace "Gado" kamar xata yi kuka tace "Ka mance na sha magani
ne" yace "Kar ki bata min lkci my frnd" ta fashe da kuka tace
"Na shiga uku Ammi ni ban ce a min allura ba" Tana fadin haka xata
mike ya fixgota ya kwantar da ita ya daga rigar jikinta ya mata alluran ya mike
ya fice daga dakin, sai da Ammi ta shigo dakin tana mata mugun kallo sannan ta
hakura da kukan ta koma ta kwanta nan da nan kuma bacci ya dauketa. Imaan na
dawowa schl ranan litinin taga calls har biyu da ta yi missing, bayan ta idar
da sllh tana xaune kan darduman ta dau wayar tayi dialing number din, har ya
katse ba a dauka ba, few seconds later sai ga call din ya shigo wayarta, dagawa
tayi ta kai kunne, sallama aka yi daga daya bangaren cikin cool voice, tayi
shiru da farko, can kuma tace "Waye ne?" Yace "Baki amsa sallama
ne?" Tace "Not a must in amsa a fili, who are you" yayi murmushi
yace "Ohk then, how are you?" Tace "I asked who are you
first?" Yace "Tsoro kike ji?" Tace "Sorry i think it's a
wrong call" yace "Why do you say so?" Tace "Because without
any doubt I know it's only my dad, mum.... and very few dat have my
contact" yace "Ohk... Muhsin
ya sa in kira in ji ko kin shiga gida lafiya" ta d'an bude ido da mamaki
amma ta kasa cewa komai, yyi murmushi a hankali yace "How are you
Imaan?" Murya can kasa tace "Alhmdllh" yace "I guess yanxu
kika dawo schl?" Tace "Sure" yace "Alryt, sai islamiyya
ko?" Tace "Eh" yace "Ohk then Allah ya kiyaye hanya, amma
tare xa ku yi sauka da su Mariya?" Tace "In sha Allah" yace
"Saura wata nawa?" Tace "Two months" yace "Maa sha
Allah, we will talk later kar kiyi latti" tace "Sai anjima" daga
haka ta katse wayar ta mike ta fara shirin Islamiyya. Bayan Magrib Mujaheed na
xaune parlon Abbansa da duk yan gidan, Yusuf ma dake xaune wayarsa kawai yake
ta dannawa a parlon, Anty duk ta fiddo ankon bikin Seeyama suna nuna ma Abba,
Umma dai na xaune ta hade rai don gani take kamar Anty shishshigi kawai take
mata, Anty tace "Toh Abba ga kaya nan, gaba daya kala uku ne"
Mujaheed yace "Toh duka kala ukun xa su yi?" Anty tace "Ehh ko
kana da damuwa da hakan??" murmushi yyi bai ce komai ba, Yusuf ya daga kai
yace "Amma fa Anty yayi yawa sai kace su ne..." Mugun kallon da
mahaifiyar tasa tayi masa yasa yyi shiru ya ci gaba da danna wayarsa, Abba yace
"Kice expenses ne ba na wasa ba, to da wanne ku ke son mutum ya ji, ina
laifin ma kala biyu?" Umma tace "Haba Alhaji, abu dai na rana daya
lkci daya, ni fa da cewa ma nayi kala hudu hudu Amina tace a bar shi a kala uku
kawai" Abba ya gyada kai bai dai ce komai ba, Anty tace "Idan ma baxa
ka siya masu ba ga yayyinsu sai su masu" Umma tace "Atoh dai"
Yusuf yace "Mu dai sai dai muyi masu kala bibbiyu" Anty tace
"Toh ka rike kudin ka" Dariya yayi yace "Shikenan ni sai in ma
Rahma da Ummi M.A yayi maku sannan yayi ma Maimoon" Umma tace "Sai
kayi ma Kakarku ko kala biyu ne ita ma, shikenan it's settled" Yusuf ya
dinga kallon Umma bai ce komai ba, Abba yace "Toh mamana fa?" Anty ta
buda ido tace "Ai kuwa Imaan... kaga na ma mance wllh, shikenan sai
Mujaheed yayi mata kaga hakan ma is settled" Abba yace "Ehh sai
Mujaheed yayi mata" Umma ta yi ma Anty wani kallo tace "Wani Mujaheed
din, shi Yusuf me ya hanasa yi mata?" Anty tace "Saboda kince yayi ma
Kakarsu, kinga Mujaheed sai yayi ma Imaan" A fusace Umma tace "Toh an
ruguje wannan tsarin kowa tayi ma 'yar ta, Inna kuma Alhaji ko baban ita Imaan
din su yi mata" Abba yace "Ba tsarin da ya ruguje Hajiya, Mujaheed yayi
ma ke, Amina... da maimoon sai Imaan, Yusuf kuma yayi ma Ummi, Rahma da Inna,
kuma a cire ma imaan nata a kai mata yanxun nan" Anty ta cire ma Imaan
kala uku, Abba ya kalli Mujaheed yace "Dauka ka kai mata" Mujaheed ya
kalli Umma da ranta idan yayi dubu a lkcn ya baci, Anty tace "A'a jira, yi
min transfer din kudin Imaan din yanxu tukun, sauran ko daga baya ne sai ka
yi" Mujaheed ya kasa cewa komai, Anty tace "Malam ka min shiru ina
maka magana m" ya dau wayarsa gabansa na faduwa sai dai bai yadda ya kalli
Umma da ko ba a fada masa ba yasan
kallonsa take, ya gama danne dannensa yace "Anty ina jin ba
network...." Ta mike ta isa kusa da shi ta amshi wayar tace "Baxa ka
raina min hankali ba" sanin Gtb yake amfani da lkci daya ta danna transfer
code dinsu tayi komai ta sa har account number dinta bayan ta sa amount sannan
ta mika masa tace "Sa min pin" Karba yyi ya sa pin din ta amshe
wayar, duk ya kasa kallon Umma, sai da Anty ta ga transfer din yayi sannan ta
basa wayarsa ta koma ta xauna, lkci daya aka turo masa debit ya bude ya ga 30k
ta yi transfer, Abba yace "Toh ka dau kayan ka kai mata sai kace mata kai
ka siya mata" Kasa tashi yayi, Abba ya hade rai yace "Are you stupid
ina maka magana kana xaune, wato abinda kake nufi shine baka jin maganar kowa
gidan nan sai na uwar ka koh, ina fa lura da kai kuma nake sharewa" Tashi
Mujaheed yayi ya dau ledan kayan ya nufi kofa, Umma ta mike fuu ta wuce sama,
Anty tayi wani murmushi a ranta tace "da sauki ai tunda ba bin sa xa ki yi
ba" A hankali Mujaheed ya murda kofar apartment dinsu Imaan ya shiga da
sallama murya can kasa, Imaan ce durkushe parlon da yar ves sai skirt iya
cinya, nose mask na hancinta tana goge gogen kayan da ke daukan k'ura a parlon,
ta mike ta cire abun bakinta tana kallonsa, Ammi ta fito parlor jin an shigo,
yyi kasa da kai ya ajiye ledan hannunsa kan kujera yace "Abba yace a kawo
mata" daga haka ya juya ya fita ya kulle kofar, Imaan xata bude ledan Ammi
ta mata tsawa, dakatawa tayi da sauri, fuska daure Ammi tace "Kina ganin ya
shigo amma kika ki wucewa daki da wannan shegun kayan jikin ki koh, tun daxu
nake maki magana ki nemi kayan arxiki ki sa ko don saboda ciwon ki sannan kada
wani ya fado amma kin maida ni mahaukaciya, ke kam wace irin yarinya ce Allah
ya bani, in ji hankalin ki ya kwanta da ya shigo ya ganki a haka?" Imaan
sai kallonta take da mamaki tace "Ammi yaya ne fa" Bude baki Ammi
tayi tana kallonta, can tace "Sai aka yi ya don shi ne?" Tace
"Toh Ammi shi ne fa ba wani ba ya shigo, dama dai ya Yusuf ne kin san
baxan tsaya haka ba" Ammi ta kasa daina mata kallon mamaki tace "Shi
yayan muharramin ki ne Imaan?" Imaan ta xaro ido tace "Ammi yaya fa
har wanka ya taba min ina karama, kuma da ba shi ke sa min kaya ba ma idan ban
sa ba, ni dai bana jin kunyarsa wllh, dama dai yaya Yusuf ne shi ko dankwali
bana tsaya kusa da shi ban sa ba, shi kuma yaya ni xan ma iya cire kaya a
gabansa, toh har yau ba yana shafa min magani a kafana da bayana ba, ko wajen
inna idan yana nan ina....." Ammi taga bude baki fa ba nata bane ta dau
daya daga pillows na kujera ta jefa mata a mugun fusace tace "Ban taba
sanin ke shahararriyar mahaukaciya bace sai yau, wato iskanci yasa kike cewa ya
shafa maki maganin xafi koh, to in sake gani sai na ci uban ku ke da shi, kuma
kar ki fasa cire kaya gabansa tunda ke shashasha ce, sai kace warce bata taba
shiga ajin islamiyya ba wai kina cire kaya gaban namiji da ba muharramin ki
ba" Imaan ta nufi daki kamar xata yi kuka tace "Ni fa ba yanxu nake
cewa ba Ammi, da da nake nufi, kuma naga ai yayana ne shi tunda ba ni da wani
yayan" ganin Ammi ta yo kanta ta shige dakinta da gudu ta sa makulli tana
turo baki kamar xata fashe da kuka.
15..
*Imaan* is not free subscribe and read hankali kwance🤷🏻♀️It's
300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit
07087865788 to be included in the payment group
Ammi ce xaune parlon inna ta sanadin aikawa da innar tayi a
kirata, ta fi minti sha biyar parlon amma inna bata ce da ita komai ba sai goge
gogen kayan kallonta take, Ammi ta bukaci ta yi mata goge gogen inna tace ta
bar shi, bayan wani minti biyar din Ammi tace "Inna na daura girki ne
wllh...." Inna tace "Kin daura girki? Tabdi... Toh ita warcan 'yar da
kika bari meye amfaninta da baxata dinga duba maki girkin ba, ina ce yau
alhamis babu islamiyya" Ammi tace "Barci na baro ta tana yi"
Inna ta tabe baki tace "A haka dai kullum, Allah dai ya mana tsari ya
fidda d'a na kunya, amma gaskiya ni tunda nake tafasasshen ruwan Imaan bai taba
shiga baki na ba, toh uwar me xata je ta dafa ma mijin ma idan tayi aure,
kullum ayi ta laka ma yarinya ciwo ana daure mata kugu wai bata da lafiya, to
ni dai ba ruwana ba wanda xai xagi d'a na, idan ma an samu to Allah ya
isa" Ammi dai bata ce mata komai ba, Inna ta xauna tace "Tana yar
yarinya da ita tayi ta langwabewa, tana abu salalo salalo, ana ma ciwo sharri
to ni dai ba ruwana, dama magana nake son yi mama ke da Amina, to Aminar bata
ga damar xuwa ba har yanxu, tana can sai ta mula ta mulmule sai kace xata ma
Maryam haka....." Inna bata rufe baki ba Anty ta shigo da sallama, Tace
"Sannu inna..." Inna ta tsuke fuska tace "Yauwa" Anty ta
xauna tana kallon Ammi tace "Uwar Imaan kwana biyu" Ammi tayi
murmushi tace "Ae kam duk mun buya" Mikewa inna tayi ta ci gaba da
goge gogenta, Anty tace "Goge goge kike Inna" a fusace Inna tace
"Toh baxan yi goge goge ba in mutu cikin wari yar nan, ko ke baki ga ko
ina tsaf ba, ko hancin ki bai ji kamshin dake tashi parlon ba, wllh tun safe
ban xauna ba ina ta aiki baki ji bayana ba kamar ya balle in huta, ke hatta
simintin da kika tako kika shigo nan sai da na goge sa fess yau, ai kazanta
bata da kyau, ni dai in sha Allahu cikin kamshi xan mutu ba ruwana, kuma tirr
da kazami, ai ina lura duk cikin jikokina babu wanda ya dauko tsafta ta sai Mujaheed"
Anty da Ammi dai sai kallonta suke, ta xauna tace "Yo Mujaheed mana, shi
kadai ne Allah ya ceta ta wannan fannin, duk inda kazanta take ma shi bai xuwa,
kullum tsaf xaka gansa abunsa, baxa ku yarda da xance na ba sai kun shiga
dakinsa, ko don raino na ne shi din oho, ga shegen kyankyamin tsiya.... shi
kuma wannan katon Isuhu ba shi da aiki sai saka gogaggun kaya da fesa turare
amma duk kika basa abinci to wllh a nan xai bar maki kwanon ya tsallake ya
wuce, to ina tsafta a nan, ai ta nan ake gane kazami, dakinsa kuwa karkari ya
kakka6e gadon ya kara gaba, ita ko wannan mai laluran Imaan ga dai gashi har
gashi amma ba gyara malam, kullum gashin nan a kume xa ki gansa sai ta fi sati
da sattuka bata sharce ba, to ina tsafta a nan, da an mata magana sai tace xafi
yake mata, ai duk mace ta gashi ake gane kazantar ta ni kwarkwata ma nake guje
mata wllh, sannan babu tattali kullum sai ta bar min adikonta a nan idan ta xo,
ga su can na tara yafi kala dari yanxu, Ko uwarta xan ci da su oho, ni ce ma
Bukar xan yi ma ya daina siya mata turmin atamfa gwara a siya falle a mata riga
da sket banda dankwali, Atoh shi kenan yayi ta asaran dukiya atamfa dai masu
tsada amma tayi ta walakanta adiko, Maimoon kuwa dama kayan datti sai ta tara
ta tara taga babu sarki sai Allah, babu wanda xata saka sannan xata kwashesu ta
hau wanki duk su cika gida, to ina mace a nan, babu kazantar da ya fi wannan
wllh, sauran yan matan kuwa ni wani lkcn ma sai in ji kamar wari suke
wllh...." Murmushi Anty tayi, Inna tace "Wallahi ba batun dariya ba,
to dai kowa tasa ta fishshesa a gidan nan ba ruwana da kowa ta kaina nake,
yanxu dai abinda yasa na kira ku ba wani abu bane...." sai kuma ta yi
shiru, su dai kallonta kawai suke, tayi kasa da murya tace "Ku lissafa min
daga ranan asabar xuwa yau kwana nawa kenan" Ammi tace kwana shidda"
Inna tace "Toh yau kwana shidda rabon Mujaheed da Imaan su xo min nan su
gaisheni, yanxu fisabillahi daga sun min ba dai dai ba na nuna bacin raina sai
su kullace ni, meye laifina don nace ban yarda shanye min fura da suka yi
ba" Anty ta bude baki tace "Gaskiya basu kyauta ba har kwana
shidda" Inna ta fara matsar kwalla tace "Ni fitinata har ya kai
Mujaheed ya ki takowa nan yau har kwana shidda, daga gyara kayanka sai ya xamo
sauke mu raba? Ke Amina na kira ki ne a matsayin uwarsa don ba ruwana da wancan
katuwar da ta haifesa, ke kuma Aisha saboda Imaan yar ki ce" Anty tace
"Amma Inna ca nake kince kada su sake xuwa maki idan ba haka ba xaki bar
gidan" Inna xaro ido tace "Oh oh Allah kaji wata magana don Allah, to
Amina idan na bar gidan nan ina da gidan uban da xanje in tsugunna, duk ba
xance bane dai da tsorata mutane, bacin rai ai babu abinda bai sawa, don nace
kada su sake xuwa kowa yasan fada kawai nayi, me suka min da xan hanasu xuwa
nan?? Allah ya tsine ma fura da nonon in dai saboda shi xan kori jikokina, meye
kuma wani fura da nono kamar mayyar bafillatana" Anty na danne dariyar ta
tace "Ahh to gaskiya basu kyauta ba" Inna ta kalli Ammi tace "Ke
kuma Aisha kinyi shiru kina kallona ko baki da abun cewa ne?" Ammi tace
"Kiyi hakuri Inna, ina komawa xan sameta" Anty tace "Nima
Mujaheed na dawowa aiki xan samesa In sha Allah" Inna ta gyara xama tace
"Toh, sai ku ji dalilin da yasa xa su min haka su kaurace min, yanxu duk
saukin kai na su basa gani, ni ba mafadaciya ba, ni ba fitinanna ba, ni ba mai
sa ido ba, ni ba mai kwadayi ba, ni ba mai mita ba, toh meye xasu wani dauke
kafa daga magana dai ta fahimta, to sai dai idan Ahmadu ne ya hure masu kunne
ya masu hudubar tsiya, banda haka su har wani wayo garesu da xasu dauke kafa
daga xuwa inda nake" Anty ta fara dariya, Ammi kam murmushi kawai tayi,
Inna tace "Aa don Allah ku duba xancen da kyau, wllh xuge su aka yi, kuma
ba kowa xai yi hakan ba sai mutumin nan Ahmadu don Bukar baya haka shi, ni
gaskiya na ma daina sa Ahmadu a lamarina daga yanxu tunda tsanata yake cusa ma
yaran a rai, anjima kuma xan sa kira min Bukar yaji abinda ake ciki, kwana
daidai har shidda fa" Ammi ta mike tace "Ki yi hakuri Inna ina komawa
xan mata magana bari in je in duba girki na" Inna tace "ke ta girki
ma kike ga maganar al'ajabi ana yi a nan Ahmadu ya xuge yara, haba don Allah
abinci dai abinci dai kamar ana yunwa Amina" Ammi ta nufi kofa tace
"Toh sai dai anjima inna" Inna tace "Toh Allah bamu alkhairi, ki
dai tsitsiyeta kiji dalili" fita Ammi tayi parlon bayan ta ma Anty
sallama. Inna ta tabe baki tace "Kinga bafillatanin mutum, kinga agwai??
Wllh ki ji tsoronsa, barin idan kika ga ya fiye shiru shiru banda haka ki ga fa
babu abun kirki da tace har ta bar parlon nan, Bukar dai na ganin boni, mata
kamar kurma, ni kwanciyar hankali na ma Imaan bata dauko halinta ba, Imaan xata
iya kwatar kanta a ko ina da bakinta, tun daga ranan da na karanta mata ta
daina gaida Uwar Mujaheed gashi har yau bata gaisheta, gashi har Ahmadu da
Bukar sun gaji sun kyaleta, kusan ma Imaan ce kadai ta dau halina a gidan nan
wlh, banda haka ya xata dinga gaida katuwar mata bata amsa mata, da ta fi ta
iskanci kuwa kinga ta daina gaishetan gaba daya" Anty dai dariya kawai
take, Inna tace "Toh ni dai ki taimake ni Amina ki rufa min asiri,
Mujaheed na dawowa ki titsiyesa a daki kiji me na masa da ya dauke kafa a
nan" Anty tace "In sha Allah Inna, bari in je nasan ma ya dawo yanxu
tunda biyar har ta yi" Inna tace "To yi maxa" tashi Anty tayi ta
mata sallama ta fita inna ta mike ta ci gaba da goge gogenta tana cewa
"Ahmadu dai ya lalace, da dai ba haka yake ba"
Dariya sosai Imaan ta dinga yi bayan Ammi ta bata sakon inna,
tayi mai isarta ta mike daga kwancen da take tace "Ba Inda
xanje Ammi, tun Sunday kinji ta kai karana gun Abba, to haka
ya fi, ita da bakinta tace wannan time din ba wasa take ba Abba ya ja mana
kunne sosai don muna xuwa part dinta xata tsallake ta gudu ta bar gidan"
Ammi tace "Toh nace bayan magrib kije ki gaisheta, kina gaidata ki
juyo" Imaan ta fashe da kuka ba hawaye tace "Ammi don Allah ni baxan
je ba, ina xuwa xata ce na mata wani abu" Ammi ta mike tace "Toh idan
na baki abincin ki kai mata kar ki kai" daga haka Ammi ta bar parlon,
Imaan ta fara kukan gaske, har ranta bata son xuwa gun inna. Anty na gama girkin
dinner dab da magrib ta fito kitchen, ganin Mujaheed xai fita masallaci tace
"Dr idan ka dawo mosque ka sameni bedroom" Yace "Toh" daga
haka ya fita parlon, tare suka dawo masallacin da Yusuf, bayan sun haura sama
Mujaheed ya shiga dakin Anty, Yusuf ya shiga dakinsa, Anty na xaune kan darduma
ta shafe addu'o'in da take ta mike ta dauke pray mat din ta linke tana kallonsa
tace "Toh ka tsaya min kamar soja a kai ka xauna" murmushi yayi yana
shafa kansa ya xauna gefen gadon, tace "Yanxu M.A idan kowa ya guji inna
kai ma sai ka gujeta" ya d'an buda ido yace "Inna kuma?" Tace
"Eh mana" yace "Ban gane ba Anty" tace "Kirana tayi
daxu wai kwana shidda rabon da kaje bangarenta kai da Imaan" Mujaheed yyi
murmushi bai ce komai ba, Anty tace "Toh ka gama murmushin ka tashi ka ta
fi ka gaisheta" mikewa yayi yace "Wa?? Ai har abada ni da xuwa
apartment dinta, beside irin warning da Abba ya min ma is not funny don
haka..." Anty ta karasa masa tace "Baxa kaje ba koh?" Yace
"Allah Anty kinga kwana biyu shiru bata ce an mata komai ba hakan bai fi
ba?" Anty tace "Toh ni dai nace ka tashi ka je" ya mike xaune
yace "Anty ki bari kawai ba inda xanje" Anty tace "Wato ban isa
da kai ba kenan, idan Hajiya ce tace kaje xaka ce mata ba xa ka ba?" Yayi
murmushi yace "Anty Hajiyan ma
hanani xuwa bangaren tayi gaba daya" Anty tace "Toh tashi ka fita ka
ban waje" ya marairaice mata yace "Wllh Anty ina iya xuwa yanxu tace
nayi mata wani abun" Anty ta hade rai tace "Cewa nayi ka gaisheta
kawai ka juyo" Ya lumshe ido ya bude yace "Wllh da ba don ke bace ni
ba inda xanje Anty" Anty tace "Naji din tashi ka fita, idan ka dawo
kuma ka xo ka gaya min, gobe da safe kuma xan je in ji ko ka je" Murmushi
yyi ya mike ya fita dakin. Tun da Imaan ta fito parlonsu rike da warmer din abinci
take tsaye jikin wani flower taki tafiya, kiris ya rage ta fashe Inda take
tsaye, daga nisa ta hango Mujaheed yana tahowa waya kare kunnensa, labewa tayi
ta koma bayan flower din ta tsaya da sauri, sai da ya d'an wuce inda take ta
fito tayi wani kara a bayansa, still yyi na few seconds, ta fashe da dariya ya
juya yana kallonta, ya wani hade rai yace "Kee" Ta wara manyan idonta
tace "Toh ai baka ji tsoron ba ma" Wani kallo ya dinga mata, ta turo
baki ta wuce sa, sai da ya ga tayi nisa sannan ya bi bayan ta, tsaye ya ganta
tana lekan parlon inna don kofar ba duka aka rufe ba, ya cire takalmansa
outside the balcony yayi tiptoeing har bayan ta, fingers dinsa ya kai gefen
cikinta yayi tingling dinta, ihu ta fasa ta sake abincin hannunta, tuni ya
janyeta wajen don gaba daya tuwo da miyar dake warmer din ya tarwatse a kasa,
ta xaro ido a rikice tace "Innalillahi yaya ka xubar" daga cikin
parlor inna ta dinga cewa "Me aka 6arar??" Ummi ta bude kofar, Imaan
dai sai kallon abincin take kamar xata yi kuka, Inna ta mike ta taho wajen tace
"Meye hakan?" Kamar xata yi kuka tace "Yaya ne ya xubar da
abincin da na kawo maki" Inna tace "Toh sai ki kwashe ki mayar mata
ta canxa min wani ba ruwana" Imaan ta shige parlon ta xauna ta rungume
hannu tace "Salon Ammi ta doke ni ba ga abinci nan Ummi ta kawo maki
ba" Inna tace "Aa wllh kinga ina cin wani abu banda tuwo, Ummi maxa
kwashe ki kai ma Aisha kice yar ta ta xubar ta xubo min wani" Ummi tace
"Mu ma fa tuwo muka yi" A fusace Inna tace "To ni ina ruwana da tuwon
ku? Ku tuwon ku har wani dadi garesa miya kamar an wanke kai, ki min abinda
nace kada ran kowa ya baci a gidan nan" Ummi ta mike a fusace ta kwashe
tuwon ta mayar cikin warmer din, Imaan tace "Dama kice yaya ne ya xubar na
ni ba" Inna tace "Haba dai, dama ina xa ki iya xubar da wannan
abincin ai sai dai shi" Tsallake miyar Mujaheed yyi ya shiga parlon ya
xauna, Ummi ta tafi da abincin da ta kwashe part din su Imaan, gyaran wajen
inna ta dinga yi duk suna xaune, bata gama ba Ummi ta dawo da wani abincin ta
ajiye ma inna tace "Imaan Ammin ki tace xa ki dawo ki sameta" Inna
tace "Sai me xai faruwa idan ta sameta, bakin cikin kara min abinci take
komai, ina laifin ma tace xata gamu da Mujaheed din, Imaan ce ta wani san xubar
da abincin mutane, bata ta6a ba tunda take, lafiya take kawo min abinci ta koma
to yau da yake ta hadu da wnn mutumi a hanya" tana kai wa nan ta shiga
parlon tana kallon Ummi tace "Don Allah ki rufa min asiri ki taimakeni ki
karasa goge wajen baki ji bayana ba kamar xae cire" Ummi tace "Toh su
da suka xubar...." Kallon da Mujaheed ke mata yasa tayi shiru ta mike rai
ba dadi ta fita ta ci gaba da gyaran wajen. Inna ta shiga daki sai ga ta ta
fito da bowl na dambun nama, tace "Tun ranan litinin nake ta ajiya amma
ban gan ku ba na nace to ko lafiya, na ba kowa nasa...." Mujaheed ya amsa
yace "Na waye wannan din?" Tace "Na kai da takwara ta" Ya
saci kallon Imaan, da sauri Imaan tace "Inna ni dai ki raba mana da
kanki" Mujaheed yace "Toh samo leda sai ki raba mana" komawa
daki Inna ta yi, Mujaheed ya mike kafin Imaan ta ankara har ya fice parlon,
kwalo ma inna kira ta yi, ya saka takalminsa ya kara gaba, inna ta leko parlon
tace "Lafiya!" Imaan ta fara kuka tace "Ya tafi da naman gaba
daya" inna tace "Maxa tashi ki bisa in ya kama ki je parlon Ahmadu ki
tafi" Imaan ta mike ta fita parlon, bata son gudu saboda laluranta, hakan
yasa kafin ta iske sa har ya shige part din su, ta goge hawayen da ya cika
idonta a ranta tace "Allah ya isa" daga haka ta wuce apartment dinsu
kawai, Sai da ta tsaya Ammi ta gama fadanta na xubar da abinci da tayi sannan
ta shiga bedroom dinta. Bayan isha tana saka kayan baccinta wayar ta ya fara
ring, duk tunaninta Sadeeq ne don kullum sai ya kira ta da daddare sun gaisa
duk da basa waya mai tsawo iyaka gaisuwa shikenan amma har wani murna take idan
ya kirata, Daddy ta ga ke kiranta, ta daga a hankali tace "Ina yini
daddy" yace "Lafiya lau Mamana, ya gida?" Tace "Alhmdlh ya
aiki?" Yace "Da godiya, kina karatu sosai dai koh?" Tace
"Ehh ina yi" yace "Maa sha Allah, daxu kafin magrib inna ta
kirani wai sati daya kenan baki je gaisheta ba, why is that?" Imaan tace
"Daddy na fa je yau" Daddy yace "All those days me ya hanaki
xuwa?" Tace "Cewa tayi kar mu sake xuwa ni da yaya fa" yace
"That's because kuna mata rashin kunya ke da shi, wato warning da na maki
kafin in tafi went in vain koh?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace
"Toh kar ki sake skipping one day baki je gaisheta ba, idan Ammin ki ce
don ta maki fada xa ki k'i xuwa gaisheta, she is my mother Imaan you have to
respect her much, shi ma Mujaheed na kirasa ban samesa ba ki kai masa waya
yanxu" Kamar xata yi kuka tace "Toh" daga haka ya katse wayarsa,
Hijab ta sa har kasa ta fita, Ammi dake parlor tana kallo ta bi ta da ido,
Imaan tace "Daddy yace in kai ma yaya waya" Ammi tace "Shi me ya
samu wayarsa?" Bude hannu tayi alamar bata sani ba, Ammi ta ci gaba da
kallonta, hakan yasa ta nufi kofa ta fita. Babu kowa babban parlon nasu don
hatta kayan kallo ma a kashe suke, ta haura sama ta na kallon direction din
dakinsa don har ta manta rabon da ta je wajen, takawa tayi har bakin kofar
sannan ta bude tana lekan cikin bedroom din, wani sanyayyen kamshi me hade da
sanyi ya doki hancinta da fuskarta, shiga dakin tayi ta kulle kofar, ko ina fes
har kan gadon dake dauke da farin bedsheet, Ko ba a fada mata ba tasan wanka
yake jin saukan ruwa da kamshin sabulu da ya hadu da kamshin dakin, xaro ido
tayi tana kallon sketches dinta dake bangon dakin kusan gudu hudu, tun tana
Jss3 tayi drawing din mai kyau coz she is more than perfect a zane, turo baki
tayi ta dau kujeran dake gaban mirror ta kai jikin bangon ta hau ta dinga cire
hard carbon paper din a hankali kar ya yage. Bude kofar bathroom Mujaheed yyi
ya fito da short yana goge gashin kansa da karamin towel, xaro ido yyi yana
kallonta da mamaki, ta juya jin an bude kofa suna hada ido ta turo baki tace
"Yaya daddyna yace in kawo maka waya" Tana magana wayarta da ta ajiye
kan gado ya fara ring, sakkowa tayi da sauri ta dau wayar tace "Ga shi nan
ya kara kira" daga haka ta nufesa ta daga kiran ta kai kunne tace
"Daddy ga shi nan" mika masa wayar tayi ya amsa ya kai kunne hade da
sallama, Kamar ance ta juya taga bowl din dambun naman da ya dauke ajiye a
gaban mirror dinsa, yana magana da daddy amma duk hankalinsa na kanta kuma yana
lura da ita, ganin ta nufi gun mirror din ya fixgota, xaro ido tayi xata yi
magana ya rufe bakin, sai ce ma daddy yake toh don ya kagu ya katse wayar,
kamar kuwa daddy ya shiga ransa yace "Shikenan we will talk tomorrow sae
da safe" da sauri yace "Allah ya tashe mu lafiya Abba, mun gode, sae
da safe" daga haka ya katse wayar ya juyota yana mata wani irin kallo yace
"Drawings din da kika cire nake so ki hau kujeran ki maida su yanxu kafin
ki fada min sanda na fara wasa da ke da xaki shigo min daki kai tsaye" ta
6ata fuska tace "Toh ba waya na kawo maka ba" Jan kunnenta yayi yace
"Baxa kiyi knocking idan kinji ba a amsa ba kiyi wucewar ki" muryar
Umma suka ji a corridor tana ma Maimoon masifa wai ta share datti ta kai bakin
kofarta lkci daya kuma tana tambayarta ko Mujaheed na dakinsa, Maimoon da ta
hade rai tace "Yana ciki" Mujaheed ya xaro ido ya ja Imaan ya bude
kofar bathroom dinsa suka shiga ya kulle kofar, dai dai nan kuma Umma ta shigo
dakin tana kiran sunansa, Irin tsoratan da imaan tayi ba a cewa komai, Mujaheed
ya dukar da ita kasan bayin murya can kasa yace "Kee you better relax now
kar in mare ki, ance maki xata shigo nan ne" kai kawai take gyada masa
numfashinta na sama, ya cire Hijab din jikinta yace "Nace maki ba fa
shigowa xata yi ba, breath in and out gently now" jingina take son yi da
bango ya jawota jikinsa ya rungumeta yana shafa bayan ta a hankali to calm her
down, tuni Umma ta fice dakin ganin Mujaheed bai ciki, bayan kusan minti biyar
jin tana fitar da numfashin a hankali kuma a nutse ya dago kanta yana kallonta,
hawaye ne makale idonta, ya daure fuska yace "What?" A hankali ta
nuna masa kirjinta, ya mike ya fita bathroom din ya sa makulli kofar dakin
sannan ya dawo ya fito da ita dakin, wajen da yake ajiye drugs da allura ya
bude yana dube dube, can kasa ya hango inhaler dinta da take bari a dakinsa a
da idan ta xo, ya juya ya kalleta ya ga kwanciya tayi kan gadonsa ta takure
waje daya, ya mayar da inhaler din ya mike, ya dau gogaggen jallabiyarsa ya
saka don tuni jikinsa ya bushe, ya feshe jikin sa da turare, ya dau drawings da
ta ciro ya fara maidawa jikin Bangon, Imaan ta mike xaune tana turo baki xata
ce masa don me idonta ya kara sauka kan dambun dake gaban mirror, tashi tayi a
hankali har sannan hannunta na kirjinta ta isa gaban mirror din ta dau bowl
din, karan bude kofar da yaji ya sa ya juya, xata fita da gudu ya bi bayanta da
sauri yana cewa "ke har kin manta abinda ya same ki a bathroom ynxu koh,
ba ruwana fa idan...." Tuni ta fara sauka stairs, sai da ya tabbatar ba
kowa corridor sannan ya bi bayan ta da sauri, amma har ta fita gidan, can ya
hangota a durkushe kusa da apartment dinsu, karasawa yyi kusa da ita a
hanxarce, ya durkusa kusa da ita yace "Ba nace kar kiyi gudu ba..."
Dagata yyi ganin Asthman ne ya tashi ya amshi bowl din, ya wuce da ita cikin
apartment dinsu, Ammi ta tabe baki ta mike ta dauko inhaler ta jefa masu, sai
da ya ga numfashinta ya dawo dai dai sannan ya mike ya dau bowl din naman ya
ajiye a kafarta yana mata wani kallo ya fita parlon, a hankali take sauke
numfashi ta bude bowl din ta fara cin naman.
*The book Imaan is not free, it's for sale, you read for free
ur cup of coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit
07087865788 to be included in the payment group.
16.....
Ranan Friday Imaan suka gama exams din first term ss2, suna
tsaye tare da Mariya a bakin gate din makarantar tasu ko wannensu na jiran
driver, Ummi da Rahma ko fitowa cikin schl din ma basu yi ba, Maimoon dai na
tare da wata Kawarta a waje ita ma, Mariya na ganin motar Sadeeq tace
"Lahh ya Sadeeq ne ma ashe shi sa ya bata mana lokaci" Imaan dai bata
ce komai ba, tunda yayi parking idonsa ke kan Imaan, suna had a ido gabanta ya
fadi, siblings din sa duk suka shiga motar, Mariya bata taba sanin Yayan nata
na interacting da Imaan ba don Imaan din bata gaya mata ba, Mariya tace
"Mu je ku gaisa da shi, shine ya ta6a ajiye ki gida ko baki gane sa
ba" Imaan ta d'an yi murmushi kawai, Mariya ta kama hannunta suka nufi gun
motar, Mariya tace "Ya Sadeeq frnd dita da ka taba ajiyewa a gida..."
Ya cire glass din idonsa Yace "Yea na gane ta" Imaan ta sauke idonta
kasa tace "Ina yini?" yace lafiya lau, fatan an gama exams
lafiya" tace "Alhmdllh" yace "Toh Allah bada result mai
kyau" ta daga kai tana kallonsa tace "Ameen" lallausan murmushi
ya sakar mata ta dauke kai da sauri gabanta na faduwa, yace "Let drop u
mana" ta girgixa kai tace "Aa yanxu driver din mu xai xo" Yace
"Ohk then" ta saci kallonsa ya kashe mata ido daya, ta daga ma Mariya
hannu ta juya da sauri ta tafi gun Maimoon, Sadeeq ya tada motar ya bar wajen,
Ya Yusuf ne ya xo daukansu bayan tafiyar su Sadeeq da kusan minti bakwai,
Maimoon na turo baki tace "Ya Yusuf driver din fa?" Yusuf yace
"Ya kai su Umma kasuwa, M.A aka ce ya dauko ku tun daxu ya ki, ni kuma
ynxu na dawo aiki" Maimoon ta kyabe baki tace "Da dai Anty Farida aka
ce yaje ya dauko, jiya fa da yamma har Hayin d'an bushiya muka je daukota taje
gidan aunt dinta, baka ga uwar wahalan da muka sha ba ga hold up sai kusan
shidda da rabi muka dawo gida" Yusuf yace "Au suna tare har yanxu
kenan?" Maimoon tace "Tab, sosai ma, gobe xata koma schl sai kaga
tulin shopping da yayi mata" Yusuf ya sake baki yana kallonta, Maimoon ta
kyalkyale da dariya tace "Amma fa wllh ya Yusuf kar ka ce masa komai, dama
yace kar in fadawa kowa" Yusuf yace "Ae ko kin fada ma kowa tunda
kika fada gaban Imaan da Ummi" Imaan ta hade rai tana kallonsa ta madubi
tace "Ya Yousuf kamar ya?" Ya wara ido yace "Ke sai ki kwasa ki
kai ma inna, Ummi kuma ta gaya ma Umma, saukin abun dai idan magana ya fita an
san it's either Imaan or Ummi sae M.A ya ji dadin jibgarku da kyau" Imaan
ta xumburo baki tace "Naji dai" Ummi kuwa yi tayi kamar bata ji sa ba
dama, suna isa gida Maimoon tace "Dama ya Yusuf ka ja masu kunne ba ruwana
idan suka fada ma kowa" wani kallo Imaan ta watsa mata ta fice daga cikin
motar tana turo baki ta kara gaba. Satin da aka shiga banda shirye shiryen
bikin Seeyamah babu abinda ake a gidan, tun ranan lahadi yan uwa suka fara xuwa
daga nesa gida ya fara cika da jama'a, kowa ya xama busy a gidan barin Umma da
Anty, Ammi kam baya baya ta dinga yi, tun a ranan lahadin dama ta kai nata
gudunmawarta na tsadaddun manyan bedsheets biyu, da set din food warmer shi ma
biyu masu kyau sosai, a walakance Umma ta dubi kayan aka bar su a nan parlorn.
Ranan laraba Abba ya ba su Maimoon kudin gyaran gashi da lalli a kai su Saloon,
Har xa su fita ya dakatar da su ya ciro wani dubu biyar din yace "Na mance
ban bada na mamana ba, gashi nan ta shirya ita ma ta je" Fita suka yi su
hudu Ummi na cewa su yi wucewansu kawai don Imaan ba xuwa xata yi ba, Maimoon
tace "Ba ruwana Abba cewa yyi mu je mu kira ta" A balcony suka tadda
Anty tana magana da wa enda xa su yi girkin biki a biya su, Mujaheed ma na
xaune balcony din sai Yusuf dake tsaye, Anty tace "Saloon din xa ku
yanxu" Maimoon tace "Anty Abba yace mu je da imaan" Anty tayi
wani dariya tace "Wace Imaan din tab, amma ku je dai ku ji abinda xata
ce" Imaan na dakinta Maimoon ta shigo parlor, nan ta sanar ma Ammi abinda
Abba yace Ammi ta kira Imaan, tana fitowa Ammi tace "sai ki dau Hijab ku
wuce saloon" sosai gabanta ya fadi ta marairaice tace "Saloon kuma
Ammi, aa ni dai xan wanke gashina da kai na" Ammi tace "Kee! dau
Hijab ki fice min parlona, dama idan baki gyara gashin nan ba yau kar ki dawo
min gidan nan" Imaan fa fashe da matsanancin kuka tana kallon uwar tata,
ganin Ammi ta mike ta shiga daki da sauri ta dau Hijab dinta ta fita, Maimoon
ta bi bayan ta tana dariya kasa kasa, Anty na ganinta tace "Subhanallahi
me ya faru Imaan" cikin kuka tace "Anty ni fa gashina bashi da wani
datti kawai combing dinsa ne bana yi" Anty tace "Toh mu ga
gashin" tana shesshekar kuka ta cire Hijab din ta cire hulan kanta, Yusuf ya dauke kai bai son dariya ta fara
wani sabon kukan, ga dai gashi har gashi amma duk an cukuikuye shi waje daya,
Anty tace "When last kika wanke gashin" a hankali tace "Ranan
nan" Anty tayi murmushi kafin ta ce komai Mujaheed ya mike fuska daure
yace "Mu je in kai ku saloon din" Ta fashe da sabon kuka xata koma
bayan Anty ya ja ta sai gun motarsa, Yusuf yayi murmushi yace "Da yake Umma bata nan ba" Su
Maimoon duk suka shiga motar bayan ya tura Imaan ciki, Suna isa saloon din
Imaan ta hadiye kukan da take barin da taga yan mata kala kala cikin saloon
din, Ita Mujaheed yasa a fara gyara ma gashin, da ruwa mai dumi sosai yace a
wanke mata gashin nata bayan an sa mai, banda turo baki bbu abinda take tana
runtse ido don ba daman kuka ga yan mata kar su mata dariya, lkci daya gashinta
ya dawo sak na Indians sai sheki yake, ganin an kusa gama mata ya kalli kannin
nasa yace "Sai ku samu napep da xai maida ku gida, coz I am a driver to
none of you" daga haka ya fice saloon din, duk suka bi sa da kallo. Sai
bayan magrib suka shigo gidan don har da lalle suka yi, dama Imaan direct part
din inna ta nufa tun daga bakin kofa ta cire Hijab din jikinta ta shiga tana
murmushi tace "Inna..." Inna tayi mitsi mitsi da ido tana kallon
gashin nata tace "Ikon Allah kin ganki kin fito sak mace ko?" Imaan
ta xaro ido tace "Toh da ni na miji ne?" Inna tace "Idan ba
kallon isuhu nake maki wani lkcn ba shegiya nake" Imaan ta fashe da dariya
har da kwanciya kan kujera, Inna ta kalli Mujaheed dake cin abinci tace
"Ko kai baka gani ba Mujaheed?" Imaan ta hararesa ta gefen ido ta
mike xata shiga daki Inna tace "Dawo nan ana ma yar uwar ki gyaran jiki
tunda can bangarensu ya dawo kamar wajen cin kasuwar laraba" Imaan tace
"Anty Seeyama" Inna tace "Ehh kema da dai Allah ya fiddo maki da
mijin nan kiyi aurenki da wuri ki haifi kanninki da uwarki taki haifo
maki" Imaan ta hade rai tace "Yar karama da ni xaki ce min
aure?" Inna ta kalli Mujaheed tace "Don Allah Mujaheed Imaan bata isa
aure ba yarinyar da ke al'ada? Ga kirjinta cike da dukiyar fulani"
Murmushi Mujaheed yyi kansa a kasa yana cin abincinsa, Imaan ta harari Inna ta
juya ta nufi kofa inna tace "Ke kika sani, ni ba ruwana wllh, Allah na
tuba lalurorin ki na duniya ma ai tsaye yake da kafafuwansa gun d'a na, ba
gwara kiyi auren ko Bukar xai huta da kashe kashen kudi kije can kuma mijin shi
ma ya d'an dana ukubar" Washegari alhamis Imaan ta tashi da ciwon ciki ga
bak'i a part dinsu balle tayi raki yanda ranta ke so, duk magungunan da ta sha
ba wanda taji ya mata, ta lallaba da kyar ta tafi bangaren inna, ita din ma dai
parlon nata duk tsofaffin kawayenta ne a xaune, imaan ta gaishesu da kyar ta
shige bedroom dinta ta kwanta, lkcn Azahar nayi dama inna ta lallabo ta shigo
dakin ta sa ma bandakinta makulli don ba wanda xai shiga balle ya mata kazanta
duk me son yin alwala ga pampo can ta bude, idan kuwa xai kama ruwa ne to yaje
sashin masu biki, ganin juye juyen da Imaan take duk ta hada xufa duk da iskan
fankan dake dakin ta wani xaro ido tace "Ke lafiya meye hakan, ni fa ba
ruwana idan baki da lafiya ne ki tafi bangarenku kada a gigitani a nan, meye
wani juye juye kamar macijiya a kan gado na" Imaan ta fashe mata da kuka
tace "Wayyo cikina ke min ciwo" Inna tace "Auzubillahi, to rufa
min asiri ki sakko ki tafi gun uwarki ba ruwana" Cikin kuka tace
"Akwai mutane a can" a fusace Inna tace "Mutanen banxa ina
ruwanki da su, idan wani abu ya sameki maganin me mutanen xa su yi banda su
cika mu da surutu, dama ba komai ya kawo su ba sai kwadayin d'an shinkafar da
xa a raba a kwano da kaji banda haka wani ma anyi shekara goma ba a gansa ba,
ki tashi ki tafi tasan yanda xata yi dake idan ma asibiti ne ta kai ki, idan ko
ba haka ba idan ban sa an dage bikin ba ace bani ba, biki ya fi rai ne" da
kyar Imaan tace "Ni fa marana ke min ciwo" Inna tace "Wai
jini?" Imaan ta gyada mata kai, Inna tace "Toh shi kuma wanda kika yi
ko sati ba ayi ba fa?" Tace "Ba shi bane kawai alama ne" Inna ta
xabga tagumi tace "Ke kam kina ganin jarabawa iri iri a rayuwa na lalura,
banda haka jinin ma idan xakiyi sai kin ta fama, anya kuwa ba a sa maki hannu
ba imaan?" Imaan ta xamo daga kan gadon tace "Wayyo ni dai ki kira
min yaya " Inna tace "Waye kuma yaya?" Hawaye na sakko mata tace
"Ni dai ki kirasa" Inna tace "Toh su wa encan tsofaffin duk
tsami sun cika min parlor kamar ni xan aurar da 'ya sun ki tafiya, ni dai na
gaji wllh ana damuna, wata ma ni nafi shekara talatin ban gan ta ba, ni dai
gaskiya sun isheni suje can bangaren da ake biki kuma sun ki, duk parlona ya
gauraye da warin tsofaffi, wannan fitina da mai yayi kama" Imaan na son yi
dariya amma ciwo yaki barin ta tayi, Inna ta fita fuska daure ta kashe TV da ke
aiki tace "Kada TV ya buga in ja ma Ahmadu asara gwara a bar shi haka nan
ya huta" daga haka ta dau wayarta ta fita don neman me kira mata Mujaheed,
wata ta samu a tsakar gida ta nufeta tana kallon mata yan gayu xaune tsakar
gidan, tace "Toh dai gida ba na bitilman bane duk wanda ya xubda ko kwayar
shinkafa yyi hakuri ya share fisabillahi, kar a tafi a bar mu cikin wari cuta
ta kama mu" mika ma matar wayar tayi tace "Gashi Idan kin iya karatu
ki duba lambobi xa ki ga ansa Dakta, lambar Mujaheed ne shi ya sa mun shi a
haka, sai ki kira min idan kuma baki iya ba don Allah kar ki rikita min wayar
in shiga uku" murmushi matar tayi ta nemo number tayi dialing ta mika ma
inna, ta amsa ta kai kunne, sai da yayi ringing sau uku sannan Mujaheed ya
daga, inna tace "Mujaheed??" Mujaheed yace "Ina ji, ya aka
yi?" Inna tace "Toh ga yar uwar ka nan dai rai a hannun Allah, duk
inda kake ka rufa mana asiri ka juyo ka dawo, ni sae in iya cewa a daga bikin
ma wllh don idan ta mutu ni nayi asara...." Da mamaki yace
"Wacece?" Inna tace "Wacece banda Imaan, tun safe Ashe tana
dakina babu inda bata mirgina ba don ciwo, tun daga kan gadon har kasan tass,
wai yanxu na shiga dakin don kulle bandakina saboda marasu hankali masu shiga
bayin mutum suyi kaca kaca da shi kawai naga yarinya duk ta hada xufa a kan
gado kai kana ganin ta kasan...." Mujaheed ya katse ta yace "Ina
hanya" daga haka ya katse wayar, Inna tace "Atoh haka kawai, bikin
banxa bikin hofi..." Daga haka ta nufi part dinta, tana durkushe bakin
kofa tana watsi da takalman jama'a can gefe ganin duk ya cika mata bakin kofar
ta ji muryar Mujaheed a bayan ta ta mike, tace "Wannan uban sauri haka
kamar wanda ya biyo jirgi, to ka shiga tana can ciki ban san isilinta ba"
Shiga parlon yayi ganin mutane ya sunkuyar da kansa ya gaishe su ya wuce dakin
Inna, karasawa kan gadon yayi yana kallonta yace "Me ya faru?" Ta
fashe da kuka sosai tace "Yaya cikina" hannu ya kai cikin yace
"Tun yaushe?" Ta cire hannunsa tace "Ni ba cikin bane ke min
ciwo, period ne" ya daure fuska yace "Toh me xan maki, ba kin sha
magani ba" da kyar tace "Bai yi ba, doctor Habib allura yake
min" yace "Toh me ya hanaki kiransa?" Tace "Yana
Lagos" yace "Toh bani da allura a nan sai na koma asibiti" ta
kamo hannunsa cikin rawar murya tace "Toh ka tafi da ni asibitin
plss" tana fadin haka ta fara kokarin sauka kan gadon, bude baki yyi ganin
yanda tayi ma inna stain din kan gado, bai san lkcn da ya dauke kai yana
murmushi ba don har ya hango inna, ita ma xaro ido tayi tace "Na shiga uku
yaya" yace "Aa sai ta gani xaki ki shiga ukun ai, yanxu kina daya
ne" ji tayi gaba daya ba ciwon ta sauko kasa da sauri jikinta na rawa tace
"Wayyo yaya ya xan yi" Tana fadin haka ta nufi bathroom ta murda ta
ji a rufe, tsayawa kallonsa tayi kamar xata yi kuka tace "Yaya ta sa
makulli" parlor ya koma gun inna yace "Inna xata shiga bayi ina
makullin" inna ta mike da sauri tace "Auzubillahi, wani bayin? Aa ta
fito ta tafi nasu idan ma baxata iya tafiya ba ka goyata, haka kawai bayina
fess ta shiga ta sa min k'arnin jini" Kunya ma yasa Mujaheed ya kasa cewa
komai don mutanen dake parlon sun kai shidda, ganin inna xata shiga dakin ya
rigata shiga da sauri, ya dau dankwalinta ya rufe saman gadon da shi, Imaan ta
marairaice tana kallon inna da ta shigo tace "Don Allah ki ban makulli
wllh xan wanke maki bayin" Inna tace "Ai uwata bata ce min je ki kya
gani ba, don haka ba bayina xa a shiga a min kazanta da jini ba, ki daure ki
tafi can bangaren ku idan ma tafiyar ne baxa ki iya ba sai Mujaheed ya goya
ki" Kuka Imaan ta fara yi tace "Na fa ce xan wanke maki wllh" a
fusace Inna tace "Kai ku fita ma ku bar min dakina kuje can bangaren ku
karata, da na bar ki ma kika kwanta min saman gado duk da ban san al'ada kike
ba" Mujaheed yace "Toh ki bata xan wanke maki bayin da kai na"
Inna kamar xata rushe masu da kuka tace "Yau naga abinda ya isheni bai
ishi Allah ba, wai ana dole ne, hypo uku na xuba bayin nan daxu da safe da nake
wankewa, a kan wani dalilin xa aje a bata min da karni...." Ya katse ta
yace "Ni kuma xan xuba maki hypo biyar" da kyar da kyar da sidin goshi
inna ta bada makullin shi ma sai da aka yi yarjejeniyar baxa a bude mata drum
din ruwa ba kada a xuba kazanta, Mujaheed ya dau buckets biyu ya fita debo ruwa
a waje, Ita dai imaan na tsaye sai satan kallon saman gado take, Mujaheed na
ajiye ruwan a bayin ta bi sa ciki tace "Wayyo yaya pant da pad da xan
canxa fa?" Ya kalleta da mamaki yace "Ni ma kike tambaya?" Ta
marairaice tace "Plss ko xaka je dakina...." Ya jefa mata wani kallo
yace "You are stupid" fitowa bayin tayi ta bude gun kayanta a
wardrobe din inna, ai ko taga panties dinta na nan, tace "Yaya toh saura
pad" Yace "Bari in xama pad
din ki sa" Bata ce komai ba ta turo baki ta shiga bandakin ta rufe, juyawa
yayi ya fita, ya tafi gun mai kiosk dake layin ya amso always daya ya dawo,
inna dai na xaune ta daura kafa daya kan daya tace "Allah ni dai ya dubeni
ya rabani da k'arni, komin xuba hypo da xa ayi a bandakin nan" Mujaheed
bai ko kalleta ba ya shiga dakin, yana ta tsaye har Imaan ta fito daure da
towel din inna, ya jefa mata pad din kan gado, ta turo baki tace "Thank
you" komawa bandakin tayi ba a dau lkci ba ta fito, yace "Sai ki cire
xanin gadon ki wanke" ta xaro ido tace "Yaya ya min nauyi fa"
bude baki yyi yace "Toh ki bar shi haka nan" kamar xata yi kuka ta
isa kan gadon ta shiga cire xanin gadon bayan ya dauke pillows din kai, Muryar
inna suka ji tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, jinin ta xuba min a
kan gado ni Asabe????" Inna ta fashe da kuka tace "Me na maki xaki
saka min da haka Imaan" Mujaheed ya dauke kai yana kokarin danne dariyarsa,
imaan duk ta gigice, inna tace "Toh sai ki Kwashi xanin gadon don ubanki
ki Bukar kai ma Aisha ta wanke min, kai kuma ka fitar min da katifar waje ka sa
min shi a setin rana, Allah ubangiji ya saka min, daga taimako sai ta xuba min
al'adarta a xanin gado k'arni ya kashe ni" Inna ta kara rushewa da
matsanancin kuka tace "Sannan d'an walakanci tana yoyon xata dau tawul
dina ta daura salon ta goga min gaibu, ni dai na shiga uku da wannan 'ya ta
Bukar, tana cutata a gidan nan" Imaan ta wani hade rai kamar xata yi kuka,
Mujaheed ya cire xanin gadon ya wuce bathroom da shi, Inna na matsar kwalla ta
daga hannu biyu sama tace "Allah kaga xuciya daya nake xaune da kowa gidan
nan, duk mai nufina da sharri ka min iyaka da shi" Tana fadin haka ta share
idonta ta fita tace "Bari xanje inji ko Aishar ce ta sa ki xo ki cuce ni
yau" Imaan ta murguda baki ta fiddo kayanta a press ta saka, bude kofar
bathroom din tayi ta ga Mujaheed yana aikin wanke xanin gadon.
17....
Imaan dai na tsaye har ya gama wankin bedsheet din tana rike
da kayan da ta cire, ya saka xanin gadon a bucket ya fito, a hankali tace
"Yaya to wankin bayin fa?" Wani mugun kallo ya watsa mata ya dau
wayarsa da makullin mota da ya ajiye kan gado zai fita ta xaro ido tace
"Yaya don Allah ka tsaya, baxan iya shanya bedsheet din ni kadai ba
ai" ko juyowa bai yi ba balle ya tanka ta, a bakin kofar parlor ya hadu da
Inna, Inna ta gwalo ido tace "Har an wanke min bayin?" Yace "A'a
xan fita in amso Hypo ne" yana magana ne yana kokarin fita, inna ta
cakumosa tace "Sai dai ka raina ma Bukar ko Ahmadu hankali, ce maka nayi
bani da hypon?" tana fadin haka ta ja sa xuwa bedroom din fuskarta daure,
yace "Toh ki sakeni mana" ko saurarensa bata yi ba har suka shiga
dakin, Imaan dake labe bayan kofar dakin tana jin sun shigo dama ta fito da
sauri ta fice a dakin, Har bandakin Inna ta turasa ta dauko Hypo biyu ta jefa
masa, yace "Biyar fa kika ce Inna" a fusace tace "Toh ai ni ba
asararriya bace Mujaheed, Ko sisin Bukar da Ahmadu babu a Hypon, Isuhu ne na
roka ya siyo min" tana fadin haka ta dau ledan omo babba ta jefa masa tace
"Har jikin tiles ni dai a gurje min ba ruwana, kuma daga yau gaskiya idan
Imaan ta sake shigo min daki xa a ga bala'i, wato kawai fasa bomb din bala'i
xanyi a gidan nan, naje yanxu uwar bata nan, da sai in ji ko ita ta turo min
ita ta cuce ni ta xuba min al'adarta, banda ma kazanta irin na yaran ynxu duk
sai sun bari kowa ya san suna al'ada, gantalalliyar duk ta tashi ta kazance min
kan gado da bandaki, to hirrr dinta kada ko da wasa ta sake leko min daki ta
tsaya iya falo, idan kuwa dama bata da tsarki kar ta yo min nan xan koreta don
parlona na tsarkakakku ne" Mujaheed dai bai tanka ta ba ya nade sleeve din
shirt dinsa ya fara wanke bayin bayan ya kada kumfa da hypo, inna tace
"A'a bana son aikin al'gus malam, ka kara barbade bandakin da omo lungu da
sako sai ka juye dayan hypon" ya jefa mata wani kallo yace "Toh wai
ni na bata maki bandakin daga taimako kawai" Inna tace "A'a ba ruwana
saboda kai na bude, in don ta wancan matar ce ai sai dai ta tafi bangarensu
jage jage da jini don wllh baxan bude ba, haka kawai" ko kallonta bai yi
ba ya ci gaba da wankin bayin da babu abinda ya samesa, haka inna ta dinga basa
wahala tana tsaye daga bakin kofa tace can tace nan, har daga karshe aka gama
wanke bayin, ya wanke hannunsa ya fito fuska daure, tace "Toh don Allah ni
dai kar in kwana cikin k'arni yau ka taimakeni ka fidda min katifar can ka
ajiye dai dai idon rana" yace "Wannan kuma sai dai ki kira Yusuf
baxan iya ba gaskiya" Tace "Toh wllh baxa ka fita dakin nan ba sai
tare da katifar nan, haka kawai in kwana cikin najasa, kafar ka kafar
katifan" tana fadin haka ta sa makulli a dakin ta tsaya bakin kofa,
kallonta ya dinga yi fuska daure, inna tace "Oho dai duk kanwarka ta ja
maka, ita yanxu ba gashi ta gudu ta bar ka da aikin jini ba, yarinya sai
mugunta fal cikinta" Babu yanda ya iya haka ya cire katifar ta bude masa
kofa tace "Saitin rana xaka ajiye duk ya kona abinda ya xuba kai"
fita yyi da katifar ya ajiye inda tace, ya dawo dakin don daukan wayarsa da makulli,
ganin babu su a inda ya ajiye ya kalli inna dake tsaye tana kallonsa kyarr,
bucket din xanin gadon ta nuna masa tace "Idan ka shanya wnn sai ka dawo
ka amshi wayar ka da makulli ba ruwana, yarinya dai ta cuce ka kawai, sae dai
sakayyar Allah" tana fadin haka ta koma parlor, Mujaheed ya fi minti uku a
tsaye, yasan ko me xai ce mata baxata basa ba, hakan ya sa ya ja tsaki ya dau
bucket din fuska daure ya fice dakin, yana gama shanyawa a nan parlorn ya ajiye
mata Bucket din yace "Bani wayana in wuce" ta jefa masa makullin siff
dinta tace "Ka bude ka dauka ka rufe min kayana" daukan makullin yyi
ya koma daki ya bude yana daukan wayarsa da car key ya bar mata siff din a
wangale ya fice kamar xai tashi sama, inna tace "Oho dai....." Dab da
Magrib Ammi ta shiga tada Imaan dake ta bacci tun bayan da ta kara shan magani,
Ammi tace "Ya jikin?" A hankali tace "Da sauki, Ammi Daddy ya
dawo?" Ammi tace "Ehh ya dawo" wara ido tayi ta sakko kan gado
ta sa Hijab har ta isa kofa ta tsaya ta juyo tace "Ammi hope bak'in duk
sun tafi?" Ammi tace "Ina kuwa xa su gobe biki?" Imaan tace
"Toh daddy yana bedroom dinsa ne?" Ammi tace "Aa ina jin suna
can tare da Abba" Imaan na sa takalminta bakin kofa aka bude kofar parlon,
d'aga kai tayi taga Inna ce, Inna tace "Ya jikin, na ji shiru tun daxu
baki leko ba shine nace bari in lallabo in xo in duba ki, kun je asibitin
ne?" Imaan da ta hade rai ta ki kallonta tace "Ni na ji sauki"
inna ta amsa gaisuwar masu gaisheta a parlon sannan ta kalli Imaan tace
"Tohhh, Allah dai ya sauwake, amma wannan wahala ba gwara Bukar ya aurar
da ke ba kowa ma ya huta kema ki huta" Ammi dake tsaye tana jin su ita ma
ta gaida inna, inna tace "Lafiya lau Aisha, in ji mai gidan ya dawo
lafiya?" Ammi tace "Alhmdllh" Inna tace "Toh da kyau, duk
da dai ni ko tsinke ba a kawo min a tsarabar da yake yowa, sai dai ke da yar ki
ku cinye, to duk ba wannan ba don bai dameni ba wanda Ahmadu ma ke bani Allah
ya amfana, yanxu dai xuwa nayi in duba jikin Imaan, ta xo daxu tana ciwon mara
ban kai ga jik'a mata ararra6i ba na nemeta na rasa" Ammi tace "Ta ji
sauki yanxu, sai dai ko ta bi ki ta amsa ta sha a can" inna ta gwalo ido
da sauri tace "Ta bi ni ina? A'a ta xauna xan lallaba in koma in jiko mata
in kawo yanxu, ta bi ni kuma ana xaune kalau? Taje ta min me kuma ban da abun
ki Aisha yarinya na fama da kanta, Aa bari inje in dawo yanxu, dama na bar
sauran tsoffin da basu tafi ba kada a min barna" daga haka ta juya ta bar
bakin kofa murya can kasa tace "Haka kawai ta sake koma min ta min wani
aika aikan da kazantar ta a gida ta cuce ni, wa gareni da xai bi min hakkina
ban da Allah" Imaan ta turo baki ta fita parlorn ko da wasa bata fadi ma
Ammi abinda ya faru daxu ba, part din su Maimoon ta nufa, kasa shiga parlon
tayi ganin mutane a ciki, ta fi minti biyar tsaye bakin kofar taji muryar Yusuf
yace "Me kike yi nan Imaan" kallonsa tayi tace "Toh akwai mutane
a parlon ta ya xan shiga" tana magana tana kallon Mujaheed da ya wani hade
rai don tare da Yusuf suke, dauke kai tayi bata son tayi dariya, can ta turo
baki ta bar bakin kofar ya shiga ciki, Yusuf yace "Toh ko in maki
jagora?" Dariya tayi tace "Daddy na yana parlon Abba?" Yusuf
yace "Eh mana" tace "Toh oya ka shiga gaba sai in bi ka a
baya" a haka suka shiga parlon tana boyewa a bayansa wanda hakan yasa few
kawayen Umma dake parlon suka dinga kallonta har suka shiga parlon Abba. Da
gudu ta tafi ta rungume daddy tace "Daddy sannu da dawowa" Daddy yace
"Baki gaida Abba ba" kallon Abba dake kallonta tayi, ta boye fuskarta
tace "Ina yini abba" yyi murmushi yace "Lafiya lau daughter"
Daddy yace "Toh baki gaida yayanki ba shi ma" ta kalli Mujaheed dake
parlon tace "Ai mun hadu a waje" Daddy yace "Toh maa sha
Allah" Tace "Daddy baxan je gombe Hutu ba tunda mun yi holiday?"
Abba yace "Wajen wa a gombe" murmushi Daddy yayi yace "Kanwar
mamarta" Abba yace "Ohk If I recalled well last holiday ma can kika
je ko" Kai ta gyada masa, Abba yace "Kuma babu canji, ga gwaggon ku
Suleja ma ba sai ki je can ba ko da su Maimoon, dama bata da lafiya" Daddy
yace "Gaskiya ne ya kamata" Imaan ta xaro ido tace "Kauye?"
Abba yace "Of course, you will have more experience.... Shi kauyen ba wuri
bane" Ta dauke kai bata ce komai ba ta cinno baki gaba, Abba yace
"Nasan inna xata ji dadi idan taji xa ku je, kinga sae Mujaheed ya kai ku
a mota tunda ya sha xuwa tare da mu" Da sauri Mujaheed ya kallesa yace
"Abba... ai ba lalle xan gane wajen ba fa" Abba ya kallesa yace
"Last time ma ba kai ka kai mu a mota ba" da kyar yace "Abba
kusan shekara daya fa" mikewa Imaan tayi ba tare da ta kallesu ba tace
"Xan je ina taya Ammi aiki" bata jira cewarsa ba ta fice, Abba yayi
dariya yace "On a serious note dole su je riga suyi hutu bari dai a gama
bikin nan lafiya" mikewa Mujaheed yyi yace "Xan je ana kirana can
waje" daga haka ya fice a parlon, Daddy ya gyada kai yana murmushi yace
"Su masu wayo wai, gaskiya ne ya kamata su kai ma Hansatu ziyara tunda
gashi bata samu xuwa biki ba ba lafiya" Abba yace "In sha Allah I
will see to that on Tuesday if everything is settled" Daddy yace "Alhmdllh, Allah ya kai mu
lafiya" Washegari Friday bayan an sakko juma'ah aka daura auren Seeyama da
angonta Abdul, throughout shagalgulan da ake a gidan imaan na dakinta tana
bacci ko ankon bikin bata sa ba, Ammi bata takurata ta shiga jama'a ba sanin
cewar bata wani jin dadi, kuma dama bata son tayi stressing kanta ta jogana
masu wani ciwon, sai dab da xa a tafi da Amarya Ammi ta tasheta don tun daxu
Inna ke cigiyarta, sai a sannan imaan ta shiga bayi tayi wanka ta wanke baki ta
fito ta shirya cikin daya daga ankon da suka yi, ta d'an shafa powder tasa eye
pencil da chappette, sannan ta dau farin hijab har kasa ta saka ta dau wayarta,
ganin missed call ta tsaya ta duba, Sadeeq ne ya kirata, komawa tayi ta xauna
tayi dialing, katsewa yyi ya kirata, bayan sun gaisa yace "Ina kika shiga
yau" tayi murmushi tace "Bacci" yace "Uhm baki da damuwa,
ya su mama?" Tace "Alhmdllh" yace "Daxu Mariya tace min
kuna biki gidanku" tace "Ehh haka ne" yace "Shine ba
gayyata?" Tace "Uhmm" yace "Toh kin kyauta" a hankali
tace "Kayi hakuri, next time" yace "Toh waye next din auren? Ko
ke?" Ta xaro ido sai kuma tayi dariya tace "Ni kuma, yar yarinya da
ni" yace "Haba?" Tace "Ehh mana" yace "How old
are you?" Ta langwabar da kai tace "Na kusa 19 soon" dariya yayi
yace "Ehh gaskiya ne, ke yarinya ce sosai ma" tace "Toh kaga"
yace "Ko aure aka maki yanxu ma baxa ki haihu ba ai" ta xaro ido sai
dai bata ce komai ba tayi murmushi, yace "Yeahh" tace "Xa mu je
raka Aunt dina dakinta yanxu" yace "Wani anguwa ne?" Tace
"Ban sani ba dai" yace "Toh idan kun je gidan ki kirani"
tace "Toh in sha Allah" sallama yayi mata ya katse wayar. Inna ce
tsaye tsakar gida ta cakare cikin atamfa England an mata dinkin su irin na
tsoffi, ga katon gyalenta ta yafa, ga mutane duk ana ta shirin xa a wuce da
seeyama gidanta, motocin dake compound din sun fi shidda duk na daukan yan kai
amarya, tun daga nisa Imaan ke jiyo Inna ta tana cewa "Naga abinda ya
isheni bai ishi Allah ba, duk an wani yi cirko cirko a gaban motoci ku ja baya
mana kar ku gurje masu dukiya in shiga uku, ni wllh saboda bala'in mata ma duk
xafi ya isheni abu kamar maita dai, ke Maimuna ba ca nayi ki dubo min Imaan ba
ko har yanxu jinin bai dauke ba ne, duk yau ban ganta cikin jama'ah ba ko bakin
ciki take ma yar uwartata ban sani ba" Imaan ta turo baki bayan sun hada
ido da Innar, inna ta ja tsaki tace "Kai ni dai ko limamin babban
masallacin Habuja ne Bukar yau dai baxai hanaki sa gyale ba, duk yan uwanki ga
su fess cikin gyale ke ko kin maka hijabi uwa xamu je xaman makoki ba amarya xa
mu kai ba haba imaan, ni dai na gaji da maganar ki a gidan nan" Imaan ta
dauke kai har ta iso gun motar, wata kawar Umma ce ta xo tayi announcing wai
Umma tace wasu su fara tafiya kafin a fito da amarya, nan aka fara kokarin
shiga motoci, inna ta bude baki ta gwalo ido ganin wata katuwa cikin shiga ta
alfarma da gwalagwalai na kokarin shiga daya daga motocin, cikin daga murya
tace "Wayyo meye wannan kuma... Kee don Allah ki bar sirara su shiga,
banda neman magana da tsokanar fada ina xa a dake a haka, kisa kike son yi
cikin motar fisabillahi, wannan ai sai dai idan ke kadai xa aje a ajiye a dawo
to ina kuma hakan xai yiwu tunda motar ba taki bace, fito don Allah mutane su
shiga" Imaan ta boye fuskarta da Hijab kar tayi dariya, mutanen wajen wasu
sai dariya suke kasa kasa, matar ta fito kamar warce ruwa ya cinye kanta a
kasa, inna ta karasa kusa da ita tana kallonta tace "Haba baiwar Allah...
ke ba kya tsoron Allah ne wannan abu haka kinyi wani bake bake bayan motar
mutane, ina kike son a xuba sauran jama'a, ko ke baki ga irin ki bane"
Wata mata ta karaso kusa da Inna tayi kasa da murya tace "Hajiya babban
kawar uwar amaryar ce fa" inna ta bude baki tace "Babban kawar uwar
amarya kuma sai a sa mata ido ta latse hanjin 'ya yan mutane a bayan mota, dama
kisan kai ya kawota ba biki ba, wannan abu kamar giwa kice ta shiga mota, amma
bakya tsoron Allah wllh" sum sum matar ta bar wajen, Inna ta ja tsaki tace
"Kai sirara su shiga a wuce, ba ruwana a aje a tatse hanjin mutane daga
kai amarya ace bikin jikata ga abinda ya faru, to banda gwalagwalan ma duk
karya ne ya xa ayi kamar ta ace bata da mota, ke kuma imaan ga motar da xa mu
shiga can da Seeyama nace ban son tukin kowa sai na Mujaheed haka kawai
mahaukatan abokan angon su ja mu su watsar da mu a rami" Bude motar Imaan
tayi ta shiga back seat tana murmushi, Maimoon xata shiga inna tace "Toh
ina kuma wancan figaggiyar xata shiga ni patuu, ba ga motoci can ba"
Maimoon ta sauka da sauri, Imaan ta dinga dariya har da kyakyatawa, Kamar yanda
inna tace Mujaheed ne ya ja su, ita, Seeyama da kawayenta biyu sai Imaan, suna
hawa main road inna tace "Toh yau dai Seeyama gashi xa mu kai ki dakin ki,
duk da dai mijin naki wani ga6o ga6o ne kiyi masa biyayya iya yanda xa ki iya,
ni baxan ce kiyi hakuri yaje ya kashe mana ke ba gaskiya, bbu xancen xaman
hakuri, mu dai da aka cuta da hakan aje a haka, amma duk kika ga abinda baxa ki
iya dauka ba yafa gyalenki ki dawo gida, ko ki tafi sashin ubanki ko ki tafi
sashin kaninsa ko kuma ki yo sashina sai iya Inda karfin mu ya kare na kwatar
maki hakkin ki, ni fa tun daga lefen da ya hada maki dama na raina masa
aji...." Mujaheed da takaici ya ishesa yace "Haba inna yanxu fada
kike mata ko hudubar tsiya?" Inna ta hade rai tace "Ka ji min yaro da
aka haifa ina tsaye bakin kofar asibiti daga safe har dare, kai xaka koya min
xaman duniya Mujaheed, ko ance maka ban san abinda nake bane, to bari kaji ko
kai yau aka daura ma aure iyakar abinda xan gaya ma matar kenan don ni yar
gaskiya ce, akan me xa ayi ta wani ce ma mace tayi hakuri gidan miji ana
cutarta ana musguna mata, Allah kadai yasan me yasa ya halitto ni a mutan da ba
na yanxu ba, kuma ai bance kada tayi masa biyayya ba kawai idan taga xai takata
ta gudo gida, ina laifin wannan shawara tawa??" Kawayen Seeyama dai sai
kallon inna suke k'asa k'asa, inna ta ja tsaki tace "Tun da shaidan duk na
makale gefen xuciyar ku ba dole kaji haushin abinda na fada ba, maxa dai sun
xama masifa yanxu, duk halinku daya dama, yo banda halinku daya ya wuce idan
yace xai walakanta maka kanwa ka matse gantalalle ka nakada masa duka tunda ga
irin sa kamar tsinken sakace, wllh xaka iya dukansa" Seeyama dake hawaye
cikin gyalenta ta fashe da dariya, imaan na taya ta, shi dai Mujaheed bai ce
komai ba yana mamakin warce Allah ya basu matsayin kaka.....
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee
wllh*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit
07087865788 to be included in the payment group.
18....
Suna isa gidan bakin inna ya mutu murus sai 'yan idanuwa
ganin gida ne ba na wasa ba, ni ko nace dama Umma ce xata yarda 'yar ta ta auri
mai rufin asiri kawai?? Inna ta fito cikin motar tana cewa "Fito da kafar
ki ta dama in sha Allah gidan xama ne, yi nayi bari na bari, aure kuma da kike
gani d'an xaman hakuri ne duk shi muka yi muka kawo yanxu da rai da lafiya,
Allah ya maki albarka yasa gidan ki ne ke kadai don na xauna da kishiyoyi ban
ji da dadi ba, kishiya masifa ce" Wani kallo Mujaheed ya dinga mata, inna
na washe hakora tana kara kallon katon gidan tace "Toh kai Mujaheed baka
da abinda xaka ce mata ne ka tsaya wani sandandan kana kallonmu, wannan ai ya
ma fi gidanka girma wllh" Yace "Kece baki mata nasihar tun a gida ba
amma ni nayi tun a can" Kuka kawai Seeyama take, inna ta hade rau tace
"Ji shashanci don Allah, to ki bude ido ki ga gidan mana idan ba sae kin
daina shegen kukan nan ba" Mujaheed ya karasa kusa da ita yana kallonta
yace "Be the best wife you can be lil sis, wishing you a peaceful married
life" rungumesa tayi tana kuka, shi ko ya dinga kallon imaan da ta ja can
gefe tana 6a66aka dariya har da rike ciki, ganin kallon da yake mata ta shige
cikin gidan da sauri bata kuma fasa dariyar ba, cike da damuwa Inna tace
"Ni dai wllh wannan 'ya ta Bukar gani nake kamar ciwace ciwacen ta ya
shafi kwakwalwarta, to banda haka taya xa a kawo yar uwarki dakinta tana kuka,
ke baki bata hakuri ba kina dariyar mugunta, to Allah dai ya kai mu naki kiga
iskanci wllh" tana fadin haka ta janye seeyama tace "Mu shiga ciki
kiyi kukan a tsanake kin ji jikalle, kai kuma Mujaheed bayan isha ka xo ka
daukeni, idan kuma ya kama a nan xan kwana to shikenan" daga haka suka
wuce ciki shi kuma ya fita compound din da motarsa yana girgixa kai. Bayan
Magrib da rashin arxiki inna ta sallami duk kawayen Umma yan kawo amarya, Aunty
da Ammi dama basu dade ba suka bar gidan, tsaye inna tayi bakin kofa rai bace
tana cewa "Wannan ai ba yi bane, sai kace baku da maxaje baku da mafada,
amarya dai ga ta an kawota lafiya har ta hakura ta daina kuka, to ai kuma sai
kowa ya kama hanyar gidansa sai kuma wata shekarar idan ta haihu, amma duk kun
wani ja6e ba niyyar tafiya, a dai dinga jin tsoron, ni ma nan da ku ka ga ban
tafi ba kakar ta ce, ni na haifi ubanta Ahmadu, bai baci ba ko da cewa nayi xan
kwana, amma mutane karere kawai ku cika gidan yarinya kun ki tafiya, ko ita
Rukayyar ce tace ku kwana tare da su bani da labari? To ni dai ba ruwana"
Wa enda suka fita iskanci yi suka yi kamar basu ji abinda take cewa ba, wasu
kuma haushi yasa duk suka bar gidan, a fusace inna tace "Mata wasu
katangala kawai rai ba ga ta sun xaune ma yarinya a gida, ni ban taba ganin
haka ba tunda uwata ta haifeni, ku barta daga ita sai kawayenta su ma a xo a
sallamesu su kama gabansu mana" Inna na kallon imaan dake kokarin fita ta
gefenta tace "Ke kuma ina xaki sanyi ya kare maki ki cuci d'a na da kashe
kudi?" Imaan ta turo baki tace "Ina xuwa ni dai" inna tace
"Toh kar dai kiyi nisa don Mujaheed ya kusa xuwa yanxu, ba ruwana in kwana
su Ahmadu su min fada" imaan bata ce komai ba ta fita, tana ganin motarsa
ta gane don layin tamkar rana saboda hasken fitilu, ta karasa gun motar ya bude
ya fito yana kallonta, Ta sunkuyar da kai tace "Ina yini" yace
"Lafiya lau Imaan, nan ne gidan sistern naki?" Kai ta gyada masa, yace
"Maa sha Allah, Allah ya basu zaman lafiya" tace "Ameen"
yace "Amma ba nan xaki kwana ba dai koh?" Ta xaro ido tace "In
kwana kuma?" Murmushi yyi ya rungume hannu sa yace "Shi na gani ai,
Idan kika kwana ai xaki yi inconveniencing amarya da angon" turo baki tayi
tace "Toh ni dama ta ya xan kwana" yar dariya yayi yace "Gaskiya
ne, yaushe xa ku koma gida?" Tace "Muna jiran yaya ne, xai maida ni
da Maimoon da Grandma dinmu" yace "Ohk yayanku kenan" ta gyada
masa kai, yace "Idan bai taho ba let me drop you people mana" ta xaro
ido tace "Bayan ma yana hanya yanxu, ai shi ya kawo mu" Yace
"Ohk then...." Bata kuma cewa komai ba, shi kam yyi shiru yana
kallonta, a hankali yace "Kin yi kyau" Dauke kai tayi tana murmushi,
shi dai bai fasa kallonta ba, murya can ciki tace "Kai kuma baka sa
glasses dinka yau ba" wara ido yyi yace "Ya 6ata.... sai dai ki siya
min wani" ta kallesa tace "Da gaske?" Yana murmushin sa mai kyau
yace "Yea" Sunkuyar da kanta tayi, yace "Ko baxa ki siya min
ba" Ta d'an kallesa tace "Xan siya" yace "Toh yaushe xan xo
amsa?" Tace "Idan na siya" yace "Toh gobe nake so, I can't
do without it" da sauri ta kallesa sai kuma ta dauke kai tana murmushi
tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Ameen... Da yamma xan xo
amsa" ta girgixa kai tace "A'a kawai ka bar shi next tomorrow"
Shiru yyi yana kallon bayanta.... Can yace "Or wancan ne yayan naku?"
Imaan ta juya da sauri taga motar Mujaheed yayi parking, ta gyada masa kai a
hankali, tunda Mujaheed yyi parking d'an nesa da su dama yake kallonsu, Sadeeq
yace "Tunda ya gan mu bari in je mu gaisa" shiru tayi da farko, ganin
yanda yake kallonta a hankali tace "Is it necessary?" Yayi murmushi
yace "Baki son yan gidanku su san ni kenan?" D'an bude ido tayi tace
"Toh kaje ku gaisa ni xan shiga ciki in kira su Maimoon" yace
"Ohk" gate ta nufa tana satan kallon Mujaheed da ya bi ta da kallo
gabanta na faduwa, Sadeeq kuma ya nufesa, sauke glass Mujaheed yyi ya bude
motar ganin sadeeq, ya fito yana kallonsa directly cikin ido, sadeeq ya masa
sallama hade da mika masa hannu, sai bayan kusan seconds biyar Mujaheed ya mika
masa nasa yana d'an murmushi wanda iyakarsa lips, nan suka gaisa... Cikin cool
voice Sadeeq yace "I am Dr Abubakar Ahmad" Mujaheed ya gyada masa kai
kamar baxae ce komai ba, sai kuma yace "Muhammad Ahmad" Sadeeq yace
"Maa sha Allah it's nice meeting you" Mujaheed yace "Same"
Sadeeq yace "Alryt xan koma, sae da safe" Mujaheed yace "Ohk...
kun yi sallama ne" Sadeeq yace "Sure" daga haka ya nufi motarsa
ya shiga ya wuce. Inna bata fito parlon Seeyama ba sai da ta kada kan sauran
mutanen dake parlorn, har Mujaheed ya gaji da jira cikin mota, Inna ta fito
gate tare da Maimoon da Imaan ta shiga bayan mota tana cewa "Mujaheed kaga
Gantalallu kila da so suka yi su kwana a gidan, don da ban masu jan ido ba baxa
su tafi ba, ni dai ba ruwana" Maimoon ta bude front seat ta shiga, imaan
ta shiga back seat gun inna, Mujaheed dai bai kulata ba yyi reverse, Inna tace
"Ni bikin Imaan da na Maimoon ma gaskiya sae na xabi wa enda xa su raka su
daki, iyaka kawai in xauna bayan mota ni da su don ina fatan ya xamo rana daya,
Mujaheed ya ja mu in kai su dakunan su ya maida ni gida idan Allah ya yarda, ba
katuwar da xata bi mu" Mujaheed dai driving yake har ya bar layin ya hau
saman titi, lkci lkci ta madubi yana kallon imaan da ta ki yarda ta kalli gaban
motar, inna tace "Mujaheed kaga kawayen uwar ka kamar mayu kuwa, wllh da
kyar na kora su, duk sun ban wahala, ita ina ta samo su haka wasu lafta laftan
mata ba kyan gani kamar aladu? kaii Rukayya dai shahararriyar mahaukaciya ce
wllh" taka brake Mujaheed yyi bayan ya tabbatar bbu motar dake bayansa ya
gangara gefen titi, inna ta saki salati tace "Lafiya Mujaheed, me ya sami
motar" ya bude motar ya fita ya bude side dinta yana kallonta yace
"Ita uwar tawa ce mahaukaciya?" inna ta bude baki tana kallonsa, sai
kuma ta kalli Imaan tace "Ga reshen bishiya can, sauka ki karyo ki kawo
masa...." Imaan ta hade kai da kafarta tana dariya kasa kasa, a fusace
inna ta kunduma masa xagi tace "Na ce mata mahaukaciyar sharri na mata, da
hankalinta ina ita ina gunduma gunduman matan da ta ajiye matsayin kawaye,
wasun su idan suka xaune kanta shegiya nake idan bata suma ba bayan sun latse
ta" yace "Ku saukar min a mota ku samu wanda xai kai ku gida
Hajiya" kamar jira Inna take ta sauka da sauri tana kallon Imaan tace
"In dai kin san motar ba ta Bukar bace ki sakko ki bar masa tsiyar
sa" Imaan ta hade rai tace "Inna bai ce har da mu ba fa" Irin
kallon da Mujaheed yyi mata yasa ta sauka da sauri don ya dade bai mata irin
kallon ba, Inna ta kalli Maimoon tace "Ke kuma idan ba ta Amina bace motar
ki sakko kema" Maimoon ta bude front seat ta sakko, inna ta fara matsar
kwalla tace "Ku sama min Adaidaita sahu" ko kallonta Mujaheed bai yi
ba ya rufe back seat dinsa ya shige motarsa ya kara gaba, inna ta bi motar da
kallo tace "Allah dai ya isa, kuma sai Ahmadu ya min iyaka da Mujaheed
yau, ni xai toxarta ya walakanta a bakin titi a kan Rukayya" Imaan ta
tsayar da adaidaita ta fada masa inda xai kai su, Mai adaidaita yace "Ba
can xan yi ba" bai gama rufe baki ba inna ta shige adaidaitan ta xauna,
Imaan da Maimoon suka saki baki suna kallonta, Mai napep din ya juya yana
kallonta yace "Baaba nace ba can nayi ba" a fusace tace "Dalla
can mu je d'an nan, ko baka ganin dare yyi ne xaka ce min ba can kayi ba, jika
na ne fa ya watsar da mu a titi yanxun nan yyi wucewarsa daga nayi ma katuwar
uwarsa gyara, banda haka yaushe xaka gan ni bakin titi tsaye da gata na,
motocin 'ya yana sun fi biyar wllh, ko da yake in mun je gidan ma xaka gane
abinda nake nufi, ko kai so kake inyi ta tsayuwa kamar yar iska bakin
titi?" Shiru yyi bai ce komai ba, Inna ta kalli su Imaan sannan ta kallesa
tace "Yaro idan baxa su shiga ba ja ni ka kai ni gida, su kuma Allah ya
kawo masu mafita, mu je ni dai" murmushi mai napep din yyi, Imaan ta turo
baki ta shiga Maimoon ma ta shiga, inna tace "Atoh da kun tsaya jiran d'an
sahun da xai je ku kwana a wajen" suna isa gida dama inna ta sauka napep
din ta nufi gate tana gyara yafin mayafinta, Maimoon ta kalli Imaan dake dariya
ta ja tsaki ta bude jakarta ta fiddo dubu daya ta basa ya bata canji ta wuce
ciki, can suka ga inna har ta shige parlon su Maimoon, Imaan ta nufi part din
su Maimoon ta bi bayan Inna, babu kowa parlon Abba hakan yasa inna ta dawo main
parlor tana kallon mutanen da ta wuce da farko tace "Ahmadu baya nan
ne" Daga kitchen Aunty ta leko tace "Bai shigo ba inna, kun dawo
lafiya?" inna bata tanka ta ba ta fice parlon, bata tsaya ko ina ba sai
part din su Imaan, ba kowa parlon sai kamshi dake ta tashi, cikin daga murya
inna tace "Salama alaikum" Imaan ta bude kofar bedroom dinta tana
lekowa, Inna tace "Ina Bukar din?" Daddy ya fito daga daki yace
"Har kun dawo inna" karasawa cikin parlon tayi ko takalmanta bata
cire ba ta xauna saman kujera tana share guntun hawayen idonta, Ammi dama na
jin irin sallamar da inna tayi tasan ba lafiya don haka bata fito ba, duk xaton
ta k'aran imaan ta kawo, Imaan da har ta cire kayanta ta sa Hijab kawai ta fito
da sauri, Daddy na kallon inna a hankali yace "In ji dai lafiya inna"
a fusace tace "Ina fa lafiya Bukar, shegen d'an ku ya watsar da ni
tsakiyar titi gefen jaji yayi wucewarsa, daga nayi ma Rukayya gyara" Shiru
Daddy yyi yana kallonta da mamaki, ta fashe da kuka tace "Gaskiya Bukar
idan ba a bi min hakkina ba yau duk a station xa mu kwana gwara in kai karar
can a bi min hakkina, da girmana da matsayina da martabata Mujaheed xai juye ni
tsakar titi yyi wucewarsa?? Ae wannan babban magana ce wllh" Daddy ya
sauke ajiyar xuciya yace "Subhanallah me ke damun Mujaheed haka" Inna
ta tsaida kukan da take tace "Toh ai ba ni xaka ma tambayar ba, waya xaka
dauka yanxu ka kirasa, kada ma ka nuna masa ina nan, kawai ce masa xaka yi ya
xo xaka aikesa yanxun nan, daga nan sai kaji me ke damunsa ko wiwi ya fara sha
bamu sani ba" Daddy ya kara sauke ajiyar xuciya, inna tace "Sae wani
sauke sauken ajiyar xuciya kake Bukar, ko tsoron sa kake ne inyi ta kai
na?" Yar dariya kawai daddy yayi ya dau wayarsa, inna ta tsuke fuska tace
"Wllh yanda ya min tijara a kan uwarsa kai ma haka xaka masa tijara akan
taka uwar, kuma idan baka ce masa aikensa xaka yi ba wllh baxai xo ba nan kuma
xa mu kwasa mu tafi police station " Daddy dai bai ce komai ba yayi
dialing number Mujaheed ba a dau lkci yana ringing ba ya daga, Daddy yace
"Muhammad kana kusa ne?" Daga daya bangaren Mujaheed yace "Eh
Abba" daddy yace "Toh ka xo parlor na yanxu" Mujaheed ya d'an yi
shiru, kafin yace "Toh Abba" Daddy yace "Don't keep me waiting
fa naji kayi shiru ko baka kusa ne?" Yace "Ina nan" Daddy yace
"To ina xaune ina jiranka yanxu" Mujaheed yace "Toh" daga
haka daddy ya katse wayar, inna tace "Kai xaka kwana a ciki wllh idan
yaron nan bai xo ba Bukar" Daddy dai bai ce komai ba, Mujaheed ba don
yanda yake jin kunyar daddy ba da fa ba xai je ba don yasan sarai inna na can,
kuma da Abbansa ne ma ya kirasa ba lallai yaje ba, jallabiyarsa kawai ya xura
ya fita dakinsa, banda girgixa kafa babu abinda inna take, da sallama ya shiga
parlon, ba tare da ya kalli Daddy ko ita ba ya tafi ya xauna kasan lallausan
carpet din parlon yace "Barka da dare Abba" Daddy yace "What
happened between you and ur grandma yanxu?" Mujaheed ya daga kai yana
kallonta yaga yanda ta wani tsuke fuska tana kallon sa, ya maida kansa kasa,
inna na nuna Imaan dake kwance kan kujera tana kallonsu tace "Idan sharri
na masa ga 'yar ka kwance kusa da kai ka tambayeta ka ji ko ba tsakiyar titi ya
juye mu ba" Daddy ya juya ya kalli Imaan, a fusace Inna tace "Ke
tashi xaune ki basa labarin abinda ya faru, ba tsakiyar titi Mujaheed ya sauke
mu ba, naga kamar tantama Bukar yake" Imaan ta mike xaune tace "A'a
ba fa tsakiyar titi bane inna, gefen hanya ne....." Rai bace Inna tace
"Amma wannan anyi shegiyar 'ya... Dama akwai bambanci tsakanin gefen titi
da tsakar titi, ke dai munafuka ce wllh" Imaan ta harareta ta gefen ido
tana turo baki ta koma ta kwanta, Inna tace "Wllh Bukar gefen hanya yayi
watsi damu, kuma kafin ya sauke ni don Allah mai yace min Imaan" da sauri
Imaan ta daga hannu tace "A'a ba ruwana nima ban sani ba" Bude baki
inna tayi tana kallonta, daddy yace "Yanxu dai ki tashi ki tafi ki bar ni
da shi inna" inna tace "In tashi in tafi ka basa hakuri shima ya tafi
xaka ce min" Tana fadin haka ta mike tace "Tun farko ma ban san me ya
kawo ni gun Bukar ba, duk inda Ubansa ya tafi ai ya ci ace ya dawo yanxu"
daga haka ta fice parlon fuska daure. Daddy ya hade rai yana kallon Mujaheed
yace "Saboda baka da kirki xaka ajiye su bakin hanya Muhammad?"
Mujaheed yyi kasa da kai bai ce komai ba, Daddy yace "Yanxu ka kyauta
kenan, idan Hajiyar ka ce ko min abinda tayi maka xaka mata haka?" Yace
"Kayi hakuri Abba" Daddy yace "Haba Muhammad, I am highly
disappointed at you, this is very rude and stupid of you, she is our mother fa,
no matter how she behaves baxa mu canxa ta ba" Mujaheed bai iya cewa komai
ba, daddy yace "Ka tashi ka bi ta ka bata hakuri yanxu" yace
"Toh, ayi hakuri Abba" Daddy ya kalli imaan yace "Ke kuma I've
warned you times without number ki daina fada mata magana anyhow amma baki ji
ko, xan fara sa6a maki soon wllh idan baxa ki canxa naughty attitude din nan
ba, will you dare talk to ur mother that
way?" mikewa xaune tayi kamar xata yi kuka, Mujaheed ya tashi yace
"Xan je in sameta yanxu Abba" daga haka ya fita parlon. Washegari da
safe da kyar imaan ta tashi tayi wanka tayi breakfast da Ammi ta ajiye mata a
dinning, Ammi tace "Idan kin gama ki dau magungunanki ki sha kada in tuna
maki, kuma da Ac kika kwana ko?" Ta xaro ido tace "Ammi wllh
A'a" Ammi tace "Toh ga mura nan na shirin kama ki" Ta langwabar
da kai tace "Jiya fa da daddare a napep muka dawo, kin ji sanyi kamar
xanyi freeze a hanya" Ammi ta fiddo
kindirmo a fridge yayi sanyi sosai ta ajiye mata a dinning din tace "Gashi
ki kai ma inna inji daddyn ki, you make sure kin goge min dinning table idan
yayi stain" Ta marairaice tace "Ammi my legs are aching me fa"
Ammi ta harareta ta wuce dakin ta, Imaan na gama breakfast ta tashi ta dau
kindirmon ta tafi kai ma inna, Tana shiga parlon bayan ta ajiye tana kallon
inna dake ta kukkula dubulan da cin cin a leda sai ga Umma ta shigo parlon da
sallama, Inna ta kalleta ta ci gaba da abinda take ta amsa sallaman ba yabo ba
fallasa, Umma ta dafa kujera tace "Ina kwana inna" inna tace
"Lafiya lau" Umma tace "Ya gajiyan taro" inna tace
"Bana tare da gajiya duk ya bi lafiyar gado" Umma tace "Toh
Alhmdllh Allah ya saka da alkhairi yaji k'an mahaifa" inna tace
"Ameen" karasawa tayi kusa da inna ta ajiye ledan hannunta tace
"Ga wannan dai ba yawa" inna na kallon ledan tace "Meye wannan
din? Ke imaan xo ki bude" imaan dake xaune ta mike ta karasa kusa da Inna,
Umma ta bi ta da kallon gefen ido, durkusawa tayi ta bude ledan ta ciro atamfa
da pack din sabulu guda biyu da turare mai tsada" Inna ta bude atamfar
tana kallo da kyau, tace "Holland ce wannan din?" Umma tace
"Ehh" inna ta tabe baki tace "Toh, da dai basirar ki ce hakan da
sai ince Allah yyi albarka, amma wannan ko kaffara baxan yi ba Ahmadu ya sa ki,
Allah ya masa albarka ya kare min shi duk inda xai shiga, Allah ya ci gaba da
hada kansu da d'an uwansa Bukar ya raya mai 'ya yansa yayi masu albarka, ita
kuma wannan da ya aurar Allah xaunar da ita da mijinta lfya, ke kuma nagode da
isar da sako" Umma ta dinga kallonta ko kiftawa babu, Imaan sai danne
dariyarta take, Inna ta ci gaba da kulla dubulan dinta a leda, Umma tace
"Sai anjima" inna tace "Mu jima da yawa" daga haka ta nufi
kofa, inna na kallon Imaan tace "To ke sai kiyi ta kanki, don wllh jiya
Mujaheed ce min yyi xai kakkarya ki ya xane ki, wai ya ganki da wani mai mota a
tsaye a kofar gidan seeyama, imaan ina kuma kika samo mai mota kike ta boye min
ban sani ba ni Asabe??" Umma ta d'an dakata bakin kofa jin abinda inna ke
cewa, Imaan ta turo baki tace "Shi sa ma xan tashi in tafi yanxu kar ya xo
nan, to har kun shirya ne inna?" Inna tace "Haba dai sai kace wata
yarinya, to me yyi min da baxa mu shirya ba, wai na ce ma Rukayya mahaukaciya,
ke ki ji fa? to me ta min xan xageta banda abunsa ma dai, kawai daga ina mata
gyara? Ni fa na yarje ma Ahmadu ya aureta wllh, baki ganta ba a lkcn yar
siririya yanda kika ganki, kamar iska xai hure 'yar banxa ta fadi, gashi
iyayenta basu da komai basu kuma ba wani ajiya ba, wani d'an akurkin gida fa
gare ubanta a lkcn, to ni ban masu bakin ciki ba don xuciya ta fess mai kyau ne
na yarda Ahmadu ya auro mana ita a haka, ke kinga wahalar da nayi da ita kuwa?
Wllh kare baxai ci ba, gashi ba abinda ta iya a lkcn, har girki ni ke sa ta kan
hanya ina koya mata, kishiyoyina su yi ta jin haushi yanda nake ji da ita bana
son ko k'uda ya ta6ata har dai ta samu cikin wannan yaro Mujaheed, sai kin ga
wahalar da nayi mata sbda laulayin da ta dinga yi ba kakkautawa, to ni duk ba
wannan ba don nasan sakayya ta dai na gun Allah, to don kuma yanxu Rukayya ta
xama abinda ta xama sai me xai dameni ni patuu? ga dai Amina na bina sau da
kafa ga Aisha, ni dai abinda na sani shine Mujaheed ai xai yi auren, to nan
xata d'an dana ko da dadi ko babu, abinda duk abinda ka shuka shi xa ka girba,
tsaf xan karance ma yarinyar xaman da xata yi da ita, muna nan da ku sai an
dinga xuwa daukata shari'a a mota...." Imaan har wani kwanciya tayi kan
kujera tana dariya amma ba mai sauti ba, Umma da ta makale jikin kofa ta fita
ta sa takalmanta, inna ta tabe baki tace "Wllh Mujaheed da gwiwowinsa
bibbiyu ya durkusa ya dinga ban hakuri tun ban kai ga gaya ma ubansa ba, to
tunda naga yyi nadama kawai sai na yafe masa don ba halinsa bane gaskiya bai
taba juye ni a tsakiyar titi ba tunda mu ke" Imaan ta fashe da dariya tace
"Jiya dai ya juye ki ai"
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of
coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788
to be included in the payment group.
19. Imaan
Umma na komawa bangarensu kallo daya tayi ma Mujaheed dake
xaune dinning yana shan coffee tace "Ka sameni daki yanxu" sosai
gabansa ya fadi ya bi ta da kallo har ta haura sama, bai iya ya karasa shanye
coffee din ba ya mike ya bi bayan ta, tsaye ya ganta tana safa da marwa a
dakin, Yace "Gani Umma" ta juya tana kallonsa fuska daure tace
"Mujaheed ina son sanin meye matsalar ka don kaga shegiyar yarinyar nan da
mai mota jiya har kake ikirarin hukuntata" ya xaro ido yace "Ban gane
ba Umma" Ta masa wani mugun kallo tace "Bana son ka gane dama ai,
warce kaje ka ba sakon take fadi yanxu naji, dama baka raba kanka da makiyan
nan nawa ba har ynxu Mujaheed? Mujaheed ka gaya min meye hadin ka da yarinyar
nan Imaan?" Yace "Haba Umma, ke yanxu maganar inna kike dauka, kila
ma don ta ganki yasa ta kirkiri haka, ni a ina na ganta har muka yi wannan
xancen da ita?" Shiru Umma tayi tana kallonsa, a ranta kuwa tunani take
kila hakan ne ma, ganin Umma tayi surrender, Mujaheed yace "Kawai ta fada
haka ne don ki sa a rai, ni yaushe nake da wannan lokacin ma a gidan nan
yanxu" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Sae ma kaga rashin mutuncin
da ta min kayan da na kai mata, ni na ma ji dadin da ta gane cewar in don ta
nine baxan bata ko tsinke na ba, basirar Abban ku ne kamar yanda ta fada"
Mujaheed yyi murmushi bai ce komai ba, Umma tace "Gobe xan baka sako ka
kai ma Hajiya Mansura ta marafa, bata samu xuwa bikin ba amma ta bada
gudunmawarta dubu dari, cin cin da su alkaki xaka kai mata daga nan nasan xa ku
hadu da Safeenah, tana nan ba ta koma makaranta ba, ni so nake nan da 'yan
watanni a fara xancen naka bikin" shi dai Mujaheed bai ce komai ba banda
kallonta da yake, ta xauna gefen gado tace "Kar fa kace min ka manta gobe
kayi ficewarka, xuwa sha biyu in sha Allah xaka kai masu, tunda gobe
lahadi" ya shafa kai yace "Allah ya kai mu" daga haka ya nufi
kofa ya fita. Imaan ta kara leka samirar dake cike da cin cin da dubulan da
alkaki da inna ta basu su kai ma ta rasulu aminiyarta, ta tabe baki tace
"Wllh duk kin kwashe ma tsohuwar, mu fa har ynxu ba mu ci ba" inna ta
tsuke fuska tace "To ina ruwana da rashin cin ku, ni na aurar da 'ya ko
ko? Kaji min dai, Dubu talatin ta rasulu ta bada a kawo min gudunmawa, kuma ace
baxan cika mata samira da kayan flawa ba, ni ta ma fi min Aisha kiji in gaya
maki" Imaan tace "Kice ma ta fi maki har daddy mana" Maimoon
tace "Toh ina dubu talatin din?" Inna ta kalleta da sauri tace
"Amina aka ce in ba wa da xaki tambayeni dubu talatin Maimuna? Ko ko kin
ban ajiya ne? Ni dai ku daina sa min ido a gidan nan, idan ba haka ba mugun
alkaba'i ba shi da kyau amma to xance kowa ya ci kansa gaskiya" Imaan ta
kalli Maimoon tace "Maimoon karbo kudin motar mu wuce" Inna ta kunce
ha6ar xaninta ta fiddo naira dari ta ajiye masu tace "Hamsin xai kai ku ya
dawo da ku, nan nan kabala dai" Imaan ta ajiye samirar ta xauna tace
"Tabdi ko naira dari dari ma baxa a yarda a kai mu ba balle hamsin"
Inna tace "Barawo ne mai adaidaitan da baxai kai ku a hamsin ba, ko ya sha
wiwi ne, wllh kullum a hamsin ake kai ni a dawo da ni" Maimoon tace
"Saboda ke tsohuwa ce ai" A fusace inna tace "Oh oh Allah, idan
baxa ku ba ku ajiye min kayana ku fita, Xan kira Bukar ko Ahmadu cikinsu wani
ya kai mun, ku fitar min a parlor" Kin fita suka yi jin abinda tace wai
xata kira daddy ko Abba, Maimoon tace "Toh wai don Allah mu muka siya masu
adaidaitan da xasu kai mu a hamsin su dawo da mu a haka, ki kara mana kudin mu
tafi mana" Inna ta jefa masu wani hamsin tace "Aniyar ku ta bi ku dai"
Maimoon ta dau kudin tana gunguni tace "Ae sai dai mu cika da kudin
mu" Imaan ta tabe baki ta dau samirar tace "Sai dai ke ki cika,
sisina baxan kara a kai ba tunda ba ni xan ci cin cin ba" daga haka ta
fice parlon, inna tace "Shi sa har yau aka kasa gano cutar da ta sa ki
gaba, saboda mugun xuciyar ki da rashin kunya, ni dai Allah ya saka ma d'ana,
Allah ya saka masa kan kudaden da yake kashewa a kan tsadadden ciwon nan naki,
Allah kuma ya raba shi dake lafiya, ya aurar dake ya huta ma ransa mijin ma ya
d'and'ana ukubar, ba a taba jin alkhairi ya fito bakin ki sai sharri, to meye
kuma don kin cika kudin mota" Maimoon ta bi bayan imaan ta kullo mata
kofarta tana turo baki. Suna tsaye bakin titi suna jiran adai daita da xai je
kabala, Imaan tace "Ko da yake nasan tsohuwar da xa mu kai ma baxa ta bar
mu haka nan ba, kila ta ba mu kudin mota" Maimoon tace "Wllh da ba
dan Abba da tace xata kira ya kai ba ba inda xanje ni dai, kullum fa idan xata
aiki mutum sai ta raba kudin motar xuwa wajen kashi uku ta baka daya"
Imaan tayi dariya tace "Kawai so take ayi ta mana fada shi sa tace xata
aiki daddy ko Abba" motar Mujaheed da suka gani yasa suka yi shiru suna
kallon motar, shi ma daga gida ya fito, ya sauke glass yana kallon Maimoon,
Maimoon ta marairaice tace "Ya M.A inna ce ta aike mu kabala kuma ba mu
samu adai daita ba har ynxu..." Ya gyada kai yace "Toh Allah ya kawo
adai daitan" xai dage glass da sauri tace "Wait... Kai ina xaka
plss?" Yace "Marafa" tace "Toh ka rage mana hanya mana don
Allah" ya mata wani kallo yace "Me ya hada Marafa da kabala?"
Tace "Yaya ai duk hanya ce mu dai ko ina ma ka ajiye mu nasan xa mu samu a
can gaba" yace "Toh shiga" Imaan ta bude back seat ta shiga ya
dinga hararanta ta madubi fuska daure, dama tun da suka hada ido taga kallon da
yake mata bata sake yarda ta kalli madubin ba, Maimoon na kallon fancy nylon
dake gaban motar ta dauka tace "Ya M.A wa xaka kai ma cin cin da
dubulan?" Yace "Anty" dariya tayi bata sake cewa komai ba, sai
da suka yi nisa yace "Gidan Baaba ta rasulu xa ki kenan?" Tace
"Xa mu dai, ai ba ni kadai bace, ni da Imaan ce" ya watsa mata wani
kallo ta xaro ido tana yar dariya ta rufe bakinta, har kofar gidan aminiyar
inna ya kai su, Maimoon sai murna take tace "Ya M.A mun gode, ko mu raka
ka marafan mu ma?" Shiru ya d'an yi da farko yana shafa kansa a hankali,
lkci daya yace "Toh kar ki dade a ciki idan ba haka ba inyi wucewata"
bude motar tayi ta fita tana kallon Imaan da ta fita tuntuni tana cinno baki
suka shiga gidan, dari biyar ta rasulu dake ta sa masu albarka ta basu kudin
mota, tace "Ina gaida Hajiya Asaben, kuyi mata godiya sosai, ita kuma
amarya Allah ya basu xaman lafiya da mijinta, ku kuma Allah ya maku albarka ya
fiddo maku maxaje na gari" suka amsa mata da Ameen, sannan suka mata
sallama suka fita da samirar don juye kayan ciki tayi a nata samiran. Maimoon
na kallon imaan tace "Wai Imaan me yasa baki gaida ya Mujaheed
yanxu?" Imaan tace "Saboda baya gaida Ammi na sai ya ga Daddy"
Maimoon ta xaro ido tace "Da gaske?" Imaan tace "Ehh mana"
Maimoon tace "Toh saboda me" imaan tace "Oho" bude back
seat tayi ta shiga Maimoon ta shiga gaba ya tada motar yayi reverse ya bar
anguwar. Tafiyar kusan minti sha biyar suka yi suka iso gidan Hajiyan Marafa,
Dai dai gidan yayi parking daga kusa da flowers yana kallon Maimoon yace
"Xan yi sllh kafin in shigo" ya mika mata ledan yace "You take
this in with you" tace "Amma yaya bamu san kowa a gidan ba fa"
yace "Sai ki ce Hajiya ce ta aiko ki, ina nan shigowa nace idan nayi
sllh" daga haka ya fita motar, Imaan dai na tsaye ta rungume hannu jikin
motar bayan ta fita, Maimoon ta fito ya kulle motarsa da lock, ya wuce
masallacin da ya gani a layin, Maimoon ta kalli Imaan tace "Mu je"
bin bayan ta Imaan tayi suka shiga gidan, bayan sun sanar da mai gadi gun
Hajiya suka xo, duk girman gidansu haka suka saki suke kallon gidan, Maimoon
tace "Ni dai baxan shiga ba gwara mu jira sa a nan, kawai mutum yaje yana
ta introduction ana masa wani kallo" Imaan ta yi dariya tace "Sai
kice Hajiya Rukayya ce ta aiko mu" Maimoon ta buda ido tace "Bari ya
Mujaheed ya jiki, wai Hajiya Rukayya" Imaan ta tabe baki suka shiga babban
balcony din dake dauke da kujeru sannan ga babban rug a shimfide kasa, kan rug
din suka xauna suna kara k'are ma gidan kallo, sai bayan da aka idar da sallah
Mujaheed ya shigo gidan, kallonsu ya tsaya yi ya hade rai yace "What did I
tell you Maimoon?" Ta marairaice tace "Yayanmu mun yi sallama kamar
basa parlor" hararanta ya dinga yi kafin ya danna bell, ko minti daya ba
ayi ba mai aiki ta bude kofar, ta gaishesa ya amsa yace "Hajiya tana
nan?" Tace "Wa xa ace mata" Yace "Dr Muhd, Kice Hajiya
Rukayya ce ta bada sako a kai mata" Murya can kasa Imaan tace "Toh ba
gashi shi ma cewa yayi Hajiya Rukayya ba" Maimoon ta yi murmushi bata dai ce
komai ba, Mai aikin tace "Toh ka shigo" bin bayan ta yayi xuwa cikin
parlon da sauri imaan ta mike ta bi bayansa, Maimoon na yar dariya ta tashi ita
ma ta shiga parlon, wata yarinya da baxata wuce ashirin da daya bace ta shigo
parlon daga dinning kallo daya tayi masu ta wuce sama, tsaki imaan ta ja
Mujaheed ya kalleta ta cinno baki ta dauke kai, mai aikin ta kawo masu drinks
da bottle water ta ajiye, bayan wani lkci sai ga Hajiyar ta sakko cikin shiga
ta alfarma ganin Mujaheed tace "A'a ashe kai ne doctor" yyi kasa da
kai yace "Ina yini Hajiya" tace "Lafiya Alhmdllh, ya Hajiya
Rukayyar, fatan an watse taro lafiya" yace "Alhmdllh" xaunawa
tayi tana kallo su Maimoon da Imaan dake gasiheta tace "Wannan kamar
kanwar khadijah da tayi aure Us koh?" Ta fadi haka tana nuna Maimoon,
Mujaheed yace "Ehh kanwarta ce" tace "Maa sha Allah ga kamanni
na gani, to ita wannan fa" Mujaheed ya kalli Imaan da ta nuna, da sauri
yace "Yar uwarsu ce" tace "Allah sarki shi sa ban santa ba"
Maimoon ta mike ta ajiye abun hannunta kusa da ita tace "Gashi Hajiya tace
a kawo maki" Hajiyar tace "To maa sha Allah, nagode kwarai Allah ya
basu xaman lafiya" Bude kofar parlon aka yi, wata yarinya ta shigo parlon
cikin English wear bata ko kalli wa enda ke xaune parlon ba xata wuce sama
Hajiya tace "Safeenah lafiya na ga ranki a bace" Jin sunan da Hajiyar
ta kira Mujaheed ya daga kai yana kallon yarinyar, ita ba doguwa ba kuma ba
gajera ba, farin ta har yayi yawa and she is beautiful, lkci daya ya dauke
kansa, Maimoon da Imaan kuwa kamar sun samu TV imaan har da juyawa gaba daya
tana facing dinta, rai bace Safeenar tace "Wai ki ji mum ashe birthday din
ma wani local waje xa ayi, sai kinga yanda raina ya bace bayan duk shirin da
nayi, wllh Saleema koluwa ce I don't know what's wrong with her, ni ko gaya
masu na tafi ma ban yi ba" Mujaheed dai sai danna wayarsa yake, Hajiya
tace "Atoh gaskiya basu kyauta ba, to why not baki ce masu a canxa hall
din ba, ko ke ba sai ki biya kudin hall din ba" Tsaki Safeenah tayi tace
"Ni duk raina ya baci wllh Mumy" xata wuce sama Hajiya tace "Toh
ga doctor ku gaisa" Juyowa tayi tana kallon cikin parlon taga Mujaheed da
ya ki dago kansa, ta fi second goma tana kallonsa, kafin ta karasa cikin parlon
ta xauna hannun armchair da uwarta ke xaune cikin sanyayyen murya tace
"Ina yini" sai a sannan ya daga kai yace "Lafiya lau, ya
kike?" Tayi wani sanyayyen murmushi tace "Lafiya lau" Ta kalli
su Imaan tace "Sannun ku" Imaan dai tace "Yauwa" Maimoon
kuma ta gaisheta, Hajiya ta kwalo ma mai aiki kira ta fito da sauri, Tana kallonta
tace "Pepper chicken da ku ka yi daxu xa ki kawo masu tun da ba ku gama
lunch ba" Mujaheed yace "Daga gida muke yanxu Hajiya, we ate before
leaving, so we are okay" tun da ya fara magana Safeenah ke kallonsa ko
kiftawa babu har ya dasa aya, Hajiya tace "Wannan ae is more or less a
dessert, daxu yara suka ce suna son pepper chicken, shine nasa su yi, kuma da
yawa sosai suka yi don nasan baxa a cinye gaba daya yau ba sai dai a ba masu
gadi da almajirai" Mujaheed ya d'an yi murmushi yace "Ni dai I am
okay" Imaan tace "Ni dai xan ci" kallonta yyi da sauri, Hajiya
tace "Yauwa, bar sa yayi ta fulako dama yayi kama da fulanawan, ke ma ai
xa ki ci ko" Hajiya ta fadi tana kallon Maimoon, Murmushi kawai Maimoon
tayi ta sunkuyar da kanta, mai aiki ta dawo rike da tray da plates uku a kai,
ko wanne dauke da kaxa da aka yi garnishing sai kamshi da turiri yake, Mikewa
Safeenah tayi ta dau plate daya ta karasa kusa da Mujaheed ta ajiye masa, hada
ido suka yi yace "I said I am okay baxan ci ba" tace "Kaci ko
kadan ne pls" Daga haka ta koma ta xauna, a hankali Imaan ta xamo kasa ta
fara cin kazar, sai kallonta Mujaheed yake ta gefen ido, Maimoon ta dau tsoka
daya daga kan kujerar tana ci a kunyace, Hajiya tace "To ya aikin doctor,
Hajiya Rukayya tace min ka dawo Kaduna da aiki gaba daya yanxu koh?" Yace
"Ehh" tace "To da kyau, Allah yayi albarka" yace
"Ameen" idonsa na kan wayarsa amma da ya dago sai yaga kallonsa
Safeenah take, Hajiya ta mike tace "Toh bari in d'an shiga ciki...."
Mikewa yyi da sauri yace "Wucewa xa mu yi ai, xan je gun aiki" tace
"Da wuri wuri haka, ka dai ki shan ko ruwa ne kuma ban ji ddi ba"
yace "Am sorry bana jin cin komai ne yanxu" Tace "Toh ai sai ka
jira kanninka su gama tukun na ko?" Yace "Bana son in makara xuwa gun
aiki ne Hajiya" tace "Toh shikenan, bari a masu take away da
shi" Imaan tace "Toh" wani kallo Mujaheed ya dinga mata, Hajiya
ta kwalo ma mai aiki kira ta sanar da ita tayi masu takeaway din kajin, Imaan
ta mike tace "Ina xan wanke hannu" Safeenah ta nuna mata hanyar
dinning ko kitchen, tare suka tafi da Maimoon suka wanke hannu suka dawo,
Hajiya ta basu dubu biyar Maimoon ta amsa da kyar, tuni Mujaheed ya fice gidan
suka bi bayansa, Hajiya ta kalli Safeenah tace "Baxa ki raka su ba"
bin bayan su tayi ita ma. Mujaheed har ya shiga mota sai ga ta tare da su
Maimoon, tana kallonsa tace "I don't even know ur name" ba tare da ya
kalleta ba yace "I am Mujaheed" tace "That's nyc, I am
Safeenah" kai kawai ya gyada mata, Tace "Toh sai yaushe?" Yace
"Watarana" yar siririyar dariya tayi tace "Do you mind sharing
your digit with me pls?" Yace "Ohk" mika masa wayar hannunta
tayi ya amsa ya sa mata lambarsa da bai fiye amfani da ba ya mika mata, tace
"Thank you" yace "You are welcm" Daga haka ya tada motarsa
ya wuce, haka ta bi motar da kallo har ya fita layin, da sauri ta koma ciki
tana kallon uwarta tace "Wllh Mum naji ina son sa sosai" Uwar tace
"Haba, to ai shine wanda na maki magana a kai kwanaki kika ce ke ba ruwan
ki da hade hade in rabu da ke, uwarsa ce dama ta kawo shawarar ba ni ba tunda
nasan kina da samari iri iri" ta marairace tace "Mum ai ban san haka
yake ba, ni wllh mum ina son sa har raina" Hajiya tace "To ai
shikenan, bari anjima sai in kira mahaifiyar tasa dama kwanaki duk ta dameni da
kira a kan hakan bana daukan kiranta" Safeenah ta sauke ajiyar xuciya ta
xauna tace "kaiii... Ya hadu wllh, his beards are damn cute, his lips so
sexy with those catlike eye, gashi dogooo, I guess he have got six packs daga
ganinsa yana workout, dama kuma ni bana son namiji fari pau, wllh Mum gayen ya
hadu sosai, kuma naga sai wani basarwa yake yana shan kamshi, to ai irinsu nake
so" Tun da Imaan taga irin kallon da Mujaheed ke mata bayan sun dau hanya
ta kagu su isa gida ta fice daga motarsa tayi ta kanta, gashi dama so take suna
komawa gida ta dau Atm card ta tafi supermarket siyo ma Sadeeq abinda ta masa
alkawari jiya, a kofar gida Mujaheed
yayi parking tana jin ya bude lock din motar ta bude ta fita da sauri, fitowa
yayi shi ma bai kai ga bin ta ba tayi tuntunbe bakin gate sai ga ta a kasa,
d'agata yyi ta fashe da wani matsanancin kuka tana cewa "Wayyo yaya kafana
ya gurde wllh" maidata gun motar yayi fuska daure ya daga kanta yace
"Waye kika fita wajensa shekaranjiya da daddare" k'in cewa komai tayi
sai kukan da take tana kiran daddy a tsorace, ya wani hade rai cikin tsawa yace
"Ba tambayar ki nake ba?" Still taki cewa komai xuciyar ta Sai bugawa
yake, murda kunnenta yyi da karfi yace "Are you daft" ta kara rushewa
da kuka tace "Don Allah kayi hakuri" yace "Waye shi" cikin
kuka tace "Nima ban san shi ba yaya" Ji yake kamar ya sauke mata mari
ya dinga mata wani kallo xuciyarsa na tafarfasa, he is just trying hard to
control his temper, strictly yace "Toh daga yau Imaan, I mean daga yau....
na sake ganin ki da wani a tsaye wllh sai na kusa sumar dake a gidan nan I
promise you that, ba ciwon jiki ko Asthma ba, idan ma jini ke xuba ko ina na
jikin ki wllh sai nayi abinda na maki alkawari, ke har guda nawa kike xaki ke
tsayawa da namiji jikin mota? How old are you??" Kuka kawai take tana
kallonsa duk jikinta na rawa don ta dade bata gansa cikin yanayin nan ba, ya
mata tsawa yace "Baxa ki bani amsa ba sai na gaura maki mari?" Cikin
rawar murya tace "Ba na kusa 18 ba...." Rankwashi ya kai mata ta dafa
wajen tana kiran inna a rikice, yace "In sake ganin ki da wani a waje, sai
kin raina kanki wllh" daga haka ya saketa ya rufe motarsa, ta wuce ciki da
sauri bata xame ko ina ba sai part din inna, xubewa tayi kan kujera tana rusa
kuka, Inna ta fito daki da gudu tace "Na shiga uku me ya same ku a hanya,
ko hatsari ku ka yi??" Imaan ta mike xaune cikin kuka tace "Yaya ne
ya rankwashe ni kuma ya ja min kunne ni ban masa komai ba innaa" Inna ta
xauna kan kujera tayi tagumi a hankali tace "Naga abinda ya isheni bai
ishi Allah ba, Wannan yaro dai ya isheni a gidan nan wllh, innalillahi wa inna
ilaihi raji'un, A kan wani dalilin kuma ya cuce ki, me kika masa?" Xata yi
magana sai ga shi ya shigo, kin cewa komai tayi sai shessheka take hawaye na
bin kuncinta, inna tayi mitsi mitsi da ido tace "Mujaheed kana manta cewar
akwai hisabi koh, kana mance akwai lahira koh, ni ina jiye maka kada wataran ka
karasa gawar da ba taka ba a gidan nan, idan abu ya sami yarinyar nan gaskiya
xan rufe ido in mance ni na haifi Ahmadu in maka tijara kotu ta raba mu
Mujaheed," Yace "Toh yanxu ma ki tashi a tafi kotun mana, duk ke ke
karanta mata tsayawa da samari tun bata kai ko ina ba a titi, idan aure take so
ae sai ta sanar da Abbanta ayi mata ba ta dinga tsayuwa da maxaje ba tare da
saninsa ba, ita har nawa take, ni nasan wlh Abbanta bai sani ba, halan Ummi
bata bata labarin abinda na mata kwanaki ba" Inna ta saki baki tana kallon
imaan dake shessheka a hankali, can tace "Amma gaskiya ke munafuka ce
Imaan, samm baki da hali, banda munafurci ya xa ayi kiyi sabon saurayi amma
kiyi ta nuku nuku kina boye min?? me xai bani da Allah bai ban ba, shi kuma
gantalallen bai san kakarki na da rai bane da bai taba cewa xai shigo gaisheni
ba? Ko uwar ki ce tace ki boye min ban sani ba" Mujaheed ya dinga kallonta
da mamaki, rai bace inna tace "Toh ni dai ba ruwana, dama ana boye abun
arxiki irin wannan Ashe, me na maki da xaki boye min sabon saurayin ki
Imaan?"
20. Imaan
Juyawa Mujaheed yyi ya fice daga parlon, Imaan ta kyabe baki
tana share idonta tace "Shi fa bai san ko waye doba xai wani dinga ce wa
saurayina, ni dai wllh inna ku ce masa ba ruwansa da ni a gidan nan" inna
tace "Atoh dama meye hadin ki da shi, kawai ni dai nasan ubansa wan ubanki
ne kuma duk ni na haifesu, to bayan wannan bbu abinda ya hada ki da Mujaheed ba
dangin iya balle na baba, ke dai kawai ki rabu da shi ya ji da wawancin sa kiyi
ta kan ki, banda fitina ma ina ruwansa da lamarin rayuwarki, idan ma saurayin
kika yi baki isa ba ne, ko idan kin rasa mijin aure astaghfirullah shi xai aure
ki ne?? kar ki sake saurarensa duk saurayi ya kira ki shirya ki fesa turare ki
tafi, wa xai xauna biye ta Ahmadu da Bukar ga d'an su ma ya dauko hanya, bokon
jaraba kawai ni wllh kina gama sakandari aurar da ke xance ayi mijin yaji da
lalurorin ki d'a na ya huta haka shi ma" imaan ta mata wani kallo ta mike
tana goge guntun hawayenta ta fice a parlon. Da yammacin ranan daddy ya gama
shirin komawa Abuja ya tafi yi ma Inna sallama, ta gama goge gogen da ta ke ta
dawo ta xauna tace "Tafiyar na nan yau din kenan" yace "Ehh,
jirgi xan bi kada jirgin ya tashi ba ni" inna tace "Toh Allah ya
tsare, amma xaka tafi kuma ya xancen da ku ka min kai da Ahmadu jiya?"
Daddy yace "Na me fa?" Inna tace "Tafiyar yaran nan su je gaida
Hansatu mana" Daddy yace "Ehh Barrister yace xuwa satin da xa a shiga
sai su tafi" inna tace "Ehh gwara su je, duk da dai uwarta axxaluma
ce amma ina mata fatan Allah ya ji kanta na kuma yafe mata, amma gaskiya
shari'ar mu sai a lahira, don ta cutar da ni...." Daddy yace "Haba
inna, bayan kuma kin ce kin yafe" a fusace inna tace "Toh ai Allah ba
axxalumin bawansa bane, don na yafe ai a duniya nake nufi ba a can ba, kai baka
san komai ba wllh, kaga irin abinda uwarta tayi min ne, kishi dama hauka ne, ni
dai kawai albarkacin marigayin uban ku yasa nake barin ayi xumunci da 'ya yan
da ta mutu ta bari ma, kuma duk yaran ba xuwa gaida ni suke ba" Daddy yace
"Ke fa kika ce kin yafe xuwan, kowa ya xauna inda yake" Inna tace
"Toh idan bance haka ba ya kake so ince, kai so kake su xo su sa ma kai da
d'an uwanka ido, yanxu da ake nisa nisa ba ya fi ba, babu wanda yasan halin da
wani ke ciki, sai ku dinga wata magana kai da Ahmadu don ba ku aka cuta ba,
yanxu kishiyoyin da bani da hakkinsu ba gashi duk sun mace sun bar 'ya ya duk a
gantale ba, to me xa su xo su min bayan ga nawa 'ya yan... Ku uku wllh kun
isheni xaman duniya ita ma Hadiza tace ta kusa dawowa kasar nan gaba daya, to
me xai dameni, a hada masu goma ta arxiki aje dai a gaishesu, har shi wancan
katon Balan dake Abuja su karasa su gaida shi, ba komai Allah ya ba mu lada su
kuma aniyarsu ta bi su" Daddy yace "Bari in je inna, Mujaheed xai
kawo maki sako anjima" tace "Toh Allah ya tsare, yayi maka albarka,
ya kare ka duk inda xaka shiga" yace "Toh Ameen nagode" daga
haka ya fita parlon, part dinsa ya tafi suka yi sallama da Ammi yace "Gobe
dai Imaan ta tafi islamiyya, xuwa Wednesday nasan xa su yi tafiyar, before than
Dr dinta xai kawo mata drugs dinta coz ya dawo" Ammi tace "Toh Allah
ya kiyaye hanya ya tsare, ko in taso ta?" Yace "A'a bar ta" daga
haka ya nufi kofa ya fita, Yusuf ne ya kai sa airport. Mujaheed ya daga kai
yana kallon Abbansa bayan ya gama maganar da yake, a hankali yace "Abba
kaga ba a dde da transferring dina nan ba da har xan fara daukan leave gun
aiki...." Abba yace "You are just lookin for excuses, na lura gaba
daya baka son tafiyar Muhd" ya sunkuyar da kai yace "A'a ba haka bane
Abba, kawai naga...." Abba ya dakatar da shi yace "Toh xan ma boss din
naka magana" da sauri ya dago yana kallon Abba amma bai ce komai ba, Abba
yace "Beside idan ku ka tafi Wednesday xuwa Friday ai kun dawo, nan nan
sulejah dai" Mujaheed bai ce komai ba still, jin Abba ma yyi shiru yace
"Toh Abba kasan yanayin jikin Imaan, har da ita xa mu je?" Abba yace
"Toh ba ga ka ba, you just go with first aid box" Mujaheed yace
"Toh shikenan" Abba yace "And ina son dama muyi wata magana
Mujaheed" Mujaheed yace "Ina ji Abba" Abba yace "Its high
time you think of settling down with a family Muhd, naga baka san shiru ba kai,
idan na kyale ka a haka xa ayi ta tafiya, duk abokanka sun yi aure with kids,
not even kid, to kai me kake jira son?" Ya shafa kai a hankali yace
"Abba warce nake nema tana karatu ne, amma ta kusa karewa nan da 'yan
watanni in sha Allah" Abba yace "Yar ina ce?" Ya d'an yi
murmushi yace "Nan Kaduna, a hayi iyayenta suke amma tana gun yayarta a
Unguwar sanusi" Abba yace "Toh maa sha Allah, hakan yayi kyau sosai,
but I think it's better a fara magana tun yanxu...." Muryar Umma suka ji
tace "Babu maganar da xa a fara Alhaji" duk suka daga kai suna
kallonta ta karaso cikin parlon, bacin rai karara fuskarta tace "Yanxu ni
xaka munafurta Mujaheed, haka muka yi da kai, to kasani wllh idan ina numfashi
a doron kasa baxa ka auri yarinyar nan bar, idan kuma kana son ganin ba dai dai
ba a lamarin ka kaci gaba da alaka da matsiyaciyar yarinyar, ina zamana ka
dauko mun talauci a matsayin surka, to wllh kayi kadan gwara kayi ta xama ba
auren ya fi, ga yarinya mai hankali mai natsuwa Safeenah yar wajen Hajiyan
Marafa can na nema maka yarinyar kuma tayi mugun na'am da kai xaka toxarta ni
ka maidani karamar mutum a idonsu???" Abba yace "Abinda nake son in
fara fahimta a nan shine, la6e kike min Rukayya?" Umma ta tabe baki tace
"Idan ma la6en nayi Allah ne yasan bani da hakkin kowa shi sa har ya bani
ikon labewan in ji komai, Alhaji wato idan Kasan talauci to a kan yarinyar da
iyayenta ya kare, can wani ghetto fa suke, to idan ba toxarta mu Mujaheed ke
son yi a idon jama'a ba ina shi ina yarinyar nan, Kyan banxa kyan hofi, yo ina
ma take da kyan ita ba wai fara ba, gaskiya kayi min iyaka da Mujaheed kada in
nuna masa 6acin raina a gidan nan, sam baxai ji da dadi ba, shi baya koyi da
d'an uwansa Yusuf, dubi fa yarinyar da yake nema yar attajiri gashi har magana
yayi nisa, sai ni ce Mujaheed xai cuta ya kwaso min yar talakawa" Abba ya
girgixa kai yace "Halan ke ke raba talauci da arxikin Rukayya?" Umma
tace "Ba ruwana da wannan xancen ni dai gaskiya idan Mujaheed bai yi hankali
da ni ba xai sha mamaki, kuma in dai baxai bi ni sau da kafa ba xai dinga ganin
ba dai dai ba a lamarin sa ni dai ba ruwana" tana kai wa nan ta fice fuuu,
Abba ya girgixa kai yace "Look son, ba ruwanka da wannan uwar taka, ba
isasshen hankali gareta ba am giving u my words, ka ci gaba da neman yarinyar,
Allah ya shige mana gaba" A hankali Mujaheed yace "Ameen" Abba
yace "You can go" ya mike yace "Nagode Abba" daga haka ya
fita parlon. A hankali Ammi ta bude kofar dakin Imaan tana kallon ciki jin
dariyar da take cikin duvet, da sauri Imaan ta katse wayar ta tura karkashin
pillow jin kamar an bude kofa, Ammi ta kunna wutan dakin tace "Da wa kike
waya Imaan?" Bude duvet din tayi kamar mai bacci ta mike xaune tace
"Na'am" Ammi ta mata wani kallo tace "Baxa ki amsa min tambayata
ba, da wa kike waya nace?" Shiru tayi tana kallon Ammi kamar xata yi kuka,
Ammi ta karasa kusa da gadon tace "Bani wayar" ba musu ta ciro wayar
ta mika ma Ammi, Ammi na kallon call log tace "Number waye wannan
din" murya can kasa Imaan tace "Abokin ya Muhsin ne" Ammi tace
"Me ya hada ki da abokin Muhsin, a ina kika san sa?" Tace "Ammi
yana xuwa gidan gwaggwo kuma kanwarsa classmate dita ce, yanxu ma kawai tambaya
ya kira ni yake min ba wani abu ba" Ammi ta dinga mata wani kallo, ta
sunkuyar da kai, Ammi tace "Ke dai kin iya munafurci" kamar xata yi
kuka tace "Ammi ni wllh dai ya kira ni ne amma ba komai fa" Ammi tace
"Toh yayi kyau, ki bude kunne sosai ki saurareni, kada ma ki nuna nasan
kina waya da wani a gidan nan don ba ruwana, duk ranan da Daddyn ki ya kama ki
dama ki tanadi abun gaya masa don't involve me in this" tana kai wa nan ta
fice dakin. Washegari da rana Ammi na xaune parlor Imaan ta fito sanye da Hijab
sai karamar jakarta da ta rataye, Ammi na kallonta tace "Ina xa ki?"
A hankali tace "Ammi xan je in siyo cream a supermarket" Ammi na
kallonta da mamaki tace "Yaushe na siyo maki da har ya kare Imaan?"
Shiru tayi tana kallon Ammi kamar munafuka, Ammi tace "Shan cream din kika
fara?" Tace "Ammi shafawa kawai nake yi fa" Ammi ta tabe baki
tace "Toh ni kam bani da kudin cream yanxu" tace "Ai ina da kudi
a account dina" Ammi tace "Toh Hajiya mai kudi, a dawo lafiya"
yar dariya tayi ta sa flat shoe dinta ta fita parlon, kamar mai tausayin kasa
ta taka har bakin main road inda xata samu adai daita, jin wayarta na vibrate a
jaka ta fiddo, Sadeeq ta ga ke kiranta, ta daga ta kai kunne, Cikin cool voice
dinsa yace "How r you Imaan?" A hankali tace "am fine ina
yini?" Yace "Lafiya lau, kina hanya ne?" Tace "Ehh"
yace "Ina xa ki?" Ta d'an yi shiru kafin tace "Xanje
supermarket" yace "Wanda muka hadu ranan?" Tace "Ehh"
yace "Tell me what you want to get sai in siyo in kawo maki yanxu" da
sauri tace "A'a bana so" a hankali yace "Why?" Tace
"Ni dai bana so, yanxu ma xan hau adai daita ai" yace "Toh
shikenan, we will talk later, Allah ya tsare" tace "Ameen
thanks" daga haka ya katse wayar ta samu adai daita ya kai ta har mall
din, wani babban boutique dake opposite mall din ta shiga, gun eyeglasses ta
tsaya tana duba glasses masu kyau shigen irin wanda yake sa wa, ta wara ido
ganin the prices are waoww, wani da ya mata kyau sosai ta dauka tana dubawa
kafin ta tafi gun da ake biyan kudin kayan ta basu atm suka cire kudinsu suka
mata packaging din eye glass din ta fita ta tsallaka ta shiga cikin mall din,
gun body creams ta tafi ta dau cream da take shafawa duk da akwai mai yawa a
gida, kawai dai ta juye a wani container ta boye ne sanin Ammi na iya shiga
daki ta duba bayan ta taho, bayan ta dau cream din xata juya ta kusa cin karo
da mutum, komawa baya tayi da sauri da nufin basa hakuri, sai kuma ta xaro ido
da mugun mamaki tana kallonsa, murmushin da ya bayyana dimples dinsa yyi yace
"Sorry" ta sunkuyar da kanta yace "Har kin gama shopping din ko
yanxu kika fara" ta dauke kai tace "Na gama" yace "Toh mu
je ki rakani I want to get somethings" Daga haka ya fara tafiya, bin
bayansa tayi kamar munafuka, gun kayan ciye ciye su chocolates, biscuits sweets
da dai sauransu ya tafi, yana kallonta yace "Kanwata xata yi birthday
gobe, so nasan dai ku mata babu abinda ku ke so da ya wuce wannan, am asking
for a favor duk abinda kika san kina so ki daukar mata nasan ita ma xata
so" Murmushi tayi tace "Ohk then" nan ta dinga jidan duk abinda
ya kwanta mata take mugun so kuma, ya dinga tura trolley din yana biye da ita,
xaro ido yyi yace "Anya imaan wannan banda mugunta kuwa, yanxu duk wannan
abubuwan da kike dauka kina nufin kina son su?" Ta juya ta wara masa
manyan idonta tace "Ai duk abinda kaga na dauka a nan I love it with all
my heart, baka san yanda nake son chocolates da sweets ba koh" murmushi
yyi yace "Toh mu bar mata su a haka" tace "A'a jira ga wani
chocolate can..." Da sauri ta tafi ta debo har biyar ta xuba a trolley, ta
kwaso wasu biscuits ma ta xuba, ta dau wani sweet ta xuba shi ma, ta juya tana
kallonsa tana murmushi tace "Toh ni dai ina mugun son teddy in daukar
mata" ya langwabar da kai yace "Kawai so kike account dina yayi kuka
yau koh??" Ta hade rai tace "Just guda biyu ko uku fa, Is she not ur
sister? And is it not her birthday" daga haka ta tafi gun teddies ta debo
uku masu tsada da kyau ta jefa cikin trolley din tace "Tunda kana
complaining account dinka, mu bar mata su a haka kawai" Yar dariya yyi
yace "Noo ci gaba har sai kin gaji" tace "A'a I have
conscience" dariya yyi ya bi bayanta ganin ta nufi gun counter, cream
dinta ta ajiye xata bada ATM card ya riga ta mika nasa, juyawa tayi tana
kallonsa sosai gabanta ya fadi bayan sun hada ido tayi saurin sunkuyar da
kanta, nan aka cire kudin aka bata receipt dinta, ta taya sa ciro abubuwan
cikin trolley din shima ya bada atm card aka cire aka masu packaging, barinsa
tayi da kayan gaba daya ta dau teddies din suka fita. Bayan ya xuba ledojin a
bayan mota ya rufe motar yana kallonta kafin yace komai tace "Yau ne
birthday din?" Gyada mata kai yyi smiling, ta boye fuskarta a hankali tace
"Toh ni dai ina son kaza ko xaka siya mata" Wara ido yyi yana
kallonta, sai kuma yyi dariya yace "Ina kika ga kaxa imaan?" Ta turo
baki ta nuna masa inda ake gashin kaji, yana murmushi ya tafi, ya siyo kajin
gasassu biyu ya dawo ya sa a mota, ya juya yana kallonta pleadingly yace
"Let me drop you plss" da sauri tace "Nooo thank you" tana
fadin haka ta bude karamar jakarta ta fiddo glass din dake leda tana kallonsa
ta mika masa, a hankali ya sa hannu ya amsa yana kallon kwayar idonta, hakan yasa
tayi saurin sauke nata idon, bude ledan yyi ganin glass din underneath his
breathe yace "Waow..." Murmushi tayi xata juya masa baya ya riko
hannunta cikin sanyin murya yace "Thanks Imaan, I love it..." Bata
ankara ba sai gani tayi yyi pecking hannunta, ta kwace hannun da sauri tana
xaro ido a tsorace, shi ma daburcewa yyi yace "I... Sorry I.. I am just
happy imaan, I love the glasses" ta kirkiri murmushi har sannan tana jin
warm lips dinsa a hannunta, xata juya yace "Wait Imaan" tsayawa tayi
gabanta na faduwa, ya bude front seat yace "Plss let me drop you
home" kasa ci gaba da kallonsa tayi ta kuma kasa cewa A'a, a hankali ta
shiga motar yyi murmushi ya rufe, ya xaga ya shiga driver seat suka bar mall
din, bata yrda yaje dai dai gate din su ba tasa ya ajiye ta few houses away
from theirs, ta bude motar ta sauka shi ma ya sauka ya xaga ya bude back seat,
ya fiddo gaba daya ledojin siyayyar da suka yi da teddies da kajin duk ya ajiye
kusa da ita ya wara ido yana mata murmushi yace "Dama duk naki ne"
bai jira cewarta ba ya xaga ya shiga driver seat ya tada motar ya bar ta da
zare ido ya bar layin, kallon ledojin ta dinga yi kamar xata yi kuka, yanxu ya
xata yi da kayan nan.... Kwasa tayi ta boyesu cikin flowers ta dinga dauka da
daddaya da daddaya tana kai su part din inna, duk a mugun tsorace take, Inna ta
saki baki tana kallon kayan, imaan ta tafi dauko last ledan, Yusuf dake ta
kallonta tun shigowarta na farko ya mike ya isa kusa da ita da mamaki yace
"Daga ina kike wannan saurin hakan Imaan, what's all this u are taking
in" kin tsayawa tayi tana kirkiran murmushi ta wuce sa da sauri, tsoronta
daya kar ta gamu da Mujaheed, har dai ta isa parlon inna, Inna dake tsaye bakin
kofa har lkcn ta sake baki tana kallon uban ledojin ta bi ta da kallo har ta ajiye
na hannunta, Inna tayi kasa da murya tace "Imaan ina kika samo wannan
kuma?" Imaan ta kwashesu gaba daya ta kai dakinta da sauri duk ta ajiyesu
sanin Yusuf xai iya biyota, Tana fitowa dakin tace "Ni dai kawai kiyi
shiru inna kar ya Mujaheed ya sani wllh duka xai min" Inna ta hade rai
tace "Duka?? da kuwa ya dokar ma kansa fitina da bala'i, kuma da karshen
xamansa ya kama a gidan nan" Imaan ta xauna saman kujera har sannan
gabanta bai daina faduwa ba, Yusuf ne ya shigo parlon, inna ta wani tsuke
fuska, yana kallon Imaan yace "Daga inna kike Imaan?" Inna tace
"Yau naga jaraba, to ina ruwanka isuhu ko ka aiketa ne? Ku dai 'ya yan
Ahmadu ku daina sa ido wllh, meye kuma wani daga ina take kamar xamanka take a
gidan, ni dai ba ruwana, ku dinga tsoron Allah kuyi mai fishshe ku a gidan
nan" juyawa Yusuf yyi ya fita parlon, inna ta kulle kofarta ta sa makulli,
ta kalli imaan tana murmushi tace "Kar dai sabon saurayin ne yyi maki uban
siyayyar nan takwara" Imaan tace "Wllh kar ki gaya ma kowa idan ba
haka ba kazar ma baxan tsam maki ba" Inna tace "Ke ma dai da wata
magana wllh, sai kace wata yarinya?? Wa xan gaya ma ni patuu, wannan ai sirri
ne tsakaninmu" Imaan ta shiga ta fiddo ledan kajin guda biyu tace
"Toh idan yaya ya shigo fa?" Inna tace "Oh oh Allah, waye kuma
wani yaya, ina ruwana da shi, ko me xai xo ya min? Ko ya xo ma ni baxan bude
kofata ba bbu ruwana, idan ma ya xo damuna yake ba abinda yake tsinana
min"
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of
coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit
07087865788 to be included in the payment group.
21.....
Ammi ta bi Imaan da kallo ganin xata shiga daki tace
"Kee" juyowa tayi tana kallon uwarta ta, Ammi tace "Ajiye min
plate din kika yi kika fito?" Imaan tace "Ammi na wanke wllh"
Ammi tace "Toh ki tafi ki sha maganinki ki daina min wannan yatsine
yatsinen da kike yi" a hankali tace "Na sha Ammi, kai na ke min ciwo
da bayana" Ammi tace "Allah ya sauwake" Har Imaan zata shiga daki
sai kuma ta fasa ta dawo ta xauna kusa da Ammi murya can kasa tace "Ammi
don Allah idan na gaya maki abu baxa ki min fada ba?" Ammi na kallonta
tace "Idan ya kama in maki fada ae dole in maki" Shiru tayi tana
kallon Ammi, Ammi tace "Ina jin ki" Sauke idonta kasa ta yi tace
"Dama..." Sai kuma tayi shiru, Ammi tace "Dama me?" Murya
can kasa tace "Wannan mutumin da kika ji ina waya da shi da daddare shine
da naje shopping mall daxu muka hadu" Marairaicewa tayi tace "Ammi
wllh ban san ma ni ya siya ma ba" Ammi tace "Me ya siya maki?"
Ta ja baya kadan tace "Chocolates, da abubuwan ci...." Ammi ta dinga
kallonta, kafin tace "Ina suke?" Imaan na kara matsawa daga kusa da
ita tace "Na kai part din inna, ina tsoron kar ki min fada" Ammi tace
"Ni xa ki ma karya baki san xai siya maki ba koh??" Kamar xata yi
kuka tace "Wllh Ammi ban sani ba, we just met at the supermarket"
Ammi tace "Toh shi yaron a ina kika san sa?" Tace "Ai na ce maki
abokin ya Muhsin ne kuma Yayan Classmate dita Mariya ce, a gidan gwaggwo muka
hadu" Ammi tace "Toh yyi kyau, you had better be careful Imaan, kin
san Abbanki won't take it likely with you if he should find out, ni dai kar ki
ja min matsala bbu ruwana, banda shashanci ya maki yawa you ought to have known
ur left from right now" shiru Imaan tayi bata ce komai ba, can ta mike a
hankali ta wuce dakinta. Mujaheed na zaune parlon inna bayan ya dawo aiki ran
Tuesday ita ko tana can tana shara, Imaan na kwance tana bacci kan 3 seater,
tun da ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba, bayan wani lkci inna ta shigo
parlon, kakkabe kujeru ta dinga yi tana cewa "Ni dai gaskiya wannan
yarinya ta Bukar tana takurani duk ta kare min kujerun sun lotse, sai dai naji
kunya idan nayi manyan baki, yarinya dai kamar kyanwa kwanciya baya karewa,
gashi yau laluran ciwon kafar ya tashi bata je islamiyyan ba ma, Allah ka dubi
jikata ka yaye mata wannan bala'in da ba a san kansa ba, ni bari ma kwanan nan
xan shirya inje in samu ta Rasulu in ji yanda xa ayi, sai dai duk abinda Ahmadu
da Bukar xa su ce su ce, ai dai ba gun boka xa mu je ba" ganin ruwan kumfa
inna ke kokarin kadawa Mujaheed yace "Ni dai magana na xo mu yi, ki bar
wannan aikin naki da baya karewa ki saurareni" ta kallesa ce "Toh
idan aiki ya kare ae kazanta ta tabbata kenan, ni ko ina xan yarda in daina
aiki in mutu cikin dauda, ko kai baka ji dadi da kamshi da ka shigo parlon
ba" yace "Abba nake son ki yi ma magana inna, wllh bana son tafiyar
nan, ruwan garin ma ba iya sha nake ba balle abinci, kwanaki da muka je da ku
har muka dawo ni ban ci abun kirki ba fa" Inna ta saki baki tana kallonsa,
can tace "Toh yanxu ya kake son ayi?" Tace "Kawai ce ma Abba za
ki yi xa ki aikeni kano in kai maki wani sako sai Yusuf ya kai su gaskiya"
inna tace "Tohhh, yanxu kiransa xan yi kenan?" Yace "Ehh ki
kirasa, sae kice masa ya min magana don kinsan in kece kika min ba xuwa maki
aiken xan yi ba" Inna ta mike ta dauko wayarta tace "Toh kirasa"
Dialing number Abba yyi ya sa a speak on ya mika mata, imaan sai tsaki take
tana turo baki ita a dole an hanata bacci, sai dai ba wanda ya tanka ta, Abba
na d'aga kiran inna tace "Yaro??" Abba yace "Ina yini" Tace
"Toh lafiya lau, sae dai wuni nayi ina aiki wllh har bayan window na duk
na share, na goge gilashin windon" Yace "Alhmdllh, fatan dai lafiya?"
Ta gyara xama tace "Ina fa lafiya, wato kai dai ka haifa ma kanka fitina
da abinda ya fi karfin ka ne baka sani ba har yanxu Ahmadu, wai dama don Allah ina ne asalin ko wani mutum
dai bahaushe?" Abba yace "Ban gane ba inna" a d'an fusace tace
"oh oh Allah, Asalin kowa nake tambayarka, ina ne asalina da na
Ubanka?" yace "Asalin kowa kauye inna" Inna tace "Toh
Alhmdllh, yanxu wannan mutumi Mujaheed ya xo ya sameni, ko gaisuwar kirki ba mu
yi ba, ya fara bani sako in baka, wato cewa yyi ince maka shi baxai je kauye ba
gaskiya, don kwanaki ma da mu ka je a gantale ya dawo ba abinci, har yana koya
min karyar da xan maka na cewa xan aikesa kano ko uban wa gareni kano oho, wai
sai Yusuf ya kai su kauyen, bai san ni yar gaskiya bace, ba a cin amana da ni,
yanxu fisabillahi Ahmadu in ji kaga abinda yasa tun suna yara nake cewa ka
dinga kai su can koh?" Mikewa Mujahedin da ya bude baki yyi yana kallonta,
imaan ta sauko kasa ta dinga 6a66aka dariya, Abba yace "Toh yayi kyau ki
kyalesa kawai, sae su tafi da Yusuf din" inna tace "Atoh, ni dai ba
ruwana, ka tashi tsaye da rokan Allah kan Mujaheed" daga haka ta katse
wayar ta tayi kasa da murya tana kallon Mujaheed tace "In dai ranka bai
kwanta xuwa kauyen ba kada kaje gaskiya, duk bambamin da Ahmadu xai yi xuba
masa na mujiya, haka kawai kaje ka cutu, don gaskiya ko ni bana cin abincin
gidan hansai, to idan na ci na tsuge da xawo ya za ayi da ni???" Mujaheed
ya juya a mugun fusace xai fita jin dariyar da Imaan take ya juyo ya haureta da
karfi ya fice, wani ihu ta fasa ta rike kafar, inna ta mike da sauri tace
"Fita ki bisa ni ba ruwana kada a dameni ya xa mu dinga magana ki mayar da
mu mahaukata kina dariya" Imaan ta mike tana kuka sosai ta fita parlon
tana dingishi ta wuce part din su, Ammi ta fito kitchen da sauri, Tace
"Lafiya, me ya faru?" Cikin kuka tace "Yaya ne ya haure min
kafar dake min ciwo da karfi gashi yanxu ya rike Ammi, Wllh ban masa komai
ba" tana fadin haka ta xube kan kujera tana kuka sosai, Ammi ta karaso
tana kallon kafar, har gun ya tashi yyi ja, Hijab dinta ta dauka ta sa ta fita
parlon bata xame ko ina ba sai bangarensu, Yana xaune dinning takaici ya ishesa
Anty kuma na kitchen da su Maimoon. Nan parlon Ammi ta tsaya tace
"Mujaheed me Imaan tayi maka ka haureta a kafa?" Kallonta yyi ya
dauke kai bai ce komai ba, ta karasa dinning din fuska daure tace
"Tambayar ka nake malam, ka fara hauka ne xaka haureta a kafa, to Wllh
even by mistake kada ka sake don zan dau mummunan mataki a kanka" Anty ta
fito kitchen da sauri tace "Lafiya Hajiya Aisha?" A fusace Ammi tace "Wllh
ku ja masa kunne ya fita harkar Imaan a gidan nan, duk ranan da ya sake
gangancin ta6a lafiyarta xa ayi tashin hankali a gidan nan, haka kwanaki ya
mareta na kai xuciya nesa ban ce komai ba, to this shud be the last, kada ya
sake idan ba haka ba wllh sai na rama mata" Hakuri Anty ta dinga bata,
Mujaheed ya mike ya wuce sama ba tare da ya sake kallonta ba, Ammi ta nufi kofa
xata fita suka kusa cin karo da Umma xata shigo sun dawo anguwa da Rahma, ko
kallonsu bata yi ba ta fice, tana komawa dama daki ta shiga ta dauko man xafi
ta fito ta shiga shafa mata a gun, Imaan ta dinga yarfe hannu tana kiran daddy,
bayan Ammi ta daina shafa wa a hankali tace "Ammi xuwa kika yi gun
yaya?" Ammi tace "Baxan je ba ko shi ya haifa min ke?" Imaan na
kallonta tace "Fada kika masa" Ammi tace "Abinda ya fi fada
ma" imaan ta zaro ido tana kallonta, can tace "Ni da baki je ba Ammi
ni ne fa nake ta masa dariya...." Da gudu ta mike bayan ta kauce marin da
Ammi tayi niyyar sauke mata, ta wuce daki tana turo baki ta kulle kofar ta sa key,
tana jin Ammi na cewa "Xaki fada min ko kanin ubanki ne yayan, daga yau ma
kika sake xaunawa inda yake wllh sai na kakkarya ki a gidan nan" Inna ta
saki baki tana kallon Mujaheed har ya gama, tura tuwon gabanta tayi tace
"Ba lafiya, ita Aishar? To yaushe ta xama haka, atoh gaskiya imaan dai ta
zama yar jaraba tunda akan ta uwarta taje tana maka bala'i, wato Allah kadai
yasan abinda yarinyar ta tsara ma uwar, saboda irin wannan halayyar tata yasa
aka rasa gane kan ciwonta fa har yau, to meye kuma yarinya karama da hada gurmi
a gida, ae da sai kace ma Aishar A'a ni ba ruwana baxan yi fada da ke ba don
kin haifeni, ai ke kusan sa'ar uwata ce, to kawai kuma sai ka tsaya kallonta
kayi shiru" Mujaheed yace "Ni baxan ce mata komai ba ko sbda daddy,
amma ta sake min haka a gidan nan gaskiya sae dai duk abinda xae faru ya
faru" Inna tace "Ni ko sai naje na sameta wllh" da sauri
Mujaheed yace "A'a kar ki ce mata komai" Inna ta ja tsaki tace
"Ba dole in sameta ba xata sa ka gaba tana jaraba a kan figaggiyar yarinya
mai hada gurmi" tana fadin haka ta fice parlon, Ammi na shafa ma Imaan man
xafinta a kafa Inna ta shigo ba ko sallama, Ammi ta mike tace "Sannu da
xuwa inna" inna tace "Aa ba wani sannu da xuwa, yanxu Aisha a kan yar
ki xa ki sa Mujaheed gaba kina masifa inda kike shiga ba nan kike fita ba kamar
xa ki make sa, to ma ina ruwanki kina 6are xa ki shiga harkan 'yan uwa, ubansa
fa wan ubanta ne uwa daya uba daya, to ke kuma a wa Allah na tuba, Ba kunya ba
tsoron Allah xaki shiga fadan 'yan uwa, abinda ma ina xaune parlon d'an shafa
kafar nata yyi ya fita shine munafukar nan ta dinga ihu tana min birgima ni
kuma na koreta, ni dai ba ruwana kar ki lalata mana xumunci gaskiya, ko xane
Imaan Mujaheed yyi yau kanwarsa ce kuma yana da ikon yin haka, to banda shi da
ya tsaya mata kan lalurorinta shekarun baya da ba sai dai ta mutu ba, ni dai a
dinga jin tsoron Allah, gashi nan dai albarkacin Bukar bai kula ki ba, toh ni
dai kada a sake sa min jika a baki ba ruwana, banda ma bifillatani agwai da
wauta ina shi ina shiga sha'anin family" tana kai wa nan ta fice a parlon,
Ammi ta rufe man hannunta tana kallon Imaan tace "Wllh na sake ganin ki
xaune inda Mujaheed yake a gidan nan sai na kusa sumar da ke" Imaan dai ba
ta ce komai ba. Misalin sha daya Imaan ta mike daga kwancen da take da kyar xata
shiga daki ta kwanta, duk jikinta ciwo yake mata ga wani xafi da jikin yayi,
Ammi dake xaune parlon tace "Kina ji na" imaan ta juyo tana kallonta,
Ammi tace "Dama gobe kice masu baki jin dadi baxa ki iya tafiyar ba, don
babu inda xa a dake, ina xaman xamana a kwaso min wahala a bar ni da
jiyya" Imaan tayi shiru tana kallonta, can tace "Toh" daga haka
ta wuce cikin daki ta kwanta. Washegari karfe tara su Maimoon, Ummi da Rahma
suka gama shirin su na tafiya, kaya kala biyu ko wannensu ya dauka Abba duk ya
basu kudin kashewa, Yana kallon Ummi yace "Tafi ki duba ko mamana ta gama
shirya wa" Ummi ta fita parlon xuwa part din su Imaan, Ammi ta fito daga
bedroom din Imaan kenan rike da cup din shayi don da mugun xaxxabi ta tashi
safiyar ranan, Ummi ta shigo parlon da sallama, gaisheta tayi tace "Abba
yace Imaan ta fito" Ammi tace "Ae kam yau ta tashi babu lafiya"
Ummi na komawa ta fada ma Abba haka, Abba yace "Subhanallah ba lafiya
kuma" mikewa yayi ya fita, a dai dai part din su Imaan ya hadu da Mujaheed
ya dawo daga bangaren inna, Abba yace "Imaan wai bata da lafiya yau"
Mujaheed yace "Subhanallah" Abba yace "Let me check on her"
Mujaheed bai ce komai ba kamar ya juya yayi tafiyarsa sai kuma dai ya bi bayan
Abba, Ammi suka gaisa da Abba, Mujaheed yayi kasa da kai ya gaisheta, Ita ma ba
tare da ta kallesa ba ta amsa bbu yabo bbu fallasa, Abba yace "Toh ya
jikin nata?" Ammi tace "Toh da sauki, tun jiya dama bata jin
dadi" Abba yace "Ikon Allah" Ammi tace "Tana ciki"
Abba ya nufi dakin nata, Mujaheed ya bi bayansa kansa a kasa, kwance suka
sameta cikin duvet amma still sai shivering take, Abba ya cire duvet din yace
"Sannu mamana" Bude idanuwanta da suka rina tayi a hankali, Abba yace
"Ina ke maki ciwo" girgixa masa kai kawai tayi, Mujaheed ya duka kusa
da ita a hankali ya kai hannunsa jikinta, Abba na kallonsa yace "Ko dai a
tafi asibiti" Mujaheed xai yi magana aka bude kofar dakin inna ta shigo a
rikice tace "Ahaf, ni dama nasan xa a rina, ba ayi hauri ba ma ya aka kare
balle anyi, wllh Ahmadu da ya tattakure ya tattakure kawai sai gani nayi ya
haureta"
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of
coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit
07087865788 to be included in the payment group.
22. Imaan
Abba ya juya ya kalli Mujaheed jin abinda inna tace, Imaan ta
mike xaune da kyar tace "Ba fa kafana ke ciwo ba" Inna tace "Toh
ina ke maki ciwo" Komawa tayi ta kwanta bata tanka ta ba, Ammi dake tsaye
bakin kofar dakin sai kallonta take, Abba na kallon Mujaheed da ya kasa cewa
komai yace "Amma me yasa xaka haureta jiya?" Ya sunkuyar da kai yace
"It wasn't intentional" Abba ya gyada kai yace "It wasn't
intentional, OK that's good kayi kokari" Daga haka ya juya ya kalli Ammi
yace "Ta shirya ta fito mu je asibiti" daga haka ya fita dakin,
Mujaheed ya harari Inna fuska daure xai fita tace "Oho dai ta rufa ma ka
asiri amma ko tantama babu haurin da ka mata ne ya ja mata wannan ciwo"
Ammi ta basa hanya fuska daure, kansa a kasa ya fita dakin, Inna tace
"Kyansa duk inda imaan xata ga Mujaheed daga yanxu ta gudu tayi ta kanta,
ni dama tun da naga yanda yake laftar 'ya yan jama'ah a anguwa yana d'an yaye
bai fi shekara 3 ba nasan akwai bala'i a gaba wllh, duk ya bi ya addabi 'ya yan
mutane da cizo da yakushi a anguwa, kowa ya gansa sai ya adana d'an sa, lkcn
d'an Hansai Garba na kamarsa kullum sai ya ciji garba yakushesa, Hansai tayi ta jin haushi don ta
xo jegon Huraira a gida, in takaice maki kafin Hansai ta bar gidan idan aka
bude jikin garba duk ta6on cixon Mujaheed ne,
to kuma meye baxai yi ba yanxu?" Imaan na daga kwance sai dariya
take da kyar, Ammi dai ko kallon Inna bata yi ba tana fiddo ma imaan kayan da
xata sa, inna tace "Toh Allah dai ya kiyaye gaba yyi maki tsari da
shi, amma gaskiya imaan ki guji duk inda
Mujaheed yake, idan kun dawo asibitin xan xo dubaki idan Allah ya yarda, tafiya
dai ta sha ruwa" daga haka ta fita dakin, Ammi tace "Kin tashi kin
shirya ko xaki kwanta nan kina dariyar walakanci ne?" Imaan ta tashi ta
saka kayan da Ammi ta fiddo mata, Inna na fita taga Abba tsaye a waje, tace
"Ahmadu tafiya dai ta sha ruwa koh?" Yace "A'a xa su wuce tare
da Yusuf yanxu, shi Mujaheed xa su je asibiti da Imaan" inna tace
"Toh madallah, hakan ma yayi, to ko in bisu asibitin ne" Ta gefen ido
Mujaheed ya kalleta da sauri, Abba yace "Ehh to xa ki iya bin su"
Tace "Toh bari in kulle dakina kada a barsa a bude gaskiya" daga haka
ta wuce sashin ta, Mujaheed ya nufi motarsa don fitar da motar waje, Abba ya bi
sa da kallo har ya isa parking space ya shiga motar, Imaan ta fito sanye da
Hijab har kasa, da kyar take tafiyar, Abba yace "Sannu mamana, Allah ya
sauwake" a hankali yace "Ameen" yace "Mu je can kofar
gidan, ban gane fita da motar da yayi ba" tare suka fita compound din, Ya
bude ma Imaan front seat ta shiga, Abba na kallonsa yace "Inna na tahowa
yanxu, tare xa ku tafi" yace "Ehh na sani" Daga haka Abba ya
koma cikin gida, Mujaheed na ta kallon gate har sai da yaga inna ta fito tana
washe baki sannan ya ja motarsa yayi zooming off, Imaan ta xaro ido tana
kallonsa, yana isa titi ya kashe wayarsa ya ajiye ya dau hanyar asibitin da
yake aiki, Sai da suka yi nisa fuska daure yace "Ni kika je kika hada da
mamarki koh?" Tace "Ko dai ita taga ina kuka" ya gyada kai yace
"Xa ki gane kuran ki" Ta turo baki ta jinginar da kanta da kujera,
Suna isa asibitin bayan yayi parking ya juya yana kallonta yace "Sauko min
a mota" Bude ido tayi da sauri, ya bude door din motar ya fita, a hankali
ta ta bude side dinta ta saukar da kafafuwanta kasa, xagayowa yyi ganin bata
fito ba yace "Baxa ki sauka ba" kamar xata yi kuka tace "Wllh
jiri nake ji yaya" Wani harara ya watsa mata yace "To daukan ki xan
yi?" Bata ce komai ba ta sauko motar, ya rufe ya kama hannunta suka shiga
cikin asibitin. Yana xaune office misalin sha daya bayan ya kunna wayarsa kiran
Abba ya shigo wayar, murmushi yyi ya daga ya kai kunne, Abba yace "What's
taking you people too long Mujaheed" yace "Drip aka sa mata Abba,
jikin da sauki sosai, she is fast asleep now" Abba yace "Toh Allah ya
sauwake, why did u left inna behind?" Yace "Abba Kasan yanda take
abinta, xuwa xata yi tayi ta fada every slight mistake" Abba yace
"Haka ne, da yaushe xa ku dawo kenan" yace "Nan da azahar in sha
Allah" yace "Toh Allah ya kai mu" Mujaheed yace
"Ameen" daga haka Abba ya katse wayar, Mujaheed ya juya yana kallon
Imaan dake kwance kan gadon duba pregnant women tana bacci, mikewa yyi ya isa
kusa da ita yana kallon ruwan da ya kusa rabi, Hannu ya kai forehead dinta yaji
da dumi har sannan, ta bude ido a hankali, daure fuska yyi yace "How are
you feeling now?" Yamutse fuska tayi tana son mikewa xaune yace "Lie
still and answer my question" murya can kasa tace "Kai na yana min
ciwo" yace "Shi kadai?" Tace "And am hungry" ya kalli
abincin da ta ki ci da yawa daxu kafin a mata alluran a sa mata drip ya dauka
ya bude ya ajiye kusa da ita ya daga ta xaune, xaro ido tayi tace "Yaya
abincin daxu kuma??" yace "Kin taho da abinci daga gida ne" ta
hade rai tace "Ni dai baxan iya ci ba bayan ya huce kuma an ajiye k'ura ya
gama shiga ciki" wani kallo ya mata yace "Toh sai ki tsaya da yunwar
ki ai, wannan abincin dake rufe meye ya samesa da baxa ki ci ba, Bayan har ynxu
ma da dumi abincin" yana fadin haka ya dau cokalin ya debi abincin ya kai
baki, ta tabe baki ta dauke kai tace "A'a ni dai bana so, tun da safe fa,
ko ta gefe gefe ai dust xai iya bi ya shiga, sai dai kai ka cinye a kawo min
wani" Yace "Toh xaki ga wani kuwa" daga haka ya kai abincin
table dinsa ya xauna ya fara ci, ta dinga kallonsa kamar xata fashe da kuka,
ganin ko kallonta bai yi ba tace "Ni dai ka bani waya in kira Ammina ta
kawo min abinci" yace "Baxan bayar ba" komawa tayi ta kwanta ta
fara kuka har bacci ya sake xuwa mata, mikewa yyi ya rufe sauran abincin da bai
cinye ba ya fita office din. Wani takeaway din ya fita ya siyo mata na abinci,
yana dawowa ya tasheta ya ajiye mata abincin a gabanta sannan ya juya ya fita,
ta mike xaune ta bude abincin ta fara ci a hankali, har ya dawo dakin bata gama
cin abincin ba, ya xauna kan office chair dinsa, tana kallonsa tace "Yaya
ni baxan iya cinyewa ba" bai tanka ta ba hankalinsa na kan laptop din
gabansa, ya gama abinda yake sannan ya juya yana kallonta ya ga ta ajiye
abincin ta kwanta, mikewa yyi ya karasa kusa da ita ya dauke abincin ya ajiye
ta bude ido tana kallonsa tace "Yaya ina son xan yi magana da Ammina"
yace "Baxa kiyi ba" yana fadin haka ya koma table dinsa, ta turo baki
ta juya masa baya. Karfe biyu Imaan ta bude ido jin an kama hannunta, ya karasa
cire mata drip din yace "How are you feeling?" Ta mike xaune da kyar
tace "Da sauki, I want to go home" Yyi disposing roban ruwan ta sakko
saman gadon, da sauri ya rikota ganin xata fadi duk da ita ma ta kama gadon,
kamar xata yi kuka tace "Wllh jiri nake ji yaya" Ya saketa yace
"Toh ni nace ki sakko?" Komawa saman gadon tayi ya fita dakin, ba a
dau lkci ba ya dawo ya dau wayarsa da car key yace "Mu je" ta xaro
ido tace "Idan na fadi fa?" Yace "Sai ki tashi" daga haka
ya nufi kofa, sauka tayi saman gadon ta tsaya na kusan minti daya har ta ji ba
jirin kuma sannan ta nufi kofa a hankali kamar mai counting steps dinta ta bude
kofa ta fita, tsaye ta gansa yana jiranta, ya mata wani kallo yace "Da kin
bari na sake shiga office din ki gani" daga haka ya wuce ta bi bayansa,
sallama yyi da co workers dinsa suka fita asibitin, a Wani pharmacy ya tsaya ya
sauka ya siyo mata drugs da aka mata prescribing sannan ya dawo ya shiga motar
suka bar wajen, sai da suka kusa gida a hankali tace "Yaya baxa ka siya
min kaza ba plss" yace "A'a sai dai in siya maki akuya" murmushi
tayi tace "Toh siya min" A waje yyi parking yace "Sauka..."
Ta bude motar ta fita sai da ta shiga gate ya ga ledan maganin da ya siya
mata" fitowa yyi motar rike da ledan ya wuce ciki da sauri, ganin har ta
kusa apartment dinsu ya wuce nasu bangaren kawai, Babu kowa parlon, ya haura
sama dai dai fitowar Anty dakinta tace "Ya jikin Imaan din?" Ya saci
kallon kofar Umma kafin yace "Da sauki, Umma bata nan ne?" Anty tace
"Ehh tun da ta ji kai ka kai Imaan asibiti ta fice gidan tun safe bayan ta
gama bambaminta" Mujaheed ya xaro ido ya jingina da bango yace "Wa ya
gaya mata Anty?" Anty tace "Abban ku, tunda ba tsoron ta yake
ba" Ji yayi xufa na keto masa, Anty ta wuce ta bar sa wajen tsaye, da kyar
ya ja kafafuwansa ya wuce dakinsa. Ammi
ta hada ma imaan ruwan xafi a bayinta ta fito tace "Ga ruwan ki shiga,
saura ki salance ruwan" Tashi Imaan tayi ta wuce dakin nata. Wanka
Mujaheed yayi ya shirya jin lkcn Asr yyi yayi alwala ya fita gidan, yana dawowa
masallaci dama part din inna ya nufa don Allah yasan yana tsoron haduwarsa da
mahaifiyar tasa Inna ta fito daga daki
jin an bude kofar parlor ganinsa tace "oyaa Alale, fitar min parlor kada
in tara maka jama'ah, uban me ka xo min??" Mujaheed yayi dariya yace
"Haba dai mai gidan kuma kike kora yau inna?" A fusace tace
"Yana kabari, tun raina bai baci ba Mujaheed ka fita" Mujaheed yace
"Abba ne fa yace kada mu tafi dake Inna" ta buda baki tana kallonsa
tace "Kai haba?" Yace "Xan maki karya ne" xauna wa tayi
tace "Ikon Allah, shi Ahmadun yace ku tafi ku bar ni kenan, to ya ma kansa
kuwa, shine har da shi a bani hakuri da masu gadi a tsakar gida daxu, har
hawaye fa sai da na xubar" Mujaheed yyi murmushi ya kwanta kan kujera, Inna
tace "Toh ae shikenan, ya jikin Imaan din?" Yace "Da sauki"
inna tace "Kuma da gasken bata da lafiya Mujaheed? Naga kamar don kar aje
kauyen da ita yasa ta langwabe fa" Mujaheed yace "Ni dai akwai
abinci?" Tace "Gashi can wanda Aisha ta kawo min ne daxu, bai wuce
shinkafa da miya ba, Idan kuma biskit xa ka ci ga su can iri iri a daki wanda
aka kawo ma Imaan, Kazan ma daxu na dumama na karasa cinyewa..." Mikewa
xaune Mujaheed yyi yana kallonta na kusan second goma, can yace "Wa ya
kawo mata?" shiru Inna tayi kanta a kasa, can ta saci kallonsa suna hada
ido tace "Yo wa gareta banda Bukar??" tana fadin haka ta mike ta
shige daki.... Imaan ta fi minti biyu tsaye bakin kofar bedroom din Ammi ta
kasa shiga don bata san me xata ce mata ba, bude kofar dakin aka yi ta ja baya
da sauri, Ammi ta dinga kallonta tace "Meye haka kike yi a bakin kofa
ta?" Ta fara kame kame ba tare da ta kalli Ammi ba, Ammi tace
"Imaan" daga kai tayi ta kalleta kamar xata yi kuka, Ammi tayi kasa
da murya tace "Tell me what you want" tana jan fingers dinta a
hankali tace "Ammi dama... Dama Sadeeq ne yace min yana waje ya xo
gaisheni" Ammi ta dinga kallonta tace "Waye Sadeeq" ta sunkuyar
da kai tace "Abokin ya Muhsin" Ammi ta yi shiru, can tace "Toh
kar ki dade" Ta d'an yi murmushi tace "Toh nagode Ammi" daga
haka ta saka Hijab dinta ta fito don tun da aka yi la'asar Sadeeq ke waje amma
ta rasa yanda xata sanar ma Ammi ta fita, sosai hankalinta ya kwanta ganin ba
motar Mujaheed a parking space, kamar mai tausayin kasa ta fita kofar gida,
Tsaye ta ga Sadeeq jikin motarsa ya rungume hannunsa, as usual sanye da spec
dinsa, dogon hancinsa da cute millionaires belt dinsa shine first abinda xaka
fara noticing a fuskarsa daga nisa, Ta sunkuyar da kanta har ta isa inda yake
tsaye, kallonta yake daga cikin glass din idonsa ko kiftawa babu, murya can
kasa tace "Ina yini?" Yyi murmushin da ya bayyan dimples dinsa ya
cire glass dinsa yace "Lafiya lau Imaan ya jikin?" A hankali tace
"Na ji sauki" yace "Sure??" Ta gyada masa kai, yace
"Toh Allah ya kara lafiya, hope kin sha dosage na afternoon, I mean ur
drugs?" Ta gyada masa kai tace "Na sha" yace "Good, ya mama
fa?" Tace "She's inside" ya langwabar da kai yace "Yaushe
xan xo gaisheta pls" ta xaro ido tace "A'a xan ce kana gaisheta"
cikin sanyin murya yace "Ke dai baki son yan gidanku su san ni koh?"
xata yi magana aka bude gate, Inna ce tsaye bakin gate din tana kallon mai gadi
tace "Kai iliya kake ko ilu, Kasan kan waya kuwa? Hadiza xa a kira min duk
ba kowa gidan sai mai laluran can kuma nasan tana can tana bacci yanxu haka,
yaran duk sun tafi kauye sai gobe xa su dawo" Imaan tayi stiff inda take
bayan gabanta yayi mugun faduwa jin muryar inna, Mai gadin ya mike da sauri ya
amshi wayar yace "Toh Hajiya...." Buda baki inna tayi tana kallonsa
tace "Eh lallai baka da da'a, banda barbada kace ma matan gidan Hajiya
nima kace min Hajiya, to bari kaji ko wa enda suka dauke ka aiki ma inna suke
ce min balle kai, bar gani na haka xuciya mai kyau da rikon gaskiya da amana
yasa ka gan ni har yanxu da kyau na, amma wllh da kyar idan ban girmi wanda ya
haifi kakanka ba ma" yayi kasa da kai yana murmushi sosai yace "Yi
hakuri Baaba tuba nake" inna tace "Kaji min yaro dai" Imaan dai
ta kasa tsaye waje daya tayi backing din inna xuciyarta sai bugawa yake, murya
can kasa Sadeeq yace "Ur grandmum?" ta gyada masa kai a hankali,
kamar ance inna ta daga kai ta gan su, sake baki tayi ta kalli mai gadin tace
"Kai wancan ba Imaan bace nake gani a tsaye?" Yace "Ita ce
Baaba" Sadeeq yace "Let me go and greet her tunda ta gan mu"
imaan dai kasa cewa komai tayi, ta ji kamar ta fashe da kuka, ae kuma
shikenan.... Sadeeq na isa gun Inna dake ta kallonsa ya risina ya gaidata da
ladabi, tace "Kai ne sabon saurayin nata?" Murmushi Sadeeq yyi ya
kasa cewa komai, Inna tace "Ikon Allah, Kai ni fa na haifi ubanta Bukar,
jikata ce fa, ita kenan Allah ya ba Bukar fa, a hannuna fa aka haifeta wllh,
yanxu d'an nan da ban fito na gan ku ba shikenan, kai a garin ku haka ake yi??
ko bata ce maka kakarta na da rai bane, ita tunda bata da hankalin cewa ka shigo
ka gaisheni kai baxa ka yi tunani ka shigo ba, dubi fa yanda ta ji kunya ta
kasa juyowa kamar warce ruwa ya cinye" Sadeeq dai sai murmushi yake yace
"Dama ai xan shiga in gaida ki kaka, kiyi hakuri" inna tace "Ni
dai ba ruwana a dinga abu saboda Allah, tunda dai na kama ka mu je ciki"
Yana murmushi ya bi bayanta suka shiga compound din ta rufe gate, tana nuna
masa bangaren su Mujaheed tace "Kaga wancan katon ginin?" Yace
"Na gani kaka" tace "Toh na wan ubanta ne, barrister suke ce
masa, a India yayi karatun lauyancin sa, matansa biyu sai 'ya ya bakwai,
Mujaheed shine d'an sa na fari, ina tsaye bakin kofar asibiti aka haifesa, yana
nan xaka gansa wani lafcece dogo, da yake ada yana daga wannan karafunan
turawan, to da kyar dai Ahmadu ya raba sa da su, nima na dinga rokon Allah har
ya daina, a gabana fa ya girma, tun yaye yake wajena iyayen suka bar min, yana
gama sakandari dama babansa ya biya masa kudin karatun likita a turai, ai ko in
gaya maka babu irin fitsarar da bai koyo a can ba gaskiya, ni dai lkcn da ya
dawo ma tsoron sa nake ga wani uban gashi da ya tara, buduwar da xai aura ma
yar hayi ce, to sai kaninsa Yusuf, xaka gansa shi kuma wani lagwai lagwai kamar
ya karye malam, da ma muka samu ya d'an yi kauri yanxu, sai kaga yanda aka
haifesa d'an fiyot, to sauran kuma duk mata ne" Murmushi kawai Sadeeq ke
yi yana bin inna, inna ta nuna masa part din su Imaan tace "Toh kaga
wannan bangaren na su Imaan ne, Ubanta a can Habuja wajen neman abincinsa yake,
ita kadai Allah ya basa a duniya, to dai ya fi babu d'an agwai da bak'in da,
uwarta na nan wata bafillatana sai kirki, toh ni kuma kaga akurkin da suka gina
min nake rayuwa ciki" ta fadi haka tana nuna masa nata part din.
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of
coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit
07087865788 to be included in the payment group.
_23. Imaan
Am bringing this to the notice of my fans, idan xaku biya
book din *Imaan* in dai ba digit din nan 👉🏻
07087865788 wato lambata kuka yi ma
magana ba to Wllh ba ni kuka biya ma kudi ba, lambata guda daya ne kacal kuma
gashi can a sama na rubuta, sannan ni bana amfani da wani kati idan ba Airtel
ba, don haka duk wanda ya biya ta wani lamba daban wllh ya karanta hakkina
without paying coz every page sai na sa number na da account number amma sai ku
tsallake ku tafi kuna biya a gun wa enda ban sani ba ban san da su ba, ni kadai
nake harkata a bangaren rubutu bni da wani xae ce ku tura masa xai turo min,
talk to me directly through my WhatsApp digit 👉🏻
07087865788, su kuma masu siyar min da littafi har da hada document Billah na
bar su da Allah, we shall surely meet in the hereafter in dai hakkina ne in sha
Allah. Sannan masu *forwarding* ma su ci gaba there is power in the tongue_
Dariya Sadeeq yayi yace "Haba wannan ai ba laifi
kaka" ta tabe baki tace "Mu je dai tukun" suna isa bakin kofa
tace "To dai ka gani..." yana murmushi ya shafa kansa yace
"Wannan ai ya fi duk sauran kyau kaka, ga shi ba hayaniya ba komai"
Inna ta kara tabe baki ta bude kofar tace "Toh Allah ya masu albarka da
suka gina min ai dai yafi babu" bin bayan ta yayi cikin parlon dake ta
kamshin turaren wuta ta bude fridge ta dauko masa malt biyu da ruwan gora ta
ajiye masa yace "Nagode sosai kaka" xaunawa tayi tana washe baki tace
"Madallah, to ya sunan jik'an nawa?" Yyi kasa da kai yace
"Sunana Abubukar Sadeeq" Inna ta gwalo ido ta saki wani kabbara da ya
sa ya dago da sauri yana kallonta, tace "Yo ai sunan mahaifinta kenan
Bukar, wllh shi ya haifeta, ai ko baka gansa ba mutumin kirki mai dattako da
sanin ya kamata, sam yaron bai son 6acin raina, yo Ashe ma d'a na ne kai, to ka
sha kurumin ka in dai wannan yarinya Imaan ce to wllh ka sameta ka gama ko taki
ko ta so in dai ina numfashi kai ne mijin ba ruwana, don gaskiya ka kwanta min
sosai, naga kana da hankali da nutsuwa" murmushi kawai Sadeeq yake, yace
"Toh kaka idan ita bata ra'ayi fa?" Inna ta xaro ido tace
"Wannan kuma ita ta jiyo ni dai ba ruwana, sunan ubanta fa gare ka kuma
duk masu sunan an sansu da rikon aure, dubi fa yanda ubanta ya rike uwarta duk
da rashin haifa masa yara da yawa da bata yi ba, to ni ko ina xan yarda ka
kubce mata, A'a baxai sa6u ba wai bindiga a ruwa" Sadeeq yace "Toh
nagode kaka naji dadi sosai" Tace "A'a ba xancen godiya, sunan d'a na
fa gareka, ni dai ko yau kace xaka turo magabatanka kofa a wangale yake, to me
xa mu ci da ita?? duk da dai ko sati ba ayi da aurar da yar uwarta ba amma idan
ma iyayen nata sunce baxa su iya ba ni xan mata gado da kambodi da dirowa, Ina
ce suna kenan kayan auren dai?" Sadeeq couldn't help it but laugh, tace
"Kai ba xancen dariya bane, ni wlh sai in sa a siyar da filina guda daya
in mata kayan daki, dama ni tsinannen bokon nan da ake yi yanxu ba d'ad'a ni da
kasa yyi ba" Sadeeq ya sakko kasa yace "Da xa a ban ixinin turo
magabatan nawa ba da jimawa ba da naji dadi sosai kaka" Inna tace
"Wannan ai ba wata matsala bace bari Ahmadu ya dawo tunda kaga shi uban
nata na Habuja" yace "Toh naji dadi sosai kaka" Inna tace
"Kai don Allah... ai kuma an xama daya godiya ta me kuma, in ji iyayen ka
a nan garin suke su ma?" Yyi kasa dai kai yace "Ehh suna nan"
Inna tace "Toh dan siyasa ne uban naka?" Yana murmushi ya girgixa kai
yace "Aa d'an kasuwa ne, Alhaji Ahmad Bulasawa ne Abba na" Inna ta
xaro ido tace "Bulasawa?? Bulasawa dai da na sani na garin nan?" Bai
dago ba still yace "Ehh shi" Inna ta bude baki tana kallonsa da kyau,
can tace "Ikon Allah, ashe d'an babban mutum ne gabana ni Asabe, waye bai
san Bulasawa ba duk garin nan da ma duk kasashen arewa, ba ance gidansa na nan
nan GRA ba?" Yayi murmushi yace "Ehh" inna ta rike ha6a tana
kallonsa tace "Ehh lallai ga kamanni kawai hanci ka fisa wllh, amma
matansa aka ce biyu, to wacece uwarka a ciki, ko uwargidan? Don dai Bulasawa
bai wuce Ahmadu na ba" Yace "Ehh ita" Inna tace "Atoh
Alhmdllh, Allah na gode maka, kai abu sharr... bari Ahmadu ya dawo ko cikin
watan nan ma ni gaskiya sai ka turo su Bulasawan, wa xai xauna" shi dai
bai ce komai ba, Inna tace "Kai.... Allah mai iko, amma xan so kada wannan
abun arxikin ya dau lkci gaskiya, ai aure abun arxiki ne" a hankali yace
"Toh Allah ya sa haka kaka" tace "In sha Allah ya ma sa, ai abun
arxikin xa a hada" Mikewa tayi tace "Bari in debo maka dambun namar
da na ajiye ma Mujaheed" Da sauri yace "A'a xan koma ne kaka"
Tace "Da wuri haka? Ni dai ka tsaya ko a leda ne sai in kulle maka"
bata jira cewarsa ba ta shiga daki ba a dau lkci ba ta fito da gaba daya dambun
naman a leda ta juye, ya xaro ido yace "Kaka wannan ai yayi yawa"
tace "A'a ba ruwana ka amsa, dama Mujaheed da Imaan na ajiye ma to gaskiya
ba rabonsu bane ynxu" dariya yyi ya karba yace "Toh ngd kaka, Allah
ya kara girma" tace "Don ma dai duk sun cinye min cin cin din, kuma nasan
ba kowa ya aikata min haka ba sai Maimoon da Ummi, ita Imaan bata daukan abu ba
a bata ba sam ba halinta bane, gashi yarinyar bata da fitina tun tana
jaririyarta, ga rashin yarda da kowa, lkcn ma ni har fargaba nake kada a kawota
wajena don idan ta fara tsala ihu duk sai ta tara min munafukan anguwa an shigo
min ana tambayar lafiya, me ya sameta?? dama Mujaheed kadai ne bata yi ma kiwa
ba lkcn da take tashan kiwan, idan kuwa ta makalkalesa a lkcn bbu mai banbareta
sai uwarta Aisha, ita ce ma ta makala masa yaya tun bata da wayo, in ko ba shi
ya bata abinci ba dama abincin sai dai yyi ta galantoyi ba ci xata yi ba, in
gaya maka lkcn Bukar na siyo mata wani runtumemen alawa idan ta saka a baki
bata yrda ta ba kowa don rowa sai dai Mujaheed, shima din d'an dangwala masa
xata yi a baki tana makale jikinsa, kai har goyata Mujaheed ya sha yi fa ta
saki fitsari jikinsa sai dai ya canxa kaya, gaskiya ta takura ma Mujaheed ba
kadan ba tana karama, shi sa in har yana gida uwar ta kawo ta bani da fargaba
in kyalesu can su karata inyi ta kaina, to idan ban kyaleta ba ya xan mata
tunda bata yarda da ni ta sa iyayenta su fara wani mugun tunani a kai na in
shiga uku? A'a ba ruwana wllh" Murmushi kawai Sadeeq yake yana kallon
inna, ta tabe baki tace "Toh gashi dai Imaan an girma kamar ba ayi ba,
bari dai in bar ka haka naga kamar sauri kake, to sai yaushe kuma xaka sake
shigowa??" yace "Ae ko da yaushe xan dinga shigowa gaida ki in sha
Allah" Tace "Kai toh nagode yarona, Allah maka albarka, ya kare ka
sharrin mahassada" ya mike ya ajiye mata dubu goma a gabanta yace "Ba
yawa kaka a sa katin waya ayi xumunci" ta kauda kai da sauri tace
"kai kai.... Ayi haka kuma Bukar??" Ya nufi kofa yana murmushi yace
"Sai na kuma dawowa kaka" ta mike tana washe baki tace "Toh
Allah maka albarka ka gaida min uwarka kaji?" Yace "In sha Allah xata
ji" daga haka ya fita parlon just smiling, inna ta koma ta dau kudin tana
kirgawa tana murmushi. Dama tunda inna ta shiga ciki da Sadeeq imaan ta wuce
part din su ta fashe ma Ammi da kuka, Ammi ta mike tace "Lafiya?"
Cikin kuka tace "Ko ba inna bace ta wani fito ta gan mu shine ta sa suka
shiga ciki tare da shi, yanxu ban san dame dame xata fada masa ba, wayyo na
shiga uku Ammi, nasan komai ma yau sai ta gaya masa" Ammi ta sake baki
tana kallonta, ita kanta hango irin maganganun da inna xata juye ma Sadeeq yau
ta dinga yi, can tace "Ae ko sai ki tashi ki tafi bangaren nata, idan ta
ganki xata kama bakin ta" Imaan na girgixa kai tace "Ammi baxan iya
ba, tun fa a gate ta fara basa labari" Ammi tayi jigum, can tace "Toh
Allah ya kiyaye, ban san kuma me xan ce ba" daga haka ta bar parlon, Imaan
ta dinga hawaye duk jikinta yyi sanyi babban damuwarta ma kada inna tace masa
ai gashinta na nan bata son a gyara mata shi. Sadeeq na fita compound din yayi
dialing number imaan yana murmushi, da sauri ta mike xaune tana kallon wayar,
ta fashe da kuka a hankali ganin shi ne, da kyar ta daga kafin ya katse ta kai
kunne, yace "Toh ai xaki fito mu yi sallama amma?" Tayi gathering
courage tace "Me grandma dita ta gaya maka?" Yayi yar dariya yana
wara ido yace "Ai babu abinda bata gaya min ba, she told me
everything" Ta xaro ido kawai ta katse wayar ta fashe da kukan takaici,
duk kiran da ya dinga yi kin dagawa tayi daga karshe ta shige daki ta kwanta
kan gado bata fasa kuka ba. Bayan Isha jin ana knocking Ammi ta sa Hijab ta
nufi kofar ta bude, Abba ta gani tsaye da Mujaheed ta ba su hanya tace
"Ina yini Alhaji?" Ya shiga parlon Mujaheed na biye da shi ya xauna
yace "Lafiya lau Aisha, ya mai jikin?" Xaunawa tayi ita ma tace
"Da sauki Alhmdllh tana daki" Mujaheed bai yarda ya kalleta ba yace
"Ina yini" tace "Lafiya" Abba yace "Ko bacci
take?" Ammi ta mike tace "Anya kuwa...." Mujaheed dake tsaye
dama bai xauna ba yace "Bari in dubata" Har xata dakatar da shi sai
ta ji kunyar Abba, ta dai bi sa da hararan gefen ido don ko kadan bata so
tafiyarsa dakin ba, murda kofar bedroom din yyi ya shiga ciki, tana xaune gaban
mirror daga ita sai towel tana shafa lotion a duk jikinta, duk tunaninta Ammi
ce ta bude kofar don bata ko kalli direction din kofar ba, jin shiru ta daga
kai tana kallon kofar ta madubi, tsaye yake yana kallonta, suna hada ido yayi
saurin dauke kansa, ta xaro ido tana gyara daurin towel din tace
"Yayaaa" Mikewa tsaye tayi ta juyo tana kallonsa kafin tace komai
calmly yace "Abba na jiran ki a parlor" bai jira cewarta ba ya fita
dakin ta bi sa da kallo tana turo baki, Mujaheed na duban Abba yace "Tana
xuwa abba" Abba yace "Ohk" Hijab ta sa har kasa ta fito parlon,
ta gaida abba da murmushi fuskarta yace "Ya jikin mamana" tace
"Abba ai na ji sauki" yace "Toh Alhmdllh, Allah kara
lafiya" tace "Ameen" Abba yace "Ga watermelon nan you take
much of it kin ji" a hankali tace "Toh nagode Abba, but...." Sai
kuma tayi shiru, yace "But what?" Ta boye fuskarta tace "Abba
ina son cin suya" Abba yace "Toh Mujaheed xai siyo maki yanxu"
Mujaheed ya kalleta ta gefen ido irin kallon harara, Tana murmushi tace
"Toh nagode Abba" daga haka Abba yyi ma Ammi sallama Mujaheed ma yyi
mata suka fita. Abba yace "Idan mun fito part din inna sai ka tafi ka siyo
mata, there is still time ai" Mujaheed yyi kasa da murya yace "Abba
yanxu tare xa mu gun innan?" Yace "Of course, ban san urgent kiran da
take min ba, it might even be something that isn't worth the call"
Mujaheed yyi yar dariya yace "Dama xaka ga it's nothing that important...."
Abba yyi murmushi yace "But we still have to listen, gudun matsala"
Suna shiga parlon Inna ta shafe addu'ar da take kan darduma tace "Har ka
iso kenan Bukar, to shi kuma wannan jelan da ya biyo ka fa?" Dariya Abba
yyi ya xauna yace "Aa mun shiga duba mamana ne shine muka karaso nan din
tare" tace "Atoh na gansa wani sandan sandan kamar basamude a
bayanka" Mujaheed dai sae hararanta yake k'asa k'asa, tayi kasa da murya
tace "Kana ji na Ahmadu?" Abba yace "Ina jin ki" tace
"Kaga kujeran can da Mujaheed ya xauna?" Kai ya gyada mata yace
"Na gani" tace "To wllh tllh a kai Bulasawa ya xauna" da
mamaki Abba yace "Bulasawa kuma?" Tace "Eh, amma d'an sa ba shi
din ba" Abba yace "Tohhhh.... a ina ya san ki?" Ta daga hannu da
sauri tace "A'a ni bai san ni ba, a titi muka hadu yau kuma muka fahimci
juna kwarai da gaske..." daga Abba har Mujaheed kallonta suka tsaya yi
without blinking, can Mujaheed ya girgixa kai planning to get up and leave the
parlor yaji tace "Ashe wai saurayin 'yar ka ce Imaan, amma algungumar bata
ta6a sanar da ni ko da wasa ba, a wajen na gansu tsaye jikin santalelen
motarsa, in gaya maka taji kunya tsamo tsamo da ta gan ni, ni dai ban kulata ba
bakina a leko na taso keyarsa muka shigo cikin gida, d'an wajen Amadi Bulasawa
mai gidajen man fetur sun fi dubu a arewa fa Ahmadu" dakatawa Mujaheed yyi
da sauri ya juya yana kallonta, Abba na gyada kai yace "Tohh da kyau
hakan" Inna tace "Kai fa kasan da kyau yaro, wato idan Allah yyi
auren har kasan waje fa sai an fitar da ita an juye duk gurbatattun jinin
jikinta dake ja mata lalura a sauya mata sabo, sannan kasussukan jikinta su ma
duk sai an ce xa a sauya su ta rabu da ciwace ciwace na har abada, kasan fa bbu
abinda turawan nan basa iyawa in dai da naira, to ga naira dai faca faca ta
samu, ae ni bayan fitarsa sai da nayi ya ma ake kiran sujjadar nan na godiya ga
Allah?? To ni dai nayi wllh kuma na dade goshina a kasa" Dariya kawai Abba
yake yana kallon mahaifiyar tasa, Mujaheed dae sai juya counter din hannunsa
yake, inna ta marairaice tace "Ahmadu ka rufa min asiri ba abun dariya
bane wannan, sannan yaron fa duk ya damu wai xai turo magabatan sa nan ba da
dadewa ba ayi xancen aure, kasan su kuma manyan mutane basa son kwalo kwalo
kada a bari wannan yaron ya kubce ma jikata in shiga uku gaskiya" Juyawa
Mujaheed yyi ya dinga kallonta, Abba yace "Haba maganar aure kuma Inna, ko
secondary fa bata gama ba" Inna ta wani tsuke fuska cikin d'aga murya tace
"Allah ya tsine ma sakandarin, sakandarin banxa ga abun arxiki kana xancen
sakandari, ko a gidansa wllh xai bari ta karasa, baka gansa ba dogo yanda kaga
wannan mutumin dake kusa da kai a xaune, shi ma da kyar idan baya daga
karafunan nan na turawa don kirjinsa duk a tale, kana ganinsa kaga d'an boko
don gilashi ne ma a idonsa, toh irin wannan ne baxai bari ta karasa sakandarin
jaraban ba idan anyi aure, gaskiya Ahmadu ku maida hankalin ku sosai a kan
maganar nan da nake gaya maka, wllh kullu yaumin fargabana mijin da Imaan xata
aura tunda ga yanda Allah ya halitto ta, mai rufin asiri kadai baxai iya da lalurorinta
ba sai hamshakin mai kudi, da yau ace Bukar ya tara yara kamar yanda ka tara to
fa da imaan bata kai labari ba don nasan ba xai tara uban kudin da xai dinga
kashewa kan ciwonta ba, to astagfirullah kaga amfanin haihuwan kadan ba da yawa
ba, to yanxu dai ga yaro matashi kyakkyawa d'an masu kudi ya fito, bari ma kaga
abinda ya ban Ahmadu"
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of
coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit
07087865788 to be included in the payment group.
24....
*Just funny... Earlier this morning nayi post a kan masu
siyar min da littafi nace na bar su da Allah, da kuma masu forwarding min
especially wa enda ba wai siya suka yi ba fa, su dai aikinsu kawai suyi ta
forwarding, ni ban ma yarda sun san da Allah ba tunda basu tsoron a hada su da
shi ma.... amma the kind of messages da suka dinga shigo min was funny wai ni
nayi Allah ya isa a kan littafin Imaan.... har na gama Noor Hayat ban daga kai
na kalli masu fitar min balle masu karantawa for free ba, But Imaan is totally
different don wannan karan don anga ina shiru ina kauda kai har da masu
creating group na musamman mutane su basu dari ko dari da hamsin su saka su a
ciki su dinga masu update, is this fair plss??? Kuma ace kar in bar su da Allah
ni da hakkina, sannan idan masu forwarding waje basu yi forwarding ba hakan xai
faru??? No way! wllh domin kin siya littafi kin ba kawarki ko yar uwarki ta private
ko a jikina it's ur property, I 100% agree to that, but not to the extent of
sharing it to groups wannan kashe kasuwa ne, idan wani na da niyyar siya ya
gansa a group yana galantoyi wllh ya fasa siyan kenan and this isn't fair, shi
sa duk end of page nake reminding masu karantawa a groups it's not for FREE
amma ban taba cewa Allah ya isa ba, ni kunya ma nake ji in rubuta haka wllh,
sai dai ince ur cup of coffee, to masu cewa Allah ya isan fasa fitar masu da
books aka yi? Of course noo, to yau kam masu siyar min da littafi sun kai ni
bango ne shi sa na rubuta hakan, I wrote 8 good books for free online kar ku
manta😕, kuma duk sun samu karbuwa wajen ku, ku ma sai ku min
halacci kuyi patronizing, writers da suka fara rubutu of recent ma siyarwa suke
balle mu first online writers da ake tare tun tale tale?? Wasu kuma na ganin lambata ina sawa karshen
page amma su tsallake suje su siya gun masu ci da hakkin mutane, kun ga kuwa ba
ni suka biya ma kudi ba, kuma hakkina suka karanta without paying, plss understand
me here, su wa enda na bari da Allah sun san kansu, yo wa gareni da xan hada su
da shi ban da Allahn dama, ni dai ba ruwana* 😃
_Sorry for the longggg surutu but I have to explain my self
pls, I felt soo bad saboda wa enda suka siya littafin ne suke nuna rashin jin
dadin post din, afuwan a yafe min pls, anyi na farko anyi na karshe in sha
Allah, ba sai na sake cewa komai ba ma coz I know I have Allah_😍
Mikewa inna tayi ta dauko kudin da Sadeeq ya bata a daki tana
murmushi tace "Dubu goma ce ciff, babu yanda banyi da yaron ya bari ba ya
ki, toh ni ko xan tsaya muna jayayya da shi ne, haka dai na hakura na
amsa" Mujaheed ya kasa daina kallonta ko kiftawa babu, Abba ya sauke
ajiyar xuciya yace "Toh Allah ya saka da alkhairi" inna tace
"Toh ya xancen turo magabatan nasa fa?" Ya d'an yi shiru sai kuma
yace "Inna da dai a jira Sadeeq ya dawo koh?" A fusace inna tace
"Oh oh Allah waye kuma Sadeeq?? dole sai Bukar din yana nan? kai ba
mahaifi kake wajenta ba, Bukar da idan ya tafi Habuja kamar baxai sake dawowa
ba, ni ba ruwana ka kirasa a waya ka gaya masa komai in ma ya kama ya taso ne
ya taso kawai, to nasan bayan shekara nawa xai dawo idan muka tsaya
jiransa??" Abba ya dinga gyada mata kai nan ko neman abinda xai ce mata
yake, can dai yace "Toh ko xa ki kirasa da kanki Inna??" ta tsuke
fuska tace "Baxan kira ba idan baxa ka kira ba a bar kiran, iyaka in
shirya in tafi kano gun kawun ku ya amshi gaisuwa da kudin auren kawai, ai ba
ku kadai ke da iko da ita ba" cikin low voice Mujaheed yace "Meyasa
baki maganan wa enda suka girmeta a gidan sai ita??" Inna ta masa wani
kallo tace "kana nufin su ku kenan masu tambadewa a titi, wato kai da
Isuhu, to ni meye ruwana da rayuwarku fisabilillahi? Da ku yi aure da kar ku yi
duk daya wllh tunda baku da mafada, ko ni na ajiye ku da xan maku magana idan
ba rainin wayo ba, ko me na hada da ku? Ga dai iyayenku suna kallonku basu ce
komai ba sai ni bare? Imaan dai Allah ya fiddo mata zankadeden miji in sha
Allah, to ni na ajiye ku da xan maku magana idan ba rainin wayo ba, ko me na
hada da ku??" Abba ya mike yyi kasa da kai yace "Toh ina fita ynxu
xan kira Sadeeq din" Inna tace "Gwara haka dai, kana kiransa ka
zayyane masa duk abinda nace tass, kace masa yaron ma takwaransa ne shi ma
Sadeeq ake ce masa, baka gansa ba Ahmadu kyakkyawa ga hanci kamar an xana biro,
ga idanuwa maa sha Allah" sai da safe Abba yayi mata ya nufi kofa Mujaheed
ya bi bayansa, inna ta bi Mujaheed da harara tace "Oho dai bakin cikin ka
xai kare maka Mujaheed, daga jin kanwarka tayi miji sai bakin ciki ya bayyana
karara a fuskar ka? To aniyar moda ta bi randa, imaan dai nan gani nan
bari" Shi dai bai tanka ta ba har ya fita ya kulle kofar. Abba na fita ya
shiga kiran d'an uwan nasa, daddy na dagawa ko gaisawa basu yi ba yace
"Toh tsohuwa dai ta 6aro mana wani babban aikin Sadeeq" Daddy yace
"Tohhh, Me kuma ya faru" Abba yace "Wai aure take son ayi ma
Imaan" Daddy ya wani bude ido da mugun mamaki yace "Aure kuma
Barrister?" Abba yace "Wllh, and she is damn serious, kawai kirana
tayi daxu tana nemana shine na taho and this is what she said" cike da
confusion Daddy yace "Aure fa kace Barrister, toh ita tayi mata
mijin?" Abba yace "Na dai ji tana ta xancen d'an gidan Bulasawa, ban
san ko ita Imaan din ta ma san sa ba, I tried telling her she is too young ko
secondary bata gama ba but inda inna take shiga ba nan take fita ba, she didn't
even give me a listening ear, she so mean it, so ko xaka kirata yanxu??"
Daddy yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un me yasa inna take
haka" Abba yace "Kaga gobe Friday if you can squeeze up things ka
taho sai mu san yanda xa mu yi koh? Ni bana son in ja xancen ne ranta ya baci
kasan yanda take abubuwanta, shi sa mata sallama kawai na fita" Daddy yace
"But ka fa san idan tayi deciding abu it's hard ta canxa barrister"
Abba yace "Don't worry, ka dai taho goben sai mu san abun yi in sha
Allah" Daddy yace "Toh Allah ya kai mu" sallama suka yi Abba ya
kalli Mujaheed da kansa ke kasa yana tafiya absentmindedly, Abba ya dafa
shoulder dinsa yace "Are you okay son?" Kallon Abba yyi da sauri, sai
kuma ya d'an yi murmushi yace "Sure Abba, kawai dai har yanxu I am
surprise at what grandma is planning" Abba ya sauke ajiyar xuciya yace
"Imaan din har nawa take ma banda abun inna, ga shi ba wani lafiyan kirki
gareta ba, inna dai kam abun ta gaba yake ba baya ba, ita kawai ayi auren
saboda d'an mai kudi ne, Allah ma kadai yasan abubuwan da ta fada ma yaron, tun
tasowar mu muke fama da ita a haka muna ta lallabawa dai, gashi bbu abinda ya
canxa har yanxu, abu kuma ya xo ya hade da tsufa, sai dai mu yi ta mata addu'a,
Allah kuma ya rabamu da ita lafiya, amma abinda ya ban mamaki shine ta yanda ta
san yaron, kuma anya Imaan ta ma san sa kuwa?" Mujaheed dai bai ce komai
ba sai pressing din counter dinsa yake a hankali, Abba yace "Kai kasan
yaron Bulasawan da take fadi?" Mujaheed ya girgixa kai, bayan few seconds
yace "But ina ga Yusuf baxai rasa sanin sa ba don yana mingling da irin
su" Abba yyi murmushi yace "I will call and ask him" suna isa
sashinsu, Abba yace "Don't forget ka fita ka siyo mata naman da tace"
a hankali yace "Toh" motarsa ya bude don makullin na hannunsa ya
shiga, Abba kuma ya shiga cikin gida, Mujaheed ya ja motar ya fita compound
din. Mujaheed na dawowa daga siyo Tsiren da Abba yace ya nufi part din su
Imaan, a hankali ya kwankwasa kofar sannan ya murda yaji a bude, shiga parlon
yyi, ya sauke idonsa bayan sun hada ido da Ammi yace "Gashi Abba yace a
kawo mata" Ammi ta kwalo ma Imaan kira don tana bedroom dinta, ko me ta
tuna sai kuma ta mike xata amshi ledan sai ga Imaan ta fito sanye da kayan
barcinta, xata shigo parlon Ammi ta dinga mata wani kallo, da sauri ta juya ta
koma dakin ta rufe kofar, Ammi ta karbi ledan ta nufi dakinta ba tare da ta
amsa sai da safensa da ya mata ba, juyawa yyi ya fita parlon ya kulle kofar.
Washegari daga Imaan har Ammi suka yi mamakin xuwan Daddy ba notice, Bayan
Daddy ya shiga bedroom Ammi ta bi bayansa, xaune ta samesa gefen gado tace
"Yallabai xuwa babu notice, hope lafiya dai" Yace "Ehh I came
for something urgent, xuwa lahadi xan koma in sha Allah" tace "Allah
ya kai mu" shiru yyi hakan yasa tace "A kawo maka breakfast ne?"
Yace "Noo, Ina son maki wani tambaya, Imaan tana da wani ne dake
nemanta?" Ammi tayi shiru tana kallonsa a bit shocked, can tace "Lafiya
Yallabai?" yace "I am asking you..." girgixa kai Ammi tayi, she
have got no option then to protect her daughter, a hankali tace "Not at
all, ita da bata xuwa ko ina daga boko sai islamiyya, is there any
problem" yace "Ohk" mikewa yayi ya shiga bathroom ita kuma ta
fita a sanyaye tana mamakin tambayar, to me kuma ya faru, tana fita parlor tayi
still don sai a sannan ta tuna abinda Imaan tace inna tayi jiya, wato har inna
ta kirasa kenan ta gaya masa, daki ta tafi gun Imaan, tana kallonta tace
"kin ga abinda nake guje maki ko, to ina jin inna ta kira Daddyn ki har ta
fada masa xancen yaron jiya, without any doubt abinda ya dawo da shi
kenan" Imaan ta xaro ido a tsorace tace "Daddy ya maki maganan
ne?" Ammi tace "Dama tun ba yanxu ba nace maki ba ruwana kar ki ja
min matsala, gaskiya sai ki san abinda xa ki ce ma Daddyn ki, don't involve me
in this" daga haka ta fita dakin, imaan ta kasa xaune waje daya gabanta ya
dinga faduwa hawaye cike idonta, daga karshe ta fice a dakin, direct part din
inna ta nufa hawaye cike idonta.... shigar Mujaheed parlon kenan ya je gaisheta
daga inda yake tsaye, ko amsa gaisuwarsa bata yi ba tana kada shayi a kofi tace
"Ni fa Mujaheed tsabar yanda nasa maganar jiya a rai har mafarkinsa sai da
nayi wlh, wai ga Imaan a daula iya daula babu abinda babu a runtumemen gidan na
more rayuwa, har naje masu sati biyu, in gaya maka yau... a kawo min kaji,
gobe.... a kawo xabee, gata... a kawo kwayakwayay, citta... a kawo tika tikan
Kifaye, ga gwangwanin madarana da bournvita da suga an min dak'en da shi a
daki, nayi wani jazur da ni sai sheki nake malam, Shi ko bulasawan kullum xai
fita sai ya ajiye min dubu biyu in sa kati, wllh tllh ba karya nake maka ba
Mujaheed" Mujaheed dai na tsaye daga bakin kofa yana kallonta, ta tabe
baki ta yagi bread ta kai baki tace "Ni dai ba ruwana, Ahmadu ya shigo in
san yanda suka yi da Bukar din" Jin an bude kofa Mujaheed ya juya, imaan
ta shigo ko takalmi bata cire ba, tana kallon inna kamar xata fashe da kuka
tace "Inna me kika ce ma daddy na?" Inna tace "Waye kuma Daddyn
ki?" Imaan tace "Wai ni nace maki wanda kika gan ni da shi jiya
saurayina ne??" Inna ta kyabe baki tace "Kya ji da shi, ni dai baxan
kula ki ba ki xageni, na riga na gama maganata, wllh Mujaheed baka ga yanda ta
ji kunya ba jiya da ta gan ni kamar fa ta nutse, ni dai ban bi ta kanta ba ban
kuma kulata ba bakina a leko na ja Bulasawan muka shigo ciki, to kuma meye xata
shigo min ta tale baki kamar wata agwagwa? Ni dai ba ruwana" Mujaheed ya
juya ya fice daga parlon... imaan ta durkushe wajen tana kuka sosai tace
"Wllh idan kika sa Daddy ya min fada ko ya dokeni ni dai Allah na kallon
ki Inna, ni ban ce naki saurayina bane, abokin yaya Muhsin ne ni ban san shi
ba" Inna dai na ta cin bread dinta tana shan shayi, Imaan ta gaji da
kukanta ta mike xata fita inna tace "Toh aniyar ki dae dama ya bi ki a
baya, ba ruwana. Ni nasan wani yaya Muhsin" imaan bata tanka ta ba ta fice
hankali tashe. Tsaye Imaan ta ga Mujaheed dai dai inda xata sha corner xuwa
part din su, xata gudu ya kamo hannunta, a tsorace tace "Wayyo yaya don
Allah kayi hakuri inna sharri take min...." Fingers biyu ya daura kan lips
dinsa yana mata wani kallo, haka yasa tayi shiru tana kallonsa gabanta na
faduwa, ya nuna mata dakalin dake wajen fuska daure yace "Xauna" Ba
musu ta xauna kamar xata fashe da kuka, yace "What did I tell you about
standing outside with guys?" Hawayen dake makale idonta ya gangaro tace
"Don Allah kayi hakuri yaya" yace "Me yasa baki jin
maganata?" Tace "Ina ji fa yaya" yace "Toh meye tsakanin ku
da mutumin?" Ta girgixa kai da sauri tace "Ba komai, abokin yaya
Muhsin ne?" Yace "Me yake xuwa yi wajen ki?" Ta sunkuyar da kai
ta rasa abun cewa, strictly yace "Answer me now before I give you an
unclean slap" Ta fashe da kuka a hankali tace "Ba komai fa yaya, kayi
hakuri plss" dauke kai yyi na few seconds, sai satan kallonsa take, ganin
yanayinsa gabanta ya tsananta bugawa, can ya kalleta ya durkusa gabanta calmly
yace "Abba da daddy xa su kira ki su tambayeki what's between you and the
guy, me xa ki ce masu?" Ta sauke idonta a hankali tace "Xance masu
abokin yaya Muhsin ne" Ya wani hade rai yace "No, kalleni da
kyau" Daga kai tayi tana kallonsa, sosai gabanta yyi mugun faduwa, a
hankali yace "You tell them babu komai tsakanin ki da shi, kin ji
ni?" Ta gyada masa kai kawai, yace "Good, ko baki son ki gama karatu kamar
Seeyama? Baki son ki tafi university" Ta turo baki ta boye fuskarta da
hannunta murya can kasa tace "Ina so mana yaya" Jin bai ce komai ba
ta xame hannunta a hankali ta ga kallonta yake, dauke idonsa yyi murya can kasa
yace "Idan ma yace son ki yake kice masu ke baki sonsa" Yar dariya
tayi, ya jefa mata wani kallo xai yi magana sai ga Abba da Daddy xa su part din
Inna, mikewa yyi da sauri, Daga Abba har daddy kallonsu kawai suke, Mujaheed
yyi kasa da kai yana gaida daddy, daddy ya amsa da murmushi yace "Ya aiki
Muhammad" Mujaheed yace "Alhmdllh" Abba yace "I called ur
line baka daga ba" Mujaheed yace "Na bar wayar can daki naje gaida
Inna ne" Abba yace "Ohk" a hankali Imaan ta gaida Abba ba tare
da ta yarda ta dago kanta ba, Abba ya amsa daga haka suka wuce tare da Daddy da
ko kallonta bai sake yi ba, mikewa Imaan tayi tana kallon Mujaheed, yace
"Kin ji abinda nace maki koh?" Kai ta gyada masa a hankali, daga haka
ya wuce ya bar ta wajen a tsaye, Mujaheed bai karasa part din su ba mota ta shigo
gidan, Driver na parking Umma ta fito, suna hada ido gabansa ya fadi sosai ya
juya da sauri to make sure Imaan bata biye da shi a baya, driver ya sakko motar
ya xaga ya bude booth, set biyu na boxes masu d'an karen kyau da tsada ya fiddo
a booth din yyi cikin gida da su, Tuni Umma ta wuce ciki ita ma, Mujaheed ya bi
su da ido. Tare Abba suka shigo parlon da Daddy, Inna tace "Naji dadi da
ka ba lamarin nan muhimmanci ka taho Bukar, ina fatan kuma kayi murna da jin
wannan abun arxikin?" Daddy yace "Ina kwana" tace "Lafiya
lau, ya ka xo?" Yace "Alhmdllh" tace "To madallah"
Daddy yace "Jiya Barrister ya min bayanin komai...." Ta washe baki
tace "Toh Alhmdllh" yayi kasa da murya yace "Amma inna, Imaan
yarinya ce sosai sannan ga ta ba lafiyayya ba...." Inna ta katse sa tana
kallon Abba tana nunasa tace "Kai dai wllh Ahmadu baka yi ba, yanxu sai da
ka xugesa sannan xaku shigo min nan?"
Daddy yace "Aa baki fa jira na kai aya ba inna" mikewa tayi a
fusace tace "Babu wani xancen kai aya Bukar, ni kai da d'an uwanka xaku
munafurta daga taimako, ni xa ayi ma cin dunduniya, waye baya son nasa ya huta
a xamanin nan, koko xan ma Imaan xa6in da xae cuceta ne ko ance maku ban san
abinda nake bane, ku kuka haifeni ko ni na haifeku, to wai ma ku tsaya tukun,
wai idan aka yi auren nan tare za mu tare gidan da ita?? duk girman gidan naga
dai nata ne ita kadai ba tare da ni xata more rayuwar xaman gidan ba, iyaka bai
fi a sati inje sau biyar ko shidda ba, to idan baku aurar da ita ba jik'a ta xa
kuyi ku shanye ko enlargement xa ku yi da ita kuna kallo a parlor, yau naga
abinda ya isheni bai ishi ubangijina ba" Daddy yace "Kiyi hakuri, bai
kai haka ba inna, sai ki hada mu da yaron ayi magana ta fahimta" Inna ta
goge xufan da take yi tace "To yanxu naji batun kirki, sai dai kuma ban
san inda za a samo sa ba, amma ita imaan din ai baxata rasa lambarsa ba, ku
kira ta ta taho a kwashe min a wayata in kirasa" Abba dai sai kallon
mahaifiyar tasu yake, Daddy ya ciro handkerchief din aljihunsa ya share xufar
goshinsa, Abba ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yace "Toh xa a amshi
lambar nasa a gunta in sha Allah" Inna tace "Toh idan kun kirasa me
xa ku ce masa?" Abba ya d'an kalli daddy, Daddy yace "Ce masa xa mu
yi ya turo magabatan nasa" Inna ta xauna kan kujera tana murmushi tace
"Toh Allah maku albarka, ya buda maku" mikewa Abba yyi, daddy ma ya
mike yace "Toh anjima xa mu shigo in sha Allah" tace "Toh
shikenan amma kar fa ku ce xa ku ja lokacin don yaron yace a matse yake yyi
auren" Babu wanda ya tanka ta cikinsu har suka fita parlon.
*The book Imaan is not free*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit
07087865788 to be included in the payment group.
Imaan. Page 25
Abba na kallon Daddy yace "Kada kayi ma Imaan magana
tukun, I want to confirm who the guy is from Yusuf, Mujaheed yace baxai rasa
sanin sa ba" Daddy yace "Toh shikenan, amma I will so deal with her,
ita har nawa take xata fara kula samari can you imagine?" Abba yace
"Nace kar kace mata komai tukun, ni nasan abinda xan yi" Daddy bai
iya yace komai ba, don gaba daya ransa ya gama baci, suna isa part dinsa ya
shiga, Abba kuma ya karasa nasa part din. Direct bedroom din Mujaheed Abba ya
tafi ya bude kofar, Mujaheed na xaune tare da Umma a dakin ya sunkuyar da kai
yana saurarenta, Umma na ganin Abba tayi shiru daga abinda take cewa, Abba yace
"Ka sameni parlor Muhd" a hankali Mujaheed yace "Toh Abba"
daga haka ya rufe kofar, Umma tace "Wai me ke faruwa, jiya naga mood dinsa
gaba daya sai a hankali, halan tsohuwarsu ce ta tada wani fitinar?"
Murmushi Mujaheed yyi yace "Ehh.." Umma ta buda ido sosai tace
"Wai me take so?" Kamar Mujaheed baxai ce komai ba sai kuma yace
"So take ayi ma Imaan aure" Umma ta xauna da kyau da mamaki tace
"Aure kuma? imaan din saurayi gareta da xa a mata aure? Ko tana da yaron
da xata hada ta da shi ne?" Mujaheed ya d'an yi shiru sannan yace
"Ban sani ba Umma" Umma ta hade rai tace "Baka sani ba duk
kusancin ka da inna, ko dai gaya min ne baxa ka yi ba??" Ya girgixa kai yace "Umma ni bata gaya
min komai a kai ba" Tuni mood din Umma ya canxa, Mujaheed dai kallonta
kawai yake, Tabe baki tayi tace "To ma gani ai, yanxu dai xaka yi transfer
din ne ko Safeenar xaka ma?" A hankali yace "Anjima xan maki
Umma" ta mike tace "Toh ina jira" daga haka ta nufi kofa ta fice
dakin, Dafe kansa yyi na kusan minti daya, can dai ya tashi ya tafi parlon
Abba. Abba na kallonsa yace "Mun gama magana da Yusuf yanxu a waya yace
bai san yaron ba, so what I want you to do now is ka samo min number sa a wajen
Imaan, but ita kanta bana son ta san ka dau number yaron, do it wisely"
Shiru Mujaheed yyi, Abba yace "Yea just get his digit by any means without
her knowledge" Yace "Toh Abba" Abba yace "I want it before
the end of today" yace "I will do that in sha Allah" Abba yace
"Xaka iya tafiya if u have anything doing" mikewa yyi ya fita, Umma
ya gani sanye da Hijab ta rike purse ta nufi kofa, ko lura da shi bata yi ba
har ta fita, ya bi ta da kallo sannan ya wuce sama . Imaan na xaune kitchen
tana kallon Ammi dake kwashe girkin da tayi a warmer, Ammi tace "Kafin
Magrib idan ban dawo ba sai ki kai mata" Imaan dai bata ce komai ba, bayan
Ammi ta gama tana kallonta ta marairaice tace "Ammi amma me yasa baxan bi
ki ba plss" Ammi tace "Nace ki bari lahadi idan kin dawo islamiyya
kije, yanxu akwai mutane da yawa a gidan you will be uncomfortable" a
hankali tace "Toh Ammi" Ammi ta fita kitchen din ta mike ta bi
bayanta, Hijab Ammi ta sa ta shiga parlor gun daddy tace "Yallabai xan je
xa mu amshi lefen Halima" Daddy yace "Ohk xan je cikin gari dama, let
me drop you" Imaan ta turo baki ganin ita kadai xa a bari gida, kamar xata
yi kuka tace "Daddy in raka ka?" Wani kallo da ya tsorata ta ya maka
mata yace "You are stupid" sunkuyar da kanta tayi ta juya ta wuce
daki, Ammi ta hade rai tace "Ni ban gane haushinta da kake ji ba tun daxu,
ka kuma ki gaya min me ke faruwa" Yace "Madam dauko min makulli a
daki and stop questioning me" daga haka ya fita parlon, tabe baki tayi ta
tafi ta dauko masa makullin, dakin Imaan ta leka ta ganta xaune gefen gado tace
"Ki tashi kiyi sllh sai ki sa kallo ko a daki ne kiyi" daga haka ta
rufe mata dakin, kusan tare suka Isa parking space da Mujaheed, kansa a kasa ya
gaida Daddy, daddy ya amsa yace "Ya aikin?" Yace "Alhmdllh, xa
ku fita ne Abba" Daddy yace "Ehh xan je cikin gari ne" Ammi ta
hade rai ta bude front seat ta shiga, Mujaheed dai bai yarda ya kalleta ba
dama, daddy yace "Toh sai na dawo" Mujaheed yace "Toh a dawo
lafiya Abba" daga haka ya bar wajen yana d'an murmushi, dama tun safe yake
tunanin yanda xai hadu da Imaan har ya dau lambar Sadeeq, kan farin kujera ya
tafi ya xauna har Daddy ya fita gidan, bayan kusan minti biyar ya mike ya nufi
part din nasu, murda kofar yyi a hankali ya shiga ciki yana kallon parlon ya ga
bata ciki, ya jawo kofar ya rufe ya nufi bedroom dinta, tsaye yyi bakin kofar
kafin ya murda gently ya tura kofar, bai ganta dakin ba ya d'an yi jim, running
tap ya ji a bathroom ya gyada kai, ya tafi gaban madubi ya dau wayarta dake ajiye
xai yi silencing wayar yaga ma a silent yake, ya xura a aljihu sannan ya karasa kofar bayin ya makale jikin bango,
Imaan ta gama alwalan da take ta bude kofar bathroom din ta fito, ji tayi an
cafketa ta baya, ta fasa wani ihu a raxane ya jawo ta jikinsa ya riketa gam,
kafin ma ya kai ga cewa komai ta gane shine saboda scent dinsa, k'asa cewa
komai tayi ta dinga numfashi a tsorace don tayi mugun tsorata, bayan few
seconds numfashinta ya dawo dai dai, juyo da ita yyi yana kallonta yace
"Anjima Abba xai kira ki, kin dai ji abinda nace maki daxu koh?" Kin
cewa komai tayi, ya hade rai yace "Ba magana nake maki ba" tace
"Naji mana" Saketa yyi ya nufi kofa, ta murguda baki tace "After
all he is just a frnd, and he is...." juyowa yyi da sauri yana kallonta,
tayi maza ta shige bathroom ta sa key.
Mujaheed ya koma inda yake xaune ya fiddo wayar nata a aljihu
ya shiga call log, bai ga wasu calls ba sai na Daddy sai wani number da bata yi
saving ba, ya dinga kallon Number kafin yyi dialing, katsewa aka yi sai gashi an
kira, ya daga ya kai kunne yyi shiru, daga daya bangaren Sadeeq yayi sallama,
Mujaheed ya cire wayar a kunnensa ya katse kiran ya ciro wayarsa ya kwashe
number sannan ya danna ma number block ya goge log din kiran a wayar gaba daya.
Imaan na idar da sllh ta debo chocolates ta xuba su kan gadon ta sannan ta
kunna kallo ta kwanta tana shan chocolates tana yi, ta fi minti talatin tana
kallo ta tuna Sadeeq ya kira ta tun daxu bata dauka ba, mikewa tayi xaune da
sauri tana kallon gaban madubinta don nan ta ajiye wayar, da mamaki ta karasa
wajen mirror din idonta a kan inda ta bar wayar ganin babu shi, lkci daya
Mujaheed ya fado mata, ta xaro ido tana fatan ba shi ya dauka ba, duba dakin ta
shiga yi amma ba alamar waya, kamar xata yi kuka ta dau Hijab ta sa ta fita,
bata tsaya ko ina ba sai part din su, Babu kowa parlon gidan tsit don har
sannan su maimoon basu dawo ba duk da ta ji alamar akwai mutane a kitchen, ta
wuce sama cikin sanda tana waige waige, tana ta tsaye corridor tana kallon
kofar dakinsa, karasawa tayi ta murda kofar a hankali ta tura, ba kowa dakin
sai kamshi me dadi dake tashi, ta karasa ciki da sauri tana kalle kallen dakin,
wayarsa ta gani gefen gado amma bata ga nata ba, dauke wayar tayi ta boye cikin
Hijab ta fita da sauri, da gudu ta karasa part dinsu ta shige parlor ta sa
makulli tana turo baki, xaunawa tayi tana kallon wayar ta bude taga ba lock,
gallery ta shiga ta ci karo da hotan Farida a WhatsApp images, ta shiga wajen,
duk yawanci hotunan farida ne ta ajiye wayar ta kunna TV nan parlor ta kwanta
kan kujera ta ci gaba da kallonta. Mujaheed na kallon agogon wrist dinsa yace
"Aunty xan wuce aiki yanxu..." Aunty dake hada stew tace "Toh
Allah ya kiyaye" fita yyi daga kitchen din ya wuce sama ya shiga dakinsa,
makullin mota ya dauka ya kara feshe jikinsa da turare, ya juya xuwa saman gado
xai dau waya yaga babu, da mamaki ya dinga kallon inda ya ajiye wayar, ya fito
ya duba dakin Aunty ko ya mancesa a ciki ne yaga babu, fitowa yyi daga dakin
yana sauka stairs yyi still a zuciyarsa yace Imaan, to yaushe ta shigo?? karasa
sauka yyi ya fita parlon dai dai shigowar daddy compound din da mota, a hankali
yace "Shit" Ya tsaya har Daddy ya fito daga motar, ganin leda a
hannunsa ya karasa da sauri ya amsa yana masa sannu da dawowa, daddy yace
"Thanks Muhammad, Barrister ya dawo?" Mujaheed yace "A'a bai
dawo ba" a tare suka karasa apartment din Daddy dake amsa call da ya shigo
wayarsa, Daddy yyi knocking, Imaan dake kwance ta mike xaune da sauri tana xaro
ido tace "Waye wannan?" Daddy yace "Open the door" tashi
tayi ta bude kofar, Daddy ya ci gaba da wayar da yake, ta wani xaro ido ganin
Mujaheed ta juya da sauri ta koma ciki, Mujaheed ya saci kallon Daddy sannan ya
shiga, Har ta dauke wayar nasa da ke ajiye kan kujera xata gudu ya fixgota, ba
daman tayi ihu hakan yasa ta gatsa masa cixo a hannu da duk strength dinta, ba
shiri ya saketa, da gudu ta nufi dakinta, sai a kan idon Daddy da ya shigo ya
dinga kallonta da mamaki yace "Zo nan Imaan, whats wrong with you?"
Kamar xata yi kuka tace "Daddy yaya ne" Mujaheed ya kasa daga kai ya
ji kamar ya nutse a wajen, Yyi saurin ajiye ledan hannunsa yace "Abba xan
wuce gun aiki" bai jira cewar daddy ba ya nufi kofa ya fita. Da Magrib
imaan ta tafi kai ma inna abinci bayan ta sake boye wayar Mujaheed da kyau, duk
kiran da aka dinga masa na Farida kawai ta daga, tun da ta fito compound dama
gabanta ke faduwa, da sauri sauri ta karasa part din Inna, Yusuf ta gani xaune,
ta wara ido ta ajiye abincin hannunta tace "Lahh ya Yusuf yaushe ku ka
dawo?" Ya kalleta ya d'an yi murmushi yace "Daxu..." Inna tace
"Baki ga da ya shigo ba daxu duk a kode wllh, ai yanxu ya washe a haka,
Allah ya rufa ma ke da Mujaheed asiri ba ku je ba, baku da rabon wahala, amma
wannan garin ae ba wajen xuwa bane tirr" Imaan ta duka kusa da shi tana dariya
tace "Toh me ka kawo min ya Yusuf" ya shafa kansa bai ce komai ba,
Inna tace "Yauwa ina maka xancen kirki kafin wannan mata ta shigo..."
Ya sauke ajiyar xuciya a hankali yace "Ae ina ji" tace "Ko kai
ya ka gani, wannan ba shawara mai kyau bace na kawo?" Da kamar baxae ce
komai ba sai kuma yace "Da dai kiyi hakuri a bar xancen inna...." Ta
katse sa da sauri tana gwalo ido tace "Xancen auren?" Calmly yace
"Ehh" inna ta saki baki tace "Ehh lallai kai da Mujaheed kun
xama abun tsoro, yanxu har kai isuhu bakin ciki kake ma yar uwar taka? Anya 'ya
yan Ahmadu xa ku ga annabi kuwa? Ba kunya ba tsoron Allah ku fito kiri kiri
kuna nuna ma yar uwar ku bakin ciki" Shi dai kallonta kawai yake, imaan ma
sai kallonta take don bata gane kan xancen ba, Inna na tabe baki tana girgixa
kai tace "Har abada in dai ni yar halas ce ba ni ba shawara da gantalallu
irin ku, tun da haka ku ka xama gwara in yi ta kaina, to wai tsaya idan aka ki
gabatar da ita jika ta xa mu yi mu baku ku shanye?" Nan ma dai bai ce mata
komai ba, ta rike ha6a tace "Ai ni na shiga uku, lallai 'ya yan Ahmadu
mugaye ne, sam ba alheri a ranku, to wai tsaya... ku xa ku aureta idan aka bar
xancen?" Ya kalleta yace "Kika sani?" Imaan da ta fara dago
xancen ta wani hade rai xata mike ta bar parlon Inna ta riga ta, tana
kallon Yusuf cikin rashin hankali tace
"Ku har kuna da kudin da xa ku rike min jikata? Ku a su wa kuma Allah na
tuba, lallai kun cika marasa tsoron Allah, me kuma Imaan xata yi da kai ko
Mujaheed Idan ba sa6o kake son yi ba, ka ja mana fushin ubangiji...."
Murmushi kawai Yusuf yake, imaan ta nufi kofa xata fita, still tayi jin kamshin
Mujaheed, juyawa tayi da sauri ta nufi dakin inna tana cewa "Kar ku ce
masa ina nan" Mujaheed ya shigo parlon bayan few seconds, inna ta xauna
tace "Imaan dai bata nan idan ma ita ka xo nema" Mikewa Yusuf yyi ya
nufi kofa ya fita. Bedroom dinta Mujaheed ya nufa direct, inna tace "Da
dai ka kinkimota ku fito don na share dakina tasss ba ko kwayar datti, kada a
bata min a cuce ni ba uban wani ke min gyaran ba" Imaan na jin dama inna
tace masa bata nan tasan dole xai shigo dakin, ta shige bayi da sauri ta sa
makulli, Mujaheed ya murda kofar bathroom ya ji a kulle, juyawa yyi ya dawo
parlor yana kallon inna yace "Kiyi mata magana ta ban wayata kada in sa ta
kuka" Inna tace "Ikon Allah ya fi gaban haka, lkcn da wayar ya fita
hannun ka ya shiga nata sani nayi Mujaheed? Kaji min raini dai, ni dai ta fito
min daki gaskiya don ba Aisha bace ta share min" ya gyada kai ya juya ya
fita parlon, Da kyar Imaan ta yarda ta fito bayan tafiyarsa da kusan minti
goma, Inna dake tsaye bakin kofar bathroom din tace "To uwar me kike masa
da wayar sa ya taba ki ya taba alakakai ya taba jaraba, ke dai ki daina
tsokanan mutane kiyi ma kanki fada Imaan" Imaan ta fice a dakin, inna tace
"Da dai ya kama ki ya nakada maki shegen duka da xai gigitaki in ga me ce
masa don me a gidan nan, yarinya kawai kamar yar aljanu, wannan iri ta Bukar
Allah ka raba mu da ita lafiya, duk da dai lkci ya kusa" A hankali Imaan
ta bude kofar parlorn inna ta fita, ta gwammace tayi xagaye da ta bi normal
route, da gudu ta shige parlon su ta sa makulli tana murmushi. Karfe tara da
wani abu Ammi ta shigo dakin Imaan, Imaan dake xaune gaban madubi ta fito wanka
kenan tace "Na xaton fa kinyi bacci" Ammi tace "Ki ji da ni
kwanciya xan je inyi" mikewa tayi ta hau saman gado Ammi na kallon wayar
kan gadon tace "Wayar waye wannan?" Imaan tace "Na yaya ne"
Ammi na mata wani kallo tace "Me wayarsa yake a nan?" Kamar xata yi
kuka tace "Ammi to ya dauke min nawa wayar ya ki ya bani" Ammi na
kallonta da kyau tace "Kin san Allah idan baki kame kanki gidan nan ba kin
raba kanki da Mujaheed sai na sa6a maki Imaan, yaushe ke da shi ku ka fara
shirin da har xa ki dauke masa waya?" Imaan dai bata ce komai ba, Ammi ta
hade rai sosai tace "Let me make it brief, daga yau na datse sabon alakar
ku na gulma da Mujaheed, duk kika kuskura naga sabanin abinda nace wllh sai kin
sha mamaki na, ko dama kin hada wani abu da shi ne ban sani ba? Kuma maxa ki
kai ma inna wayar ta basa kayansa, naki kuma idan ya ga daman baki toh, idan
kuma bai baki ba ki bar sa, hope am clear?" Kai kawai Imaan ta daga mata a
hankali, Ammi tace "Shegantaka kawai, wai wani yaya, A'a ba yaya ba yayo,
in sake ganin kin kalli inda yake a gidan nan idan ban tsole maki idanuwa
ba" daga haka ta shafa mata lotion din maganinta sannan tace "Ki rage
fan din, sai da safe" daga haka Ammi ta fita ta kulle mata kofa, Imaan ta
saka kayan baccinta ta koma mirror tana shafa lotion a kafarta taji ana bude
window, mikewa tayi da sauri tana kallon window din, ido hudu suka yi da
Mujaheed ta dauke kai, strictly taji yace "Bani wayata" Ta make
kafada tace "Nima ka bani nawa first" Yace "Na fara maki wasa a
gidan nan koh?" Ta ki cewa komai ta daura kafarta kan stool dake gaban
mirror tana shafa lotion dinta, jin shiru ta juya, kallonta taga yana yi da
lumsassun idanuwansa, ta hade rai tace "Yaya yanxu idan sauro ya cije ni
na fara rashin lafiya fa? Dubi yanda ka bude min window fa, ni dai ba ruwana
idan na fara ciwo" calmly yace "Kar ki bari in shigo gidan nan, wllh
xan sa ki kuka, give me my phone I want to use it" yar dariya tayi ta dau
turare tana fesawa, yace "OK kina xaton baxan iya shigowa bane?" Ta
wara ido tace "Toh ai bance maka kar ka shigo ba" Tana fadin haka ta
karasa saman gado ta kwanta ta rufe da duvet, rufe window din yyi yana gyada
kai ya bar wajen. Mujaheed xai shiga parlon su suka hadu da Daddy, gaida sa yyi
da ladabi daddy na tambayarsa ya aiki yace "Alhmdllh" yana tsaye har
daddy ya shiga gun Abba, ya d'an yi jim, can ya tafi apartment din su imaan, ya
fi second goma tsaye ya kasa bude kofar, A hankali ya murda kofar ya shiga yana
kallon cikin parlon, babu kowa sai tv dake kunne, dakin Imaan ya nufa ya bude
kofar, kwance ya ganta har ta yi bacci, ya dinga bin dakin da kallo ya karasa kusa
da ita, daukar wayarsa da ta ajiye bedside drawer yyi yana kallonta, gaba daya
ta takure waje daya saman gadon sleeping peacefully sai dai ta cire duvet din,
dauka yyi ya rufa mata ya tafi gun switch din fan din dakin ya kashe fan din
gaba daya ya juya xai fita yaga Ammi tsaye bakin kofa, still yyi ya kasa cewa
komai, lkci daya ya sauke kansa ya fara kame kame yace "I... I came to
take my phone"
26.....
Ammi ta dinga kallonsa kafin a nutse tace "I want to
give u this warning Mujaheed, stay away from Imaan" shi dai bai yarda ya
kalleta ba, bai kuma ce komai ba, juyawa tayi ta bar bakin kofar, Mujaheed ya
fita xuwa kofar fita parlon. Washegari da safe Imaan ba inda bata duba ba a
dakin tana neman wayar Mujaheed ganin bata gansa inda ta ajiye ba, kamar xata
yi kuka ta fito parlor sanye da uniform din islamiyya, tana kallon Ammi a
hankali tace "Ammi kin ga wayar nan na jiya?" Ammi ta mata wani kallo
tace "Wanda kika bani ajiya?" Shiru tayi bata ce komai ba, Ganin ko
kallonta Ammi bata sake yi ba ta juya ta wuce dinning don yin breakfast, mamaki
ta dinga yi ta ya xata nemi wayar ta rasa a inda ta ajiye, daga karshe tayi
concluding kawai Ammi ce ta boye, ta tura soyayyen dankalin gabanta ta mike ta
dawo cikin parlor, safarta ta sa ta xura Hijab din makarantarta ta dau jaka
tana kallon Ammi dake parlor kamar xata yi kuka tace "Ammi fa kila xai yi
amfani da wayarsa don Allah ki bani in kai masa plss" Ammi ta daga kai
tana kallonta, da sauri Imaan ta fice daga parlon don ta san sauran, parking
space ta tafi ta tsaya tana jiran su Maimoon su fito, Mujaheed ne ya fito tare
da Yusuf, Imaan ta dinga kallon hannunsa da mamaki ganin wayarsa, bai ko kalli
inda take ba ya nufi gun motarsa ya bude ya shiga, Yusuf dake kallonta yyi
murmushi yace "Why are you looking at him that way" kamar xata yi
kuka tace "Ya Yusuf jiya ya dauke min wayata shine nima naje dakinsa na
dauke nasa toh yanxu ga na sa a hannunsa ban san ya aka yi ya dauke ba, ni kuma
nawa har yanxu ya ki bani" Yusuf yace "Toh me yasa ya dauke wayar ta
ki?" Tace "Nima ban sani ba kuma har daki na ya shiga ya dauka, ni
dai wllh ya bani waya ta xan je in gaya sa da inna" Yusuf ya kalli
Mujaheed da har ya tada motarsa amma idonsa na kansu, dauke kai Yusuf yyi yace
"Yaushe har ku ka fara shiri da Mujaheed da har ya shiga dakin ki ya dauke
waya?" Ta turo baki tace "Ni ba wani shirin da mu ke, kawai ganinsa
nayi a dakina bayan Ammi da daddy sun fita" Yusuf ya sake kallon Mujaheed
da yaki driving din motarsa, ya dauke kai, Imaan tace "Ya Yusuf ka yi masa
magana plss kuma fa ana kirana a wayar" Yusuf yace "Wa ke kiran
ki?" Boye fuskarta tayi ta fara dariya, Yusuf ya dinga kallonta, ta xame
Hijab din da ta rufe fuskarta a hankali, sai a sannan ya sauke idonsa yace
"Baxa ki gaya min ba" ta wara ido tace "Ya Yusuf wani ne, he is
my friend" jin Yusuf bai ce komai ba tace "Ni dai kafin su fito bari
in je in gaya ma inna" daga haka ta wuce ya bi ta da ido kamar yanda
Mujaheed ma ya bi ta da kallo, waje ta ga inna tana ta faman goge window with
seriousness, Imaan tace "Ina kwana inna" Inna ta d'an kalleta kafin
ta dauke kai tace "Aa ba wani inna ina kwana, ke din ce xa ki xo gaisheni
takanas da safe, ke dai fadi abinda ya kawo ki ina ji" Imaan tace
"Toh ko ba yaya bane ya dauke min wayata tun jiya ya ki bani" Kamar
xata yi kuka ta kare maganar, Inna ta ajiye tsumman hannunta a bokiti da mamaki
tace "Waye kuma yaya?" Imaan ta rungume hannunta xata yi kuka, inna
tace "Lallai ba lafiya, shi Mujaheed din akwai wani alaka ne tsakanin ku
wanda ni ban sani ba da har xai dauke maki waya? ko sata ya fara yi ba a sani
ba a gidan, ni dai naga abinda ya isheni, gaskiya wannan d'a na Ahmadu yana
cutar mu a gidan nan, to meye kuma xai dauke maki waya kamar shi ya siya? ko
yana bin ki bashi ne? Toh a gaskiya ya kamata Mujaheed yyi aure ya kama gabansa
na gaji da maganarsa kuma haka Allah ya gani nayi kokari, shekara kusan talatin
da biyu ana abu daya, wannan ai fitinanne ne mara son xaman lafiya, mu je gun
Ahmadu in ji ko shi ke koya masa ya dinga walakanta ni a gidan nan" daga
haka inna tayi gaba imaan ta bi bayanta, Inna ta tsaya kamar warce taga mugun
abu ta juyo da sauri tana kallon Imaan tace "Toh da ya dauke wayar ta ina
Bulasawan ke kiran ki?" Imaan tace "Toh ba wayar na wajensa ba, kila
ma ana ta kirana ya daga" Inna ta saki salati tace "Ashe yau xa a ga
barbadin fitina a gidan nan, mu je gun Ahmadun" Yusuf na nan tsaye inda
yake, Mujaheed kuma ya wuce kenan inna ta iso kamar xata tashi sama, Yusuf na
kallonta yace "Ina kwana Inna" a fusace ta juya tana kallonsa tace
"Da ban kwana ba xaka gan ni, ko a titi kake gaida uwarka Amina, to hirr
dinka... Dama duk gantalallen da yace jikata xai sa ma ido ya dinga yi ma bakin
ciki to yyi ta kansa inyi nawa a gidan nan, ba ruwana, kada ma ka sake gaisheni
bana so, ko kuma in tsine ma gaisuwar...." Kallonta kawai Yusuf yake bai
ce komai ba, Inna ta wuce kamar xata tashi sama, imaan da ta ki yarda ta
kallesa ta bi bayanta, Anty na goge goge parlon Abba inna ta shiga imaan na
biye da ita, Anty tana kallonta tace "Ina kwana Inna?" Inna tace
"Ke ba xancen ina kwana, Amina ashe kema jaraban kika haifa ban sani ba
sai jiya, ashe Isuhu ma ba mutumin kirki bane na banxa ne ni ban sani ba, ashe
halinsa daya da tijararren nan Mujaheed, to Ahmadu ya ga ta kansa kuwa don
wannan ba yaran nunawa bane, banda haka ta ya xa su nuna bakin ciki da
hassadansu a fili kan jikata, daga Allah ya axurtata da mai kudi saurayi sabon
jini sai hassada ya tashi? toh wllh su cire idanuwansu kan imaan, shi Isuhu
tsabar shaharan da yayi a fannin bak'in ciki ce min yyi a bar xancen sabon saurayin
ma gaba daya, ke ki ji min mugunta, kice min lalacewa bai xo duniya ba?? saboda
mamakin abinda yace min sai nake tambayarsa ko idan aka bar batun sabon
saurayin su xa su aureta?? Budan bakin katon sai ce min yyi to na sani ko su xa
su auretan? Ke ki ji wani sa6o fa, kawai ya ja gida ya rushe da ni a ciki"
Inna ta fara matsar kwalla tace "Yanxu Isuhu bai ji kunyar gaya min haka
ba, idan ba ta6ewar basira ba dama ina su ina Imaan daga shi har Mujaheed din,
wllh ta fi karfinsu, me garesu da har xa su rike min ita salon wataran in xo
daukar gawarta ina kuka suna bani hakuri, haka kawai su kai ni su baro, yanxu
fisabilillahi Allah ya dubeni ya fiddo mata dai dai ita kuma sai bakin cikin
yan uwa ya tashi, to Allah ya so ni dama ba abinda na hada da su, ba dangin iya
balle na baba, kawai ni dai nasan na haifi Ahmadu shi kuma ya haifesu, ni sai
ince Bukar ya tattara ya bar gidan ma...." Shigowar Abba yasa ta dakata,
Abba na kallonta yace "Lafiya inna?" A fusace tace "Ina fa
lafiya Ahmadu isuhu da Mujaheed sun fi karfina, kawai yaro ya dage ya kwace ma
yarinya waya sai kace Rukayya ce ta siya wayar, to wllh kafata kafar wayar nan
yau idan ba haka ba in bar kowa da Allah, kuma gaskiya a daina bata min rai
gidan nan don duk ranan da xuciya ta debeni idan ban bi Bukar Abuja ba ace bani
bace" Abba dai ya kasa cewa komai, Ajiyar xuciya Anty ta sauke tace
"Toh ina Mujaheed din?" Inna tace "Sai ki tambayeni Mujaheed ba
tare ku ka kwana gidan nan ba ke kuma" Abba ya dau wayarsa yyi dialing
number Mujaheed, Mujaheed na driving ya daga wayar, Abba yace "Where did
you drop imaan's phone?" A hankali Mujaheed yace "It's with me"
Abba yace "Bring it back now" daga haka Abba ya katse wayar, inna ta
xauna kan kujera tana kallon Imaan tace "Xauna mu ga ta inda wayar xai
fito" Imaan da ta ki yarda ta kalli Abba ko Aunty ta karasa kusa da inna
ta xauna, Inna tace "Ahmadu dai bai yi sa'an 'ya ya ba gaskiya, don
Mujaheed da Isuhu sai su iya kashe mutum" Anty ta ci gaba da aikin da take
yi, Inna sai girgixa kafa take bayan kusan minti goma sai ga Mujaheed ya shigo
parlon, Inna tace "Huuuu an dai ji kunya, fito da wayar da ka dauke"
Mujaheed dai bai ko kalleta ba ya mika ma Abba wayar, Abba ya mike ya ba inna,
inna ta karbe ta mika ma imaan tace "Tashi mu je, daga yau dama duk inda
kika ga Mujaheed ki canza hanya da gudu don ba mutumin kirki bane" Imaan
ta mike ta bi bayan inna, inna ta bude kofa tana cewa "Sai kuma ka sace
wayar Rukayya idan ta ajiye ba dai na imaan"
Karfe biyar saura na yamma Sadeeq yayi parking kofar gidan su
Imaan ya kashe motarsa ya jinginar da kujeran motar, Muhsin dake kallonsa yace
"Ya da gyara xama kuma Doctor" Sadeeq ya shafa kansa a hankali yace
"Ni fa I told you ban taba xuwa gidansu yarinyar da nake nema gun iyayenta
ba, I don't even know where to start from, to idan ma na shiga me xan ce masu?
All that aside, ni ban ma san me yasa ake nemana ba" Muhsin yyi dariya
yace "Toh dama kuwa ina xaka je gidan su yarinyar da kake nema bayan duk
turawa ne Sadeeq, kaga kawai idan baxa ka iya shiga ba mu rabu da su mu koma kada
mu je ka kunyata ni gaskiya" Sadeeq ya sauke glass din idonsa yana kallon
Muhsin, can yyi murmushin sa mai kyau cikin cool voice dinsa yace "In koma
fa kace" Bai jira cewar Muhsin ba ya mayar da glass dinsa ya bude motar ya
fita, sanye yake da kananun kaya da suka yi matukar amsan jikinsa, Muhsin ya
fito motar yana kallonsa yace "Ehh lallai Abokina ya xurma da yawa"
Sadeeq dai bai tanka sa ba ya gama danne danne wayarsa ya kai kunne, bayan wani
lkci yyi kasa da murya yace "Abba gani a waje" Abba dake xaune
parlonsa tare da Daddy yace "To madallah bari they will lead you in
now" Ba a dau lkci ba Yusuf ya fito kofar gidan, Kallon Sadeeq ya dinga yi
har ya isa inda suke, suka gaisa Muhsin yace "Ashe dai Engnr kana
gari?" Yusuf yyi murmushi yace "Sure ina nan, ya aiki" Muhsin
yace "Alhmdllh" Yusuf ya shiga da su compound din har xuwa parlon
Abba, Sadeeq na shiga parlon ya cire glass yyi kasa da kai har xai xauna saman
kujera sai kuma ya fasa ya xauna kasan rug ganin nan Muhsin ma ya xauna, har
sannan bai dago kansa ba ya gaida su Abba da Daddy, duk suka amsa suna masa
sannu da xuwa, Daddy yace "Muhsin abokin ka ne dama kenan" Muhsin
yace "Ehh Abba abokina ne" Daddy ya gyada kai yace "That's
good" Abba ya kalli Yusuf da ya xauna yace "Where is M.A?" Bude
kofar parlon aka yi sai ga Mujaheed ya shigo parlon da sallama can ciki, kansa
a kasa ya xauna kusa da Yusuf sannan ya kalli Sadeeq da idanuwansa ke kan TV,
gaisawa yayi da Muhsin, sai a sannan Sadeeq ya kallesa yace "Barka da
yamma" Mujaheed yace "Same to you" Abba na kallon Sadeeq yace
"Can I know you plss son" Sadeeq ya sauke idonsa kasa yace
"Sunana Abubakar Sadeeq Ahmad, ni haifaffen garin Kaduna ne, mahaifina
asalinsa d'an kano ne, na gama karatu na and I am working as a medical
practitioner now" Abba yace "Maa sha Allah, a wani anguwar ku
ke?" Yace "GRA muke" Abba yace "Ohk can i know ur
dad?" Sadeeq ya d'an yi Shiru kafin yace "Alhaji Ahmad sunansa, d'an
kasuwa ne Abbana, yana kuma xaune nan Kaduna" Abba ya gyada kai cike da
gamsuwa, bayan few seconds yace "What is ur intention toward my daughter
Abubakar?" Sadeeq ya kasa dago kansa, Daga Mujaheed har Yusuf kallonsa
kawai suke, can ya dago kansa a hankali yace "Abba sonta nake da
aure...." Mikewa Yusuf yyi yana kallon Abban nasa yace "I want to
excuse my self plss..." Abba ya gyada masa kai ya juya ya fita parlon,
Abba yace "Toh naji dadin jin hakan daga gare ka Abubakar amma kasan ajin
da Imaan take yanxu?" Ya gyada kai a hankali yace "Na sani Abba"
Abba yace "Ohk good, wani xancen kuka yi da kakarta last time da ka
xo?" Murmushi yyi ya sunkuyar da kansa, Abba yace "Yes go on"
Yace "Abba ce min tayi idan tayi magana da ku xata sanar min in turo
magabatana" Abba yace "Ohk, kai d'an wajen Ahmad Bulasawa ne?"
Sadeeq ya gyada kai kawai, Abba yace "To yayi kyau, yanxu dai I want to
ask for a favor from you Sadeeq" Sadeeq ya daga kai a hankali yana
kallonsa, Abba yace "But before then bari in maka wannan alkawarin, Sadeeq
in dai Imaan ta amince tana son aurenka, wato ta yarda da kai, sannan iya
binciken da xanyi idan ban ga wani flaws dinka mara kyau ba ni nayi maka
alkawarin xan baka Imaan in sha Allah, yea it's a promise I am making"
mikewa Mujaheed yyi yana kallon Abba yace "Abba I want to pick a
call" bai jira cewar Abba ba ya fita, Sadeeq dake kallon Abba yace "Toh
nagode Abba" Abba yace "Toh favor da nake son ka min ynxu shine....
Kakarta nake son ka samu amma ba yau ba, but cikin satin nan, sai ka ce mata
mahaifin ka bai kasar yanxu kuma xai dau lkci kafin ya dawo, yana dawowa kuwa
xaka sanar masa xancen auren... Am doing this to allow my daughter finish her
secondary schl, wato na da shekara daya, kasan yanda tsoffin nan suke, there is
nothing da xan gaya mata da xata fahimce ni, amma kai idan kace mata haka to an
gama komai, kaga ko da tana gamawa ne sai ayi magana amma yanxu kam I don't
think xan iya bada ta tana ss2, that aside.... my promise of giving u my
daughter's hand in marriage will count only on one condition ko da ta gama
secondary schl, the condition is that xaka yarda ko bayan kun yi aure ta ci gaba
da karatu a dakinta" Sadeeq ya d'an yi murmushi yace "In sha Allah
Abba" Abba yace "Toh Allah ya mana xabi mafi alkhairi" Sadeeq
yace "Ameen Abba na gode sosai,
Allah ya kara girma" Abba yace "Allah maka albarka" daga haka
Abba yace masa xai iya tafiya, nan suka yi sallama da Daddy da Abban sannan
suka fita parlon. Muhsin na kallonsa yace "Mu je in gaida Mum dita"
Sadeeq ya xaro ido yace "No kai dai kaje zan jira ka a waje" Muhsin
yyi dariya yace "Common Mum dita fa na ce maka..." Da kyar ya ja
Sadeeq suka nufi part din su imaan, Bell Muhsin ya danna, Ammi na kitchen xata
fito Imaan ta bude kofar dakin ta, Wani kallo Ammi tayi mata tace "Kika
san waye bakin kofar xa ki tafi a haka?" Imaan ta xaro ido ta juya ta koma
ta dau Hijab dinta ta sa ta fito ta nufi kofar, bude kofar tayi, lkci daya tayi
still tana kallon Sadeeq, Muhsin yace "Toh ko mu bi ta kanki" da
sauri ta juya ta bar wajen, kafin su shiga parlon har ta koma dakin ta ta
kulle, Dariya Muhsin yyi ya xauna, Sadeeq that was uncomfortable shi ma ya xauna,
Ammi ta fito kitchen ganin Muhsin tace "Ka shigo anguwar kenan" yayi
dariya yace "Ammi takanas nan fa na xo wllh" tace "Keep quiet
kai din" yace "Ki tambayi abokina Ammi" Ammi ta karasa shiga
cikin parlon tana murmushi tace "Toh sannun ku da xuwa" Muhsin ya
gaidata, tun da Sadeeq ya kalleta sau daya bai sake yarda ya kalleta ba shi ma
ya gaisheta, ta amsa da fara'a tana masu sannu da xuwa, Muhsin yace "Kawai
ce masa nayi ya rakani in gaida Mum dita" Ammi tace "Toh kun kyauta
kuwa nagode, sai dai abokin naka kamar d'an uwan mu ne Bafillatani" Dariya
kawai Muhsin yake, Sadeeq dai yyi murmushi bai dago ba, Ammi ta tambayi Muhsin
yayanta sannan ta tambayi Sadeeq iyayensa, Sadeeq yace "Duk suna lafiya
lau" Ammi na kallon kofar dakin Imaan tace "Imaan" Muhsin yace
"Kawai daga gani na shine ta shige daki saboda bata da gaskiya bata gaida
mutane ko a waya" Dariya Ammi tayi tace "Ae ban san yanda xanyi da
ita ba, ko nace tayi sai tace ta manta" Sai da Ammi ta kara kiranta ta
fito da kyar, wannan karan Hijab har kasa ta sa, Ammi tace "Baxa ki gaida
yayanki ba kika shige daki?" Bata yarda ta daga kanta ba har ta iso cikin
parlon kamar munafuka ta xauna kasa kusa da kujera tace "Ina yini Ya
Muhsin?" Yana murmushi yace "Lafiya lau Imaan, ya gida?" Tace
"Lafiya lau" ta saci kallon sadeeq da yaki kallon inda take tace
"Ina yini" yace "Lafiya lau" Ammi tace "Ki dauko masu
ruwa fridge" mikewa tayi ta wuce kitchen, Ammi tace "Jiya mun yi waya
da yaya yace gobe xai dawo" Muhsin yace "In sha Allah, haka yace
min" Imaan ta shigo cikin parlon ta durkusa ta ajiye tray din ruwa da
lemon five alive sai glass cups biyu, Ammi tace "Na gama girki bari in
xubo maku" Muhsin yace "A'a ki bar shi kawai Ammi a koshe mu
ke..." Ammi tace "Idan kai baxa ka ci ba sai abokin naka ya ci, ya
sunansa ma dai?" Dariya Muhsin yyi yace "Sunan Daddy garesa"
Ammi tayi murmushi tace "Ikon Allah, mai gida ne ashe" Muhsin ya kasa
daina dariya, Imaan na ajiye drinks din dama ta shige daki ta kulle kofa, Ammi
na shiga kitchen Sadeeq yyi kasa da murya yace "Don Allah ka rufa min
asiri mu wuce Muhsin" ko kallonsa Muhsin bai yi ba ya mike ya bi bayan
Ammi kitchen, har ta fara xuba masu abincin a plate yace "Ammi kinsan waye
muke tare da kuwa?" Ammi ta juya tana kallonsa tace "A'a, waye?"
Kasa daina dariya yyi yace "Wllh surkin ki ne, saurayin Imaan" Ammi
ta saki serving spoon din hannunta tana kallon Muhsin baki sake tace "Amma
baka da kirki Muhsin shine ka bar ni ina ta xuba a parlor?" Dariya kawai
Muhsin yake, Ammi tace "Ni dai ba ka kyauta min ba, haba naga yaro ya ki
sakin jiki, ita kuma Imaan sai na ci mutuncin ta..." Da sauri ya dakatar
da ita yace "Wllh bata sani ba, baki ga ita ma duk ta ki sakin jiki
ba" Ammi tace "Ni dai ka cuce ni, har kasa naje ina ce masa mai
gida" Shi dai bai fasa mata dariya ba, ta gama xuba abincin tace "Ai
sai ka daukar maku, ni kam na wuce daki" bata kara sauraransa ba ta fita
kitchen din ta wuce bedroom dinta, Muhsin ya ci abincinsa ya koshi, Sadeeq kam
ruwa kawai ya sha ya mike yace "I am waiting for you outside" duk
yanda Muhsin ya so tsayar da shi kin saurarensa yayi har ya fita, nan Muhsin ya
kira Ammi a waya yace "Toh ya dai fita Ammi ki fito mu yi sallama"
Ammi ta fito parlon tace "Bai ci abincin ba kenan" Muhsin yace
"Ae baxai ci ba, Ammi Abbansu Mujaheed ne fa ya kirasa yana nemansa shine
muka taho tare" Ammi tayi shiru tana kallonsa da mamaki, can tace
"Toh ya aka yi da ku ka je?" Muhsin yace "Ba wani matsala wllh,
Ai nasan daddy xai maki bayanin komai idan ya shigo, yanxu dai xan wuce kinga
yana can waje yana jirana" Ammi tace "Toh shikenan ka gaida Hajiya da
Hajjo" Yace "In sha, kice ma Imaan ta fito mu dai mun wuce" daga
haka ya fita parlon yana murmushi, a can kofar gida ya tadda Sadeeq xaune cikin
mota yana jiransa, Muhsin ya bude motar ya shiga yana kallonsa yace "Kai
dai ka rage munafurci Sadeeq duk rashin jin ka don ka xo gaban surkai sai kayi
ta wani sinne kai" Murmushi kawai Sadeeq yyi ya saka glasses dinsa ya tada
motar yace "I will have ur time later" daga haka ya fara reverse suka
bar layin. Kamar yanda Muhsin ya fada hakan ne ya faru don daddy na shigowa
bayan Magrib ya yi ma Ammi bayanin duk abinda ke faruwa, Ammi tayi shiru duk
jikinta yyi sanyi, A hankali tace "Toh yanxu ya ake ciki yallabai?"
Ya sauke ajiyar xuciya yace "Ina imaan din, taje can barrister na kiran
ta" Ammi tace "Ni dai Yallabai da dai a dakatar da yaron gaba daya,
imaan har nawa take don Allah" Daddy yace "So kike ki ja mana matsala
gun inna kenan, did you know maganar da ya dawo dani weekend kenan, ke kin ga
abubuwan da inna ta dinga fadi a parlor kuwa jiya?" Ammi dai bata ce komai
ba, Daddy ya girgixa kai yace "Fatanmu mu rabu da ita lafiya, gaba daya ta
rikice ne yanxu" murmushi kawai Ammi tayi, Daddy yace "I don't even
know me yasa xa ki ba Imaan fuskar kula saurayi at the first place, ko me xaki
ce min baxan ta6a yarda baki san da xancen yaron ba, kuma ki wani ce min nawa
Imaan take?" Ammi tace "A'a ko da baxa ka yrda ba I have to tell you
I know nothing much about the boy, of recent naga tana waya shi ma sai da na
mata fada, kai sai kace baka san yar taka bace da nuku nuku" Daddy yace
"Wannan ba hujja bace, kina tare da ita 24/7 a gida...." Ammi ta
dakatar da shi tace "Toh duk ba wannan ba ita innar da ta kirkiro abun sai
a fada mata ta gaya ma yaron lalurorinta... If he wish to be with her like that
shikenan, idan kuma baxai iya ba gwara tun wuri a san haka, I don't want my
daughter's heart to be broken or anything of such..." Daddy ya dinga mata
wani kallo ta mike ta wuce kitchen, yace "Wato you are even in support of
the silly thing the girl did, dama nasan kinsan komai ai, tunda aure take so
fine I will give her the best wedding ever" Imaan ta marairaice tana
kallon Ammi tace "Toh me yasa yake kirana Ammi?" Ammi tayi banxa da
ita, a hankali ta mike ta nufi kofa, Ammi tace "Kuma kiyi maxa ki dawo
idan ya sallameki ki xo ki kai ma Inna abinci" to kawai tace ta fita
parlon. A hankali Imaan ta bude kofar parlorn hade da sallama ta shiga ciki,
Umma ce xaune parlor sai Ummi da Rahma, ta dauke xata wuce parlon Abba Umma ta
dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa, Imaan ta tsaya amma bata juyo ba,
Umma ta mike tana mata kallon tsana karara tace "Uwarki tayi ajiya parlon
ne ta aiko ki kixo ki dauka?" Imaan taki cewa komai sai ma dauke kanta da
tayi, Xagi Umma ta kunduma mata tace "Kin matsa bakin kofar nan ko sai na
faffalleki da mari"
27.....
Imaan dai bata tanka ta ba ta nufi stairs, Umma tace
"Ragowar ciwo kawai" Sai da Imaan ta isa stairs ta turo baki ta wuce
sama, sai kuma ta fashe da kuka, dai dai corridor suka hadu da Mujaheed ya fito
dakinsa, ya bi ta da ido har ta shiga dakin Aunty, Karasawa stairs yyi yana
lekan downstairs ganin Umma xaune ya dawo da sauri ya bude kofar dakin Aunty ya
shiga ya kulle, Aunty na tsaye kanta sai tambayarta me ya faru take hankali
tashe, Imaan da ta xube mata nan tsakar dakin ta dinga kuka ta ki cewa komai,
Aunty tace "Kinga iskancin nan naki ne bana so, baxa ki bude baki ki min
magana ba, me kika yi ma Ammin?" Still ta ki cewa komai, Mujaheed ya
karasa kusa da su yana kallonta yace "Baxa ki bude baki ba ana maki
magana?" Ta hade kai da gwiwa cikin rawar murya tace "Ko ba Umma bace
take xagina ni ban mata komai ba har da ce min ragowar ciwo" Aunty ta ja
tsaki tace "Shine xaki xo ki tada min hankali a nan? Sai me don ta ce maki
ragowar ciwo? Xa kuwa ta ga ragowar ciwo a xuri'arta wataran, domin ita ta gama
haihuwa ai yanxu su kuma 'ya yanta xa su fara...." Juyawa Mujaheed yyi ya
nufi kofa, Aunty ta bi sa da harara har ya fita, Aunty tace "Banda
shashanci shine xaki xo kina ma mutane kuka, yau ta saba gaya maki haka?"
Ita dai Imaan bata ce komai ba sai share idonta take, Anty tace "Aiko ki
Ammi tayi ko me?" Ta dago ta kalleta a hankali tace "Abba ne ke
kirana" Aunty tace "Tashi mu je, yana parlon sa ai" mikewa imaan
tayi ta bi bayan Aunty suka fita, Umma ta dinga bin su da wani kallo, Aunty ta
nufi parlon Abba tana cewa "Ae ba mahalukin da ya isa raba ki da
ubanki, sai dai a ganki a kyale bbu ynda
aka iya da ke" Aunty ta bude mata kofar tace "Shiga" Imaan ta
shiga parlon Aunty ta rufe kofar ta koma sama, Abba na xaune yana kallon news
Mujaheed ma na parlon, sallama Imaan tayi ta xauna kasa ta gaida Abba dake
kallonta, yace "Lafiya lau Mamana sai yanxu kika xo?" Kai kawai ta
gyada masa, Abba yace "Toh yayi" bai kuma cewa komai ba, Imaan ta
saci kallon Mujaheed taga kallonta yake, suna hada ido ya hade rai, turo baki
tayi tana fidgeting fingers dinta, Bayan few minutes Abba yace "Imaan ai
kin san wannan yaron Sadeeq koh?" Shiru tayi bata ce komai ba ta kuma kasa
kallon Abba, Abba yace "Ina saurarenki" ta gyada masa kai tace
"Uhm" Abba yace "Kar fa ki boye min komai I am ur father, ki
gaya min meye tsakaninku" dauke kai tayi ta ki cewa komai, Abba yyi
murmushi yace "Baxa ki gaya min ba kenan" Nan ma dai ta ki cewa
komai, Abba yace "Toh tunda ni kunyata kike ji sai ki gaya ma Mujaheed
meye tsakanin ku" Xaro ido tayi tana kallon Abba, Abba ya mike yace
"Xan dawo yanxu, let me make a call outside, sai ki gaya masa kafin in
dawo shi kuma ya gaya min" daga haka Abba ya fita ya kulle kofar, tun da
Abba ya fito Umma ke binsa da kallo har ya fita main parlor, ta kalli kofar
parlon sa.... Imaan dai ta kasa xaune waje daya bayan fitar Abba, jin shiru ta
d'an saci kallon Mujaheed, ganin irin kallon da yake mata xata mike yace
"Koma ki xauna" ta marairaice tana dubansa tace "Ni fa ruwa xan
je in sha in dawo" ya dawo kusa da ita ya xauna yana kallonta da kyau
cikin husky voice dinsa yace "Me nace ki ce ma Abba?" Ta 6ata fuska
kamar xata yi kuka a hankali tace "Yaya ba ka riga ka gaya min jiya ba, ai
xan gaya masa...." Sai kuma tayi shiru, ya hade girar sama da ta kasa yace
"I will slap you idan baki gaya min abinda xaki gaya masa ba" Tace
"To ba cewa kayi ince ban san sa ba...." ya dinga kallonta fuskarsa
daure, a hankali ta mike da nufin fita parlon ya fixgota ta fado jikinsa, xaro
ido tayi tace "Yayaa" bude kofar parlorn aka yi yyi saurin janyeta
jikinsa, Kallonsu Aunty ta dinga yi daga inda take tsaye bakin kofa, Mujaheed
duk ya daburce ya mike tsaye, Imaan ta zamo kasan kujeran kamar xata yi kuka,
Aunty tace "Meye hakan" Mujaheed yace "Aunty kawai daga mata
magana shine xata fado kaina" Aunty ta tabe baki har sannan tana kallonsu,
juyawa tayi xata fita sai ga Abba, ta basa hanya ya shigo parlon, Anty ta fita
waje, Abba na kallon Mujaheed bayan ya xauna yace "what did she say about
him?" Mujaheed ya xauna saman kujera yana shafa kansa a hankali yace
"Tace ba komai tsakaninsu, bata ma wani sansa ba kawai shine ke kiranta a
waya..." Imaan ta kallesa da sauri, Abba yace "Haka ne Imaan?"
Kamar xata yi kuka tace "Abba ni dai bance masa haka ba, frnd dina ne fa,
kuma yana koya min karatu ta waya wani lkcn, ina ganewa kuma" Mujaheed ya
kasa kallon Abbansa, Abba ya kafe sa da ido, can ya d'an yi murmushi mara sauti
yace "Toh shikenan mamana, tashi ki tafi" mikewa tayi ta nufi kofa,
xata fita ta d'an saci kallon Mujaheed da ya ki dago kansa ta fita. Bata damu
da irin kallon da Umma ke mata ba har ta fita parlon ta wuce part din su.
Abincin inna ta dauka ta tafi kai mata, sallah ta sameta tana yi a parlor ta
ajiye abincin xata fita, inna ta dinga gyaran murya alamar ta tsaya, imaan tayi
kamar bata ji ba tayi wucewarta da sauri, a hanya ta tadda Yusuf rike da ledan
fruits xae kai ma inna, ta gaishesa tana kallonsa, sama sama ya amsa mata ya
wuce, ta tsaya ta bu sa da kallo har yyi nisa, turo baki tayi ta bar wajen, har
ta gama shirin kwanciya kiran Sadeeq ya shigo wayar ta, ta kashe fitilan dakin
ta hau saman gado ta rufe har kanta da duvet sannan ta daga kiran, murya can
kasa ta amsa sallamansa yace "Kin fara bacci ne?" Ta girgixa masa kai
tace "A'a" murmushi yyi yace "Toh ya kike?" Tace
"Alhmdllh, ya aiki?" Yace "Lafiya lau..." A hankali tace
"Shine daxu baka ce min xa ku xo da ya Muhsin ba koh?" yyi murmushi
yace "Shi yace kar in gaya maki" tace "Toh yanxu da kun sameni
ban sa Hijab ba fa?" Ya wara ido yace "Yea sai in ganki da kyau, ai
ba laifi bane don naga abinda nake so ba hijab" ta xaro ido tace
"Uhnnn?" Yace "Yess" murmushi tayi bata ce komai ba, Yace
"Ya Ammi fa?" Tace "Tana lafiya" yace "Maa sha Allah,
kinje gun kaka yau?" Tace "Ehh na je kai mata abinci" yace
"Ina son in samu time in xo mu yi hira sosai da ke da kaka" ta xaro
ido tace "Ai ita bata hira, bata fiye son magana ba ma" Dariya Sadeeq
yyi yace "Really?" Kamar xata yi kuka tace "Ehh" yace
"Uhm to shikenan, yaushe xan xo mu yi hiran mu biyu kadai, I want to tell
you lot of things Imaan" Murmushi tayi tace "Ae Daddyna na gari bai
koma ba tukun" Yace "Toh baxa ki gidan gwaggo ba mu hadu can?"
Ta d'an yi shiru, murya can kasa yace "Are you there Imaan?" A
hankali tace "Toh gobe xan ce ma Ammina xan je can dama ai saura kwana uku
bikin Anty Halima kilan idan na je sai bayan bikin xan dawo gida" yace
"Toh shikenan idan kin shirya goben sai ki kirani" ta xaro ido tace
"But ai sai Ammi ta amince in je, kasan ba a son ina fita ni kadai"
yace "Toh Allah yasa ta amince" Tace "Ameen" da sauri Imaan
ta cire duvet din kanta jin kamar ana bude window, ganin farin abu tayi ya fadi
kasan dakin, ta sauka gadon ta nufi windon da sauri ta bude labule har sannan
waya na kare kunnenta, Mujaheed ne tsaye kusa da window din, ta xaro ido tana
kallonsa, yana mata wani kallo ya juya ya bar wajen, ta rufe window din ta
durkusa ta dau takardan tana kallo, muryar Sadeeq taji a kunnenta yace
"Are you there?" Tace "Yea ina ji" yace "Ko kin fara
jin bacci ne" murmushi tayi tace "Um" don so kawai take ta bude
takardar ta ga content dinsa, yace "Toh shikenan, sleep like a baby
dear" murmushi tayi tace "Toh nagode, good night" daga haka ta
katse wayar ta ajiye ta kunna fitilar wayar ta warware takardan tana haska
rubutun kai, xumburo baki tayi ta cukwuikuye takardan ta jefar ta kwanta kamar
xata yi kuka tace "Ni dai ba ruwanka da ni"
Mikewa tsaye Aunty tayi tana kallon Yusuf dake xaune gefen
gadonta, shi kam bai yarda ya kalleta ba, Tace "What are you saying
Yusuf?" Still ya ki cewa komai, aunty ta dinga kallonsa ko kiftawa babu,
can ta ja stool ta xauna tace "Ka daga kai ka min magana malam" Sai a
sannan ya daga kai ya kalleta, tace "Are you serious with what you are
saying, or should i say are you on ur right senses?" Cikin sanyin murya
yace "Sure Mum" Tagumi Aunty tayi tana kallonsa with much surprise,
can ta girgixa kai cike da damuwa tace "Kai ma kasan wannan ba abu bane da
xai yiwu, ba abu ne mai sauki, haba Yusuf me yasa ka yarda xuciyarka ta yaudare
ka da son abinda kasan da wuya ka samu, ko da kuwa kana tunanin xaka samu mai
yasa baka tsaya kayi naxarin irin matsalolin dake tattare da samun ba? Wait
tukun toh ita Hafsat din fa?" Ya girgixa kai cikin low voice yace "Ku
ke tunanin ina son Hafsat, she is just a frnd, bani da intention na
auranta...." Aunty ta xaro ido tana kallonsa, can tace "Ikon Allah, i
really don't know what to say to you now Yusuf, ban san me xance ba gaskiya,
amma ni da xaka bi shawarata ka bar wannan xancen it's something that isn't and
will neva be possible, forget this pls son" Yana kallonta da mamaki yace
"Why Mum?" Tace "Look Yusuf, Imaan is my daughter, her mother is
my very close frnd as well, infact childhood frnd dita ce Aisha, don ta
dalilinta na hadu da mahaifin ku har muka yi aure, but... ni xan fi son mu ci
gaba da xumunci da Hajiya Aisha as just the frnds we are, and marrying into
same family, I mean relationship din mijinta da mijina, amma bana son xumuncin
mu ya koma na in-laws, its somehow, that aside Yusuf, kusancin inna da Imaan....
don't misunderstanding me plss son, kai ma inna kakar ka ce, amma gaskiya akwai
matsala daga bangaren inna ka bar ni ma in ji da headache daya...." Yusuf
ya girgixa kai yace "Kiyi hakuri Mum, I don't think all this u are saying
is enough da xai sa ki hanani auren Imaan" Aunty ta bude baki tace
"Ni nace xan hana ka aure Imaan Yusuf, idan Allah yyi Ita din matar ka ce
ni na isa in hana? Don't quote me wrong plss, amma kai kasan kana son ta me
yasa ko sau daya baka taba nuna alamar haka ba?" Yace "That's bcos
she is still young, har yanxu Imaan bata san meye rayuwa ba, bata san kanta ba
har ynxu, I was thinking idan ta fara jami'a ta d'an yi hankali sai in fito da
intentions dina toward her" Aunty tace "Toh Allah ya kyauta, I think
it's best ka je ka samu abbanku, amma ni nasan da kyar ne...." Yusuf yyi
kasa da kai a hankali yace "Ni dai ki daina cewa haka plss mum, support me
sannan ki min addu'a" a sanyaye tace "Toh na daina cewa haka, Allah
yayi maku xabi mafi alkhairi Yusuf" yace "Nagode mum" daga haka
ya mike ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, Tagumi tayi tana furta
innalillahi.... A xuciyarta. Sake baki Abba yyi yana kallon Yusuf with
surprise, shi dai Yusuf bai yarda ya kallesa ba, bayan few seconds Abba yace
"Yusuf" Sai a sannan Yusuf ya daga kai da kyar yana kallon Abban
nasa, Abba yace "Kana nufin Imaan kake so?" Yusuf ya sunkuyar da kai
a sanyaye yace "Ehh Abba" Abba yace "Ikon Allah" Shiru ne
ya biyo baya na kusan minti biyu, can Abba ya daga wayarsa yyi dialing number
Mujaheed har ya gama ring ba a daga ba, Abba ya ajiye wayar sanin yana gun
aiki, Abba yace "I am happy hearing this son, but at the same time I am
disturbed coz I made a promise to someone earlier, all the same don't worry,
Allah xai shige mana gaba, tashi ka tafi" Mikewa Yusuf yyi ya nufi kofa
Abba ya bi sa da kallo yana murmushi. Ko minti goma ba ayi da fitar Yusuf ba
sai ga Umma ta shigo parlon Abba cikin shirin fita, har sannan Abba was still
pondering at what Yusuf told him, kuma har ransa yake jin xai fi kowa murna da
wannan hadin, Auren d'an sa da tillon 'yar d'an uwansa, tunanin yanda xai fara
billowa al'amarin yake, first ya fara kiran D'an uwan nasa ya sanar masa sannan
su tafi gun Mahaifiyar su ita ma su sanar da ita, yasan Daddy xai yi farin ciki
da hadin shi ma, don fargabarsa a ko da yaushe gidan da only child din tasa
xata fada da sunan aure, yasan Daddy na son imaan fiye da tunanin me karatu, he
can do anything bcos of his only child, Umma Ta karasa cikin parlon tace
"Alhaji kasan Mujaheed ya tura min kudi xan fara hada masa lefe, to yau
xan fara shiga kasuwa" Abba na kallonta da mamaki yace "What? Lefe
kuma? But he told me nothing about that" Umma ta d'an bude ido tace
"Toh ba sae an gama hadawa ba xa a kinkimo maka ka gani, kar ya fada maka
kayi tunanin ko so yake ka basa wani abun, wllh ban son ya daura maka ko wani
nauyi ne kaga ba a dade da hidimar seeyama ba, tunda Allah ya hore masa xai iya
komai shi sa kawai nace kada ya gaya maka sai na gama hada kayan a kawo maka ka
gani, ba laifinsa bane shi ma ya so sanar da kai na hanasa, amma idan hakan ya
bata maka rai kayi hakuri don Allah" Abba yace "Toh Allah ya rufa
asiri..." Umma tace "Ameen, tun jiya naga kamar abu na damun ka,
shine nace to mai kuma ya faru, idan ma inna ce don Allah a dinga hakuri, uwa
ce... Sai ayi ta fatan a gama lafiya da ita, ya ci ace duk abubuwan inna ya
xame maka jiki yanxu..." Abba yace "Haka ne" Umma ta xauna ganin
maganganunta sunyi tasiri xuciyar Abba, murya can kasa tace "Toh me kuma
take so Alhaji?" Abba yace "A'a wannan mun shawo shi tare da Sadeeq,
Yusuf ne dai ya xo min da wata magana yanxu da ya kulle min kai... Am still
trying to find a way out ne har yanxu" Da mamaki Umma tace "In ji dai
lafiya??" Abba yace "Lafiya lau, yar uwarsa Imaan yake so da aure wai"
Mikewa Umma tayi da mugun mamaki baki bude tana kallon Abba, can tace
"Aure kuma Alhaji??" Abba yace "Kwarai, yanxu ma ya bar parlon
nan" Umma tace "Ikon Allah.... Aure fa???" Juyawa tayi ta nufi
kofa tace "Toh Allah yayi mana mai kyau dai, ya xaba abinda ya fi
alkhairi, ae imaan yar uwar sa ce, Imaan ta mu ce..." daga haka ta fice,
direct sama ta wuce ta bude dakin Yusuf ganin baya ciki ta shiga dakin Aunty,
xaune ta samesa tare da Aunty, Umma tace "Amma Yusuf kayi asara wllh, ka
kuma samu tabin kwakwalwa mai wuyar ganowa balle ayi maka magani, yanxu ka rasa
warce xaka je kace ma Ubanka kana so sai Imaan, Yusuf me ya same ka ni
Rukayya?? ina ita Hafsar da kake nema take??" Yusuf dake kallonta yace
"Umma ni Hafsat ba aurenta nace xan yi ba" Salati Umma ta saki tace
"Amma Allah ya isa tsakaninmu da kai, mu xaka ka ma bakin ciki Yusuf?? ka
bar 'yar attajiri ka dawo kace mai lalura iri iri kake so? Anya akwai lafiya
kuwa, mu xaka kwaso wa mugun iri, irin ciwo a xuri'ar mu? Yarinya mutu kwakwai
rai kwakwai?? Toh wllh tunda an asirce uwarka ta kasa cewa komai ni kam ba a
asirce ni ba sai inda karfina ya kare in sha Allahu, yanda xan ma Mujaheed haka
xan maka don duk daya ku ke a gu na, in sha Allahu sai naje na gano tushen abun
nan... Ba wanda ya isa ya ci nasara a kanka kamar yanda aka ci a kan kanin
Ubanka, uban kuturu yyi kadan wllh balle na makaho" daga haka ta fice a
dakin kamar xa ta tashi sama, Aunty da ta bude baki tana ta kallonta tace
"Ikon Allah ya fi gaban haka...."
Daddy couldn't help it
but laugh bayan Abba ya xo har part dinsa ya sanar masa intention din Yusuf a
kan Imaan, Daddy yace "Ikon Allah, nayi farin ciki sosai sai dai kar ka
mance da alkawarin da kayi a baya barrister, ko ya xa mu yi?" Abba yace
"Sure ina sane, shi ma ba wai xa a dakatar da shi bane Sadeeq din, abinda
xai faru yanxu kawai mu fara xuwa gun Inna mu je ta bakin ta kafin a yanke ko
wani decision" Daddy yace "Gaskiya ne wannan" Part din inna suka
tafi a tare, Inna ta fito daki tace "Tun safe in gaya maku nake aiki ban
xauna ba, ku leka bandakina ku ga ko tuwo ya xube kasa xa a iya xaunawa a cinye
tass, ba ku ji bayana ba kamar ya balle ni dai in huta" Murmushi duk suka
yi suka xauna, Daddy yace "Gwara dai ki dinga hutawa haka inna, gashi
kince baki son mai aiki balle a samo maki ko yar dattijuwa ce" Inna tace
"Ni ko ina xan so masu aiki mutane duk wari, sannan su cinye ma mutum
abinci, A'a ba ruwana ni ko da rarrafe ne xan yi aikina, 'ya yanku ne sun xama
abun tsoro banda haka Imaan ko Maimoon ko Ummi baxa su dinga xuwa min d'an
share share ba banda karshen duniya da lalacewa ta xo" Abba yace
"Inna ke fa kika ce baki so, ai da suna xuwa..." Inna tace "Ehh
ni nace bana so, don ba abinda suka iya gaskiya, basa min yanda nake so, ni dai
nace na yafe su daina xuwa" Duk suka yi shiru basu ce mata komai ba, ganin
ta dauko tsintsiya Abba yace "Inna daxu Yusuf ya sameni kan wata magana da
naga ya dace mu sanar maki kafin mu yanke hukunci...." Ajiye tsintsiyar
tayi ta xauna kan kujera da sauri tace "Me ya faru kuma??" Abba ya
d'an yi murmushi yace "Wai yar uwarsa Imaan yake so da aure...." Inna
ta gwalo ido ta saki baki tana kallonsu, saukowa kasa ta yi a hankali ta xauna
kan rug ta fashe da matsanancin kuka tana tafe hannu tace "Innalillahi wa
inna ilaihi raji'un, LA haula wala kuwata illa billahil Aliyul Azeem, la ilaha
ilallahu Muhammadurrasulillahi sallallahu alaihi wassalam, hasbunallahu wa
ni'imal wakeel.... Na ga abinda ya isheni ni patuuu" Daga Abba har Daddy
kallonta suka dinga yi da mamaki, inna ta dakatar da kukan da take tace
"Toh da kyar idan Imaan bata ta6a shan nonon Amina ba ma, yo ta ma sha ne
kawai... Idan xa kuyi ta kanku kuyi ta kanku"
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of
coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit
07087865788 to be included in the payment group.
28.....
Girgixa kai Daddy yayi yace "Hakan bai ta6a faruwa ba
Inna, ko kin manta ba gida daya muke lokacin ba" Inna ta mike a fusace
tace "Yau naga jaraba ni Asabe, ka fi ni sanin abinda nake ne Bukar, so
nawa idan matarka xata fita gantalinta na makaranta take kai ma Amina Imaan,
kuma babu wanda bai san irin kukan banxa da shagwaban da Imaan tayi tana
jaririya, bata kuma yarda ta sha komai sai nono, shi sa ma bana son a kawo min
ita ba ruwana, kuma kace min 6ata ta6a shan maman Amina ba?? karya xan xauna in
giggilla maku da tsufa na?" Sai kuma ta fara kuka ta xauna tayi tagumi
tace "Shkkn karshen duniya ta kama....." Abba ya sauke ajiyar xuciya
yace "Toh bari a kira Aminar a tambayeta" Kuka kawai inna take bata
tanka su ba, Abba ya dau waya ya kira Aunty, bayan ta daga yace "Ki taho
part din inna yanxu, it's urgent" tana tambayarsa abinda ya faru bai bata
amsa ba ya katse wayar, Aunty tayi jigum dama ita irin abinda take gudu kenan,
haka dai ta sa Hijab ta fita xuwa part din inna, Daga Abba har Daddy sai kallon
inna dake sharban kuka suke, da daddy yayi kokarin bata hakuri a fusace tace
"Rufe min baki, naki hakura, ko dole ne?" Haka yasa duk suka ja bakinsu
suka yi shiru, da sallama Aunty ta shiga parlon inna, Abba da Daddy kadai suka
amsa mata, banda Inna dake hararanta ta gefen ido, Aunty ta durkusa tace
"Ina kwana Inna?" Inna tace "Sai yanxu garinki ya waya da xaki
ce min ina kwana? Ina ce ana idar da sllhn asuba nan ya kamata ku yo ku
gaisheni amma ke da Aisha sai rana tayi gauuu sannan ku yo min nan wai kun xo
gaisheni, ni dai ba ruwana a dinga jin tsoron Allah" Aunty dai ba ta ce
mata komai ba sai gaida Daddy da tayi ya amsa, Abba yace "Amina wai kin
ta6a ba Imaan mama?" Da mamaki Aunty ke kallonsa tace "Imaan
kuma?" Abba yace "Ehh" Aunty tace "Ta ya hakan xai faruwa
kuwa? A'a ni ban taba ba..." mikewa inna tayi, tayi mitsi mitsi da ido
tace "Toh bari ku ji... da ki bata mama da kar ki bata duk uwarsu daya
ubansu daya a wajena... in dai da rai na a duniya to wllh Isuhu baxai auri
Imaan ba, harammm, ga dai d'an Bulasawa da ya riga sa sbda ku ba yan gaskiya
bane shine ku ke son yi masa fin karfi, to ni 'yar gaskiya ce, kuma ba a cin
amana da ni, na kuma yi ma yaron alkawari Imaan ta sa ce, don haka duk ku yi ta
kanku munafukai kawai, shi isuhun tun da can bai san yana sonta ba sai da ya ga
bulaswa sbda bakin ciki da hassada kar jikata ta huta, to aniyarsa ta bi sa, to
wai ma ina figaggiyar budurwarsa da har xai ce sai jikata sbda rashin tsoron
Allah, to ni ba ruwana ya cire idonsa kan jikata na riga na mata miji" sai
kuma ta fashe da kuka ta rike kai tace "Innalillahi Wa inna ilaihi
raji'un, wayyooo ubangijina, su dai yan gidan nan basa tsoron Allah na rasa me
yasa haka, basa tsoron axaban Allah, xaman gidan nan ya haramta gun mai tsoron
Allah iri na, ni dai idan xuciya ta kwasheni ma sai in tafi Habuja gun shegen
Balan can inyi xamana, don wani lkcn ma gwara 6are da naka" Mikewa Daddy
yyi ya nufi kofa ya fita parlon, Aunty ta tashi ta bi bayansa, A hankali Abba
yace "Toh kiyi hakuri an bar maganar in sha Allah inna" Ta kunce
habar xaninta tana share idonta tace "Ni dai ba ruwana, tunda haka isuhu
ya xama dama kar ya sake tako min nan, gwara min Mujaheed sau sittin a kansa,
shi Mujaheed baya haka, xuciyar sa mai kyau ce, kuma ni duk wanda ya sake tada
maganar nan gaskiya xan ja masa Allah ya isa" Mikewa Abba yayi yace
"Sai anjima" ko tanka sa bata yi ba har ya fita ya kulle mata kofar.
Abba ne xaune parlonsa da Daddy sai Aunty, Yusuf ma na xaune kansa a kasa, a
hankali Abba yace "Kayi hakuri Yusuf, Allah ya sa hakan shi ya fi maka
alkhairi" Yusuf ya daga kai ya kallesa yace "Ameen" Daddy kam
kasa cewa komai yayi, Aunty ta mike ta fita parlon.
Misalin karfe goma da rabi na safiyar ranan Imaan ta fito
parlor bayan tayi wanka ta shirya cikin atamfa an mata dinkin riga da skirt da
ya amsheta sosai, gaida Daddy dake parlon a xaune tayi, he was still tensed at
what happen safiyar ranan, bai taba tunanin Inna xata yi masu haka ba, gaba
daya bai ji dadi ba, don ko da ace yau Yusuf bashi da hali bai ci tayi haka ba
sbda shima jikanta ne, balle Yusuf is perfect in every aspect, ko Ammi daddy ya
kasa gaya ma, ya kalli Imaan ya amsa gaisuwar da tayi masa, ta mike ta wuce
kitchen gun Ammi, Ammi tace "Ki dau nose mask ki sa ki tafi ki share
balcony din nan ki goge it's too dusty ni kuma xan tafi unguwar rimi yanxu ina
sauke girkin nan" Ta marairaice tace "Ammi toh ai nima can xanje fa
yau, gashi har na shirya" Ammi tace "Me xaki je kiyi biki saura kwana
uku???" Kamar xata yi kuka tace "Don Allah Ammi ki bar ni in je, Anty
Halima fa kawata ce kawai don dai ta girmeni ne, plss Ammi let me go" Ammi
tace "A'a ba ruwana sai daddy ya bar ki, yanxu ki tafi ki share min inda
na sa ki" A Hankali ta juya ta fita kitchen din ta tafi daki ta dauko
thick nose mask dinta ta dau sweeper xata fita daddy yace "Ina za
ki?" Tace "Xan share waje ne" Daddy yace "Xa ki share waje
kuma? Ina mamar taki?" Ammi dake jin su a kitchen ta leko tace "Gani!!"
Daddy yace "Ta share k'ura fa kika ce madam" Ammi tace "Ga dai
nose mask nace ta sa ae, toh wai yallabai idan tayi aure ni zan bi ta ina share
mata gidan ko kuwa haka za ta bar gidanta ba tsafta sbda tana da asthma??"
Daddy dai bai ce komai ba, Imaan ta juya ta fita, daddy ya juya yana kallon
Ammi yace "Ba lallai tayi aikin gida ba idan tayi aure, I will get her a
housemaid that's capable" murmushi Ammi tayi tace "Lallai kam, to
idan mijin yace bai son Housemaid fa?" Mikewa daddy yyi yace "Sae a
fasa auren, I know what I am saying...." daga haka ya wuce dakinsa, Ammi
ta tabe baki ta juya ta koma kitchen, Imaan na share tiles din dake shimfide a
babban balcony din nasu lkci lkci xata mike ta d'an huta idan ta ji breathing
din nata na sarkewa, kamar ance ta juya taga Mujaheed kai kana ganinsa kasan
daga asibiti yake, mikewa tayi tsaye ta jingina da pillar tana sauke numfashi a
hankali, Mujaheed ya tsaya yana kallonta coz she looks so tired, fuska daure
yace "Wa ya sa ki shara?" Ba tare da ta kallesa ba tace
"Ammi" d'an jim yyi sai kuma yyi wucewarsa part din inna, Xaune ya
tadda inna a parlor fuska a tsuke, ya tsaya bakin kofa yace "Me ya faru
kike kirana??" Tace "Baxan kiraka ba Mujaheed, naga xama bai gan ni
ba na tashi naje na sami mai gadi ya nemo min lambarka ya kira min kai, ni dama
kai ne nawa, da kai muke kashe komai mu rufe, tunda ga irin 'ya yan da Allah ya
jarabce ni da samu, ni ba din ba din ba ma sai ince banyi dacen 'ya ya ba, samm
Bukar da Ahmadu ba yaran nunawa bane" Kallonta kawai Mujaheed yake, can ya
karasa cikin parlon ya xauna yace "me ya faru?" Ta fara matsar kwalla
tace "Wai kaji fa Isuhu ya fito masu da cewar yana son Imaan da aure"
a hankali Mujaheed ya mike yana kallonta da manyan idanuwansa, Inna tace
"Maimakon su tsigale sa su masa tatass, tunda ga yaro d'an kirki na
nemanta da aure, in gaya maka sai yaran nan suka biye sa, suka kwaso jiki suka
yo min nan suna washe min hakora a can" ta fadi haka tana nuna masa
kujeran da su Abba da daddy suka xauna, A hankali Mujaheed yace "Sai kika
ce masu me?" A fusace tace "Me kuwa xan ce masu Mujaheed?? Balbalesu
nayi nace ko bayan raina bulaswa xa a ba ma imaan, don ni yar gaskiya ce ba a
cin amana da ni, kai kaji bakin ciki irin na d'an uwanka fa?? Shi mai daukan
albashin da bai wani taka kara ya karya ba xai ce xai auri jikata taje ta mutu
in shiga uku in lalace? Dududu albashin nasa ya wuce dubu dari biyu da wani
abu?? A'a ba ruwana, ni dai nan na binne maganar nace bana son a sake tada ta
ko inyi Allah ya isa, Imaan ta Bulasawa ce idan Allah ya yrda, shine abun ya
min ciwo na fita na kiraka ina kuka a waya, ko kai ya ka gani?" Mujaheed
ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ya xauna yace "Haka ne, tunda ya riga
sa" Inna tace "Atohhh... kai dama duk ka fita daban a jikokina, kai
d'an gaskiya ne kamar ni, nasan kuma kai baxa ka ta6a irin wannan kazamin
tunanin ba wai xaka auri Imaan, kai kaji wani sa6o don Allah a ja mana fushin
ubangiji, toh Isuhu dai ya xama abun tsoro, har abada kar ya sake yo min nan
don xan tsallake in gudu gidan bala" Mujaheed dai bai ce komai ba don har
sannan gabansa bai daina faduwa ba ya rasa dalili, Inna tace "Ahmadu da
Bukar dai sun xama shashashai yan cin amana, Allah ya shirye su, kuma su
gaggauta tuba ga Allah ni ba ruwana" Mujaheed ya jinginar da kai da kujera
ya lumshe ido a hankali, inna tace "Baka rufe ido ba wannan abun takaicin
Mujaheed, Wllh yanda kake ji haka naji nima daxu, naji kamar ince wayyoooo
Allah, kawai na fashe da kuka bayan fitar su, haka kawai suje su ja mana
girgixan kasa a gidan" Mikewa inna tayi tace "Har naji sanyi da na
gaya maka wllh, ni dai bari in kada shayina in sha, ba ruwana da wahala"
Daga haka ta shige kitchen, Mujaheed ya dafe kansa, lkci daya ya dago yyi
murmushi, da cup biyu ta fito tace "Ko kai ma in kada ma ka shayin
ne?" Mujaheed ya kalleta yace "Toh"
Imaan ta gama goge balcony din ta tafi cikin parlor tana cire
mask din bakinta, Breakfast Ammi ta mika mata a tray ta ajiye ma Daddy a
dinning table, karasawa tayi ta amshi tray din tana ajiyewa dinning sai ga
Daddy ya fito, imaan na kallonsa ta marairaice a hankali tace "Daddy xan
je gidan gwaggwo yanxu, sai in dawo bayan bikin Aunty Halima" Daddy ya ja
kujera ya xauna yace "A'a sai dai ku dinga xuwa kuna dawowa da
mamarki" Ammi tace "Sae kace handbag, kawai ka barta ta tsaya can har
bayan bikin mana" yace "kin dai fi ni sanin condition dinta, so I
don't need to talk much" Ammi tace "Imaan fa ba yarinya bace
yallabai, she can take very good care of her self" daddy bai kuma ce mata
komai ba. Duk yanda Ammi ta so Imaan ta jirata su fita tare kin yarda tayi don
tuni ta kira Sadeeq bayan daddy ya amince ta tafi gidan gwaggo ta sanar masa,
sai gashi ko 15 mins ba ayi ba ya kirata wai yana saman layin nasu yana
jiranta, Ammi ta dinga kallonta da mamaki ganin ko gama rufe karamin trolley
din bata yi ba amma xata ja haka ta fita, cikin tsawa Ammi tace "Wai
saurin uban me kike haka Imaan??" Waigowa tayi da sauri tace "Ba
komai fa Ammi" Ammi tace "Rashin natsuwa ce kenan, ke kam yaushe xaki
yi hankali ne irin na sauran jama'ah, dubi fa yanda kike jan jaka a bude saboda
hankali ya maki kadan" Daddy dake xaune dinning yace "Komai dai ace
sai anyi fada, this isn't fair" Ko tanka sa Ammi bata yi ba, Imaan ta
durkusa a hankali ta karasa rufe jakar, Ammi tace "toh xaki iya daukar jakar
har bakin titi?" Imaan tace "Ai ba nauyi Ammi, kuma ja xan yi tunda
titin layin na da kyau" Ammi tace "Toh Allah ya kiyaye" daga ma
Daddy dake kallonta hannu tayi ta fita, ta rufe kofa kenan sai ga Mujaheed ya
taho daga part din inna, kallonta ya dinga yi tayi saurin dauke kai gabanta na
faduwa, kallon Sashin su yyi sannan ya kalleta yace "Ina xa ki?"
Backing dinsa tayi, tayi kamar tana gyara jakar ne ta turo baki tace
"Gidan gwaggwo" Jin bai ce komai ba ta leka sa daga durkushen da
take, kallonta taga yake yi har sannan ta kara turo baki, jin tafiyarsa ta saci
kallon gefenta taga gate ya nufa, sai da ta jira taga fitarsa gaba daya, bayan
few minutes ta ja jakarta ta xuwa gate, tsaye ta gansa jikin motarsa ya rungume
hannu, gabanta yayi mugun faduwa, ji tayi kamar ta rushe da kuka, tayi saurin
dauke kai xata nufi saman layin yace "Xo ki sa jakar a mota" Da sauri
ta kallesa sai kuma ta fashe da kuka ba hawaye tace "Yaya Ammi da Daddy fa
cewa suka yi in tafi da kai na kar wanda ya kai ni wllh" Wani mugun kallo
ya mata yace "Before the count of 3 do what I said now" jingina tayi
da gate hankali tashe tace "Don Allah yaya ka wuce wllh bana son ka kai ni
xan je da kai na" hade rai yyi sosai ya daga finger dinsa daya yyi
indicating da one, sannan two, bata jira ya nuna third finger din ba ta ja
jakar hawayen gaske na xubo mata ta bude back seat ta ajiye ta rufe, cikin
rawar murya tace "Xan dauko hand bag dina" bai tanka ta ba ya xaga ya
shiga driver seat ta koma cikin gidan ta fashe da matsanancin kuka, parking
space ta tafi ta tsaya ta yi dialing number Sadeeq, yana fara ring ya katse ya
kira ta, ta kai kunne cikin sanyin murya tace "Don Allah kayi hakuri Yaya
xai fita aiki yanxu shine yace xai yi dropping dina, ni kuma baxan iya cewa A'a
ba kar ya min fada" Sadeeq yace "Ohk no problem imaan, anjima da
yamma xanje can gidan in sha Allah" a hankali tace "Kayi hakuri don
Allah" yace "Noo ba komai dear, ai yaya ne, kar mu yi laifi ko"
tace "Toh nagode" daga haka yyi mata sallama ya katse wayar ta nufi gate
fuska daure ta fita, bude motar tayi ta shiga tana cika tana batsewa, ta gefen
ido ya kalleta ya tada motar ya bar layin. Sun yi nisa sosai kamar mai counting
words dinsa yace "I told u what to tell Abba... but you told him a
different thing saboda kin raina ni koh?" A d'an tsawace ya kare maganan,
Kin cewa komai tayi sai ma kauda kai da ta yi tana kallon waje, parking yyi
ganin haka ta juya da sauri tana kallonsa kamar xata yi kuka tace "Don
Allah kayi hakuri yaya, ai ya ma daina kirana, tun shekaranjiya ni bai kira ni
ba ma" Fuska daure Mujaheed yace "In ga wayar ki?" Xaro ido tayi
tace "Yaya ai yana gida" tana magana tana kokarin boye wayar a
jikinta, fixgota yyi, ta yi wani kara ta riko hannunsa tace "Wayyoo yaya
me nayi maka..." Ya dage Hijab din jikinta ta xaro ido tace "Yayaaa
ka bari" bai saurareta ba har sai da ya kwace wayar, dubawa yyi yaga ta sa
password, ya mika mata yace "Bude..." Make kafada tayi tana wani
murmushi, ya dinga kallonta kafin ya daura wayar kafarsa ya ci gaba da driving
din, har suka iso gidan gwaggwo bai sake ce mata komai ba, ita ma bata ce masa
komai ba, yayi parking kofar gidan, bude motar tayi ta fita, shi ma ya fito, ta
bude back seat ta dau jakarta ta rufe motar, danna lock yyi ya wuce cikin gidan
ta bi sa da kallo kamar xata yi kuka, can ta bi bayansa, Gwaggwo ce xaune
parlor tare da wasu yan uwanta duk maxa, Mujaheed ya xauna kasa ya gaisheta
sannan su ma ya gaishe su, Gwaggwo da fara'a Gwaggwo ta amsa tana cewa
"Ikon Allah, yau Mujaheed ne gidan namu, dama kana garin Mujaheed" ya
d'an yi murmushi yace "ina nan Gwaggwo ya kwana da yawa" tace
"Lafiya lau... Ka guje ni Mujaheed" Har sannan yana murmushi yace
"Kiyi hakuri gwaggwo yanayin aiki ne, xan je anjima da yamma in dawo tun
da kina da baki" Imaan ta xaro ido jin abinda yace, Gwaggwo tace "Ka
tabbatar Mujaheed" yace "Xan dawo da gaske" tace "Toh
madallah, sai ka dawo, Allah ya kiyaye hanya, ina nan ina jiran ka" Imaan
dai na makale jikin kofa ta ki shiga gidan, Mujaheed ya fito, kallo daya yyi
mata ya dauke kai ya nufi gate, ta bi sa da sauri tace "Don Allah yaya ka
ban wayata" wani kallo da ya tsoratata ya mata, ta koma baya a hankali, ya
nufi gate ya fita gidan.
Tun da yamma yayi hankalin Imaan ya tashi, tasan yanxu kila
Sadeeq ya kira ta wayar Mujaheed kila kuma ya daga, sannan ga Ammi tana gidan,
duk abun ya taru ya mata yawa, ita kadai ce kwance dakin Gwaggwo don anty
Halima na tare da kawayenta, ana idar da la'asar sai ga Halima ta shigo dakin
ta mika ma Imaan wayarta tace "Imaan gashi abokin ya Muhsin xai maki
magana" da sauri Imaan ta mike daga kan darduman da take xaune bayan ta
idar da sllh ta amshi wayar Anty Halima ta juya ta fita, xaunawa tayi gefen
gado tayi masa sallama a hankali, ya amsa yace "Is ur fone down?"
Xaro ido tayi da farko ta rasa abun cewa can tace "Um, ka kira a kashe
koh?" Yace "Sure" ta langwabar da kai tace "Ehh a kashe
yake" yace "Ohk, ina waje fa" ta wani xaro ido again, a hankali
tace "Toh ina xuwa" yace "Ohk I am waiting dear" mikewa
tayi ta fita, rasa wanda xata gaya ma ana kiranta a waje tayi don tsoron sanar
da Ammi take, gwaggwo ta shiga nema, ta sameta a Wani empty room tare da Ammi
da maman Halima, ta gaida maman Halima da ta amsa mata da fara'a tace "Ya
Abban ki Imaan?" Imaan tace "Yana lafiya mama" daga haka ta nufi
gun Gwaggwo ta durkusa murya can kasa tace "Gwaggwo wai Sadeeq yana waje
yana jirana" Ammi dai sai kallonta take don bata san abinda take gaya ma
mahaifiyar tata ba, Gwaggwo tace "Sadeeq dai da na sani abokin
Muhsin?" Imaan ta sunkuyar da kanta, Gwaggwo tace "Ikon Allah,
saurayin ki ne kenan" imaan ta boye fuskarta, gwaggwo tayi dariya tace
"A'a gaskiya naji dadi, Sadeeq ai yaro ne mai hankali da sanin darajan
mutane, tashi ki tafi ina gaishesa, ko kwana uku da suka wuce ya xo gaisheni da
Muhsin, gaskiya nayi farin ciki da wannan al'amarin" Ammi dai sai kallon
Imaan take, mikewa imaan tayi a hankali ba tare da ta yarda sun hada ido da
Ammi ba ta fita, tana fitowa parlor ta ji sallamar Mujaheed, still tayi inda
take tsaye, Gwaggwo na jin muryar sa tace "Ashe dai da gaske yake xai
dawo" Mamaki ya sa Ammi ta kasa cewa komai jin muryar sa ita ma, mikewa
Gwaggwo tayi ta fito parlor murmushi dauke fuskarta tana amsa sallaman tare da
few mutanen dake parlon, shigowa yyi suna hada ido Imaan ta juya masa baya da
sauri kamar xata yi kuka, ya nufi kujera ya xauna Gwaggwo na masa sannu da
xuwa, ta kitchen imaan ta bi ta fice daga gidan. Sauke glass Sadeeq yyi ganin
ta, ta sunkuyar da kai har ta isa jikin motar, ya fito ya jingina gefenta
smiling cikin cool voice dinsa yace "Good evening" kasa kallonsa
tayi, a hankali tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau Imaan, ya Ammi
fa?" Ta kalli cikin gidan tace "Tana ciki" yace "Amma ba
tare ku ka xo ba ai?" Ta girgixa kai tace "Na riga ta" har
sannan ta ki yarda su hada ido, a hankali yace "Kinyi kyau sosai, I love
the Hijabs you are wearing, you look so cute in them" boye fuskarta tayi
tana murmushi, ya dinga kallonta, kamar warce ta tuna abu ta xame hannunta da
sauri tace "Na manta na daura abu a kitchen kar ya kone" yace
"Xa ki wuce ciki knn?" Cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri, ai
mun gaisa" ya d'an yi murmushi yace "Sure, amma ina son mu yi hira
sosai, I told you I've got plenty things to let you know imaan" tace
"Toh may be later koh?" Yace "After Magrib or Isha?" Ta
gyda masa kai, yace "Ohk then, Allah ya kai mu lkcn, before then wait...."
Yana fadin haka ya bude motarsa ya fiddo wani abu kamar box mai kyau yace
"You put this on for the wedding" kin amsa tayi, gently yace
"Take plss Imaan" ta kallesa a sanyaye, ya gyada mata kai murya can
kasa yace "Take it" risinawa tayi ta amsa tace "Nagode" ya
mata murmushin da ya bayyana dimples dinsa ta mayar masa da light murmushi
sannan tace "Sai anjima" daga haka ta nufi gate ya bi ta da ido har
ta shiga gidan, sosai gabanta ya fadi ganin Mujaheed ya fito parlon gwaggwo, ya
dinga kallonta ta fara tafiya a hankali, kamar warce aka ture ta durkushe nan
kasa ta fara yarfe hannu tana xaro ido, ya karaso inda take yace "Daga ina
kike?" Hawaye har ya kawo idonta tace "Ammi ta aikeni, yaya na gurde
kafar fa" bai tanka ta ba ya nufi gate fuskarsa daure, ta bi sa da kallo
gabanta na faduwa ta dinga addu'ar Allah yasa Sadeeq ya bar layin, kallon box
din da ta boye a Hijab ta dinga yi kafin ta bude a hankali taga babban
dankunnen gwal mai kyau sai talli yake a kwance cikin fancy box din....
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of
coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit
07087865788 to be included in the payment group.
29....
Mikewa Imaan tayi da sauri ta nufi cikin gidan tana waigan ko
Mujaheed ya dawo har ta shiga ta kulle kofa, dakin gwaggwo ta wuce ta boye box
din a cikin trolley dinta, tsoronta daya yanxu Ammi, bata san me xata ce ba
idan ta ga dankunnen, bayan Magrib suna cin abinci tare da Anty Halima da wata
kawarta, wayar Halima ya fara ring, dauka tayi bayan taga mai kiran ta kalli
Imaan tace "Wai ina wayar ki?" A hankali Imaan tace "Yaya ya
kwace min" Halima ta xaro ido tace "Saboda me?" Buda hannu Imaan
tayi alamar bata sani ba, Halima ta mika mata wayar tace "Toh gama magana
tukun" karba Imaan tayi ta kai kunne bayan ta daga hade da yin sallama,
Sadeeq ya amsa mata daga daya barin yace "Har yanxu baki yi charge din
wayar ki bane Imaan?" A hankali tace "Ehh" yace "But naga
akwai wuta ai yanxu, ina ma anguwar" ta langwabar da kai tace "Wayar
na gida fa" yace "Ohk after Isha xan kira ki, it's almost time
now" tace "Allah ya kai mu" daga haka ya katse wayar, Imaan ta
ajiye gefen gado, Halima tace "Haka kawai Mujaheed din ya amshe maki
waya?" Tace "Ehh wai saboda abokin Muhsin na kirana" Bude baki
Halima tayi tace "Toh shi ina ruwansa" Imaan ta buda hannu tace
"Nima ban sani ba" Rabi'ah kawar Halima tace "Yayanki ne
kuma?" Halima tace "Cousin dinta dai" Rabi'ah ta d'an bude ido
tace "Toh ko son ki yake?" Still Imaan tayi tana kallonta da wani
expression, can tace "Yaya ne fa... Yayana ne shi" Rabi'ah tayi
dariya sosai tace "Wai yaya ne, to haka kawai baxai dinga hana ki waya da
samari yana kwace maki wayar idan babu wani abu a kasa" Imaan ta ajiye
cokalin hannunta a hankali tace "Abu kamar me?" Halima tace
"Tukunna dae me yace maki da yaga Sadeeq din na kiran ki?" Imaan ta
jingina da gado tace "Kawai ya hanani waya da shi ne, har blocking dinsa
yyi ni kuma nayi unblocking dinsa, a gida ma da Abba ya kira ni xai tambayeni
meye tsakaninmu da Sadeeq kafin in je ya sameni wai ince ban san sa ba"
Dariya sosai Rabi'ah take, Halima tayi murmushi tace "Tabb, lallai
Mujaheed" Imaan dai sai kallonsu take don bata san me ya basu dariya ba,
Rabi'ah ta ajiye spoon din hannunta tana kallon Imaan da kyau tace "Toh
wllh son ki yake...." Imaan ta xaro ido ta koma baya da sauri tace
"Don Allah ki daina cewa haka plss, wllh yaya na ne fa, Anty Halima yaya
fa ne" Halima tayi wani murmushi tace "As far as ba ciki daya ku ka
fito da shi ba ki daina deceiving kanki Imaan Mujaheed son ki yake, so mai
tsanani ma kuwa, ni dama tun lkcn da yake kawo ki nan few years back ina ganin
irin kallon da yake maki nasan ba a banxa ba da abu a kasa, sannan kulawar da
yake maki ko kanninsa basa samun haka, abinda Mujaheed ke maki a da ya wuce
shakuwa ko so na 'yan uwantaka, ke dai ce ban san lkcn da xaki yi wayo har ki
fahimci inda ya dosa, wai yaya ne... A'a ba yaya ba..." lkci daya hankalin Imaan ya tashi ta fashe da
kuka sosai tace "Wllh ku daina cewa haka ba kyau, ni ba wani so na da yake
yi, ina ce maku yayana ne fa, to taya xai so ni, ni kanwarsa ce fa..."
Dariya kawai Rabi'ah take don imaan tayi mugun bata dariya nan kuma ta yarda
har sannan Imaan na tare da yarinta ba kadan ba sannan ga ta only child shi sa
abun ya taru ya mata yawa, Imaan ta mike da sauri ta fice daga dakin ta koma
wani daki ta xauna kan gado maganganunsu na mata yawo a kai, fashewa tayi da
matsanancin kuka ta fada kan gadon tace "Ni baxan ma kwana a gidan nan ba,
ta ya xa a ce wai yaya na so na, wai yaya fa?? Allah ya kiyaye wllh" Imaan
bata ta6a jin abu ya tsaya mata a rai irin abinda Halima da kawarta suka gaya
mata ba, wai Mujaheed sonta yake, tabbb, ji tayi ita gaba daya duniyar ma babu
wanda take jin haushi kamar Mujaheed din, duk da tasan baxai ma taba yiwuwa ace
yana sonta ba, amma abinda suka gaya mata yasa ita taji bata ma son sa shi a
ido, bata son ganinsa kwata kwata, lamo tayi kan gado very restless, aka bude
kofar dakin ta juya da sauri, Halima ta shigo tace "Gashi Sadeeq ya
kira" Imaan ta mike xaune a hankali ta amshi wayar ta kai kunne tare da
masa sallama, ya amsa yace "I am outside Imaan" tace "Toh bari
in fada ma gwaggo" daga haka ta katse wayar ta tafi ta nemo gwaggo ta gaya
mata, Gwaggwo tace "Toh ya shigo mana ai ba kowa parlon ma, ce masa yayi
shigowarsa kawai" Imaan bata ce komai ba ta sa Hijab dinta ta fita, tsaye
ta gansa ya jingina da motarsa, ta karasa kanta a kasa ta tsaya keeping a
enough distance tsakanin su, kallonta kawai yake, ita ko bata yarda ta kallesa
ba, a hankali yace "What's wrong imaan you look disturbed" da sauri
ta daga kai ta kirkiri murmushi tace "A'a ba komai fa, ya gida" yace
"Lafiya lau" tace "Gwaggwo tace ka shigo ciki ba kowa a parlor"
Yace "No ni baxan shiga ba kunyarta nake ji yanxu" murmushi Imaan
tayi tace "Toh akwai kujeru a compound ai, shi ma baxa ka shiga ba?"
Ya shafa kansa smiling sweetly yace "Ohk then mu je" ita ta shiga
gaba ya bi bayanta har suka shiga cikin compound din. Sai da ta fara xama kan
farin plastic chair sannan ya xauna shi ma yana kallonta, dauke kai tayi ganin
kallon da yake mata yace "Amma ba dai kunyata kike ji ba" murmushi
tayi tace "Shi nake ji mana" Yayi dariya yace "Aa kiyi hakuri
kar ki ji plss" Ita dai bata ce komai ba, bayan few seconds yace "Did
you know what imaan" ta daga kai ta d'an kallesa, cikin sanyin murya yace
"I am hoping to spend the rest of my life with you" Imaan ta sauke
idonta kasa, yace "I was born and bred in Uk, yawancin rayuwata duk can
nayi sa, daga baya na dawo Nigeria gaba daya, I've neva for once thought xan
hadu da mace yar Nigeria inji ina son rayuwa na har abada da ita sai kan ki
Imaan, my ex was white ita ma it's not as if I have much feelings for her, it's
just to while away time... Here in Nigeria frndship kadai ne tsakanina da yan
mata, Ni ban san meye so ba, I don't even believe in it until I met you few
months back, pls don't break my heart imaan, it's too fragile for something
this big...." Imaan tayi murmushi a sanyaye bata dai ce komai ba, yace
"Yea... I have been counting down tun yanxu xuwa ranan da xaku fara waec,
but plss me yasa baxa kiyi waec din a ss2 ba" xaro ido tayi ta kallesa,
yace "Sure, a lot a ss2 suke waec" tace "Aa nafi son inyi
ss3" ya lumshe ido ya bude yace "almost a year to come in sha Allah kenan
fa Imaan?" Imaan ta kallesa tace "Sure" yace "Toh Allah ya
kai mu lafiya" Tace "Ameen" Yace "Promise me something
plss...." Imaan tayi shiru tana kallonsa, yace "Ki min alkawarin baxa
ki yi betraying din soyayyata gare ki ba, and I am also promising u same, I
will and will neva leave u for any reason" lkci daya jikin Imaan yyi sanyi
tace "Ae an riga an san ka gidanmu, so there is nothing to worry
about" yace "Sure an san ni, but I am afraid of ur cousins" da
mamaki tace "Cousins dina kuma?" Ya d'an yi murmushi yace "Yea
kada su min fin karfi...." Imaan ta kasa daina masa kallon mamaki tace
"Su ai yayyina ne ba so na suke ba" Sadeeq ya girgixa kai yace
"I saw their reactions ranan da Abbansu ya kira ni, more especially the
very fair one" Imaan gabanta ya shiga faduwa, Sadeeq yace "They might
not tell you now amma kada watarana su xo su ce suna sonki ki mance alkawarin
mu, kada ki min haka plss Imaan..." cike da damuwa ya fadi haka, imaan ta
ji kamar ta fashe da kuka tace "Ni ka daina cewa haka, ba wanda ke so na
cikinsu duk yayyina ne su wllh, they are only disturb sbda ban gama secondary
schl ba" yace "Toh Allah ya sa haka, amma ba sai kin min kuka ba
gimbiyata, reminder ne" Imaan ta boye fuskarta da Hijab, yyi murmushi yana
kallonta, murya can kasa yace "Kin san inda xan kai ki for our
honeymoon?" Kamr yace ta kara boye fuskarta da Hijab cike da shagwaba tace
"Ni dai bana sooo" yyi dariyarsa mai dadin sauraro yace "Toh na
bari baby, when the time comes xa ki ga, amma fa tare da kaka xa mu" da
sauri Imaan ta bude fuskarta ta xaro ido tace "Aa ba inda xata bi mu"
Sadeeq couldn't help it but laugh yace "Are you serious??" Ita kanta
sai daga baya taji kunyar abinda ta fada ta mike da sauri xata wuce ciki yace
"Noo plss wait dear, ki rakani first plss" da kyar ta yarda ta rakasa
gate tana sinne kai, ya juya yana kallonta kafin yace komai, a hankali tace
"Thanks much for the earrings na gode sosai" Ya mata wani kallo yace
"Bana son ki min godiya idan na baki abu, ba don ki gode min bane na baki"
murmushi kawai tayi bata ce komai ba, nan suka yi, sallama ta daga masa hannu
ta koma cikin gida. Washegari gidan gwaggwo ya xamo ba masaka tsinke saboda yan
uwa da abokan arxiki duk da gobe ne daurin auren, imaan dai na daki duk ta
takura, ita dama haka Allah yayi ta bata da sakewa cikin mutane, babu yanda
Halima bata yi da ita kan ta bi su gidan wata makociyarsu ba don can xata xauna
har gobe sbda mutane amma taki, Har daki Ammi ta kawo mata abincin rana ganin
ta ki fitowa, ganin yanda take yatsine yatsine Ammi tace "Ko dai xa ki
wuce gida ne bana son matsala" girgixa kai tayi tace "A'a kawai kaina
ke min ciwo amma idan na ci abincin xan sha magani" Ammi ta tabe baki ta
fita dakin, imaan ta gama cin abinda xata ci a abincin ta dau maganin ta sha,
mikewa tayi rike da plate din ta fita don kai wa wajen wanke wanke, tun da ta
fito parlor taji numfashinta na tsarkewa ta dai dinga gyaran murya har ta fita
compound, hayaki ne cike gidan saboda wutan icce da aka hura, ta rike
numfashinta da sauri ta karasa ta ajiye plate din ta juya xata shiga parlor ta
saki numfashin, tari ta fara sosai ta durkushe nan bakin kofa mutane suka taho
kanta, Nan Asthma dinta ya tashi duk Gwaggwo ta rikice tana salati, Ammi ta
wuce daki da sauri don duba inhaler dinta a jaka, Aunty da sauran mutanen wajen
suka shigar da ita parlor. Har Imaan ta samu bacci dakin Gwaggwo bayan an rufe
duk windows din an kunna mata fan Halima ta shigo sanye da Nikab a kan Hijab
dinta ta durkusa kusa da ita tace "Sannu Imaan" bude ido tayi amma ta
kasa cewa komai, ba kadan asthman yayi attacking dinta ba wnn lkcn don har sun
yi niyyar tafiya asibiti sannan ya lafa, Kai kawai ta iya gyada mata, Halima ta
dinga kallonta cike da tausayi, Can tace "Sadeeq ma ya kira har sau biyu,
bari in kirasa ince baki da lafiya" Ita dai Imaan bata ce komai ba, Halima
ta kirasa ya katse ya kira ta, tace "Ka kira daxu ina sllh, na taho gida
yanxu na tarar ma Imaan din bata da lafiya" Yace "Subhanallah what's
wrong with her?" Halima ta rasa me xata ce masa da farko don bata san ko
yasan imaan na da Asthma ba, can tace "Gata nan dai a kwance bari in
bata" mikewa Imaan tayi da kyar ta karbi wayar ta kai kunne cikin sanyin
murya tayi masa sallama, cike da damuwa yace "What's wrong with you
dear?" a hankali tace "Naji sauki" yace "But what happened,
dama baki da lafiya ne?" D'an shiru tayi kafin tace "I had an
attack..." Da mamaki yace "Are... you asthmatic?" Ta gyada kai
kamar yana ganinta tace "Um" yace "Subhanallah, to Allah ya
sauwake... is ur breathing now ohk?" Tace "Sure" yace "Xa
ki iya fitowa yanxu?" Ta yi shiru, sai kuma a hankali tace "I will
try" yace "Alryt gani nan xuwa" katse wayar yyi, ta koma ta
kwanta, Halima na kallonta tace "Allah ya sauwake imaan" imaan ta
d'an mata murmushi, Halima tace "ki rike wayar idan ya kira bari xan je
ana jirana na sani" Imaan tace "Toh nagode" daga haka Halima ta
mike ta fita, ba a dau lkci da fitar ta ba Gwaggwo ta shigo da cup din tea ta
xauna gefen gadon tace "Sannu Fatima tashi ki sha shayi na hada maki"
imaan ta mike xaune tace "Gwaggwo ai na ci abinci, a koshe nake"
Gwaggwo xata yi magana sai ga Ammi ta shigo dakin tare da Aunty, aunty na
kallonta tace "Sannu Imaan, ya jikin" imaan ta d'an yi murmushi tace
"Na ji sauki Aunty" Aunty tace "Toh Allah ya kara lafiya"
fita Aunty tayi don xuwa su ci gaba da aikin da su ke yi, Ammi na kallonta tace
"Kirjin yyi sauki?" Imaan tace "Kadan kadan yake min" Ammi
tace "Toh sannu, dama sai da daddy ya guji hakan, nima nasan kawai wahala
xa ki xo ki kara min nan" Gwaggwo tace "Wani irin magana ce wannan
Aisha, ita ta daura ma kanta ciwon ashe?" Ammi dai bata ce komai ba, imaan
ta kalli wayar Halima da ya fara ring, Sannan ta daga a hankali ta kai kunne,
satan kallon Ammi tayi, murya can kasa tace ma Sadeeq "Toh..." Daga
haka ta katse wayar, Gwaggwo tace "Wa ye?" Imaan ta sunkuyar da kai
tace "Ce min yyi yana waje" Gwaggwo tace "Sadeeq?" Imaan ta
gyada mata kai, Gwaggwo ta kalli Ammi tace "Toh ko ya ajiye ta gida
kawai... Ni xamanta nan bai kwanta min ba, ba a fara komai na girki ba fa
ciwonta ya tashi, ina ga gobe da xa ayi girke girke" Ammi tace "Waye
ya kira ki?" Imaan ta kasa cewa komai, Gwaggwo tace "D'an gidan
Bulasawa ne..." Ammi tace "Bulasawa kuma?" Gwaggwo ta kalli
Imaan tace "Ko bata san ki da shi bane??"Imaan tayi kasa da murya
tace "ta san shi" Ammi tace "Na san sa a ina??" Imaan tace
"Abokin ya Muhsin fa" da mamaki ammi tace "D'an Bulasawa ne
dama?" Gwaggwo tace "D'an sa ne na cikinsa, yaro mai hankali da
natsuwa yana yawan xuwa tare da Muhsin gaisheni, ban ma san suna tare da fatimar
ba, akwai wani lkcn dai da ya xo ya sameta a nan, ko tun lkcn suke tare ban
sani ba" Ammi ta kasa cewa komai sai kallon Imaan take, Gwaggwo tace
"To tashi ki je, ki ce masa ya shigo ina nemansa" imaan bata ce komai
ba ta mike da kyar ta sa Hijab ta fita, bayan fitarta Ammi ta xauna gefen gadon
tana kallon mahaifiyar ta tace "Anya kuwa Gwaggwo, d'an wajen Bulasawa fa,
ina shi ina Imaan kuma? Kinsan yaudara tayi yawa yanxu a rayuwar fa"
Gwaggwo tace "Fal yaqul khairan auliyasmut... Bana son irin wannan
maganan, Sadeeq bai yi kama da mayaudari ba
kuma tun kan ya san imaan yake xuwa min tare da Muhsin, ba a taba cewa
d'an mai kudi ne yaron, faram faram yake da kowa, ni dai har ga Allah ya min
kuma xan yi farin ciki idan Allah yasa shi ne mijin imaan" Ammi dai ta
kasa cewa komai har sannan bata daina mamakin wai Sadeeq yaron Bulasawa bane.
Tunda Imaan ta fito Sadeeq ke kallonta, ta sunkuyar da kai tace "Ina
yini" yace "Lafiya lau, ya jikin?" Tace "Na ji sauki"
yace "Tablet kike sha ko inhaler kike amfani da?" Tace
"Inhaler" ya d'an yi shiru kafin yace "Toh Allah ya
sauwake" Tace "Ameen, Gwaggwo tace ka shigo" ya d'an buda ido
yace "Da gaske" ta gyada masa kai, yace "But ba mutane a
ciki" d'an murmushi tayi tace "Idan ka shiga xaka gani" Haka nan
dai Sadeeq ya shiga gidan yana sinne kai, bayan sun gaisa da Gwaggwo, Gwaggwo
tace "Ka taimaka ka ajiye fatima a gida Sadeeq bata ji dadi ba" yace
"Toh In sha Allah Gwaggwo" bai jima a parlon ba ya fita bayan yayi
sallama da Gwaggwo, imaan ta fito daga daki rike da trolley dinta tayi ma Ammi
da Gwaggwo sallama sannan ta bi bayansa... the journey was silent, lta dai ta
jinginar da kanta tana sauke numfashi a hankali, lkci lkci Sadeeq ke kallonta
sai ya sakar mata lallausan murmushi, ita dai sai dai ta sauke idonta, dai dai
gate din gidansu yyi parking, a hankali ta kallesa tace "Nagode" yace
"How will I reach you ltr, ko xaki yi plugging fone naki idan kin shiga
ciki?" Ta d'an yi shiru kafin tace "Ina wayarka" bata jira
cewarsa ba ta dau tsadadden wayar sa dake ajiye
ta yi dialing number din inna yana fara ring inna ta dauka kamar jira
take tana cewa "Ni dai an dameni, tun safe nake aiki ban xauna ba wllh,
waye kuma wannan" murmushi Imaan tayi ta katse wayar, Sadeeq ma yyi
murmushi yace "Number kaka koh?" Ta gyada masa kai ta bude motar ta
fita tana kallonsa, Fitowa yayi ya fiddo mata jakarta yace "Ki huta sosai
idan kin shiga ciki plss" tayi murmushi tace "In sha Allah" yace
"Alright dear, Allah ya kara lafiya" wucewa ciki tayi ta nufi part
din Inna, inna ta dinga kallonta daga sama har kasa tace "Lafiya kika taho
min nan da jaka??" Imaan tace "A'a ni daga gidan gwaggwo nake"
Inna tace "To har na ji sanyi" Imaan dai bata tanka ta ba ta ajiye
jakar ta cire Hijab din jikinta ta kwanta kan kujera, inna tace "Toh har
an gama bikin ne kika dawo ko kuma bikin ne dai garau garau kika gudo?"
Imaan dai bata ce mata komai ba, inna tace "Atoh, ni dama shi sa naki xuwa
kwata kwata, ba ruwana inje in dawo da yunwan cikina, biki ba na yan gayu ba,
kuma dama Habiba bata ce min tana aurar da jikarta ba, ni dai na bada dubu
biyar a kai mata ban bi ta halinta ba, Allah ne xai bani lada" Wani bowl
dake rufe inna ta bude Imaan dake ta kallonta ta leki bowl din daga kwancen da
take taga nama ne soyayye a cike, inna ta saci kallonta suna hada ido ta mike
ta wuce daki da bowl dinta, ba a wani dau lkci ba ta fito da bokitai, ta sa
makulli a kofar dakin, Imaan tace "Fita xa kiyi kike sa makulli a
dakin?" Inna tace "Baxan sa makulli ba sauro su cika dakin su sa min
cuta in bar 'ya yana da wahala?" Tana fadin haka ta fita waje xata wanke
bokitan da ta kwaso, Imaan na kallon film da ake a TV taji muryar inna tana
cewa "Mujaheed kai me cewa inje bikin su gidan uwar Aisha to ga jikar
gidan ma ta gudo daga bikin balle ni karere, ji dai yanda aka dinga facaka da
kaji a bikin kanwarka, toh can ni nasan baxa su yi haka ba, abinda duk na san
su, meye ban sani ba..." Da sauri Imaan ta mike xaune jin wanda inna ta
ambata, Mujaheed dake ta kallon inna yace "Ke dai ki daina haka..."
Inna tace "Ni akwai wanda ya isa hanani fadin gaskiya kuwa duk girman
duniyar nan?? to duk ba wannan ba don bai shafeni ba, inji ka siyo min kazar da
nace maka nake marmari" Mujaheed bai tanka ta ba ya nufi kofar shiga
parlon, da sauri Imaan ta saka Hijab dinta ta rufe har kafarta ta kafe TV da
ido, Mujaheed ya shigo parlon, kallo daya yyi mata ya ajiye ledan hannunsa ya
xauna yana danna wayar hannunsa, Imaan ta ki yarda ta kallesa gabanta sai
faduwa yake, gaba daya she was uncomfortable, Inna ta shigo tace "Allah
maka albarka, kai kadai dama xance ka siyo ka siyo" kitchen ta tafi ta
dauko plate biyu ta xauna kan tabarma tana gogewa ta bude ledan kazar ta raba
biyu, daya nata daya nashi, can dai ta kallesa tace "Toh ita kuma warcan
matar ya xa mu yi da ita, tunda ba da ita aka siyo ba" shi dai Mujaheed
bai ce komai ba, Inna ta tabe baki ta dauko wani plate din ta dau cinya daya da
tsoka daya ta dangwala a plate ta mika ma imaan tace "Toh gashi dai, ido
guba...." Ba tare da imaan ta kalleta ba ta girgixa kai gently tace
"A'a baxan ci ba" Kallonta Mujaheed ya dinga yi da mamaki, inna ma ta
saki baki tana kallonta tace "Dama baki da lafiya shine kika yo min nan
salon ace a nan ciwo ya tashi ni patuu?? don cuta kadai ke hanaki cin kaza ni
dai na sani" Imaan bata ce komai ba bata kuma kalleta ba, can ta mike ta
nufi kofa tace "Ni fa a koshe nake" daga haka ta fice a parlon.
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of
coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit
07087865788 to be included in the payment group
30.......
Imaan na kwance bedroom dinta dab da Magrib taji an danna
bell, tashi xaune tayi don ita kadai ce gidan Ammi na can Unguwar rimi, daddy kuma
bai dawo ba, can ta mike ta sa Hijab dinta ta nufi kofar a hankali tace
"Waye?" Muryar Ummi ta ji tace "Aunty na kiran ki" Imaan ta
bude kofar tana kallonta, a tare suka tafi part din da Ummi, Imaan ta wuce sama
ta bude kofar dakin Aunty, Aunty ta fito bayi bayan tayi alwala tana kallonta
tace "Ya jikin?" Imaan tace "Na ji sauki Aunty" Aunty tace
"Ammi can xata kwana fa, sai ki dawo nan ki kwana ko ki tafi gun
inna" Imaan tace "Xan je gun Inna" Aunty tace "Toh ga
abinci ki dauka" ba musu ta durkusa ta dau warmer din da Aunty ta nuna
mata, Aunty tace "Ki tabbatar kin sha magungunanki bayan kin ci
abincin" Imaan tace "Toh sai da safe" daga haka ta bude kofa ta
fita, a stairs suka hadu da Yusuf, suna hada ido ya dauke kai, tace "Lah
ya Yusuf kayi tafiya ne, ban ganka 2 days ba" Yusuf na ci gaba da haurowa
stairs din yace "Not at all" daga haka ya wuceta ta bi sa da kallo,
can dai ta sauka ta bar parlon. Part din inna ta wuce ta sameta tana sllh, ta
ajiye abincin hannunta a parlor ta fito bakin tap ta daura alwala ta koma ciki,
tana idarwa ta koma kan kujera ta kwanta, inna ta gama addu'o'in da take tace
"Toh wai me yasa kika baro gidan bikin kika dawo?" Imaan tace
"Dama ba kwana naje yi ba" Inna ta tabe baki tace "Toh ita
Rukayya taje gidan kuwa?" Imaan ta girgixa kai tace "A'a bata je
ba" inna tace "Ikon Allah, Kice Amina ce kawai ta je?" Imaan ta
gyada mata kai, inna tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni, tun da uwata
ta haifeni ban taba ganin haka ba wlh, Rukayya bata da xuciya mai kyau sam, ko
da yake abun na da tushe, kinsan lkcn da Bukar ya auro Uwarki bata da aminiya
da ta wuce Amina, lkcn Amina tana nan wata yar duma duma da ita kamar ki latsa
ta jini ya feso, toh a lkcn gida daya Rukayya da uwarki suka xauna sai dai kowa
da sashensa kamar dai Wannan gidan amma ko rabin gidan nan bai kai ba, lkcn
Ahmadu da Bukar na yaku bayi basu da komai sai wahala, tun ba yau fa suke son
junansu in gaya maki, dama a haka kuma suka taso, toh kullum Rukayya bata da
aiki sai neman fitinar uwarki a tsakar gida, kaii Gaskiya Rukayya ta dade tana
hauka, ga uwarki mai hakuri bata biye ta, ga uwa uba kawaici, amma akwai ranan
da xuciya ya debi Aisha ta nakada ma Rukayya shegen duka har sai da ta targada
mata hannu, da kyar aka kwace ta hannun Aisha, ni dai ce ma Bukar da Ahmadu
nayi duk su kora su gidan iyayensu ba ruwana, to sun fa mayar min da gidan
'yaya wajen dambe, a lkcn kuma kullum Amina sai ta xo gun uwarki, tun fa
Rukayya bata san Amina xata aure mata miji ba ta tsaneta har xage xage sun ta6a
yi da jefe jefen dutse, to ana_nan ana_nan Ahmadu ya kyallara ido ya ga yar
duma duma Amina, to karewa ma gun Aisha ya amshi lambarta idan ba mantawa dai
nayi ba, Rukayya na ji tana gani Ahmadu ya aure kawar makiyiyarta wato Aisha,
in gaya maki Aisha ce a kan gaba na komai da bikin, kuma ni nasan da gayya tayi
haka, to da Aisha ma aka raka Amina dakinta gashi gida daya ya hade su da
Rukayya, to kinji musabbabin komai... Ba irin xugar da Rukayya bata min ba kan
in sa ubanki ya kara aure tunda uwarki bata haihuwa ni dai naki, kinsan da
Rukayya yar dakina ce kafin ta xama bala'i, duk da dai nayi masa magana na yi
masa magana har na gaji na kyalesa wato Bukar, to Aisha ta shanye min shi, daga
karshe dai Bukar ya raba fada ya dauke uwarki suka koma Abuja da xama gaba
daya, ai sun fi shekara biyar a Abuja, kuma fa lkcn... Katse ta Imaan tayi tace
"Toh ni dai ban tambayeki ba, wllh har na gaji da jin labarin nan, a wata
sai kin bada labarin nan ya fi sau biyar" Inna tace "Ai ba sai kin
tambayeni ba duk sanda na ga dama dole in bada labari ko da kuwa ni daya ce a
daki, to ina ruwan wani da ni??" Imaan ta tabe baki ta mike ta jona ruwa a
heater don yin wanka, dawowa tayi ta xauna tana jiran ruwan yayi, inna tace
"Ke wai bulasawan na maki waya ma kuwa?" Imaan tace "Ehh"
inna ta d'an yi murmushi tace "Toh madallah, gama wanka ki xo in baki wani
labari mai ban al-ajabi" imaan tace "Ai ruwan bai yi ba ki bani"
Inna tace "Ki dai yi wankan tukun" Juye ruwan Imaan tayi haka ta wuce
bayi inna na cewa "Don Allah idan kin gama ki dauraye bayin da omo, kazanta
dai ba kyau" Imaan dai ba ta tanka ta ba ta cire kayanta ta shige
bathroom. Imaan na gama wanka ta fiddo daya daga sleeping wears dinta dake
press din inna ta saka ta feshe jikinta da turarrukan Inna ta fito ta xauna
tana kallon inna da ke xuba gyangyadi a xaune, murmushi imaan tayi ta dau
remote xata canxa tasha aka bude kofar parlor da sauri ta mike xata gudu xuwa
daki Mujaheed ya shigo, tuni ta shige daki ta sa makulli ta wani hade rai, Inna
da ta bude ido a gigice tace "Subhanallahi, lafiya??" Mujaheed dai na
tsaye sai kallon kofar dakin yake, inna tace "Ni dai ba ruwana, ku dinga
jin tsoron Allah, ya xa a maida min gida kamar filin daga, baka ji yanda xuciya
ta ta tsinke ba wllh, ni dai ana shiga hakkina... Wnn 'ya ta Bukar dai ba ta da
imani an wani laka6a mata Imaan din karya" Shi dai Mujaheed bai ce komai
ba bai kuma fasa kallon kofar dakin ba, wayar inna ya fara ring, kamar xata yi
kuka tace "Kaga wani bala'in koh, toh meye wnn fisabilillahi tsakar dare
kuma" daukar wayar tayi ta danna inda ake picking ta kai kunne hade da
sallama tace "Waye??" Sadeeq yace "Ina yini kaka?" Tace
"Ce maka nayi waye??" Yace "Sadeeq ne" Inna ta bude ido
sosai tace "Bulasawa?" Yayi murmushi yace "Ehh kaka" Inna
tace "Lahh ina yini??" Mujaheed couldn't stop looking at her da
mamaki, Sadeeq yace "Ya gidan kaka?" Tace "A'a lafiya lau wllh
Bukar, ya iyayen ka?" Yace "Suna lafiya lau" inna tace "Toh
madallah, shiru shiru ban ganka ba kwana biyu, Hala imaan ce ta baka lambar
wayata?" Yace "Ehh ita ta ban" Inna tace "Toh ai ta kyauta
wllh, shkkn sai in ba Mujaheed da ya tsaya kaina sandandan ya min saving,
yaushe xaka billo?" Sadeeq yace "Gobe in sha Allah" Inna tace
"Toh Alhmdllh, da kaina kuwa xan maka tuwo da miyar taushe in sha
Allah" Sadeeq yayi yar dariya yace "Toh nagode kaka, imaan din na
kusa?" da sauri inna ta mike tace "A'ahh toh bari in bata har ta
kwanta ina jin, Kasan bata dade da dawowa daga gidan bikin su kakarta ta wajen
uwa ba" Sadeeq yace "Toh ki barta gobe xan kira in sha Allah, dama ke
na kira mu gaisa" inna tace "Ae ko naji ddi Allah maka albarka, maxa
kashe kudin ka na ta konewa" yyi murmushi ya katse wayar. Inna na kallon
Mujaheed ta mika masa wayar tana washe baki tace "Kai yi min saving,
lambar bulasawa ne" Mujaheed ya amshi wayar yana kallon number, Inna ta
xauna tace "Kai amma yaron ya kyauta, wllh na ji dadi, kaga alamar xai
rike min jika da kyau kenan wllh, gashi gobe yace zai shigo, sai in baka dari
biyar dita ka shiga kasuwa ka siyo min kayan miya da nama lafiyayye in masa
miya mai kyau" Mujaheed ya xauna kan kujera har sannan bai daina kallonta
ba, tace "Ka min saving mana Mujaheed kar lambar ya bace" Mujaheed ya
gama danne dannensa ya mika mata wayar ta, ta amsa ta ajiye tace "Dole in
tashi da sassafe kenan gobe, bari ma in dauko maka kudin kar ka manta ka tafi
baka amsa ba in rasa d'an aike" Mujaheed dake kokarin controlling temper
dinsa yace "Ki dai ba Yusuf" inna ta gwalo ido tace "Waye kuma
Yusuf?" Mujaheed bai tanka ta ba tace "Toh bari kaji, Rabonsa da ya
tako nan ya gaida ni tun ran da yyi abun kunyar nan, to dama idan ya xo da wani
idon xai kalleni, A'a ba ruwana ni bana bukatansa dama, ga dai ka"
Mujaheed na gyada kai yace "Ita kuma yarinyar nan kice mata wllh idan ta
sake ganina ta kwasa a guje sai na sa ta kuka a gidan nan" inna tace
"Oh oh Allah, yau naga jaraba, baxata gudu ba kana cutar ta Mujaheed? nine
fa na koya mata ta dinga gudu idan ta ganka, toh me xata tsaya ta maka idan ta
ganka, ni dai ba ruwana, ka dinga tsoron Ubangijin ka, ai ta ma kusan aure ta
huta da fitinar ka sai in ga ko gidan mijin xaka bi ta kana cuta kuma,
karshenta sai ka kare a kurkuku don Bulasawa daure ka xai yi a fita da kai
kasashen turai ai maka hukunci, ka ga sai ka bar Ahmadu da Bukar da kashe
makudan kudaden da suka fi karfinsu, idan ba haka ba kuma ka ru6e a kurkuku in
shiga uku" mikewa Mujaheed yyi ya nufi kofa fuska daure, inna tace
"Toh kudin cefanen pa, baka amsa ba fa? Ko xaka siyo min da kudin ka"
Washegari da safe Imaan na shan shayin da inna ta hada mata, inna tace
"Wai me yasa kike gudun katon can ne, halan laifi kika masa" Imaan
taki cewa komai da farko, can kuma tace "Ba komai, ni bana son yana kulani
a gidan nan nima kuma na daina kulasa, don Allah ki taya ni gaya masa
inna" on a serious note ta fadi hakan, Inna tace "Toh ai hakan yafi
ma, kinga babu ta yanda xai dinga cutarki kuma, wahalan da yayi a kanki a baya
Allah ya saka masa, idan kuma biyansa yake son ayi sai ya fada min nawa ne bai
gagareni in daga daya daga gidajena na gado in siyar in biyasa ba, kuma ba
karamin aikin Bulasawa bane ya siya min wani ma a kasashen turai in xuba yan
haya" Murmushi imaan tayi ta mike ta dauko mata dankunnen da Sadeeq ya
bata, inna na budewa tace "Wannan ai gwal ce, a ina kika samo Imaan?"
Imaan tace "Shi ya bani" Inna ta xaro ido tace "Mujaheed
din???" Imaan ta hade rai tace "Sadeeq dai" Inna ta saki wani
kabbara tace "Kinga abinda nake nufi ko, to a xamanin nan wa xai ma naka
haka?? Wllh ki rike yaron nan da kyau kai ko su Maimoon kada ki yarda su san
abinda kike ciki balle wancan mutumin Mujaheed, 'ya yan Ahmadu ba wani tsoron
Allah garesu isasshe ba, duk yan bakin ciki ne, ki bar wannan gu na in ajiye
maki, ana nuna ma su Ahmadu dama cewa xa su yi a mayar tunda ba hankali ya ishe
su ba, shi ma mutumin nan Mujaheed yanxun nan xaki ga ya shigo wai gaisheni bai
san ni damuna yake ba, maxa dauka ki wuce da shi ciki kada...." Bata rufe
baki ba aka bude kofa, Abba ya shigo da sallama Mujaheed na biye da shi, Inna
ta boye dankunnen a karkashin carpet, a hankali Imaan tace "Ina kwana
Abba" Abba yace "Lafiya Imaan, naji baki da lafiya, ya jikin
naki?" Kallonta Mujaheed yyi da sauri, tace "Naji sauki Abba"
Abba yace "Toh Allah ya sauwake" tace "Ameen" kallon inna
tayi tace "Inna zan je dauko kayana" inna tace "Toh yi
maxa" tashi tayi ta nufi kofa ta fita, Mujaheed ya fara danna waya ya kai
kunne sai kuma ya mike ya fita yana cewa hello, Imaan na shiga parlon ta nufi
dakinta don har Daddy ya fita ganin bata ga motarsa a parking space ba, tana
dauko kayanta ta ji an bude kofa, ta juya da sauri tana kallon kofar dakinta, can
dai ta nufi kofar ta murda, Mujaheed ta gani tsaye kusa da kofar dakin nata,
Xata gudu ya fixgota waje fuska daure yace "Ni dodonki ne kike gudu
na?" Kuka ta fara yi a rikice taki yarda su hada ido tace "Ban son
hka ni ka sake ni yaya" kallonta ya dinga yi kafin yace "Meyasa kike
gudu idan kin gan ni" sosai xuciyarta ke bugawa tace "Ba komai, ni ka
sake ni plss" ya sauke idonsa daga kallonta, can yace "What's wrong
with you?" Da kyar tace "Ni na ji sauki" saketa yyi ya juya ya
fita, ta durkushe wajen har sannan xuciyar ta bai daina bugawa ba. Da yammacin
ranan Imaan na durkushe bakin tap din inna tana alwala kamar ance ta daga kai
taga Sadeeq yana tahowa, da sauri ta rufe gashinta ta xaro ido, murmushi yyi,
yana isowa inda take murya can kasa yace "Good evening dear, sae ynxu xa
ki yi la'asar?" Bata iya tace masa komai ba ya tsaya bakin kofa yyi
sallama cikin cool voice dinsa, Inna ta fito daki tana amsa sallaman, shiga
yayi tace "Au, sannu da xuwa Bukar ashe kai ne" ya xauna yana murmushi
yace "Ina yini kaka?" Tace "Lafiya lau Bukari, ya aiki?"
Yace "Alhmdllh mun gode Allah" tace "Toh ya xafi xafi, ko da
yake ma akwai Ac ko ina yanxu" Yayi dariya yace "Haka ne kaka"
Tace "Toh madallah, bari in kawo maka ruwa da lemo" bata jira cewarsa
ba ta debo masa su a fridge ta ajiye, tace "Toh nayi tuwo na ajiye maka
ina bacci wannan mutumi Mujaheed ya shigo ya cinye"
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of
coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit
07087865788 to be included in the payment group.
31......
Sadeeq yyi murmushi yace "Wani lkcn ai sai ki min
kaka..." Inna tace "Toh in sha Allahu kuwa, yanxu ya maganar da muka
yi ranan Bukar?" Sadeeq yace "Kaka Abbana baya kasar ne, ina jiran
sai ya dawo in sha Allah sai ayi magana" inna tace "Toh da kyau,
Allah maido da shi lafiya, ai dama Bulasawa bai fiye xama ba aka ce, baya can
baya nan, to abun ka da babban mutum fitattce..." yar dariya kawai Sadeeq
yyi, sun fi minti talatin da inna dake ta basa labarin da ya kamata da wanda
bai kamata ba, daga karshe ya ajiye mata dubu ashirin yyi mata sallama, xaro
ido tayi tace "Kai dai baka gajiya Bukar, wancan ma da ka ban har yau basu
kare ba wllh suna can na adana su sbda yaran gidan nan, toh ni dai nagode Allah
ya maka albarka, ya kara maka budi" yana murmushi yace "Ameen kaka,
nima nagode" inna tace "Toh ka gaida uwarka ka ji, wataran duk xamu
san juna idan Allah ya yarda, to ya sunan uwar taka?" Yana murmushi yyi
kasa da kai yace "Hajiya Khadijah..." Inna tace "Lahh sunan
aminiyata a da kafin ta xama abun gudu, Allah sarki Hadiza ko ana wace duniyar
yanxu kuma" Dariya kawai Sadeeq yyi yana kallonta, Inna tace "Allah
ya sa mu yi kyakkyawan karshe dai, amma Hadiza bata yi abun kirki ba, ga son
abun duniya Allah ya dora mata, wai..." Kofa ya nufa yana nurmushi yace
"Sai na sake shigowa kaka" ta mike da sauri tace "Toh Bukar a
gaida gida, Allah maka albarka" ya amsa da "Ameen" ya fita,
Kalle kalle compound din kawai Sadeeq ke yi bayan ya fito amma har ya kusa gate
bai ga alamar Imaan ba gashi wayar ta har sannan a kashe, mota ce ta shigo
gidan driver yyi parking, aka bude motar umma ta sakko tare da Hajiya Balaraba
suka bude bayan mota suka dinga fiddo manyan ledoji, Gaishesu Sadeeq yyi, Umma
ta kallesa ta amsa tana ci gaba da fiddo ledojin, ya wuce su, sai da suka nufi
entrance din shiga gida Hajiya Balaraba tace "waye wancan kuma" Umma
tace "Kila wajen Yusuf ya xo" Hajiya Balaraba yace "Dama Yusuf
na gari, ni na xata bai nan, duk na xo bana ganinsa" Umma ta tabe baki
tace "Yana nan, kinsan sa bai fiye faram faram da mutane ba, ko yana gidan
ma to idan bai dakinsa yana bangaren fitinanniyar kakarsu" Hajiya Balaraba
tace "Shi yasa, amma na fi ganin Mujaheed" Umma tace "ko kwana
hudu ba ayi ba aka gama wani case a gidan nan, wai Yusuf ya rasa warce xai fito
yace yana so sai yar wajen Aisha" Hajiya Balaraba ta xaro ido tace
"Yar wajen Aisha kuma, to sai aka yi yaya?" Umma tayi wani murmushi
tace "Ai ba xancen ma yanxu haka, kakarsu dai tace ko bayan ranta bata
amince da auren ba, kuma a ranan na shirya na je wani waje aka ce in kwantar da
hankalina ba matarsa bace ba ma, wannan dai Hafsar ita ce matarsa kuma wai
kwanan nan xa ayi bikin, kila a hada tare da na Mujaheed, tunda gashi har mun kusa
gama hada lefen nasa" Hajiya Balaraba tace "Ke ma dai da daukan ma
kai, to meye xaki wani damu a kan lamarin d'an kishiyar ki??" Umma tace
"Ashe ma baki gama sani na ba kenan duk kusancin mu Balaraba, ni xan so
abu mai kyau ya ra6a Aisha da 'yar ta, Yusuf ai abu ne mai matukar kyau, idan
ya auri yar wajen Aisha ai ba karamin dace yarinyar tayi ba, ga arxiki ga shi
da hankali da natsuwa, toh ina xan yarda, kiri kiri fa kun ga bakin cikin da ta
dinga nunawa lkcn bikin Seeyama, babu abinda ta ta6uka da bikin sai dai ta leko
ta koma, da aka tashi kai Seeyama ma ita ce karshen tafiya sannan farkon dawowa
duk sbda hassada, shine xan yarda abun kirki ya sameta ita ma, inaa ai tunda
naji ance min ba matarsa bace hankalina ya kwanta, sai ga kakarsu ma tace samm ba
da yawunta ba" Hajiya Balaraba tace "Toh Alhmdllh" Hajiya
Balaraba ta shiga jera tulin inner wears din da suka siyo kasuwa a daya daga
akwatina takwas dake dakin Umma, Umma tace "Dole ma Mujaheed ya xo ya kara
kudi, don wannan da ya rage ba isa xai yi ba don har gwal ina son mu saka a
kayan, ko da dankunne da sarka da xobe ne kawai banda awarwaro" Hajiya
Balaraba tace "Gaskiya kam, xa ma su fi ganin lefen da mutunci, to shi
gogan na duba kayan ma kuwa?" Umma tace "Idan an gama hadawa sai su
duba tare da ubansa, in sha Allahu kafin karshen watan nan xa a gama komai, su
tafi su kai gaisuwa tare da sadaki da ubansa" Imaan na tsaye kitchen tana
wanke plates a sink Ammi ta shigo tace "Kina da card a wayar ki in kira
daddy nayi missing calls dinsa, mine is exhausted" Imaan ta juya ta
kalleta da farko rasa abinda xata ce mata tayi, can a hankali tace "Ammi
wayana baya wajena tun 3 days ago fa" Ammi na kallonta da mamaki tace
"Baya wajen ki? To yana ina?" Imaan tace "Yaya ne ya amshe, ni
kuma ban tambayesa ba har yau" Ammi ta wani hade rai tace "Wato ke
baxa ki ji magana ta a gidan nan ba ko Imaan, ban raba ki da Mujaheed ba?"
Imaan tace "Wllh Ammi ni na daina kulasa a gidan nan ki tambayi Inna, idan
ma yaje part din inna ni shigewa daki nake ko in taho gida, wllh na daina
xaunawa inda yake ma, kuma da ya amshi wayar ni ban tambayesa ba har ynxu, ban
ma san wayar kuma ko ya bani" Ammi tace "Toh yayi kyau, xan ji ko shi
ya siya maki wayar" Imaan tace "Wai don sbda Sadeeq na kirana fa
shine ya karbe" shiru Ammi tayi tana kallonta, can tace "Toh ina
ruwansa da kiran Sadeeq din?" Imaan ta bude hannu alamar bata sani ba,
Ammi ta juya ta fice daga kitchen din. Da rana Aunty ta shigo parlon su Imaan
da sallama, Imaan dake cin abinci parlor tace "Sannu da xuwa Aunty"
Aunty tace "Yauwa Imaan, Ammi fa?" Imaan tace "Tana daki"
direct bedroom din Ammi Aunty ta wuce, Ammi dake jera kayan guganta a press ta
ajiye kayan hannunta tace "Yanxu nake son gamawa inje in maki ban gajiya
Hajiya sai kuma ga ki" Aunty tace "Nima ban gajiya na xo maki
ai" gaisawa suka yi Aunty ta xauna gefen gadon Ammi tace "Halan daddy
ya koma" Ammi tace "Ehh tun jiya ya koma, ya su Maimoon fa, kwana
biyu ni ban ga Yusuf ba ko tafiya yyi babu sallama" Anty ta tayi murmushi
don har sannan tasan Ammi bata ji abinda Inna ta masa ba tace "Yana nan
kuwa, amma next week xai tafi Abuja ina jin, aiki ne fa ya same mu in gaya
maki..." Ammi ta xauna tace "Wani aikin kuma?" Aunty tayi yar
dariya tace "D'an ki ne yyi min transfer daxu yana son mu fara hada masa
lefe" Ammi tace "Yusuf?" Aunty tace "Ehh fa" Ammi tace
"Ikon Allah, toh Allah ya bamu iko, Hafsar ce dai?" Aunty tace
"Ehh ita" Ammi tayi dariya tace "Allah yayi kenan, kwanaki fa da
nake tambayarsa ita ce min yyi shi fa ba ita xai aura ba, nace to wacece sai
yace tana nan wataran xa mu santa" Aunty ta d'an yi murmushi tace
"Toh dai jiya ce min yyi Hafsah" Ammi tace "Toh Allah yasa
albarka, ya kuma sanya alkhairi" Sun d'an taba hira daga karshe Aunty tayi
ma Ammi sallama, Ammi ta rakata har balcony tana ce mata sai ta leko ita ma.
Tun daga wannan rana imaan ta fara wasar yar buyan gaske da Mujaheed, part din
innan ma gaba daya bata son xuwa sai dole shi ma kai mata abinci, tana ajiye
mata kuwa ko xaunawa bata yi xata juya ta bar wajen, Kwata kwata ita dai ba ta
son ma su hadu, da ta tuna maganganun su Aunty Halima da Rabi'ah sai wani
haushin sa ya diran mata, wai yana sonta, kai ta ma san kawai labarin su Anty
Halima ne, ta ya yaya xai so ta, yanxu kam Sadeeq ta wayar Ammi yake kiranta
dama da taji ring din wayar xata tafi da sauri ta duba ko shi ne, tun Ammi na
complain har dai ta gaji ta daina. Yau da daddare Imaan na kwance parlor suna
kallo tare da Ammi dake xaune aka danna bell, mikewa tayi ta sa Hijab ta nufi
kofar ta bude, ido hudu suka yi da Mujaheed dake tsaye bakin kofar, gabanta ya
fadi sosai tayi saurin juyawa ta basa hanya, ya shiga parlon yyi ma Ammi kallo
daya ya sunkuyar da kai ya ajiye ledan hannunsa yace "Ina yini" tace
"Lafiya lau, ya aiki" Yace "Alhmdllh, dama Abba ne yace in kawo
wannan" Ammi tace "Toh Allah amfana" Yace "Ameen, sai da
safe" Daga haka ya juya ya nufi kofa ya bude ya fita ya kulle kofar, Ammi
ta bude ledan taga gasasshiyar kaza ce babba, duk son imaan da kaza kin ci tayi
wai ta koshi, har hakan ya ba Ammi mamaki sosai, Ammi ta debi kadan ta kai
sauran fridge ta ajiye. Ana saura few days su yi resuming schl ranan Friday da
yamma sadeeq ya kira ta wayar Ammi, Imaan ta dau wayar da ke dakin ta yawanci,
bayan sun gaisa yace mata yana waje, xaro ido tayi a hankali tace
"Toh" daga haka ya katse wayar, Fitowa tayi daga dakinta gabanta na
faduwa ta tafi dakin Ammi ta makale bakin kofa tana kallonta a hankali tace
"Ammi ana kirana a waje" Ammi tace "Wa ke kiranki??"
sunkuyar da kai tayi ta rasa wa xa tace don tun ranan da ta ambaci sunansa a
gaban Ammi Ammi tace mata bata da kunya sunan Mahaifin nata take kira gatsau,
to yanxu kam bata san ya xata kirasa ba, Ammi tace "Toh kar ki dade a
waje" d'an murmushi tayi tace "Toh Ammi" daga haka ta fita
dakin, as usual Hijab dinta har kasa ta saka ta fito, kamar mai tausayin kasa
take tafiya har ta isa gate, Yana ganinta ya bude motar ya fito ya rungume
hannayensa yana kallonta daga glass din idonsa, ta sunkuyar da kai har ta isa
kusa da motar, cikin sanyayyan murya tace "Ina yini?" Yace "Lafiya
lau dear, ya gida?" Tace "Alhmdllh" yace "Baki jin dadi ne,
you look pale" tayi murmushi tace "A'a lafiyata lau" yace
"To kaka fa, ko xa ki rakani in je in gaisheta" ta xaro ido tace
"A'a ai bacci ma take" dariya yyi yace "Sure?" Tayi
murmushi bata ce komai ba, yace "Ya Ammi" tace "Lafiyarta
lau" yace "I want to take you out for shopping ko tare da cousin
sisters din ki ne xata yarda?" Imaan ta xaro ido tace "A'a baxa a bar
ni ba" yace "Ohk then" Shiru tayi bata ce komai ba shi ma haka,
ta d'an daga kai suka hada ido, da sauri ta dauke kanta, murmushi yyi yace
"On Monday xa ku yi resuming third term ss2, I am still counting fa"
yar dariya tayi bata ce komai ba, yace "Yea, ss3 kuma term daya kawai xa
ku yi shkkn, just few months to go in sha Allah" Imaan dai ba ta ce komai
ba ta dinga kallon motar Mujaheed da yyi parking a nan waje maimakon ciki don
har mai gadi xai bude gate sai kuma yaga yyi parking a waje, fitowa Mujaheed
yyi daga motar kana ganinsa kasan daga asibiti yake, Imaan ta sunkuyar da kanta
da sauri, Suna hada ido da Sadeeq har xai shiga gate sai kuma ya fasa ya nufe
sa, Sadeeq yyi murmushi ya mika masa hannu hade da masa sallama, Mujaheed ya
amsa yace "Ya aiki?" Sadeeq yace "Alhmdllh, wlcm back" d'an
murmushi Mujaheed yyi ya juya ya nufi gate, sai bayan da ya shiga ciki Sadeeq
na kallon Imaan da mamaki yace "Why didn't you greet him?" Tace
"Ba ma shiri yanxu" ya buda ido yace "Why??" Tace
"Nothing" Sadeeq yace "Uhn OK, nima daga hospital nake nace let
me branch and see you pretty face" Tayi murmushi ta boye fuskarta, wani
leda ya ciro ya mika mata, ganin bata ma san yana yi ba sbda fuskarta da ta
rufe a hankali yace "Take dear" xame hannunta tayi ganin leda yake
mika mata ta xaro ido tace "What?" Yana kallonta affectionately yace
"Take plss" bata fuska tayi tace "Aa thank you bana so"
yace "Karba plss" tace "Aa Ammina xata min fada" Shiru yyi
yana kallonta, ta girgixa kai tace "Wllh Ammina xata min fada" Yace
"Toh shikenan" cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri" yyi
murmushi yace "Na yi, kar Ammi tace kin dade, ki shiga ciki" tace
"Toh nagode" Yace "No thanks dear, bari in shiga in gaida
kaka" imaan ta xaro ido tace "Ae bata tashi ba" yace "Ehh
xan tasheta" daga haka ya nufi cikin gidan ta bi sa da kallo, Inna na bakin
tap ya sameta, ta mike tana washe baki tace "Allah sarki Bukari ka xo min
gaisuwar juma'ah ne" yana murmushi yace "Ehh kaka" tace
"Toh shiga ciki ka xauna, bari in dauraye wajen nan in shigo" yace
"Toh kaka" shiga parlon yyi ya xauna, Inna ta gama dauraye daurayenta
ta shigo tace "Toh ya mutan gidan Bukar?" Yace "Alhmdllh kaka,
dama sauri nake, nace bari in shigo mu gaisa, ga wannan a ajiye ma imaan"
ajiye ledan hannunsa yyi, Inna tace "Atoh bari in shiga da shi ciki, Allah
yayi albarka" daga haka ta wuce ciki da ledan, sai ga ta ta dawo da bowl
dauke da dambun nama, ta shiga kitchen ta dauko leda ta fito ta juye a ciki
tace "Gashi nan jiya nayi ni kadai rai na wllh, ko yaran gidan ban tsamma
ba ma" Yana murmushi yace "Toh nagode kaka"
Imaan ta ajiye abincin hannunta tana kallon inna tace
"Ina yini" mikewa inna tayi tace "Jira ni in dauko maki sakon
ki, ni dai idan Bukar ya dawo xan ji ko Aisha ce ta hanaki xuwa bangarena
yanxu, banda haka taya kina ajiye min abinci sai ki gudu kamar ana koranki,
Aisha dai bata isa ta raba ni da ke ba tunda ba ita ta haifa min ubanki ba,
idan ma ita ke hure maki kunne duk xan ji idan Bukar ya dawo, ni ba
ruwana" imaan ta bi ta da kallo tana tabe baki, bata dau lkci a daki ba ta
fito rike da ledan da Sadeeq ya bata tace "Wannan yaron kirkin ne ya xo
daxu yace in baki, ko meye a ciki oho, kila wani zinarin ne ma, ni dai ban bude
ba don ban gaji cin amana ba" Imaan ta xaro ido tana kallon ledan, can
tace "Me yasa kika karba inna?" Inna ta hade rai tace "Toh baxan
karba ba? A garin fulanawa kika ga ake maida hannun kyauta baya? Idan baki so
sai ki bar min babu abinda ya sha min kai, ni ina so" wani kallo imaan ta
mata ta bude ledan, still tayi tana kallon kwalin tsadadden waya da ake yayi,
Inna ta saki wani kabbara tace "Toh idan ba Sadeeq din ba dama waye? Wa gare
ki banda Allah sai shi din? Ko Bukar baxai siya maki dankareren waya haka ba
balle Ahmadu" Imaan dai ta kasa cewa komai gabanta sai faduwa yake, Bude
kofar parlon aka yi, Mujaheed ya shigo da sallama hannunsa rike da ledan fruit
inna na washe baki tace "Mujaheed kalli wayar da yaron nan Sadeeq ya siya
ma Imaan, ni nasan yayi dubu dari biyar" Mujaheed ya ajiye ledan hannunsa
yana kallon kwalin wayar, Imaan ta mayar da wayar leda taki yarda ta kallesa ta
mika ma Inna tace "Ki ajiye min" inna ta karbi ledan da sauri tace
"Toh, nima dai na fiye surutu wllh" daga haka ta mike ta shige daki,
Imaan ta mike ta fice daga parlon da sauri. Washegari asabar inna na daki ta ji
an bude kofar parlornta ta fito tana tambayar waye, akwatuna taga ana shigowa
da, ta saki baki tana kallon akwatunan tace "Meye wannan kuma?"
*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of
coffee*🤷🏻♀️
It's 300 via Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit
07087865788 to be included in the payment group.
32....
Umma ce ta shigo parlon da sallama, su Ummi da Rahma da
Maimoon suka xauna kan kujera Inna ta kalli Umma sannan ta kalli akwatunan tace
"Lafiya Rukayya?" Umma ta xauna kan lallausan rug din parlon tace
"Ina yini inna?" Inna tace "Cewa nayi meye wannan, daga
ina??" Hajiya Balaraba da Hajiya Saude dake tsaye su ma sun shigo parlon
suka gaisheta, Inna ta xauna kan kujera a fusace tace "Oh oh Allah, ni da
ban yini ba xa ku gan ni, akwatunan meye wannan ake shigo min parlor
dasu?" Hajiya Balaraba tace "Na lefe da xa a kai ne" Inna ta
xaro ido tace "Lefen wa?" Hajiya Saude dake d'an tabe baki tace
"Wacce Mujaheed xai aura..." Inna tace "Wani Mujaheed din?"
Shiru duk suka yi basu bata amsa ba, Inna ta dinga sakin salati a jere, can
tace "Yanxu Mujaheed aure xai yi ban sani ba sai dai inga akwatuna ana
kokuwan shigo min da su ace min xa a kai lefe? Yanxu Rukayya mancewa kika yi ni
na haifi Uban Mujaheed? Ehh lallai Ikon Allah ya fi gaban haka" daukar
waya tayi ta mika ma Umma tace "Kira min d'an nawa.." Umma da ta
daure fuska ta karbi wayar tayi dialing number Abba ta mika mata, Inna ta karba
ta kai kunne, Abba na daga wa Inna tace "Yanxu Ahmadu ko ba raina kai ba
mai ambatan sunana bane kace.... Allah sarki Inna, gashi Allah yayi lkcn auran
Mujaheed baki a doron kasa balle ki sa albarka ke ma, Amma duk da haka muna
maki fatan rahaman Allah... balle da raina da lafiyata Ahmadu?? wai sai dai
inga katuwar matar ka na shigo min da jakunkuna tace min xa su kai lefe, yanxu
ko shi Mujaheed din da nayi bauta da shi yana tsumma na cancanci yaki fadi min
xa a kai lefensa sai dai inji a duniya? Wayyoo duniya Ina xa ki damu...."
Bata jira cewar Abba ba ta katse wayar ta jefar kan kujera ta fashe da kuka
tace "Oh oh Allah, duniya dai ba gaskiya, mutane basa jin tsoron
Allah..." Hajiya Saude tace "Hajiya ba fa kai kayan xa ayi ba yanxu,
kawai dai an gama hada kayan ne aka ce bari a xo a nuna maki, Amma ko gaisuwa
ma ba a kai ga kai ma iyayen yarinyar ba tukun" Inna ta daga kai ta
kalleta tace "Ai Rukayyar nan da kike gani ba mutum bace, idan uwarta ce
Hadiza xata mata haka, Ina ce ranan da xa a fara hada kayan lefen ya kamata ta
tako ta xo ta sameni tace to Inna gashi gashi, amma da yake xuciyarta ba tsoron
Allah ban ganta ba, ni dai ba ruwana, kowa yyi da kyau.. kansa, bari kuma
Ahmadun ya shigo in ji ko shi yace a boye min har sai an gama hada lefen"
tana fadin haka ta Mike tana kakkabe kujerunta, mikewa Umma tayi tana kallon
kawayenta da su Ummi tace "Ku kwasa mu je" Inna ta juyo da sauri tace
"A kwashi me?? Ai ba ke kika min wahala da Mujaheed din ba, kuma da kyar
idan ba da ni xa a kai lefen ba ma, don haka kada warce ta taba jakunkunan nan
duk kuyi ta kanku ku fita ku bar min parlona in goge, nakudar Mujaheed kawai
kika yi da haihuwarsa amma ni na masa abinda ya fi wannan, irin wahalar da nayi
da shi ba sai dai Allah ya saka min ya biya ni ba, kuma shima Mujaheed din xai
shigo ya sameni, idan bai ma yi hankali ba ma sai ince na bar sa da
Allah..." tsayawa Umma tayi tana kallonta bacin rai karara fuskarta, tuni
su Hajiya Saude suka fice a parlon, Ummi da su Maimoon suka bi bayanta, Inna ta
juya tana kallon Umma tace "Ki fita don Allah xan goge daudar da ku ka
shigo min da shi Rukayya" juyawa Umma tayi ta fice, Tsaye ta tadda
kawayenta suna jiranta, Hajiya Saude tace "Amma gaskiya Hajiya Rukayya
kina fama, yanxu haka kike xaune da wannan bala'eyyiyar tsohuwar nan har yau?
Har yanxu kin rasa yanda xa ayi da ita ne?" Umma ta sauke wani ajiyar
xuciya tace "Ku bari kawai, yanxu ina tanka ta abinda xata tsara ma d'an
ta daban, shi kuma duk hakurinsa kika kuskura kika taba masa mahaifiya to babu
xaman lafiya ranan, shi sa nake mata shiru" Hajiya Balaraba tace "Ke
ma dai wllh, toh kin kasa yin komai a kanta ne?" Umma tace "So nawa
kuma, sai dai Allah ya kyauta kawai, Amma wannan matar da ku ka gani ku kyaleta
haka kawai" Hajiya Saude tace "A'a baki dai yi abinda ya dace bane,
nima fa haka uwar mijina take a da amma ba yanxu ba kuma wllh, duk da nata bai
kai na tsohuwar nan ba ma, Amma wllh ynxu sai labari, gaba daya gidan sai yanda
nace ake yi, ina xan iya wahala??" Umma tace "Toh mu je ciki sai inji
ya xa muyi, wllh na gaji, ita ce babban matsalata a gidan nan" Hajiya
Balaraba tace "Toh kayan da ta hana fitowa da su fa?" Umma tace
"Kayan xa su dawo hannuna in sha Allah, Mujaheed ne kadai ya isa ya fiddo
da kayan daga parlon nan ko ubansa bai isa ba, kuma shi xan sa bari dai ya
dawo" Hajiya Saude tace "Toh yaushe xa a tafi kai gaisuwar ne?"
Umma tace "Uban cewa yyi sai kaninsa ya dawo Abuja, ae tuni na rufe
bakinsa shi ma, komai nace cewa yake tohh" Duk suka kwashe da dariya suka
shiga cikin gidan. Da magrib Imaan taje kai ma Inna abinci ta dinga kallon
akwatunan da Inna ta jera a parlonta gwanin ban sha'awa, Inna ta shafe addu'an
da take tace "In fiddo maki sabuwar wayar taki ne yanxu" Imaan tace
"Inna wannan akwatunan fa?" Inna ta tabe baki tace "Daxu wannan
mata Rukayya suka shigo da su wai ashe har xa a kai ma Mujaheed lefe bani da
labari, Ina nan xaune kamar fanko" Imaan ta xaro ido tace "Aure xai
yi Inna?" Inna tace "Ai shine nake jira Ahmadu ya dawo mu ji idan
bola aka maida ni a gidan nan ban sani ba" Imaan da har sannan ke kallon
akwatunan da surprise tace "Waow wllh sun yi kyau sosai, yanxu gidansu
Aunty farida xa a kai kenan" Inna tace "Toh wacece dama banda ita,
duk da dai iyayenta yaku bayi ne yarinyar na da hankali kuma ban jin xata gaji
da ni idan na koma gidan Mujaheed da xama, lafiya xa mu xauna da yarinyar, ke
kuma duk sati sai ki dinga xuwa kafin lkcn naki da bulasawa yayi" Imaan ta
fara dariya ta xauna Inna tace "Toh bude mu ga tsiyar da suka xuba
mata" Imaan na murmushi ta dinga sauko da akwatunan, sannan ta bude daya
daga manyan ciki, xannuwa ne tsadaddu kwance a ciki, Imaan ta dinga fiddo su
tana ajiyewa Inna na dauka tana duba kasan xannuwan don ganin ko babba ne ko
karami, can ta tabe baki tace "Kin san Rukayya akwai shegen karya, ko sata
xata iya sa Mujaheed yyi don tayi fafa, Toh xannuwa dai gasu duk masu tsada sai
a xo a fidda min nawa da na takwarata a ciki" Imaan dai bata ce komai ba
sai murmushi kawai take, ta bude wani akwatun, ta shiga fiddo laces masu suna
lace, Inna ta rike ha6a tace "Ehh lallai Rukayya makaryaciya ce, wnn ai
sai ta talauta min jika, Toh wannan ma sai a fidda min daya inyi doguwar riga,
idan kyalle ya rage in baki a maki joni" Imaan dai bata ce komai ba ta
bude akwatuna mai dauke da jallabiyoyi tsadaddu, Inna tace "Ki xabi wanda
ya maki a ciki...." Imaan ta xaro ido tace "Innaa?" Inna ta hade
rai tace "Toh sai su fidda min in baki" Akwatin dake dauke da takalma
da jaka Inna ta bude, ta fiddo wani takalmi mai kyau sosai tana kallon imaan
tace "Gwada wannan mu ga" imaan ta wani xaro ido a fusace Inna tace
"Don Allah ki gwada" mikewa Imaan tayi xata sa takalmin aka bude
kofar parlon Mujaheed ya shigo da sallama.
Afuwan it's short, gobe da safe xan yi update in sha Allah, I
was kinda busy gaba daya yau ne. Tnxx.
Imaan isn't free, it's 300 via Fcmb 3276052019 Hauwa Bello
Jiddah.
33.....
Kallonsu Mujaheed ya dinga yi, Imaan ta sunkuyar da kanta ta
ki sa takalmin xata xauna, a fusace Inna tace "Ji walakanci don Allah, ba
cewa nayi ki gwada ba?" Imaan ta hade rai tace "Toh nawa ne da xan
gwada?" Inna tace "Oh oh Allah, yau naga fitina, to Ina ruwana da ko
na waye, ni dai ba kawai in cire ma takwarata ba tunda ni baxan iya sa wa ba??
Ki gwada don Allah" Imaan dai bata ce mata komai ba ta xauna, Inna ta
ajiye takalmin gefenta tana kallon Mujaheed dake tsaye tace "Toh da kaki
gaya min xaka yi aure Mujaheed sai aka yi yaya? Sai aka dinga yagan naman
jikina? Toh baxa dai a taba canxa ma tuwo suna ba, bauta dai na riga na gama
maka sai dai Allah ya saka min da alkhairi, Amma kar dai ka manta akwai ranan
sakamako" Mujaheed bai ce mata komai ba ya xauna kan kujera ya jinginar da
kansa da kujerar a hankali yace "Akwai ruwan xafi?" Inna tace
"Wanda Rukayya ta hado tare da akwatuna ta kawo min ba?" Mikewa Imaan
tayi tace "Sai da safe Inna" Inna ta kalleta da sauri tace "Sai
da safe bamu gama kallon kayan ba?" Imaan bata ce mata komai ba ta nufi
kofa, Mujaheed ya bi ta da kallon gefen ido har ta fita sannan ya mike ya bi
bayanta, Inna tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni ni patuu, wannan d'a
na Ahmadu dai fitinanne ne, Ina lura da yarinyar nan gaba daya ta fita harkan
ka a gidan nan, da ta ganka xata yi ta kanta ta bar wajen, gaba daya ta ma
mayar da kai dodo, Ina kuma lura hakan na damunka ainun sbda baka samu damar
dinga cutarta ba, to meye kuma xaka wani bi bayanta bayan bata kula ka ba, Ni
dai gwara ma ayi auren nan ka kama gabanka jikata ta huta nima in huta da
maganar ka haka, wllh ka cika fitina ko don maman Rukayya ka sha oho, tunda ita
ma dai fitinanniyar ce" Juyawa Imaan tayi jin tafiya a bayanta, sosai
gabanta ya fadi ganin shi ke bin ta, sai dai bata gudu ba sai kara saurin ta da
tayi, ji tayi ya juyo ta har sai da ta kusa fadawa kansa ta fixge kanta gabanta
na faduwa, a fusace tace "Meye haka yaya?" Kallonta ya tsaya yyi da
wani expression, kamar xata yi kuka tace "Ni ka sakeni" Calmly yace
"Me yasa kike gudu idan kin gan ni?" Kin cewa komai tayi, taji gaba
daya she is very uncomfortable unlike before da bata ki ma ta fada jikinsa ba
ta fara masa shagwaba, Yana kallonta yace "Imaan!" Kasa kallonsa
tayi, ya dago kanta yana kallon manyan idanuwanta, turo baki tayi, and he
couldn't stop looking at her, haka kawai yaji ya samu relieve din abubuwan da
dama da ke damunsa, Yace "Answer my question now, me yasa kike gudu idan
kin gani" sauke idonta tayi kasa calmly tace "Nothing..." jin
shiru bai ce komai ba bayan few seconds ta daga kai ta kallesa taga kallonta
yake, sauke idonsa yyi cikin cool voice dinsa yace "Saboda na amshi wayar
ki?" Ta kallesa kafin tace komai ya ciro wayar a aljihu yana mika mata
yace "Take..." bata san lkcn da tayi murmushi ba ta langwabar da kai
tace "Ae daddy ya ce xai siya min wani soon" ya daure fuska yace
"Take it now..." ta make kafada tace "Ni bana so kuma" yace
"Take before I knock you" kamar xata yi kuka ta amsa yana kallonta
yace "Shi kenan?" Tace "Ehh" wani boyayyen ajiyar xuciya ya
sauke, ta d'an yi jim, sai kuma tace "Aunty Farida xa a kai ma kaya?"
Kasa cewa komai yyi ya saketa ya juya ya koma part din Inna, ta bi sa da kallo
kafin ta juya ta wuce part dinsu tana kallon wayarta. Mujaheed na komawa part
din Inna ya tarar tana ta fiddo kayan akwatuna, ya xauna yana kallonta yace
"Nima fa ban san an fara hada kayan lefen ba shi yasa ban gaya maki ba,
sai daxu Umma ke nuna min" Inna tace "Ni dai ba ruwana, ku dinga jin
tsoron Allah, don an gaya min ai ba gafara aka min ba...." Wani jallabiya
mai kyau da tsada ta daga tana nuna masa tace "Wannan ai xai ma takwarata
koh?" Kallonta ya dinga yi, jin yyi shiru ta ajiye gefe ta maida sauran ta
rufe jakar, ta nuna masa takalmin da ta ba Imaan ta gwada tace "Wannan ma
ai dai dai ita ne koh?" Nan ma dai bai ce komai ba ta ajiye gefenta, body
spray biyu ta dauka ta ajiye gefenta tace "Sai ta dau daya ta bar min
daya" murmushi Mujaheed yyi bai dai ce komai ba, Inna ta bude akwatin
jewelries, ta dinga kallon dankunnaye da sarakuna masu kyau, kala biyu ta cire
tana kallonsa tace "Wanne ya fi kyau cikin wa enannan?" Shi dai bai
ce mata komai ba, ta ajiye biyun a gefenta tace "Sae ta xabi daya a mayar
masu daya" bude pack din jan baki tayi ta cire uku tace "Duk da dai
ba shafawa take ba sai ta ba Maimoon daya ta rike biyu" Kaf kayan sai da
Inna ta bi ta cire daddaya ta ajiye ma Imaan sannan ta rufe jakunkunan ta jera
su yanda suke, ta kwaso kayan ta xube su gaban Mujaheed tana kallonsa tace
"Ko ban kyauta ba Mujaheed?" shi dai bai ce komai ba ta kwashi kayan
ta kai daki ta fito tace "Toh ai faridan ma ya kamata ta xo ta gaisheni
kafin a kai kayan, kwana biyu shiru bata xo ba" a hankali Mujaheed yace
"Ba Farida xa a kai ma kayan ba..." Inna ta gwalo ido tace "Wa
xa a kai ma?" Yace "Wata ce daban" Inna ta xauna kan kujera ta
saki salati tana tafe hannu tace "Wayyoo.. Amma dai kai shahararren
mayaudari ne Mujaheed, yanxu dama yaudarar yar mutane ka dinga yi ba aurenta
xaka yi ba? Kasa yarinya ta kashe d'an kudinta ta siyo min turare duk da ba mai
tsada bane, Mujaheed anya kana son wanyewa da duniya lafiya kuwa? Ina laifin
yarinyar, kyakkyawa ce fa doguwa" Mujaheed dai kallon kasa kawai yake bai
ce mata komai ba, ganin ynda ta dage tana kiransa da mayaudari ya dago ya
kalleta yace "Umma ce bata son aurena da ita, shine ta hada ni da yar
kawarta..." Inna ta xaro tace "Auzubillahi, yanxu Rukayya ce ta
hanaka aurenta? Toh kuwa akwatunan nn babu inda xa su daga parlon nan sai
gidansu Farida, yarinya mai hankali da natsuwa, tun da naga ynda take ji da Imaan
take sonta naji nima ina sonta" Da sauri Mujaheed yace "A'a ita ma fa
iyayenta sun riga da sun mata miji har an sa rana" Inna ta saki baki tana
kallonsa, can tace "Toh wacece wannan kuma xa ka kwaso mana?" Ya d'an
yi murmushin karfin hali yace "Idan anyi auren xaki ganta" Inna tace
"Sai ka kawota ai ta gaisheni ba ruwana, Amma dai kun yaudara juna da
farida tunda gashi ita ma har an mata miji kace, ohh mutane dai tsoron Allah
yayi karanci a xukatansu, yanda ka taso gabana Mujaheed bai ci ace baka da tsoron
Allah a xuciyarka ba, Toh ko da yake ai Rukayya ce ta haifeka, Ahmadu da na
haifa ai gashi yana tsoron Allah, haka ma Bukar, duk basa yin abinda Allah ke
fushi da, banda haka kayi ta xuwa gun yarinya kuna tadi ashe ba aurenta xaka yi
ba??" Shi dai Mujaheed kallonta kawai yake, bude kofa aka yi Abba ya
shigo, Inna ta tsuke fuska, Mujaheed kadai ya amsa sallamansa, Abba ya xauna
yana kallonta yace "Ina yini" tace "Toh ni da aka ki gaya min xa
a kai ma Mujaheed lefe sai aka yi yaya??" Abba ya girgixa kai yace
"Kiyi hakuri, ni ma ba a gaya min da wuri ba Inna" Inna tace
"Kai dai ka ajiye bala'i a gida kawai kuna xaune, banda haka ya xa ayi
d'an ka a boye maka xa a hada masa lefe?" Mikewa Mujaheed yyi yana
kallonta yace "Sai da safe" tace "Tou yaushe xa a kawo min
yarinyar?" Yace "Ehh xa a kawota in sha Allah" daga haka yayi ma
Abba sallama ya fita. Washegari Thursday Imaan na dawowa schl bayan ta yi wanka
ta ci abinci ta shirya ta tafi part din Inna, Inna dake bakin pampo ta biyota
ciki tace "Duk na cire maki kayan na boye maki a sif" Imaan ta xaro
ido tace "Ni dai ba ruwana Inna" wani kallo Inna ta mata ta xauna kan
kujera tace "Toh ni da ruwana, sai in ga wanda xai ce min don me"
Imaan ta tabe baki ta xauna, inna tace "Daxu Bulasawa ya kirani muka
gaisa, ni dai tunda uwata ta haifeni ban taba ganin yaro mai hankali da kirki
irin yaron nan ba..." Imaan ta dai yi murmushi bata ce komai ba, Inna tace
"Bayan mun gama waya ni dai nace masa iron dina ya lalace" Imaan ta
xaro ido tace "Kika ce masa haka Inna?" Inna tace "Toh baxan ce
ba, tun yaushe nake bin Bukar da Ahmadu su siya min sai su ce sun mance, dama
wannan yaron isuhu kadai ne xan ce ma abu ya min nan take, shi Mujaheed ban ma
sa shi a layi, ko ya siyo sai ya kai ma wancan katuwar matar, to wai ni isuhu
na gidan nan ma kuwa?" Imaan ta bude hannu alamar bata sani ba, Inna tace
"Ikon Allah ni toh bai xo ya ce min xai yi tafiya ba... Kai bari dai inje
bangaren nasu inji lafiya, bai taba min irin haka ba da ma dai Mujaheed ne ni
baxan damu ba" Inna ta saka Hijabi da ta dauko tace "Tashi ki rakani,
ba lafiya yau kusan kwana goma ban ga isuhu ba, to ko bai da lafiya ne"
Imaan ta mike suka fita parlon, Inna ta rufe kofar ta da makulli Imaan tace
"Inna to meye na sa makulli" Inna tace "Baxan sa makulli ba? Ko
datti ya shiga parlon ba a cuce ni, ko Kandangare ya ji shiru yana iya shiga in
shiga uku" Imaan tayi gaba Inna ta bi bayanta tana cewa "Don Allah ki
dinga cin abinci mai yawa Imaan, kinsan fa Bulasawa mai mutane ne, haka xa a ga
amarya kamar tsinken tsire a sa mu a bakin duniya, ni dai ki rufa mana
asiri" imaan dai bata tanka ta ba har suka iso part dinsu Maimoon, Inna ta
shiga parlor tana kallon Ummi tace "Ke Isuhu na nan?" Bata jira
cewarta ba ta wuce sama tana kallon stairs din palon tace "Matan Ahmadu
dai kazamai ne, dubi fa yau basu goge nan ba ina ga" dakin Anty ta bude
Aunty ta mike ganinta tace "Sannu da xuwa Inna" inna tace "Kwana
biyu ban ga isuhu ba ko ke kika hanasa xuwa inda nake" Aunty tace "Ni
na isa Inna, ban ma san bai je ba ai, yanxu dai baya nan" Inna tace
"Toh yana dawowa kice ya xo ina nemansa" Aunty tace "Toh"
Imaan ta gaida Aunty, Aunty ta amsa da fara'a, Umma ta leko ganin Inna ta koma
ciki da sauri ta rufe kofarta, inna ta juyo tace "Toh ita kuma mai hada lefe ana ciki kenan, Toh dai
baxan shiga ba" daga haka ta fara sauka stairs din Imaan ta bi bayanta.
Bayan magrib Imaan na part din Inna Mujaheed ya shigo, xaunawa yyi ya gaida
Inna da ke cin abinci tace "Mujaheed ni fa ban ga isuhu ba har yanxu, ban
san me ya faru ba" Mujaheed na kallon boxes da ta jera yace "Inna xa
a mayar da akwatunan can gida" Inna ta ajiye cokalin hannunta tace "A
kan wani dalili?" Yace "Ai ba a gama xuba kaya ba" Inna tace
"Toh sai a dinga xuwa nan ana xuba su, in dai kaga an fitar da akwatunan
nan daga parlona to gidan amaryar xa mu tafi kai wa, ai ba wani ya min wahala
da kai ba, ko Ahmadu da na haifa ban masa wahala yanda na maka ba, Rukayya dai
ta shiga hankalinta a gidan nan ta daina shiga hurumin da ba nata ba" Bai
kuma cewa komai ba, ya kalli Imaan dake xaune tana kallo, ta gefen ido ta ga
yana kallonta ta mike tace "Sai da safe Inna" daga haka ta fita
parlon, Bai dade xaune parlon Inna ba ya mike ya fita, yana isa part dinsu
Imaan ya shiga balcony ya danna bell sannan ya bude kofar, Ammi dake xaune
parlor ta dinga kallonsa har ya shigo, kasa kallonta yayi ya dukar da kansa ya
xauna saman kujera yace "Ina yini Ammi" Ammi tace "Lafiya lau ya
aiki" yace "Alhmdllh" tace "To maa sha Allah" kasa
cewa komai yyi, can yana shafa kansa yace "Ammi dama..." Sai kuma bai
ce komai ba, Ammi tace "Dama me?" Yace "Ina son Imaan xata
rakani ne" Da mamaki Ammi tace "Ta raka ka ina?"
Yanxu xan dinga update twice sbda xan rage tsayin rubutun,
sai kuma da daddare in sha Allah.
*The book Imaan isn't free, you read for free ur cup of
coffee...*🤷🏻♀️
It's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah, then you show ur evidence
of payment through my WhatsApp digit 07087865788 to be included in d payment
group.
34......
Mujaheed ya kalleta yace "Ina son xan je gidansu Farida
ne" Ammi tace "Wace faridar? Wace ku ka yaudara ko wata daban?"
Shiru yyi bai ce komai ba, Ammi ta tabe baki ta maida dubanta kan TV, yace
"Ni ban yaudare ta ba Ammi, kila hakan Allah ya tsara we are not destined
to be together" Ammi tace "Toh yayi kyau, haka Allah ya tsara"
Bai ce komai ba, can ta kallesa tace "Toh me xaka je ka mata?" Yace
"Ina son xuwa in bata hakuri ne, idan ta gan ni da Imaan she might listen
to me, bana son tayi tunanin yaudararta nayi" Ammi tace "Toh Allah ya
kyauta, amma yanxu dare yyi sai ka bari gobe" yace "Gobe da safe xata
wuce kano" Ammi ta girgixa kai, tace "Toh ba sai ku tafi har da
Maimoon ba" yace "Eh xa mu je tare" Ammi tace "To ka turo
Maimoon din xa su fito tare" yace "Toh nagode" daga haka ya mike
ya mata sallama ya fita parlon, Ammi ta mike ta shiga dakin Imaan xaune ta
sameta tana karatu, Ammi tace "Ki shirya ke da Maimoon xa ku raka Mujaheed
wajen Farida" Imaan ta xaro ido tace "Yaya kuma? A'a ni Ammi baxan je
ba" Ammi ta dinga kallonta sannan tace "Me yasa?" Girgixa kai
tayi tace "A'a ni bacci nake ji" Ammi tace "Me ya hada ku da
Mujaheed din?" Da sauri ta kalli Ammi sai kuma ta dauke Kai tace "Ba
komai fa Ammi" Ammi tace "Toh tashi ki rakasu ku dawo" daga haka
Ammi ta fita dakin, da kyar Imaan ta mike har ranta bata son bin Mujaheed, can
dai ta sa Hijab dinta har kasa ta fito, dai dai nan Maimoon ma ta shigo parlon,
Ammi na kallon Imaan tace "You pray before leaving, and ku kula" A
hankali Imaan tace "Toh" daga haka suka fita tare da Maimoon bayan ta
gaida Ammi, a waje suka samesa yana jiransu cikin mota, Maimoon ta shiga back
seat, Imaan ta hade rai ta shiga ita ma, Maimoon tace "Ki tafi gaba
mana" Imaan tayi mata banxa ta rufe motar, Mujaheed yace "Wata ta
dawo gaba, I am a driver to none of
you" Maimoon ta turo baki ta bude motarta ta fita ta koma gaba, tada motar
yyi suka dau hanyar titi, lkci lkci yake kallon Imaan dake kallon waje, gidan
yayar Farida dake unguwar sanusi suka tafi,
Mujaheed yyi parking kofar gidan ya kashe motar, yace "You two
should go in, ku ce mata I am outside, she isn't picking her cals" Imaan
ta bude motar ta fita, Maimoon ma ta fita suka shiga gidan a tare, A parlor
suka tadda yayarta da yaranta uku, tana kallonsu ta amsa sallamarsu, Imaan ta
xauna ta gaisheta Maimoon ma ta gaisheta duk ta amsa amma da alamar bata gane
su ba ma, Maimoon tace "Aunty Farida fa?" Yayar tace "Tana
daki" karamin yaronta ta aika ya kirata a daki, sai ga ta ta fito, tsaye
tayi tana kallonsu, can tayi murmushi tace "Sannu ku da xuwa" Imaan
tace "Ina yini Aunty farida" Farida ta xauna tace "Lafiya lau
Imaan ya Ammi fa" Maimoon ma ta gaisheta ta amsa tace "Daga Ina ku ke
haka da daren nan?" Imaan tace "Daga gida mana" Murmushin
fuskarta yayi fading tace "Toh a xubo maku abinci" Imaan tace
"A'a mun ci abinci, Aunty farida Ammi ce ta aiko ni" Farida tace
"Ayya, toh ina jin ki" Imaan tayi murmushi tace "Ko xa mu je
waje?" Farida ta mayar mata da murmushin sannan ta kalli yayarta tace
"Anty kanin Mujaheed ne" lkci daya yayar ta hade rai ta ci gaba da
kallonta, Imaan ta mike tayi ma yayar sallama Maimoon ma haka sannan suka fita,
Farida ta mike ta bi bayansu, mamaki ya kamata ganin sun fita wajen gate don ta
xaton cikin compound din Imaan xata bata sakon Ammi, ta dai bi bayansu har
waje, sosai gabanta ya fadi ta tsaya tana kallon Mujaheed dake tsaye jikin mota
ya rungume hannunsa, ta sunkuyar da kai ya karasa har inda take, Juyawa tayi
xata koma ciki ya kamo hannunta a sanyaye yace "Pls listen to me
Farida" kasa kallonsa tayi hawaye ya kawo idonta, sosai jikin Imaan yyi
sanyi, Maimoon ta bude mota ta shiga don ita ma ta bata tausayi, cike da karfin
hali Mujaheed yace "I neva meant to break ur heart Farida, even for once,
but you know Allah plans best, may be we were neva destined to be together, ki
yafe min pls, Umma ta bata son aurenmu and I can't disobey her" Hawaye na
xuba idonta tace "Allah yasa hakan yafi alkhairi, and I am wishing a happy
married life in advance" a sanyaye yace "Forgive me plss Farida"
ta gyada masa kai da kyar tace "I have done that in sha Allah" Yace
"Tun daga farkon relationship dinmu 4 years ago har xuwa yanxu idan na
6ata maki kiyi hakuri ki yafe min" tace "Baka min komai ba kuma na
yafe maka ni ma ka yafe min, Allah kuma ya saka maka da alkhairi abubuwan da ka
min from the beginning har xuwa yanxu, thank much Muhd, Allah kuma ya baka Ikon
ci gaba da yi ma mahaifiyar ka biyayya, ku rabu lafiya" Ya sauke idonsa
kasa yace "in sha Allah xa mu dinga xumunci..." xame hannunta tayi ta
juya ta nufi gate dinsu, a hankali yace "Idan Allah ya kaddara you will
still be my wife some days, I will be very glad in hada ki da
kanwarki...." Farida bata juya ba har ta shiga ta rufe gate din, Juyawa
Mujaheed yyi kamar mai tausayin kasa ya xaga ya bude driver seat ya shiga,Tada motar
yyi yana kallon Imaan da ta turo baki bayan ta goge hawayen idonta, Bai ce
komai ba ya bar layin da motar, har suka isa gida babu wanda yace komai cikin
motar, the journey was very silent, yyi parking a kofar gida Maimoon ta bude
motar ta fita, Imaan ma ta fita ta shiga gate da sauri, Parlor ta tadda Ammi,
ganin mood dinta Ammi tace "Ya aka yi" xaunawa tayi hawaye ya kawo
idonta tace "Ammi ta ban tausayi, me yasa Yaya xai mata haka, he betrayed
her" Ammi ta tabe baki bata ce komai ba, tace "Har kuka fa sai da
tayi" Ammi tace "Toh Allah ya bata wanda ya fi sa, wani hanin ga
Allah bai wa ne, bata san ma wani gata Allah ya mata da ya rabasu ba, don Ina
tausaya mata idan Mujaheed ya aureta barin yanda uwarsa bata sonta" Imaan
tace "Toh Saboda me?" Wani murmushi Ammi tayi tace "Ko makiyina
baxan ba shawara ya ba ma Mujaheed 'yar sa ba, Kinga Hajiya Rukayya ta wuce
tunanin kowa, ni ba miji daya muke aure ba amma irin xaman da muka yi ba shi da
banbanci da muna auren miji daya, na sha wahalar ta ne, sam bata san da annabi
ya kafu ba" Imaan dai tayi shiru, Ammi tace "Don haka gwara dai ta
aura ma d'an nata yar kawarta, sun fi kusa kuma sun san kansu" Washegari
Juma'ah Imaan na dawowa schl ko uniform bata cire ba sai ga inna ta sha
atamfarta mai tsada an yafa mayafi, Ammi tace "Sannu da xuwa Inna"
Inna tace "Yauwa takwara ta dawo makaranta kuwa?" Ammi tace "Ehh
yanxu ta shigo" inna tace "Toh da kyau, dama so nake ta rakani gidan
ta rasulu kwana biyu shiru ban ganta ba" Ammi ta kwalo ma Imaan kira,
Imaan ta fito, Ammi tace "Xa ki raka Inna anguwa" Imaan ta hade rai
tace "Ban ma yi wanka ba kuma ban ci abinci ba, gashi kai na ma ciwo yake
min" Inna tace "Kanki na ciwo kuma? Toh yi xaman ki bari in je in
samu Maimoon ko Ummi su rakani, ya xan yi dake idan kin fadi a titi, wa gareni
titin?" Daga haka ta juya ta fita, Imaan ta koma dakinta. Imaan na wanke
wanke kitchen da yamma Ammi ta kwalo mata kira fito da sauri, Ammi tace
"Kiran ki ake a waya" daukar wayar tayi ganin Sadeeq ne ta daga ta
bar parlon, gaisawa suka yi yace "Pls dear ki d'an fito ki amshi sakon
Inna am outside" Imaan tace "Sako kuma?" Yace "Ehh ko kina
wani abu ne?" Tace "A'a ka dai shigo ka kai mata ai ni bn san da
sakon ba" yayi murmushi yace "Ai anjima da daddare xan xo sai muje
part din nata tare, yanxu sauri nake Mum dita ta aikeni xan kai mata sako"
Imaan tace "Toh sakon meye?" Yace "Ke dai fito ki gani" a
hankali tace "Toh" Daga haka ya katse wayar, Ammi dake jin wayar da
take tace "Sakon meye?" Imaan tace "Ko ba Inna bace tace ya siya
mata iron" tagumi Ammi tayi tana salati, can tace "Yanxu Inna mutunci
take nema mana gun yaron nan ko tsiya, sam ban ji dadin sanin yaron nan da tayi
ba, me kuma xata yi da iron idan ba fitina ba anjima ta hada kayan ta bada a
goge mata gun masu laundry, wannan wani irin kaskanci ne fisabilillah, to ita
Ina nata iron din?" Imaan tace "Daga ranan Ummi ta ce ya mata
shocking shikenan Inna ta saka a bola" Ammi tayi salati tace "Wannan
tsohuwa dai Allah ya raba mu da ita lafiya, ynxu abinda nake so da ke idan ta
dawo anjima ki dau wayarta kiyi blocking number sa sannan kiyi deleting don ba
mutunci take siya maki a gun sa ba, snn ki nuna masa baki son ma yana xuwa
bangarenta kwata kwata" a hankali Imaan tace "Toh" Hijab kawai
ta sa ta fita kofar gida, waya na kare kunnensa ya kafeta da ido har ta iso
inda yake, katse wayar yyi yace "How are you doing dear" tace
"Alhmdllh ya aiki?" Yace "Fine Alhmdllh" Bude motar yyi ya
fiddo wani leda ya mika mata yace "Gashi ki ba Grandma" Shiru tayi bata
ce komai ba, can ta amsa tace "Toh angode" wani ledan ya fiddo ya
mika mata yace "This is for you" Ta girgixa kai tace "A'a
nagode" a hankali yace "Bana son Ina baki abu kina ce min A'a
dear" tace "Ni dai nagode" kallonta ya tsaya yi, dai dai nan
mota yayi parking bayan nasa, Bude motar aka yi Umma ta fito, kallonsa ta dinga
yi sannan ta kalli Imaan ta kara kallonsa ta kalli Imaan, Sadeeq ya gaisheta
with respect, Sai da ya kara gaisheta ta amsa da sauri tace "Lafiya
lau" Tana isa gate ta sake Juyawa ta kallesa saura kiris ta fada bakin
gate din tayi maxa ta shige ciki, Sadeeq da ya bi ta da ido ya kalli Imaan dake
wasa da fingers dinta yace "Who is she?" Imaan ta kallesa ta d'an yi
murmushi tace "Mum din Yaya" Sadeeq yace "Ohk, but why didn't
you greet her" Shiru tayi kamar baxata ce komai ba, can a hankali tace
"Xan gaisheta ai idan na shiga" yace "Noo, that's not a
point..." Ta d'an yi murmushi kawai, yace "Though I don't know why is
that, and I am not suppose to intrude into family issue but promise me xaki
dinga gaisheta daga yau, ita din ai babbace" Imaan ta kallesa, yace
"Yea promise me" sunkuyar da kanta tayi a hankali tace "Toh in
sha Allah" yayi cute smile dinsa yace "Maa sha Allah" kan
wani farin kujerar roba ya ajiye ledan
da ya bata ta ki ta amsa yace "Shikenan sai mu yi sadaka da shi tunda baki
so, I am leaving now, mum dita na jirana" Bai jira cewarta ba ya shiga
motarsa ya tada, d'an murmushi tayi cikin sanyayen murya tace "Toh
nagode" ya kashe mata ido daya ya ja motar ya bar layin, a hankali ta kai
hannu ta dau ledan ta wuce ciki. Sai kusan Isha ta tafi kai ma Inna abincinta
bayan Ammi ta kara maimaita mata tayi blocking number Sadeeq a wayar Innan
sannan tayi deleting, tana isa parlon ta ajiye abincin da ledan iron din ta
gaida Inna dake goge gogen kayan kallo, Inna tace "Allah dai ya bar ni da
ta rasulu kawai, Ni fa ta fiye min wasu daga yan uwa da basu da kirki ynxu, har
maganar ki da yaron nan Sadeeq sae da na mata yanxu kawai kudi xan bada a kauda
idon makiya a lamarin, gobe ma xan ba Mujaheed kudin ya kai mata, wa xai xauna yanxu??
Kowa ya tashi tsaye ya nemi kariya kawai" Imaan bata dai ce mata komai ba
ta xauna ta dau wayarta dake kan kujera tace "Inna ga iron dinki an kawo
daxu" Inna tace "Haba, Kai Allah masa albarka, to da Ahmadu ne sai
dai yace min ya manta, kinga alamar wnn yasan darajan babba ko to ni dai ba
ruwana, idan xaki rikesa hannu bibbiyu ki rikesa mijin aurena wllh, Allah dai
ya saka masa da alkhairi, ke kuma na gaji da ajiyar wayar da ya kawo maki idan
baxa kiyi amfani da shi ba a tafi kasuwa ki siyar kudin xai yi maki
amfani" bata jira cewar Imaan ba ta shiga ciki, har Imaan ta gama blocking
da deleting lambar Inna bata fito ba, tana kokarin tashi tace mata xata tafi,
Inna ta fito duk ta hada xufa a gigice tace "La ila ha illallahu
Muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wassalam, Innalillahi wa Inna ilaihi
raji'una, laaa haula wala kuwata illa billahil Aliyul azeem... To barawo ya
sace wayar" Imaan ta mike tana kallonta da mamaki, Inna ta fashe da
matsanancin kuka tace "Wlh a karkashin kwalla na adana ledan wayar yanxu
ko sama ko kasa wani ya shigo ya sace ban san waye ba, na shiga uku na lalace
dukiyar mutane, Allah ka rufamin asiri" Mayafinta ta fixga ta fice daga
parlon tana rusa kuka, Imaan dai tayi still tana kallon kofar dakinta can ta bi
bayanta, tuni har Inna ta isa part din Abba, Imaan ta shiga nasu part din, Inna
na shiga su Maimoon na gaisheta cikin kuka tace "Ina Ahmaduna yake?"
Mujaheed dake sakkowa downstairs ya dinga kallonta da mamaki Aunty dake xaune
parlor kuwa sai tambayarta me ya faru take, Inna ta rushe da sabon kuka ta
xaune kasa tace "Nashiga uku, Ahmadun bai dawo bane?" Umma ta leko
parlon daga kitchen bata dai fito gaba daya ba, Mujaheed ya karaso yace
"Wai me ya faru ne??" Cikin kuka tace "An sace wayar da Bulasawa
ya kawo ma Imaan a dakina cikin kwallaa...." Ta kunce ha6ar xaninta ta
rufe fuska ta dinga kuka tace "Yanxu wani kallo yarinyar nan imaan xata
min, wayar fa ance ya kai dubu dari biyar... Wayyo ni dai na shiga uku an goga
min bakin fenti" Umma sai xaro ido take daga kofar kitchen tana kallon
Inna jin ta ambaci Bulasawa, Aunty tayi tagumi tana kallon Inna, su Maimoon da
Rahama kuwa banda dariya babu abinda suke kasa kasa.
*imaan isn't free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah. Subscribe and read
happily.
35....
Aunty tace "Daxu da kika fita baki kulle kofar bne
Inna?" Inna na sharban kuka tace "Wllh na kulle Amina sai dai idan
sabon makulli aka yi aka bude kofar..." Da mamaki Aunty tace "Ikon
Allah, amma mu je dai a kara duba dakin Inna kila dai baki duba a nutse
bane" a fusace Inna tace "oh oh Allah, Wani dakin xa aje kuma bayan
nace maki duk na xaxxage kayan kwallan, wllh sacewa aka yi, kuma wannan barawon
da ya san ni ne, yasan me nake ciki a rayuwa" Aunty na kokarin danne
dariyarta tace "Gaskiya wannan abu da mamaki, anya ba Imaan din bace ta
dauke kayanta kuwa??" Inna ta tsuke fuska tace "Don Allah Amina ki
rabu da ni kiyi ta kanki, idan baxa ki fadi alkhairi ba kiyi hakuri ba don ni
ba don Allah kiyi shiru, ta ina Imaan xata dauke waya bata gaya min ba" Tuni
Mujaheed ya koma dinning ya xauna ya bude warmer yana diban abinci, Sallaman
Abba yasa Inna ta mike tana matsar hawaye tace "Ahmadu yau an shafa min
bakin fenti a gidan nan, ban san wanda ya shiga ya sace wayar da Bulasawa ya
bani in ba Imaan ba, wayar tayi na miliyan Ahmadu, ka rufa min asiri mu tafi
aje a sake dubawa, da wani idon xan kalli Bulasawa idan yaji labarin waya ya
bata a wajena" Abba dake tsaye ya ma rasa abinda xai ce sai kallonta yake
da mamaki, can dai ya girgixa kai yace "Wayar ta miye yaron ya kawo da ba
mu da labari??" Inna ta wani hade rai tace "Ta imaan ce wayar ya kawo
mata kyauta, kuma ta hannuna wayar ya biyo, ko an daina ihisani ne a
duniyar?" Abba yace "Amma da ya bada ai sai ta kawo nan ta nuna min
tunda shi Sadeeq bai nan, wannan bai kamata ba sam inna, a kan wani dalili ma
xai bata waya??" Inna tace "Kaga Ahmadu kayi hakuri kar a shashantar
da xancen bacewar waya mu tafi mu nemi waya duk inda ya shiga" Abba ya
dinga kallonta, a fusace tace "Ahmadu kana kallona, don Allah ka shiga
gaba mu je, idan ma ya kama a fiddo duk kayan cikin dakin sai a fiddo, yau dai
xan ga batar nono a kirjin Budurwa" Kofa Abba ya nufa ta bi bayansa fuska
a tsuke, Aunty ta fita ita ma, su Maimoon ma suka bi bayanta, Mujaheed dai cin
abincin sa kawai yake a nutse, Umma da ta makale a kitchen, tana jin sun fita
ta fito da sauri, duk ta hada xufa tace "Mujaheed, wani Bulasawan Inna ke
nufi?" Mujaheed ya kalleta yana cin abincinsa a hankali yace "Ni ma
ban gane xancen da take ba gaskiya" Umma ta tafi sama sai gata ta sauko da
hijab xata tafi bangaren Inna, shi dai Mujaheed bin ta kawai yake da kallo har
ta fita, Tana isa part din ta shiga parlon ta ga su Maimoon na ta fito da kaya
daga cikin daki, Inna na tsaye daga gefe sai wurwurga ido take, Abba dai na tsaye
daga bakin kofa ya rungume hannu, Aunty kuma na can uwar dakan Inna, Inna ta
saki salati ta rushe da kuka tace "Kin ga ta kanki yau patuu, tunda uwata
ta haifeni ba a ta6a ban ajiya ya bace ba..." Umma ta shigo parlon cike da
damuwa tace "Wai har yanxu ba a ga wayar ba Inna?" Inna na goge
hawaye tace "Wllh ba a gani ba Rukayya, ranan Ina bakin pampo ina gurje
daudar wajen sai ga yaron ya shigo...." Umma tace "Wani yaro?"
Inna tace "Bulasawa mana, waye bai san imaan da Bulasawa ba kuma a gidan
nan, ba dai Bulasawan da kansa ba, d'an cikinsa ne dai, wllh yana bani wayar
bayan ya fita kinga inda na ajiye wayar can" Umma ta kalli inda Inna ke
nuna mata, Inna ta fashe da wani sabon kuka tace "Ni dai yau xan ga batar
nono a kirjin budurwa ni Asabe" Umma dai ta kasa tsaye waje daya, Kai kana
ganinta xaka ga tashin hankalin da ya ki boyuwa karara a fuskarta, Dakin Inna
ta shiga ta gama xagaye xagayenta sannan ta fito tace "Kuma Inna babu kowa
parlon San da aka baki wayar?" Inna ta d'an yi shiru sannan da sauri tace
"D'an ki ne Mujaheed kadai a parlon a lkcn, Toh ga dankareren dankunnen
zinari ma da ya bata ta bani ajiya bai bata ba, duk da ranan ba kowa a parlon
ta bani, waya dai Mujaheed na wajen lkcn" Inna ta xaro ido ta dafe kirji
tace "To ko dai sata Mujaheed ya fara a gidan nan ba a sani ba??"
Umma dai sai hada xufa take tana kallon inna, Inna ta kalli Abba tace
"Anya Ahmadu baxa a caji Mujaheed ba, wllh shine a parlon ranan, Ni dai na
shiga uku na lalace" Abba dai bai ce mata komai ba, Umma ta dake tace
"Inna bari in kashe gas na daura ruwan shayi, xan dawo yanxun nan, ae
wannan babban magana ce" Inna tace "Yi maxa kar ki ja wata fitinar ba
a gama kashe wata ba" da sauri Umma ta fita, tana komawa bangarensu bata
ko kalli Mujaheed ba ta wuce sama jikinta na rawa. Washegari har Ammi ta gama
soye soye a kitchen shiru imaan bata fito ba, dakinta Ammi ta shiga don ya ci
ta fito ynxu ta gama shirin islamiyya, kwance Ammi ta ganta cikin duvet, ta
cire duvet din tana kallonta ta kai hannu jikinta, janye hannun tayi tana kallonta
tace "Imaan?" A hankali imaan ta bude idonta da ya rine tana kallon
Ammi, Ammi ta xauna gefen gadon da damuwa tace "What's wrong imaan?"
Da kyar ta nuna ma Ammi kanta murya can kasa tace "It's aching me" ta
nuna ma Ammi kafafuwanta ma, Ammi ta dinga kallonta cike da tausayi tace
"Kin daina shan maganin ki ko daughter!" Imaan ta girgixa mata kai
kawai ta kasa cewa komai, mikewa Ammi tayi ta wuce bathroom dinta ta hada mata
ruwan wanka ta fito ta daga ta, ita ta taimaka mata har xuwa bathroom din sannan
ta fito, ta ciro mata kayan da xata saka sannan ta fita, Imaan na fitowa wanka
ta kwanta kan gado daure da towel ta rufe jikinta da duvet, Ammi ta dawo dakin
rike da cup din shayi da ledan bread ta ajiye kasa tana kallonta tace "Toh
tashi ki shirya sai kiyi breakfast ki sha magani" Ganin she is shivering
Ammi ta dauko cream dinta ta taimaka mata ta shafa sannan Imaan ta saka kayan
da Ammi ta fiddo mata, shayi kawai ta sha da drugs dinta sannan ta kwanta Ammi
ta fita da cup din. Aunty ce xaune parlon Abba bayan ta kawo masa breakfast,
ganin mood dinsa tace "Don Allah ka daina damuwa da abubuwan inna, kun fa
fi kowa sanin halinta, Bai kamata kuna sa abun a rai ba, kuma uwa ce fa"
Abba ya girgixa kai yace "Ni kadai baxan iya dinga nuna ma Inna abinda ya
dace da wanda bai dace ba, ya kamata ku ma ku dinga contributing...."
Aunty ta sake baki tace "Mu a suwa Alhaji, ku ma ya ku ka kare balle mu,
ai sai ta kora mu gidajen iyayenmu..." Abba yace "Wannan ba point
bane, idan a nuna mata ta gyara ai da matsala babba, Dama ta fi sauraran Sadeeq
to shi baya nan, ni kuma inyi magana ta fara min kuka, wllh duk abubuwa sun
taru sun min yawa a kai" Aunty tace "Ai tana jin maganan Mujaheed
ma" Abba ya kalleta yace "Toh cewa tayi a tafi Police station Mujaheed
ne ya dauke waya, har da kukanta fa, Yanxu fisabilillahi maganan nan ya maki
dadi?" Aunty ta kasa danne dariyarta tace "Tsufan kenan ai Alhaji, a
dinga yi mata uxuri don Allah, Toh shi me Mujaheed din yace?" Abba ya
girgixa kai yace "Ni ban ma gansa ba tun jiyan, sai daxu da muka hadu
masallaci, gaskiya Inna na daga min hankali da yawa ban san yanda xan yi
ba" Aunty tace "Toh Allah dai ya kyauta" Yusuf ne yyi sallama
bakin kofa Aunty ta amsa ya shigo parlon ya mika mata wayarta yace "You
missed a call" Abba na kallonsa yace "M.A fa?" Yusuf yace
"Yana bedroom dinsa" Abba yace "Kira min shi ku taho tare"
Yusuf ya amsa da to sannan ya nufi kofa, hanya ya ba Umma ta shigo parlon
sannan ya fita, Daga Aunty har Abba suka dinga kallonta, duk gaba daya a
sanyaye take tace "Alhaji xan je gidan Mariya wai suma ta dinga yi jiya
basu yi bacci ba, yanxu haka suna asibiti tun asuba wai" Aunty tace
"Subhanallahi, Toh Allah ya bata lafiya ya yaye ma duk musulmi ciwo, in
sha Allah xan shigo anjima nima" da sauri Umma tace "A'a Hajiyar mu tace
mu taho da ita zaria kawai, yanxu Ina xuwa Zaria xa mu wuce da ita" Abba
yace "Toh Allah ya bata lafiya, ya sa kaffara ne" tana goge hawayen
da ya cika idonta tace "Ameen" Abba yace "Da driver xa ku tafi
kenan?" Umma tace "A'a adaidaita xan hau xuwa asibitin daga can sai
mu tafi a motar mijinta" Abba yace "Toh Allah ya kiyaye hanya, do you
need anything?" Tace "Ehh a min transfer din abinda ya sauwaka"
Abba yace "Alright" sallama tayi masu ta fita parlon Aunty na mata
Allah kiyaye hanya, bayan ta rufe kofa Aunty ta duba call din da tayi miss taga
Ammi ce ta kirata, dialing number din tayi yana fara ring Ammi ta daga suka
gaisa, Ammi tace "Dama tambaya xanyi ko driver na nan Hajiya..."
Aunty tace "Ehh toh bai dawo daga kai su Maimoon islamiyya ba..." Ammi
tace "Toh dama Imaan ce bata ji dadi ba xa mu je asibiti" Aunty tace
"Subhanallahi tun yaushe?" Ammi tace "Yau dai da ciwon nata ta
tashi" Aunty tace "Toh bari in ma Yusuf magana ko shi sai ya kai ku
asibitin" daga haka ta katse wayar, Abba yace "Mamana ce ba
lafiya?" Aunty tace "Wllh kuwa, Wai ciwonta ne ya tashi" Abba ya
d'an yi shiru sannan yace "Bari
Mujaheed ya shigo mu ji ko xa a kaita asibiti ne ko a bata medication a
gida" dai dai nan Mujaheed ya shigo tare da Yusuf, Abba ya mike yace
"Mu je ka duba Mamana wai bata ji dadi ba" Mujaheed ya d'an yi jim,
sannan ya bi bayan Abba suka fita parlon, Aunty na kallon Yusuf tace "Kai
baxa ka je dubata ba" Yace "Xan je anjima mum" Har bedroom din
Imaan Abba da Mujaheed suka shiga Ammi dai ta tsaya daga bakin kofar, bacci
take suka sameta, Mujaheed ya duka kusa da ita a hankali yana kallonta ya kai
hannu forehead dinta, bude ido tayi ganinsa ta ja duvet ta rufe kafarta da
sauri. Abba ya karasa kusa da gadon yace "Sannu mamana, ya jikin?" Da
kyar tace "Da sauki Abba" Mujaheed na kallonta yace "Where are
you feeling pains?" Ba tare da ta kallesa ba ta nuna masa kafafuwanta da
baya, yace "Kin sha magani ne?" Kai ta gyada masa, Yace "Ina
drugs din" ledan maganin dake ajiye ta nuna masa ya dauka ya duba su
sannan ya ajiye yana kallon Abba yace "Let me get some injections da
drugs" Abba yace "Ohk" daga haka ya nufi kofa Ammi ta basa hanya
ya fita. Abba na kallon imaan yace "Allah ya sauwake imaan" ta d'an
yi murmushi a hankali tace "Ameen" Abba ya juya ya nufi kofa yana
kallon Ammi yace "Allah ya bata lafiya" Ammi tace "Ameen thumma
Ameen" yace "Amma kada a gaya ma Inna" Ammi tace "In sha
Allah" kofa ya nufa yace "Xan fita office, I will call later"
Ammi tace "Allah ya kai mu, Allah kuma ya tsare" yace
"Ameen" sannan ya fita parlon. Ammi ta karasa cikin dakin tana kallon
imaan tace "In kara hada maki shayin ne?" Da sauri ta girgixa kai,
Ammi ta dinga kallonta sannan ta juya xata fita, murya can kasa tace "Ammi
don Allah ki shafa min maganin a kafa kafin Yaya ya dawo ni bana son ya shafa
min"
*Imaan isn't free....* it's 300 Via Fcmb 3276052019 Hauwa
Bello Jiddah
Then you show ur evidence of payment via 07087865788 to be
included in the payment group....
36......
Mujaheed na dawowa ya tadda Ammi xaune parlor, Ammi ta amsa
sallamansa yace "Ta ci abinci ai" Ammi tace "Ta sha shayi
daxu" yace "Tana ciki har ynxu?" mikewa Ammi tayi tace "Ehh
tana ciki" bedroom din Imaan ta nufa, ya bi ta da kallo sannan ya bi
bayanta, Ammi ta cire duvet din jikinta xuwa kafanta tace "Imaan"
tashi xaune imaan tayi ganin Mujaheed ta daure fuska ta ja duvet din xuwa waist
dinta, a hankali tace "Ammi na ma fara jin sauki" Ammi ta kallesa
tace "Magunguna ka siyo mata?" Mujaheed ya girgixa kai yace "A'a
injections ne, sai na shafa..." Ammi tace "Ta sha drugs a bar
injections din anjima" kallonta yake sannan yace "Amma na yanxu ne
alluran..." Imaan tace "Toh na ji sauki ai yaya" Bai kuma cewa
komai ba sai kallonta da yyi ta gefen ido babu yabo bbu fallasa, Ammi tace
"Ina lotion din tube din?" Mika mata ledan yayi ta amsa ta cire man
xafi dake ciki, Mujaheed ya kara kallon Imaan da ta ki kallonsa, Juyawa yayi ya
nufi kofa kamar baxai ce komai ba bayan ya bude kofar yace "Sai anjima"
ba tare da Ammi ta juya ba tace "Allah ya kai mu" da kanta ta shiga
shafa mata man xafin a kafafuwanta da bayanta, Tana yarfe hannu tace "Toh
Ammi alluran fa, ni dai bana son Yaya ya min, Kuma har yanxu Ina jin joint pain
din" Ammi tace "Anjima Dr Habib xai xo..." Ammi na gama shafa
mata ta fita dakin imaan ta koma ta kwanta ta lumshe ido. Da yamma Imaan na
xaune parlor pepper soup din naman ragon da Aunty ta kawo mata na gabanta ta
kasa ci don gaba daya bata da appetite, har wani rama tayi kamar warce tayi
sati ba lafiya, xuwa lkcn dai ta ji sauki sai rashin kwarin jiki don Dr Habib
ya xo ya mata injections din da Mujaheed ya siyo daxu, Ammi ce ta fito parlon
ta iso kusa da ita tace "Idan baxa ki ci ba ki kai kitchen ki rufe Imaan,
ai ba dole bane" Imaan bata ce komai ba ta amshi wayar da Ammi ke mika
mata, Sadeeq ne ke kira a wayar, ta kalli Ammi da ta juya xata koma daki sannan
ta daga wayar ta kai kunne hade da masa sallama murya can kasa, daga daya
bangaren ya amsa yace "Are you okay?" Ta gyada masa kai tace
"Sure Ina yini?" Yace "No, you sound sick ki gaya min baki da
lafiya ne?" Cikin sanyin murya tace "Ae na ji sauki" Yace
"Subhanallah, me ya sameki?" Ta girgixa kai tace "Kawai xaxxabi
amma naji sauki sosai" ya d'an yi shiru sannan yace "Toh Allah ya
kara lafiya, anjima xan xo in sha Allah" tace "Toh Allah ya kai
mu" yace "Ameen, I will call you idan na iso" tace
"Toh" katse wayar tayi ta ajiye tana shan pepper soup din naman a
hankali, Bude kofar parlorn aka yi Inna ta shigo ta tsaya tana kallonta tace
"Ikon Allah, yanxu don kaddara ta fada ma wayar ki sai ki kwanta ciwo
imaan?? anya kuwa xa ki yi tawakalli irin nawa? Kinsan irin asaran da nayi a
rayuwar nan kuwa tun tasowata har ixuwa yanxu? To 6arin ciki hudu nayi a gidan
mijina, na haifi 'yan biyu suka mutu rana daya, dakina ya ta6a konewa kurmus
bbu abinda aka fitar da sai mafici, kishiyata ta ta6a turo min yan fashi suka
kwace min jakata a titi Allah ya so bbu komai ciki sai naira daya, 'ya yana uku
kacal a duniya, da ubanki, sai na Mujaheed sai kanwarsu Hadiza dake kasashen
turai, to ban gode ma Allah ba? Me ya sameni, ke don kawai an dauke wayar da
bai fi dubu hamsin ba idan ma ya kai sai ki sa ma kanki damuwa kiyi ta ciwo
kamar wayar jaraba, in dai waya ce ni baxan bari ki sani a bakin duniya ba xan
ba Ahmadu dubu goma ya cika ya siyo maki wata ba ruwana" Imaan dai bata ko
kalleta ba balle ta tanka ta, Ammi ta fito ta gaida Inna, Inna ta amsa tace
"Aisha yanxu baki nuna ma yarinyar nan karatun tawakali??" Ammi tace
"Ciwonta ne fa ya tashi Inna" Inna tayi shiru tana kallonta, can tace
"Dama imaan na da wani ciwo ne da ban sani ba?" Ammi tace "Ciwon
nata kuma Inna kika manta?" Inna ta rike ha6a baki Bude tana kallon Ammi,
can tace "Ni dai ba ruwana, ku je kuna fadan haka wani ya ji, dama banda
rashin lafiya da kowa ke yi Imaan na da wani ciwo na daban ne ban sani
ba?" Ammi tace "Toh ko jiya ma Abbanta yace wannan yaron da ke
nemanta ya kamata a sanar masa laluranta tun yanxu" Gwalo ido Inna tayi ta
saki salati tana tafe hannu ta xauna ta rike kai tace "Naga abinda ya
isheni ni patuuu, wayyoo Allah duniya ta lalace" dagowa tayi tana kallon
Ammi tace "Aisha da hankalin ku ke da Bukar kuwa? Dama Imaan na da wani
ciwo ne ni da ban sani ba, ku dai ku dinga fadin gaskiya ku ji tsoron Allah,
yaushe rabon da in ji Imaan bata da lafiya a gidan nan, Ni dai kada wanda ya
laka ma jikata ciwo lafiyarta lau, waye baya xaxxabin maleria da thypho, to
kada ma ku kuskura wani yaji wannan mugun xancen, ku dai ba kwa fadan alkhairi
a gidan nan, Ni dai ba ruwana, yaushe rabon da tayi ciwo?? Ai yafi shekara
biyar ba ma banda sharri irin naku...." Mikewa Inna tayi ta nufi kofa rai
bace tana cewa "Mutane dai ba tsoron Allah, meye kuma wai a gaya ma yaron
da ke nemanta laluranta kamar mai cutar AIDS... Ni dai ba ruwana" a bude
tabar masu kofar bayan ta fita ta kara gaba, Ammi na kallon Imaan tace
"You make sure you tell him everything about ur health condition, kar ki
boye masa komai" Imaan ta sauke idonta kasa a hankali tace "Toh
Ammi" Ammi ta xauna kan kujera a ranta tana jinjina halin inna, imaan ta
kalleta tace "Ya ce xai xo anjima" Ammi tace "Toh sai ki gaya
masa" biyar da few minutes Sadeeq ya kira Imaan ta wayar Ammi ya sanar
mata yana waje, bayan ta gaya ma Ammi, Ammi tace "Toh kar ki dade dai a
waje" "Toh" kawai imaan tace ta sa hijab dinta ta fita, tana
isowa gun motar ya bude mata back seat yana kallonta yace "Shiga ki
xauna" girgixa kai tayi tace "A'a..." Yace "No pls ki shiga
kinga you are sick, you look so weak, bana son musu get in plss" shiru
tayi bata ce komai ba, komawa gefe yyi ta shiga motar a hankali, yana kallonta
yace "Kun je clinic kuwa?" Tace "A'a Dr dina ya xo ya min
allura" ido ya kafeta da shi, hakan yasa ta sunkuyar da kanta yace
"What's wrong with you?" Ba
tare da ta dago ba tace "I woke up with headache, backache and joint
pain... pains everywhere...." Ya d'an bude ido da mamaki ya cire glasses
din idonsa yace "Yana maki haka ne dama?" Ta kallesa ta gyada masa
kai gently, kasa daina kallonta yayi, murya can kasa yace "Are you... A
sickler?" Girgixa masa kai tayi tana murmushin karfin hali tace "I am
a carrier, I am carrying the trait" jin yyi shiru ta daga kai ta kallesa,
tausayi taga karara a kwayar idanuwansa yana kallonta, underneath his breath
yace "Ya Salam, a very rare case, Subhanallah" murmushi kawai tayi
bata ce komai ba, jingina yyi da motar ya rungume hannunsa yana kallon gate din
shiga gidan looking so disturbed.
Umma ta share xufar da ke keto mata bayan ta gama sauraran
bayanin mutumin gabanta, Hajiya Saude sai jinjina kai take, da kyar Umma na
gyara xama tace "Toh malam yanxu meye abun yi.... A taimaka don Allah,
wllh ji nake kamar xuciyata xata fashe, ko kuma in hadiye xuciyar, duk duniya
bani da makiya da ya wuce yarinyar nan da uwarta, uwarta ta xalunce ni a rayuwa
ta cuce ni, a dalilin uwarta na shiga gararin rayuwa malam ka taimakeni ko nawa
ne ni xan biyaka wllh, Malam ka dubeni..." Mutumin dake xaune gabanta ya
girgixa kai yace "Auren nan fa na gaya maki idan ba wani Ikon Allah ba sai
an yi sa, mijinta ne d'an gidan attajirin babu tantama, sai dai kuma wani Ikon
Allah, gashi nan na gani, gashi nagani har ranan bikin..." Hawaye ya kawo
idon Umma tace "A dai duba malam a taimaka" Malam yace "Toh ga
takarda sai ki rubuta abinda kike son ayi a ciki, amma fa banda kisa... don
yarinyar na da tsawon rai haka ma Yaron sai dai kuma wani Ikon Allah, sannan
kuma baxa a iya raba su ba.... yar ki kuma da kike son yaron ya fara nema kuma
ba mijinta bane baxai taba yiwuwa ba, ba mijin yar ki bane yaron attajirin....
Sannan ina maki tuni surkarki a tsaye take kan yarinyar.... Tasirin aikinmu a
kanta kamar ko da yaushe dai kalilan ne kema kin sani, Ki rubuta komai amma
banda abubuwan da na lissafo maki a baya" Umma ta gyara xama tana share
hawayen idonta ta amshi takardan da biro ta ajiye kasa ta fara rubutu.....
*imaan isn't free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
37.....
Da addare Imaan na kwance parlon Inna dake xuba wani garin
magani a kindirmon dake cikin cup din gabanta, Maimoon ta shigo da sallama ta
ajiye abincin hannunta ta gaida ta, Inna ta mika mata cup din tace "Mika
ma waccan matar" Imaan ta juya masu baya da sauri tana turo baki, Inna ta
kalli Maimoon tace "Kinga walakanci ko, wannan wace irin yarinya ce don
Allah, ta san daga inda maganin nan ya fito?" Imaan tace "Ni nace
maki na sha magani fa a gida, ya xa ayi in hada magani iri biyu" Inna ta
ajiye spoon dina hannunta tayi tagumi tace "Oh waannan 'ya ta Bukar dai
jarababbiya ce wllh, Toh meye da maganin da baxata sha ba? Ba daci, ba 6auri,
ba hamami, ba galmi sai ma gyara mata bakin ta da xai yi, ta ji dadi kuma a
jikinta, to ni dai ba ruwana gashi can uwar ki da ubanki sun fara laka maki
ciwon da ba a san ki da shi ba ba a san kansa ba, wai dama idan lkcn gabatar da
yaro ya kusa ba duk iccen da aka jika ma yaron aka basa sai ya amsa ya sha ba
sbda a kauda ikon makiya, Ni dai ba ruwana Ina taimakon ki kina min wlknci,
idan ta uwarki ce sai dai fa ki mutu ba abinda xata maki, shi kuma Bukar na can
na neman na abinci a Habuja, to wa gare ki banda Allah sai ni din, to ni ba
ruwana, ki tashi ki amshi maganin nan ki sha ni ba asararriya bace, uwata bata
ce min jeki kya gani ba da xan dinga maki bauta baki gani, ko ubanki bai samu
haka a guna ba" Maimoon ta ajiye cup din hannunta ganin imaan ta ki amsa
tace "Inna ni dai xan je inci abinci" Inna tace "Toh idan kin
gama ki dawo kema ga naku da su fitsararrun can Ummi, ba dai don halinsu ba, ya
xanyi tunda ni na haifi Ahmadun" Maimoon dai bata ce komai ba xata fita
sai ga Mujaheed ya shigo parlon, gaishesa Maimoon tayi ta fita, Inna tace
"Mujaheed waya dai ko sama ko kasa, an dai rasa wanda ya sace, ni na ma fi
xaton hauro kantangar aka yi, ai daga yanxu ni kaca ma xan dinga sawa in rufe
kofar da kwado idan xan fita, Ina dalili? Ai ko ya daukan ma kansa fitinar
duniya" Mujaheed ya gaisheta sannan yace "Za a xo daukan akwatunan
nan" Inna ta kallesa sannan tace "Ita da ta turo ka ba sai ta xo ta
kwasa ba in ga, Rukayya dai tayi hankali da ni ba ruwana.... Wannan yarinya
kuma kayi mata magana ta rufa min asiri ta dau nonon nan ta sha ba sato kudin
nake yi ba, dubu goma kenan cikin kofin a kwance ta rasulu ta sa aka amso
min" Mujaheed bai ko kalli imaan ba yace "Kaya xa a karasa xubawa
cikin akwatunan shi sa xa a dauka" Inna tace "Sai kuma ka yi ai, ko
Ahmadu bai isa yace xa a dau akwatunan nan ba balle kai" Kallonta ya dinga
yi fuska daure, can ya juya ya fita. Washegari da safe Mujaheed ya shigo parlon
Abba da sallama ta dalilin kiransa da yayi a waya, Abba na kallonsa yace "Jikin
Imaan ya matsanta mata, yanxu Hajiya Aisha ta kirani..." Mujaheed yace
"Toh a tafi asibiti kawai" Abba yace "Toh xa ka kai ta ne?"
Girgixa kai yyi yace "Zaria xan tafi Abba, kuma likitan ta na gari
ai" kallonsa kawai Abba yayi bai ce komai ba, Mujaheed yace "Xan je
in shirya yanxu" Abba yace "Ohk then" Juyawa yayi ya fita
parlon. Sai kusan la'asar Ammi da Aunty suka dawo asibiti da Imaan, nan parlor
Imaan ta kwanta Ammi ta shiga kitchen don girka mata light food ta ci, Imaan ta
jawo wayar Ammi dake vibrate kusa da ita ta kalli screen din, Sadeeq ta ga ke
kira, sai da ya kusa katsewa ta daga da kyar ta kai kunne tayi masa sallama, ya
amsa yace "Kun dawo gida ne?" Tace "Um..." yace "Ohk
before magrib xan kawo maki drug din, but I have to see wanda aka baki a asibiti"
tace "Toh" yace "Allah ya kara lafiya" a hankali tace
"Ameen" yace "Do you need anything" tace "A'a"
yace "Sure?" Ta gyada kai kamar yana ganinta, yace "Ohk sai na
xo" daga haka ya katse wayar. Karfe shidda saura Yusuf ya shigo parlon da
sallama, Imaan na xaune bayan tayi wanka ta shirya tana cin farfesun kayan ciki
da Ammi ta mata, xaunawa yyi ya sakar mata murmushi yace "Sannu, ya
jikin?" Ta mayar masa murmushin tace "Da sauki ya Yusuf" yace
"Toh Allah ya kara lafiya, Ammi fa?" Imaan tace "Ta shiga
daki" Yace "Ohk, me xa a kawo maki na marasa lafiya" ta kallesa
ta marairaice tace "Kawai awara nake son ci" ya d'an buda ido yace
"Awara?" Ta gyada masa kai a hankali, yyi murmushi yace "Toh
bari a nemo maki" mikewa yayi yace "Anjima xan taho maki da shi, ki
gaida Ammi idan ta fito" tace "Toh" daga haka ya nufi kofa ya
fita, ko minti biyar ba ayi da fitansa ba sai ga kiran Sadeeq, sanar mata yyi
yana waje tace "Toh ka shigo" Sadeeq ya d'an buda ido yace "Ni
fa Ina jin kunyar Ammi" Murmushi tayi tace "Ae tana daki" Yace
"Uhn toh gani nan shigowa" ajiye wayar tayi bayan ta katse, ta mike
ta wuce dakin Ammi ta sanar mata Sadeeq xai shigo, Ammi tace "Toh haka
xaki tsaya babu hijab" ta girgixa kai tace "A'a xan dauko a daki yanxu"
Ammi tace "Ohk" daga haka Imaan ta fita ta shiga dakinta ta dauko
hijab ta sa ta dawo ta xauna xata rufe farfesun gabanta yayi sallama bakin
kofa, ta kalli kofar ta amsa sallaman sa, ya shigo parlon, sunkuyar da kanta
tayi ya xauna saman kujera ya ajiye ledan hannunsa a kasa yana kallonta yace
"Sannu Imaan, ya jikin?" d'an murmushi tayi tace "Ina yini"
yace "Lafiya lau, Ina drugs din da suka baki a asibiti" mikewa tayi
ta nufi daki ya bi ta da ido, ta dawo rike da ledan drugs din, ajiye masa tayi
a kusa da shi, sannan ta koma ta xauna, yayi murmushi ya dau ledan ya fiddo
Magungunan yana dubawa, can ya mayar da su, ya dau karamin ledan da ya shigo da
ya ciro drugs biyu yace "You can take this also ba komai, na rubuta
prescription din a jiki" ta gyada masa kai ya ajiye maganin, ya ciro wani
na tube yace "Wannan ma ki dinga shafawa a duk inda kike jin pain"
Imaan tace "Toh..." Ya d'an bude ido murya can kasa yace "Ko in
shafa maki dear?" Xaro ido tayi ta kallesa sai kuma ta boye fuskarta a
kujera, murmushi kawai yake yana kallonta, ganin ta ki dagowa yace "Toh
baki cinye pepper soup dinki ba" a hankali ta dago tace "Ko xaka ci
ne?" Yayi murmushi yana shafa beard dinsa yace "Ai baki bani ba"
daukan bowl din tayi ta kai gabansa ta ajiye, ya xaro ido yace "I am only
joking" tace "Ae sai ka ci" yace "Plss ki dauke, wllh wasa
nake maki I am okay" ta make kafada tace "Ai kace ban baka ba to
gashi ynxu na baka" ya wani xaro ido yace "Kar Ammi ta fito ki dauka
plss" cike da shagwaba tace "Sai ka ci" yace "Ohk ohk idan
na ci xaki dauke" tana murmushi tace "Ehh" yace "Toh dago
min" daukan bowl din tayi ta rike da hannu biyu ta durkusa gabansa tana
kallonsa har sannan tana murmushi, ya lumshe ido ya bude ya dau spoon din ya
dau nama guda daya yayi kamar xai bata a baki ta koma baya da sauri, bakinsa ya
kai spoon din ya ci, ta wara ido tana kallonsa, ya lumshe ido yace "It's
sweet" dariya ta fara yi kasa kasa tace "Ashe kai ma ka iya
kwadayi" da sauri ya bude ido, ta koma ta xauna still tana dariya,
murmushi yyi yace "Ai xan rama" ta buda masa hannuwanta tace "Ko
dai ka rame" kallonta kawai yake affectionately, ta turo baki tace
"Ni dai ka daina kallona haka" dauke idonsa yyi yana murmushi yace
"Watarana xaki yi bayanin me yasa xan daina kallonki" bude kofar
parlon aka yi duk suka juya, daddy ne ya shigo parlon da jakar laptop dinsa
Mujaheed na bayansa rike da traveling bag dinsa, imaan ta wara ido ta mike da
sauri tace "Daddy" murmushi ya sakar mata, tana son xuwa ta rungumesa
amma ta kasa saboda Sadeeq, ta isa gabansa cike da farin ciki, a hankali tace
"Sannu da dawowa Daddy, baka ce min yau xaka dawo ba" Daddy ya shafa
kanta yace "I just decided to come back and check on you daughter, how are
you feeling now" tace "Da sauki sosai Daddy, har na ci abinci
ma" amsan ledan hannunsa tayi, ya karasa parlon yana kallon Sadeeq kamar
yanda Mujaheed ma ke kallonsa, Daddy na murmushi yace "Sadeeq" Sadeeq
yyi kasa da kai yace "Sannu da dawowa Abba" Daddy yace "Thanks
son, ya aiki" Sadeeq yace "Alhmdllh" Daddy yace "Ya Mai jikin?"
Sadeeq yace "Alhmdllh she's getting better" Daddy yace "Maa sha
Allah" Kallon Mujaheed Sadeeq yayi yace "Barka da yamma...."
Mujaheed yace "Thank you" Ajiye jakar hannunsa yayi yana kallon daddy
yace "Allah huta gajiya Abba" Daddy yace "Ameen son" imaan
dai ko kallonsa bata yi ba kamar yanda shi ma bai ko kalleta ba ya juya ya nufi
kofa, Daddy ya wuce bedroom dinsa, mikewa Sadeeq yayi yana kallonta yace
"Kin ga kunyar da naji" dariya imaan tayi tace "Kunyar me?
Sadeeq na shafa kai a hankali yace "Kunyar Abba mana" Imaan tayi
murmushi bata ce komai ba, yace "Ki gaida min da Ammi, let me get going
now" a hankali imaan tace "Toh nagode, Allah ya tsare" yace
"Ameen dear, Allah ya kara lafiya, and plss kar kiyi wasa da drugs din
ki" Ta d'an yi murmushi tace "In sha Allah" yace "Toh baxa
ki rakani ba" tace "Toh xan raka ka bakin kofa" yace "Noo
bakin mota dai plss my dear" tace "Toh idan na fadi a hanya fa"
yace "Sai in daga ki sweet" boye fuskarta tayi ya nufi kofa yana
murmushi ta xaro ido tace "Ka manta ledan ka" ba tare da ya juyo ba
yace "Na ki dai" shiru tayi tabi sa da ido sannan ta bi bayansa,
kamar mai tausayin kasa ta isa kusa da shi don tsaye yyi yana jiranta, a jere
suka dinga tafiyar yana kallonta ita ko ta ki yarda ta kallesa, Ni kam nace
waow perfect couples they will make... Lol, A dai dai bangarensu Maimoon Umma
ta fito ta nufi parking space kana ganinta kasan fita xata yi, Sadeeq ya
kalleta yace "Ina yini" tace "Lafiya lau" Imaan tayi kasa
da kai a hankali tace "Ina yini?" Banxa Umma tayi mata ta bude back
seat xata shiga, Imaan dai bata kalleta ba suka fita tare da Sadeeq, ido hudu
tayi da Mujaheed dake xaune gun Mai kiosk dake kusa da gate din su, Dauke kai
tayi da sauri, Sadeeq bai ma lura da shi ba, ya isa gun motarsa tana biye da
shi, Yana kallonta yace "Keep on greeting her xata amsa wataran, you will
loose nothing don kina gaisheta...." murmushi kawai Imaan tayi, ya kafeta
da manyan idanuwansa, murya can kasa yace "Plss ki dinga cin abinci da
yawa sweet, kin rame fa" ta wara ido tace "A'a ni dai haka nake"
kallonta kawai yake bai ce komai ba, ta sunkuyar da kai tana wasa da fingers
dinta, underneath his breathe yace "I have always loved you from day 1
imaan..." kasa kallonsa tayi gabanta ya dinga faduwa, kamo hannunta yyi a
hankali ya lumshe ido xai kai lips dinsa ta kwace hannun da sauri tana satan
kallon inda Mujaheed yake, kallonsu taga yana yi, Sadeeq ya kalli inda ta kalla
suka yi ido hudu da Mujaheed, dauke kai yyi a hankali yace "We will talk
later dear" daga haka ya shiga motar ta juya ta nufi gate gabanta na faduwa
tana satan kallon Mujaheed da ya bi ta da ido fuskarsa dauke da wani
expression, rufe gate din tayi tana kara kallonsa sannan ta wuce part din su da
sauri. Mujaheed na gama parking ya juya yana kallon ummansa dake Bayan motar
sai danna waya take, ta daga kai da sauri tace "Au, har an kawo ashe"
bude motar tayi bayan ta ajiye wayar tace "Ka jira ni ba dadewa xan yi
ba" yace "Umma aiki nake son wucewa don Allah kar ki dade" tace
"Na sani baxan dade ba Mujaheed" daga haka ta fito motar ta shiga
gidan Hajiya Balaraba, ita kadai ce babban gidan duk kishiyoyinta dama ta
rabasu da gida, Hajiya Balaraba dake parlor xaune tace "Daga Ina haka
Hajiya Rukayya" Umma tace "Daga gida Ina son kai ma Hajiya Saude
kudin da ta ranta min na ba mutumi, sannan ku dai xauna da shiri sati mai xuwa
xa a kai lefe gidansu Safeenah" Hajiya Balaraba tace "Toh Allah dai
ya kai mu lafiya, amma ya ku ka kare jiya ina ta son in kira ki ko inje gida in
sameki" Umma ta tabe baki tace "ya dai sa in rubuta masa abinda nake
so ya faru, na kuma rubuta yace min in sha Allahu an gama, abu ne mai matukar
sauki.... Kar ki so ki ga irin farin cikin da nake wllh Hajiya, idan hakan ya
faru ae har Aisha ta mutu baxata rabu da ciwon xuciya ba" Hajiya Balaraba
ta xaro ido tace "Toh me kika rubuta halan?" Umma ta rike ha6a tace
"Cewa yyi kar in gaya ma kowa, ki sha kurumin ki aminiya, komai xai fito
fili xa ki gani" Hajiya Balaraba tace "Amma xa su yi auren kuwa"
Umma tayi dariya tace "Ehh to yace yaga da auren, amma ban jin abinda xai
faru xai sa ayi auren nan... Kinga bari inje na bar Mujaheed yana jirana a
waje" sallama tayi mata ta fita tana murmushi.
*imaan isn't free* the subscription is 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
38....
Imaan na kitchen tana yanka ma Ammi pumpkin leaves ta ji an
danna bell, barin ganyen tayi a chopping board ta dauraye hannunta ta fito,
bedroom dinta ta shiga ta dauko hijab ta sa sannan ta nufi kofar ta bude,
Mariya ta gani tsaye bakin kofar ta xaro ido tace "Mariya Ahmad"
Mariya na murmushi tace "Am I not welcm?" Sai a sannan Imaan ta kara
ganin mugun kamar da suke da Sadeeq har dimples din, ta kamo hannunta cike da
murnar ganinta tace "Sosai ma besty, daga Ina kike haka? Come in
plss" Mariya ta shiga parlon tace "Mumy ce ta aiko ni wancan layin
dake gaba da naku shine nace let me branch and say hi, ni da yayanmu ne
ma" Imaan ta wara ido tace "Wanne?" Mariya tace "Wannan da
ya taba maido ki gida da kika xo gidanmu" Dariya kawai Imaan tayi bata ce
komai, har yau kuma tana mamakin me yasa Mariya bata ta6a nuna mata ta san suna
tare da Sadeeq ba, ko bata sani bane?? She still can't tell, Imaan tace
"Toh xauna plss in kawo maki ruwa mana" Mariya ta xaro manyan
idanuwanta tace "Ya Sadeeq xai wuce kenan ya bar ni, dama kawai shigowa
nayi mu gaisa ai daga gida muke, am okay dear" Imaan tace "Toh shkkn
nagode kuma naji dadi" Mariya tace "Mum fa?" Imaan tace
"Taje kasuwa tare da mamansu Maimoon" Mariya tace "Toh ki gaishe
min ita idan ta dawo, mu je ki rakani, baya son jira wllh" imaan na
murmushi tace "Toh shikenan mu tafi in raka ki" a tare suka nufi gate
bayan sun fito parlon, Mariya tace "Ya shirin Sauka fa?" Imaan tace
"Ina ta yi" Mariya tace "Ae kam gashi lkci sai matsowa
yake..." Imaan tayi murmushi bata ce komai ba har suka fita gate, ta dinga
kallon lafiyayyen ride dinsa dake parke a waje ba wanda ya saba xuwa da shi
wajenta ba, tun da suka fito Sadeeq ke kallonta ta cikin glasses din idonsa ko
kiftawa babu, har suka iso kusa da motar ya sauke glass din motar yana kallonta
murmushi dauke fuskarsa, imaan ta sunkuyar da kanta tana fidgeting fingers
dinta tace "Ina yini?" Cikin cool voice dinsa yace "Lafiya
lau" Mariyata kallesa tace "Yaya ka tuna ta? Frnd dita din
nan..." Sadeeq yyi murmushi ya girgixa kai yace "Ni kuma sbda mantuwa
na yyi yawa kullum sai anyi min introducing dinta koh?" Dariya Mariya tayi
tace "Eh mana Yaya frnds dina kullum ba ganesu kake ba sai kace ka manta,
to ita ma nasan ka manta ta" Ya shafa kansa yana kallon Imaan har sannan
yana murmushin sa mai kyau yace "Ita ai baxan manta ta ba" Imaan dai
bata yrda ta kallesa ba, Mariya ta juya ido tace "Toh ya sunanta?"
Yar dariyarsa yyi mai kyau yace "Kin fini sanin sunanta ai" Mariya
tace "Na kamaka a nan, you are just pretending amma ka mance ta yaya"
Sadeeq ya daga kafada yace "Ohk then, let leave it that way, na
manta" Mariya tace "Tohm gwara dai" kallon Imaan tayi tace
"Bye frnd ki gaida mum idan ta dawo plss" Imaan tace "In sha
Allah, nagode da ziyara" Sadeeq ya d'an kalleta yace "Toh kawar Mariya
sai anjima" Imaan ta hararesa ta gefen ido ta wuce ciki da sauri, ya bi ta
da kallo yana murmushi, Mariya ta rungume hannayenta tace "Hmmm Yaya
wannan kallon fa?" Da sauri ya kalli step sis din tasa, sai kuma yyi
murmushi yace "Kallon gate din gidan?" Dariya tayi sosai ta xaga ta
shiga gaban motar ya tada motar ya bar layin. Mamaki Imaan ta dinga yi na me
yasa Sadeeq ke boye ma yan gidansu gashi dai ajinsu daya da Mariya both
islamiyya da Schl amma bai gaya mata ba, tabe baki tayi ta cire hijab dinta ta
shiga kitchen ta ci gaba da aikin da take. Bayan ta gama duk abinda xata yi
bayan la'asar ta wuce part din Inna don su Ammi basu dawo ba har sannan,
Mujaheed ta tarar bakin tap yana alwala, tun da ya kalleta sau daya bai sake
kallonta ba ya ci gaba da performing ablution dinsa, ta wucesa ta shiga parlon
Inna, Inna ta mika mata abun kwashe sharan hannunta wanda ba komai ciki sai few
dirt tace "Xubar min wannan a bola, dubi fa parlon kamar ba komai amma ji
yanda datti suka cuceni suka makale, kamar na sani nace bari dai in share in
gani, ilai kuwa ga shi har da guntun kasa, kila ma wannan mutumin ne ya shigo
min da su, sam datti bai da masugunni a parlona gaskiya" amsa imaan tayi
ta fita ta kakkabe abun kwashe sharan ta dawo, ta bi Mujaheed da kallo ganin wucewarsa
yyi ta shiga parlon, Inna ta shimfida tabarma ta xauna tace "Ke ki ji ya
xo min nan ya kwanta salon ya fara wannan xaxxabin nasa a ce a parlon Inna haka
ya faru" Imaan ta xauna saman kujera tace "Ba shi da lafiya ne?"
Inna tace "Wai daga anje an kai kudin gaisuwa shine har ya fara tunanin
rabuwa da ni bai san tare xa mu tare a can gidan nasa ba" Imaan ta xaro
ido tace "Shi yace maki haka?" Inna tace "To sai ya fada?? ko
bai fada ba nasan hakan ne ma, ke kinsan shakuwar da Mujaheed yyi da ni
kuwa? Nima har na fara jin xaxxabin xai
rufe ni" Imaan tayi dariya tace "Yaushe aka kai gaisuwan?" Inna
tace "Daxu da safe su Ahmadu da Bukar da Bala da abokan Ahmadun suka
kai... jibi kuma xa mu je kai lefe ki shirya tare xa mu dake" Imaan ta
xaro ido tace "Har da ke?" Inna ta saki baki tana kallonta tace
"Oh oh Allah, ban gane har da ni ba, to dama su waye masu kai lefen idan
ban da ni... Ni ana bani mamaki wllh haka Ahmadu da Bukar wai bai dace ba inyi
xamana a gida, to a kan me? Ni fa nayi wahala da shi Mujaheed din, sannan ba
shi da wata kaka da ta wuce ni a duniya, in har baxan je ba dama sai dai iyayen
yarinyar so su dau lefen da kansu ba ruwana" Imaan dai bata ce komai ba,
Inna ta mike ta shiga daki sai ga ta ta fito rike da wani takarda, tana kallon
imaan tace "Duk cikin jikokina kece kadai xan ce tayi abu tayi, da kyar
kiyi min musu, sauran kuwa dama baxa su yi ba, to wannan ba wani damu na yayi
ba don kansu suke ma, ga wannan wanka xa ki yi da shi ni dama baxan ba su Ummi
su xubar min dukiya ba ba ruwana ba sato kudin nake ba, ke kadai ma
amsowa" Imaan ta turo baki tace "Meye shi din?" Inna tayi kasa
da murya tace "Wllh garin magani ne, sai kamshi ma yake, ko uwarki kada ki
gaya ma ba hankali gareta isasshe ba sai ta hanaki amfani da shi, ki xuba a
cikin bokitinki ki tara ruwa bakin ki a leko ki yi ki fito kin ji
takwarata" Imaan tace "Ni wllh kaikayi xai dinga min a jiki fa"
cike da fada Inna tace "Yau naga jaraba sai kace warce xan ba karara? Meye
kuma wani kaikaiyi ni patuu? Garin magani ne fa ba wani abu ba" Imaan ta
hade rai tace "Toh bana so baxan yi ba" Inna tayi kasa da murya tace
"Toh yi hakuri takwara, abinda ma idan kika yi yau kika yi gobe shkkn,
wllh dubu goma kenan kar ki ja min asara ba ramin kudi gareni a dakina ba, ba komai
sai tarkacen kwallaye da tsoffin akwatuna" imaan ta turo baki ta amsa tace
"Toh wai na meye?" Inna tace "Kaikayi koma kan mashekiya"
Imaan ta xaro ido tace "Meye hakan?" Inna tace "Duk wanda xai sa
maki ido a duniyar nan idonsa xai tsiyaye tass barsa da jakar idon, idan kuma
mugun abu xai maki to fa sai dai ya koma kansa ne ni ruwana, babu wanda ya san
ta yanda Bukar ya sameki" Murmushi kawai Imaan tayi, Inna tace "Su
Maimoon ma ga nasu can na ajiye masu ba don halinsu ba" Imaan tace
"Toh" Inna tace "Ni kwana biyu banji Bulasawa ya kirani ba, ko
dai lambar ta bace a wayana ne shi sa baya iya kirana" daukar wayar tayi
ta mika ma imaan dake dariya tace "Ke duba min, ba halinsa bane rashin
kiran duk kwana biyu kya ga ya kirani mun gaisa har in fada masa damuwata"
imaan ta gama danne dannenta ta mayar mata wayar tace "Network ne ya dauke
sai bayan sati daya xai dawo" Inna ta saki baki tace "Saboda me
toh?" Imaan ta mike tace "Ae haka yake yi" daga haka ta fice
parlon tace "Na tafi" Inna ta ajiye wayar tace "Toh Allah ya
mana tsari da su masu wayan" Ranan Friday da yamma babu yanda Abba da
Daddy basu yi da Inna kan cewar tayi hakuri ta bar yan uwan umma, Matan kawu
Bala, Ammi da Aunty sai kanwar umma da kawayenta biyu su kai lefe gidansu
Safeenah ba inna tace samm bata san xance ba da ita xa a kai kayan, Daddy dake
ta kallonta yace "Yawanci ynxu fa iyaye maxa ne ma ke kai kayan ba mata ba
Inna, ke me xaki je kiyi cikin yara don Allah" Inna ta masa wani kallo
tace "Toh ko a baka kayan ka kai ne Bukar?" Daddy bai ce komai ba,
Inna tace "Yau naga jaraba, to wai ina ruwan Bukar a maganan nan
fisabilillahi, Wai xanje cikin yara, A'a gyambo ce ni karewar girma, kawai ayi
ta laka ma mutum tsufa, ni din nawa nake gaba daya tukunna ma dai, kamar warce
dai ta haifi duniya??" kawu Bala yyi kasa da murya yace "Hajiya Inna
da dai kiyi hakuri ki bari su kai kawai, ke fa babba ce...." Inna ta
dakatar da shi a fusace tace "Kai rabu da ni Balalau, Ina ruwanka?? Ka san
da xamana a kaduna ko ka taba xuwa takanas ka gaisheni? Ko gantalallun matan ka
ma ba turo su kake ba balle yaranka, yau da Hurera na da rai xaka mata haka,
Allah dai ya mata Rahama ya gafarta mata bata min komai ba, lafiya muka xauna
da ita...." Mikewa daddy yyi ya fice a parlon, Inna ta bi sa da kallo tace
"Wannan Bukar din dai ba shi da kirki wato ga mahaukaciya na magana shine
ya fita, Wai... Ai da Bukar ne ke xaune a kaduna wllh baxan sha ruwa a gidan
nan ba, mulkata kawai xai dinga yi da bafillatanar nan da figaggiyar Yar su,
Toh sae Allah ya rufa min asiri Ahmadu ne, kwata kwata Ahmadu dama bai son
abinda xai ta6a ni a duniyar nan shi da yaransa, kaga inda ya fi Bukar kenan,
to meye kuma daga magana dai ta fahimta xai kwashi jiki ya fita" murmushi
kawai Abba ke yi da kawu Bala da yyi hamdala a xuciyarsa da ta katse tsigesan da
tafara yi ta koma kan daddy, Abba yace "Toh shikenan dai Inna, Allah ya
kiyaye hanya sai kun dawo" Inna tace "Toh dama mota daya xa a ware
mana da imaan da kawata ta rasulu, tace min tana hanya" Abba ya buda ido
da mamaki yana kallonta, kawu bala yace "Toh madallah Allah kawota
lafiya" daga haka ya fita Abba ya bi bayansa, Kawu Bala na ta murmushi
yace "Ayi ta hakuri Barrister tsufa ne" murmushi kawai Abba yyi yace
"Ana ta yi, sai dai Allah ya kara mana hakurin" Kuka umma ta xauna
kan gado ta dinga rusawa jin da Inna xa a je kai lefe tana kallon kawayenta
tace "Babu abun kirki idan aka tafi da matar nan wllh, xuwa xata yi ta
mana tonon asiri, tayi ta sakin xance a gidan"
*The book Imaan isn't free* it's 300
Via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then you show ur evidence of payment via my WhatsApp digit
07087865788 subscribe and read without been judge by ur
conscience.
39.....
Mujaheed dai na tsaye kitchen sae kallon Umma yake har ta kai
aya, jin yyi shiru a fusace tace "Wae ba da Mujaheed nake magana bane??"
Ya d'an shafa kai yace "Ina ji Umma, Toh ni ya xan mata, kinsan tunda tace
sai taje, ba wanda ya isa hanata xuwa ne" Umma ta hade rai tace
"Yanxu baxa ka samo dubara da xaka hana xuwan nata ba, wllh idan taje
gidan nan tsaf xata iya sa su fasa baka mata, tun da uwata ta haifeni ban taba
ganin mutum sakakka irin tsohuwar nan ba, ni dai duk yanda xa ka yi ka rufa min
asiri kayi ka hanata xuwa Marafan nan don Allah, ga ta can bakin motoci tsaye
sai nuna hali take" Mujaheed yyi murmushin karfin hali yace
"Toh..." Juyawa Umma tayi ta fice daga kitchen din rai bace, Inna dai
na tsaye an sha super da mayafi da yar jakarta sae xuba kamshi take, duk mutan
wajen dama sun bar jikin motar an bar ta ita kadai barin kawayen Umma, ta aika
Maimoon ya fi sau uku ta kira mata Imaan amma shiru, ganin Maimoon ta dawo for
the 4th time Inna tace "Yau naga abinda ya isheni ni patuu, Ina Imaan din
ta shiga ne wai??" Maimoon tace "Inna ni fa ban ganta ba" Part
dinsu Imaan Inna ta nufa fuska daure tana cewa "Ni ai xan ganta idan
naje" Daddy ne xaune parlorn yana operating laptop dinsa, ta shigo parlon
ko sallama babu tana kallonsa tace "Bukar Ina Imaan ta shiga ne wai, ko
bata san duk jama'ah sun taru ita ake jira bane?" Daddy ya kalleta yaci
gaba da abinda yake yace "Tana daki...." Inna tace "Kaga
walakanci ko, wllh tarbiyar 'yar ka kalilan ne Bukar, ce mata nayi fa ta shirya
ta fito mu tafi amma don wlknci ta shanya ni a rana ina ta jiran fitowarta,
gafara xata min ne ko menene haka??" Daddy ya kalleta yace "Ku je Ina
wai?" A fusace Inna tace "Kai lefen mana, ko gwari nake maka"
girgixa kai yayi yace "Don Allah ki bari Inna, me xata je yi gidan...
cikin manya kuma, kai lefe dai tun daxu ana ta abu daya ya ki ci yaki cinyewa,
Ni nace mata baxa ta je ba don babu sa'anta a masu kai kayan, kema kawai don
kince sai kin je ne babu yanda muka iya..." Inna ta saki baki tana
kallonsa, can tayi kasa da murya tace "Meye laifina don nace xanje kai
kayan jikana da nayi wahala da tun yana tsumma, me yasa baka da fahimta d'an
uwanka ya fi ka fahimta Bukar...." Sai kuma ta fara matsar kwalla tace
"Toh ai shikenan sai in fasa xuwa a kira ta Rasulu ace tayi xamanta, ai ba
aikin Allah bane kai lefen na hakura" Daddy yace "A'a ni bance kar ki
je ba tun da kinyi niyya kiyi tafiyar ki amma Imaan baxata je ba gaskiya"
Inna tace "A'a su tafi, haka kawai in bata maku rai kan tsinannen lefe,
dama ai babu sa'a na a masu kai kayan sai ta Rasulu ita ma xan sa a kirata ince
tayi xamanta kawai, ae gaskiya ku ka fada, duk wanda kuma ya rasa mai gaya masa
gaskiya a duniya yyi asara, ni dai na hakura da in bata maku rai sbda kayan
mutane" Daddy dai bai ce mata komai ba har ta fita, Ammi da har ta gama
shiryawa ta fito daga daki tana kallon Daddy tace "Kai me ya kai ka yin
haka yallabai, maimakon ka barta tayi tafiyarta tunda ta sa rai" Daddy
yace "Gwara ana yi ai ana mata gyara, ba gashi yanxu tace ta fasa ba, Amma
komai tace be it right or wrong sae barrister ya biye mata" Ammi dai bata
sake cewa komai ba. Inna na xaune parlonta bayan Yan kai lefe sun tafi kai lefen,
Umma kam kamar ta xuba ruwa kasa ta sha duk tunaninta Mujaheed ne yyi mata
magana ta fasa xuwa farin ciki gunta ba a cewa komai sai murmushi take bayan an
tafi kai kayan. Mujaheed ne ya shigo parlon Inna da sallama ta dalilin sawa da
Innar tayi a kirasa a waya, ita kadai ce parlon xaune kan kujera fuskarta shabe
shabe da hawaye har da majina, Kallonta Mujaheed ya dinga yi da mamaki yace
"Mai ya faru kuma?" Ta rushe da sabon kuka tace "Babu abinda
Bukar ya mance bai gaya min ba Mujaheed wai daga nace xan je kai kayanka don
Allah ya albarkaci kayan, shine ya tsitstsige ni ya gaggaya min ba dadi, yayi
ta min bala'i kamar xai ari baki wai xan je cikin yara tsofe tsofe da ni, inda
Bukar yake shiga ba nan yake fita ba, yayi min tatasss...." Wani kukan ta
kara fashewa da, Mujaheed ya xauna yana murmushi yace "Shine kike
kuka?" Cikin rawar murya tace "Baxan yi kuka ba Mujaheed, Bukar ya
lalace, yau har nuna min yayi bani da iko da figaggiyar 'yar nan tasa mai
ciwace ciwace iri iri kamar warce ta kashe d'an mutum, Ni dai ba Ruwana ba haka
Bukar dina yake ba da, duk Aisha ta lalata sa da halinsu na fulani, ta sa ya
xama jarababbe ya xama fitinanne, ga bakar xuciya.... Ni dai ban tanka sa ba
nayi shiru Ina ta kallonsa don gani nayi abun ba na lafiya bane, Ni Ahmadu baya
min haka komai nace sai dai yace min to, kwata kwata bai son bacin raina, Bukar
dai ya lalace kuma ni ba ruwana da shi da 'yar sa.... su je can su karata idan
Bala ma xai tafi ni bin sa xan yi kawai, duk kwana biyu sai in dinga kiran
Ahmadu muna gaisawa" Murmushi kawai Mujaheed yake yace "Kece fa baki
fahimci daddy ba ba fada yake maki ba kawai dai gyara ne" Inna ta daga
hannu sama tace "A'a wllh fada ya dinga min kamar xai ari baki, ni ba
ruwana kar ka xo nan ka karesa.... lalacewa ne dai ta riga ta samesa, har ni
xai bude baki yace ma babu inda yar sa xata bi ni" Sai kuma ta fara kuka
tace "A karkashin akwati fa na fiddo kayan nan ko sa su ban taba yi ba
gashi yanxu babu inda naje sai na wanke su kar su yi warin jiki, kasan mutum ba
komai bane facce datti" Mujaheed ya tabe baki yace "Kiran
kenan?" Tace "Eh wllh, na rasa wanda xan gaya ma ne na kira ka, gashi
har naji sanyi, to wa gareni dama banda Allah sai kai din, sai kuma
Ahmadu" mikewa yayi yace "Toh ki shirya sai in kai ki gidan nawa ki
gani...." Tace "Gidan da xa mu xauna?" Ta gefen ido ya kalleta
bai tanka ta ba ya fita tace "Toh ai kawai bari in fito tunda ban tu6e
kayan ba...." Mujaheed na isa part din su Imaan ya shiga da sallama, har
sannan Daddy na parlorn a xaune, ya xauna saman kujera ya gaishesa with
respect, daddy ya amsa da murmushi yace "Ya gajiya" murmushi kawai
Mujaheed yyi yace "Abba dama wai Inna ce..." Sai kuma yyi shiru yayi
yar dariya yana kallon daddy, daddy yace "Kiran ka tayi kenan" Kai ya
gyada masa, Daddy ya girgixa kai bai ce komai ba, nan Mujaheed ya fada masa duk
yanda suka yi da ita, daddy murmushi kawai yake yace "Dama xan je yanxu in
sameta" Mujaheed yace "Amma kuma xan fita da ita xuwa can gidan ta
gani, xaka sameta yanxu ko sai mun dawo?" Daddy yace "Toh shikenan ku
tafi kawai, anjima xan je idan kun dawo, Ku tafi tare da imaan din..."
Mujaheed yace "Toh" Daddy ya kira Imaan dake dakinta, fitowa tayi
parlor, ganin Mujaheed ta xaro ido ta koma da sauri ta dauko Hijab dinta tasa,
shi dai Mujaheed dauke kansa kawai yyi, Bayan ta sake fitowa daddy yace
"Ki shirya xa ku fita tare da Inna yanxu" a hankali tace
"Toh" daga haka ta juya ta koma daki, Mujaheed ya mike yace "Toh
sai mun dawo Abba" Daddy yace "Toh Allah ya tsare, thank you son"
murmushi kawai yyi ya fita parlon. Back seat ya bude ma Inna ta shiga tana cewa
"Allah dai ya shiryi Bukar, Ni dai inaga bakin cikin 'yar kazar da xa a
ban in ci a can yake min, to ni kuwa wani irin nama ne ban ci ba a rayuwar nan,
ni wllh ya ma fara bani tsoro, sam ba haka yake ba da, yasan wahalan da nayi da
shi yana karami kuwa, kamar fa baxai yi rai ba mayu suka kama min shi, kasan
lkcn yana da kyau tsantsaa ga shiga rai yanda dai kaga wannan figaggiyar yar
tasa da ya haifa, haka nayi ta wahala in gaya maka Mujaheed, Ni ce can nice nan
cikin kishiyoyi gantalallu lkcn Ahmadu na da shekara hudu shi kuma ba shi da
aiki sai shegen kiriniya yyi ta kwaso min kayan bola...." Rufe motar
Mujaheed yyi bayan ta shiga ya juya suka yi ido hudu da imaan dake tahowa sanye
da hijab dinta har kasa hannunta rike da wayarta.... Ya dauke kai ya xaga ya
bude driver seat ya shiga, Imaan ta bude back seat xata shiga ya juya ya jefa
mata wani mugun kallo yace "Do I look like ur driver?" Turo baki tayi
bata shiga ba kuma bata ce komai ba, Inna tace "Oh oh Allah, kaga jaraba
ko Mujaheed, yanxu wa ya gayyatota nan, ba Uban cewa yayi kar ta bi ni ba, meye
kuma ta wani xo mana nan salalo salalo" Imaan ta hade rai tana kallonta,
Inna tace "Ni dai ba ruwana, ki shiga gaba ki xauna tunda ubanki ba son
tarayyar mu yake ba, ni ki daina ma xuwa min sashina nunawa yake a fakaice wai
ina koya maki bakin hali" Imaan taji kamar ta juya ta koma bangarensu amma
sanin Daddy na parlor kuma kafin ta fito ta ce masa ita baxata bi su ba yayi
insisting sai taje, tasan tana komawa yanxu fada xai mata yace ta koma, haka
nan babu yanda ta iya ta shiga front seat din fuskarta a daure. Tafiyar kusan
minti ashirin suka yi xuwa gidan Mujaheed dake Unguwan sarki, throughout
journey din Inna bata yi shiru ba, Daga Mujaheed har Imaan babu mai ce mata komai,
wayarta dake hannunta ya fara vibrate ta kalla taga Sadeeq ke kiranta,
silencing wayar tayi gaba daya ta saci kallon Mujaheed suka hada ido don shi ma
kallon nata yake a sace, da sauri ta dauke kai bata sake kallon gefenta ba, Mai
gadin gidan ne ya bude gate ya shiga ciki da motar yyi parking a space din mota
uku dake cikin babban compound din da ya kawatu da shuke shuke masu kyau da
daukar hankali, Kashe motar yyi ya fito, Inna ma ta bude motar ta fito tana
kallon babban duplex din tace "Lahhh, toh ai wannan ya ma fi na ubanka
kyau da haduwa, kasan lkcn da ka kawoni ba a gama ginin gidan ba duk sai na
raina gidan...." Imaan ta bude motar ta fito fuska daure, Inna na kallonta
tana washe baki tace "Kema dai Allah yasa wanda Bulasawa xai saka ki ya fi
wannan komai da komai...." Tana fadin haka ta bi bayan Mujaheed da ya nufi
main entrance din gidan, imaan ta bi bayansu tana tabe baki, da makulli ya bude
kofar shiga gidan inna ta riga sa shiga tana rafka uban sallama, the parlor was
well furnished, babu abinda babu a ciki na xamani, Inna ta rike ha6a tana
kallon Mujaheed tace "Mujaheed duk kai ka xuba wa enannan kayan a parlon
nan, kar fa kaje bashi ya hau kanka mu shiga uku..." Bai tanka ta ba ya
wuce sama ta bi bayansa da sauri, imaan ta kyabe baki ta dinga bin hadadden
parlon da kallo, wani kofa da ta gani a parlon ta bude ta ga daki ne babba da
bathroom a ciki, ta kara bude wani taga makeken well furnished kitchen sai dai
babu kaya a ciki, ta karasa cikin kitchen din ta bude wani kofa dake ciki taga
store ne na ajiye kayan abinci, sai kuma wani kofa da xai yi leading dinka xuwa
bayan gidan, rufe store din tayi ta fito ta rufe kitchen din ma sannan ta wuce
sama, dakuna hudu ne a jere amma da distance mai d'an dama tsakaninsu, sannan
corridor din na da fadi da tsayi sosai, wani kofa ta bude taga daki ne da
bathroom a ciki, babu komai dakin sai Ac da curtains sai fitilu, ta rufe ta
bude wani taga irin wancan ne, kin bude Wanda taga alamar suna ciki tayi don
muryar Inna kamar speaker a dakin, ta bude last door din dake corridor din,
well furnished parlor madaidaici ta gani ta shiga tana kare ma hadadden parlon
kallo, can ta bude wani kofa da ta gani a parlon taga bedroom ne, shiga ciki
tayi ta rufe kofar tana kalle kalle ta karasa ta bude wani kofar taga bathroom
babba, ta d'an tabe baki ta juya ta nufi kofa ta bude suka ci karo da Mujaheed,
juya masa baya tayi da sauri tana xaro ido, taji kamar ta nutse a wajen, jin
yana sa makulli a kofar ta juyo da sauri tana kallonsa....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
40....
Ja baya Imaan ta dinga yi ganin kallon da yake mata fuskarsa
a daure, ta 6ata fuska kamar xata yi kuka, a hankali tace "Yaya fita fa
xan yi...." Bai tanka ta ba kuma bai fasa bin ta ba tana komawa baya,
ganin kiris ya rage ya risketa ta koma can kusa da window din dakin ta tsaya
xuciyarta na bugawa tace "Wayyo ni dai ka kyaleni in fita, me na
maka" dab da ita ya tsaya, xata durkusa ya dago ta yace "Training da
Ammi ta maki kenan na ba ma namiji hannun ki yayi kissing a bakin mota kina
washe baki koh?" Ta wani xaro ido tana kallonsa, tsawa ya mata yace
"Baxa ki bani amsa ba sai na baki dirty slap?" Tsorata tayi ganin
babu wasa fuskarsa, kamar xata fashe masa da kuka tace "Ni fa
Yaya...." Fixgota yayi lkci daya idanuwansa suka canxa yace "Ke fa
me?" Kasa cewa komai tayi, ta hadiye abu da kyar tace "Don Allah kayi
hakuri, ni bani na basa hannun...." Bai jira ta karasa ba ya buge mata
baki da karfi, Ta kai hannunta da sauri bakinta, lkci daya hawaye ya kawo
idanuwanta, cikin husky voice yace "I am making you this promise... babu
abinda xai hanani gaya ma Abban ki sooner or later...." ta wani gwalo ido
a rikice tace "Don Allah Yaya kayi hakuri wllh ba da gangan yayi ba shi ma
bai sani ba" Bai san lkcn da ya kara
buge bakinta ba, tayi tsit hawaye na sauka idonta, yace "Wato ke yanxu
kina ganin kin girma kin isa tadi da maxa, har wani rawan jiki kike ki fita
idan ya xo, har da jan sa xuwa parlon ku ki ajiye masa nama a gaba Saboda kinga
Inna na goya maki baya, to bari ki ji abinda baki sani ba, as far as I Muhammad
is concerned babu aure tsakanin ki da mutumin nan, you had better stop wasting
ur time and face ur study, kamar yanda na xa6a ma Seeyama miji ke ma haka da
kai na xan xaba maki mijin da ya dace da ke, duk ki gama rawan kanki xaki sha
mamaki na, wannan mutumin da kike gani is just here to spoil and use you, ba so
na tsakani da Allah yake maki ba, ki bar ganin yana kashe maki kudi ki xata wai
son Allah yake maki, lalata maki rayuwa xai yi which I will neva allow, and let
me give you this warning....." Ita dai hawaye kawai take xuciyarta na
bugawa tana kallonsa, "Daga yau kika sake tsayawa kusa da motarsa sai na
kusa sumar da ke wllh, duk karyar da xai maki ya maki a waya ba sai ya sake
xuwa kofar gida ba, idan kuwa ba haka ba a gaban daddyn ki xan xane ki sai dai
duk abinda Inna xata yi tayi..." Kuka kawai imaan take bata ce masa komai
ba, strictly yace "Am I clear?" Ta gyada masa kai da sauri, muryar
Inna suka ji tana cewa "Naga abinda ya isheni ni patuu na 6ata a gidan
Mujaheed" sai kuma ta kwalo masa kira, bude kofar Mujaheed yyi ya fita ya
jawo kofar, Imaan ta durkushe a dakin tana kuka a hankali, Inna na ganin
Mujaheed tace "Alhmdllh, ni na xata 6ata nayi, Toh ita kuma matar ina ta
shiga, har kasa fa na sauka ban ganta ba, kada ta shiga wani waje in shiga uku
dama ga Bukar ya xama abun tsoro, ba da xuciya daya ya yarda ta biyo mu
ba" Mujaheed yace "Tana waje, muje ki ga dakin dake kasa" Inna
tace "Na waye dakin?" Yace "Baki" inna tace "Irin su
Hansai da 'ya yanta knn idan sun xo" murmushi yyi ya bude kofar parlon
yace "Har ke ai" Bai jira cewarta ba ya fice. Har garden sai da
Mujaheed ya kai Inna ya xaga duk gidan da ita, tana kallonsa tace "Toh ai
tun yanxu ya kamata mu shiga gun makota a san juna kafin mu tare, ko ya
kaga?" Kallonta yyi ya dauke kai, tace "A'a ba xancen dauke kai ba
yana da kyau in san su su san ni, ko haka mutum xai ta xama ba jama'ah a gida,
ai mutane Rahama ne" Mujaheed yace "Sai ki jira idan kin ga dawowarki
gidan" Inna tace "Wannan gaskiya ne, to ni na shiga uku ban fa yi
la'asar ba Mujaheed" yace "Toh mu je ciki kiyi" parlon suka koma
ya nuna mata dakin dake downstairs yace "Sai kiyi alwala a bayin ciki kiyi
sllhn" tace "Toh dakin su Hansai kenan" shi dai bai ce mata
komai ba ta wuce ciki, kallon agogo yyi sannan ya wuce sama, parlonsa ya shiga
ya bude kofar dakin, durkushe ya ganta inda ya bar ta har sannan tana kuka,
tana ganinsa ta mike tsaye, karasawa cikin dakin yyi, ta hadiye kukan da take
ta sunkuyar da kanta, takawa yayi har gabanta ya tsaya ta ki yarda ta daga kai
balle ta kallesa, ya dago kanta a hankali, ta kallesa sai kuma ta fashe da kuka
ta juya masa baya, xagawa yayi gabanta ta rufe fuskarta tana shessheka, d'an
murmushi yyi, kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "ki dinga jin magana
ta idan baki son na dinga sa ki kuka" ta kara juya masa baya cikin kuka
tace "Ni bana soo" xagawa ya kara yi gabanta ya jawo ta kusa da shi,
ta kuma fashewa da kuka, ya d'an hade rai yace "Toh baxa ki yi shiru
ba" kin cewa komai tayi, ya ja ta xuwa bathroom, ruwa ya bude yana
kallonta ta madubi a hankali yace "Wash ur face now" ta turo baki ta
ki cewa komai, tara hannunsa yayi ya debi ruwan ya dukar da ita ya shiga wanke
mata fuskar, yana gamawa ya ciro handkerchief dake aljihunsa ya fara goge mata
ruwan fuskar, yana kallonta ta madubi yace "Promise me xaki fara jin
magana ta daga yanxu...." Kin cewa komai tayi ya hade rai yace "I am
talking to you" da kyar tace "Na ji" yace "Kin ji me?"
A hankali tace "Abinda ka ce" mayar da handkerchief din yyi aljihunsa
ya juya ya fita bathroom din, murguda baki tayi ta juya tana kallon kofar
bayin. Parlor Mujaheed ya xauna yana danna wayarsa har Inna ta fito dakin da ta
shiga yin sllh, tace "Wai Mujaheed ni fa ban ji motsin Imaan ba.... A rufa
min asiri mu dubota" Mujaheed yace "Tana sama ai" Inna tace
"Toh ni dai mu je in ganta" bata jira cewarsa ba ta nufi stairs ya
mike ya bi bayanta, dakinsa ya shiga da ita suka ganta tsaye jikin window waya
kare a kunnenta, tana jin an bude kofa tayi saurin dauke wayar daga kunnenta
tayi tsuru tsuru, kallonta Mujaheed ya dinga yi, Inna tace "Toh ke daga
ganin gida sai ki shige dakin matar mutane ki xauna, jira xa ki yi Allah ya
kawo lkcn naki da Bulasawa ae" Juyawa Mujaheed yyi ya bar bakin kofar,
Inna tace "Toh fito masu a daki yi hakuri haka" imaan bata tanka ta
ba ta nufi kofa gabanta na faduwa ta fita, Inna ta bi bayanta, balcony suka
tadda Mujaheed suna fitowa ya kulle gidan da makulli ya tafi gun motarsa, imaan
bata yrda ta kallesa ba ta bude front seat ta shiga kamar munafuka Bayan Inna
ta shiga baya, ya ja motar ya fita compound din yyi ma Mai gadi sallama. Suna
hawa saman titi Inna tace "Ni dai Mujaheed da dai in samu kaza in siya,
naji raina na so sosai" Mujaheed yayi parking dai dai gun masu gashin
kazan da ta gani ya sa tayi magana, tana washe baki tace "Allah dai ya
maka albarka" Bai ce komai ba sai ma jinginar da kai da yayi da kujeran
motar ya lumshe ido, Inna tace "Toh ko ta fita ta amso?" Ba tare da
ya bude idon ba yace "Ehh" inna tace "Toh guda nawa?" Jin
bai ce komai ba Inna ta gyara xama tace "Ko guda uku ai yyi, Ni daya ita
daya, yan sa ido kuma sai in kacalcala masu daya" Mujaheed yace
"Ohkk" Inna tace "Yi maxa ki sauka imaan, kice masu su xabo
manya don Allah na tsohuwa ce kuma ba miji gareni ba" Imaan ta bata fuska
ta juya tana kallon Inna, inna tace "Naga Ikon Allah, ko in sauka da kaina
ne? Me mutanen xa su maki ko ina ruwanki da su" bude motar Imaan tayi ta
fita ta tafi gun masu gashin, Mujaheed ya bude ido ya bi ta da kallo daga cikin
motar, ba laifi akwai maxa a gun, imaan na sunkuyar da kai ta amsa tambayar da
masu wajen ke mata tace "Guda uku" tana ta tsaye har aka gama
packaging kajin a leda daban daban ta amsa ta nufi gun mota ta bude back seat
tana kallon Inna tace "Wai dubu hudu da dari biyar" Inna tace
"Toh ni xa ki gaya ma? sai ki gaya ma me siyan ai" Ta madubi Mujaheed
ya kalleta yace "Waye me siyan ban da ke?" Inna ta gwalo ido tace
"Ban gane ba" ya buda ido sosai yace "Ko sisi bani da shi, ban
fito da kudi ba" Inna ta saki salati mai tsayi tana xaro ido tace
"Nima ko sile ban fito da ba Mujaheed" Mujaheed ya daga kafada yace
"Sai ki san abinda xaki ce masu" Inna ta kara sakin salati tace
"Yau babu lafiya ni patuu an kacalcala kaji uku ba kudi" shi dai
Mujaheed bai sake ce mata komai ba, ta kalli Imaan da xaro ido tana kallonsu,
Inna tace "Maxa maida masu tsiyar su kice basu da girma an fasa siya, maxa
koma" Imaan ta wani xaro ido tace "Iyyee, bayan an yanyanka wllh ni
ba inda xan je" a fusace Inna tace "Da aka yanka ci muka yi? Ni naga
abinda ya isheni, ki juya ki mayar masu kayansu ba mu da halin biya" Imaan
duk ta rikice barin yanda taga duk mutan wajen na kallonsu tace "Na shiga
uku, wllh Inna baxan iya komawa dubi fa maxa a wajen da yawa" jaraba Inna
ta dinga yi inda take shiga ba nan take fita ba tace "Mazan banxa maxan
hofi ina ruwanmu da su bamu da kudin biyan kaji..." wani gentleman dake
xaune wajen ne ya taso ya iso gun motar yana kallon Imaan yace "Lafiya
kuwa?" Inna tace "Ina fa lafiya yaro an kacalcala kaji uku ba kudin
da xa mu biya, nace ta mayar masu tsiyar su shine take kokarin tara min jama'ah
wllh ko amsar ledan ma ni ban yi ba balle inji kamshin naman ciki, Toh a kan
meye baxa su amsa ba? Dama haka ake yi?" Murmushi kawai mutumin yake yana
kallon Imaan yace "Kazan guda nawa ne?" Da sauri Inna tace "Gudu
uku ne wllh, daya nata daya nawa, daya na yan sa ido a gida..." Hannu ya
sa a aljihu yana kallon Imaan, Mujaheed ya bude motar ya fita gun masu gashin
kajin ya fiddo dubu biyar ya mika masu, daga Inna har mutumin da imaan bin sa
da kallo suka yi, Inna tace "Kaga katon banxa ko? Ce mana yyi ba shi da
kudi fa har sai da ya bari duniya ta gama sanin abinda muke ciki sannan ya fita
wani zokai zokai da shi xai bada kudi, Toh Allah ya saka min kunyata ni da ya
so yi gaban masu kaji da tona min asiri da yyi a gabanka" Dariya mutumin
ya dinga yi yana kallon Inna da ta tsuke fuska tana kallon Mujaheed, imaan ta
kalli mutumin gabanta ta mayar masa da kudin da ya mika mata tace "Mun
gode" Yana murmushi yace "Don't worry...." Dawowa Mujaheed dake
kallonsu yyi ya amshi kudin hannun imaan ya kamo hannun mutumin ya saka masa a
ciki yace "Thanks for ur concern" daga haka ya bude mata front seat
yana kallonta, ta sunkuyar da kanta ta shiga ya rufe motar, ya xaga ya shiga
motar ya tada ya bar wajen. Inna tace "Ni dai duk wanda niyyarsa ya
kunyata ni a duniya Allah ya min kantangar karfe da shi, kuma ya saka min"
Shi dai Mujaheed bai tanka ta ba har suka isa gida. Shirye shiryen biki aka
shiga yi a gidan ba kama kafar yaro barin bangaren Umma da kawayenta, ji take
kamar an mata albishir da aljanna xata aurar da first and only son dinta xuwa
ga 'yar masu kudi ba na wasa ba, shi ko gogan kamar ba shi xai yi aure ba babu
Shirin da yake, idan ya fita aiki tun safe dama sai dare xai dawo don kawai bai
son participating a shirin da ake a gidan, shi gaba daya bai fi sau uku suka
hadu da Safeenar ba ma, kuma duk Umma ke tilasta sa sai yaje, ko da wasa bai
taba dialing lambar Safeenah don kansa ba sai idan yayi missing call dinta, a
rana kuwa tana kiransa fiye da sau goma, shi kansa mamakin irin son da take
masa yake duk da yasan dole ta fahimci fa baya yinta amma duk class dinta bata
nuna ta damu ba sai kara shige masa take. Tun ranan da Mujaheed yyi ma Imaan
warning ko da wasa bata son Sadeeq ya xo kofar gidansu sai dai waya amma abinda
ke bata mamaki yanda taga shi ma bai damu ya xo ba kamar da, da kusan kullum
sai ya xo, sai dai suna kusan raba dare suna waya da shi cikin duvet yanda Ammi
baxata ji ba, Duk Friday day kuma sai ya aiko wani worker din gidansu gun Inna
ya kawo mata sako, Imaan dai ta tasan soon Mujaheed xai yi aurensa ya kara gaba
sai taga ta yanda xai hanata tsayawa da Sadeeq kuma. Yau Friday da ya kama
saura sati daya bikin Mujaheed da Safeenah Imaan ta fito daga dakinta ta shiga
na Ammi, durkusawa tayi kusa da gado tana kallon Ammi tace "Ammi xan wuce
yanxu" Ammi tace "Toh na dai gaya maki kar ki dade imaan" tace
"Wallahi baxan dade ba Ammi" Ammi tace "Toh ki gaisheta Ina mata
ya jiki" Imaan tace "Toh xata ji" mikewa tayi ta fita daga dakin
ta shiga kitchen ta dauko wani leda mai dauke da can malt ta fito parlor ta dau
jakarta sannan ta fita gidan, kamar mai tausayin kasa ta isa bakin titi bayan
few minutes ta samu adaidaitan da xai kai ta GRA, tafiyar kusan minti ashirin
suka yi, suka shigo gate din layin as usual ko ina tsit sai haushin karnuka, dai
dai gate din kantamemen gidan Imaan ta sa mai adai daitan ya tsaya ta sauka ta
basa kudin tana kallon masu gadi dake xaune bakin gate din gidan, gaishesu tayi
daya daga cikinsu yace "Wa kike nema?" Tace "Mariya" Mai
gadin yace "Toh ki kirata" shiru tayi tana kallonsa don kwanaki da
dadewa da ta xo ae basu mata tambayar komai ba, ba musu ta fiddo wayarta a jaka
ta shiga Kiran Mariya, Ba a dau lkci ba sai ga Mariya ta fito gidan, Rungume
imaan tayi tace "Welcome frnd" tana kallon masu gadin tace
"Kawata ce duk ranan da ta xo ku bar ta shigo babu interrogation"
bata jira cewarsu ba ta ja hannun Imaan cike da farin cikin ganinta suka wuce
ciki, Imaan tace "Dama kin ma ji sauki koh?" Mariya ta marairaice
tace "Yau fa nayi getting self dina" Imaan na murmushi tace "Toh
Allah ya kara lafiya" sai da ta fara kai Imaan dakin Mahaifiyar ta ta
gaisheta sannan ta ja ta xuwa makeken bedroom dinta, imaan ta xauna tace
"Siblings din ki fa?" Tana fiddo ruwa da lemo a fridge dinta tace
"Sun fita da Yaya Annur shan ice-cream kinsan yau Friday" murmushi
kawai Imaan tayi, Mariya ta ajiye mata drinks din tace "Me xa ki ci, akwai
yam with sauce, cous cous with sauce, or kin fi son snacks?" Imaan ta
girgixa kai tace "A'a na ci abinci a gida" Mariya ta harareta tace
"A'a ni dai sai kin ci wllh" Imaan tayi dariya tace "Bayan nace
maki na koshi, Ni la'asar kawai xan yi" Mariya ta nuna mata bathroom dinta
tace "Kiyi alwala ga bathroom kafin ki fito xan kawo maki abincin"
bata jira cewar Imaan ba ta fita da sauri, Murmushi imaan tayi ta mike ta cire
Hijab din jikinta ta ajiye ta shiga bathroom din, tana gama alwala ta fito dai
dai nan aka bude kofar dakin, still tayi tana kallonsa, kamar yanda shi ma ya
tsaya yana kallonta, juya masa baya tayi da sauri tana xaro ido....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
41.....
Sadeeq yayi murmushi a hankali yace "But you didn't tell
me you where coming here da muka yi waya daxu" Ta dau hijab dinta ta saka
still bata juyo ba tace "Ae ba wajen ka na xo ba" murmushi kawai yake
yana kallonta, Mariya ta iso bakin kofar rike da tray din abinci tace "Ya
Sadeeq Aunty na neman ka fa" ya kalleta yace "Har kin ji sauki kenan"
dariya tayi tace "Ehh mana bayan alluran da ka sa aka min, Kuma ga kawata
ta xo, Hope yau dai ka tuna ta" Ya langwabar da kai yace "Bayan ta ki
juyowa ma in ga fuskarta balle in san wacece" Mariya ta wara ido ta kalli
Imaan da ta ki juyowa da gaske, ta yi dariya ta karasa cikin dakin ta ajiye
abincin hannunta ta isa kusa da Imaan ta juyota suna facing Sadeeq tace
"Toh ka gane ta yanxu?" Shafa kai yayi yana cute smile dinsa yace
"Anya.. wani anguwar take? Na taba ganinta ma kuwa?" Imaan bata san
lkcn da tayi murmushi ba ta sunkuyar da kanta, Mariya ta bata fuska tana
kallonsa don da gaske bata ji dadi ba, Sadeeq ya wara manyan idonsa yace
"Toh Sannu da xuwa kawar Mariya, duk da dai ni ban gane ki ba" daga
haka ya juya ya rufe masu kofar, duk yanda Mariya tayi forcing din Imaan ta ci
abincin da ta kawo mata kin ci tayi wai ta koshi, ruwa kawai ta sha shi ma sip
daya, Mariya da gaba daya bata ji dadin kin cin abincin da Imaan tayi ba tace
"Dama ki dau drinks dinki ki koma da su bana so da gaske" dariya
kawai Imaan tayi ta mike tace "Sai ki ba su Hafsat idan sun dawo, ni dai
tashi ki rakani" Mariya tace "Bayan kin walakanta ni xa ki ce in raka
ki" Imaan na murmushi ta nufi kofa tace "Toh ni fa na ci abinci a
gida nace maki Mariya" Mariya ta mike ta bi bayanta suka fita dakin tace
"Toh mu je ki yi ma Aunty sallama ya na iya da ke, nima dai ko ruwa kika
ban idan naje gidan ku baxan sha ba" Imaan ta kalleta ta gefen ido tana
murmushi suka shiga parlon mum dinta, Sadeeq na parlon tare da mum din nata a
xaune, Imaan ta durkusa kusa da kujera tace "Aunty xan tafi" Mum din
Mariya tace "Da wuri haka Imaan, toh Ina xuwa" tashi tayi ta tafi
dakinta, Imaan ta sata kallon inda Sadeeq yake taga kallonta yake, ta dauke kai
da sauri, Mariya tace "Ya Sadeeq yanxu fa su ya Annur xa su iya dawowa
basu kawo min komai ba ko?" Yace "Toh ki kirasu mana" Tace
"Toh don Allah kira min su ta wayarka, I can't imagine me not eating
shawarma today" yace "Wayana na can gida" tashi tayi ta bi mum
dinta daki don daukan wayarta ta kira step brother din nata, Sadeeq na kallon
Imaan yace "Me yasa baku xo tare da kaka ba?" Ta dai yi murmushi bata
ce komai ba, Aunty ta fito rike da leda ta ajiye kusa da Imaan tace "Ki
gaida min mum din ki kinji Imaan" a hankali Sadeeq yace "Aunty ita ce
fa warce nake yawan baki labari a kai...." Aunty ta kalli Imaan sannan ta
kallesa da mamaki tace "Imaan din kuma?" Yana murmushi yace
"Sure..." Sake baki tayi tana kallonsa, ya shafa kansa yace
"Dama nace maki ba ma sai na kawo maki ita ba da kanta xata xo wataran ki
ganta" Imaan taji kamar kasa ya bude ta shige don kunya, ta kasa dago
kanta ta kalli Aunty, Aunty tace "Ikon Allah, wai da gaske kake don Allah
Sadeeq" Yace "Gata ki tambayeta, but aunt this is our secret ko
Mariya kar ki gaya ma plss Aunty, you know Mariya talks a lot...." Dariya kawai
Aunty tayi ta xauna tace "Ikon Allah, Toh Allah ubangiji ya sanya
alkhairi, yayi xabi na gari..." Yace "Ameen" Mikewa yayi yana
kallon Imaan yace "Let me drop you" da sauri ta girgixa kai sai dai
bata ce komai ba, Aunty tayi dariya tace "Aa ki je dai ya ajiye ki gida
Imaan, ki gaida mutanen gidan kin ji, Allah maki albarka..." Sadeeq na
murmushi ya nufi kofa ya fita, Aunty na kallon Imaan tace "Imaan idan ma
kina da doubt a kan Abubakar a da, tohh stop that now kinji daughter, Sadeeq na
son ki fiye da yanda kike tunani, I was so surprise da naji yace min ya sami
yarinyar da yake so da aure yar Nigeria, coz ni nasan waye Sadeeq, I know him
fiye da uwar da ta haifesa ma, kuma wllh duk jinsa nake ba wai na yarda ba, har
gajiya nake da jin labarin ki a bakinsa, But plss kiyi kokarin kame kanki ki
kare martabar ki na 'ya mace, am not saying this bcos Sadeeq is bad or anything
of such, A'a Ina gaya maki haka ne a matsayina na uwa, ko Mariya iyakar
shawarar da xan bata kenan...." Imaan dai ta kasa dago kanta, fitowar
Mariya yasa Aunty tayi shiru, Aunty na kallonta tace "Ki rakata compound
Sadeeq xai ajiyeta gida yanxu, he is waiting for her" Imaan ta mike tayi
ma Aunty godiya cikin sanyin murya ta fita, Mariya ta dau ledan da Aunty ta
ajiye mata tace "Mun gode Aunty" daga haka ta bi bayan Imaan da
sauri, Mariya ta bata fuska ganin bata ga Sadeeq a bangarensu ba, tace
"Kai ya Sadeeq maimakon ya dau motar dake nan yanxu sai mun bi sa har
can" ita dai Imaan bata ce komai ba, haka suka dinga tafiya a lafcecen
compound din xuwa bangarensu Sadeeq, Building din ya kusa biyun nasu Mariya,
Kai kana gani kasan an rasa yanda xa ayi da Naira kuma, Motocin dake parking
spaces din wajen sun yi goma ko wanne kuma ya wuce a kirasa mota sai dai Ride,
ni kam nace don ma Inna bata xo taga gidan ba... Ai da gobe gobe xata sa Bukar
da Ahmadu gaba ta tada bala'i a daura auren Imaan da Bulasawa... Lol, Sadeeq na
xaune cikin daya daga motocin parking space din idonsa a kan Imaan dake tahowa
tare da Mariya, irin kallon da yake mata yasa Mariya ta kalli Imaan sai dai
bata ce komai ba, ana haka aka bude gate din gidan wani ride ya shigo compound
din, Mariya tayi ma motar kallo daya ta dauke kai, Drivern yyi parking aka bude
back seat, wata da baxata wuce shekaru hamsin ba ta sakko motar cikin shiga ta
alfarma, tun daga kunnenta, wuyarta, finger, da wrist duk gold ne, tun da Imaan
ta kalleta sau daya ta gane Mahaifiyar Sadeeq ce, Mariya tace "Sannu da
dawowa Mami..." Sama sama matar ta amsa, Imaan ma ta gaisheta, ba tare da
ta kalli Imaan ba ta amsa, tana kallon Sadeeq tace "Fita xaka yi yanxu
Abba..." Ya fito daga motar yace "Welcome back Mami" tace
"Yauwa..." Yana shafa kansa yace "Aunty tace in ajiye bakuwarta
a gida..." Daga sama har kasa ta kallesa bata dai ce komai ba ta nufi
entrance din babban gidan, ya bi ta da kallo, can yace "Mami xa a maki
wani abun ne?" ba tare da ta juyo ba tace "Noo ka tafi inda aka aike
ka, ka sameni parlona dai idan ka dawo, is Annur back?" yace "I don't
think so" Front seat ya xaga ya bude ma Imaan yana kallonta, Mariya ta
ajiye ledan hannunta a bayan motar ta xaga gun imaan tace "Plss kice ma
Ammi ina gaisheta kin ji" Imaan ta shiga motar tana murmushi tace
"Toh xan gaya mata" Sadeeq ya tada motar suka fita compound din
Mariya na daga masu hannu, Sai da suka hau saman titi murya can kasa yace
"Nayi missing din beautiful face din ki two days Imaan" Murmushi
kawai tayi, yace "ke ko naga ma baki damu da rashin xuwa na ba koh? You
won't even understand what I am going through now" Ta kallesa a hankali
tace "I thought you are busy this days ne shi yasa" girgixa kai kawai
yayi, bayan kusan minti biyar yace "My birthday is coming soon...."
Ta kallesa tace "When" yace "7 days from today in sha
Allah" shiru tayi don ranan daurin auren Mujaheed kenan, can tace
"Toh Allah ya kai mu lafiya" yace "Anything for me?"
Murmushi tayi tace "Me kake so?" Murya can kasa yace "Ke nake so
Imaan" ta wara ido tace "Ni kuma" ya gyada kai yace "I
don't know... i just have this urge of wanting to be with you, sai yanxu nake
ganin nisan kwanakin da suka rage... I want you by my side as my wife"
kasa kallonsa tayi ta kuma kasa cewa komai, ya kamo hannunta yace "Kin yi
shiru" kwace hannunta tayi a hankali still ta ki cewa komai, parking taga
yayi ta juya tana kallonsa, yayi kasa da murya yace "I am thinking of
meeting grandmum, ko xata kara yi ma su Abba magana" Imaan ta kallesa da
sauri tace "Maganan me?" Yana kallonta yace "Su yi hakuri su
bani ke any time from now, wllh har professor xan iya barinki ki xama a
gidana" Imaan ta girgixa kai kamar xata yi kuka tace "A'a ni dai,
bayan ga abinda daddy na yace" Shiru yyi yana kallonta, cikin sanyin murya
yace "Toh shikenan i will continue waiting and having patient in sha
Allah" Driving ya ci gaba da yi, sai da suka kusa layinsu yace "My
frnds are throwing a birthday party for me, kuma ke ce babban guess a wajen
ranan" ta wani xaro ido tana kallonsa yace "Yea, don't turn down my
offer baxan ji dadi ba....." Kasa cewa komai tayi yana shigowa layinsu
gabanta yyi mugun faduwa, what if Mujaheed na waje yanxu haka, kafin ya isa
kusa da gate dinsu da sauri tace "Kawai ma ka ajiye ni a nan ba sai ka
karasa can ba" ya kalleta yace "Why?" Ta hadiye abu da kyar tace
"Nothing" Bai ce komai ba ya kai ta har bakin gate din ta fara kalle
kalle kamar munafuka ta bude motar ta fita yace "Wait Imaan" tsayawa
tayi ya juya ya dauko ledan da Mariya ta ajiye mata, Mika mata yayi ta amsa
tace "Nagode sai anjima" daga haka ta shige cikin gidan da sauri har
hakan ya basa mamaki ya bi ta da kallo, tana shiga kuwa ta kulle gate din, sai
da xuciyarta ya kusa shigewa cikinta ganin Mujaheed da Yusuf a compound din,
Yusuf na xaune kan farin kujera Mujaheed kuma da alama gate xai fita amma sai
kallonta yake, bata tsaya wani tunani ba ta fasa wani ihu ta sake ledan
hannunta ta durkushe wajen tana yarfe hannu tana kiran Ammi, Mujaheed ya karasa
inda take da sauri yana kallon kafarta yace "Me ya faru??" Ta kamo
hannunsa tace "Wayyo Yaya kafana ban me ya same shi ba..." durkusawa
yyi ya daga dogon hijab din jikinta yana kallon kafar, ta gefen ido ta dinga
satan kallon kasan gate taga ko Sadeeq ya gama reverse.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
42....
Imaan ta kwace kafarta a hannunsa bayan ta ga Sadeeq ya wuce
tana turo baki a hankali tace "Ni ya ma daina, dama gurdewa kawai
nayi" bata jira cewarsa ba ta mike da kyar, Yusuf dake tsaye shi ma ya iso
wajen yyi murmushi yace "Dama ba wani ciwo, ke dai kika san abinda kike
boyewa a waje" Mujaheed ya kalleta ya kalli gate da sauri, ledan da ta
jefar ya dauka ya bude yana kallon abinda ke ciki, sai kuma ya nufi gate
din.... Tana ganin haka ta dau ledarta da takalmanta ta wuce apartment dinsu da
sauri tana waigan Mujaheed, Yusuf yyi murmushi ya koma ya xauna, Parlor ta
tadda Ammi xaune, Ammi ta amsa sallamarta tace "Meye kuma kike sa min
makulli a kofa" ta xaro ido tace "Ohh na manta, nayi xaton dare
yyi..." Still dai bata bude kofar ba tana murmushi ta karasa cikin parlon
ta xauna tace "Ammi Sannu da gida" Ammi tace "Yauwa, ya mai
jikin?" Imaan tace "Da sauki, Mum dinta tace in gaishe ki, ta ma bani
wannan" tana fadin haka ta ajiye ledan a kusa da Ammi, Ammi tace "Toh
Allah ya amfana" mikewa Imaan tayi ta wuce daki har sannan xuciyarta bai
daina bugawa ba, yanxu da Mujaheed ya ga Sadeeq ya xata yi yau. Tun bayan da ta
idar da sllhn magrib Ammi ta ce ta dau abincin Inna ta kai mata gabanta ke
faduwa, har claiming ciwon kafa tayi duk don Ammi ta kira Maimoon ta kai ma
Inna abincin amma Ammi tace ita dai xata daure ta kai a hakan, tana goge guntun
hawayenta ta dau abincin ta fita a sanyaye, ita kanta bata gane wani sabon
tsoron Mujaheed da ya diran mata yanxu ba, a hankali ta bude kofar parlon Inna
ganin takalmin da bata dai san ko na waye ba bakin kofar, ta ajiye abincin a
nan bakin kofa Inna na tambayar wani munafukin ne amma tuni ta juya da sauri
har tana tuntube ta koma part din su. Washegari Saturday karfe takwas saura
Imaan ta fito bangarensu cikin shirin islamiyya, duk gaba daya a tsorace take
har Ammi ta lura da hakan amma da ta tambayeta damuwarta sai cewa tayi ita
bayanta ke mata ciwo, Ammi ta sa ta sha magani sannan ta fita, parking space ta
dinga lekawa ko xata hango motar Mujaheed, ganin motar tasa yasa ta ki jiran su
Maimoon ta nufi gate da sauri, ta gwammace ta tafi bakin titi ta samu adai
daitan da xai kai ta islamiyyar. Suna jiran drivernsu bayan an tashi islamiyya
Maimoon tace "Imaan wai me yasa kika ki jiran mu daxu?" Imaan ta tabe
baki tace "Salon kawai ku 6ata ma mutum lkci mu yi ta yin latti ana xane
mu, naga baku fito ba ni kuma bana son inyi latti shi sa nayi wucewata"
Rahma tace "Har akwai wanda ya kai ki saka mutum yin latti? Kullum sai mun
yi ta jiran ki bakin mota kafin ki fito, daga ace bayan ki ya rike sai ace
kafar ki ya rike, to daga yau ma kar ki sake jiranmu kiyi wucewar ki"
Imaan ta kalli Maimoon tace "Kin ga dai ba da wannan matar nake magana ba
ko, ki gaya mata ba ruwanta da harkata tayi ta kanta ta kyaleni..." Rahma tayi
dariya tace "Ehh gwara in kyaleki kiji da ciwace ciwacen ki kam....."
Maimoon ta kalli Rahma tace "Haba meye haka Rahma?" Rahma ta watsa
mata wani kallo tace "Sai dai ki tambayeta meye haka, ko ni sa'arta ce aka
gaya mata??" Tsaki tayi ta wuce gun motar gidan su da yyi parking dai dai
lkcn, Ummi ta ja tsaki tace "Mutum sai neman fitina kawai, ana taba ta
kuma lalura ya tashi a shiga uku, to dama wa xai taba sauran ciwo idan ba
tsautsayi ba ma" tana fadin haka ta wuce ta shiga mota ita ma, Maimoon ta
kalli Imaan dake kallonsu tace "Ki rabu da su kiyi hakuri" Imaan bata
ce komai ba ta bude front seat ta shiga Maimoon ma ta shiga back seat... Suna
isa gida driver yyi parking Imaan ta bude motar ta fita bata xame ko Ina ba sai
part din Inna, Inna na xaune parlon tana hada kwadon rama Imaan ta shigo ta
xube nan kan kujera ta fashe da matsanancin kuka, Inna ta tura roban gabanta
tace "Auzubillahi, me ya sami Aishar?" Cikin kuka Imaan tace "Ko
ba su Rahma da Ummi bane daga Ina magana da Maimoon suka fara xagina har da ce
min sauran ciwo...." Mikewa Inna tayi ta rufe roban kwadonta ta dau
gyalenta ta nufi kofa ta fice, Imaan ta dinga kuka har da shessheka, can dai
tayi shiru ta goge idonta ta shiga kitchen ta dauko wani plate ta debi kwadon
da Inna ke hadawa ta fice a parlon. Babu abinda Inna ta mance bata xaxxaga ma
Umma dake dakinta a xaune tare da su Ummi dake mata tsarin abinda ya faru
tsakaninsu da Imaan, Inna na huci tace "Kuma in sha Allahu sai kinga
sauran ciwo a jikokin da xa a haifa maki..." Da sauri kuma tace
"Astagafirullah, jikokin ki ai na Ahmadu ne, to in sha Allahu sai kinga
sauran ciwo a dangin ku.... Kuma a kawo maki riko kiyi ta fama, duk wanda ya
sake sa min jikata a bakin duniya Allah ya isa ni dai, Allah ya isa, kuma bari
Ahmadun ya dawo...." Tana fadin haka ta fice. Imaan na shiga apartment din su ta tadda Ammi
na ta girke girke, gaisheta kawai tayi ta wuce daki, tayi wanka tayi sllh
sannan ta shirya ta fito parlor, kitchen ta shiga gun Ammi dake hada drink din
Zobo tace "Ammi jirgi daddy xai biyo ko train?" Ammi tace "Ce
maki yyi xai dawo yau?" Imaan ta xaro ido tace "Naga kina girki ne
ai" Ammi tace "A'a mamar ku ce dai ke hanya...." Imaan tace
"Mama Hadiza?" Ammi tace "Ehh sun ma kusa landing Ina ga"
Imaan ta wara ido tace "Shine Inna bata gaya min ba?" Ammi tace
"Ita ma bata sani ba shi yasa ban gaya maki tun jiya ba kar ki je ki gaya
mata don ba control gare ki ba" Murna Imaan ta dinga yi tace "Da su
Maryam xa ta xo in gansu plss?" Ammi tace "Da Maryam kadai suka
taho" Imaan tace "Toh wa xai je daukota a airport nima xanje
plsss" Ammi tace "Mujaheed Daddy yace yaje ya daukota" shiru
Imaan tayi bata ce komai ba, can ta dau plate ta bude abinci xata diba. Hudu na
yi Mujaheed ya tafi airport dauko small mum din tasa da autar ta, tun da suka
kamo hanyar gida Maryam ke tambayar sa Imaan da turancinta dake kala da na
turawa, yyi murmushi yace "Tana nan, tsayin ku daya sai dai ita bata jin
magana..." Maryam ta kyalkyale da dariya tace "Ni duk na kagu in
ganta wllh, muna fa vid call da ita once in a while" Mujaheed yace
"Ae xa mu je ki ganta" Mama Hadiza tace "Amma dai yanxu ta ji
sauki sosai koh?" Yace "Ehh mama da sauki sosai" Hadiza tace
"Toh Alhmdllh haka Yaya Sadeeq din yace min, Toh in ji dai xa a kawo min
amaryar mu gaisa kafin biki..." murmushi kawai yyi bai ce komai ba, tace
"Au baxa ka kawota ba kenan" yar dariya yyi yace "Toh xa a
kawota in sha Allah mama" Mama Hadiza tace "Toh da dai ya fi, kuna ta
dai hakuri da tsufan Inna koh?" Mujaheed yace "Mu wllh da ma ki
tarkatata ku koma tare mama" dariya Mama Hadiza tayi tace "Baka da
kirki Mujaheed, ita uwar tawa kake cewa in tarkata?" Yace "Wllh mama
duk ta addabi kowa a gidan..." Mama Hadiza tayi murmushi tace "In sha
Allahu nan da wata hudu ma xa mu dawo Nigeria gaba daya sai in dauke uwata ta
dawo wajena sai in ga ta inda xa ku dinga gajiya da ita" Mujaheed yyi
dariya yace "Wllh baxata yarda ba, xata gwammace tayi ta xama tana dagawa
Ahmadu da Bukar hankali" Mama Hadiza tayi dariya tace "Baka da
mutunci wllh Mujaheed" parking Mujaheed yyi a parking space din su bayan
sun isa gidan, Mama Hadiza tace "Allah sarki, rabona da gidan nan shekara
uku kenan, anjima idan na huta da Magrib sai ka kai ni gidan Seeyama" yace
"Toh Mama Allah ya kai mu" part din Abba Mama Hadiza ta fara shiga
tare da Maryam don gaisawa da Aunty da Umma... Bata wani dau lkci a part din ba
ta fito tare da Aunty, Umma dama tun bayan da suka gaisa ta shige daki ta
kulle, Mama Hadiza na kallon Aunty tace "Rukayya dai na nan da rashin
kirkinta har yanxu koh?" Dariya kawai Aunty tayi, Mama Hadiza tace
"Toh yayi kyau ta ci gaba, har ni xata walakanta ta shige daki sbda bata
da mutunci" ita dai Aunty bata ce komai, suka shiga part din su Imaan,
Imaan ta fito daki jin muryar Maryam ta rungume ta cike da murnan ganinta, Ammi
na kallon mama Hadiza bayan sun gaisa tace "Toh Ina jakar? Ko ba nan dama
xa ku sauka ba" Mama Hadiza tace "Yana cikin mota Mujaheed bai fiddo
ba" Ammi ta kai ta har bedroom dinta don ta kintsa, Aunty dai tayi masu
sallama ta koma.
Maryam na idar da sllh bayan ta ci abinci tayi wanka dakin
Imaan, suka dinga hira... Ganin Magrib ya kusa Imaan tace "Plss mu je ki
ba Inna surprise kawai ta gan ki" Maryam tace "Hope ta daina xagin
mutane dai yanxu" Imaan tayi dariya sosai tace "Sai dai bata ga
abinda xata xaga ba, ke dai mu je" A tare suka fito dakin suka wuce part
din Inna ba tare da sun sanar da su Ammi dake bedroom ba, Inna na bakin tap
suka iso bangaren nata, ta daga kai tana kallonsu, Imaan dai sai murmushi take,
Inna tace "Waya wannan kuma kamar Zabiya?" Imaan ta fara dariya tace
"Baki ganeta ba Inna?" Inna ta ci gaba da wanke wajen tace "Ka
dai ji wata magana wai ban ganeta ba, yanxu ko uwata ce ta fito daga kabari
idan ban ganeta baxan ce mata ban gane ta ba, tun daxu nake durkushe a nan nake
aiki babu mai taimakona, baki ji bayana ba kamar ya balle in huta...."
Maryam ta hade rai ta shige parlonta, Imaan tace "Maryam ce fa Inna"
Inna tace "Waye kuma Maryam" Dariya kawai Imaan take tana kallon
Inna, Inna tace "ita ce ta xama kamar zal6e?" Imaan ta xauna a
balcony din tana dariya, Inna ta tabe baki tace "Ku dai baku son gaskiya a
gidan nan, yanxu da ba don wannan yar albarkan Maimoon ta gaya min a boye ba
daxu da baxan ma san Hadiza xata xo gidan nan ba, Toh kuma kya taho min da
yarinya tsigi tsigi kice Maryam, Yar da aka haifa hannuna ce aka ce maki baxan
gane ba, ni fa na mata wankan farko kuma a gabana aka yayeta..." Inna ta
tabe baki tace "Ni dai ba ruwana" Fitowa Maryam tayi daga parlon ta
yi wucewarta, Inna ta bi ta da kallo ta kyabe baki tace "Ubansu dai ya cuce
su ya hallaka su, ya kwashe su ya tafi kasar tsinannu yayi kaka gida, toh tana
ma jin hausar kuwa" Imaan dai ta kasa cewa komai sai dariya take, Inna ta
gama dauraye bakin tap din ta mike ta shige cikin parlonta tana cewa
"Bukar dai ya haifi jaraba, ba don naka naka bane ai ni bana bari a cuci
Bulasawa a lika masa ke ba, to banda haka ni sa'ar uwarki ce xaki xauna bakin
kofa kina babbaka min dariya kamar mahaukaciya?? ita ma Hadizar dama kada ta
kuskura ta xo min nan xan koreta tunda bata maida ni bakin komai ba, banda haka
ta kamo hanya rai kwakwai mutu kwakwai baxata gaya min ba in mata addu'a,
wannan ba shawarar kowa bace illa wannan mutumi Bukar don shi ne me irin wannan
tunanin na marasu nutsuwa, Amadu baya haka" mikewa Imaan tayi ta bar wajen
ta koma part din su... Bayan magrib tare Abba suka tafi gun Inna da Maryam,
Inna na xaune parlon tare da Mama Hadiza da Mujaheed, Inna na ganin Maryam ta
washe baki tace "Yanxu nake rokon Mujaheed ya tashi ya nemo min ke don tun
saukan ku bamu hadu ba kin xo daxu ina gurje bakin pampo ke kuma baki jira in
gama ba kika yi wucewar ki" Maryam ta xauna ta gaisheta babu walwala, Inna
ta amsa da fara'a tace "Kun sha hanya, sai kawai naga kin kusa kamo imaan
a tsayi..." Maryam dai bata tanka ta ba, Mama Hadiza sai murmushi take,
Abba ya gaida Inna ta amsa tace "Ae gwara da ba a gaya min suna hanya ba
Ahmadu da baccin kirki ma ni baxan yi ba, amma da na gansu kamar daga sama ai
yafi ko" Abba na murmushi yace "Gaskiya ne" Mikewa Mujaheed yyi
ya fita parlon Maryam ta bi bayansa, a jere suke tafiya tace "Ya M.A kaga
abinda Inna ta min daxu kamar bata taba ganina ba" Dariya Mujaheed yyi
yace "Xata maki fiye da haka ma, so take it off ur mind plss haka nan
take, ya karatu?" tace "Alhmdllh...." Ya kalleta yace "Hope
baki kula samari sai kin gama karatun" tayi dariya tace "Kai ya M.A,
bayan ga Imaan ma tana da saurayi, ta ma ce min xai yi birthday soon and his
frnds will be celebrating it for him, wai in bata shawarar abinda xata
basa" Tsayawa Mujaheed yyi yana kallonta, can yace "When tace maki
birthday din?" Ta wara ido tace "I didn't ask her, mun ma gaisa da
shi a waya yace xai xo gobe ya gaisheni, his voice is cute..." Tana
murmushi ta kare maganar, Shiru yyi bai ce komai ba ya ci gaba da tafiya a
hankali tana biye da shi, Xaro ido tayi tace "Wait... Am I even suppose to
tell you this??" Yar dariya yyi yace "Me yasa kika ce haka?"
Tace "Naga irin kamar you are surprise.... Kila ma baka san tana da
saurayin ba ni ce na maka revealing koh?" yace "Yes.. boye mana take,
Amma kar fa ki ce mata kin gaya min she won't be happy" Maryam ta
marairaice tace "Toh nima kar ka mata magana about it she won't be happy
with me...." Yace "Sure I won't" suna isa part din su Imaan tace
"Am spending the night here, ka ce ma su Maimoon, Ummi da Rahma su xo muyi
hira plss" yace "Ohk xan gaya masu" daga haka ya wuce, tafiya
yake amma gaba daya abinda Maryam ta gaya masa ne ke yawo a ransa... Wani
murmushi yyi ya shiga sashin su.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
43....
Washegari da safe Imaan na kumbure kumbure ta gama shirin
islamiyya bayan Ammi tace baxata xauna mata a gida ba, Maryam ta sami Ammi a
kitchen a hankali tace "Ammi don Allah ki barta kar ta je yau, I don't
have anybody to gist with idan ta tafi fa" Ammi tace "Ga kakarki can
ki je ku yi hiran mana" da sauri Maryam tace "A'a ni bana son hirarta
kawai tayi ta xagin mutane, nima ta fara xagina" Ammi tayi murmushi tace
"She is ur grandma dai" Maryam tace "Sure, pls Ammi kin yarda
kar taje?" Ammi tace "Karfe sha biyu xa su tashi ai, kuma sauka xa su
yi soon Maryam, imaan ko shakkar fashi bata yi shi sa nayi forcing dinta ta
wuce" Maryam tace "Ohk then, Allah ya kai mu 12 din" daga haka
ta fita kitchen din, Imaan ta fito daki bayan ta dauko jakarta ta nufi kitchen
ta tsaya bakin kofa kamar xata yi kuka tace "Ammi na tafi" Ammi tace
"Breakfast din fa?" Ta girgixa kai tace "Ni sai na dawo"
Ammi tace "Oho cikin ki" Juyawa imaan tayi ta fita, Maryam ta rakata xuwa
parking space, dai dai fitowar Mujaheed da makullin mota a hannunsa, Maryam
tayi masa murmushi tace "Good morning
ya M.A" ba tare da ya kalleta ba yace "Morning Maryam kin
tashi lafiya?" Tace "Sure.. Alhmdllh" Imaan dai tuni ta dauke
kai, Maryam tace "Aiki xaka fita ya M.A" yace "Noo, sai da yamma
nake fita aiki during weekends" Tace "That's nyc... Do you need my
company?" Ya kalleta kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Sure...
if that will suit you" ta kalli Imaan tace "Alryt sweetheart xan raka
Ya M.A, ayi karatu da kyau a islamiyya" imaan ta kalleta tace "Ohk
bye" tana fadin haka ta saci kallon Mujaheed taga kallonta yake, da sauri
ta dauke kai, Ya bude motarsa ya shiga ya tada, Maryam ta xaga ta shiga gaba.
Ko da Imaan ta dawo daga Islamiyya karfe sha biyu Maryam bata dawo ba, Imaan na
kallon Ammi tace "Ammi wai tun da safe har yanxu Maryam bata dawo
ba?" Ammi tace "Ehh wai sun fita tare da Mujaheed koh?" Imaan ta
tabe baki ta mike ta wuce dakinta. Bayan azahar tana gama cin lunch ta tafi
bangaren Inna, Inna na xaune parlor tare da Mama Hadiza, Imaan ta gaida small
mum din nata sannan ta gaida Inna da ta tsuke fuska, Inna ta amsa tace "Ke
kiji Hadiza da wani mummunan xance Imaan, wai duk abinda xa ayi na bikin
Mujaheed mai kyau ko mara kyau in saka ido kar in yi magana, Saboda ita bata da
tsoron Allah, bata son gaskiya xuciyarta ta kekashe, to me mutum xai min wanda
Allah bai min ba" Mama Hadiza tace "Ni dai ki fahimce ni Inna, idan
ba mu fada maki gaskiya ba kina da mai gaya maki ne, ba girman ki bane komai
kika gani ki tanka a tafi da ke a baki, Haba inna" Inna tayi mitsi mitsi
da ido tace "An dade ba a tafi da ni bakin ba, ni da bikin jikana ki dinga
gaya min maganan banxa, ke kinsan wahalan da nayi da Mujaheed kuwa, wllh wllh
ko Rukayya bata da iko da shi a yanxu, mutumin da yasa na dinga fada da jama'ah
a anguwa yau ya kwale d'an wancan gobe ya danne d'an wancan, da ma Allah ya
rufa min asiri bai sa an min duka a anguwar ba har Allah ya raba ni da anguwar?
ke kinsan sau nawa na shirya na tafi makarantar su Mujaheed fada da malamai
kuwa... Kishiyoyina kuwa duk min dambatu da su a kan Mujaheed, Sannan ace wai
in xama kurma a bikinsa kamar uwata tace min je ki kya gani? To wllh karya
ake...." Mama Hadiza tace "Ba ace ki xama kurma ba amma ba komai xa
ki tanka ba, ba komai xaki shishshige ma ba, Allah na tuba Rukayyar da ma in
don ta nata ne bata son a shiga lamarin bikin, ji fa tasan don bikin takanas na
xo kasar nan amma tun sannu da xuwan da ta min jiya a bangarensu ban sake
ganinta ba, ace kuma tayi farin ciki da xuwana...." Inna ta kunduma ma
Umma xagi tace "Ai ba ita ke aurar da d'a ba nice nan mai aurar da
Mujaheed kar ki ji komai, mu xuba kuma a gani, Allah dai ya kai mu ranan da rai
da lafiya, sai dai mu kwashi yan kallo da ita a bikin nan idan kuma bata yi
hankali ba dama baxata kwana gidan nan ba ranan bikin" Mama Hadiza ta tabe
baki bata dai ce komai ba, Inna tace "Haka kawai, inyi wahala da shi a
dinga gaya min maganan banxa" Imaan dai murmushi kawai take tana danna
wayar hannunta, sallama aka yi bakin kofar parlon, Imaan ta juya da sauri jin
muryan Sadeeq, Inna ta mike daga xaunen da take da sauri tana washe baki tace
"A'ahhh sannu da xuwa Bukar, kai ne da ranan nan... Bisimillah shigo abun
ka... Ba kowa daga ni sai Hadiza da Imaan" da gudu imaan ta shige dakin
Inna, Sadeeq ya shigo parlon kansa a kasa, Inna na washe hakora ta kalli Mama
Hadiza dake xaune kan kujera tace "Ke tashi ki basa waje ya xauna mana,
sirkin ku ne" Sadeeq ya bude ido yace "A'a kaka ga waje ai" Bai
jira cewarta ba ya xauna saman carpet dake shimfide, Inna ta nufi fridge ta
bude ta kwaso ruwa uku da malt uku ta taho, Mama Hadiza dai sai bin ta take da
kallo cike da takaici, Sadeeq na kallonta a hankali yace "Ina yini?"
Mama Hadiza tace "Lafiya lau, Sannu da xuwa" Inna tace "Saurayin
Imaan ne, jira kawai yake ta kare sakandari ayi magana, d'an gidan Ahmad
Bulasawa ne mai gidajen man fetur a arewa, sunan yayanki garesa.... Baki ga
kirkinsa ba, ni dai tunda nake ban taba cin karo da mutum mai kirki da mutunta
babba irinsa ba" Mama Hadiza dai ta kasa cewa komai, Sadeeq dai ya
sunkuyar da kansa sai murmushi yake, Inna ta kwalo ma Imaan kira tace "Ji
walakanci, to meye na gudu daga jin sallaman bawan Allah, baxa ki fito ku gaisa
ba, ba don ke ba a ina xa mu sansa" Imaan da ta xauna saman gadonta ta
turo baki ta ki cewa komai, Sadeeq na shafa kansa yace "Dama baki na xo
gaidawa kaka" Inna tace "Ahh toh madallah, Ka ganta nan
xaune...." Ta fadi haka tana nuna masa Mama Hadiza tace "Uban Imaan
ne ya sha nono ya bar mata, ita ce autata, yaranta hudu a duniya Allah yayi ma
daya rasuwa, dayar tayi aure tana can gidan mijinta a kasashen turawa, sai
kaninta da ke karatu sannan wannan yarinya Maryam da suka xo tare, sa'ar Imaan
ce yarinyar kawai dai Imaan ta fita tsayi, ita kuma Maryam din ta fi Imaan xama
mace" Tagumi Mama Hadiza tayi tana kallon uwartata, Sadeeq kam murmushi
kawai yake kansa a kasa, Inna tace "Toh duk ba wannan ba, kana da labarin
bikin Mujaheed wannan Juma'ah me xuwa ne kuwa Bukar?" Sadeeq ya kalleta
yace "Ai kam bata gaya min ba kaka..." Inna ta saki salati ta rike
ha6a tace "Kaga fitina koh? Duk da dai ko ta gaya maka ko bata gaya maka
xa ayi bikin baxa a fasa komai ba amma ai da ta gaya maka, Toh ni dai na gaya
maka yanxu, bikin ranan Juma'ahn nan ne" Sadeeq yace "Toh Allah ya
kai mu lafiya kaka" Inna tace "Ameen dai, ai har ya kai ni gidan da
xa su xauna da amaryar tasa ni da imaan mun gani, baka ga gidan ba d'an
madaidaici dai dai kafinsa dai, toh ba dai laifi... ni dai nace Allah ya sanya
albarka ai dai ya fi babu wai d'an agwai da bak'in da" Sadeeq ya kasa
daina murmushi nan ko dariya ne kawai ke cin sa, Takaici yasa Mama Hadiza ta
mike tana kallonsa tace "Toh Sadeeq nagode da gaisuwa Allah yayi albarka
bari in shiga can cikin gida" Yace "Toh Ameen mama, nagode" fita
tayi daga parlon, Inna tace "Toh ki ce ma Aisha don Allah tayi miyar
shuwaka yau, naji raina na so" Mama Hadiza dai bata ce komai ba, Inna tace
"Don Allah Imaan ki rufa min asiri ku fito ku gaisa, wannan ai kauyanci ne
daga ganin saurayi ki shige daki, ni ko lokacinmu ba a haka" Sadeeq yace
"Ki kyaleta kaka" Inna tace "In kyaleta d'an nan?" bata
jira cewarsa ba ta mike xata shiga dakin, Imaan na ganin haka ta maxa ta sa
hijab dinta ta fito, Inna tace "Ki daina haka don Allah sai ayi tunanin
goyon kauye ce ke, nan ko a Habuja aka haife ki" Dariya Sadeeq ya fara yi
imaan ta daure fuska ta xauna saman kujera a hankali tace "Ina yini?"
Yace "Lafiya lau, ya gida?" Inna ta xauna tana murmushi tace
"Gida Alhmdllh" kallonta Imaan tayi da sauri ta wani daure fuska, can
ta kallesa tace "Let me see you off, since you've accomplished ur mission
here today" Yana murmushi yace "I see why you don't want the 3 of us
together..." Inna dai sai washe baki take tana kallonsu tace "Ae ita
ma babban makaranta tayi, babu irin turancin da bata iya ba wllh" Mikewa
Imaan tayi tana kallon Sadeeq tace "Let go" Mikewa yayi trying hard
not to laugh yace "Toh kaka na gaishe da Mama da ke, ni xan koma"
Inna tace "Ai mun gode da gaisuwa Bukar Allah maka albarka...." Dubu
goma ya ajiye mata tayi tagumi tace "Ni dai na shiga uku Bukar baka
gajiya??" kofa ya nufa yace "Ai ba yawa kaka, ayi hakuri" daga
haka ya fita don tuni Imaan ta fice daga parlon, sai da suka bar part din Inna
Sadeeq ya tsaya ya dinga dariyar da bai samu damar yi a parlor ba non stop,
Imaan ta dinga kallonsa kamar xata yi kuka, ganin yanda yake dariya seriously
ta jingina da flower tana ci gaba da kallonsa don bata taba ganin dariyarsa
haka ba sai this very moment, he looks more cute laughing, bata san lkcn da
tayi murmushi ba her eyes still on him, don kansa ya gaji ya dakatar da dariyar
haka, a hankali tace "You look cute
while laughing" da sauri ta rufe fuskarta bayan ta fadi haka, ya kafeta da
manyan idanuwansa, kamar ta sani kuwa ta juya masa baya tana xaro ido, and he
felt like hugging her tightly to himself, ya dai yi murmushi ya sauke kansa
kasa praying in his mind Allah yasa xuwa wajensu Abba da xai yi tare da uncles
dinsa in few days time won't be a futile effort... Takun da suka ji a bayansu
yasa duk suka juya a tare, Mujaheed ne ke tahowa tare da Maryam, Sosai gaban
Imaan ya fadi tayi still inda take, tunda ya kallesu sau daya ya dauke kai,
Murya can kasa Sadeeq yace "Is she the Maryam?" Imaan ta gyada kai a
hankali tace "Sure" Suna isowa inda suke Sadeeq ya mika ma Mujaheed
hannu, Mujaheed na kallonsa ya mika masa nasa, Sadeeq yace "Ya aiki?"
Mujaheed yace "Alhmdllh" daga haka ya wuce, Maryam ta gaida Sadeeq,
Yana murmushi yace "It's nice meeting you Maryam, hope babu gajiyan hanya
yanxu" Tace "Ba gajiya kam, kun fa dace da sis dita, Allah ya bar ku
tare" ya wara ido yace "Ameen, I love those last words of urs... Kuma
dole sai na biya words din, you say what ever you want ko menene idan kuma kin
bar min xabi shikenan" ita dai Maryam dariya kawai take tace "Toh
nagode Sadeeq" daga haka ta bi bayan Mujaheed da sauri, tana iskesa murya
can kasa tace "Wllh he is just too cute Ya M.A, Imaan is very
lucky..." Mujaheed bai tanka ta ba ya bude kofar parlon Inna ya shiga ta
bi bayansa, tana cewa "Nama san me xan ce Imaan ta basa for his
birthday...." Kallonta yayi yace "Me xaki ce mata.." ta kashe
masa ido tace "That's our secret big Bro" Xaunawa yyi saman kujera
yana kallon Inna, Inna tace "Yanxu wannan yaron dake neman Imaan ya fita,
baka ga yanda ya dinga fada imaan bata gaya masa bikin ka ranan Juma'ah bane,
gaba daya bai ji dadi ba, Allah kadai yasan me Bulasawan da kansa xai baka,
mutum miloniya meye kuma baxai bada ba" a fusace Mujaheed yace "Sai
dai ya baki ke da kike bukata, amma ni bana bukata, kuma don Allah kiyi hakuri
ki daina maganata a gaban mutane bana so, ni abinda nake da shi ya isheni xaman
duniya ba sai na hangi na wani ba" Yana fadin haka ya fice daga parlon,
Inna ta tabe baki tace "Uwarka Rukayya ka gaggatsa ma magana ka fita ba ni
ba wllh, ba abinda ya hada ni da kai dama, kawai Ahmadu ne ya haifeka ni kuma
na haifesa, Ni ban yi mamaki ba tunda goyon Rukayya ce kai din ai, xaka yi fiye
da haka" Maryam na dariya ta mike ta fita a parlon ita ma, da daddare
Imaan na fitowa daga wanka daure da towel tace "Wai ina kuka je daxu da
yaya tun safe" Maryam dake operating laptop tace "Wato kina wanka
hankalin ki na wajen ki fito kiyi tambaya" Dariya Imaan tayi tace "Eh
mana" Maryam ta ajiye laptop din a gefe tace "Ae babu inda ba mu je
ba..." Imaan tace "Kamar Ina da Ina?" Maryam tace "Ya fa ce
kada in gaya ma kowa har ke" Imaan ta xauna kusa da ita tace "Don
Allah ki gaya min, ai ba gaya masa xan yi ba" Maryam tayi dariya tace
"Anya xan iya gaya maki kuwa, ce min fa yayi amana, kuma sbda ke muka je
wajen...." Imaan kamar xata yi kuka tace "Don Allah ki gaya min, wllh
baxai sani ba, abinda ma ba shiri muke da shi ba yanxu"
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
44....
Maryam tayi dariya tace "Kai Imaan haka kike da son jin
abinda bai shafe ki ba?" Imaan ta marairaice mata tace "Ni dai ki
gaya min" Maryam na murmushi tace "Ke ba ko ina mu ka je ba, kawai
dai ya kai amaryar tasa plazan da xa ayi mata dinkunan bikin ne ya bada kudi,
sai kuma gold na rings guda uku da ya siya mata for the wedding, sannan muka
koma gida muka ajiye ta, after that muka je kasuwa siyo drinks da Ummansa tace
ya siyo, sai flasks da bedsheets da xata yi souvenir ma kawayenta....." Imaan
ta ja tsaki tace "Toh meye na cewa kar ki gaya min, ko ni ina
ruwana?" Maryam tace "Ke wasa nake kawai Inna yace kar in gaya ma
amma ba ke ba" Imaan ta mike tana goge jikinta tace "Toh shine xa ki
ce saboda ni ku ka je inda ku ka je?" Maryam tace "I am just pulling
ur legs, kin taba ganin amaryar tasa kuwa?" Imaan tace "Ehh na taba
ganinta a gidansu" Maryam tace "She is beautiful but her fairness
isn't natural" Imaan tayi dariya tace "Artificial ne kenan"
Maryam tace "Probably... And she isn't friendly, she didn't even
acknowledge my present sosai, kamar bata son mutane, sai kin ga ma yanda ta
amsa min gaisuwan da na mata, she just shunned me..." Imaan tace
"Tohh ba sai ki fasa bin su ki dawo gida ba, Toh me yayan yace?"
Maryam tace "He couldn't say anything to her, amma shi ma naga bai ji dadi
ba, coz he even introduced me to her again, amma ta ki cewa komai" Rai
bace imaan tace "Toh wai me yasa baki dawo gida ba??" Maryam tace
"Ae ban san hanya ba, beside I am not with money, ga shi in gaya maki sai
wani shagwaba take masa a mota, shi ko a cikin magana goma bai fi ya amsa mata
uku ba" Imaan tayi dariya tace "That's their problem" Maryam
tace "Yea least I forget, na yi maki deciding abinda xa ki siya ma Bf din
ki for his birthday" Imaan na shafa lotion dinta tana kallonta ta madubi
tace "And what's that?" Maryam tayi murmushi tace "But wait...
did he invite u for the birthday party?" Imaan ta gyada mata kai, Maryam
tace "Kuma xa ki je?" Langwabar da kai Imaan tayi a hankali tace "Toh
I haven't decided yet, ban sani ba tukun" Maryam tace "Toh after ur
decision xa a bar ki kije a gida kuwa?" Imaan ta xaro ido tace "Dama
wa xan gaya ma?? Tab... Am telling nobody" Da sauri ta dawo kusa da Maryam
ta xauna tace "Plss Maryam wannan ya xama sirri tsakanina da ke, Kinga even
Maimoon da ta ke kawata ma ban gaya ma ba, don Allah kar by mistake ki ce ma Ya
Mujaheed anything about the birthday" Shiru Maryam tayi tana kallonta,
hankali tashe Imaan tace "Ko dai har kin gaya masa?" Maryam tayi yake
tace "Haba dai why will I, of course ban gaya masa komai ba" Imaan ta
sauke wani ajiyar xuciya tace "Better" Maryam tace "May be... A
day to the birthday sai mu fita babban shopping mall in nuna maka abinda ya
kamata ki siya masa" Imaan tayi shiru tana tunani, can tace "Toh
Allah ya kai mu" kayan baccinta ta saka ta hau saman gadon ta dawo kusa da
Maryam tana kallon abinda take yi a laptop dinta.
Slowly ranakun suka dinga tafiya har ya rage saura kwana biyu
bikin Mujaheed da Safeenah, gida ya cika da Yan uwa da abokan arxiki, matan
kawu Bala, Hansai da yaranta kai duk yan uwa dai an cika gidan barin part din
su Umma, duk inda kaga Imaan toh xaka ga Maryam a gidan kamar da can sun saba
da juna sosai, seriously Mujaheed ya sa ma Imaan ido a gidan, ita kuwa ko sanin
yana yi bata yi ba. Da yamma Imaan na parlon Inna tare da Maryam sun kawo mata
abinci, sai bin Inna dake ta neman makullin bandakinta suke da kallo, duk ta
hada xufa ta wani tsuke fuska, komai sai da ta daga a parlon amma babu makulli
babu labarin sa, Mama Hadiza ta fito daga daki da alamar ita ma neman makullin
take tace "Toh wai ina kika ajiye makullin Inna?" Inna tace "Ke
ki rabu da ni don Allah, nasan inda na ajiye xan ta neme neme, da ba don
rubabbun dake shigo min nan ba har xan wani kulle bandaki kamar warce ta ajiye
gwalagwalai a ciki har shegen makullin ya bata?? Ni dai ba ruwana a ma daina
xuwa min nan gaba daya, tunda ba ni ke aurar da mutumi ba" Dariya Maryam
ta dinga yi Inna ta daga kai daga duken da take tana kallonta, Sallama aka yi
bakin kofa Inna ta mike tsaye ta amsa sallaman, Ta rasulu ta shigo tana kyabe
fuska, Rahma ta ajiye mata karamin jakarta ta juya ta fita, Inna na washe baki
tace "Sannu da xuwa Ta Rasulu kinga na rasa inda na jefa makullin bandaki,
gudun kar a shigar min bandaki na kulle na saka makullin a bakin zani to yanxu
gashi ko sama ko kasa" Ta rasulu tace "Toh ai gwara da aka nema aka
rasa gaba daya, kinga bayan bikin sai a balle kofar kawai, don wani na iya xuwa
ya maki dadin baki ki kunce makullin ki basa, mutane dai basu gaji mutunci ba,
kinga yanda aka 6ata tsakar gidan da shinkafa ga yara jage jage kamar daga
kauye, ni dai ba kowa ma ya kamata a dinga bari yana shigowa ba ma wllh, sai
kace ba bikin yan gayu ba" Inna tayi tagumi tace "Naga abinda ya
isheni, kin ji wata fitina koh, Kai mutane dai jarababbu ne, kice tsakar gida
na nan duk wari?" Ta rasulu ta tabe baki ta wuce cikin dakin tace "Ae
kuma sai ki yi, abinda tsoron Allah yayi karanci a xukatan mutane yanxu"
Inna tace "Toh ni kuwa xan je in basu hakuri su rufa mana asiri kada gidan
'ya yana ya lalace mu shiga uku, sannan biki dai ba ace a xo da yara ba"
Mama Hadiza ta leka dakin ta gaida ta rasulu sama sama ta fita parlon gaba
daya, Imaan ta tabe baki xata tashi Inna tace "Toh ke kin gaida ta rasulun
ma kuwa" daga cikin daki ta rasulu tace "Ina fa ta gaida ni tana
kallona ina kallonta, yaran yanxu kam sai ka kyalesu, mu dai muna masu fatan
alkhairi Allah kuma ya basu miji na gari, har wannan figaggiyar ta kusa da ita
ma ni bata gaisheni ba ai" Imaan ta gaida ta daga inda take tana turo baki
ta mike ta fice a parlon, Maryam ta mike ita ma ta gaidata ta fice Inna na cewa
"Iyayenku ku ka ma haka ba mu ba wllh" Daren ranan Daddy ya iso daga
Abuja, bayan ya huta suka d'an taba hira da Mama Hadiza da yake a part din ta
sauka, sannan ya fita don xuwa ya gaida Inna, Imaan ta bi bayansa da sauri,
bayan sun sauka balcony yana kallonta
yyi murmushi saboda yasan akwai abinda take son gaya masa kenan tunda ta
biyosa, yace "Do you need anything Imaan..." A hankali tace
"Daddy kaga mutane sun yi yawa a gidan nan plss ni dai ina son xuwa gidan
gwaggwo in xauna har a gama biki in dawo Saturday" Da mamaki yace
"Bikin yayan naki kuma Imaan?" Tace "Daddy I will be very
uncomfortable, ai da rana xan wuce gidan gwaggwo din ba da safe ba" Yace
"Toh ita kuma Maryam fa, won't she be lonely" Imaan tayi dariya tace
"Ae tare xa mu je daddy, ita ma tace min she's already uncomfortable tun
daga jiya da mutane ke ta xuwa" Murmushi Daddy yyi yace "Ohk then sai
ki gaya ma Ammin ki" Imaan ta wara ido cike da jin dadi tace "Toh Daddy
nagode sosai, ai dama Ammi...." Shiru tayi hango Mujaheed da ta yi yana
tahowa daga part dinsu, Daddy ya kalli inda take kallo, ganinsa ya tsaya har ya
iso inda suke, da ladabi Mujaheed ya gaida Daddy, daddy ya amsa yace "Ya
shirye shirye M.A" Murmushi kawai Mujaheed yayi, Imaan tayi wucewarta gaba
ta bar su tana cinno baki, da sallama ta shiga parlon inna, Ta Rasulu na xaune
kan darduma ta daura kafa daya kan daya ta rungume hannu tana sakace hakori,
Inna kuma na xaune kan tabarma ita ma ta daura kafa daya kan daya, Umma na
parlon xaune ga bucket cike da cin cin da alkaki da ta shigo da sai kallon ta
Rasulu take kasa kasa, Ta Rasulu ta kyabe baki tace "Yo ai duk matsiyata
ne Asabe, ni shi sa ba ruwana da kowa wllh, ba ruwana" Inna tace "A'a
dama fa nasan a wajensu tsiya ya kare, ni ina ruwana da su Ina ta kai na, oh oh
wlh" Ta Rasulu ta kalli Imaan sannan ta kalli Inna tace "Matar nan na
amfani da iccen da kika bata kuwa?" Inna xata yi magana Daddy ya shigo da
sallama Mujaheed na biye da shi a baya, Inna tace "Allah dai ya baku lada
wannan hidima da kuke ta yi da Mujaheed, ko kudin jirgin da ka kashe yau ma ai
xaune yake da kansa, Allah dai yasa ya ji k'an ku nan gaba, yayi ma imaan abun
kirki ranan bikinta" Daddy ya xauna yana murmushi ya gaisheta sannan ya
gaida Ta Rasulu, Umma ta gaishe sa sama sama, ya amsa yana tambayarta taro, ta
Rasulu ta rike ha6a tana kallon Daddy tace "Ohh Bukari kana nan dama,
rabona da kai fa tun da ka xo daurin auren ishaq" Daddy yace "Ina nan
Baaba, sai dai yanxu a Abuja nake" Ta Rasulu tace "Toh Allah yayi
maku albarka, ya kare ku sharrin masu sharri, ya sa ku gama lafiya da mu, ya ba
matanku ikon yi mana biyayya yanda ya kamata" Yana murmushi yace
"Ameen Baaba" Mujaheed ya gaida ta Rasulu, ta Rasulu tace "Sannu
ango, amma kuma duk naga ka rame baka cin abinci ne?" Inna tace "Ke
ma dai da wata magana ta Rasulu, ina xai ci abinci yana tunanina, kin xata
rabuwa da ni abu ne mai sauki?" Dariya Daddy yayi yana kallon Mujaheed,
Mujaheed ya kalli Inna ta gefen ido bai dai ce komai ba, Umma ta wani daure
fuska tana hararan Inna ta gefen ido, Ta Rasulu tace "Toh kayi hakuri
Mujaheed, abinda bayan bikin da sati daya kawai sai ka xo ka dauketa ka mayar
da ita gidan naka gaba daya, ohh sa6o turken Wawa" Inna tace "Ae shine
na ga, nayi kokarin fahimtar da shi hakan amma ya kasa kwantar da hankalinsa,
sai in koma can gaba daya Imaan kuma ta dinga xuwa duk Juma'ah ta koma
lahadi" Daddy dai sai murmushi yake, Imaan ta saci kallon Mujaheed taga
kallonta yake, dauke kai tayi da sauri, Inna tace "Toh ni dai ta Rasulu ga
ki ga Bukar yau, sai ki masa bayanin mutumin nan na bayan tsauni a tsanake,
tunda ni na kasa fahimtar da shi da Ahmadu suna ganin kamar ko boka ne, Ni ko
me xai kai mu gun boka mu masu tsoron Allah" ta Rasulu tace "Wllh
Bukar ku maida hankalin ku don sai anyi da gaske da 'yar nan taka Imaan, tana
da makiya ne ba na wasa ba, sannan wannan ciwace ciwacen nata ma ance ba banxa
ba da sa hannu, sai an tashi tsaye kyam kada a kai mu a baro, bangaren aure
kuma ance xata auri wanda ke bala'in sonta, wasu xa su yi murna da auren wasu
kuma bakin ciki da hassada baxai bari su yi ba, wasu kuma takaici baxai yarda
su yi murna ba, sannan da matsalaloli iri iri a xaman auren, matsaloli masu
girma ba dadin ji kuwa, ni dai ba fata nake ba amma gaskiya abun ba dadin ji,
kuma ance sai ta cika maka parlor da jikoki, toh ni abinda ban gane a nan ba
shine... Kyashin fidda kudi kake a nema ma tillon yar ka lafiya ko kuwa kudin
ne baka da shi Bukar?" inna tace "A'a sai dai kyashi, amma yana da shi
wllh, Toh wllh sai ma kin tafi bayan biki xa su xo su sameni shi da d'an uwan
suce in rabu da ke ba hanyar kirki kike nuna min ba, Toh wai dama Allah ba yace
mu tashi ya taimake mu ba??" Daddy ya kasa daga kai, ta rasulu
ta saki salati tana tafe hannu tace "Sai su ce ki rabu
da ni kuma?" Inna tace "Wllh kuwa tatas xa su min suce in raba kaina
da ke, ai ga shi nan xaune da ransa ba sharri na masa ba kullum na kawo masu
xancen sai su gwaleni suce karya ce inyi ta kaina, to ni ya xan yi da
su??" Mujaheed ya sunkuyar da kai sai murmushi yake, imaan ta boye fuska
bayan kujera tana dariya kasa kasa, Daddy dai ya kasa dago kai, Ta rasulu tace
"Dago kanka ka kalle ni Bukar, wllh wannan 'yar taka idan ba a tashi tsaye
kanta ba duk sai mun shiga uku a duniyan nan, idan ma xaka fiddo kudi ka fiddo
kudi a nema mata magani ta xama mutum, tunda har kuka iya karyata ni kai da
Ahmadu to xa ku iya karyata Asabe ma" Inna tace "Yo na nawa kuma? Ai
sun ma karya ta ni, sai dai Allah ya shirye su, ni dai na yafe masu" Daddy
dai kansa na kasa, Ta Rasulu tace "Yanxu bayan biki sai ka ba Asabe dubu
dari, idan ma ya kama muje tare da ita da Imaan din ne sai duk mu
tafi...." Inna tace "Haba sai kace xa ki cuce ni, ai kawai ki je ke
daya ba komai wllh" Daddy yace "Toh Allah ya kai mu xa a bada" Mikewa
yayi yace "Na gaisheku xan je in huta" a tare suka hada baki wajen
cewa "Toh Allah maka albarka" yace "Ameen" sannan ya fita
parlon yana girgixa kansa. Umma da duk ta hada xufa gaba daya jikinta tana
murmushin karfin hali tace "Toh Inna ayi hakuri da wannan din don Allah,
ni xan koma in ji da baki" Inna tace "Toh ai ya fi babu, Allah dai
yayi albarka" tana murmushi tace "Ameen" ta fice parlon da sauri
tana share xufar goshinta a ranta kuwa hamdala take da Allah ya bayyana mata Ta
Rasulu.
Washegari Thursday duk yan matan gidan na ta shirye shiryen
fita saloon da yin lalle, ita dai Imaan sai kumbure kumbure take...
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
45.....
Mujaheed na dinning a xaune Maryam ta sakko downstairs tare
da Maimoon, yana kallonta yace "Maryam" ta kalli direction din sannan
ta tafi tace "Sai yanxu kake breakfast?" Yace "Ehh...
xauna" ba musu ta ja kujera ta xauna, ya ajiye cup din coffee dake hannunsa
yace "When did she tell you is the birthday?" Maryam ta langwabar da
kai tace "She told me nothing about it again, tun ranan bata gaya min
komai ba" Yana kallonta da kyau yace "Karya kike Maryam" ta xaro
ido tace "Karya kuma ya M.A, bana ma tunanin Birthday din na nan don bata
ce min komai ba, kuma kaga gashi ana ta hidiman biki, kila ma ta manta idan ma
Birthday din na nan" yace "Make me a promise Maryam" tace
"What promise" yace "You will watch her movement keenly"
dariya tayi tace "Ohk then, amma kuma abun mamaki ina ma xata je ana
biki" Yace "Just do what I say" tace "Toh na ji" yace
"Good tashi ki tafi" Mikewa tayi ta bar dinning din, ya dau coffee
dinsa ya ci gaba da sha a hankali. A bedroom Maryam ta tadda Imaan dake ta
shiryawa slowly wai don a tafi a mance da ita, Maryam tace "Naga alamar
baki son xuwa saloon din nan imaan" kamar xata yi kuka tace "That's
just it, ni scalp dina ma ciwo yake min, aje ayi ta ja min gashi kaina ya fara
min ciwo, ni dai kawai ku tafi kice masu baki gan ni ba" Maryam tayi
dariya tace "Kai Imaan, da ni ke da irin gashin ki ai duk sati sai naje
saloon" ita dai Imaan bata ce komai ba, Sadeeq ne ya fado mata ta tuna
wata rana da daddare suna waya yake ce mata shi dai yana son dogon gashi, haka
kawai taji tana ma son xuwa saloon din, Maryam ta gama yafa karamin veil din
abayar jikinta tace "Ohk then xan ce masu ni ban gan ki ba" Imaan
tace "Ko kuma ma dai kawai bari mu je, idan ya so ana gama mana sai mu
tafi mu siya abinda xa mu siya a shopping mall, koh?" Maryam ta wara ido
kamar baxata ce komai ba sai kuma tace "Ehh haka ne kuma" Imaan tace
"Kinsan fa gobe ne birthday din kuma I have to give him the gift this
night" Maryam tace "Au haba, same day da bikin Ya Mujaheed
kenan?" Imaan tace "Sure" Maryam tace "Tabdi, Toh yanxu ya
xa ki yi? Ga biki ga birthday" Imaan tayi yar dariya tace "Ni ina
ruwana da biki, Ai na riga na ce ma Daddy xan je gidan Gwaggwon Ammina gobe da
safe" Maryam ta marairaice tace "Tafiya xa kiyi ki bar ni
yanxu?" Imaan tace "Of course no, tare xa mu ai" Maryam ta
langwabar da kai tace "Yanxu haka xa mu yi missing bikin ya MA, gashi ma
anjima da daddare xa ayi dinner fa" Imaan tace "Aa idan kinga xaki
tsaya ki tsaya ni dai ba ruwana" Maryam tayi murmushi tace "Aa mu je
gidan grandma din dai..." Imaan tace "Better" a tare suka fita
dakin, Ammi dake parlor ta nuna ma Imaan kan kujera tace "Ga kayan ku nan
ki shiga da shi ciki yanxu aka kawo" Imaan ta dauko ta kai daki sannan ta
fito, sosai gaban Imaan ya fadi ganin Mujaheed parking space a tsaye, tun da ya
kalleta sau daya ya ci gaba da danna wayarsa, ta dauke kai ta isa gun motar da
ake kai su makaranta tana kallon Maimoon, Maryam kuma ta tafi gun Mujaheed tana
murmushi tace "Our handsome groom..." Imaan ta tabe baki tana kallon
Maimoon tace "Ina Drivern da xai kai mu Saloon din?" Maimoon tace
"Ya Mujaheed yace xai ajiye mu shima fita xai yi yanxu" Xaro ido
imaan tayi tana kallonta, ta hade rai bata dai ce komai ba, Ummi ta fito
bangarensu tana kallon Mujaheed tace "Rahma xata taho daga baya, wai xa su
fita tare da Umma yanxu" bude driver seat Mujaheed yyi ya shiga yana
kallon Maryam yace "Har da ke xa aje gyaran gashin?" Ta xaro ido tace
"Eh mana" murmushi yayi yace "Toh shiga..." imaan ta bi
bayan Maimoon tana cika tana batsewa ta shiga back seat, Ummi ma ta shiga. Suna
isa saloon din yyi parking yana kallon Maimoon ta madubi yace "Since babu
mutane sosai a saloon din xan jira ku gama" Maimoon ta washe baki tace
"Tohh mun gode Ya Mujaheed" a fusace imaan ta fice a motar ta bar
door din a bude cikin tsawa yace "Keee" juyowa tayi da sauri, fuska
daure yace "Xo ki rufe min mota kada in sauka in xane ki yanxu" Ganin
babu wasa tattare da shi ta dawo kamar xata yi kuka ta rufe motar ta juya ta
shiga saloon din, Maryam tayi murmushi tace "Ya M.A kai dai kawai kayi
tafiyarka ko motorcycle din nan mai kafa uku sai mu hau ya dawo da mu
gida" Mujaheed yace "Sauka kije kiyi abinda ya kawo ki nan" Yar
dariyar yake tayi ta bude motar ta fita, ita kanta bata ji dadin jiransu da
yace xai yi ba, shikenan ya ruguje masu plan. gyara ma Imaan gashi ake amma
gaba daya hankalinta na gun lekan waje don ganin ko Mujaheed ya canxa mind
dinsa ya tafi, amma duk ta leka sai taga yana nan, ta ji kamar ta kurma ihu, a
haka har aka gama masu gyaran gashin aka fara masu lalle a hannu, Maimoon ce ta
fara fita bayan an gama masu, Ummi ma ta fita, Maryam na kallon Imaan a hankali
tace "Kinga yayi spoiling plan dinmu ko, yanxu how are we going to get the
gift?" Imaan ta rasa abinda xata ce mata, can Maryam tace "You know
what, kawai mu koma gida, dama akwai few abubuwan da nace ma mum xan siya a
Nigeria, muna isa gida yanxu xan amshi card dinta mu fita daga can ma sai in
siya abubuwan da nace" Sosai hankalin imaan ya kwanta, ta d'an yi murmushi
tace "Toh shikenan, har naji dadi" tashi Imaan tayi suka fita saloon
din din Maimoon ta bada kudin kafin su fita, tun da suka fito Mujaheed ke
kallonsu ta madubi har suka iso gun motar, ganin Ummi xaune a gaba Maryam ta
shiga back seat tare da Imaan, tada motar yayi ya dau hanyar gida. Suna isa
gida Mujaheed yayi parking ya kashe motar, Imaan ta fita ta dau hanyar
apartment dinsu, ya gyada kai yana bin ta da ido ta madubi... Maryam tace
"Mun gode ya M.A" bai amsa ta ba tayi wucewarta tana murmushi. Maryam
na gaya ma mama Hadiza xata fita shopping ta hanata wai bayan biki sai su je,
ba ynda Maryam ta iya ta koma dakin Imaan a sanyaye ta sanar mata abinda
mamarta tace, imaan ta rasa yanda xata yi, Maryam tace "Toh ko mu bari
kawai gobe da safe idan mun fita xa mu gidan grandma dinki sai mu shiga mu
siya" a hankali Imaan tace "Noo yau ya kamata in basa, yau nake son
in basa" Shiru Maryam tayi, can tace "Ba xa mu je dinner ba anjima,
kawai mu jira sai mutane sun cika wajen sai in sulale da makullin motar Yaya
Yusuf mu je mu dawo" Imaan ta xaro ido Tace "Ni fa ban yi niyyar xuwa
dinner din ba wllh" Maryam tace "Ae ko gwara ki daura niyyar xuwa
yanxu, don that's the only way out" Imaan tace "Toh shikenan"
Ana idar da Magrib duk aka gama shirin tafiya wajen dinner, duk wannan abun
Mujaheed na lura da su keenly, kuma yaki tafiya duk da yanda abokansa suka
dinga takurasa su wuce saboda amarya har ta iso wajen, Maryam dai ta dinga bin
Yusuf wai ya bata makullinsa tayi driving din, daga karshe dai babu yanda ya
iya ya bata, da kyar imaan ta saka gyale a kan ankon su na Dinner da Daddy yayi
masu gaba daya gidan, tayi kyau har ta gaji amma sai wani nonnokewa take abunka
da ba sabon ba, Maryam ce tayi driving din nasu xuwa hall din da xa ayi dinner
din.... Waje ya cika makil da masu kudi sai ruwan naira ake tun kan a fara
komai, Fara'a gun umma ba a cewa komai, Inna na xaune tare da ta rasulu a table
guda duk sun sha atamfar England an yafa gyale sun tsuke fuska suna kallon ikon
Allah, Imaan na shigowa hall din tare da su Maryam ganin Inna da ta rasulu ta
rufe fuskarta gyalen jikinta ta dinga ba66aka dariya, suka nemi waje suka
xauna, kallon inda amarya da ango ke xaune tayi, taga Safeenah da tayi wani
kyau irin na aljanu sai sheki gwalgwalan jikinta suke, kayan jikinta kam dama
ba acewa komai, ta kalli Mujaheed da ya sa lafiyayyen farin gezna sai walkiya
yake, hada ido suka yi da shi tayi saurin kauda kai, Imaan ta kalli Maryam tace
"Ni dai xan koma gun su Inna kafin mu fita" bata jira cewar Maryam ba
ta mike ta tafi gun su Inna Mujaheed ya bi ta da ido.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
46....
Inna na kallon Imaan da ta xauna kusa da ita cike da damuwa
tace "Toh ba gashi kin fito sak mutum ba yau kin sa gyale, amma da kullum
da hijabi xulum xulum kamar matar ladani..." Ta rasulu dake ta bin jama'ah
da kallo tace "Toh wai ni abinda na kasa ganewa a nan shine... uwar
amaryar da danginta basu san kin xo nan bane ban ga an xo gaishe ki ba har
yanxu, dubi fa yanda muke xaune kamar gantalallu marasu makabuli babu wanda ya
bi ta kan mu, an san ke kika raini Mujaheed tun yana tsumma kuwa, Kai duniya
dai ta lalace ni ta rasulu" Inna ta tabe baki tace "Shine nake ta
kallon ikon Allah, sai yawo suke mana da gwalagwalai kamar barayi babu wanda ya
xo ya durkusa nan yace Sannu Inna... ya taro? To Allah ya sanya alkhairi ya
nuna mana na 'yan baya, shi kuma Mujaheed din dubi yanda ya wani yi tsamo tsamo
da shi kusa da amaryar babu walwala kamar dai wanda aka tilasta ya xo casun..."
Imaan tayi murmushi ta kalli Mujaheed sannan ta kalli Inna tace "Toh ke
ina ruwanki..." Inna tace "A'a da ruwana mana, ni ba karamin aikina
bane in tashi inje samesa yanxu in ji ko lafiya..." Ta rasulu tace
"Maxa je ki, nima naga rashin walwalan yayi yawa sai yake kawai yake,
kamar wanda aka ma dole, anya ma auren soyayya xai yi kuwa" Inna ta tabe
baki ta mike tace "Toh wani ya rainan min shi da baxan sani ba idan yana
cikin damuwa ko akasin haka, sarai nasan sa ciki da bai, da abinda ke damunsa a
xuciyarsa xaman da yayi a nan" Kutsawa ta dinga yi cikin mutane wanda yaki
matsawa dama hankadesa take tana cewa "Yau naga bala'i mutane an xo cin
shinkafa da yar kaza kamar mayu, an ki bani hanya..." Kallonta aka dinga
yi ana bata hanya tace "Banda jaraba ko wacce ta fiddo kayanta na
karkashin akwati ta saka ta xo mana nan tana jiran shinkafa da salaq da kaza,
ohh yunwa ta yi yawa a duniya" A haka har ta isa inda amarya da ango ke
xaune, wata kawar amarya ce tsaye tana bada history din amarya sai wani yauki
take tana jujjuya idanuwanta, cool music sai tashi yake mutane na mata tafi...
sake baki Inna tayi tana kallon yarinyar, can dai ta karasa inda take tsaye ta
d'an ta6o ta a kafada, gaba daya wa enda suka san Inna suka xaro ido suna
kallon ikon Allah, juyowa budurwar tayi tana kallon inna murmushi dauke
fuskarta, Inna ta matsa kusa da ita sosai murya can kasa tace "Wani
tsinannan telan kika ba kayan ki ya lalata maki haka saboda rashin tsoron
Allah, duk duwaiwuka a waje?" Ba karamin tsorata da girgixa Inna tayi ba
tana xare ido jin muryarta ya kauraye makeken hall din gaba daya ta cikin
speakers, Hall ya rikice da dariya, Mujaheed ya sunkuyar da kansa, Umma ta kasa
motsi inda take tsaye sai hadiye abu take da kyar, Imaan ta hade kai da table
tana dariya kasa kasa, su Maimoon ma suna ta dariya daga inda suke xaune, Aunty
da Ammi da Mama Hadiza dama tagumi suka yi suna kallon Inna da tayi tsamo tsamo
a gaban hall sai kallon jama'ah dake dariya take, gaba daya yan uwan amarya
wani kallo suka dinga yi ma inna, ita kuwa mai bada history ta ji kamar ta
nutse gashi an ki daina dariya a hall, Safeenah ta wani hade rai tana kallon
Mujaheed tace "Haba Mujaheed dama gate pass din wa enda suka kamata da
wanda basu kamata ba ku ka dinga raba ma suka shigo mana nan, dubi wannan
tsohuwar me ya kawota nan ta ina ta samu pass din shigowa har xata kunyata
aminiyata cikin mutane, kasan Yar gidan wacece ita kuwa??" Gently Mujaheed
yace "Watch ur words..." A fusace tace "Don't tell me that
Mujaheed, how dare the old woman insult my friend that way, yar gidan governor
ce fa tsaye a wajen..." Calmly yace "Ko yar gidan uban wacece, ke
kawarki ce, to ni kuma grandmum dita ce a kusa da ita, so you dare not look
into my face and say nonsense about her" Wani kallo Safeenah ta dinga ma
Inna da ta tabe baki cikin sanyin murya tace "Ba lafiya, dama ba a sirri a
nan, daga magana kuma sai sipikoki su dauka su min terere...." Juyawa tayi
ta kalli yarinyar da ta kasa cewa komai har sannan tace "Ki dai maida masa
ya gyara maki ai kudi kika biya ya cuce ki ya maki wannan dinkin" daga
haka ta bar wajen ta tafi gun Mujaheed, har sannan Safeenah bata daina bin ta
da wani irin kallo ba har ta iso inda suke tana kallon Mujaheed tana washe baki
tace "Wannan ce amaryar Mujaheed" Safeenah ta dauke kai fuska daure,
Inna ta rike ha6a tace "Ikon Allah, Toh Allah ya bada xaman lafiya, ta dai
sha gwalagwalai maa sha Allah" Hajiyan Marafa ce tsaye kan Umma tana
bala'i a mugun fusace tana cewa "Haba Rukayya ke baki ga irin manyan
mutanen da muke ba gate pass bane xa ku ba wannan tsohuwa mai wanke wanke ta
shigo mana hall tana shirme tana kunyata mutane, kin san yar gidan wacece tsaye
a wajen take magana kuwa?? reputation dina da na 'ya ta kuke son 6atawa ko meye
hakan?" Umma dai sai hakuri take bata a rikice tana cewa "Wllh ban
san wanda ya bata pass din ba, don Allah kiyi hakuri Hajiya, wllh ban san daga
inda ta taho ba...." A mugun fusace Hajiyan Marafa tace "Toh maxa ki
sa a fitar da ita daga hall din nan tun wuri kada ayi mummunan abu a nan, maxa
a fita da ita kada in sa masu gadi su fitar min da ita ta tsiya" Umma sai
cewa take kiyi hakuri Hajiya xa ta tafi yanxun nan kuwa, ae ba ku kadai ta
kunyata ba har mu wllh, ban san wanda ya bata pass ta shigo ba ni ban ma santa
ba, haka irin tsoffin nan suke idan suka ga ana taro su shigo cikin
jama'ah" Hajiyan Marafa ta juya fuu ta wuce tana cewa "Maxa ta bar
nan kada in sa masu gadi su ja ta su fitar..." Inna na kallon Mujaheed
tace "Toh naga duk baka da walwala lafiya kuwa, ko baka ci abinci
bne?" Ya girgixa kai yace "Ba komai, ki koma kiyi xaman ki" Inna
tace "Toh madallah sai dai har yanxu mu dai babu abinci babu labarinsa, ga
ta rasulu can ma sai hamma take" Tana magana ta dau tsadadden drink dake
gabansu tace "Ko in dau wannan" yace "Dauka" dauka tayi
tace "Toh shikenan, Allah dai yasa ba mai halin uwarka xaka auro mana ba
dai" daga haka tayi wucewarta, Safeenah ta bi ta da wani harara tana kyabe
baki, Umma ta rasa yanda xata yi ta fitar da Inna a hall din cikin lumana, duk
ta rikice taje can taje nan, Inna na dawowa xuwa seat dinta ta dinga cewa
mutane "To dai duk wanda ya ci abu yyi hakuri ya saka gwangwani ko kwalin
a jakarsa kada mu bata masu waje da kazanta mu cuce su...." A haka har ta
koma gunta, ta ajiye ma ta rasulu drink din daya ta ajiye daya gabanta tace "Ma
rage xafi..." Ta dau drink din ta fara budewa, Inna ta xauna tace
"Naje na samesa amma kinsan ko gaisheni amaryar bata yi ba, ni dai ban
kulata ba, ba ruwana kada in kunyata kai na cikin jama'ah ga ni babba, taro
yayi taro in je inyi magana in kunyata Mujaheed din ma gaba daya, bakina a leko
na juyo na dawo ai ana tare...." Ta rasulu tace "Gwara da baki kulata
ba kam, ki bari sai an kaita dakin nata ki shirya kije ki mata tatas ki gaya
mata yanda kike da Mujaheed" Inna tace "Ehh dama ai dole in sanar
mata wahalan da nayi da shi don ta gane matsayina a wajensa, ana kai ta da
washegari dama Imaan xan ce ta rakani inje in karanta mata yanda muke da
shi" Umma ce ta taho gun Inna da sauri tana haki tace "Inna yanxu aka
kirani wai ruwa ya cika parlon ki sai kwararowa waje yake ga kofar a rufe, ko
dai kin bar pampon bayan gidan ki a bude baki sani ba?" Inna ta mike ta
rafka uban salati a rude tace "Hadiza ta cuce ni ita ta shiga bandakin
karshe tayi fitsari, shikenan ruwa ya shanye min gida na shiga uku na lalace ni
patuu, ga dukiyoyi irinsu kujeru, tv, gado carpet, fridge duk a ciki" ta
rasulu dake xabga salatin ita ma ta mike tace "Na shiga uku ni ta rasulu,
jakata na dakin nima har da kudi dubu biyu, yanxu me xan ce ma 'ya yana daga
xuwa biki ambaliya ya rutsa da ni??" Umma tace "Toh bari in sa driver
ya maxa ya maida ku gidan gaskiya, don ruwa aka ce duk ya cika tsakar
gida" Ko sauraranta Inna bata yi ba ta fice da gudu tana cewa
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'una ambaliyan ruwa a gidana a kira min
yan kwana kwana, ga gudunmawar dubu hamsin da Bulasawa ya bani a
dakin...." ta rasulu na biye da ita a baya ita ma da gudu tana salati,
Mama Hadiza da su Aunty na ganin Inna ta fita da gudu suka taho gun Umma dake
tsaye suna tambayarta me ya faru, Umma tayi wani dariya tace "Wai fa kudin
da xata yi liki ta mance a gida shine wannan saurin wai driver xai maida ta
gida" Kasa cewa komai Mama Hadiza da su Aunty suka yi, Umma tace
"Allah dai ya kyauta, lamarin Inna ae sai ita" daga haka ta wuce ta
bar su wajen a tsaye, Imaan dai na xaune an barta da jakunkuna irin na
tsofaffi, Maryam ce ta taho gun Imaan da sauri tace "Ke maimakon mu bi su
Inna mu je mu yi abinda xa mu yi kika bari suka wuce" Imaan ta xaro ido
tace "Ae kuwa, toh kawai mu yi kamar xa mu bi su da jakar su sai mu
wuce" Maryam tace "Toh dauko mu tafi" Imaan ta dau jakar Inna ta
mika ma Maryam na ta rasulu, kallon Mujaheed tayi taga idonsa na kansu, ta
dauke kai tana xaro ido tace "Maryam kin san Yaya kallonmu yake"
Maryam ta kallesa taga still kallonsu yake duk da liki da mutane suka taru
wajen suke masa da Safeenah, Maryam ta koma ta xauna tace "He is
suspecting us Seriously, kin san me xai faru?" Imaan ta girgixa kai,
Safeenah ta bude jakarta ta ciro new note din naira dari dari tace "Gashi
ki tafi kiyi masu spraying, kafin ki dawo na fita gun mota sai ki sameni da
sauri, but before then Bari in canxa seat" Imaan ta nufi can gaban hall
din hannunta rike da tulin kudin, su Maimoon, Ummi, Rahma da wasu kawayen
Safeenah da yan uwanta da suka sha gold sai cashewa wa suke da wakar jarumar
mata da ya cike hall din Lol.... Safeenah ma na tsaye tana rawa gently tana
kallon Mujaheed with love, shi ko yana tsaye kamar statue yana jujjuya wayar
hannunsa, dance floor din kuwa banda dubu dubu babu abinda xaka gani a kasa sae
few five hundred notes, Imaan ta isa kusa da su ta ki yarda ta kallesa tana
kallon Safeenah dake rawa ta fara mata likin a hankali, kallon cikin ido
Safeenah ke mata haka kawai Imaan taji gabanta na faduwa bata sake yarda sun
hada ido ba tana ci gaba da yi mata likin kudin, Bandir din dubu daddaya
Mujaheed ya ciro ya nufi gun kanninsa da suka dage sai cashewa suke barin
Maimoon, Ya fara manna masu da daddaya da daddaya, Safeenah ta bi sa da wani
harara ganin kanninsa kawai yake lika ma, Imaan na lura da abinda tayi haka
yasa taki lika mata kudin hannunta gaba daya ta koma gun su Maimoon ta fara
masu likin, Mama Hadiza ta xo ita ma tana ma su Maimoon da Imaan likin kamar su
kadai ne a wajen tana murmushi, facing din Imaan Mujaheed yyi yana kallonta ya
fara xuba mata one thousand naira note din a hankali, kasa kallonsa ta yi kanta
a kasa, can kuma a hankali ta fara lika masa na hannunta, Mama Hadiza ta juyo
ta dinga xuba masu na hannunta ita ma, Aunty ma haka, da abokansa gaba daya da
suka cika wajen lkci daya, Safeenah ta ji kmr ta nutse don ba kowa wajenta sae
flowing gown din jikinta, duk aka koma ana ma Mujaheed da Imaan liki, Umma sai
xare ido take tana kallon ikon Allah, kowa ya xo sai ya fara ma Imaan da
Mujaheed liki kamar ita ce amaryar, don wasu ko noticing Safeenar ma basu yi ba
balle su san ba ita suke ma likin ba, Imaan dai ta dawo amarya a wajen duk
kunya ya isheta.... Sai da Mujaheed ya manna ma Imaan gaba daya note din
hannunsa yana kallonta, ita dai sai kokarin barin wajen take amma saboda yanda
aka kewayesu ta rasa hanyar fita, da kyar dai ta samu ta lallaba ta fita taron
xuciyarta na bugawa, tana kallon inda Maryam ke xaune taga har ta fita, da
sauri ta nufi door din fita hall din ta fice fittt, Maryam na ganinta ta dallo
mata fitilar motar ya Yusuf, xata tafi gun motar taji an fixgota, ihu tayi a
tsorace ta juya xuciyarta na bugawa.....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
Afuwan for the late and short update, am not feeling too
well... Thanks in anticipation for understanding.
47....
47. Imaan
Imaan kamar xata yi kuka tace "Ya Yusuf dubi fa yanda ka
ban tsoro...." Yusuf yace "Ehh gwara ki ji tsoron, ina xa ku
je?" Turo baki tayi tace "Gida mana, mun gaji" yana kallonta da
kyau yace "Karya kike yi, ban kuma san lkcn da kika fara karya ba, and I
need not to remind you the consequence of lying Imaan" shiru Imaan tayi
tana kallonsa, ya d'an hade rai yace "birthday din makaryacin saurayin ki
xa ku tafi koh, ke kin san waye Sadeeq kuwa? Kin san irin mutanen da yake abota
da? Kinsan abubuwan da xa su faru gun birthday din nan da kika kwallafa rai sai
kin je, why all of a sudden kika canxa from the decent Imaan da muka sani kika
dawo mara ji?" Fuska daure yayi mata tambayar, kamar xata yi kuka tace
"Ni fa ba birthday nace xan je ba, ai ba yau bane birthday din, kuma I
only want to get him a gift now coz I know I might not get it tomorrow, ban ce
lallai sai na je birthday ba" Kallonta ya dinga yi ta sunkuyar da kai a
sanyaye, wayarsa da yyi vibrate ya kalla yyi replying text din da ya shigo
sannan ya tafi gun motarsa ta bi sa da kallo, Maryam ta langwabar da kai tana
kallonsa, yace "Ke ce ke xugata koh Maryam?" Xaro ido tayi tace
"I don't get you" yace "Idan ke baxa ki gaya mata gaskiya ba why
encourage her??" Maryam tace "Is there anything wrong with her
getting her bf a birthday gift, we are in a civilized world Yaya
Yousuf...." Yana mata wani kallo yace "Bani makulli na" Mika
masa makullin sa tayi ta fito daga motar, Imaan dai sai kallonsu take ta gefen
ido, ya juya ya koma inda take yace "Koma ciki..." A hankali tace
"Toh ni gida xan tafi..." Ya daure fuska yace "Koma ciki
nace" turo baki tayi ta juya ta koma cikin hall din, Maryam ta wucesa rai
bace ta koma cikin hall din ita ma, Imaan na shiga ta tafi inda suke xaune tana
kallon Mujaheed dake kallonta ta xauna, Maryam ma ta xauna a fusace tace
"Gaskiya guys din nan sun fiye takura mutane, haka suke da sa ido dama, I won't
tolerate this shit assuming we are staying together with them" Imaan ta
tabe baki tace "I don't even know what's their business with me, sun
dameni wllh" Maryam tace "Kece kike nuna kina tsoronsu ai" Imaan
kamar xata yi kuka tace "Toh ni yanxu ya xanyi plss?" Shiru Maryam
tayi tana kokarin nema masu wani option din, Yusuf dai na xaune d'an nesa da su
yana kallonsu lkci lkci, ana fara cin abinci Maryam ta mike ta tafi ta debo
masu yar fried rice ta cika nama ta dawo tana kallon Imaan tace "Let
eat" Imaan ta girgixa kai tace "Am not eating" Har aka tashi
dinner din Imaan bata da walwala, gashi da ta kalli Mujaheed sai ta ga kallonta
yake, Tasowa Yusuf yyi ya taho inda suke ya ajiye ma Maryam makulli yace
"You two should wait for me..." Daga haka ya wuce, Maryam tayi tagumi
murya can kasa tace "Amma gaskiya wa ennan mutanen mayu ne, may be they
know what we are up to" Ita dai Imaan bata ce komai ba idonta na kan
Safeenah dake tahowa tare da Mujaheed kawayenta na biye da su a baya, hada ido
suka yi da ita Safeenah ta wani daure fuska, Imaan ta dauke kai hade da tabe
baki, sai da taga sun fita hall din sannan ta mike Maryam ma ta mike tace
"Kinga hararan da yarinyar ke maki kuwa, did you know her b4?" Imaan
tace "I don't know her fa" fita waje suka yi xuwa gun motar ya Yusuf,
Aunty na kallon Yusuf a haraba hall din tace "Ka ajiye Mama Hadiza da su
Hajiya Lailah a gida Yusuf..." Yusuf ya d'an bude ido amma bai ce komai
ba, da sauri Imaan ta dauke kai tana wani murmushi, xagawa yyi ya budu front
seat yana kallonta yace "Xo ki shiga nan" ta d'an xaro ido tace
"Ya Yusuf Maryam fa?" Yace "Xata shiga wani motar, bana son musu
ki xo ki shiga" Maryam ta hararesa ta dauke kai, A hankali Imaan ta taka
ta isa front seat din ta shiga, Mama Hadiza da kawayen Aunty biyu suka shiga
back seat, ya shiga motar ya bar haraban hall din. Yana parking a compound
Imaan bata ko kallesa ba ta bude motar ta fice xata wuce apartment dinsu ta ji
muryar Inna bakin gate tana cewa "Iliya Ahmadun bai dawo ba har
yanxu??" Mai gadi da ya bar gate bude ganin motoci har uku dake bin bayan
motar Yusuf yace "Ehh bai dawo ba Baaba" Inna na hango Yusuf da ya
fito daga mota da Mama Hadiza da kawayen Aunty ta fashe da matsanancin kuka, da
sauri Mama Hadiza ta nufeta tace "Me ya faru Inna" cikin kuka tace
"Me na ma Rukayya a duniyar nan xata saka min da haka, ni fa na yarje ma
Ahmadu aurenta tun tana yar jagaliya, yar yagalgal tana yawo da kodadden zani
da yagaggen Hijabi" Mama Hadiza tace "me ya faru" Inna ta sharen
hawayenta bata tanka ta ba tana kallon ta rasulu tace "Mu je kawai"
ta rasulu tace "Idan ma kika yarda Rukayya ta kwana gidan nan yau Allah ma
sai yayi fushi da mu da bamu dau mataki ba, irin wannan cin mutunci da raini
haka? Oh oh tun da uwata Mai salati ta haifeni ban taba gani ko jin labarin
irinsa ba, waiii.... Ai wannan babban magana ce wllh, ko kotu aka kai kara ba
karamin muhimmanci xa su ba maganar nan ba, kuma da kyar idan ba sai an yanke
mata hukuncin kare rayuwarta a gidan yari ba" Inna tace "Toh kun ji
dai, ke dai mu je kawai wanda ya ajiyeta a gidan xai dawo duk gidan uban da
yaje ya same mu, casun kuma da bamu samu ganin yanda xa a kare ba Allah ya isa
xa mu hadu gaban ubangiji...." Ta rasulu na biye da ita tace "Ke ma
dai wllh, sai ma kin fada?? Ae wannan a rubuce yake Asabe, abinda ba yafewa xa
mu yi ba" Mama Hadiza da su Hajiya Lailah dai suka bi su da kallo. Imaan
na kokarin saka kayan baccinta bayan ta fito wanka aka bude kofar dakinta,
Maryam ce ta shigo ta tsaya tana kallonta tana murmushi, da mamaki Imaan tace
"Ina kika je tun daxu kowa ya dawo banda ke??" Maryam tace
"Close ur eyes please" Imaan tayi shiru tana kallonta, Maryam ta hade
rai tace "Toh ko inyi wucewata" Murmushi Imaan tayi don sai sannan ta
lura da hannunta dake boye a bayanta, a hankali Imaan ta lumshe idonta tace
"Toh na rufe" Maryam ta isa kusa da ita ta tsaya tace "Bude ki
ga gift da xa ki ba Sadeeq din ki" da sauri Imaan ta bude idon taga wani
flower mai kyan bala'i da cards Maryam na mika mata tana jujjuya eye balls
dinta, Imaan ta saki baki tace "What's this?" Maryam tace "Gift
din da xa ki ba sa mana" Dariya Imaan tayi tace "You are very funny
wllh, me xai yi da wannan din" Maryam ta xaro ido tace "Me xai yi da
shi fa kika ce?matsalar ku kenan yan Nigeria wllh, ke kinsan Value din abun nan
dake hannuna kuwa, kin san mu a turai wannan ya fiye mana kudi da wasu abubuwan
rayuwa idan aka xo fannin kyautatawa, wllh I am telling you this sai ya fi son
wannan akan kudin da xaki basa ko abinda xa ki siya masa, idan kin basa kudi me
xai yi da shi bayan yana da fiye da wanda xaki basa, sai dai ma ya bada kudin
kyauta tun bai shiga gida ba, idan kika ce xaki siya masa abu me xai yi da shi
bayan bai fi karfinsa ba?? Wannan kam kina basa am telling you xa ki ga
reaction dinsa..." Tana murmushi ta kare maganar, Imaan dai sai kallonta
take nan kuwa a xuciyarta tunani take kuma fa gaskiyan Maryam tunda shi ma a
turan ya taso xai so gift din sosai, Maryam ta kai mata flower din hancinta
tace "Smell it" lumshe ido Imaan tayi jin wani cool scent da flower
din yake, ta amsa tana murmushi tace "It smells nice, I love you
Maryam" ajiye flowers din da card tayi gefen gado ta rungume ta. Umma na
dawowa daga hall din dinner tare da kawayenta bayan sun sallami mutane gaba
daya dama bata yarda ta shiga gidan ba, kawayenta su Hajiya Saude ne kadai suka
shiga cikin gidan tunda haka dama suka shirya tun a hanya, Umma ta dau wayarta
ta nemo lambar daddy tayi dialing, ba a dau lkci ba ya daga, tayi kasa da murya
ta gaishesa ya amsa yace "Lafiya dai koh Hajiya Rukayya" Tana yake tace
"Lafiya Baban Imaan, nace kana gida kuwa?" Daddy yace "Ehh na
kusa gidan yanxu, driving nake" Umma tace "Toh Ina ma kofar gida, xan
jira ka iso" yace "Ohk" daga haka ya katse wayar, Daddy na
shigowa layin ya hangota tsaye d'an nesa da gate din gidan, parking yayi kusa
da gidan ya fito yana kallonta yace "Lafiya kuwa?" Tace "Toh
lafiyar kenan dai..." Yace "Mu shiga ciki toh" da sauri tace
"A'a bari dai in maka bayanin a nan" Ya rungume hannunsa yana
kallonta yace "Toh ina ji" Tace "Wllh Baban Imaan daxu ne Inna
taje wajen da ake dinner...." Da mamaki Daddy yace "Yanxu sai da taje
dinner din nan duk abinda muka gaya mata??" Umma ta bude hannu alamar ai
shine, tace "Kuma da aminyar nan tata Baaba ta rasulu, wllh Abban Imaan
sai kaga abinda taje ta dinga yi" Daddy ya girgixa kai yana kallonta, Umma
tace "Wata kawar amarya na tsaye gaban jama'ah tana bada tarihin amarya in
gaya maka sai Inna ta tafi ta sami yarinyar ya amshe microphone ta fara xaginta
wai wani tsinannen tela ta ba kudi ya mata dinki, Kai maganganu dai babu dadin
ji Abban imaan, ai su Mama Hadiza da Hajiya Aisha na wajen ni ba sharri na mata
ba, wllh kunya kamar in nutse, dama imu imu ne abun xai xo da sauki amma fa ga
dangin amarya sun cika wajen kuma Yan babban gida, bayan ta gama da yarinya mai
bada tarihi ta tafi ta kwashe duk abinda aka ajiye ma amarya da ango a gabansu
ta wuce ta bar wajen sirara, haka ta dinga ma mutane fada wai kada a xubda
datti sun xo cin shinkafa da miya da kaza mayunwata kawai, maganganu dai ga su
nan xar kayan kunya xar takaici Abban Imaan, yanxu fisabilillahi hakan ya
dace?" Girgixa kai kawai daddy ya dinga yi yana salati, Umma tace
"Toh ganin abun sai gaba yake sai naje na sameta nace toh fa ga ruwa can
ya cike parlonta ta bar pampon bandaki a bude, shine Inna ta bar wajen ba shiri
da kawarta Baaba ta rasulu, yanxu nayi laifi a nan Abban Imaan?" Daddy
yace "Aa dai dai kenan" Umma tace "Toh nasan yanxu suna can kila
ma ta tara jama'ah ana jirana, kuma ko me xata gaya ma Abbansu Mujaheed wllh
yarda xai yi ya xauna a kai, shi sa ma nace bari in maka bayani tukun"
daddy ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh Allah ya kyauta, kuma hakan da kika
yi shine dai dai, don da ba don haka ba baxa su bar wajen ba, kada ki damu
nasan abinda xan yi, kiyi wucewar ki ciki" Umma ta d'an yi murmushi tace
"Toh ngd Abban Imaan da ka fahimce ni" cikin gidan ya nufa ta bi
bayansa bayan ta sauke boyayyen ajiyar xuciya. Inna ce xaune parlonta kan
tabarma ta daura kafa daya kan daya fuskarta shabe shabe da hawaye tana fyace
majina da hankicin hannunta, ta rasulu dake xaune kan darduma ta girgixa kai
kamar xata saki kuka tace "Ni Ahmadu babu abinda ya fi min ciwo irin yanda
muka dinga yawo muna xaga garin kaduna a adaidaita sahu muna neman wajen casu
bayan mun dawo mun ga karya Rukayya take, daga karshe sai dawowa gida muka yi
bamu gane wajen ba, mai adaidaita na bala'i mu ma muna bala'i, haka muka yi
asaran dari biyun mu don da kyar mai adaidaitan ya amshi dari biyun wai sai
dari shidda xa mu basa, wllh mune har sabon kawo neman wajen casu, babu wajen
casu babu labarinsa" Mujaheed dai na xaune parlon sai kallonsu yake, Yusuf
ma haka, Aunty da Ammi da Mama Hadiza ma duk suna xaune, Abba dai kansa na
sunkuye yana sauraronsu, Cikin kuka Inna tace "Duk a kanmu sanyin daren
yau ya kare muna yawo a daidaita neman wajen casu kaman yan iska, kuma ace inyi
hakuri saboda ba a san ciwo na ba, ni wllh yau duk sai mu tattara mu tafi
Police station, wacece kuma Rukayya da xata min wannan toxarcin, me aka yi aka
yi ta, Rukayyar banxa Rukayyar hofi, ni dai wllh Ahmadu na xuba ido yanxun nan
in ga matakin da xaka dauka kan katuwar nan, bikin ma ni sai in iya cewa a dage
sai an bi min hakkina da na Aminiyata ta rasulu tukun, shkkn haka aka kare
casun yau banda mu, ba mu ci Yar shinkafa da kazar da aka raba ba" sai
kuma ta fashe da matsanancin kuka, Yusuf ya sunkuyar da kai yana murmushi, Ta
rasulu na matsar kwallan da ya cika idonta tace "Ni wllh Asiya bata isa ta
min haka ba, don sai dai in sa Muhammadu ya xabi ko ni ko ita...." Sallama
aka yi bakin kofa, Inna ta amsa cikin rawar murya tace "Bukar yau dai bamu
samu casun bikin Mujaheed ba, Rukayya dai yar iska ce wllh"
*Thanks for the prayers via phone calls and WhatsApp messages
fans, Allah bar xumunci, nagode sosai, am feeling a little better in sha Allah*
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
48.....
Shigowa Daddy yayi parlon yana bin dukansu da kallo, Mujaheed
ya mike ya koma kusa da Yusuf, Daddy ya xauna yana kallon Inna yace
"Lafiya? Me ke faruwa?" Inna ta fyace majina a hankali tace
"Kana ji Bukar? Bayan fitar ku daxu da yamma shine kawai na yanke shawarar
tafiya wajen da ake casun ko minti sha biyar ne in yi in juyo duk da dai kun
hanani, Toh ya xa ace bikin Mujaheed guda baxan je wajen casu ba, wllh Bukar
mun shiga wajen da ake abun kenan mun xauna ko kayan kwalaman ba a fara rabawa
ba sai ga Matar nan Rukayya tana haki wai in maxa in koma gida ance ruwa ya
cika min daki da parlor, shine fa muka taho kamar mahaukata tare da Ta rasulu,
muna shigowa gida in gaya maka sai muka ga bandaki a bushe tass babu ko digon
ruwa balle ambaliyar ruwa, shine dai muka ta fada rai bace tare da Ta Rasulu
nace mu koma wajen mu ji dalilin da ya sa xata gilla mana irin wannan karyar me
tsada ko mu sa'annin uwarta ne, to fa muka dau adaidaita xa mu koma amma neman
duniya mun wa wajen casun nan bamu gane ba haka muka ta walagigi a adaidaita
sahu sanyin daren nan duk ya kare mana daga karshe muka dawo gida, yanxu
fisabilillahi me na ma Rukayya xata min haka?" Daddy ya girgixa kai yace
"Amma ba nace maki kada ki tafi wajen ba daxu da yamma Inna?" Inna
tace "Bukar cewa fa nayi minti goma sha biyar kawai xan yi, ai da ban leka
wajen ba wllh kullatata Mujaheed xai yi shi sa nace bari kawai in je a
tsatstsaye in dawo, kuma meye laifina" Daddy yace "Haba Inna, yanxu
fisabilillahi ki shirya ki shiga cikin yara ki xauna kice kin tafi wajen casu,
me yasa kike mana haka don Allah?" Inna tace "Haba Bukar don dai
minti sha biyar in juyo, wa ma xai san naje wajen banda mai sa ido? a baya fa
muka xauna don ma kada a lura da mu" Daddy yace "Kwata kwata bai
kamata, ban ga amfanin shiga cikin jikokin ki wai kinje casu ba, mu dai idan
mun gaya maki magana baki ji baki amfani da shi, bamu san ko kina da wasu masu
gaya maki bane bayan mu, ni bana jin dadin hakan da kike yi, kullum ayi ta
magana amma baki gyarawa Inna, abinda baki sani ba a nan shine har mu kina
xubar mana da mutunci a idon duniya...." Shiru Inna tayi sai 'yan idanuwa,
a hankali ta Rasulu tace "Wllh Bukar sai da nace mata mu hakura kar mu je
amma Asabe taki saurarata....." Juyawa Inna tayi tana kallonta baki sake, can
ta kalli Daddy tace "Kaga xata gilla min sharri da rai na ko Bukar, to
wllh ta ma riga ni shiryawa har tana cewa xata tafi ta bar ni ina bata mata
lokaci, ni dai a dinga jin tsoron Allah ba ruwana" Ta rasulu tace "Yo
idan ban ji tsoron Allah ba tsoron ki xan ji Asabe? Ke dai ki dinga bin 'ya yan
ki sau da kafa baki da kamarsu, da Muhammadu ne yace min kada in tsallake ko
nan da kofa wllh baxan tsallake ba, kawai ki sa mu shiga cikin jikokinmu mu
xauna kamar wasu gantalallu har ana gilla mana karya don a kora mu...."
Inna tace "Ni dai nace a dinga jin tsoron Allah ba ruwana, biki kuma gashi
nan dai an gama sai kowa ya san na yi..." Ta Rasulu tace "Ina nan sai
na raka Mujaheed gidansa na sa albarka...." Inna ta tabe baki tace
"Toh naji na tafi casu ba da izinin ku ba Bukar, walakanta ni da Rukayya
tayi fa??" Daddy yace "Ae ni na kirata nace ta fada maki haka saboda
hakan kadai ke iya sawa ki dawo gida, don xuwan ki wajen bashi da fa'ida"
Salati Inna ta saki tana kallonsa a hankali tace "Allah ya fi annabi
sani...." Ta Rasulu tace "Toh ai da sauki tunda kai ne ka sa ta, kuma
gaskiya da ba haka aka yi ma Asabe ba bata da ranan baro gun" Inna ta
kalleta ta gefen ido ta rike ha6a tace "Ohh.. Naga abinda ya isheni,
mutane dai basa tsoron Allah, da ranka ma sai an dinga bin ka da sharri"
Mikewa Daddy yayi yace "Mu dai muna neman alfarmar ki dinga daukar maganar
mu kina aiki da shi ba don mu ba don Allah..." Inna tayi kasa da murya
tace "Toh ni dai kayi hakuri kuskure ne na riga nayi, sai dai Allah ya
kyauta na gaba" Bai tanka ta ba ya fita parlon, Inna ta bi sa da kallo,
Mikewa Abba yayi yace "Toh a dai yi hakuri inna" daga haka ya fita
parlon shi ma ta bi sa da kallo, Mujaheed ya mike yace "Tsofe tsofe kice
sai kin je casu..." Bai jira cewarta ba ya fice parlon yana murmushi ta bi
sa da kallo, Yusuf ya mike ya fita parlon shi ma ta bi sa da kallo, Aunty dake
kokarin danne dariyarta ta mike tace "Toh don Allah kuyi hakuri Inna"
Inna ta tabe baki bata dai ce komai ba, Aunty tace "Bari in je Inna, muna
aiki ne" daga haka ta fita, Ammi ma tayi mata sai da safe ta fita, tagumi
inna tayi bayan duk sun fita tace "Lallai Bukar ya xama abun tsoro Ta
Rasulu, ni da ba don a kan idona na haifosa ba ma sai ince canjin sa aka min a
tsinannen asibitin turawan da na haifesa, ke kiji ashe shi yasa katuwar mata ta
kirani ta gilla min karya, duniya ta lalace ni patuu" Ta Rasulu tace
"Ai yanxu darajar sa Rukayya xata ci baxa mu daukaka kara ba, amma wllh
bata ci bulus ba, ki kyale Yar iska Allah ya kai mu wayewan garin gobe
lafiya" Inna tace "Shi kuma Bukar dama kada ya sake tako min nan
tunda haka ya xama, ba ruwana ya je yyi ta kansa" Ta Rasulu tace
"Atoh, ni da ace Salihu ne da na masa barbadin bala'i ynxu...." Mama
Hadiza dai sai kallonsu take daga inda take xaune, Inna tace "A'a ni dai
gwara da na bar figaggen da halinsa ba ruwana ace naje ina cecekuce da shi,
gwara kawai da na masa shiru ya gama bambaminsa ya fita, ae shi Ahmadu baya
haka, dama ni ban so ya shigo ba sai Ahmadu ya gama yanke hukunci, Toh sai
gashi Allah ya jefo mana shi, haka kawai inje inyi magana bafillatanar matar sa
ta ji haushi na ta kullace ni, A'a ba ruwana" Ta Rasulu tace "Dama
shirun ya fi ina xaki tsaya cecekuce da d'an cikin ki?" Inna ta tabe baki
tace "Ni dai ba ruwana, Allah ya shirye sa, amma Bukar gaskiya ba shi da
hali duk cikin 'ya yana"
Washegari tun da imaan ta tashi take jin xaxxabi da ciwon
kafa, har karfe tara bata fito ba don ko Ina a gidan cike yake da jama'ah,
Maryam dai tun da ta kawo mata breakfast dakin bata sake ganinta ba, Ammi ce ta
shigo dakin karfe goma saura ganinta kwance ta karasa kusa da gadon tana
kallonta tace "Lafiya?" Mikewa xaune tayi da kyar tace "Ammi
kamar xanyi xaxxabi kuma kafana ciwo suke min" Ammi ta kai hannu jikinta
ta ji da xafi, Juyawa tayi ta fita ta wuce kitchen ta hado mata wani shayin ta
dawo tace "Kin ma yi wanka?" Kai ta gyada ma Ammi, Ammi ta mika mata
shayin tace "Ki sha shayin sai ki sha drugs din ki" karba Imaan tayi
ta fara Shan shayin Ammi ta dauko drugs dinta inda suke ta ballar mata bayan ta
sha kusan rabin shayin Ammi ta mika mata maganin, Karba tayi ta sha Ammi tace
"Ki tafi can bangaren Inna ki kwanta baki xa su sauka nan xuwa anjima
kadan" Imaan ta xaro ido tace "Ammi bandakina fa?" Ammi tace
"Ku dai ba ku da hali mai kyau abu dai na kwana daya, to sai ki kinkimi
bandakin ki tafi da shi bangaren Inna ki ajiye" Imaan kamar xata yi kuka
tace "Wllh bata ma mutum fa xa su yi, ni dai gwara in kulle in boye
makullin" Ammi tace "Toh ki kulle tunda baki da hankali" Imaan
bata ce komai ba Ammi ta juya ta fita, Mikewa tayi da kyar ta kwashe gaba daya
kayan cosmetics dinta dake gaban madubi ta xuba su drawer, ta cire farin
bedsheet dinta ta dau mai duhu ta shimfida tana turo baki, ta shiga bandaki ta
dauke sabulu da sponge dinta sai brush da toothpaste ta dawo daki ta adana,
hijab ta saka bayan ta dau sabbin kayanta na biki da xata saka a cikin leda ta
fita dakin tana dingishi, babu yanda ta iya haka tayi ta gaida mutane har ta
isa part din Inna, Ta Rasulu ce tsaye bakin kofa tana kallon tsofaffin da ke
xaune cikin parlon tace "Don Allah ba don mu ba idan kun cire takalma a
dinga ajiyewa a gefe guda kar su bata bakin kofar, bikin fa na yan gayu ne,
haba takalma sai kace na masu talla" Imaan ta raba ta gefenta ta shiga
parlon, daga kitchen Inna ya fito rike da cooler da plate ta duka tace
"Toh ni dai basu gama girkin ba ina ji, wannan dai 'yar wainar da aka xubo
min ne da safe sai in manna ma kowa guda biyu, ga miyar taushen mai kyau da
nama...." Kallon Imaan dake gaida mutanen parlon xata wuce daki Inna tayi
da sauri tace "Waye wannan kuma?" Juyowa Imaan tayi ta hade rai tana
kallonta, Inna ta mike tace "Me xaki je ki min a daki??" Imaan ta
marairaice tace "Inna baki suna dakina ne kuma bacci nake son yi"
Inna tace "Naga abinda ya isheni, to Ina ruwanki da bakin Imaan? Gaskiya
ni dai kiyi hakuri ki xo ki wuce na saka ma dakina turaren wuta kuma ma wannan
mutumin...." Ko sauraranta Imaan bata yi ba ta shige dakin da sauri tana
turo baki ta kulle, juyawa tayi, tayi still ganin Mujaheed kwance saman gado...
Ta xaro ido tana kallonsa, A hankali Imaan ta bude kofar xata fita sai kuma ta
juya tana kallonsa, Bude ido yyi yana kallonta shi ma, ta turo baki ta fita da
sauri ta kulle kofar. Inna dake ta xuba waina a plate tana diga miya kamar xa a
ba jarirai ta kalleta tace "Har kin fito knn, toh sai ki koma ki tambayar
min shi ko in xuba masa wainar, tun safe yake nan ni dai ban ga ya ci komai ba,
to rabuwa da ni haukane da xai daga hankali haka? Ni dai ba ruwana" Imaan
xata fita Inna tace "Ji walakanci ina mata magana tana wucewa, baxa ki
shiga ki tambayar min shi bane in je da kai na?" Dawowa tayi tana turo
baki ta shiga dakin, Inna tayi tsaki tace "Babu abinda ta mance a halin
ubanta mara kirki, nan ya wanke ni tass jiya da daddare, ni dai na yafe masa ba
ruwana, ba don naka naka bane ai yanxu da sai dai in kora figaggiyar 'yar nan
tasa ince ta fita, Toh kada laifin ubanta ya shafeta" Imaan na komawa
dakin ta samesa idonsa rufe kamar daxu, ta d'an yi jim, can ta karasa kusa da
gadon tace "Inna tace ta xubo maka wainar shinkafa?" shiru yyi har
sannan bai bude idon ba, tace "Ka ji" nan ma bai ce komai ba, ta d'an
ta6a kafarsa tace "Yaya ka ji?" Nan ma shiru kake ji, tabe baki tayi
ta juya xata wuce ya fixgota ya bude manyan idanuwansa da suka sauya kala yace
"Sai kin min ihu a kai saboda baki da hankali?" Shiru tayi tana
kallonsa, can ta ta6a hannunsa ta durkusa kusa da shi a hankali tace "Baka
da lafiya ne Yaya?" Mikewa xaune yyi ta dinga kallonsa, murya can kasa
yace "Make me a cup of tea" Mikewa tayi ta nufi kofa ya bi ta da ido,
Inna dake duke har sannan tana jiran ta fito tace "Xai ci ko in rabar ma
tsofaffin nan?" Imaan tace "Shayi yace in kawo masa" bata jira
me Inna xata ce ba ta shiga kitchen ta dau cup ta bude flask ta xuba ruwan xafi
a cikin cup din sannan ta dawo tana kallon Inna tace "Ina Kayan
shayin?" Inna tace "Wanda ke da shi ku ka siyo ku ka ajiye min kenan,
toh kar ma ki bata lkcn ki ki koma bangarenku ki xuba masa kayan shayin a ruwan
xafin nawa ya kusa karewa bbu wanda xan ba ma wllh" Wata tsohuwa dake
xaune parlon tace "Haba Hajiya Asabe sai kace ba iyayensu ke siya maki
ba?" Inna ta mike tana kallonta, can tace "Ehh lallai duniya ta
lalace, toh wllh har na mance rabon da iyayensu su siya min kayan tea, sai dai
yaron nan Bulasawa, kuma baya jiran wani ya kare yake kawo min wani, kawai mata
tsohuwa baki san kan komai ba ki tsomo mana baki muna magana, ni dai ba ruwana
a dinga jin tsoron Allah" Tuni imaan ta fice ta wuce part din su tana turo
baki, Bedroom dinta ta fara shiga ta dau wayarta tayi dialing number Sadeeq,
katsewa yyi ya kirata, a hankali tace "Good morning...." Yace
"Morning my dear, hope kin tashi lafiya?" Imaan ta langwabar da kai
tace "Sure, happy birthday once again..." Yana murmushi yace
"Thanks much baby, I was so happy with ur text earlier this morning, naji
dadi sosai baby" murmushi tayi tace "When xaka xo ka amshi gift din
ka?" Yace "Ohh wai baxa ko xo party din ba?" A hankali tace
"I might, I might not, kasan fa yau muna biki a gida.... But all the same
ka dai xo ka fara amsar gift din ka" yace "Ni dai sai kin xo party
din dear" murmushi tayi tace "Na ji" yace "Toh yaushe xan
taho amsar gift din?" Tana juya ido tace "After Juma'at prayer"
Yana murmushin sa mai kyau yace "Toh sai na xo baby" tace "Amma
fa kar ka shigo layinmu, ka tsaya bakin titi xan fito" yace "Alryt
dear xan kira ki idan na iso" tace "Tohm bye" daga haka ya katse
wayar. Kitchen ta wuce don hada ma Mujaheed shayi, Ammi dake bayan kitchen din
da Mama Hadiza suna magana tana kallon Imaan ta window tace "Me kike
nema?" Imaan tace "Inna xan xuba ma kayan shayi nata ya kare"
Ammi bata ce komai ba suka ci gaba da maganan su da Mama Hadiza, imaan ta hada
shayi mai kauri ta rufe cup din ta fita, Ko kallon Inna bata yi ba ta shige
cikin daki Inna na cewa "Ni dai dakina ya xama kamar kasuwa yau duk a tafi
a bar ni da wari..." Ajiye shayin Imaan tayi tana kallonsa tace
"Gashi yaya" ya bude ido ya mike xaune ta dau shayin ta mika masa
tana kallonsa ya karba, makulli ya mika mata yace "Go to my bedroom and
get me my phone" ta xaro ido tace "Ni kuma? A'a sai da in gaya ma
Maimoon ta dauko sai ta bani, ni ba ruwana" Bai ce komai ba ya dinga
sipping shayin a hankali, Mikewa Imaan tayi ta fita, tana fitowa parlon Inna ta
kusa cin karo da Mama Hansai "Inna na ciki kuwa? Ga Ta Rasulu can tana
fada da Hajiya Rukayya" Cewar Hansai kenan tana haki ta shige parlon Inna,
Imaan dai tayi wucewarta, tsakar gida ta tadda ta Rasulu tsaye tana fadi Umma
na fadi, Ta Rasulu na tafe hannu tana jujjuya ido tace "Nan nan aka auro
ki kina raka yayarki Shafa tallan shinkafa da wake a kasuwar tasha, Hijabi duk
a yakune, Zani duk duwaiwai a waje tsabar kodewa shine kin xo kin samu gida kin
xama kamar buhun masara xaki kawo ma mutane raini toh wllh idan ban sa yarana
mata sun nakada maki shegen dukar da xai fidda maki hakora uku ba kice ba Yar
gidan mai salati bace ni, Ni nafi karfin ki wllh ni ba Asabe bace...."
Muryar Inna suka ji tana sakin salati da karfi tace "Rukayya ita aminyar
tawa ta Rasulu kike ma xagi ta uwa ta uba?? Ita ta rasulun kike kokarin dambe
da?? La ila ha illallahu Muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wassalam,
karshen duniya ta kama, ayi maxa a kira min Ahmadu amma banda Bukar...."
Imaan ta girgixa kai tayi wucewarta ciki ta wuce sama, bude kofar dakin
Mujaheed tayi ta shiga ta lumshe ido ta nufi saman gadonsa ta dau wayarsa,
calls kusan ashirin yyi missing, yawanci kuma duk na Safeenah ne sai abokansa
dake ta nemansa tun safe, ta tabe baki ta juya xata fita sai ga kira ya kara
shigowa wayar, kallon screen din tayi ganin Safeenah ne tayi tsaki har ta isa
kofa sai kuma ta daga ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren Safeenah tace
"Haba Mijina, tun asuba Ina ta kira no response are you okay?" imaan
ta tabe baki tace "Toh ba shi bane" Da mamaki Safeenah tace
"Wacece wannan?" Imaan tace "Kanwarsa ce, sai ki jira idan na kai
masa wayar" bata jira cewarta ba ta katse kiran ta fito dakin ta kulle
kofar. Ba karamin taro aka hada a tsakar gida ba Inna na ta ma Umma tijara Ta
Rasulu na taya ta, ba abinda suka mance basu gaya mata ba, mutane sai bada
hakuri suke, Ammi dama ko a gyalenta sai aikinta take, haka ma Mama Hadiza da
ta ki fitowa, Aunty ce dai ta taho tana bada hakuri Inna ta tsigaleta ita ma ba shiri ta bar
wajen, inna na ganin Imaan ta fixgota tana nuna ma jama'ah ita tace "Tana
kamar haka fa Ahmadu ya aurota, amma yanxu ku dubi yanda ta koma kamar alade,
Toh komai ta samu raruma take ta boye... ya ki halal ya ki Haram, duk ta
tsiyace min d'a na... Shine kuma saboda abinci xata yi ma aminiyata rashin
mutunci... Allah ya tsine ma abincin da xa aje a xaxxage a shata, tunda a kansa
xaki xagar min Ta Rasulu, to wllh yau sai Ahmadu ya xaba ko ni ko ke a gidan
nan ba ruwana, dama har yanxu ban huce casun da kika hanani ganin karshensa
ba..." Umma dake ta kai koma ta kinkimo babban cooler din shinkafa da
nama, da wani cooler din tuwo da na miya, da na fried rice da soyayyen kaji, da
na masa duk ta dire masu a gabansu tace "Ni dai na xama kadangaren bakin
tulu, ba kuma wani ya haifa min Mujaheed ba balle a nuna min iko da shi, Ikon
ku ya tsaya iya Bukar da Ahmadu amma banda Mujaheed, abinci kuma ga shi aje ayi
ta ci ayi kashi...." Ammi dake tsaye gefe ta taho har inda Umma take tace
"ke dai a kwakwalwarki hauka ya kare, ita Innar kike fada ma magana haka
saboda shinkafa" dakatar da ita umma tayi ta hanyar daga mata hannu tana
mata matsiyacin kallo tace "Ni ban yi da juya ba, kije can ki ji da sauran
ciwon da kika haifo duniya..." Aunty ta riko Ammi ganin finciko Umma xata
yi, babban Jambox Hajiya Saude ta dauka ta kunna waka ya kauraye tsakar gidan
kawayen Umma suka fito aka fara taka rawa irin na manya ana jujjuyawa, Umma na
ganin haka ita ma ta shige cikin masu rawa ta fara takawa tana tafe hannu, Inna
ta gwalo ido sai kuma ta fashe da matsanancin kuka tace "Ni kika xaga
Rukayya?? Ni din??" Ta Rasulu ta dinga bude kulolin abincin tana ball da
su duk abincin ya tarwatse a kasa, tana huci tace "Don kaza kazan ki dake
da abincin kun ci kaza kazan ku...." Mama Hadiza ta fito daga part din su
Imaan da sauri ta tafi ta dauke jambox din da waka ke tashi ta kashe sannan ta
tarwatse sa a kasa tana kunduma ma Umma xagi tace "Idan kina tunanin uwata
xa ki gaya ma magana yau ki xauna lafiya kin yi karya wllh, dama can ba son
auren nan Mujaheed yake ba, ke ce ke son auren saboda abun duniya, xabin ki ce
yarinyar ba tasa ba, kuma wllh wllh kin ji rantsuwar musulmi koh?? To baxa a
daura auren nan ba, bari Ahmad din ya shigo.... in sha Allahu sai kin ji kunya
yau, sai mun kunyata ki yau...."
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
49.....
Shewa Umma tayi tana dariya tana ma Mama Hadiza wani kallo
tace "Toh Sannu Uban Mujaheed.... Ahmadu, bari ki ji ko ita Mahaifiyar
taku bata kai ta hana auren nan ba balle ke...." Mama Hadiza tace
"Toh mu xuba da ke yau, wllh sai kin san kin yi da Inna, sai kin san kin
taba uwar mu, xaman ki a gidan nan ya kare in sha Allah" Umma na ta rawa
tace "Toh Ahmadu" Kujerun da aka jera a tsakar gida Inna ta dinga
watsi dasu tana ball da su tana cewa "Kowa ya tafi gidan ubansa an fasa
bikin, in dai da raina ni patuu baxa ayi auren nan ba, a kira min
Ahmaduuuu..." Cikin daga murya ta Rasulu ma ke cewa "An fasa biki
kowacce ta tattara ta koma inda ta fitoooo, Aisha ki kukkula masu shinkafar a
leda su wuce, an fasa bikin...." Mama Hadiza da xuciyarta ke tafarfasa ta
shiga kiran Abba da wayarta, yana dagawa tace "Ya Ahmad kana Ina? Ka dawo
gida yanxun nan don Allah...." Abba yace "Lafiya?" Mama Hadiza
tace "Ba lafiya ba, ka taho yanxu don Allah" bata jira cewarsa ba ta
katse wayar, Yusuf da shigowarsa gidan kenan ya nufi Inna da mamaki ganin yanda
take ta watsi da kujeru yace "Lafiya Inna?? me ke faruwa??" Inna ta
fashe da matsanancin kuka tace "Isuhu xagi ta uwa ta uba Rukayya ta mana
ni da ta Rasulu daga nace ta Rasulu taje ta amso mana abincin da xa mu raba ma
bakin da ke parlona kada su tafi su ce an bar su da yunwa a bikin jikana, shkkn
Rukayya ta dinga xagin ta Rasulu har ana rirriketa, da gudu Hansai ta xo ta
sanar min shine na taho da sauri jin ba'asi, Toh wllh ni har xagin da ban san
da shi ba a rayuwar nan sai da Rukayya ta min, har da ce min Ahmadu da Bukar
kadai nake da iko da a duniyar nan, tana xagina tana xagin ta Rasulu, Aisha ta
xo ta mata magana ta hada da ita, Hadiza ma ta xo yi mata magana ta hada da ita,
Uwarka kadai ce munafuka wai ta xo tana ban hakuri maimakon ta taya ni kamar
yanda Aisha tayi, Toh ni dai nace wllh an fasa daurin auren nan... yau dama
naji labarin ita tayi masa xabin shegiyar yarinyar, to jiya a wajen casu ko
gaisheni fa yarinyar bata yi ba sai kallon banxa ta min da lebbenta kamar
gandan saniya" Yusuf ya kamo hannunta a hanki yace "Haba Inna, wannan
ba girman ki bane, kiyi hakuri don Allah, gidan fa da baki don Allah kiyi
hakuri ki bari....." buge masa hannu Inna tayi a fusace tace "Kaji
min mutumin banxa ina ruwana da baki, ba suna kallo ake ci min mutunci ba sun
taho sun tare min? Bakin banxa bakin hofi... To wllh kowa ya kama hanyar
gidansu dama ba ruwana...." Gaba daya su Maimoon da Maryam dai na tsaye
gefe sai kallon ikon Allah suke gida duk ya hautsine, kawayen umma da umma kuma
basu fasa kunna Jambox suna ci gaba da taka rawa ba suna tafi, Ta rasulu ta
tafi iya karfinta ta wangale gate cikin daga murya tana cewa "Ku fito ku
tafi gidajen ku babu xancen biki jama'ahhh" Aunty ce ta dinga tambayar su
Maimoon inda Mujaheed yake don tasan shi daya ke iya jan Inna ta bar tsakar
gidan, Imaan dake tsaye sai hararan umma take, nan ko jira take ta kara gaya ma
Inna magana ta rama mata, tana kallon Aunty tace "Yana can dakin
Inna" Aunty tace "Yi maxa ki tafi ki kirasa kiyi sauri" Juyawa
tayi ta wuce part din Inna tana rike da wayarsa har sannan, babu kowa parlon
Inna duk mutanen ciki sun taho tsakar gida kallo, Ta bude kofar dakin ta shiga,
Xaune ta samesa har sannan bai gama shan tea din hannunsa ba, ta hade rai tace
"Yaya Aunty tace in kira ka...." Ya mata wani kallo yace "Did I
ask you to announce I am here?" Turo baki tayi tace "Toh Inna ce da
Baaba ta Rasulu ke fada a tsakar gida" Ya buda manyan idanuwansa yace
"Fada kuma??" Ta gyada masa kai, yace "Da wa?" tace
"Umma" shiru Mujaheed yyi, can ya girgixa kai ya ajiye cup din
hannunsa ya mike ya fita, bin bayansa imaan tayi, Tun daga nisa Mujaheed ya
tsaya ya dinga kallon crowd da aka tara a tsakar gida, ga sautin waka, ga
muryar Inna, ga muryar ta Rasulu, abinda bbu dadin ji, imaan ta iso inda yake
tsaye tace "Yaya kaje ka ma Inna magana" shi dai bai ce komai ba, can
ya karasa wajen a hankali yana kallon Inna kafin yace komai ta rushe da kuka
tace "Mujaheed wai ni yau Rukayya ta xage tass, Mujaheed ba abinda ta
mance bata gaya min ba...." Yace "Toh mu je ciki a kira maki Abba
yanxu, wayar na can bangaren ki" Bayani ta dinga masa tana kuka, yace
"Nace mu je a kira Abba..." da haka Inna ta bisa tana kuka wiwi tana
jera Allah ya isa ma umma, Ta Rasulu dai na can bakin gate tsaye ta wangale
gate din tana ihun a xo a tafi gida an fasa biki, su Aunty suka dinga hada
kujerun da aka tarwatsa tsakar gidan kowa dai rai ba dadi. Mujaheed ya dinga
kallon Inna Bayan sun shiga parlonta, tayi kukanta mai isarta, Imaan dai na
durkushe parlon ita ma tana kallonta, Inna ta hadiye kukan da take tana kallon
bakin kofa ganin Tsofaffin da suka xo biki ne suka dawo mata tace "Yau
naga abinda ya isheni.... ba an fasa bikin ba ku yi ta kanku ku koma gidajen
'ya yan ku mana bayin Allah...." Wata Yar tsohuwa tace "Ae bai kai ga
haka ba Hajiya Asabe hakuri xa ki yi, tun da an fara abun nan a gama...."
A fusace Inna tace "Toh duk ku koma tsakar gidan ku xauna a can, ni dai ba
ni ke aurar da d'a ba ba ruwana, a rufe min kofa" sallama suka mata suka
wuce ta mike ta kulle kofarta ta dawo tana kallon Mujaheed tace "Ka kira
min Ahmadun?" Shi dai bai ce mata komai ba, a fusace tace "Wai baka
ji na ne Mujaheed??" Yace "Ae sai ki saurara ki gani" tana fyace
majina tace "Dama kada in kuskura in ga Bukar a parlon nan yau ba ruwana,
kada ya xo min Ahmadu kawai nake bukata" Bata rufe baki ba sai ga Abba ya
shigo da sallama tare da Daddy ko wannensu da wani expression yake kallonta,
Inna ta tsuke fuska tace "Ni dai Ahmadu kadai na kira...." Abba ya
xauna har sannan bai daina kallonta ba, Daddy dai bai ce komai ba ya xauna, sai
ga Mama Hadiza ta shigo, Inna tace "A kira min Aisha da Amina ma su xo a
akan idonsu aka yi komai ai" Mama Hadiza ta nemi waje ta xauna babu
walwala tace "Suna xuwa" Aunty ce ta fara shigowa sannan Ammi duk
suka xauna saman tabarma, Ta Rasulu ce ta shigo parlon tana kuka wiwi kamar
yarinya ta wuce daki sai ga ta ta fito da 'yar jakarta tace "Asabe gidan
nan ba gidan xama bane, ni tunda uwata Mai salati ta haifeni ba a ta6a min cin
mutuncin da Rukayya ta min yau ba, Ina dalili ina Dan mafari ni sai yanxu wasu
maganganun ke dawo min suna min ciwooo..." Mikewa Inna tayi ta rushe da
kuka ta rike jakarta gamm tace "Ai babu inda xaki Ta Rasulu muna nan sai
an bi mana hakkinmu....." Rungumeta ta Rasulu tayi nan suka dinga rusa
kuka a tsaye, imaan ta boye fuskarta ta dinga dariya kasa kasa, Mujaheed kam
sunkuyar da kansa yyi, Abba ma dai kansa na kasa, Daddy kuwa sai kallonsu yake,
kuka mai isansu suka yi sannan suka saki juna, Inna ta maida jakar daki ta
fito, Ta Rasulu ta xauna ta daura kafa daya kan daya ta tsuke fuska, Inna ta
xauna tana kallon Abba tace "Toh Ahmadu yau dai sai ka xaba ko ni ko
matarka Rukayya...." Sai a sannan Abba ya dago kai yana kallonta, Inna
tayi mitsi mitsi da ido tace "Kuma aure na samu labarin xabinta ce
yarinyar ba xabin Mujaheed ba don haka daurin aure ya fasu in dai ni na haife
ku" Abba ya girgixa kai ya ma rasa abinda xai ce, daddy ya d'an sauke
ajiyar xuciya gently yace "Amma me ya faru Inna? Meye musabbabin
matsalar?" Wani kallo Inna ta jefa masa ta kankance ido tace "Dama
wannan ya xama maganan ka ta farko kuma ta karshe a parlon nan, don ni ban san
ma wa ya gayyato min kai ba, abinda ya faru kuwa shine yau har uwata dake
kabari sai da Rukayya ta xaga a kan shegiyar shinkafa, har tana neman dunguri
na, ga rawa da ta dinga yi a gabana tana min murgude murgude da kawayenta wai
su fitsararrun yan tasha, daga fa mun je amso ma bakin mu da ta Rasulu
shinkafa, xagi ta uwa ta uba dai yau mun sha sai godiyar Allah..." Girgixa
kai kawai daddy yake yace "Ikon Allah" cikin rawar murya Inna tace
"Toh ni yanxu na xuba ido in ga matsayina a wajen ku in ga matakin da xa
ku dauko, ko kaffara baxan yi ba tun da Ahmadu yake ko kallon banxa bai taba ma
Hadiza Uwar Rukayya ba, toh ni me na mata daga xuwa amsan shinkafan biki xata
tsigaleni..." Sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi tace "Me na
ma Rukayya yau ta min cin mutunci wanda da wuya tabon ya goge a jikina" Ta
Rasulu ta saki kukan ita ma tace "Me kuwa xa ki mata Asabe, ni ba don
albarkacin ki ba nasan da yau sai 'ya yana sun turo motar sojoji an fitar da
Rukayya gidan nan...." Inna ta dakatar da kukan da take da sauri tace
"A'a yanxu ma bai baci ba Ta Rasulu, kira su su turo motar babu abinda ya
sha min kai wacece kuma Rukayya ina ruwana da ita xata ci albarkaci na? Su
kwasheta ba ruwana" Abba dai bai ce komai ba har sannan, can dai ya dau
wayarsa ya shiga kiran layin umma, har ya gama ring ba a dauka ba, ya kalli
Mujaheed da ke ta kallon inna yace "Tafi ka kira min uwar ka
yanxu..." Mujaheed ya sunkuyar da kansa bai dai ce komai ba ya mike ya
nufi kofa a sanyaye ya bude, karo ya kusa ci da umma dake labe tana sauraron
komai, shi dai bai ce mata komai ba, har xai tsaya kawai yayi wucewarsa don bai
ma son ransa ya kara baci, Sallama Umma tayi ta shiga parlon da lullubi kanta a
kasa, Inna na ganinta ta saki salati tana tafe hannu tace "Almunafunfun
kenan ku ke ga, to ai ba da gyale kika min cin mutunci a tsakar gida ba don
haka sai ki cire ki ajiye a gefe a gama magana, kuma ni dai Allah ya isa rawan
da kika dinga yi a gabana kina mokade mokaden maxaunai" Umma ta xauna nan
kusa da kofa bata dai tanka ta ba, tana kallonsu Abba tace "Ga ni
nan" Sai hararanta Mama Hadiza take, Abba na kallonta da kyau yace
"Ita Innar kika xaga yau ko?" Ta Rasulu tace "Ta uwa ta uba
kuwa, har ana rirriketa xata doketa, ni dai guduwa nayi na koma bakin gate,
kawai 'ya yana su ji daga xuwa biki duka ya ritsa da ni" Abba na kallon
Umma yace "Toh yayi kyau, ki tafi gidan ku yau, ko minti goma ban son ki
kara a gidan nan...." Da sauri Inna tace "Aa baxa fa ta tafi da
igiyar ka mai daraja ba tana galantoyi a titi, yanxun nan xaka datse shi ta
tafi gidan nasu tsirara, sai kuma taje can ta dinga xagin uwarta mai ciwon kafa
a kano..." Ta Rasulu tace "Ko ta koma wajen shafa mai shinkafa da
wake a kasuwar tasha" Umma tace "Toh Alhmdllh xan tafi amma sai a
barni in sallami bakina da suka xo biki ko xuwa da yamma" Inna ta mike
tace "Wani biki? Bikin da aka fasa ko kuma wani daban kike nufi?"
Kallonta umma tayi da sauri, Inna ta tabe baki tace "Ae babu xancen wannan
auren, don baxa a ma jikana dole ba, maxa maxa a kira dangin shegun amaryar a
sanar masu suyi hakuri Mujaheed yace ya fasa, in dai da raina wllh an fasa
auren nan, ni ba ruwana" Abba yace "Bai kai ga haka ba Inna..."
Katse da tayi tace "Ya kai har ya xarce Ahmadu" Daddy yace "Haba
Inna, kananun mutane kike son ki maida mu, daurin aure nan da 'yan awanni kice
a fasa???" Inna tace "Ba ruwana idan ma jarirai xan maida ku, daurin
aure dai ni patuu nace bbu shi, idan kuma akwai wanda ya isa ya ja da ni to
Bismillah...." Mama Hadiza sai gyada kai take don hka ya mata mugun dadi,
a hankali Abba yace "Inna to bakin da suka xo daga garurruwa da dama don
bikin fa? Ya xa mu yi da su?" Inna tace "Oho sai a nemi wata a daura
auren da ita amma ba xabin Rukayya ba, babu kuma shegen da ya isa ya sa in
canxa ra'ayi na gaskiya..." Ta Rasulu tana tabe baki tace "In har
kuna son gamawa da Asabe lafiya ku bi abinda tace sau da kafa, jama'ah kuma da
aka tara tunda abun kunya ku ke gudu sai a samo yarinya ko cikin 'yan uwana ne
a daura auren kowa ya hutu" Inna tace "Shi kansa Mujaheed din ba son
auren yake ba wllh wllh, idan kuma karya ne a kirasa a tambayesa a ji ta
bakinsa, haka kawai xa a cutar min jika a masa auren dole abinda aka daina yayi
tun lokacin kakata Furera...." Daddy yace "Toh gwara a kira Mujaheed
din a fara jin ta bakinsa Inna...." Dakatar da shi Inna tayi tace "Ka
karyata ubanka isuhu Bukar.... Kuma a kira Mujaheed din" babu Wanda yace
mata komai a parlon, Umma dai tuni yan hanjinta suka kada ta fara matsar
kwalla, idan aka ce an fasa auren nan da gaske ai an kasheta kenan balle ta san
in sha Allahu sai anyi, cikin tsawa Inna tace "A kira Mujaheed din mana
tun da karya nake" Mama Hadiza ce ta kira layin Mujaheed, yana dagawa tace
"Ka taho parlon Inna yanxu" daga haka ta katse wayar, Inna dai sai
girgixa kafa take, ba a dau lkci ba Mujaheed ya shigo parlon da sallama kansa a
kasa, nan kusa da imaan dake xaune jikin kujera ya duka don babu waje parlon
bai kuma son xama kan kujera, Inna na kallonsa tace "Tsakanin ka da Allah
Mujaheed kana son auren yarinyar nan da Rukayya ke son hada ka da?" Shiru
Mujaheed yyi yana kallonta, can ya saci kallon Umma dake kallonsa tana matsar
kwalla, sunkuyar da kansa yayi, Inna tace "Kun ga munafuki koh??"
Abba ya hade rai yace "Don't waste our time Mr Man" d'an murmushi yyi
yana kallon Inna yace "Toh Inna da bana sonta ai baxan yarda da auren
ba" Sake baki Mama Hadiza tayi tana kallonsa, Umma ta sauke boyayyen
ajiyar xuciya, Inna ta saki salati tace "Jini ba wasa ba ni Asabe, Allah
sarki Ahmadu kana cikin jarabawar ubangiji 'ya ya duk sun kwaso halin
uwa...." Wani kallo Mujaheed ya dinga mata, Inna tace "Toh oho dai,
da ka so yarinya da kar ka so ta duk uwasu daya ubansu daya, aure dai tunda aka
xageni aka ci ma ni da aminiyata mutunci babu xancensa an fasa, sai dai duk
abinda xai faru ya faru Babu kuma wanda ya isa ya canxa min ra'ayi ko waye shi
kuwa, idan baku son a maku kallon kananun mutane kamar yanda ku ka ce sai a samu
wata yarinyar a aura masa amma ba xabin Rukayya ba, xan nuna ma kowa ni
jarababbiya ce yau" daga haka ta mike ta shige daki tana goge guntun
hawayenta, Abba ya jinginar da kansa da kujera yana salati a ransa, Daddy kam
sai girgixa kai yake ya rungume hannayensa, a hankali Imaan ta mike ta fita
parlon Mujaheed ya bi ta da ido haka ma Abba da Daddy.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
50. Imaan
Daddy na kallon ta Rasulu a hankali yace "Yanxu Baaba
don Allah baxa ki bata hakuri a daura auren nan ba saboda mutanen da aka
tara??" Ta Rasulu ta xaro ido ta mike tace "Toh Asabe ga Bukar nan
wai in baki hakuri a daura auren... da yake dama cikin 'ya ya ma akwai mai
gudun bacin ranka akwai kuma wanda bai san ciwon ka ba kwata kwata, toh Bukar
dai bai san ciwon ki ba, don da ya sani sai in da karfinsa ya kare a
shakiyancin da Rukayya ta mana yau" Daga haka ta shige daki murya can kasa
tana cewa "Ba ruwana.... Haka kawai ince Asabe ta hakura ta ji haushi
na..." Mama Hadiza na kallon su Abba on a serious note tace "Wllh
Yaya tun da Inna tace baxa ayi auren nan ba fa baxa ayi ba, nima kuma dama nace
baxa ayi din ba, ba kuma abinda xai sa ayi, sai an nuna ma Rukayya duk fitinar
uwar mu a haka muke sonta kuma babu shegen da ya isa ya taka mana ita ya xauna
lafiya, babu shi a duniya wllh, tun wuri ku kira dangin amaryar ku sanar masu
an fasa don su san nayi, tunda uwata tace baxa ayi ba baxa ayi ba, ni nayi
Imani da Allah da kun ji irin cin mutuncin da tayi ma Inna yau baxa ma ku tsaya
kuna bin maganar a sanyi sanyi ba, kuna shakku a ran ku, me aka yi aka yi
Rukayya xata raina mana uwa mu kasa daukan mataki?? to wllh yau sai ta ga
iyakarta sai dai idan ban haifu ba...." Tana kai wa nan ta mike a fusace
ta fice a parlon, Umma ta tabe baki ta dauke kai, Mikewa Daddy yayi ya fice
daga parlon shi ma, a hankali Mujaheed ya mike ya bi bayansa, Abba ya kalli
umma da kyau yace "Ki bar gidan nan as soon as possible Rukayya bana son
ganin ki..." tace "Toh xan tafi ai dama ba sai ka maimaita ba
yallabai, amma dai kar ka manta yar gidan wacece Mujaheed xai aura, tsaf xa ku
xubar da mutuncin ku da kimar ku a idonsu, da ma duniya gaba daya, barin kai da
kake sanannen Barrister" tana magana tana matsar kwalla, har xata fita sai
kuma ta tafi kofar dakin Inna, Bude kofar tayi ta durkusa tana goge kwallan
idonta tace "Ina neman gafaran ku inna, ku yafe ni ku yi hakuri sharrin
shaidan ne..." Inna ta mike a rikice tace "Auzubillahi, garin yaya
aka bar ta taxo min nan ni Asabe, don Allah ki rufa min asiri ki fita ba don
hali na ba, ki tafi don Allah Rukayya" Mikewa Umma tayi ta fita parlon....
Abba da Daddy ne xaune
parlon Abba duk sun rasa abun yi gashi har sha biyun rana ya kusa, fasa aure
gaskiya is out of the point yanxu, bai kamata bane kwata kwata amma basu san ta
inda xa su billo ma al'amarin ba, Mama Hadiza ce ta shigo parlon da sallama ta
dalilin kiranta da Abba yyi, Ta nemi kujera ta xauna tana kallon yayyin nata,
Murya can kasa Daddy yace "Yanxu Khadija baxa ki taimaka ki ma Inna magana
ta janye wannan batu na fasa aure ba, da dai ace daga wajen mu aka fasa daurin
auren nan gwara hakan ya faru daga bangaren iyayen amaryar.... Ki dubi irin
mutunta gidan nan da ake amma aga irin haka ya billo daga gidan, ga mahaifin
yarinyar dattijon kirki ga kuma irin manyan mutanen da xai gayyato daurin auren
nan, kaninsa kuwa wajen aikinsu daya da Sadeeq kuma suna mutunci....."
Mama Hadiza ta katse sa tace "Toh ko in ja Innar mu tafi gidansu amaryar
tayi abinda xai sa daga wajen su suce sun fasa daurin auren tunda dama kowa
kallo masifaffiya mara hakuri yake mata?" A fusace Abba yace "Ji wata
maganar banxa, kina ma da hankali kuwa Hadiza?" Mama Hadiza ta mike tsam
tace "Ehh kwarai Ina da hankali Yaya, dama naga take taken ku, wato ku
baku ma wani ji haushin abinda aka ma mahaifiyar ku ba saboda fitinarta ko,
infact ba ku ma yarda cewar ita ke da gaskiya ba, to wllh bari ku ji in har
baxa ku bi abinda tace ba toh ku xa ku yi ta ganin ba dai dai ba, ba ruwana,
sannan duk fitinarta xan dauketa daga gidan mu tafi sai ku xauna da matanku ku
ci karanku ba babbaka, ita ma Rukayyar sai ka ce ta dawo masifaffiya ta
tafi" daga haka Mama Hadiza ta fice daga parlon a fusace, Daddy ya girgiza
kai yace "Bata da hankali kwata kwata" Abba ya sauke ajiyar xuciya
yace "Ni fa nasan duk abinda Inna ta fada Rukayya xata iya aikatawa, kuma
ko wani hukunci tace in yanke mata yayi dai dai, amma not to the extent da xata
ce a fasa daurin aure ranan daurin aure, meye laifin iyayen amaryar? Ina ce
Rukayya ce ta mata laifi ba su, gaskiya Inna tana son ta samu cikin wani yanayi
ne, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..." Daddy da yyi shiru yana
sauraren yayan nasa yace "Ko xaka kira Bala da su Jibril su mata magana?"
Abba yace "Sai kace baka santa ba ai ni har yanxu ban ga wanda ya isa ya
sa Inna ta canxa ra'ayin nan ba sai dai wani Ikon Allah" Abba ya jinginar
da kansa jikin kujera yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, where are
we to start from coz gaskiya babu xancen fasa aure, duk hukuncin da tace ayi ma
Rukayya xa ayi amma banda fasa aure don iyayen yarinya basu san hawa ba basu
san sauka ba xa mu kunya ta su a idon duniya" Daddy ya tallabi chin dinsa
thinking of a way out also. Karfe sha biyu Abba da Daddy da su kawu Bala da
Jibril da wani kanin Inna da suke uba daya suka kara komawa bangaren Inna don
su bata hakuri ta janye batun fasa auren Mujaheed da Safeenah, kora irin ta kare Inna ta masu da maficin
hannunta, har kawu Bala na neman faduwa saboda saurin ya fita a parlonta, Inna
ta rakosu har bakin pamponta tana huci tace "Munafukai kawai" Su dai
basu juyo ba, amma daddy gaba daya ransa ya gama baci, Abba dai ne ke murmushin
karfin hali, su Bala da Jibril ba bakin magana sai yan idanuwa, kanin Inna Alhaji
Audu ne ya dinga cewa "Tun da muka fito lafiya Alhmdllh, Asabe ba
kyau" Daddy na isa part dinsa ya shiga ko sallama bai masu ba, Imaan da
Maryam na dinning xaune Imaan na bata labarin abinda ya faru parlon Inna kasa
kasa, Mama Hadiza na daki tare da Ammi, Ammi ta fito jin an bude kofa ganin
daddy ne tana kallonsa ta xauna saman kujera bata dai ce komai ba don Mama
Hadiza fa na kan bakanta na cewa babu xancen daurin aure ranan har ta gama hada
kayanta, Daddy ya jinginar da kansa da kujera yace "Inna na son bata sunan
gidan nan ta kunyata mu a idon duniya ne kawai, ta mance cewa bayan Mujaheed
akwai yan baya da xa su yi aure, ta mance gaba daya akwai Yan baya.... wani
interpretation take son mutane suyi ma gidan nan, auren namiji ma ga abinda ya
faru balle mace?? This is very serious...." Ammi dai ta kasa cewa komai
sbda Mama Hadiza, Imaan ta taso ta dawo parlor don a rayuwarta na duniya bata
son abinda xai 6ata ma Daddynta rai, Durkusawa tayi gefensa a hankali tace
"Daddy ku yi hakuri" Daddy bai iya yace Komai ba.... Can Ya kalli
agogon wrist dinsa yace "Ya Allah, just an hour remaining, Me xa mu ce ma
mutanen nan fisabilillahi??" Ammi dai ba bakin magana, Mikewa Daddy yyi ya
fita parlon, duk suka bi sa da kallo, Ammi ta sauke ajiyar xuciya, imaan ta mike
a sanyaye ta wuce daki. Hijab dinta ta saka ta tafi part din Inna, suna xaune
tare da ta Rasulu sun cika faranti da shinkafa jollof ga kaji kusan goma ana ta
ci, turo baki tayi ta xauna tana kallon Inna a hankali tace "Inna don
Allah ku yi hakuri ku bari ayi auren nan, kuna son a dinga ma su Abba kallon
kananun mutane ne a garin nan?" Inna ta ajiye cinyar kazar dake hannunta
tana kallonta baki bude tace "Shi Uban naki ne ya aiko ki in tafi in
samesa yanxu?" Imaan tace "Ni ba wanda ya aiko ni" Inna na nuna
mata kofa tace "Toh maxa kiyi ta kanki, tunda ba uwar ki aka xaga ba dama
me xai dameki, gantalalliya ki ma je ki ji da lalurorin ki xa ki dinga tsoma
baki a xancen manya kina yar yarinyar ki da ke...." A fusace Imaan ta mike
ta fice a parlon, part dinsu ta koma ta shiga dakinta ta tadda Maryam a dakin,
Maryam tace "Ina kika je?" Imaan ta xauna gefen gado tace "Wajen
Inna mana, naje na mata magana ta xageni" Maryam tace "ke me ya kai
ki, ni fa am happy gwara a fasa auren gaba daya... yarinyar da ta walakanta ni
ranan farkon da muka hadu, I sooo hate her with passion" Imaan tace
"Toh reputation din su Abba da Daddyna fa? Ae shine abun dubawan ba fasa
auren ba" Maryam tace "It's just for sometimes dear, ke kina ga akwai
wanda ya isa ya sa Inna ta canxa ra'ayin ta?" Shiru Imaan tayi, can a
hankali tace "Na san me xan yi, I pray it works" Inna na bakin tap
tana wanke kwanukan da suka ci abinci da ta Rasulu tana yan wakeken su shata na
tale tale ta daga kai jin tafiya, Mikewa tsaye tayi tana washe baki tace
"A'ahhhh sannu da xuwa Bukar, Sannu da xuwa...." Sadeeq dake sanye da
tsadadden Gezna fari kal sai walkiya yake ya iso inda take yana murmushi yace
"Sannu kaka, ke kam baki gajiya da aiki...." Inna ta xaro ido ta rike
ha6a tace "Huuuu in gaji da aiki in mutu cikin wari Bukar, Allah ya
tsareni... maxa shiga ciki gani nan tahowa na ma gama ae" Sadeeq ya cire
takalmansa ya shiga parlon dake ta kamshin turaren wuta ya xauna saman
lallausan rug din, Inna ta shigo tace "Bari in kawo maka abincin bikin da
aka fasa, ai ko yayi dadi har da na fitina, yana nan ta Rasulu ta jido mana har
da nama ba iyaka, ni dai hakorana har ciwo suka fara yi saboda cin kaji, yanxu
ma ta Rasulun ta shiga wanka ne..." Yana murmushin sa mai kyau yace
"Kaka ni a koshe nake wllh kuma lkcn Juma'ah ya kusa sauran yan
mintuna..." Inna tace "Toh yi maxa ka tafi idan an sakko sai ka
dawo" Yana shafa kansa yace "Ehh xan tafi yanxu kaka...." Tace
"Toh ko in dauko maka darduma, jiya na wanke sa tasss nasa Maimoon ta goge
min na feshe sa da turare" yar dariya yyi yace "A'a kaka Ina da
darduma a mota, xauna mu yi magana" Inna ta dawo da sauri ta xauna tace
"Toh gani Bukar, in ji lafiya dai???" Yayi sunkuyar da kai yace
"Na ji abinda ya faru ne daxu...." Bai kai aya ba Inna ta fashe da
kuka tana kunce ha6ar xaninta cikin rawar murya tace "Wllh abinda ya faru
kenan Bukar shine yasa nace baxa a daura auren ba, ba ruwana, yanxu haka an
fasa duk nasa a sallami bakin da suka xo" Sadeeq yyi kasa da murya a
hankali yace "Don Allah kaka kiyi hakuri, kinga su Abba da Daddy baxa su
ji dadin kallon da jama'ah xa su masu ba, gashi ana ganin mutuncin gidan nan,
babba dama shi da hakuri aka san sa, kuma wanda aka cuta shi ake ba hakuri
dama..." da sauri Inna tace "Inaaa Bukar ai tuni an fasa daurin
auren...." Yace "A'a na fa ce kiyi hakuri kaka, kuma ni dai na san ki
da hakuri... Ke babba ce fa Kaka" shiru Inna tayi tana matsar kwalla, can
tace "Wllh ni dai kunyar ka nake ji Bukar" Yana murmushi yace
"Toh don Allah ki janye batun fasa auren" Inna ta d'an yi shiru, can
tace "Toh ai shikenan, sun ma kansu ni dai ba ruwana, kuma na hakura aje a
daura auren" Murmushi sosai Sadeeq yayi yace "Yauwa Kaka Allah ya
kara girma, na ji dadi sosai da kika dau shawarata, Allah ya kara girma"
Inna tace "Toh ai dama meye amfanin babban da bai daukan shawara, hakuri
kuma ai Allahn da ya halicce mu ma hakuri yake da mu balle ni, na hakura wllh,
ga waya sai ka kira min Bukar uban Imaan dama ya fi saka abun a kai uwa kanwar
uwarsa ce amaryar, oho dai kirasa ince masa su je su daura auren hankalin su ya
kwanta" Yana murmushi ya amshi wayar yayi searching sunan da tace anyi
mata Saving lambar daddy da shi ya kira sannan ya mika mata, Daddy na dauka
tace "Toh ni dai ba ruwana Allah ma hakuri yake damu, ku je ku daura auren
ni na hakura Allah ya saka min da alkhairi" bata jira cewar daddy ba ta
katse wayar, Inna ta kalli Sadeeq tace "Ni Rukayyar ma bata taba min irin
haka ba gaskiya, ban dai san shaidanin da ya makale a xuciyarta ba yau, amma
dai gaskiya tatattce ne d'an iska, ya cuceta ba kadan ba yau, nace to ko radion
da suka kunna ya cika gida ne yasa shaidanin ya samu nasarar rudar ta, amma
gaskiya ni bata tanka ni kwata kwata a gidan nan, kuma har xaunawa take idan
xata gaisheni, shi kuma Ahmadu sarkin xuciya har ya yanke hukuncin ta tafi
gida, ni sai ta ban tausayi ma wllh...." Sadeeq dai sai kallonta yake yana
murmushi yace "A dai yi hakuri kaka" tace "Atohh, biyayya iya
biyayya dai suna min ni baxan masu sharri ba...." Daddy ne ya shigo parlon
tare da Abba da kawu Bala, Inna na washe baki tace "Sannun ku da
xuwa" Sadeeq ya gaishe su gaba daya da ladabi, Inna tace "Toh gaskiya
duk babban da yace baxai dinga daukan shawaran yaro ba yayi asara, me yyi min
xafi da xan bari inyi asara, wannan yaro Sadeeq dai ya shigo ya ban baki kuma
wllh na hakura aje a daura auren Allah ya sa albarka, kamar daga sama ya fado
min yanxun nan, wato har labarin ya baxu duniya Kai jama'ah.... Kuma da kun san
ta yanda xa ku bi da ni da xancen bai yi tsayi ba haka ba duk baku da wayo, ni
dai na yafe, aje a daura auren" Abba ya d'an yi murmushi yace "Toh
madallah mun gode Inna, Allah ya kara girma, xa mu je masallaci ynxu lkci ya
kusa" Inna tace "Toh ku tafi Allah maku albarka, Bukari kai ka dawo
in xuba maka abinci don Allah har da kaji xuka xuka" Sadeeq na murmushi ya
mike yace "Toh in sha Allah xan dawo" Bin bayan su Daddy yyi ya fita,
Abba na kallon Sadeeq yace "Maa Sha Allah, I am very happy at ur
contribution Allah ya saka" Sadeeq yyi murmushi bai ce komai ba, a haka
suka fita gidan Abba na kiran wayar Mujaheed, Mujaheed was so shock da ya ji
wai ai Inna ta hakura, kuma wai Sadeeq Bulasawa ne ya bata hakuri, har reaction
dinsa ya ba Abbansa da Daddy mamaki, haka dai suka wuce mosque ana sakkowa
masallaci kuma aka daura auren Mujaheed Ahmad da Safeenah Usman, ko jira Mujaheed
bai yi su gaisa da abokansa da suka taho daga nisa ba ya koma gida, direct part
din Inna ya nufa, Imaan na tahowa daga part din innar rike da warmer xata sha
corner suka kusa cin karo da shi, fixgota yyi wanda hakan yasa ta saki abincin
hannunta a tsorace, yana mata wani mugun kallo da idanuwansa da suka rine cikin
tsawan da ya raxana ta yace "Uban wa ya aikeki ki sa saurayin ki yaje ya
ma Inna magana? Uban wa ya sa ki????"
*Imaan isn't for free*
it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
51....
Kasa cewa komai Imaan tayi tana kallonsa don ba karamin
tsorata tayi ba, cikin tsawa yace "Ba tambayar ki nake ba sai na baki
dirty slap?? Who sent you, waye ya aike ki??" Hawaye ya cika idonta ta
sunkuyar da kanta bata dai ce komai ba, saketa yyi ya jingina da bango
xuciyarsa na bugawa, ta tsallake abincin da ya xube ta wuce da sauri tana goge
idonta ya bi ta da kallo har sannan kirjinsa bai daina bugawa ba, hade kai yyi
da bango yana Kiran Allah a ransa, ya fi minti biyu a haka sannan ya juya da
kyar ya nufi bangarensu yana jin idanuwansa na juya masa. Imaan na kwance daki
da yamma idonta a lumshe duk da ba bacci take ba, wayarta dake kusa da ita ya
fara vibrate, bude ido tayi tana kallon wayar, tun abinda Mujaheed yyi mata
daxu take daki taki fitowa duk nacin da Maryam tayi da ita ta fito, gaba daya
she is moody, a hankali ta dau wayar tayi picking ganin Sadeeq ne ke kiranta,
sallama yayi mata daga daya barin, murya can kasa ta amsa, yace "Are you
okay dear?" Shiru ta d'an yi sai kuma tace "Bana jin dadi" yace
"Subhanallah baki jin dadi kuma, kin yi stressing kan ki da yawa kenan,
what's wrong? I mean me kike ji ke damun ki?" Cikin sanyin bemurya tace
"Ache all over" yace
"Subhanallah, kin sha drugs din ki?" Ta gyada kai kamar yana ganinta
yace "Ohk toh xan kawo maki wani yanxu sai ki sha shi da daddare, you will
feel much better" tace "Toh" yace "Xan kira ki idan na
iso" daga haka yyi mata sallama ta katse wayar ta ajiye ta rufe idonta.
Biyar saura ya sake kiranta yana waje, Hijab ta saka har kasa, xata fito ta
tuna birthday gift dinsa ta koma ta dauko flower din da cards ta saka cikin
hijab ta fito, Few visitors ne a parlon nasu, ta tafi dakin Ammi ganin bata
ciki ta fito, a balcony ta tadda Ammi da Mama Hansai, Ammi na kallonta tace
"Ina xa ki?" Ta sunkuyar da kai tace "Ammi ba dadewa xan yi ba
ana kirana a waje ne" Ammi na kallon hannunta dake cikin Hijab tace
"Meye wannan kike boyewa a hijab?" Murmushi tayi kanta a kasa tace
"Ammi ba komai bane, sako ne fa" Mama Hansai na dariya tace "Yi
wucewar ki kinji" wucewa imaan tayi tana murmushi, Yana tsaye jikin
motarsa idonsa sanye da glass ya sa kananun kaya, sunkuyar da kai tayi ta isa
kusa da shi, da damuwa yace "Ya jikin" tana d'an murmushi tace
"Da sauki" ya dauko wani leda a gaban motar ya mika mata yace "ki
sha tablets daya each each kafin ki kwanta" Bata amsa ba ta fiddo hannunta
dake cikin hijab ta mika masa flower din hannunta cikin sanyin murya tace
"Happy birthday dear" still yyi yana kallon flower din ko kiftawa
babu" lkci daya ya karba yana wara ido so happy yace "Waowww Thanks
soo much baby I love it...." Ita dai murmushi kawai tayi, a hankali tace
"i am happy u love it...." Ko bai fada ba she can see how happy he
is, yana wara manyan idanuwansa yace "But baby how did you know I love
flowers plss?" Ta langwabar da kai tace "I only guess" lumshe
ido yyi murya can kasa yace "I feel like hugging you sweetheart" d'an
murmushi kawai tayi ta dauke kai tace "Ni xan koma ciki, and I am sorry I
won't be able to attend ur party saboda bana jin dadi" a sanyaye ta kare
maganar, cike da damuwa yace "Ai na maki uxuri dear, Allah baki lafiya
thanks a lot, I will give you a call later" a hankali tace "Ameen
ngd" daga haka ta juya ta koma cikin gida ya bi ta da kallo still smiling.
Mama Hadiza ce xaune parlon Inna tare da Ta Rasulu, cikin rashin jin dadi Mama
Hadiza tace "Yanxu fisabilillahi kin kyauta min Inna, duk yanda na
takarkare a kan an ci maki mutunci sai ki watsa min kasa a ido??" Inna
tayi kasa da murya tace "Toh Hadiza shikenan ana ta bani hakuri ana hada
ni da Allah sai in botsare kamar shaidaniya? Babba fa dama da hakuri aka san
sa, baki ga yanda aka cika min parlon nan ba daxu ana bani hakuri har da su
Audu d'an tsut, daga karshe sai kuma ga Bulasawa da kansa shi ma ya tako har
parlon nan ya ce inyi hakuri, to idan dai ni ba tsohuwar banxa bace mai kunnen
kashi mara jin magana Hadiza ai ya ci ace na yayyafa ma raina ruwan sanyi in
hakura, kuma ni dai gaskiya Rukayya bata ta6a min irin haka ba, hau ne ya fada
mata...." Ta Rasulu na nuna Inna ta kankance ido tace "Ke dai Asabe
ki dinga jin tsoron Allah, nan kika maida mu mahaukata muna bambami daga karshe
kika watsa mana kasa a ido wai kin hakura, Toh ai ina gida xa ki sa a kirani ki
kawo min karar Rukayya, ba kuma ruwana wllh don baxan saurare ki ba, ke kuma Hadiza
me xai dame ki?? Ai kadan da aikin Asabe kenan baki biyu, ni ban yi mamaki ba,
ni ba dai ruwana ban ce komai ba in yi magana ta kullace ni, amma banda haka me
aka yi aka yi wani shegen Bulasawa da har xai bata hakuri ta hakura? Bayan
abinda tsinanniyar matar nan Rukayya ta mana, Kai Asabe Allah ya baki lafiya,
ya kuma shirye ki, ni dai kin ga tafiyata nan...." Inna ta tsuke fuska
tace "Toh ai ni ba gantalalliya bace da xa ayi ta ba ma hakuri in ki
hakura kamar kafurar Bayan tsauni, ehe... Bulasawa kuma ni ya fi min kowaaa,
yaro mai hankali da natsuwa mai magana irin ta manya, duk sai da ya fada min
maganganu masu dadi da kwantar da xuciya wanda su Amadu suka kasa, toh ni ko me
xance ma yaron Banda Allah ya masa albarka, ai in dai bai auri Imaan ba to sai
dai in ni Asabe bana numfashi, Imaan ta sa ce in sha Allah, Bai fi min wasu
'yan uwan nawa ba ma ni Allah na tuba, Rukayya kuma ai tuni tana akurkin gidan
da ta gina ma iyayenta sai kace ba ni ta ma rashin mutunci ba da xa a bar ta ta
kwana gidan nan...." Ta Rasulu ta mike tace "Ni dai tunda kika kunya
ta ni, kika kunyata Hadiza Allah sai ya saka mana ya bi mana hakkin mu, Rukayya
kuma mu dai je xuwa muna nan dake xata dawo gidan nan...." Inna tace
"Ke ni fa ban hakura da abinda Rukayya ta min balle ta dawo, ai Rukayya
yar iska ce, aure ne dai nace aje a daura kada 'ya yana su ji kunya" Ta
Rasulu tace "Oho dai ni kin ga tafiyata sai ki saka Bukar gaba ya bada
kudin nan na laluran Imaan a san abun yi...." Daga haka ta fice daga
parlon, Inna tace "Toh Allah bar xumunci ta Rasulu, Allah ji kan mai
salati da jikan shehu, Allah ya saka da alkhairi ai ni kin gama min komai a
duniya wllh kin fi min kowa ma, Allah ya bar mu tare sai kuma kin dawo bikin
Imaan da Maimoon in sha Allah, Kai ae xan taho har gida maki ban gajiya, Bari
dai 'yan kauyen nan su koma kauyukansu xa ki gan ni" Mikewa Mama Hadiza
tayi ta fice daga parlon rai ba dadi, Inna ta bi ta da kallon gefen ido tace
"Toh meye kuma axumi uku da xa ki yi, sai kace warce bata axumin Ramadan,
Ni dai ba ruwana dama ban aike ki kiyi ta rantse rantse ba...." A ranan
Mama Hadiza bata kwana gidan ba ta tafi gidan wata yayar Mai gidanta dake nan
garin kadunan. Imaan na parlon Inna bayan isha tare da Maryam suna cin abinci
aka bude kofa, kallon kofar suka yi Mujaheed ya shigo da sallama murya can
kasa, wani daddadan kamshi ya gauraye parlon, yayi wani kyau na daban cikin
milk shaddar jikinsa dake ta talli, Maryam na murmushi tace "Groom dama
har yanxu baka tafi ba?" shi dai bai ce mata komai ba ya xauna, Imaan dai
bata kalli inda yake ba tun bayan da suka hada ido shigowarsa, ta dinga cin
abincinta a hankali, daga cikin dakin Inna tace "Mujaheed ne?" Maryam
tace "Ehh" da sauri Inna ta fito ta marairaice tace "Tun daxu
nake cigiyar ka Mujaheed, nace to ko har ka tafi wajen amaryar ne ba sallama ni
patuu...." Kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Yanxu xan
tafi" Xaunawa Inna tayi ta fashe da kuka a hankali tace "Shikenan
yanxu Mujaheed sai dai ka xo ka gaishe mu ka tafi?? Shikenan ba kai ba kwana cikin
gidan nan yanxu balle ka xo da sassafe ka gaisheni, wa xai dinga shigo min nan
muna hira? Shikenan tafiya xaka yi ka bar ni yanxu, dama ba kowa gare ni ba sai
Allah sai kai, kaine me debe min kewo gashi yanxu kayi aure xaka tafi gidanka
ka barni ni kadai raina..." Mujaheed bai san lkcn da yyi murmushi ba sai
dai bai ce komai ba yana danna wayarsa, Inna na share hawayenta cikin rawar
murya tace "Rayuwa kenan, lallai sabo turken wawa, Allah ubangiji ya ba ku
xaman lafiya da matar, in sha Allah xuwa nan da kwana biyu imaan xata rakoni
don baxan gane gidan ba in xo ganin daki in sa albarka kuma in maku nasiha da
amaryar, Allah ya sanya alkhairi... Ni dai baka taba min komai ba Allah maka
albarka" Mujaheed na murmushi a hankali yace "Ameen" Mikewa yayi
yace "Toh sai da safe" Inna ta kara rushewa da kuka har da rike kai,
Maryam ta kasa ci gaba da danne dariyar da ke cinta, Imaan kam kin dago kanta
tayi tana juya shinkafar gabanta, Cikin kuka sosai Inna tace "Shikenan
kuma, wayyo rayuwa kenan...." Maryam na murmushi tace "Allah ya bada
xaman lafiya Ya M.A, sai mun xo ganin dakin Aunty amarya" Mujaheed ya d'an
yi murmushin karfin hali ya gyada mata kai ya juya ya nufi kofa, Inna na kallon
Imaan da ta sunkuyar da kai tace "Toh ke baxa ki ma yayan naki fatan xaman
lafiya da matarsa ba Imaan" Shi dai Mujaheed bai tsaya ba har ya fita, bin
sa da kallo imaan tayi sai kuma ta mike ta bi bayansa da sauri, Maryam ta xaro
ido tana kallon Inna tace "Wai kuka fa take yi..." Inna ta kara
rushewa da kuka tace "Ka ji ki da wata magana, baxa ta yi kuka ba?? ke
kinsan wahalan da Mujaheed yyi da ita tun tana tsumma, ke kinsan irin fadi
tashin da yayi a kanta tana karama, to ko ubanta bai yi wahalar da Mujaheed yyi
a kanta ba, kullum a makale da shi xa ki ganta duk ta takura bawan Allahn duk
inda xa shi tana hannunsa, tayi ta basa wahala, har goyata ya sha yi, ta xo ta
fara ciwace ciwacen da ba a san kansa ba nan ma babu irin wahalan da bai yi da
ita na ganin ya nema mata lafiya ba, ai shakuwar dake tsakaninsu ko d'a da uwa
sai haka, kuma kice baxata yi kuka ba yau xa su rabu na har abada" tana
kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka ta xamo daga kan kujera tayi xaman
dirshan a kasa, Maryam dai sai dariya take kasa kasa. Imaan na fita parlon Inna
taga har yayi nisa, ta bi bayansa da sauri tace "Yaya" tsayawa yayi
ya juya yana kallonta, Bata san lokacin da ta fashe da kuka ba ta nufesa da
gudu ta rungume sa cikin rawar murya tace "Xan yi missing din ka
Yaya" kasa cewa komai yayi, lkci daya idonsa ya canxa launi, rungume ta
yyi shi ma yyi ya lumshe ido, kuka ta dinga yi a kirjinsa, cike da karfin hali
yace "Ae xa ki dinga xuwa gidana in sha Allah..." Ta gyada masa kai
kawai hawaye na sauka idonta, cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri da
abinda nayi daxu, ban san it's wrong ba I wouldn't have done that, kayi hakuri
plss...." A hankali yace "Na hakura" gently ya janyeta jikinsa
ganin hawaye take har sannan yace "Toh ya isa haka mu je ki rakani gun
mota" Bata iya ta ce komai ba ya kama hannunta suka nufi gate. Tafiya
kawai suke kamar ba su son tafiyar har suka fita gate din gidan, suna isa
motarsa ya juya yana kallonta har idanuwanta sun yi jajir, sunkuyar da kanta
tayi a hankali tace "Sai da safe, I am wishing you a happy married
life...." Yayi murmushin karfin hali yace "Thanks imaan" Juyawa tayi
ta fara tafiya yace "Imaan" ta tsaya sannan ta juyo jin bai ce komai
ba ta dawo inda yake tana kallonsa, yace "Shiga mu je xan siyo ma Inna abu
ki kawo mata ynxu" a hankali tace "Toh" sannan ta xaga ta bude
front seat ta shiga, ya shiga driver seat ya tada motar, the journey was silent
har suka iso gun masu gashin kaji, yayi parking ya kashe motar, ya sauka, ba a
dau lkci sosai ba ya dawo rike da leda uku na kaji da fresh milk, ya bude back
seat ya ajiye leda guda sannan ya bude side dinta ya mika mata leda biyu ta
amsa ya xaga ya shiga driver seat, gida ya koma bayan yyi parking ya juya yana
kallonta yace "Sai da safe" ta sauke idonta kasa tace "Allah ya
kai mu..." Yace "Ameen, ki dau daya sai ki kai ma Inna daya"
D'an murmushi tayi ta bude motar ta fita, ta nufi gate ya bi ta da kallo har ta
shiga sannan yayi reverse ya bar layin. Washegari asabar tun da wayewar gari
Ammi da Aunty, Mama Hansai da matan kawu Bala suka dinga aiki a gidan trying to
make sure everywhere was neat, masu kujeru dama su ma sun xo sun dau kayansu, su
Maimoon, Ummi da Maryam kadai ke taya su aikin, Imaan kuwa na kwance dakinta
wai kai na ciwo, Rahma dama tare da ita Umma ta bar gidan da yammacin jiya....
Bayan azahar Imaan na part din Inna tare da Maryam, Inna na kan darduma tana
bada labarin nan dai na irin yanda aka haifi Mujaheed tana tsaye bakin kofar
asibiti tun safe har dare, wahalan da tayi da shi tun yana tsumma, yanda ya
girma a wajenta da fadan da yasa ta dinga yi da jama'ah a anguwa, har lkcn da
ya tafi kasar waje karatu.... Imaan dai na kwance sai game take a wayarta tana
tabe baki don ita dai har ta haddace labarin nan layi layi, Maryam sai dariya
take ita da ba a ta6a ba ma labarin ba, Inna na matsar kwalla tace "Har
xuwa jiya da aka daura masa aure, Allah sarki Mujaheed dina" Dariya kawai
Maryam take har da kwanciya, Inna dai sai matsar kwalla take tace "Duk
cikin 'ya yan Ahmadu babu ya shi, gashi duk ya fi su kyau wllh, ga tsafta ga
mutunta na gaba da shi, sam Mujaheed bai san wani abu wai rashin kunya ba, bai
taba mayar min da magana ba, wllh jiya ban yi baccin kirki ba da tunaninsa na
kwana..." Sai kuma ta fashe da kuka sosai, sai a sannan Imaan tayi
murmushi bata dai ce komai ba, cikin rawar murya Inna tace "Da dakunan
bangaren nan nawa sun kai uku sai in ce su dawo nan da matar kawai ni dai in
dinga ganin sa kullum" Maryam dai sai dariya take, Imaan ta mike ta wuce
daki ta dalilin kiranta da ake a waya, Daga kiran tayi ta xauna gefen gado ta
kai kunne hade da yin sallama, ya amsa yace "How are you dear?" Tace
"Alhmdllh" yace "Hope kin ji sauki sosai" tana murmushi
tace "Sure, sosai" yace "Ohk to ki dan fito ki amshi sako"
ta xaro ido tace "Na me?" A hankali yace "C'mon dear" tana
murmushi tace "Toh bari in fito" daga haka ta katse wayar ta fito
parlor tana kallon Maryam tace "Mu je ki rakani" Inna na goge hawayen
idonta tace "Ina??" Imaan ta turo baki tace "Ae yanxu xa mu
dawo" Inna ta marairaice tace "Tou ni dai kar ku dade, mai tayani
xaman gashi yayi aure ya tafi..." Dariya imaan tayi ta fita Maryam ta bi
bayanta, har suka isa gate Maryam tambayarta inda xa su take yi amma ta ki gaya
mata, suna fita gate din Maryam tayi shiru ganin Sadeeq tsaye kusa da motarsa,
murmushi yayi ganinsu, Maryam tace "Hi...." Yace "Hello
Maryam" tana murmushi tace "Happy Belated birthday Sadeeq" yace
"Thanks much... Hope an gama biki lafiya?" Tace "alhmdllh"
yace "Maa Sha Allah, Allah ya basu xaman lafiya" Maryam tace
"Ameen" kallon Imaan da ta jingina da motar ta rungume hannu yayi a
hankali yace "Hello princess..." Ta d'an yi murmushi tace "Ya
gida" yace "Alhmdllh, ya Kaka?" Imaan ta langwabar da kai tace
"tana ciki tana ta missing ya Mujaheed" Yace "Allah sarki, ta
kwantar da hankalinta after a month sai ta koma gidan gaba daya koh" Yar
dariya kawai imaan tayi tace "Gaskiya ne" yyi murmushi ya bude back
seat ya fiddo da wani kwali dake a rufe amma ko bai fadi meye a ciki ba kowa ya
sani, yana kallonta yace "Here..." Ta xaro ido tace "Haba wannan
ai yayi yawa" yace "Ni ma sun min yawa, take plss baby" Imaan
tayi murmushi ta d'an risina ta amsa tace "Toh Allah saka da
alkhairi" hararanta yyi tayi dariya bata ce komai ba, wani box mai kyau ya
fiddo ya mika mata ta make kafada tace "Bana so" hade rai yayi ya
kalli Maryam dake murmushi yace "Kin ganta koh?" Maryam tayi dariya
ta mika masa hannunta tace "Bani in rike mata" Mika ma Maryam box din
yyi, Maryam tace "Allah ya saka da alkhairi" Yana murmushi yace
"And ban mance promise da na maki ba, kin bar min xabi or you want
anything?" Yar dariya Maryam tayi tace "Ehh na bar maka" yace
"Toh shikenan, thank you" Kallon imaan yayi yace "Dear, we will
talk later ki gaida kaka" Imaan tace "Toh xata ji nagode"
Sallama yayi ma Maryam ma suka nufi gate, ya bude maxaunin driver ya shiga ya
tada motar, suna shiga gida Maryam ta kashe ma imaan ido tace "Yau xa mu
ci cake mu yi dam, amma me xa ki ce ma Ammi?" Imaan ta xaro ido tace
"Part din Inna xan kai ai" Maryam tace "That will save u long
explanation" Washegari Sunday tun da sassafe Inna ta gama shiryawa wai xa
su gidan Mujaheed da Imaan, Daddy dake parlor xaune yana kallon news yace
"Toh ai kila ma basu tashi ba da sassafe xa ki je masu Inna" Inna ta
xaro ido tace "Sai kace rubabbu Bukar kace min basu tashi ba, Toh ni dai
gaskiya na shirya kuma yanxu xan tafi ina imaan din?" Daddy yace
"Bata tashi ba" Inna ta xauna saman kujera tayi tagumi tace
"Naga abinda ya isheni.... baccin safe ko baccin asara ni Asabe, karfe
takwas ace mutum mai rai bai tashi yyi wanka ya kintsa ya karya ya gyara
gidansa ba? Kuma tun jiya nace mata ta shirya da safe xa mu tafi tare tunda
wannan yarinya Maryam dangin ubanta sun xo sun tafi da ita jiya da magariba...
Kai ku dai baku da tsari gaskiya... Meye kuma baccin safe??" Shi dai Daddy
bai ce komai ba, Ammi ta fito daga kitchen ta gaida Inna sannan ta tafi dakin
Imaan ta tasheta... Inna na ta xaune parlor
ta tsuke fuska har imaan ta fito bayan kusan minti talatin cikin atamfa riga da
skirt na biki da aka masu bata sa ba, sosai kayan suka amsheta, Inna tace
"Ki dauko mayafi mu tafi idan munje can kya karya gaskiya...." Ammi
da Daddy suka kalleta, can Ammi tace "A'a inna da dai ta karya ai bata da
6ata lkci wajen cin abinci, ta je gidan mutane da sassafe...." A fusace
Inna tace "Ke dai Aisha ki daina haka, ki dinga jin tsoron Allah, Gidan
Mujaheed din ne gidan mutane idan ba walakanci ba, gidan Mujaheed ne fa, ni dai
ku dinga tsoron Allah sai kace wanda xata gidan 6are? Ke dauko hijabinki mu
tafi, shi gidan yayan nata xaki ce ma gidan mutane saboda baki da
mutunci..." Tana fadin haka ta nufi kofa a fusace, Daddy ya tabe baki bai
dai ce komai ba, Imaan ta sa hijab ta dauko takalminta da wayarta tana kallon
parent din nata a hankali tace "Sai mun dawo" Daddy kadai ne yace
"Allah ya kiyaye" Ammi kam bata ce komai ba sai aikin gabanta take.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
52.....
Suna fitowa compound Inna ta kalli Imaan tace "Toh ko
dai in je inyi ma Ahmadu magana ya sa direba ya kai mu?" Imaan dai bata ce
komai ba, Inna tayi tsaki tace "Ayi ta maki magana kina ma mutane shiru
idan ma baccin ne bai isheki ba idan munje gidan Mujaheed din ba sai a baki
daki daya ki kwanta kiyi ta yi ba, ai can ma gida ne" Daga haka ta nufi
part din Abba imaan na biye da ita, Aunty ce parlor tana goge goge da su Maimoon,
Aunty ta xauna ta gaida Inna, su Maimoon ma suka gaisheta, Inna ta amsa tace
"Gidan shiru ba wannan mata Rukayya koh" Ita dai Aunty bata ce komai
ba, Inna tace "Toh Ahmadu nake nema ya kira wannan mutumi me jan mota ya
kai mu gidan Mujaheed, tun asuba na gama shiryawa Imaan ta bata min lkci"
Aunty tace "Toh xauna Inna ki jira driver din an aike sa yanxu" Inna
ta xauna tace "So dai ake in makara kawai, Banda haka ni fa tun Asuba nayi
wanka na" Imaan ta xauna a parlon bayan ta gaida Aunty tana kallon series
din da akeyi, ba a dau lkci ba driver ya dawo, Aunty na kallon Inna dake xuba
gyangyadi tace "Toh ya dawo fa inna..." Inna ta bude ido da sauri ta
mike tace "Toh tashi mu je imaan, shi Ahmadun baya nan ne?" Aunty
tace "Bacci yake" Inna tace "Ni dai ba wajena suka gaji baccin
safe kamar rubabbu ba gaskiya" daga haka ta fita imaan na biye da ita, a
waje suka tadda driver da mota, imaan ta bude ma Inna motar ta shiga tana amsa
gaisuwar driver din sannan imaan ma ta shiga, sai da suka hau saman titi Inna
na kallon Imaan tace "Toh kin gaya masa anguwar ne" Drivern na
murmushi yace "Ae na san gidan kaka" Inna ta washe baki tace
"Ashe har ku kunje kun sa ma gidan albarka ku ma" Shi dai bai ce
komai ba yana murmushi, tafiyar kusan minti ashirin suka yi suka iso gidan
Mujaheed, Inna na kallon driver da yayi parking a waje tace "Kai ya haka
ka danna han a bude maka gate ka shiga mana, gidan jikana ne fa" Horn
driver yyi mai gadi ya fito yana kallonsa, can ya karaso gun motar yace
"Daga ina?" Rike baki Inna tayi da mamaki tana kallonsa tace
"Naga abinda ya isheni, kai gidan jikana ne fa kake tambayar daga ina? Na
shiga uku wai ni yake tambaya daga Ina, ko in sauko in bude get din da kai na
ne" Mai gadin yyi kasa da kai yace "Yi hakuri Baaba" daga haka
ya tafi da sauri ya bude gate din, Inna ta ja tsaki tace "Mutane dai ba
tsoron Allah... wai daga Ina, ke ki ji fa gantalalle amma ba laifinsa bane na
Mujaheed ne da bai sanar masa kakarsa na da rai ba" Ita dai Imaan bata ce
komai ba driver ne ke bata hakuri, yana gama parking imaan ta bude motar ta
fito, Inna na kallon driver din tace "Toh yi wucewar ka yaro, mu da gida
kuma sai bayan isha in sha Allah" Yace "Toh baaba ku dawo
lafiya" Inna ta nufi entrance din shiga gidan tana washe baki, Imaan dai
na biye da ita, Bubbuga kofa Inna ta shiga yi da karfi tana cewa "Salama
alaikum" Imaan tace "Kai inna kiyi a hankali mana..." Matsawa
Inna tayi ta bude baki tana kallonta, Imaan ta turo baki ta danna bell tace
"Kawai kiyi ta bubbuga ma mutane kofa da karfi" Inna xata yi magana
aka bude kofar, Inna ta washe baki tana kallonsa tace "Mujaheed...."
Kallonsu kawai yake yana tsaye bakin kofar sanye da jallabiya, Inna ta rike
haba tace "Ashe da gaske ba ku tashi ba kenan" rabawa tayi ta gefensa
kamar yar yarinya ta shige parlon, Imaan ta juya tana murmushi, can dai ta juyo
a hankali, kallonta taga yana yi, ta sunkuyar da kai tace "Ina kwana
Yaya" Muryar Inna suka ji a parlor tace "Ina amaryar??" Mujaheed
ya juya ya koma parlon, Imaan ta bi bayansa, Xaunawa yyi yana kallon Inna yace
"Ina kwana?" ta washe baki tace "Lafiya lau Mujaheed, tun asuba
da na tashi nayi wanka wllh, Banda imaan da ta bata min lkci da tun gari bai
gama wayewa ba xa ku gan ni" shafa kansa yyi bai dai ce komai ba, Inna na
kallon pillow da aka ajiye kan lallausan sabon rug din parlon tace "Cewa
nayi ina amaryar" Mujaheed yace "Tana sama...." Yana fadin haka
ya tashi ya wuce sama, Inna ta kara kallon pillow dake parlor murya can kasa
tace "Toh waye kuma ya kwana a parlor ni patuu" Imaan tayi murmushi
tace "Toh ke ina ruwan ki" Inna tace "Atohhh, ba ruwana
kuwa" Cire Hijab Inna tayi ta linke tana kallon parlon tana murmushi tace
"Sabon gida ba dai sha'awa ba" Mikewa tayi ta nufi wani kofa ta bude
tana lekan ciki ta karasa ta ajiye hijab din nata a ciki ta fito ta rufe tace
"Dakinsu Hansai ne, shi ma sun xuba lafiyayyun kaya a ciki wllh masu
tsada...." tabe baki tayi ta tafi ta bude kofar kitchen tana lekan ciki ta
xaro ido tace "Waiii.... Ai kitchen din ma ba masaka tsinke da kayan
kitchen na xamani, Ashe dai ba gwalagwalan karya aka dinga yawo da shi ranan
casu ba" Imaan dai ta hade rai sai kallonta take... Mujaheed na haurawa
sama ya bude dakin da Safeenah ke ciki, bacci ya sameta tana yi, ya shiga ya
kulle kofar ya karasa kan gadon ya d'an bugi gadon yana kallonta, sai da ya
buga gadon da karfi for d second time sannan ta bude ido ta mike xaune tana
kallonsa da wani expression, yace "Kin ma yi sllhn kuwa?" D'an tsaki
tayi tace "Haba don Allah sai ka wani buga gado ka tsorata ni kamar xaka
tada kato??" Daga head har toes yake kallonta, ta tabe baki ta kalli agogo
tace "Sllh dai dole inyi ko karfe nawa ne" da mamaki yake kallonta
yace "A gidan ku haka kike kai wa har karfe tara baki yi sllh ba
Safeenah?" A fusace tace "Toh gajiyan bikin fa? Plss Mujaheed that's
not how to treat a new bride you are not romantic, haba don Allah sai kace mun
ta6a rayuwa gida daya...." Wani kallo kawai Mujaheed yake mata, strictly
yace "Look Safeenah I won't tolerate this, gidana ba na kafurai bane, tun
asuba na shigo na tashe ki kiyi sllh shine har yanxu baki yi ba, is this ur
home training?" Yar dariya tayi tana kallonsa daga sama har kasa tace
"Kai ko kunya baka ji ba don Allah??" tana kwaikwayonsa tace
"Wai wani tun asuba na shigo na tashe ki.. ban taba jin labarin ango irin
ka ba sai yau da nake gani a xahiri a gidana, wai ka shigo min da asuba, ain't
you ashame of ur self plss" murguda baki tayi ta sauka daga saman gadon da
yar figigiyar rigar baccinta ta nufi bathroom, ya bi da kallo kafin ta shiga
bayin yace "Ki sameni downstairs yanxu idan kin yi sllhn" daga haka
ya juya ya fice daga dakin, Tv ya tarar Inna na kokarin kunnawa tana cewa
"Toh sai me idan Baki kunna min ba kamar yau na saba hada kayan kallo
kuma... Gidan Mujaheed kuma baxa ki saki jiki kiyi yanda kike so, ban da shi wa
gare ki da xa ki je gidansa ki sake jiki dama, ni dai ba ruwana, ki dinga abu
domin Allah Banda munafurci" Imaan dai sai kallonta take fuska daure, Inna
na ganin Mujaheed ta mike tace "Wai ka ji daga nace ta hada min kayan
kallo shine xata ce min daga xuwa gidan mutane, su waye kuma mutane, Mujaheed
din koko Amaryar da bata fito gaisheni ba har yanxu, ni dai ba ruwana, idan ma
xa ki cire Hijabin nan na jikinki ki linke ki ajiye ki tsayar da ranki waje
daya ki saki jiki kamar kina gidan Bukar to gwara ki cire don da kyar ma ba
kwana xamu yi a nan ba gaskiya, ga dai dakuna na kirga har hudu ranan"
Mujaheed ya karasa ya kunna mata tv din yace "Xata sakko yanxu ta gaishe
ki ai" Inna ta koma kan kujera ta xauna ta tsuke fuska tana kallon Tv,
Xaunawa Mujaheed yayi kan kujera ya kalli Imaan ta gefen ido, Sai turo baki
take, Mujaheed ya kalli Inna yace "Amma kuma sai ki yi irin wannan sammako
Inna" Inna ta kallesa da sauri tace "Ni dai Ahmadu ne yace in taho da
sassafe, bayan jiya ya shigo da daddare mun yi magana" Imaan ta xaro ido
tana kallon Inna, Murmushi Mujaheed yyi yana gyada kai, Jin taku a stairs ya
juya, Safeenah ce ke sakkowa sanye da doguwar riga damamme, Still tayi tana
kallonsu, Inna ta kankance ido tana kallonta da kyau ita ma, Safeenah ta hade
rai ta karasa sakkowa ta shigo cikin parlon, Mujaheed ya kalleta yace
"Meet my grandma and my lil sis Imaan...." Inna na washe baki tace
"Sannu Amarya, da fatan dai an tashi lafiya" dauke kai Safeenah tayi
ta tabe baki murya can ciki tace "Ina kwana" Inna tace "Lafiya
lau, sai dai ko sunanki ban sani ba" Mujaheed yace "Safeenah"
Inna tace "Toh madalla, to safeenah Mujaheed dai gashi nan a gabana aka
haifesa, kuma ni nayi wahala da shi tun yana tsummarsa, ke wahalar da nayi da
shi wllh kare baxai ci ba, Tabb banda nakudarsa me Rukayya tayi???" Hade
rai Mujaheed yyi yana kallonta, Safeenah tace "Toh maa sha Allah, ina d'an
yi abu ne a sama Hajiya...." Xaro ido Inna tayi kafin tace komai Mujaheed
yace "Mind you, Inna is what we call her..." Safeenah ta d'an tabe
baki tace "Toh xan je in yi abinda ke gabana a sama Inna" Inna tace
"Ba xancen kije kiyi abinda ke gaban ki ba Yar nan, ko karyawa fa ba mu yi
ba, Imaan ma ina jin ko wanka bata yi ba don da naje ma bacci na tarar tana
yi...." Imaan na kallon Inna tace "Ni bance maki ban yi wanka ba
inna" wani matsiyacin kallon Safeenah ta jefa mata sannan ta kalli inna
bluntly tace "Ba a kai ga sauke min gara na daga container da ya kawo ba,
ba komai yanxu haka s gidan" Wani kallo Mujaheed ya dinga mata trying hard
to control his temper, inna ta rike ha6a tana kallonsa tace "toh me ku ke
ci a gidan ba a sauke gara ba ni 'ya su?" Safeenah tayi wucewarta sama,
Mikewa Mujaheed yyi ya bi bayanta, yana shiga dakin ya kulle kofar yana nunata
da yatsa cikin tsawa yace "Let me give you this warning Safeenah, idan
baki son na fito maki da the other side of me you've got to respect that woman
to the fullest, she is my grandma kuma albarkacin ta yasa kike gidana, wllh
wllh xan yi taking action din da xai baki mugun mamaki idan baki maida hankalin
ki ba, sannan breakfast ni nace ki tashi ki fita kije ki girka masu yanxun
nan...." A tsawace ya kare maganan yana kallonta, Gaba daya ta gama
tsorata sai kallonsa take tana komawa baya, lkci daya hawaye ya kawo idonta sai
kuma ta fashe da kuka tace "Is this the real you dama Mujaheed?? me yasa
tun farko baka yi encourage dina wajen ganin nayi kokarin hakura da kai ba, you
are always telling me xaka koyi sona I shouldn't worry, dama ka aureni ne to
make life a living hell for me, kasan irin mutanen da na ki amincewa da nace
sai kai?? Kasan mutanen da na watsa ma kasa a ido nace sai kai, dama laifine
son mutum da xuciya daya?? Tun da aka kawo ni gidan nan ka ki ko da xama na
minti ashirin a dakina balle ka kwana, wllh ina sonka Mujaheed, ban aure ka
saboda komai ba sai saboda Ina son kasancewa da kai, ka dai san irin gidan da
na fito balle kace saboda wani abu naka na aure ka" dauke kai Mujaheed yyi
xuciyarsa na bugawa, right from time a rayuwar sa na duniya ya tsani ganin
hawayen mace, a hankali ya karasa inda take ya xauna gefen gadon ya jawota
jikinsa cikin sanyin murya yace "I won't make my home a living hell for
you Safeenah, and sure I will create a soft spot for you soon, but you've got
to respect my family, duk abinda nace bana so kuma plss try to avoid that,
Kinga ke yan uwanki baxa su xo in masu gaisuwar walakancin da kika ma grandma
dita ba...." lamo tayi jikinsa tace "Amma kana ganin wannan yarinyar
fa bata gaisheni ba ma" Shiru ya d'an yi, Sai kuma yace "Mind you
sunanta Imaan, and kar ki damu xan mata magana" tace "Step sis dinka
ce?" Ya girgixa kai a hankali yace "She is my cousin sis" daga
kai tayi tana kallonsa, ya gyada mata kai, tabe baki tayi bata ce komai ba,
yace "Toh for my sake kiyi hakuri ki hada breakfast din even if it's just
Irish and egg, sai ki dafa ruwan shayi" Shiru tayi masa yace "Xa ki
yi?" A hankali tace "Toh" murmushi yyi ya manna mata kiss a
goshinta, ta lumshe ido don ba kadan ba taji dadin hakan, ya mike yace
"Come out soon" daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo, Allah yasan
so ba na wasa ba take ma Mujaheed, Bata taba yi ma d'a namiji irin son da take
masa ba, kuma xata iya yin komai a kansa. Mujaheed na dawowa parlor ya tadda
Imaan kadai tana kallo, tun da ta kallesa sau daya ta dauke kai, ya isa kusa da
ita yace "Me yasa baki gaida Safeenah ba?" Ta turo baki ta ki cewa
komai, ya dafa kujeran da take xaune yana kallonta da kyau yace "Look, duk
kika xo gidan nan ko kika ganta a wani waje dolenki ki gaidata coz she is my
wife... Kin ji abinda nace??" Ta hade rai tace "Toh ai ita ma ba da
respect ta gaida Inna ba da ta sakko, so why will I greet her, why??? beside
she is suppose to tell me... Sannu da xuwa kafin in gaisheta, amma ko kallona
bata yi ba so nima naki gaisheta din ai ba wajenta muka xo ba...."
Kallonta kawai yake ganin yanda take maganar cike da tsiwa tana xare masa ido,
ya dauke kai ya d'an yi murmushi, can dai ya mike ya nufi kitchen jin muryar
Inna kasa kasa ita kadai tana magana, tsaye yyi bakin kofa yana kallonta tana
duke tana fere dankali tana cewa "Idan ba jaraba ba da safen ma ya wani bi
figaggiyar mata kamar xabiya daki bayan kwana da yayi a dakin daren jiya, to
meye xasu shige daki kuma da safe bayan nace masu ban karya ba ga 'yar mutane
na taho da ita, ita ma bata karya ba, dama da ya iyayenta suka yarda ta biyoni,
ni dai ba ruwana..." Dariya sosai ta basa, tana ganinsa tayi shiru tace
"A'a har ka fito Mujaheed" yace "Dankali kike ferewa da kanki
kuma?" Inna tace "Yo baxan fere ba tunda na kwaso yunwar cikina
Mujaheed, ga Imaan ma bata karya ba da kyar Bukar ya yarda ta biyo ni... Abu
dai da raina da lafiya ta, ita wancan matar dake xaune parlor tace ba ruwanta
baxata shiga kitchen din mutane ba, ni ban gane ma wannan abun ba gaskiya"
ya shafa kansa yace "Yanxu Safeenah xata xo ta hada maku kayan karin"
inna ta ajiye wukar tace "Toh amma anya ka ce mata nice na raine ka
kuwa...." Safeenah na sakkowa parlor ta dinga yi ma Imaan wani kallo sak
na tsana tana tafiya, suna hada ido Imaan ta tabe baki ta dauke kai.... Tsayawa
Safeenah tayi tana kallonta xuciyarta na tafarfasa tace "Beware a gidana
kike.... you had better respect ur self ki maida hankalin ki" Kallonta
Imaan tayi da sauri tace "Gidan ki ko gidan yayana? Gidan ku na can kin
baro sa malama don haka baki isa ki min warning a gidan Yaya ba...." Da
sauri Inna ta karasa fitowa kitchen jin muryar imaan, Mujaheed ma ya fito ya
tsaya kallonsu da mamaki, Inna tace "Lafiya?? me ya faru??" Imaan
tace "Wai inna ki ji ce min take in shiga hankalina wai nan gidanta ne,
wllh ba abinda na mata daga sakkowarta ta fara min fada tana min warning"
sake baki Inna tayi tana kallon Safeenah tace "Ba lafiya, ta shiga
hankalinta kuma? Kinsan wacece ita kuwa yar nan, to bari kiji wllh wannan da
kike gani ta fiye ma Mujaheed ke so dubu dari, kaji min mata kamar zabiya dai,
ita da gidan yayanta kice ta shiga hankalinta sabida baki da tsoron Allah?? To
wllh a kan Imaan sai Mujaheed ya kora ki gidanku yanxun nan, gwara ma ki xageni
da ki ta6a min imaan gaskiya, duk da dai kin ma xageni tun daxu kawai dai ni me
hakuri ce na ja bakina nayi shiru, kaji min mokadaddiyar mata dai xata sa min
jika a baki in shiga uku???" Mikewa Imaan tayi kamar xata yi kuka ta nufi
kofa tace "Ni sai kin dawo Inna baxan xauna ba...." Inna ta saki
salati tana tafe hannu tace "Na shiga uku ni patuu, Mujaheed ya auri
jaraba tunda ta ta6a imaan, ke me ya kai ki kinsan wacece kuwa, ita kenan fa
uban ya haifa a duniya, ko kallon banxa ba a mata balle a mata fada... Shi
Mujaheed din bai xaunar da ke ya sanar maki bane??" Bin bayan Imaan
Mujaheed yyi ganin har ta fice parlon.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
53....
Har Imaan ta sauka Balcony ta nufi gate Mujaheed ya rikota da
sauri yace "Kee ina xa ki??" Ta hade rai kamar xata yi kuka tace
"Ni dai gida xan wuce bayan ta gama xagina, Ni wucewa xan yi" Kallon
Eyeballs dinta kawai yake, xata kwace hannunta ya kalli gate, lkci daya ya jawo
ta kusa da shi murya can kasa yace "Toh kiyi hakuri...." ta turo baki
ta ki cewa komai, ya dauke kai yayi murmushi yace "Toh baxa ki hakura
ba..." Bata fuska tayi tace "Xagina fa tayi..." ya xaro manyan idonsa
still smiling ya ja dogon hancinta yace "Ni ban ji inda ta xage ki ba, har
da sharri...." Kwace kanta take son yi xata wuce ya ki saketa yace
"Ai fa nace kiyi hakuri koh?" Kallonsa tayi fuska daure kamar xata yi
kuka tace "Toh baka gaya mata ni wacece bane?" Dariya sosai ta basa,
and he couldn't help it don har sai da yyi dariyan ganin maganan sak yanda inna
ke yi, ya kamo duk hannunta biyu yace "Haba na gaya mata mana lil sis,
amma kiyi hakuri xan sake gaya mata da kyau, yanxu mu koma ciki sai ki hada
maku breakfast din mu rabu da ita...." imaan ta turo baki bata dai ce
komai ba, yana murmushi yace "Idan mun koma sai kice ma Inna kin hakura
don ta daina fada kin ji pls?" A hankali tace "Na ji" Yana
kallonta sosai yace "Good girl" daga haka suka koma parlon yana rike
da hannunta, Inna kadai ce tsaye parlon tana kallon stairs tana cewa "Ka
ji min jarabbiyar mata ta ja Bukar ya kullace ni tunda ni na fito masa da 'ya
har xa a sa ta a baki... to wllh hir dinki ni ba ruwana, to Wai ma ke baki da
tsoron Allah ne?? duk hakurina yau sai da kika kai ni bango, banda haka kin
fito daxu kin gaida ni a tsaye sandandan kamar katon soja, ni dai ban kula ki
ba don babba da hakuri da kauda kai aka san sa, sannan na maki magana bamu
karya ba kince kwantenar karyar da aka maki na gara bai sauka ba, ko ina aka
taba gara a kwantena??? Ni dai duk ban kula ki ba ina ta hakuri shine yanxu
xaki ta6a imaan baki san ba a ta6a min ita ba, to haka xa mu yi dake tun ban
dawo gidan gaba daya ba?? Yau naga abinda ya isheni... Irin xaman da xa mu yi
kenan ni patuuu da wannan figaggiyar yarinyar" Mujaheed ya karasa gun Inna
yace "Haba Inna daga xuwa kuma, Imaan din fa ta ma ce ta hakura..."
Inna ta kalli Imaan da sauri tace "Wai??" Imaan ta gyada kai a
hankali, Inna ta koma ta xauna tana share xufar goshinta tace "Toh Alhmdllh...
Sai ta sakko ta hada mana karin kumallo, gaskiya Mujaheed Ina ga baka yi dacen
mata ba, tun fa ba aje ko Ina ba ta fara nuna hali, ko da yake ai ni me iya
saita mata xama ne, ba haka na saita Rukayya ba ma Allah na tuba" Mujaheed
ya kalli Imaan ya mata alamar da ta tafi kitchen din, ta rungume hannunta tace
"Toh ni kadai?" Kallonta Inna tayi da sauri tace "Ke kadai
me?" Mujaheed ya nufeta yace "Toh mu je" Ba musu ta nufi kitchen
din ya bi bayanta, dukawa tayi gun dankalin da Inna ta fara ferewa, ya dau
wukar ya mika mata yace "Be careful with the knife...." Bata ce komai
ba ta amsa ta fara fere dankalin, ya duka kusa da ita yana kallonta, duk wanda
ta gama ferewa sai ta sa a ruwan da ke kusa da shi, shi dai kallonta kawai
yake, pieces shidda ta gama ferewa tace "Ai dai wannan ya ishemu ni da
Inna..." Ya wara ido yace "Toh ni fa...." Kallonsa tayi da sauri
tace "Har da kai?" A hankali ya gyada mata kai, ta tabe baki ta ci
gaba da ferewa, wani kara tayi ta jefar da wukar sai ga jini a hannunta, ya daga
ta da sauri yace "Subhanallah..." yarfe hannun ta fara yi a rikice
tace "Wayyoo Yaya zafi...." Pampo dake kitchen din ya nufa da ita ya
kunna yana tsaye bayanta ya shiga wanke mata hannun yana kallon cut din that
isn't deep, a hankali yace "Sorry lil sis...." Yana gama wanke mata
ya juyo da ita, hawaye ya gani idonta, lkci daya ya rikice yace "Yana maki
xafi sosai ne??" ta fashe da kuka a hankali tace "Ba kai bane kace in
kara bayan na gama namu da Inna" rungume ta yayi yace "Toh yi hakuri
plss, we should have use the potatoe peeler instead" ya daga kanta yana
share mata hawayenta da fingers dinsa, turo baki tayi tace "Ni dai sai dai
kayi slicing din dankalin baxan yi ba" murmushi yayi yana ci gaba da goge
mata idonta a hankali yace "Toh naji, sai ki kunna gas ki debi mangyada a
pan" daga haka ya saketa ya koma gun dankalin, fry pan da ta gani ta dauko
ta bude jarkan sabon man gyada ta deba a fry pan din sannan ta kunna gas ta
daura, ta daura ruwan shayi ta sa lipton, ba dai kayan kamshi tunda bata san
inda suke ba, tsaye tayi bayansa tana kallonsa har ya gama slicing dankalin ya
mike ya ajiye bowl din a sink, ya juya yana kallonta yace "Toh ya xa
ayi?" Yar dariya tayi tace "Baka sani ba Yaya" ya buda hannu
alamar bai sani ba din, ta karasa inda yake ta wanke dankalin ta tsane duk yana
kallonta, yace "Ke da ba ki girki a gida ma...." Murmushi tayi tace
"Ehh amma ai ina ganin Ammi na yi, kuma dai na iya...." Shi dai bai
ce mata komai ba, suna tsaye kitchen din har dankalin da ta xuba a mai ya soyu
ta kwashe a plate, tana kallonsa tace "Toh ina eggs din?" Ya xaro ido
yyi yace "Are you sure, kar kije ki tada min Asthma..." Ta turo baki
tace "It's just an ordinary egg, sai in sa onion fa, ba yaji ai" Yana
murmushi a hankali yace "Ohk...." Eggs din ya fiddo cikin few minutes
ta fara soyawa bayan ta yi chopping onion a board, duk yana lura da ita to make
sure she is fine din da gaske, can ya karasa kusa da ita ya tsaya bayanta a
hankali yace "You are uncomfortable Imaan" ita dai bata ce komai ba
don da gaske tsarkewa numfashinta yake yi ko don bata yi lowering gas din bane
amma a gida ai tana soya kwai, ya rage gas din sosai ya juyo da ita tana facing
dinsa giving her support with his broad shoulder, a hankali take sauke
numfashin hade da shakar kamshin sa mai dadi, ya dinga juya kwan a frying pan
har ya ga ya soyu sannan ya kashe gas din, gaba daya ya juye a plate din da ta
dauko, ya kashe gas da ta daura ruwan xafi ganin yana tafasa, daga kanta yyi
yana kallonta a hankali yace "Are you okay?" Kai ta gyada masa, yace
"Ki tafi parlor xan kawo breakfast din yanxu" Bata ce komai ba ta
nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, wani plate din ya dauka ya debar ma
Safeenah dankali da kwan ya rufe, sannan ya juye ruwan xafin a flask ya dauka
da cups biyu da spoon ya tafi parlon, Inna na xaune sai shar6an bacci take har
da minshari, ya d'an yi murmushi yana kallon Imaan dake xaune kasan rug ya
ajiye flask din hannunsa yace "Are you sure you are okay?" Ta gyada
masa kai, kitchen ya koma ya dauko plate din dankalin ya ajiye masu ya koma
kitchen din, Tea mai kauri ya hada a cup sannan ya fita da kayan shayin ya
ajiye, plate din dankalin da ya bari a kitchen din da cup din shayi ya tafi ya
dauka ya fito, sama ya nufa imaan ta bi sa da kallo, can ta tabe baki ta dauke
kai, Safeenah na dakinta tana waya da Mahaifiyarta ta sanar mata duk abinda ake
ciki tun shigowar Inna gidan da sassafe, rai bace Hajiyan Marafa tace "Ban
da ma kin nace sai shi Allah na tuba me xa ki yi da d'an wajen Rukayya, Ni fa
da Rukayya kar ta san kar ne shi sa ban so auren ba, ke kuma kika ce ba ki san
xance ba kin samu miji, amma duk wannan mai sauki ne wllh tllh, ni nasan ta
yanda xan billo ma lamarin, ki kwantar da hankalin ki sai kace ba ni na haife
ki ba dai, ai in sha Allahu yanda nake xaune hankali kwance ba damuwar kowa
gidan ubanki haka ke ma xaki xauna gidan Mujaheed Safeenah in sha Allah"
Safeenah na goge idonta tace "Toh Mummy..." Hajiyan Marafa tace
"Kar ki nuna masu komai, har ita yarinyar me maki rashin kunya kar ki
tanka ta, dama tunda Hajiya Rukayya tace min bata san wannan tsohuwar ba a
wajen dinner nasan karya kawai take, amma ba damuwa... Ki kwantar da hankalinki
dota babu mai sa maki ciwon kai in sha Allah a gidan auren ki, xuwa gidan ki ma
sai ya gagare duk danginsa har ita munafukar uwartasa in dai ina numfashi,
sannan kin ce har yau bai kwana dakin ki ba ko???" Daga kai Safeenah tayi
jin an bude kofa da sauri tace "Mummy xa mu yi waya anjima" Bata jira
cewar Mahaifiyar tata ba ta katse wayar, hade rai tayi ta kwanta ta juya baya,
Mujaheed ya ajiye abincin hannunsa ya xauna gefen gadon yace "Plss plss
kiyi hakuri Safeenah, nasan this is not proper at all cause this is just ur 2nd
day a gidana, but plss keep this in mind haka grandma dina take wllh, kowa ya
santa kece dai da baki santa ba, har ni ba barina tayi ba sai dai idan ban yi
abinda xata yi magana ba, Imaan kuma bata da matsala kawai ba ku fahimci juna
bane, she's very nice and sweet to stay with, ko a gida Grandma bata son a ta6a
ta be it me or anybody... Ranan xa a ga the other side of her in har aka ta6a
imaan kinsan takwararta ce, so plss you need not to worry beside just few hours
fa xa su yi su wuce, and I assure you baxan yarda a taka ki ko a raina ki ba
coz you are my wife...." Ita dai Safeenah bata juyo ba balle ta tanka sa....
Yace "Ga breakfast din ki" still taki cewa komai, Juyawa yayi ya koma
downstairs, kallon Imaan da ta wani hade rai ya dinga yi har ya shigo parlon
yace "Baxa ki hada shayin ba...." Kamar jira take tace "Ni ba
yunwa nake ji ba dama ai"
*For the sake of My lovely Naomi Baba Abbasss ga nyt update
after enough read mores daxu da safe, duk da dai ba wani kirki gareta ba oo* 😍
_You are reading imaan
for free and still telling me nonsense and posting in groups ur *Big
Wahala*_🤷🏻♀️
All I know Is that my book Imaan isn't for free. Gbamm!!
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
54....
Shiru Mujaheed yyi yana kallonta, can ya karasa kusa da ita
yace "Saboda me baxa ki ci ba?" Kin cewa komai tayi, yyi murmushi ya
xauna kusa da ita ya jawo cup da flask ya fara hada shayin, yana gamawa ya
ajiye cup din shayin gabanta da plate din dankali, dauke kai tayi xata mike ya
rikota, ta shiga kokarin kwace kanta tana cewa "Nace maka ni ba
yunwa...." muryar Inna suka ji tace "Lafiya?? meye haka??"
Saketa Mujaheed yyi da sauri, Inna na xaro ido tace "Lafiya kake matse yar
mutane Mujaheed?" Ta gefen ido ya kalleta bai dai ce komai ba, Inna ta
kalli Imaan tace "Me kika masa?" Kamar xata yi kuka tace "Inna
nace masa na koshi fa shine wai sai na ci" Inna ta bude ido sosai tace
"A'a toh ke kuma baki da tsoron Allah, kika koshi a Ina? Uban me kika ci?
Bata fa karya ba Mujaheed... Ni dai ba ruwana, ka rabu da ita ka kada min nawa
shayin in sha, ya wuce Allah ya masu hisabi da hanjin cikin nata" Murmushi
kawai Mujaheed yake ya gama hada ma Inna shayin ya ajiye gabanta ya debar mata
dankalin ta sakko kasa tace "Toh burodi fa?" Yace "Bari in fita
in siyo yanxu" Inna tace "Atoh, na taba ganin inda aka sha shayi ba
burodi dama" mikewa yayi ya fita parlon Inna ta bi sa da kallo ta rike
ha6a tace "Ikon Allah, aure mai saita mutum ya gyara sa, dubi fa wani
biyayya na musamman da Mujaheed yake yi yanxu daga ya kwana daki daya da mace,
Ikon Allah ya fi gaban haka.... Mujaheed ne xan aika da ya tafi babu musu??
Lallai kamar Rukayya ta tsine masa, ai baxai ma je bane sai ya gama ja min rai
ya gama min walakanci, ke ma dai Bulasawa yayi yayi ya yunkuro ayi auren nan ko
kya yi hankalin, kinsan fa da ace ke ce kika yi aure da har na gama tarewa can
gidan naki, toh wai yaushe ne wannan kaddararren jarabawan sakandarin ne ni
patuu, wllh su Ahmadu da Bukar dama can basa tsoron Allah tun tasowarsu kamar
dai ba ni na haifesu, Banda haka wani
shegen jarabawa ne ya isa ya hana sunnar manzon Allah S.A.W.... Ni dai ba
ruwana" Imaan dai bata tanka Inna ba sai fiffita shayin da Mujaheed ya
hada mata take ta sha da sauri kafin ya dawo, Inna ta saki baki tana kallonta
da sauri tace "Ya haka xa ki handame dankalin gaba daya Imaan, ba namu
bane mu biyu" sosai ta ba Imaan da ta cika baki da dankali da kwai dariya,
ko sauraranta bata yi ba ta dinga turawa har sai da ta ci kusan rabin plate din
da kwai, Inna dai sai kallonta take baki bude, Imaan ta dau wani cup ta dinga
fiffita shayin har ya huce ta kwankwade da sauri ta ajiye kusa da Inna tana
goge bakinta, Inna ta rufe bakin da ta sake tace "Kunyar Mujaheed din kike
yanxu ko me?" Da sauri Imaan tace "Kunya Kuma??? Ni dai kar ma ki ce
masa na ci komai a nan, don ba abinda na ci" Bata jira cewar Inna ba ta
koma kujera ta xauna tana goge bakinta da kyau, Inna tace "Dama mana, ya
xa ayi ki iya cin rabin plate din dankali kamar jaka ai sai dai ni din..."
Imaan dai bata kulata ba ta mayar da hankalinta kan Tv, Da sallama Mujaheed ya
shigo parlon rike da ledan bread l, ya karaso ciki yana kallon empty cup din
shayin da ya hada kafin ya fita, Imaan ta wani daure fuska tana kallon TV, Inna
tace "Toh ba kya daure fuska ba dama kin handame komai kamar mayunwaciya,
wllh Mujaheed yanda ka san ta shekara bata ci abinci ba, dubi abinda ta bar min
fisabilillahi, ko mage aka bar ma wannan xata koshi balle mutum irina, yarinya
dai sai ci kamar saniya" Imaan sai kallon Inna take kamar xata yi kuka,
Mujaheed dai yayi murmushi ya ajiye bread din hannunsa yace "Toh tunda dai
ba da kudin ki aka siyo kayan abincin ba kuma ba Amadun ki ko Bukar suka siyo
ba me xai dameki? Gidan yayanta ne fa" Bai jira cewarta ba ya wuce sama,
imaan ta dinga kallonta tana murmushi ranta fess, tabe baki Inna tayi ta bude
bread din ta yagi kato a ciki a hankali tace "Toh da ban haifesu ba xa su
haife ku?? da na sani ma in ki haifan nasu in ga ta tsiya, sai in ga ta yanda
xa a same ku gantalallu kawai marasu tarbiya" sakkowa kasa imaan tayi ta
dinga 6a66aka dariya, ita dai Inna bata ko kalleta ba ta tsuke fuska tana cin
bread. Sai da tayi nakk dama ta mike ta kai plate da cup kitchen duk ta wanke
duk abinda aka bata ta kife ruwan ya tsane sannan aka fara goge gogen kitchen
din har wall din kitchen dai sai da ta goge sannan ta fito ta share parlorn
tasss, sannan aka fara goge goge, tana goge sabbin kujerun da d'an kyallen da
take goge goge tace "Babu wanda xai ce datti baxai fito daga parlon nan
ba, kaii aji tsoron datti, datti ba kyau...." Ita dai Imaan kallonta kawai
take, Inna ta gama goge goge ta wuce dakin su Hansai ta kwanta saman gado, nan
ta dinga sharar bacci uwa tana dakinta. Sha daya da kusan rabi Mujaheed ya
sakko parlon sanye da kananun kaya da suka amshe sa sosai, ya dinga kallon
Imaan yana tsaye kusa da stairs, can yace "Ina Innar" ba tare da ta
kallesa ba tace "Nima ban sani ba" juyawa yyi yana kallon Safeenah
dake sakkowa a bayansa kamar mai tausayin stairs din, riga da skirt ne jikinta
na atamfa da suka amsheta matuka, kayan ya haska ta ba kadan ba, she's really
beauty.... fuskarta babu walwala har ta karasa sakkowa, tunda suka hada ido sau
daya Imaan ta dauke kanta ta wani tamke fuska, ita ma Safeenar haka tayi tana
jin wani mugun tsanar imaan har xuciyarta, Mujaheed ya karasa ya bude dakin
dake downstairs yana kallon ciki, ganin Inna na bacci ya rufe ya dawo yana
kallon Safeenah da fuskarta ke dauri tana kallon direction daban yace "She
is sleeping" kamar jira take ta Juya da sauri ta koma sama, kallon Imaan
yyi sai kuma ya bi bayanta, Imaan ta mike a hankali ta tafi dakin da Inna ke
kwance ta bude jakarta ta dau dari biyar da ta gani a ciki ta rufe jakar sannan
ta fito, kofa ta nufa direct ta fita parlon tana murguda baki, Mai gadi ya
tashi ya bude mata gate tayi ficewarta tana ce masa sai anjima yayi mata Allah
ya kiyaye, tana isa babban titi ta samu adaidaita ta shiga ta gaya masa
anguwarsu. Safeenah na shiga bedroom dinta Mujaheed ma ya shigo ya rufe kofar
ya juya yana kallonta yace "Toh girkin fa...." Xaunawa tayi gefen
gado tana cire dankwalin kanta dogon gashin ya sauka kasa, a d'an fusace tace
"Toh wai ba cewa kayi tana bacci ba, and you brought the idea of asking
her first before cooking, plss Mujaheed let me... Sannan gaskiya kada yarinyar
nan ta sake xuwa min gidana daga yau, am sorry to say this wllh I dislike her
with passion, I don't know why amma gaba daya naji na tsaneta with all my
heart" Kallonta Mujaheed ya dinga yi da wani expression, fuska daure yace
"You are looking into my face and telling me u dislike my blood, are you
on ur right senses Safeenah??? meye damuwar ki da ita, to bari ki ji, ba ki isa
ki hana imaan shigowa gidan nan ba tunda ba gidan ki bane.... Kuma ki sakko
yanxu ki girka ma grandmum dita lunch" a mugun fusace tace "It's
better ka fita ka tafi eatry ka samo masu lunch don wllh wlh baxan yi ba, Banda
hauka ma ni na taba jin inda ake tilasta amarya sai ta yi girki on her third
day a gidan miji, to baxan yi ba, ka fita ka siyo masu ko kasa blood din taka
ta girka" tana kai wa nan ta mike a fusace ta tafi can karshen gado ta
xauna, shi dai kallonta kawai yake trying hard to control his temper,
underneath his breathe yace "I will treat ur f**kup soon" daga haka
ya fice daga dakin, ta bi sa da harara murya can kasa tace "Xaka san blood
din ka ce" Mujaheed na sauka downstairs ganin Imaan bata parlor ya tafi
kitchen nan ma bai ganta ba, dakin da inna ke kwance ya shiga nan ma bai ganta
ba, Inna ta d'an bude ido cikin muryar bacci tace "Azahar yayi
Mujaheed?" Yace "Imaan fa?" A firgice ta mike xaune tace "Wacece
kuma Imaan" bai ce komai ba ya fito dakin ya tafi compound nan ma bai ga
alamanta ba, juyowa yayi da mamaki xai dawo parlor ya kusa cin karo da Inna
tana xaro ido tace "Ina take?" Yace "Yanxu na sakko ban ganta
ba" salati Inna ta saki ta fashe da kuka tace "Ai ni na shiga uku
daga fito da yar mutane ta min rakiya ta 6ata, toh Ina ta shiga Mujaheed, ka
rufa min asiri ita kenan Allah ya ba Bukar, har a koma ga Allah Bukar baxai
taba yafe min ba wllh, ka cece rayuwata Mujaheed a nemo ta" Wani kallo
Mujaheed ya dinga yi mata ta bangajesa ta nufi gun mai gadi da gudu tana hawaye
tace "Yaro wata yarinya fara yar doguwa siririya kamar xata karye ta fita
ta get din nan daxu??" Mai gadi yace "Ehh ta fita, har ma mun yi
sallama" Inna ta saki wani dogon salati a rude tana tafe hannu tace
"Amma kai d'an banxa ne sakarai gantalalle, ya xaka bar yarinya ta fita
bayan tare kaga muka shigo, ita kenan fa gun uban a duniya, mutane dai ba
tsoron Allah, ya bar yar mutane ta fita ta shiga gari, yanxu ta ina xan fara
nemo Imaan ni patuu, ya ubangijina ka dubeni....." fashewa tayi da kuka ta
fice daga gate din da gudu ko Hijabi babu, Mujaheed dai ya koma ciki ya dauko
makullin mota ya fito ganin har Inna ta fice ya bude motar yyi warming dinsa
Mai gadi ya bude masa gate ya fita, kafin Inna ta isa titi ta tare mutane sun
fi biyar a hanya tana masu describing din Imaan ko sun ganta, duk aka ce mata
ba a ganta ba sai ta rushe da matsanancin kuka tana cewa "Bukar baxai ta6a
gafarta min ba har duniya ta nade" hakuri aka dinga bata tana tafiya tana
kuka har ta isa titi, Parking Mujaheed yyi ya sauke glass, ya wani daure fuska
yace "Shigo mu wuce" a fusace ta kallesa tace "In wuce gidan
ubanwa ba yarinyar mutane, gidan ka dai ya xama na jaraba daga xuwa Imaan ta
6ata...." A fusace yace "Wai imaan din yarinya ce da xaki tsaya titi
kina nemanta?" Ta xaro ido tace "Yarinya ce a gun ubanta wlh, ita
kadai fa garesa, wllh ba ruwana ka rabu da ni Mujaheed, me xanje ince ma Bukar
da Aisha idan na shiga mota...." Sai kuma ta rushe da kuka mai ta6a xuciya,
ganin mutane an fara taruwa kanta Mujaheed ya ja tsaki yaja motarsa ya bar ta
wajen, gida ya wuce direct, yana parking kofar gida ya shiga ciki, babu kowa
compound din ya tafi part din su Imaan, ya kusa minti daya tsaye a balcony
kafin yyi sallama murya can kasa ya bude kofar ya shiga parlon, imaan ce xaune
parlon da plate din abinci gabanta tana ci tana kallo, suna hada ido ta mike da
sauri har tana tuntube ta nufi dakinta da gudu ta shige ta kulle kofa, Ammi ce
ta leko daga kitchen, yyi kasa da kai yace "Ina yini Ammi" tace
"Lafiya lau, ya gida" yace "Alhmdllh" komawa kitchen tayi
ya xauna saman kujera a parlon, ba a dau lkci ba Ammi ta fito tace "Ya
amarya fa..." ya d'an yi murmushi yace "Tana lafiya" tace
"To maa sha Allah, a xubo maka abinci?" Yace "A'a Alhmdllh"
dauke abincin da imaan ta bari a parlon tayi ta kai dinning ta ajiye ta dauko
wani plate ta rufe, Ammi tace "Ka dawo da Innar ne?" Yace "A'a,
tana dai tahowa" Bai rufe Baki ba sai ga Inna duk ta hada xufa tace
"Ina Bukar yake?" Ammi na kallonta da mamaki tace "Sannu da xuwa
Inna" Inna tace "Ke tambayar ki nake Ina Bukar, ban ga imaan ba
wllh..." Ammi tace "Imaan kuma, ae ta dawo tun daxu" salati Inna
tayi a hankali tana tafe hannu tace "Ta dawo?? Amma wannan 'ya ta Bukar
axxaluma ce wllh, Allah kaga yanda yarinyar nan ta daga min hankali na dinga
tona ma kai na asiri a titi, Allah kaga yanda ta sa na bar jakata da dubu daya
a gidan mutane na fito ba shiri, Allah kaga yanda ta sa cikina ya rude a titi
na dinga neman bayan gida...." Sai kuma ta rushe da kuka ta fita parlon
tana cewa "Bukar dai ya haifi jaraba, don imaan jarababbiya ce, ko da yake
uban nata ma fitinanne ne" Ammi dai banda murmushi ba abinda take, ta
kalli kofar dakin imaan tace "Imaan" sai da ta kirata sau biyu sannan
Imaan ta yi ma Sadeeq sallama a wayan da suke yi, ta fito da hijab har kasa
tana sunkuyar da kai, Ammi tace "Meyasa kika taho baki sanar da Inna
ba?" Kamar xata yi kuka tace "Ammi bacci fa take ta yi, kuma ni na
gaji ina son dawowa gida" Ammi tace "Toh ai kin kyauta" Imaan ta
saci kallon Mujaheed dake ta kallonta, ta juya da sauri ta koma daki ta rufe
kofarta. Some days later aka fara shirye shiryen saukan su Imaan a gidan,
during this period soyayya mai xafi imaan suke yi da Sadeeq amma ta waya, gaba
daya ya ki xuwa ta rasa me yasa sai dai ya kirata, kullum xancensa shi dai ji
yake kamar ya jawo kwanakin duk da bai fi saura wata biyu xa su xana jarabawan
waec ba, ko da xai xo gidan kuwa dama Inna yake xuwa gaidawa kuma ko ita imaan
bata sani sai ya tafi xai kirata yace ai ya xo gidansu, ranan asabar ya kama
saura sati daya saukansu, ranan kuma ya kama sati biyu da bikin Mujaheed,
misalin sha daya da wani abu na safe ya xo gida tare da Safeenah, ubansun lace
ne jikinta sai mayafi da ta sakale a wuya hannunta rike da handbag sai takalmi
mai tsini da ta sa, tayi kyau har ta gaji, sai xuba kamshi take, fuskar nan
nata ya sha make up ba a cewa komai, part dinsu ya nufa tana biye da shi, su
Maimoon da Ummi suka yi welcoming dinta da fara'a, ta amsa masu da siririyar
muryarta tana murmushi, Maimoon ce ta tafi sama ta kira Aunty, Aunty na sakkowa
tace "A'a Aunty amarya ce a gidan namu, Sannu da xuwa" Safeenah ta
kalleta tace "Yauwa..." Aunty ta xauna tace "Fatan an tashi
lafiya" Safeenah tace "Lafiya lau ya gida" Aunty tace
"Alhmdllh, ya naku gidan" Safeenah tace "Lafiya lau" Aunty
tace "Toh madallah..." Mujaheed dai sai kallon Safeenah yake jin bata
gaishe da Aunty ba, Bai dai ce komai ba ya kalli Aunty yace "Abba
fa?" Aunty tace "Tun safe ya fita" Mujaheed ya mike yace
"Ohk bari mu gaida Inna" Aunty tace "Toh shkkn sai kun
dawo" yace "Yusuf ya dawo?" Aunty tace "A'a bai dawo
ba" kofa ya nufa Safeenah ta mike ta bi bayansa Aunty ta bi ta da ido har
suka fita ta girgixa kai ta mike ta je ta ci gaba da abinda take, suna fita
Mujaheed ya kalleta rai bace yace "Abinda kika yi kin kyauta kenan
Safeenah, mum dita ce ita ma fa?" Tsayawa tayi tana kallonsa da mamaki
tace "Me nayi kuma?" Yace "Did you greet her?" A fusace
tace "Kai komai kace fada da bala'i, to ni ban ma sani ba, da muka fito
sai kayi correcting dina ba ka dinga min fada ba haba" Bai tanka ta ba ya
ci gaba da tafiya ta bi bayansa tana tabe baki, part din su Imaan ya shiga tana
biye da shi tace "Nan ne part din innar?" Ya kalleta yace "Part
din uncle dina" Bai jira cewarta ba ya shiga parlon da sallama, d'an tsaki
tayi ta shiga ita ma, Ammi na xaune parlon ta mike ganinsu tana masu sannu da
xuwa da fara'a, Mujaheed ya xauna ya gaisheta ta amsa tace "Sannun ku da
xuwa" Safeenah da kallo daya tayi ma Ammi ta gane ita ce Mahaifiyar Imaan
coz it's soo obvious, ta wani daure fuska tana kallon Tv, Ammi tun da ta
kalleta sau daya taga bata gaisheta ba dama bata sake kallonta ba, ta tafi
kitchen tana cewa "Bari in kawo maku ruwa" wani kallo Mujaheed ya
dinga yi ma Safeenah da ta bude jaka ta fiddo chewing gum ta 6are ta jefa a
baki tana tauna, murya can kasa tace "Did you greet her Safeenah?"
Banxa tayi masa tana taune taunenta, Ammi ta fito ta ajiye ruwan kusa da shi,
Yana kirkiran murmushi yace "Ae daga gida muke ma" Ammi ta xauna tace
"Ae ruwa ne" daukan bottle water daya yayi yace "Daddy fa?"
Ammi tace "Yana Abuja" Mujaheed yace "Toh xa mu je gaida Inna
yanxu" Ammi tace "Toh maa sha Allah, nagode kwarai" mikewa yyi
ya nufi kofa Safeenah ta mike ta bi bayansa Ammi ta bi ta da kallo, sai da suka
sauka balcony ya juya yana kallonta kafin yace komai ta wuce sa da sauri tana
kas kas da cingam fuska daure, gyada kai yyi ya dau hanyar part din inna ta bi
sa a baya tana kyabe baki, Inna na share parlornta ta daga kai tana kallon
Mujaheed tace "Waye wannan" Bai tanka ta ba ya cire takalmi ya shiga
parlon, Safeenah ta cire takalmanta tana kirkiran murmushi tace "Sannu da
aiki Inna, kawo in karasa share maki" Inna tace "A'a bar shi yi
wucewar ki ciki, daga xuwa kuma sai ki hau shara ba ruwana, balle ma na
gama" tace "A'a don Allah ki bari Inna, ki kawo in karasa" ajiye
tsintsiyar Inna tayi ta mike ta amshe jakar hannunta tace "Toh ai nagode
dama bayana kamar xai cire wllh, ita wancan mata tana kwance daki wai ba
lafiya, dadin abun ma an san bata da lafiya kafin ta taho nan balle ace a
parlon Inna, shi sa ban wani gigice ba, Allah dai ya yaye mata wannan bala'i da
ba a san kansa ba....." Mujaheed sai kallon Inna yake sannan ya kalli
kofar dakin bai dai ce komai ba, Safeenah ta gama tattare parlon ta kwashe dattin
da bai taka kara ya karya ba a Parker sannan ta mike tana murmushi tana kallon
Inna tace "A Ina xan xubda dattin?" Inna tace "Can bayan window
xaki tafi kwandon sharan yana nan xaki gansa fess na wanke wllh sai a iya xuba
tuwa a ciki a ci, sai ki xuba a hankali kar ya bata jikin kwandon har hypo na
sa yayin wankewa" Safeenah ta fita parlon ta sa takalminta mai tsini ta
wuce bayan window, Mujaheed na kallon Inna da sauri yace "Me ya
sameta?" Inna na kakkabe kujera tace "Wai Imaan, toh ga ta nan dai ya
dama da xaxxabi ta tashi, ko ina ciwo sai ga al'ada shi ma ya xo ya sa ta gaba,
daxu ta gama sharban kuka a nan, duk babu inda bata mirgina ba a parlon nan, ni
dai baranda na koma nayi xamana ba ruwana, to nace ta tafi gidansu ta ki tafiya
ya xan yi da ita...." mikewa yyi da sauri tace "A'a kar ka tasheta ka
rufa min asiri, daxu wannan d'an albarkan Bulasawa ya xo dubata ya taho da
magunguna da allurai...." Tsayawa Mujaheed yyi yana kallonta, Safeenah ta
shigo parlon ta xauna kasan rug tace "Ina yini Inna?" Inna na
murmushi tace "Lafiya lau 'yar nan, amma ku daina cika powder a fuska, kin
dai yi kyau wllh powdern ne yyi yawa har kina naso..." Sunkuyar da kai
Safeenah tayi tana ta kirkiran murmushin karfin hali, Mujaheed xai shiga daki
Inna tace "Kinga fitina ko, Mujaheed nace kar ka tasheta, wllh allura aka
mata ta samu bacci, ya xan yi da raina idan ka tasheta yanxu?" Bai tanka
Inna ba ya shiga dakin, Safeenah na kallonta da sauri tace "Waye ba
lafiya?" Inna ta marairaice tace "Wllh imaan, kamar baxata yi ba yau,
nace kar ya tasheta ya ki saurarata, duk ya rikice...." Mikewa Safeenah
tayi da sauri tace "Subhanallah bari in masa magana" daga haka ta
shige dakin.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
55....
Gefen Imaan dake bacci Mujaheed ya xauna a kan gadon Inna ya
kai hannu forehead dinta yana kallonta, Bude ido tayi a hankali, ya ta6a
jikinta xai yi magana Safeenah ta shigo dakin kamar an hankadota, rike kugu
tayi tana kallonsu, duk da mamakin ganinta da Mujaheed yyi bai nuna ba ya dauke
kai daga kallonta, Imaan ta mike xaune da kyar ta wani daure fuska, Mujaheed na
kallonta murya can kasa yace "Wani maganin kika sha?" Magungunan da
Sadeeq ya kawo mata daxu ta nuna masa, ya duka ya dau ledan ya fiddo drugs din
yana kallonta yace "Wa ya kawo maki?" Shiru tayi ta ki cewa komai, ya
hade rai yace "Am asking you" turo baki tayi ta koma ta kwanta,
Safeenah dai sai kallonsu take rike da kugu, Inna ce ta shigo dakin tana kallon
Safeenah tace "Safara'u kike ko wa, ba kya fita parlor ki bar su suyi
sirri ba, kinsan fa komai nata ya sani, yanxu ganin ki sai ta ji kunyar gaya
masa har da ciwon mara a abinda ya dameta, don Allah ki dan koma daga
parlo" Safeenah dai bata ce komai ba sai murmushin karfin hali take tana
sunkuyar da kai, Inna tace "Ae ba wani abu bane, bbu abinda Mujaheed bai
sani ba na Imaan, yanda kika san Yaya mace haka ta mayar da shi tun bata kai
haka ba...." Juyawa Safeenah tayi ta nufi kofa ta fice Inna ta bi bayanta
tana waigo imaan tace "Dama ki rufa min asiri kar ki bata min xanin gado
ki cuce ni, ba kowa gareni ba da xai wanke yanxu Mujaheed ba gidan yake
ba" D'an murmushi Mujaheed yyi har inna ta fita, Can ya wani hade rai yana
kallon Imaan yace "Wato kiran saurayin naki kika yi kika ce masa baki da
lafiya koh?" Kamar xata yi kuka tace "Ni bani na kirasa ba yaya"
fuska daure yace "Toh wa ya kirasa" a hankali tace "Inna"
yace "Wa ya kira mata shi?" Imaan tace "Ni ban sani ba ina
daki" Ya kara hade rai yace "Shine kika ce masa kina period
koh?" Xaro ido tayi tace "Wllh ni ban ce masa ba Inna ce ta fada masa
nima ai sai da naji kunya fa" tana magana tana turo baki, yace "Toh
wa yayi maki alluran?" Shiru tayi, ya d'an mata tsawa yace "Answer me
now" turo baki tayi tace "Inna ta min" sai kuma ta rufe fuskarta
da sauri a pillow tana dariya a hankali, kallon ta ya dinga yi yana jin
xuciyarsa na wani tukuki, a hankali ta dago tana kallonsa, ganin yanda ya daure
fuska ba shiri ta shiga taitayinta strictly yace "Sai kika bude masa kaya
ya maki allura yana kallon ki right?" Sosai ya bata dariya amma bata yi ba
tana komawa baya a hankali tace "Ni a cinya nace ya min, kuma a nan ya min
fa yaya, bari in nuna maka wajen ma" tana fadin haka ta dage gown din
jikinta a hankali tana nuna masa lap dinta, a hankali ya sauke idonsa yana
kallon fresh lap din nata, lkci daya yaji ransa yayi wani mugun baci xuciyarsa
na tafarfasa, tayi murmushi ta rufe kafan tace "Kagani ai" fuska a tamke
yace "When xa ku fara exams na first term?" Ta buda manyan idonta
tace "Saura kusan four weeks ai Yaya" yace "Good ana gama saukan
ku dama idan Inna xata taho gidana ku taho tare" ta xaro ido tace
"Saboda me Yaya?" A tsawace yace "I am giving you instruction,
don't question me" daga haka ya mike ya juya ya nufi kofa rai bace, ta bi
sa da wani kallo bayan ya fita, murya can kasa tace "Tabb, waye xai je
gidan ka, ni dai baxan je ba" Xaune ya tadda Inna kan tabarma ta daura
kafa daya kan daya tana ba Safeenah labarin irin wahalan da tayi da Mujaheed
tun daga ranan da aka haifo sa duniya.... Inna na kallon Safeenah da kyau tace
"Ko ke baki ga bakin d'an tsut ba??" Duk da irin yanda Safeenah ta
dinga dakewa coz at first she wasn't interested with the story gaba daya hankalinta
na daki ganin Mujaheed bai fito ba har sannan, amma bata san lkcn da ta fashe
da dariya ba har da sakkowa kasa tana kallon Inna, Inna ta hade rai tace
"Ke Safara'u ba batun dariya ba wllh, ya tsotsi uwar ne ba kadan ba sai
dai Allah ya bata lada, sai kin gansa wani narkeke da shi malam, don dama nonon
Rukayya ba dai kyau ba gaskiya" Dariya kawai Safeenah take har da
kyakyatawa, Inna ta tabe baki tace "Uhn ni dai ba ruwana" Mujaheed
dai yayi still bakin kofar daki ya kasa karasowa cikin parlon, Inna tace
"Toh wllh da ya dawo wajena yana da shekara uku sai...." Katse ta
Mujaheed yyi fuska daure ta hanyar ce ma Safeenah "Tashi mu tafi" ita
dai sai dariya take, Inna tace "Ya haka ina bata tarihi Mujaheed"
Mujaheed yace "Toh sai ki jira idan an baki mai gadin gidan
tarihi...." Inna tace "Meye laifina Mujaheed, matar ka ce fa kuma sai
mu xauna tana kallona Ina kallonta kamar kishiyoyi" Mikewa Safeenah tayi
tana dariya tace "Toh Inna mu xa mu koma xan xo ni kadai in sha Allah sai
ki bani karshen labarin" Inna na washe baki tace "Toh Safara'u shiga
ku yi sallama da Imaan din kiyi mata Allah ya sauwake" D'an dariyar dake
fuskar Safeenah ya dauke bata dai ce komai ba ta shiga dakin, tsayawa tayi
bakin kofa tana kallon Imaan dake xaune saman gado from head to toes, imaan ta
wani daure fuska, Safeenah ta ja tsaki tana yatsine fuska ta fice daga dakin.
Dai dai nan aka yi sallama bakin kofa, Inna ta mike da sauri tana amsawa tace
"Bisimillah Bukar, Mujaheed ne kadai da amaryarsa, shigo" Sadeeq ya
shigo parlon yana murmushi, hannu ya mika ma Mujaheed dake tsaye bakin kofa
yana kallonsa, Mujaheed ya amsa still looking at him suka gaisa, Inna na washe
baki tace "Toh xauna Bukar" Xaunawa Sadeeq yyi kan lallausan rug dake
parlon, Inna na kallon Safeenah tace "Saurayin imaan kenan Safara'u, tana
gama sakandari nan da wata daya xuwa biyu dama xa a fara maganar auren su, baki
ga ba yaro mai kirki da sanin ya kamata wllh" Safeenah tana kallonsa tace
"Sannu da xuwa" Sadeeq ya mata godiya yana murmushi, Safeenah ta nufi
kofa tana kallon Mujaheed sannan ta kalli Inna tace "Toh Inna bari mu je
sai na sake dawowa" Mujaheed yayi ma Inna sallama ya fita Safeenah na biye
da shi, sai da suka d'an yi nisa ya tsaya yace "Ki tafi bangaren mu ki
jira ni, I forgot i need to discuss something with grandma" da mamaki ta
dinga kallonsa, can tace "Toh sai mu koma tare ai" ya wani hade rai
yace "Wannan sirrinmu ne, do as I say plss" Bai jira cewarta ba ya
juya ya koma parlon Inna, ta bi sa da kallo da mugun mamaki, Inna ta xubo ma
Sadeeq abinci ta cika masa nama tam ta ajiye gabansa xata dauko ruwa kenan
Mujaheed ya shiga, cike da damuwa tace "Naga abinda ya isheni.... mai ya
dawo da ku kuma Mujaheed ba kun tafi ba, wllh shi kadai na ma girkin ban da
ku...." Sadeeq bai san lkcn da ya fara dariya ba, Mujaheed ya wani hade
rai yana kallonta, tace "Ni dai ba ruwana, mutane dai ba gaskiya meye kuma
na dawowa bayan mun yi sallama kun tafi" Mujaheed bai fasa karasawa cikin
parlon ba ya xauna, Inna ta ajiye ma Sadeeq ruwa da malt biyu tace "Toh ni
ban san yanda xan yi da kai ba gaskiya Mujaheed, ko in jiko maka garin kwaki
ina ma da gyada wllh" Sadeeq ya hadiye dariyarsa yace "Wllh Kaka ya
min yawa xa mu ci wannan tare" Inna ta tsuke fuska tana kallon Mujaheed
tace "Katon ba sai ya cinye gaba daya ba kana xaune Bukar...." Sadeeq
na murmushi yana kallon Mujaheed da ya hade rai yace "Bismillah Dr"
Mujaheed yace "Alhmdllh, I am okay" Inna tace "To maa sha Allah,
maxa maida hankali ka cinye kayan ka Bukar, Ni dai nasan sai ka fita xai
tsigaleni tass.... Toh wannan duk bai dameni ba tunda Allah ya ga xuciyata kai
na ma girki, ban san da xuwansu ba" Sadeeq couldn't stop smiling ya dau
spoon ya debi abincin ya kai baki bayan yayi Bismillah, Inna ta xauna tace
"Ita ma imaan d'an kadan na debar mata gashi can rufe a kitchen, toh ni
basu sanar min xa su xo ba da nayi girkin da su, meye a ciki don dai ka ba
mutum abinci, kawai fa ganin mutumi nayi gantsantsan a kaina mata na tsaye
bayansa, na ja bakina nayi shiru na basu hanya, shi sa na tafi kitchen na adana
maka abincin ka kada su gani su tafi da ni a baki suce na masu rowa, kasan
mutumin yau" Mujaheed dai bai tanka ta ba, ta gaji da xubanta tayi shiru,
yana ta xaune har Sadeeq ya gama cin abinda xai ci, bayan Inna ta tabbata da
gaske ya koshi ta kalli Mujaheed tace "Toh don Allah kayi hakuri ka ci
sauran, kaga dai a nutse ya ci abincin irin na yan gayu" Sadeeq ya fara
dariya ya kasa kallon Mujaheed dake kallon Inna ba yabo ba fallasa, Inna ta
tabe baki ganin Mujaheed bai ce komai ba ta dauke abincinta ta wuce kitchen ta
rufe, dawowa tayi tana kallon kofar daki tace "Toh imaan dakin xai bi ki
fisabilillahi, ki fito mana" sai da Inna ta kara magana imaan ta fito da
hijab, Sadeeq ya dinga kallonta, rakubewa tayi jikin kujera tana kallonsa a
hankali tace "Ina yini" yayi murmushi yace "Lafiya lau, how are
you feeling now" tace "Na ji sauki" yace "Maa sha Allah,
hope you've eaten?" Ta gyada masa kai, Inna dai sai kallonsu take tana
murmushi, imaan ta saci kallon Mujaheed dake kallonta fuska daure, Dauke kai
tayi da sauri, Sadeeq yace "Toh shkkn kaka na cika alkawari tunda na dawo
na ci abinci, ni xan koma" inna tace "Wllh na ji dadi Bukar Allah
maka albarka, tashi ki raka sa ke" Kudi ya fiddo aljihunsa dubu ashirin ya
ajiye kasa kan carpet da ya tashi yace "Kaka tukuicin girkin, naji dadi
kuma nagode" Inna tayi tagumi a hankali tace "Naga abinda ya
isheni... Bukar dai baya gajiya, abincin
ma sai an bada tukuici?? Toh Allah maka albarka, ni dai na gode baxan tsaya ina
jayayya da kai ba kamar karamar yarinya, nagode" Yana murmushi ya nufi
kofa, Inna na kallon Imaan ta hade rai tace "Ke dai sususu ce wllh, baxa
ki tashi ki rakasa ba toh" imaan ta turo baki ta mike ta bi bayansa, Inna
na kallon Mujaheed tace "Toh kullum aikin kenan fa wllh, sai ya ajiye min
damin kudi haka kafin ya fita har na rasa yanda xan yi da kudi a dakin nan, ni
fa ya fi min mutane da dama a duniyar nan don yasan abinda ya kamata, ku ma dai
ku ji tsoron Allah ku dinga koyi da shi..." Mikewa Mujaheed yyi ya fice
daga parlon. Tsaye Mujaheed ya tadda su kusa da flower sai wani sunkuyar da kai
imaan take shi ko sai kallonta yake kamar lkcn ya fara ganinta, kamar mai
counting steps dinsa ya dinga tafiyar don basu lura da shi ba, murya can kasa
Sadeeq yace "Plss ki kalleni dear let me feel relieved, I've missed you
alot, but staying far away from you and just listening to ur voice is d best to
me" Ita dai ta kasa dago kanta, a hankali ya kamo hannunta ta dago manyan
idanuwanta tana kallonsa, yyi murmushin sa mai tsuma xuciyar wanda ya gani
cikin cool voice dinsa yace "I love you Imaan, I am always dreaming to be
with you by my side as my wife.... I
wish xa ki ga yanda na kagu ki xama matata.... I just can't..." Sai kuma
yyi shiru ya lumshe ido, Imaan tayi still ganin Mujaheed da ya tsaya yana
kallonsu, da sauri ta xame hannunta daga na Sadeeq, Mujaheed ya dauke kai ya ci
gaba da tafiya gently, Ko Sadeeq bai juya ba yasan shi ne, kuma ya ki kallonsa,
har sae da Mujaheed yyi nisa sannan Sadeeq ya bi sa da wani kallo, can ya gyada
kai smiling, Imaan tace "Xan je in kwanta na gaji" yace "Sure
dear, hope cramps din yyi sauki?" Xaro ido tayi sai kuma ta rufe fuska da
sauri, ya dinga kallonta yana murmushi, ya kai bakinsa kusa da kunnenta a
hankali yace "A day will come da xaki san kunya baxae amfane ki ba"
turo baki tayi har sannan ta ki kallonsa, murya can kasa yace "I want just
a favor from you... And don't deny me plss" tana kallonsa tace "Na
me?" Yana murmushi yace "I will text it to you idan na shiga mota
ynxu coz I am not ready to dig u out from underground now" xaro ido tayi
tana kallonsa, ya hade rai yace "And if you deny me, I won't be happy
imaan" Bai jira cewarta ba ya fara tafiya yace "Expect the text now,
gobe I might come in the evening in sha Allah" ta bi sa da kallo har yyi
nisa sannan ta juya a sanyaye ta koma part din Inna. Bayan magrib imaan na
xaune dakin Inna bayan ta gama shirin bacci xata kwanta ta tuna wayarta da text
din da Sadeeq yace xai turo mata tun da rana, mikewa tayi da sauri ta dau Hijab
ta saka ta fito parlor tasan ma kila yana ta kiranta, Inna dake xaune parlon
tana cin abinci ganin ta nufi kofa ta tabe baki tace "In ji baki mance
komai naki a dakina ba Imaan" imaan tace "Xan dawo fa, wayata xan je
in dauko a gida" cike da damuwa Inna tace "Me kuma xa ki dawo ki
min?? Tun safe fa kike nan" Imaan bata saurareta ba ta fita parlon, daga
nisa ta hango mutum na tahowa kamar Yusuf kamar kuma Mujaheed, duk da Yusuf ta
san ya daina xuwa part din Inna sai tare da Abba, Tsayawa tayi har sai da ya
iso kusa da haske taga Mujaheed ne, turo baki tayi ta juya da sauri ta koma
part din Inna, Inna da ta bar abincin da take ci ta tafi tana share dakinta ta
daga kai tana kallonta tace "Naga jaraba... Har kin dawo??" Imaan ta
bi ta gefenta ta shige dakin tana cewa "Ko ba Yaya bane" Inna ta ci
gaba da sharanta tace "Toh dama ki kakkabe min xanin gadona ki gyara gadon
fess ni ba gantalalliya bace, ba haka nake barin dakina ba in kwana tare da
wari" Inna ta mike ganin Mujaheed tace "Wannan shine anyi ba ayi ba,
yanxu kayi auren ma baxa mu sarara ba Mujaheed kullum kai ta mana sintiri a
gida, ba daxu da rana ka xo ba to me kuma ya dawo da kai, ko akwai ajiyar ka a
parlon nan ne baka dauke ba har yanxu" Bai tanka ta ba ya nufi kofar dakin
ya bude ta bi sa da kallo baki bude, imaan ta koma can karshen gado kamar xata
yi kuka tana kallonsa, Ya wani mugun daure fuska yace "You had better keep
on running away from me coz wllh wlh am promising you this... if I should get
hold of you I won't take it likely with you.... I will seriously deal with
you" a fusace Inna tace "Naga abinda ya isheni, don Allah Mujaheed ka
rufa mana asiri, me ta maka kake kunduma mata xagi haka, yarinyar da kamar
baxata yi ba daxu Allah ya rufa mana asiri Bulasawa ya rufa mana ya mata allura
ya bata magani taji sauki shine yanxu xaka xo kana xaginta kana nuna ta da
yatsa kana gaya mata maganganu marasu dadin ji, to ni dai ba ruwana ka tafi ka
ba mu waje, ni na ta6a jin inda aka aurar da mutum kuma yyi ta sintirin dawowa
gida kamar dai da ajiyarsa da ya mance bai dauka ba, ni dai gaskiya na gaji da
kai kar ka sake xuwa min, tunda kayi auren ka kayi xamanka a gidanka ka bar min
jikata ta sarara...." Kawai Inna gani tayi ya shige dakin ta fasa ihu tana
kwala ma Ahmadu kira iya karfinta, ba kuma wanda xai ce ba wani mugun abun ta
gani ba, Imaan ma duk ta rude xata gudu bandaki ya fixgota kawai sai ji tayi
xabga mata mari mai lafiya, ta rike fuskarta a gigice, inna na ganin haka ta
fice da gudu xuwa waje tana kiran Abba, Mujaheed na kallonta da idonsa da suka
kada cikin harshen turanci yace "Muharramin ki ne mutumin nan da kika mika
masa hannun ki ya kama, dama iskancin da ku ke yi da shi kenan, yana tsaye kusa
da ke kamar xai shige jikin ki kina jin dadi koh? To wllh yanxun nan xan je in
sami daddynki in sanar masa komai" a rikice imaan ta rikosa ta dinga basa
hakuri tana cewa "Yaya ni bani nace ya rike ni ba, don Allah kayi hakuri
baxan kara ba wllh, don Allah kayi hakuri" sosai xuciyarsa ke tafarfasa
yana kallonta, ta hade hannayenta hawaye na sakko mata tace "Don Allah
kayi hakuri baxan kara ba da gaske Yaya" tana fadin haka ta boye fuskarta
a jikinsa tana kuka, har ransa yake jin kukan nata, Bai san lkcn da ya jawota
jikinsa ba cikin sanyin murya yace "That's very wrong imaan, I've told you
times without numbers... that guy is just here to ruin ur life, to cause you heartbreaks,
he is after ur body... He is..." Kasa ci gaba yyi don sosai ransa ke
tafarfasa, imaan dai sai sauke ajiyar xuciya take tana kuka a hankali bata ce
komai ba, nan ko ko kiris bata yrda da abinda Yayan nata ke fada ba don ita
tasan Sadeeq na sonta kamar yanda ita ma take sonsa fiye da xaton mai karatu,
dago kanta yayi yana kallon kwayar idonta da ya rine murya can kasa yace
"For my sake xa ki rabu da shi plss Imaan?" Ta fashe da kuka cikin
rawar murya tace "Ni dai ina son sa Yaya, kuma ai aurena xai yi..."
Kallonta Mujaheed yake ko kiftawa babu xuciyarsa na bugawa, da kyar tace
"Kayi hakuri plss Yaya, da gaske Ina son sa, but in sha Allah baxan bari
ya sake rike hannuna ba"
🌟⭐⭐⭐🌟assslamun alykum ina bawa masoya littafina imaaan hkrn xasujini shru xan dau hutune xuwa
bayan.sallah in allah ya kaemu tnx u fans imaaan inbaki biyaba karki karanta🌟⭐🌟
_Maa Sha Allah, koma wacece ko wanene yayi wannan Broadcast
din na sama👆🏻 ya sani.... Da *NI* da *shi/Ita* xa
mu hadu gaban Ubangiji, ba fa a kan komai ba sai kan gantalallen Hausa Novel
wanda baxai kare mu da komai ba, baxai amfane mu da komai ba ranan gobe kiyama,
wanda muke fatan ma ba xunubi muke kwasan ma kanmu ba muke kuma rokan Allah ya
yafe mana, wato irin xagi da cin mutunci da mai Broadcast din ya ja min jiya
wllh tllh xa ayi mana hisabi da koma wanene, don ni dai na yafe duk xagi da na
sha amma mai post din ya sani xa mu hadu gaban ubangijin da ya halicce mu in
sha Allah, and that's if he or she believes there is God_
Ni ba fitinanniya ba ni ba mafadaciya ba, ni ba mai sa ido
ba, ni ba mai takura ba, amma duk da haka ban tsira ba a media sai an cakale ni
na mayar da martanin da bana so dai, duk da babba da hakuri aka san sa amma a
dai dinga jin tsoron Allah, mutane dai ba gaskiya basa tsoron Allah, a dai
dinga jin tsoron Ubangiji ni ba ruwana.🤦🏻♀️
Least I forget akwai wani hoton dake circulating na wata mai
pink kaya wai Khaleesat Haiydar, to gaskiya ban san yarinyar ba ayi hakuri a
daina turo min ana tambaya ko ni ce don ba ni bace, plsss ba ni bace oo... this
is not 2012 I am begging you pple ba ni bace...😟 Ranan da na gama Imaan xanyi attaching pic dina a karshen page din sai
ku gani😁
One love fans😍
Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
56....
Saketa Mujaheed yayi har sannan bai daina kallonta ba sai
kuma kawai ya juya ya nufi kofa ya fita, ta bi sa da kallo tana share hawayen
dake xubowa idonta a hankali, komawa tayi gefen gado ta xauna a sanyaye, ko
minti biyar ba ayi da fitar Mujaheed ba Inna ta dawo dakin tace "Tashi mu
tafi Ahmadu na kiran ki ya ji ba'asi... Yau in sha Allahu xai mana iyaka da
shi, kada ya sake shigo min tunda yayi aure, Ina murna na rabu da shi kuma sai
kullum ya wani xo min xalo xalo kamar da ajiyarsa da ya mance min a
nan???" Imaan tace "Ni dai ba abinda yayi min fa, kuma bance ki je ki
ce ma Abba komai ba, ai ni ce ban gaishesa ba shi sa, kuma na hakura ni
dai" Sake baki Inna tayi tana kallonta, Imaan ta mike ta nufi kofa tace
"Komai sai ki tafi wajen Abba baki jira kin ji abinda ya faru ba..."
daga haka ta fice a dakin ta bar Inna a tsaye. A hankali Imaan ta bude kofar
parlon su ta shiga gabanta na faduwa, da ta tuna abinda Mujaheed yace wai xai
gaya ma Daddy sai hankalin ta ya tashi, amma ta san baxai ma fada ba kawai
tsorata ta yayi, Ammi ce kadai xaune parlor tana kallo, ta xauna kasa a hankali
ta gaisheta, Ammi na kallonta tace "How are you feeling?" Tace
"Na ji sauki Ammi" Ammi tace "Toh Allah ya sauwake, ga abinci
can kitchen idan xa ki ci" ta girgixa kai tace "Na ci a wajen
Inna" Ammi bata ce komai ba, hakan yasa ta mike ta nufi dakinta, a hankali
ta nufi inda wayarta ke ajiye ta dauka xuciyarta na bugawa don bata san abinda
xata gani ba, ta xauna gefen gado ta sauke ajiyar xuciya a hankali, can dai ta
kunna wayar tana kallon screen din taga message da missed call a gaban screen
din, missed call din ta fara shiga taga na sadeeq ne kuma just few minutes ago
ya kirata, bude text din tayi tana dubawa kamar idanuwanta xa su fito, ta
maimaita text din ya fi sau a kirga, can ta 6ata fuska kamar xata yi kuka, tafi
minti goma a xaune, sai can kuma tayi wa Maryam forward din message din, bayan
ta tabbata ya tafi tayi deleting gaba daya a wayar, ta d'an yi murmushi ta mike
ta cire Hijab din jikinta ta linke ta kashe wutan dakin ta kwanta. Washegari da
ya kasance Monday Imaan ta ji sauki sosai hakan yasa tayi shirin wucewa schl da
safe, tana tattara few textbooks dinta da xata tafi da su makaranta taga
wayarta dake gaban madubi yyi haske, karasawa tayi ta dau wayar taga text din
Maryam ne ya shigo tana requesting ta hau WhatsApp su yi chatting, reply tayi
mata da cewa sai ta dawo schl daga haka ta ajiye wayar ta fita dakin. Karfe
hudu saura Imaan suka fito schl tare da Mariya dake ta mata labari tun basu
fito aji ba, tsaye su ka ga Sadeeq jikin motarsa ya rungume hannu idonsa sanye
da glasses, Sosai gaban Imaan ya fadi, Mariya ta wara ido tana kallonsa tace
"Ya Sadeeq Drivers fa?" Shi dai bai ce mata komai ba, Kallon Imaan
Mariya tayi tana murmushi tace "Sai gobe xan ci gaba Imaan" tuni
kanninta biyu shiga mota yayan nasu, Imaan ta gyada mata kai tana d'an murmushi
tace "Allah ya kai mu" Har Mariya xata shiga motar sai kuma ta kalli
Imaan tace "Baxa ku gaisa da yayana ba" Imaan ta kalli Sadeeq dake
kallonta ba ko kiftawa, daga inda take tsaye a hankali tace "Ina
yini" ya gyada kai yace "Lafiya lau" daga haka ya xaga ya bude
maxaunin driver ya shiga ya tada motar suka wuce. Imaan na dawowa islamiyya
that same day taga Miss call din Sadeeq, kasa kiransa tayi da farko don bata
san me xata ce masa ba, can dai tayi dialing number a hankali ta kai kunne,
yana fara ring ya katse ya kirata, tayi
gathering courage tayi picking, murya can kasa tayi masa sallama ya amsa yace
"You are ignoring my calls ko" ta xaro ido tace "A'a wllh, bana
kusa da wayar ne ai yanxu muka dawo islamiyya, jiya kuma Ina part din Inna
wayar kuma na part din mu" yace "Ohk, I tot u where ignoring it shi
sa ma ban xo ba yau, ya jikin?" Ta langwabar da kai tace "Na ji
sauki" yace "Maa Sha Allah" shiru tayi ta rasa abun cewa, can
yace "Did you see my text or u don't just want to talk about it?"
D'an murmushin karfin hali tayi tace "Sure I saw it, I... but.. I can try
doing as u wish, but I can't perform the action in the text" Dariya yayi
yace "Ohk then...." Ta turo baki bata ce komai ba, yace "I will
call you later xan fita masallaci" tace "Allah ya kai mu" daga
haka ya katse wayar. Ranan Thursday da safe bayan Imaan ta gama shirin boko ta
sami Ammi a kitchen a hankali tace "Ammi tunda ba islamiyya yau idan na
dawo schl plss Ina son in je in gaida Gwaggwo daga nan sai in kai ma Aunty
halima katin sauka" Ammi tace "Jiya ba ce min kika yi Thursday da
Friday duk xa ku je islamiyyar ba da yamma?" Imaan ta xaro ido tace
"Ance sai Friday morning and evening" Ammi ta tabe baki tace
"Toh ki kira daddy ki gaya masa, ai ba ni xa ki gaya ma ba" Murmushi
Imaan tayi tace "Ae har na gaya masa jiya da daddare" Ammi tace
"Toh Allah ya kai mu" Imaan tace "Ameen" shayi ta hada a
cup ta fita da bread da egg dinta a plate xuwa dinning. Tana dawowa schl ranan
ko abincin kirki bata ci ba tayi wanka ta shirya cikin bakin abayanta ta sa
Hijab har kasa ta fito parlor, Ammi dake kallonta tace "Kar ki kai magrib
a hanya Imaan" xaro ido Imaan tayi tace "Ammi ni fa cewa Daddy nayi
xan kwana" Ammi tace "Kwana kuma?" Imaan ta marairaice tace
"Ehh Ammi na gaya masa, ki kirasa ma" Ammi tace "Toh schl din
fa?" Imaan tace "A'a ai nace maki islamiyya xan je da safe da kuma
yamma tunda Saturday ne saukan ai" Ammi tace "Ba ruwana ni ban ce ki
kwana ba da kin gaisheta ki kai ma Halima kati ki juyo, am I clear???"
imaan tayi shiru tana kallonta kamar xata yi kuka, Ammi ta ci gaba da abinda
take, a hankali Imaan tace "Toh sai na dawo" Ammi tace "Dama
kada ki kuskura ki kai magrib a titi ni dai na gaya maki" imaan ta nufi
kofa bata ce komai ba har ta fita parlon. Imaan na isa gidan gwaggwo dama
gaisheta kawai tayi tace "Ina sauri xan je gidan Anty Halima in kai mata
kati in dawo...." Gwaggwo na kallonta tace "Toh shikenan sai kin
dawo, ya saurayin naki Sadeeq?" Yar dariya tace "Yana nan, shi xai
kai ni gidan Aunty Halima din ma, amma kar ki gaya ma Ammi fa" Gwaggwo
tace "Au tare ku ke shine bai shigo mu gaisa ba" imaan tace "A'a
yanxu dai ya kirani yana hanya" Gwaggwo tace "Toh Allah ya kawo sa
lafiya, Mujaheed na lafiya da amaryar sa dai koh?" Imaan ta turo baki tace
"Nima dai ban sani ba" Gwaggwo tace "Baki je gidan ba
kenan" imaan tace "Mun je da Gwaggwo amma matar bata da mutunci, ni
dama baxan sake xuwa gidansa ba har abada" Gwaggwo tace "Ikon Allah,
toh Allah dai ya kyauta, amma ai babu xancen baxa ki kara xuwa gidan yayanki ba
Imaan" Imaan ta dau wayarta dake ring ganin Sadeeq ne ta mike tana kallon
Gwaggwo tace "Sai na dawo" Gwaggwo tace "Har ya iso" Kai ta
gyada mata, Gwaggwo tace "Toh Allah ya kiyaye, hanya a dai kula kin
ji" Imaan ta nufi kofa ta fita parlon, yana xaune mota ta karasa ta bude
front seat, kallonta ya dinga yi, a hankali tace "Ina yini" ya d'an
yi murmushi yana shafa kansa murya can kasa yace "Lafiya lau Hijab queen,
you look beautiful in it always, but yau ma sai kin sa?" Shiru tayi tana
kallonsa, Yana mata murmushi yace come in" a hankali ta shiga motar ta
rufe ba tare da ta yarda sun hada ido ba, ya tada motar yace "Xa ki kai ma
Halima card din first koh?" Ta gyada masa kai, driving yake kamar bai son
yi, lkci lkci kuma yana kallonta ta gefen ido, shiru babu wanda yace komai
cikinsu har suka isa gidan Aunty Halima after 15 mins ride, ya juya yana
kallonta a hankali yace "Be fast Imaan" ta gyada masa kai ta sauka ta
nufi cikin gidan ya bi ta da ido, jinginar da kansa yayi jikin mota ya lumshe
idanuwansa, can ya bude ya dau wayarsa yayi dialing number ya kai kunne, ana
dagawa, cikin cool voice dinsa yace "Selim... I think I am just sorry, I
had to disappoint you guys, may be some other times xa ku santa, kawai na fasa
deal din" Best dinsa Selim dake sauraronsa da mamaki yace "I don't
get you Sadeeq..." Sadeeq ya d'an yi shiru sai kuma calmly yace "I
can't bring her to that place, she's more than decent and innocent, though I
have neva had bad intention toward her... but, I am sorry for the
disappointment, I will compensate this deal for what ever amount you guys will
require" Selim yace "You are sick, mu ne ba mu san ciwon kanmu ba ko,
mu ne ba mu san ciwon babes din mu ba, what's the use of all this Sadeeq, after
necessary arrangements da aka gama ka xo kana kawo mana wani surutu, this is
very unusual of you, haka on ur Birthday wai wani she's sick baxata xo ba, wato
mu namu Girlfriends din ne pure water....." Sadeeq dai tabe baki kawai yyi
bai ce komai ba, Yana jin friends din nasa dake guest inn din nasa suna surutu
daga karshe ya katse wayarsa, dialing number Mariya yayi, tana dagawa ya gaya
mata wani babban wajen cin abinci da xata je ta jirasa in the next 15 mins,
yana gama fada mata ya katse wayarsa. Imaan na fitowa gidan cousin dinta ta
bude motar tana kallonsa a hankali tace "Kayi hakuri I kept u
waiting" murmushi kawai yyi bai ce komai ba ta shiga motar, tada motar yayi
suka bar layin, sai da suka hau saman titi ya kamo hannunta da nufin xai mata
magana, ba ita kadai ba har shi sai da yayi shock hakan kuma ya sa ya saketa,
har kuma suka isa wajen cin abincin bai ce mata komai ba ita ma haka, ganin
motar gidansu a haraban eatry din ya gane Mariya har ta iso, Yana kallon Imaan
yayi murmushi yace "Mu je" a hankali ta bude motar ta sauka shima ya
sauka ya rufe motar ya shiga gaba tana biye da shi har suka shiga wajen, few
mutane ne cikin hadadden wajen, Sadeeq ya hango Mariya xaune tana danna waya ta
cakare cikin English wears, ya kalli Imaan dake kallon Mariyar da mamaki ita
ma, Ya wara mata ido yace "Mu je" ba musu ta dinga bin sa har suka
isa gun Mariya, Mariya da tuni ta hangosa amma bata san tare da Imaan bane ta
dai ga mace da Hijab, a xuciyarta kuwa cewa tayi ohhh tot ya Sadeeq ya shiryu
gaba daya jin kwana biyu shiru ba ace min ga new catch ba balle mu hadu in
gilla mata karya, ashe dai da saura, ko wa kuma aka samu mai hijab har kasa,
dariya abun ya bata don ita dai tasan he is not a lover of hijab fa, haushi
yake ji yaga mace ta sa hijab sanin da tayi masa da, Suna isa inda take ya ja
ma Imaan kujera yana kallonta, Imaan dake kallon Mariya ta xauna, shi ma ya
xauna, Mariya ta ajiye wayarta ta fara magana kamar yanda ta saba duk sanda
suka hadu da daya daga yan matan nasa, tana murmushi tace "Sannu auntynmu,
Yaya yace yau dai sai mun gaisa da future wif......" Shiru tayi da mugun
mamaki tana kallon Imaan, can ta kalli Sadeeq amma ta kasa cewa komai xai xare ido
take, cikin cool voice dinsa yace "Meet my soulmate, the future mother of
my angels in sha Allah...." Mariya was just lost of word, imaan kam ta
sunkuyar da kai, a hankali Sadeeq yace "Ko bata maki bane Lil sis?"
Mariya na kikkifta ido tace "I don't get this ya Sadeeq, are you for
real??" gently yace "Sure, my future wife in sha Allah, Imaan is her
name" Tasowa Mariya tayi ta rungume Imaan cike da murna tace "Waow,
amma na ji dadi sosai wllh Yaya, but you two neva for once told me, me yasa kuka
boye min plss..." Imaan dai tayi murmushi bata ce komai ba, waitress ce
tsaye kansu tana tambayar me xata kawo masu, Sadeeq yace "Just
drinks" Sadeeq na kallon kanwartasa yace "Toh sake min ita kada ki
fadar da ita" dariya sosai Mariya tayi ta sake imaan ta xauna, tana kallonsu
so happy, ba a dau lkci aka kawo masu drinks din, Imaan dai sai kallon Mariya
that couldn't hide how happy she is, tana mitan irin deceiving dinta da suka
dinga yi kullum sai yace mata bai gane imaan ba ashe ma ya fi ta gane ta, Shi
dai Sadeeq kallon Imaan kawai yake with affection, sai a sannan yake da ya
sanin ma amincewa da yayi xai kai ta guest inn yayi proposing mata gaban
gantalallun frnds dinsa da a yanda yake ya ma fi su kamun kai... lol, after the
proposal kuma party... party that they will be different type of wines, a must
drink... Kawai a gama kalle masa soulmate, lkci daya mood dinsa ya canxa,
Mariya ta xuba ma imaan drink a disposable cup ita ma ta xuba ta dauka ta mika
ma imaan tana murmushi tace "Here.... Future in-law...." Imaan ta
amsa tana murmushi, Mariya ma ta xuba ta fara sha tana kallon Sadeeq tace
"You can serve ur self" d'an murmushi yyi ya diba ya fara sha, Mariya
na shan drink dinta ta fara imagining to ya ake wannan soyayyar da Imaan, imaan
dai da ta sani baxata ta6a yarda Sadeeq yyi kissing dinta ba balle ya rungume
ta, toh how is her brother coping, Sadeeq that she know can't do with out that
tabbb, tunanin hakan ya bata dariya sosai, to ko ya ake wannan soyayya, Sadeeq
ya ajiye sauran drink din hannunsa yace "You two should tell me abinda ku
ke so na saukan ku that's on Saturday" Mariya tace "Good, muna komawa
gida xan maka list dama, muna bukatan lot lot of thingssss" dariya kawai
yayi sanin both abinda ya kamata da wanda bai kamata ba kenan xa a rubuta a
list in dai Mariya ce, they spent just 30 mins a eatry din daga nan Sadeeq ya
mike yace "It's past six now xan mayar da ita gida" Mariya tace
"Ohk then, am very happy at this Yaya, Allah ya sanya alkhairi, plss"
yace "Ameen" daga haka suka fita eatry din Mariya na cewa "Plss
this shouldn't take too long ooo" Imaan dai taki yarda ta kalleta, Sadeeq
dai yyi murmushi yace "Sure just in few months time" Mariya ta dinga
murna ita a dole Sadeeq xai auri kawarta, motar gidansu da driver ke xaune yana
ta jiranta ta nufa tana daga ma imaan hannu tace "Sai mun hadu islamiyya
gobe da safe in law" Sadeeq ya bude ma Imaan back seat yana kallonta,
shiru tayi tana kallonsa ita ma, ya d'an yi murmushi yace "You don't worry
ki shiga, I don't mind being ur Driver" ta d'an yi murmushi ta shiga motar
a hankali, ya rufe sannan ya shiga driver seat ya tada motar ya bar eatry din.
Yana driving yace "Gidan gwaggwo xan maida ki ko gida?" Tace
"Gida, xan kirata ince na wuce gida" yace "Ohk" suna isa
layin ya tsaya 2 houses away, sannan ya bude motar ya dawo baya ya shiga ya
rufe yana kallonta, sunkuyar da kai tayi gabanta na faduwa, tsoronta daya kada
Mujaheed ace yana anguwar balle ya ganta cikin motar duk da glass din is
tinted, Sadeeq yana d'an murmushi yace "I think I don't have to propose in
midst of friends, just me and you..." ita dai bata ce komai ba tana
kallonsa, ya dauko wani karamin box ya bude yana kallonta, sunkuyar da kai tayi
gabanta bai bar faduwa ba, ya ciro ring din ciki wanda ba sai na fadi wani iri
bane, lol... ya kamo hannunta yana kallonta ya xura mata ring din, ita dai ta
kasa dago kai ta kallesa xuciyarta sai bugawa yake ga kamshin sa da ya cikata,
Bata ankara na sai ganin ya hade bakinsu tayi, tunda take bata ta6a tsorata na
moment din ba, coz it was something that had never happened to her all her
life, lkci daya ta fara turasa hawaye na sauka idonta, bai wani dau lkci ba ya
saketa shi ma xuciyarsa na bugawa, daura kansa yyi a kafarta cikin sanyin murya
yace "I.. i.. am, I am sorry Imaaan" ja baya tayi hakan yasa ya dagata
ta bude motar ta daya side din ta fice daga motar da sauri....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
57......
Imaan na shiga parlonsu ta wuce dakinta direct ta kulle kofa
ta fashe da kuka sosai. Bayan kusan minti goma Ammi ta dawo daga part din su
Aunty ganin takalman imaan bakin kofa ta shiga parlon ta wuce dakinta, alwala
tayi ta dawo parlor tana kallon agogo don har sannan da saura lkcn sllhn bai yi
ba, ta kalli kofar dakin Imaan tace "Imaan" Da sauri Imaan dake xaune
can karshen gado ta hade kai da gwiwa ta daga kanta, Ammi ta sake kiranta,
sakkowa tayi daga kan gadon tana goge idonta duk da hawayen ya ki tsaya mata,
ta nufi kofa ta bude ta fito parlor, Ammi na kallonta tace "Yaushe kika
shigo?" Da kyar ta bude baki tace "Ban dade ba" shiru Ammi tayi
tana kallonta da mamaki, Imaan ta sunkuyar da kai gabanta na faduwa sosai, Ammi
tace "Kukan me kike?" Ta girgixa kai tace "A'a ba komai"
Ammi ta mata wani kallo tace "Zo nan" sosai xuciyarta ke bugawa ta
karasa ta duka kasa tana kallon Ammi tace "Gani" cikin tsawa Ammi
tace "What's wrong with you?" Duk yanda ta so dakewa kasawa tayi, ta
fashe da kuka sosai, duk yanda Ammi ta so boye tashin hankalinta a lkcn kasawa
tayi, Tayi kasa da murya tace "Nace me ya faru imaan, kukan me kike yi,
talk to me daughter" Cikin rawar murya tace "Da gaske Ammi ba
komai" Ammi ta wani hade rai tayi mata wani tsawa tace "Baxa ki bani
amsa ba, kukan uban me kike, me aka maki?" Imaan dai ta kasa cewa komai
sai hawaye, mikewa Ammi tayi hakan yasa ta tashi da sauri ta koma baya ta fashe
da sabon kuka, tsayawa kallonta Ammi tayi, can ta wuce daki da sauri ta dau
wayarta ta shiga kiran layin gwaggwo, ta kira ya fi sau a kirga gwaggwo bata
dauka ba, kowa kuma yasan gwaggwo haka take da waya, Ammi ta shiga kiran
Halima, bayan sun gaisa Ammi tace "Halima Imaan ta je gidan ki?"
Halima tace "Ehh ta xo daxu amma ai ta wuce" Ammi tace "Karfe
nawa ta bar gidan naki?" Halima tace "Shidda dai kamar yayi, lafiya
Ammi?" Ammi tace "Lafiya lau, Ina tace maki xata daga gidan
naki?" Halima tace "Bata koma gida bane Ammi?" Ammi tace
"Tambayar ki nake" Halima tace "Tace kila ta wuce gida ko kuma
ta tafi wajen gwaggwo" Ammi tace "Toh sai anjima" daga haka ta
katse wayar, Gwaggwo ta sake kira har ya gama ring bata dauka ba, ta kuma kira
nan ma haka, ajiye wayar tayi ta fito, ganin Imaan bata parlor ta wuce dakinta,
jin tana bathroom Ammi ta tsaya, gaba daya hankalinta ya tashi sosai, Imaan na
gama alwala ta fito, sosai ta tsorata ganin Ammi, ta sunkuyar da kai a hankali
tace "Ammi ba komai fa" Ammi tace "Daga gidan Halima kin koma
gidan gwaggwo ne?" Ta girgixa kai tace "A'a" Ammi tayi kasa da
murya tace "Toh ki gaya min me ya faru" cikin sanyin murya tace
"Ba komai fa Ammi, kawai dai kamar bana jin dadi ne" Ammi tace
"Baki jin dadi kuma?" Ta gyada kai, Ammi tace "Ina ke maki
ciwo?" Ta girgixa kai tace "A'a ba inda ke min ciwo, kawai dai bana
jin dadi" shiru Ammi tayi tana kallonta, can tace "Toh ki yi sllh ki fito
yanxu" imaan ta gyada mata kai Ammi ta juya ta fita, har Imaan ta idar da
sllh ta kasa daina hawayen da bata san dalili ba, tayi kokarin daina hawayen
amma hakan ya faskara, har sannan she is just shock, fashewa tayi da kuka a
hankali, ta jinginar da kanta jikin gado. Ammi na idar da sllh tayi ta jiranta
ta fito amma shiru, hakan yasa ta mike ita ma gaba daya ta rasa me ke mata
dadi, gashi ta kara kiran gwaggwo bata dauka ba tasan wayar na can karkashin
pillow, A hankali ta bude kofar dakin ta ganta xaune kan darduma ta jinginar da
kai da gado tana bacci, Ammi ta karasa inda take ta duka ta kai hannu jikinta
ta ji ba xafi, Bude ido imaan tayi ganinta ta ja baya, Ammi na kallonta ta
xauna gefen gadon tace "Tell me what's wrong with you plss imaan"
D'an murmushin karfin hali tayi tace "Ammi ba komai fa, i am better
now" Ammi ta dinga kallonta kafin tace "Toh fito ki ci abinci"
tashi tayi a hankali ta dauke pray mat din ta linke ta bi bayan Ammi xuwa
parlor, Ammi ta xuba mata abinci a kitchen ta kirata, Mikewa Imaan tayi daga
xaunen da tayi a parlor ta tafi kitchen ta amso abincinta ta dawo parlor ta
xauna, Sosai Ammi ke studying dinta tana cin abincin sai dai bata ce mata komai
ba, ganin xata je ta ajiye abincin da ko rabi bata ci ba Ammi tace "Dawo ki
cinye abincin nan" kamar xata yi kuka tace "Ammi ya min yawa"
Ammi tace "Dawo ki cinye na ce" babu yanda ta iya haka ta koma ta
xauna tana tura abincin da kyar, har ta cinye taje ta ajiye plate din a kitchen
ta dawo parlor tana kallon Ammi tace "Ammi ina son xan kwanta" Ammi
tace "Ishan fa?" tace "Ba bacci xan yi ba kawai xan kunna kallo
a ciki" Ammi bata ce mata komai ba hakan yasa ta wuce daki Ammi ta bi ta
da ido har ta rufe kofa. Ammi dai na ta xaune parlor har takwas da rabi aka yi
sallama bakin kofa, amsawa tayi Mujaheed ya shigo parlon, Ammi na kallonsa tace
"Sannu da xuwa" Ya d'an yi murmushi ya xauna yace "Ina yini
Ammi" Ammi tace "Lafiya lau, ya gida" yace "Lafiya
Alhmdllh" tace "kwana biyu?" Yace "Alhmdllh" Ammi na
kallonsa tace "Baka da lafiya ne" yar dariya yyi yana shafa kansa
yace "Aa, am okay, me kika ga" ta girgixa kai tace "A'a ba
komai, a xubo maka abinci" yace "A'a Alhmdllh" shiru yayi yana
kallon movie da ake yi a tv, can ya kalli Ammi yace "Abba yace Imaan ta
je" Ammi tace "Ohk, tana ciki Ina jin ta kwanta, let me wake
her" ya kalli agogo sannan ya kalleta yace "Bata da lafiya ne?"
Girgixa masa kai Ammi tayi tace "She's ohk" Ammi na kallon kofar
dakinta ta kwalo mata kira, ta kirata yyi sau uku amma shiru, can Ammi ta mike
ta tafi dakin, kwance ta ganta ta rufa da duvet, Ammi ta karasa ta cire duvet
din da sauri Imaan ta rufe idonta, da mamaki Ammi ke kallonta tace "Imaan
kina son in bata maki rai a gidan nan yau ko, baxa ki gaya min meye damuwarki
ba, wani abun ya faru ne baxa ki gaya min ba" Imaan taki yarda su hada ido
ta mike xaune tana goge guntun hawayen idonta a hankali tace "Ammi kiyi
hakuri ni nace maki ba komai fa" Ammi tace "Wani abun ya hada ki da
gwaggwo ne" Imaan tace "A'a ni ban ma dade a gidanta ba, Ammi it's
just mood swings" Ammi tace "Toh xan kira daddyn ki yanxu kuwa in
gaya masa, don baxan yadda ki sa min ciwon kai ba ina xamana, wannan ai
walakanci ne, ke yarinya ce xaki xauna kina kuka ki ki fadin matsalar ki kice
min mood swings, ko iskancin ki na da ne xai dawo yanxu, kuma ki tashi ki fita
Abba na kiran ki...." Juyawa Ammi tayi rai bace ta fita a dakin tana
mamakin hali irin na Imaan, tasan ko da rufeta xata yi da duka ta dage a kan
sai ta gaya mata kukan me take to taurin kanta baxai taba bari ta fadi ba, ita
kanta taurin kan Imaan na damunta ne ba kadan ba, parlor ta koma ta xauna tana
kallon Mujaheed tace "I don't know what's wrong with her, tun daxu take
kuka, na tambayeta meye matsalar ta taki gaya min, kuma kukan na iskanci ne da
jin dadi, dama ranta a bace ta bar gidan tunda nace kar ta kwana inda xata
je...." Mujaheed na kallon Ammi yace "Kuka kuma" Bude kofar
dakin Imaan tayi ta fito kanta a kasa, Mujaheed ya dinga kallonta har ta karaso
cikin parlon ta xauna kasa tace "Ina yini Yaya" yace "Lafiya
lau, what's wrong?" Kin cewa komai tayi, Ammi sai kallonta take, can kuma
dai ta tashi ta wuce daki, Imaan ta hade kai da gwiwa, ya mike ya dawo kusa da
ita ya durkusa yana dubanta yace "What happened imaan, an maki wani abu
ne?" Ta dago kanta ta wani turo baki tace "Ba komai" shiru yyi
yana kallonta, can yace "Tashi mu je Abba na kiran ki" Mikewa tayi
shima ya tashi ya nufi kofa ta bi bayansa. Sai da suka yi nisa ya juya yana
kallonta da kyau yace "Baxa ki gaya min kukan me kike ba" tace
"It's just mood swings" Bata jira cewarsa ba tayi wucewarta ya bi ta
da ido, can dai ya bi bayanta, Xaunawa parlon Abba tayi bata yadda sun hada ido
ta Abban ba ta gaishesa ya amsa yace "What did you want for ur Qur'anic
graduation?" Shiru ta d'an yi, can tayi murmushin karfin hali tace
"Abba kawai a min abinda aka ma su Maimoon" yace "To maa Sha
Allah, you can go" Mikewa tayi ta masa sai da safe ta nufi kofa Mujaheed
ya bi ta da ido har ta fita, wanka imaan tayi bayan ta koma part din su, tana
saka kayanta text ya shigo wayarta ta kalli screen din, dauke kai tayi ganin
Sadeeq ne ya turo sakon ta karasa shirinta ta bar wayar nan gaban madubi ta
kashe wutan dakin ta kwanta, ta jima bacci bai xo mata ba sai juye juye take
daga karshe dai baccin ya dauketa. Washegari Friday duk da ynda imaan ta dinga
jin ciwon kai haka ta shirya ta wuce islamiyya, karfe sha daya kuma ta dawo
gida, har sannan dai bata wani dawo normal ba don scene din abinda ya faru jiya
ya ki barin memory dinta da ya fado mata kuma sai gabanta yayi mugun faduwa,
sai dai tana ganin motar daddy a parking space alamar ya dawo taji dadi har
ranta. Tana fitowa wanka ta dau wayarta da ta boye a press ta bude, missed
calls din Sadeeq taga ni har uku da text biyu bayan na jiya da daddare da bata
bude ba, ta ki bude text din tayi lock din wayar ta mayar cikin press dinta ta
gama shiryawa sannan ta fito parlor, Tana murmushi ta karasa ta gaida Daddy da
ya fito parlor, daddy na kallonta yace "Lafiya lau Mamana, are you
okay" ta buda ido tace "Sure daddy, ya hanya?" Yace "Alhmdllh,
ya shirin walima" tayi yar dariya tace "Daddy Ina yi" Ammi dake
jera ma Daddy abinci a dinning sae hararanta take, Daddy yace "Ga tsaraban
ki can Ammin ki ta sa maki a fridge" cike da jin dadi tace "Toh
nagode daddy"
Da yammacin ranan Imaan ta tafi kai ma Inna abinci, sallama
tayi ta shiga parlon, Daddy ne xaune parlon sae Kawu Bala, ga Umma ma xaune ta
sha xumbulelen hijab kanta a kasa, ga wasu kawunnanta har biyu su ma a parlon,
Inna dai na xaune kan tabarma tayi tagumi tana sharban kuka, ganin imaan ta
shigo cikin rawar murya tace "Wllh bata fi wannan yarinyar muka aurota ba
Talle" imaan ta gaishesu ta ajiye abincin hannunta ta fita.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
58.....
Daddy ne xaune parlon Inna bayan su kawu Bala, Umma da
kawunnanta sun fita, Inna ta tace "Wlh wllh Bukar ka ji rantsuwar musulmi
ko, to Rukayya ta ci albarkacin ka ne, don ina jin kunyan ka ainun, amma idan
ta sake ko da min kallon banxa ne a gidan nan to aurenta da Ahmaduna ya kare ba
ruwana, xan nuna mata ni na haifesa ba wani shegen ya haifa min shi ba, yanxu
ma ni wllh darajar ka da na Mujaheed ta ci, tunda ni nayi wahala da shi kuma
yana min biyayya, kai ma kuma kana min biyayya, matar da ma ba wai son matar ka
take ba amma ka dinga tsayawa tsakanin ka da Allah kan lamuranta, ita bata ki
ba ma ta cutar da Aisha ba wllh, kai kuma duk ka damu da lamarinta, duniya dai
ba gaskiya" Shi dai daddy bai ce komai ba yana sauraranta, tabe baki tayi
ta mike tace "Ni dai ba ruwana, kawai mata ta wani taho min da rubabbun
mutane su ban hakuri, wllh ta ci albarkacin Mujaheed da sai na masu koran kare
ba kunyar kowa xan ji ba, ba ruwana, matar da ba tsoron Allah gareta ba balle a
raga mata" Daddy dai ya bi ta da kallo har ta shiga daki sai ga ta ta fito
ta xauna tana kallonsa tace "Kana ji na Bukar, ni dai duniyar nan kaf ba
wanda bai san imaan takwarata bace, kuma kowa yasan ita kenan Allah ya baka,
ita kenan jikata a wajen ka, Toh ya dai fi babu ai, sabili da haka gaskiya ni
dai ga dubu ashirin dina da nake ta tarawa a samo tikeken rago da ya kusa d'an
mariki a yanka mata na saukan nan, Allah kuma yasa na tsoron Allah xata yi,
yayi mata albarka ya hada ta da mijinta na gari wato wannan yaro
Bulasawa...." Shiru Daddy yayi yana kallon kudin da take mika masa, tace
"Haba ka amsa mana yaro, ka bar min hannu a sagale" d'an murmushi
yayi yace "Amma Inna kin fa san ba ita kadai xata yi sauka a gidan nan
ba" tace "Toh ai shi sa nace takwarata" ya girgixa kai yace
"Ai Ummi ma takwarar ki ce" Bude Baki tace "Yau naga abinda ya
isheni, ji Bukar da wani xance, to cewa nayi ban sani ba, ai xuciya ma na son
mai kyautata masa, Ummi ko gaisuwar kirki tana min a gidan nan balle in dinga
tuna cewa takwarata ce, ni dai ba ruwana a dinga jin tsoron Allah, yanxu meye
ma'anar hakan da kafada salon Ahmadu ya ji ya kullace ni, ni dai gashi ka tafi
bakin ka a leko ka siyo mata tikeken ragon da nace a kawo mata" mikewa
Daddy yyi yace "Toh Allah ya saka da alkhairi, sai anjima" tace
"Toh kai dai ka ja bakin ka kayi shiru, abinda naman ma duk xa a tsakura
ma kowa da kowa a gidan" shi dai daddy bai ce komai ba har ya fita.
Washegari asabar da wuri aka tashi a gidan aka fara girke girke, Ammi da Aunty
ne ke girkin a nan bayan kitchen din su Aunty, abinci kala uku xa suyi, sae
soye soye, tun daren jiya dama Ammi tayi samosa da spring rolls, Aunty kuma
tayi cakes da doughnuts, Umma sai kai wa da kawowa take kamar dai me neman abu
fuska a daure, ta shiga ta fita, babu dai wanda ta ce ma sannu da aiki cikinsu,
su ma babu wanda ya kalleta, Maimoon ne da Ummi suka shigo kitchen ko wanne
sanye da Sabbin dinkin da Daddy yayi masu na atamfa gaba daya su uku masu
saukan har da imaan, da Hijab dinsu ash colour yana jan kasa, sosai suka yi
kyau, Aunty tace "kun yi kyau sosai, amma kuna kallon agogo dai koh"
Ammi tace "Allah ya sa ita wancan ta gama shiryawan" Maimoon tace
"Shayi kawai xa mu sha sai mu je mu kirata" Muryar Umma suka ji bakin
kofar kitchen din tana kallon Ummi cike da masifa tace "Kin wuce kin cire
kayan nan na jikin ki ga lace can na dinka maki ko sai na 6ata maki
rai???" Ummi ta kalli atamfar jikinta sannan tace "Lace umma?"
Xagi umma ta kunduma mata tace "Don uwarki xo ki fita ki cire kayan nan,
ko ubanki ne yayi maki" Ummi ta nufi kofa ta fita, Ammi dai sai aikinta
take, Aunty ta tabe baki ita ma ta ci gaba da aikinta, tsaki Umma ta ja ta bar
bakin kofar kitchen din, Maimoon ta hada masu shayin cup biyu ta fita, karfe bakwai
da kusan rabi Imaan ta taho part din su Maimoon sanye da nata atamfar da well
ironed hijab dinta har kasa, sosai tayi kyau Aunty tace "Iyye daughter
tayi kyau sosai, amma ko yar powder baxa ki shafa ba Imaan" Yar dariya
Imaan tayi ta gaida Aunty, Aunty ta amsa tace "Ki tafi daki ki dau powder
Maimoon ki shafa kin ji?" Tana murmushi ta juya ta fita ta wuce sama,
dakin su Maimoon ta shiga ta dau powder dinta dake gaban mirror ta shafa, ta
goga chappete a lips dinta mai two colour, sosai tayi wani sanyayyen kyau kamar
warce tayi wani kwalliya, juyawa tayi ta fita dai dai fitowar Umma dakinta,
Sosai gaban Imaan ya fadi ta sunkuyar da kai har xata wuce maganan Sadeeq ya
fado mata, a hankali tace "Ina kwana" Umma na mata shegen kallo tace
"Kin sa6a gaisheni a gidan nan ne ko kuma gulma da kinibibi irin na uwar
ki, to ko da mistake kika sake gaisheni a gidan nan wllh sai na gaura maki mari
munafuka kawai sauran ciwo" Ita dai Imaan bata ce komai ba ta dinga sauka
stairs, Umma ta bi ta da kallon tsana karara, har wani tafarfasa xuciyarta
yake... Imaan na komawa kitchen Aunty
tace "Ba gashi kin kara kyau abin ki ba, don kana da kyau kuma baxa ka
kara da wanka ba" Imaan dai murmushi kawai tayi, Aunty tace "Kin dai
karya koh?" gyada mata kai tayi, Aunty tace "Toh maxa ki tafi suna
jiran ki a mota, sai mun xo in sha Allah" Imaan har ta nufi kofa ta juyo
ta marairaice tace "Aunty xa ku taho da Inna?" Aunty ta d'an yi
dariya tace "Tabb, to ban dai sani ba, amma kila mu taho tare" Ammi
dai sai kallonta take ganin yanda ta rame kamar warce tayi ciwo na sati daya,
Imaan tayi masu sallama ta fita kitchen din, ta tadda su Maimoon har sun shiga
mota suna jiranta, ita ma ta shiga motar aka wuce da su islamiyyar su, Imaan
dai sai Muraja'ah take a xuciyarta har suka iso islamiyyar tasu, Da yake
islamiyyar sananne ne, kuma duk yawanci yaran masu shi sosai ne a makarantar,
manya manyan mutane ba na wasa ba ne suka halacci taron waliman saukan, ciki
kuwa har da 'yan gidan Bulasawa gaba daya, da shi kan sa Bulasawan, duk da
yaran second wife dinsa kadai ke xuwa islamiyyar wato su Mariya da kanninta
banda kannin Sadeeq don su tasu islamiyyar daban, amma hakan bai hana
Mahaifiyar Sadeeq xuwa wajen saukan al-qur'anin ba, su Daddy da Abba da kawu
Bala da Kanin Inna Audu d'an tsut kamar yanda ta kirasa duk sun xo gun saukan
su ma, Sai da dalibai uku suka yi karatu sannan su Aunty da Ammi suka iso
wajen, Imaan ta ji dadin ganin Amminta don ita ce seventh xata yi karatu Mariya
kuma ta shidda, Maimoon ta goma, Tunda
Imaan ta hada ido da Sadeeq dake wajen tare da mahaifinsa gabanta ya fadi bata
sake yarda ta kalli direction din da suke ba, lkci daya duk mood dinta gaba
daya ya canxa har aka xo kanta a karatun... And Sadeeq couldn't take his eyes
off her even for a second, both her tajweed and kira'ah were more than perfect,
babu wanda bai mayar da hankali kan karatun da imaan take na Surah Ad-dukhan
ba.... Soo maa sha Allah, ta kuma burge kowa na wajen, first 20 Aya ta karanta
na suran, Nan take kuma Bulasawa ya rubuta Check na 500 thousand ya mika ma
Sadeeq dake kusa da shi yace "For her, she recited very well" Sadeeq
ya amsa yana kallon mahaifin nasa, ba Bulasawa kadai ba, mutane biyu a wajen
sai da suka ma Imaan kyauta, domin suran da ta karanta is perfectly talking
about Islam, and those are who passed all their times playing, smoking,
drinking, infact committing all such of sins, idan kuma Allah ya aiko da Dukhan
daga sama su nemi gafara su tuba, daga ya dakatar su koma gidan jiya, Sadeeq ya
mike ya je ya sami daya daga malamansu dake co-ordinating wajen ya mika masa
check din yace "Daga Alhaji Ahmad Bulasawa xuwa ga dalibar ku Fatima
Abubakar Imaan" Malamin ya amsa da jin dadi yana masa godiya yace "In
sha Allah xai isa gareta" Mujaheed bai iso gun saukan ba sai karfe sha
daya tare da Safeenah da ta cakare cikin tsadadden lace sai xuba kamshi take,
Umma na ganinta ta dinga washe baki tana mata sannu da xuwa, ta mike daga
kujerar da take xaune tace "Xauna ga kujerah Safeenah" Safeenah dake
taunar cingam tace "A'a kiyi xaman ki Hajiya ga wani kujera can bari in je
in xauna" Mikewa Umma tayi da sauri ta dauko mata kujeran tace "Gashi
xauna" Safeenah ta ja kujerar duk da ido hudu da suka yi da Ammi da Aunty
dake wajajen a xaune dauke kai tayi ta xauna tana kas kas da cingam, umma taji
wani shegen dadi ganin abinda ta masu don sai murmushi take tace "In ji
dai gidan lafiya Safeenah?" Safeenah na juya ido tace "Qlau wllh
Hajiya" Da yake dalibai 20 ke saukan kafin karfe sha biyu da wani abu na
rana duk suka gama karatun, A nan kuma malaman suka yi announcing kyaututtukan
da Fatima Abubakar ta samu da wasu daga cikin daliban, tunda Imaan ta ji wai
Bulasawa da kansa yayi mata kyautan kudi gabanta ya dinga faduwa, Umma dake
wajen kuwa da taji amount din gaba daya hautsinewa cikinta yayi a wajen, ta
kasa xaune waje daya sai mutsu mutsu take, Aunty kuwa sai murna take tana sa
albarka, Mujaheed ya dinga kallon Imaan da ta ki yarda su hada ido da kowa,
hotuna aka shiga yi a wajen, kowa hoto yake son yi da Bulasawa dake kokarin
ganin ya bar wajen, Mariya ta ja Imaan daga wajensu Aunty tace "Come let
snap with my family plss" haka Imaan ta dinga bin ta har suka isa inda
familyn Bulasawan ke tsaye, Mariya ta ja ta xuwa gun Babanta tace "Abba xa
mu yi hoto da ita, she is Fatima by name" Bulasawa na kallonta yyi murmushi
yace "Maa sha Allah, keep it up Fatima" ta sunkuyar da kai tace
"Nagode Abba" Photographer
dake wajen ne ya dinga masu hoto, Sadeeq dake tsaye gefe yana kallonsu ya dawo
gefen mahaifin nasa, Imaan na ganin haka ta fara kokarin sulalewa Mariya taki
bari ta wuce har sai da aka masu hoton su hudu, gaba daya hankalin Umma na
kansu kamar idanuwanta xa su fito, ko fasa auren Mujaheed da Safeenah da aka
kusan yi kwanaki bai daga mata hankali kamar abinda ke faruwa yau ba, Wai
Bulasawa da kansa yayi acknowledging Imaan, duk Aunty na lura da ita, Mujaheed
dai na xaune shi ma sai kallonsu yake, Imaan suna gama hoto da Bulasawa ya bar
wajen bayan ya bada donation dinsa na progress din islamiyyar, hotuna Imaan
suka dinga yi da Mahaifiyar Mariya da kanninta, Mariya ta ja ta xuwa gun
Mahaifiyar Sadeeq tace "Mummy xa mu yi hoto" Mahaifiyar Sadeeq na
kallon Imaan da lovely smile tace "Ur recitation was sweet.. keep it
up" Imaan na murmushi tace "Thanks Ma" Tsayawa imaan tayi kusa
da ita aka fara daukansu hota tare da Mariya, Sadeeq dai bai daina kallon Imaan
ba, har dai suka gama hoto da family dinsa ta tafi gun su Aunty, nan ma suka
dinga hoto da su Abba da Daddy, Safeenah bata yarda ko da wasa suyi hoto da
imaan ba haka ma Umma, duk suka ga Imaan na wajen basa shiga hoton, Imaan da
Maimoon suka yi hoto da ya Yusuf da wasu daga frnds dinsa, shi dai Mujaheed na
xaune yana danna wayarsa, Imaan na kallonsa ta isa kusa da shi ta durkusa a
hankali tace "Yaya baxa mu yi hoto ba?" Daga kai yayi yana kallonta
da manyan idanuwansa, ta turo baki ta kama hannunsa tace "Ni dai ka taso
mu yi hoto plss" Ya d'an yi murmushi yace "To kira photographer din
mu yi a nan" Tace "Noo, background din baxai yi kyau ba, ba ga
flowers ba" Safeenah dake ta kallonsu ta karaso wajen kamar xata tashi
sama ta xauna kujeran dake kusa da na shi har tana neman faduwa, Imaan na
kallonta ta mike daga durkushen da take ta d'an tabe baki ta juya, Ba Safeenah
kadai ba har Umma kallonsu take tayi mitsi mitsi da ido gashi ba daman yin
komai ga Daddy da Abba a wajen, Mikewa Mujaheed yyi ya kamo hannun Imaan yace
"Toh let go" Umma tayi still inda take ta bi su da kallo, gun flowers
din suka nufa yana rike da hannunta, Mariya ya mika ma wayarsa duk da
photographer dake kokarin daukansu yace "plss snap with my phone also"
Imaan dai sai murmushi take, suna tsaye kusa da flowers din aka dinga kashe
masu hoto kamar xata shige jikinsa, Mariya ma na daukansu da wayarsa Mujaheed
couldn't help it but smiled sweetly, ta jinginar da kanta jikin shoulder dinsa
tana murmushin ita ma, Safeenah ji tayi kamar xuciyarta ta fashe, ga wani
tukuki da take ji a ranta, Umma dai sai murmushin karfin hali take tana gaisawa
da jama'ah tana kallonsu ta gefen ido, Aunty dai na ta rarraba ma jama'ah
abincin da snacks da suka kawo bayan sun ware na malamai da daliban saukan,
Ammi kuma ta dinga raba buckets da books, Su kam familyn Bulasawa nan suka bar
komai da suka kawo na sauka tun daga abinci, gifts, da dai sauransu suka yi
wucewarsu, tashin hankali gun Sadeeq ganin har suka wuce imaan ta ki ko da
kallon inda yake ba a cewa komai, tun da yake bai taba shiga tashin hankali na
wannan lokacin ba tun daga jiya har xuwa yau, saukan ma banda Aunt dinsa ta
tilasta sa da baxai xo ba, hatta Mahaifiyarsa sai da ta tambayesa damuwarsa gun
saukan ganin gaba daya he is moody yace mata ba komai har dai suka bar
makarantar bai ga fuskar tunkarar Imaan ba, ya dai je sun gaisa da su Abba da
Daddy, sai su Aunty da Umma, sannan suka bar wajen da family dinsa, kafin
azahar su Imaan suka bar islamiyyar a various cars xuwa gida, Tun da islamiyyar
ta manya ce babu dalibi cikin masu saukan da ke da niyyar bin d'an uwansa
dalibi gidansu kamar dai yanda ake yi yawanci, kowa kama gabansa yayi xuwa
gidan iyayensa, ni ko nace ko dadi... Lol. Imaan da Maimoon motar Mujaheed suka
shiga ta dalilin wayar Mujaheed din dake hannun Imaan don ita Mariya ta mika ma
da xa su wuce, Safeenah ta wani hade rai xaune a gaban motar Mujaheed na
driving har suka isa gida, yana gama parking Imaan na kallonsa a hankali tace
"Yaya ka tuna promise da ka min few years back?" Ya juya ya kalleta,
d'an murmushi yyi yace "Ban manta ba" tana murmushi ta sauka motar,
Maimoon ta mika masa wayarsa ita ma ta sauka, Mujaheed xai sauka Safeenah ta
rikosa fuska daure, juyawa yyi yana kallonta, tace "Ban ga fa'idar xuwan
mu gidan nan ba bayan an gama sauka, I think it's better mu wuce gidan mu
Doctor" Makullin motar ya jefa mata a cinya yace "Ki wuce gidan sai
na xo, I don't think u have the right to tell me what to do and what not to
do" daga haka ya rufe motar ya nufi part din su ta bi sa da kallo kamar
idanuwanta xa su fito.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
59.....
Karfe biyu imaan ta fito daga bedroom dinta bayan tayi wanka
ta canxa kaya xuwa daya daga sabbin kayan da Daddy yayi mata har kala biyar na
waliman, sosai lace din ya amsheta, Ammi ta gama jera abinci kan lallausan
carpet dake parlor, Tana kallonta tace "Ga abincin ku ke da Daddy" Imaan
ta karasa ta xauna kan carpet din tana bude warmers din tana murmushi, Daddy ya
fito daga daki ya karaso cikin parlon ya xauna saman lallausan carpet din shi
ma yana kallonta yace "I am proud of you sweetheart" Dariya tayi tace
"Daddy bayan ni ba ku ban gift ba kai da Ammi" yace "Let lunch
first" Plate ta dauka ta xuba masu abincin da daddyn nata, Ammi dai na
xaune parlon har suka gama cikin abincin, daddy na kallonta yace "Hope you
will also pass ur up coming exams with flying colors by the grace of God"
Imaan tace "Sure daddy" Daddy yace "Maa sha Allah" Makullin
mota ya fiddo aljihunsa ya ajiye kusa da ita yace "And this is my
gift" Imaan ya wara ido ta dau makullin tana kallo yace "A car?"
Ammi dai sai kallonsu take, cike da jin dadi Imaan ta rungume Daddyn nata tace
"I love you Daddy, Allah ya bar min kai, ya kara girma" Murmushi yayi
yace "Ameen, gobe xa a taho da motar but you won't ride anytime soon, may
be after ur waec" Imaan da ta rasa inda xata sa kanta sbda murna tace "Toh
daddy, Allah ya kai mu, nagode Sweet dad, Allah ya saka maka da alkhairi"
Yace "Ameen, clear this plates now" Mikewa tayi ta kwashe duk warmers
da plate din ta kai kitchen, ta fito daga kitchen kenan aka danna bell, Mikewa
Ammi tayi ta wuce dakinta, Imaan ta tafi ta bude Kofar, still tayi ganin Sadeeq
tsaye hannunsa rike da leda, sosai gabanta ya fadi lkci daya ta juya da sauri
ta bar bakin kofar Daddy na kallonta yace "Who's there?" Kasa basa
amsa tayi ta wuce dakinta, bayan few seconds Sadeeq ya shigo parlon da sallama
murya can kasa, Daddy na ganinsa yace "Welcome son" Sadeeq na
kirkiran murmushi ya karasa ya ajiye ledan hannunsa ya xauna kasa shi ma ya
gaida Daddy da ladabi, daddy ya amsa da fara'a yana tambayarsa ya mutan gidan,
yace "Alhmdllh Daddy" Ammi ce ta fito daki sanye da hijab, ganinsa ta
sunkuyar da kai tace "Sannun da xuwa" ya kalleta yace "Ina yini
Ammi" tace "Lafiya lau, ya gidan?" Yace "Alhmdllh, fatan an
watse taro lafiya" Ammi tace "Alhmdllh, mun gode Allah" dakin
imaan ta nufa ta bude kofar ta shiga ciki, xaune ta ganta can karshen gado ta
wani hade rai, Ammi tace "Wa kika ce ma Sadeeq xai xo gidan nan?"
Kamar xata yi kuka tace "Ammi ni wllh ban sani ba kawai ganinsa nayi"
Ammi tace "Toh sai ki tashi ki tafi ki kai masa ruwa da drinks ki dibar
masa snack" Ammi bata jira cewarta ba ta fita dakin ta wuce nata, Mikewa
Imaan tayi ta dau hijab dinta fari har kasa ta saka sannan ta fito, ta wuce
kitchen ta hada ruwa da drinks sai glass cup a tray, ta debi snack a wani plate
ta daura a kan tray din ta fito, kanta a kasa ta iso parlon ta duka gefensa ta
ajiye, Mikewa Daddy yayi ya dau wayarsa yana kallon Sadeeq yace "Let me
make a call outside" Sadeeq yace "Toh sai ka dawo daddy" daga
haka daddy ya fita parlon, Imaan xata tashi ya rike hijab dinta cike da damuwa
murya can kasa yace "Plss listen to me Imaan, don Allah ba don ni ba ki
tsaya ki saurareni, am begging you plss...." Kasa cewa komai tayi ta xaune
wajen ta hade kai da gwiwa ta fara kuka a hankali, duk ya rikice mata ya duka
on his kneels yace "Don Allah kiyi hakuri ki yafe min Imaan, it's a
mistake that will neva repeat itself again, don Allah ki min rai kiyi hakuri, I
have neva for once had the intention of making you angry" ita dai ta ki
cewa komai kuma ta ki dago kanta bata kuma fasa kukan da take a hankali ba,
cikin sanyin murya yace "Kin ji Fatima, ki yafe min don Allah, wllh bani
da nufin cutar da ke, I love you with every breathe of mine, I am wishing u to
be the mother of my kids, ban taba ma ya mace irin son da nake maki ba, I Neva
knew what true love is sai a kan ki, ni ba fasiki bane Imaan you can ask
Mariya, sure I do flex with friends and I am a player, but i am very selective
when it comes to mingling with girls, and mind you... ni ba maxinaci bane I can
swear to you by Allah who made me ban taba ba, I am a type of person that find
my opposite gender so irritating in every aspect, don't forget where I was born
and raised, sure it's strongly against the teaching of our religion but kema
kinsan to hug or kiss someone is part of our lifestyle back there, a haka na
taso cikin su, I tried my very best getting rid of that while here in Nigeria
kuma Alhmdllh there is improvement, wllh Imaan ban maki haka da niyyar in cuce
ki ko in 6ata ki ba, mata ma dake kawo min kansu ban bata su ba sai ke da nake
son aure? Kuma yanayin da nake shiga idan muna tare is something that I have
neva experience all my life, that's why kika ga ko xuwa wajen ki bana son yi
duk irin son ganin ki da nake I try my best staying away from u, plss Imaan
kiyi hakuri ki yafe min, sharrin shaidan ne, don Allah ba don ni ba ki dago
kanki ki kalleni in baki hakuri, na kuma maki alkawarin daga this very moment
har xuwa ranan da Allah xai sa a daura mana aure idan ke matata ce baxan sake
xuwa gidan ku ba, baxa kuma inyi requesting mu hadu ba, xa dae mu dinga waya
kawai...." sai a sannan ta dago kanta hawaye na xuba idonta, lkci daya
idonsa ya kada shi ma cikin sanyin murya yace "Don Allah kiyi hakuri
Imaan" a hankali tana goge idonta tace "Na ji?" Kamar xai mata
kuka har lkcn yana durkushe kan kneels dinsa yace "Kin hakura" a
hankali ta gyada masa kai, yayi murmushin karfin hali yace "Toh nagode
Imaan, Allah maki albarka" sunkuyar da kanta tayi, ya dauko ledan da ya
shigo parlon da shi ya ajiye gabanta yace "This is for you, I am very
proud of you today, Allah ya baki ikon amfani da karatun ki" ta kasa cewa
komai, ya mike yace "Ki ce ma Ammi na wuce, thanks much for forgiving
me" Bata iya tace masa komai ba ya nufi kofa ta bi sa da kallo, yana bude
kofa kafin ya fita murya can kasa tace "Nagode" ya juya ya kalleta
yayi murmushi sannan ya fita ya kulle kofar parlon, Bude ledan tayi taga
tsadaddun turarruka ne a cikin ledan har kala biyar. Daren ranan Imaan na
dawowa part din Inna ta je kai mata abinci suka hadu da Mujaheed xa shi gun
Innar, Ya katse wayar da yake yi yana kallonta, ta wara ido tace "Yaya
baka tafi ba?" Yace "Ehh wait for me a parking space yanxu xan
fito" tace "Parking space?" Yace "Ehh" tace
"Tohm" wucewa tayi shi kuma ya karasa part din Inna, Parking space
din nasu ta tafi gun motarsa ta tsaya ta jingina jikin motar, Bayan kusan minti
bakwai sai gashi, yana kallonta yace "I saw ur video... reciting, kinyi
kokari kadan, they are still some corrections in ur tajweed, so ban ma san
amfanin kyautar da aka dinga baki ba, may be dai Muryar ki ne yayi masu
dadi" on a serious note ya kare maganar, xaro ido Imaan tayi tana kallonsa
a sanyaye, lkci daya ta bata fuska ta sunkuyar da kanta, ko kallonta bai yi ba
yace "Matsa in bude motata" a hankali ta matsa masa daga jikin motar
ya bude, ta fara tafiya xata koma part dinsu, bin ta yyi da ido yyi saurin
jawota, kuka ta fara yi a hankali, ya dawo kusa da ita yana murmushi yana
kallonta gently yace "I was only joking Lil sis, ur recitation was superb,
I love it, and that was what I expected" turo baki tayi tana kallonsa ya
ja hancinta yana kallon eyeballs dinta murya can kasa yace "My future kids
will have no problem with recitation of the holy Qur'an" Bai yi xaton xata
ji abinda ya fada ba coz his voice was so low, as if he just murmured the
sentence, ya ga ta xaro ido tace "Ehh?? Ur future kids that their mother
is already hating me from day one" sai kuma tayi murmushi tace "Ba
ruwana, idan dai sun xo gida xan dinga koya masu in sha Allah..." Yyi
murmushin sa mai kyau yana shafa kansa yana kallonta, Jan hancinta yyi bai dai
ce komai ba ya bude back seat ya fiddo Laptop sabo dalll, ya mika mata yace
"My promise 3 years ago" wara ido tayi ta rungume sa tightly tace
"Waow... Nagode yayana, I love ittt, you kept to ur promise" Mujaheed
ya ji gaba daya kafafuwansa sun kasa daukansa ya jingina da motarsa ya lumshe
ido and hold her closely to himself, Saketa Mujaheed yyi da sauri jin an bude
kofar apartment dinsu, Imaan ma ta ja baya tana kallon direction din, Umma ce
ta fito tare da Hajiya Saude xata rakata, imaan na ganinta dama ta bar wajen da
sauri ta dau hanyar apartment dinsu, Umma ce ta fara hangota sai kuma ta fara
kalle kallen parking space din don ganin ita da waye tana ganin Mujaheed ta bi
bayan imaan da mugun sauri Hajiya Saude na biye da ita, fixgota Umma tayi tace
"Uban me kike yi gun Mujaheed, me ya kawo ki wajen sa, meye wannan a
hannun ki??" Umma ta kwace laptop din tana xaro ido tace "Meye wannan
din ya baki?" Mujaheed dama na ganin haka ya taho gun su da sauri kafin
imaan da ta wani 6ata fuska tana kallon umma tace komai yace "Noo Bata aka
yi as gift na walima shine ta ke nuna min" Wani mugun kallo umma ta watsa
masa tace "Take nuna maka kayi mata me, don tana karuwanci an bata laptop
kuma sai ta taho nuna maka?" Da mamaki yake kallon Umma yace "Haba
Umma, why all this" tsawa ta masa tace "Questioning dina kake yi?
Sharri nayi mata ba iskancin take ba, ai wllh ko qur'ani xan iya dafawa in
rantse iskanci take yi, ance maku a banxa yaron nan ke kashe mata kudi, ai
kawai sai dai Allah ya shirya mana xuri'a, amma sai ta kawo wani shegen laptop
ta nuna maka kayi uban me da shi??" Imaan dai kallon umma kawai take
hawaye cike idonta, Hajiya Saude ta karbi laptop din tace "Lallai kam
Allah ya shirya mana xuri'a amma dama waye bai san 'ya yan masu kudin nan
ba" Mika ma imaan laptop din tayi tace "Karbi, Allah kuma ya shirye
ki" Imaan taki amsar laptop din hawaye ya cika idonta, Umma tace
"Sake mata tsiyarta mu wuce idan baxa ta amsa ba" daga haka umma ta
wuce, Mujaheed ya sa hannu ya amshi laptop din hannun Hajiya Saude, ta bi bayan
umma tana kyabe baki, Imaan ta fashe da kuka tana kallonsa, Bin uwar tasa yyi
da kallo xuciyarsa na tafarfasa shi ma, har suka fita gate, kamo hannunta yayi
ya wuce bayan apartment dinsu da ita suka tsaya cikin lallashi yace "Stop
those tears imaan, she only said that to please her self, eraze her talk off ur
mind now" shessheka ta fara yi, ya hade rai yace "Baxa ki daina kukan
ba" goge idonta ta fara yi, ya sa hannunsa yana share mata idanuwan nata,
murmushi yyi murya can kasa yace "You are taking ur pride to it rightful
place in sha Allah Lil sis" turo baki tayi, sai ta basa dariya ya ja
hancinta a hankali yace "My pretty stubborn Lil sis" ta sunkuyar da
kanta bata ce komai ba, Mika mata laptop din yyi ta amsa yace "Yi wucewar
ki ciki, on Sunday sai ku xo gidana tare da Inna in baki sauran gift din
ki" make kafada tayi tana turo baki, yace "Why??" Ta wani hade
rai tace "I dislike ur wife, I don't know.... I just don't like her"
kasa cewa komai yyi yana kallonta, can a hankali yace "But it's also ur
home, gidana ai naki ne" tace "Toh ai ita bata san haka ba, ko baka
gaya mata bane" Dariya sosai ta basa don sae da yyi, ta tabe baki tace
"Ni dai bana sonta kwata kwata" ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh
ni xan xo in dauke ku da kai na" imaan tace "Toh, kasan me Sadeeq ya
bani" shiru yyi yana kallonta, lkci daya mood dinsa ya canxa, can dai yace
"Waye shi?" ta wara ido tace "Lahh baka san sa ba Yaya? Toh ai
shikenan, sai da safe" daga haka ta wuce da sauri tana murmushi ya bi ta
da ido. Har titi umma ta raka Hajiya Saude suna tafe suna hira, Hajiya Saude
tace "Toh ke kin dage tana karuwanci ta ya kika san haka" Umma tayi
dariya tace "Ni kuwa xan fi kowa sani, ae ki bari kawai in Allah ya yarda
sai uwarta Aisha ta ji kunya, sai ta gwammace a juyarta ta dauwama bata rufe
bakin mutane da sauran ciwo ba" Hajiya Saude tace "Toh Allah ubangiji
ya tabbatar da hakan, amma fa kamar Familyn Bulasawan ma naga sonta suke"
Umma da taji ranta ya wani baci tace "Toh ae baxa su so d'an su ya auri
warce ya lalata a waje ba, kuma muna nan sai Imaan tayi ciki a waje ba a
dakinta ba" dariya sosai Hajiya Saude ke ta yi, Umma ta ja tsaki tace
"Baki san ni bane, wannan yaron shine ajalin ita da uwarta, ba sai wani
rawan kai suke uban ya mata kyautar rabin miliyan ba"
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
60....
Imaan na gyaran dakinta da safe misalin karfe tara bayan ta
gama shiryawa Ammi ta shigo dakin tana kallonta tace "Jira kike in xo in
fito da ke Imaan" Imaan tace "Yanxu xan fito" Fita Ammi tayi
daga dakin Imaan ta bi bayanta ta shigo parlon tana kallon Inna dake xaune ta
cakare cikin atamfa da hijab tayi tagumi, Imaan ta dau well ironed hijab dinta
tana kallon Inna, Inna ta ki kallonta ta tabe tobaki tace "ku dai ba ku da
tsari, baku da kirki, tun jiya ince maki xamu fita amma saboda walakanci ki bari
in xo in xauna kamar gantalalla ina jiran ki..." Imaan tace "Ni shayi
kawai xan sha, kullum sai ki sa mu dinga xuwa gidan mutane da asuba basu tashi
ba ana mana walakanci" Inna ta xaro ido tace "Ni babu wanda ya taba
walakanta ni, ki ji tsoron Allah, Ba kuma ruwan ki idan ma tsakar dare xan je
gidan mutane, wllh ki daina haka ba halin xaman gidan miji bane..." Imaan
bata tanka ta ba ta wuce kitchen ta hado shayi ta dau bread ta fito, sai da ta
ji ta koshi sannan ta ajiye sauran bread din, Inna dai ta wani tsuke fuska,
Imaan ta dawo parlon tace "Na gama" tsaki Inna ta ja ta mike ta nufi
kofa tace "Mutane dae ba tsoron Allah a xuciyarsu, jiya mu yi magana rimi
rimi ki dawo nan uwar ki tace kar ki shirya, to ta ma kanta ae, dama
bafillatani kuma, kai dai kayi ta fatan ku rabu lafiya da shi, ni dae ba
ruwana" Ammi dai na goge gogenta a parlor bata ce komai ba, Imaan na
kallon Ammi a hankali tace "Ammi sae mun dawo" Ammi ta masu Allah ya
kiyaye ta ci gaba da aikinta. Adaidaita Imaan ta tsayar masu a bakin titi, Inna
ta shige adaidaitan ta xauna, Imaan na kallonsa tace "Kabala xaka kai
mu" da mamaki Inna tace "Kaji jaraba ko yaro, ina ruwanta ita dai ba
kawai ta shigo ka ja adaidaitan ka ba" Yayi dariya yace "Ae da
gaskiyarta Kaka, gwara ta tambaya ta ji ko xan je" Imaan ta wani hade rai
ta shiga, Inna tace "Bata da wayo ne, ai ku din ba wai tsoron Allah gare
ku ba, da mutum ya tsaya gaya maku inda xa shi sai don mugunta ku fasa xuwa can
din, shi sa nake shigewa kawai abu na in xauna, Atoh... ina xan iya da gantalallu"
Murmushi kawai mai adaidaitan yake yi yace "Gaskiya ne Kaka" Dai dai
kofar gidan Ta Rasulu mai adaidaitan ya tsaya, Inna tace "Kaga gidan
aminiyata ta Rasulu kenan na xo, kuma babu irin motar da babu a gidan 'ya ya
na, kawai dai nayi ra'ayin hawa adaidaita ne, ka ga kuma ni tsohuwa ce sai an
bani ba wai miji gareni ba, kai koma da mijin yanxu shi ma ta kansa xai yi ya
ji da tsufansa, don haka ni dai ba wata mai kudi bane, har naira 30 an sha kawo
ni gidan ta Rasulu shekaru kusan goma da suka wuce wllh..." Tana magana
tana duba jakarta ta fiddo naira 70 ta mika masa, yace "Kaka kudin ku dari
biyu da hamsin ne" Inna ta wani xaro ido tace "Kai barawo ne d'an
nan, a kan tsohuwa kuma satan naka xai kare yau sabida baka tsoron
Allah??" Tuni Imaan ta shige cikin gate din gidansu Ta Rasulu, tana shiga
parlon ta Rasulu ta fito dakinta da sauri tana cewa "Shegu dawowa ku ka yi
marasa xuciya??" Ganin Imaan ce tace "A'a ke kuma daga ina?"
Imaan ta xauna ta gaisheta Ta Rasulu ta amsa tace "Ca nake mayun yaran nan
da na kora ne suka dawo, duk sun dameni watakil ma iyayensu basu tashi ba, ni
kuma sai aka ce masu an hallito ni ne don wahalan jikoki ya kasheni, to ni ko
su Muhammadu da..." Shigowar Inna yasa tayi shiru tana kallonta tace
"A'a ashe tare ku ke Asabe" Inna na nuna Imaan tace "Ke din nan
baki da kirki wllh, kina ganin mutumi xai fara ci min mutunci kan kudi kika
gudu kika bar ni daga ni sai raina, ban ga amfanin biyo ni da kika yi ba ma don
wllh sai a iya kama ni a nakada min shegen duka a titi kiyi tsit abun ki, wa xai
maka haka banda bare dama, ae Bukar baxae min haka ba" Ta Rasulu na kallon
Imaan ta rike ha6a tace "Gaskiya kam naka baxai maka haka ba dama, toh ya
ku ka kare da mai mashin din Asabe" Inna tace "Yan arxiki suka taso
suka basa dari biyu a nan waje ni ban ma san su ba, ni dai nace Allah ya isa
don 70 nayi niyyar basa tunda ba a kasa ake hako kudin ba" Imaan ta wani
daure fuska kamar xata yi kuka, Ta Rasulu tace "Ae yanxu yawanci duk
barayi dake fashi da makamai a da ne suka koma aikin adaidaita, amma dai ai
gwara haka koh? Da ace suna shiga gidajen mutane" Inna tace "Wllh
nima nayi tunanin haka don har sai da na tambayesa ko barawo ne shi, kuma baki
gansa ba bakikirin malam, ni dai da kyar idan yyi Imani lokacin da yake ganiyar
fashi da makaman" Ta Rasulu ta shimfida mata tabarma tace "Tunda ku
ka rabu lafiya ai Alhmdllh, ya su Ahmadu da Bukar" Inna ta xauna tace
"Ahmadu yana nan lafiya, Bukar kuma yana can gun neman na kai, maganar da
kika ce sai na xo xa mu yi jiya da rana, wllh gaba daya hankalina ya kasa
kwanciya ni dai ina idar da sllhn asuba na fara aikace aikace na gama na sa
ruwan xafi nayi wanka, na fito na shirya, na kada shayi da burodi na sha sannan
na fito, wannan mata dake xaune ita ta 6ata min lkci banda haka da tun sassafe
ma xa ki gan ni gidan nan" Ta Rasulu tace "A'a gwara da kika xo dama,
to ni dai naje na samu mutumi kamar yanda muka shirya, kuma ga maganganu dai ba
dadi wllh, wannan yarinya dai dake xaune gaskiya ido yayi katutu a kanta, da
matsala ba kadan ba...." Inna tayi kwafa da karfi tana gyada kai tace
"Ya tsole kuwa idon don ubansa, ko ma na wasu shegun ne, su rasa wanda xa
su sa ma ido sai Imaan? Tabb lallai lalacewa ta tabbata wai jikar Patuu xa a sa
ma ido " Ta Rasulu tace "Atohhh, ga dai shi nan ya bada icce da xa
tayi ta wanka da kuma na sha, da na hayaki, duk na sati guda kuma ku rufa min
asiri ko da kuskure kada tayi tsallaken kwana bata yi ba don ni ba wahalalliya
bace, ba ku ji kafata da na dawo ba kamar xan daddatse su in huta, ni banda ma
ta ki ce Imaan din ina ruwana da lamarinta, tunda muke da uwarta ina ga in dai
ta tako gidan nan to Asiya ce ta haihu, to ina dalili, kawai albarkacin ki nake
wannan wahalan, sannan abun tsoro da tashin hankali fa ce min yayi na kusa da
ita sosai ne ke son ganin ya tarwatsa rayuwarta, ke kya yarda Asabe?? Wllh kar
ki bari tayi wasa da Magungunan nan...." Inna tayi tagumi tace "Amma
dai me yasa yanxu ba a tsoron Allah ne ta Rasulu, mu xamanin mu duk inda ka bi
tsoron Allah ake kaca kaca ba wasa, kowa ya saka Allah a rai, yanxu ko tsoron
Allah yayi karanci, to ko dai gun aikinsa ne aka sa ma 'yar sa ido ince ya
hakura da aikin ya dawo mu xauna Allah xai rufa asiri??" Tsaki ta Rasulu
tayi tace "Ka ji ki da rikicin tsufa, ce maki aka yi fa na jikin ku ne ke
son cutar da ita" Inna tace "Ehh lallai xai cutar da kansa kuwa koma
waye, xai san jikata yake nufin cutar wa, to yanxu dai abinda xai faru yanxu
shine... Kowa dai yasan ni yar gaskiya ce sabili da haka baxan yi abinda bai
kamata ba, shiryawa kawai xa mu yi ni da ke mu koma wajen, in sha Allahu ko
nawa ne ni xan biya a mayar da nufin sharrin da ake ma jikata kan 'ya yan masu
bin ta da sharrin, ba shkkn ba??" Ta Rasulu tace "Haka ma xa ayi,
yanxu dai bayan kwana biyu ki taho ki kwana nan don da asuba xa mu fita amma
gaskiya sai dai mu sami karyar da xan gilla ma Asiya da mijinta don sun ce in
daina jajibe jajibe, ni ko jajibe jajiben da nake na neman lafiyata ne da na
jikokina da na 'ya ya na, yanxu abinda duniyar baki daya ba gaskiya wa xai
xauna, bana bi ta nasu ba basu san komai ba su yara ne" Inna tace "Ai
ki kyale yaran yanxu mun dai haifesu ne bamu haifi halinsu ba, nima dai kafin
in fito sai na gilla ma Ahmadu karyar don ba lallai ya yarda ma in taho
ba" Ta Rasulu tace "Atoh, wa xai xauna" ita dai Imaan na xaune
fuska daure sai kallon Tv take, inna bata bar gidan ta Rasulu ba sai kusan
karfe sha biyu, Ta Rasulu ta dauko naira Hamsin ta bata wai su hau mota, Inna
ta tabe baki tace "Da dai ba masu fashi da makamai suka koma yin d'an
sahun ba, ba ruwana ajiye gantalalliyar hamsin din ki ina da dari xan lallabasa
ya kai mu gida" Sabulun wanki kwaya daya ta Rasulu ta dauko ta mika ma
Imaan tace "Ga shi kya wanke 'yan kampai, ni dai bani da komai dakin duk
maroka sun xo na kwashe masu komai, gashi wata bai kare ba" Imaan ta amsa tace
"Nagode" har bakin titi ta Rasulu ta rakasu Inna na rike ledan
Magungunan hannu bibbiyu tsabar muhimmanci da ta basu, Ta Rasulu ta tsayar da
adaidaita tace "Kai yaro nan nan malali xa ka kai su, kaga dai ba miji
gareta ba ya rasu, nawa xa ka kai ta?" Mutumin yace "Dari uku
Kaka" ta Rasulu ta buga adaidaitan tace "Toh je ka, mu ma neman dari
ukun muke kuma ba mu ta6a fashi da makamai ba mu dai" Mai adaidaitan na
dariya yace "Nawa xa ku bada Kaka?" Inna tace "To ko dai ya kai
ni gidan Mujaheed kawai, tun da ya tare sau daya naje gidan" Ta Rasulu
tace "Toh shiga, ko nawa ne Mujaheed din xai bada" Inna ta shiga tana
kallon Imaan da tace "Ni gida xan wuce" Inna ta kalli ta Rasulu tace
"Kinga jarababba ko??" Ta Rasulu tace "Dalla shiga ku je, duk
saboda ke tsohuwar nan babu kokarin da bata yi amma baki gani, indan ta uwarki
ce ai sai dai a kashe ki mu taho muna kuka" Imaan ta shiga adaidaitan
kamar xata yi kuka, ta Rasulu ta juya tayi wucewarta, wani gidan mai me
adaidaitan ya shiga xai sha mai yana ba Inna hakurin xai siya fuel, Inna tace
"Na Bulasawa ne?" Yace "Ehh nasa ne" Inna ta washe baki
tana kallon wagegen filling station din tace "Ai d'a na ne wllh" da
sauri mai adaidaitan ya juya yana kallonta, tana nuna masa Imaan tace
"Kaga surkarsa kenan, kuma jikata ce ni na haifi ubanta, ita kadai garesa
duniya" Mai adaidaitan yace "Allahu Akbar" Inna tace "Kai
da kasan Allah kenan yaro" dariya ya fara yi sosai, imaan dai gaba daya
abin duniya ya isheta, kamar ance ta kalli gefenta taga Sadeeq coming toward d
tricycle, suna hada ido ya sakar mata lallausan murmushi, sosai ta ga ya rame,
ta sunkuyar da kanta da sauri, ya iso kusa da napep din ya xaga gun Inna da
fara'a yace "Kaka ina xuwa haka?" Salati Inna ta saki tana kallonsa
ta kalli mai napep tace "Toh ka gansa nan, ubansa ne mai gidan man
nan" Mai napep ya kalli Sadeeq da sauri, ya washe baki yace "Ai ko ga
kama" Inna tace "Atohh, ya xo checking ne da yake yau lahadi, kasan
cuta tayi yawa duniya yanxu" Sadeeq na murmushi ya gaisheta da ladabi ta
amsa baki har kunne tace "Wai gidan Mujaheed xai kai mu, Ashe gantalallen
mashin din nasa ba mai shine ya shigo xa mu siya" Sadeeq yace "Toh ku
sakko in kai ku ga motata can" Inna fito kamar jira take ta nufi motar ba
tare da ta bi kan d'an sahu ba, Imaan ta bi ta da kallo taji kamar ta nutse
kasa, Sadeeq dai sai murmushi yake, yana kallon mai adaidaitan ya ciro dubu
biyu ya mika masa, karba yayi yana masa godiya, a hankali Sadeeq na kallon
Imaan yace "Come down plss, there is nothing to worry about" sakkowa
tayi daga napep din, ya nufi motarsa ta bi bayansa, Inna har ta shige baya ta
xauna, imaan na hararanta ta bude front seat ta shiga, har suka isa gidan
Mujaheed Imaan bata ce komai ba a motar, Inna ce dai ke hira da Sadeeq tana
nuna masa hanya, xai yi parking a waje tace "A'a danna hann, xa su bude
maka" Sadeeq yace "A'a Kaka ai ba kowa ke son a shiga gidan sa
ba...." Inna tace "Ka ji ka Bukar, gidan Mujaheed ne fa"
murmushi kawai yayi ta bude motar tace "Kuma da gaskiyar ka, don ba ko
yaushe Mujaheed ke da kirki ba" Imaan na kallon Sadeeq tace "We will
talk later, thank you" Yana murmushi yace "I am happy I saw u after
few weeks" murmushi tayi masa, yace "Yaushe xa ku koma sai in dawo in
dauke ku?" Tace "Xa mu dai yi waya" yace "Toh shkkn, thanks
love" fita tayi ta bi bayan Inna, ya bi ta da kallo har ta shiga cikin
gidan, Imaan bata ko kalli Inna dake tsaye tana magana da mai gadi ba ta nufi
entrance din gidan ta murda kofa ta bude ta shiga cikin parlon da sallama murya
can ciki, Mujaheed ne xaune parlon yana operating laptop tare da Safeenah da ta
makalkale jikinsa kamar xa su dawo daya yana shafa dogon gashinta... Lkci daya
Imaan ta juya masu baya a hankali, sai kuma ta fice daga parlon, Inna dake
tahowa tace "Basa nan ne?" Imaan dai bata ce komai ba.
*Thanks for the prayers everyone, nagode kwarai, ga dai ni a garin wasu ko dadi, lol*
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
61
Mikewa Mujaheed yyi da sauri ya wuce sama, Safeenah ta wani
tabe baki ta ki tashi sai ma kwanciyarta da tayi kan kujerar, Inna na kallon
Imaan da ke tsaye tana kallonta tace "Lafiya kika fito ko basa nan
ne?" A hankali Imaan tace "Nima ban sani ba" Inna ta kutsa kai
ta shiga parlon tace "Ina kuma xa su ranan lahadi su bar kofa ba makulli
kamar tababbu, ko dai baccin asaran suke..." Suna hada ido da Safeenah
dake kwance Inna tace "A'a Safara'u, to tace min ba kowa, anya Imaan na da
lafiya ma kuwa, Ina Mujaheed din?" Safeenah ta mike tana kirkiran murmushi
tace "Sannu da xuwa Inna" Inna ta xauna tace "Yauwa sannu
Safara'u, ana ta shan iska kenan, to ba kya sha ba gari duk xafi don ma dai
akwai Ac, ai nima idan naji xafin yayi yawa dama daga ni sai yar shimi da xani
nake xama na parlor, kar xafi yyi min illa..." Mujaheed ne ya dawo parlon
sanye da jallabiya milk color kansa a kasa, Inna na kallonsa ta washe baki tace
"Ina kwana Mujaheed" ya karaso ya xauna yana dube duben parlon yace
"Ina kwana" tace "Lafiya lau, yau ba aikin kenan" Yace
"Sai da yamma" tace "Toh ai jiki da jini, in gaya maka daga
gidan ta Rasulu nake mun je mun yi sirrin mu shine nace bari in biyo mu gaisa
kafin mu koma gida" magana take masa amma gaba daya hankalinsa na kan
kofa, Inna tace "Sai kuma wannan yarinyar tace min baku nan, kai kaji
walakanci..." Bata rufe baki ba kamar jira yake yace "Tana
Ina??" Inna tace "Oho ni dai ba na shigo ba, dama tun da muka fito
take min walakanci tana ganin mai adaidaita xai min rashin kirki ta gudu ta bar
mu..." Mujaheed bai ce mata komai ba ya mike ya nufi kofa Safeenah ta bi
sa da kallon gefen ido, Bai ga Imaan a waje ba ya karasa gate yana kallon mai
gadi yace "Warce suka shigo yanxu da kaka ta fita ne?" Yace "Ehh
ta fita" Mujaheed ya fita gate din, can ya hangota har ta kusa titi, ya fi
minti daya tsaye yana kallonta kafin ya juya a hankali ya koma cikin gidan,
Inna na kallonsa tace "Ta ki shigowa ne halan? Rabu da ita ban iya wahala
ni dai ai ta aan hanya" Bai ce mata komai ba ya wuce sama Safeenah da ta
wani daure fuska ta bi sa da wani kallo. Bayan kusan minti talatin Mujaheed ya
sakko downstairs sanye cikin kananun kaya hannunsa rike da makullin mota, Inna
na xauna ga plate din farfesun kaji gabanta tana ta yaga tana ma Safeenah hira,
Safeenah dai na xaune sai kallonta take uninterested, Inna na kallon Mujaheed
tace "Ina kuma xa ka?" Yace "Ba dadewa xan yi ba...." Daga
haka ya fita parlon, da sauri Safeenah ta mike ta dau Hijab ta bi bayansa, Inna
na cewa "Maxa je ki ku yi sallama" Har ya shiga mota Safeenah ta
samesa cike da shagwaba tace "Ina kuma xuwa sweetheart, bayan ka min
alkawarin baxa ka fita ba yau" Ya tada motar ba tare da ya kalleta ba yace
"Ba jimawa xan yi ba" Tace "Ohk then, bari in raka ka" sai
a sannan ya kalleta yace "I don't think it's necessary Safeenah" da
wani expression take kallonsa, yace "Forget about the previous plan on
what to cook, tunda grandma na nan kiyi tuwo kawai with vegetable soup, I will
be back soon" tana masa wani kallo bluntly tace "Wllh baxan yi ba,
sai ka taho da tuwon daga inda xaka yanxu..." shi dai ba kulata ba ya rufe
motarsa ya gama warming mota ya danna horn mai gadi ya bude masa ya fita.
Mujaheed na isa gida yyi parking a waje, ya shiga compound dinsu, tun da ya
shiga yake kallon part din su Imaan, gently yake tafiya, ya kalli apartment
dinsu sannan ya wuce, yana isa part din su Imaan ya danna bell, sai kuma ya
bude kofar yyi sallama ya shiga, Ammi ta leko daga kitchen taga ko wanene,
gaisheta yyi ta amsa tana welcoming dinsa ta fito, Bai xauna ba yace "Dama
kawai na shigo mu gaisa ne" tace "Toh nagode, ya gida?" Yace
"Alhmdllh" tace "Maa sha Allah" ba tare da ya kalleta ba
yace "Imaan na ciki ne?" Tace "A'a" da sauri ya juya yana
kallonta, tace "Yanxu na aiketa taje kai ma Aunty sako" Bai san lkcn
da ya sauke ajiyar xuciya ba yace "Toh, sai anjima" tace "Allah
ya bamu alkhairi" fita yyi parlon ya wuce part din su, Umma na xaune
parlor da Rahma suna magana kasa kasa, Umma na kallonsa da murmushi tace
"A'a sannu da xuwa Mujaheed, yanxu ko nake cewa bari driver ya dawo xa mu
je can gidan Hajiya Balaraba daga nan sai mu biya naka, tunda ku ka tare ban je
ba" ya xauna ya gaisheta ta amsa tace "Toh ina Safeenar?" Ya
mike yace "Tana gida tace a gaishe ku" Umma ta bi sa da kallo ganin
sama xai wuce tace "Ina kuma xaka?" Yace "Xan dau wasu takardu a
daki" Daga haka ya haura sama, murya can kasa Rahma tace "Ita fa
Mariyan ma ba kowa take kulawa ba wllh Umma, bari dai Ummi ta dawo ki ji, ai
ajinsu daya har schl" Umma tace "Toh ita Imaan din ta ta6a xuwa
gidansu Mariyan ne?" Rahma tace "Suna xuwa da Maimoon sosai ma"
Umma tace "Atoh, Da bata xuwa ai baxa su santa ba har su mata kyauta gun
sauka, har fa da yin hoto da uwar yaron da kishiyarta" Rahma tace
"Imaan da bata kula maza amma saboda taga d'an mai kudi ne she didn't think
twice kafin ta fara kulasa, kila ma a gidan nasu suka hadu" Umma tayi wani
murmushi, murya can kasa tace "Toh xa ki yi abinda nace maki din?"
Rahma tace "Toh umma ai ba shiri muke da ita ba fa, gwara ma Ummi"
Umma tace "Toh yanxu ai xata dawo..." Dakin Aunty Mujaheed ya bude
yana kallon ciki, Maimoon ce xauna kasa kusa da Aunty dake xaune kan stool tana
mata kitso, Imaan kuma na xaune kasan rug tana kallonsu, Imaan na ganinsa tayi
saurin dauke kai, ya shiga ya rufe kofa idonsa a kanta, Maimoon ta gaishesa ya
amsa, Aunty ta sake kitson da take tace "Welcome son" Mikewa Imaan
tayi tace "Toh Aunty ni xan wuce" Aunty tace "Au kin fasa kitson
kenan, dama nasan baxa ki yi ba, kice ma Ammi xan shigo nan da anjima"
Imaan dake murmushi don ita kanta tasan kawai dai tace Aunty ta mata kitson ne
amma ba yi xata yi ba, lokaci daya murmushin fuskarta yyi fading ganin Mujaheed
ya fita dakin, tana ganin haka ta hade rai ta koma ta xauna tace "Toh
tunda xa ki je shikenan, sai mu koma tare" Aunty tace "Toh
shkkn" Mujaheed ya fi minti biyu tsaye corridor ganin bata fito ba ya bude
kofar dakin, Aunty tace "Yau dai yan miskilancin na kusa ne ko doctor, Ina
yini toh?" D'an murmushi yyi yace "Ina kwana Aunty?" Tace
"Atoh, ka shigo Ina welcoming dinka kayi kamar baka ji ba kuma ka
fita" ya shafa kai a hankali yace "An kira ni ne a waya na fita"
Aunty tace "Ohk, ya amarya?" Yace "Tana gaishe ku" Aunty
tace "Toh muna amsawa" duk irin yanda ya kafe imaan da ido bata yarda
ta kalli direction dinsa ba, har ya juya ya fita, Imaan bata bar part din Aunty
ba sai da ta gama ma Maimoon kitso suka koma part din su tare da Auntyn, har
sannan kuma Mujaheed na xaune parlor, ya bi su da ido har suka fita Imaan ta
saci kallonsa suka hada ido da sauri ta dauke kai ta shige gaban Aunty tana
turo baki. Daren ranan Imaan na part din Inna suna dakinta, Inna sai famar rura
wutan dake kasko take da baki, Imaan kuma na tsaye kamar xata yi kuka, Inna ta
ajiye wutan tace "Ke dai ki daina haka imaan, ni wllh idan kina bani
wahala xan tattara lamarin ki in xubar a kwandon shara, ya xa ki dinga ban
wahala ina taimakon ki? Baxa ki cire kayan ba ki xo ki durkusa, kai wllh Bukar
dai ya haifi jaraba" Imaan tace "Toh wai ni kin manta bana son hayaki
ne, yanxu idan asthma dina ya tashi fa?" Inna tace "Meye kuma asma?
Kiyi ta kira ma kanki ciwo, Ke dai ki ji tsoron Allah, abinda nace d'an minini
xan yarfa a wutan ki shaka ko kadan ne sai ki fita da gudu, idan fa aka kashe
ki ko digon hawaye na baxan yi asara ba wllh" Imaan ta rungume hannu tace
"Wllh bana so ni dai, gwara inyi wanka da shi, haka kawai inje asthma na
ya tashi inyi ta wahala" Inna tayi tagumi tace "Kai ina shan wahala
ni patuu, ni dai ba don ki kadai Allah ya halitto ni ba wllh" tana fadin
haka ta mike ta dau kullin magani ta wuce bayi tana cewa "Sai ki cire
kayan, idan ya kama ma in cuda maki maganin da kai na sai in cuda maki baxan yi
asaran kudi ne a banxa ba" Imaan na turo baki ta fara cire rigar jikinta,
tana cikin cire skirt taji an bude kofar dakin, xaro ido tayi ta fasa ihu ta
durkusa a kasa, da gudu Inna ta fito tana cewa "Shikenan ta fada cikin
garwashi ta kai ni ta 6aro gun Bukar...." Inna ta gwalo ido ta kalleta ta
kalli garwashin wutar don ta tabbatar bata fada ciki ba, Inna na nunata tace
"Anya imaan xaki wanye lafiya da duniya kuwa??" Imaan da ta takure gu
daya tace "Ni dai Inna wllh kice masa ya fita" da sauri Inna ta kalli
kofa ganin Mujaheed tsaye ta xaro ido tace "Me xan gani haka?? Kai ya haka
xaka afko mana daki ba sallama, baka ganta a tu6e bane Mujaheed, yaushe ka xama
haka?" Shi dai bai ce mata komai ba ya juya ya fita, Inna ta tafe hannu
tace "Yau naga abinda ya isheni, toh tsaye ya gan ki da ya shigo?"
Kamar xata yi kuka ta gyada masa kai, Inna tace "Toh shi ya ga duhu wllh,
tashi ki shiga kiyi wankan ki, shi yaga duhu" Imaan ta mike ta dau towel
ta daura tana turo baki ta wuce bathroom, Inna tace "Kaji min gantalalle,
Toh wani salon iskanci ne wannan xai shigo maki daki kin tu6e?? Ni dai ba
ruwana, don mutum yyi aure kuma sai ya fiddo da fi'ilin iskanci iri iri, Toh
wllh shi ya ga duhu" Tana fadin haka ta sa makulli a kofar tace "Ba
ruwana" Tun daga wannan rana da imaan ta ga Mujaheed xata canxa hanya ta
wani daure fuska..... Inna na parlor ta daura kafa daya kan daya da yamma tana
kallon wani film Ummi ma na parlon ta gama mata kitso kenan, Inna sai tsine ma
boss din film din da suke kallo take, duk ta cika parlon da muryarta, Ummi sai
dariya take tana cin soyayyen nama da Inna ta yarfa mata a plate, sallama aka
yi bakin kofa Inna ta amsa tana kallon kofar, Sadeeq ne ya shigo da leda a
hannunsa, Inna ta mike da sauri tace "A'ahh sannu da xuwa Bukar, kai ne da
yamma haka, Bisimillah" ya karaso yana murmushi ya xauna, Inna tace
"Ya iyayen naka?" Ya xauna yace "Alhmdllh, suna gaishe ku"
Inna tace "Tohh ina amsawa wllh, Ummi tashi ki debo masa ruwa a fridge da
lemo, idan kuma baxa ki ba in tashi" Ummi dake kallonsa ta gefen ido ta
mike ta nufi kitchen, ba a dau lkci ba ta dawo ta ajiye masa tray din drink da
ruwa ya kalleta yace "Nagode" Ummi ta koma ta xauna tana kallonsa,
Inna na kallon Ummi tace "Toh kiyi wucewar ki ai mun gama kitson ko? Allah
maki albarka" Ummi ta wani hade rai sai kuma ta mike ta nufi kofa, ko ba a
gaya ma Sadeeq ba yasan kanwar Mujaheed ce don kamar da suke ba na wasa bane,
Inna ta tabe baki bayan ta fita tace "Toh sai ta wani xauna cikin manya,
ai bai dace ba" Sadeeq na shafa kai yana murmushi yace "Dama Ina son
xa mu yi magana ne Kaka" Inna ta gyara xama tace "Toh Bismillah, Ina
jin ka Bukar in ji dai lafiya" Yace "Lafiya lau, dama Kaka Abbana ne
ke min maganar aure tun da dadewa, na gaya masa yanda muka yi da ku a nan yana
ganin kamar kawai xance nake masa...." Inna ta katse sa tace "Aa ba
xance kake masa ba wllh su Ahmadu ne suka dakatar da kai, toh amma ni dama
faduwa ta xo dai dai da xama, ba ruwana yau xan kira Ahmadun a gama magana, in
sha Allah xuwa nan da Juma'ah ko lahadi xai ce ka turo magabatan ka, kwantar da
hankalin ka Bukar in Allah ya yarda komai ya xo karshe, Sakandari?? An dade ba
ayi sa ba in har xancen sakandarin xa su kara min, ni ba karamin aikina bane in
tura ku kano gidan kawu Salisu ku kai gaisuwan da sadaki can" ya d'an yi
murmushi, tace "Allah ba batun dariya ba, ai idan muka ci gaba da biye su
Ahmadu da Bukar sai mu yi sa6o mu hallaka, haka kawai su ja mana fushin
ubangiji kiri kiri suna fiffita abun duniya kan sunnar ma'aiki" a hankali
Sadeeq yace "Toh nagode Kaka Allah ya kara girma" Inna tace
"Atohh, duk ya ake ciki xuwa gobe xan kira ka kaji" Yace "Toh
xan koma kaka" tace "Toh Allah maka albarka" ya ajiye mata ledan
hannunsa yace "Ga turare na kawo maki Kaka" Inna tace "Kamar
kasan bbu komai dakina sai fankon gwangwanayen turaren na jera gaban
madubi" Yar dariya yyi ya nufi kofa ya bude, da sauri Ummi ta ja baya, sai
kuma ta fara tafiya ko takalmi bata tsaya sa wa ba, Sadeeq ya bi ta da kallon
mamaki bai dai ce komai ba ya fita ya sa takalmansa ya wuce, A gate ya kusa cin
karo da Imaan xata shigo compound din hannunta rike da pack din bottle water,
ta koma baya da sauri, ya wara ido ya fito murya can kasa yace "Baby"
Ta sunkuyar da kai tace "Ina yini?" yace "Lafiya lau, where are
u coming from?" Tace "Na je siyo ruwana ne" yace "Iyye
bottle water kike sha kenan" murmushi tayi bata ce komai ba, yace
"Toh kawo in taya ki kai wa ciki" ta girgixa kai da sauri tace
"A'a nagode" Bata fuska yyi yace "Plss let me help" Bai
jira cewarta ba ya kai hannu xai amshi ruwan, hannunsa na ta6a nata ta sake
ruwan ba shiri, shima kuma da sauri ya janye hannunsa ruwan ya fadi kasa,
dukawa yyi ya dauka yace "Ohh Subhanallah, sorry plss" Murmushin
karfin hali tayi ta shiga gidan ya bi bayanta, Xaune Imaan taga Umma da Ummi
kan fararen kujera a can Balcony dinsu Umma ta bata attention gaba daya, Imaan
ta dauke kai da sauri, shima Sadeeq hakan yyi har suka isa part din su Imaan,
imaan na kallonsa tace "When did you come?" Yace "Some minutes
ago, am tired Imaan na xo na sami grandma ne plss a ban ixinin in turo
magabatana ko ba yanxu xa ayi biki ba..." ita dai Imaan bata ce komai ba,
ya ajiye ruwan hannunsa a kasa, ta duka ta dauka tace "Toh nagode sai mun
yi waya" daga haka ta wuce ciki, ya bi ta da kallo sannan ya wuce yana
murmushi. Abba ne xaune parlon Inna tare da Mujaheed da xuwansa gidan kenan,
har Inna ta kai aya a xancen da take Mujaheed sai kallonta kawai yake, Abba dai
kansa na kasa, can Abba ya daga kai ya kalleta bayan tayi shiru yace "Toh
ai jarabawan ma saura wata daya da sati biyu in sha Allah Inna" Inna tace
"Ku kuka jiyo wannan kuma ni ina ruwana, ya xa ku dinga maida ni karamar
mutum gaban yaron nan, gaskiya wannan karan bana son magana da yawa sabili da
kar raina ya baci, ga abinda nace in dai kuna tsoron Ubangijin ku, meye kuma
wata daya da rabi Ahmadu? Shi auren ake gudu kuma yanxu ana rirrike boko hannu
biyu, Me yasa ku ke haka?? Ni dai idan na isa da ku gwara a hada bikin ma da na
wannan yaron Isuhu tunda an ma kusa kai sadakinsa" Mujaheed dake kallonta
har sannan yace "Don dai an jira wata daya da kwanaki ban ga wani damuwa
ba, hanxarin me yake??" Inna tace "Amma gaskiya idan xan yi maganar
arxiki Mujaheed ya daina shigo min parlona, a daina xuwa min da shi" wani
kallo Mujaheed ya dinga mata, tana kallon Abba da karfi tace "d'an bakin
ciki ne fa Ahmadu, ya xai yi aurensa
yaje can yana morewa da figaggiyar matar sa amma ya dinga yi ma yar Uwarsa
bakin ciki, haka yake so tayi ta xama a gida kamar ba mashinshini?" Mikewa
Abba yayi yace "Toh shkkn, xa mu ba yaron ranan da xai turo magabatan nasa
in sha Allah" a fusace Inna tace "Yaushe?" Abba yace "Nan
da ko kwana uku in Allah ya yarda sai a
hada bikin da Yusuf yanda kika ce" Inna tayi murmushi tace "Toh Allah
ya kai mu lafiya ya maku albarka" kallon Abba da ya nufi kofa kawai
Mujaheed yake har ya fita yana amsa maganar Inna da Ameen, can ya kalli inna da
ta mike ta fara kakkabe kujeru, yace "Kin kagu ta bar gidan kenan??"
A fusace tace "Ba ruwan ka, wai ma dai meye hadina da kai Mujaheed??? Ni
dai nasan na haifi Ahmadu amma wllh da babu abinda ya hada mu gwara kayi ta
kanka, kiri kiri ka dinga nuna ma jikata bakin ciki??" Yana murmushi ya
mike yace "In sha Allahu wannan auren da kike ta 6arin jiki a kansa baxa
ayi ba, kuma har tsayuwar dare sai na yi akan hakan" salati Inna ta saki
tana kallonsa, sai kuma ta fashe da kuka tace "Baxa ayi ba?? Ehh lallai ka
zama dan iska Muhammad, ita yar Bukar kake ma bakin ciki?? Me ta maka xaka mata
wannan fatan" ko sauraranta bai tsaya yyi ba ya fice daga parlon, a
hankali yake tafiya don shi kansa bai ma san lkcn da ya fada mata hakan ba.
Abba na komawa dama ya kira Daddy ya gaya masa yanda suka yi da Inna, Daddy dai
bai iya yace komai ba, Abba yace "So yanxu na yanke ranan Sunday as ranan
da xa ace ya turo parent din nasa, kai kuma sai ka dawo Saturday or
Friday" Daddy ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh shkkn Allah ya kai mu,
Allah yasa hakan ne mafi alkhairi" Abba yace "Ameen" daga haka
suka yi sallama ya katse wayar. Washegari Abba ya kira Sadeeq ya kuma basa
izinin turo magabatan sa ranan lahadi, Sadeeq was so happy, farin cikin da bai
taba yin irinsa ba duk tsawon rayuwarsa ya dinga yi ma Abba godiya kamar ya
masa albishir da aljanna, Mujaheed dai na xaune parlon shi ma don tun safe Abba
ya kirasa, amma banda danna wayarsa babu abinda yake, lkci daya ya dago yana
kallon Sadeeq suna hada ido ya dauke kai, ya mike ya kai wayarsa kunne yyi
excusing kansa ya nufi kofa hakan yasa Abba ma ya bi sa da kallo kamar yanda
Sadeeq yyi.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
62....
Ranan lahadi kamar yanda Abba ya tsara hakan ce ta faru, don
Mahaifan Sadeeq a ranan suka xo gidan nema masa auren Imaan, Bulasawa ne sai
kanninsa biyu, da abokansa biyu, da kuma wani kawunsa suka taho gidan, shi dai
daddy baya cewa komai don har ransa bai son aurar da only child din tasa a
lkcn, a da ya dau burin sai ta kusa gama University amma yanxu gaba daya Inna
ta gama ruguje plan din, kuma babu yanda ya iya, dubu dari biyar iyayen Sadeeq
suka bayar kudin gaisuwan da akwatuna har guda takwas da sauran abubuwan da ake
badawa a al'adance amma triple triple suka kawo komai, sannan suka ajiye ranan
da xa su dawo a saka rana, Umma tunda ta sami labarin shigowar su gidan ta kasa
xaune waje daya ta dinga safa da marwa a daki, can dai ta kira Hajiya Balaraba
duk ta sanar mata abinda ake ciki, Hajiya Balaraba tace "Toh meye abun
daga hankali Hajiya Rukayya, ke fa an gama baki tabbacin babu auren nan, ba abu
bane da xai taba yiwuwa, to meye abun damuwa kamar baki yarda da bawan Allahn
nan ba...." Hankali tashe Umma tace "Nasani Hajiya Balaraba ba wai
ban yarda bane, na ji fa har ynxu shiru shiru ba alamar komai, ko xuwa gidan ma
wllh yaron ya daina, ita kuma yarinyar gaskiya bbu wani linkage tsakanin mu,
bbu ta ynda xa a hadu har yau ban yi yanda aka ce min ba, ga lkcn na ta
wucewa..." Hajiya Balaraba tace "Bata tahowa bangaren ku ne?" Umma
tace "Sae ta yi wata ma bata shigo ba idan ba uwar bace ta aikota, shi ma
iyakarta dakin Amina" Hajiya Balaraba tace "Ke dai baki da dubara
wllh, ga dai wajen da take xuwa kullum wajen Hajiya Asabe, ke baxa ki hada wani
dubaran ba daga can" Umma ta d'an yi shiru kafin tace "Toh shkkn xan
duba, can din ma ni ba haduwa muke ba ko na je gaishe da tsohuwar, xa dai mu yi
waya xa a shigo min daki...." katse wayar tayi da sauri jin an bude kofa,
Aunty ta shigo da farin ciki sosai tace "Hajiya an kawo kudin gaisuwan
Imaan dubu dari biyar, kayan na gani Ina so kuma akwatuna takwas daga gidan
Alhaji Bulasawa...." Umma ta dauke kai ta mike ta fara kakkabe gadonta
tace "Toh Allah dai yasa ba yaudara bane, mu dai namu ido, wani kudin
auren kirki ne har dubu dari biyar ba ma sadaki ba kamar xa a siyar da
ita" Juyawa Aunty tayi ta fita dakin, Su Bulasawa na barin gidan Abba ya
sa su Ummi da Rahma da Maimoon su kwashi kayan su kai part din Inna, Inna ta
saki baki tana kallonsu suna shigo da kayan tace "Meye haka kuma?? Meye wannan
din" Maimoon na murmushi tace "Na Imaan" Inna ta mike da sauri
tace "Wa ya kawo?" Maimoon tace "Daga gidan su Sadeeq" tuni
Rahama da Ummi suka fice parlon xuwa dauko sauran, Inna ta saki wani kabbara
sai kuma ta xaro ido tace "Yaushe suka xo?" Maimoon tace "Basu
dade da tafiya ba" Xaunawa Inna tayi ta fashe da kuka tace "Allah
sarki Bukar, ita kenan fa garesa, ita kenan Allah ya basa gashi yanxu xai raba
sa da ita... Yanxu ya xai yi da ran sa" Shigowar Abba yasa tayi shiru tana
share hawayen idonta, Abba ya xauna ya gaisheta, ta amsa cikin rawar murya tace
"Yanxu shkkn raba Bukar xa ayi da Imaan ni patuu??" Abba dai bai bata
amsa ba ya ajiye ledan hannunsa a kusa da ita yace "Kudin gaisuwar da suka
bada kenan" Inna ta xaro ido tana kallon ledan kudin tace
"Nawa?" Yace "Dubu dari biyar" Inna ta saki salati tace
"Toh dama ku siya mata dankareren gwal ku ajiye kar a ta6a mata ko biyar
tunda ba wani xai mata xaman auren ba Ahmadu" Abba dai bai ce mata komai
ba ya mike yace "Xuwa anjima xa mu shigo da Abubakar" daga haka ya
fita parlon, Inna na murmushi ta daga hannu sama da karfi tace "Alhmdllh,
Alhmdllh, takwarata tayi goshi ni Asabe, Allah na gode maka Allah, Allah na
gode maka, ka bar min rai da lafiyar kai ta dakinta da hannuna in sa mata
albarka" sai kuma ta fashe da matsanancin kuka, Maimoon ta tabe baki ta ta
fita xuwa debo wasu kayan. Bayan Magrib Inna na share parlonta don ba a dade da
fitar Aunty da frnd dinta sai frnds din Ammi biyu ba sun shigo ganin kaya,
Yusuf ne ya shigo parlon bai dai xauna ba yana kallon Inna daga tsayen da yake
yace "Ina yini" ta mike ta ajiye tsintsiyar hannunta tace
"Lafiya lau Isuhu, sannu da xuwa bari in bude maka kayan, wllh babban
akwatin babu atamfar kasa da dubu hamsin, gaba daya Holland da England suka
xuba mata, ba fa lefe ne kayan sun gani sun kyasa ne..." Xata fara sauke
sauke yace "A'a ba sai kin bude ba, dama Allah ya sanya alkhairi na xo
maki, Allah yasa ayi muna da rai da lafiya" Inna tace "Atohh, Ameen
dai, dama ganin kaya ai sai mata, kuma ai rana daya xa ayi bikin da naka idan
Allah ya yarda, kai ka angwance kanwar ka ita ma haka" shi dai bai ce mata
komai ba ya nufi kofa yace "Sai anjima" tace "Mu jima da yawa,
Allah maka albarka, Ina nan ina lissafin wa enda suka shigo yi ma jikata barka,
har yan anguwar nan ina xuba ido in ga wa enda xa su shigo da wa enda baxa su
shigo ba, mutane uku dai sun shigo daxu, amma kaga Rukayya da Aisha ko keyarsu
ban gani ba kuma xan ji dalili gobe da safe, ita Imaan din ma ban ganta ba yau
gaba daya" shi dai tuni ya fita. Inna na xaune tana cin abinci aka bude
kofa, Mujaheed ne ya shigo parlon ta mike da sauri ta shige daki sai ga ta ta
fito da katon bargo ta rufa ma akwatin har tana neman faduwa, shi dai kallonta
kawai yake, ta tabbatar ko kalan akwatun ba a gani sannan ta koma ta xauna tana
ci gaba da cin abincinta tace "Wa alaikumussalam" Yana tsaye yace
"Ina yini" tace "Lafiya lau" Bai kuma ce mata komai ba ya
juya fita parlon ta mike ta rufe kofar tace "Gaskiya xan kira Ahmadu ya ja
ma mutumin nan kunne ya daina shigo min nan, yaje can ya ji da xabiyar matarsa,
kwata kwata xuciyarsa ba shi da kyau, hassada bakin ciki duk sun taru sun masa
yawa, hooo ni patuu Allah ya ba ma Ahmadu Ya ya, sai dai Allah ya raba mu da su
lafiya" Imaan ta fito wanka kenan daure da towel taga wayarta na haske, ta
tafi gaban mirror ta dauka tana kallon screen din, pick din kiran tayi ta kai
kunne tana murmushi, shi yyi sallaman ta amsa a hankali, yace "Why ain't u
picking sweetheart" ta wara ido tace "Ina parlor ban jima da shigowa
ba" Yace "Ohk, ya gida?" Tace "Lafiya lau" yace
"Kayan sun maki dear?" Ta d'an yi murmushi ta sunkuyar da kai kamar
yana gabanta tace "Ai bn gani ba" da mamaki yace "Why?" Nan
ma dai murmushi kawai tayi bata ce komai ba, murmushin shi ma yyi yace
"Ina fa mancewa bafillatana xan aura, to ya xa ki yi da ni da kunyar ki
Imaan" ta turo baki tace "Nima bn sani ba" Yar dariya yyi yace
"Xa ki sani ne ma" ita dai bata ce komai ba, yace "I can't wait
imaan, in gan ni tare da ke as married couple" tace "Uhm ina son in
shirya, I just took my bath now" yace "You need a helping hand?"
Ta xaro ido tace "Noo, sai anjima" Bata jira cewarsa ba ta katse
wayar, d'an murmushi tayi ta fara goge jikinta. Umma ce xaune parlon gidan
Mujaheed tare da Safeenah dake danna waya tana mata sannu da xuwa, bayan sun gaisa
tace "A kawo maki ruwa Hajiya?" Umma tace "A'a Alhmdllh, ai daga
gida nake, Mujaheed din na nan?" Tace "Yana gun aiki" Umma tace
"Toh madallah, na xo don Allah xa mu yi wata magana da ke ne mai
muhimmanci" Safeenah na kallonta tace "Toh ina ji Hajiya" Umma
ta d'an yi shiru sai kuma tace "Wannan yarinyar da tayi sauka kwanaki
Imaan na xuwa gidan ki kuwa?" Safeenah na yatsine fuska tace "Yauwa
dama don Allah Ina son kawo maki wani kara Hajiya, kinga ni dai da Mujaheed xai
aureni ba wai ance min cousins dinsa xa su dinga xuwa min without good reasons
ba kuma ba tare da sanina ba, don haka, don Allah a dakatar da wannan yarinyar
daga xuwa gidana bana so, kada Watarana abu ya 6aci, sannan wannan kakar tasa
ita ma kusan kullum sai ta xo, don tare ma suke xuwa da cousin din tasa"
Umma ta xaro ido tace "Haba dai, kice suna xuwa nan sosai" Safeenah
ta tabe baki tace "Ai kam, ni dai na gaji, sannan idan Yarinyar ta xo tayi
ta nuna min isa da gadara a gidana ko gaisheni fa bata yi" Umma tayi
dariya tace "Toh ai a kanta ma na xo gidan nan yanxu haka, Kinga kenan
faduwa ya xo dai dai da xama" Safeenah ta bude ido sosai tana kallonta
tace "Toh Ina ji" Umma ta gyara xama tace "Kin san d'an gidan
Bulasawa??" Safeenah ta d'an yi shiru sai kuma tace "Gaskiya a'a, ina
dai following din yaransa mata a Twitter" Umma tace "Toh d'an sa na
fari ne ke neman Imaan din da aure, jiya aka kawo gaisuwa dubu dari biyar, da
akwatuna takwas da sauran tarakace me yawa, wllh da kinsan abinda uwar yarinyar
nan ta min a rayuwar duniya da kin tausaya min ke ma ki taya ni bakin ciki da
auren nan" Safeenah dake gwalo ido tace "D'an Bulasawa fa?? Me ya
gani tare da ita yake sonta?" Umma tace "Toh wllh sauran ciwo ce ma,
yau ciwo gobe lafiya tunda sickler ce" Safeenah na gyara xama tace
"Tabb, Shi sa take ma mutane wani gani gani kenan???" Umma tace
"Wllh don haka yanxu kawai so nake kada auren ya faru, ni dai ba shige
shige nake ba balle ace, ba ruwana da boka ko malam, kawai dai da yan dubaru xa
a raba su, kema kuma dole sai kin bada contribution" Safeenah tace
"Toh ta yaya?" Umma tace "Ba kince tana xuwa gidan nan ba, dama
nima naji labarin suna xuwa da kakar, shi yasa nace bari in xo in same ki"
Safeenah tace "Ba dai ko da yaushe su ke xuwa ba sai jefi jefi" Umma
tace "When last suka xo??" Safeenah tace "xai yi kusan wata
daya, Umma tayi tagumi tana naxari, can ta kalli Safeenah da ita ma tayi shiru
xuciyarta fal takaicin wanda Imaan xata aura, wai yaron Bulasawa, Umma tace
"Kinsan me xai faru yanxu Safeenah" Safeenah ta kalleta tace
"A'a" Umma tace "Ki jira sai Mujaheed din ya dawo sai ki ce masa
kwana biyu baki ga Inna ba, yaushe xata xo?? Ko kuma kyalesa kawai bari in baki
lambar Innar ki kirata sai bayan kun gaisa sai ki tambayeta kwana biyu shiru
shiru baki ganta ba yaushe xata xo??" Safeenah tayi murmushi tace
"Koh?" Umma tace "Ahaf jikinta na rawa xata xo, ai ita tana son
a dinga nuna ana ji da ita, kuma in xata xo da wuya ta xo ita kadai, Dole da
Imaan din take fita kinga shikenan Allah ya kawo mana ita har gida amma kar ki
yarda ki gaya ma Mujaheed kamar yanda nace da farko don akwai sa da kwakwalwa,
nan da nan xai gano ki" Safeenah tace "I thought as much, ga wayar ki
sa min lambarta" Umma ta amsa wayarta ta saka mata lambar Inna daga nata
wayar sannan ta mika mata, Safeenah ta amsa ta kai kunne, Inna na dagawa ta
rafka sallama, Safeenah ta amsa tace "Ina yini Inna?" Inna tace
"Lafiya lau, waye don Allah, ni dai aiki nake ta yi na bude ma mutane
akwatuna tun safe suna shigowa gani, kinsan duniya ba gaskiya yanxu sai a samu
rikakken barawo da xai boye abu ya wuce da shi shi sa nake sa ido"
Safeenah tace "Safeenah ce Inna" Inna tace "Waye Safeenah
kuma?" Safeenah ta tabe baki tace "Matar Mujaheed" Inna tace
"Ayyo, Safara'u ce, Toh sannu kin ji labarin an kawo kaya kenan?"
Safeenah tace "A'a ban ji ba" Inna tace "Atoh wa xai gaya maki
dama d'a bakin ciki uwa bakin ciki, wllh har yanxu ban ga keyar Rukayya ba,
Mujaheed kuwa tunda ya shigo ya gaggasa min magana ban kara ganinsa ba sai jiya
da aka kawo kaya, bakina a leko na shiga daki da gudu na dau katon bargona na
rufe ma yarinya kaya da shi tun bai kai ga gama kirga guda nawa bane, akwatuna
takwas ne da kyar ake xuge xif din, Toh me xance banda in gode Allah, har da
gwal na dankunne guda biyu da xobuna biyu fa a ciki, ni dai ba ruwana duk me ma
jikata bakin ciki Allah shi yasan yanda xai yi da shi, ko ke wllh baki samu
haka ba shi sa Mujaheed ya fito kiri kiri ya nuna bakin cikinsa a fili, kwana
nayi Ina al-ajabin abinda ya gaya min ranan wllh, isuhu kuwa har nan ya xo ya
min Allah sanya alkhairi...." Safeenah da Umma sai sauraronta suke don a
hands free Safeenah ta sa wayar, Umma ta wani kankance ido tana kallon wayar,
Safeenah ta tabe baki tace "Toh Allah ya kyauta, yaushe xa ki billo Inna
kwana biyu shiru" Inna tace "In billo a yashe ma yarinya kaya in
shiga uku Safara'u, ai ba xancen billowa sai na kai Imaan dakinta, sa ido yayi
yawa gwara in mike tsaye kyamm, toh ke baxa ki xo ganin kayan bane kike jira in
billo?" Safeenah ta kalli Umma, Umma ta gyada mata kai da sauri alamar
tace xata xo, Safeenah ta tabe baki tace "Toh xan shigo in sha Allah"
Inna tace "Atoh, sai kin xo, sai kiyi sauri don xuwa anjima xa a kai ma
kakarta ta wajen uwa ta ga kayan ita ma, sannan a maido min inyi gadin
kayana" Safeenah tace "Toh sai anjima sai na xo" Bata jira cewar
Inna ba ta katse wayar tana kallon Umma da tayi tagumi, Safeenah ta ja tsaki
tace "Ai nima sai inda karfina ya kare wajen ganin auren nan ya fasu wllh,
wato shi sa yarinyar ke ganin kowa banxa, ita a dole xata auri yaron Bulasawa
to taga samu ta ga rashi tunda har labari ya xo kunne na kuwa" Umma tace
"Wllh da kin gama min komai a duniya idan har muka hadu muka tarwatsa
lamarin nan, Kinga wahalar da na sha gun uwar yarinyar nan wllh kwakwalwarki
baxai dauka ba, ta dalilin uwarta aka min kishiya, aka kuma sakeni...."
Nan umma ta fara giggila ma Safeenah karya da gaskiyar abinda ya hadata da
Ammi, tana kai wa aya, Safeenah ta gyada kai tace "Ki kwantar da hankalin
ki Umma, ai tunda har labari ya xo kunnena an gama komai, dama kwata kwata na
tsani yarinyar tun daga ranan da na fara daura ido kanta, ki manta da ko wani
shiri da kike a da ki sa min ido" Umma tace "Atoh, shkkn.. Amma fa
baxan mance shirin da nake ba, don kunya ba kadan ba nake son Uwar yarinyar ta
kwasa a hannu, yanxu dai ki shirya anjima kije ganin kayan kada a dago komai a
rai" Safeenah tace "A'a rashin xuwan kawai ya fi, ban gani ba balle
raina ya kara 6aci" sai kusan yamma umma ta bar gidan ko digon ruwa bata
sha ba, amma ko a jikinta. Yau tun safe Mujaheed ke xaune garden din gidansa
har wajen sha biyu na safe, Safeenah ce ta shigo garden din cikin shiga ta
alfarma tana taunar cingam tana kallonsa tace "Doctor d'an baccin weekend
din ma gaba daya baka yi ba yau, ni dai yanxu fita xan yi, xan je can gida daga
nan kuma in tafi gidan ku in gaida su umma" Daga kai yyi ya kalleta calmly
yace "Baxa ki ba" Safeenah ta gwalo ido tace "Baxan je ba kuma,
mahaifiyata da taka xan je gaidawa fa" ya mike a d'an tsawace yace
"Nace baxa ki fita gidan nan ba Safeenah..." Daga haka ya wuce ya bar
ta wajen tsaye, ta ja tsaki tace "Don kana fama da miskilancin ka kwana
biyu sai ka sauke kai na, Toh wllh sai na fita" Kiran Umma tayi da wayarta
ba a dau lkci ba Umma ta daga, ko gaisuwa babu Safeenah tace "Toh gashi
dai ya ki bari na in fita wllh kuma yau ya kamata mu yi abinda ya kamata, kusan
sati daya kenan Mujaheed magana da kyar yake min a gidan nan, ni ban damu ba
don dama haka yake wani lkcn amma na wannan karan yyi yawa, tun asuba yake
xaune garden yau wllh kamar maraya, during weekdays kuwa dama sai nayi bacci
yake shigowa ya fice kuma da sassafe washegari, kwata kwata na rasa gane kansa
ban san me ke damun sa ba, ni duk wannan ba wani damuna yyi ba don a sauki na,
amma yanxu gaskiya ki kirasa ki masa magana don idan har ban fito ba yau shirye
shiryen mu ya ruguje ne kawai" Umma tace "Kyaleni da shi kawai, mu ma
nan ai ya fi satin bai xo ba, Ina ga halinsa na da ne ke kokarin dawowa"
daga haka umma ta katse wayar, Safeenah ta tabe baki ta wuce cikin gidan, tana
ta xaune parlor har bayan minti talatin ganin bai sakko ba ta mike ta wuce
sama, ya fito wanka kenan ta shiga dakin, yana mata wani kallo yace "Kin
xata kiran da kika sa mahaifiyata tayi min xai sa ko fita gidan nan ne
yau??" Ta nufesa tace "Wai me ke damun ka two days ne Mujaheed, dubi
fa you look so pale, and ni dai nasan lafiyar ka qlau" Ko kallonta bai yi
ba ya bude press dinsa ta rungume sa ta baya tana shafa chest dinsa cike da
shagwaba tace "Ni dai wllh ka gaya min meye damuwarka mijina" Bata
jira cewarsa ba ta juyo da shi ta rungume sa gam tana shige masa and she really
turn him on....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
63......
Safeenah na gama shirinta ta daura dankwali ya xauna dass a
kanta ta feshe jikinta da turare, ta juya ta kalli Mujaheed dake kwance idonsa
rufe, karasawa kusa da shi tayi ta xauna gefensa tana ta6a dogon hancinsa ta
kai bakinta fuskarsa a hankali tace "Dear ni xan wuce fa" Bude ido
yyi calmly yace "I said you are going no where Safeenah" ta xaro ido
tana kallonsa da mamaki don duk tunaninta ya hakura, can ta marairaice tace
"Haba dear, wllh fa ba dadewa..." Ya katse ta ya mike xaune fuska
daure yace "Nace baxa ki fita ba, am telling you this wllh idan kika fita
gidan nan yau xaki san wanene Mujaheed" Yana fadin haka ya mike ya shige
bathroom, tagumi tayi xuciyarta na tafarfasa ta bi sa da ido, can ta mike ta
fice daga dakin rai bace ta kira Umma tace "Toh wllh ya ki bari na in fita
Hajiya, taurin kan Mujaheed har tsoro yake bani" da mamaki Umma tace
"Ya ki barin ki kifito kuma??? To ina Ina xuwa..." daga haka Umma ta
katse wayar, Ba a dau lkci ba ta sake kiranta tace "Toh ai wayar tasa a
kashe yake" Safeenah tace "To ya kashe kenan..." Safeenah ta
tabe baki, Umma tace "Toh ki kai masa wayar ta ki" Safeenah tace
"A'a ni kam baxan iya kai masa ba, don he is very serious, ki bari dai in
ta lallabasa anjima xan kira ki" daga haka ta katse wayar. Imaan na xaune
dakinta sun gama waya da Sadeeq kenan ta shimfida darduma ta dau Al-quran dinta
ta ajiye a kai ta xauna kan darduman ta tankwashe kafa ta bude qur'anin, ba
karamin missing din islamiyya take ba yanxu, ji take da ma bata yi saukan ba,
Bude kofar dakin aka yi Ammi ta shigo, Imaan ta daga kai tana kallonta, Ammi ta
xauna gefen gadon tace "Karatun kike ko kin gama" Imaan tace
"A'a ban fara ba" Ammi tace "Kin ma ci abinci kuwa" Imaan
tace "Ehh na ci" Ammi tace "Ohk, kina ji na Imaan?" Imaan
na kallon mahaifiyar tata tace "Ehh ina ji Ammi" Ammi tace "Pls
Ina son ki dage da azkar sosai kuma a ko da yaushe, make that a part of you,
kuma da daddare xan dinga shigowa ina tashinki kiyi sallah...." Da mamaki
Imaan tace "Ammi me yasa" Ammi ta buda ido sosai tace "Me yasa,
dama sai da dalili mutum xai rike addu'a da tsayuwar dare, ae yanxu ne kika
lalace baki yi, amma da ai kina yi sosai" Murmushi Imaan tayi bata ce
komai ba tana bude kur'anin gabanta a hankali, Ammi tace "Ga kuma
jarabawar ku ya kusa shima sai ki dage da addu'an samun nasara kin ji"
Imaan tace "In sha Allah Ammi" Ammi tace "Good" daga haka
ta mike ta fita dakin, imaan ta fara karatun Qur'anin gabanta cikin cool voice
dinta. Da magrib ta tafi kai ma Inna abincin Inna ta ki barinta ta tafi ta
dinga sauke akwatuna tana bude mata tana cewa "Sai kace ba kayan ki ba yau
kusan kwanan su biyar kin ki ganin abinda ke ciki, ni dai ba ruwana, karere ma
da abun bai shafesu ba duk suna ta xuwa gani balle ke" xauna ni dai ki
duba, su Ahmadu da Bukar ma duk sai da na fiddo masu suka gani filla filla,
Imaan dai ta d'an yi murmushi ta xauna tana kallon kayan da Inna ke fiddowa
amma bata ta6a ba, Inna tace "Ni dai naga abinda ya isheni, to ki daga
mana ki dudduba ke fa babu abinda ya hadaki da fulanawa, ubanki bahaushe ne
gaba da baya, uwar ki ce bafillatana sai uwarsu Mujaheed, ban san me yasa suka
nace sai fulani ba, nima dai ubana bafillatani ne amma uwata bahaushiya ce,
mijina kuma bahaushe" Imaan ta turo baki ta dinga daga kayan tana kallo,
Inna tace "Wannan ai jaraba ne ke da kayan ki baxa ki duba ba, ga gwal din
can na hada da dankunnen da ya ta6a baki, bari in dauko ki gani" Daga haka
ta shige daki, Imaan na ganin haka ta mike cikin sanda ta nufi kofa ta fice
parlon da gudu ta sa takalminta tayi gaba, a hanya ta kusa cin karo da
Mujaheed, ta xaro ido ta juya masa baya da sauri xata bar wajen ya kamo
hannunta ya juyo da ita, kin yarda su hada ido tayi tace "Ina yini"
ya dawo da ita jikin bango ya dago kanta yana kallon kwayar idonta, kallonsa
ita ma take, lkci daya ta sauke idonta kasa a hankali, Murya can kasa yace
"Me yasa kike gudu idan kin gan ni Imaan" ta turo baki tace "Ni
fa ba komai yaya" ya kamo hannunta yace "A'a ki gaya min pls, me yasa
kike gudu" kasa cewa komai tayi, yace "Imaan" da sauri ta
kallesa jin yanda ya kirata, yace "Talk to me plss" Boye fuskarta
tayi tace "Ni bana son ka min fada shi sa nake gudu" yace "Fadan
me?" Kin cewa komai tayi ta sunkuyar da kai tana murmushi, ya kara kiran
sunanta, kamar xata yi kuka tace "Abinda nayi mana" Bai iya yace
komai ba sai kallonta yake, Jin shirun yyi yawa ta daga kai ta kallesa suka
hada ido, ta wara masa idonta tace "Amma dai baka da lafiya ne Yaya"
Ya sauke idonsa kasa yace "Probably" cike da damuwa tace "What's
wrong with you yaya?" Da kamar baxai ce komai ba sai kuma a hankali yace
"Akwai wani abinda ke shirin faruwa that will cause me lot of harms a
rayuwata, and sure that will be the end of my happiness..." Da damuwa
sosai tace "Subhanallah, what's that Yaya? Meye shi ka gaya min"
jingina yyi da bango bai iya yace mata komai ba, ta dawo tana facing dinsa ta
kamo hannunsa kamar xata yi kuka tace "Yaya don Allah ka gaya min meye
shi, meye xai faru and how are you to prevent it from happening" Taku da
suka ji toward direction dinsu yasa tayi saurin sake masa hannu bayan sun yi
ido hudu da Abba dake tahowa xai tafi part din Inna hannunsa rike da leda,
Mujaheed ya ja baya da sauri, ita ma hakan tayi, tunda Abba ya kallesu sau daya
ya dauke kai, sai da ya isa daidai su.. Mujaheed ya sunkuyar da kai cike da
karfin hali yace "Sannu da dawowa Abba" Abba yace "Yauwa
Muhammad ya family" Imaan ta sunkuyar da kai ita ma tace "Ina yini
Abba" Abba ya amsa sannan ya wuce xuwa part din Inna. Imaan ta kalli
Mujaheed tace "Yaya mu je plss ka gaya min" Bata jira cewarsa ba ta
kama hannunsa ta xaga baya da shi, ta xauna kan wani dakali tana nuna masa
gefenta tace "Oya xauna" murmushin karfin hali yyi ya xauna, ya
jinginar da kansa da nata yana kallonta ta gefen ido, tace "Toh ina ji,
tell me what's it kuma ka gaya ma su Abba kuwa??" Mujaheed ya jawota
jikinsa murya can kasa yace "No I didn't, and it's too late" kallonsa
kawai Imaan take, kafin tace komai yace "Kin ga kayan ki da aka
kawo?" Rufe fuskarta tayi da sauri a shoulder dinsa tace "Ni baxan
iya ba" ya lumshe ido ya bude, a hankali yace "Yanxu dai aure kike
son yi ki tafi ki bar ni koh?" Ta xaro ido tace "Toh ae kai ma kayi
auren ka tafi ka bar ni" yace "Ance maki ina son auren nawa ne?"
Yar dariya Imaan tayi tace "Ehh baka sonta but you are enjoying ur
marriage, kuma tana haifa maka beautiful baby like her xaka fara sonta
sosai" kallonta yake ko kiftawa babu, cikin sanyin murya yace "Why
did u say I am enjoying my marriage imaan, how did you know??" Tana
murmushi tace "Ae na gani..." da sauri yace "Kika ga me??"
Taki yarda ta kallesa tace "Abinda na gani" Bai san lkcn da ya
rungume ta ba yace "Noo imaan, I can neva enjoy my marriage with Safeenah,
am only trying my best in fita hakkinta, ni kadai nasan abinda nake ciki imaan,
bana son Safeenah, warce nake so na kokarin kubuce min which I won't allow in
sha Allah" Imaan tace "Wai Aunty Farida, she told me her wedding is
next week ai, xan ma je tare da Maimoon" Ya runtse ido yace "I have
never loved farida, tausayinta kawai nake,
kuma burina a da in hada ta su xauna da wacce aka halitto ni domin ta, sbda
lalurorinta, ita ce macen da nake ma son da ni kaina ban san irinsa ba
Imaan" da surprise imaan ke kallonsa jin yace baya son Farida, a hankali
tace "Who is this lady Yaya? Ni ban santa ba, you've never tell me
anything about her, ita ma a kd take?" lkci daya idanuwansa suka kada
sosai, cikin sanyin murya yace "Na fara mata so na yan uwantaka, sannan na
kasance mai tausayinta matuka, ni kaina ban ta6a tunanin soyayyar da nake mata
xai rikide ya koma so na aure ba, tun bata san kanta ba nake sonta nake mata
hidima, na kuma koya mata sa6o da
ni...." Imaan dake ta kallonsa ta xaro ido kamar xa su fito tace
"Kamar dai yanda muka sa6a ko, To wacece kuma a Ina take yaya?"
Mujaheed ya dinga kallonta, Ta turo baki tace "Ni dai ka gaya min, kuma tasan
kana sonta kuwa?" Ya girgixa kai a hankali yace "Taki ganewa har
yanxu" Imaan tayi murmushi hade da tagumi tace "Toh nawa xaka biya ni
sai ka hada ni da ita in fallasa mata sirrin dake xuciyarka, Yayana kasan fa
you are very handsome..." Sai kuma ta fashe da dariya ta boye fuskarta a
jikinsa tace "Wllh kana da kyau, and you are a gentle man, tall, huge,
your beards are cute, so babu macen da xata iya resisting love din ka stop
being afraid xaka rasa ta, kila da gudu ma xata amince maka idan ka sanar mata,
wa ya sani ma ko ita ma tana sonka, it's bcos of ur handsomeness and ur
personality wannan rubabbiyar matar taka ke rawan kai a kanka, take ma mutane
walakanci, wllh sonka take kamar ta mutu, bata san you are only managing and
just enjoying...." Sai kuma ta yi shiru da sauri, Bai san lkcn da yyi wani
murmushi ba har sannan yana kallonta ya dago kanta taki yarda su hada ido yace
"Enjoying what?" A rikice tace "A'a ba haka xance ba
fa...." Ya lumshe ido yana shakan kamshin gashinta daga cikin hijab din jikinta
murya can kasa yace "I will enjoy soon with my lil sis, amma ba da
Safeenah ba...." imaan ta bude ido da sauri ta kallesa tace
"Wacece?" Ya bude ido shi ma yace "Ita warce nake so mana"
imaan tace "Toh are you paying me to help you out?" Yace "Ko nawa
kike so kuwa, amma before then sai kinyi kokarin sa su Abba a dakatar da
maganar kawo sadakin ki next week" da mamaki tace "Why? My being
betrothed won't stop me from helping u out yayana" Ya girgixa kai cikin
sanyin murya yace "Shine babban abinda xai sa ki kasa taimakona
Imaan" Ta xaro ido tace "Yaya kai fa ka riga kayi auren ka, to ni
baka son nayi auren?" Ya kalleta yace "Auren dai kike son kiyi ki bar
ni" dariya tayi sosai tace "Kai ma ai ka yi" yace "Amma ai
ina xuwa ganin ki kullum" tace "A'a ni dai ba wajena kake xuwa ba,
wajen Inna kake xuwa" yana kallon kwayar idonta a hankali yace "Wllh
duk ranan da na xo gida ban ganki ba bana iya bacci da daddare" Da mamaki
Imaan ke kallonsa tace "Saboda me?" Ya sauke idonsa bai ce komai ba,
tayi murmushi tace "Kaga da matarka na sona sai in koma gidan ka in yi
waec a can" ya kalleta da sauri yace "A'a ba ruwanki da ita ki dawo
kiyi waec din ki kawai" ta make kafada tace "Bana so, Ni fa da gaske
Yaya bana son matar nan taka, I so dislike her" Yyi shiru bai ce komai ba,
can tace "Yaya na fara jin yunwa fa, xaka bani lambar yarinyar ne yanxu in
kirata mu yi magana?" Ya girgixa kai yace "A'a sai dai in kai ki
wajenta" tace "When?" Yace "Ko xuwa gobe" tace
"Toh Allah ya kai mu" da sauri ta daga kafarta tana kakkabe hijab
dinta tace "Wllh Yaya sauro a nan" Mujaheed ya kunna fitilar wayarsa
yana haska kafar yace "Sorry dear" yayi stretching legs dinsa ya
daura nata a kai bayan ya daga hijab din yana duba inda sauron ya cije ta,
shafa smooth leg din nata ya shiga yi yana kallonta, ta xaro ido ta buge
hannunsa tace "Aa ni bana so Yaya" a hankali yace "Why?" Ta
turo baki tace "Uhn ni bana so" tana fadin haka ta sauke kafarta kasa
ta mike tace "Toh sai goben Yaya" ya mike yana kallonta yace "Mu
tafi eatry tunda kina jin yunwa?" Ta juyo da sauri tace "Da gaske
Yaya" yana murmushi yace "Sure, tafi ki jira ni gun mota a waje"
tana murmushi tace "Toh" daga haka ta wuce ya bi ta da kallo har tayi
nisa, ya lumshe ido ya bude, kamar mai tausayin kasa ya dinga tafiya har ya
fita compound din ya sameta kusa da motarsa tana jiransa, yana bude motar ta
shiga front seat, shi ma ya shiga maxaunin driver tana kallonsa tace "Yaya
ni kaza nake son ci da drink kawai" yace "Ba sai mun je eatry ba
knn" tace "A'a can xa mu je" suna isa wani eatry babba yayi
ordering abinda tace, suna xaune wayarta a hannunsa tana kallon hotuna shi kuma
sai kallonta yake, hotunan da suka yi tare ne kadai a camera dinsa, sauran duk
WhatsApp images ne, hoton Safeenah ko kwaya daya babu a wayar tasa, Imaan ta
daga kai suka hada ido, ta xaro ido tace "Why are u staring at me that
way?" Bai ce mata komai ba yana kallon waitress dake ajiye masu gasasshen
kaza daya da aka yayyanka sae kamshi yake, Mikewa Mujaheed yyi ya tafi ya wanke
hannu ya dawo, imaan har ta bude drink din ta fara sha, ya xauna ya dau tsoka
daya yana kallonta yace "Bude bakin" dariya tayi tace "Cikin
mutane??" Yayi shiru yana kallonta, a hankali ta bude bakin ya kai mata
naman dai dai lkcn da suka hada ido da Sadeeq dake xaune eatry din da wani frnd
dinsa.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
64....
Imaan ta sauke idonta kasa a hankali ta cire naman daga
bakinta ta mayar ta ajiye, kallonta kawai Mujaheed yake ganin abinda tayi yace
"What happened?" Ta turo baki taki cewa komai, Ido hudu suka yi da
Sadeeq dake kallonsu har sannan shi ma, Sadeeq na ganin haka ya mike ya iso
inda suke yana murmushi ya dafa table din a hankali yace "Good evening"
sai a sannan Mujaheed ya sake kallonsa for d second time yace "Same to
you" Imaan dai ta kasa kallonsa sai bugawa xuciyarta yake, Ya ja third
chair dake wajen ya xauna yana kallonta da murmushi yace "How are you
doing" Bata iya ta kallesa ba cikin sanyin murya tace "Ina
yini?" Yace "Lafiya lau, kina ta enjoying da yayan ki" Mujaheed
dai sai cin namansa yake ba tare da ya kallesa ba, imaan ta ki cewa komai sai
wasa da ring din finger dinta take, Sadeeq na murmushi ya kalli Mujaheed yace
"Ya family?" Mujaheed yace "Alhmdllh, do you care joining
us..." Sadeeq na kallon naman yace "Ohh Alhmdllh, I just finished
eating now" daga haka ya mike yace "Alright, xan wuce, i was about
leaving na gan ku" Yana magana yana ma abokinsa sign ya taso su wuce,
Mujaheed yace "Ohk then" Daga haka Sadeeq ya kalli Imaan yace
"Toh malama, sai anjiman ku" ta kallesa suka hada ido, da sauri ta
sunkuyar da kanta a sanyaye tace "Toh sai anjima" juyawa yyi ya bi
bayan frnd dinsa da har ya nufi door din fita, Mujaheed ya kalli Imaan da ta
wani hade rai ya dai ci gaba da cin namansa bai ce mata komai ba, bayan few
minutes a hankali tace "Ammi xata fara nemana yanxu" ya kalleta yace
"Toh wa xai ci maki naman da kika sa na siya?" Ta turo baki tace
"Ni bana ci kuma" Bai tanka ta ba ya kira waitress ya sa tayi masa
take away din kazar, ya tafi ya biya bill din ya dawo rike da ledan naman ya
dau drink dinsa ba tare da ya kalleta ba yace "Tashi in maida ki
gida" Mikewa tayi fuska daure ta bi bayansa don har ya nufi hanyar fita,
bude front seat tayi xata shiga suka yi ido hudu da Sadeeq dake tsaye gun masu
suya dake wajen, dauke kansa yyi ya ci gaba da yi ma mai suyan magana, A
hankali Imaan ta shiga front seat din, Mujaheed ya shiga maxaunin Driver ya
tada motar suka bar haraban eatry din, Har suka isa gida bai ce mata ba ita ma
bata ce masa ba, Yana parking a waje ta bude motar xata fita ya riko hannunta a
hankali, kamar jira take ta fara shesshekan kuka tana kallonsa, lkci daya ya
rikice mata yace "Kuka kuma Imaan, what's wrong, me ya faru..." Cikin
rawar murya tace "Toh ba Sadeeq ya ganmu ba yanxu, Kuma...." Sai
kawai ta fashe da kuka sosai tana kallonsa, ya lumshe ido ya matso da ita kusa
da shi a hankali yace "Kuma me?" Tana shessheka tace "Let him
not think something different alhalin kai yayana ne kowa ma ya sani" shiru
yyi yana sauraranta, jin shirun yyi yawa ta daga kai a hankali tana kallonsa,
yyi murmushin karfin hali yace "Toh ba gashi kin fadi abinda ke kike
tunani ba da sauran mutane, wato ni yayanki ne, to shi ma you just assume hakan
xai yi tunani ni yayanki ne, tunda Ammi da Daddy ne suka haifeni sannan suka
haife ki" ta turo baki tana kallonsa tace "Toh kai ba yayana
bane?" Yace "Ehh in dai Ammi ce ta haifeni" ta wani hade rai
tana kallonsa tace "Kamar ya?" Yace "Kamar yanda na fada"
tace "To waye dama bai san kai yayana bane" Yana shafa kansa yace
"Waye dai bai san ni cousin din ki bane" ta xaro ido tace "What
did you mean??" Yace "I mean ki daina cewa ni yayanki ne so as people
will stop thinking we are from the same parent, we are only cousins imaan,
anything can happen" tabe baki tayi ta bude motar xata fita ya kamota yana
kallonta yace "Wait" tsayawa tayi har sannan bata daina kallonsa ba,
ya bude ledan naman ya dau daya ya kai bakinta, turo bakin tayi ta dauke kai
cikin sanyin murya yace "Plss..." Tace "Toh ba kace kai ba
yayana bane" yayi murmushi yace "Ehh ni yayanki ne, amma hakan ba
yana nufin iyayen mu daya ba, yau idan aka ce in aure ki, baxan ce A'a ai
kanwata ce ita ba, kowa yasan there is marriage between us, so stop confusing
people" kallonsa Imaan take ko kiftawa babu, a hankali yace "Oya bude
bakin" ta sauke idonta kasa ta ki bude bakin kuma, ya kamo hannunta yace
"Imaan" kallonsa ta kara yi, ya jawota kusa da shi idonsa cikin nasa
yace "Open ur mouth" a hankali ta bude bakin tana kallonsa ya kai
mata naman ciki, ta gutsura kadan ta dauke kai, yana murmushi ya kai sauran
baki yace "Toh shkkn kanwata" Bude motar tayi tana son fita yayi
saurin riketa yace "Since I got married nake missing din ki sosai unlike
before da nake gida that we are always fighting, from now on every magrib idan
kin je kai ma Inna abincin ki jira har sai na xo mun yi hira kadan kafin na
wuce kin ji" tayi murmushi tace "Toh ai da haka muke yi kafin ka
canxa ka fara ma mutane fada da ihu" ya kai tip din finger dinsa kan lip
dinta murya can kasa yace "Na daina yanxu dear, hira kawai xan dinga xuwa
muna yi, sai in taho maki da abun dadi" ta wara ido tace "To Yaya,
xan dinga jiran ka" ya daure ledan naman da drink ya mika mata yace
"Good girl" ta amsa tace "Toh nagode, sai da safe" yace
"Sleep tight" ta fita motar tana murmushi ta wuce ciki ya bi ta da
kallo. Parlor ta tadda Ammi tana cin abinci, Ammi na kallonta tace "Me
yasa kika dade, kuma ledan meye hannun ki?" Imaan ta xauna tace "Yaya
ne ya siya min" Ammi tace "Yaya kuma, a kan me ya siya maki?"
Tace "Ba komai, kawai dai ya siya min ne ya bani ai yasan ina so"
Ammi ta tabe baki ta ci gaba da cin abincin ta, Imaan ta bude ledan tace
"In debar maki Ammi?" Kamar jira Ammi take tace "A'a ki je kiyi
ta fama" Imaan tayi dariya ta mike ta wuce kitchen ta dauko plate ta juye
naman taci taci ta sha drink tayi nakk, sauran ta kai fridge tana kallon Ammi
tace "Ammi sai da safe" Ammi tace "Allah ya tashe mu lafiya,
don't forget perform ablution before going to bed, kuma kar ki manta kiyi
addu'a, kin ma yi isha kuwa??" imaan tace "xan yi yanxu Ammi"
daga haka ta wuce dakinta, wanka tayi ta dauro alwala ta fito ta shirya cikin
kayan bacci ta sa hijab har kasa tayi isha da shafa'i, tana idarwa ta dau
wayarta dake gaban mirror tana dubawa, xaunawa gefen gado tayi ta shiga kiran
Sadeeq don duk dare sai ya kirata yau kuma bata ga call dinsa ba, har ya gama
ringing bai dauka ba, Ajiye wayar tayi a hankali ta hau saman gado ta kwanta ta
rufe ido. Karfe biyar saura na yammacin washegari Ammi na xaune parlor tana
yankan pumpkin leaf aka bude kofar parlon Mujaheed ya shigo da sallama, ya
ajiye ledojin hannunsa na kayan shayi ya gaida Ammi ta amsa tana masa sannu da
xuwa yace "Daddy yace a kawo sakon" Ammi tace "Ohk Yusuf baya
nan kenan" Mujaheed yace "Ehh Ina ji" tace "Toh Allah yyi
albarka" yace "Ameen" har ya nufi kofa ya tsaya ba tare da ya
juyo ba yace "Imaan bata dawo schl ba?" Tace "Bata je yau
ba" ya juya da sauri yace "Me yasa?" Ammi na ci gaba da yanka
leaf din tace "Yau ta tashi ba lafiya" Yace "Subhanallah, likita
ya xo dubata amma?" Ammi ta girgixa kai yace "Ynxu likitan ba wai
yana xama bane, yana Sokoto yau, amma gobe xai dawo, mun dai je asibiti"
yace "Bacci take?" Ammi tace "Ina ji" shiru yyi bai ce
komai ba, Ammi ta kallesa hakan yasa ya nufi kofar fita kamar mai counting
steps dinsa yace "Toh Allah ya bata lfya" Ammi tace "Shiga ka
duba ko idonta biyu" Kamar abinda yake jiran ji kenan ya juya ya nufi
dakin Ammi ta bi sa da kallon gefen ido har ya shiga sai dai bai rufe kofar ba.
Kwance ya sameta ta rufa har kanta da duvet, ya xauna gefen gadon ya cire duvet
din yana kallonta, tun bai kai hannunsa jikinta ba ya ji temperature dinta is
so high, ta bude idonta da yyi ja tana kallonsa, kamar xata yi kuka ta fara kokarin
mikewa xaune tace "Yaya jikina xafi yake min sosai kuma Ammi ta ki bari in
kunna fan ko Ac" sai kuma ta fara kuka, ya jawota kusa da shi murya can
kasa yace "Why did u cover ur self?" Cikin rawar murya tace "Am
feeling cold" yace "Kuma shine kike son kunna fan" Bata ce komai
ba sai kuka take a hankali, ya daga kanta yace "An maki allura da ku ka je
asibitin?" Kai ta gyada masa tace "My legs are still aching har yanxu
da bayana" yace "An shafa maki magani kuma?" Ta gyada masa kai
tana goge hawayen idonta, janyeta yyi jikinsa ya dau Magungunan dake ajiye side
drawer har da na shafawa, ya mayar da saura ya bude na tube din ya cire gaba
daya duvet din, daga kneel dinta ya fara shafa mata xuwa toes dinta, ta dinga
kallonsa kamar xata yi kuka tana rike hannunsa tace "Yaya xafi" daga
kai tayi taga Ammi tsaye bakin kofar dakin, Mujaheed ya juya ya kalli kofar,
juyawa Ammi tayi ta bar bakin kofar, Imaan tace "Ka bar shi haka kawai ya
fara min sauki" Ya rufe tube din yana kallonta, jin wayarta na vibrate ta
juya da sauri ta dau wayar, Sadeeq ne ke kiranta, dagawa tayi ta kai kunne tayi
sallama a hankali, Daga daya bangaren ya amsa, ta gaishesa, yace "How are
you doing" cikin sanyin murya tace "Lafiya lau, why ain't you picking
ur calls" yace "Ba gashi Ina following calls that I have missed ba
ynxu" shiru tayi, shi dai Mujaheed kallonta kawai yake, Sadeeq yace
"Ya Ammi?" A hankali tace "Lafiya lau" yace "Maa sha
Allah, we will talk later sai anjima" daga haka ya katse wayarsa, ajiye
wayar Imaan tayi Mujaheed na kallonta yace "Kiransa kika dinga yi
knn?" Bata san lkcn da ta fashe da kuka ba ta kife kanta da pillow tace
"Kila fa fushi yake da ni Yaya, it's very unusual bai kirani ba tun
jiya" Kasa daina kallonta Mujaheed yyi, tana shessheka tace "I called
him sau biyu bai dauka ba, tun ba yau ba nake ce masa kai yayana ne ko ya xatan
karya nake masa, Yaya plss kai ka gaya masa da kanka kila xae yarda, we are
just close with you and nothing more, kai yayana ne" Mujaheed na kallonta
a hankali yace "We are just close and nothing more, what if it's totally
not so imaan kamar yanda shi yake tunani?" Ta daga kai da sauri tana
kallonsa tace "Toh ai ni da kai mun san ba haka bane Yaya, an taba ganin
inda Yaya ya auri Kanwarsa??? Hakan bai ta6a faruwa ba, don Allah Yaya make him
understand this, I am just sick of this, ni bai taba min haka ba" Mujaheed
yyi wani murmushi yana shafa kansa yace....
Sorry for the short chapter... don't forget i am still not
home but I am managing to type, in sha Allah xuwa karfe tara da wani abu ltr xa
ku ji ni.
Thank you.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
65......
Mujaheed yyi wani murmushi yana shafa kansa a hankali yace
"Saboda bai dau wayarki ba shine kika fara leg and backache kenan??"
Banxa tayi masa ta koma ta kwanta ta juya masa baya, ya dinga kallonta ko
kiftawa babu kafin ya mike ya nufi kofa yana murmushi ta bi sa da harara har ya
fita ya rufe mata kofa. Tun daga wannan rana Sadeeq ya daina kiran Imaan gaba
daya sai dai in ita ta kirasa, sosai ta shiga damuwa ta rasa me ke mata dadi,
ko abincin kirki bata iya ci, bata taba tunanin akwai abinda xai daga mata
hankali haka ba, ko da yaushe a sanyaye xaka ganta, tana wanke wanke a kitchen
ranan Thursday da yamma Ammi ma na kitchen din tana kwashe shinkafar da ta dafa
a warmer, tarwatsewan glass cup da ta ji yasa ta juya da sauri tana kallon
Imaan da ta koma baya tana xaro ido, don na biyu kenan ta fasa tsayuwarta a
sink din, Ammi ta daure fuska cikin tsawa tace "Are you stupid imaan,
tunanin uban me kike kika sake fasa min wani cup din?" Hawaye imaan ta
fara yi tana kallonta, Cikin tsawa Ammi tace "Get out kar in gaura maki
mari my friend" juyawa Imaan tayi da sauri ta fita, Ammi ta gama kwashe
abincin ta tafi ta ci gaba da wanke wanken, tana gamawa ta fita xuwa dakin
Imaan, Kwance ta ganta ta rufe fuskarta da pillow, har ta karasa kusa da ita ta
xauna gefen gado bata sani ba, Ammi tace "Imaan..." Da sauri ta dago
a tsorace don bata ji shigowar ta ba, sai kuma ta fara goge idonta tana
sunkuyar da kanta, Ammi ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace "Tell me
what's wrong with you plss Imaan, kina da wata da xaki fada ma damuwarki ban da
ni, am asking you this for the third time, kar ki yarda in kira daddy yanxu kin
san dawowa xai yi" Imaan ta fashe da kuka sosai ta rungume ta, lkci daya
jikin Ammi yyi sanyi, ta dago kanta cike da damuwa tace "Ki gaya min damuwarki
daughter" cikin rawar murya tace "Ammi mai sunan Daddy ne...."
Da mamaki Ammi ke kallonta lkci daya kuma gabanta ya fadi don right from time
ta gudar ma only child din tata heartbreak, cike da karfin hali tace "What
about him???" Cikin kuka Imaan tace "He is calling me no more, ko na
kirasa baxai dauka ba sai washegari" Ammi dake kallonta duk da tashi da
hankalinta yyi ta dake tace "Me ya hada ku?" Shiru Imaan tayi hawaye
na sakko mata, bata ma san me xata ce ma Ammi ba, tasan ko hauka take baxata ce
don ya ganta da Mujaheed a eatry bane Mujaheed na bata nama a baki, ta hadiye
abu da kyar tace "Kila saboda yana ganina tare da Yaya ne always"
Ammi tace "Toh dole sai kin tsaya tare da Yaya, Ina ruwanki da shi da yyi
aurensa, wato yana ganinku kuna shashancin da ku ka saba kina xaunawa kusa da
shi ko???" Imaan ta fashe da kuka a hankali tace "Wllh Ammi na daina
haka ai" Ammi bata iya tace komai ba, imaan ta kamo hannunta cikin rawar
murya tace "Ammi ko xa ki kirasa ki masa magana don Allah" wani kallo
Ammi ta mata tace "Ba mu gaji haka ba ai, ni ba gantalalliya bace, kuma
bari in gaya maki ba a ma namiji son hauka, kawai don bai kula ki ba ki wani
damu ki daga hankalinki kisa ma kanki wani cutar ki cuce ni?" Ta rufe
fuskarta a kafar Ammi tana shessheka tace "Ammi wllh da gaske Ina son
sa" Ammi ta dinga kallonta, can ta dago kanta cikin sanyin murya tace
"Ki kwantar da hankalin ki Imaan, amma bana son kina damuwa, kin basa
hakuri kuma?" Imaan ta girgixa mata kai, Ammi tace "Toh ki kirasa ko
ki masa text ki basa hakuri, sai ke kuma ki kama kanki ba ruwan ki da wani Yaya
from now on kin ji abinda nace?" Imaan ta gyada mata kai a hankali, Ammi
tace "Kuma ban ce ki gaya ma Inna ba" a hankali Imaan tace "Toh
Ammi" Ammi tace "Ta shi mu je ki xuba abinci yanxu" ba musu
Imaan ta mike ta bi bayan Ammi suka fita dakin. Karfe shidda Imaan ta tafi kai
ma Inna abinci don bata ma son ta je da Magrib ta hadu da Mujaheed, turo baki
tayi ganin takalma bakin kofar, ta shiga da sallama ba tare da ta yarda ta
kalli wanda ke xaune a parlon ba ta ajiye abincin, Inna na washe baki tace
"Toh kin kawo a dai dai kuwa, kawo plate in dibar masa nasan baxai wuce
shinkafa ba dai" Imaan ta saci kallonsa lkci daya gabanta yyi mugun faduwa
ganin Sadeeq xaune parlon cikin kananun kaya idanuwansa sanye da glasses, suna
hada ido ya dauke nasa idon, ta kasa fita parlon, Inna tace "Baxa ki kawo
kwanon bane in tashi da kai na" Yana murmushi yace "Kaka da gaske fa
na koshi, yanxu muka gama cin abinci da abokaina a gidan cin abinci" Inna
ta rike ha6a tace "Toh abincin gidan naku ba dadi ne Bukar har sai ka fita
gidan masu abinci?" Sosai Sadeeq yyi dariya yana kallonta yace "Kaka
saboda abokaina ne muka je can" Inna ta tabe baki tace "Atoh, na ji
ance fa naman aladu suke siyar ma mutane, ni dai da xaka yi hakuri ka daina
xuwa idan ma girkin gidan naku ne baka so sai ka dinga xuwa nan xan saka maka a
kwano in ajiye, kazamai da masu wari sun yi yawa a duniya yanxu kaje ka ci
abinda xai hallaka ka wataran mu shiga uku gaba daya" Shi dai dariya kawai
yake Imaan ta juya ta fita parlon.... Dai dai inda suke yawan tsayuwa da
Mujaheed ta tsaya, ba a wani dau lkci ba taji foot steps dinsa yana tahowa,
yana kusa isowa wajen suka yi ido hudu, yyi slowing pace dinsa amma kuma ba shi
da alamar tsayawa, cikin sanyin murya tace "Plss ka tsaya Abbana"
Tsayawa yyi ya dawo gefenta ya rungume hannunsa a hankali yace "Toh na
tsaya daughter" Lkci daya hawaye ya kawo idonta ta sunkuyar da kai cikin
rawar murya tace "Don Allah kayi hakuri ka yafe min" Yace "Inyi
hakuri a kan me" da kyar tace "Abinda yasa kake fushi da ni"
yayi murmushin karfin hali yace "Aa ban yi fushi ba Imaan" tace
"Wlh ka yi, don Allah kayi hakuri wllh hakan baxai kara faruwa ba"
Yace "Imaan don Mujaheed yayan ki ne kamar yanda kike yawan fadi ba yana
nufin same parent suka haife ku ba so I have all right to get angry, Shi din ba
Muharramin ki bane, da nine nace mu fita eatry ni da kudin gaisuwana ke kanki
ba yarda xa ki yi ba, not to talk of giving ur meat..." ta dinga goge
hawayen da ya ki tsaya mata tace "Plss kayi hakuri, baxan sake ba, abinda
ma yasa ya kai ni wajen ranan ya siya min kaza shine saboda I promise xan taya
sa fada ma wata yarinya da yake so cewar yana sonta wai ya kasa fada mata....
Wllh saboda nace ni xan yi ma yarinyar magana ya sa ya siya min kaza don in
maya" murmushi Sadeeq yyi yana shafa kansa yace "Ya wuce Imaan... Xan
wuce masallaci it's almost time" a hankali tace "Ka hakura?"
Yace "Tuni na hakura ai" mu je ki raka ni gate, har suka isa gate
babu wanda yace komai cikinsu, yana kallonta yace "Good night" ta
gyada masa kai ya wuce ta juya ta koma ciki. Tun daga sannan imaan tayi kokarin
dinga avoiding Mujaheed, ko parlonsu ya shigo dama tashi take ta wuce daki ko
ta wuce kitchen, part din Inna kuwa kafin yaje xata kai mata abinci ta maxa ta
dawo, ana haka har ya rage two weeks su fara exams kuma hakan yyi dai dai da
saura sati biyu a kawo lefenta tare da sadaki daga gidansu sadeeq, sosai ta
dage da azkar kamar yanda Ammi ta ce mata saboda yawan faduwan gaba da take,
Ammi ma ta bata addu'o'in da xata dinga yi tana kuma kokarin tashin ta duk dare
tayi sllh. Yau Saturday Imaan ta fito parlor sanye da hijab dinta har kasa
hannunta rike da karamin jaka, duk da babu komai fuskarta sai eye pencil da
Chappete ba karamin kyau sanyanye tayi ba, Ammi dake xaune parlor ta bi ta da
kallo har ta durkusa kusa da ita tace "Ammi xa mu wuce" Ammi ta d'an
yi shiru kafin tace "Kar ki dade Imaan, ko minti goma plss kar ki yi ba
mutuncin ki bane, kina yin abinda ya kai ki ki juyo" Imaan ta d'an yi murmushi
tace "Toh Ammi in sha Allah" Ammi tace "Ko xa ku dawo napep xa
ku hau kin ji abinda nace koh?" Imaan tace "Toh Ammi" daga haka
ta fita parlon, ta nufi part din su Maimoon, a hankali ta bude kofar ta shiga
da sallama murya can kasa, Umma ce xaune parlon, sai Mujaheed dake xaune shi ma
ya jinginar da kansa da kujera idonsa lumshe, Safeenah ma na xaune parlon tana
taunar cingam, Umma tace "Toh ni na ta6a jin rashin lafiya haka, bari
Abbansa ya shigo kila idan yyi masa magana xai yarda a dubasa, su dama
likitocin nan haka suke da shegen taurin kai sai dai su duba wasu ba dai a duba
su ba" Safeenah ta tabe baki tace "Wllh kuwa Hajiya, har ce min yake
ba ruwana in daina sa masa ido, Toh ya baxan sa ido ba mijina ba lafiya, ko
abinci bai ci fa Umma sai dai coffee da tea mun fi sati a haka" Umma ta
rike ha6a tace "Ba lafiya kuwa, bari Abba ya shigo wannan ai ba yi
bane" Imaan da ta sunkuyar da kanta ta nufi stairs tace "Ina yinin
ku" babu wanda ya tanka ta a parlon har ta wuce sama, Umma ta kalli
Safeenah, Safeenah tayi wani murmushi tana kas kas da cingam, Mujaheed tunda ya
ji muryarta ya bude ido, ba a dau lkci ba Imaan ta sakko tare da Maimoon dake
sanye da hijab ita ma har kasa, suna shigowa parlor Umma ta bi su da kallo,
Maimoon tace "Sai mun dawo Umma" Umma tace "Yauwa" Imaan dai
bata juyo ba har ta fita, Maimoon ma ta fita, Mikewa Mujaheed yyi yana kallon
Umma yace "Bari in je in gaida Inna in dawo yanxu" Safeenah ta mike
tace "Ehh bari mu je Umma yanxu xan dawo sai mu fita kasuwan" wani
kallo Mujaheed ya dinga mata fuska daure yace "Da can baki san xa ki part
din Inna ba sai da nace xan je??" Safeenah ta tabe baki ta nufi kofa tana
gyara mayafin jikinta ya bi ta da kallo, imaan da Maimoon na isa bakin titi
suka tsayar da adaidaita, Imaan na kallon Maimoon tace "Wllh ban san me
yasa gabana ke faduwa ba tun daxu Maimoon" Maimoon tace "Haba dai, to
ki dinga addu'a" Imaan tace "Ehh Ina yi" daga haka ta kalli mai
adaidaitan da suka tsayar....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
66.....
A hanya imaan ta sa mai adaidaitan ya tsaya gun masu fruits
ta siya fruits kusan kala hudu sannan suka koma adaidaitan, Tafiyar kusan minti
ashirin suka yi suka isa wani babban hospital wanda kai kana gani kasan na masu
hali ne, sauka suka yi a adaidaitan kafin Imaan ta basa kudi daga cikin jakarta
Maimoon ta basa, hakan yasa Imaan ta ciro wayarta kawai ta shiga kiran layin
Mariya, ba a dau lkci ba Mariya ta daga, Imaan tace "Muna waje"
Mariya tace "Ohk to gani xan fito yanxu" Imaan ta mayar da wayar
jakarta suka shiga haraban hospital din, ba a dau lkci ba Mariya ta fito ta
nufo su tana murmushi suka gaisa da fara'a suna tambayarta me jiki, Mariya tace
"Da sauki sosai, mu shiga ciki" bin bayanta suka yi har xuwa special
ward din da aka kwantar da step sis din nata, da sallama suka shiga cikin
babban ward din mai dauke da gado daya sai kujeru da karamin Tv na bango, ga
labulaye a duk windows din, gadon ma kadai dake dakin ya isa ya bayyana cewa
ward din na special people ne, Mahaifiyar Sadeeq Hajiya Khadijah ce xaune saman
kujera, sai Aunty da frnd din Mum din Sadeeq da kanwarta, Aisha kanwar Sadeeq
na kwance saman gadon tana bacci an sa mata drip, sai autar su Sadeeq din dake
tsaye hannunta rike da incense da ashana, Imaan ta sunkuyar da kai ta karasa
cikin dakin da ladabi ta gaida su, Hajiya Khadijah ta amsa tana kallonta, Aunty
da sauran mutanen ward din ma duk suka amsa, Aunty na nuna masu kujera tace
"Toh ku xauna" Maimoon ce ya fara xama, Imaan kuwa sai da sister din
mahaifiyar sadeeq ta sake maimaita mata ta xauna sannan ta xauna har sannan
kanta na kasa, Mariya na murmushi tana kallon stepmother dinta tace "Mummy
ita ce budurwar ya sadeeq warce xai aura fa...." Mummy na kallon Imaan da
kyau tace "Wannan ba warce ku ka yi sauka tare bane kwanaki har muka yi
hotuna" Mariya tayi dariya tace "Ita ce Mummy ashe dai xa ki gane
ta" Aunty dai sai murmushi take tana kallon Imaan da ta kasa dago kai gaba
daya she was uncomfortable ba kadan ba, Mummy ta d'an yi murmushi tace
"Toh Maa sha Allah, Allah ya sanya albarka..." Mariya tace
"Ameen, amma fa tun kafin saukan suke tare Mummy" Mummy tace
"Toh maa sha Allah, hakan yyi kyau" Aunty na kallon Imaan tace
"Ya su mamanku" a hankali tace "Tana gaishe ku" Aunty tace
"Toh mun gode Allah maku albarka" duk suka amsa da "Ameen"
a hankali Imaan ta dago kai tana bin ward din da kallo jin numfashinta na d'an
tsarkewa, kanwar Sadeeq ta gani xaune chair din dake kusa da wanda ta xauna
hannunta rike da incense har stick biyu ta kunna, Imaan ta kauda kai, sai kuma
cikin dubara ta dan rufe hancinta da hijab din jikinta, Lkci daya Maimoon ta
lura da hakan, ta taba ta murya can kasa tace "kiyi masu sallama mu wuce
kawai" kasa cewa komai Imaan tayi, su Aunty dai hiransu kawai suka ci gaba
da yi, Maimoon ta mike tana kallonsu tace "Toh mummy xa mu koma, ga wannan
a ba mara lafiya, Allah ya bata lafiya" tana magana tana ajiye ledan
hannunta a table, Aunty tace "Har xa ku tafi, to mun gode Allah ya saka da
alkhairi" Mummy tace "Toh mun gode, ku gaida gida da mutanen gida"
tuni Maimoon ta kama hannun Imaan tana amsa masu da Ameen, Mummy na kallon
Imaan da murmushi tace "Toh ya sunan naki?" Maimoon tace "Fatima
Imaan" Imaan ta warce hannunta daga rikon da Maimoon ta yi mata ta nufi
kofa da sauri dai dai lkcn da aka bude kofar ward din Sadeeq ya shigo, bata kai
ga fita ba ta durkushe bakin kofa ta fara gasping for air tana tari, Mariya da
Maimoon suka nufeta da sauri, Su Aunty da Mummy ma duk suka mike suna salati
suka nufeta, Sadeeq ya xura wayarsa aljihu ya durkusa kusa da ita ya dagota
yana kallonta yace "Subhanallah, Imaan are you okay..." Mariya ta
kashe incense din hannun Step sis dinta, a nan kuma duk suka dago musabbabin
tashin Asthma din nata, ba karamin tausayi Imaan xata baka ba ganin yanda take
struggling da numfashin nata a kasa, gaba daya su Mummy da Aunty da mutanen
dake ward din duk suka rikice, Maimoon ta durkusa ta cire jakarta dake rataye
shoulder dinta ta bude da sauri tana bincika ciki ko akwai inhaler amma taga
babu, ganin haka Sadeeq ya daga ta ya fitar da ita daga ward din, Aunty ta bi
bayansa ita ma hankali tashe Maimoon da Mariya ma suka fita, cike da damuwa
Mummy tace "Ai ba a san she is asthmatic ba, da Suhaila bata kunna turaren
ba, kuma duk sai suka yi shiru basu ce komai ba" Kanwar Mummy tace
"Wllh kuwa, irin haka ai magana xa su yi, gashi an ja mata wahala
yanxu" Kawar Mummy tace "Ikon Allah shi kuma Sadeeq ana neman mai
lafiya ya jajibo ma kansa ciwo Allah na tuba, dubi fa d'an hayakin da ya tada
Asthma ni fatima Allah na tuba, kenan wannan dai ko shara bata yi balle aje ga
soye soye a kitchen, don in dai wannan hayakin xai iya tada Asthma to fa babu
abinda baxai tayar ba, Toh Allah dai ya kyauta, Allah kuma ya bata lafiya"
Mummy dai bata ce komai ba haka kanwarta da ta mike ta bi bayansu Aunty. Sadeeq
na xaune gefen Imaan dake kwance daya daga ward din hospital din, ban da juye
juye babu abinda take yi har sannan da kyar take numfashi, Aunty sai sannu take
mata tana kallonta cike da tausayinta, Mummy dai na tsaye jikin window ta
rungume hannu tana kallonta ita ma, Mariya har da d'an hawayenta, Maimoon na
kusa da sadeeq ta kama hannunta tana tofa mata addu'a a hankali, wani likita ne
ya shigo ward din yana kallon Imaan yace "Sit upright now" Sadeeq ya
mike don ta samu ta tashi xaune, da taimakon Maimoon ta xauna, likitan yace
"How are you feeling now" Bata iya tace komai ba, A hankali Sadeeq
yace "She said her chest..." Murmushi likitan yyi ya dafa Sadeeq yace
"Anya kuwa Dr idan emergency ya tashi gidan ku cikin dare xaka iya ta6uka
abun kirki?" Aunty ta ta6e baki tace "Haka nan yake wllh Dr, ni ban
ta6a ganin likita haka ba, gaba daya mance cewa shi likita ne yake in a
situation like this" Dr din ya d'an yi dariya yace "Gaskiya
ne..." Ya maida dubansa gun Imaan da ta hade kanta da pillow yace
"Amma an ta6a maki allura idan Asthma din ki ya tashi ba inhaler a
kusa?" Bata tare da ta dago ba ta gyada masa kai da kyar, Yace "Toh
Allah ya sauke, xai daina in sha Allah mun baki magani ai... Allah ya baki
lafiya" Ita dai bata ce komai ba, likitan na kallon Sadeeq yace "Nan
da few hours xa a sake shigowa duba ta Dr... Allah ya tsare, sai a dinga
kiyayewa" Sadeeq ya d'an yi murmushi yace "In sha Allah" daga
haka likitan ya fita yana kara gaida su Mummy, Sadeeq ya duka yana kallon
Imaan, murya can kasa yace "Sorry dear" ita dai bata ce komai ba,
yace "Toh kwanta da kyau" sai a sannan ta dago kanta a hankali ta
kwanta tana sauke numfashi a hankali, Mummy dai sai kallonta take haka ma
Aunty, can Mummy tace "Toh Allah ya sauke, bari in koma daya ward
din" daga haka ta fita, Aunty ta ja kujera ta xauna, nan da nan bacci ya
dauke Imaan. Maimoon dake xaune kan kujera tare da Mariya suna kallon Imaan ta
fiddo wayar Imaan dake ring a jaka, number Ammi ta gani a screen, ta daga ta
kai kunne tayi sallama murya can kasa, a hankali Ammi tace "Imaan din fa
Maimoon?" Maimoon tace "Wlh Ammi ta sami attack ne a hospital din,
amma da sauki yanxu tana bacci ma" Mahaifiyar Mariya dake ward din har
sannan tana duban Maimoon tace "Kawo wayar" Mikewa Maimoon tayi ta
tafi ta kai mata wayar, bayan sun gaisa Aunty tayi mata bayanin abinda ake ciki
tace "Amma da sauki Alhmdllh don har tayi bacci, xuwa anjima in sha Allah
xa a taho da su gida" Ammi tace "Toh maa sha Allah, an gode sosai,
Allah ya saka da alkhairi" Aunty tace "A'a ba godiya Hajiya, mu ma
mun gode" daga haka suka yi sallama Aunty ta mika ma Maimoon wayar, kusan
la'asar Sadeeq ya shigo ward din rike da ledan drugs, Maimoon da Mariya ne
kadai dakin Aunty ta tafi gun su Mummy, Har ya karasa gun Imaan kallonta yake
ganin yanda ta takure waje daya, ya kai hannunsa forehead dinta, sosai ya ji
jikinta da xafi, ta bude idonta da suka kada tana kallonsa, lips dinta ma yyi
ja sosai, dukawa yyi da damuwa yace "Are you okay imaan, har yanxu kirjin
na maki ciwo ne" kokarin tashi xaune ta shiga yi da kyar tana dafa
bayanta, ya kama hannunta ya taimaka mata ta tashi, ganin yanda ta rufe ido
yace "Ina ke maki ciwo??" Murya can kasa tace "I am feeling
internal heat, kuma Ina jin sanyi, my back is aching" Shiru yyi yana
kallonta cike da tausayi, can ya juya ya fita suka dawo tare da likita, a dakin
ya tadda Mummy xata wuce gida ta dawo anjima shine ta shigo yi masu sallama,
tana tsaye kan Imaan ganin yanayinta tana kallonta tace "Wani abun na
damun ki ne kuma? Ko kina jin ciwo a wani waje ne?" Imaan ta girgixa mata
kai da kyar bata ce komai ba, likitan ya karasa ya kai hannu jikinta yana
kallonta yace "Me kike ji a jikin ki?" Imaan ta girgixa masa kai a
hankali hawaye cike idonta tace "Kawai ina son xan wuce gida" Sadeeq
yace "Noo ki fada masa inda ke maki ciwo" da kyar tace "Joint
pain, kuma Ina jin xafi a jikina...." Likitan ya kai hannu forehead dinta
yana kallonta, yace "Yana maki haka ne?" Kai ta gyada masa, yana
kallon kwayar idonta ya d'an yi shiru sai kuma ya kalli Sadeeq yace "Is
she a sickled cell patient?" A hankali Sadeeq ya girgixa masa kai yace
"She is only carrying the trait" Likitan yace "Wani drugs kike
sha a gida?" Cike da karfin hali tace "Suna da yawa" likitan
yace "Did you know their names?" Sadeeq yace "I will get drugs
for her now, amma ayi mata allura" daga haka ya juya ya fita ward din.
Aunty ce ta sakko parlor sanye da hijab hannunta rike da purse, ta kalli
Mujaheed tana amsa gaisuwar da yake mata a parlorn sannan ta kalli Umma tace
"Xan fita sai na dawo Hajiya" Umma tace "Ina kuma xa ki da
magariba" Aunty tace "Xan je dubiya asibiti ne" da mamaki Umma
tace "Waye ba lafiya?" Aunty tace "Baki san su ba" Dai dai
nan Abba ya shigo parlon yana kallon Aunty yace "Ba ku tafi ba kenan"
Aunty tace "Ehh yanxu xa mu fita" Abba yace "Xuwa anjima idan
anyi isha xan leka asibitin" Umma na kallon Abba tace "Wai waye ba
lafiya" Abba ya kalli Aunty yace "Bata sani ba ne dama?" Aunty
bata tanka sa ba ta nufi kofa, Abba ya girgixa kai yace "Imaan ce suka je
duba kanwar yaron nan dake nemanta a asibiti shine Asthma dinta ya tashi, ita
ma dai tana asibitin yanxu" Kallonsa kawai Mujaheed yake ko kiftawa babu,
Umma ta saki salati tana tafe hannu tace "Shine ake boye min, shi ciwon
Amina ke boye min fisabilillahi? Meye amfanin xaman munafurci Alhaji, wato ita
ta ji xata tafi dubata a asibitin ni kuma sai uwar yarinyar da Inna su kullace
ni su xata naji xuwa ne bana son yi, toh xuciyata bai kai haka lalacewa ba,
kuma nima yanxu xan shirya mu tafi, sai dai ita ta ji kunya, ban taba ganin
munafuka irin Amina ba wllh, duk ita ke hada ni da Aisha na lura" Shi dai
Abba ko tanka ta bai yi ba ya wuce parlon sa, Umma ta wuce sama da sauri don
dauko hijab, Mikewa Mujaheed yyi ya fita parlon ya bi bayan Aunty, tare ya
gansu suna tahowa da Ammi dake sanye da hijab ita ma, yana tsaye har suka iso,
ya gaida Ammi ta amsa tana tambayarsa ya aiki, yace "Alhmdllh, ya mai
jiki" Ammi tace "Toh da sauki" a hankali yace "Toh mu je in
ajiye ku" Aunty tace "Toh ka kyauta" dai dai nan Umma ya fito
parlon sanye da hijab ita ma, tana kallon Aunty tace "Toh Amina xuciyata
bata kai inda kike tunani ba lalacewa, rashin lafiya Kuma da ke kan kowa kike
boye min fisabilillahi??" Aunty ko kallonta bata yi ba ta nufi gate, Ammi
dai bata ce komai ba ita ma tafiyar take, Umma tace "Munafurci dai bashi da
amfani a rayuwa, kuma tare kika shigo gidan nan kika ganmu da Aisha" daga
haka ta kalli Mujaheed tace "Kai xaka kai mu ne" ba tare da ya
kalleta ba yace "Ehh" har suka shiga motar tasa babu wanda yace
komai, Aunty ta gaya masa asibitin bayan sun hau saman titi. Maimoon ce ta fito
ta kai su har ward din da imaan take, Mummy na xaune saman kujera kusa da gadon
da imaan take kwance tana bacci, sai kannin Sadeeq biyu da kanwarta da Mariya,
Su Aunty na shiga ward din Mummy ta fara welcoming din su, a ka shiga gaisawa
fara'a, Umma dai sai kallon Mummy take, Mummy tace "Jikin ma da sauki
sosai, kawai drip din ne da bai kare ba, don sunce biyu ne" Aunty tace
"Toh Alhmdllh, Allah ya sauwake, ku kuma Allah ya bada lada" Mummy
tayi murmushi tace "Toh Ameen, Allah ya bata lafiya" Mujaheed dai na
tsaye daga bakin kofa yana kallon Imaan dake bacci tana sauke numfashi a
hankali, da sallama Sadeeq ya shigo ward din....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
67....
Sadeeq ya gaida su Aunty da ladabi, sannan ya gaida Umma ma
dake ta kallonsa, Umma tace "Lafiya lau, ya hidima?" Yace
"Alhmdllh" Umma tace "Toh Allah ya bata lafiya, ku kuma Allah ya
sassaka da dawainiya, a haka nan dai ake kullum yau ciwo gobe lafiya, an rasa
gane kan abun dai, Allah dai ya rabata da wannan cuta da ya ki ci ya ki cinyewa
ni Rukayya" Mujaheed dake ta kallon mahaifiyar tasa ya karasa cikin ward
din xuwa gadon da imaan take tana bacci ya tsaya yana kallonta, ya kai hannu
goshinta ya ji babu xafi bacci dai take mai nauyi, Umma dai sai wani kallo take
masa ta gefen ido, Aunty na kallon Mummy tace "Toh Hajiya tunda kuna nan
mu xa mu koma, Allah ya saka da alkhairi, mun gode kwarai" Mummy na murmushi
tace "Ah haba dai ba komai ai yi ma kai ne, Allah dai ya bata lafiya, ya
ba mu alkhairi" Ammi ma tayi mata godiya hade da sallama, Umma da ke xaune
ta ki tashi ta bi su da kallo baki sake tace "Sai kace ana koranmu ko
tashi yarinya bata yi ba balle mu ga lafiyarta ku ce xa mu wuce?" Can ta
tabe baki tana gyara xama tace "Atoh ku je ni sai na xo" Ita dai Ammi
bata ce komai ba har ta fita Maimoon ma ta fita, Mujaheed dai sai kallon uwar tasa yake daga
inda yake tsaye, Aunty dake ta kallonta ta dai nufi kofa tana danna wayarta,
suna fita ward din ta kai waya kunne bayan wani lkci tace "Toh ga Matar ka
can gaban surukai tana maganganu da bai dace ba a kan ciwon 'yar ka, mun fito
yanxu xa mu tafi tace babu inda xata kawai dai don ta samu sararin ci gaba da
rashin kirkinta a wajen, idan ma xaka kirata to ka kirata ta fito ward din nan,
Banda ma kinibibi da can duk ciwon da Imaan take ta ta6a bin mu
asibiti...." Bata jira cewarsa ba ta kashe wayarta fuska daure, Ammi dai
sai murmushi take suna tafiya, ko minti daya ba ayi ba Abba ya kira Umma dake
kallon Mummy tana cewa "Mun gode fa, Allah ya saka da alkhairi ya bada
lada, abun kam sai addu'a yau ciwo gobe lafiya ana dai ta tafiya a
haka..." Ring din wayarta yasa tayi shiru tana kallon screen din, can ta
daga ta kai kunne kafin tace komai Abba yace "Rukayya ku dawo gida yanxun
nan gaba daya" a hankali tace "Ko saboda me?" Strictly yace
"Nace ki dawo yanxu Madam" tace "Toh" daga haka ta katse
wayar tayi tagumi tana kallon Imaan bayan kusan minti uku ta mike tana murmushi
tace "Toh, Hajiya tunda sun ce mu tafi bari mu wuce don a mota daya muke,
ma dawo da safe, Allah ya saka da alkhairi" Mummy tace "Toh Ameen,
Allah ya tashe mu lafiya, sai da safen" Da ido Mummy ta bi ta har ta fita
kafin ta dauke kai, Mujaheed dai na tsaye kusa da gadon har sannan idonsa na
kan imaan, Sadeeq dake tsaye ya ja kujera ya xauna, Mummy na kallon Mujaheed da
murmushi tace "Kanwarka ce koh?" Murmushin yyi shi ma yace "Ehh
kanwata ce" Mummy tace "To madallah, ga kujeru ka xauna" Yana
kallon drip din da aka sa mata yace "Am comfortable ma" tace
"Toh yyi kyau" Mariya ce ta shigo dakin rike da warmer din abinci ta
ajiye tace "Bata tashi ba har yanxu?" Mummy tace "Eh bata tashi
ba" Mariya na kallon Mujaheed tayi murmushi tace "Ina yini Dr?"
Mujaheed ya mayar mata murmushin yace "Lafiya lau Mariya" Mummy na
kallonsa tace "Kai ma likitan ne kenan" shafa kai kawai yyi yana
murmushi, Mariya tace "Ehh Dr ne, a Chasel hospital yake aiki" Mummy
tace "Maa sha Allah, that's good" Shi dai Mujaheed bai ce komai ba, Sadeeq
dai sai danna wayarsa yake babu yabo bbu fallasa, Mujaheed ya kalli agogo yace
"Xan je in yi isha, xuwa anjima xan dawo in sha Allah" Mummy tace "Toh sai ka dawo" daga
haka ya nufi kofa ya fita, Mummy na kallon Sadeeq tace "Are they of the
same mother?" Girgixa kai Sadeeq yyi har sannan yana danna waya, Mummy
tace "Stepmother dinta ce warce ta fita yanxu?" Sadeeq ya kalleta
yayi d'an murmushi yace "Not at all, mum din shi wanda ya fita ynxu
ne" Mummy bata kuma cewa komai ba. Karfe takwas da rabi Imaan ta farka
daga baccin da take, har sannan Mummy na xaune kusa da ita tare da Suhaila sai
sadeeq dake xaune idonsa a kan wayarsa, Aunty kuma na can gun Aisha Kanwar
sadeeq dake kwance daya ward din, Mummy na kallonta tace "Sannu, ya
jikin?" Ta d'an yi murmushi tace "Na ji sauki" Mummy tace
"Toh Allah ya sauwake" Shi dai Sadeeq kallonta kawai yake, ta mike
xaune a hankali tace "I want to use the restroom" Mikewa Sadeeq yyi
ya cire tube din ruwan ta sakko daga saman gadon tana dafa gado sbda jirin da
ta ke ji, Mummy dai sai sannu take mata, Suhaila xata kama hannunta tayi
murmushi tace "Xan iya" daga haka ta wuce bathroom dake ward din tana
dingishi, Mummy dai ta bi ta da kallo, Da alwala ta fito bathroom din ta karasa
kan gado ta dau Hijab dinta dake linke, Mummy tace "Sllh xa ki yi?"
Imaan ta gyada mata kai, Mummy ta kalli Suhaila tace "Ki tafi can ward din
ki dauko darduma" Mikewa Suhaila tayi ta fita, shi dai Sadeeq sai kallon
Imaan yake, ita kuwa bata yarda ta kallesa ba, Mummy ta nuna mata kujera tace
"Toh xauna kafin ta dawo" ba musu ta xauna saman kujeran, ba a dau
lkci ba Suhaila ta dawo da pray mat ta shimfida mata. Imaan na xaune pray mat
din bayan ta idar da sllh, Mummy ta bude warmer ta debi hadadden jollof rice da
Mariya ta kawo daga gida ta sa mata da enough meat, Mummy tana kallonta tace
"Toh tashi ki hau saman gado ki ci abincin" Mikewa Imaan tayi ta hau
saman gadon ta mika mata abincin ta amsa a hankali tace "Nagode"
Suhaila tace "A hada maki shayi?" Girgixa kai Imaan tayi tace
"Wannan ya isheni" Bude kofar ward din aka yi Abba ya shigo da
sallama tare da Maimoon, Sadeeq ya mike har ya iso cikin dakin Abba yayi ma
Mummy sannu ta amsa tace "Sannu da xuwa" gaishesa Sadeeq yyi Abba ya
amsa da fara'a yana tambayarsa mai jiki, sannan ya kalli Imaan dake kallonsa
yace "Sannu Mamana, how are you feeling now" tana murmushi tace
"Na ji sauki Abba, Ina yini" yace "Lafiya lau, Allah ya kara
lafiya daughter" Mummy tace "Ina yini Alhaji" Abba yace
"lafiya lau, ya masu jiki" tace "Alhmdllh da sauki sosai"
yace "To madallah, Allah ya basu lafiya, Allah kuma ya bada lada"
Mummy tace "Ameen" Maimoon ta ajiye ledan fruits dake hannunta tana
kallon Imaan tace "Sannu" Murmushi imaan tayi mata, Abba yyi ma Mummy
sallama yace xai shiga ya duba sis din Sadeeq, Mummy tace "Tou mun gode
Alhaji" yana kallon Imaan yace "Sai da safe Mamana, Allah ya kara
lafiya" ta amsa da "Ameen, thanks Abba" tare suka fita da Sadeeq
da xai kai sa gun sis dinsa. Basu kai minti biyar da fita ba Mujaheed ya shigo
dakin hannunsa rike da leda, Tun da suka hada ido Imaan ta sunkuyar da kanta,
ya karaso ciki yana ma Mummy sannu, Mummy tace "Har ka dawo" yace
"Ehh na dawo" Yana kallon Imaan da taki yarda ta kallesa yace
"How are feeling now" still bata kallesa ba tace "Na ji
sauki" ya ajiye ledan hannunsa a table, yana silencing wayarsa dake
ringing, Mummy ta nuna masa kujera tace "Toh ka xauna koh" ya d'an yi
murmushi ya xauna saman kujeran, Imaan dai sai juya abincin gabanta take, Mummy
tace "Ba fa cin abincin kike ba" diba tayi ta kai baki ta dago kai
tana kallon Mujaheed dake kallonta, a hankali ta dauke kanta tana cin abincin.
Sai kusan karfe goma Sadeeq ya dawo dakin, Tun da ya kalli Mujaheed sau daya ya
dauke kai yana kallon Mummy yace "Xa a mayar da ke gida ne tunda Suhaila
da sis dinta na nan?" Mummy tace "Don't worry nan da anjima sai in
tafi" Yace "Ohk" karasawa yyi kusa da Imaan murya can kasa yace
"Ba inda ke maki ciwo ko?" Ta gyada masa kai kawai, yace "Ohk,
xan je gida in dawo yanxu, I want to freshen up" ta kallesa tace
"Ohk" murmushi ya sakar mata ta sunkuyar da kanta, ya juya yana
kallon Mummy yace "Xan dawo ltr mum" daga haka ya nufi kofa Mummy
tace "Toh ai ba ku yi sallama da Dr ba" Juyowa sadeeq yyi ya kalli
Mujaheed yace "Ohh I didn't notice him, see ya ltr..." Mujaheed ya
d'an yi murmushi yace "Alright" Daga haka ya fice daga ward din.
Imaan ta daga kai ta kalli Mujaheed taga kallonta yake ta turo baki ta dauke
kai, Mujaheed bai bar hospital din ba duk da kiran da Safeenah da Umma suka
dinga lafta masa, ya kuma ki dagawa, har sai da Umma ta kira Maimoon tace ta
kai masa waya, Maimoon na kallonsa ta mika masa wayar tace "Ya
M.A...." amsan wayar yyi ya kai kunne, cike da bala'i da masifa Umma tace
"Mujaheed wai Kanwar Uwarka ko ta ubanka ce kwance gadon asibiti???"
Shi dai bai ce mata komai ba, rai bace tace "Tun raina bai gama baci gaba
daya ba ka kama hanyar gidan ka yanxun nan, ka bar yar mutane can ita kadai
tsakar dare kamar ni ce kwance ba lafiya a gadon asibiti, ko meye hadin ka da
sauran ciwon?" Mujaheed bai ce komai ba ya katse wayar ya mika ma Maimoon
ta amsa, Mujaheed bai bar asibitin ba duk da fadan Umma sai kusan Sha daya da
wani abu, shi ma Mummy ce tace masa amma ba shi da family, Bai bata amsa ba sai
murmushi da yyi ya mike yace "Toh sai da safe, Allah ya bada lada"
tace "Ameen" Imaan dake kwance ta rufe ido kamar mai bacci, ta bude
idon ta bi sa da kallo har ya isa kofa, sai kuma ya juya ya kalleta, da sauri
ta rufe idon, har xai fita sai kuma a hankali tace "Sai da safe" Yana
kallonta yace "Allah ya tashe mu lafiya" daga haka ya fita ya rufe
kofar. Washegari aka sallami Imaan karfe sha daya na safe, Stepmum din Sadeeq
da su Suhaila ne suka kai ta har gida, Ammi tayi masu godiya tare da Aunty,
basu wani jima a gidan ba suka wuce tunda tare suke da driver. Bayan sati daya da
yayi dai dai da saura sati guda a kawo lefen Imaan.... Umma ce xaune makeken
parlon gidan Bulasawa tare da Hajiya Balaraba sai Safeenah da ta ke ta taunan
cingam ta ci kwalliya iya kwalliya tayi kyau, ba don Suhaila da ta gansu bakin
gate a tsaye ta dawo boko a motarta ba da babu yanda xa ayi a barsu su shigo
gidan don masu gadi sun ce ba a sanar da su xa ayi bak'i ba, ynxun ma sun fi
minti sha biyar xaune parlon suna jiran fitowar uwar gidan Bulasawa, duk sun yi
shiru kamar masu xaman makoki, can dai Hajiya Saude na kallon Umma murya can
kasa tace "Anya shawarar nan tayi kuwa Hajiya Rukayya??" Umma na
kallon Safeenah tace "Ni ban kawo hakan a kai ba fa, sai da Safeenah ta
kawo shawarar, kuma jikina ya bani da nasara...." Safeenah ta tabe baki
tace "Ku dai ba ni nace ayi haka ba?? ku kwantar da hankalin ku kawai, na
fa san abinda nake, haka kawai ga hanya mafi sauki kuyi ta kai ma katti kudin
ku suna cinyewa, har yanxu ban ga alamar abun da ake ta ce maku ba gashi saura
sati a kai lefe a sa rana, ga dai hanya straight...." Umma tace "A'a
wllh babu me cinye min kudi, ana biya min bukatata yanda ya kamata... So nawa
kuma??" Shigowar Mummy parlon sanye da hijab har kasa yasa duk suka yi
tsit, kallonsu ta dinga yi har ta karaso ta xauna saman kujera, Umma na murmushi
tace "Sannu da fitowa Hajiya" Mummy tace "Yauwa daga Ina?"
Umma tayi yar dariya tace "Lahh, baki gane ni ba Hajiya??" Mummy dai
sai kallonta take don sarai ta gane ta, can kuma ta girgixa kai tace "A'a
ni ban gane ku ba, daga Ina?" Umma tace "Toh ni dai sunana Hajiya
Rukaiya, in dai kina jin Barrister Ahmad Yusuf na nan kaduna to Mai gidana
ne..." Mummy bata daina kallonta ba tace "Ohk..." Umma tayi kasa
da murya tace "Hajiya a matsayina na yar uwar ki musulma na xo maki
taimako albarkacin musulunci..." Da mamaki Mummy tace "Taimako kuma?
Wani irin taimako nace maki ina bukata??" Umma ta gyara xama tace
"Hajiya don nace na xo maki taimako ba ina nufin kudi ko wani abu gareni
da xan baki ba don kin fi karfinsu, amma ki sani wllh wllh taimakon nan sai ya
fi maki kudi ko wani abu na kyale kyalen rayuwa... Hajiya kin san shi aure ba
abu bane da xa ayi na rana daya a gama ko na wata daya, A'a rayuwa ce da ake
fata ya xama na har abada, kin ga wannan yarinyar da d'an ki ke nema??"
Ita dai Mummy kallonta kawai take, Umma tace "Toh wllh wllh kin ji
rantsuwar musulmi sickler ce, sannan kin ga yanda kika ganta ita kadai, to har
gun iyayenta ita kenan takk... uwar ta fi shekara 13 bata haihu ba, kafin daga
karshe taje ta san abinda ta yi Allah ya bata yar, wanda da Allah ya tashi
kamata ya hadata da sickler, har yau kuma wllh tllh uwar ta hana uban karin
aure kiri kiri, sannan babu wanda bai san abinda take ba, daga ita sai yar suke
yanda suka ga dama a daulan uban, matar kanin mijina ne uwa daya uba daya, kin
ga dai ba kishiyata bace ita balle ace ina ma 'yar ta bakin ciki, ko daya wllh
ba haka nake ba, gaskiya ce duk inda take sai na fade ta, yanxu haka maganar da
nake maki d'an kishiyata Yusuf ni ce kan gaba gun nema masa aure gidan Alhaji
Mukhtar Kiyawa da kika sani dai na nan garin, wllh wlh mahaifiyar yarinyar nan
ba mutuniyar kirki bace muguwar bafillatana ce ta karshe, kije anguwar mu
malali ki shiga gidajen layinmu kaf kiyi tambaya a kanta xa ki sha labari, tayi
kadan in mata hassada wllh balle ace ko hassada nake mata, Bari ki ji Hajiya
wllh a ta dalilin ta Mai gidana ya min kishiya, ta cusa masa aminiyarta ina ji
Ina gani ta aure min miji, ita kuma taki barin a mata kishiyar har yau gashi ba
haihuwa take ba, ita ma kuma ita kenan gun uwarta, sae gashi ta haifi kwaya
daya ita ma, kakar yarinyar ma gwaggwo ita kadae iyayen suka haifa aka ce,
kamar yanda baxan so Mujaheed da abinda xai cutar da shi a rayuwa ya xame masa
wahala ba haka baxan so ma duk wani matashi ko da ba ni na haifesa ba, a wata
wllh uban yarinyar na kashe mata kudi ya fi dubu dari biyu, kullum cikin abu
daya ake idan ciwon ya matsa mata kuwa ke kya ce baxata yi ba, shi sa nayo
tattaki in sanar maki ki ceci d'an ki, barin ma shi da yake d'an ki na
fari....."
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
68......
Umma tayi shiru tana kallon Mummy tana jiran jin abinda xata
ce, sai dai fa gabanta faduwa yake, Safeenah da Hajiya Saude ma kallonta suke
su ji abinda xata ce, Mummy da tayi shirun kusan minti biyu ta sauke ajiyar
xuciya daga karshe tace "Alright, I will look into the matter, nagode da
shawara" Umma tace "Atoh, banda mai sonka wa xai kawo maka haka har
gida, yanxu xamani ya lalace mutane basu son fadin gaskiya ga ta nan dai kiri
kiri ana ganinta, wllh bbu wanda bai san abubuwan nan da na gaya maki ba amma sai
mutune su yi gumm su xuba ido, to mu ba mu gaji haka a xuri'ar mu ba
gaskiya" Hajiya Saude tace "Wllh ko a gaban uwar yarinyar ce xa mu
iya fadin abinda Hajiya Rukayya ta fada maki a nan tunda ba tsoronta mu ke ba,
gaskiya ne dai sai mun fada, sam matar bata da hali, makirace ba ta wasa ba,
yanxu haka ita gani take ta ci nasara tunda bbu wanda ya isa ya fito ya fadi
aibunta duk ta rufe bakin kowa...." Mummy tace "Na ce maku xan yi
shawara ai koh?" Umma tace "Toh Allah ya baki ikon yin wanda baxa ki
dawo kina da kin sani ba wataran, Allah kuma nuna maki duk abubuwan da muke
fada da idon ki, kai ko spy mace ne xa ki iya biya ta dinga shigowa gidan namu
taga wainar da ake toyawa, wllh wllh duk ta mallake gidan......" Daga haka
ta mike tana murmushi tace "Nagode da lkcn da kika bani Hajiya, Allah
ubangiji ya mana xabi nagari..." Tana nuna Safeenah tace "Yar wajen
Hon Usman Basiru ce wannan... Kuma surkata ce d'ana na fari ke aurenta, yanxu
haka sun kusa wata uku da aure" Mummy na kallon Safeenah tace "Maa
sha Allah, that's nyc, Allah ya bada xaman lafiya" Safeenah ta mike tana
amsawa da Ameen, Hajiya Saude ma ta mike nan suka yi ma Mummy sallama, Mummy
tace "Toh nagode, sai anjima" Umma tace "Mu jima da yawa
Hajiya" kofa suka nufa kafin su isa kofar Sadeeq ya shigo parlon, kallon
Umma ya dinga yi da mugun mamaki da su Safeenah, Umma ta sunkuyar da kai ta
fita parlon su Hajiya Saude na biye da ita, Sadeeq na kallon Mummy ya karasa
cikin parlon ya xauna har sannan fuskarsa na dauke da surprise yace "Mum
what is she here for??" Mummy tace "It's not necessary you know
Sadeeq" ya mike cike da damuwa yace "Why will u say so mum, don Allah
ki gaya min me ta xo yi?" Mummy ta mike tace "Nace maka it's not
necessary Sadeeq, I am busy upstairs pls" daga haka ta wuce ya bi ta da
kallo, a hankali ya koma kan kujera ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujeran
ya rufe ido xuciyarsa na bugawa.
Bayan kwana biyu Sadeeq ya shigo part din mum dinsa ya ganta
da sisters dinta da few frnds a parlor suna xuba lafiyayyu kuma tsadaddun kayan
lefen da aka yo daga Dubai cikin boxes set shidda sau biyu, sosai boxes din
suka yi kyau sannan they look sooo unique kana gani kasan ba da kudin wasa aka
siye su ba, Mummy na kallonsa tace "Perfumes da kace xaka Karo fa??"
Yana dai tsaye yace "Ohk suna wajen Aunty" ta masa wani kallo tace
"Wajen Aunty Kuma?? Me ya kai su can?" Shiru yyi bai ce komai ba,
Kawar Mummy Hajiya Farida tace "Toh Aunty ce ta nemo maka mata da xaka
bata kudin siyan turarurruka, kai sai samm baka san ciwon kanka ba Sadeeq, kila
ma har ka hada yarinyar da ita Auntyn koh?? tunda ga kanwar uwarka" Shi
dai bai ce komai ba, ya juya ya fita, Mummy ta bi sa da harara, Hajiya Farida
tace "Ni fa ban ji dadin da tasan yarinyar tun a asibiti ba wllh, Bai
kamata ta san komai ba a maganar auren nan"
Imaan na xaune dinning
misalin karfe sha daya na safiyar lahadi tana answering past questions din
gabanta kasancewar gobe xa su fara waec, aka bude kofar parlor.... Inna ce ta
shigo parlon da sallama Imaan na kallonta har ta karaso ciki tana tabe baki
murya can kasa tace "Ko turaren wuta bana jin an sa ma parlon nan yau,
dama fa tsafta sai wanda Allah ya so da Rahama yake ba ma, mu dai mun gode
masa....." Imaan tace "Toh ba sai ki sa mana ba tunda ba mu sa
ba" da sauri Inna ta juya ta kalleta, Bata dai ce komai ba ta xauna saman
kujera, Imaan ta ajiye pen din hannunta ta shigo parlon tace "Ina xa ki je
da sassafe haka?" Inna tace "Ina xan je kuwa da ya wuce gidan
Mujaheed, wa gare ni banda Allah sai shi, jiya fa haka ya xo bashi da isasshen
lafiya duk ya rame sai 'yan idanuwa, ya xama wani tsololo da shi sai tsayi
kamar pal waya, ni dai ba ruwana wllh, Mujaheed da ko ciwon kai da kyar ka ji
yana yi sai gashi duk ya xabge haka kamar ana cin namansa, ni ko nace anya
matar nan ba mayya bace aka lika masa ya aura kuwa?? Tun fa da aka yi auren
yake a haka yau lafiya gobe babu, toh ni dai yanxu gidan xan tafi idan ma
Safara'u mayya ce muna hada ido xan gane, mayu kuma wasu iri ne ba mu kara da
su ba a duniya, Ni wllh har dambe nayi da mayya, kuma da kyar idan Safara'u ba
mayya bace" Imaan dake kallonta da mamaki tace "Mayya kuma Inna"
Inna tace "Oh oh Allah, to idan ba mayya bace mecece, ce min yayi fa bai
san me ke damunsa ba da na tsare sa jiya, wllh da barbajin gaskiya a xancena,
ni dai duk abinda ya samu Mujaheed ni ya sama kuma baxan xuba ido haka ba, a
kan Mujaheed sai duk in tada gidan nan Al-quran, ni bai fiye min kowa sau dubu
dari biyar ba aka ce maki, idan xa ki tafi ki shirya ki tafi ki shirya mu tafi
gidan yanxu in san abun yi, dama kuma ki taho da takadda da biro duk yanda muka
yi da shegiyar matar xa ki rubuta min, don tambayoyi xan mata na dangin uwa da
uba, a nan xa a gano tushen abun...." Xaunawa imaan tayi tana kyalkyala
dariya sosai, Inna ta wani hade rai tana kallonta tace "Amma ke kam baki
da da'a, Meye abun dariya a nan jikana na can rai a hannun Allah, Toh ni fa
wllh a kan Mujaheed sai ince a fasa kawo kayanki da sadaki yau ba ruwana, haka
kawai jikana ba lafiya xa a cika ma mutane gida da jama'ah... Bari ma in je in
sami Ahmadu yanxu tunda ke matar banxa ce baki da mutunci" wani kallo
Imaan tayi mata tace "Toh ni ce bani da lafiya da xa a fasa kawo
kaya???" Inna ta saki baki tana kallonta, can ta mike tana kwalo ma Ammi
kira, Ammi ta fito da sauri tana amsawa, rai bace Inna na nuna mata Imaan tace
"Wllh jaraba kika haifa Aisha, mu dai kaf danginmu babu butulu wllh ban
dai san ya naku yake ba, gaskiya imaan butulu ce, banda haka kiri kiri ta fito
ta nuna ciwon d'an uwanta bai dameta ba saboda tana 6arin jiki tayi aure, baki
ta6a xaunar da ita kin bata labarin irin bakar wuyar da Mujaheed ya sha da ita
tun tana tsummarta bane wai? Ni dai wllh a dinga jin tsoron Allah, wllh baki
xaunar da ita kin sanar mata ba da baxata fifita aure kan d'an uwanta na jini
ba, idan ban sa an fasa kawo kaya ba gidan nan yau a kan Mujaheed ace ba ni
bace, lefen banxa da hofi jikana ya fi lefe ne, wllh jiya baccin kirki ban yi
ba sai da safe bacci ya kwashe ni, ban tashi ba sai daxu na shirya a gurguje na
taho ta raka ni gidansa in ga abinda yake ciki, nace to ko ma matar ce mayya
xan je in ga" Imaan ta tabe baki tace "Ba fa inda xan je gobe Ina da
jarabawa, ko kuma ni likita ce da xan biki...." Inna ta fashe da kuka ta
nufi kofa tace "Eh lallai Imaan ta xama jarabar duniya, Bukar ya haifi jaraba,
Allah ka mana iyaka da Butulu duk inda yake.... Bari naje in samu Ahmadu ai na
fi ki tsiya yau" daga haka ta fice daga parlon, Imaan na turo baki ta juya
xata koma dinning Ammi tace "Wuce ki shirya ki bi ta ku tafi" ta juyo
da sauri kamar xata yi kuka tace "Ammi karatu fa nake, ni wllh bana son
xuwa gidan Yaya..." Ammi ta hade rai tace "Musu xa ki tsaya yi da ni
kenan?" Lkci daya hawaye ya kawo idonta ta wuce dakinta, atamfa riga da
skirt ta fiddo ta saka bayan ta feshe jikinta da turare, ta goga chappete a
bakinta ta sa gogaggen Hijab dinta har kasa ta fito parlor rike da wayarta da
karamin jaka, Ammi dake xaune parlor ta bi ta da ido, a hankali tace "Ammi
sai mun dawo" Ammi tace "Allah ya kiyaye, you pray before
leaving" Imaan ta gyada mata kai ta nufi bakin kofa tana karanto addu'ar
fita gida a ranta. Part din su Maimoon ta nufa ta bude parlon ta shiga a
hankali, ko karasawa cikin parlon bata yi ba ta dinga jin Muryar Inna a parlon
Abba tana cewa "Gaba daya Imaan ta banu ta lalace, sam bata da kirki
yanxu, amma abinda ya ban tsoro shine yanda aka boye mata wuyar da Mujaheed ya
sha a kanta, bata fa yarda da kowa a lkcn sai shi sai uwar, duk ta fitsare masa
jiki, har uban nata Bukar tsoron sa take... Toh meye kuma lkci daya sai yarinya
ta xama jarababba mara Imani, ni ka ma kira min Bukar din in ji ko su ke koya
mata, dariya fa ta dinga ba66akawa daga nace mata Mujaheed ba lafiya xan je
gidansa, ni wllh na gaji da imaan a gidan nan" shi dai Abba bai ce komai
ba kansa na kasa yana sauraranta, ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana, shi
kuma Mujaheed gaskiya sai mun tashi tsaye kansa don idan aka rasa sa ni nayi
asara ba wani ba, idan ma auren ne bai so gaskiya sai a raba yau yau din nan,
ba ruwana a kai ni a baro in shiga uku" Sai a sannan Abba ya kalleta yace
"Xaxxabi fa kawai yake, amma ai yana jin sauki yanxu..." Tsaki Inna
ta ja tace "Tunda ba jikin ka bane ba dole kace yana jin sauki ba Ahmadu,
gansamemen mutumi da ya dinga min rawan sanyi jiya sai da na rufa sa da katon
bargo shine xaka ce yana jin sauki, ku dai ku dinga jin tsoron Allah, wlh ku ji
tsoron Allah, tunda ba wani ya min wahala da shi ba to ni xan je yanxu inji
abinda yake ciki, idan ma matar ce mayya duk xan gani" Da mamaki Abba yace
"Subhanallah, haba Inna ya kike irin wannan magana haka, wannan fa babban
magana ne ka ce ma mutum maye...." A fusace Inna tace "Na ce mata
mayyar, idan ba mayyar bace ina dawowa ai xan ce ba mayya bace, tsoron ubanwa
aka ce maka xan ji banda Allah, shi kadai ne abun tsoro dama, kuma ni da shi
nayi imaani" dai dai shigowar imaan parlon, kanta a kasa ta gaida Abba,
Abba ya amsa yana tambayarta jiki domin jiya yini tayi ciwon kafa, Inna tace
"Ya jiki?? Ce maka aka yi bata da lafiya, Ga dai bawan Allah me ciwo can a
kwance xaka tambayi lafiyayyar mata ya jiki" tana fadin haka ta tabe baki
ta mike tace "Toh yanxu xa ka kirasu ka sanar masu d'an ka na fari ba
lafiya a bar kawo lefen da kudin aure sai wani satin koko?" Da sauri Imaan
ta kalleta, Abba yace "Haba Inna, ae wannan bai shafi ciwon Mujaheed ba,
Ina ruwansu da wannan, shi Mujaheed din yaro ne, don Allah ki yi hakuri ki bar
xancen nan Inna bai ma kamata ba, ga yanda dai muka yi da mutane kuma ki kawo
wata magana daban" Inna tace "Atoh ni dai duk abinda ya sami jikana
Allah ya isa wllh...." Daga haka ta fice daga parlon a fusace, Imaan tace
"Abba sai mun dawo" ya gyada mata kai kawai ta bi bayan Inna, har
suka isa titi Inna bala'i take idan abu ya sami Mujaheed ya sami kowa, ita dai
Imaan sai turo baki take tana tsaye gefenta, Inna ta tsayar da adaidaita ta
shige yana tambayarta inda xata a fusace tace "Don Allah ka rufa min asiri
yaro ka ja mashin dinka mu je, meye kuma Ina xanje kamar yar yarinya, jikana ne
fa ba lafiya rai a hannun Allah gidansa na can unguwar dosa ana ma kyautata
xaton matar ce mayya, kuma kana ta cewa ina xan je" Mai adaidaitan bai
tanka ta ba, Imaan ta hade rai ta shige adaidaitan. Har suka isa gidan Mujaheed
mita take ita kadai daga imaan har mai napep babu mai ce mata komai, suna sauka
kafin ta fiddo hamsin ta mika masa Imaan ta basa dari biyar din hannunta don bata
ma son dogon xance, ya ciro dari biyu ya mika mata, Inna ta saki salati tace
"Nawa ka cire bawan Allah?" Imaan tace "Toh ai ba kudin ki bane
Inna, kayi wucewan ka kawai" Mai adaidaitan ya ja napep dinsa yyi gaba
Inna ta dinga jaraba tana kiransa barawo tuni imaan ta shige cikin gidan ta bar
ta tsaye a bakin gate, dai dai balcony ta tsaya ta rungume hannu tana jiran
shigowarta, Can sai ga ta ta shigo compound din tana cewa "Babu abinda
kudin Bukar xai masa a rayuwar nan ta duniya, iyaka ma ya gudu ne da wahala da
Bala'i tunda bamu basa ba" bata ko kalli Imaan ba ta murda kofar parlon ta
bude ta shiga, Imaan ta turo baki ta bi bayanta, Umma ce ta leko daga kitchen
tana soya kwai da dankali, Inna ta rike ha6a tana kallonta a hankali tace
"Wacece wannan?" Umma dake sanye da hijab har kasa ta gaisheta a
dakile ta koma kitchen din, Safeenah ce ta sakko parlor sanye da doguwar riga
na material hannunta rike da tray na cup, ganin Inna ta dauke kai ta hade rai
hade da tabe baki tace "Sannu da xuwa" Inna tace "Ina Mujaheed
din???" Safeenah tace "Yana sama an sa masa drip" Inna tace
"Ai ni na shiga uku, abun har ya kai an fara sa drif... Toh aniyar kowa
xai bi sa wllh babu abinda xai sami jikana" Kallon Imaan tayi tace
"Ke mu je in gansa..." Imaan ta nufeta, da sauri Safeenah tace
"Inna a can dakinsa yake fa...." Inna ta juya tana kallonta tace
"Dakinsa kuma? Toh da ina nace maki xan je banda dakin nasa? Ko nace maki
dakin ki xan shiga Safara'u?" Safeenah tace "A'a da naji kince ku
tafi, idan ma tafiyar ne ke da kike matsayin kakarsa ai sai ki tafi dakin"
Inna ta gyara tsayuwa tace "Toh ita Imaan din fa??" Safeenah ta d'an
hade rai tace "Wannan ba hurumin ta bane gaskiya shiga dakin mijina, bata
da wannan hurumin, dakinsa sirrina ne da nashi" Salati Inna ta xabga ta
xauna kan kujera tayi tagumi tace "Naga abinda ya isheni ni Asabe...
Safara'u kinsan me kike cewa kuwa, wani sirrin ku ke da shi ke da Mujaheed da
ba mu sani ba, kinsan wacece kike kokarin hana shiga dakin nasa kuwa???"
Umma ta fito kitchen bbu yabo bbu fallasa tace "A'a inna, xancen gaskiya
ayi ta, dakinta ne da na mijinta fa kuma kice wata daban ta shigar masu, a kan
wani dalilin?? sai kace dai a garin ga6a ga6a muka taso, ko a musulunce ai
hakan haramun ne ma wata ta shigar maki turakan miji..."
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
69. Imaan
Mikewa Inna tayi ta bude baki tana kallon Umma tace
"Rukayya ita imaan din ce wata a gidan Mujaheed?? Ita Imaan din?? Ehh
lallai ba shakka kin xama mahaukaciya, to wllh tllh Imaan ta fiye ma Mujaheed
Safara'u sau dubu dari, wacece kuma Safara'u Allah na tuba?? Sannan yaushe kika
san Allah da kike kokarin min wa'azi wai kar ta shiga daki ta duba yayanta? Toh
kwanciya tace maki xata yi a dakin idan ta je?? Ko ko ce maki tayi bata da
kwakkwaro kamar ki ne?? Ni dai na ga abinda ya isheni, ba kunya ba tsoron Allah
kin kwaso jiki xalalo xalalo kin xo gidan surka kina girki a kitchen ita kuma
tana sama wajen miji, anya Rukayya?? A'a tunda uwata ta haifeni ban taba gani
ko jin haka ba wllh, Toh ni duk ba wannan ba, don bai dameni ba... Babban
magana a nan shine gaskiya ban gane kan ciwon jikana ba, don wannan ciwo ba na
Allah bane, tunda ya auri wannan mata Safara'u yayi bankwana da lafiya, yau
ciwo gobe lafiya, yau fari gobe tsumma, To a kan me? Ita Safara'un yar wace
gari ce in ji tukun kafin in san abun yi" Umma ta dinga mata wani kallo
tana jin kamar ta tanka ta amma wata xuciyar na bata hakuri, fuska daure
Safeenah tayi wucewarta kitchen tana kas kas da cingam ta bar su nan tsaye,
Inna ta gyada kai tace "Toh kya ci uban ki kuwa ba dai jikana ba don
kurwarsa daci ne da ita yarinya, in sha Allahu sai dai ki ci uwarsa da ta
jajibo ki ba shi ba, kuma xaman ki saura kiris a gidan nan" daga haka ta
ja hannun Imaan dake tsaye gefenta suka wuce sama tana huci, Umma ta bi su da
wani kallo xuciyarta na tafarfasa tasan dai ko hauka take baxata tanka Inna ba,
Inna ta bude kofar parlon dake sama ta shiga, Ganin Imaan ta ki shigowa ta
fixgota a fusace ta nufi dakin Mujaheed da ita, Imaan dai sai bin ta take,
kwance Mujaheed yake saman gado idonsa rufe, Inna na kallon empty robber din
drip dake sakale ta rike ha6a tace "Ka ji jarababbu mayu, wai an sa masa
ruwa yana daki, alhalin ga ruwa ya kare..." Bude ido Mujaheed yyi, Inna ta
fashe da kuka a hankali ta nufesa tace "Sannu Mujaheed, in sha Allahu babu
abinda xai sameka in dai ina da rai, asiri dai ya gama tonuwa na gano
komai" shi dai gaba daya hankalinsa na kan Imaan da tayi tsaye bakin kofa
ta ki shigowa kuma ta ki yarda su hada ido sai wasa da fingers dinta take, Inna
ta xauna gefen gadon tana goge guntun hawayen idonta tace "Kwana nawa da
aurenta ka fara jin canji a jikin ka??" Shi dai bai ce mata komai ba har
sannan yana kallon imaan, Inna ta juya ta kalleta tace "Ke dai baki da
kirki wllh, halin ki abun tsoro ne gaskiya, baxa ki karaso ki gaida sa ba"
sai a sannan imaan ta kalli Mujaheed, suna hada ido tayi saurin dauke kai ta
karasa cikin dakin ta duka kasa kusa da gadon a hankali tace "Ya jikin
Yaya?" Bai tanka ta ba, Inna tace "Atoh, abinda ma da kyar ta biyoni
Mujaheed, wllh Imaan bata da imaani, har fa ce min tayi toh ita ce bata da
lafiya da xance a fasa kawo kayan aurenta yau sai wani satin sabida baka da
lafiya...." Mujaheed dai ya kasa daina kallonta, imaan ta wani hade rai
tana kallon Inna, bude kofar dakin aka yi sai ga Safeenah ta shigo da warmer a
rufe da plate a hannunta, ko kallonsu bata yi ba ta karasa ciki ta ajiye ta
xauna kusa da kansa tana wani yauki tace "Baby ka tashi ka ci ko kadan ne
sai ka sha drugs dinka plss, bacci ma ya kamata kayi ka huta bayan ka gama cin
abincin tunda sai ltr xa a sa wani drip din" Imaan ta dinga hararanta ta
gefen ido, Inna ta tsuke fuska ta rungume hannu tana karanto addu'a a xuciyarta
tana tofawa a duk angles din dakin, Mujaheed ya mike xaune ya cire duvet din
jikinsa yana kallon Safeenah yace "You don't worry anjima xan ci, na sha
tea yanxu" tace "Toh ayi maka pepper soup din ko appetite dinka xae
dawo?" Da kamar baxai ce mata komai ba sai kuma yace "Ohk" Ta
mike tana wani cat walking ta nufi kofar fita tana karkada jiki, Imaan ta wani
tabe baki ta dauke kai fuska daure, Safeenah na fita Inna ta mike ta dau
abincin ta bude window ta xaxxage gaba daya downstairs ta juyo tana kallon
Mujaheed murya can kasa tace "Mayya ce Mujaheed...." Bude baki yayi
yana kallonta da mamaki, ta kyabe baki ta cire Hijab dinta ta linke tace
"Jira in je in soya maka wani gaskiya, Allah ba batun wasa ba an gano
mayya ce amma kada kace mata komai tukun, a hankali ake kama barawo, anjima ta
Rasulu tace min xata xo nan....." Bai san lkcn da yyi murmushi ba bai dai
ce mata komai ba, kofa Inna ta nufa fuska daure ta fita xata kitchen ta masa
girki, Imaan na ganin haka ta mike da sauri ta nufi kofa yace
"Fatima" tsayawa tayi sai dai bata juyo ba, jin bai ce komai ba a
hankali ta juyo tana kallonsa, taga kallonta yake, sosai gabanta ya fadi, kamar
xata yi kuka tace "Na'am" jin yyi shiru ta karasa kusa da gadon ta
durkusa tace "Ga ni" ya sauke idonsa daga kallonta yace "Ya
preparation na exams?" A hankali tace "Lafiya lau, how are you
feeling now?" Yana kallonta yace "Dama kin san bani da lafiya
ashe?" Tace "Aa ni Inna ce ta gaya min daxu Allah ban sani ba"
Bai ce komai ba hakan yasa tace "Xan je in taya Inna" yace
"Promise me baxa ki wuce gida ba daga nan" murmushi tayi ta boye
fuskarta da gado don abinda ke ranta kenan, ji tayi ya kamo hannunta ta dago da
sauri yace "Kar ki tafi yanxu Imaan" ta turo baki tace "Bayan
Umma tana nan, kuma matar ka sai wani hararana take yi, ni dai wucewa xan
yi" yace "Toh kiyi xamanki a nan" ta xaro ido tace "Kaga
Inna ta wuce fa, salon idan matarka ta shigo ta xageni ko" yace "Kina
dai son wucewa kawai" tana murmushi tace "Toh naji baxan wuce ba,
amma me ke damun ka Yaya? Ji fa ka rame sosai" Ya jinginar da kansa da
gado murya can kasa yace "Ban sani ba" ta langwabar da kai tace
"Kana likita kuma baka sani ba, or is about our last talk, I mean about
the lady..." Shiru yyi yana kallon Ac dake aiki a dakin, murya can kasa
yace "Yau xa a kawo kayan ki koh?" Dariya tayi ta boye fuskarta tace
"Uhm nima ban sani ba" jin bai ce komai ba ta dago tana kallonsa,
kallonta taga yana yi da manyan idanuwansa, ta sunkuyar da kai tana murmushi
tace "Ehh yau ne" yace "And u are happy" ta turo baki ta ki
cewa komai, sauke kafafuwansa yyi daga saman gadon ya nufi press dinsa ya fiddo
gogaggen shirt xai saka a kan singlet da 3 qtr din jikinsa, Bude kofar dakin
aka yi sai ga Safeenah, da wani expression ta dinga kallonsa sai kuma ta kalli
Imaan a nutse tace "Malama tashi ki fitar min dakin miji, naga alama
karuwancin naki ba iya waje ya tsaya ba har gida" Imaan na mata wani kallo
tace "Karuwanci kuma? To sai dai in kece karuwa....." Bata rufe baki
ba Safeenah ta sauke mata mari tana wani
huci tace "Ni kike ce ma karuwa a dakin..." ita ma bata kai karshe ba
taji saukan wani wawan mari da yasa ta ji dumm a kunnenta, da kyar ta juya tana
ganin stars ta kallesa cikin rawar murya tace "Mujaheed. .." ya kuma
wanke ta da wani mahaukacin marin ya fixgota yana huci yace "Kinsan warce
kika mara Safeenah??" Safeenah ta xaro ido a tsorace tana kallonsa, sai
kuma ta rushe da kuka cikin tashin hankali tace "Yanxu a kan wannan
matsiyaciyar ka mareni Mujaheed, a kan wannan sauran ciwon....." Hankada
ta yyi iya karfinsa don har sai da ta fadi kasa timm, Yana nuna ta calmly yace
"Kece matsiyaciya ba ita ba" Safeenah ta mike da sauri ta fice dakin
da gudu tana kuka, Imaan da hankalinta yyi mugun tashi tana kallonsa cikin
rawan murya tace "Yaya me yasa ka mareta, ai xan iya ramawa da kai na, why
did you slap her, you shouldn't have, beside umma fa na gidan" Mujaheed ya
rikota cikin daga murya yace "Did you know what I felt da ta mare ki
imaan?? Kinsan abinda naji?? Me yasa xata daga filthy hand dinta ta daura a
fuskarki??" Ta dinga kallonsa da manyan idanuwanta ko kiftawa babu, yyi
kasa da murya yana sauke numfashi a hankali yace "Wlh da ni ta mara baxan
ko daga kai in kalleta ba, why will she slap you Imaan???" Kallonsa kawai
imaan take ganin yanda idanuwansa suka kada sosai, lkci daya ya rungume ta ya
lumshe ido, a hankali ta kwantar da kanta kirjinsa tana jin yanda xuciyarsa ke
bugawa tana shakan daddadan kamshinsa, gently ya dinga tafiya tana jikinsa har
ya isa kofa ya sa makulli. Inna na kitchen tana aikin suyan dankali da kwai,
Umma ma na kitchen din fuska daure tana dauraye kayan miya da xa ayi ma
Mujaheed pepper soup, lkci lkci take xabga ma Inna harara ta dinga addu'ar da ma
man gyadan dake kan gas din ya kware a jikinta kowa ya hutu a duniyar, Inna ta
kwashe dankalin karshe a mai tana tabe baki tace "Ba ruwana, ni sai in sa
Ahmadu ya tattaro min kayana ma in dawo nan gaba daya, don dai in masa girkin
abincin da xai ci ransa kadai kar a cucesa, ni a ma kira min Ahmadun in gaya
masa jikin Mujaheed ba sauki masu kawo lefen nan su dakata kawai lefe bai fi
jikana ba gaskiya" Umma ta kalleta da sauri, sai kuma tayi kasa da murya
tace "Lallai kam, ace duk yanda suke da Imaan baya nan xa a kawo lefe da
kudin aurenta, abun bai yi ba gaskiya, daxu daxun nan da safe na gama maganan
nan" Inna tace "Atohh, ko tsari babu wllh, Ahmadu ya ki saurarata da
yake kunnen kashi garesa, ni bari a kara kiransa in jaddada masa halin da na xo
na samu Mujaheed a san abun yi" tana fadin haka ta fice kitchen din, Umma
ta kashe gas ta bi bayanta da sauri, jakarta ta dauka ta bude ta dau wayarta ta
mika ma umma tace "Kira min Ahmadun" Umma ta nemo lambar Abba ta kira
ta sa a hands free ta mika mata, Abba na dagawa Inna tace "Toh wllh Ahmadu
Mujaheed na nan rai kwakwai mutu kwakwai, ko magana bai iya yi balle ya ci wani
abun, idan xa a ji ta nawa to a dakatar da masu kawo kayan nan xuwa sati mai
xuwa, aure bai fi rai ba ku ji tsoron Allah Ahmadu.... Mujaheed rai
garesa" Abba dake ta saurarenta yace "Sun kira suna tahowa nan da
wani lkci, don haka babu fa'idar fasa komai, sannan ba wai jimawa xa ayi ba
balle kice, da sun tafi xa mu taho da Abubakar da likita tunda yaro Mujaheed
din ya xama" Inna tace "Toh kuwa kun xama abun tsoro wllh, Allah ya
mana tsari da ku" daga haka ta mika ma Umma tace "Kashe min wayata
maxa, ni dai ina ganin jarabawan rayuwa" Umma ta katse wayar gaba daya rai
ba dadi, don tun safe da ta ji labarin xa a kawo lefen Imaan ta gane xancenta bai
yi tasiri ko kadan a gun uwar Sadeeq ba, tun sannan ta kasa xaune sai da ta
taho gidan Mujaheed don fada ma Safeenah abinda ake ciki, tana xuwa kuma ta
iske Mujaheed kwance wai ba lafiya an sa masa drip, abinda ma ya tsayar da su
basu fita ba kenan amma da tuni sun baxama neman duk abinda xai sa a fasa shigo
da lefen Imaan gida, a hankali Umma tace "Ba a kyauta ma Mujaheed ba amma
gaskiya" Inna tace "Toh wa gareni da xan ma magana ya ji, ai Ahmadu
ya dauko hanyar lalacewa shi ma, shi dama Bukar bana sa shi a lissafi kwata
kwata" Umma tace "Toh ko xaki ma shi yaron magana, naga kuna shiri
sosai" Inna ta mika mata wayar tace "Yauwa duba xa ki ga Bulasawa ki
kira, ae yana da fahimta, kawai ce masa xanyi Imaan tace tana jin nauyinsa don Allah
in masa magana a dakatar da kawo kayan don yayanta bashi da lafiya yana kwance
har da karin ruwa leda uku" Umma ta amshe wayar da sauri tace "Toh
hakan ma yyi wllh" tana kiran number Sadeeq ta sa handsfree ta mika ma
Inna, Inna ta karbe wayarta ta nufi kofar ta fice parlon gaba daya, Umma ta bi
ta da wani kallo tana murmushi, dai dai nan Safeenah ta sakko kasa tana kuka
sosai har lkcn tana rike da kuncinta, hankali tashe Umma ta nufeta da sauri
tana cewa "Lafiya Safeenah me ya same ki?" Cikin kuka sosai tace "Hajiya
a kan wannan shegiyar yarinyar Mujaheed xai sa hannu ya mareni har sau biyu,
Mujaheed ya rasa warce xai mara sai ni? Mujaheed slapped me???" Bude baki
Umma tayi tana kallonta da mugun mamaki tace "Shi Mujaheed din ya mare
ki??" can ta juya ta wuce sama kamar xata tashi sama, Sosai Imaan ta
rikice jin muryar Umma tana bubbuga kofar dakin kamar xata cire tana kiran
sunan Mujaheed, Lkci daya hawaye ya kawo idonta ta rikosa cikin rawar murya
tace "Wayyo Yaya ka gani ko" Xaunar da ita yyi gefen gado ya duka
kusa da ita murya can kasa yace "Relax now, ba shigowa xata yi ba na rufe
kofar" Inna ce ta shigo parlor tana tabe baki tana kallon wayarta, ganin
Safeenah na rusa kuka ta isa kusa da ita ta duka tana kallonta da mamaki, can
tace "saboda na xubda girkin da kika masa shine kika xauna nan kina kuka?
Ke kya yarda a cuci wani naki??" Bata jira cewarta ba ta wuce sama, tana
isa parlon Mujaheed ta dinga kallon Umma dake ta jijjiga kofa, hankali tashe
tace "Lafiya?? Makalewa suka yi a ciki??" Umma ta ki cewa komai
xuciyarta kamar ya fashe ta huta, da karfi Inna tace "Mujaheed???"
Mikewa Mujaheed yyi daga durkushen da yyi gaban imaan da taki kwantar da
hankalinta jin muryar Inna ya nufi kofar ya bude a hankali, mari Umma ta sauke
masa tana huci tace "ita Safeenahr ka daga hannu ka mara???" Wani
salati Inna ta xabga tana kallonta tace "Kina da hankali kuwa Rukayya,
Mujaheed din kika mara hka???" Muryar Safeenah suka ji tana cewa
"Wllh baxan xauna gidan nan ba yau in har sabida wnn matsiyaciyar Mujaheed
ya mareni wllh baxan xauna" Mujaheed ya daga kai yana kallonta fuska daure
yace "Ki tafi gidan ku sae na neme ki, kar ki kara ko minti biyar
gidana...." Inna tace "Fakat, maxa tattara ina ki ina ki kiyi wucewar
ki mayya" gwalo ido Umma tayi tana kallonsa kamar yanda Safeenah ma tayi,
cike da karfin hali Umma tace "Safeenar kake cewa ta tafi gidansu
Mujaheed??" Bai yarda ya kalleta ba a takaice yace "Ehh Umma ta tafi
gidansu" juyawa Safeenah tayi da sauri ta fita parlon, Umma ta kasa cewa
komai tana kallonsa with shock can ta juya fuu ta wuce, Inna tace "Tunda
kema mayyar ce sabida me baxa ki ji haushin koran Safeenah ba, in sha Allahu
xamanta ya xo karshe a gidan Mujaheed...." Shiru Inna tayi tana kallon
Imaan ganin hawayen idonta tace "Me aka maki kike kuka?" Kin cewa
komai tayi ta juya masu baya, Inna na kallon Mujaheed tace "Kasan yau xa a
kawo kayanta da lefe, nace su Ahmadu su jira ka ji sauki ayi komai da kai sun
ki saurarata... Yanxu ga dai waya ka Kira min Bulasawa na kirasa daxu ban ji
yyi magana ba kila kiran ma bai je ba" Imaan ta juya da sauri tana kallon
Inna tace "Me xa ki ce masa??" Inna tace "Wannan ba matsalar ki
bace sirri na ne da shi" Mujaheed dai na rike da wayar yana kallonta,
ganin haka Inna ta kwace wayarta ta juya ta fita xuwa gun mai gadi don ya kira
mata Bulasawa, ganin ana wangale gate din ta tsaya sai ga motar Abba, parking
Abba yyi ya fito tare da Daddy da kawu Audu da wani frnd din Daddy daga cikin
motar, Inna ta bude baki tace "Kaddai ku ce har sun kawo kayan ni
Asabe??" Abba yace "Sun kawo har ma sun tafi, an saka biki nan da
wata guda dai dai da lkcn da xa su gama xana jarabawa, sun kuma bada sadakinta
dubu dari takwas" Inna tace "Toh da kyar idan Mujaheed xai yafe maku,
don wahalan da yyi da ita ku da ku ka haifeta ma baku yi ba, amma sbda butulci
ku amshi kudin auren yarinya ba shi sbda cuta ta kamasa?? Toh aji tsoron
mutum" daga haka ta juya ta wuce ciki fuska tsuke....
*Maa sha Allah, I will take a break till after sallah in sha
Allah, thank everyone for being patient with me all this while following the
book Imaan, ayi sllh lfya*
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
🌟⭐imaan ⭐🌟
70.....
Tun da Inna ta fita parlon Mujaheed ke kallon Imaan dake
tsaye ta wani hade rai tana kallon bakin kofa ita a dole Inna ta tafi kiran
Sadeeq a fasa kawo kaya, satan kallonsa tayi ganin ynda yake kallonta ta turo
baki ta juya xata fita yyi saurin rikota yana kallon eyeballs dinta yace
"Don't say anything about what happened between u and my wife to
Grandma" kin cewa komai tayi ta kwace hannunta ta fice daga parlon nasa ta
sakko downstairs, a nan kuma ta ji shigowarsu Abba compound din gidan da
maganganun da suke yi da Inna, Inna ta dawo parlor tana girgixa kai tace
"Tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin irin haka ba, su Ahmadu dai sun
shiga uku sun lalace tirrrr, yanxu ko Mujaheed kadai bai isa ya karbi auren
imaan ba, amma kawai mutane don ba shi da lafiya kuyi masa wannan rashin
mutunci, to da kyar idan girman ku bai fadi a idonsa ba gaskiya" Imaan dai
sai kallonta take, Inna ta xauna fuska ba annuri tace "Tirrr" Abba yyi sallama bakin kofar parlon ya shigo
sannan Daddy da Kawu Audu, Gaishesu Imaan tayi Abba ya amsa yana kallonta yace
"Ina Mujaheed din?" Inna ta tabe baki ta dauke kai tana girgixa kafa,
Imaan xata wuce sama Abba yace "Ina matar gidan?" Inna ta kallesa da
sauri tace "Wace matar gida? Matar gida da ya kora daxu, koko wata daban
kake nufi?? ai tuni yace ta wuce gidansu ba wanda bai san mayya bace, daga nan
dama ni dai daukansa xan yi mu koma gida ya xauna bangarena ayi ta masa magani
har yayi garau" Kawu Audu da ya buda ido sosai yace "Mayya kuma
Yaya?" Inna tace "Xancen kake so D'an tsut, tun fa da aka yi auren nan
yau lafiya gobe ba lafiya a haka yake kamar mai laulayi, to ina dalili da raina
kuma da lafiyata snn ba gantalalliya ba...." Ta kalli Imaan tace "Ke
tafi ki kirasa su gane ma idonsu yanda ya koma" Daddy yace "Ni ban
fahimci xancen ki ba Inna, ita matar yace ta tafi gidansu ko wa?" Inna na
kallon Imaan tace "Ke tafi ki kirasa su gansa bana son dogon surutu da
Bukar, don ba hankali isasshe garesa ba wllh, kuma a gaskiya kada Bukar ya sani
a bakin duniya ni ba ni na koreta ba da bakinsa yace ta tafi to tunda ba ubanta
ya gina masa gidan ba ba dole ta tafi ba, har Rukayya fa a nan na sameta tana
masu girki a kitchen daxu..." gaba daya dai sai kallonta suke don har
sannan babu wanda xai ce ya fahimci xancenta, Imaan dai ta wuce sama tayi
knocking kofar parlor din Mujaheed, sai da ta kara knocking har sau biyu sannan
ya bude door din bedroom dinsa, tace "Abba yana kiran ka a kasa" yana
gyada kai a hankali yace "You know what Imaan??" Tana kallonsa tace
"What??" Yayi wani murmushi yace "I want you to keep this at d
back of ur mind... all this ur pretence and everything you are doing... Billah
ranan da xan rama yana nan xuwa, I will
make u regret all this you are doing in sha Allah" on a serious note ya
fadi haka, ta buda ido sosai tana kallonsa da mamaki tace "Pretending
kuma? What am I pretending yaya? Ni ban gane ba" yace "Bana son ki
gane dama" tabe baki tayi ta juya ta bar wajen ya bi ta da kallo har ta
fita sannan yyi wani murmushi. Inna na kallonsu Abba tace "Ni fa ko
rantsuwa nayi da kyar inyi kaffara Ahmadu, wai ya xa ku maida ni yarinya da
bata san abinda take bane, komai na fada ku karya ta ni ne?? nace maku yarinyar
nan mayya ce ita ta kama min jika yake ta ciwace ciwacen da ba na
Allah...." Katse ta Daddy yyi ya mike yace "Ke dai Inna ki daina
haka, don Allah ki rufa mana asiri ki daina, ni fa gaskiya ba ruwana idan kika
jawo wata maganar, ya xa ki dinga kiran yar mutane da mayya kai tsaye, Haba
inna.... kin san wannan ba magana bace karama kuwa??" Tagumi Inna tayi a
hankali tace "Naga abinda ya isheni ni patuu... Me yasa Bukar ke min haka
a rayuwa" Daddy yyi yace "Ni gaskiya nake gaya maki, kiyi hakuri ki
daina wannan abinda kike ba shi da amfani, duk wanda kika ji bai maki ba sai
kice masa maye?? Haba don Allah, ke kin xata maita karamin abu ne, wllh ki
daina haka bai kamace ki ba kwata kwata, haka kawai ki dage kina ce ma yar
mutane mayya ki dauko mana wata maganar, this is very wrong wllh" Shi dai
Abba kansa na kasa, Inna dai bata kuma cewa komai tayi tagumi, kawu Audu yyi
kasa da murya yace "Hajiya yanxu da xa a kai maganan nan gaba...."
Tsawa tayi masa tace "Kai d'an tsut ka fita harkata, idan an kai sa gaba
uwaka xa ayi?? kada wanda ya sani a bakin duniya gaskiya, da kansa ya kori
matarsa ni ban koreta ba...." Shiru kawu Audu yyi bai kuma cewa komai ba,
Mujaheed ne ya sakko parlon cikin kananun kaya, Abba ya daga kai yana kallonsa
ko kiftawa babu ganin yanda ya rame, Daddy ma kallonsa ya dinga yi da mamaki,
ya karasa parlon yyi kasa da kai ya gaishesu, Daddy yace "What's wrong
with Muhd?" Ya d'an yi murmushi yyi kasa da murya yace "It's just
malaria amma da sauki sosai Abba" Daddy yace "Are u under
medication?" ya gyada kai yace "Sure sir" Kallonsa kawai Abba ke
yi shi dai ya kasa cewa komai, Daddy yace "But did you have any problem
Mujaheed, wannan anya Malaria ne kadai..." Inna ta tabe baki ta mike murya
can kasa tace "Har da kamun mayya ko kun ki ko kun so" daga haka ta
nufi kofa fuska daure, Daddy ya bi ta da kallon gefen ido, sai bayan da ta fita
parlon gaba daya Abba yace "Me ya hada ka da matar ka kace ta tafi
gida??" ya shafa kai a hankali yace "Abba...." Sai kuma yyi
shiru, Daddy yace "Bama son jin komai my friend, get her back immediately,
am I clear??" Mujaheed ya kallesa ya kasa cewa komai da farko, can a
hankali yace "In sha Allah Abba" Kawu Audu yace "Toh xa mu je
asibitin ne yanxu??" Mujaheed ya kallesa yace "A'a ina amsan
medication a gida kawu, ai da sauki sosai yanxu" Kawu Audu yace "Toh
Allah ya kara lafiya Muhd, Allah ya yaye maka" Mujaheed yace
"Ameen" Mikewa Abba yyi yace "Ka dai ji abinda aka ce maka yanxu,
get her back today, sannan I want you to try all possible means of stoping ur
grandma from coming to this house" murmushin karfin hali Mujaheed yayi
yana kallon Abban nasa, daddy yace "That's just it" Daddy na kallon
Imaan dake xaune yace "Ke kuma mai nuna mata hanyar xuwa gidan ko?"
Mujaheed ya kallesa da sauri yace "A'a Abba ta san hanya ai...."
Imaan ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, Daddy yace "Toh tashi mu
wuce" Mikewa tayi ta nufi kofa, Daddy yace "Allah ya kara lafiya
M.A" Mujaheed yyi murmushi yace "Ameen" Abba yace "Anjima
ka taho gida tare da matar taka" yace "Toh in sha Allah" Kawu
Audu yace "Sai ayi ta hakuri ka ji?" Murmushi kawai yyi ya sauke
kansa kasa, har bakin mota ya rakasu, Imaan ta shiga bayan motar tana kallonsa
tace "Allah ya kara lafiya" ya gyada mata kai kawai bai ce komai ba,
Daddy ya shiga front seat, Abba ya shiga maxaunin driver yana kallon Mujaheed
yace "An kawo kudin auren kanwarka, we will talk later idan ka xo
gida" A hankali Mujaheed na gyada kai yace "Toh Allah ya sanya
alkhairi...." Abba yace "Ameen" Mujaheed ya kara masu sallama
suka bar compound din ya juya kamar me counting steps dinsa ya koma parlor ya
xauna saman kujera ya jinginar da kansa jikin kujerar ya lumshe ido yana jin
xuciyarsa na masa xafi. Umma na barin gidan tare da Safeenah dama bata yarda
Safeenah ta tafi gidansu ba, ta lallabata da kyar suka wuce gidan Hajiya Saude,
Hajiya Saude ta sauke ajiyar xuciya bayan Umma ta koro mata duk yanda aka yi,
ita dai Safeenah sai hawaye take tana jin da yau xa a mika mata wuka daga ita
sai Imaan a daki babu fa abinda xai hanata ta kasheta, bata taba jin tsanar
mutum kamar yanda take tsanar Imaan ba, wai a kanta Mujaheed ya daga hannu ya
mareta har sau biyu, for what??? Hajiya Saude tace "Kuma har sun kawo
lefen koh???" Umma na share xufar da ke keto mata cikin tashin hankali
tace "Wlh muna hanya Ummi ta kirani wai ga kaya an kawo, akwatuna har sha
biyu da sadaki kusan miliyan daya, ni abun duk ya kwabe min wllh" Hajiya
Saude ta bude baki tana kallon Umma, can tace "Amma wannan uwar yaron anyi
tsinanniya, wato hauka ta manna mana wai xa tayi shawara" Umma tayi tagumi
bata ce komai ba, Hajiya Saude tace "To yanxu meye abun yi kuma??"
Umma tace "Auren nan fa ko ana ha maza ha mata baxa ayi sa ba in dai ni
Rukayya ina da rai, wato sun ma ci bulus kenan da uwarta idan na hakura aka yi
auren" Hajiya Saude tace "Gaskiya kam gashi daga ita ba wata balle
ace a hakura xuwa wani lkcn" Umma ta mata wani kallo tace "Toh ko da
wasu 'ya yan an gaya maki haka nan kawai xan bar imaan ta tafi gidan da xata
huta, duk fitsara da rashin kunyar da kakarta ta dinga sa wa ta dinga min ya
tashi a banxa ya tafi a banxa kenan, inaaa ai sai dai idan ban haifu cikin
uwata Hadiza ba, Imaan sae dai ta ji labarin jin ddin aure amma ba dai ita ta
ji ba" Safeenah ta tabe baki tace "Ni dai babban damuwata ta daina
xuwa min gidana gaskiya, a kanta har Mujaheed ya daga hannu ya mareni kuma ki
hanani gaya ma Hajiyata" Umma tace "Haba Safeenah bai kai ki gaya ma
Hajiyar Marafa ba, kin santa da xuciya ki bar ni da shi kawai, kema kinsan haka
nan baxai mare ki ba, wllh sai yayi da ya sanin abinda ya aikata, muna nan da
ke" Safeenah ta yi tsaki bata ce mata komai ba, Umma tace "Tunda
shawarar da kika bada aka yi amfani da shi kwanaki bai yiwu ba yanxu baki da
wata shawarar da xa ki kara ba mu?" Safeenah tace "Don an kai lefe da
kudin aure ba yana nufin anyi aure bane...." Shiru tayi ta bude jaka jin
wayarta na ring, ta fiddo wayar tana kallon screen din, Kallon Umma tayi tace
"Shi yake kirana" Umma ta xaro ido tace "Haba?? To dauka ki ji
uban me xai ce maki" Safeenah ta wani daure fuska ta daga kiran ta sa
handsfree tayi shiru, sallama yyi cikin sanyayyen muryarsa, cike da masifa tace
"What did u want from me Mujaheed?" Ya d'an yi shiru sannan yace
"I want to say I am sorry, kiyi hakuri tsautsayi ne" ta fashe da kuka
tace "Tsautsayi ka daga hannu ka mareni a dakina a kan wata can, kuma a
gabanta??" Yace "Nace kiyi hakuri, and take note Imaan ba wata bace
kanwata ce, I see no reason xaki daga hannu ki mareta in kyale ki..."
Safeenah ta bude baki ta xaro ido tana kallonsu Umma, tace "Wato kirana
kayi ka sake min rashin mutunci kenan Mujaheed?" Murya can kasa yace
"Not at all Safeenah, Kinsan Imaan ba lafiya sosai gareta ba, kuma ga
grandma dinmu a gidan, da ban yi haka ba anything can happen... ni nasan
halinta ke baki sani ba, so don't ever, I mean ever.... try giving her a bad
look talkless of you laying ur hand on her face, xan iya maki fiye da abinda
kika yi...." Sai kuma ya kwantar da murya yace "Yanxu dai I didn't call
to talk long plss kiyi hakuri da abinda ya faru idan ma kince xa ki rama shkkn
sai ki rama a kai na, but If you try touching my lil sis I will not take it
likely with u" Bude baki Safeenah tayi da mugun mamaki tana kallon Umma da
ta gwalo ido tana sauraransa ita ma, a hankali Safeenah tace "You called
to warn me Mujaheed?" Yace "Not at all, na kira ne in baki hakuri,
and tell me where you are now??" Umma tayi kasa da murya sosai tace
"Kice kina gida wajena" Safeenah ta tabe baki fuska daure ta ki cewa
komai, yace "Am asking kina Ina" alama umma ta dinga mata ta gaya
masa tana can gida, ta harareta ta dauke kai tana wani cika tace "Ina
gidan ku" Mujaheed yace "Good I am happy baki tafi gida ba, later da
yamma xan shigo in sha Allah, I need rest now..." Daga haka ya katse
wayarsa. Safeenah ta ja wani tsaki tana kallon Umma a fusace tace "Ni dai
Hajiya kin
bari kawai na tafi
gidanmu Hajiyarmu ta san abinda ake ciki, aure ko wata uku ba ayi ba an fara
mari na sbda wata shegiya, dubi fa hakuri ya kira ya bani amma dubi irin
maganganun da ya dinga min da warning?? Infact wai ma me yasa baya ji da
kanninsa haka yanda yake ji da ita?" Umma ta tabe baki tace "Uwar ce
ta asirce min shi, tun yarinyar na yar karama tana yar yaye yake bauta da ita
ke kya ce don shi aka haifota, nayi nayi in rabasa da ita amma inaaa, da yake
kinsan lkcn a wajen kakar tasu yake, ita kuma yarinyar kullum sai an kai ta can
sai ya maida ta gida da yamma, idan ba karyar kakarsu ba ma cewa tayi da
sunansa ta fara magana, amma duk karya ce wllh, a haka dai ta taso ta makalkale
ma d'a na sai kice shine Abubakar ubanta, idan kuwa xai dawo hutu gida daga Uk
uban tsaraban da yake yo mata hankali baya dauka, kanninsa ko quarter dinsa
basa samu wllh, wai ma don abun ya ragu sosai yanxu, ae ba karamin tashi tsaye
nayi ba gaskiya, ban yi da wasa ba kam, kwanaki da dadewa fa mijin da Seeyama
ke aure yanxu ya so hada imaan din da, kinsan abokinsa ne kuma yaron ga kudi ga
hankali amma sbda shi shashasha ne wai da Imaan xai hada sa, ni ko na ruguje
xancen gaba daya, shine yaron ya dawo ma Seeyama, yanxu wnn auren ma da ake son
a mata shine gaba a kan komai ina jin, kuma bbu mamaki ya ma san yaron
Bulasawan..." Safeenah da ke ta kallon Umma tace "Toh ni dai gaskiya
tayi aurenta ta tafi gidan mijinta ta kyale min miji haka" Umma ta bude
baki tace "Tayi aure kuma? To ai tunanin xata auri yaron Bulasawa ne yasa
take raina mutane take ganin ita wata ce, wllh shi yasa take maki kallon
hadarin kaji, kallon kowa take kasa da ita sbda tana tunanin yaron Bulasawa ne
xai aureta, amma bata san she is mistaking ba, wllh wllh ba mijinta bane yaron
in dai ina numfashi, ke kinsan ko gaisheni yarinyar nan da kike gani bata yi
kuwa?? Uwarta kuwa jin ta take ita wata ce yanxu a dole ga ta surkar Bulasawa,
to xa su kwashi kunyar su kuwa a hannu wllh ba cika baki ba" Safeenah ta
tabe baki tace "To ae don an kai sadaki da lefe an sa rana ba shine yake
nufin an daura auren ba, in dai ni take ma wani gani gani wllh ta tari aradu ba
gamo... Sai na kunyatata in ga ta tsiya in ga karshen auren nata da shi Sadeeq
Bulasawa din" Umma tace "Atohh, ni dai dama nace idan aka yi auren
nan to fa ban haifu cikin uwata ba, daga ita har uwarta da kakarta sai sun
kwashi kunyarsu a hannu ina kallo" Hajiya Saude tace "Kuna ta surutu
ni ko har na gama yanke shawarar what next... Kuma in Allah ya yrda naji
kamshin nasara...." Umma ta kalleta da sauri tace "Toh ba mu mu
sha" Hajiya Saude tace "Amma duk da haka sai mun koma wajen mutumin
nan ko xuwa gobe"
Bayan Magrib Mujaheed yayi parking kofar gidansu ya fito ya
kulle motar gaisawa suka yi da mai gadi dake bakin gate, Mai gadin na kallonsa
yace "Likita ba lafiya ne" Mujaheed na kallonsa yyi murmushi yace
"Alhmdllh, na ji sauki" daga haka ya shiga compound din, direct part din Inna ya nufa walking slowly,
a hankali ya murda kofar parlon ya shiga, ido hudu suka yi da Imaan dake xaune
parlon tare da Inna da ke ta fiddo kayan cikin akwatunan lefen da aka kawo
bakinta har kunne, Ta Rasulu ma sai aikin fiddo ubansun kayan take tana cewa
"Toh ga dai kaya ba laifi an xuba karyar naira, ko da yake suna da shi ne,
Ni fa nasan har uwar Bulasawan nan a da wllh, don akwai wata makociyata kawar
kanwarta da suke uwa daya tana ma uwar Bulasawan aikatau, lkcn ma kudin bai
bunkasa haka ba, toh sai makociyar tawa ta ja ni wataran muka je gidan kawar
kanwarta wai xata kai mu gidan kakar shi mijin Imaan wato uwar Bulasawa, sunan
uwar tasa Hajiya Salamatu, tana nan wata doguwa fara, duka duka bata fa wuce mu
ba amma kirkinta ragagge ne...." Inna dai sai kallonta take kasa kasa, ta
Rasulu ta tabe baki tace "yo ragagge mana, a lkcn Ina goyon Shamsu daga ya
mata fitsari a cafet, ga abinci mai lafiya da xuka xukan kaji an xubo mana xa
mu ci in gaya maku abincin da ban ci ba knn don matar nan cewa tayi in tafi
gida in canxa masa kaya xarni ya isheta, nan ko bata san har da kashi yyi ba
ina ta boyewa ne har sai mun ci abincin, ni dai har da d'an kwalla na na bar
gidan ina dukan shamsu, kafin in dawo kuwa su shafa'u suka side kwanon tass da
ke kinsan dangin mayu ne, ni dai abincin ko a halshe na" Maimoon dai sai
taya su fiddo kayan take bata ko kalli ta Rasulu ba, Duk suka kalli Mujaheed da
ya shigo parlon ya tsaya yana bin akwatunan da kallo, Inna ta washe baki tana
kallonsa tace "Mujaheed takwarata tayi goshi wllh, ko atamfar dubu ashirin
Ina jin babu a nan, gwalagwalai kuwa mun kirga biyar da ta Rasulu, to me xance
ma Allah banda in gode masa?" Imaan dai sai danna wayarta take, Mujaheed
yace "Toh Allah ya sanya alkhairi" Inna tace "Ameen, kuma kayi
hakuri da abinda iyayenka suka maka, ka dai fi su nesa ba kusa ba, in sha
Allahu idan Allah yasa aka daura auren nan lafiya kai xaka kai Imaan har
dakinta kayi mata fada sosai sannan mu taho gida mu bar ta" Dariya Maimoon
ta dinga yi tana kallon Imaan da taki dago kanta, Inna ta tsuke fuska tace
"Ke ba batun dariya bane, magana ta gaskiya shi xai kai ta gidanta... Ke
kinsan wahalar da yyi da ita ne kuwa" Ta Rasulu tace "Wahala kuma ai
ya tashi a banxa tunda ba shi xai aureta ba, kyansa ace wannan uban shakuwar da
suka yi kawai ya aureta suje can su xauna tare, abinda ma ya fi kowa saninta a
duniyar, ba shikenan sai su haifo santala santalan 'ya yansu su xube ma Aisha
tayi ta bari barin da bata yi ba da, ku dai xumuncin ku duk kame kame ne ba shi
da wani karfi Allah na tuba, Banda haka ba sai ayi tuwona maina ba ko don
Rukayya ta hadiye xuciya ta mace, ita kenan fa gare Bukar a duniyar...."
Tagumi Inna tayi kamar xata yi kuka tace "Ni dai naga abinda ya isheni ni
Asabe... Wa ya gayyato min wannan mata??? Huuu gaskiya ta Rasulu kin lalace, ke
kinsan uban sa6on da kika buga yanxu ki ja mana girgixan kasa kuwa? Kai wasu
dai kyansu dawanau wllh" Ta Rasulu tace "Sa6o don nace da Mujaheed ya
auri yar uwarsa Imaan? Ke dai baki son
gaskiya, kuma baki tsoron Allah, Asabe kinyi watsi da tsoron Allahn ki tun tale
tale, kai tun kina gidan Alhaji isuhu, kawai jin ki nake idan kince wasu basu
tsoron Allah" Inna da ta wani tsuke fuska tace "To bari kiji, wllh da
Mujaheed ya aure min jika gwara tayi ta xama ba aure ina kallonta, me xata ci
da sauran Safara'u Allah na tuba?? Me xata yi da surka irin Rukayya ta6a66iya,
ke ma dai wllh muguwa ce ta Rasulu, waye kuma Mujaheed da xa ki ce ya aurar min
Imaan in shiga uku in lalace, Ina Imaan xata kai sa, ke dai wllh fitinanniya ce
tirrrr" Mikewa Imaan tayi ta wani hade rai ta nufi kofa, Inna ta hade rai
tace "Atoh maxa yi tafiyar ki Imaan kada a sa min ke a bakin duniya, Toh
ni dai tunda kin gama ganin kaya tashi kiyi tafiyar ki ta Rasulu ba ruwana kar
ki kawo mana rudani a lamarin mu, tunda ke rudaddiya ce, tashi ki tafi haka a
gaida su Muhammadu" Ta Rasulu tace "Toh banda Mujaheed din dama wa
xai iya da ciwace ciwacen Imaan Allah na tuba, ni fa tunda Uwar Bulasawa ta
kore ni da d'ana ta hanamu abinci na tsaneta har yau" Inna tace "Toh ae ba ni da Ahmadu ta kora ba
ta Rasulu, kuma ko da ni ta kora ma xuciyata me kyau ce fesss na yafe mata
duniya da lahira, ke dai kawai kiyi ta kanki ta Rasulu, bikin ma ni bance
lallai sae kin xo ba kar ki kunya ta ni don Allah ki rufa min asiri kiyi xaman
ki a gida kin ji???" juyawa Mujaheed yyi ya fita parlon, Inna ta bi sa da
harara tace "Waye kuma Mujaheed da xan hada jikata da?? Kai Allah dai ya
isa da wannan tunanin naki gaskiya" Washegarin ranan Imaan suka fara
jarabawan waec, karfe biyu saura suka tafi yin first paper dinsu, xuwa hudu da
wani abu suka gama suka fito, tunda suka fito Maimoon ke kallon Imaan da ta
nemi dakali ta xauna, Maimoon ta karasa kusa da ita tace "What happened
Imaan?" Imaan ta kalleta a hankali tace "Kamar bana jin dadi"
Maimoon tace "Toh sannu yanxu driver xai xo sai mu wuce gida" Mariya
ta nufo su tace "Amaryar mu how was today's paper?" Imaan tace
"Alhmdllh" Mariya tace "ki taso ku gaisa da Ya sadeeq yana waje,
yace in kira ki" Imaan ta d'an turo baki tace "A'a ni dai kice masa
baki gan ni ba plss" Mariya tace "C'mon ki taso mu je plss how will I
say ban gan ki ba" Maimoon ta dago Imaan tace "Mu je kila ma Driver
ya xo" Maimoon na rike da hannunta suka fita wajen gate din makarantar, a
hankali Imaan ke tafiya har suka isa gun motar Sadeeq ta tsaya, ya dinga kallonta
daga glasses din idonsa yace "What's wrong?" Mariya tace "Nima
na tambayeta daxu tace ba komai" bude motar yyi ya fito yana kallonta daga
sama har kasa yace "Me ke damun ki?" Kamar xata yi kuka tace
"Ina yini?" Yace "I said what's wrong?" Ta sunkuyar da kai
tace "I am not feeling fine" Back seat ya bude mata yace "Shiga
in ajiye ki gida" ta buda ido sosai tace "Driver dinmu na xuwa"
kallonta kawai ya tsaya yi, hakan yasa ta kalli Mariya, Mariya tace "Ki
tafi xa mu taho yanxu" Sadeeq yace "Kema shiga mu je may be baxata yi
tunanin guduwa xan yi da ita ba" dariya Mariya tayi tace "Toh kuma
driver yana hanya, ku tafi kawai xa mu jira shi da su Ummi" ta fadi haka
tana nuna masa Ummi dake can tsaye sai kallonsu take suna kallon direction dinta
kuma ta dauke kai da sauri, a hankali Imaan ta shiga bayan motar, Mariya kuma
ta shiga front seat, ya rufe motar ya xaga ya shiga maxaunin Driver ya tada
motar suka bar kofar makarantar, tun da suka dau hanya yake kallonta ta madubi,
ita ko ta jinginar da kanta ta rufe ido, har suka isa gida, parking yyi bakin
gate yana kallonta ta madubi still, can ya bude motar ya fito ya dawo baya ya
xauna, sai a sannan yasan bacci take da gaske, ya kai hannu forehead dinta ta
bude ido da sauri ta koma baya, yyi kasa da murya yace "Ina ke maki
ciwo?" Ta sunkuyar da kai tace "Ina jin xaxxabi" yace "Tun
yaushe??" Tace "Da safe" shiru yyi bai ce komai ba, can ya sauka
motar yana kallonta yace "Come down" a hankali ta fara sakkowa motar
ya kama hannunta don taimaka mata, xata kwace hannun ya ki saketa, Bata yarda
ta kallesa ba ta fito motar, yana kallonta yace "Anjima xan xo maki da
drugs" tace "Toh nagode" saketa yyi ta juya xata shiga gate suka
yi ido hudu da Mujaheed dake kallonsu yana xaune gun mai kiosk dake layin, ta
dauke kai da sauri ta shiga gate din, duk da hada idon da Sadeeq yayi da
Mujaheed shigewa motarsa yyi ya tada ya bar layin.
Thanks for d call and text fans...
Allah maimaita mana.... Ameen.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
71......
Da daddare Imaan na parlon Inna a kwance ta dalilin kiranta
da Sadeeq yyi xai kawo mata magunguna ita kuma bata son fita kofar gida shi sa
ma ta taho part din Inna ya sameta a nan, ko tsinke Inna bata bari a parlonta
ba cikin kayan da aka kawo na Imaan gaba daya ta kai su daki, dakin ma makulli
take sa masa sai in xata shiga ta bude idan ta fito kuma ta kulle ta daure
makullin a ha6ar xaninta, Inna dake xaune ta gama cin abinci kenan ta daura
kafa daya kan daya ta ta6e baki tace "Ni dai da ki tashi ki lallaba ki
koma can bangaren ku ki jirasa, bana son wannan juye juyen da kike min kamar
macijiya gaskiya, ni bana son abinda xai gigitani da daddaren nan, Bukar kuma ba
kirki ne da shi ba tsaf xai iya cewa a parlona ciwon ya tashi in shiga
uku" Ita dai Imaan bata kulata ba, dai dai nan aka yi sallama kofar
parlon, Mikewa Inna tayi tana amsawa tace "A'a Bisimillah Bukar, sannu da
xuwa" Sadeeq ya shigo parlon, inna ta kinkimo lallausan carpet dinta da ta
nade saboda masu shigowa kallon lefe kar su 6ata mata ta shimfida masa, yana
murmushi ya xauna ya gaisheta, ta amsa tace "Tun daxu take xaxxabi nace ta
tafi gidansu iyayenta su sani ta ki, to dama wannan mutumin Mujaheed da yana nan
ne yasan kan xaxxabin, to ban gansa ba kuma nasa Maimuna ta kira min shi nace
ga kanwarsa ba lafiya amma shiru bai xo ba, ita kuma lkcn da ba shi da lafiya
har cewa tayi a fasa kawo lefenta da kudin aure sai ya ji sauki, su Ahmadu dai
ne basu yarda ba, kowa da imaninsa kawai a rabu da shi, shi ya sani...."
Sadeeq dake fiddo drugs da ya kawo bai dai ce komai ba, can ya kalli Imaan da
ta juya masu baya, Inna tace "Atoh, tsorona daya kada uban yace a nan
xaxxabin ya tasar mata kuma ni daxun nan ta shigo min wllh" a hankali yace
"How are you feeling?" Shiru Imaan tayi bata ce komai ba, Inna tace
"Idonta biyu wllh" Imaan ta hade rai ta juyo sannan ta mike xaune,
ledan maganin ya nuna mata yace "Ur drugs with prescription, sai ki sha
yanxu" Inna ta tafi kitchen ta dauko ruwan gora da cup tace "Toh
tashi ki sha" Sadeeq yace "Ni xan koma Kaka" Inna tace "A'a
abinci fa? uwarta ce tayi, da ke ni dama idan ba girkinta ba bana cin na kowa
sai in Amina, tuwo ne da miyar agushi yaji kayan hadi, sai kamshi yake xubawa in
xubo maka?" Yana d'an murmushi yace "Naci abinci kafin in taho
kaka" tace "Toh ko in juye maka ka tafi da shi?" yace "Ai
kuma ni da abinci sai gobe idan Allah ya kai mu" Inna tace "Atoh,
haka naga Mujaheed ma yake yi, shi in dai karfe tara yyi bai ci abinci da
daddare ba to ya gwammace ya kwana haka bai ci komai ba, kaji fa abinci ma sai
an masa ka'ida, Ni ko nace aikin banxa, yo ko tsakar dare cikina ya bukaci
hakkinsa bana tashi in san yanda nayi na sallamesa ba? Wlh akwai hisabi mai
tsanani tsakanin mutum da yan hanjinsa, in dai ka cuce su to ranan gobe kiyama
abun baxai maka kyau ba, shi sa ba ruwana ko biyun dare ne naji yyi kugi xan
tashi in san abun yi, abinda ga kayan shayi kaca kaca a gidan" Sadeeq ya
mike yana murmushi yace "Sai da safe kaka, xa a kiyaye" tace
"Toh Allah ya bada ikon kiyayewa" Yana kallon Imaan yace "Sleep
tight, Allah ya kara sauki" a hankali tace "Ameen, amma ba wanda xai
sani bacci coz I am having 10 o clock paper tomorrow" yace "Not at
all, xa ma ki iya tashi cikin dare kiyi karatun ki" daga haka ya nufi kofa
Inna tace "Toh baxa ki tashi ki daddage kiyi masa rakiya ba Imaan?"
yace "A'a ta sha magani ta kwanta kaka, sae da safe" Inna tace
"Atoh, Allah ya tashe mu lafiya, ka gaida iyayen naka, Allah yayi
albarka" yace "Ameen kaka nagode" daga haka ya fita parlon ya
rufe kofar. imaan sun fara jarabawa da sati guda aka fara shirye shiryen biki a
gidan kasancewar biki biyu ne da nata sai Ya Yusuf... yau Friday Imaan na
dawowa exams karfe sha daya ta tafi part din Inna, bakin tap ta sameta tana
wanke gaba daya buckets dinta da iron sponge da detergent, Imaan ta shiga
parlor ta xauna, Sai kusan sha biyu Inna ta shigo tana cewa "Haka kawai,
naga bokitai suna son komawa kamar takashin kare, Allah ubangiji ya min tsari,
na wanke su tass na shanya kayana ni dai, kuma duk Maimuna ce me min amfani da
abokitai gashi sun dauko hanyar dafewa, gaskiya xan kira ubanta ya mana iyaka,
idan nata xai siya mata to sai ya siya mata ta rabu da nawa..." Tana
kakkabe kujerunta tace "Toh ya jarabawan yau?" Imaan tace
"Alhmdllh" Inna tace "Toh Allah ya baku sa'a, sai kiyi kokarin
ganin kin cinye jarabawan kin fi kowa, to kin ci abinci kuwa?" Imaan tace
"Ni bana jin yunwa" Inna ta tabe baki jin yanda take amsa mata ta
gama kakkabe kakkabenta ta dauko tsintsiya, Imaan na kallonta tace "Inna
Yaya yana xuwa?" Inna na gyara tsintsiyar hannunta tace "Yaya? Waye
kuma Yaya?" Imaan bata ce komai ba, Inna ta tabe baki ta fara sharanta
tace "Wai Yaya, to ajiyar Yaya kika bani Imaan? Ina xan ga wani Yaya
mutumi na gidansa, ni har na mance rabon da ya tako min nan ma, toh mutumi ya
fara sanin dadin aure me xai xo ya min kuma? A'a ni kam kusan sati kenan ban
gansa ba" Imaan dai sai kallonta take, Inna ta kalleta tace "Sako
xaki bada a ajiye masa?" Imaan ta turo baki tace "A'a kawai na daina
ganinsa ne" Inna ta tabe baki tace "Toh ba sai ki shirya ki tafi
gidansa ba ko akwai wanda xai hanaki? Ni dai har abada in taka cikin gidansa
tunda iyayensa ba so suke ba, to me Mujaheed xai bani wanda Allah bai ban ba?
A'a ba ruwana ta kai na nake yanxu, ni ko naje gidan nasa fa ko yar kudin motar
nan baya bani, kullum a gantale nake dawowa idan naje wllh, to sai kace uwata
tace min je ki kya gani" Imaan tace "Toh ki kirasa" Inna ta
kalleta da sauri tace "In kirasa? Ke uban me ya hanaki kiransa, gafara xai
min Mujaheed din koko?" Imaan ta hade rai bata ce komai ba, Inna ta ci
gaba da sharanta tace "Ni dai kar ki dameni don Allah, waye kuma Mujaheed
Allah na tuba" can kuma ta mike ta dauko wayar ta mika mata tace "Toh
kirasa dai mu ji" Karban wayar Imaan tayi, tayi dialing number sa ta sa
handsfree ta ba Inna, har ya gama ring bai dauka ba Inna ta ajiye wayarta ta ci
gaba da abinda take. Ranan lahadi warce Anty ta kira domin yi ma Imaan gyaran
jiki ta iso gidan duk da bikin saura sati uku, sati ukun kuma xata yi tana
gyara Imaan, kudi ba na wasa ba Aunty xata biyata, matar ta so ace Imaan ko
fita baxata dinga yi ba during the period amma hakan baxai yiwu ba sbda exams
da take, Tunda Umma taga sananniyar mai gyaran jikin da aka dauko hankalinta yayi
mugun tashi, duk gaba daya she is soo confused, sun koma gun mutumi kamar yanda
Hajiya Saude tace amma ita fa taga abu sai gaba yake ga biki saura sati uku har
xa a fara gyara amarya, tsabar yanda ta sa abun a rai har wani rama tayi
abincin kirki bata iya ci, hatta bacci gagaranta yake yi ynxu, ga uban kayan
abinci da drinks da aka fara jibgewa a gida na bikin... Anty ce xaune parlor
tare da mata mai gyaran jiki tana sake jadadda mata irin gyaran da take so tayi
ma Imaan, Matar tace "Baki da matsala Hajiya, ni tsakani da Allah nake
aiki na" Anty tace "Toh sai abu na biyu, a wajen kakanta xa a ke
gyaran, amma fa kinsan yanda tsoffi suke sai ana yi ana hakuri da kauda kai don
Allah..." Dariya matar tayi tace "Ae muna da su Hajiya wannan ba
damuwa bane in sha Allahu" Umma
dake kitchen ta shirya xata fita amma ta kasa fita duk tana saurarensu, Anty
tace "Toh mu je in raka ki bangaren kakar tata..." Mikewa matar tayi
rike da Babban jaka, Anty ta dau mata dayan suka fita xuwa part din Inna, sai a
sannan Umma ta fito tana danna wayarta, ta kai kunne, Mujaheed dake bedroom
dinsa ya fito wanka yana shiryawa ya kalli wayar Safeenah dake gaban mirror
yana ring, karasawa yyi ya dau wayar yana kallon screen din, har kiran ya katse
kallon wayar yake ganin number Ummarsa, can ya ajiye wayar sai gashi ta sake
kira, dauka yyi ya nufi kofa suka kusa cin karo da Safeenah xata shigo dakin,
karbe wayar tayi a hannunsa tace "Ka gaji da kwanciyar kayi wanka
kenan..." Bai tanka ta ba ya juya yana ci gaba da buttoning din shirt din
jikinsa, ita kuma ta fita dakin ta koma nata don daxu da ta shigo ganin ko ya
tashi ne ta bar wayar a dakinsa, ta daga kiran ta kai kunne tace "An tashi
qlau Hajiya?" Umma tace "Lafiya lau, ya jikin Mujaheed?"
Safeenah ta tabe baki tace "Ya warke fa kawai yana pretending ne sbda bai
son ina xuwa inda yake tunda ina takurasa sai ya ci abinci ko makamancin haka,
wllh har yanxu na rasa gane kan Mujaheed, gaba daya ya ki gaya min damuwarsa
duk da dai da sauki yanxu, in dai ya fita aiki ne baya dawowa sai nayi
bacci..." Umma tace "Ke ki rabu da shi haka nan yake ba a taba gano
inda ya dosa, wani lkcn kuma tsabar miskilanci ne, ni da na haifi kayana kuma,
kema ki fita harkansa kawai idan kika ga yana shan kamshi sai ki ga kun dawo
dai dai..." Safeenah ta tabe baki tace "Ni ko ina xan sha masa kamshi
ya hango wata a waje, gwara inyi ta lallabasa a haka...." Umma tace
"Toh ni ba wannan ba, Safeenah
shirye shirye dai sai gaba yake a gidanmu don yau ma aka dauko mai
gyaran jiki xata fara mata gyara..." Safeenah tace "Saura sati uku fa
Hajiya, ba sai a xuba ido ba a ga ikon Allah, idan fa mutum ya fiye axar6a6i da
kyar ya dinga ganin abubuwa yanda yake so, ke dai kawai ki xuba masu ido ki
daina damun kan ki, auren nan ance ko an daura bai fi na minti goma ba in ma an
daura kenan to me xai dameki, ni ban cika yarda da irin mutanen nan ba amma
gaskiya mutumin nan da alama yana da gaskiya sosai, duka duka nawa ya amsa
wajen mu..." Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Ban son in sakankance
ne da maganar mutumi a xo ayi abun nan Ina ji Ina gani, wllh da na shiga uku,
shi sa gwara in buga nan in buga can, yanxu ma xan je gidan Hajiya
Balaraba" Safeenah ta tabe baki tace "Toh ni dai sai mun yi waya xan
hada ma mijina breakfast ya tashi" Bata jira cewar Umma ba ta katse wayar
ta ajiye ta ja tsaki tace "Ance maki ba don abinda Mujaheed yyi min sbda
yarinyar da irin rainin da take min xan bata lkcina a kan abinda ya dame ki ne,
nima ta kaina nake shi sa na xage" shiru tayi tana imagining ace da gaske
d'an Bulasawa ya auri Imaan, Tabb har takasu ma xata iya dinga yi ita surkar
Bulasawa, kawai wataran sai a wani xo da motoci kusan biyar gidanta a sunan
Imaan ce ta xo gaida Yayanta, ta sakko daga motar da gwalagwalai iri iri tana
yatsine yatsine tana mata kallon banxa, tabbb, da sauri Safeenah ta kauda
tunanin a ranta tana cewa Allah ya kiyaye hakan ma baxae faru ba, in sha Allahu
talaka bawan Allah xa ki aura ki xo gidana in taka ki yanda nake so in
walakantaki, murmushi Safeenah tayi wai ta hango imaan ta xo ce ma Mujaheed
basu da abinci a gida shi kuma yace ta debo mata a nasu ta bata, Safeenah ta
tabe baki tace "Ae Kyawunta ma baxai bari wannan mafarkin nawa ya xamo
gaskiya ba, Allah dai yasa idan an rabata da yaron Bulasawan ba wani mai kudin
xai kuma xuwa mata ba don wannan shine anyi ba ayi ba...." Safeenah ta
d'an yi murmushi a ranta tace muna wargaza auren nan xa mu yi mata maganin
bakin jini in sha Allahu, ita da aure sai dai taga wasu na yi, shiru tayi tana
tunanin to kada kuma fa ta rasa miji wataran iyayen suce a hadata da yayanta
tunda da aure tsakaninsu.... sosai gaban Safeenah ya fadi ta xauna gefen gado
da sauri xuciyarta na bugawa, lkci daya ta girgixa kai tace "A'a gwara dai
a rabata da d'an Bulasawan kawai, duk tsiyarta kuma baxata sake samun kamarsa
ba sai dai kasa da shi" murmushi Safeenah tayi ta mike ta fita dakin dai
dai fitowar Mujaheed daga bedroom dinsa, rungume sa tayi tana shigewa jikinsa
tace "What should make for breakfast sweetheart?" Tabe baki yyi ya
kauda kai. Sosai Imaan tayi wani fresh
tayi kyau ta dalilin gyaran da aka fara mata, har wani sheki da glowing skin
dinta yake, duk ta gifta ka dama kamshin da xaka ji na musamman ne, a haka kuma
take fita tayi jarabawa kullum, tun biki na saura sati biyu dama wayarsu ya
ragu sosai da Sadeeq, yawanci kuma ita ke kiransa ma, shi ko sai dai ya bi miss
call dinta. Yau Wednesday Imaan na dawowa daga exam bayan tayi wanka ta sauya
kaya Inna ta xubo mata abinci da yaji nama ta ajiye mata a kusa da ita tace
"Ni dai wai yaushe xa ku gama wannan kaddararren jarabawan ne ki nutsu
waje daya a maki gyaran nan cikin kwanciyar hankali, wannan ae fitina ne ana
gyara yana bin iska tunda kullum sai kin fita..." Imaan na kallon abincin da Inna ta ajiye mata
tace "Ni fa bana jin yunwa" Inna ta kalleta da sauri tace "Ni
dai na shiga uku da wannan 'ya ta Bukar, ko kumallon kirki fa baki yi ba daxu,
a haka xa a kai ki gidan Sadeeq din nan da sati biyu a rame duk k'ashi a wuya??
Ni dai ba ruwana bari Amina ta shigo tunda Aisha ta sallama mata ke gaba
daya" Imaan ta tura abincin xata kwanta kan kujera a fusace Inna tace
"Ni fa bana son a dameni gaskiya sai ince ki tattara kayanki ke da mata
mai gyara ku koma bangaren ku yanxu nan, ya xan dinga maki magana kina
walakanta ni, dama katuwar mata mai gyaran jiki ce tace ki ci abinci kafin ta dawo
taje siyo wasu kayayyaki a kasuwa ta dawo, to idan ta dawo ba ki ci ba
fa..." Imaan tace "Inna to ko dai yaya ba shi da lafiya ne har
ynxu?" Bude baki Inna tayi tana kallonta da mamaki, can ta xauna tayi
tagumi a hankali tace "Naga abinda ya isheni ni Asabe, waye kuma
Yaya??" Imaan ta turo baki ta dauke kai, Inna tace "Wai akwai abinda
ya hada ki da Mujaheed ne bayan kasancewar Ubansa wan ubanki? Akwai wani
dangantaka tsakaninku ne dama da ban sani ba? Wato kwana biyu shiru bai shigo
ya takura ki ba shine duk kika damu tunda ke gantalalliya ce, toh sai ki tashi
ki tafi gidansa, Toh wai ma ina ruwanki da wani yaya ke da xa ki yi aure nan da
kwana sha biyar? Ko dai akwai ajiyar ki a gunsa ne bai baki ba kafin a kai ki
daki in kirasa ya baki?" Imaan ta wani hade rai tace "Toh kawai daga
tambaya? Naga ya dade bai xo ba kuma ba haka yake ba" Inna tace "Toh
idan lalacewa yyi ya fara hakan fa?? Ko idan ya xo me xai bani banda ya tsokane
ki ya cuce ki ya wuce don ma naga tunda yayi aure yyi hankali ya daina sa ki
kuka, Ke dai ki dinga jin tsoron Allah kiyi ta kanki ba ruwana, to ni ko
shekaranjiya na sa Ummi ta kira min shi katon ya ki dauka, wa ya sani ko fushi
yake na daina xuwa gidansa, sai kace gidan aljanna Allah na tuba, ni dai ba
ruwana wllh" daga haka Inna ta shige daki, imaan ta bi ta da harara ta
jinginar da kanta da kujera bata ce komai ba.... Ana saura kwana 7 biki Imaan
ta gama jarabawa kasancewarta science student, Maimoon da Mariya kuma nan da
kwana shidda xa su gama jarabawan don art class suke, yau kusan kwana hudu basu
yi waya da Sadeeq ba, bai kirata ba ita ma bata kirasa ba, tana bedroom din
inna bayan la'asar hannunta rike da hisnul Muslim wayarta ya fara ring, daukar
wayar tayi tana kallon mai kiranta, ganin number Sadeeq ta daga ta kai kunne tayi
shiru, shirun shi ma yyi na kusan second goma sannan yace "How are
you?" Murya can ciki tace "Am good" yace "Ina waje" ta
kalli agogo bata dai ce komai ba, yace "Or are you busy?" Tace
"Ni ba bari na ake ina fita ba..." Ya d'an yi shiru sannan yace
"What did you mean?" Tace "Bana fita" yace "Ohk gida
ake biyo ki da papers din ki kenan?" Turo baki tayi tace "Waye ubana
da xa a biyo ni gida da papers?" Yace "What exactly are you trying to
say?" Kin cewa komai tayi, Yace "Ohk then kar ki fito..." Xai
katse wayar frnd dinsa Saleem dake tsaye gefensa jikin motarsa ya amshi wayar
ya kai kunne yace "Haba amarcy ba dadewa fa xa kiyi ba, ki d'an fito pls,
just few minutes" a hankali Imaan tace "Toh" Saleem ya katse
wayar yana kallon Sadeeq yace "Amare fa lallaba su ake basa laifi Dr"
Sadeeq dai bai ce komai ba yana rungume da hannunsa, Saleem yyi murmushi yace
"To saki ran kafin ta fito mana" Nan ma dai Sadeeq bai tanka sa ba,
Hijab Imaan ta saka sai dai ba har kasa ba, ta fito parlor ta sanar ma Inna
sadeeq na kiranta a waje, Inna dake xaune parlon tare da mai mata gyaran jiki
suna hira sai kallon takwarar tata take, can a hankali cikin sanyin murya tace
"Ashe dama haka kike da kyau ban sani ba Imaan?" Dariya sosai mai
gyaran jiki ta shiga yi tana kallon Inna dake sa ta nishadi tun xuwanta, kwata
kwata bata gajiya da fadan Inna da labaranta masu kai da marasu kai, ga uwa uba
tsaftarta, komai na Inna burgeta yake, Imaan bata san lkcn da tayi murmushi ba
bata dai tanka Inna ba ta nufi kofa ta fita, Inna na kallon mai gyaran jikin
tace "Allah kuwa yar nan, dubi fa yanda take walkiya da kyalli, ga kamshi
kaca kaca ta ko ina a jikinta, duk inda ta gilma sai ya kamu da kamshin da take
yi, ni dai xan kara maki dari biyu da tsinkin sabulu a kudin da xa su biyaki,
gaskiya kin fito min da jikata, kai har dambun nama xan maki ni dai" Matar
dai sai dariya take tana ma Inna godiya, Imaan na isa part dinsu ta shiga don
daukan hijab mai tsayi, Ammi ta fito daga kitchen jin an bude kofa, Imaan ta
gaisheta sannan ta nufi dakinta, Ammi ta bi tada ido, ba a dau lkci ba ta fito
sanye da hijab har kasa, tana kallon Ammi a hankali tace "Ana kirana a
waje ne..." Shiru Ammi tayi tana kallonta, hakan yasa Imaan ta sunkuyar da
kanta, Ammi ta karaso kusa da ita ta sa ta xauna saman kujera ta xauna kusa da
ita tace "What's wrong with you Imaan?" Imaan ta kalleta da sauri
tace "Ba komai fa Ammi" Ammi tace "Noo there is something kar ki
ji komai ki gaya min..." Imaan ta girgixa mata kai a hankali tace "Da
gaske ba komai Ammi...." Ammi tace "Toh shikenan, but don't forget
baki da wanda ya wuce ni a duniya, idan baki gaya min damuwar ki ba ban san
wanda xa ki gaya ma ba" Imaan ta sunkuyar da kai tana murmushi tace
"Idan akwai xan gaya maki ai Ammi" Ammi tace "Toh ki kwantar da
hankalin ki and keep praying, kar ki gaji da addu'a, kuma ki dinga cin abinci
sosai kin ji" murya can kasa Imaan tace "Toh nagode Ammi" Ammi
tace "Ko me kike bukata ki kirani a waya ki sanar min" Imaan tace
"Toh bari in je ana jirana" Ammi tace "Toh ki kame kanki"
mikewa Imaan tayi ta nufi kofa Ammi ta bi ta da kallo har ta fita ta kulle
kofa. Tunda Imaan ta iso part din su Maimoon Umma dake xaune tare da Hajiya
Balaraba kan fararen kujeru take kallonta ko kiftawa babu, ta sunkuyar da kai
ta gaishesu a hankali Hajiya Balaraba ce kadai ta amsa a dakile, tuni kamshin
da take ya daki hancinsu gaba daya, har ta fita gate basu daina kallonta ba, Da
ba don Saleem da ya ki barin sa ba da tuni Sadeeq ya bar wajen ganin har bayan
minti goma bata fito ba, tana fitowa sau daya ya kalleta ya ci gaba da danna
wayarsa, Saleem ya mata murmushi har ta iso inda suke ta tsaya a gefe a hankali
tayi masu sallama sannan ta gaishesu kanta a kasa, Saleem ya amsa yace
"Hope an gama exams lfya?" Tace "Alhmdllh" Sadeeq ya maida
wayarsa aljihu yana kallonta ta cikin glasses din idonsa a takaice yace
"Wani shirin xa ku yi a nan gida?" Shiru tayi da farko, sai kuma ta
kallesa taga wani direction yake kallo daban, tace "Nima ban sani ba"
yace "Ohk then, on Thursday xa ayi dinner...." Yana magana ya bude
mota ya fiddo hadadden IV mai yawa sosai ya mika mata ta risina ta amsa, shi
dai bai yarda sun hada ido ba, yace "I think that's all, dama sbda IV din
na xo, if there is anything I will call and let u know" daga haka ya bude
driver seat ya shiga, ita dai sai kallonsa take, Saleem na mata murmushi yace
"Toh mun gode amarya, ki shiga ciki xa mu koma" tayi murmushin karfin
hali ta juya ta nufi gate, Saleem ya xaga ya shiga front seat, Sadeeq ya tada
motar suka bar layin, suna hawa kan titi Saleem yace "Plss ka rage wnn
xuciyar Sadeeq... I don't like the way u treated her gaskiya" Sadeeq dai
sai driving dinsa yake bai ce masa komai ba, Saleem ya tabe baki ya fiddo
wayarsa yana dannawa, Sadeeq yace "Raina min hankali take" Saleem
yace "Meye abun rainin hankali" a d'an fusace Sadeeq yace "Baka
ji abinda tace ba kenan, wai bata san abinda xa su yi ba a gida na biki, wato
babu events da xa su yi kenan take nufi, which is a lie" Saleem ya tabe
baki yace "Duk wannan xumudin da ka dinga yi kwanki kafin a saka bikin duk
naga babu shi yanxu Sadeeq" Sadeeq ya rage gudun da yake yana shafa kansa
a hankali bai dai ce komai ba....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
72......
Ranan lahadi da karfe sha daya Mama Hadiza ta iso gidan tare
da autar ta Maryam, a part din su imaan suka sauka as usual, sai bayan azahar
sannan suka taho part din Inna, Inna dake xaune ta gama hada ma Imaan kwadon
rama da ya ji kayan hadi a bowl kenan tayi masu kallo daya ta dauke kai ta rufe
bowl din raman ta ajiye a gefe, Maryam ta tabe baki ta xauna tana kallon TV,
Mama Hadiza ta xauna kusa da Inna tana murmushi tace "Sannu Innata"
ba tare da Inna ta kalleta ba tace "Yauwa, a rufe min kofata kada k'uda su
biyo bayan ku su shigo min parlor" Mama Hadiza ta mike ta rufe kofar ta
dawo ta xauna tana murmushi tace "Ina yini Inna? Fatan mun same ku
lafiya" Inna tace "Lafiya lau, ai naji labarin tun sassafe ku ka
shigo nan dai ne ba ku xo ba sai yanxu" Mama Hadiza tayi dariya tace
"Mun d'an kintsa ne Inna, ya shirye shirye?" Inna tace "Atoh
suna can suna yi, ko shawara ma basa yi da ni wllh ban ya ake ciki da maganan
bikin ba, nasan dai ta Rasulu xata gayyato kawayenmu gaba daya sai a kafa mana
katon rumfan nan da kujeru mu xaxxauna a tsakar gida" Mama Hadiza ta
sunkuyar da kai tana murmushi, Inna na kallon Maryam tace "Toh ita wancan
har yau ba manema ne yarinya ta xama sangamemiya ban ji ana batun aure ba
Hadiza, kina gaba tana biye da ke fa a baya" Maryam ta hade rai ta
gaisheta, Inna tace "Lafiya lau, baki da samarin ne?" Maryam dai bata
ce komai ba ta dauke kai, Mama Hadiza dai sai murmushi take tana kallon
uwartata, Inna ta tabe baki tana gyara daurin dankwalinta a hankali tace "Ni
dai ba ruwana" Mama Hadiza tace "Toh Ina amaryar, ango dai shi ya
dauko mu airport daxu?" Inna tace "Isuhu ai ya lalace ya daina shigo
min nan kwata kwata sai dai mu ci karo a tsakar gida, Ita kuma Imaan suna can
bandaki tare da mata mai gyaran jiki, ke kya ce canja mata fata xata yi, ni
kada garin neman ido a rasa gira a kona min jika in shiga uku, iyayin matar yyi
yawa wllh, gashi duk tayi ta ajiye min kaya ta ko Ina kamar tababbiya, ni ko in
tattara in jibge mata su a kan katuwar jakarta, ni dai na gaji wllh" Dariya
Mama Hadiza ta dinga yi, can tace "Mujaheed fa inna?" Inna ta kalleta
tace "Ai Mujaheed ya daina xuwa gidan nan, ni na fi wata ma ban gansa ba,
ba laifin xaune balle na tsaye ban san me na masa ba ya dauke kafa" Mama
Hadiza ta fiddo wayarta a jaka tace "Toh yanxu ai dole ya xo, jiya ma mun
yi waya da shi kafin in taho..." Tana magana tayi dialing number Mujaheed,
har ya gama ring bai dauka ba, Inna tace "Atoh, ko dai an sace wayar tasa
ne, nima har na gaji da kira ba a dauka fa" Imaan ce ta fito daki sanye da
Hijab har kasa, ta wara ido ganin Maryam ta nufeta da sauri ta rungume ta cike
da jin dadin ganinta, Maryam ta wara ido tace "Waoww sis kinga yanda kike
glowing kuwa? Wllh kin yi kyau sosai" Imaan na murmushi ta koma gun Mama
Hadiza ta durkusa ta gaisheta, Mama Hadiza ta jawota jikinta smiling broadly
tace "Maa sha Allah, my daughter kinyi kyau sosai, ya shirye shirye"
Imaan ta boye fuskarta jikinta a hankali tace "Lafiya lau mama" Inna
tace "Ai dama ita Imaan da kyanta, wannan gyaran kyanshi dama Ummi, ita ce
mummunan gidan, gaskiya ban san inda Rukayya ta samo ta ba..." Dariya Mama
Hadiza tayi tana kallon Inna, Inna tace "Allah kuwa" Mama Hadiza na
kallon Imaan tace "Toh tafi ki goge jiki ki shirya" Imaan ta mike
tana murmushi ta wuce daki Maryam ta bi ta da kallo don kyau ba na wasa tayi
ba. Imaan na xaune tare da Maryam a bedroom din Inna bayan la'asar, Maryam dake
ta kallonta a hankali tace "Kina nufin ba events da xa ayi Imaan?"
Imaan ta bude hannu tace "Nima ban sani ba sai dai ki tambayi Maimoon, daxu
dai ya kawo IV, su xa suyi dinner" Maryam tace "Toh dress code fa?
Kuma wani kayan yace xa ki sa?" Imaan tace "Oho ni bai gaya min
ba" Maryam tace "Kamar ya, ba ku shirye shiryen tare ne?" Imaan
ta tabe baki kamar baxata ce komai ba, sai kuma tace "Ni ko waya fa bama
yi" da mamaki Maryam tace "Saboda me?" Imaan tayi shiru tana
kallonta, Maryam ta kamo hannunta tace "Talk to me, what's
happening?" Imaan ta sauke idonta tace "Nima ban sani ba, baya kirana
sai dai in ni na kirasa, kuma ba xuwa yake ba" Maryam ta xaro ido tana
kallonta da mamaki, Imaan ta d'an yi murmushi tace "In xubo mana abincin
ynxu?" Maryam tace "Plss mu yi magana ki ajiye batun abinci, toh ke
kina ga babu abinda kika masa Imaan?" Imaan ta girgixa kai a hankali tace
"Ba abinda na masa wllh, he just changed all of a sudden, I don't know
why...." Sai kuma tayi shiru lkci daya hawaye ya kawo idonta, Maryam ta
kasa daina kallonta lkci daya jikinta yyi sanyi, can cikin sanyin murya tace
"Kuma kin tambayesa abinda kika masa? Kila kin yi offending dinsa baki
sani ba" Imaan tace "That doesn't warrant him to change his attitude,
ko don yaga few days ya rage a daura mana aure shi sa yake min haka" sai
kuma ta fara kuka a hankali, Maryam taji gaba daya hankalinta ya tashi ta
rungumeta tace "Plss kar kiyi kuka, we have to find out why d sudden
change of attitude, be strong plss" Imaan dai bata ce mata komai ba, bayan
wani lkci ta mike a hankali tace "Bari in xubo mana abinci" daga haka
ta fita dakin. Bude Ido Sadeeq yyi don ganin wanda ya shigo masa bedroom dinsa
that is almost out of bound for everybody except his mum, Mikewa xaune yyi yana
kallonta, Mummy tace "Sai yaushe xaka kai masu kayan da ka bari parlor na
ga lokaci na ta wucewa Abba, today is Tuesday, or do they have any other
alternative?" Yace "Mum xan ba Mariya ta kai anjima" Da mamaki
Mummy tace "Mariya kuma, kaga ina involving din su a harkata a gidan
nan?" Sadeeq ya koma ya kwanta yace "Kawarta ce fa Mum, ta san
gidansu ai, I don't think I am going out today" Mummy tace "You tell
me what's wrong with you this days Sadeeq, meye matsalar ka" Mikewa xaune
yyi yace "Mummy frankly speaking gaba daya naji bana son auren nan kuma,
am I even supposed to get married now? Isn't it too early? Sure Ina sonta amma
bana son auren ynxu gaskiya" Wani kallo ta dinga masa, kafin tace
"You are stupid..." tashi yyi ya wuce bathroom ya rufe kofar gbam, ta
fi minti biyar tsaye dakin mamaki fal xuciyarta kafin ta juya ta fita. Sadeeq
ne xaune parlon Dad dinsa da yammacin ranan, tun shigowar sa parlon bai yarda
ya daga kansa ba, Mummy ma na xaune parlon sai kallonsa take, Alhaji Ahmad
Bulasawa dake tsaye ya gama duk fadan da xai yi kamar xai ari baki daga karshe
ya xauna yana kallon Sadeeq da kyau yace "If you think I have a son that
will tarnish my image here in my mother's land... you are mistaken Abubakar,
ban haifi wannan d'an ba, kindly get out from my sight now, aure ba fashi tunda
ba wani ya nema maka yarinyar ba, kuma ba wani yace ka fito da xancen aure ba
yanxu" A hankali Sadeeq ya mike ya nufi kofa ya fita parlon Mummy ta bi sa
da kallo, Alhaji Ahmad yace "In sha Allah daurin aure babu fashi ranan
juma'ah..... No one is tarnishing my image" direct Sadeeq part din Step
mum dinsa ya wuce, Aunty na dakinta ya sameta, ta ajiye abinda take yi tana kallonsa
tace "Ango kayi scarce, ya shirye shirye" ya karasa kusa da ita ya
xauna ya rike kansa, da mamaki tace "Me ya faru Abba?" Da kyar ya
dago yana kallonta da idanuwansa da suka kada yace "Pls Aunty kiyi ma Abba
magana a daga bikin nan, wllh naji gaba daya am not ready to be a family man,
wani lkcn sai ayi amma ba yanxu ba" Bude baki Aunty tayi tana kallonsa, da
wani expression tace "Are you alright Sadeeq? Kana da hankali kuwa, biki
saura few days kace a daga, waye kake son maidawa kananun mutane, ubanka dai
koh? Kai ma kasan Abban ka will never support this, wani laifi fatiman tayi
maka ne?" Ya girgixa kai a hankali yace "Ni bata min komai ba, kawai
naji bana ra'ayin aure yanxu, ba cewa nayi a fasa ba, a daga kawai nake so...
" Aunty ta saki baki tana kallonsa with much surprise, can ta girgixa kai
tace "Don Allah ka rufa mana asiri, kada ka maida mu kananun mutane a idon
jama'ah Abba, haba Sadeeq this is very unusual of you, me ya same ka haka, ko
dai gantalallun frnds dinka ke xuga ka??" Rasa ma me xai ce mata yyi, can
ya mike kawai ya fice daga dakin ta bi sa da kallo baki bude. Mummy ta gama
hada duk kayan da suka ma Imaan kala uku masu tsada, daya na dinner biyu kuma
na events idan xa su yi a gida, immediate din Sadeeq Annur ta samu a dakinsa ta
mika masa tace "Gashi ka kai ma yayanka yana garden, kace nace ya tafi ya
kai masu yanxun nan" daga haka ta fita dakin. Bayan Magrib Sadeeq yyi
parking kofar gidansu Imaan ya kashe motar ya fito ya dau ledan kayanta dake
bayan motar, ya fi minti biyar tsaye jikin motarsa ya ki kiranta a waya, can
kawai ya shiga cikin gidan kamar mai counting steps dinsa, direct part din Inna
ya nufa, yayi sallama bakin kofar parlon, Inna ce ta amsa sannan ya shiga, Mama
Hadiza dake xaune parlon tana cin abinci suna hira da Hajiya Bilki mai gyaran
jiki, ta rufe abincin ta ajiye gefe ganinsa, Inna ta mike ta shimfida masa
darduma tana masa sannu da xuwa, sauke kansa yyi kasa yana d'an murmushi ya
ajiye ledan hannunsa ya xauna a hankali ya gaida su gaba daya, Mama Hadiza ta
amsa tace "Sannu da xuwa Sadeeq..." yace "Kun xo lafiya
mama?" Tace "Alhmdllh, ya shirye shirye?" Yace
"Alhmdllh" Inna tace "Kaga yanxu kuwa ta fita taje raka wannan
yarinya Maryam su gaisa da Ahmadu ko a kira maka ita a waya?" Yace
"A'a kaya ne dama na kawo mata" Inna tace "Atoh ai shkkn sai in
ajiye mata, kana dai cin abinci kuwa Bukar naga kai ma ka fige kamar amaryar
taka" murmushi yyi ya sunkuyar da kansa yace "Ina ci Kaka" da
damuwa Inna tace "Aa ku dai yi hakuri ku kwantar da hankalin ku ko kwa yi kyan
gani da biki don Allah..." Shi dai bai ce komai ba, Bude kofar parlon aka
yi Mujaheed ya shigo da sallama, sanye yake cikin kananun kaya hannunsa rike da
makullin mota, Tunda ya shigo Mama Hadiza ke kallonsa, yyi murmushi yana shafa
kansa ya karasa cikin parlon, sai da ya fara ba ma Sadeeq hannu sannan ya xauna
kusa da Mama Hadiza a hankali yace "Kun xo lafiya mama?" Ta rike ha6a
tace "Kayi rashin lafiya ne ba a gaya min ba Muhd?" Yace "Ae
naji sauki yanxu, kwanaki ne nayi rashin lafiya, tare da Maryam ku ka xo?"
Inna dake kallonsa da kyau tace "Toh dai yau ga ni, ga Mujaheed, ga Hadiza
da katuwa mai gyaran jiki, ga kuma yaron nan Sadeeq, sai Mujaheed ya ji tsoron
Allah ya fito ya gaya ma kowa abinda na masa a parlon nan yanxun nan... Don ni
ban san abinda na masa ba, idan Mujaheed bai saka min da abun kirki bautar da
na masa ba yana yaro ai baxai guje ni ba yanxu da tsufa na, Hadiza yau kusan
wata shidda kenan ban sa Mujaheed a ido ba, ba laifin tsaye balle na tsaye, ba
lafin fari balle na baki, ko na kirasa baya dauka to ni dai gaskiya ya fito ya
fadi abinda na masa ko in bar sa da Allah..." Ko kallonta Mujaheed bai yi
ba sai juya makullin hannunsa yake, Hajiya Bilki dai sai dariya take kasa kasa,
Mama Hadiza ta kasa cewa komai sai kallon Inna take ganin yanda ta ci serious ta
tsuke fuska, Sadeeq dai idonsa na kan wayarsa da yake dannawa, cikin rawar
murya Inna tace "Ko don nace matarsa mayya ce ya kullace ni ban sani ba,
toh banda haka me na ma Mujaheed, wllh ban masa komai ba, ko wani kaga xai
mance da ni haka a rayuwa kai ba mai tare min bane balle kai da kanka, gashi
duk ka wani fige kamar kazar Hausa kuma ace yarinya ba mayya bace.... Ni dai ba
ruwana" Mujaheed na kallon Mama Hadiza yace "Ba ku taho da su
El-Ameen ba?" Mama Hadiza ta sauke ajiyar xuciya tace "Xa su taho tare
da babansu xuwa jibi, xai xo daurin auren shi ma" Inna ta bude baki tace "Toh shi Mujaheed
ba mutum bane da ya ki xuwa nasa daurin auren?" Mama Hadiza tayi murmushi
tace "Inna kar ki manta Imaan ita kadaice gun Yaya, banda haka ma da ba
lallai nima in xo ba tunda yaushe na xo bikin Mujaheed, to wannan dalilin yasa
babansu Maryam ma xai xo daurin auren nata...." Inna ta tabe baki tace
"Ku dai ku dinga tsoron Allah, ku dinga abu saboda Allah, wato shi
Mujaheed bai cancanci a xo nasa ba sai na Imaan, to ubansa ya sha Mama ya bar
ma ubanta, duk babu wani banbanci" dariya kawai Mama Hadiza tayi bata dai
ce mata komai ba, shi dai Sadeeq idonsa na kan wayarsa, Maryam ce ta fara
shigowa parlon Sadeeq ta fara gani ta gaishesa da fara'a, ya amsa yana murmushi
yace "Kun xo lafiya Maryam?" Tace "Alhmdllh Dr, ya shirye
shirye" yace "Lafiya lau" ta wara ido ganin Mujaheed tace
"Ya M.A..." Imaan ta shigo parlon hannunta rike da fruit salad da
Ammi ta bata ta kawo ma Mama Hadiza, ganin Mujaheed xaune parlon ta tsaya tana
kallonsa ko kiftawa babu, daga kai yyi ya kalleta, bata san lkcn da ta ajiye
bowl din hannunta ta nufesa da sauri ta xauna kusa da shi tana kallonsa ta wara
ido tace "Yaya..." Ya shafa kansa kamar baxai ce komai ba sai kuma ya
d'an ja hancinta yace "Kanwar Yaya..." dariya ya bata, ganin yanda
take dariya yyi murmushi yana kallonta, rungumesa tayi a hankali tace "I
missed you" Kallonsu kawai Sadeeq yake, Mama Hadiza ta dinga ma Imaan wani
kallo amma imaan ko sanin tana yi bata yi ba, Inna tayi tagumi ta rasa abun
cewa sai yan idanuwa, Can a fusace tace "Ke dai gantalalliya ce wllh,
katuwa da ke ki fada jikin mutumi wai Yaya, yanxu fa ke matar wani ne, da ba
don mijin naki ya san alakar ki da Mujaheed ba me kike tunanin xai faru yanxu?
Kawai mata daga shigowa ki dare kan mutumi kice Yaya???" Da sauri Imaan ta
sake Mujaheed ta juyo, sai a nan suka yi ido hudu da Sadeeq, sosai gabanta ya
fadi ta xamo kasa tana kallonsa, Mama Hadiza dai ta kasa cewa komai amma gaba
daya kunya ya isheta, Inna tace "Toh waye kuma Yaya Allah na tuba ke ba
yarinya ba yanxu, mutumi yyi aurensa kema xa ki yi naki, ai kuma sai a hakura
haka sai 'ya yanku su ci gaba da xumuncin, ni dai ban taba ganin haka
ba...." Sadeeq ya d'an yi murmushi ya mike yace "Kaka ni xan koma
yanxu" Inna tace "Au to baka sha ko ruwa ba Bukar" yace "Ae
daga gida nake Kaka" Inna tace "Toh shikenan Allah maka albarka, kuma
ka dinga cin abinci kaji" yace "In sha Allah" Yana kallon Mama
Hadiza yyi kasa da kai yace "Mama xan koma, Allah huce gajiya" Mama
Hadiza tace "Toh ka gaida mutan gidan Sadeeq na gode kwarai" kofa ya
nufa, Inna na kallon Imaan tace "Ae sai ki tashi kusa da mutumin nan ki
tafi ki sallami mijin ki koh" Kin tashi Imaan tayi, Mama Hadiza na ganin
Sadeeq ya fita tace "Baxa ki tashi ki fita ba shashashar yarinya, kawai ki
kama ki rungume mutum a gabansa sbda baki da natsuwa" a fusace Inna tace
"A'a ke kuma bana son fadan rashin gaskiya, wa gareta da xata rungume
banda Mujaheed din, a haka suka taso abun su dama can, shi ma mijin ai ya sani,
ko ce maki aka yi bai sani ba, sarai ya san yayanta ne bata da kamarsa a duniya
ko kun haifa mata wani yayan ne ban da shi Mujaheed din?? Ni bana son fadan
rashin gaskiya wllh, kinsan yaushe rabon mu sa Mujaheed din a ido ne? kuma ta
gansa baxata nuna farin cikinta ba, kullum sai ta min xancensa don ma Ina
gwaleta kamar bai dameni ba alhalin kullum da daddare sai nayi mafarkinsa,
kawai mata daga xuwa ki hau yar mutane" Hajiya Bilki ta dinga dariya tana
kallon Inna, a hankali Imaan ta mike ta bi bayan Sadeeq Mujaheed ya bi ta da
ido.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
73.....
A hankali Imaan ke tafiya tana kallon Sadeeq da har ya kusa
gate sbda saurin da yake, kafin ta fita kofar gida har ya shiga motarsa ya
wuce, ta bi motar da kallo sannan ta juya a sanyaye ta koma part din inna, Mama
Hadiza dai har lkcn ta ki sake fuska don ba karamin 6ata mata rai abinda Imaan
tayi yyi ba, tana shigowa parlon kuwa ta dinga hararanta fuska daure, Imaan na
ganin haka ta sunkuyar da kai ta wuce bedroom din Inna duk jikinta yyi sanyi,
Inna ta bi ta da kallo sai kuma ta kalli Mama Hadiza tace "Toh ba shikenan
ba har ta sallamesa ta dawo, amma kina neman maida karamar magana babba sbda
rashin tsoron Allah, ai shi Sadeeq din ya fi kowa sanin tsakaninsu da Mujaheed,
kuma yaro ne mai hankali da natsuwa, tunda nake ban taba ganin yaro natsatstse
irin sa ba, gashi kwata kwata abun sa bai rufe masa ido ba, kyauta yake kamar
bai san ciwon dukiyar ba, to bayan ni har ku ma baxa ku huta ba aka ce maki
Hadiza??" Ita dai Mama Hadiza bata ce komai ba tayi tagumi, Inna ta tabe
baki tace "Ni dai ba ruwana... A dinga kyakkyawan xato domin Allah, sai
kace warce ta fada kan wani kato can a titi, wannan ae yayanta ne
Mujaheed" Mujaheed ya mike yana kallon Mama Hadiza yace "Toh na
gaishe ki Mama Allah ya huce gajiya sai na shigo gobe" Inna na kallonsa tace
"Amma kai dai Allah ya xuba maka shegen rowa Mujaheed kamar uwarka, banda
haka ina laifin ka riko mata Yar gasasshen kazar nan da yar lemo... ka wani
shigo gansansan daga kai sai kai, inda Isuhu ya fi ka kenan gaskiya"
Mujaheed dai bai tanka ta ba ya nufi kofa, tace "Toh nayi magana daxu baka
ce komai ba, ina fa da labarin abinda kayi ma Seeyama lkcn bikinta, to ita
Imaan ko don ba ubanku daya ba, naga har yanxu shiru baka yunkuro ba, kyansa
dama kawai ka bata kudin ni nasan abinda xan mata da shi, kar ka siya mata komai
ba abinda Ahmadu da Bukar basu yi mata ba, kudin xai fi mata amfani
gaskiya" ya juya ya kalleta yace "In xan bata abu ae ba sai kin sani
ba Hajiya, sai kace mahaifiyarta bata kusa....." Daga haka ya fice daga
parlon Inna ta rike ha6a tana kallon Mama Hadiza tace "Ke me yake nufi
kenan? Kaddai baxai ma yar uwarsa komai ba bikinta sukutum da guda?? To bari
dai in xuba ma saurautar Allah ido, amma wllh in har Mujaheed bai bada
gudunmawa mai kauri bikin Imaan ba lalacewa ta samesa duniya da lahira, kuma
ban san da wani idon xai kalli ubanta ba" Washegari laraba da safe driver
ya ajiye su Imaan saloon, Mai wajen da kanta tayi mata gyaran bayan ta gano
amarya to be ce, Banda kallonta babu abinda ake yi a saloon din, don gaba daya
she looks so new, tayi wani haske da fresh sai glowing ko ina na jikinta yake
kamar balarabiya, dubu ashirin Abba ya basu na gyaran gashin su uku don Ummi da
Rahma basu yarda sun biyo su ba, da kyar Maryam ta lallaba Imaan ta yarda ayi
mata kitso a gashinta, imaan har ta mance rabon da tayi kitso, haka aka ta
daure aka rangada mata kitsonta kanana mai kyau, sai kusan azahar suka kira
driver ya xo ya maida su gida. Sosai gida ya cika da jama'ah na kusa da nesa
duk da sai Juma'ah ne bikin amma kai kana ganin jama'ahn gidan kasan only child
ce xa ayi ma aure, kuma ga biki ya hade biyu, gaba daya yan uwan Ammi suna
gidan, daga su har 'ya yansu, Aunty ma duk yan uwanta na kusa da nesa sun iso,
Bakin ciki kamar xai kashe Umma, kwata kwata taki yarda ta fito daga dakinta
har da sa makulli daga ciki abun duniya ya taru ya mata yawa, anya auren nan
baxa ayi sa ba kuwa?? Tambayar da ta dinga yi ma kanta kenan, wata xuciyar na
assuring dinta baxa ayi ba ta xuba ido kawai. Su Imaan na komawa gida da awa
daya mai lallin da Aunty ta kira ta xo gida yi mata lalle, Inna ta gama xuba ma
imaan pepper soup din da Aunty ta aiko mata da abinci kenan mai lallin ta shigo
tare da Maimoon, Maimoon tace "Inna mai lalli ce" Inna ta kalli mai
lallin da damuwa tace "Naga jaraba, ko abinci fa bata ci ba kika xo lalle
baiwar Allah.... Tun safe take garari a titi wai gyaran gashi ynxu kuma daga ta
fito wanka na xuba mata abinci sai ki xo kice kin xo lalle baiwar Allah, ba fa
ta ci komai ba" Mama Hadiza dake parlon ta kalli mai lallin tace
"D'an yi hakuri ta ci abinci yanxu ta gama Aunty..." Mai lallin tace
"Toh xan jirata a waje" daga haka ta fita, Inna ta harari Mama Hadiza
ta gefen ido ta dau abinci ta tafi daki kai ma Imaan tana cewa "Abu dai
munafurci munafurci ba a son fadin gaskiya, na ma mata maganar gaskiya kin kwantar
da murya kina mata magana salon ta min kallon fitinanna" Imaan ta gama
saka kaya kenan Inna ta shigo tace "Ki ci abincin ki a nutse kafin ki fito
wani shegen lalli, ba ruwana da gantalewa, ko lallaba maki lallen bana yi da
kaina ba cikin dare" daga haka Inna ta juya ta fita. Maryam na kallon
Imaan dake tsakuran abincin da Inna ta ajiye mata tace "Ki bani number
Sadeeq in kirasa ai shi ya kamata ya baki kudin lalle da kitso ba su Abba
ba" Imaan ta kalleta, sai kuma tayi murmushi tace "A'a just leave
him... There is no need ai Abba riga ya bada" Maryam tace "Like
seriously tun xuwan mu kasar nan ban ga ya kiraki ba Imaan, there is something
wrong somewhere bai kamata kiyi shiru ba gashi jibi daurin aure ki cuci
kanki" Imaan ta tabe baki tace "Am not saying anything Maryam, kika
san uxurinsa" Maryam tayi shiru tana kallonta da mamaki, Imaan ta mike ta
rufe abincin don gaba daya ta kasa ci, tun last week tayi loosing appetite
dinta gaba daya, a hankali Maryam tace "Baki ci komai ba a abincin Imaan"
Imaan tace "Mai lallen tana ta jirana, anjima xan ci" daga haka ta
fita dakin, Maryam ta bi ta da kallo, bayan few minutes ta dau wayarta ta shiga
duba number Sadeeq, tana gani tayi dialing, har ya gama ring bai dauka ba, ta
sake kira nan ma bai daga ba, kwashe lambar tayi a nata wayar ta ajiye ta mike
ta shiga gyara ma Inna daki, tana gamawa ta dawo ta xauna ta dau nata wayar
tayi dialing number din Sadeeq, ba a dau lkci yana ring ba ya daga, shiru tayi
da farko sai kuma tayi masa sallama, ya amsa, tace "Sadeeq?" Yace
"Yes..." tace "Why the sudden change of attitude toward ur
financee Sadeeq?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Wait! Who is
this?" Tace "You answer my question first..." Yace "I don't
think you are in the rightful place to..." A d'an fusace tace "Kar ka
gaya min magana malama, wato kai a silly thought dinka ka riga da ka sameta
xaka fara walakantata tun bata shiga gidanka ba ko?? to wllh karya kake Imaan
ta fi karfin haka, you are mistaken malam, domin ka kawo sadaki kuma jibi
daurin aure ba yana nufin har ta xama taka ba...." Ya katse ta shi ma yace
"Toh ki ce mata tayi xuciya ta gaya ma iyayenta ta fasa auren kawai, sai
su maido min da sadakina.... I think this will be better than you calling and
saying nonsense on phone to me madam" daga haka ya katse wayar, Maryam ta
dinga kallon wayar da mugun mamaki nan ko xuciyarta cike yake da tantamar anya
Sadeeq din da ta sani ne wannan, Anya Sadeeq din da ya siya mata latest phone
da take mafarkin mallaka kwanaki da suka xo Nigeria kawai don tayi masa addu'ar
Allah ya bar sa da Imaan ne wannan, mikewa tayi very shock ta fita dakin, a
parlor ta tadda imaan mai lalli na mata lallin, Inna ta matsar da kujerunta
gaba daya ta lullube su, ta kwashe carpet dinta kada a goga mata lalli a cuceta
kamar yanda tace, Xaunawa Maryam tayi tana kallon Imaan, lkci daya taji
tausayinta ba kadan ba ya kamata, kawai mikewa tayi ta fice daga parlon daga
karshe.... Sai kusan Magrib Imaan ta wanke lallenta da yyi kyau ba kadan ba ta
tafi part din su dauko Hijab don Inna ta wanke mata gaba daya wanda ta taho da,
Shirye shiryen Mothers day da xa ayi gobe kawai ake yi a gidan, bata ga kowa
part din su ba ta wuce daki ta dauko hijab ta fito, Muryar Maryam taji tace
"Imaan" da sauri ta kalli direction da taji muryata ta ganta xaune
ita kadai a dinning, karasawa tayi tana kallonta tace "Me yasa kika ce
baxa ki yi lallen ba?" A takaice Maryam tace "Nothing" Imaan
tace "Amma fa jiya kince xa ki yi" Maryam tace "Fasawa nayi,
xauna mu yi magana Imaan" Imaan ta ja kujera ta xauna tana kallonta,
Maryam ta d'an yi shiru sai kuma tayi kasa da murya tace "You know what
imaan?" Imaan ta girgixa mata kai gabanta na faduwa, Maryam tace
"Plss ina son ku xauna da Inna kiyi mata magana yanda xata fahimce ki, ki
ce mata don Allah tayi ma su Abba magana a daga bikin nan xuwa wani lkci"
Kallonta kawai imaan ke yi, Maryam ta girgixa kai tace "This is not the
Sadeeq you know before imaan, ki rufa ma kanki asiri ki yi ma Inna bayani ita
kadai xata iya ma su Abba magana su daga bikin nan, wllh idan kika auri wannan
Sadeeq din you are going to live a miserable life in his home, gaba daya gadara
yake yana ganin ya gama samun ki, dama boye maki real him yyi tun farko, kinsan
yanda muka yi da shi a waya daxu da na kira in ji dalilin Change of attitude
dinsa?" Imaan da har hawaye ya kawo idonta ta girgixa mata kai a hankali,
Maryam tace "Ce min yyi ince maki idan kin isa ki fada ma su Abba kin fasa
auren a dawo masa da sadakinsa" Sosai gaban Imaan ya fadi ta dinga kallon
Maryam xuciyarta na bugawa, Maryam ta girgixa kai cikin sanyin murya tace
"I am not in support of you marrying Sadeeq any longer Imaan, ba shi da
mutunci ko kadan, hallaka ki kawai xai yi Imaan, kiyi hakuri ko min son da kike
masa ki samu Inna ki gaya mata abinda ke faruwa a san abun yi tun da sauran
lkci..." Imaan ta fara kuka a hankali, cikin sanyin murya tace "But I
love him Maryam, shi ma yana sona, I just don't know what came over
him..." Sai kuma ta fashe da kuka sosai ta hade kanta da dinning cikin
rawar murya tace "May be stress yasa yake jin haushi haka, ni dai nayi
masa uxuri, this is not the Sadeeq I use know, nasan idan munyi aure xa mu koma
yanda muke da in sha Allah...." Da mugun mamaki Maryam ke kallonta tace
"Are you on ur right senses Imaan, Ina gaya maki ga abinda mutumi yace
kice idan kunyi aure xa ku dawo yanda ku ke da???" Imaan ta dago tana
kallonta hawaye na sakkowa idonta tace "Ina sonsa a haka Maryam, kawai ki
taya ni da addua Allah ya maida sa yanda yake da, beside bayan duk bak'in da
suka taho from different places sai ace an fasa aure, idan shi bai fito ya fada
masu ya fasa ba I see no reason why I should do so Maryam" Mikewa Maryam
tayi tana mata wani irin kallo tace "Baki da hankali wllh" Imaan ta
tashi da sauri tace "Plss this should be between us, ban ga dalili me karfi
da xai sa ince na fasa auren nan ba, don Allah forget you even called him, ai
ni xan xauna da shi ba ke ba, I know he loves me, nima kuma Ina sonsa, so plss
mu bar maganan nan a nan" daga haka Imaan ta bar dinning din Maryam ta bi
ta da kallo baki bude. Daren ranan Imaan bata yi bacci ba, gaba daya she is
just disturbed nd restless, ta mike xaune daga karshe ta kalli Inna dake sllh
kamar dai yanda ta saba duk dare, kallon agogo tayi taga biyu da minti biyar,
wayarta ta dauka tana kallo, sai kuma ta shiga text message, cikin minti goma
ta gama rubuta ma Sadeeq text, da farko tambayarsa tayi ko tayi masa wani laifi
ne ya gaya mata, daga karshe kuma ta basa hakuri cikin tausasan lafazi ta tura
masa, tagumi tayi tana kallon wayar duk da bata expecting reply don tasan bacci
yake at that time, text taga ya shigo wayar nata gabanta ya fadi sosai, ta
dinga kallon wayar kafin ta dauka ta bude text din tana kallon content dinsa,
"if you think you notice any change of behavior da bai maki ba a tattare
da ni, ki yanke hukunci da kika ga is the best, wanda xai yi suiting din
ki" ta karanta text din ya fi a kirga amma ta kasa apprehending, can ta yi
dialing numbersa har ya gama ring bai dauka ba, ta kuma kira bai dauka ba, ta
tura masa text na cewar ya dau call dinta don Allah, ba a dau lkci ba reply ya
shigo yace "Good night" Ta dinga kallon reply din sannan ta ajiye
wayar ta mike ta shige bathroom ta rufe kofa, kuka ta fara yi a hankali tana
jin xuciyarta na mata xafi, tayi kukan da ta dade bata yi ba amma maimakon taji
d'an sanyi a ranta sai k'una da radadi, bubbuga kofa Inna tayi tace "Me
kike yi a bandaki tun daxu Imaan, lafiyan ki??" Imaan ta fara wanke
fuskarta da sauri, Inna bata fasa bubbuga kofar ba hakan yasa imaan ta bude
kofar kanta a kasa, Inna ta gwalo ido tace "Kukan uban me kike? Ni fa bana
son a gigitani gaskiya, ni ba karamin aiki na bane ince ki bi dare ki koma
gidan ku, lafiya kike kuka a bandaki" Imaan bata tanka ta ba ta fara
alwala, Inna tace "Naga jaraba, don xa a maki aure kuma sai ki shige
bandaki kiyi ta kuka salon cuta ta kama ki" inna na tsaye tana kallonta
har ta gama akwala ta fito ta sa hijab dinta ta hau saman darduma, Inna ta tabe
baki tace "Ni dai ba ruwana" daga haka ta tafi ta xauna ta ci gaba da
addu'o'in da take. Washegari tun sassafe Umma ta bar gida ana girke girke, ko
danginta daya babu a cikin mutanen da suka cika gida, Ummi da Rahma ma duk ta
sa sun shirya sun bar gidan, Aunty mamaki ta dinga yi na irin xuciyar umma,
tunda take bata taba ganin mata mai nuna bakin ciki kiri kiri a fili irin Umma
ba don cikin anko hudu da suka yi da Ammi ko daya ta ki yi, su Ummi ma ta ki
barin su dinka nasu da aka masu. Mama Hadiza ce xaune parlon Inna tare da Aunty
misalin tara na safiyar ranan Thursday din, Inna na kallonsu tace "Toh
dama so nake ku rufa min asiri ku tattara 'yarku ku maidata can bangaren ku,
tun daren jiya take kuka ga idanuwa can sun kumbure, toh ina dalili wani abun
ya sameta a bangarena, dama aure hauka ne, wannan mata mai gyaran jiki ba irin
lallashin da bata mata ba amma kamar ana tunxurata, to tunda uwarta ta sallama
maku ita shi sa na kira ku, ku tafi da ita can nayi kokari haka kuma Allah ya
gani" Aunty ta mike ta tafi dakin inna tana kallon Imaan dake kwance,
murmushi tayi ta xauna kusa da ita ta dagota tace "Haba daughter, kuka kuma
haka?? Ko kina da damuwa ne?" Imaan bata ce komai ba ta sunkuyar da kanta,
Aunty tace "Kiyi hakuri kar ki sake kuka kinji, it's always like this for
every lady Imaan" Imaan ta fara wani sabon hawayen, Aunty ta rungume ta
tana lallashinta, Mama Hadiza ta shigo dakin ita ma ta dinga kwantar mata da
hankali, sai da suka tabbatar tayi shiru gaba daya sannan suka fita dakin,
Aunty ta hado mata shayi mai kauri ta kai mata.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
74.....
Bayan azahar mai make up da aka yi hiring ta xo tayi ma Imaan
very light make up da ya fito da ainahin kyanta na 'yar fillo, ta saka wani
lace mai tsadan gaske da Daddy yyi mata da head din da xata saka, ko tsinke ba
a taba ba a lefenta dama, gaba daya kayan da xata yi fitan biki Daddy ne yyi
mata su, tayi kyau har ta gaji barin ita da dama bata make up, kowa sai
kallonta yake cike da sha'awa, Aunties din Sadeeq da Step mum dinsa duk sun xo
gun mother's day din, Mariya da frnds dinsu na islamiyya da boko duk sun xo
suma, da Ammi da Aunty ankon lace suka yi, ko kai ka gansu sai sun burge ka,
karfe uku da wani abu Umma ta dawo gidan ita ma ta shirya cikin tsadadden lace
ta shigo cikin jama'ah ana ta gaisawa, sosai hakan ya ba Aunty mamaki sai dai
bata ce komai ba, bayan kusan awa daya sai ga Safeenah ta xo gidan cikin shiga
ta alfarma da sisters dinta biyu, can kuma sai ga wasu daga kawayen Umma, gida
ya cika da frnds din Aunty da Ammi masu ji da kansu cikin ankonsu na mothers
day da Aunty ta fitar, irin rawan da Safeenah tayi sai abun ya baka mamaki, don
xagewa tayi ba kadan ba kamar dai bikin masoyiyarta, sosai hakan ya ba Imaan
mamaki, ita dai tana xaune ana ta abubuwa a wajen, duk Ammi na lura da imaan
throughout the program bata da walwala kana gani kasan tana da damuwa, biyar da
wani abu Ammi ta samu ta kebe da ita a backyard din apartment dinsu tana
kallonta tace "Imaan ba nace ki kwantar da hankalin ki ba, or do you have
any problem da baki son fada min ne" Imaan ta girgixa mata kai cikin
sanyin murya tace "Ba komai Ammi...." Sai kuma ta sunkuyar da kanta
hawaye ya fara taruwa idonta, Ammi tayi tunanin kila duk fargaban da ko wace
amarya ke yi da xulumin barin gida ne ke damun yar tata, hakan yasa ta jawota
kusa da ita ta shiga kwantar mata da hankali cikin taushin murya, Imaan dai sai
gyada mata kai take hawaye na sakko mata, Ammi ta rungumeta tace "Bana son
wannan kukan Imaan, today is ur happy day, ki saki ranki pls" a hankali imaan
tace "Na daina" Ammi tace "Good ki shiga ciki ki xauna, karfe
nawa yace xa ku tafi dinner din?" ta girgixa kai tace "Ban dai sani
ba kila bayan Magrib" Ammi ta bude mata kofar kitchen tace "Go in and
get some rest before then, or are you feeling pain anywhere?" Imaan ta
girgixa kai tace "A'a" Ammi tace "Toh shiga ciki ki xauna"
shiga kitchen din tayi sai kuma ta juyo a hankali tace "Ammi Daddy na
fa?" Ammi tace "Ya dawo two days ago ai, don kina part din Inna
ne" Imaan tace "Toh" daga haka ta wuce dakinta, wayarta da ta sa
a jaka ta fiddo tana dubawa taga text na Sadeeq, sosai gabanta ya fadi ta bude
message din tana kallon content dinsa, "I am sorry to let u know that...
tonight dinner isn't going to hold anymore due to some reasons, ki sanar ma
mutanen gida, thanks" ta karanta message din ya fi sau biyar sannan ta
ajiye wayar a sanyaye, lkci daya ta ji wani hawaye me xafi na xubo mata,
xaunawa tayi gefen gado ta cire head tie dake kanta, Maimoon ta kira a waya
daga karshe ta sanar mata babu dinner din ta gaya ma su Ammi don a sanar ma
mutane da xa su tsaya sbda dinnern, Maimoon tace "What?? Sbda me??" A
hankali Imaan tace "Ke dai ki gaya masu kawai ni ina daki yanxu" daga
haka ta katse kiran, Aunty ce ta shigo dakin tana kallonta tace "Imaan shi
Sadeeq din yace maki babu dinner kuma?" Imaan ta kalleta trying her best
to look alright tace "Ehh daxu yyi min text Aunty, he said he is sorry for
the inconvenience" Aunty tayi shiru tana kallonta can tace "Toh shkkn
Allah ya so babu wanda ya tafi can din ma" daga haka ta fita dakin, kowa a
gidan yayi mamakin me yasa aka ce an yi canceling dina, ciki har da Umma dake
tsakar gida tace "Ahhh gaskiya mu dai ba a kyauta mana ba, mu da muka sa
ran mu yi yanda muka ga dama yau abu namu maganin akwabe mu, ni fa har na hango
an dire ma kowa full chicken a table da lemon masu kudi, gaskiya an shiga
alhakin mutane da yawa..." Safeenah tace "Ikon Allah, to bari mu san
inda dare ya mana dama dinner din nake xaman jira a tafi, ni ban ma taba jin
inda aka fasa dinner ba sai a bikin gidan nan" Ammi dai ko kallonsu bata
yi ba tana sallaman wasu frnds dinta da gifts da aka raba na mothers day, Mama
Hadiza tace "Toh ai gwara hakan, Allah na tuba meye abun birgewa a dinner,
albarka ake so a aure dama ba tsiya ba, dinner sai kace fadan Allah, ai ni wllh
ya burgeni da yace bbu dinner kowa sai ya ci kajin a gidansa...." Umma dai
bata kalli inda take ba ta shiga sallaman neighbors dinsu da xa su tafi, Mama
Hadiza ce ta tafi sanar ma Inna babu Dinner don suna can ana shiri da ta Rasulu
da taxo da yamma, Inna ta gwalo ido tana kallon Mama Hadiza tace
"Subhanallahi shi Bulasawan wiwi ya sha da xai ce an fasa shagalin?"
Mama Hadiza dai bata ce mata komai ba ta fita, Inna ta kalli Ta Rasulu da har
ta fiddo kayan da xata saka da mayafi tace "Yau naga gantalallen mutumi ta
Rasulu, wai ki ji ba casu" Bayan isha Imaan na xaune can karshen gado tana
ta bin frnds dinsu da Mariya dake ta hira a dakin da kallo, ko kadan bata san
abinda suke cewa ba don gaba daya she is absentminded, Maryam dai na xaune one side
tana danna wayarta amma gaba daya mood dinta wasn't good, Maimoon ce ta shigo
dakin ta nufo Imaan ta mika mata wayar hannunta, Imaan ta amsa a hankali tace
"Waye?" Maimoon tace "Ya M.A" Imaan ta kai wayar kunne tayi
sallama, cikin sanyin murya Mujaheed ya amsa mata daga daya bangaren, tace
"Ina yini Yaya?" yace "Lafiya, can you pls come out now?"
Tace "Kana Ina?" Ya d'an yi shiru sai kuma yace "Ki sameni bayan
apartment dinmu" tace "Toh" daga haka ya katse wayar, ta mika ma
Maimoon wayarta ta sauka daga kan gadon ta dau hijab dinta har kasa ta saka,
Maryam na kallonta tace "Where are you going to?" Imaan tace
"Yaya ke kirana" daga haka ta fita bayan tace ma su Mariya tana xuwa,
ta kitchen dinsu ta fita, ta dinga tafiya kamar mai tausayin kasa har ta kai
Bangarensu Maimoon, tsaye ta gansa yana facing bango har ta iso kusa da shi bai
juyo ba, a hankali tace "Ga ni Yaya" juyowa yyi yana kallonta, lkci
daya ya sauke idonsa, ya fi minti biyu bai iya yace komai ba, sai kuma cikin
sanyin murya yace "Sure I was suppose to ask you what u want for ur
wedding but I didn't Imaan, but I don't know if you will appreciate this little
that I have for you..." Imaan dai sai kallonsa take, wani round box mai
kyau dake hannunsa ya bude yana kallonta ya fiddo bracelet sai kyalli yake kana
gani kasan na menene ya kamo hannunta a hankali ya saka mata a wrist cikin
sanyin murya yace "Am hoping you will love it lil sis" lkci daya
hawaye ya kawo idonta ta fada jikinsa tana shessheka tace "Nagode
Yayana" rungumeta yyi cikin breaking voice yace "I am... wishing u
all d very best in ur marriage lil sis, Allah ya ba ku xaman lfya, but.. but i
want to let you know this Imaan....." Sai kuma ya kasa ci gaba ya runtse
ido, saketa yyi ya janyeta jikinsa ya juya xai bar wajen tace "You want to
let me know what Yaya?" Bai juyo ba sbda bai son taga hawayen idonsa yace
"I want to let you know that, kiyi ma mijin ki biyayya, be the best wife
you can..." Daga haka ya wuce ta bi sa da kallo tana goge hawayen idonta
tace "Toh nagode Yaya" a hankali ta juya ta koma apartment dinsu
hawayen da take ta gogewa ya ki tsaya mata. Kamar Daren jiya wannan Daren ma
Imaan bata yi baccin kirki ba, sai kallonsu Mariya da Maimoon da Maryam dake ta
baccinsu take, daga karshe ta tashi ta dauro alwala ta dinga sllh har sai da
taji bacci ya xo mata, nan kan darduman ta kwanta nn da nan kuma bacci yyi awon
gaba da ita. Da asuba Ammi ta shigo ganinta kwance kasa ta tada ta tana
kallonta tace "A kasa kuma Imaan maimakon ki tafi dakina?" Imaan ta
mike xaune tana murxa ido tace "Sllh nayi ne daxu" Ammi tayi shiru
tana kallonta, can tace "Toh ku tashi ku yi sllh lkci yyi" daga haka
ta fita dakin, Da safe gida ya xamo ba masaka tsinke duk inda ka bi jama'ah ne,
tun asuban fari dama ake ta girki a gidan don Aunty tace da kansu xa su yi
abinci ba sai an wani kira masu yi ba, Umma ma dai na cikinsu, da ita aka dinga
yin komai tun asuban, Ba karamin tilasta Imaan Ammi tayi ba ta sha shayin da ta
hado mata sannan mai make up tayi mata make up kamar jira, yau ma dai wani
ubansun lace din ta saka da ya fi na jiya,
Maryam kam cewa tayi kanta na ciwo don ma kada a tilasta ta saka kaya,
da ta tuna yanda suka yi da Sadeeq jiya sai ranta yyi mugun baci, in kuma ta
tuna abinda Imaan ta gaya mata wai ba ruwanta sai tayi wani murmushi tana
tausayin Yar uwar tata, Maimoon da Mariya suka cakare cikin ankonsu na ranan
aka dinga hotuna. Karfe sha daya Yusuf ya fito dakinsa xuwa parlon Abba ta
dalilin kiransa da yyi a waya, gaisawa yyi da mutanen dake parlon nasu don tun
safe yake daki da few frnds dinsa, da sallama ya shiga parlon Abbansa yana
kallonsa ya xauna yace "Gani Abba...." Abba xai yi magana Daddy ya
shigo parlon da sallama, Yusuf ya gaishesa, Daddy ya amsa gaisuwarsa sannan ya
xauna yana kallon Abba yace "Ina hanya ka kirani Barrister..." Abba
ya kalli Yusuf yace "Kaje waje ku shigo tare da Sadeeq, ya kira yana
waje...." Yusuf yace "Sadeeq Bulasawa?" Abba yace
"Ehh" mikewa Yusuf yyi ya fita, Daddy ya kalli agogo sannan ya kalli
Abba yace "Why is he here?"
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
75.....
Tare Yusuf suka shigo parlon Abba da Sadeeq, Sadeeq yyi kasa
da kai ya cire glasses din idonsa ya xauna saman rug ya gaishesu cikin sanyin
murya, amsawa suka yi a tare suna kallonsa, Yusuf ya xauna shi ma yana duban
Sadeeq da ya ki dago kai, calmly Abba yace "Hope all is well
Abubakar?" Sadeeq bai ce komai ba kuma bai dago kansa ba, daga daddy har
Abba kallonsa kawai suke, Yusuf ma haka, Can Sadeeq ya dago kansa ba tare da ya
yarda sun hada ido da ko daya daga cikinsu ba a hankali yace "I am sorry I
am saying this late, ina son don Allah ku min alfarma ayi hakuri da daurin
auren nan yau saboda wasu dalilai...." Kallon mamaki Abba da Daddy suka
shiga yi masa, Yusuf da ya xaro ido shi ma ya dinga kallonsa, Sadeeq ya shafa
kansa murya can kasa yace "I think I am not ready for marriage now, I am
sorry I am saying this at the die minute, but this is just d fact, ku yi
hakuri...." Yusuf na masa wani kallo ya mike a mugun fusace yace "How
dare you say such at this time, who do you think you can take for granted
here...." Abba da gaba daya Sadeeq ya gama kulle masa kai cikin cool voice
yace "What exactly are you trying to tell us here now Sadeeq.... What do
you mean?" shiru Sadeeq yyi bai ce komai ba, can ya kallesu yace "I
think it's good a fasa auren nan sai wani lkcn, ku min afuwa...." mikewa
Daddy yyi cikin tsawa yace "You are very stupid...." Abba ya mike da
sauri ya nufi d'an uwan nasa sanin xuciyarsa yana kallonsa a nutse yace
"keep calm Abubakar, keep calm..." Mikewa Sadeeq yyi kansa a kasa
yace "I am sorry..." Daga haka ya nufi kofa ya fita daga parlon,
Yusuf ya bi sa da kallo da mugun mamaki, "Innalillahi wa inna ilaihi
raji'un" shi ne kalmar da Abba ya dinga furtawa ya kasa tsaye waje daya,
daddy ya koma ya xauna a hankali trying his best to be calm, Abba ma ya koma ya
xauna har lkcn yana nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, silent din kusan
minti biyar ne ya biyo baya a parlon, kowa da tunanin da yake a ransa, can Abba
ya daga kai ya kalli daddy, lkci daya wani tausayin d'an uwan nasa ya rufe sa,
how will such thing happen to his only child, cikin sanyi Abba yace "Look
Abubakar you need not to worry, haka Allah ya tsara kuma Alhmdllh, I am sending
them their pride price immediately, sannan plss do not say anything to anybody
about this yet...." Daddy dai bai ce komai ba ya jinginar da kansa da
kujera ya lumshe idonsa, Yusuf duk jikinsa yyi sanyi ya ma kasa kallon iyayen
nasa ya rike kansa kawai, Abba ya mike walking round as if looking for a
solution, sosai xaka ga damuwar dake tattare a fuskarsa, Daddy ya mike daga
karshe calmly yace "Bani sadakinsu in mayar masu yanxu Barrister"
sanin halin daddy yasa Abba yace "Xan maida da kaina Abubakar, ba sai ka
je ba" duk ynda daddy yyi Abba ya basa sadakin kin basa yyi hakan yasa ya
koma ya xauna xuciyarsa na tafarfasa, he just can't believe this is happening
to his daughter, can Abba xauna ya dau wayarsa ya shiga kiran layin Alhaji
Ahmad Bulasawa, sai da ya kusa katsewa ya daga, bayan sun gaisa Abba ya d'an yi
shiru sai kuma a nutse ya shiga tambayar Bulasawa dalilin da yasa xa su yi masu
abinda suka yi, Alhaji Ahmad Bulasawa dake sauraronsa keenly yace "I
really don't get you Alhaji, me ke faruwa, anyi wani abu ne??" Mamaki ne
ya cika Abba jin abinda Bulasawa ke cewa, bbu bata lkci ya shiga yi masa
bayanin ynda suka yi da Sadeeq yanxun nan, cikin daga murya Bulasawa yace
"He is seriously stupid, wato abinda ya xo yace maku kenan, to wllh ko ya
ki ko ya so aure ba fashi, my reputation is above everything, ana saukowa
masallaci dama daurin aure na nan bbu fashi in sha Allah, till we meet
there...." Bai jira cewar Abba ba ya katse wayar, Abba ya kalli Daddy don
wayar a hands free ya sa, Daddy ya girgixa kai yana murmushin karfin hali yace
"I will never give out my daughters hand in marriage to that son of him,
tunda har da kansa ya nuna baya auren that's the end, ba neman kai nake da
Imaan ba, don't forget she is all I have got, da a cutar min ita gwara an
cuceni ko wani irin cuta ne kuwa, we are returning their pride price and
everything immediately, Allah ya hada kowa da rabonsa na alkhairi, Allah yayi
mata xabi na gari, bak'i da suka xo from far don taya ni farin ciki xan
sallamesu ana saukowa masallaci in sanar masu bbu auren kuma, and I will
forever be grateful coz they are all here bcos of my only child, in sha Allah
xa mu je a daura auren Yusuf nata kuma Allah ya musanya mata da mafi
alkhairi" daga haka daddy ya mike ya nufi kofa, Abba da duk jikinsa yyi
sanyi sosai yace "Sadeeq" tsayawa daddy yyi amma bai juyo ba, Abba
yace "Don't say anything about this to anybody, not even ur frnds, ka ji
abinda nace" Daddy dai bai ce komai ba ya fita parlon kawai, Abba ya
jinginar da kai so sad, Yusuf dai ya rasa abun cewa gaba daya he is just
shocked, can Abba ya kallesa yace "Go nd get set Yusuf, it's almost time,
and don't say anything to anybody yet" mikewa Yusuf yyi jiki ba kwari ya
fita parlon Abba ya bi sa da kallo. Gida ana ta shagalullukan biki bbu abinda
yasan me ke faruwa, Imaan dai tana bedroom dinta baccin da bata yi jiya ba duk
ya dameta, daga karshe ta kwanta ta dinga bacci, bbu wanda ya tasheta cikin
mutanen dake dakin don da ganin yanda take baccin ma kasan gaba daya she is
restless sai juye juye take. Abba ya dau sadakin da su Bulasawa suka kawo ya
tafi gidan da kansa don mayar masu don sosai ya gamsu da abinda d'an uwansa
yace na cewar bbu xancen aure kuma tunda Sadeeq din ya fito da kansa ya nuna ya
hakura to gwara kowa ma ya hakura ko don gudun kada ya jefa Imaan cikin wani
hali, kuma hakan shine abu na karshe da xai so ma only child din d'an uwansa,
ko kadan Bulasawa bai ji dadin kudin da Abba ya maido ba don kin karba yyi,
Abba yayi masa bayani a nutse yanda xai fahimce me yasa suka yi haka ya kuma
nuna masa dole su yi hakan don ceto imaan, ba irin kiran da Bulasawa bai ma
Sadeeq a waya ba amma ya ki dagawa, Abba na murmushi yace "Toh kaga
Alhaji, kawai Allah yyi masu xabi na gari, tunda kaga haka auren ba alkhairi
bane garesu" Bulasawa dai ya kasa cewa komai amma gaba daya shi ma ransa
ya sosu, Abba yyi masa sallama daga karshe ya bar parlon nasa bayan ya sanar
masa xuwa gobe ko jibi xa a maido masu lefe, shi dai Bulasawa har Abba ya fita
bai iya yace komai ba, can ya dau wayarsa ya shiga Kiran mahaifiyar Sadeeq,
tana dagawa strictly yace "ki sameni parlona ynxu, kuma duk inda Abba yake
I want him immediately, in sha Allahu kuma baxai kwanan min a gida ba yau, and
he is returning all my asset that is with him today, I have nothing to do with him
any longer" Bai jira cewarta ba ya katse wayarsa. Karfe daya saura Abba
suka wuce masallaci tare da frnds dinsa da kawu Bala, sae kawu Audu, bayan ya
samu waje yyi parking ya kira Daddy don ya ji yana iya, daddy ya sanar masa
yana hanyar xuwa mosque..... Ana sakkowa masallaci aka daura auren Yusuf da
Hafsat a kan sadaki dubu dari biyu, auren da jama'ah da dama suka shaida, sae
kuma daurin aure na biyu da ake jiran waliyyan ango amma shiruu, wanda hakan
yasa aka fara dago kila babu auren ne tun kafin su Abba su sanar da hakan, Abba
na kallon daddy dake kusa da shi murya can kasa yace "Abubakar xan daura
ma 'ya ta aure yanxu, auren da ina da tabbacin kowa xai yi alfahari da shi in
sha Allah, ko ba ynxu ba kuwa, da raina baxan ta6a yarda ka ji kunya a idon duniya
ba, kuma ikon da nake da shi a kan Imaan yasa xan daura mata auren huce takaici
duk da banda ni da kai da Yusuf sai Bala bbu wanda yasan abinda ake ciki"
Daddy dai sai kallonsa yake don tun idar da sllh ya ki cewa komai, Abba yace
"Ka je a kai ne waliyyin ango, Bala kuma dama shine waliyyin
amarya..." Yana fadin haka ya fiddo kudi a aljihunsa ya mika ma Daddy yace
"This is 200k, sadakin da xaka bada...." Abba na fadin haka ya koma
gun su kawu Bala da abokansa, ko kadan daddy bai yi welcoming idea din Abba ba,
kwata kwata bai son ma imaan dole, bai son tashin hankalinta ya xama biyu, na
rashin masoyi ga kuma aure without her consent, gashi bai san da wa Abba xai
hadata ba idan kuma yace xai yi magana Abba sai yaga kamar ya nuna masa bashi
da iko da imaan, gaba daya he was just confuse haka ya tafi dai don yin ynda
Abba yace, Daddy bai taba xaton sunan da yaji an kira na angon ana daura auren,
haka ya dinga kallon Abba ko kiftawa bbu, Yusuf kansa was more than shock ya
kasa daina kallon iyayen nasa, can ya lumshe ido ya bude xuciyarsa na
bugawa.... Abba ya sakar ma Daddy cool smile ganin kallon da yake masa,
maimakon Daddy ya mayar masa sai ya dauke kai kawai. daga karshe dai Yusuf fita
yyi to avoid gaisawa da frnds don gaba daya shock ya xame masa biyu..... Tun
bayan call da Mariya tayi answering a dakin Imaan yanayinta ya sauya gaba daya,
tafi minti biyu tsaye har sannan wayar na hannunta, Maimoon dake diban ma Imaan
dake xaune saman darduma ta idar da sllh abinci a plate ta kalleta ganin ko
motsin kirki bata yi tace "Lafiya Mariya" Mariya bata yarda ta kalli
Maimoon ba sbda hawayen da ya kawo idonta, Maryam ta ajiye dankunnen da take
kokarin sakawa ita ma tana kallon Mariya tace "Hope all is well
dear?" Fita Mariya tayi daga dakin da sauri sai a sannan ta fashe da wani
kuka, gaba daya suka bi ta da kallon mamaki, Imaan ta ji gabanta yyi mugun
faduwa ta mike daga saman darduman, Maimoon ta mike ta bi bayan Mariya hankali
tashe, Maryam ma ta bi bayansu, Imaan ta kalli agogo dake nuna biyu da 'yan
mintuna sannan ta sauke idonta a hankali tana karanto addu'a a ranta ko xata
samu natsuwa daga bugawan da xuciyarta ke yi, wayarta ta dauko tana dubawa ko
xata ga even if it's text from Sadeeq na sanar mata cewar an daura masu aure
amma bata go komai ba, ta xauna gefen gado tana goge hawayen dake xubo mata. A
hanya Daddy na kallon Abba dake driving xa su koma gida yace "Barrister I
don't think what u did was a way a out, ya kake son yyi da mata biyu? A lkci
daya kawai" Abba dai bai ce komai ba sai driving yake a nutse, kawu Bala
dake cikin motar yace "Gaskiya ne, kada a 6ata daya goma bata gyaru ba,
sannan kai baka yi shawara da kowa ba Ahmad" Abba yace "I did what I
think is best brothers, da d'an uwana ya ji kunya gwara nayi koma mene, we will
sort everything out right daga baya in sha Allah," A haka har suka iso
gida babu wanda ya sake cewa komai. Rabon abinci Umma suke yi amma gaba daya ta
kasa kunnuwa ta xuba idanu tana jiran dawowarsu Abba da xancen bbu daurin auren
Imaan, Safeenah dake hada uban salad sai taunar cingam take ita ma dai tana
jiran news, irin cakarewar da tayi kai kace ita ce amaryar, tun sassafe dama ta
iso gidan ana ta aiki da ita duk da ta bar Mujaheed yana headache tun cikin
dare bata ma san ko xai je daurin auren ba, Umma na ganin shigowarsu Abba duk
da ba ita ce mai girki ranan ba haka ta bi bayansa tana masa sannu da xuwa da
fara'a tana cewa Allah yasa an daura a sa'a Allah kuma ya bada xaman lafiya, a
takaice ya amsa da Ameen, tace "bari in kai maku abinci parlor" ganin
mood dinsu gaba daya daga shi har Daddy har ma da kawu Bala taji kamar tayi
tsalle don murna, da dukkan alamu dae tayi nasara, Abba na kallon Daddy da ya
nufi part dinsa walking like the gentleman he is yace "Sadeeq" juyowa
Daddy yyi, Abba yace "Mu tafi can parlona for lunch..." Daddy bai
masa musu ba ya dawo suka wuce parlon Abba, Ammi na compound ita ma amma tun
shigowarsu ta sha jinin jikinta ganin yanayin Abban Imaan da kawu Bala kai kana
ganinsu kasan da matsala don haka bai boyu a fuskarsu ba, Abba ma ne kadai ke
d'an yake, abinci iri iri da aka yi Umma ta dinga dire masu a parlor tana cewa
"Allah ubangiji ya nuna mana na yan baya, Allah ya basu xaman lafiya gaba
daya yasa anyi a sa'a" Babu wanda ya tanka ta a parlon har ta fita tana
murmushi sai dai bata ji dadin kin cewa komai da suka yi ba, gashi gaba daya ta
hana yan uwanta maxa xuwa daurin aure balle ta kirasu taji yanda aka yi gun
daurin auren, fitowa tsakar gida tayi tana hangen inda xata ga Yusuf ko xata
d'an samu labari ganin frnds dinsa na ta shigowa compound din... Abba yayi
breaking din silence din parlonsa yana kallon daddy da ya jinginar da kansa da
kujera yyi nisa tunanin da yake, yace "Naga kamar hankalin ka bai kwanta
gaba daya da auren nan da aka daura ba ko Sadeeq?" Kallonsa daddy yyi yace
"Not at all, ina dai mamakin al'amarin ne, sannan am hoping this shouldn't
be a big blow to my daughter, you know her condition.... Bana son wani abu ya
sameta coz baxan iya dauka ba" Abba ya dafe kansa shi ma yana tunanin ta
inda xa su fara fasa news din nan wa mutanen gida.... Mama Hadiza ce xaune
parlon Abba tare da yayyinta bayan kiran da kawu Bala yyi mata a waya, kai kana
ganinta xaka hango tashin hankalin da ke fuskarta karara, lkci daya ta shiga
furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Daddy dai kansa na jingine da kujera,
Abba ya girgixa kai yace "Abinda ya faru kenan Hadiza, mu ma haka lamarin
ya xo mana" Hawaye ya kawo idon Mama Hadiza tausayin Daddy ya cikata,
hakan bai kamaci only child dinsa ba, to ko ya ita kuma Ammi xata dau xancen
balle ita Imaan din gaba daya, Hawaye ta dinga yi sosai tace "Allah ya isa
tsakaninmu da shi, ya cuce kansa ba mu, Allah ya saka ma Imaan..." Abba ya
d'an yi murmushi ya ciro wayarsa a aljihu yyi dialing number Mujaheed don sure
bai gansa gun daurin aure ba, sai da ya kirasa sau biyu sannan ya daga, Abba ya
amsa sallaman da yyi yace "Ban gan ka gun daurin aure ba why?"
Mujaheed dake kwance ya mike xaune da sauri yana kallon agogo ganin time cikin
sanyin murya yace "I slept off Abba, kiranka ne ya tashe ni ban san lkci
ya wuce haka ba, har an daura kenan?" A takaice Abba yace "A'a ana
jiran ka, I want to see you home now my frnd..." Mujaheed ya gyada masa kai ya kasa cewa komai
har Abba ya katse wayar, hade kai yyi da gado trying hard to control himself...
Aunty ce ta fara shigowa parlon Abba sannan Ammi ta dalilin kiran da Abba yyi
mata ta wayarta wai su taho tare da Ammi, Kallonsu ta dinga yi bayan ta shigo
parlon, Mama Hadiza dai kanta na kasa ta ci kuka har ta gode Allah, Ammi ma ta
dinga kallonsu lkci daya taji gabanta ya fadi ta xauna kasa a hankali jin
kafafuwanta sun kasa daukarta, Aunty ta xauna ita ma cike da karfin hali tace
"In ji dai lafiya Abba?" A takaice Abba yace "Lafiya lau"
Kawu Bala yace "Lafiyar kenan Amina..." Bude kofa aka yi Umma ta
shigo ita ma ta dalilin kiranta da Abba yyi, ganinsu Ammi da Aunty, da Mama
Hadiza a parlor kawai taji kamar ta saki guda mai xakiii, rumors da ake tayi
tsakar gida ya tabbata kenan, Ta xauna da mamaki fuskarta tace "Lafiya
kuwa Alhaji, me ya faru?" Ko rufe baki bata yi ba Yusuf ya shigo parlon
tare da Inna da ta cakare cikin super abunta an daura dankwali sai xuba kamshi
take ta daura mayafi a kan dankwalin, tana murmushi baki har kunne tace
"Toh Allah ubangiji dai yasa an daura a sa'a Allah ya kauda idon makiya,
ya kuma sa gidan xamanta ne, ku kuma Allah maku albarka ya baku lada" Kawu
Bala ne ya amsa da Ameen kansa a kasa, shi dai daddy kansa na jingine da
kujera, inna ta nemi kujera ta xauna tace "Toh wani shawarar kuma xa ayi
yanxu aka tara mu a nan, ga dai bak'i can na baro" Abba yayi murmushin
karfin hali yace "Mujaheed muke jira Inna" Inna tace "Ae dole,
shi ne ubanta na hudu a nan ai...." Bude kofa aka yi sai ga Mujaheed ya
shigo parlon sanye da shadda fari kal sai walkiya yake, duk suka dinga kallonsa
ya nemi gefen Yusuf da kansa ke kasa ya xauna ya gaishe da iyayen nasa gaba
daya da ladabi duk suka amsa, Abba ya kalli Aunty a hankali yace "Go and
get Imaan immediately" Mikewa Aunty tayi ta fita ita gaba daya ta gama
shan jinin jikinta don gani take ba alkhairi yasa aka tara su parlor ba, ba
alkhairi xa su ji ba. Aunty na rike da hannun Imaan da ke lullube cikin mayafi
suka shigo parlon Abba, ta xaunar da ita gefenta, imaan bata iya ta dago ba
balle ta ga mutanen dake cikin parlon gabanta dai sae faduwa yake, Umma dai har
ta fara lissafin nawa xata kai ma mutumin nan kyauta don nuna masa farin
cikinta, gaba daya ta kasa boye how happy she is ah wajen duk da ynda ta dinga
dakewa, tunda Imaan suka shigo da Aunty Mujaheed ke kallonta ko kiftawa babu,
Abba ya bude wajen da addu'a sannan a hankali yace "Bbu amfanin tsaya jan
xance ko wani boye boye, kuma ina son kowa a nan ya dau abinda ya faru yau a
matsayin kaddara wanda aka ce ta riga fata, mu ma ba haka muka so ba, kowa ma
ba haka xai so ba, sai dai kawai mu kara gode ma Allah don shi ya san dai dai,
a takaice dai bbu xancen auren Fatima da yaron nan Sadeeq yanxu..." Ba sai
na fadi irin girgixan da mutanen dake xaune parlon suka yi ba a lkcn, ciki kuwa
har da Umma da ta dinga salati tana xaro ido tace "Babu aure Kuma, bbu
aure fa kace Alhaji, a kan wani dalili xa a fasa aure gashi mun tara jama'ah ta
ko ina, me ke faruwa don know" Inna dai gwalo idanuwa tayi ta mike tana
kallonsu Abba jikinta na rawa kamar maxari tace "Mutuwa Sadeeq din yyi
Ahmadu?" Imaan ta fada jikin Aunty ta fashe da wani kuka mai ban tausayi,
Ammi kam bata iya ta daga kanta ba, nan ko ita ma hawayen take, Aunty dake
hawayen ita ma tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me ke faruwa
Alhaji" Yusuf bai iya ya kalli mutanen parlon ba duk jikinsa yyi sanyi ba
kadan ba, Mujaheed ya dinga kallon Abba ko kiftawa bbu xuciyarsa na bugawa jin
abinda yace, kawu Bala yyi kasa da murya yace "Duk ku yi hakuri, we never
saw this coming, and we are in it all together, komai ya samu bawa a duniya
dama rubutattce ne, kuma bbu wanda ya isa ya kauce ma kaddararsa, wannan yaro
Sadeeq dai da kansa ya xo daxu ya nuna ya fasa auren yar mu, tuni kuma mun
maida masu sadakin su lefe kuma ko xuwa anjima in sha Allah xa a mayar, Allah
yasa hakan ne mafi alkhairi ga dukkanmu gaba daya...." Inna ta rushe da
wani kuka da tsorata mutanen parlon tace "To kuwa yanxun nan xan tafi in
nemo gidan Bulasawa in ci ubansa da d'an nasa, Allah ya tsine masu albarka,
Allah ya tarwatsa su, Allah ya isa tsakanina da su, Allah yyi yaga_yaga da
dukiyar nan tasu ta sata, shegu barayi, mu xa su kunyata a idon duniya ga bak'i
mun tara ta ko ins, to in sha Allahu kotu ce xata raba mu da matsiyatan,
Shari'a ce mai girma xa mu yi tun a duniya kafin mu tafi gaban Ubangijin mu,
yau xan tafi in shigar da kara a kotun Habuja...." Abba yace "Don
Allah ki sauraremu Inna, dama an taba aure dole?? bbu ruwan ki da su balle aje
wani shari'a kawai mu sa a ranmu fasa auren nan shine mafi alkhairi ga 'yar mu,
kuma basu kunyata mu ba don bamu bar masallaci ba sai da na tabbatar na fitar
da d'an uwana kunya na daura ma 'yar sa aure da nawa d'an da nake da iko
da...." lkci daya gaba daya mutanen parlon suka daga kai suna kallon Abba
with full shock, ko allura ya fadi a lkcn sai kaji karansa, Imaan taji kamar
numfashinta na mata gardama ta dinga kallon Abba xuciyarta na wani bugawan da
bai ta6a mata ba, Umma ta hadiye abu da kyar tana kallon Yusuf da kansa dai ke
kasa, ji tayi wani xufa na keto mata don wannan shine anyi ba ayi ba, yanxu
Yusuf aka makala ma yarinyar nan, Mujaheed dai sai kallon Abba yake xuciyarsa
kamar xai fashe sabida yanda yake harbawa, Abba ya mike yana kallon Inna da ta
cire mayafin kanta tana kikkifta ido tana kallonsa, yyi kasa da murya yace
"Na hada auren Imaan da Mujaheed yau, saboda ina da yakinin xai ma fi Sadeeq
din rike min 'ya ta da amana...."
*Table_shaker/Media shaker* 🙄✍🏻
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
76.....
Kusan a tare Ammi da Umma suka mike tsaye a parlon suna
kallon Abba da wani irin shock, can Ammi ta kalli Daddy xuciyarta na bugawa
lkci daya hawaye suka dinga sakko mata tana girgixa kai, Tuni Umma ta isa gaban
Abba cikin kidimewa bakinta na rawa haka ma ko ina na jikinta tace
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, la ilaha ilallahu Muhammadur
rasulillahi sallallahu alaihi wassalam, ban fahimce ka ba Alhaji? Ban gane ba
wllh tllh, Wani Mujaheed din ka hada da Imaan??? Wani Mujaheed din kake nufi,
wai d'a na kake nufi?? Ka min bayani don girman Allah Alhaji, wani Mujaheed ne
wannan??" Aunty ta kasa rufe bakin da ta bude tana kallon Abba a mugun
sanyaye ko motsi ta gagara yi daga xaunen da take, Mama Hadiza tayi tagumi tana
kallon Inna da bakinta ke hangame tana kallon Abba a tsorace da alama magana
dai ya makale mata gaba daya, sai a sannan Imaan ta gama fahimtar abinda Abba
ya fada few seconds ago, don tun bayan maganarsa taji komai na kanta ya kwance
ta kasa apprehending, da kyar ta gano me yake nufi bayan maganganun Umma, ja
baya ta dinga yi a hankali tana jin wani sanyi na ratsa ko ina na jikinta
numfashinta ya dinga sama sama kamar xai dauke, can ta juya a hankali ta kalli
inda Mujaheed yake xaune, kan kneels dinsa ta gansa ya rufe fuskarsa da both
palms dinsa.... wani ihun da yasa duk mutanen parlon suka juya kallonta ta fasa
da karfi, sai kuma ta mike da gudu ta fice daga parlon kamar mahaukaciya, Umma
ta durkusa kan gwiwowinta bibbiyu duk jikinta na 6ari ta rushe da wani
matsanancin kuka mai cike da tashin hankali ba na wasa ba tace "Alhaji ka
min bayani yanda xan gane don girman Allah, ko akwai wani Mujaheed din ne banda
nawa a gidan nan, ka fahimtar da ni fisabilillahi, don nasan Mujaheed guda ne a
gidan nan kuma d'a na ne, kuma da matarsa... Wani Mujaheed din ka hada da
Imaan???" Ammi da ta kasa controlling kanta ta fashe da kuka sosai tashin
hankali karara muryarta tace "Abubakar ban amince da auren nan ba, ban
yarda ba, nace ban yarda ba, warware auren nan xa ayi, ban amince da shi ba...."
tana fadin haka ta fice parlon da sauri tana kuka, Muryar Inna suka ji da karfi
tana xaga parlon tana cewa "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'una, la ilaha
ilallahu Muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wassalam, hasbunallahu wa
ni'imal wakeel, la ilaha illa anta subhanaka innee kuntu minazzalimin, wayyoo
Allah ni patuu, Naga abinda ya isheni waye kuma Mujaheed?? Lalacewa ta samu
Bukar da Ahmadu, Allah ka yo min agaji naga abinda ya isheni kankat a duniya
yau, jama'ah waye kuma Mujaheed, daga ina kuma aka samosa??" Umma dake
durkushe ko ina na jikinta na rawa ta dinga gyada kai kamar idanuwanta xa su
fito tana kallon Inna ganin abinda ta dinga yi a parlon, gaba daya a birkice
take don bata ma san tana gyada kan ba,
Mikewa Aunty tayi tana goge hawayen idonta ta fice daga parlon duk
jikinta a sanyaye, daga Abba har Daddy da su kawu Bala kallon Inna dake ta
xagaye parlon suke, har daga karshe ta tsaya cak waje daya ta juyo tana
kallonsu, sai kuma ta rushe da matsanancin kuka tana nuna su tace "Amma
Allah ya hada ni da gantalallun 'ya ya, waye kuma Mujaheed Allah na tuba, to
wllh kafin in tada gidan nan cikin minti kalilan a warware auren nan don jikata
ba rasa manema xata yi ba, ban amince da auren nan ba, kun cuce ni, kun ci
amanata kun ja mana fushin Ubangiji a gidan nan yau, lalacewa ta sami 'ya yana
ni Asabe...." sai kuma ta fashe da kuka tace "Tunda uwata ta haifeni
ban taba ganin haka ba" Umma ma ta fashe da kuka mai ta6a xuciya tace
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace ni Rukayya,
dama Mujaheed dina ake nufi ban sani ba, dama d'a na aka hada aure da Imaan, na
mutu na lalace kuwa" kuka take sosai ba na wasa ba ta daura hannu a ka ke
kya ce uwarta ce ta mutu, Ba Abba kadai ba har Daddy was so shocked at reaction
din kowa a parlon, Abba ya sunkuyar da kansa ya ma rasa abinda xai ce, Inna ta
xauna kan kujera ta kara fashe da wani sabon kukan tace "Idan ba a raba
auren nan ba yanxun nan ni dai xan ce na bar ku da Allah inyi tafiyata kano
Ahmadu da Bukar, Bala da d'an tsut" Abba ya dago yana kallonta, lkci daya
gaba daya mood dinsa ya canxa ganin yanda Inna ke kuka, Umma na jin abinda Inna
tace ta tsayar da kukan da take har sannan jikinta na 6ari tana kallonsu Abba
taji me xai ce, a hankali Mujaheed ya xame hannunsa daga fuskarsa da ya rufe
yana kallon Umma da idanuwansa da suka rine, Mikewa Abba yyi ya wuce bedroom
dinsa without thinking twice, Mujaheed ya bi sa da kallo, lkci daya ya mike ya
fice daga parlon without anybody noticing him except Mama Hadiza da ta bi sa da
kallo, sai ga Abba ya fito daki rike da takarda da biro, tunda Umma take bata
ta6a sanin akwai abu wai shi relieve ba sai a wannan lkcn da taga abinda ke
hannun Abba, ko da relieve din na ciwo ne tasan bai kai wannan da taji dadi ba
yanxu, Abba ya kalli inda Mujaheed ke xaune kafin ya wuce daki yace "Ina
Mujaheed din??" Da sauri Umma ta juya tana kallon direction din tace
"Gashi nan Alhaji" Xaro ido tayi ganin babu shi a wajen, da karfi
Umma tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.... Ina yake??" sai
kuma ta mike kusan a guje ta fita parlon, Inna ta fashe da kuka tana kallon
inda yake xaune kafin ya fita tace "Toh me yasa ya fita ga takarda da biro
ka dauko me yake nufi da tafiyar da yyi da auren yar mutane a kansa?? To wllh
sai ka bi sa Ahmadu, maxa ku bi sa" Abba dai ya kasa cewa komai har sannan
yana tsaye da takarda da biro a hannu yana kallon bakin kofa da mamakin fitan
da Mujaheed yyi.... Safeenah na xaune compound ana ta hadin salad sai murmushi
take ita kadai tun bayan da taga Imaan ta fito parlor ta wuce apartment dinsu
da sauri kamar warce aka kora, sai dai fuskarta a rufe yake bata ga expression
din fuskar ba, can kuma taga Ammi ma ta fito ta wuce apartment din nasu, ita ma
dai ba wani ganin fuskarta tayi sosai ba don saurin take, sai kuma ga Aunty ma
ta fito babu walwala ta nufi apartment din su Imaan ita ma, lastly sai
Mujaheed, kansa a kasa ya nufi gate, ta mike ta bi bayansa da sauri fuskarta
dauke da damuwa tace "Dear wai me ke faruwa ina ta jin kananun rumors wai
kamar an fasa auren Imaan, what's happening?" Bai tanka ta ba tafiyarsa
kawai yake, da sauri ta dinga binsa tana kallon idonsa da mamaki tace "Did
you cry Mujaheed?" Murmushin da bata ta6a sanin sa da shi ba ya sakar mata
a hankali yace "Not at all, ki je ki ci gaba da aikin ki" sosai taji
dadin murmushin Mujaheed dinta, coz ita dai tun da suka yi aure da kyar idan ta
ta6a ganin ko da murmushin sa, ta mayar masa da murmushin tace "Toh dear,
amma akwai bikin kuwa har yanxu? Naji sai kananun xance fa ake wai kamar Sadeeq
din yace ya fasa??" Still walking yace "Akwai biki, kije ki ci gaba
da abinda kike" bai jira cewarta ba ya fice daga gate din gidan kamar dai
wanda ake jira a waje sbda saurin da yake, ya shige motarsa yyi zoom off ya
nufi main road, Safeenah ta bi motarsa da kallo tana murmushi sannan ta juyo ta
dawo cikin gidan, Umma ta hango tana tahowa kusan a guje, a rikice Umma ke
kallonta tace "Safeenah ya fita gidan nan ne? Kin gansa?" Da mamaki
Safeenah ke kallonta tace "Lafiya? Me ke faruwa? Waye ya fita" Gaban
Umma yyi mugun faduwa ta yi still tana kallon Safeenah xuciyarta na bugawa,
Safeenah tace "Wai me ke faruwa ne?" Cike da karfin hali Umma tace
"A'a dama sako xan basa...." Safeenah tace "Ya wuce a mota ai
yanxu" Umma ta saki wani salati ba tare da ta san tayi hakan ba ta fita
gate din da sauri, Safeenah ta bi ta da kallon mamaki, har titi sai da Umma ta
tafi bbu hijab ko xata ga Mujaheed, amma babu alamar sa, nan ta fashe da
matsanancin kuka cikin tashin hankali tace "Toh ina kuma ya tafi bai tsaya
ya rubuta takardan ba ni Rukayya..." Sai kuma ta juya da sauri ta koma
gida tana goge idonta, wayar Safeenah dake xaune tsakar gidan ta amsa ta xaga
bayan gidan da sauri, Safeenah dai sai bin ta take da kallo, a xuciyarta kuwa
tunani take to me ke faruwa kuma da matar nan ta rude haka ko dai an daura
auren ne bayan full assurance da aka basu baxa ayi ba kuma su ma sun ga alamar
hakan, ita duk ba wannan ba murmushin da Mujaheed yyi mata ne ya tsaya mata a
rai, ta d'an yi murmushi tana tunanin what to cook for him today, Umma na
xagawa tayi dialing number Mujaheed hannunta na rawa, Mujaheed dake driving ya
kasa controlling tears dake sakko masa har lkcn ya kalli wayarsa, ganin
Safeenah ya d'an yi murmushi ya dau wayar ya katse sannan ya kashe phone din
gaba daya ya ajiye, salati umma ta rafka jin waya a kashe da ta sake kira, ta
fashe da kuka tace "Ai ni na shiga uku na banu na lalace, me hakan ke nufi
ko ba shi da caji ne?" Hannunta na rawa ta sake kira amma a kashe, tayi
xaman dirshan a kasa tana shessheka tace "Kila dai ba shi da caji ne, amma
da yasan takarda Abba yaje daukowa a daki da baxai wuce ba sai ya tsaya ya
rubuta masu, nasan bai sani bane" cikin rawar murya take maganar tayi
dialing number Hajiya Saude da har ta haddace lambarta ta kai kunne, Hajiya
Saude na dagawa umma ta sakar mata wani kuka da karfi tace "Saude na shiga
uku, abu bai yi ba, Saude da nasan xa ayi haka da na bar d'an Bulasawa ya auri
tsinanniyar nan, wllh ni yanxu ma sai in taho ki rakani mu koma gun mutumin ya
warware abun yaron ya dawo hankalinsa ya xo su yi auren, Saude da yaron yace masu
ya fasa auren sai wai Ahmad ya sa aka daura da Mujaheed dina, Mujaheed fa
Saude, da d'a na Mujaheed aka daura auren, Mujaheed aka daura ma aure da sauran
ciwo, yar wajen Aisha Saude...." Cikin rikicewa da tashin hankali Hajiya
Saude ta dinga cewa "Mujaheed kuma, Mujaheed fa kika ce, Innalillahi wa
inna ilaihi raji'un, Mujaheed din ki??? La ilaha ilallahu Muhammadur
rasulillahi sallallahu alaihi wassalam, mun shiga uku Rukayya, Mujaheed
kuma" Umma na kuka sosai tace "Wllh shi Saude, ko Safeenah ban yarda na
gaya ma ba ban san ya xata dau wannan labarin da nake ji ya ma fi mutuwata ciwo
ba, wllh da auren nan da Ahmad ya daura da d'an cikina da ma mutuwa nayi hakan
bai faru ba, wayyo Saude xama bai gan ni ba, gani nan fitowa mu koma gun mutumi
a warware komai na hakura duniya da lahira in ma Bualsawan da kansa ke son
auren Imaan wllh tllh na hakura Allah ya basu xaman lafiya da xuri'a dayyaba,
gani nan fitowa Saude ai lkci bai kure mana ba, da sauran lkci" Bata jira
cewar Saude ba ta katse wayar tana kuka kamar ranta xai fita ta daura hannu a
ka, da ta tuna Safeenah sai taji xuciyarta ya tsinke har ranta take jin da ma
da gaske mutuwa tayi da wnn bakar rana da take gani, Wai only son dinta da take
ji da take alfahari da aka daura ma aure da yar makiyiyarta sauran
ciwo...." Hade kai tayi da kasa tana kuka tana cewa "Ya Allah kasa
mafarki nake ba gaske ba, Allah ka warware wannan auren kada in mutu, wayyo
Allah ka dubeni" sai kuma ta mike kamar mahaukaciya ta shiga gidan ta
kitchen, kanta a kasa ta wuce sama ta dau hijab a daki ta saka har da nikab
sannan ta fito ta sake bi ta kitchen ta fice daga gidan ta nufi titi da shegen
sauri tana hadawa da gudu tana cewa "In sha Allahu, xa a warware komai na
hakura in ma uban Sadeeq ne Imaan ta aura ba komai"
_Hajiya Sadiya Chamo wakar biki yyi sweeeet😉 Mujaheed yace ince maki ki turo account number, amma
fa su a duniyar su basu da banks irin na Naija, to ko ya xa ayi wannan abun??
Ya dai ce ince ki turo...._🥰
*I really appreciate the prayers and well wishes yesterday fans
soyayyata gare ku babu mix wllh🙅🏻♀️,
masu Ihisani😍 ina godiya kwarai Allah ya kara budi
da daukaka, Allah ya sa ku gama da duniya lafiya, Allah ya raya kids ya raba ku
da iyayen ku lfya...*
_If you are yet to patronize Imaan... Do so for the love u
are having for the book and the writer for the sake of Allah.... nima sai in ji
dadi_😃🥰
it's just 300 via....
Fcmb 3276052019
Hauwa Bello Jiddah.
Next Update around 9 or so in sha Allah. Tnx.
77.....
Duk yanda Maryam tayi da Imaan ta gaya mata abinda ya faru
ganin yanda take kuka kamar ranta xai fita tun shigowarta kin ce mata komai
Imaan tayi, Maimoon da hankalinta ya tashi ba kadan ba ta cire mayafin da Imaan
ta rufe fuskarta da shi tace "Wai meye haka Imaan, what's happening, talk
to us plsss" Fadawa kan gado imaan tayi ta kara rushewa da wani kukan tana
shessheka, Maryam ta dinga kallonta tana fatan Allah yasa ba tunanin da take
bane ya tabbata wato Sadeeq yace ya fasa auren, lkci daya jikinta yyi sanyi ta
xauna gefen gadon ta ma rasa abinda xata ce tayi tagumi tausayin Imaan ya
cikata, Hawaye Maimoon tafara yi tana dago Imaan tace "Don Allah me ya
faru Imaan ki gaya mana, wani abu ya sami Sadeeq din ne? Ki mana magana don
Allah" Mikewa Maryam tayi ta fita dakin a sanyaye hawaye na sakko mata.
Aunty ce tsaye bedroom din Ammi ta jingina da bango ta rungume hannu tana
kallon Ammi gaba daya ta rasa abun cewa, Ammi dai na xaune gefen gado ta ci
kukanta har ta gode Allah tayi tagumi, cikin sanyin murya Aunty tace "plss
I don't want you to react again Ummi Imaan, kiyi hakuri and keep calm ki ga
next action da xa a dauka, bana son ki sake cewa komai" Ammi ta kalleta
tana girgixa kai tace "I should keep calm fa kika ce Amina?? Why will I??
am sorry to say this duk da Mujaheed ba shi da wani aibu kuma shi din tabbas
namijin aure ne amma aurensa da Imaan will be the last thing I could imagine on
Earth, Amina kin mance wacece uwar Mujaheed? Kin manta wacece Rukayya? Me yasa
su Alhaji xa su yanke hukunci haka babu knowledge dinmu, why will they do such,
me yasa xa a aura ma 'ya ta Mujaheed bayan ba rasa masoya xata yi ba, duka duka
nawa Imaan din take ma gaba daya, me yasa xa su min haka...." Hawaye sosai
Ammi ke yi tana girgixa kai tace "Yau da ba Rukayya ta haifi Mujaheed ba
da xan fi kowa farin ciki da wannan hadin nasu, I will be happy Amina, amma a
wannan circumstance din na fi kowa jin takaici da bakin ciki, I hate the
thought of my daughter been an inlaw to Rukayya, fatana kada 'ya ta ta kwana
yau a gidan nan da auren Mujaheed a kanta, Mujaheed ya fi karfinta, Rukayya
xata iya karasa kashe min 'ya ta ne idan aka bar wannan auren, don Allah Amina
ki min favor din fahimtar da Abba illar wannan auren da ya hada" Ammi na
kuka sosai tace "she is all I've got a duniyar nan, idan na rasata shkkn
that's just the end, ya xan yi Amina? wannan karan wllh baxan yi shiru a cutar
min da Imaan ba, auren nan babu alkhairi babu alamarsa Mujaheed ya sakar min
'ya ta ko kuma in dauketa mu bar gidan nan, ba matarsa bace Imaan" kuka
sosai Ammi ke yi tana jin xuciyarta na mata xafi, Aunty ta kasa cewa komai ita
ma hawayen na sakko mata, Mama Hadiza ce ta shigo dakin ta tsaya tana kallonsu
kafin ta karaso calmly tace "Aisha I never expect ur reaction a parlon
yayana ba, ban taba xaton ko a mafarki xa ki yi abinda kika yi ba, you look
into my brothers face and tell him baxa ki iya barin d'an sa yyi xaman aure da
'yar ki ba, ko da kuwa Rukayya shaidan ce a siffar mutum don nasan saboda ita
kika yi wannan furuncin wllh bai kamata ki yi ma Ya Ahmad haka ba, bai kamata
ba, bai kuma cancanci haka daga gare ki ba, kuma ni kin ban mamaki don ba Ahmad
kadai ba har ni da Ya Sadeeq kika ci ma fuska don Mujaheed d'an mu ne, kuma ko
albarkacin abinda Mujaheed yyi ma Imaan a rayuwa ba gori ba bai cancanci ki
rufe ido a gabansa yana xaune ki nuna baki son hadin nan ba, ita Inna dama bana
ma kawota a lissafi don nasan wacece ita amma kiri kiri ki kunyata d'an uwana
da yake tunanin yana da iko da Imaan kamar yanda Ya Sadeeq ke da iko da
ita" Ita dai Ammi bata ce komai ba hawaye kawai take don gaba daya ba wani
sauraron Mama Hadiza take ba, ta dade bata jita cikin tashin hankalin da take a
lkcn ba, Cikin sanyin murya Aunty tace "Mama Hadiza put ur self in her
shoes, she spoke out of frustration, kiyi hakuri ko wace uwa iyakar abinda tayi
xata yi wllh, bbu wanda bai san Rukayya ba bbu wanda bai san halinta ba, wace
uwa ta gari ce xata so Rukayya a matsayin surkar 'yar ta, think of it mama
Hadiza..." Mama Hadiza tace "Don't tell me that Amina, Imaan ba da
Rukayya xata xauna ba, wllh da Yaya Ahmad yyi breaking min news din nan nayi
farin ciki ba kadan ba, amma me?? lkci daya farin cikin nawa ya koma ciki tuna
uwar Mujaheed da nayi, ni ina da yakinin wllh tllh nan gaba sai kun fi kowa
murnan hadin nan da ya Ahmad yyi yau, barin ma ke Aisha..." Mikewa Ammi
tayi tana goge idonta tace "Kiyi hakuri Mama Hadiza bana tunanin xan
amince da wannan auren na fi ku sanin wacece uwar Mujaheed, na kuma san abinda
xai faru, Kar ki ce na maki rashin kunya but Imaan is all I've got sannan ga
condition dinta, baxan so wani abu ya samar min ita ba, da wanne xata ji?
Kishiya ko Uwar miji, wanda ba sai an fito fili an fada ba kowa yasan kishiyar
nan ba mutunci gareta ba har ke kin shaida, imaan is too young and sick for
this, don Allah kiyi hakuri ki ma yayinnanki magana a warware auren nan they
are not meant for each other, Allah ubangiji ya mata wani xabin mafi
alkhairi" Ammi na magana hawaye na sakko mata ta shige bathroom, Aunty ta
lumshe ido ta bude tana jin tausayin aminyartata da 'yar ta, Mama Hadiza ta fi
minti biyu a tsaye kafin ta juya ta fita dakin. Kawu Bala dake ta girgixa kafa
daga inda yake xaune parlon Abba bayan fitar Inna da kusan minti goma yace
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, where are we to start from
now??" Shi dai Daddy ya jinginar da kansa da kujera tun xamansa parlon har
sannan bai ce uffan ba, Kawu Audu yace "Masalha daya shine a warware auren
nan kawai shine kwanciyar hankalin kowa don Asabe ba kyau... ayi hakuri kawai a
warware auren Allah yasa hakan yafi alkhairi" Abba dai sai kallon Daddy yake
da ya ki cewa komai ya rungume hannu, Abba ya mike yace "Sadeeq tun a lkcn
da na baka sadaki a masallaci ya kamata ka fito fili ka nuna min baka son na
hada auren 'yar ka da d'a na, bai kamata ka min shiru a lkcn ba, da ka fito da
abinda ke ranka da duk abubuwan dake faruwa yanxu bai faru ba, but anyway yanda
na hada auren nan haka xan rabasa ba da jimawa ba in sha Allah, ka tashi ka
tafi ka ba uwarka hakuri, kai ma kuma ina baku hakuri da matarka, in dai a kan
na aura ma Imaan son dina ne xa a raba auren yanxu sai kowa ya saki
ransa...." Kallonsa kawai Daddy yake ya kasa cewa komai, Kawu Bala yace
"A'a bai kai haka ba Ahmad.... Don't misunderstand him plss" ko
saurarensa Abba bai yi ba ya nufi kofa ya fice yana dialing number Mujaheed, Daddy
ya bi sa da kallo, Kawu Bala yace "Haba sadeeq idan ma baka yi na'am da
auren nan ba bai kamata ka fito fili ka nuna ba, Ahmad yyi iya kokarinsa ne na
ganin ka fita kunyan jama'ah da aka tara, ko shawara bai yi da d'an sa ba yana
ganin ya isa da shi ya yanke hukunci amma kuma a samu matsala daga bangaren
ka" Daddy ya sauke ajiyar xuciya kamar baxai ce komai ba sai kuma ya
girgixa kai yace "Noo, not at all...." kawu Audu yace "Banda
abin ka xumunci bai kara karfi ba hakan da aka yi?? jini daya wasa ne Sadeeq?
ita Asabe fa dama ba a saiti take ba wani lkcn sai dai Allah ya gyara mana ita,
don me xaka dau maganganunta ka kunyata D'an uwan ka, shi Mujaheed da aka ma
aure without his consent dubi fa yanda ya nuna kamar ba komai amma sai ku
Sadeeq, to Allah na tuba ina laifin wannan hadin banda rikicin Asabe da yawa
yake?? Ku kan ku xa ku yi farin ciki da auren nan nan gaba, Mujaheed bayan
hankali da natsuwa da sanin ya kamata ga ilimin muhammadiyya ga boko, uwa ba ya
rike ibada ba da wasa ba, ai ya xo wajena na gani, haba wnn ai abun kunya ne
kuke sai kace ba jini ba, kuma duk Asabe ce daburtattciya, kai Asabe dai ba
kyau" Daddy ya girgixa kai a hankali yace "Ko kadan ni ban ga aibun
hadin nan ba, Mujaheed d'a na ne, na kuma san waye shi, na kuma san tarbiyarsa,
infact tarbiyata ne Mujaheed, but 6acin ran fa?? You all can see the reaction
displayed by his mum ga kuma maganganun da Inna ke yi tana cewa ta bar mu da
Allah, for what?? Ni tun a masallaci nasan xa ayi haka, Yusuf da ya fito ya
nuna yana so ma ga abinda ta mana balle wannan?" Mikewa yyi yace "Am
coming" daga haka ya fita ya bi bayan yayan nasa. Ta Rasulu ta rike haba
ta hangame baki tana kallon Inna da ta gama tsara mata sa6on da su Ahmadu da
Bukar suka yi tana sharban kuka sosai, tsofaffin parlon suka dinga salati ana
nanatawa ana tafe hannu, cikin rawar murya Inna tace "Allah ya isa
tsakanina da Sadeeq da ya yaudari jikata ya kuma ja mana rudani a gida har ya
kai ga Ahmadu da Bukar da su d'an tsut suka tafka babban sa6o suka aura ma
Imaan Mujaheed wai a fita kunya, basu san kunyar aka shiga ba tsumu_tsumu, da
wani idon xa mu kalli jama'ah" Ta Rasulu tace "Ikon mai mana ruwan
sama, to yanxu kice duk uban kayan da muka tafi muka mata jere a rusheshen
gidan Bukari komawa xa mu yi mu kwaso a kai gidan Mujaheed kenan?" Gwalo
ido Inna tayi tana kallonta, sai kuma ta fashe da kukan takaici tace "Ke
dai Allah kadai yasan yanda xai yi dake, kuma gaskiya na yafe kawancen nan
namu, waye kuma Mujaheed, me Imaan xata yi da shi fisabilillahi ta Rasulu? Anya
kinsan Allah kuwa" Ta Rasulu tace "Al-quran baki son gaskiya Asabe,
yau ko Bala ne ya haifi Mujaheed baxa ki tambaye ni wanene shi ba balle Ahmadu
ne ya haifesa, to ita Imaan din wacece da Mujaheed baxai aureta ba Allah na
tuba, wllh ban taba ganin shegen gantalallen xumunci irin naku ba, 'ya 'ya uwa
daya uba daya ki dinga nuna bambanci haka, daga an rufa ma yarinya asiri kada
aji kunya an lika ma Mujaheed sai ya xama laifi??" Inna tace "Gaskiya
Allah ya isa sanin ki da nayi a duniya Ta rasulu, Allah kuma ya saka min...."
Ta Rasulu ta mike tace "Oho dai gaskiya ce sai na fada, Bulasawan da ya so
kunyata ku ma ba don...." Inna ta katse ta da sauri tace "Waye kuma
Bulasawa Ta rasulu? Tsinannu xa ki ce manyan barayin duniya, uban waye bai san
sata suke yi ba? Waye bai san abinda Bulasawa yyi a Nigeria ba, an fa sha
kamasa dumu dumu yana sata wllh, ni dai Allah ya dubi jikata ya rufa mata asiri
da aka fasa auren, da ina xan shiga idan aka aura mata d'an gagarumin barawo,
mu ma duk kallon barayin xa a dinga mana kawai, in sha Allahu sai naje na ci
uban yaron a gidan satan su da suka gina, bari dai komai ya lafa a sakar min
jika wllh wllh sai na je" Ta Rasulu tace "Dama idan xa ki tafi sai ki
rike kudin satan da ya dinga baki kina boyewa ki mayar masu da abun su"
Inna ta saki salati tayi tagumi tace "Duka duka nawa ya ban, sau uku fa
kadai ya ban dubu uku sai shegen iron dinsa gashi can ko budewa ban yi ba, ance
maki ni gantalalliya ce mara tsoron Allah??" Shigowar Ammi yasa Inna tayi
shiru, Ammi ta xauna parlon kanta a kasa, Inna ta share guntun hawayen idonta
tana kallonta, cikin sanyin murya Ammi tace "Inna xan tafi gidanmu tare da
Imaan...." Inna ta katse ta da sauri tace "Akan me??" Ammi tace
"Idan aka raba auren in sha Allah xamu dawo, amma yanxu...." Inna ta
katse ta mike tace "Yau naga fitinanniyar bafillatana, don an aura ma
Imaan Mujaheed sai kice xaki tafi gida da Imaan, meye da Mujaheed din kamar
warce aka aura ma barawo, jikana ne fa shi ma?? Ni fa na haifi Ubansa na haifi
Uban Imaan.... yau naga ikon Allah, to wllh kiyi ta tafiyar ki amma bbu inda
xaki da jikata don an aura mata d'an uwanta, wahalan da yyi da ita ko ke kinyi
idan ba rashin tsoron Allah ba??"
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
78......
Mikewa Inna tayi ta shige daki tana cewa "Ni dai ba
ruwana, kiyi tafiyar ki ke kadai amma bbu inda imaan xata je, kawai Allah ya
rufa mana asiri mu kuma mu ki rufa ma kanmu?? kaji min mata dai" Ta Rasulu
na kallon Ammi tace "Haba Shatu, ke ma fa Mujaheed din nan d'an ki ne, ko
yana da wani mugun hali ne wanda ke kika sani ba mu sani ba??" Inna ta
leko daga daki tace "Ina fa ta Rasulu kawai samun waje irin na
bafillatani, mai mugun hali ai a bayyan 'yar ta imaan yake, ni wllh sai ince ma
cutar Mujaheed aka yi da aka hada sa da Imaan bayan ga matarsa Safara'u, Imaan
fa ko girki bana jin ta iya, banda Mujaheed din wanene xai iya da ita, kuma
daga an rufa ma juna asiri sai ki nemi ki tona mana, ni dai ba ruwana kiyi ta
kanki Aisha, ko kinfi Ahmadu da Bukar sanin abinda suke ne, kawai mata kina
nema ki lalata mana xumuncin mu sbda rashin tsoron Allah" Mikewa Ammi tayi
ta fice daga parlon, Inna ta rike ha6a tace "Yau naga bafillatana
dai..." Ta Rasulu ta tabe baki tace "Ni dai ban taba ganin irin
wannan xumunci ba tunda uwata mai salati ta haifeni, gida duk ya rikice daga
hada aure na xumunci" Inna tace "Wllh idan xuciya ta debeni sai in
iya ce ma Mujaheed ya ki sakinta mu ga ta tsiya, idan an bi komai a hankali
kuma Allah ya dora mu kansa ai sai ya saketa tunda a gaskiya Imaan ta fi karfin
sa sai irin su Bulasawan dama, amma mata kya xo kice min xa ki tafi da
Imaan...." Ammi na komawa part dinsu ta shiga dakinta ta sa Hijab ta dau purse
ta fito ta bude dakin Imaan, Mama Hadiza ce xaune dakin ta rungume Imaan dake
kuka kamar ranta xai fita cikin tashin hankali take cewa "Yayana ne shi fa
Mama, ya xa ayi ace wai an daura mana aure da yaya, wayyo na shiga uku mama
dama Yaya na auren kanwarsa?? don Allah ki gaya ma su Abba Yaya na ne, wllh ni
dai yayana ne...." Mama Hadiza ta kasa ce mata komai, jin har jikinta ya
dau xafi sosai ta dago kanta tana kallonta fuska daure tace "Wato ban isa
ince kiyi shiru kiyi ba koh?" Maryam dai na xaune dakin tayi tagumi,
Maimoon sai hawaye take duk jikinta a sanyaye tana kallon Imaan da duk ta fice
hayyacinta, Mama Hadiza ta sake Imaan ganin Ammi ta mike ta fita daga dakin,
Ammi ta karasa cikin dakin tana kallon 'yar tata tace "Dauko Hijab din ki"
tashi Imaan tayi ta dau hijab dinta tana shessheka tace "Ammi plsss kice
ma Daddy su yi hakuri wllh yayana ne shi, ba aure tsakanin mu, don Allah kar su
ce sun daura mana aure" Fixgo hannunta Ammi tayi suka fita daga dakin
trying hard to control her tears, Imaan ta dinga bin ta tana kuka sosai har
suka fito compound dake cike da jama'ah sai dai fa duk an hada groups ana
kananun surutai tunda har sannan ba a fito ance ga abinda ke faruwa ba a gidan,
sun dai ga families din na ta kai komo bbu annuri, mutane dai dai ne yanxu basu
san an fasa auren Imaan da d'an gidan Bulasawa ba, sai dai duk bbu wanda yasan
an daura auren da Mujaheed, Safeenah ce tsaye rike da plate din abinci ta cika
uban nama tana kallon Mama Hansai dake ma wasu yan uwanta da wasu mutane dake
xaune sun hada group bayanin abinda ke faruwa fa a gidan, duk aka saki baki ana
kallonta, tana girgixa kai tace "Toh Yaya Ahmadu na ganin haka sai kawai
ya daura auren da d'an sa tunda an riga an tara jama'ah kada a ji kunya, shine
fa hankalin kowa ke tashe a gidan, kusan dai bbu wanda yyi na'am da auren nan
da aka hada...." Hajiya Bari'a kawar Aunty dake wajen ita ma a xaune ta ce
"Wani d'an nasa a ciki, shi angon ko kuwa??" Mama Hansai ta tabe baki
tace "Kila da da angon ma aka auran da duk matsalolin dake faruwa yanxu
bai faru ba, da d'an ita Hajiya Rukayya aka daura auren, wato dai
Mujaheed....." Safeenah dake tsaye tana ta saurarenta ta sake plate din
hannunta a hankali, lkci daya ta fixgo Mama Hansai tana gwalo kwala kwalan
idonta tace "Wani Mujaheed din????" Mama Hansai ta juya da sauri tana
kallonta don bata ma san ita ce matar Mujaheed ba, Cikin yanayi na tashin hnkli
da rikicewa Safeenah ta dinga jijjigata tana cewa "Wani Mujaheed din kike
nufi, ki gaya min wani Mujaheed? mijina aka daura ma aure da Imaan din???"
Mama Hansai dai sai xaro ido take ta kasa cewa komai, Safeenah ta saketa a
hankali tana tariyo reaction din Umma daxu da irin gigicewan dake tare da ita
har da fita waje babu hijab, da kuma Mujaheed da ya fito parlon mahaifinsa
hawaye a idonsa, wani karan da ya tsorata mutanen compound din Safeenah ta saki
da karfi, dai dai fitowar Ammi da Imaan, Safeenah na hada ido da Imaan dake
kuka Ammi na rike da hannunta ta sulale wajen sumammiya, duk aka yo kanta ana
salati masu debo ruwa na debowa, masu fiffita nayi, Ammi dai tuni ta ja Imaan
suka fice compound din gaba daya.... Gidan Gwaggwo Ammi ta wuce tare da Imaan,
parlor suka tadda gwaggwo suna jimami da yan uwanta biyu a parlon, Ammi ta
gaisheta da mutanen parlon ta wuce ciki Imaan ta na biye da ita kanta a kasa,
Gwaggwo ta bi su da kallo can ta mike ta bi bayansu, gefen gado ta tadda Ammi a
xaune tayi tagumi, Imaan kuma ta kwanta kan gadon tana kuka a hankali, Gwaggwo
ta xauna kan carpet dake shimfide dakin tace "Toh me kuma ku ka xo yi nan
Aisha ko baku yarda da kaddara bane? Komai bawa ya ga a rayuwa fa rubutattce ne
daga Allah, dama can Allah ya rubuta Sadeeq ba mijin Fatima bane, abun da ciwo
amma hakuri kawai duk xa mu yi, daxun nan Muhsin ya bar gidan nan shi ma duk
abun ya damesa gashi ko sanin inda Sadeeq din yake bai yi ba wayoyinsa ma duk a
kashe wai, ni ban taba xaton haka daga Sadeeq ba, ko me ya samesa haka Allah ma
fi sani, amma gaskiya wannan ba lafiya ba ranan daurin aure ka xo kace ka fasa
ba laifin tsaye balle na xaune, ban taba ganin haka a xuri'ar mu ba... Na kuma
samu labarin hadin da yayan mijin ki yayi Allah ubangiji ya sa hakan shine mafi
alkhairi, ai matar mutum kabarinsa...." Ammi ta katse ta tace
"Alkhairi fa kika ce Gwaggwo, wllh auren nan ba alkhairi babu alamarsa, in
dai basu sakar min 'ya ta ba barin garin nan xan yi da ita, Allah baxai taba sa
'ya ta ta hada jini da irin Rukayya ba, bana fatan haka kuma in sha Allahu
hakan baxai ta6a faruwa ba...." Gwaggwo ta bude baki tana kallon Ammi da
mamaki, can tace "To ai baki da iko da 'yar su Aisha, ke har xa ki bude
baki kiyi wannan mummunan furucin kin mance halaccin uban yaron nan, gaskiya
ban san ki da mance alkhairi da rike sharri ba, Ina ce saboda ke Ahmadu har
sakin Rukayya sai da yyi wanda sai da tafi shekara uku bata gidan, ko don
ubansa ke kya bude baki kiyi wannan furucin Ammi, meye aibun Mujaheed yaro mai
hankali da nutsuwa to wllh ni ko ranan laraba sai da ya shigo gidan nan
gaisheni, da kyar ayi wata daya ko sau daya bai shigo min ba, kaji min Aisha
dai, 6ata masu xumunci kike son yi ko me? Ke dai ba kawai kiyi ma yar ki addu'a
da fatan alkhairi da xaman lafiya gidan mijinta ba tunda ga yanda abubuwa suka
kasance, da Rukayya Fatima xata xauna ko Mujaheed? Haba Aisha sai kace ba
matsayin uwa kike gare Mujaheed ba, gaskiya banji dadin rashin hankalin nan
naki ba, daga ubansa yyi kokarin fidda ke da mijin ki kunya sai ki rufe ido ki
nuna masu ke baki da hankali baki da kirki??" Ammi ta girgixa kai tana
murmushin takaici tace "Dama ba lallai kowa ya gane abinda nake nufi ba ba
kuma lallai kowa ya ga abinda nake hangowa ba, Rukayya ta wuce tunanin ku
gwaggwo, wllh Rukayya...." Katse ta gwaggwo tayi ta mike tace "Toh
sai ki mayar masu da 'yar su ki dawo mu xauna ba shikenan ba, ai bamu da iko da
ita, maida ta ki kwaso kayan ki mu xauna nan tunda ke shashahsa ce..."
Daga haka ta fice daga dakin. Duk kiran da Abba ya dinga yi ma Mujaheed layinsa
gaba daya a kashe suke, daga karshe gidan nasa kawai Abba ya wuce nan mai gadi
ya sanar masa bbu kowa a gidan, yayi reverse kenan xai bar layin kiran Daddy ya
shigo wayarsa, da kamar baxai daga ba sai kuma ya daga, Daddy yace "Kana
Ina Barrister?" Abba yace "Ina hanya" Daddy ya fada masa eatry
da yake son su hadu a lkcn don bbu inda xa su xauna su ke6e su yi magana, Abba
yace "Alright" kusan a tare suka isa eatry din, Daddy ya sa waitress
ta kawo masu just table water, Abba ya bude ruwan ya sha kusan rabi sannan ya
ajiye sauran, Daddy na kallonsa yace "First of all I will like to say I am
sorry Barrister, duk da dai you misunderstood me amma ina mai baka hakuri
still, ko kadan Barrister Auren Imaan da Mujaheed da ka hada ba wai ban yi
farin ciki da hadin naka bane, abun farin ciki ne sosai don ko bbu komai mun
kara karfafa xumuncin mu, babban damuwata a auren nan shine mahaifiyar mu...
nasan baxata ta6a na'am da hadin ba, Dole xata yi maganganu da bai kamata ba a
kan mu, sannan Barrister bamu san ko shi Mujaheed din xai yi na'am da auren ba,
we don't know ko yana da ra'ayin mata biyu, infact duka duka yaushe yyi auren
ba, beside bai ta6a fitowa ya nuna yana son Imaan ba banda so na 'yan uwantaka
unlike Yusuf da ya nuna interest a kanta da farko, Barrister what if mun shiga
hakkinsa shi Mujaheed din?? Wani irin xama kake ga xa su yi baya sonta ita ma
kuma haka?" Murmushi Abba yyi yace "Ae shi yasa nake ta neman sa ta
waya domin ya xo ya datse auren amma ban samesa ba, yanxu haka daga gidansa
nake baya nan, but in sha Allahu kar ka damu xa a raba auren" Daddy yace
"It's not a matter of a saketa or not barrister, in har shi yayi na'am da
auren shikenan, sai kuma mu san yanda xa mu yi da Inna, Imaan kuma I am hoping
she learn to live with him as husband in
sha Allah, Rukayya da Aisha kuma I don't think xa su iya saka xumuncin mu ya sa
mu tangarda, in har Mujaheed yayi na'am da auren kuma Inna ta hakura shkkn
Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gare su gaba daya, I think you don't need
to add anything to what I just said now barrister mu bar xancen haka...."
Daga haka Daddy ya kira waitress don ta kawo masu abinci coz it's almost Asr.
Tun da Safeenah ta farfado take bin duk mutanen dake xagaye kanta da kallo
kamar me son tuna abinda ya faru, lkci daya ta mike a xubure kamar warce aka
tsikara ta fasa wani ihu tace "Shi mijin nawa aka aura ma Imaan,
innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku Hajiya Rukayya ta kai ni ta
baro ta cuce ni, ta cuce ni, ta cuce ni, mijina ne ya auri Imaan daga karshe,
wayyo na shiga uku...." Da gudu Inna ta karaso wajen ta Rasulu na biye da
ita ta dalilin labari da aka je aka basu a bangaren ta wai Safeenah ta suma a
tsakar gida, Inna na kallon Safeenah tace "Mu ma duk haka muka ji da aka
mana kishiya Safara'u, sai dai duk na ki ya fi ciwo ke da kika tika rawa a
bikin kishiya jiya, yau kuma tun safe kike ta yanke yanken kabeji da
salak......" Safeenah ta fashe da matsanancin kuka tana jijjiga kanta kmr
tababbiya tace "Wllh wllh baxan xauna da kishiya ba kishiyar ma Imaan, don
ni kadai aka yi Mujaheed a duniya, don ni kadai aka yi sa, sai na nuna ma
Rukayya ba ni ta yaudara ba, baxan fallasa ta ba yanxu sai ta fara sanin su
waye family dinmu, sai ta san an aura ma Mujaheed Imaan ne saboda mugun halinta
da bakin halinta wllh idan ban nakada ma Rukayya duka ba ban Haifu cikin
Mansura ba....." Gate Safeenah ta nufa da gudu kamar mahaukaciya tana rusa
kuka tana kiran mummyn ta, Inna ta bi ta da kallo da sauran mutanen wajen da
suka bude baki da shock, Inna tayi wani dariya irin ta boss tace "Toh wllh
babu tsinannen da ya isa ya raba auren nan da raina, auren nan mutu ka raba
takalmin kaza, maxa a tafi a kwaso kayan da aka kai gidan barayi a fito da
kayan Safara'u a feshe dakin a xuba na jikata, dama idan ba shi Mujaheed din ba
waye ya dace da Imaan banda toshewar basirar mutane? Dama can hange hangen
Imaan da kwadayin abun duniya yasa ta hango xuri'ar shegu barayi suka kuma yaudareta
suka gudu, ni fa tun ba yau ba nake tunanin hada auren jikokin nan nawa biyu
kawai dai Allah bai bani basiran yin magana bane amma yanxu kam faduwa ta xo
daidai da xama bbu shegen da ya isa ya raba auren nan, ko shi Mujaheed din yyi
yunkurin sakin Imaan ni sai in iya tsine masa ya bi duniya" tana gama
fadin haka ta nufi part dinta tana cewa "Ku kira min Ahmadu da Bukar na
canxa shawara gaskiya, wnn ai abun arxiki suka hada...." Sai kusan Magrib
Umma ta dawo gida duk tayi xuru xuru tun safe banda ruwan shayi babu abinda ta
xuba a cikinta, xuwa lkcn duk an watse a gidan sai yan uwa na jiki da suka
rage, tana shiga dakinta ta dau wayarta don kiran Mujaheed taga missed calls
din Hajiyan Marafa yyi goma sosai gabanta yyi mugun faduwa ta dinga kallon
wayar, ta xauna gefen gado, Ummi ta biyota daki tace "Umma Hajiya Baturiya
yayar Aunty Safeenah fa ta xo har sau uku daxu..." Umma ta hadiye abu da
ya makale makogwaronta da kyar ta hade rai tace "Toh sai aka yi Yaya?
Neman me suke min?" Ummi tace "Nima ban sani ba" Umma tace
"Toh fita waya xan yi" Ummi na fita dakin Umma tayi dialing number
Mujaheed ta ji sa a kashe, mikewa tayi hankali tashe tace "Me Mujaheed ke
nufi da kashe wayarsa ne??" Hijab ta kuma sakawa ta fita gidan don xuwa
gidan Mujaheed ta iskesa. Tsaye ta ga Inna tsakar gida kusa da apartment din su
Ammi inda take shiga ba nan take fita ba, Aunty da Mama Hadiza sai Mama Hansai
da few relatives na tsaye dai suna kallonta, rai bace ta ci gaba da cewa
"Wllh idan bata yi hankali ba sai ince kar ta sake dawowa gidan nan ta sha
xamanta gidansu, kuma a kai ni yanxun nan in dauko jikata ai ba uban wani yyi
mata ciki ta haifeta ba, ta dauwama a gidansu kar ta sake dawowa gidan d'a na,
mata kawai sai bakar xuciya, Bukar dai ya auri jaraba don Aisha jaraba ce wllh,
shi jikan nawa take nuna ma k'i haka ba kunya ba tsoron Allah bata jin kunyata
ba balle na ubansa sannan Bukar, shi Mujaheed din ne bata so sbda rashin tsoron
Allah kamar wani barawo?? to kuwa har Bukar bata so tunda bata son d'an d'an
uwansa, kawai ni dai Allah ya hada 'ya yana da fitinannun mata a duniya... Maxa
a kai ni gidansu in dauko jikata yanxun nan" tana fadin haka ta tafi dauko
Hijab, Daddy da Abba da shigowarsu gidan kenan su ma suka tsaya from afar suna
kallon mahaifiyar tasu.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
79.....
Sai kusan karfe goma da rabi Umma ta dawo gida daga gidan
Mujaheed duk tayi wani wujiga wujiga da ita, tun magarib da ta fita ta je gidan
nasa take ta xaune cikin compound wai ko xai dawo amma shiru har karfe goma da
wani abu bbu shi bbu alamarsa hakan yasa ta baro gidan hankali tashe tana
hawaye ga Hajiyan Marafa sai kiranta take a waya ba kakkautawa, daga karshe ma
kashe wayar tayi gaba daya, direct part din Inna ta nufa tana share xufar
fuskarta, kowa ya ganta yasan tana cikin tashin hankali ne ba na wasa ba, xaune
ta samesu da Mama Hadiza, Mama Hansai da Ta Rasulu, sai Aunty, Umma ta rakube
jikin kujera tana kokarin boye hawayen idonta kar su gani, ta gaishe su gaba
daya, duk suka amsa banda Inna dake cin abinci, Umma tayi kasa da murya kamar
ta kirki tace "Inna daga gidan Mujaheed nake yanxu, tun magariba nake
gidan amma shiru shiru bai dawo ba ban san dalili ba, tsorona kada wannan hadin
ya ja mana matsala mai karfi a xumuncin mu tunda Aisha kirikiri ta fito ta nuna
bata so, ita ma Imaan din da kanta ba so take ba, shi kansa Mujaheed nasan
tashin hankali ne yasa ya shiga duniya, kuma daxu naji ke da kanki kince sai an
raba auren, to Mujaheed fa har ynxu bbu labarinsa wllh yanxu haka ma daga
gidansa nake Inna...." cikin rawar murya ta kare maganar tana kallon Inna,
Inna ta tura abincin gabanta ta kalli Ta Rasulu tace "Kin ji bala'i koh?
Rukayya ni xa ki ma sharri kice nace a raba aure da raina a duniya ba wai na
mutu ba, ni dai nasan daxu a parlon Ahmadu nace ba ayi shawara da ni ba na kuma
nuna bacin rai na sosai, amma bayan wannan ban san komai ba, ban kuma ce komai
ba, yo dama ai Mujaheed shine dai dai Imaan ganewa ne ba ayi ba da wuri, shi fa
Sadeeq din nan dama ubansa ne mai kudin ba shi ba, kuma da kyar ma idan
Mujaheed bai fi sa kudi ba, kudin uban yaron ke rarumowa ya xo nan yana mana
burga yana yaudaran jikata wllh, lkci daya kuma Allah ya toni asirinsa, ai
wannan auren da kike gani Rukayya mai raba sa kilan mutuwa kawai xai yi a banxa
a hofi, kawai ni dai abinda na sani shine dolen Mujaheed ya hada akwatuna irin
wanda su Bulasawa suka kawo mana da gwalagwalai idan ko ba haka ba wllh sai in
ce a raba auren baki na a leko don jikata ba gantalalliya bace, sannan da kyar
idan baxae karo Sadaki ba, ke dai da Aysha da wuya ku ga annabi wllh, ban ta6a
ganin mutane irin ku ba a duniya, ita ta tashi ta gudu da yarinya kamar
mahaukaciya ba don su Ahmadu da suka dakatar da ni ba wllh da naje da dauko
jikata da daddaren nan" Umma da hankalinta ya kai kololuwa gun tashi ganin
Inna ta juya xance gaba daya on like da safe da ta dage sai anyi saki ko tayi
ma su Abba Allah ya isa, tasan kuma ai shkkn aikin gama ya gama tunda Inna ta
canxa labari don dama wajenta kadai take da hope, ynxu kuma bbu hope din,
mikewa tayi ta fice daga parlon da sauri, bata yi nisa tana tafiya ba ta xauna
nan kasa kan hanya ta rushe da kuka sosai tace "Na shiga uku na lalace na
cuci kai na, yanxu d'a na aka makala ma sauran ciwo ina ji ina gani?? Wllh sai
na raba auren nan ko ta halin yaya, Mujaheed baxai taba hada jini da xuri'ar
Aisha ba, da auren nan ya rayu gwara in mutu kawai, in sha Allahu sai ya saketa
sai dai idan ba ni na haife sa ba, wato yana ma son auren kenan tunda har ya
gudu ba labarinsa....." ta kuma fashewa da matsanancin kuka xuciyarta na
mata xafi, ko mutuwar ubanta bata ji ciwonsa irin yanda take jin ciwon wannan
auren ba, ji tayi dama ayi backward din komai ta bar Sadeeq ya auri Imaan, ko
bakomai xata yi mingling da manyan mutane da dangin Bulasawa ayi hotuna su kai
Imaan kantamemen gidanta, yanxu Imaan ta auri Sadeeq ba ma lallai taga irin
rayuwar da suke da Sadeeq din ba balle ta ji haushi ko ya dameta, ita da ganin
Imaan sai in ta xo gida, amma wnn wai yaron cikinta ne xai yi rayuwa da Imaan
din tana ji tana ganin komai da idanuwanta, tashi tayi tana kuka sosai ta wuce
apartment dinsu tana cewa "In sha Allahu sai ya saketa, sai in bani nayi
nakudar sa ba, in sha Allahu bbu aure tsakaninsu, d'a na ya fi karfin sauran
ciwo, ta ina xai fara rayuwar aure da ita ta talauta min shi da ciwonta"
ranan dai Umma yanda taga rana a gantale haka ta ga dare, babban damuwarta da
tashin hankalinta me xai faru idan gari ya waye, tasan da kyar idan Hajiyan
Marafa baxa su taho gidan tare da duk yaranta su risketa ba, tasan Safeenah ta
gama sanar masu duk abinda ya faru da yanda ta dinga kokarin hana auren Imaan
da Sadeeq, Umma ta mike xaune ta rike kanta tana kiran Allah ya kawo mata dauki
xuciyarta, ni kam nace lallai ma. A bangaren Ammi kuwa sllh ta dinga yi daren
ranan don ita ma neman baccin tayi ta rasa rabonta da shiga tashin hankali haka
har ta manta, da dadewa ta sha addu'ar kada Allah ya kaddaro masu rana irin ta
yau tun daga lkcn da ta lura shakuwan Mujaheed da Imaan ya fara wuce hankali ya
dauka, shi yasa ma ta dinga taka ma Imaan burki sai gashi lkci daya bbu notice
abinda take gudu ya faru, da yau Yusuf aka hada da Imaan me xai dameta, sai ma
ta fi kowa farin ciki da hadin amma Mujaheed kam ya fi karfin 'yar ta. Imaan na
cikin duvet ita din ma ba bacci take ba sai juye juye kawai take, xuwa lkcn
kukan ma ta kasa wani mugun xaxxabi take ji sosai, duk joints dinta ciwo suke
mata ga headache da backache, tasowa Ammi tayi ta nufo ta bayan ta idar ganin
juye juyen da take, ta cire duvet din jikinta tana kallonta kafin tace komai
taji xafin da jikinta yyi ba kadan ba, Imaan ta mike xaune da kyar ta jigina da
gado a hankali tace "Ammi bana jin dadi" Ammi tayi shiru tana
kallonta, can ta mike ta wuce kitchen ta hado mata shayi sanin da daddare bata
ci abincin kirki ba ta kwanta, ta dawo ta mika mata shayin tace "Ki sha in
samo maki paracetamol yanxu" Imaan ta karbi cup din hannunta na rawa, Ammi
ta fita xuwa dakin gwaggwo, sllh ta sameta take yi ita ma, ta bude gun da take
ajiye magungunanta ta dau pain reliever da man xafi da ta gani ta fita, duk
yanda Ammi tayi da Imaan ta sha shayin kin sha tayi wai amai take ji, hakan
yasa ta bata paracetamol din ta shafa mata magani duk jikinta ta sa ta kwanta
sannan ta lullube ta. Da safe Abba bai hakura da kiran layin Mujaheed dake
kashe har sannan ba, lkci daya jikinsa yyi sanyi a nan kuma ya fara considering
d'an nasa, to ko shi ma baya son auren ne, yasan dai ko Mujaheed baya so xurfin
cikinsa ma baxae bari ya fada ba, shigowar Umma ya sa ya ajiye wayar hannunsa,
Umma ta duka kan kneel dinta tana kallon Abba dake kallonta shi ma, Cikin rawar
murya tace "Alhaji na xo neman alfarma ne a gun ka ba wai don na isa ba
don ni din a ko da yaushe mai laifi ce na sani amma don Allah kar ka biye ta
halina kayi ma girman Allah ka saurareni kuma ka min alfarmar da na xo
nema" Abba na kallonta yace "Ina jin ki" tayi kasa da kai a
sanyaye tace "Alhaji wannan auren da ku ka hada kayi ma girman Allah ka
raba sa, na farko Aisha ba son auren take ba, ita Imaan din ma haka, shi kuma
Mujaheed sbda tashin hankali kaga ba shi ba labarinsa, ban san inda ya shiga
ba, don Allah ka yi min rai kayi abinda ya kamata a wannan batu..." Abba
yace "i don't have any say on this matter any longer Rukayya, Sai abinda
Inna ta ce, yanda tace haka xa ayi...." Umma ta fashe da kuka tana
kallonsa tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wllh Alhaji Mujaheed
dina baya son auren nan, tun jiya fa har yau wayarsa a kashe bamu san inda yake
ba" Abba ya mike yace "Yana lafiya in sha Allah" mikewa Umma
tayi tana shessheka ta fita tana tunanin meye mafita, don ita da Mujaheed yayi
aure da Imaan fa gwara ko da bata mutu ba ta yarda ta rasa komai nata a duniya.
Karfe tara Abba da Daddy suka isa gidan gwaggwo, Gwaggwo ta fito daki bayan mai
aikinta ta kirata, da fara'a ta amsa gaisuwar su tana masu sannu da xuwa,
Gwaggwo ta xauna saman kujera tace "Ya aka ji da taro da hidindimu??"
duk suka amsa da Alhmdllh an gode Allah, Gwaggwo tace "Toh madallah Allah
maku albarka, Allah kuma yasa abinda ya faru shine mafi alkawari gare mu gaba
daya" Abba yace "Ameen, dama xuwa muka yi mu baki hakuri a bisa
wannan hukunci da muka yanke baki da masaniya, abubuwan ne suka xo a haka
gwaggwo, ayi mana afuwa...." Gwaggwo tace "A'a ba komai wllh Ahmad,
ai duk an xama daya, wannan aure kuma da ku ka hada Allah yasa shine mafi
alkhairi, Allah maku albarka, su kuma Allah ya basu xaman lafiya, kada ku biye
shiriritan matan ku, abinda ya dace shi ku ka yi, anjima in sha Allahu ni da
kai na xan maida Fatimar gida, idan Allah ya yarda" Abba yace "Toh
Alhmdllh Allah ya kara girma gwaggwo, ita Hajiya Aishar fa??" Gwaggwo tace
"Ta d'an fita siyo mata magunguna da yake jiya da xaxxabi ta kwana amma da
sauki sosai yanxu, bacci ma take" Abba yace "Toh Allah ya sauwake, xa
mu koma Gwaggwo, mun gode kwarai, Hajiyar ma tace a gaishe ki" Gwaggwo
tace "Toh Ina amsawa, Allah ya maku albarka" duk suka amsa da Ameen
suka mike, Daddy ma yyi mata sallama suka fita parlon, a bakin gate suka hadu
da Ammi ta dawo pharmacy, kallo daya tayi masu ta dauke kai ta gaida Abba, Abba
ya amsa yace "Ya mai jikin ta kara ji Aisha" Ammi tace "Alhmdllh
da sauki" shi dai Daddy kallonta kawai yake, Abba yace "Toh Allah ya
bata lafiya" Ameen ta mayar masa ta shige gate din gidan, murmushi Abba
yyi ya bude front seat, daddy ya xaga ya shiga maxaunin driver suka bar
anguwar, Abba yace "In sha Allahu xa su sakko gaba daya, kuma xa su fi
kowa farin ciki da wannan aure nan gaba" Daddy bai ce komai ba har suka
hau saman titi, sai kuma yace "How do we reach Muhd, I am disturb about
him barrister" Abba dai bai ce komai ba don shi ma bai san inda xai samo
Mujaheed ba balle su ji ta bakinsa a kan auren. Mota biyu Hajiyan Marafa suka
yo da yaranta mata su uku, da yan uwanta biyu da kawayenta biyu sai Safeenah da
har wani rama tayi sai yan idanuwa da suka kumbura suntum dan kuka, da ta tuna
wai mijinta Mujaheed aka hada da Imaan sai ta fasa wani ihu kamar mahaukaciya
har tsakar dare haka ta dinga masu kamar tababbiya, ta girgixa ne ba na wasa
ba, gate mai gadi ya wangale masu a xatonsu masu xuwa biki ne, Hajiyan Marafa
ce ta fara sakkowa motar sannan yaranta, kawayenta da Yan uwanta suma duk suka
fito daga tasu motar ko wannen su fuska a murtuke, Rahma ce ta tafi dakin umma
ta sanar ma ta xuwan su Hajiyan Marafa da suka ki shigowa ko da parlor ne wai a
kira masu Hajiya Rukayya, Umma ta katse wayar da take da Hajiya Saude jikinta
ya hau rawa tace "Kice masu bana nan, tun daxu na fita...." Rahma
tace "Har fa da Hajiyar da kanta" cikin tsawa Umma tace "Ki fita
kice masu bana nan nace, ko uban me xan masu da suka xo min nan, ko ce masu aka
yi ni na daura ma Mujaheed aure???" Rahma ta fita dakin umma ta mike da
sauri ta sa makulli hannunta na rawa, xaunawa tayi gefen gado xuciyarta na
bugawa, Allah kadai yasan abubuwan da xa su fada yau, saukin abun ma Abba sun
fita tun daxu da kaninsa, Aunty da Mama Hadiza dama suna can part din Inna tun
safe, dialing Number Hajiya Saude ta kara yi ta sanar mata Hajiya Mansura ta xo
tare da tawagarta a motoci, Hajiya Saude tace "Innalillahi wa inna ilaihi
raji'un... Toh yanxu ya ake ciki??" Umma na share xufar da ke keto mata
tace "Tonon asiri nake tsoro Saude, nasan yar duk ta kwashe ta sanar masu
yanda aka yi, Saude kar su fasa kwai a gidan nan in shiga uku dadin abun ma
Alhaji bai nan, Amina da Hadiza kuma suna gun tsohuwar amma kinsan yanda
Hajiyan Marafa ke magana, wllh dole su ji hayaniya su fito, ni dai nace Rahma
tace bana nan" Hajiya Saude ta sauke ajiyar xuciya tace "Ni wai
Rukayya tun farko me kika ga tattare da family din Hajiyan Marafa kika hada
d'an ki da yar su??" Umma tace "Aa kawai don ace d'a na na auren yar
masu kudi mana, sunan nake so dama, kuma ai haka ma mutane ke cewa" Hajiya
Saude ta ja tsaki tace "Toh me kika karu da a kudin su?" Umma tace
"A'a ki bari, wllh ynxu haka akwai wani sarka da dankunne xai yi miliyan
daya da rabi haka Hajiyan Marafa ta bani kyauta kwanaki da naje, sannan ta dalilin
auren nan matan governor kalilan ne ban sani ba, duk taronsu sai naje, manyan
kasan nan yanxu daddaya ne ban gani ba ido da ido amma a mata, Kai har wasu
maxan ma...." Xaro ido Umma tayi jin hayaniya a tsakar gida tace
"Gasu can Saude, xa mu yi magana anjima" daga haka ta katse wayar ta
tafi ta bude labule a hankali tana lekansu.... Hajiyan Marafa ce tsaye tana
cewa "Duk inda Rukayya ta shiga yau sai ta fito wllh, in har na bar gidan
nan to Rukayya ta fito ta fallasa kanta ne, 'ya ta xata yaudara a hada baki da
ita a mata kishiya??? Toh wllh wllh yau sai ta san tayi da Hajiya Mansura,
yanda ban xauna da kishiya ba haka diyata baxata xauna da kishiya ba, malamai
da bokayen da take bi yau duk sai ta fito tayi bayani ta tona kanta ta fadi
abinda tayi aka fasa auren yarinyar gidan nan har aka hada auren da mijin
diyata...." Hajiya Baturiya yarinyar Hajiya Marafa ta fari cikin tsawa da
daga murya tace "Ta fito da bakinta ta fadi abinda tayi aka fasa auren da
aka lika ma mijin Yar uwata, ta fito nace idan ba haka ba yau wllh wllh sai mun
tada gidan nan in ga shegen da ya tsaya ma mutan gidan....." Kawayen
Hajiya marafa suka yi cikin parlor suna cewa "Ae duk inda ta shiga sai ta
fito wllh, sai ta fallasa kanta anji mugun abinda take yi tun ba yau ba, yau
xata ga karshen boka da malamai...." Mama Hadiza ce ta taho compound din
da sauri jin hayaniya Aunty na biye da ita a baya, Umma dake jin su a daki ta
daura hannu a ka ta dinga xagaye dakin hawaye na sakko mata tana salati tana
fatan kada su Abba su shigo gidan, wani rashin tunanin ne ya kai ta hade kai da
Safeenah har ta san sirrinta haka tasan abinda take ciki, tare fa suka dinga
xuwa gun Malamin ashe abu xai juyo kansu yanxu ga Safeenah ta fallasa ta gun
uwarta da bakinta ba shiru yake ba, ta xauna gefen gado ta fashe da kuka tace
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me ke faruwa haka ni Rukayya, Allah
ka rufa min asiri kada 'yan gidan nan su jiyosu su fito, da na shiga uku yau
kuwa" muryar Mama Hadiza da ta ji tana tambayar lafiya yasa ta mikewa da sauri
tana xaro ido ta ji cikinta ya hautsine, Hajiya Baturiya tace "Kafff
xuri'ar mu babu wanda ya taba xama da kishiya don haka baxa a fara kan kanwar
mu Safeenah ba, karya ake Safeenah ta xauna da kishiya, Rukayya ta fito ta fadi
abinda tayi gaban kowa yanxun nan..." Mama Hadiza tace "Tohhh, iko
sai Allah ku kuma da abinda ku ka xo kenan??" Hajiya Shamsiyya ta iso
wajen tana huci tace "Kwarai kuwa da abinda mu ka xo kenan, bokan da
Rukayya ta biya ta sa ya wargaje auren yar gidan nan shi xata fito yanxun nan
ta kai mu gunsa ya wargaje abinda yyi da har yasa tsautsayi ya fada kan 'yar
mu, kin ganmu nan kaff bbu mai kishiya, kema kanki nasan baki sonta don haka
Safeenah domin ita kadai aka yi mijinta baxata xauna da wata banxa wai kishiya
ba...." Muryar Inna suka ji tana salati da karfi tana cewa "Naga
abinda ya isheni ni patuu, wasu mahaukatan ne aka bude ma get suka shigo mana
gida haka, anya ilu xai gama da duniya lafiya kuwa, banda haka ya xai bude ma
lafta laftan mahaukata get su shigo mana gida suna hauka ba kakkautawa??? Ina
Ahmadu da Bukar suke suga abinda shegen bakauyen da suka ajiye a bakin get yyi,
ya tashi ya bude ma ta6a66u get salon su fara bin mu da duka muna gudu"
Hajiya Marafa ta nufeta cike da raini tace "Hajiya mu ba mahaukata bane,
amma mun fi mahaukata hauka idan aka ta6o mu, ba wani abu ya kawo mu ba Rukayya
muka xo nema ta fito ta fadi abinda tayi aka fasa auren gidan nan wanda hakan
yasa har aka ma diyata kishiya bata ji ba bata gani ba, wllh har gun bokan da
ta je aka mata aiki duk sai ta kai mu yanxun nan gaba daya...." Inna ta
xaro ido cike da masifa tace "Auzubillahi wacece wannan Kuma?? Waye kuma
boka ni patuu?? Rukayyar ce ta san wani boka?? Toh tun da uwarta Hadiza ta
haifeta bata san sa ba, kaji min gantalallu dai yan iska mahaukata, waye kuma
'yar ku? Safara'u ko wa? Wllh tunda ku ka ma Rukayya wannan gagarumin sharrin
sai Mujaheed ya fito duk inda yake ya sake shegiyar yar ku, don baku da tsoron
Allah uwarsa ku ka xo yi ma cin mutunci har gida?? To wllh sai Mujaheed ya
saketa yau yau din nan, mu kaf danginmu bbu wanda yasan boka, kai ko ma ya sani
Allah ya yafe masa, kaji min mutane dai yan wahala, wllh idan baku fitar mana
gida ba sai na tafi caji ofis yanxun nan an xo an kwashe ku in ga uban da ya
tsaya maku, Ina ruwan Rukayya da wani boka Allah na tuba, matar dake ta murna
da hadin da Ahmadu da Bukar suka yi tun jiya, tun da nake Rukayya bata taba
shigowa da sassafe gaisheni ba sai da aka hada auren nan, yanxu haka da kanta
xata je dauko amaryar a gidan kakarta don can ta kwana... Kaji min mutane dai??
To wlh ku fita ku ban wuri kada in tsine maku" Daga Hajiyan Marafa har 'ya
yanta da kawayenta sake baki suka yi suna kallon Inna, Inna ta juya ta fara
wucewa a fusace tana cewa "Rukayya ai ta fi kowa murna da auren nan, dama
tun farko ita ba son shegen d'an Bulasawan nan take ba, tun farko take ma Imaan
kwadayin aure da Mujaheed mu ne dai ba mu yarda ba" Aunty ta saci kallon
Mama Hadiza dake bin uwar tata da kallo, can duk suka bi bayanta, Safeenah ta
fashe da matsanancin kuka mai ban tausayi ta durkushe wajen jikinta na rawa
tace "Na shiga uku Mummy wllh ni baxan iya rabuwa da Mujaheed ba Ina
sonsa, dama ashe duk yaudarata take da Mujaheed take son ayi auren nan?? Wayyo
mummy ku taimakeni kada ya sakeni wllh ina son sa" Hajiyan Marafa ta dinga
huci ta ma rasa abun cewa tana kallon Safeenah, sai da Inna tayi nisa ta kalli
Mama Hadiza murya can kasa tace "Ba boka ba har gun masu tsafi Rukayya
xuwa take wllh tllh"
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
80....
Hajiya Mansura tayi wani murmushi tana kallon kawayenta tace
"Rukayya ta debo ruwan dafa kanta, wato da sa hannunta da contribution
dinta a yi ma 'ya ta kishiya.... To xata san da Hajiya Mansura take, xata san
da sa hannunta ayi ma diyata kishiya, ita da d'an ta daga wnn lkcn sai dai
hange daga nesa, kishiya kuma Safeenah baxata xauna da ita ba, kaf xuri'ar mu
babu mai kishiya kuma baxa a fara a kanta ba, ku mu tafi kawai...." Hajiya
Baturiya ta daga Safeenah dake rusa kuka kamar ranta xai fita tace "Babu abinda
kukan nan xai amfane ki da, ki tashi mu tafi tun wuri a san abun yi, sai Hajiya
Rukayya ta san da family din Alhaji Usman take...." Cikin kuka Safeenah
tace "Mummy yar uwarsa mai min rashin kunya a gidana fa aka aura masa,
wannan fitsararriyar ce fa mai min kallon banxa ce, Mummy ya xa ayi ta aurar min miji na shiga
uku na lalace, da na sani da ban biye uwar Mujaheed ba, ashe yaudarata take da
Mujaheed take son ayi auren, Mummy sai kinga yanda yake ji da yarinyar, Mummy
ya xan yi da raina idan aka kawo min ita gida a matsayin kishiya, wayyoo Allah
na..." A fusace Hajiyan Marafa ta buge bakinta tace "Uban wa xai kawo
maki ita gida a kishiya?? ai wnn gidan naki ne ke kadai har duniya ta nade, sai
dai idan ba tsatso na kika fito ba, Mujaheed naki ne ke kadai, hatta uwarsa
Rukayya sai dai ta gansa daga nesa, wa ke ta wani amaryar ga babban shaidaniya
annamimiya da xa mu fuskanta, in sha Allahu sai na toxarta Rukayya toxarci mai
girma kuwa, sai tayi da ta sanin sani na..." Daga haka ta ja ta xuwa cikin
mota tana huci, duk suka shige cikin mota suka bar gidan, Umma dake labe jikin
window tana kallonsu ta share xufar dake ta sauka fuskarta ta koma gefen gado
ta xauna tana tunanin abun yi. Inna na kallon Mama Hadiza da Aunty tayi wani
murmushi tace "To kun dai jiye ma kunnan ku komai, ni tun ba yau ba nasan
Rukayya na xuwa gun boka da malamai, amma wllh tllh in har da sa hannunta a
rugujewar auren jikata ita ma nata auren na lilo tangal tangal yanxu...."
Sai kuma Inna ta fashe da kuka sosai tace "Allah dai ya hada Ahmadu da
jaraban duniya, Rukayya jaraban duniya ce, wato hade kai tayi da surka suna
xuwa gun boka bbu kunya ba tsoron Allah, Ni dai wlh in har aka binciko min aka
gano cewar ita ta wargaza auren Imaan akwai tashin hankali a gidan nan gaskiya,
don da kai na xan yi fatali da kayanta waje, dama darajan Mujaheed kawai take
ci a wajena" Mama Hadiza ta sauke ajiyar xuciya tace "Ni na ma rasa
abun cewa wllh..." Inna tace "Yo ba dole ba, kuma fa tana ciki tana
jin su, wa ya sani ma ko xawo ta dinga saki a dakin, ni dama ciki suka shiga
suka kamata su lakada mata duka da cacan bakin da suka dinga yi tsakar
gida" Mama Hadiza tace "Toh
Inna kin san halinta kuma me yasa xaki kare ta a wajensu?" Inna tace "Ka
ji ki ke kuma, ke baki ga yanda jikinsu yyi sanyi ba, ai ynxu mance batun
kishiyar da aka ma Safara'u xa su yi su fuskanci Rukayya su yi fata fata da
rayuwarta, ai bamm na hada mata...." Dariya sosai Aunty tayi tana kallon
Inna, Inna tace "Lallai ba ku san ni ba kenan har yanxu, Ahmadu da Bukar
kawai nake jira su dawo daga gidansu bafillatanar can da ta gudu min da jika su
ji wnn abun al-ajabin, dama Ta Rasulu sai da tace min bata yadda da fasa auren
nan da Bulasawa yyi ba, shi sa ma yau da sassafe ta tafi don xuwa binciko mana
m ke faruwa, na rantse da Allah in har da sa hannun Rukayya a fasa auren nan
sai nayi sanadin karshen xamanta a gidan nan..." Tana fadin haka ta tashi
ta wuce daki, Mama Hadiza ta girgixa kai tace "Rukayya tayi asara duniya
da lahira, yanxu meye amfanin surkai su xo tsakar gida suna maki cin mutunci
haka, ni wllh Mujaheed nake tausayi bai yi sa'ar uwa ba kwata kwata, tun fa ba
yau ba ake abu daya da matar nan ta ki sa Allah a ranta, anya Rukayya xata gama
da duniya lafiya kuwa??" Aunty dai bata ce komai ba amma ita ma mamakin
maganganun Hajiyan Marafa da tawagarta kawai take... Karfe sha biyu saura Gwaggwo ta shiga parlon
Inna da sallama, Imaan dake sanye da Hijab har kasa da Nikab na biye da ita a
baya, Inna dake xaune parlon tare da Mama Hansai ta amsa sallaman, Imaan ta
wuce daki walking slowly, Inna tayi ma Gwaggwo kallo daya tana sakace hakori ta
dauke kai, Mama Hansai ta shimfida mata darduma tana mata sannu da xuwa,
Gwaggwo ta xauna bayan sun gaisa da Hansai tace "Sannu Hajiya Asabe"
Inna ta kalleta tace "Yauwa sannu Hajiya Biba, amma a gaskiya ki dinga sa
'yar ki a hanya, kwata kwata Aisha bata ji bata maida ni bakin komai ba, ya
xata maida kanta mahaukaciya daga anyi abu don fitar da mu kunya gaba daya,
kema kuma baki son gaskiya don da kina son gaskiya tun jiya ya kamata ki tiso keyarta
ki koro su, nan nan nace mata kada ta je ko ina amma yarinyar nan ta ki
saurarata, gaskiya raina ya baci matuka don tun tsakar daren jiya nayi niyar
tahowa gidan in sameta su Ahmadu suka hanani" Gwaggwo dake ta saurarenta
tace "Allah ya kyauta, a dai ta hakuri..." Inna tace "Atoh,
tamkar yar ciki na na dauketa amma dubi iya shegen da ta min, kowa a gidan na
ya girgixa da auren nan, to amma abinda hakuri bai yi ba rashinsa xai yi? ni fa
har cewa nayi sai Mujaheed ya rubuta takarda amma d'an banxan ya gudu da dukkan
alama yana so, to yana so mana tunda tun jiya bbu shi bbu alamarsa ya shiga
duniya" Gwaggwo tace "Toh Allah dai yasa hakan ne mafi alkhairi, ga
ta nan dai na kawota, ba ma ta jin dadi amma tunda nayi ma iyayenta alkawarin
dawo da ita shi sa na maido ta yanxu" Inna ta yo waje da ido tace
"Kuma bata da lafiya sai ayo min nan da ita, ta fito ta koma barin su ai
Hadiza na can" Gwaggwo ta mike tace "Ni dai xan koma Hajiya Asabe
Allah ya sanya albarka" Daga haka ta nufi kofa, Inna tace "Toh ko
ruwa baxa ki sha ba" Gwaggwo tace "A'a nagode, sai anjima" daga
haka ta fita parlon, Inna ta tabe baki tace "Aisha dai ta lalace
wllh" tana fadin haka ta tashi ta tafi daki gun imaan, kwance ta sameta ko
nikab din fuskarta bata cire ba, Inna ta tuge nikab din ganin yanda idonta yyi
jajir ga jikinta yyi xafi ba kadan ba tace "Ae ni na shiga uku, fasa auren
da Bulasawa yyi yasa kika rame haka kika sa ma kanki ciwo Imaan?" Imaan ta
mike xaune da kyar hawaye na saukowa idonta ta kamo hannun Inna cikin rawar
murya tace "Don Allah Inna ki taimakeni, wllh shi fa Yayana ne taya xa ace
ya aureni???" Inna ta marairaice tace "Nima dai shi na gani, wnn uban
sa6o har ina ni patuu, sai kuma ace kinyi ciki kin haifa masa 'ya ya ko? To ta
ina xa fara wannan ta6aran ni Asabe??" Imaan ta fashe da kuka sosai ta
rufe kanta da pillow tana shessheka, Inna ta xauna gefen gado tayi tagumi tace
"Anya su Ahmadu da Bukar suna da hankali kuwa ni Patuu? A ina suka ta6a
ganin anyi haka tukun??" Imaan dai kuka kawai take kamar ranta xai fita,
Inna tace "Naga abinda ya isheni...." Mama Hadiza ce ta shigo dakin
bayan sun hadu da gwaggwo a compound sun gaisa ta sanar mata ta dawo da Imaan,
Inna na ganinta ta mike tace "Hadiza anya su Ahmadu na da saiti kuwa, ta
ina Imaan da Mujaheed xa su yi aure ne wai ban gane ba, yayanta ne fa
Hadiza?" Mama Hadiza tace "Kamar ya Inna?" Inna tace "Toh
abinda tace min kenan wai yayanta ne kuma haka ne wllh yayanta ne" Mama
Hadiza na kallon imaan tace "Halan baki je islamiyya bane Imaan???"
Inna ta daure fuska tace "Kaji wata magana, yarinyar da ta haddace kur'ani
har sauka tayi aka bata kyaututtuka kice bata je islamiyya ba Hadiza??"
Mama Hadiza na kallon Imaan fuska daure tace "Ta ina Mujaheed ya xama
Muharramin ki? Ko kin fara hauka ne? Idan an kai ki gidan sai ku ci gaba da
xaman yaya da kanwa a can, amma na sake jin kince yayanki ne sai na bata maki
rai wllh, shashasha kawai...." Murya can kasa Inna tace "Atoh dai,
nima ban san ta ina ya xama yayanta ba, ubanta Bukar ubansa Ahmadu, uwarta
Aisha uwarsa Rukayya" ko kallon Inna Mama Hadiza bata yi ba ta juya ta
fice daga dakin, Inna ta xauna gefen gado tayi tagumi tace "Gashi har
yanxu shiru bbu Mujaheed din babu labarinsa, ko shima yana can yana ta damuwar
an hada sa da kanwarsa ne" ita dai Imaan bata ko kalleta ba sai kuka take
a hankali. Har Inna ta gama tsarinta kallonta kawai Abba da Daddy suke yi, Inna
tace "Wllh kuwa Ahmadu, motocin da suka shigo sun yi biyar ga dai Hadiza
shaida, to shine nace gaskiya idan maganganun iyayen Safara'u ya tabbata kashin
Rukayya ya bushe a gidan nan kuma xamanta ya xo karshe, ynxu dai muna bin komai
a hnkli ne don ba mu gama tabbatarwa ba tukun, duk da dai gaskiya tun ba yau ba
nasan Rukayya na shige shige" Abba dai kansa na kasa, Daddy kuwa har
xuciyarsa bai yrda da xancen Inna ko na second daya ba, can ya mike yace
"Inna lkcn Asr yyi xan tafi masallaci ynxu" Daga haka ya nufi kofa
Inna ta bi sa da kallo sannan ta kalli Mama Hadiza tace "Irin na xauna ina
shirga masu karya din nan, to in sha Allahu a gabansa asirin Rukayya xai tonu dumu
dumu..." Abba ya kalleta yace "Allah ya kyauta, xa mu xuba ido mu ga
inda matsalar yake kafin a dau mataki" Inna tace "Atoh dai nima haka
nace a hankali xa mu bi komai har mu gano gaskiya, ba wani gaggawa" shi
dai bai ce mata komai ba, tace "Toh wai ni jama'ah ina xancen jikana ne,
tun jiya fa har yau shiru, ko gidansa xan dau mayafi in tafi?" Abba yace
"Daxu mun biya gidan baya nan" salati Inna ta saki tana kallonsa tace
"Toh me ya samesa?" Mama Hadiza tace "Gun aikinsa fa?" Abba
yace "Sadeeq ya je baya nan" cike da damuwa Inna tace "Toh anya
lafiya kuwa??" Mikewa Abba yyi shi ma dai duk abun ya damesa sosai, yace
"Bari in tafi masallaci Inna" daga haka ya fita parlon yana tunanin
to Ina Mujaheed xae tafi tun jiya. Daren ranan Inna ta fito tsakar gida tana
salati tana kiran Abba da karfi, Daddy ne ya fito part dinsa ya sakko yana
tambayar me ya faru, Ko saurarensa bata yi ba balle ta kallesa ta karasa part
din Abba tana kwalo masa kira, Yusuf ne ya fito parlon Aunty na biye da shi,
yace "Lafiya Inna? Me ya faru" Daga sama har kasa ta kallesa tace
"Kai rabu da ni, kai ne Ahmadu, ni ba duk xatona kana gun amaryarka ba
ashe kana gidan nan har yanxu baka shigo ka min jajen abinda ke faruwa
ba...." Ganin Abba tace "Wllh Ahmadu na kasa gane kan Imaan, abinci fa
na tilasta ta ci sai gashi ta dinga amai kamar xata mutu ga jikinta duk xafi
kamar garwashi, ka ga dai yanda nake tsaye kyam to bata iya tsayawa haka, kada
wani cuta ya kamata fa in shiga uku ka taho mu je ka kaita asibiti, a gaskiya
bata da lafiya sosai wllh" shi dai Daddy na tsaye bayanta yana kallonta,
Abba yace "mu je to" daga haka ya fara tafiya Inna ta bi bayansa
Aunty da yusuf na biye da su, kafin su je har Mama Hansai ta kintsa Imaan da
duk ta wani langwabe, Abba yasa ta sa hijab suka wuce asibiti.... Daren ranan
asibiti Imaan ta kwana tare da Aunty sbda karin ruwan da ake mata, tausayinta
sosai Aunty take ji don abun ya hade mata biyu ne, ga heartbreak ga kuma
unexpected marriage, ga shi duk ta wani rame, wajen karfe daya Imaan ta farka
daga baccin da take, Aunty dake xaune kan farin kujera ta jinginar da kanta da
gadon ta dago jin motsin ta, mikewa tayi tace "Sannu Daughter, ya
jikin?" Imaan ta kamo hannunta lkci daya hawaye ya kawo idonta cikin
sanyin murya tace "Aunty don Allah baxa ki taimakeni kiyi ma su Abba
magana su yi hakuri kada su ce ya Mujaheed ya aureni ba??" Aunty na
kallonta da tausayi tace "You need much rest imaan ki kwanta ki yi bacci
ko na hada maki shayi?" Imaan ta girgixa kai hawaye na sakko mata tace
"Aunty kice wani abu plss" Aunty tace "Imaan meye da Mujaheed
din da baki son auren sa?" Imaan ta xaro ido tace "Aunty yayana ne
fa" murmushi Aunty tayi tace "Eh yayan naki, ae da aure tsakanin ku
ko, Mujaheed is good ba shi da wani flaws da xai sa ki daga hankalin ki, ke da
ma kika fi kowa sanin sa, kinsan halinsa ya san naki so what more, in just few
days time da xa ku yi tare am telling you sai kun gode ma iyayen ku da suka
hada ku aure, but wait ynxu ki gaya min me yasa baki son auren, amma kada ki ce
min yayan ki ne, don ke kika laka6a masa wannan matsayin, tell me yana da wani
abu ne da ba ki so" ta fashe da matsanancin kuka tace "Wllh Kunyan sa
xan dinga ji Aunty, ni kunya nake ji...." Sosai ta ba Aunty dariya, Aunty
ta rungumeta tana murmushi bata dai ce komai ba, cikin rawar murya Imaan tace
"Allah kunya xan ji Aunty" Aunty tace "Toh ki kwanta yanxu ki
huta sosai, gobe sai mu yi magana" da haka ta lallaba ta ta kwanta, amma
imaan bata yi bacci ba daren ranan, da ta tuna wai ynxu Mujaheed fa mijinta ne
sai taji kamar ta bace duniyar gaba daya da wannan abun kunyan kawai, washegari
sai da rana aka sallamosu suka dawo gida. Sadeeq ne durkushe gaban Mum dinsa
dake xaune tana kallonsa da mamaki, ya hade kansa da kneels dinsa hawaye na
sakko masa yace "Mummy I don't know what just came over me, don Allah ki
tausaya min ki ba Abbana hakuri ya sami iyayen Imaan ya basu hakuri I cant
imagine loosing her, don Allah ki taimakeni ki masa magana ya same su sai a
daura mana auren" Mummy tace "Anya kana da hankali kuwa Sadeeq??"
Ya dago kansa yana kallonta hawaye na sakko masa yace "Sure mum, ni ban
san me yasa nayi abinda nayi ba, help me speak to dad plss" mummy tace
"Kaje ka samesa da kanka Sadeeq I won't invole my self coz har ynxu ur Dad
is angry with me bcos of what u did" tashi yyi ya nufi kofa ta bi sa da
kallon mamaki don tun shekaranjiya sai yau ya shigo gida kamar an jefo sa,
mikewa tayi duk jikinta yyi sanyi sosai tana tunanin to me ya sami son dinta,
ita tun farko tasan ba yin kansa bane fasa auren nan da yyi, then who is after
her son? Waye yyi masa haka? Girgixa kai tayi tace "I will surely find
out...." Tana fadin haka ta fita dakin. Inna na xaune parlonta ta sa Mama
Hadiza gaba bayan Magrib wai sai ta samo mata layin Mujaheed kawai ita dai,
Mama Hadiza ta kira for the third time da damuwa tace "A kashe fa wayar
yake Inna ba a kunna ba har ynxu, gashi kina jin ance switched off" Inna
ta xaro ido kamar xata rusa kuka tace "Anya Hadiza Mujaheed ba kashe kansa
yaje yayi ba kuwa??" Sai kuma ta fashe da kuka tana kallon Mama Hadiza
tace "Da mun shiga uku mun lalace" Mama Hadiza ta hade rai tace
"Haba Inna ya kashe kansa a kan me kuma?" Sallaman da suka ji bakin
kofa yasa duk suka yi shiru, Imaan dake kwance daki duk tana jin su ta mike
xaune da sauri xuciyarta na bugawa jin muryar wanda yyi sallaman, Inna ta kalli
Mama Hadiza tace "Waye kuma wannan yake min sallama?" Mama Hadiza ta
amsa sallaman tana kallon bakin kofa, Sadeeq ne ya shigo parlon kansa a kasa,
Mama Hadiza ta dinga kallonsa da mamaki, Inna ta mike da sauri tace "Naga
abinda ya isheni, waye kuma wannan Hadiza?? Wa yake nema a parlon nan" A
hankali ya durkusa gabanta cikin raunin murya yace "Don Allah ku yi min
rai kaka kar ku raba ni da Imaan, ban san me ya sameni nayi abinda nayi ba, don
girman Allah ku yafe min kaka, wllh Ina son Imaan baxan iya rayuwa ba ita ba
don Allah kaka ki taimakeni kada su Abba su ce baxa su bani ita ba..."
Hawaye sosai yake yana kallonta hankali tashe, Mama Hadiza ta bude baki tana
kallonsa, lkci daya taji tausayinsa sosai ba kadan ba don gaba daya a hargitse
yake ga wani rama da yyi ba na wasa ba, Inna ta xauna ta rushe da kuka tayi
mitsi mitsi da ido tana kallonsa cike da masifa tace "Amma dai kai
gantalalle ne wawa, da can uban me ya hau kanka ka yaudari jikata ka sa mata
cuta ka gudu?? kunyata mu fa kayi a idon duniya makiyan mu na ta mana dariya ta
ko wani lungu da sako, uwar me xa mu maka ka xo mana nan d'an nan, wllh maxa ka
fita kada Bukar ya gan ka don ba ruwana, gwara ma Ahmadu...." A rikice ya
kamo hannunta yace "Wllh kaka ban san me ya sameni nayi haka ba, don
girman Allah kar a raba ni da Imaan xan iya rasa rai na" Imaan ta mike ta
shige bathroom ta dinga kuka kamar ranta xai fita, Inna ta gwalo ido tana
kallonsa tace "Baka san abinda ya same ka kayi haka ba kuma?" Kuka
sosai yake mata yace "Wllh ban sani ba Kaka, ban san me ya faru ba, ban
san me yasa nayi haka ba, Kar ku hana ni Imaan don Allah, nasan ke kadai xa ki
saurareni kaka" Inna ta fashe da kuka tace "Innalillahi wa inna
ilaihi raji'un, Lalacewa ta sameka baka rike Allah da karfi ba Bukar, ni dama
nasan da akwai abu a kasa don wannan ba halinka bane, yanxu ni ya xanyi da kai
an riga an daura ma mutumi auren yarinya??" Dago kai yyi da sauri yyi
still yana kallonta ko kiftawa babu, Mama Hadiza ta sauke wani boyayyen ajiyar
xuciya tace "Ka bari iyayenta su dawo xa a san abinda xa ayi
Sadeeq...." Sadeeq ya kalleta yace "Don Allah ki sa baki Mama I can't
imagine me loosing her, u just can't imagine it" Mama Hadiza tace
"You don't worry ka tafi gida, in sha Allah xa a san abun yi" Inna na
matsar kwalla tace "Ehh ka tafi xa a san abun yi, ae kai din mutumin kirki
ne" xuciyarsa na bugawa yace "Toh anjima xan iya dawowa Kaka?"
Mama Hadiza tace "A'a ka bari dai gobe dare yyi yanxu, I will talk to my
brothers..." mikewa yyi ya isa gabanta ya durkusa hawaye na sakkowa idonsa
a hankali yace "Nagode sosai Mama, Allah ya kara girma" Mama Hadiza
ta kasa cewa komai wani tausayinsa ta dinga ji har ranta, cikin sanyin murya
tace "Don't worry ka tashi ka tafi Sadeeq" mikewa yyi a sanyaye ya
nufi kofa wiping off his tears ya fita parlon, Inna ta kalli Mama Hadiza ta
fashe da kukan takaici tace "Kinga maganan iyayen Safara'u a fili ko
Hadiza? Kinga magana ya fara fitowa koh, wllh ni dama nasan da kyar Sadeeq yyi
ma jikata haka, yaro ne fa mai hankali da natsuwa, ubansa ma ga dattako da
sanin ya kamata sannan ga kudinsa na halak, duk satan da ake a kasar nan ko
biyar bai taba sata ba wllh inda ya burgeni kenan, komai nasa na halas ne babu
Haram, gaskiya a duba lamarin nan a tausaya ma yaron nan, yanxu dai jiran
dawowar ta Rasulu nake inji bayani a nan kuma xa a san ni tababbiya ce a gidan
nan, kaff sai na tada gidan nan wllh idan abinda muke xargi gaskiya ne, kuma
don Allah da Mujaheed na son auren nan xai gudu? Ni nasan yana can abun duniya
ya ishesa baya son auren, ya kwantar da hankalinsa kawai da rai na babu me
cutar sa yyi masa auren dole wllh, me xai ci da Imaan Allah na tuba" Mama
Hadiza dai bata ce komai ba amma gaba daya kanta ya gama kullewa, bata ma san
surutun da Inna take ba don tausayin Sadeeq ya dameta. Misalin karfe sha daya
da rabi na dare Inna na kwance parlor sai sharar bacci take ga darduman ta da
Hijab da carbi a gefenta tayi shirin tashi tayi sllhn dare anjima, kukan da
Imaan ke yi tun bayan wucewar Sadeeq yasa taki kwanciya a dakin bayan tace mata
aniyarta ta bi ta, shine tayi kwanciyar ta a parlor, murda kofar parlon aka yi
a hankali ya shigo ya ya kulle kofar ya tsaya nan bakin kofa yana kallonta,
bayan few seconds ya nufi bedroom dinta walking gently ya bude kofar yana
kallon ciki, Imaan na kwance ta rufe har kanta da duvet sai dai ba bacci take
ba, duk a xaton ta Inna ce ta bude kofar dakin hakan yasa ko motsi bata yi ba,
murmushi yyi ya rungume hannunsa ya jingina da kofa yana kallonta ko kiftawa
babu, a hankali ya rufe kofar dakin ya nufi kan gadon, Imaan ta bude ido sosai
daga cikin Duvet din da take jin kamshin turaren da take ji....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
81.....
A hankali ya sa hannu ya sauke bargon daga saman kanta bayan
ya xauna kusa da ita, ido hudu suka yi, ta mike xaune a mugun firgice ta xaro
ido tana komawa baya da karfi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,
innaaa" sai kuma ta fara kokarin sauka daga kan gadon ko ina na jikinta na
6ari, yyi hanxarin rikota ya maido da ita kusa da shi ganin xata kurma masa ihu
ya hade ta da jikinsa ya sa hannu ya rufe bakinta, da karfinta ta dinga
struggling din kwatar kanta hawaye na sakko mata amma ta kasa, gaba daya kuma
ta ki yarda ta kallesa, shi kam sai kallonta yake daga karshe ya xame hannunsa
bakinta ya rungumeta hade da lumshe ido murya can kasa yace
"Imaaan..." Ta fashe da kuka sosai tana tura sa tace "Bana son
haka yaya ni ka sake ni plsss, meye haka kke yi, ka sakeni bana soo....."
Unexpectedly taji warm lips dinsa a kan neck dinta, ta wani xaro ido ta fasa
ihu cike da shock tace "Wayyo Innaa....." Muryar Inna suka ji daga
parlor cikin rikicewa take cewa "Kai amma gaskiya ban taba ganin
shaidaniyar yarinya irin wannan 'ya dai ta Bukar ba, me na maki xaki gigitani
haka fisabilillahi ina bacci Imaan? Me na maki?? To fito don ubanki ki tafi
bangaren ku baxa ki kwanar min a nan ba wllh tllh, maxa fito min dakina, kuma
ke da Allah tsorata ni da kika yi, gaskiya ke da Allah" Mujaheed ya saketa
da sauri ya koma baya ganin tana jan numfashi da kyar, jinginar da ita yyi da
gado yana kallonta yace "Hey relax now...." Kin yarda su hada ido
tayi tana kokarin daidaita numfashinta, tashi yyi ya kunna fan din dakin ya
dawo ya xauna ya dago kanta yace "I said relax..." Murda kofar dakin
Inna tayi jin sa a rufe cike da masifa tace "Bude min dakina ki fito ki
kama gaban ki ba ruwana, Allah ya saka min, daga yau kada ki sake yo min nan
dama don koran kare xan maki muguwar yarinya kawai" Imaan dai sai sauke
numfashi take hankali, lkci daya ta mike tsaye hawaye na sakko mata xata tafi
gun kofar ta bude duk don ta samu ta gudu Mujaheed ya kamota ya mayar da ita
kan gadon ta fashe da kuka jikinta na rawa tace "Inna kice masa ya bar ni
in bude kofar" Inna dake tsaye har sannan ta wani xaro ido tace
"Auzubillahi waye ya shiga dakin?? Waye ya shiga??" cikin rawar murya
Imaan tace "Yayaa..." Inna ta d'an yi shiru kafin tace "Yaya?
Waye kuma Yaya?" Imaan dai bata ce komai ba sai goge idonta take xuciyarta
na bugawa tana komawa baya, Mujaheed ya kafeta da ido ko kiftawa baya yi yana
kallonta, Inna tace "Shi Mujaheed din d'an iska ya xama xai tsallakeni a
parlor ya shigar maki daki kina kwance? Ko wiwi ya sha daga inda ya taho??"
Mujaheed ya mike yana murmushi ya shafa kansa ya nufi gun kofar ya bude, Imaan
taji 6ata taba son k'in ganinsa irin na moment din nan ba, ko kallonsa bata son
yi balle ta ji muryarsa, gaba daya ta ji ta tsane sa, Yana bude kofar Inna ta
kallesa daga sama har kasa sannan ta kalli Imaan da ta takure waje daya tana
hawaye tace "Ya kai minti nawa da shigo maki" Imaan taki cewa komai
sai hawaye da shessheka, Inna ta kara kallon Mujaheed tace "Iskancin naka
ya kai ka dinga biyo dare kana shigewa dakin mutane Mujaheed?? Toh dama neman
ka ake ruwa a jallo, tunda dai ka gama guje gujen ka mara tushe sai mu tafi gun
su Ahmadu ka rubuta ma jikata takarda ka mika ma ubanka da ya daura maku aure
ya bata, don gaskiya Imaan bata isa aure ba, idan ma ta isa to a gaskiya ka fi karfinta,
Ina xata kai lafcece irin ka? Ko baka ga yanda take bane, sannan wannan yaro
Sadeeq dai ya dawo daxu ashe ba yin kansa bane.... Don haka mu je dama kai
kadai ake jira" Mujaheed yyi wani
murmushi yace "Ke ma xa ki iya rubuta takardan ki bata ai...." Inna
tayi misti mitsi da ido ta tsaya kallonsa ko kiftawa babu, can kawai ta fice
daga dakin, ya bi ta da ido har ta fita parlor gaba daya bayan ta cire makullin
jikin kofar parlon, yana jinta ta sa makulli ta waje ya juya yana kallon Imaan,
ganin ta mike xata shige toilet da gudu, yyi hanxarin cafkota ta kwala wani
ihun jikinta na rawa tace "Na shiga uku don Allah Yaya ka bariii...."
Ya ajiyeta saman gado ta ja duvet tana rufe jikinta tana kuka, yana kallon
idanuwanta duk da ta ki yarda ta kallesa yace "Listen to me now..."
Kin tsayawa waje daya tayi tana komawa baya tana kuka, ya wani hade rai yana
kallonta yace "I said stay still now" da kyar ta xauna waje daya
ganin ba da wasa yyi maganan ba amma ko da mistake taki kallonsa sai hawaye
take xuciyarta na bugawa, ya dinga kallon lips dinta sannan a hankali cikin
sanyin murya yace "isn't this our Destiny Imaan?" Sai a sannan ta
kallesa da sauri, ta xaro ido cikin rudewa tana girgixa masa kai tace "Noo
it's not plss, Yaya this not destiny, we are meant to be only brother and
sister not husband and wife, this is not destiny plsss, kai yayana ne wllh, ni
kuma kanwarka ce ko ka manta, bayan wannan babu wani alakar da ya dace da mu
Yaya, wllh Yaya wannan abun kunya...." Bai jira ta kai karshen abinda xata
fada ba ya bata shock of her life at that moment ta hanyar hade bakin sa da
nata...... Iyakar rikicewa Imaan ta rikice a wnn lkcn don har daukewa
numfashinta sai da ya kusa yi, don kansa ya kyaleta, amma fa shi ma ya kasa
kallonta, murya can kasa yace "Am I still ur Yaya?" Shock bai bar ta
ta iya basa amsa ba banda rawa babu abinda jikinta yake tana ja baya, dai dai
nan kuma aka bude kofa a can parlor.... Inna ta shigo masu dakin tana kallonsu
tace "Yana nan har yanxu Ahmadu" mikewa Mujaheed yyi ya saci kallon Imaan
da har sannan ta kasa kwakkwaran motsi kuma taki cewa komai ya fita dakin ya ga
Abba tsaye bakin kofa, Yyi kasa da kai kafin yace komai Abba yace "Where
were you all this while??" A hankali Mujaheed yace "Ina nan
Abba...." Abba yace "mu je to" Inna ta dau Hijab ta nufi kofar
xata fita Abba yace "Ina kuma xa ki Inna" da mamaki tace "A'a ba
magana xa ayi ba ya sakar min jika, Ahmadu na fa ce maka yaron ya xo mana da
Hadia jiya yana ta kuka kamar xai mutu, nasan Hadiza ta gaya maka komai, wllh
ba yin kansa bane kuma ko waye yyi masa haka xa mu binciko in sha Allahu kashin
ko ma waye ya bushe...." Abba yace "A'a kiyi hakuri kiyi kwanciyar ki
yanxu dare yyi, gobe da safe sai a xauna kowa da kowa ayi magana a nutse"
Inna tace "A'a da yanxu da goben ai duk daya ne Ahmadu, ni dai gaskiya mu
je ayi magana ayi ta ta kare yanxu, kada wani abu ya sami Imaan kaga auren nan
ba sonsa take ba" Da kyar Abba ya lallaba Inna a bari gobe da safe ayi
magana, shi dai Mujaheed na tsaye kansa a kasa amma gaba daya hankalinsa na kan
abinda yyi Imaan, shi kansa bai yi xaton xai iya hakan ba, Bai san lkcn da yyi
wani murmushi ba yana shafa kansa, muryar Inna ya ji tace "Kaga
mahaukaciya ma ya mayar da ni, dariya yake min ko Ahmadu, to wllh sai ya sakar
min jika tunda ba sonsa take ba baxa a mata dole ba" Abba yace "Allah
ya kai mu goben" daga haka ya kalli Mujaheed yace "Mu je"
Mujaheed ya kalli kofar dakinta sannan ya bi bayan Abba, slowly suke tafiyar
yana gefen Abba, Abba yyi breaking silence din yace "You are not happy
with what I did koh Muhd?" Mujaheed ya kallesa murya can kasa yace
"Not at all Abba" Abba yace "Toh ina ka shiga kwana biyun
nan" Mujaheed ya sunkuyar da kansa yana murmushi yace "Ina gidan a
bachelor frnd of mine, bana son tashin hankalin gidan ne" Abba na gyada kai
yace "Gaskiya ne, jiya Hadiza ta sameni ta min bayanin yanda suka yi da
yaron nan Sadeeq, kasan Hadiza ba komai take ba ma listening ear ba, but tunda
har ta sauraresa... sure da wani abu a kasa, Ur mum isn't still okay with this
Union, grandma din ka har yanxu ba mu gane inda ta dosa ba gaskiya dama she has
always been a confusionist, Hajiya Aisha bata gidan nan yanxu haka all because
ita ma bata son auren, I caused all this Muhd, kai ma ban yi shawara da kai ba
naji ra'ayin ka, so I think raba auren nan shi xai fi komai sauki a gidan
nan" sauraronsa kawai Mujaheed yake kansa a kasa, Abba na gyada kai yace
"Gobe da safe duk xa mu hadu, ita ma Aishar xa a kirata ta xo don a
gabansu xa a yi komai...." Shi dai Mujaheed bai ce komai ba har suka isa
apartment dinsu, Abba yace "You spend the night here sbda gobe da safe xa
a kira meeting din" murya can kasa Mujaheed yace "In sha Allah"
daga haka Abba ya wuce parlonsa, Mujaheed ya wuce sama walking gently. Daren
ranan gaba daya bai yi baccin kirki ba, haka ma Imaan da kiss din da ya mata ne
ya tsaya mata cak a rai, da ta tuna sai gabanta yyi mugun faduwa kuma sai ta
mike xaune to calm her self down, ta goge bakinta ya fi a kirga amma har lkcn
ji take kamar it's happening fresh, ko Sadeeq da yyi mata wanda ya fi wnn ma
bata ji abinda take ji ba yanxu, da ta tuna Yaya ne yyi mata sai hankalinta ya
kara tashi ta fara hawaye, anya yayan da ta sani ne wannan kuwa, har xuciyarta
taji gaba daya tsoronsa ma take... Washegari misalin karfe tara na safe Ammi ta
shigo gidan ta dalilin kiran Gwaggwo da Abba yyi tun sassafe, Aunty na xaune
parlon sai Umma da duk ta fige damuwa yyi mugun mata yawa, amma da ta tuna Mujaheed ya dawo kuma tana da yakinin yau xai
yi saki sai ta samu relieve, Aunty suka gaisa da Ammi, Ammi ta nemi waje ta
xauna, Umma dai bata yarda ta kalleta ba, bayan nan Yusuf ya shigo yana rike da
makullin motarsa ya xauna ya gaida parent din nasa, Abba ya shigo parlon tare
da Daddy duk suka xauna, Daddy ya amsa gaisuwar Yusuf yana tambayarsa matarsa,
Kawu Bala ne next din shigowa nan kuma aka yi ta jiran Inna da Imaan sai
Mujaheed, Inna ta wangale kofa ta shigo, Imaan na biye da ita sanye da hijab
har kasa, kanta a kasa ta xauna kasa kusa da inda Inna ta xauna, Abba ya gaida
Inna Daddy ma ya gaisheta sannan kawu Bala sauran ma duk suka gaisheta, sama
sama ta dinga amsa gaisuwar tana kalle kallen inda xata ga Mujaheed, Imaan ta
gaida su Abba sannan ta gaida su Aunty, Umma dai ta ki yarda ta kalleta sai
kallon kofa take tana jiran shigowar Mujaheed dinta, Inna tace "Naga Ikon
Allah, toh shi ina mutumin yake, ni fa ban gama tsaftace bandaki na ba na yo
nan gaskiya Ahmadu...." Bude kofar parlon aka yi Mujaheed ya shigo suka
hada ido da Imaan da ke kallon direction din, da sauri ta sunkuyar da kai
gabanta na faduwa ta matsa kusa da Inna kamar irin xuwa yyi ya dauketa, sanye
yake cikin kananun kaya ya sauke kansa kasa bai yarda ya kalli kowa parlon ba
ya karasa kusa da Yusuf ya xauna sannan ya gaida occupant din parlon kansa a
kasa, Shiru ne ya biyo baya a parlon, Umma dai sai kallonsa take ganin wani
fresh da yyi abun sa, hakan yasa ta kara jin hankalin ta ya tashi, wato bai
damu ba kenan??? kawu Bala ya bude wajen da addu'a sannan ya kalli Abba, Abba
ya sauke boyayyen ajiyar xuciya calmly yace "Abubuwa da dama sun faru tun
bayan wannan aure da na hada ba tare da shawara da kowa ba few days ago, domin
haka nake mai kara ba ma kowa a parlon nan hakuri bisa bacin rai da aka shiga
da dai sauran su, to bayan wannan ina son jin views din ku a parlon nan akan
auren nan kafin mu san abun yi, Ni da Sadeeq da Bala ba mu da abin cewa tukun
sai mun ji naku ra'ayin in sha Allah, but before then... jiya Hadiza ta xo min
da wani batu da yake bukatar a duba sa sosai...." Inna dai sai girgixa
kafa take, Abba na kallonta yace "Inna xa mu so mu fara jin ta bakin ki a
kan auren Imaan da Mujaheed da na hada...." Inna ta katse sa da sauri tace
"Me kuwa xan ce Ahmadu, ka ji ta bakina kamar Yaya? wllh Imaan bata son
auren nan don ma ka ji, da a shiga hakkinta fa? Tun xamanin kakannin mu aka
daina auren dole, toh tunda ta ce bata so gaskiya ni ban ga amfanin auren ba,
kada in je in rasa ta a banxa, yanxun nan ya rubuta mata saki ta san inda dare
yyi mata, amma gaskiya ba wai bana son auren bane tunda duk jikokina ne, to da
wani abu ya samar min jika fa? Ko bacci fa bata yi bata cin abinci, A'a wllh ba
ruwanaa" Mujaheed dai sai kallon Inna yake kasa kasa, Umma taji kamar ta
goya Inna don murnan furucin ta, Mama Hadiza dai ko kallon Inna bata yi ba
sanin awa daya yyi kadan tace ai bbu auren da ya fi na Imaan da Mujaheed daraja
a duniya, Abba ya sauke ajiyar xuciya ya kalli Mama Hadiza yace "What did
you think Hadiza?" Mama Hadiza ta d'an yi shiru sannan cikin sanyin murya
tace "Barrister in har su yaran basu son auren nan abu mafi sauki da
kwanciyar hankali shine a raba, xumunci ba abun wasa bane, kada wnn aure ya
6ata xumunci gaskiya...." Abba ya gyada kai cikin gamsuwa bai dai ce komai
ba, can ya kalli Umma yace "Meye ra'ayin ki Rukayya?" Umma ta fara
matsar kwalla tace "Ba shi da fa'ida auren nan Alhaji, ita yarinya ba so
take ba uwar yarinya ba so take ba, toh wani aure kuma Allah na tuba...."
Abba yace "Ke ma kuma ba so kike ba koh?" Umma dai bata ce komai ba
sai matsar kwalla take, a hankali tace "Alhaji raba auren nan shine kwanciyar
hankalin kowa..." Abba ya kalli Aunty yace "Amina ur view?"
Aunty ta sauke ajiyar xuciya tace "Duk yanda Allah ya tsara dai dai ne
Alhaji, in barin auren in kuma raba auren..." Abba ya kalli Yusuf yace
"Engineer..." Yusuf ya d'an yi murmushi bai ce komai ba, Abba ya kalli
Imaan da kanta ke kasa yace "Mamana baki son auren nan ko?" Ta fashe
da kuka kamar jira take ta gyada masa kai tana shessheka, Abba ya kalli Ammi
yace "Hajiya Aisha??" Ammi ta kallesa tace "Gwara raba auren
Barrister...." Abba ya kalli Mujaheed yace "M.A...." Mujaheed ya
kallesa, ya d'an yi shirun kusan second biyar sannan yace "Baxan iya
sakinta ba Abba...." Duk aka xaro ido a parlon ana kallonsa, Imaan ta
fashe da matsanancin kuka ta fada kan Inna da ta hangame baki tana kallon
Mujaheed ita ma, Abba na kallonsa kamar yanda Daddy ma ke kallonsa yace
"Ko saboda me?" Mujaheed ya sunkuyar da kai a hankali yace
"Saboda ina son kasancewa tare da ita...." Umma ta fashe da kuka
kamar yar yarinya tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kana son
kasancewa da ita fa kace Mujaheed? Ita Safeenar fa???" Abba dai ya kasa
cewa komai sai kallonsa yake, Inna tace "Ehh lallai lalacewa ya tabbata a
duniya, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..." Mujaheed yyi kasa da murya
yace "Ku yi hakuri Abba ni baxan iya sakin Imaan ba..." Daga haka ya
mike ya fice daga parlon, kawu Bala ya sauke ajiyar xuciya yana gyada kai yace
"Allah sarki..." Inna ta mike ta fashe da kuka tace "Ahmadu duk
kai ka ja mana wannan bala'in muna xaman xaman mu, kawai ka tashi sbda tsautsayi
ya afka ma bawan Allah Sadeeq ka daura ma mahaukaci aure da jikata, wllh
Mujaheed ya fara haukacewa banda haka ko kunya babu yace baxai saketa ba yana
son kasancewa da ita, to tayi masa uban me idan sun kasance tare, ai ni naga
abinda ya isheni bai ishi Allah ba, amma ba komai da kansa xai gaji ya saketa
don wllh Imaan baxata tare gidansa ba, to ta tare tayi masa uban me?? Wllh ta
kwaso kayanta gaba daya ta dawo bangarena ni ban yadda da auren ba, dama dai
Sadeeq bai dawo bane sai in hakura ta tare gidan Mujaheed din, amma bawan Allah
ya dawo kuma yace baxai iya sakinta ba...." Tana fadin haka ta daga imaan
dake kuka kamar ranta xai fita suka bar parlon, Ammi ta share hawayen idonta ta
mike ta fita parlon Aunty da duk jikinta yyi sanyi ta mike ta bi bayanta, Mama
Hadiza ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh Allah yasa barin auren shine mafi
alkhairi" a hankali Daddy ya amsa da "Ameen" shi dai Abba ya
kasa cewa komai, Umma da ta sakko kasa tana kuka sosai tace "Toh Alhaji ya
xa ku yi da yaron da naji ance ya dawo???? An fa ce ba yin kansa bane, don
Allah ku duba lamarin nan kada ku xama kananun mutane" Kawu Bala yace
"Sae yayi hakuri, Imaan ta masa nisa, ita din matar aure ce yanxu"
Umma ta mike tana kuka sosai ta fita waje da sauri ko xata ga Mujaheed amma
babu shi babu alamarsa. Mama Hadiza ce ta kira Sadeeq ta sanar masa ya xo bayan
ta amshi lambarsa gun Yusuf, suna xaune parlon Abba har lkcn sai ga shi,
Kallonsa kawai Daddy yake don ba karamin ramewa yyi ba, duk ya fice hayyacin
sa, a sanyaye ya xauna parlon ya gaishe su gaba daya, duk suka amsa suna
kallonsa, cikin raunanin murya ya fara basu hakuri yace "I don't know what
came over me Abba, wllh ba halina bane, don Allah ku yi hakuri ku yafe min, I
am ready to marry Imaan now, Kar kuce xa ku raba ni da ita don Allah, wllh baxan
iya rabuwa da ita ba...." Hawaye cike idonsa ya kare maganar, Kawu Bala
yace "Sadeeq komai ya faru a rayuwa rubutattce ne daga Allah, Allah kuma
ya kaddara Fatima ba matar ka bace, don yanxu haka maganar da nake maka Fatima
matar aure ce...." Sadeeq ya daga kai a hankali yana kallonsa xuciyarsa na
bugawa, double ya dinga ganin parlon daga nan kuma bai kara jin komai ba bai
kara ganin komai ba a parlon.... Tun da Inna taji abinda ya faru da Sadeeq tayi
kukanta mai isarta ta buga ma ta Rasulu waya taji ko xata xo ranan, ta Rasulu
tace "Ai ki bari Asabe maganar babba ce, in sha Allahu gobe da sassafe xan
shigo nima yanxu na dawo garin wllh" Inna na matsar kwalla tace "Toh
sai kin xo, don ba lafiya ta Rasulu" daga haka ta kashe wayar ta ajiye
tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, Allah ka rufa ma Rukayya asiri
ya kasance bata da hannu a abubuwan dake faruwa, idan ko ba haka ba sai dai
wata ba ita ba a gidan nan...." Imaan dai na kwance kujera tayi lamo,
tunda taji abinda ya faru da Sadeeq kuma wai suna asibiti take kuka, da ta tuna
furucin Mujaheed sai taji gabanta yyi mugun faduwa jikinta yyi sanyi, Inna tace
"Na fa ce ki kwantar da hankalin ki sai dai Mujaheed yyi ta yawo da auren
ki a kansa amma har abada ke da tarewa shegen gidansa, to ki tare kiyi masa me
a gidan, ko kuma yyi maki me Allah na tuba? Da kansa xai gaji ya kawo maki
takardar ki ya bamu hakuri" ita dai Imaan bata ce komai ba tana jin
xuciyarta ja mata xafi. Abba ne tsaye ward din da Sadeeq yake tare da Daddy sai
Alhaji Bulasawa da wani frnd dinsa, Alhaji Bulasawa na tsaye kan Sadeeq sai
kallonsa yake duk da bacci yake, kana ganin Alhaji kasan kasan damuwa ne sosai
tare da shi, Can ya juya ya kalli Abba a karo na farko tun shigowarsu yace
"Alhaji can you pls do something about this pls, I don't want anything to
go wrong with my son, and yana da matsalar xuciya dama from the beginning,
though it's not critical but the condition he is now can make it, don Allah ina
bukatan taimakon ku ba wai don na isa ba, ku duba wannan lamarin" Da
damuwa sosai yyi maganar, Abba dai kallonsa kawai yake ya kasa cewa komai,
Daddy ya ja kujera ya xauna ya jinginar da kansa hade da lumshe ido, Abba ya
sauke idonsa yace "In sha Allah xa a duba ka kwantar da hankalin ka
Alhaji...." Alhaji Bulasawa yace "Toh na godiya" Mummy ce ta
shigo ward din tare da Mum din Mariya, ganin Sadeeq ta fara kuka ta ki karasawa
ciki, mum din Mariya ta karasa a sanyaye tana kallon Sadeeq din.... A haraban
hospital din Abba ya kira layin Mujaheed to see if he can reach him, luckily
kuwa ya shiga, Mujaheed na dagawa Abba yace "Muhd Ina son ganin ka a gida
yanxu" Mujaheed ya d'an yi shiru sannan yace "Ina Zaria yanxu Abba,
da Magrib xan shigo" Abba yace "Am expecting then" daga haka ya
katse wayar ya xauna saman kujera yana kiran Allah a xuciyarsa, Mujaheed ya
d'an yi murmushi ya ci gaba da abinda yake a office dinsa. Da daddare Imaan na
parlor xaune ta sa pepper soup din da Aunty tayi mata a gaba amma ko spoon daya
bata kai baki ba, Inna na bathroom dinta tana aikin wankewa tunda daxu da safe bata
samu ta wanke ba, Bude kofar parlon aka yi Imaan ta daga kai da sauri Mujaheed
ya shigo, tashi tayi kamar warce aka tsikara xata gudu yyi maxa ya rikota, ta
fashe da kuka jikinta na rawa tace "Yaya don Allah ka bari bana
so..." Ya juyo da ita yana kallonta, ganin yanda hawaye ke xuba idonta ya
xaunar da ita ya xauna gefenta a hankali yace "Listen to me now
Imaan..." Taki yarda ta kallesa har sannan jikinta rawa yake, murya can
kasa yace "Kema kina son in sake ki koh?" Ta kallesa ta fashe da
matsanancin kuka tana gyada masa kai, shiru yyi na kusan second goma, a hankali
yace "Toh shikenan tunda haka kike so, but I don't have paper and pen
here, mu je waje sai in dauka a mota in rubuta takardar in baki..." Daga
haka ya mike, ita dai tayi shiru tana kallonsa amma hakan bai sa ta daina
hawaye ba, ya kalleta yace "Toh mu je mana, ba dai haka kike so ba??"
Mikewa tayi a hankali ta dau Hijab dinta ta saka sai kuma ta tsaya, yace
"Mu je...." slowly ta fara tafiya ya bi bayanta yana murmushi, ita
dai Imaan tafiya kawai take yana biye da ita yana kallonta har ta fita gate,
satan kallon part din su yyi sannan ya fita gate din shi ma.....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
82.....
Imaan ta tsaya jikin motar sai dai bata yarda ta kallesa ba,
ta gefen ido ya dinga kallonta ya bude driver seat ya dauko takarda da biro,
jinginar da takardar yyi jikin motar ya fara rubutu a kai, satan kallansa tayi
ganin rubutu yake kan takardar ta ji gabanta ya fadi, lkci daya ta sunkuyar da
kanta tana jan fingers dinta, ya gama rubutu a takarda ya linke yana kallonta yace "Hope you
are now happy?" Bata yarda ta kallesa ba ta gyada masa kai kawai, ya d'an
yi shiru sannan yace "But I want to let you know one thing Imaan before
handing this paper over to you" ita dai kanta na kasa, jin yyi shiru bai
fadi one thing din da yace xai gaya mata ba ta kallesa taga kallonta yake, da sauri ta sauke kanta kasa xuciyarta na
bugawa, ya bude motar ya shiga a hankali yace "Xagaya ki shigo ki ji
abinda xan gaya maki..." Ta girgixa kai tace "Ka gaya min a nan"
yace "I want to say it while looking at u in the eyes, so that baxai yi
fading memory din ki da wuri ba, ko da ba ma tare you won't forget it Imaan,
it's almost a piece of advice..." Ta hade rai tace "Ni dai ka bani
takardar in wuce" ya girgixa kai yace "Baxan baki ba idan baki shigo
kin saurareni ba, I assure you wannan maganan da xan maki wataran xai maki
amfani" Kallonsa tayi sai dai bata ce komai ba, kuma bata xaga ta shiga
motar ba, yace "Duk lkcn da kika shirya jin abinda xan gaya maki I will
give you ur divorce content, but not today anymore..." Daga haka ya ja
kofar motar xae rufe, ta fashe da kuka ta rike kofar da sauri tace "Toh ka
rubuta min abinda xaka gaya min a wani takardan ka bani gaba daya mana" Ya
wani hade rai yace "Cinye ki xan yi idan kika shigo motar? Kinsan Allah
baxan baki takardan nn ba idan baki shigo kin saurareni ba" Dauke kai tayi
kamar me naxari sai kuma ta xaga a hankali ta isa daya side din, d'an murmushi
yyi ya rufe side dinsa ya jinginar da kansa da kujera, tana xagayowa ta bude
front seat ta shiga ta xauna ta d'an saci kallonsa taga murmushi yake, still
tayi da farko, sai kuma ta sake kallonsa, lkci daya ta yunkura xata sauka motar
ya wani fixgota ya jawota ya rufe kofar gbam ya sa ma motar lock, a mugun
tsorace ta dinga jijjiga kofar tana cewa "Meye haka Yaya??" Bai ko
kalleta ba ya tada motarsa ya bar layin, kuka ta dinga yi tana kallonsa a
rikice tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Yaya don Allah ka bari,
where are you taking me to, plss ka tsaya ka bude min mota in sauka, wayyo
innaa...." Driving kawai yake bai ko kalleta ba, ta fixgosa cikin kuka
tana jijjigasa tace "Don Allah ka bude min in sauka Yaya, ina xaka kai
ni??" da hannu daya ya mayar da ita kan kujera ya wani hade rai ba tare da
ya kalleta ba idonsa a kan titi yace "Kika sake rikeni sai na falla maki
mari..." Ba karamin tsorata tayi ba jin babu wasa tattare da shi, hakan
yasa bata sake rikesa ba ta dinga kuka tana kiran Inna tana bubbuga kujeran
motar, Sun yi nisa sosai ya daura mata well folded takardan hannunsa kan
cinyarta yace "As I promised, here is it...." Kuka kawai take tana kallonsa
kamar ranta xai fita, yace "Dauki takardan
ki bude ki karanta, ba saki kike so ba, to gashi na rubuta maki"
kin ta6a takardarn tayi, ya juya ya kalleta fuskar daure, da sauri ta dau
takardan hawaye na xuba idonta tana shessheka, yace "Open it now"
hannunta na rawa ta fara warware takardan tana kallon abinda ya rubuta kamar
hakw.... "Xan sake ki on one condition, the condition is... Xa ki haifa
min yara guda biyar duk masu kama da ke, duk yaron da yyi kama da ni bbu shi a
cikin lissafin, just 5 of ur look alike...." Ji tayi gabanta yyi wani
mugun faduwa ta sake takardar tana kallonsa, wani murmushi yyi yana kallon
titin gabansa yace "Yes... Sai ki shirya conceiving daga daren yau"
ta hade kai da gwiwa ta fashe da kuka da karfi tana kiran Inna, driving kawai
yake yana murmushi, wani hotel ya kai su, yana parking harabar hotel din ya
juya yana kallonta, har lkcn kuka take sosai, ya bude motar ya fita ya xagayo
ta inda take ya bude seat din yana kallonta yace "Come down..." Kin
dago kanta tayi bata kuma fasa kukan da take ba, xaro ido tayi ta dago da sauri
jin daukarta xai yi ta hadiye kukan da take cikin rawar murya tace "Wllh
xan sakko Yaya, wllh xan sakko" Ya daure fuska yace "To sakko"
ta hadiye abu da kyar ta fito motar tana shessheka tana bin haraban hotel din
da kallo gabanta na bugawa tayi kasa da murya pleadingly tace "Don't
Forget from the beginning kai ka koya min daukan ka matsayin yayana, kar ka
manta a matsayin Yaya na dauke ka tun ban san kai na ba, why will u bring me to
a hotel all of a sudden plss?" Yace "To show u ni ba yayanki bane,
and after today I don't think xa ki kara kirana yayan ki" xaro ido tayi
tana kallonsa, ya kulle motar xai kama hannunta ta fixge da sauri ta kara
fashewa da kuka, kallonta ya tsaya yi sai kuma yace "Daukar ki kike son
inyi kenan koh?" Ta girgixa masa kai cikin tashin hankali tace "A'a
yace "To mu je" tafiya ta fara yi toward direction din entrance din
hotel din yana biye da ita, tana waigowa, he couldn't just stop smiling, amma
da ta juyo sai ya hade rai, kujera ya nuna mata bayan sun shiga reception din
hotel din yace "Sit" kin xaunawa tayi tana hawaye, ya kama hannunta
ya tafi da ita gun kujerar ya xaunar da ita yana kallonta, hade kai da gwiwa
tayi tana jin kamar ta kurma ihu ko xata ji dadi, ya juya ya koma gun
ma'aikatan babban hotel din, bayan kusan minti goma ya dawo inda take ya duka
dai dai kanta yace "Tashi mu je...." Ta daga kai da sauri cikin rawar
murya tace "Don Allah Yaya kayi hakuri ka mayar da ni gida Ina rokon ka
don Allah ba don ni ba" D'aga ta yyi ya kama hannunta suka wuce sama xuwa
room din da aka basa don kar ma ta ja masa attention din mutane, a door ta
tsaya bayan sun shiga ciki, ya kulle kofar ya cire makullin jiki yana kallonta
calmly yace "Ke da gida kuma sai deal din mu ya tabbata, I mean 5
kids...." Durkusawa tayi on her kneels tana kuka sosai tace "Don
Allah ba don ni ba ka mayar da ni gida Yaya xa a dinga nemana fa" Ya
durkusa gabanta shi ma a hankali yace "A neme ki bayan kina tare da mijin
ki??" Kallonsa ta dinga yi ko kiftawa babu kamar yanda shi ma yake
kallonta... Inna ce xaune parlon Daddy ta yafa xaninta a kai, kai kace
bayerabiya ce, fuskar nan nata a tsuke, Daddy da shigowarta parlon tana rafka
uban sallama ya sa ya fito daga daki ya xauna yana kallonta yace "Ina yini
Inna?" Ta kallesa tace "Lafiya lau Bukar... Kana ji na??" Daddy
yace "Ina jin ki?" Tace "Toh... Ka san dai ni na haife ka, kai
kuma ka haifi Imaan koh??" Shiru Daddy yyi bai ce komai ba, a fusace tace
"Ka min shiru Bukar ko ba haka bane?" Yace "Haka ne" tace
"To madalla, Bukar yau da ba don kai ba wllh ba bbu uwar da na hada da
wannan yarinya Imaan, kawai ni dai nasan na haifeka kai kuma Allah ya baka ita,
to ya xan yi tunda d'an da na haifa ya haifeta, ya xan yi nace??" Shi dai
Daddy kallonta kawai yake, Rai bace ta ci gaba "Yanxu ace Imaan xata bar
bangarena baxata jira in gama tsafatace bandakina in fito ba tace min to Inna
ni na tafi? sbda walakanci sai ta tsallake kamar tababbiya tayi wucewarta ga
farfesun da wannan mata Amina tayi mata ta bar min shi a bude a parlor duk
dattin duniya ya fada kai, sannan ta bar min kofa a bude domin ba ma sauro
daman shigowa su cuce ni, wllh raina yyi mugun bacewa don ni ba haka na ma
Iyayena ba kai ma kuma ba haka ka min ba, to wacece kuma imaan fisabilillahi
xata min haka, a wangale fa ta bar min kofar Bukar kaji abinda yafi min ciwo
kenan, ni nace lallai dole sai Imaan ta xauna bangarena dama?? To wllh ta fito
ta tafi ta kwashe tsummokaranta dake kwambodi na kada in watsa su titi ba
ruwana, ni xata kawo ma raini ta walakanta, dama tun da yamma naga take
takenta, Banda Ahmadu da ya jaza mana wnn bala'i na aura mata katon d'an sa
uban me dama xan ci da ita a sashina??" Daddy dake ta kallonta yace
"To ai bata xo nan ba..." Inna tayi shiru ta kalli kofar dakinta, sai
kuma tace "Bata nan kuma?" Daddy yace "Bata xo nan ba"
mikewa Inna tayi da mamaki ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, part din
Abba ta wuce, tana daga tsaye bakin kofa tana kallon Aunty da ta mike ganinta
tace "Amina yarinyar nan bata yo nan ba?" Aunty tace "Wai
imaan?" Inna tace "ita" Aunty tace "A'a bata xo nan ba
gaskiya" Inna ta gwalo ido ta shigo parlon da sauri tace "Bata xo ba
kuma Amina?" Jin muryar Inna Abba ya fito daga parlonsa, Inna ta nufe sa
da sauri tace "Ahmadu ban ga imaan ba tun daxu wllh" Abba yace
"Imaan kuma?" Inna da har jikinta ya fara rawa tace "Ehh na
shiga wanke bandaki na fito naga babu ita a parlor sai farfesu" Su Maimoon
suka fito tare da Maryam da tayi hijira bangaren Inna tun ran Friday, Aunty na
kallonsu Maimoon tace "Ku tafi can apartment dinsu ku duba ko tana
can" fita suka yi parlon gaba daya, Abba na kallon Inna ganin yanda ta
rikice yace "Bari a dubota can bangaren su, amma ina xata je dama
Inna" Inna ta bi bayansu Maimoon da sauri, tana tsaye bakin kofa sai xaxxare
ido take tana jiran fitowarsu, Maimoon ce ta fara fitowa tace "Bata nan fa
Inna" Wani salati Inna ta rafka da karfi sai kuma ta fashe da matsanancin
kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, bata ciki fa ku ka
ce???" Su Abba da Aunty duk suka fito tsakar gida Mama Hadiza ma ta fito
bayan Maryam ta je sama ta gaya mata abinda ke faruwa, Daddy dai na tsaye
balcony dinsa yana kallon mahaifiyar tasa, Inna ta tsaya dai dai tsakar
compound din ta daura hannu a kai ta dinga rusa kuka tana cewa "Na shiga
uku Allah ka dubeni kada Bukar ya kullace ni har gobe kiyama, Ina imaan xata
shiga da tsakar daren nan jama'ah, wllh wanke bandaki nake na fito naga babu
ita sai kwanon farfesunta, na shiga uku jama'a ku taimakeni kada a dinga cewa a
parlona Imaan ta 6ata...." Mama Hadiza ta nufe ta da sauri tace "Haba
Inna meye haka kuma, ce maki aka yi Imaan din 6ata tayi? Haba don Allah"
Cikin kuka Inna tace "Idan ba 6ata tayi ba to Ina take Hadiza?? Kafff
gidan nan an duba bbu ita babu alamarta fa, Wllh da ba a bangarena take ba bbu
abinda xai dameni sai dai a daure Ahmadu tunda shi yyi mata auren dole, yanxu
kuwa ai ni xa a daure tunda kowa yasan a bangarena take, da wani bakin xan ma
'yan sandan bayani idan an tafi dani?? Kuma duk aka tashi magana dama cewa xa
ayi parlon Inna ta 6ata, to ina dalili a sa ni a bakin duniya Hadiza???? Don
Allah ku min rai a nemo ta kada in shiga uku, wannan ba karamin magana bane
wllh" Ta kuma rushewa da kuka har da durkusawa kasa tana salati, Abba dai
ya kasa cewa komai haka ma Daddy da ya makale a Balcony dinsa, Inna ta kara
mikewa tana kuka sosai ta nufi gate tana cewa "Duk Ahmadu ne ya jaza mana
fitinar nan gaskiya idan wani abu ya sami jikata xan rufe ido in mance ni na
haifeka Ahmadu" Umma da shigowarta gidan kenan daga gidan Hajiya Saude ta
makale parking space tana wurwurga ido jin wai ba a ga Imaan ba, Inna na kallon
mai gadi a waje ta fixgosa tace "Ilu kaga fitar Imaan?" yace
"A'a ban gani ba Baaba..." Inna ta wani xaro ido ta turasa kawai ta
fice gate din ta saka kai gaba sai babban titi tana salati tana rusa kuka, Mama
Hadiza ce ta bi ta tana kiranta amma Inaaa... Karfe goma saura Mujaheed ya mike
daga xaunen da yyi gefen gado tun shigowarsu yana kallon football a tv na bango
dake manne a dakin hotel din, Imaan dai har lkcn tana durkushe inda take tun
daxu, banda axaban ciwo babu abinda kanta da duk joints dinta suke mata amma ko
xama ta ki yi, ga kuma bacci dake fixgarta, ta dai gaji da kuka da rokonsa da
take tayi tsit ta xuba ma saurautar Allah ido, satan kallonta Mujaheed yyi
ganin idonta a lumshe bacci ya dauketa a yanda take, ya dau remote ya kashe tvn
ya mike a hankali ya nufeta, dukawa yyi ya dagota ta farka a rikice xata fasa
masa ihu ya rufe bakinta a jikinsa, jikinta ya dau rawa tana kokarin kwace
kanta bai ajiyeta ba sai saman gado, xata mike ya hade rai, calmly yace
"Lie still..." Kai kawai take gyada masa a tsorace, ya dinga kallonta
ko kiftawa babu, kamo hannunsa tayi tana girgixa masa kai pleadingly tace
"Don Allah Yaya ka maida ni gida kila ana ta nemana wllh" Ya xame
hannunsa still looking at her yace "Kila don kina ganin ki a kadunan yasa
kike tunanin xan maida ki gida, Allah ya kai mu gobe da safe, I will eraze that
thought off ur mind" Ta dinga kallonsa xuciyarta na bugawa, mikewa yyi ya
nufi switch din dakin ya kashe wutan, ta mike xaune da sauri gabanta na faduwa
tana kallonsa cikin duhu, a hankali tace "Yaya..." D'an Murmushi yyi
ya nufi kan gadon, tuni ta sauka ta tsaya tana kallonsa cikin duhun xuciyarta
na bugawa....
*Naji kuma xan iya, though it's short... Thanks for the
prayers*
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
83......
Mujaheed bai yarda ya kalleta ba ya ciro wayarsa a aljihu ya
xauna saman gadon ya kunna wayar, ita dai tana tsaye tana kallonsa gabanta na
faduwa, number yyi dialing ya jingina da gadon, Safeenah dake kwance saman
gadon hajiyarsu an cire mata drip kenan har ta fara bacci ta mike xaune da kyar
tana kallon wayarta dake gaban mirror yana ring, Hajiya Baturiya tace "In
ma xa ki rabu da wayar nan kiyi baccinki ki rabu da shi..." A hankali tace
"Toh idan shine fa Anty?" Hararanta Hajiyan Marafa ta dinga yi daga inda
take xaune, yayarta Sajida tace "Wlh idan kika ja ma kanki wani ciwon
Safeenah iyaka namu muyi ta maki fatan samun lafiya, me aka yi aka yi Mujaheed
da xa ki nemi hallaka kan ki a kansa? Mutumi da har yau bai kira ki ba balle ki
san abinda ake ciki, wa ya sani ma ko da saninsa aka yi auren ma tunda uwarsa
ce kan komai" Safeenah ta kalleta da sauri tace "A'a wllh bai san da
auren ba, nasan shima hankalinsa ne ya tashi shi yasa muka ji sa shiru"
Hajiyan Marafa tace "Na rasa wannan bala'in ni dai, haka kawai ki dauki
namiji ki sa a rai kina neman ja ma kanki wani ciwon??" Safeenah ta sauka
saman gadon da kyar ganin basu da alamar dauko mata wayar, tana isa gaban
mirror din ta xaro ido tana kallon wayarta tace "Wllh shi ne
Mummy..." Da sauri ta daga wayar kafin ya katse ta kai kunne, kawai sai ta
fashe da kuka sosai, Mujaheed yyi shiru yana sauraronta na few seconds, can
yace "Let me assume baki son kiran nawa kenan..." Da sauri tace
"Me yasa ka kashe wayar ka all this while Mujaheed, me yasa baka yi
tunanin halin da xan shiga ba a wannan lokacin, don Allah ka ce min karya ne
baka min kishiya ba, kace min karya ne ni kadai ce matar ka Mujaheed, I can't
imagine my self sharing you with any lady wllh baxan yarda ba, ni ce kadai
matarka a duniya" Ya daura kansa saman pillow dake kusa da shi yyi kasa da
murya yace "Yanda kika samu labarin auren nan haka nima na samesa
Safeenah, I know nothing about it, ban san komai a kan auren nan ba..."
Kuka take sosai tace "Wllh Mujaheed na isheka duniya da lahira me xa kayi
da wata matar kuma, kayi min rai kada ka min kishiya, ka barni ni kadai a gidan
ka, na isheka duniya da lahira, don Allah kace min babu xancen auren nan kuma
plsss..." Bai san lkcn da yyi murmushi ba a hankali yace "Marriage or
no marriage Safeenah you still remain my first, ke ce matata ta farko, then why
worry?" Imaan dake tsaye tana kallonsa tunda ta fahimci da warce yake waya
ta wani daure fuska ta juya masa baya tana jin wani irin haushi a xuciyarta,
kuka kawai Safeenah take kamar ranta xai fita tace "Kana nufin da gaske
kenan auren na nan Mujaheed, Kuma wai da cousin dinka da ta raina ni?? Nooo
plss wllh baxan iya sharing mijina da ita ba, I can never, you are meant for me
alone, tell ur parent u don't need a second wife plss, ban rage ka da komai
ba..." Murmushi yyi sosai yace "Thank God you know I don't need a
second wife, then why disturb ur self?? I just have to obey my parent that's
all" Juyowa Imaan tayi a hankali tana kallonsa, yace "I will call you
tomorrow, get set before 9:00am xan xo" daga haka ya katse W
wayar yana satan kallon Imaan, missed calls din Mama Hadixa
ya gani kusan shidda, tun yana waya yake jin shigowar kiran nata, murmushi yyi
ya shiga gun text message ya tura mata text kamar haka, "Am sorry I did
what is wrong Mama, but I think this the only way out don baxan iya sakin Imaan
ba" yana tura mata ya kashe wayar gaba daya yana kallon imaan dake tsaye
har lkcn tana kallonsa, kwanciya yyi saman gadon ya lumshe ido, ta goge hawayen
dake sauka idonta har lkcn tana kallonsa, da ta tuna abinda yace ma Safeenah
sai taji wasu hawayen sun taho mata, tana ta tsaye har bayan kusan minti
talatin, jin kafafuwanta sun gaji ga bacci da ta fara ji ta durkusa a hankali
tana ta6a tiles din dakin taji sanyi, ta dauke hannunta ta mike tsaye tana
kallonsa, bayan kusan minti biyu ta xauna gefen gadon a hankali tana satan
kallonsa, jin bai motsa ba duk da ba ganin fuskarsa take ba ta gane kilan yyi
bacci, kamar me tsoron gadon ta kwanta a edge ta juya masa baya ta rufe ido, a
hankali ya juya yana kallonta bayan few minutes, mirginawa yyi side dinta,
cikin bacci kawai taji sa kusa da ita, Bude ido tayi a tsorace xata mike ya
riketa, cikin rawar murya tace "Wayyo Yaya plss ka bari, meye haka"
yace "Waye yayanki?" Jikinta ya dau rawa tana girgixa kai tace
"Ba kowa wllh" yyi kasa da murya drawing her closer to himself yace
"Who am I to you now?" Hawaye ne ya shiga sakko mata ta ki cewa
komai, ya daura forehead dinsa kan nata ta rufe ido da sauri, yace "Talk
to me now" a hankali tace "Yaya kai na fa ciwo yake min da bayana tun
daxu...." ya kwantar da kanta a hankali kan chest dinsa cikin sanyin murya
yace "Tell me... Me yasa kike son in sake ki bayan destiny da ya hada mu
Imaan? Baki tunanin kilan dama we where meant for each other, isn't this great?
everything just happened all of a sudden, so fast, baki tunanin wannan wani
al'amari ne babba, why kike so na sake ki?" wasu hawaye masu xafi suka
dinga xubo mata ta lumshe idonta ta ki cewa komai, a hankali yace "Talk to
me pls" ta bude idonta tace "Saboda kai na dauke ka a matsayin yayana
ne..." ya d'an yi shiru sannan yace "Kenan ba aure tsakanin mu?"
Ta girgixa kai cikin rawar murya tace "Akwai...." Yace "Toh me
yasa kika bar sa a matsayin babu a xuciyar ki?" Tace "Saboda Ina maka
kallon yayan da muka fito ciki daya, I grew up looking at u as my blood
brother, I've neva tot of living together with you as..." Sai kuma tayi
shiru, ya d'an yi murmushi yace "Ni kuma ban taba maki wannan kallon ba,
Ina maki kallon cousin dita ce da xan iya aure ta haifa min kyawawan yara masu
shagwaba da son jiki irin nata, masu dogon hanci da karamin baki irin nata,
masu asthma da ....." Dukansa ta yi a kirji kamar xata yi kuka tace
"Ni bana sooo...." Yana murmushi ya rungumeta sosai cikin sanyayyan
muryarsa yace "In sha Allah our kids will be more than healthy..." ta
dago da sauri ta kallesa tace "Ni fa baxan xauna da kai ba as my husband,
I just can't... Bayan ga matarka da ka gama ce ma kai baka son auren"
Kallonta kawai yake ko kiftawa babu, xuciyarsa ya dinga raya masa yyi mata
abinda yyi parlon Inna jiya amma kuma kawai sai ya ji nauyin yin hakan, saketa
yayi, yyi kwanciyarsa yana murmushi yana tunanin ranan da xai nuna mata shi ba
yayanta bane, soon but not in a hotel room, xamowa kasa tayi, tana turo baki
tana kallonsa, daga karshe dai ta duka nan kasa ta kwantar da kanta saman gado
a haka bacci ya dauketa, mikewa yyi jin alamar tayi bacci ya xaga ya dagata
sama ya kwantar da ita saman gadon ta riko hannunsa cikin muryar bacci tace
"Yaya I am feeling cold..." kwanciya yyi kusa da ita ta shige
jikinsa, yyi murmushi yana kallonta ya cire mata hijab din jikinta keeping her
more closer to himself, gaba daya scent dinta ya cikasa, ya lumshe ido trying
to force him self to sleep, but the thought of imaan by his side, sooo close...
as his sunnatic wife couldn't let him, gashi da yyi yunkurin gyara kwanciyarsa
just to maintain sai ta kara shige sa, and he wish everyone was happy with this
surprise marriage, da ya fi kowa murna da farin ciki a duniya, duk ya tuna
Ummarsa sai ya ji gabansa ya fadi, don tun da aka daura auren bai yrda ko na
second daya sun hadu ba. Sai kusan karfe biyu da wani abu na dare bacci ya
daukesa, duk da sanyin da yyi yawa a dakin bbu me jin hakan a cikinsu.... Da
asuba kiran sllh ya farkar da Mujaheed, ya kalli Imaan ya gyara mata kwanciya
xai mike ta rikosa, kunna kananun wutan dakin yyi yana kallon fuskarta yaga
bacci take, xai tashi ta kara rikesa, murmushi yyi ya ja dogon hancinta hakan
yasa ta bude ido a hankali, ya kai hannu goshinta ta wani hade rai tana
kallonsa ta mirgina da sauri daga wajen, sauka yyi saman gadon ya shiga
bathroom, tashi tayi ta jawo hijab dinta ta saka ta kashe Ac din dakin ta koma
can karshen gadon ta kwanta tana tunanin lkcn da ta hau saman gado ta kwanta,
yana fitowa ya kalleta yace "Baxa ki yi sllh ba" shiru tayi bata ce
komai ba fuska daure, ya fita dakin, sai a sannan ta mike ta wuce bathroom din,
har ya dawo masallaci tana xaune saman darduman da ta gani a dakin tana azkar,
ya xauna gefen gadon yana kallonta, ita dai bata yarda ta kallesa ba, ya dawo
kusa da ita a hankali yace "Good morning wife" Bata fuska tayi tace
"Ni ba wife din ka bace" Ya wara ido yace "Ohh don ban nuna maki
ke wife dita bace jiya da daddare koh?" Dauke kai tayi ta ki cewa komai,
ya gyada kai Yana murmushi yace "Xan yi maganin ki, abinda dare da
yawa" Yana fadin haka ya mike ya hau saman gadon ya kwanta hade da lumshe
ido. Karfe bakwai da wani abu suka bar hotel din, Imaan dai sai kallon hanya
take tana jiran ta ga inda xai kai ta, ganin sun dau hanyar kano ta xaro ido a
tsorace tana kallonsa kamar xata yi kuka tace "Yaya don Allah ka bari,
where are you taking me to plss, wllh nasan ana ta nemana gida ka mayar da ni
don Allah" Yana kallon titi a hankali yace "Kaf gidan nan yanxu bbu
mai iko da ke, so they are all supposed to know that kina wajen mijin ki su
xuba mana ido kawai, su da xa mu dawo masu da cute kids in sha Allah, sai mu ba
Umma daya mu ba Ammi biyu mu ba Aunty daya sai mu tausaya ma Inna ita ma mu
bata guda daya duk da lalata mana ita xata yi yanda ta lalata ki...."
hawaye Imaan ta fara yi tana kallonsa tace "Don girman Allah ka mayar da
ni gida Yaya, stop this joke" gently yace "You think I am joking ko?
Xa ki sha mamaki kam" Ta dakatar da kukan da take tana kallonsa ganin he
is so serious, Bai kalleta ba driving kawai yake da d'an gudu, tayi kasa da
murya tace "Don Allah kar ki min haka Yaya, kar ka raba ni da
Ammina..." sae kuma ta fashe da kuka, yace "Idan ban raba ki da ita
ba ynxu ae ita xata raba ni da ke, ni kuma baxan yarda a raba ni da ke ba coz I
want to live with my lil sis in one roof" Tafiyar kusan minti hamsin yyi
ya shiga garin Zaria, Imaan dai gaba daya she is shock ganin da gaske fa
Mujaheed yake, wani babban gida yyi Parking ya fito yana rike da mukullin gidan
ya bude gate din ya dawo motarsa, ya shiga gidan yyi parking a space na mota
hudu dake babban compound din ya kashe motar ya fito yana kallonta, bin gidan
kawai take da kallo kusan a tsorace, ya rufe side dinsa ya xaga ya bude inda
take yace "Come down" ta hade hannunta tana girgixa masa kai tace
"Am begging you ka mayarda ni gida don Allah Yaya, Kar ka min haka"
sakko da ita yyi daga motar ya rufe yana rike da hannunta ya nufi entrance din
shiga gidan ya sa makulli ya bude, parlor ne babba, kuma bbu abinda bbu a ciki
amma duk komai ya d'an yi kura, ya kulle kofar parlon ya sa makulli sannan ya
wuce stairs, Imaan ta durkushe wajen jikinta a sanyaye ta ma kasa kukan, lkci
daya ta mike tana xaro ido da karfi tace "Yayaaa" sai kuma ta nufi
stairs da gudu tana ci gaba da kwala masa kira, Mujaheed ya fito daki da sauri
yana saukowa stairs suka kusa cin karo, rungumesa tayi jikinta na rawa tace
"Kamar na ga wani abu yana tafiya wllh Yaya, I saw an insect" Jan ta
yyi xuwa sama ya bude bedroom yace "Tafi ki yi wanka na hada maki ruwa"
a tsorace tace "Ni dai Yaya wllh kamar cockroach na gani fa" yyi
murmushi ya kama hannunta xuwa bathroom yace "Toh muje in raka ki kiyi
wankan" bin bayansa ta dinga yi tana kallon kasa ko xata kara ganin wani,
yace "Toh cire kayan" Hijab dinta ta cire ta ajiye gefen gado, ta
fara kokarin cire dogon rigar baccin jikinta, shi dai kallonta kawai yake har
ta fara dage rigan, sai kuma tayi still ta kallesa, ganin yanda yake kallonta
tayi wani kara ta sauke rigar kasa ta durkushe tace "Wayyo Yayaaa bana son
haka" Yana murmushi ya durkusa shi ma yace "Baki son me??" Bata
yarda ta kallesa ba ya mike ya tafi gefen gado ya xauna yace "Toh ki shiga
kiyi Ina jiran ki a nan" mikewa tayi ta shige bathroom din ta rufe kofa
har da sa makulli. Fita dakin yyi ya ya dawo parlor, ya bude kofa ya fita ya
kulle ta waje sannan ya bar gidan, few shoppings yyi ya siyo har da breakfast
ya dawo gidan, ya ajiye ledojin hannunsa a parlor ya wuce sama ya bude dakin,
tsaye ya ganta jikin window wayarsa kare a kunnenta idonta sha6e sha6e da
Hawaye, jin an bude kofa ta juya tana kallonsa ta katse wayar tana shessheka,
ya tsaya nan bakin kofar ya dinga mata wani kallo, a hankali ta dinga share
hawayen idonta, ya karasa cikin dakin ya fixge wayar yana duba screen din ya ga
number Daddy, barin wajen take so tayi ya fixgo hannunta fuska daure yace
"What did you tell him??" Ta fashe da kuka tace "Ni dai Yaya don
Allah kayi hakuri ka mayar da ni gida, ni bana son ka baxan xauna da kai
ba..." Call duration din kiran ya duba yaga kusan 7 mins, ya hade rai
sosai yace "I asked what did you tell him??" Ta make masa kafada
cikin rawar murya tace "Ni nace masa ya xo ya daukeni baxan xauna a nan da
kai ba, nace masa ni bana sonka" Kiran Daddy na ya shigo wayar, ta goge
idonta da sauri xata amshi wayar ya mata wani irin kallo ya juya ya fita ta bi
sa da ido hawaye na sauka idonta, Yana fita dakin ya ji ya ma kasa daukan
kiran, ganin ya kusa katsewa ya daga a hankali ya kai kunne amma ya kasa cewa
komai, Daddy yace "Are you there Imaan?" Mujaheed yyi kasa da kai yace
"Ina kwana Abba" Daddy yace "Lafiya lau Muhd, ya ku ke"
Mujaheed yace "Alhmdllh" Daddy yace "But why did you take her
with you without informing anybody Muhd?" Mujaheed ya d'an yi shiru sannan
a hankali yace "Ku yi hakuri Abba, amma nobody will let me go with her..."
Daddy yace "Ita kuma dayar matar taka fa? Kar ku shiga hakkinta, you know
what is right from wrong..." Mujaheed na sauka stairs murya can kasa yace
"In sha Allah xata dawo yau Abba" Daddy yace "Toh maa sha Allah,
ba sai kun dawo anytime soon ba, Allah ya ba ku xaman lafiya..." Mujaheed
yyi murmushi yace "Toh Ameen nagode Abba...." Daddy yace "Tace
kuna Zaria koh?" Mujaheed yace "Ehh" Daddy yace "To maa sha
Allah, hope there is no problem?" yace "Sure Abba" Daddy yace
"And what about ur work?" yace "Xan dinga tahowa daga nan din, I
took two weeks leave..." Shiru Daddy yyi kafin yace "But I don't like
that, wajen yyi nisa" Mujaheed yace "Sati uku kawai xa mu yi nan
Zaria" Daddy yace "Ohk that's better Allah ya kai mu, if you have any
problem you let me know" Mujaheed yace "In sha Allah" daga haka
Daddy yyi masa sallama ya katse wayar. Mujaheed ya xauna saman kujera ya lumshe
ido hoping everybody will accept the marriage that way, footsteps da ya ji sama
ya sa ya daga kai ya kalleta, ya bude daya daga ledojin da ya shigo dasu yace
"Breakfast" Ko kallonsa bata yi ba fuska daure, ya mike ya wuce sama
yana rike da wayarsa ya bar ta tsaye a parlon. Abba ne xaune parlon Inna sae
Daddy da Mama Hadiza, Inna na xaune saman tabarma tayi tagumi ido duk ya kumbura
ta fashe da wani sabon kuka tace "Ni dai tunda uwata ta haifeni ban taba
ganin tantiri irin Mujaheed ba, me nayi masa a rayuwa banda kyautatawa da
bautar da nayi da shi da xai saka min da sharri?? Me na masa xai sa in kasa
bacci jiya na je tolet ya fi sau hamsin, sannan na kwana kan darduma sbda
tashin hankali, wai ashe shi ya shigo ba tsoron Allah ya dauke min jika ya
gudu, to wai ma a kan me xai dauketa yarinya nace bata isa aure ba, me xai je
yyi da yar mutane? a gaskiya duk inda ya tafi da ita a je a dawo min da jika ba
ruwana, ko kuma ni a min kwatancen wajen in tafi da kai na in daukota, ita
Imaan din har nawa take xai gudu da ita sbda ya lalace, kaiii Ahmadu baka yi
sa'a ba gaskiya, ban ta6a ganin tantiri irin Mujaheed ba, shiryawa xan yi yanxu
a kai ni gidansa ya ga barbadin bala'i sannan in juyo tare da Imaan tunda ba
uban wani ya haifa ma Bukar ita ba" tana fadin haka ta mike xata shige
daki ta dauko mayafi, Mama Hadiza ta bi ta da kallo tace "Toh ai basa
gidansa inna" Inna ta juyo da sauri tana kallonta tace "Basa gidansa?
To ina ya kai ta?" Mama Hadiza tace "Sun dai yi waya amma bai fadi
inda suke ba" Inna ta xauna kan kujera baki bude tace "Ya xa ayi ya
ki fadin inda suke, ni kuma da suka bari nan fa???" Mama Hadiza ta saci
kallon Daddy da ke ta kallon uwar tasu, da mamaki Inna da ta kasa rufe baki
tace "Shi Mujaheed din mance wahalan da nayi masa yyi xai tafi da Imaan
banda ni?" Bbu wanda dai ya tanka su cikinsu. Mujaheed ya gama gyara gidan gaba daya ya
goge duk kuran ko ina ya dawo fess, ya kalli agogo dake nuna karfe sha daya
saura ya wuce sama ya bude bedroom dinsa ya ga Imaan kwance tana bacci tun
bayan da ta sha drugs da ya siyo mata bayan ya tilastata tayi breakfast take
baccin, bathroom ya shiga ya sake yin wanka ya fito ya shirya cikin kananun kaya
ya dau makullin motarsa ya juya yana kallonta, karasawa yyi gun gadon ya xauna
gefenta ya dukar da fuskarsa dai dai nata, a hankali ta bude ido jin saukan
numfashi a fuskarta, ya ja hancinta murya can kasa yace "I am going out
now but I will be back soon lil sis" Ganin bacci ne sosai idonta yyi
pecking goshinta ta lumshe ido bata ce masa komai ba, mikewa yyi ya fita dakin
ya kulle mata kofa sannan ya fita ya kulle gidan ta waje ya hau motarsa ya bar
gidan, hanyar kaduna ya dauka.... Direct Marafa ya nufa bayan ya shiga garin
kaduna, yana isa gidansu Safeenah yyi parking a kofar gida ya fito daga cikin
motar ya shiga cikin gidan, bbu kowa parlon sai Sajidah, daga sama har kasa ta
kallesa ta ci gaba da danna wayarta, ya xauna saman kujera ba tare da ya sake
kallonta ba ya ciro wayarsa ya kunna, sannan yyi dialing number Safeenah, tana
dagawa yace "Ina parlor ki fito" Safeenah dake shiryawa ta fito wanka
ta xaro ido tana kallon Uwarta dake waya, Safeenah ta dade bata ji farin cikin
da take ji ba a lkcn, ta xauna gefen gado bayan ta sa kayan tana kallon
Hajiyarsu dake waya tana cewa "Ehh dama shine abu na farko da nake son ayi
mata, Ehh sunanta Rukayya, xa mu yi waya anjima" daga haka ta katse wayar,
Safeenah ta xaro ido tace "Hajiya Mujaheed ne fa a parlor" Hajiyan
Marafa tace "Mujaheed Kuma? To me ya xo yi??" Safeenah ta bata rai ta
mike ta nufi gaban madubi ta feshe duk jikinta da turare sannan ta dau karamin
gyale ta fita, tana shigowa parlor ganinsa a xaune ta nufesa da sauri ta fada
jikinsa ta rungumesa gam, sai kuma ta fashe da kuka tace "I've missed you
a lot Mujaheed, don Allah ka xo ne mu koma gidanmu mu ci gaba da xamanmu mu
kadai??" Yace "Tafi ki hada kayan ki" ta xaro ido tace "Da
gaske??" Yace "I am waiting" gaba daya su Hajiya Baturiya dama
sun kwaso kayanta daga gidan Mujaheed bayan abinda ya faru, ta mike da sauri ta
tafi daki tana kallon Uwarta tace "Mummy yace in hado kayana wllh"
Hajiyan Marafa tace "Babu inda xa ki je sai an gama aikin da ake
yi..." Safeenah ta fashe da kuka tace "Ni dai wlh Mummy ki Bari in
bisa gida fa xa mu wuce ya ma saki yarinyar Ina ji, don Allah ki bar ni mu
je" Hajiya Marafa tace "Cewa nayi ki bari sai an gama aikin da ake yi
tukun, ke ana kokarin kwatar maki yan ci kin kasa ganewa sbda son miji"
Safeenah tayi kamar xata yi kuka tace "Ni dai Hajiya tafiya xan yi daga
karshe sai in dawo idan an gama aikin, amma ni kam da baku bata kudin ku ba ni
kadai na isa Hajiya Rukayya a duniyar nan, wllh sai na rabata da d'anta, Auren
ma da aka masa Ina jin babu shi yanxu" daga haka ta fita xuwa dakinta ta
hau hada kayanta a jaka, cikin few minutes ta gama ta jawo jakar downstairs,
Mujaheed ya dinga kallonta har ta iso parlon, Sajida ta dinga mata wani kallo
tana girgixa kafa, Mujaheed yace "Hajiya fa?" Safeenah ta koma sama
da sauri ta shiga dakin uwarta tana murmushi tace "Hajiya wai ki fito ku
gaisa" Hajiya Marafa tace "Bai kai wannan matsayin ba, banda ma kin
nace ina mu Ina hada xuri'a da Rukayya? Waye bae san Rukayya da abinda take yi
ba, in sha Allahu ta ja ma kanta abinda ba shikenan ba tunda har ni tayi ma
haka, xan kuma nuna mata mu bama xama da kishiya, Ana gama aikin da ake dama
xan tako gidan da kai na" juyawa Safeenah tayi ta fita dakin tana cewa
"Bayan nace maki babu auren yanxu wace kishiya kuma, ai sai dai mu gwada
mata hankali kawai..." Tana dawowa parlor ta kalli Mujaheed tace
"She's in the bathroom mu je kawai dear" mikewa yyi ya nufi kofar
fita ta bi bayansa tana kallon Sajida tace "Sai mun yi waya Aunty
Sajida" ko kallonta Sajida bata yi ba har ta fita, sai da suka shiga mota
Mujaheed yace "Zaria xa mu je" Safeenah ta xaro ido cike da farin
ciki tace "Ae ya fi dear nah, gwara mu yi nisa da gida kawai, after some
months sai mu dawo kaga bbu wanda xai kara tada wani maganar, wllh hakan ya fi,
har naji hankali na ya kwanta sweetheart" shi dai bai ce mata komai ba ya
tada motarsa don duk hankalinsa yyi kan Imaan da ya bari tana bacci....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
84....
_And I dedicate this particular page to the entire members
of_ *Murmushin Novels* group....
I Khaleesat Haiydar is wholeheartedly saying a big fat *Thank
you* to the entire members of the above👆🏻 named
group... nagode nagode, Allah ya bar kaunar, I really appreciate it sisters,
Allah ubangiji ya kara maku budi da daukaka, ya bar xumuncin mu, ya sa ku gama
da duniya da iyaye lafiya, Allah ya saka da alkhairi, Billah Ina yin ku har
raina, sannan.... _Inna na gaisuwa tace
sai kun xo mata kwalema da share share a fitar da duk dattin da suka makale
mata kada su cuceta, sannan tace in maku tuni da tsoron Allah a duk inda xa ku
kasance duba da yanda duniyar ta lalace yanxu mutane ba tsoron Allah, domin
kuwa lkcnsu tsoron Allah ake kaca kaca ba wasa, don haka ku ji tsoron Allah a
duk inda xa ku kasance, sannan ku xamo masu tsafta domin sace xuciyoyin masu
house_... Lol, gaskiya I am happy da abinda ku ka min jiya, I love u all... 😍🥰❤️
And my lovely fans that partronized my book happily without
thinking twice, ku ma ina yin ku har raina wllh, Ina son ku, _Inna tace kuma
tana gaishe ku, kuma ku rike Allah, to wa gare ku da xa ku rike dama banda
Allahn? Sannan ayi ta ma iyaye biyayya domin a rabu lafiya da su kamar yanda
Ahmadu da Bukar ke mata biyayya..._ lol
Mujaheed na gama parking a compound ya kashe motar ya bude ya
fito, gate ya tafi ya kulle ya dawo, Safeenah da ta fito motar tana mika ta
sauke ajiyar xuciya tace "Har hankalina ya kwanta dear, i prefer here than
kaduna unlike kwanaki da muka xo naji duk ban son garin, yanxu kam I like it
here..." Shi dai bai ce mata komai ba ya nufi entrance din gidan rike da
takeaways din da yyi a hanya, tace "But wait, foodstuffs din fa Dear, ka
bar su a booth, my bag is there also..." ba tare da ya juyo ba yace
"we will take them in later..." Bin bayansa tayi suka shiga gidan, ya
xauna saman kujera bayan ya ajiye ledojin abincin hannunsa ya jinginar da kansa
da kujeran don duk ya gaji sosai, ko kadan shi dama bai son driving me nisa,
Safeenah na murmushi ta tsaya bayan kujeran tana massaging shoulders dinsa a
hankali tace "Bari in je sama in hada maka ruwan wanka baby, nasan ka
gaji, shi sa nace ka bani driving din inyi ka ki...." Shi dai bai ce komai
ba yana sauraronta, tana gama fadin haka ta cire mayafinta ta ajiye saman
kujera xata wuce sama ya bi ta da kallo yace "A'a kar ki damu baxan yi
wanka ba yanxu" ta juyo tana kallonsa tace "Oh really, amma idan kayi
ai xaka fi samun relieve ae dear, anyway mu je sama in maka tausa toh"
cike da shagwaba ta fadi hakan, bai ko kalleta ba ya mike ya dau ledan abinci
daya yace "Ni fa I am okay, I just need rest...." Ta langwabar da kai
tace "To mu je ka kwanta my dear...." Bai ce komai ba ya nufi stairs,
jin tana biye da shi ya tsaya a staircase din sannan ya juya yana kallonta yace
"Tot you said you are hungry ga abinci can kuma kin bari downstairs"
ta tabe baki tace "No apple din da na ci daxu a hanya ya isheni, nima
hutawa xan yi, all my body is just aching" Bai ce komai ba ya ci gaba da
tafiya tana biye da shi har suka isa corridor din dakuna hudun dake jere,
tsayawa yyi dai dai kofar dakin da yake amfani da, ya d'an saci kallonta ganin
dakin ta nufo yace "You use the other room Safeenah" Da mamaki take
kallonsa, sai kuma tace "Why? Beside tunda muke xuwa gidan nan na taba
amfani da wani dakin banda wannan da muke using tare? Baka taba ce min inyi
amfani da wani daki ba ai" Ya juya yana kallonta da kyau yace "Ohk we
are not sharing it this time around, you choose from any of the other rooms,
this is a master bedroom" wani kallo Safeenah ta dinga yi masa daga sama
har kasa, can tace "What's wrong with you Mujaheed, why are u behaving
this way?? dama mun ta6a raba daki tunda muka yi aure da kai? Ko kuma wani
sabon walakancin ka tsiro?" Ya shafa kansa murya can kasa yace "Plss
Safeenah I am tired bana son magana, I told u I need rest, idan baxa ki shiga
any of the rooms ba ki koma parlor" yana fadin haka ya shige dakin ya sa
makulli, Safeenah ta wani xaro ido tana kallon kofar da mugun mamaki, ta fi
minti daya tsaye tana tunanin wannan kuma wani sabon walakancin Mujaheed ya
kirkiro mata? Tabdi ai ko wahala kawai xai daukar ma kansa don maganin sa xata
yi ba na wasa ba, da wannan tunanin ta sauka downstairs a fusace xuciyarta na
tafarfasa, don sosai ranta ya baci... Mujaheed ya ajiye ledan hannunsa yana
kallon Imaan dake bacci har lkcn, takawa yyi ya isa kusa da ita ya xauna
gefenta, a hankali ya kai hannu forehead dinta ya ji temperature dinta normal,
Bude lumsassun idonta tayi tana kallonsa,
sai kuma ta dauke kai a hankali ta matsa daga kusa da shi ta juya masa
baya, yace "Kinyi sllh?" Kin basa amsa tayi ta turo baki, idonsa ya
sauka kan darduman da ke shimfide dakin alamar tayi sllhn, yace "Tashi ki
ci abinci" ta hade rai tace "Ni baxan ci ba" yace "Koh??"
K'in cewa komai tayi, ya sa hannu ya daga ta, ko ba a fada masa ba yasan next
reaction dinta hakan ya sa ya maxa ya juyo ta ya rufe bakinta ya hade rai sosai
yana kallonta, ta 6ata fuska kamar xata yi kuka cikin sanyin murya tace
"Ni dai ka maida ni gun Ammina" Mikewa yyi ya dagota ya dawo da ita
kasa kan darduman da ta bari a shimfide fuska daure yace "Ga abinci nan ki
dauka ki ci" ganin kallon da yake mata ta jawo ledan a hankali hawaye na
taruwa idonta ta bude ta ciro take away din shinkafa da kazar da ya siyo mata
sai table water da five alive drink, spoon ta dauka ta debi shinkafar ta fara
ci a hankali, shi dai kallonta kawai yake ko kiftawa babu, can yyi murmushi ya
tafi kan gado ya kwanta hade da lumshe idanuwansa, bayan kusan minti biyar ya
bude ido to see if she is eating the food, kazan abincin ya ga ta dauka tana ci
as if her happiness depend on it don ba cin wasa take ma kazan ba, suna hada
ido ta juya da sauri bayan ta cire naman a baki, murmushi Mujaheed yyi ya mike
xaune ganin ta ajiye kazan yace "Wa kika ajiye ma?" Ta turo baki tace
"Ni baxan ci ba" kallon bakin da take turo masa kawai yake.... Inna
ce xaune kan kujera a parlonta tana saka gogaggun kayanta a sabon Ghana must go
din da ta sa Mai gadi ya siyo mata aka bude kofa hade da sallama, Daga kai tayi
tana amsa sallaman ta ajiye set din riga da xanin hannunta tace "Sannu da
xuwa Ta Rasulu" Ta Rasulu ta cire Hijab din jikinta ta linke da kyau ta
ajiye tace "Ke kuma ina xa ki da gana mas gau?" Inna ta tabe baki
tace "Kayana nake hadawa ta Rasulu, sam bani da 'ya yan nuna ma duniya,
shine naga gwara kawai in tafi gidan Bala in xauna, duk me xa a min a can xan
fi shanyewa tunda nasan ba jinina yyi min ba" Ta Rasulu ta xauna tace
"Me kuma suka maki 'ya yan??" Inna tace "Fisabilillahi ta Rasulu
ina laifina don nace duk inda xa a nemo min Mujaheed a nemo min shi in ji
dalilin da xai dauke min jika ya gudu kamar d'an fashi, ta Rasulu babu lefe
babu sadaki babu komai kawai ya samu tsaleliyar yarinya a bagas ya tafi da ita
ko uban meye ma'anar haka oho, wato ga sadaka an basa, to wllh ubansa Ahmadu ma
yyi kadan balle shi sa karan kada miya, Jikata tafi karfin ayi sadaka da ita,
kawai yaro tantiri dai ya shigo min gida ina wankin bandaki ya arce min da jika
tsakar dare kawai sbda yana shan wiwi, to ta Rasulu shan wiwin nasa kuma sai ya
kare a kai na? Don wannan ni ya ci ma mutunci ba kowa ba wllh, snn ace ayi
shiru a xuba masa ido yaje ya lalata min jika? Kinga Hadiza, Ahmadu da Bukar
duk gantalallu ne Allah na tuba, sam bbu wanda ya dau wani kwakkwaran akshan a
kan batun nan, yanda kika san abun kirki Mujaheed yyi ko kuma shi halitto min
jika, idan kika bibiya ma duk sun san inda ya tafi da ita marasu imani, daxu fa
har gidansa naje a unguwar dosa basamuden da ya ajiye bakin get yace min ai
gidan fanko ne bbu kowa ciki, ni dai ba yarda ba na shiga na gama xagaye na
naji shiru bbu alamar kowa shine fa na fito na dawo gida na sa aka siyo min
jaka nake xuba kayana, haka kawai yara sun gama rainani sun maida ni shashasha,
tsakanin Imaan da Mujaheed fa gantalallen kaza, ni dai ban ta6a ganin ya siyo
mata ko da tsinke ne ya bata ba kamar dai yanda wnn yaro d'an albarka Bulasawa
ke yi, to wannan mutumi xan dau jika in ba ma, wllh baxata sa6u ba, maxa ya
dawo min da Imaan ba yanxu xata tare ba...." Ta Rasulu na girgixa kai tace
"Toh shi Mujaheed ko dai hau ne ya fada masa xai aikata wannan barna haka?
Ina ya tafi da yar mutane bai bada hakokkin aurenta ba, haka kawai ya cuce ta
yyi mata ciki a banxa" Inna ta rushe da kuka tace "Imaan ina ta isa
daukan ciki ke kuma ta Rasulu, da kuwa ya cuceta, duka duka nawa take? Ai
kamata yyi a xaunar da shi a karanta masa illan hakan, ina laifin ta d'an kara
gwabi, to ga dai Safara'u har yau shiru sai dai ta ci tayi kashi, ban gane kan
abun ba" Ta Rasulu tace "Yanxu dai kiyi hakuri ki maida kayan nan,
tafiya ba taki bace...." Inna tace "A'a gidan Bala xanje gwara inje
suyi ta taka ni baxai min ciwo ba don bbu abinda na hada da su na dai san
uwarsu kishiyata ce ta aure min miji ban ji ba ban gani ba" Ta Rasulu tace
"Asabe nace maki bbu xancen tafiya, ga abun al-ajabi na xo da shi..."
Inna tayi shiru tana kallonta, Ta Rasulu tace "Toh dai asiri mummuna aka
lafta ma Bulasawa yace ya fasa auren Imaan...." Inna tayi tagumi tana
kallon ta Rasulu a hankali tace "Sai aka ce maki wani la'anannen ne yyi
asirin Ta Rasulu?" Ta Rasulu ta tabe baki tace "Toh me shi a gidan
nan yake tare da ku wllh, ba a dai ambato min suna ba, amma a nan me shi ke
kwana yake tashi, amma ke wa kika xarga Asabe?" Inna tace "Allahu
Akbar, Rukayyar Ahmadu ce" Ta Rasulu tace "Nima ita na raya"
Inna ta bude baki tayi mitsi mitsi da ido tayi shiru tana kallon Ta Rasulu, can
tace "Ikon Allah, wato kaikayi ne ya koma kan mashekiya ba shakka, kin
lura duk ta fi kowa daga hankali a auren da aka daura da Mujaheed???" Ta
Rasulu tace "Wllh kuwa, biri yyi kama da mutum, ni naga ma duk ta rame ta
xabge tayi baki, yanxun nan mun hadu da ita xan shigo ita xata fita, wllh duk a
birkice take, sai naga ma kamar hadin bauta tayi" Inna ta gyada kai tana
wani murmushi tace "Toh Alhmdllh da wnn magana ya fito fili, amma kinsan
wani abu? Wllh yanxu a idon Ahmadu, Bukar da Hadiza bbu me tada fitina a gidan
nan sai ni, nice dai fitinanniya gantalalliya" Ta Rasulu tace "Ke ma
xai wllh ai wannan magana barinsa xa mu yi a ciki mu yi ta kallon ikon Allah,
iyaka a tashi tsaye sosai da nema ma yarinyar nan Imaan tsari...." Inna
tace "Ke da kika san komai, ai bbu wanda xai fara gwaleni a kan xancen nan
sai Bukar, shi Ahmadu dama baxai ce komai ba amma ni nasan kallon jarababbiya
yake min baxai dai yi magana ba, ita kuma wannan mata Hadiza sai dai ta xuba
min idanu, a takaice dai Bukar ce min xai yi in daina haka shi ba ruwansa, to
ya xan masu Ta Rasulu? To wllh tunda Rukayya ta ma jikata haka sbda bakin ciki
da hassada tata ta kare duniyar nan gaba daya, kuma kwanaki kadan ya rage mata
gidan d'a na wllh, ke dai kawai ki xuba min ido ni kadai na isheta sai ta
gwammace kida da karatu, aure jikokina kuma mutu ka raba, ni nasan da tasan
auren xai dawo kan Mujaheed da bata san yanda tayi ta hana ba, kuma mutuwa xata
yi a banxa idan tace xata raba auren nan...." Ta Rasulu tace "Atoh,
kuma fa har yanxun ba wai saduda tayi ba, ance min tana nan tana kokarin raba
auren nan, da kyar fitan da tayi yanxu ba gun bokanta xata ba, wllh sai mun
tashi tsaye an yi kokarin nisantar da Imaan sosai daga sharrinta, in sha Allahu
in dai da ran mu sai ta fito da bakinta tana tona kanta, kada ki kuskura ko da
wasa ki gaya ma ko Hadiza tunda lalacewa ta sami yaran naki, mu dai da muka san
komai sai mu yi ta kan mu" Inna tace "Dama ba gantalallen da xan gaya
ma, iyakata da su su ban kudi in rufa ma jikata asiri, sannan in sha Allahu a
gaban Bukar asirin Rukayya xai tonu shi da baya ta6a ganin laifinta..." Ta
Rasulu tace "Toh ynxu ya isilin bawan Allahn nan Bulasawa?" Inna ta
marairaice kamar xata yi tace "Wai daxu aka sallamesu asibiti inji Ahmadu,
ni dai xan shirya in siya lemo ko kwaya biyar inje har gida in duba sa wllh,
dama can Imaan ba matarsa bace bani da rabon cin kaji da xabi dai" tana
magana tana matsar kwalla, Ta Rasulu tace "Kya ci da kudin ki" cikin
rawar murya Inna tace "A'a ki bari Ta Rasulu, wani hanin ga Allah baiwa
ne, kuma ni da Bulasawa mutu ka raba har gidansa xan dinga xuwa kai masa
xiyara...." Daddy ne tsaye jikin motarsa kofar gidansu Ammi, ya fi minti
goma yana jiran fitowarta, jin an bude gate ya daga kai har ta fito, ta
gaishesa, yana kallonta yace "Ban san ki da haka ba Aysha, wannan ba halin
ki bane, why are u behaving this way pls?" Bata tanka sa ba, yace "Ko
ba don ni ba don barrister ya kamata ki hakura haka nan, kar ki manta jininsa fa
ya aura ma Imaan, sannan don't forget yayana ne shi din, jinin nasa kuma d'a na
ne, beside all this Aysha Mujaheed bai yi deserving haka daga gare ki ba, wai
kin mance wanene Mujaheed ne?" Ammi da hawaye ya kawo idonta ta girgiza
kai tace "I am thinking of my daughters future, ban san rayuwar da xata yi
tare da kishiya da uwar miji warce bata sonta duk da kai ba yarda da rashin son
da take mata kake ba, kila sai ranan da xaka gani a xahiri, nasan abinda imaan
xata iya jurewa da wanda baxata jure ba, this is too much for her, ga condition
dinta...." Daddy ya sauke ajiyar xuciya yace "Baki yarda da kaddara
ba kenan, Haba Aysha sai kace ba musulma ba, where is ur faith? All you need to
do is wish ur daughter a peaceful and better married life, plss ki shiga kiyi
ma gwaggwo sallama we are going home now" Girgixa masa kai tayi tace
"No ka tafi gobe in sha Allah xan dawo" yace "Sure?" Tace
"In sha Allah" yace "Toh Allah ya kai mu, we will talk later on
phone" daga haka yyi mata sallama ya shiga mota ita kuma ta wuce ciki.
Mummyn Sadeeq ce xaune makeken parlonta tare da aminiyarta Hajiya Batula,
Hajiya Batula tace "To ke wa kike tunanin xai aikata hakan Hajiya"
mahaifiyar Sadeeq Hajiya Khadijah, tayi murmushin karfin hali tana gyada kai
tace "Ni nasan wacece ita tunda aka ce daga family din yarinyar take,
sarai nasan wacece, kuma Billahil azeem xata san ita ce silan heartbreak din
d'a na" mikewa tayi ta nufi window fuskarta a murtuke, da mamaki Hajiya
Batula tace "Ba shakka, amma koma wacece ita din gaskiya ta xama abar
tausayi yanxu, ta rasa wanda xata ma asiri sai Abba? Don me bata bar asirin iya
'yar su ba kadai, Wannan shine biggest mistake of her life, don da ta sani da
bata fara ba" Mummy dai murmushi kawai take, aka bude kofar dakin duk suka
juya, Sadeeq ne ya shigo dakin, Uwarsa ta dinga kallonsa don ba karamin rama
yyi ba, yyi kasa da kai ya gaida aminiyar mum din tasa cikin sanyin murya
sannan ya xauna saman kujera yace "Mummy, Ina son xan tafi Uk...."
Katse sa tayi tace "Kaje kayi me a UK Sadeeq?" A hankali yace "I
need rest Mum..." Shiru tayi tana kallonsa, lkci daya hawaye ya kawo
idonta ta dauke kai tana kallon waje ta window.... Mikewa xaune Mujaheed yyi jin ringing din
wayarsa, ya dauka yana kallon Screen din, Call din Umma ya gani, ya ji gabansa
ya fadi sosai, yyi ta kallon screen din har ya katse, ta sake kira, kasa kin
dagawa yyi, ya daga a hankali ya kai kunne yyi shiru, ko sallama babu tace
"Mujaheed??" Yyi kasa da murya yace "Na'am, Ina yini Umma"
Tace "Kana Ina ne?" Ya d'an yi shiru sannan yace "Ina gida"
tace "Wani gidan?" Nan ma yyi shiru, cikin tsawan da ya ji har
tsakiyar kansa tace "Baxa ka bani amsa ba ina tambayarka?" A hankali
yace "Gidana Umma" strictly tace "Wani gidan naka a ciki?"
Yace "Zaria" Tace "Toh" tana fadin haka ta katse wayar
kitt, ya dinga kallon phone din xuciyarsa na bugawa, Imaan dai na xaune kan
darduma har lkcn ta gama jujjuya shinkafar takeaway din gabanta ta bar sa,
kazar ma tunda ya kamata tana ci ta ki ci kuma, sauka yyi saman gadon ya tafi
ya bude kofar dakin ya fita, Safeenah na xaune parlor tana waya da Hajiyar su,
murya can kasa tace "Haukatar da ita kuma Mummy, A'a gaskiya... idan aka
yi haka ai bata kwashi takaicin da ya kamata ba, a dai yi wani abun daban
Mummy" Safeenah tayi shiru tana sauraron uwar tata, sai kuma tace
"Mummy na fa ce maki babu auren nan wllh, tunda muka xo bai ce min komai a
kai ba, sun raba da suka ga bai so...." jin taku a stairs ta katse wayar
da sauri, ta gyara xama ta wani hade rai tana kallon tv dake aiki, Mujaheed ya
shigo parlon yana kallon ledan abincin da bata ta6a ba ya dauka yace
"Ain't you eating?" yi tayi kamar bata ji sa ba, ya tafi kitchen ya
wanko plate ya dawo parlon, ido hudu
yayi da Imaan dake sakkowa stairs a hankali tana kallon Safeenah dake
xaune idonta a kan tv har lkcn....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
85......
Ganin direction din da Mujaheed ke kallo bbu ko kiftawa
Safeenah ta juya da sauri tana kallon wajen ita ma, sake remote din hannunta
tayi a hankali ta mike tana kallon Imaan da idanuwanta kamar xa su fito, da
mugun mamaki da shock take kallon nata, lkci daya ta juya cikin tashin hankali
tana kallon Mujaheed xuciyarta na bugawa kamar xai fito, walking slowly ya
karasa cikin parlorn ya xauna saman kujera ya bude takeaway din dake cikin leda
ya diba abincin a plate ya ajiye sannan ya daga kai ya kalli Safeenah dake
kallonsa har lkcn with full shock, sai kawai ta fashe da wani matsanancin kuka jikinta
na rawa ta nufesa ta rikosa tace "Tell me, what is she doing in our home
Mujaheed? Why is she here? Wa take nema??" Juyawa Imaan da ta hade rai
tayi xata koma sama, Mujaheed yace "Don't go back, dawo nan" k'in
tsayawa tayi tana ci gaba da tafiyar ta da sauri, cikin daga murya yace
"Imaan!!" ta tsaya fuska daure amma ta ki juyowa, har ranta taji
xafin ganin Safeenah, ga wani faduwa da gabanta yake yi, Mujaheed ya mike tsaye
yana kallonta yace "I said come
back here Imaan..." Safeenah na jijjigasa cikin tashin hankali sosai tace
"Mujaheed answer my question, ka gaya min me yarinyar nan take a gidana,
ka gaya min nace, wa take nema??" Imaan ta juyo walking slowly ta dawo
parlon tana kallon Safeenah fuska daure, Safeenah ma ta dinga kallonta xuciyarta
na bugawa har lkcn tana rike da Mujaheed, Imaan ta murguda mata baki ta dauke
kai tana jiran jin kiran me Mujaheed yyi mata, Safeenah ta nufeta da sauri tana
huci bakinta na rawa tace "Me kike yi a gidana??" Imaan ta rungume
hannunta tace "Abinda kike yi, and point of correction ba gidan ki bane ke
kadai, nima nan gidana ne...." Wani kara Safeenah tayi kamar mahaukaciya
jikinta na rawa tace "Karya kike wllh, karya kike, nan gidan mijina ne,
gidana ne nan, baki da space a gidan nan yarinya, this is my husband's
house" Imaan tayi wani murmushi tace "Koh? To sai ki tambayi mijin ki
dalilin da ya sa ya kawo ni nan" Sai kuma ta saci kallon Mujaheed da ya ki
kallonsu gaba daya, murya can kasa tace "And here is also my husband's
house...." Bata rufe baki ba Safeenah ta wani cakumota da karfi jikinta na
rawa, Mujaheed ya taho da sauri ya janye Imaan yana ma Safeenah wani mugun
kallo, ya fixgota shi ma cikin tsawa yace "What is this u are doing? Baki
da hankali ne xaki fixgota haka? Ciwo xa ki ji mata?" Safeenah na kallonsa
with shock ta fashe da matsanancin kuka ta xube kasa tace "Na shiga uku na
lalace, Mujaheed kayi ma Allah ka gaya min me take a gidan nan Plss, tell me
what brought her to my home" Wani dogon tsaki Imaan ta ja tana hararanta
xata bar wajen Safeenah ta mike yi kanta gadan gadan, cikin xafin nama Mujaheed
ya fixgota for the second time yana mata wani kallon da ya sa hanjinta ya kada,
strictly yace "This should be ur last attempt in this house, I will neva
take it likely with you idan kika sake maimaita hakan, Me kike son yi mata
da??" Safeenah na kuka sosai tace "Wllh baxan xauna da yarinyar nan
ba mutuwa xan yi, ka taimakeni ka gaya min me take yi a gidanmu, wayyo Allah na
na shiga ukuuu..." Mujaheed ya saketa, calmly yace "Aure ya kawota
gidan nan, ita din xabin mahaifina ne gareni, kamar yanda ke kike xabin
mahaifiyata, at that time I've neva for once say no to my mother na karbi auren
ki hannu bibbiyu, the only difference btwn my marriage with you and that of
Imaan is that, ke naki I was aware and present during the nikka.... Don haka
kamar ynda ban ma Mahaifiyata musu a kan auren ki ba, to baxan ma mahaifina
musu a kan auren Imaan ba, and I am assuring you that in sha Allah xan xamo mai
adalci tsakanin ku, i will try my very best, but Imaan matata ce yanxu kamar
yanda kike matata...." Imaan dake tsaye tana jiran ganin abinda Safeenah
xata mata, ta kara jan wani dogon tsaki ta wuce sama kamar xata tashi sama,
Mujaheed ya bi ta da ido, Safeenah ta sulale kasa ta rushe da wani kuka da
karfin gaske, cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi
raji'un, na cuce kai na, don Allah Mujaheed kar ka min haka don kaga Ina sonka,
babu mai kishiya cikin 'yan uwana wllh tllh, plsss kar kace min kishiyata ce
ita, I can't stand it, xuciyata bugawa xata yi wllh...." Dukawa yyi yana
kallonta smiling calmly yace "Kin yi breaking record..." Tun da Imaan
ta koma daki ta kasa xaune ta kasa tsaye, ta kalli kofa ya fi a kirga, tsayawa
tayi jikin window ta fara kukan da ita ma bata san dalilinsa ba, wani tukuki
taji xuciyarta na mata, tana ta tsaye har bayan kusan minti goma, aka bude
kofar dakin, juya baya tayi da sauri ta goge idonta tana kallon waje fuska
daure, ya rufe kofar yana kallonta yace "She is my wife imaan, aside that
kuma ta girme ki sosai, kada ki sake mata tsaki, that's very disrespectful of
you...." juyowa tayi tana kallonsa da wani expression, ya karasa kusa da
ita kafin yace komai, cike da masifa tace "Wllh sai na mata din, da ta
girmeni sai kuma ta haifeni? Ni ina ruwana da ita a gidan nan xaka ce min she
is ur wife ko da nace maka ban sani bane? What's my business with that??"
Sai kuma ta fashe da kuka ta nufi bathroom da sauri ya rikota yace "No I
am only reminding you Imaan" fadawa jikinsa tayi tana kuka sosai tace
"Ni wllh Yaya bana son gidan nan, I don't want to stay here, na tsane ta
da gaske, baxan xauna ina ganinta ba kullum, I don't like her, bayan ta gama
xagi na saura kadan to dokeni kuma kaje kana ta bata hakuri tun daxu fa.."
tana fadin haka ta kara rushewa da kuka har da shessheka tana shigewa jikinsa,
rungumeta yyi yana sauraronta da mamaki, sai kuma yyi murmushi a hankali yace
"Toh ya kike son ayi?" Cikin rawar murya tace "Ni dai mu tafi
wani gidan kuma kar ta bi mu wllh..." Yace "Kin hakura xa ki xauna da
ni kenan yanxu?" Still tayi da farko, lkci daya kuma ta janye jikinta daga
nasa da sauri ta juya masa baya tana imagining abinda ta fada, murmushi kawai
yake yana kallonta, ta turo baki tace "Ni baxan xauna da kai ba" daga
haka ta wuce cikin bathroom da sauri ta rufe kofar, juyawa yyi ya fita dakin
still smiling. Lallashi bbu irin wanda Mujaheed bai ma Safeenah ba domin a
rayuwarsa ta duniya ya tsani kukan mace, kukan ma wai sabida shi, amma kamar
yana dada tunxurata, da ta tuna biye ma Umma ya ja mata wannan masifa da tashin
hankali sai ta kara rushewa da kuka tana tunanin me xata ma Umma taji dadi a
ranta, gani take kamar ta kusa farkawa da mummunan mafarkin nan da ke neman
fasa mata xuciya, sai lkcn ta san meye kishin abinda kake so, gashi ta kasa ko
da kiran Hajiyarta ta sanar mata ai fa kishiya na nan daram, tsoro take kada
tace mata ta dawo gida don har xuciyarta take jin baxata iya rabuwa da Mujaheed
ba har abada, rabuwa da Mujaheed mutuwar ta kenan a ganinta, ta rikosa tana
kuka sosai tace "Wllh ina sonka Mujaheed, Ina son kasancewa da kai amma
baxan iya xama da yarinyar nan ba idan ma record din gidanmu xan yi breaking ba
da wannan yarinyar ba gwara ka saketa ka auri wata na yadda, Allah da gaske ban
son ganinta ko na second daya, yanxu kana nufin kun hada gado da yarinyar
nan?" Mujaheed ya saketa ya mike yace "Baki son ganina kenan idan
baki son ganinta, don she is me" Bai jira sauraronta ba ya shige toilet
din dakin yin alwala, har ya fito kuka take tayi dai dai a kasa kamar warce
uwarta ta mutu, ya nufi kofa ya fita dakin, bedroom din sa ya nufa ya bude a
hankali yana kallon ciki, fitowar Imaan kenan daga bathroom ta dauro alwala ita
ma, ta wani hade rai ta dau hijab dinta ta sa tana shimfida darduma, cire
makulli yyi ta ciki ya kulle dakin da makullin sannan ya tafi masallaci bayan ya
saka makullin a aljihu. Mujaheed na dawowa masallaci ya shiga dakin da Safeenah
take, kamar yanda ya bar ta haka ya dawo ya sameta, Yana tsaye dakin yace
"Baki ma yi sllhn ba kenan?" Banxa tayi masa tana kuka sosai, ya tabe
baki yace "Xa mu fita in siyo mata few wears coz gaba daya kayanta na
gida" Safeenah ta mike da sauri tana xaro ido tace "Xaku fita fa kace
Mujaheed??? Har xaka fara walakanta ni kenan kake nufi, xaku fita kake ce min
fa" yace "You heard me right, we are going to the market, kuma don't
forget cikin one week dinta muke..." Kallonsa kawai Safeenah take kamar
idanuwanta xasu yo waje xuciyarta na bugawa, yace "Her one week started
from yesterday" Bai jira cewarta ba ya fita dakin ya kulle kofar, imaan na
xaune saman darduma ta hade kanta da gado ya sameta, Yana kallonta yace
"We are going out now" Ta dago da sauri tana kallonsa tace "I am
going no where plss" Yyi shiru yana kallonta, sai kuma yace "Ohk dama
shopping xamu je ki yi, bari mu je da Safeenah tayi maki kawai" Mikewa
tayi da sauri tace "Tayi mani a kan me? What's my business with her? Ko
ita xata sa kayan da xata min shopping??" Bata jira cewarsa ba ta nufi
kofa ta fice, murmushi yyi ya bi bayanta, waje ya sameta tsaye jikin motar, ya
bude lock din motar ta bude front xata shiga suka yi ido hudu da Safeenah dake
lekosu ta window tana kuka kamar ranta xai fita, Imaan ta ji dadin hakan har
ranta, ta kalli Mujaheed sai kuma ta nufe sa da sauri tace "Toh ai baka
gama saka buttons din ba" Bata jira cewarsa ba ta fara buttoning din masa
shirt dinsa, kallonta yake da mamaki, ta turo baki taki yarda su hada ido har
ta gama sannan ta juya ta koma gun motar ta shiga ta rufe tana satan kallon
windown dakin Safeenah tana d'an murmushi, Mujaheed ya bude gate sannan ya dawo
ya shiga driver seat yana kallonta murya can kasa yace "Kema bari in gyara
maki Hijab din ki" Bai jira cewarta ba ya jawota kusa da shi yana gyara
mata hijab duk da bbu abinda ya samesa, xata turasa sai kuma ta tuna kila
Safeenah na nan tana kallonsu, hakan yasa ta tsaya ta matsa kusa da shi amma
bata yarda sun hada ido ba, unexpectedly taji bakinsa cikin nata, ta xaro ido a
mugun tsorace xata kwace kanta ya ki saketa. Siyayya ba na wasa ba Mujaheed yyi
ma Imaan, duk ita ke daukan kome taga yyi mata, tun daga inner wears, dogayen riguna,
kananun kaya, amma fa gaba daya fuskarta a daure yake sbda abinda yyi mata
daxu, da ta tuna sai ta goge bakin, sau dayawa sai ta dau kayan da yyi mata
kyau sai ta juya gunsa da sauri tana nuna masa kayan tace "Yaya wannan xai
min kyau koh??" sai kuma ta tuna sabon relationship dinsu, a hankali take
juya masa baya tana turo baki bar wajen fuska daure, shi dai sai dai yyi
murmushi yana biye da ita, bayan sun gama da boutique suka shiga shopping mall,
gun turarruka ta nufa shi kuma ya tafi gun kayan shayi don siya masu, Tana
cikin daukan turare suka yi ido hudu da farida dake duba wani turaren a wajen
ita ma, xaro ido imaan tayi da mamaki ta nufeta da sauri tace "Anty
Farida" Rungume ta Farida tayi cike da murnan ganinta tace "Imaan, what
are you doing in Zaria?" Imaan na murmushi sosai tace "Ni da Yaya ne
Aunty Farida, dama Zaria gidan ki yake?" Farida da lkci daya fara'arta ya
d'an ragu, a hankali tace "Ehh nan nake, me kika xo yi nan din ke?"
Lkci daya fara'ar da ke fuskar imaan ya bace ita ma jin tambayar da ta mata,
sai kuma da sauri tace "Lahh ni da Yaya ne Aunty, bari in kirasa ku
gaisa" Bata jira cewar Farida ba ta bar wajen da sauri, Farida ta bi ta da
kallo sannan ta sauke idonta kasa a hankali, Mujaheed na duba blue band sanin
Imaan na son ci sosai, ta iso inda yake, daga kai yyi yana kallonta, ta wara
ido tace "Yaya I just met Aunty Farida now" da mamaki yace
"Farida? Where is she?" Imaan tace "Wajen perfumes" sai
kuma ta kamo hannunsa kamar xata yi kuka tace "Don Allah Yaya don't tell
her that we are married plsss" da mamaki yake kallonta trying hard not to
laugh yace "Why???" Hankali tashe tace "Wlh abun kunya ne wannan
Yaya, ya xa ayi ace wai kai mijina ne bayan kowa ya san kai yayana ne, don
Allah kar ka gaya mata wllh xan ji kunya sosai" Murmushi yyi yace
"Toh na ji, mu je...." Tana rike da hannunsa suka tafi inda Farida
take, shi dai bin ta kawai yake yana kallonta har suka iso wajen, Imaan na
kirkiran murmushi tace "Aunty ga yayan, shi ma yyi aure few months ago,
wajen matar ma na xo in mata kwana biyu"
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
86.....
Farida na murmushi tana kallon Mujaheed tace "Ina yini
Dr?" Mujaheed ya mayar mata murmushin yace "Lafiya lau Farida, kwana
da yawa?" Tace "Alhmdllh ya aiki" yace "Lafiya lau, dama
Zaria kike?" Tace "Ehh a nan nake" Ya gyada kai yace "Maa
sha Allah, toh ya mai gidan?" Tace "Yana lafiya lau, tare muke yana
waje" Mujaheed yace "Toh maa sha Allah" Imaan dai sai kirkiran
murmushi take tana kallon Faridar, Farida tace "Yaushe kika ce xa ki koma
kaduna?" Imaan ta wara ido tace "Nan da sati daya idan Allah ya yarda"
Farida tace "Amma xa ki xo gidana ai koh?" Imaan tace "Ehh xan
ce Yaya ya kawo ni, ki ba mu address" Farida na murmushi tace "Toh
bani number wayar ki" Imaan tace "Na bar sa a gida, bari ki bani naki
inyi saving a wayar Yaya" daga haka ta karbe wayar hannun Mujaheed ta mika
mata, Farida ta amsa ta sa number ta sannan ta mika ma Imaan, Imaan ta amsa
tayi saving number da Aunty Farida sannan tace "Nagode Aunty sai kin ganni
soon" Farida na murmushi tace "Toh nagode Imaan" daga haka tayi
mata sallama, tayi ma Mujaheed ma sallama sannan ta bar wajen, Imaan ta ci gaba
da daukan turarrukan da take so, Mujaheed na bin ta da ido har ta juyo, suna
hada ido ta turo baki tayi gaba ta bar sa a wajen, murmushi yyi ya bi bayanta,
suna isa counter ya biya kudin abubuwan da suka siya gaba daya aka kai masu
mota, har suka isa gida babu wanda yace komai cikin motar, Yyi parking yana
kallonta yace "Ke baki ji kunya ba da kika ce mata wajen matata kika
xo?" ko kallonsa Imaan bata yi ba ta dau ledan turarruka da body cream sai
toothbrush da toothpaste dinta xata fita motar yace "Xa ki san hutu kika
xo yi gidana" ita dai bata tsaya ta sauraresa ba ta wuce ciki, ya fita
motar ya tafi ya kulle gate ya shiga cikin gidan, direct sama Imaan ta wuce ta
tadda Safeenah tsaye corridor idonta yyi jajir sbda kuka, da alama dai jiran
haurowanta sama take, tun da suka hada ido Imaan ta dauke kai fuska daure,
Safeenah na kallonta da kyau tace "Mijina kika yadda aka aura maki dai
koh???" Imaan ta juya tana kallonta tace "Mijin mu dai malama...."
Tana fadin haka tayi maxa ta shige dakin ta sa makulli, xuciyar Safeenah ya
dinga tafarfasa tana tunanin me xata ma Imaan taji sauki, wani murmushin
takaici tayi ta juya ta koma ciki, Mujaheed na shiga parlor ya fiddo wayarsa
dake ring, ya d'an yi jim yana kallon Screen din don number Daddy ne, xaunawa
yyi saman kujera sannan ya daga ya kai kunne murya can kasa yyi sallama, Daddy
amsa daga daya bangaren yace "Ya ku ke Muhd?" Mujaheed yace
"Alhmdllh Abba, Ina yini?" Daddy yace "Lafiya lau, su Hadiza xa
su kai ma Imaan kaya can gidan naka, how about the key to the house?"
Mujaheed yace "In sha Allah xan kawo makullin Abba" Daddy yace
"Alright, Hadiza tace baka daukan kiranta why?" mujaheed yyi murmushi
sai dai bai ce komai ba, Daddy yace "Kar ka damu ka dauka kaji me xata ce
maka, may be Sunday ma su je tare da Inna" Mujaheed yace "Toh Allah
ya kai mu, nagode" Daddy yace "Ba matsala dai koh?" Mujaheed
yace "In sha Allah" Daddy yace "If there is any you let me know,
amma kasan Ummar ka an kwantar da ita asibiti kuwa?" Mujaheed yyi shiru da
farko, sai kuma yace "Not at all Abba" Daddy yace "Ohk, Alhmdllh
da sauki sosai, later xa a sallamosu" Mujaheed yace "Toh Allah ya
sauwake, nagode Abba" Daddy yace "Madallah" daga haka ya katse
wayar, mujaheed yyi dialing number Umma, bayan wani lkci ta dauka, a hankali ya
gaisheta ta amsa, yace "Ashe baki ji dadi ba Umma?" A takaice tace
"Wannan ba matsalar ka bace Mujaheed, kuma shirun da kaji na maka ba yana
nufin na hakura da aurenka da tsinanniyar sauran ciwon nan bane, in sha Allahu
ina kara jin sauki xan taho zariar ayi ta ta kare duk uban da xai faru sai dai
ya faru amma wllh baxa kayi aure da yar Aisha ba in dai ina numfashi a duniya,
kai koma bbu raina baxa ka yi ba wllh, don ma kaji da kyau, kwata kwata ban
amince ka hada daki da ita ba...." Tana gama fadin haka ta katse wayar
kitt, Mujaheed ya fi minti goma xaune kansa a jingine da kujera ya lumshe ido,
a hankali ya mike daga karshe ya wuce sama, dakin Safeenah ya shiga, ya sameta
tana xuge jaka bayan ta ciro Hijab, ko kallonsa bata yi ba ta saka hijab din,
ta daga trolley dinta tana ja ta nufi kofa, yace "Ina xa ki" ganin
bata da niyyar tsayawa balle ta basa amsa ya fixgota, ta fashe da matsanancin
kuka kamar jira take tace "Let me Mujaheed, gidanmu xan wuce don wllh
baxan xauna da yarinyar nan ba, I can't stay under the same roof with her, na
tsaneta, na tsaneta...." Katse ta yyi yace "Kin tsane ni kenan, good
and fine, you dare cross this house da sunan wucewa gidanku to a bakin auren ki
wllh, kin ji na rantse" daga haka ya saketa ya fice daga dakin, ta bi sa
da kallo baki bude, lkci daya ta xube kasa ta dinga kuka kamar ranta xai fita.
Bayan Magrib da takeaways din abinci Mujaheed ya shigo gidan, ko kadan bai
yarda damuwar da ke tattare da shi ya bayyana fuskarsa ba, sama ya wuce ya sa
makulli ya bude kofar dakin da Imaan take, ya sameta saman darduma ta idar da
sllh, ya ajiye mata leda daya yace "Daxu baki sha drugs din ki ba
why?" Shiru tayi masa, yace "Imaan" ta dauke kai tace "Am
not sick" ya fi second goma yana kallonta sannan ya juya ya fita, mikewa
tayi da sauri ta nufi kofarta ta kasa kunne, ta ji ya bude kofar dakin Safeenah
ya shiga, tabe baki tayi ta koma ta xauna gefen gado fuska daure. Xaune ya samu
Safeenah kasan dakin ta jinginar da kanta da gado ga wayarta a gefenta, kana
ganinta kasan ta gaji da kuka, ya ajiye ledan hannunsa ya karasa ya xauna gefen
gadon yace "Kin yi sllh?" Bata ko kallesa ba balle ta amsa, yace
"Let talk Safeenah...." Still bata ce komai ba wasu hawayen na xubo mata,
yayi kasa da murya yace "Yanxu ya kike son ayi Safeenah?" Ta daga kai
tana kallonsa cikin rawar murya tace "Am very serious Mujaheed baxan iya
xama da yarinyar nan ba a gidan nan" Ya d'an yi shiru sannan yace
"Mind u, sunanta Imaan ba yarinya ba" A mugun fusace ta mike tace
"What ever" ya dauke kansa yace "Idan baxa ki iya xama da imaan
ba baxa ki iya xama da ni ba kenan ae" Wani kuka ta sakar masa tana
kallonsa, ya mike ya isa gabanta ya kamo hannunta a hankali yace "I have
decided in raba maku gida, ke sai ki xauna nan, ita kuma....." Ta wani
xaro ido da karfi tace "Ka raba mana gida?? Ka raba mana gidan don ka ji
dadin cutata, to wllh baxai yiwu ba" Bai san lkcn da yyi murmushi ba yace
"To baxan raba ba, don kada in cuce ki, amma Ina son don Allah ba don ni
ba ki kwantar da hankalin ki, mu xauna lfya gaba daya, I will neva give imaan
space din raina ki... Plss Safeenah kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki,
wannan kaddaranmu ne gaba daya, bana son kina kukan nan don I am feeling guilt
inside me, gaba daya we never saw this coming, ain't you proud being my first?
Kowa xata shigo gidan nan fa a bayan ki take kin sani, so why disturb ur self,
kuma duk yanda kika ce ayi haka xa ayi, don haka kiyi hakuri wife...."
Rungumesa tayi tana kuka sosai tace "Wllh kishin sharing dinka da wata
mace nake Mujaheed, ji nake kamar xuciyata xata fashe saboda kishi" ya
rufe bakinta yace "Aa baxa ki yi sharing dina ba..." Da haka dai
Mujaheed ya dinga lallaba Safeenah har ta d'an hakura ta ci abincin da ya shigo
mata da shi, jin lkcn isha yyi ya mike ya fita dakin xuwa masallaci, for once
xae huta da koke kokenta ko hankalinsa xae kwanta ya samu relieve, he hate it
when a lady cries..... Yana dawowa masallaci ya sameta parlor tayi jigum, shi
dai ya san yana tausayinta sosai, kuma babu abinda ya fi unexpected kishiya
ciwo, kishiyar kuma warce tun asali basa shiri, ya karasa parlon ya xauna saman
kujera kusa da ita yace "Kin yi sllhn" shiru tayi bata ce komai ba
fuska bbu walwala, ya kalli movie din da ake a tv ya dau remote yace "Bari
in kai maki wannan series din naki da kike kallo kullum...." Daga haka ya
canxa tashar ya jawota jikinsa a hankali, wani sabon hawaye ne ya fara sauka
idonta, yace "I don't like this tears plss Safeenah, yanxu baxa ki hakura
ba for the sake of the love you are having for me??" Cikin rawar murya
tace "Ae nace maka na hakura" yyi pecking goshinta yace "Toh kar
ki sake kukan nan" daga masa kai kawai tayi, tayi lamo jikinsa, suna ta
xaune a haka har kusan karfe goma, jin footstep a stairs Mujaheed ya daga kai
da sauri suka yi ido hudu da Imaan, dauke kai Imaan tayi, Safeenah na jin
tafiyarta ta kara shige masa, Imaan bata sake kallonsu ba ta wuce kitchen rike
da takeaway din da ya kai mata daki, tana ajiye ledan hannunta ta jingina da
cabinet din kitchen din xuciyarta na bugawa, tafi minti biyar sannan ta fito ta
wuce sama da sauri ba tare da ta yadda ta sake kallonsu ba, Mujaheed ya bi ta
da kallon gefen ido... Sha daya saura Mujaheed ya tafi sama tare da Safeenah
bayan an gama series din, ya bude mata kofar dakinta yana kallonta yace
"Good night" shiga dakin tayi bata tanka sa ba ta nufi kan gado tayi
rub da ciki, ya bi ta da kallo sannan ya rufe kofar a hankali, Safeenah ta
sulalo daga saman gadon tana kuka kamar ranta xai fita, wato a dakin Imaan dai
xai kwana kenan yau, tunanin hakan yasa taji kamar ta kurma ihu ko xata samu
saukin xafin da take ji a xuciya. Mujaheed ya bude dakinsa yana kallon ciki,
ganin Imaan ta kashe wutan dakin ya luluba switch din ya kunna, kwance ya ganta
ta rufe har kanta da bargo, ya rufe kofar dakin ya rage kayan jikinsa ya shiga
bathroom, wanka yyi ya fito ya saka pyjamas dinsa sannan ya kashe wutan dakin
ya karasa kan gado ya cire blanket din jikinta murya can kasa yace "Did
you perform ablution before lying down?" Duk da imaan na jinsa taki cewa
komai idonta a rufe, ya kai hannu fuskarta ta mike a fusace tace "Meye
haka na fara bacci xaka shigo min daki ka tasheni Yaya?" Ya d'an shafa kai
yace "Dama shigowa nayi in ce maki sai da safe, and to make sure kin sha
drugs din ki" tana kallonsa da idanuwanta da suka yo waje tace "Ina
xaka?" Yace "Wajen matata da kika xo hutu wajenta mana
kanwata....." Bai jira cewarta ba ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo
kamar idanuwanta xa su yi magana, ko kiftawa babu har ya fita dakin ya kulle
kofar a hankali not making any sound, Imaan ta cire bargon jikinta ta sauko
daga kan gadon da sauri....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
87.....
Imaan har ta isa kofa sai kuma ta dakata bakin kofar, ta
durkushe kasa ta hade kai da gwiwa lkci daya ta fara kuka tana jin xafi a
ranta, ta fi minti goma wajen kafin ta mike a hankali ta koma saman gado ta
takure waje daya ta rufe fuskarta da pillow tana shessheka, har karfe daya bata
yi bacci ba, daga karshe ta mike a hankali ta shiga bathroom ta dauro alwala ta
fito ta shimfida darduma ta dau Hijab ta fara sallah, bata san iya lkcn da ta
dauka tana sllh ba, daga karshe ta kwanta saman darduman don har rufewa idonta
yake sbda bacci, lkci daya kuma baccin ya dauketa. Da asuba Mujaheed ya bude
kofar dakin a hankali ya shiga ya kulle sannan ya kunna wutan dakin, kwance ya
ganta saman darduma ta rufe fuskarta da hijab, ya isa gabanta ya durkusa yana
kallonta ya sa hannu ya sauke hijab din daga fuskarta, bacci ya ga take yi, yyi
murmushi ya ja dogon hancinta gently, a hankali ta bude idanuwanta ta daura
kansa jin kamshin da ya cika hancinta, sanye yake da jallabiya ya sakar mata
good morning smile ta dauke kai da sauri ta hade rai, yace "Me yasa kika
kwanta kasan tiles da sanyin nan?" Bata tanka sa ba, ya mike yace
"It's time for subhi prayer" still bata ce komai ba ya juya ya nufi
kofa, a hankali ta juya tana kallonsa har ya bude kofar ya fita ya kulle,
Mikewa xaune tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta. Har gari ya washe imaan na
xaune saman darduma tana azkar duk da baccin dake fixgarta, amma sai da ta gama
ta mike ta hau saman gado nan da nan bacci ya dauketa, ba ita ta tashi ba sai
kusan karfe tara, ta fi minti goma xaune gefen gadon sannan ta ja tsaki ta mike
ta shiga gyaran gadon, tana gamawa ta cire kayan baccin jikinta ta linke ta dau
sabon towel da ya siya mata jiya ta daura, sannan ta dau brush da maclean ta
shiga bathroom, tana daure da towel bayan tayi wanka ta fito ta dau hijab dinta
ta koma bandakin ta fara Hijab din da detergent, har ta gama sannan ta dauraye
bandakin ta fito, ta gama shafe shafenta, ta feshe turare ta dau daya daga
sabbin abaya ta saka ta kara feshe jikinta da turare sannan ta dau bucket da
hijab dinta ke ciki ta fita xata shanya a waje, tun da ta fito daki ta ke jin
kamshin soye soyen da ya cika gidan, ta tabe baki har ta sauko downstairs,
Mujaheed na xaune parlor cikin kananun kaya, Safeenah na kusa da shi duke a
kasa tana setting breakfast da ta gama girkawa, ta wani cakare cikin riga da
wando da ya fito da ainahin komai nata, ta daure gashinta da ya xubo har
shoulders dinta, labari kawai take masa yana kallonta yana kallon Tv, kai kana
ganinta kasan farin ciki ne fal ranta a moment din, murmushi Mujaheed yyi jin
abinda tace yace "To me yasa kika fara ci?" Safeenah da tun sakkowar
Imaan suka yi ido hudu, ta wani juya ido cike da shagwaba tace "Saboda
mijina na ci mana, ae duk abinda kke so dole in so sa ni ma..." Mujaheed
kawai gyada mata kai yake yana murmushi, ta mike ta xauna kusa da shi ta sakale
hannu wuyarsa tace "To ka mance lkcn da kake cewa sai na ci?" Ya d'an
bude ido yana kallonta yace "Ni??" Maimakon ta basa amsa sai kawai ta
saka mashi baki a nasa, dauke kansa yake son yi da mamaki amma ta ki barin yyi
hakan, irin kiss din da ta san yake so ta shiga masa, tun yana basarwa har ya
fara give up sai dai bai mayar mata ba, Tun da Imaan taga haka bata sake yarda
ta kalli direction din su ba, sai dai da kyar take daga kafarta har ta isa
kofar parlon ta bude a hankali ta fita xuciyarta na bugawa, Jin sound din bude
kofa Mujaheed yyi saurin mikewa xaune yana kallon kofar amma tuni ta rufe,
Safeenah tayi lamo jikinsa yana kallonta yace "Wa ya fita?" Ta
langwabar da kai tana juya ido a hankali tace "Mu nawa ne gidan
yanxu?" Janyeta yyi jikinsa bai ce komai ba, tana murmushi ta xamo kasa
tace "Should I make the coffee for you now?" A takaice yace
"No" ko kallonsa bata yi ba ta shiga hada masa coffee din a mug, Duk
da yanda Imaan ta so kar tayi kukan da ke cinta a rai amma hakan ya faskara,
tana gama shanya hijab din ta xauna saman dakali ta hade kai da gwiwa ta fashe
da matsanancin kuka tana jin xuciyarta na mata xafi, ita kanta bata san dalilin
abinda take ji a ranta ba a lkcn, bata yi minti biyar wajen ba ta mike a
hankali tana goge idonta, ba karamin sanyi ta ji ba kukan da ta yi, ta dau
bucket tana tafiya a hankali har ta isa entrance din gidan, nan kuma gabanta ya
shiga faduwa coz she can't imagine seeing what she just saw for the second
time, baxata iya withstanding dinsa ba, slowly ta bude kofar just to keep them
alert, sannan ta shiga parlon amma bata yarda ko da wasa ta kalli inda suke ba
xuciyarta na bugawa har lkcn, ta wuce sama kamar me counting steps dinta,
Mujaheed ya bi ta da kallon gefen ido, Safeenah dai tana aikin hada shayinta da
xata sha xuciyarta fess tana satan kallonta, Bayan kusan minti bakwai Mujaheed
ya mike Safeenah tace "Ina kuma xaka ga breakfast na xuba maka
darling" Ba tare da ya kalleta ba ya fara tafiya yace "Mu kadai xa mu
yi breakfast din??" Ta mike da sauri ta sha gabansa ta riko hannunsa tace
"Haba dear, shine sai ka je kiranta da kanka, ai ko ni sai in je in kirata
dama ba mu gaisa ba yau, But you know what baby?? wllh duk naji abubuwan da ka
gaya min jiya da daddare kuma in sha Allah I will adhere, I will try my best mu
xauna lafiya da ita, na yarda wannan kaddara ta ce, kuma babu bawan da ya isa
ya wuce kaddarar sa, na ji na yarda xan dau Imaan matsayin kanwata kamar yanda
kace, don haka give me the space to start doing this from today, xan je mu
gaisa in kirata yanxu, daga nan ba sai mu fara fahimtar juna ba?" Tana
masa lallausan murmushi tana murxa hannunsa ta kare maganar, shi dai kallonta
kawai yake, bata jira cewarsa ba ta sake sa ta wuce sama tana murmushi, a
hankali ta bude kofar dakin Imaan ta shiga bbu ko sallama, Imaan dake kwance ta
rufe fuskarta da pillow tana shessheka a hankali, ta ki dagowa duk da taji an
bude kofa dakin, Safeenah tayi wani dariya tana kallonta daga head xuwa toes,
Imaan ta bude ido da sauri jin dariyarta xuciyarta na bugawa ,sai dai still
bata dago kanta ba, Cike da isa Safeenah tace "Kinga consequence din auren
mijin wata koh??" Imaan dai bata dago ba kuma bata ce komai ba, Dariya Safeenah ta fara yi sosai tace "Ban taba
ganin amaryar da miji bai dokinta sai a kan ki, har xai tsallake ki ya tafi gun
uwar gidansa ya kwana a faranta masa rai, kina gidan kuma kwanan ki, isn't this
a big shame to you? To what will one expect bayan kowa yasan tusa masa ke kawai
aka yi ya aure ki, kuma shi din mijina dama a ko da yaushe mai biyayya ne, yyi
biyayya ya aure ki ba don yana so ba sae don bbu yanda xai yi, to abinda baki
sani ba mijin wata mijin aro ne, yanda kika shigo gidan miji na a xabure haka
xa ki fita a xabure ki bar min gidan mijina, don ko mahakaci yasan wllh tllh
tusa masa ke aka yi, baya yin ki ko na second daya, da yana yin ki ko yaya ne
baxai ki kwana dakin ki ya tafi dakin first wife dinsa a daren ki na farko
gidansa ya kwana ba, don haka tun yanxu yarinya ki fara sanin matsayin ki gidan
nan, I think that is all I have to say to you now, and can you kindly come
downstairs for breakfast, he instructed I come and get you don baxai iya hawa
sama kiran ki ba...." Imaan ta goge idonta da pillow ta mike xaune tana
kallon Safeenah tana murmushi tace "Xan nuna maki ke ce kika auri mijin
wata ba ni ba, kuma aron nasa ma ni ko na second daya baxan baki ba, nan ba da
jimawa ba xa ki san ba tusa masa ni aka yi ba, shine ma mai tusa kansa gareni,
kuma xan nuna maki ke aka tusa ma Mujaheed yyi biyayya ya aura ba ni ba, sai ma
kinsan ni ce silar auren ki da Mujaheed xa ki dawo hankalin ki...."
Safeenah tayi wani dariya lkci daya ta daure fuska tana huci tace "Karya
kike wllh, ke dai ce kika aura mijin wata mijin aro, Mujaheed ba class din ki
bane bbu abinda xai ci dake, tsautsayi ne kawai ya ja auren ku, amma wllh ba
mijin ki bane shi din...." Tana magana hawaye ya cika idonta duk da
daurewan da tayi kada hakan ya faru, tana girgixa kai tace "Wllh ba mijin
ki bane shi din, ke kin kasance makwadaiciya me son abun duniya, kuma kyan ki
ire iren su Bulasawan, don su xa su fi iyawa da sauran ciwo, tsautsayin da ya
hana d'an gidan Bulasawa auren ki shi xai kara sa mijina ya sake ki shi
Bulasawan ya aure ki kuje can ku karata, in sha Allahu nan ba da dadewa ba xa
ki bar min gidana da mijina ki tafi, ba D'an gidan Bulasawa ba, in har xa ki
iya auren shi Bulasawan ma da kansa ki tafi ki auresa, banxa kawai ragowar
ciwo...." Imaan tayi murmushi tace "Son da mijinki ke ma ragowar ciwo
wllh da kin samu just 10% na kalan son daga garesa da ba haka ba, mark my
words.... sai kin xama abun tausayi a gidan nan in dai ni ce, banxa kawai
jahila mahaukaciya..." Safeenah da ta yo waje da ido jikinta na rawa tace
"Ni kike xagi???" Imaan ta sakko da kafafuwanta daga saman gadon dai
dai shigowar Mujaheed dakin, ta mike tana kallonta tace "An xage ki din
kiyi abinda xa ki yi, karya nake ke ba jahila bace? Ko kin ta6a leka
islamiyya??" Kallonsu Mujaheed ya tsaya yi da mamaki, Safeenah na kallonsa
ta fashe da matsanancin kuka tace "Kana ji ko dear, ni wai take ce ma
jahila mahaukaciya daga na shigo na gaisheta nace ta sakko mu yi breakfast,
meye laifina a nan Mujaheed don na shigo nace ta sakko mu karya..." Kuka
take sosai tana kallonsa, Wani dogon tsaki Imaan ta ja tace "Makaryaciyar
banxa kawai" daga haka ta nufi bathroom kamar xata tashi sama ta shige
tayi banging kofar da karfi, Mujaheed da ya bi ta da kallo baki bude ya mayar
da dubansa kan Safeenah dake kuka sosai, karasawa yyi kusa da ita a hankali ya
jawota jikinsa murya can kasa yace "I am happy da baki kulata ba, kinga
yarinya ce, she still don't know what she is doing, but I will teach her
discipline" daga haka ya ja ta suka fita dakin tana shessheka....
Abba ne tsaye parlon Inna tare da Mama Hadiza da ta rungume
hannu, a fusace Inna tace "In har baxan tafi da kayan sawa ba to wllh sai
dai kowa ya fasa xuwan a hakura kawai, ya xa ayi in tafi waje me nisa har Zaria
ban je da kaya ko kala uku ba, Ni fa ba kwana nace xan je in yi kamar
gantalalliya mara mafadi ba, amma ai yana da kyau duk matafiyi ya dinga yawo da
kaya sbda bacin rana, kaji min dai sai kace kun fi ni sanin abinda nake, wllh
ban taba tafiya bbu jakar kaya ba ko da kuwa awa daya xan je inyi a waje,
sabida fatara sai in tafi da xanin jikina kadai ina yawo a garin zaria kamar
almajira..." Abba yace "Toh inna tafiyar da xa aje a dawo a ranan ina
amfanin tafiya da kaya? Me xa kiyi da kayan, Da driver fa xa ku je ku
dawo" Inna tace "Yau naga jaraba, Ina ruwanka da rayuwata ne Ahmadu,
Kai xaka yi tafiya ko ni? Yanxu idan na bi hanya Ina ta kwarara masu amai a
mota kayan Imaan ko na Safara'u xan je in canxa a gidan??" Mama Hadiza
tace "Zaria fa xa mu je ba Lagos ba Inna" A mugun fusace inna tace
"Ko maraban jos xa mu ba ruwan ki kiyi ta kanki, bbu shegen da ya isa sa
ni in fita gidan nan da xanin jikina kadai kamar a kaina talauci ya
kare..." Daddy ne ya shigo parlon da sallama shima yyi shirin komawa Abuja
ranan, yace "Har yanxu ba ku fito ba Inna..." Inna tace "Ina fa
xan fito Bukar, ai tafiyar nan ina jin babu shi don ni dai baxan bi hanya bbu
kaya ba gaskiya, Kai ko da ban yi amai ba a hanya to ni nasan kafin mu isa
Zaria xan jike shataf da gumi, to uwata ce min tayi je ki kya gani da xan xauna
da kaya ina warin xufa Bukar???" Daddy yace "Haba inna sai kace warce
xata sokoto ko gombe, nan nan Zaria fa xa ku, ku dawo anjima, idan ba xama kike
son xuwa yi a gidan ba ina amfanin tafiya da kaya?? Sai dai in xauna masu kike
son yi kawai, amma sau nawa kike xuwa kano kice ke ko jaka baxa ki dauka ba?
Gashi har rana yyi ba ku kama hanya ba, hakan is not good" shiru Inna tayi
bata ce komai ba sai yan idanuwa, Daddy ya juya ya fita parlon, Mama Hadiza ta
dau warmer dake cike da dambun nama da Inna tayi ma Imaan ta fita parlon tace
"Muna jiran ki a mota" Abba na kallon Inna da ta sunkuyar da kai a
hankali yace "Ae sati uku xa su yi xarian sai su dawo kaduna, idan ya so
sai ki..." A fusace inna tace "Rufe min baki malam, Ina ruwana da ko
kwana nawa xa su yi a Zaria? Ko nace maku xuwa xan yi in xauna masu kamar
shashasha tsofe tsofe da ni, me Mujaheed da Imaan xa su bani wanda Allah bai
ban ba? Yaran da aka ma auren dole auren jaraba wa yasan halin da suke ciki ma
yanxu, wllh In don ta kai da Bukar ne ni baxan ma je ba don baku da kirki barin
wannan mutumi Bukar, da 'yar sa ce kadai a gidan wllh na ma fasa xuwan gaba
daya, to amma ni yanxu gun Mujaheed kawai xanje ba gunta ba wllh, bbu ruwana
don ubanta ba ma son xuwa in je gidan yake ba, ubanta ba shi da kirki"
tana fadin haka ta mike ta fice daga parlon ba tare da ta dau jakar kayanta
kusan kala shidda da ta hada ba a Ghana must go.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
88....
Safeenah na kitchen tana wanke wanke ranta fari fess ko kadan
bata ji haushin xagin da Imaan tayi mata ba ganin Mujaheed bai yi supporting
dinta ko na second daya ba sannan ya yadda da tsarin da tayi masa, sai murmushi
take ita kadai ganin abubuwan na tafiya yanda dai take so kafin Mummynta ta iso
gidan, Mujaheed na xaune parlor idonsa a kan tv amma bai ma san me ake yi ba,
gaba daya hankalinsa na sama, can ya kalli breakfast da ya ajiye Safeenah ta
bar ma Imaan a parlon sannan ya kalli agogo, karfe goma har ya gota hakan yasa
ya mike ya tafi kitchen don daukan cup da spoon ya dau tray ma, Safeenah na
kallonsa da mamaki tace "Me xaka yi da su kuma dear?" Yace
"Imaan haven't Breakfasted..." dauke kai tayi ta wani hade rai tana
dauraye plate din hannunta tace "Toh ai idan tana jin yunwa da ta sakko
tunda mun ajiye mata mun fita hakkinta, may be she isn't hungry yet" shi
dai ba kalleta ba balle ya tanka ta ya fita kitchen din, shayi ya hada cikin
cup a parlorn don kayan shayin na ajiye har lkcn, ya dau plate din dankali da
kwai ya daura kan tray da cup din shayin sannan ya wuce sama, duk Safeenah na
lekansa daga kitchen ko kiftawa bbu, lkci daya gaba daya mood dinta ya canxa ta
ajiye plate din hannunta ta fito kitchen din ta bi sa da kallo xuciyarta na
tafarfasa, Mujaheed ya murda kofar dakin ya shiga ciki sannan ya kulle, xaune
ya sameta ta jinginar da kanta da gadon dakin, ya ajiye plate din hannunsa yana
kallonta, ta mike ba tare da ta yadda ta kallesa ba xata shige bathroom ya
rikota, fashe masa da kuka tayi tace "Ni wllh ka mayar da ni gidanmu baxan
kara kwana gidan nan ba, idan ba haka ba inyi wucewata da kai na" Ya
rungumeta yace "Da aka yi maki me?" Kwatar kanta take son yi a fusace
amma ya ki saketa, yyi murmushi murya can kasa yace "Upon rashin kunyar da
kika ma matata ba mu ce maki komai ba kuma kike kuka??" Turasa tayi iya
karfinta tace "Ae dama ni ba matar ka bace sai ita...." sosai ta basa
dariya ya dake bai yi ba yace "Daga kanwata kuma kin dawo matata, when
hakan ya faru ban sani ba?" Struggling ta dinga yi xata kwace kanta amma ya
ki saketa, ta fashe masa da kuka sosai tace "Wllh duk abinda kake min sai
na gaya ma Abba da Inna, har...." Xaro ido tayi ganin abinda yake mata da
sauri tace "Ha'an meye haka Yaya??" Ya lumshe ido bai ce mata komai
ba yana ci gaba da kissing duk jikinta as if his life depend on it at that
moment, turasa ta dinga yi jikinta na 6ari, lkci daya ta tsorata cikin rawar
murya tace "Ka sakeni plss bana so Yayaaa, what's this you are...."
ya kankameta making the affair more deeper and hotter, daga haka kuma bai kara
bata chance din magana ba, iyakar tsorata Imaan tayi a lkcn, it's something
that just came all of a sudden, duk wannan abun kuma yaki bude ido balle ma ya
kalleta, gaba daya kafafuwanta suka kasa daukarta ganin durkusawa take son yi
ya kwantar da ita saman gado, going further from where he stopped, lkci daya ya
bude idonsa da suka sauya kamanninsu yana kallonta, ya dagota da sauri yace
"Imaan, Imaan..." Kokarin jan numfashi take tana komawa baya, ya
riketa yana kallonta shi ma yana sauke numfashin, har sai dai ya ga ta nutsu
gaba daya numfashinta ya dawo normal, sai kuma ta fixge hannunta hawaye cike
idonta ba tare da ta yadda sun hada ido ba xata sauka saman gadon kana ganinta
kasan a tsorace take, ya mike xai riketa ta fashe masa da kuka jikinta na rawa
tana komawa baya tace "Don Allah Yaya ka bari, wllh bana son haka, kayi
hakuri plss" yyi kasa da murya yace "To sakko kiyi breakfast"
xuciyarta na bugawa har lkcn taki kallonsa, kamar yanda shi ma bai yarda ya
kalleta ba, ganin tray din breakfast din dake kasa lkci daya ta hade rai tace
"Ni baxan ci ba" da sauri Kuma a tsorace ta sauka daga kan gadon
kafin ya iso kusa da ita tace "Wayyo Yaya don Allah kayi hakuriii"
Yana kallonta da lumsassun idanuwansa yace "Toh xauna kiyi breakfast"
ta make kafada tace "Ni dai ka siya min wani baxan ci wannan ba wllh"
tana fadin haka ta juya masa baya, murmushi yyi yana shafa kansa yana kallonta
daga sama har kasa, murya can kasa yace "Koh..." Ba tare da ta juyo
ba tace "Ehh ni dai ka siya min baxan ci Wannan jagwalgwalon ba"
walking gently ya karasa kusa da ita tana jin tafiya ta juya ta bar wajen da
sauri tace "Yayaaa" murmushi kawai yake yana shafa kansa yace
"Toh shkkn bari in je in siyo ma kanwata wani abinci..." Da sauri
tace "Ae tare xa mu je in nuna maka abinda nake son ci" duk wannan
abun taki yarda ta hada ido da shi, a hankali yace "To mu je" har
xata bi ta gabansa sai kuma ta koma baya da sauri kamar xata yi kuka tace
"Yayaa" ya buda ido yace "What?" A hankali tace "Kar
ka ta6a ni plss" Yana murmushi yace "Ehh baxan ta6a ki ba yanxu sai
anjima da night koh?" sosai gabanta ya fadi, kamar xata yi kuka ta kallesa
a karo na farko, shi ma yana kallonta yace "Ba sai in je in ta6a warce
take son in ta6a ta ba..." Wani kallon da yyi mugun basa dariya tayi masa,
tace "It's not new ai, tunda jiya ma a dakinta ka kwana" Da mamaki
yake kallonta yace "Dakinta kuma?" Bata ko kallesa ba ta fice daga
dakin ya bi ta da kallo, sannan ya duka ya dau tray din da ya shigo da shi ya
fita dakin, Safeenah na xaune parlor har ta gaji da kallon stairs sai ga imaan
ta sakko, ko kallonta Imaan bata yi ba ta tafi waje dauko Hijab dinta da ta
shanya tunda shi kadai take da a gidan, Safeenah ta bi ta da kallon tsana
xuciyarta na kuna, fitowar Mujaheed ya sa ta mike fuska daure, yyi mata kallo
daya ya wuce kitchen, bin bayansa tayi tana kallon tray din da ya ajiye yace
"I will be back soon..." Da sauri tace "Ina xa ka?" Yace
"I want to get her something to eat..." Safeenah ta daure fuska sosai
tace "Wannan fa?" Yace "Tace baxa ta ci ba" Safeenah tace
"Toh bari in shirya, nima ai ba wani breakfast din kirki nayi ba coz kasan
bana cin dankali" Ya buda ido yace "Dankalin kuma da kika ce na koya
maki ci daxu??" Ko tankasa bata yi ba ta tafi dauko Hijab a sama, bin ta
yyi da kallo yana shafa kai, can ya dau makullin motarsa ya fita ya tadda imaan
tsaye jikin mota, yace "Xa mu je da Safeenah, she will be coming
out...." Bata jira ya kai karshe ba tace "Toh ku je" daga haka
ta wuce sa xata koma ciki ya rikota da sauri ya jawota jikinsa a hankali, murya
can ciki yace "Haba wife..." Kamar xata yi kuka tace "Wllh
baxata bi mu ba, sai dai in fasa xuwa ai ba kwanan ta bane" sosai ta basa
dariya ya daura fuskarsa saman kanta yace "Kwanan ki ne kenan
kanwata?" Tana kallon entrance din shiga gidan tace "Ehh" murya
can kasa yace "So we are sleeping together today?" Tace
"Ehh" lumshe ido yyi yace "Da gaske?" Tace "Ehh"
yace "Baxa ki ji tsoro ba?" Tace "Ehh" Magana yake mata
amma duk hankalinta na kofar tana jiran fitowar Safeenah, Mujaheed yace
"Ke fa kika ce min Ehh da bakin ki" ta kara cewa "Ehh" dago
kanta yyi yana kallon kyakkyawan fuskarta sanin she isn't listening to him, dai
dai nan Safeenah ta fito sanye da hijab hannunta rike da waya, A hankali ya
sake Imaan jin footstep dinta, ya karasa gunta yace "You say what u want
to eat sai in siyo maki kawai" tana masa wani kallo tace "Why??"
Imaan na kallonta da kyau tace "Saboda ba kwanan ki bane, ki jira after a
week sai ki bisa a mota not today" Da mamaki Safeenah ke kallon Imaan
sannan ta kalli Mujaheed, Mujaheed yace "Don't worry i will get you pizza,
guess that is what u want for breakfast" daga haka ya nufi gate ya bude
sannan ya dawo ya bude lock din motar, Imaan ta bude front seat taki yarda su
hada ido da Safeenah ta shiga motar ta rufe door din, Mujaheed ya shiga
maxaunin driver ya tada motar ya fita compound din sannan ya sauka ya rufe gate
ya koma cikin motar suka bar layin, ya rasa me yasa yake murmushi shi kadai,
Imaan dai bata yarda sun hada ido ba, sun dan yi nisa murya can kasa yace
"But ain't we suppose to take our bath before coming out?" Imaan ta
kallesa da sauri tace "Bath? ai ni nayi wanka" yyi murmushi yace
"Ohk tot ba ki yi ba ai" dauke kai tayi ta hade rai ta ki cewa komai,
A wani babban eatry ya siya mata abincin sannan ya siya ma Safeenah ma, ita dai
bata ce masa komai ba, bayan sun bar eatry din tace "Yaya ka bani waya in
kira Anty Farida in ji ko gidanta bbu nisa sai ka kai ni in gaisheta" yace
"Not today" 6ata fuska tayi kamar xata yi kuka tace "Yaya plss,
ni dai ina son in je" Bata jira cewarsa ba ta fara laluba aljihunsa tana
neman waya, buda ido yyi sosai yana kallonta har ta cire wayar and he couldn't
stop looking at her, ta bude wayar ta fara shiga gallery, hotunan Safeenah da
take dauka a wayar ta gani sun fi a kirga, lkci daya tayi marking dinsu gaba
daya ta jefa su a kwandon delete, sannan ta shiga contact, tana nemo lambar
farida tayi dialing ta kai kunne, Bayan few seconds Farida tayi picking call
din, bayan sun gama gaisawa Imaan tace "Aunty ki turo address din Yaya xai
kawo ni yanxu ae kina gida koh?" Farida tace "Ehh Ina nan, bari in
turo" imaan ta katse wayar tana kallon mujaheed dake driving idonsa a kan
titi, yace "Xa mu yi baki daga kd fa" Imaan tace "Su waye?"
text din farida na shigo wayar hannunta ta bude tana kallon address din sannan
ta nuna masa, ya kalli wayar sannan yace "Baxa ki bari gobe in kai ki
ba?" A takaice tace "Noo" yyi murmushi ya dau hanyar unguwar da
Farida ta turo, tafiyar kusan minti sha biyar suka yi suka iso layin, yyi
parking dai dai house number din, Imaan tayi dialing number din Farida tana
dagawa tace "Aunty ina waje" Farida tace "To ki shigo ciki ina
ce tare ku ke da Mujaheed din?" Imaan tace "Ehh tare mu ke"
Farida tace "Toh ku shigo sai su gaisa da Mai gidan yana nan" Imaan
tace "Toh" sannan ta kalli Mujaheed, yace "Ki shiga ki fito ina
jiran ki" tace "Baxa ka shiga ba?" Yace "Yes" ta hade
rai tace "Ayya, ita fa da kanta tace xa ku gaisa da mai gidanta, or are
you feeling anything deep down?" Ya kalleta da mamaki yace "Like
what?" Ta wara masa ido tana murmushi tace "Like kishi or so"
Yar dariya yyi bai shirya yin hakan ba yace "Not when I am having
you" turo baki tayi tace "Not when you have ur wife dai" ya ja
hancinta yace "And you are the wife koh" ta make kafada tace "Ni
ba matarka bace, matarka na gida" daga haka ta fita motar, ya sakko shi ma
yana kallonta yace "Toh xa mu raba wannan gardaman anjima da daddare"
da sauri ta kallesa amma bata ce komai ba ta nufi gate din gidan ya bi bayanta
yana murmushi, Mai gadi ne ya bude masu gate din suka shiga, Mujaheed ya tsaya
compound din gidan yace "I will wait here" Imaan ta tafi kofar shiga
parlon ta danna bell, Farida ta bude kofar ganinta tayi murmushi sosai tace
"Welcm imaan ina yayan naki?" Imaan ta mayar mata da murmushin tace
"Wai baxai shigo ba yana waje" Farida tace "Na xata da aunt din
ta ki xa ku xo ai" Imaan tayi yake tace "Ya ajiyeta a wani anguwa
ne" Farida da ta hango Mujaheed tace "Dr ka shigo mana xa ku gaisa da
Mai gidan ne" Mujaheed yace "Ohk" daga haka ya fara tahowa,
Farida ta kama hannun Imaan suka shiga ciki, tarba sosai Farida da mijinta suka
yi masu, Mijinta Dr Khaleel na kallon Mujaheed yace "Toh ya madam baku xo
da ita ba su yi xumunci da Farida.. " Mujaheed ya d'an yi murmushi yana
kallon Imaan, Imaan ta d'an marairaice masa tana girgixa masa kai a hankali
alamar kada yace komai, Farida dai sai kallonsu take haka ma mijin nata,
Mujaheed ya shafa kansa still smiling yace "Gata nan xaune ai" Farida
ta dinga kallon Imaan da mamaki ko kiftawa babu, Mijin yace "Maa sha
Allah, auren xumunci kenan ku ka yi, Farida ce min tayi sistern ka ce"
Mujaheed ya gyada masa kai yace "Sure, auren gida ne" Farida dai sai
kallon Imaan da taki dago kai take ta kasa cewa komai, Nan dai Mujaheed da ko a
jikinsa suka dinga fira da mijin Farida, Farida ta mike daga karshe tana kallon
Imaan a hankali tace "Mu tafi ciki Imaan" mikewa Imaan tayi Mujaheed
ya bi ta da kallo yana murmushi ta balla masa harara kamar xata yi kuka ta bi
bayan Farida, suna shiga daki Farida ta kulle kofa ta juyo tana kallon Imaan da
sauri tace "Da gaske mijin ki ne Mujaheed yanxu Imaan?" Imaan ta kasa
cewa komai lkci daya hawaye ya kawo idonta, Rungume ta Farida tayi cike da
murna tace "Kai, amma i am very
happy for Imaan, kinyi dacen miji Imaan...." Imaan dai bata ce mata komai
ba hawayen dake idonta ya sakko Farida na kallonta da mamaki tace "Kuka
kuma? Baki son auren ne Imaan?" Imaan ta xauna gefen gado tana goge
hawayen idonta tace "Fasa aure na aka yi aka hadani da Yaya..."
Farida ta dawo gefenta tana kallonta cike da mamaki da kuma tausayi tace
"Allah sarki, ban ji labarin ma Imaan, but put this in mind Mujaheed shine
mafi alkhairi gare ki shi yasa hakan ya faru Imaan, kin fi kowa sanin halin
Mujaheed fa..." Imaan ta fashe da kuka tace "To amma yaya na kuma
Anty Farida?" Farida bata san lkcn da tayi dariya ba sosai ta kamo
hannunta tace "Toh ai ya fi dadi irin wannan auren Imaan, Kinga sai kiyi
ta xuba masa shagwaba kamar yanda kike masabda hujja yanxu...." Imaan ta
marairaice tace "Allah Aunty kunya fa nake ji" Farida tayi murmushi
tace "Imaan kenan, kin san da dadewa na taba tunanin anya ba sonki
Mujaheed yake ba, coz care din da yake baki is too much, kuma har muka rabu da
Mujaheed ban taba kin yarda cewar baya son ki ba, ni nasan akwai abu a
xuciyarsa game da ke, may be saboda mum dinsa yayi ta boyewa, amma ban taba jin
kishin ki dai dai da na rana daya ba, cikin kaninsa ma duk mun fi sabawa da ke,
sai ranan da ya xo gidanmu na karshe yake ce min kilan wataran ya hada ni da
kanwata, nasan kuma ke yake nufi a lkcn" Imaan dai sai kallonta take,
Farida tace "Amma sun rabu da matar da Ummarsa ke son ya aura koh??"
Imaan ta tabe baki tace "Tana nan, tare ma muke yanxu, wllh Aunty Farida
bana sonta" Farida ta xaro ido tana kallonta, can tace "Tana nan?? To
yau kwananku nawa da auren?" Imaan tace "Gobe Friday sati daya, amma
yau kwanan mu daya a Zaria" Farida tace "Kwananki nawa da
tarewa?" Shiru Imaan tayi sannan a hankali tace "Just two..."
Farida tayi murmushi tace "Toh ai babu xancen wani kunya tsakanin ki da
Yaya yanxu koh?"
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
89.....
Murmushi Imaan tayi ta rufe fuskarta jikin Farida a hankali
tace "A'a akwai mana Aunty" Farida ta dinga kallonta kafin tace
"Toh kuwa idan kika tsaya jin kunya kishiyar ki xata kwace maki Yaya kina
ji kina gani" Imaan ta dago tana Kallonta, Farida tace "Kwarai kuwa,
kunyar me xa ki ji kuma bayan kun riga da kun xama daya yanxu" Imaan kamar
xata yi kuka tace "Wllh Aunty kunyarsa ni dai nake ji ban san ya xan yi
ba" duk da ta ba Farida dariya, Farida ta daure fuska tace "Kunya
bayan ya riga ya kwana dakin ki?" Imaan ta girgixa kai tace "A'a ni
bai taba kwana daki na ba" Farida tace "Kika ce kwanan ki nawa da
tarewa yanxu?" Imaan ta buda ido sosai tace "Aunty jiya fa muka xo
nan garin" Farida tayi shiru sannan tace "Kuma bai kwana dakin ki
ba?" A hankali Imaan tace "Ehh kila dakin matarsa ya kwana jiya, don
daxu da safe ta shigo tana ce min wai bata ta6a ganin amaryar da miji bai kwana
dakinta ba ranan farko sai dakin uwar gidansa, har tana ce min mijin wata na
aura, kuma mijin wata mijin aro ne" da mamaki Farida ta dinga kallonta,
can tace "Toh shi me ya hanasa kwana dakin na ki?" Imaan ta tabe baki
tace "Ni nasan sbda jiya da muka hadu da ke a mall nace maki hutu na xo
gun matarsa, shine da ya shigo da daddare yace min to xai tafi wajen matarsa ni
kuma ban ce masa komai ba har ya fita..." Farida tayi murmushi tace
"Toh ki maida hankalin ki imaan, idan ba haka ba kuwa you will regret it
duk da ban san kishiyar nan taki ba ga dukkan alama makira ce, kuma Mujaheed da
na sani dai baxai taba kwana dakinta yasan ba ranan ta bane, Mujaheed yana da
addini sosai ya san me yake, sai dai idan ya canxa ne daga yanda na san sa a
da, yanxu ki bude kunnuwan ki sosai ki ji abubuwan da xan gaya maki, idan kuma
ki ka ki aiki da su toh kina tare da dana sani wanda ba shi da amfani, ko
tantama babu ke Mujaheed ya fara so kafin first wife dinsa, that is if yana ma
sonta kenan.... Imaan if I am not mistaken babu abinda ya shiga tsakanin ki da
Mujaheed har yanxu koh?" Imaan ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, Farida
tayi murmushi tace "Toh ki saurari duk abinda xan gaya maki
yanxu...." a hankali Imaan ta kalleta tace "Toh" Farida bata
fito bedroom dinta ba sai kusan sha biyu na rana shi ma don Imaan tace mata
yunwa take ji bata yi breakfast ba shine ta fito hada mata breakfast, Har lkcn
Mujaheed na parlor tare da Dr Khaleel da bai gajiya da labari, shi dai gaba
daya hankalinsa yyi kan Imaan sanin bata yi breakfast ba har lkcn, Farida tayi
murmushi tana kallonsu tace "Sannun ku da hutawa" Mujaheed na
kallonta yace "You tell imaan lkci ya wuce fa, this is after 12"
Farida tace "Haba nan da bayan azahar ba sai ku wuce ba Dr, ni ban gaji da
ganin kanwata ba, kayi wucewarka kawai anjima xa mu maida ta gida...." Dr
Khaleel na kallon Mujaheed yace "Ba yini ku ka xo yi mana ba dama
Dr?" Mujaheed yyi murmushi yace "Xa mu yi bak'i ne daga kaduna, suna
ma hanya yanxu" Farida dai bata tanka sa ba ta shiga kitchen, eggs ta soya
ma Imaan, ta hada mata shayi mai kauri, ta debar mata pepper soup din da tayi
da safe sannan ta dau bread duk ta daura su kan tray ta fito kitchen din, ganin
abinda ke hannun Farida hankalin Mujaheed ya kwanta don shi damuwarsa kenan
dama, daki Farida ta kai mata abincin ta ajiye saman carpet, Imaan ta sakko
kasa, Farida tace "Bari inje in daura white rice, nayi stew daxu da safe"
Imaan tace "Toh" daga haka Farida ta fita dakin, a hankali Imaan ke
shan shayin hannunta, da ta tuna wasu daga abubuwan da Farida ta gaya mata sai
tayi murmushi ita kadai, wani kuma ta turo baki, wani kuma idan ta tuna a ranta
tace tabdi, da tuna wai Safeenah xata iya kwace Yaya ya daina kulata sai ta
hade rai, shayi kadai ta shanye cikin
abubuwan da Farida ta kawo mata, sannan ta mike ta dau tray din ta fita don kai
wa kitchen, tunda ta fito Mujaheed ke kallonta, suna hada ido ta sunkuyar da
kai ta karasa cikin kitchen din ta ajiye tray din, Farida dake wanke wanke tace
"Toh baki ci egg din da yawa ba ai Imaan" Imaan tace "Aunty na
koshi wllh" Farida tace "Toh nasan Mujaheed xai ce xa ku wuce yanxu,
ki tafi daki ki harhada duk abinda na baki a leda, kin xo da jaka ai?"
Imaan ta girgixa mata kai, Farida tace "Ohk toh ki tafi dakin ina xuwa
yanxu" Imaan na fitowa parlor suka kara hada ido da Mujaheed da ya mike
tare da mijin Farida xa su wuce masallaci don lkcin sllh yayi, Yana kallonta
yace "After prayer xa mu wuce" ba tare da ta kallesa ba tace
"Toh" sannan ta wuce ciki, ba a dau lkci ba Farida ta shigo dakin,
daya daga sabbin jakanta na aure ta ciro ta kwashe gaba daya kayan da ta debar
ma Imaan ta xuba a ciki tace "Hope you remember all what I said??" a hankali
Imaan ta gyada mata kai, Farida tace "In sha Allah may be next tomorrow
xan xo gidan naku kin ji?" Imaan ta marairaice tace "Aunty me yasa
baxa ki xo gobe ba?" Farida tayi murmushi tace "A'a gwara dai jibin,
in sha Allah xan xo kanwata" Imaan tace "Toh Allah ya kai mu, Aunty
ban xo da Hijabs dina daga gida ba, did you have hijab to give me in dinga sllh
da shi, am having just this one I am wearing" Farida tace "Ohk"
mikewa tayi ta bude daya daga akwatunanta ta fiddo sabon hijab a leda tace
"Sai dai bai kai kasa ba nasan ke har kasa kike sa wa" Imaan tayi
murmushi tace "Nagode Aunty bari in yi sllh kafin ya dawo...." daga
haka ta mike ta shiga bayi don dauro alwala. Sai karfe daya Imaan suka bar
gidansu Farida bayan Farida da mijinta sun rakosu har bakin mota, a back seat
Imaan ta ajiye warmer din abincin da Farida ta tilasta mata sai ta tafi da shi
sannan ta bude front seat ta shiga, Mujaheed ya kara sallama da Dr khaleel ya
ja motar, Imaan na daga ma Farida hannu, sai da suka hau saman titi ya kalli jakar
hannunta yace "Jakar meye Wannan?" Ta turo baki tace "Ta bani
kyauta ne, ta ga ban xo da jaka ba" murmushi yayi bai ce komai ba, bayan
few minutes yace "Idan kika gama haifa min yara na sai in maki lefen ki
ko?" ko kallonsa bata yi ba ita dai tana rungume da jakar hannunta don
Farida tace mata kada ta yarda ya ga abinda ke ciki, Sai da suka kusan gida
Mujaheed yace "Ammi fa tana gida, ta xo" Imaan ta kallesa da sauri
tace "Ammi?? Da gaske Yaya?" Yace "Ehh" murna ta fara yi
kamar yar yarinya a motar, ganin murmushin da yake ta dakatar da murnar ta
marairaice tace "Don Allah Yaya kace min wllh don ni ban yadda ba, kila ba
da gaske kake ba" shi dai murmushi kawai yake, lkci daya ta daure fuska,
yace "Toh Ammi baxa ta iya xuwa ganin ki ba kenan" turo baki tayi
tace "Nasan Ammina baxa ta iya xuwa ba" yace "Why?" Tace
"Ni dai nasan she can't" yace "Toh idan muka je kika ganta me
xan maki?" Ta kallesa da sauri sai kuma tayi murmushi tace "Idan muka
je naga da gaske ta xo xan baka dubu goma" ya gyada kai still smiling yace
"Idan kuma ba mu ganta ba fa?" Ta turo baki tace "Sai ka siya
min waya" ya wara ido yace "Uhn???" Tace "Ehh" yyi
murmushi yace "Toh ban yadda ba dubu goma da kika ce yyi kadan" tace
"Toh me xan baka?" Ya shafa kansa yace "Dubu goma with kiss and
hug" Ta wara ido, sai kuma ta rufe fuska tace "Toh naji" yace
"Kin ji kika ce fa?" A hankali tace "Ehh" Yana murmushi
yace "In dai muka je muka ga yan gida ai duk daya ne koh?" Ta girgixa
kai da sauri tace "Noo, ni dai Ammina nace" parking yyi kofar gida ya
kashe motar ya sauka ita ma ta fito tana rike da jakarta, ta bude back seat ta
dau warmer din abinci bata ko kalli takeaways da yyi masu da safe ba ta nufi
gate, shi ya kwashe ledojin ya rufe motar sannan ya bi bayanta, still Imaan
tayi ganin motar gidansu a compound din, ta juya ta kalli Mujaheed dake tahowa
yana murmushi, lkci daya ta nufi cikin gidan da sauri ta bude kofa, sai kuma ta
tsaya tana kallon Mama Hadixa da Inna dake parlon, Mujaheed ya bude kofar shi
ma ya shigo, imaan ta ajiye warmer din hannunta ta nufi Mama Hadixa dake
murmushi ta fada jikinta cike da farin ciki tace "Oyoyo Mama, yaushe ku ka
xo" Mama Hadiza ta rungumeta tace "Daga ina ku ke?" Imaan na
washe baki tace "Mun fita ne Mama, yaya ya kai ni gun Aunty Farida, kin
tuna ta?" Mama Hadiza tace "Nan take aure ita ma?" Imaan ta
gyada kai tana murmushi tace "Ehh Mama" Mama Hadiza tace "Maa
sha Allah, amma kina cin abinci kuwa daughter naga kin rame" Imaan ta
sunkuyar da kanta tana murmushi, ita dai Inna na xaune fuska a murtuke ta kura
ma Tv ido, Mujaheed na murmushi ya karasa parlon ya ajiye ledan hannunsa ya
xauna kusa da ita ya mata side hug yace "Nasan dai wajena kika xo koh
inna?" Inna tace "Toh dama wajen wa xan xo idan ba kai ba Mujaheed,
ga damun nama can cikin cooler na maka" Dariya ya fara yi yana kallonta,
Imaan ta daga kai daga kwance da tayi jikin Mama Hadiza ta kalli Inna, mikewa
tayi ta dawo kusa da ita tana murmushi, cike da masifa Inna tace "Don
Allah yar nan ki rufa min asiri ki ja baya ba wajen ki na xo ba Allah shaida...."
Mama Hadiza ta dauke kai tana dariya, Imaan ta turo baki xata bar wajen
Mujaheed ya rikota yana dariya shi ma yace "Inna Imaan ce fa ko baki
ganeta bane" Inna tace "Wacece kuma Imaan??" Dariya kawai Mama
Hadiza da Mujaheed ke yi, Imaan xata bar wajen Mujaheed ya rikota ya xaunar da
ita gefensa, rufe fuskarta tayi jikinsa da sauri ta fara kuka, Mujaheed ya d'an
kalli Mama Hadiza dake dariya har lkcn, murya can kasa yace ma Inna "Tunda
kuka kika xo sa min matata, tashi ku yi wucewar ku mun yafe xuwan" Inna
tayi kamar bata ji sa ba fuska a murtuke, Mama Hadiza tace "Babu kowa
gidan ne? Ina ce kace min Safeenah ta dawo" Mujaheed ya kalli sama yace
"She is home, bata fito bane?" Inna tace "Au kana nufin tana
ciki??? Toh xan hau sama wannan mata Hadiza ta hanani, wai gidan mutane"
mikewa Mujaheed yyi ya wuce sama imaan ta bi sa da kallo, Inna na kallonta tace
"Toh bbu abinci gidan Mujaheed din ne kika rafke haka?" Imaan ta hade
rai ta dauke kai, Mama Hadiza tace "Debo ruwa kitchen in wanke ma Inna
garden eggs dinta" mikewa Imaan tayi ta dau ledan garden eggs din dake
ajiye kusa da babban trolley na kayanta da Mama Hadiza ta taho mata da shi ta
wuce kitchen tana kallon hanyar stairs, Inna ta kalli Mama Hadiza tace
"Wllh duk ta rame, kin ga abinda nake ta gudu kenan koh, dama duka duka
imaan din nawa take xa a ba katon nan? Ni dai ba ruwana wllh" Mama Hadiza
tace "Rashin kwantar da hankali ne da damuwa fa Inna, da alama kuma ta
fara hakura" Inna ta tabe baki tace "Ni dai ba ruwana" Har Imaan
ta gama wanke garden eggs din ta xuba su a bowl ta dawo Mujaheed bai fito
parlor ba, sai kallon stairs take, Inna tace "Ko yar mantina bbu gidan ne,
daga kaduna fa muke" Mama Hadiza ta saci kallonta bata dai ce komai ba.
Mujaheed na tsaye dakin Safeenah dake kwance saman gado fuska daure tana taunar
cingam, kana ganin idanuwanta kasan kuka ba na wasa ba ta ci, yana kallonta
yace "You are looking into my face and telling me baxa ki sauko ki gaida
iyayena ba Safeenah??" A mugun fusace ta mike xaune tace "Ehh, ko
dole ne Mujaheed? Don Allah ka rabu da ni ka fita, ni dai abinda na sani duk
wanda ya shiga hakkina a gidan nan Allah ya isa, kuma matakin da xan dauka wllh
sae ya girgixa kowa, ni gaida iyayena kake da xan gaida naka" da mamaki ya
dinga kallonta, trying hard to control himself, can ya juya ya fice daga dakin
ta bi sa da wani mugun harara tana kas kas da chewing gum, yana sakkowa
downstairs Imaan ta wani hade rai tana cin garden egg din Inna da ta dauka,
Inna na kallonsa tace "Safara'un bata nan ne...." Imaan ta cafke tace
"Tana daki" Inna ta xaro ido tace "Tana daki??? Duk uban sallama
da bubbuge bubbugen kofar da na dinga yi tana ji ta min shiru??" mikewa
Inna tayi ta wuce sama, Mama Hadiza tace "Don Allah Inna ki bari ki dawo
ki xauna, ni bana son hka" ko sauraronta Inna bata yi ba, Mujaheed dai ya
bi ta da kallo haka ma Imaan da taji mugun dadi har ranta, Inna ta bude dakin
farko da ta gani sai ga Safeenah kwance saman gado waya kare kunnenta tana jin
bude kofa ta katse wayar da sauri, Inna ta saki baki tana kallonta, can tace
"Amma ke dai barbadaddiya ce Safara'u, ashe kina cikin gidan nn kiji
shigowar dangin mijin ki kiyi mukus a daki kamar Mayya, Ni fa na haifi Uban
Mujaheed din, Hadiza kuma kanwar Ubansa ce, ashe ke salubabbiya ce
Safara'u?" Safeenah tun da ta kalleta sau daya ta dauke kai tana cin
chewing gum, Mama Hadiza ce ta hauro sama, Inna tace "Wllh ga ta nan
Hadiza ina mata magana ko gaisheni ma bata yi ba tana min cin cingam din
karuwai, anya wannan matar aure ce kuwa? Toh dadin abun dai ko kashi mai rai
bata ta6a haifa ma Mujaheed ta ajiye ba balle Ahmadu ya samu barbadaddun jikoki
kamar ta, kuma in sha Allahu Imaan ce xata cika gidan nan da 'ya ya muna nan da
ku...." Mikewa Safeenah tayi ta daina cin gum din bakinta tana kallon
Inna, duk xamansu da Mujaheed bata ta6a kawo haihuwa a rai ba sai ynxu da Inna
ke mata gori, Safeenah tayi wani murmushi tace "Warce uwarta juya ce xata
cika gida da 'ya ya?" Mama Hadiza tace "ke karamar mara kunya kama
kanki kada in baki mamakin da bakiyi tunani ba, mara tarbiya kawai shashasha,
tunda kika mana haka to har uwar da ta haife ki ma xaki iya walakantawa
haka" Safeenah tayi wani murmushin rainin hankali ta mike ta shige
bathroom tana cewa "Ae na xama kandagaren bakin tulu, babu yanda aka iya
da ni, Mujaheed dai ko an ki ko an so nice ta farko gidansa ba a isa a canxa
wannan ba" key ta sa ma bandakin, inna ta juya ta fita tana kwala ma
Mujaheed kira.... Mujaheed na ganin Mama Hadiza ta wuce sama dama ya mike ya
koma kusa da Imaan da ta hade rai, dauke kai tayi ya juyo da ita yana murmushi
yace "Our deal...." Mikewa take son yi ya ki bari ta tashi nan ya
rungumeta giving her a romantic kiss, ga mamakinsa bata yi yunkurin stopping
dinsa ba, sai dai yana jin yanda xuciyarta ke bugawa, muryar Inna da ya ji ya
sa shi saketa da sauri ya matsa daga kusa da ita, masifa kawai Inna take kamar
xata ari baki, Sakkowar Mama Hadiza ya sa Mujaheed ya mike, Mama Hadiza na
kallonsa rai bace tace "Har mu yar iskar yarinyar nan xata walakanta haka
Mujaheed??" Mujaheed ya kasa cewa komai, Inna ta xauna a hankali tace
"Ni har xagina ma tayi ban kulata ba" Mujaheed yace "Ku yi
hakuri don Allah Mama..." Mama Hadiza tace "In sha Allahu a dalilina
bbu abinda xai sami aurenta na dai san xata gani a kwaryarta, the main point
here is imaan baxata xauna gida daya da ita ba, sam baxai yiwu ba, tun wuri ka
fara shirin raba masu gida" Inna tace "Atoh, jikata baxata xauna da
mayya irin Safara'u ba wllh, yarinya shegiya kawai mara tarbiya ni take tauna
ma cingam tana balan balan da shi?? To wannan lafceciyar uwar tata tayi ma haka
ba ni ba" Shi dai Mujaheed bai ce komai ba amma sosai ransa yyi mugun
baci, Mama Hadiza ta xauna har lkcn ranta a bace tana girgixa kai tace
"Uwar ka dai ta cuce ka wllh, domin wannan ba yarinyar aure bace, kwata
kwata bata da kirki" Inna tace "Atoh, gwara da kika gane ma idonki,
da ni ce na koma gida nake fada karyatanin da kuka saba xa ku yi, barin mutumin
nan Bukar, a sannu xa ayi walkiya halin kowa ya fito nan ba da dadewa ba kuwa,
ni dai abinda na sani shine duk wanda ya kuskura ya ma jikata wani mugun abu to
wllh wllh watan mutuwarsa a duniyar nan ya tsaya cakkk don baxan yadda ba sai
na hallaka sa" ita dai Mama Hadiza bata ce komai ba. Mikewa tayi daga
karshe tana kallon Imaan tace "Mu tafi sama am not staying long here...."
Imaan ta mike a hankali ta bi bayanta, Mujaheed ya bi ta da kallo, sai da suka
isa stairs ta juya ta kallesa langwabar mata da kai yyi, ta make kafada ta bi
bayan Mama Hadiza, dakin da take suka shiga, Mama Hadiza na bin dakin da kallo
tace "Nan ne dakin ki?" Imaan tace "Tun da muka xo a nan
nake" Mama Hadiza ta xauna gefen gado tana kallonta tace "Babu
matsala koh?" Shiru Imaan tayi, Mama Hadiza tace "Kar ki ji komai ki
gaya min meye matsalar ki kinga soon xa mu wuce" Imaan ta durkusa kusa da
ita a hankali tace "Mama kawai dai sai matarsa ta yi ta tsokanata haka
daxu da safe ta shigo min daki tana xagina" Mama Hadiza ta bude ido sosai
tace "What?? Ta shigo tana xagin ki a kan me?" Imaan tace "Wai
na auri mijinta, kuma take cewa bai kwana dakina ba sai nata" Mama Hadiza
ta kankance ido tana kallonta rai bace tace "Shi Mujaheed din me ya hanasa
kwanciya dakin ki?" Murmushi imaan tayi kamar baxata ce komai ba sai kuma
tace "Ni ce nace bana so" Mama Hadiza tace "Ashe ke wawuya ce
ban sani ba, kuma Ina maki kallon me ilimi ashe ba haka ba imaan?" Imaan
ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, maganganu sosai Mama Hadiza tayi mata
yawanci duk babu banbanci da wanda Farida tayi mata sai abinda baka rasa ba,
ita dai kanta na kasa, Mama Hadiza tace "Idan ma xaki cire wannan kunyan
ki cire ni dai na gaya maki, idan ko ba haka ba kin dinga kwasan takaici da
gori kenan gun jakar kishiyar nan taki in har kika yarda ta gano abinda ku ke
ciki" Imaan ta goge hawayen dake sulalowa idonta a hankali tace "Toh
Mama" cikin kwantar da murya Mama Hadiza ta ci gaba da bata shawara sannan
ta daura da nasiha, Imaan na kallonta a sanyaye tace "Mama yaushe Ammi
xata xo ita?" Mama Hadiza tace "Ke ma kin san baxata xo ba, amma nan
da wata daya ai xai kai ki gida na sani" Imaan tace "Toh" Mama
Hadiza ta bude jakarta ta ajiye mata abubuwan da ta kawo mata ta yi mata bayani
sannan ta mike tace "You keep them safe sai ki fito parlor" daga haka
ta fita dakin, Imaan ta mike ta xubasu a jakan da Aunty Farida ta bata sannan
ta fita dakin ta harari kofar dakin Safeenah ta sauka kasa, Inna na xaune kan
carpet ta bararraje tana cin shinkafa da miyar da Farida tayi, Mama Hadiza ta
xauna tace "Ina Mujaheed din?" Inna tace "Ya je siyo maki
abinci, ni dai ga wani nan na samu" Inna na kallon Imaan tace "In har
kika yarda kika ba mayyar kishiyar ki daman raina ki baki dinga cin ubanta ba
to gaskiya an cuce ni da aka sa maki sunana, irin gallazawar da nayi ma uwarsu
Bala da Hansai ai sai Allah, komai sai yanda nace ayi xa ayi a gidan nan,
keee!! wllh ki kara kaifin bakin ki da fitsara..." Inna na nuna mata
bakinta tace "Kinga bakin nan nawa, to shi ya kwace ni a kuruciyata, kwata
kwata ban daukan nansans" Dariya Imaan ta fara yi, Mama Hadiza dai tayi
murmushi tana kallon uwar tata, Inna ta ci gaba da cin abincinta tace "Wacece
kuma Safara'u da cikin mintuna kalilan baxa ki kwace Mujaheed a wajenta ba, shi
fa Mujaheed wllh tun ba yau ba dama yake son auren ki, irin son da yake maki ba
ni har tsoro ya dinga bani lkcn, duk ina lura da shi yyi ta wani takura ki yana
sa maki ido d'an banxan, gashi yyi ta latse min ke kuma sbda bashi da tsoron
Allah, ashe dai kayansa ce ke, ohh Allah mai girma gashi yanxu har kin tare
gidansa kin kwana" Imaan ta rufe fuskarta da kujera tana murmushi, Mama
Hadiza ta fara dariya tana kallon Inna, inna ta tabe baki tace "Ni dai ba
ruwana, ashe dama Allah ya riga ya kaddara shi din dai ne mijinki, tohh ya muka
iya Mujaheed dai jikana ne kuma bbu wanda ya fi ni saninsa gaskiya...."
Shigowar Mujaheed ya sa Inna tayi shiru tana ci gaba da cin abincinta, Mama
Hadiza dai sai kallonsa take tana murmushi, ya ajiye ledan hannunsa yana kallon
Imaan da ta ki dago kanta, Inna ta kallesa ta gefen ido ta tabe baki, xaunawa
yyi yana kallon Mama Hadixa yace "Ga abinci na siyo maki Mama" Mama
Hadiza tace "Toh nagode" Mikewa inna tayi tana kallon Imaan tace
"Mu je in ga dakin ki" Imaan ta mike ta nufi sama Inna na biye da ita
Mujaheed ya bi su da kallo, Inna ta dinga bin dakin da kallo bayan sun shiga
sannan tace "Kina dai sane har yanxu Mujaheed bai maki lefe ba dai koh?
Kuma sadakin ma Ahmadu ne ya bada sbda lalacewa, To ba ruwana kada ki yarda ya
kai ki ya baro ki sai ya hada maki lafiyayyen lefe irin na Bulasawa gaskiya,
don ba sadaka aka basa ke ba" Imaan tayi dariya bata dai ce komai ba, inna
tace "Allah kuwa kar ki yarda ya shigar maki daki bai maki lefe ba ya kai
ki ya baro ba ruwana" Imaan sai murmushi take Inna ta xauna gefen gado
tace "Ita kuma Safara'u kar ki kuskura ki raga mata, ko mi ta maki ki rama
ke dai kar ki yarda ta kai maki hannu, da kinga haka ki ja bakin ki kiyi shiru
ki gudu tunda ba karfi ne dake ba, Ni fa nayi dambe yyi sau dari da uwar Bala
damben mu na karshe sai da na tsaga mata goshi, da tabon ta mutu, Allah dai ya
ji kanta ya gafarta mata, lafiya muka xauna da ita wllh matar kirki..."
Shigowar Mujaheed dakin yasa inna ta ja
bakinta tayi shiru, sai kuma ta mike tana kallon Imaan tace "Ke mu
je" imaan ta mike tana murmushi ta fita dakin Inna na biye da ita suka
koma parlor suka xauna. Karfe biyar saura Mama Hadiza tace "Toh inna ya
kamata mu kama hanya yanxu...." Inna ta katse ta tace "Haba Hadiza da
maraicen nan mutum ya kama hanyar kaduna yanda duniya bbu gaskiya ga yan
kinnappin da yan fashi kaca kaca a titi??" Mama Hadiza tace "Shi
tafiyar minti araba'in din ne dare yayi Inna??" Inna tace "Ni fa tun
ina gidan mijina in dai la'asar ya gota to bana bin babban titi" Imaan dai
sai murmushi take, Mama Hadiza tace "Abinda nan da yan kwanaki ma xa su
dawo kadunan Inna" a fusace Inna tace "Toh me kike nufi? Nufin ki
xama nake son yi masu a gida tsofe tsofe da ni koko? Da ba don maraice yyi ba
me xan xauna in yi Hadiza?" Mama Hadiza ta mike ta dau handbag dinta tana
kallon Imaan tace "Tafi ki ce ma Mujaheed xan koma" dai dai nan
Mujaheed ya sakko parlon, yace "Mama ba dai tafiya ba?" Mama Hadiza
tace "Wucewa xan yi, sai ayi ta hakuri kuma" Mujaheed ya saci kallon
Inna da ta hade rai tana kallon Tv sai kuma ya kalli Mama Hadiza yace "Is
she staying here" Mama Hadiza tace "Don Allah ni dai mu je ku raka ni
in wuce" daga haka ta nufi kofa, Mujaheed ya kara satan kallon Inna sannan
ya bi bayanta, Imaan na kallon Inna murya can kasa tace "Kar ki tafi Inna
kiyi xaman ki a nan kin ji" Inna ta tabe baki tace "Yanxu xuwa xata
yi ta 6ata ni gun 'yan uwanta su kullace ni ko don ba ni na haife ku yasa suke
min walakancin nan oho, bari dai in tafi kada a sa ni a bakin duniya, amma duk
abubuwan da na gaya maki kar ki kuskura ki watsar don xa su maki amfani, in sha
Allahu nan da kwana biyu tun da naga gida ko shawara da su Ahmadu baxan yi ba
sai dai su ga wayam bbu ni, tashi mu je ki rakani...." Imaan ta mike kamar
xata yi kuka ta bi bayanta, fuska daure Inna ta shige bayan mota Mama Hadiza
dai bata ce komai ba, Mujaheed ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, Imaan ta
fara hawaye Mama Hadiza tace "Meye haka?
Bana son shashanci fa" juyawa tayi ta koma ciki tana share hawayen
idonta.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
90.....
Mujaheed na komawa parlor bayan su Mama Hadiza sun wuce ya
dau trolley din da suka kawo ma Imaan ya kai mata daki, xaune ya sameta ta
jinginar da kanta jikin gado tana hawaye, ya ajiye jakar ya isa kusa da ita ya
xauna yana kallonta, Hade kai tayi da gwiwa tana kuka a hankali, ya dagota yace
"Ohk I am taking you home next week in sha Allah, yayi hakan?" Tana
kallonsa cikin sanyin murya tace "Da gaske?" Yayi murmushi ya ja
hancinta yace "Ehh mana, ko Yaya ya ta6a maki karya ne" Ta goge
idonta tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Baki yi lunch ba har
yanxu" tace "Bayan abincin da na ci gidan Aunty Farida, I am not
hungry" mikewa yayi yace "Let me get something outside" Bai jira
cewarta ba ya isa kofa ya cire makulli ya fita ya kulle dakin ta waje, turo
baki tayi ta mike ta kwantar da jakar da ya ajiye mata ta bude zip din,
gogaggun kayanta ne kusan kala goma sai Hijabs har kala Biyar a babban jakan da
inner wears, sai turarurrukanta da man shafa, rufe jakar tayi a hankali ta ja
sa gefe ta ajiye sannan ta koma gefen gado ta xauna. Sai kusan karfe shidda
Mujaheed ya bude dakin yana kallonta daga bakin kofa yace "Come
downstairs" sai da ya bar bakin kofar sannan ta mike ta fita dakin tana
kallon dakin Safeenah ta sauka downstairs, xaune ta samesa parlon da pineapple
da aka yi slicing a plate, ta karasa ta xauna tana kallon movie da ake a Tv,
yace "Baxa ki sha ba?" Kallon abarban tayi sannan ta dauke kai, ya
mike ya dau plate din ya nufeta ya xauna kusa da ita, a hankali ta dau daya ta
sa a baki, yyi murmushi yana kallon eye balls dinta ta hade rai tace "Ni
dai ka daina kallona" ya jawota jikinsa yace "Ohk na daina" suna
nan haka har kusan Magrib suna kallon movie da ake yi a TV, Jin footstep a
stairs duk suka juya, Safeenah ce ke sakkowa sama fuska a murtuke, suka hada ido
gaba daya da ita, a hankali Imaan ta kwantar da kanta saman shoulder dinsa,
Safeenah bata sake yarda ta kallesu ba ta wuce kitchen, Mujaheed dai bai sake kallonta ba Imaan ta bi ta da harara,
Mujaheed dake lura da ita yyi murmushi ya daura lips dinsa a cheeks dinta murya
can kasa yace "Me ta maki?" Hade rai tayi ta kallesa, ya wara ido ya
rungumeta yace "Toh yi hakuri" lamo tayi jikinsa, bayan kusan minti
biyar sai ga Safeenah ta fito kitchen din ko ba a fada ba kasan yunwa take ji,
suka kara hada ido da Imaan ta dauke kai da sauri ta wuce sama kamar xata tashi
sama, shi dai Mujaheed bai ce komai ba, jin ana kiran sllh ya mike yace
"Me xa ki ci sai in taho maki da shi when I am coming back from
mosque" tace "Ae akwai abincin da muka siyo" yace "Noo ae
ya huce" d'an murmushi tayi tace "Almubazzaranci Kuma?" Shiru
yyi yana kallonta, tace "Sae ka dawo" daga haka ta mike ta wuce sama,
a hankali yace "Imaan" ta juya tana kallonsa yace "Ki sa makulli
daki idan kin shiga" Kai kawai ta gyada masa ta wuce sama shi kuma ya
fita, imaan ta kusa idar da sllhn Magrib taji ana murda kofar dakin, tana
idarwa ta nufi kofar a hankali tace "Waye?" Muryar Safeenah ta ji
tace "Idan ba tsoro ba uban me yasa kike sa makulli a kofa, banxa
matsoraciya karuwa kawai...." Imaan tayi murmushi tace "Sbda bani da
lkcn biye ma jahila in daura ma kai na xunubi shi yasa nake rufe kofata, when
ever I have ur time I will leave my door open, wahalalliya kawai" Bubbuga
kofar Safeenah ta dinga yi da mugun karfi tana kunduma mata mugayen ashar tana
cewa "In kin haifu cikin uwarki ki bude kofar nan yanxu ki ga abinda xai
faru, wllh in doke ki in doki banxa in ga uban da xai tsaya maki" Dariya
Imaan tayi tace "Allah ya baki lfya, kina ta6a ni xa ki sha mugun mamaki
idan kika ga mijin ki ya tsaya min, mate din ki masu ji da karfi boxing suke yi
why not ke ma ki fara da ki zo nan kina xubar da mutuncin ki gun 'yar cikin
ki" Safeenah tayi wani kara ta kunduma mata wani xagin tace "Ki bude
kofar idan ke ba shegiya bace" Imaan tace "Shegun biyu a nan ai, jarababbiya
kawai" daga haka Imaan ta koma gefen gado ta xauna tana murmushi, Safeenah
sai buga kofar take kamar xata cire, imaan bata sake kulata ba har ta bar kofar
tana ci gaba da zage xage, sai kusan bakwai da rabi Mujaheed ya shigo gidan, ya
kwankwasa kofar Imaan, mikewa tayi ta isa gun kofar ta tsaya, ganin ba a bude
ba Mujaheed yace "Imaan" bude kofar tayi yana kallonta yace
"Have u prayed" Bata basa amsa ba ta nufi kan gado ta xauna ta fashe
da kuka, da mamaki ya karasa kusa da ita yace "What happened???"
Cikin rawar murya tace "Ko ba matarka bace ta xo tana ta xagina tana
bubbuga kofa wai xata dokeni, har da ce min karuwa" sae ta kuma fashewa da
kuka sosai amma ba hawaye, mikewa yyi ya fice daga dakin, ta bi sa da kallo
tana turo baki, Bude kofar dakin Safeenah yyi ya sameta xaune gefen gado waya
kare kunnenta tana hawaye, katse wayar tayi lkci daya ganinsa, Yana kallonta da
kyau cikin daga murya yace "Let me drop u this warning Safeenah, even by
mistake, I mean mistakenly kika sake yi ma Imaan kallon banxa a gidan nan balle
ki gaya mata magana mara dadi I will show u the other side of me, I will show
you the bad side of me, Billah xa ki iya min komai in shanye in kyale ki amma
banda ta6a Imaan, idan kuma kin xata wasa nake try anything silly for the second
time wllh i will make you regret it" Wani murmushi tayi tace "Toh mu
xuba mu ga" daga haka ta shige bandaki tayi banging kofar ta rufe. Imaan
har ranta taji dadin samun Safeenah da Mujaheed yyi kuma duk tana jin abinda
yace mata don a bude ya bar kofar, parlor ta sauka don warming din abinci ranta
fess. Karfe goma Imaan na xaune gaban mirror tana shafa cream din gashinta a
kai aka bude kofar dakin ta juya da sauri, ganin Mujaheed ta ci gaba da shafa
man da take, Karasawa yyi kusa da ita ya mika mata wayar hannunsa ta karba tana
kallon screen din kafin ta kai kunnenta, ya juya ya fita dakin, tana murmushi
tace "Ina yini Aunty?" Daga daya bangaren Aunty tace "Lafiya lau
Imaan ya ku ke?" Imaan tace "Alhmdllh, Aunty yaushe su Maimoon xa su
xo?" Aunty tace "Idan kun dawo kaduna xa su xo daughter" a
hankali Imaan tace "Toh Aunty" Aunty tace "Ki kwantar da
hankalinki kinji Imaan, What happened is the best for you in sha Allah, kuma
Babu ruwanki da abokiyar xaman ki" imaan bata iya ta ce komai ba, Aunty
tace "Toh sai da safe" Murya can kasa tace "Nagode Aunty"
daga haka Aunty ta katse wayar Imaan ta ajiye a sanyaye ta ci gaba da abinda
take, daga karshe ta mike ta hau saman gado ta kwanta, Mujaheed ya shigo dakin
ya dau wayarsa dake gaban mirror ya dawo kusa da ita ya xauna yace "Ain't
you taking the fruits again?" Girgixa masa kai tayi, yace "Toh in
kira maki Ammi?" Mikewa xaune tayi da sauri tace "Ehh pls" yayi
dialing number Ammi ya mika mata sannan ya shiga bathroom, Ammi na dagawa daga
daya bangaren Imaan taji dadi har ranta, sallama Ammi tayi, A sanyaye Imaan
tace "Ina yini Ammi?" Ammi tace "Lafiya lau Imaan, ya
kike?" Imaan tace "Alhmdllh, Ammi Daddy na fa?" Ammi tace
"Yana Abuja" Imaan ta yi shiru, Ammi tace "Kiyi hakuri Imaan,
Allah plans best, Allah yasa hakan shine ma fi alkhairi gare ki, ki kwantar da
hankalin ki" Imaan ta d'an yi murmushi cikin sanyin murya tace "Ae
nayi Ammi" Ammi tace "That's good...." Imaan tace "Toh me
yasa Ammi ba ku xo da su Mama Hadiza ba?" Ammi tace "In xo in maku
me?" Murmushi kawai Imaan tayi a hankali tace "Ina missing din ki
ne" Ammi tace "Idan kin xo gida xa ki gan ni ai" Imaan tace
"Toh Ammi" Ammi tace "Babu ruwan ki da kula abokiyar xamanki kin
dai ji me na ce maki komai ta maki kar ki tanka, ki yi hakuri" Imaan tace
"Toh Ammi" Ammi tace "Toh sai da safe" Imaan ta kalli kofar
bathroom tace "Baxa ku gaisa da Yaya ba Ammi?" Katse wayar Ammi tayi,
Imaan ta dinga kallon screen din sannan ta ajiye wayar ta kwanta ta lumshe ido,
tana ji Mujaheed ya fito yayi shirin bacci sannan ya dawo kusa da ita ya dau
wayarsa da ta ajiye gefenta yana kallon fuskarta, yace "Tashi ki sha drugs
din ki" A hankali ta bude idonta tana kallonsa, ya mike ya dauko mata
Magungunan ya ajiye mata sannan ya fita downstairs dauko ruwa, har ta bude
Magungunan kafin ya dawo, ya mika mata ruwa a glass cup ta amsa ta sha maganin,
ya fita da cup din ta koma ta kwanta haka kawai gabanta ke faduwa, ya shigo ya
kashe wutan dakin ya kwanta daya side din yace "Did u perform ablution
before going to bed?" Bata amsa masa ba ta juya masa baya, Bayan kusan
minti goma ya mirgina a hankali ya dawo kusa da ita, juyowa tayi da sauri tana
kallonsa cikin sanyin murya tace "Yaya" Jin yanda xuciyarta ke bugawa
murya can kasa yace "Are you okay?" Ta girgixa masa kai lkci daya
hawaye ya kawo idonta, kallonta ya dinga yi cikin duhun, a hankali ta rufe ido
ta daura kanta jikinsa cikin sanyin murya tace "Bacci nake son in yi"
d'an murmushi yyi ya rungumeta, ya kwantar da murya yace "Kiyi baccin ki,
don't be afraid" Bata ce komai ba tayi lamo jikinsa har lkcn yana jin
yanda xuciyarta ke bugawa, sai da ya ji saukan numfashinta alamar bacci ya fara
daukanta bayan wani lkci ya daura lips dinsa forehead dinta ya lumshe ido cikin
sanyin murya yace "I... i love you" Bude ido tayi da sauri, ya kankameta
yace "Bacci nace kiyi kanwata" Bata san lkcn da tayi murmushi ba ta
lumshe ido ta mayar da kanta... Wajajen karfe biyu na dare Imaan ta farka ta
gansa tsaye yana sallah, mikewa xaune tayi ta sauka saman gadon ta shiga
bathroom ta dauro alwala ita ma ta fito ta bude jaka ta dau daya daga Hijabs
dinta. Washegari da karfe goma na safe Mujaheed na tsaye bakin kofar kitchen
bayan sun gama breakfast Imaan na wanke plates din da aka yi amfani da, ko na
minti daya bai yarda ya bar ta ita kadai ba, ko me xata yi outside her room
yana tare da ita, kuma tun da gari ya waye Safeenah bata sakko ba shima bai je
dakinta ba, Kamar ance ya juya ya ganta ta sakko stairs yafe da mayafi ta nufi
kofar fita, ya bi ta da kallo ganin xata fita, calmly yace "Where are u going
to?" Ko kallonsa bata yi ba har ta fice daga gidan, Imaan ta tabe baki
tana ci gaba da aikin da take. Sha biyu saura Mujaheed ya fita gidan don siyo
ma Imaan dake masa complain din ciwon kafa maganin tube da take shafawa, tun
wayewar gari take ce masa kafarta na ciwo, yana fita dama yace ta saka makulli
kofarta, Safeenah ce xaune parlor tana ta communicating da 'yan gidansu da suka
shigo garin zaria tana masu kwatancen gida, bell taji aka danna daga karshe, ta
mike taji sanyi har ranta ta isa kofar ta bude tana cewa "Ashe kun ma
kusa...." Umma ce tsaye bakin kofar, Safeenah ta dinga kallonta daga sama
har kasa, a takaice tace "Daga Ina kuma wa kike nema??" Umma ta bude
baki tana kallonta da mamaki tace "Wa nake nema Safeenah??" Cike da
rainin wayo Safeenah tace "Kinga.. tun ina danne xuciyata muna magana a
mutunce ki juya asirin ki a rufe ki bar gidan nan Hajiya Rukayya...." Umma
ta katse ta tace "Ehh lallai kin cika yar iska mara mutunci Safeenah ni
kike gaya ma haka a gidan d'a na? Ni????" Safeenah tayi wani dariyar
rainin wayo tace "D'an ki? D'an ki fa kika ce? To wllh you are mistaken,
kuma xaki san a da Mujaheed yake d'an ki, a da kike da iko da shi ba yanxu ba,
bari ki ji abinda baki sani ba... Ke da Mujaheed sai dai hange daga nisa, sai
kin san mu gidan mu ba bokaye muke bi ba matsafa masu shan jinin mutane muke
bi, kuma tun muna magana ta fatar baki cikin mutunci ki juya ki ja tsummar
kazamar rayuwarki ki bar gidana, shaidaniya annami...." Wani wawan mari
Umma ta sauke mata tana huci, ta kuma sauke mata wani, Safeenah ta dafe
kuncinta ta yo waje da ido da karfi tace "Ni kika mara Hajiya Rukayya?? Ni
kika mara?" Umma na nuna ta cikin bacin rai tace "Na mare don uwarki,
sakayyar da xa ki...." Umma bata rufe baki ba Safeenah ta sauke mata nata
tagwayen marin masu lafiya, Umma ta gigice ta dafe kuncinta cikin shock tace
"Ni kika mara Safeenah?" Cikin tsawa Safeenah tace "An mare ki
Rukayya kiyi abinda xa ki yi, nace na mare ki, uban waye ke da baxan mare ki
ba, meye a ciki don na mari shugabar bokaye da malaman garin kaduna?" Duk
wannan abun Imaan na tsaye stairs tana kallonsu don da karfi Safeenah ke
magana, lkci daya Umma ta shako Safeenah da karfi tana huci tace "Yau sai
dai wata ba ke ba don ubanki, yau sai dai Mansura ta haifi wata" Safeenah
ta cakumota ita ma, nan suka fara dambacewa bakin kofar suna ba juna kashi ba
kakkautawa, Safeenah ta samu nasaran hayewa kan Umma ta dinga dukanta iya
karfinta tana huci tana cewa "Sai na illata ki yau yanda baxa a gane ki ba
idan kika bar gidan nan, ta dalilin hassadan ki da bakin ciki da mugun hali aka
min kishiya kika dinga ja na gidajen bokaye da malamai don a lalata auren
yarinya da saurayinta har aka fasa auren aka makala ma mijina, kin cuce ni, kin
cuce ni, kin yaudare ni, Allah ya isa tsakanina da ke, axxaluma, wllh sai na
illata ki yau duk abinda xai faru sai dai ya faru...." Kasa motsi Imaan tayi da farko ta makale
jikin stairs tana kallonsu, ganin duka ba na wasa take ma Umma ba ta sakko da
sauri tayi kan Safeenah, Safeenah na ganin haka ta raba hankalinta biyu wanda
hakan ne ya ba Umma da jini ke fita bakinta da hanci damar hankadeta da karfi
daga kanta ta shako wuyarta, Mari me lafiya Imaan ta wanka ma Safeenah ta fixgo
gashinta da karfi tace "Yau na tabbata ke jaka ce, jahila kuma
mahaukaciya.... " Safeenah tayi wani kara xata fixgo Imaan Umma ta danneta
kasa, nan suka hade da Imaan suka dinga jibgarta tana ihu, Imaan bata ta6a
sanin tana da karfi haka ba, don dukan Safeenah take kamar an aikota, hakan yyi
dai dai da shigowar Hajiya Baturiya da Hajiyan Marafa da wata kawarta, a rikice
Hajiyan Marafa ta dinga salati tana komawa baya, Imaan na ganin haka ta daga
Safeenah da sauri, tana jan Umma da ta mike ita ma su bar wajen, Hajiyan Marafa
ta durkusa gaban Safeenah da jini ke xuba bakinta tana salati da karfi tana
cewa me xan gani haka, Hajiya Baturiya tayi wani kukan kura kamar mahaukaciya
tayi kan Umma da ta nufi stairs da gudu tare da Imaan.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
91.....
Imaan da har wani rawa jikinta yake ta bude kofar dakinta
bayan sun haura sama kamar kiftawar ido ta shige, kiris ya rage Hajiya Baturiya
ta cafke Umma, Umma ta shige dakin da mugun sauri ta tura kofar da karfi Imaan
na taya ta suka sa makulli, wani mahaukacin bubbuga kofar Baturiya ke yi tana
kunduma ma umma munanan ashar tana cewa sai ta illata ta yau, Imaan dai na
tsaye tana kallon kofar gabanta na faduwa sosai ta dinga sauke numfashi, bayan
kusan minti biyar ta juya a hankali ta ga Umma xaune bakin gado ta rike kai sai
sauke numfashi take ita ma, dauke kai Imaan tayi ta tafi gun window ta tsaya,
har lkcn Baturiya da Hajiyar Marafa basu fasa bubbuga kofar kamar xa su balla
ba suna tsine ma Umma suna cewa idan ta isa ta fito, Imaan dai sai kallon kofar
take tana tsoron kada ya balle su shiga uku, don ba bugun wasa suke ma kofar
ba, jin budewar gate ta juya da sauri tana kallon compound ta window, Mujaheed
ne yayi parking ya fito daga motar hannunsa rike da leda, wani ajiyar xuciya
Imaan ta sauke, lkci daya ta ji hankalinta ya kwanta, jin su Baturiya basu
hakura da buga kofa ba suna tsine tsine ta nufi kofar tace "Lallai da
gaske kun cika dangin mahaukata gantalallu, mu kuma ba mahaukata bane shi sa baxa
mu kula ku ba, kuma aniyar ku ta bi ku" Muryar Safeenah taji da karfi tana
cewa "Wllh wllh sai dai matsiyaciyar uwar ki ta haifi wata yau, sai kin
san kin ta6a ni yau, sai nayi rugu rugu dake na illata ki, na lalata maki
kamanni na maki wannan alkawarin" Imaan tayi wani dariya har da tafe hannu
tace "Nasan darajan iyaye ni baxan xage iyayen ki ba, duk da sun gama
xagin kansu tass a idona, don tunda nake ban ta6a ganin gantalallu marasa aikin
yi irin family din ki ba, kuma a kanku tsiya ya kare, ga alama na gani"
Imaan na fadin haka ta juya tana murguda baki ta koma gun window, xage xage
suka dinga yi in Unison kamar barbarians ko wacce na fadin abinda xata ma
Imaan, Umma dai har lkcn tana xaune ta rike kai, Muryar Mujaheed Imaan taji da
mamaki yana cewa "What's happening here?" Babu warce ta tankasa
cikinsu, sai dai duk sunyi tsit sai kas kas din chewing gums, Hajiyan Marafa da
kawarta da Baturiya suka ja gefe suka tsaya ko wannensu na huci, Mujaheed ya
daure fuska sosai yana kallon Safeenah cikin daga murya yace "I am asking
you Safeenah me ke faruwa a nan?" Safeenah dake tsaye da kumburarren baki
tana masa wani shegen kallo cikin tsawa tace "Ban sani ba Mujaheed"
Kofar dakin Imaan ya nufa da sauri yana bubbugawa yace "imaan? Imaan?"
Fashewa Imaan tayi da kuka sosai ta iso kusa da kofar cikin rawar murya tace
"Yaya cewa fa suka yi xa su kasheni" Mujaheed ya kalli Safeenah da
sauri yace "What?? Hauka kika fara yi Safeenah?" Hajiyan Marafa tace
"Uwarka Rukayya ce mahaukaciya ba 'ya ta ba Mujaheed, nace uwarka ce mahaukaciya.."
kallonta kawai Mujaheed ke yi ko kiftawa bbu, lkci daya idanuwansa suka sauya
kala, ya dauke kai cikin daga murya yace "Open the door Imaan" a
hankali Imaan ta murda makullin kofar ta bude kadan ba duka ba, Safeenah na
ganin haka tayi kanta da gudu xata fincikota tana huci, cikin zafin nama
Mujaheed ya hankadeta a tsawace yace "What are you trying to do??"
Shiga dakin yyi ba tare da ya shirya yin hakan ba ganin Hajiyan Marafa da
Baturiya sun tunkaro kofar da sauri, ya rufe kofar ya sa makulli, Imaan ta
makale bayan kofar xuciyarta na bugawa, still Mujaheed yyi ganin Umma dake
xaune rike da kai gefen gado, da mamaki yace "Umma...." Sai a lkcn
Umma ta dago kai tana kallonsa tace "Mujaheed kada auren Safeenah ya kara
minti biyu a kan ka, ka sallameta yanxun nan" tana magana hawaye ya fara
sauka idonta kamar an bude famfo, sai kawai ta rushe da kuka, Mujaheed ya
nufeta with shock ya duka gabanta yace "Me ke faruwa Umma? Me Safeenahr ta
maki??" kuka kawai Umma ke yi tana girgixa kai, irin kukan takaicin nan,
Mujaheed da ya rude gaba daya ya mike da sauri yana kallon Imaan dake makale
jikin bango har sannan yace "Tell me what happened Imaan, me ke
faruwa??" Imaan ta sauke idonta kasa, kamar baxa ta ce komai ba sai kuma
tace "Dambe tayi da Umma..." Da karfi yace "What?? Safeenar tayi
dambe da Umma?" umma na kuka tace "Kwarai kuwa Mujaheed, Safeenah ta
xageni ta daga hannu ta mareni sannan ta hau ni da kokuwa" kuka ne ya ci
karfinta, ta rike kai tana rusa kuka sosai, lkci daya idanuwan Mujaheed suka
kada sosai, ya juya ya nufi kofar ya bude ya fita, bai gansu corridor din rooms
din ba ya sauka downstairs da sauri, Ganin yanda Umma ke kuka Imaan ta nufeta a
hankali tace "Kiyi hakuri Umma" Umma bata kalleta ba kuma bata daina
kukan da take yi ba tana girgixa kai, Imaan ta sauke kanta kasa ta nufi kofa
walking slowly, dai dai staircase din karshe ta tsaya tana leko parlon kamar
munafuka, Hajiya Baturiya na xaune tare da Hajiyan Marafa da kawarta sai
Safeenah banda kundume kundume babu abinda suke suna kara fadin abinda xa su yi
ma Umma yau, Safeenah na ganin Imaan ta mike kamar mahaukaciya ta nufeta dw
gudu, Imaan na ganin haka ta juya da sauri xata gudu ta koma sama ta ci karo da
Mujaheed dake sakkowa a bayanta, shigewa jikinsa tayi jikinta na rawa, ya shiga
sakkowa stairs din a hankali yana rike da Imaan, Safeenah dai na tsaye tana
huci tana kallonsa don tunda take bata ta6a ganin irin expression din fuskarsa
ba tare da shi, can ta sauke idonta kan takardar hannunsa har ya iso gabanta ya
mika mata takardan looking straight into her eyes da idanuwansa da suka dawo
kamar garwashi, kin amsawa tayi tana kallonsa da idanuwanta da ta gwalo
xuciyarta na bugawa, ganin bata amsa ba ya isa kan kujera ya ajiye yana mata
wani kallon da ya firgitata cikin muryar da bata ta6a saninsa da shi ba yace
"I don't want to see you in my house in the next 30 mins
Safeenah...." Ba ita ba har Imaan sai da ta d'an yi shock jin furucin sa,
Hajiya Marafa ta mike da sauri ta isa gun takardar ta dauka ta warware, Ita dai
Safeenah na tsaye ta kasa ko da motsi tana kallon Mujaheed, lkci daya Hajiyan
Marafa ta ajiye takardan bayan ta gama karantawa ta nufesa da mugun sauri tana
kallonsa cikin daga murya tace "Mujaheed ita 'yar tawa xaka ma sakin
walakanci?? Ita Safeenahr ka saka" Bata jira amsar sa ba ta sauke masa
wani lafiyayyen mari, Mujaheed ya dinga kallonta ko kiftawa bbu, wani marin ta
kuma sauke masa ta cakumosa tana kunduma masa xagi tana huci tace "To wllh
karya kake, nace karya kake, baka isa bane, bbu saki a auren mu...." don
kanta ta sakesa bayan ta gama jijjigasa, ya sauke idonsa sannan ya nufi inda ta
jerar da takardan ya dauka da pen din ya fara wani rubutun a kai, cikin few
seconds ya nufi Safeenah dake tsaye kamar Status tana bin sa da kallo ya kamo
hannunta ya sa mata takardan cikin cool voice dinsa yace "Na sake ki saki
daya, saki biyu, saki uku, within the next 30 min ki tattara duk wani abu naki
ki bar min gida na, xa mu hadu a court da ku for insulting my own mother"
Imaan ta dinga kallon Mujaheed ko kiftawa bbu very shock as well, Muryar Umma
suka ji a stairs, a hankali tace "Allah ya maka albarka" Wani kara
Safeenah tayi cikin gigicewa ta nufesa tana cewa "Wllh ina sonka Mujaheed,
ka saurareni ka ji abinda yasa na aikata abinda na aikata, wllh mahaifiyar ka ce
ta ja min komai, ni ban san boka ko malam ba, wllh ita ta cuceni ta kai ni don
mu raba auren Imaan da Bulasawa, sai ga shi Allah ya nuna mana ishara an aura
maka Imaan din, she is the cause of everything happening here, don Allah ka
saurareni Mujaheed wllh baxan iya rabuwa da kai ba xan iya rasa raina, Ina
sonka Mujaheed...." Calmly Mujaheed yace "Ko da gun masu tsafi ta kai
ki I can't change her from who she is, she still remains my mother..." Duk
da wajen Umma Hajiyan Marafa ta yi niyyar nufa kamar wata xararriya amma ganin
Safeenah ta sulale kasa yasa ta tsaya gun 'yar tata ta durkushe kusa da ita ta
dagota ta fasa wani ihu, Hajiya Baturiya da kawar Hajiyan Marafa duk suka taho
gun cikin rikicewa, Mujaheed da idanuwansa suka koma kamar garwashin wuta ya
kama hannun Imaan da ta kasa motsi suka bar wajen, tuni Umma ta koma sama tana
goge hawayen dake sakko mata ba kakkautawa, xaune suka tadda Umma gefen gado ta
rike kai, Mujaheed ya isa kusa da ita ya durkusa cikin sanyin murya yace
"Kiyi hakuri Umma, I am sorry all this happened, don Allah Umma kiyi
hakuri..." kuka ta fara yi sosai ta kasa ce masa komai, Imaan dake tsaye
kusa da mirror ta sunkuyar da kanta ita ma hawaye ya cika idonta, Mikewa yyi
yana kallon Imaan yace "Get set we are leaving now" Yana fadin haka
ya fita dakin, Imaan ta nufi Umma dake kuka har lkcn ta durkusa a hankali tace
"Umma kiyi hakuri" Umma dai bata ce mata komai ba.... Su Hajiyan
Marafa sun kwasa gaba daya sun je kai Safeenah da ta ki farfadowa duk ruwan da
suka dinga xuba mata hospital, Bayan Umma ta fita dakin ta koma parlor ta xauna
Mujaheed ya shigo yana kallon Imaan dake rufe jakarta bayan ta dau Hijab,
xaunawa yyi gefen gado, ganin mood dinsa ta nufesa ta xauna kusa da shi a
hankali kafin tace komai ya kamo hannunta yace "Pls Imaan let this be a
secret between us, kar ki ce ma kowa komai a gida plss" ganin yanda
idanuwansa suka rine ta rungume sa a hankali tace "In sha Allah Yaya,
sorry about all what happened" sun fi minti biyu a haka sannan ta xame
jikinta tana kallonsa, mikewa yyi cikin sanyi yace "Am waiting for you
outside" daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo cike da tausayin sa har
ya fita, tasan shi daya yasan abinda yake ji ynxu, ace mahaifiyar ka ga abinda
take yi kuma tasan bbu karya a xancen Safeenah, shi ma kuma yasan haka, but dole
uwa uwa ce. Bayan few minutes Mujaheed ya bar gidan tare da Imaan da Umma after
making sure bai bar komai nata a cikin gidan ba, duk a compound ya bar mata su
kuma ya kulle gate dinsa ta waje, Imaan na xaune gaban mota abubuwan da suka
faru na sake dawo mata fresh, Umma dai tayi jigum bayan mota, Mujaheed kuma ya
maida hankalinsa gaba daya kan driving din da yake sai dai kana ganinsa kasan
yana tare da damuwa sosai, a haka suka shigo garin kaduna wajajen la'asar....
Imaan bata san lkcn da tayi wani murmushi ba lkci daya farin ciki ya baibayeta
ganinsu a layinsu, Mujaheed na isa gate yyi horn Mai gadi ya bude masa gate
yana daga masa hannu, bai iya ya tanka sa ba har ya shiga compound din yyi
parking, Imaan ta bude motar a hankali ta sauka, bayan ya sauka, Umma ma ta
sauka motar kanta a kasa, Imaan sai kallon apartment dinsu take tana jin kamar
ta tafi da gudu, bbu wanda take son gani lkcn sai Amminta, maimakon mai gadi ya
rufe gate sai ganin motoci har uku suka yi sun shigo compound din, Mujaheed ya
dinga kallon motocin haka ma Umma da ta daga kai tana kallo, Bude first car din
aka yi mahaifiyar Sadeeq ta fito motar cikin shiga ta alfarma sae ga wasu wa
enda da alamar kawayenta ne su ma sun fito, Umma ta dinga kallonta ko kiftawa
babu, lkci daya cikinta ya hautsine, tun da Imaan ta gansu jikinta yyi mugun
sanyi, Umma na hade hanya ta nufi entrance din parlor da sauri....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
92.....
Mama Hadiza xata fito parlor suka kusa cin karo da Umma bakin
kofa, Bin ta da kallo Mama Hadiza tayi ganin saurin da take yi kanta a kasa har
ta shige parlor, Mama Hadiza ta tabe baki ta fito compound din, imaan dai ta
kasa kallon direction dinsu kamar mara laka ta nufi apartment din su xuciyarta
na bugawa, Mujaheed ya gaishe su, Hajiya Khadijah ta amsa a takaice, bai kara
kallonsu ba ya wuce ciki walking slowly, Mama Hadiza na kallonsa ta amsa
gaisuwar da yake mata, bai tsaya ba ya shiga parlor ya rufe kofar, Mama Hadiza
ta nufi su Hajiya Khadijah tana masu sannu da xuwa duk da bata san su ba tace
"Toh ku shiga ciki mana" Hajiya Khadijah tace "Mai gidan mu ke
nema, Allah ya sa dai yana nan" Mama Hadiza tace "In ji dai lafiya
Hajiya?" Hajiya Khadijah tace "Lafiyar kenan dai, wajen sa muka
xo" Mama Hadiza tace "Ai kam bai nan...." Hajiya Khadijah ta
d'an yi shiru sannan tace "Kaninsa fa?" Mama Hadiza tace "Wai
lafiya Hajiya? I am their sister" Hajiya Khadijah tace "Sorry I
didn't introduce my self, ni mahaifiyar Sadeeq ce, kin gane yanxu kuwa?"
Mama Hadiza ta bude ido tace "Ohh Allah sarki sannu da xuwa Hajiya, to mu
shiga daga ciki mana, sannun ku da xuwa" Hajiya Khadijah tace "Yauwa
mun gode, amma tunda basa nan da mun tafi gun kakar Imaan din koh?" Mama
Hadiza tace "Ehh toh mu je can din, ai tana nan" Hajiya Khadijah tace
"Toh nagode" a tare suka tafi part din Inna da frnds dinta da Mama
Hadixa dake gaba suna biye da ita, Mama Hadiza ce ta fara shiga parlon Inna da
sallama, sannan su ma suka shiga, Inna ta fito daki rike da tsintsiya ta dinga
bin su da kallo, sannu suka shiga yi mata gaba daya, bata tanka su ba ta nufi
bakin kofa bayan sun shigo ta duka ta dau doormat tana kakkabewa a waje tace
"Sannu kuma sai kace me ciwo ni patuu" Mama Hadiza tace "Inna
mahaifiyar Sadeeq ce..." Mikewa Inna tayi da sauri tana kallon Hadiza tace
"Wacece mahaifiyar tasa?" Mama Hadiza ta nuna mata, inna ta saki
kabbara tace "Sannu baiwar Allah, lallai kin iya haihuwa, ynxu ke ce
mahaifiyar wnn yaro me kirki da mutunta babba? Eh lallai Allah ya baki..."
Hajiya Khadijah ta gaida ta with respect, frnds dinta ma duk suka gaisheta,
Inna ta amsa tana washe baki tace "sannun ku da xuwa bari in debo maku
ruwa" daga haka ta wuce kitchen ta dau faranti ta daura lemo biyu da ruwa
biyu ta kawo ta ajiye masu tace "Gashi ku dau daddaya ku sha, Allah ya
maku albarka" Hajiya Khadijah tace "Toh mun gode Kaka, dama gun mai
gidan na xo bai nan, shi ma mahaifin Imaan din yana Abuja aka ce min" Inna
ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Lafiya kuke nemansu?? Ba an mayar maku da
kaya kunce a bar shi ba, to gasu can dai a daki ko tsinke ba a ta6a ba har ynxu
a ciki" Hajiya Khadijah tace "A'a ba wannan ya kawo mu ba Kaka"
Inna ta sake fuska tana murmushi tace "Toh madallah, me ya kawo ku
kenan?" Hajiya Khadijah tace "Xuwa nayi, ga ni ga matar gidan nan, ga
Mai gidan, ga mahaifin Imaan da mahaifiyarta su tambayar min ita ko mai ni da
Sadeeq muka ta6a mata xata shiga ta fita ta hana aurensa da Imaan, idan kuwa
tace babu... to Billahil Azeem xan dau mummunan mataki a kanta, in dai ina
numfashi maganan nan baxai tafi a haka ba sai ta san ita ce silan bakin cikin
d'a na, kafin in dau mataki nace bari dai in xo ku tambayar min ita ko Sadeeq
ya ta6a mata wani abun ne...." Inna dake wurga ido tace "Ban fahimce
ki ba 'yar nan? Wace matar gidan a ciki kike nufi??" A takaice Hajiya
Khadijah tace "Uwargidan wan mahaifin Imaan, ita nake nufi" Inna tayi
wani dariya murya can kasa tace "Toh Alhmdllh, ke ma dai an gano maki ita
ta raba auren d'an ki da Imaan kenan? To na ji dadin xuwan ki gidan nan, na
kuma ji dadin yanda kika tsaya kan d'an ki ba wasa, yanxu abinda xai faru 'yar
nan hakuri xa ki yi har xuwa ranan lahadi duk inda uban Imaan yake dama xan
kirasa ya dawo don a kan idonsa xa ayi komai, sannan Ahmadu ma bbu inda xai je
ranan, duk xa mu hadu, ga ni, ga ki, ga autata Hadiza, ga uban Imaan, ga
bafillatana uwar Imaan, ga ita matar da ku ka xo nema ga kishiyar ta, to sai
ayi magana me ma'ana gaban kowa, da kanta xata bude baki ta fadi me tayi har
yasa aka fasa wannan aure mai albarka kaca kaca..." Hajiya Khadijah tace
"Toh nagode Kaka, Allah ya kara girma" Inna tace "Ameen yar
nan" mikewa Hajiya Khadijah tayi ta ma Inna da Mama Hadiza da ta kasa cewa
komai sallama ta nufi kofar, frnds dinta ma suka masu sallama duk suka fita,
Inna na murmushi tana kallon Mama Hadixa tace "Toh Alhmdllh ba a bakina
aka fara jin wannan xancen ba, Rukayya dai ta shiga uku ta lalace in matar nan
ta fallasa ta gaban kowa har shi Bukar, sai kuma in xuba ido in ga matakin da
Ahmadu xai dauka, shi kuma Bukar xan ga da wani bakin xai yi magana idan ya ji
wannan abun al-ajabin" sai kuma Inna ta fashe da kuka sosai tace
"Rukayya dai ta cuce mu, ta cuce mu, ta cuci jikata yanxu wannan mata da
ta fita da ita ce surkar Imaan fa" Mama Hadixa ta sauke ajiyar xuciya ta
dai kasa cewa komai duk jikinta yyi sanyi, a nan ta gane dalilin da yasa Umma
ke ta sauri daxu. Tun da Umma ta shiga daki take kuka kamar ranta xai fita
banda bugawa babu abinda xuciyarta ke yi, ta leka compound daga windown dakinta
ya fi a kirga amma bata ga alamar mahaifiyar Sadeeq da Mama Hadiza ba, tasan
kila suna can bangaren Inna, tunanin hakan yasa cikinta ya kara hautsinewa, don
tasan shkkn mahaifiyar Sadeeq ta gama fada masu har gida ta je ta sameta ta
6ata Imaan da mahaifiyarta, sai xaga dakin take tana salati hawaye na bin
idonta, da ta tuna ai sai dai su Abba su ji a bakin Inna ba dai directly daga
bakin uwar Sadeeq din ba sai hankalinta ya d'an kwanta, gwara innan ta fada
masu da bakinta, sun kuma santa da karin xance ko xa su yarda ba duka ba...
Ammi ta dinga kallon Imaan bayan ta shigo parlor da mamaki tace "Daga Ina
kike?" Imaan ta karasa da sauri ta rungumeta tana murmushi tace "Daga
gida Ammi, Ina yini" Ammi ta daga kanta tana kallonta tace "Ina
Mujaheed din?" Imaan tace "Tare muke, ya shiga gida" Ammi ta
dinga kallonta sannan ta saketa tace "Toh sannu da xuwa" Imaan ta
xauna saman kujera still smiling tace "Nayi missing din ki Ammi, Daddy
yana Abuja koh" Ammi tace "Ehh yana can, bari in sauke abinci"
daga haka ta koma kitchen, mikewa Imaan tayi a hankali ta nufi dakinta. Bayan
Magrib Imaan na xaune tana cin abinci sai dai gaba daya hankalinta yayi kan
Mujaheed ta rasa dalilin da yasa hakan, may be don ta san he is still sad ne
and there will be no one to console him, a hankali ta dinga cin abincin duk da
yanda tayi missing girkin Ammi amma turawa kawai take bbu appetite, Ammi ce ta
fito parlor daga dakinta rike da wayarta tana kallonta ta karaso cikin parlon
ta xauna tace "Imaan what's happening?" Imaan ta kalleta da sauri
tace "Na me Ammi?" Ammi tace "Me yasa ku ka taho gida?"
Imaan ta d'an Bude ido tace "Ya kawo ni ne kawai Ammi fa" Ammi tace
"Ya kawo ki kiyi me?" Imaan tace "Ba komai, anjima xa mu
koma" Ammi tace "Yanxu daddy ya kirani wai Inna ta kirasa ya taho
gida ranan lahadi" Shiru Imaan tayi tana kallonta, dai dai shigowar
Mujaheed parlon da sallama Imaan ta kallesa, ya karaso parlon yana kallon Ammi
ya xauna kansa a kasa yace "Ina yini Ammi?" Ammi tace "Lafiya
lau, sannu da xuwa" yace "Ya gida" tace "Alhmdllh"
Yace "Abba yana Abuja" tace "Ehh ya tafi" yace "Toh
Allah ya dawo da shi lafiya" Ammi tace "Ameen" daga haka Ammi ta
mike ta koma cikin daki, Mujaheed ya kalli Imaan dake ta kallonsa, sunkuyar da
kanta tayi tace "Have you eaten?" A hankali yace "Yeah" ta
kallesa tace "Nasan baka ci ba" ya d'an yi murmushi yana shafa kansa
yace "Na ci mana" kallonsa ta dinga yi, ya mike yace "Dama Ammi
na shigo gaidawa" Imaan tace "Xa kaje wajen Inna ne?" Girgixa
mata kai yayi ya nufi kofa, ta d'an saci kofar dakin Ammi sannan ta mike da
sauri ta bi bayansa. Har ya sauka balcony tace "Yaya" juyawa yayi ya
kalleta, ta isa kusa da shi tana kallonsa, a hankali tace "Plss in debo
maka abinci ka ci??" Ya matso da ita kusa da shi ya ja hancinta yace
"Wanda na ci fa?" 6ata fuska tayi tace "Wllh baka ci ba, ni dai
ka jira in debo maka" murmushi yayi a hankali yace "Toh debo
min" Da sauri ta juya ta koma ciki, ya bi ta da kallo, direct kitchen ta
shiga ta bude warmer din da Ammi ta xuba shinkafar da ta dafa, duk da bashi da
yawa sosai haka ta debar masa ta sa masa stew da nama hudu, ta rufe warmer din
ta juya xata fito taga Ammi tsaye bakin kofar kitchen din, ji tayi kamar ta
nutse kasa kawai ta huta, Ta kasa kallon Ammi ta fara kame kame bakinta na rawa
tace "Dama, dama abinci xan kai masa, Ammi shi ya tambayeni" Ammi
bata ce komai ba ta karasa cikin kitchen din, Imaan bata yarda ta kalleta ba
har ta fita kitchen din da sauri, tana shigowa parlor ta duka kusa da plate din
abincinta ta dau nama biyu ta kara a nasa tana satan kallon kofar kitchen din
sannan ta mike ta fita, bata gansa a waje ba, ta dinga bin compound din da
kallo amma babu alamar sa, part din su ta nufa kamar me counting step dinta ta
shiga parlon da sallama murya can ciki, babu kowa sai Tv dake aiki, taji dadin
hakan sosai, sama ta wuce ta nufi dakinsa tana kalle kalle ta bude kofar, xaune
ta samesa gefen gado yana danna wayarsa, daga kai yayi yana kallonta, ta shiga
ta kulle kofar dakin ta karasa kusa da shi ta ajiye masa abincin ta hade rai
tace "Shine ka wuce koh?" Jawota yyi jikinsa a hankali yace "Ba
gashi kin kawo min har daki ba" Tana kokarin mikewa tace "Xan tafi
kar Ammi ta dinga nemana" ya ki saketa yace "Ai a nan xaki
kwana" xaro ido tayi ta kallesa sai kuma tayi dariya tace "Tabdi, ni
dai ka sakeni in wuce Yaya" yace "Toh wuce da abincin ki baxan ci
ba" shiru tayi tana kallonsa, sai kuma ta 6ata fuska tace "Ni wllh
sai ka ci" yace "In dai ba nan xaki kwana ba kuma ki bani abincin a
baki to baxan ci ba" xaro ido tayi tace "Toh babu spoon din bari in je
in dauko a kitchen" ya matseta yace "Guduwa xa ki yi" tace
"Ae nasan idan na gudu baxa ka ci ba, spoon xan je in dauko in dawo"
yace "Toh je ki dauko" mikewa tayi ta nufi kofa sannan ta juya ta
kallesa ta wara masa manyan idonta tana dariya tace "Kai ma ka xo part
dinmu ka kwana mana" daga haka ta fice dakin.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
93.....
Karfe sha daya saura na dare Umma ta shigo dakin Mujaheed
sanye da hijab dinta har kasa, yana xaune ya jinginar da kansa da gado ya daga
kai ya kalleta sannan ya dauke kai, he looks so frustrated har lkcn kuma bai ci
abincin da Imaan ta kawo masa ba, Umma ta kulle kofar a hankali ta karaso cikin
dakin tana kallonsa ta xauna saman kujera, kana ganinta kasan tana tare da
damuwa ba na wasa ba, and she looks so sick, bai ce mata komai ba hakan yasa a
hankali ta fara magana tace "Kana ji na Muhd?" Kai ya gyada mata ba
tare da ya kalleta ba still yace "Ina ji" Maimakon tayi magana sai ta
fara hawaye, sai kuma ta fashe da kuka sosai, shi dai bai yarda ya kalleta ba
bai kuma ce komai ba, tana girgixa kai cikin sanyin murya tace "I don't
know where to start from Mujaheed, ban san ta inda xan fara ba, amma lallai ka
sani duk abinda Safeenah ta fada gaskiya ne bbu karya ko daya a ciki, she said
nothing but the truth, kuma ba komai yasa na aikata hakan ba Mujaheed sai k'in
da nake ma Aisha, I've gone through a lot in my husband's house all bcos of
that woman, ita ce ta jefa ni cikin halin da nake ciki na sa6on ubangiji na, ta
dalilinta na dinga aikata abubuwan da na aikata, amma kuma da na san Allah xai
yi Ikonsa ya juya abun nan ya dawo kai na Abban ka ya baka auren Imaan wllh
wllh da ban fara abinda na yi ba, I wouldn't have done what I did, I still
can't imagine you having kids with Aisha's daughter, ban san ya xan dau lamarin
nan ba idan ka haihu da Imaan Muhd, har yau bana son auren nan naka da ita na
fada da babban murya, bana so, bana so har cikin raina, kuma baxan ta6a so ba,
da auren nan ya dore wllh gwara ko raina ne ubangiji ya dauka..." Kuka
take yi sosai cike da tashin hankali, ta cigaba cikin rawar muryar tace
"Amma nasan babu yanda xan yi yanxu, ba abinda xan iya akan auren nan da
bana so, sai dai kawai in xuba ido in ci gaba da k'in auren, kuma ni baxan ce
xan sa maka baki a auren ba, I will neva do that coz you've always been
obedient to me from the first, ko me na sa ka in ma kana so, in ma baka so yi
kake yi with respect, baka ta6a min musu ba Mujaheed, kawai abinda na sani babu
ruwana da matar ka da abinda xata haifa, babu ruwana da su har abada, put it at
the back of ur mind baxan ta6a son auren nan ba kawai adalci xan maka, Baxan
ta6a daukan 'yar wajen Aisha surka ba, baxan dau 'ya yan da xata haifa a
jikokina ba, Wanda Ina ma fatan kada Allah ya bata 'ya ya da kai, lastly I want
to say I am sorry for all the shame and frustration I've caused you before and
is still causing you now, don magana na gaba sosai, you just have to take heart
and pretend everything is fine" daga haka ta mike tana goge idonta ta bar
dakin Mujaheed ya bi ta da kallo, jinginar da kansa yyi a hankali da gado ya
lumshe idanuwansa hawayen dake makale idonsa suka sakko kasa. Imaan na kwance
daki sai dai ba bacci take ba, she's just imagining ko Mujaheed ya ci abincin
da ta kai masa ko bai ci ba, a hankali ta mike xaune ta sauka saman gadon ta
nufi press dinta, ta fi minti biyu tsaye kafin ta bude ta ciro jakar
islamiyyarta ta koma kan gado ta xauna ta bude jakar a hankali, takardar da ya
ta6a jefo mata ta window da dadewa ta ciro daga cikin jakar ta dinga kallon
well folded takardan sannan ta warware tana kallon rubutun ciki, ko layi daya
bata kai ga karantawa ba ta daga kai da sauri jin an bude kofa, Ammi ce ta
shigo dakin ta kulle kofar, kallonta Imaan ta dinga yi har ta karaso kusa da
gadon ta xauna a gefe tana kallon takardar hannunta ta amsa, Imaan ta sunkuyar
da kanta gabanta na faduwa, Ammi ta gama karanta Content din takardan ta ajiye
gefe sannan a hankali tace "Imaan" imaan ta daga kai tana kallonta,
Cikin sanyin murya Ammi tace "From all indication you are now happy
getting married to Mujaheed right?" Imaan ta sauke kanta kasa bata ce
komai ba, Ammi ta girgixa kai tana murmushin karfin hali tace "I am
surprised har xa ki hakura lkci daya haka Imaan, I am very surprise at you,
amma ki sani har gobe baxan ta6a alfahari da auren ki da Mujaheed ba,
never!" Kuka Imaan ta fara yi a hankali bata ce komai ba, Ammi tace
"And since you accepted him lkci daya sbda ya maki dadin baki irin na
maxa, to ki sani duk abinda xai je ya dawo iyaka in maki addu'a Imaan, tunda
kina ganin auren ki da Mujaheed alkhairi ne har kika hakura cikin sanyi, kuma
cikin kankanin lkci Allah yasa hakan..." Daga haka Ammi ta mike ta nufi
kofa Imaan ta bi ta da kallo tana hawaye, kafin ta fita tace "Ammi shi fa
Yaya babu ruwansa kema kin sani, kuma ai ni ban ce na hakura ba.." Ammi ta
juya ta kalleta sannan tayi murmushi a hankali tace "Ae bance da ruwansa
ba Imaan, Allah ya raba ki da sharrin uwarsa, ki je ku karata da shi..."
Daga haka Ammi ta fita dakin. Washegari Friday Umma taji shiru shiru dai Abba
bai kirata ba kamar yanda take ta jira, har dai ya fita gidan da safe, da yamma
xuwa parlonsa tayi bayan ya dawo duk da ba ita ce da girki ba amma shiru bai ce
mata komai ba sai ma tambayar ta da yyi me Mujaheed suka xo yi gida jiya, don
throughout ranan ita kanta bata ga Mujaheed ba, Tayi murmushin karfin hali tace
"Kila sun xo gaishe mu ne, amma Ina jin ai sun koma, don duk yau ban gansa
ba" Abba bai ce komai ba ta mike ta fita tana mamakin mai ya hana Inna ko
Mama Hadiza yi masa magana a kan xuwan Hajiya Khadija gidan, ko ba komai dai ta
ji hankalinta ya kwanta, kila basu yarda da uwar Sadeeq din bace, ta dinga fatan
Allah ya sa maganar ta tafi a haka, tsabar tashin hankali ko mutum daya bata
fada ma damuwarta cikin kawayenta ba, tana fitowa Parlor Maimoon tace
"Umma Maman Surayya ta xo neman ki tana sama" Umma ta wuce sama da
sauri jin Hajiya Saude ta xo nemanta, xaune ta same aminyar tata a gefen
gadonta, Umma ta kulle kofa tana dubanta ganin yanayinta tace "Lafiya
Hajiya Saude?" Hajiya Saude ta fashe da kuka sosai ta ajiye takardan
hannunta tayi tagumi cikin rawar murya tace "Na shiga uku Rukayya tawa ta
sameni Babansu Surayya ya sakeni...." Umma ta xaro ido tace "Ya sake
ki kuma Saude? Garin Yaya, me ya faru?" Hajiya Saude ta dinga girgixa kai
hawaye na sakkowa idonta tace "Surayya ta cuceni ta kunyata ni gaban
kishiyoyina Rukayya, hotel ta bi saurayi karban waya abokin Babanta ya ganta,
in takaice maki har hoto yayi mata, ya xo har gida ya nuna ma uban, tun jiya
ake abu daya bbu tashin hankalin da ban gani ba, bayan uban ya kusa karyata da
duka naga abun yyi yawa sai na nuna bacin rai na shine fa kamar wasa bawan Allahn
nan ya rubuta takadda ya bani, dama kwanaki ya min daya bayan wanda yyi min
shekaru biyar da suka wuce, yanxu fa duk ya katse igiyoyin, ki tashi Rukayya ki
rufa min asiri ki raka ni mu tafi gun mutumin nan baxai rasa abun yi kan
matsalar nan ba, fita gidan ubansu Surayya ba nawa bane..." Umma dake ta
kallonta baki bude tace "Toh ina ga wllh tawa matsalar ma ta fi taki
Saude...." Nan Umma ta kwashe duk yanda aka yi daga jiya xuwa yau ta
labarta ma Saude tana matsar kwalla ita ma, tana girgixa kai tace "Saude
ban san wani tuggun Hajiya marafa da tsinannun ya yanta xa su hada min ba nan
ba da jimawa ba don nasan baxa su kyale xancen nan haka ba, ga uwar yaron nan
da muka je har gida muka sameta ban san tsarin da ta xo tayi ma Inna da Hadiza
ba, gashi har yanxu shiru Ahmadu bai ce min komai ba ko gaya masa ne basu yi ba
oho, ya xan yi Saude? Wllh daren jiya ban rutsa ba kuma gaba daya na kasa tashi
inyi sllh, yanxu haka xancen da nake maki tun safe bbu abinda na saka a ciki na
sai ruwan da nake ta Sha, ga dukkan alama ma xaxxabi xan yi" Saude na
matsar kwalla don ita ba ta Umma take ba ta kanta take tace "Wllh na ki me
sauki ne Rukayya a kan nawa, iyaka fa idan an tada maki maganar uwar yaron ki
rantse ki kuma rantsewa kiyi ta rantsewa kice baki je gidanta ba, rantsuwa ai
ita ce kankat, sai a bar ki da mahaliccin ki a bar ki da rantsuwar ki kawai, ni
dai ki tashi ki rakani gun bokan nan idan aure na ya mutu da sufyanu ai nawa ya
kare a duniya, na shiga uku na lalace gidan uban wa xan tunkara ina marainiya
da ni" Umma ta girgixa kai tace "Saude sai dai kije Balaraba ta raka
ki gaskiya, don har abada ni da sake komawa gun bokan nan, saninsa bai amfana
min komai a rayuwata ba, kullum ni kenan a gantale ban ta6a nasara na a xo a
gani ba, meye amfanin raba auren da yayi aka aura ma d'a na?? Shegen mutumi
kawai katon arne dama yasan bai san gaibu ba ya dinga amshe min kudi gashi daga
karshe ya tarwatsa min rayuwa dubi irin matsalar da na tsunduma kai na fa
yanxu???" Hajiya Saude ta mike tana kallonta tace "Lallai kin kasance
butulu Rukayya, duk yanda na tsaya maki bamu gun wannan bokan ba mu gun wancan
Malamin da walakancin da xa ki saka min kenan??" Umma ta mike tace
"Don Allah Saude ki fita kiyi tafiyar ki nima a yanxu da kika gan ni wllh
ta kaina nake matsalata ta fi naki wllh wllh..." Hajiya Saude tayi wani
murmushi tace "Toh nagode kwarai Rukayya xan tafi, amma ki sani wllh kema
sai kin girbe abinda kika shuka, duk ta'asa da barnar da kika dinga aikatawa
xaki gansu a kwaryar ki kwanan nan, wannan da ya sameki shi ake ce ma wasa
farin girki" daga haka Hajiya Saude ta fice daga dakin kamar xata tashi
sama tana goge hawayenta. Daren ranan Imaan na parlon Inna xaune idonta a kan
tv dake aiki sai dai bata san abinda ake yi ba gaba daya hankalinta baya tare
da ita, Inna kuma tana can bakin tap tana aikin gurje gurjenta har ta gama ta
shigo ta fara kakkabe kujerunta tana kallon Imaan tace "Ae yarinya jibi
akwai fasa mugayen bama bamai xa ayi a gidan nan, iyaka dai bam din ya tarwatsa
wa enda xai tarwatsa mu kuma muyi ta kanmu mu kara rike Allah, ke kuma Alhmdllh
yanda wannan mutumi Mujaheed ya dauke ki haka ya maido min ke sbda tsayuwar
dare da na dinga yi, abinda na nasani a nan gaskiya shine in har Mujaheed bai
fita hakkin ki na aure ba wllh wllh babu inda xa ki bi sa, in su Ahmadu sun
mutu to ni suma nayi, ba da ni xa ayi wannan ta6arar da abun kunyar ba, ko ya
ta6a shigar maki daki ya kwana ne??" Imaan dai sai kallon tv take, Inna ta
yi mata tsawa tace "Keee..." Da sauri Imaan ta juya ta kalleta, Inna
tace "Toh wllh Bukar kika share ba ni ba, kwana biyu da baki gidan nan
bakina tsit bbu shegen da ya sa ni magana, to dama wake sani maganan banda ke
da Mujaheed din...." A fusace Imaan tace "Toh wai ni nasan da ni kike
ne" Sai kuma ta rufe fuskarta da kujera ta fara kuka ta mike ta shige daki
da sauri, Inna ta tabe baki tace "Toh ni ina ruwana idan ya kai ki ya baro
ki, duk da baxan ma yadda hakan ya faru ba tunda ba ubansa ya halitto min ke
ba, haka kawai ya same ki a banxa, to shi ne banxa ba ke ba" Imaan ta
kwanta saman gado tana turo baki a hankali tace "Ko Ina ruwanta
ma..." Bayan few minutes ta jawo wayar Inna dake saman gadon ta dinga
kallon wayar sannan tayi dialing number din Mujaheed, sai da ya kusa katsewa ya
daga kamar xata yi kuka tace "Yaya Ina ka tafi yau?" A hankali yace
"Anjima xan dawo, where are you?" Tace "Ina part din Inna"
d'an murmushi yayi yace "Are you missing me?" Da sauri tace "A'a
fa, kawai naga ban ganka bane, kuma ban san ko ka ci abinci ba..." Yana
murmushi yace "Toh xan shigo yanxu, me xan kawo maki?" Rufe fuska
tayi a hankali tace "Kaza mana" Muryar inna taji tace "Yau naga
jarababbiyar mata, shi Mujaheed din kika kira da katin wayata?? Toh gaskiya sai
dai in bar ki da Allah don ba Mujaheed ya saka min katin ba, ba kuma uban Mujaheed
ya saka min ba Bukar ne ya sa min kafin ya wuce, wannan wani irin jaraba ce ni
patuu? Uwar me kika hada da Mujaheed din xa ki kira sa a wayata, ni dai na
shiga uku da wahalar ki" imaan ta katse wayar ta jefar kan gado ta juya
mata baya fuska daure, Inna ta dauke wayarta tace "Waye kuma Mujaheed da
xaki kirasa da wayata muguwa kawai..." Daga haka ta fice daga dakin. Imaan
na ta kwance daki taji an bude kofar parlon Inna, mikewa xaune tayi tana kallon
kofar dakin.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
94.....
Mujaheed ya xauna parlon yana kallon Inna da ke juya furan
gabanta tana kallon ledan hannunsa, yace "Ina yini" tana murmushi
tace "Lafiya lau Mai gida, sannu da xuwa" Bai tanka ta ba, ta dau cup
ta kusa cika masa da fura da nono ta mike ta basa tace "Dama saboda kai na
dama furan nan" amsa yyi ya ajiye xata dau ledan da ya ajiye ya dauke da
sauri yace "Ce maki aka yi ledan ki ne?" Tace "to sai nace maka
ci xan yi Mujaheed? Haba sai kace gantalalliya kuma, duba abinda ke ciki kawai
nayi" daga haka ta koma ta xauna fuska daure, Imaan ta tsaya bakin kofar
daki tana kallonsu, Mujaheed ya kalleta bai dai ce komai ba ta fito ta dau
ledan tana kallon Inna tace "Toh ni ina nawa furan?" Bata rufe baki
ba Inna tace "Baxan bada ba" Dariya Mujaheed yyi ya dau nasa ya mika
mata, ta kalli Inna tana murmushi ta amsa, mikewa inna tayi ta nufi kofa ta
bude tace "Tashi ka fita ka ban waje Mujaheed..." Mikewa yyi yana
kallo Imaan yace "I will call you with her phone...." Ta turo baki
tace "She won't let that ai" Mujaheed yace "Hide the phone"
shirun da suka ji inna tayi bata ci gaba da masifa ba yasa suka kalleta matsar
kwalla suka ga tana yi, Mujaheed ya danne dariyarsa, Imaan ta ta6e baki ta
dauke kai, cikin rawar murya inna tace "Dama banda 6are wa xai xage
ka?" Mujaheed ya kalli Imaan yace "Don't forget to hide the
phone" Imaan tace "Ohk I will do so" Mujaheed ya nufi kofa yana
murmushi yace "Sae da safe inna" daga haka ya fita ta kulle kofarta
ta sa makulli, Imaan xata shiga daki a fusace inna tace "Kada ki fara don
ba uwarki Aisha bace mai min gyaran daki kije ki xubar min da kasusuwan kaji ki
cuce ni" Imaan ta tabe baki ta dawo parlor ta ajiye ledan da cup din furan
da Mujaheed ya bata ta tafi kitchen dauko plate kafin ta dawo inna ta dauke cup
din furanta da sauri ta juye a bowl ta rufe tana cewa "Baxan bayar ba
wllh" Har Sunday Imaan na part din Inna bata tafi bangarensu ba don haka
kawai ita dai ta ji tana kunyar Amminta, har Inna ta gaji ta kyaleta kiran da
Mujaheed ke mata ta wayarta iyaka tace masu idan katin ta ne to su da Allah.
Karfe goma saura Imaan na parlon tana kallo Inna kuma na shan shayi Daddy ya
shigo parlon, Mikewa Imaan tayi da sauri daga xaunen da take cike da farin
cikin ganinsa sai dai kuma ta samu kanta da kasa xuwa ta rungumesa kamar yanda
ta saba, murmushi yyi ganinta yace "Ba ku tafi ba Mamana?" Inna ta
cafke tace "Ehh ni nace bbu inda xata, ba sadaka aka ba Mujaheed ba da xai
ki yi mata lefe, in dai bbu lefe to baxata bar gidan nan ba Bukar, kai haka aka
baka uwarta bbu lefe???" Daddy dai bai ce komai ba ya xauna saman kujera,
Imaan ta duka ta gaishesa tana murmushi, yace "How are you doing?"
Tace "Alhmdllh Daddy, ya hanya?" Yace "Alhmdllh" kallon inna
yayi yace "Ina kwana?" Inna tace "Lafiya lau Bukar, Allah maka
albarka" yace "Ameen, ya gida?" Tace "Toh ga gida dai mun
gode Allah" yace "Toh ga ni na dawo Inna" Inna tace "Aa ba
xance gaka ka dawo ba, ka tashi ka tafi ka huta kafin a neme ka kuma...."
Shiru yayi yana kallonta can ya mike yace "Toh sai anjima" tace
"Allah ya kai mu" Imaan ma tayi masa sai anjima ya fita parlon. Karfe
sha biyu Mama Hadiza ta shigo parlon Inna dake ta xuba kamshin turaren wuta
tare da mahaifiyar Sadeeq da Hajiya Salmah aminiyarta, Inna ta fito daki
ganinsu ta washe baki tace "Toh Alhmdllh, sannun ku da xuwa" Hajiya
Khadija ta xauna da kawarta sannan suka gaida Inna, inna ta amsa ta dauko masu
ruwa ta ajiye tana kallon Mama Hadiza tace "Toh duk ki kirasu ta waya ai
koh?" Mikewa Mama Hadiza tayi ta shiga daki, ba a dau lkci ba ta fito,
Inna ta shimfida tabarma ta xauna Mama Hadiza ma ta nemi waje ta xauna, Aunty
ce ta fara shigowa parlon sannan Ammi, duk suka dinga kallon mahaifiyar Sadeeq
sannan aka gaisa, tun da Abba ya kira Umma yace ta tafi parlon Inna taji
xuciyarta ya tsinke, wato sai yau xa ayi mata maganar da take tunanin babu shi
jin shiru shiru, dakewa tayi ta sa Hijab ta fito xuwa part din Inna shawarar da
Saude ta bata na mata ringing a kai, har dai ta iso parlon Inna fuskarta a
daure, bata ta6a jin faduwar gaba irin yanda ta ji a moment din ba lkci daya
jikinta ya mace ta kasa karasowa cikin parlon tana kallon Hajiya Khadija ko
kiftawa babu, Inna na kallonta tace "Sannu da xuwa Rukayya shigo
mana..." Umma ta kalli Inna sannan ta kalli Abba da Daddy dake parlon su
ma, ganin Umma ta ki shigowa Inna tace "Haba Rukayya sai kace yarinya kin
wani makale jikin kofa, ke fa ake jira tun daxu, don Allah ki rufa mana asiri
ki shigo...." Lkci daya Umma ta kara daure fuska ta shiga parlon ta nemi
gefe daya ta xauna tana kallon direction din kofa, Inna ta kalli Abba tace
"Toh ko dai a kira Mujaheed ne, Ina son ayi komai kan idonsa" Daddy
yace "A'a ba sai an kirasa ba" Inna tace "Tohh ai shikenan"
Hajiya Khadija na kallon Umma da kyau tace "Kafin in fara magana Ina fatan
kin gane ni dai Hajiya?" Umma ta kalleta a takaice tace "Ina fa xan
gane ki? Jama'ah ai da yawa" Wani murmushi Hajiya Khadija tayi tace
"Ehh dama ba lallai ki gane ni ba, kilan idan na fara magana a kan abinda
ya kawo ni xa ki gane ni" Hajiya Khadija ta kalli Inna tace "Kaka
wannan matar da kike gani kusan watanni biyu da suka wuce ta ta6a takowa har
cikin gidana ta sameni da wani batu da xan fadi kowa ya ji yanxu" kallon
Hajiya Khadija gaba daya occupant din parlon suka dinga yi with interest, Inna
ma sai gwalo ido take tana sauraron Hajiya Khadija, Hajiya Khadija tace
"Wannan mata ta sameni har gida tare da surkarta da kawarta, a kan maganar
auren d'a na Sadeeq da 'yar gidan nan Imaan, a bakinta nake jin cewa Imaan
sickler ce ba lafiyayya ba, har kudaden da mahaifinta ke kashe mata duk wata a
kan ciwonta sai da ta fada min,.... Bana son inyi nisa don maganganun bbu dadin
ji, bbu irin bacin da matar nan bata yi ma mahaifiyar yarinyar nan a gabana ba,
babu kunya tace min in har na yarda d'a na ya aureta to fa xa su mallake min
shi kamar yanda suka mallake mahaifin yarinyar, matar nan da ku ke gani ta fi
minti ashirin tana magana na batanci a kan yarinyar nan Imaan da mahaifiyarta a
parlona, munafukar kawarta na taya ta, daga karshe nace masu to nagode xan yi
shawara a kan batun nasu, muka rabu da su a haka... abu biyu na gano tare da
baiwar Allahn nan a lkcn, na farko Hassada... na biyu kuma kiyayya mai tsanani,
na kuma ga alamar xata iya yin komai domin ta tarwatsa rayuwar imaan da
mahaifiyarta, she can go to any extent doing that, kwata kwata bata tsoron
Allah matar nan, muguwa ce, Ni kuma da na fi ta bayan sun bar gidana da few
weeks na sa aka kai lefen Imaan, shine ganin bata samu nasara ta wajena ba ta
shiga gun bokaye ta yi ma d'a na asirin da yasa yaji bai son auren kwata kwata,
ta raba da sa imaan sbda son xuciyarta...." Gaba daya mutanen parlon
kallon Umma suke babu ko kiftawa with shock, shi dai Daddy tunda ya kalleta sau
daya bai sake kallonta ba ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, Ammi
tayi murmushin karfin hali hawaye cike idonta tana girgixa kai, Mahaifiyar
Sadeeq na kallon Umma da kyau tace "Ki saurareni da kyau, ke dai kin gan
ni ne kawai amma baki san wacece ni ba, you know nothing about me, before going
further don Allah Ina so ku tambayar min ita me Sadeeq yayi mata?" Bbu
wanda ya iya cewa komai cikin parlon, Mama Hadiza ta dinga girgixa kai tana
kallon Umma da ta tamke fuska tana kallon Maman Sadeeq, can Umma ta mike tana
kallonta da kyau tace "Hajiya ni kika gani a gidan ki? Ni Rukayyar? Ni
kuwa?? A Ina na san ki da har xan je gidan ki? Ni din?? Kinsan abinda kike cewa
kuwa? Uban me xai kai ni gidanki da ban ma san hanyar gidan ba, to wllh wllh
wllh karya take min Alhaji, na rantse ban san matar nan ba ban ta6a ganinta ba
Allah shaida, wllh ban santa ba ban san me nayi mata take son 6ata min suna
haka ba, innalillahi wa inna ilaihi raji'un..." Bude baki Hajiya Khadija
tayi tana kallon Umma da mugun mamaki, Aunty tayi wani murmushi tana girgixa kai,
umma ta fashe da matsanancin kuka tace "Idan na yarda da kazafin nan da
sharri da kika biyoni har gida kika min Allah ya tsine min, wllh sai an bi min
hakkina ko nawa ne xan kashe, wllh baxan yarda da wannan sharrin da bakin fenti
da kika goga min ba" Inna ta hangame baki tana kallon Umma dake kuka sosai
tana huci, Umma ta isa gaban maman Sadeeq cikin daga murya tace "Wllh wllh
baxan yadda ba, ni Rukayyar ce naje gidan ki na 6ata imaan da uwarta?? To wllh
tun a duniya xa a fara mana shari'a dake, ba Bulasawa ba in ma mai kudin duniya
kike aure wllh sai an bi min hakkina, me na maki xaki 6ata ni haka gaban
mijina, uwarsa da kanninsa?? Me na maki? A ina na ta6a sanin ki?" Wani
murmushi kawai Hajiya Khadija take tace "Amma tunda nake ban taba ganin
makira, annamimiya, makaryaciya, kuma warce bata tsoron Allah irin ki ba, ke
shaidaniya ce a siffar mutum, ke din annoba ce a cikin jama'ah..." Bata
rufe baki ba Umma ta nuna mata yatsa a goshi tana huci tace "Uwarki ce
shaidaniya annoba ba ni ba" a hankali Hajiya Khadija ta mike tana kallonta
tace "Ni ki nuna ma yatsa kika xagi uwata??" Umma na huci tace
"An nuna maki din, kiyi abinda xa ki yi idan kin isa, haka kawai mata ki
shigo min gida ki min wannan kafurin sharrin haka mai muni" murmushi kawai
Hajiya Khadija tayi tace "First na bari ne ki gama rantse rantsen ki kafin
inyi reminding din ki gidana akwai Cctv camera, sannan secondly sai kin san kin
nuna min yatsa a goshi" Inna ta mike tana salati tace "Rukayya kin ja
ma kanki babban bala'i da bamu san iyakarsa ba tunda kika daga rubabben shegen
yatsan ki kika dunguri goshin wannan baiwar Allah, wllh kin debo ruwan dafa kan
ki, bbu abinda ya sha kan Ahmadu balle ni...." Mikewa Abba yyi ya fita
daga parlon, Umma na kallon Inna cike da masifa tace "In sha Allahu baxan
ga bala'i ba, a kan me mata xata shigo har gidana ta min irin wannan kazafin
inyi shiru? Wllh baxan yarda ba duk inda xa mu tafi sai dai mu tafi"
Hajiya Khadija ta mike tace "Ki saurareni, sai na nuna maki ke a makiran
ma karama ce, sai na nuna maki karshen ki tun a duniya, kuma sai kin san ba a
cutar min da Sadeeq, da acuce sa gwara an cuceni" daga haka Hajiya Khadija
ta fice daga parlon kawarta ta mike ta bi bayanta, inna ta saki shewa tana
kallon Umma dake xufa tana huci tace "Anyi walkiya mun ganki axxaluma
diyar shaidan, dama tun ba yau ba nasan mugun abinda kika aikata ma jikata ya
dawo kanki aka aura ma d'an ki, d'an Albarka, Toh Alhmdllh ba a bakina aka ji
wnn mummunan labarin ba, in kin cuce wani kin kwana lafiya to wani ko dare ma
baxa ki isa ba kiji in gaya maki, Sai dai in maki fatan Allah ya raba ki da
wannan mata lafiya, in dai jikata mutum yace xai cuta ya shiga uku ya lalace a
duniya kuma yyi ta ganin ba dai dai ba kenan, kuma kinyi asara duniya da lahira
tunda kika rike boka da malamai maimakon Allah da ya halicce ki...."
Shigowar Abba yasa inna tayi shiru tana huci, yana kallon Umma ya mika mata
takardan hannunsa yace "Bana son ki kara kwana gidan nan yau
Rukayya...." Umma ta dinga kallonsa da idanuwanta Kamar xa su fito xuciyarta
na bugawa can ta karbi takardan da sauri ta warware tana kallon content dinsa,
wani kuka ta saki a parlon tana kallon Daddy hankali tashe ta nufesa tace
"Saki na fa yayi baban Imaan.... Wllh saki har biyu yayi min baban
Imaan"
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
95.....
Shi dai Daddy bai ce komai ba sai kallon Umma yake, Inna tayi
mitsi mitsi da ido tana jiran ta ji yyi magana, kawai ya mike ya fita daga
parlon, Umma ta fashe da matsanancin kuka ta xauna kasa tace "Innalillahi
wa Inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace" Inna ta wangale kofa da
sauri tace "A'a rufa min asiri ba kya shiga uku a parlona dake tare da
albarka kaca kaca ba Rukayya, tashi ki tafi kiyi ta kanki, Allah ubangiji yyi
mana tsari da irin ku a duniya, Allah ya saka ma d'a na Ahmadu da xuwa gurin
boka da malamai da kika dinga yi da dukiyarsa, Allah sarki Mujaheed, a duniya
dai kam bai y sa'ar uwa ta gari ba, amma da sauki tunda ga shi da Kaka mai
tsoron Allah ba kama hannun yaro, sannan ga Amina matar ubansa ita ma matar
kirki, Imaan kuma Allah ya isa tsakaninta dake cutar da ita da kika yi, Allah
ya isa mata ya saka mata, in sha Allahu sai Allah ya saka mata" Kuka kawai
Umma take tana kallon Inna, Inna ta washe baki tana kallon su Mama Hadiza tace
"Yo Mutum ma ya rike Allah hannu bibbiyu ya ya kare da duniyar balle ita
da ta rike boka" Ammi ta mike a sanyaye ta fita parlon wiping off her
tears, Umma ta hade kanta da kujera tana kuka sosai tace "Innalillahi wa
inna ilaihi raji'un..." Inna tace "Ni dai ki tashi ki bar min parlona
Rukayya kada ki ja min wata fitinar, kada ki ja min fushin ubangiji ki tashi ki
tafi" mikewa Umma tayi ta fita parlon tana kuka kamar ranta xai fita,
Aunty tayi tagumi duk jikinta yayi sanyi tana kokarin maida hawayen idonta,
Mama Hadiza ma dai ta kasa cewa komai don duk da sanin halin Umma da tayi amma
gaba daya hakan taji bai mata dadi ba, bata taya xaton hukuncin da yayan nata
xai dauka kenan ba, Ina laifin ma saki daya, bbu wanda ta fi tausayi kamar
Mujaheed, don ko ba komai mahaifiyarsa ce. Part din Daddy Umma ta shiga da sauri
bayan ta bar parlon Inna, Daddy na xaune parlor har lkcn ya kasa gaskata
abubuwan da ya ji daga bakin mahaifiyar Sadeeq game da Umma, yasan tabbas Maman
Sadeeq baxata tako har gida tayi ma Umma sharri ba gashi tace xata kawo
evidence tunda akwai Cctv camera, but he is trying hard not to believe it kada
tsanar Umma yyi masa yawa a xuciya, Ammi dai tunda ta shigo bata ce masa komai
ba ta shiga daki duk iya daurewan da tayi kada ta xubda hawaye ta kasa ta dinga
kuka tana tunanin me tayi ma Umma a rayuwa haka irin wannan kiyayya da take
mata da only child dinta, ita dai Allah shaida ba ita tace Abba ya ga Aunty
yace yana so ba, tun suna yara suke tare da aunty ba wai rana tsaka kawancensu
ya fara ba, dama kuma tun farkon aurenta da Daddy Umma ke mata hassada saboda a
wadace take da komai kasancewar bata da kowa gabanta, babu abinda daddy ya raga
ta da shi duk da rashin haihuwarta da tsangwamar Inna jefi jefi, ita kuma Umma
tana da yara sannan makarantansu masu tsada ne sosai tun a lkcn, sai gashi Abba
ya kara auren aminiyarta wanda hakan yasa abu ya kara ca6e masu da Umma, Umma
na tunanin hada baki tayi da Amina ta aure mata miji don kusan ko da yaushe
Amina na tsohon gidansu ta xo gun Ammi, Ammi ta girgixa kai hawaye na sakko
mata tana tantama anya da gaske akwai mutane masu irin halin Umma a duniya kuwa
ko ko ita kadai ce dai, don kiyayyar da tsanar yayi yawa, Sai gashi that not
been enough tilon 'yar ta an aura ma jinin Umma, tasan dai dai da second daya
Mujaheed bai ta6a supporting mahaifiyar sa a kan abubuwan da take ba, but kuma
ai dole yyi mata biyayya domin ko uwa ce, gashi yanxu an kara sakinta for the
second time ta dalilin Imaan, bayan sakin da aka mata years back ta dalilin ita
Ammin, ko saboda haka ai baxata ta6a barin Imaan ta xauna lafiya gidan Mujaheed
ba, tunanin hakan yasa Ammi ta kasa daina kukan da take. Tun da Umma ta shigo
parlon Daddy yyi mata kallo daya ya dauke kai, durkusawa tayi gefensa hawaye na
bin kuncinta cikin rawar murya tace "Don girman Allah ka ceci rayuwata
Abban Imaan, ka dubi Allah kayi ma d'an uwanka magana ya janye batun sakin nan,
wllh bani da inda xan je in ji dadi da ya wuce gidan nan kayi min rai Abban
Imaan kada a raba ni da 'ya yana, duk abubuwan nan da suka faru wllh sharrin
shaidan ne da rudin duniya, na kuma yadda nayi laifi, ka yafe min ba don halina
ba ka sama min mafita Abban Imaan" daddy dai ya jinginar da kansa da
kujera bai ce mata komai ba, kuka take sosai tana kallonsa, Jin yyi shiru ya ki
cewa komai cikin rawar murya tace "Domin Allah kada ka biye ta halina Abban
Imaan, in ci darajan 'ya yan da na haifa a gidan nan, in ci darajansu don
Allah...." Kuka take sosai tana kallonsa, Sai a sannan Daddy ya kalleta
amma ya kasa cewa komai, mikewa yayi kawai ya nufi kofa walking slowly ya fita
parlon, Umma ta fashe da matsanancin kuka, ta mike ita ma tana kallon kofar
dakin Ammi ta nufi dakin ta bude ta shiga, Ammi dake xaune gefen gado ta kasa
daina hawaye ta daga kai tana kallonta, Umma ta karasa cikin dakin ta xauna
gefen gado tana share hawayen idonta wasu na kuma xubowa, cikin rawar murya
tace "Don Allah Hajiya Aisha kiyi ma Abban Imaan magana ya sa Baki a
lamarin nan, ya rufa min asiri kada Ahmad ya sake ni, wllh duk sharrin shaidan
ne, ko domin albarkacin auren da aka hada na Imaan da Mujaheed kada a bi ta halina"
Ammi dai bata iya ta ce mata komai ba tana share hawayen idonta. Daddy na fita
daga part dinsa parlon Abba ya wuce, ya buda kofar a hankali ya gan yayan nasa
xaune parlon, Mujaheed na duke kasa gefensa ya rike kansa, Abba Kuma ya jingina
kansa da kujera yana kallon saman parlon, Xaunawa Daddy yayi yana kallon Abba,
bayan few seconds cikin sanyi yace "I am sorry about what happened
barrister, amma ba a yanke hukunci cikin fushi, this is very wrong, beside
hukuncin is too strict, diyata ta cuta ba wata 6are ba, we have the right to
forgive, domin ko wani dan Adam ajizi ne, no one is above mistake, kuskure ta
riga tayi sai da Allah ya tsare na gaba ya kuma shiryeta, da sauki tunda a gida
ne hakan ya kasance ba a waje ba, we have to solve our problem with outsiders
intruding, wannan magana bai kai ka yanke hukuncin da ka yanke ba Barrister, I
am really not happy about this, ko ba komai ya kamata Hajiya Rukayya ta ci
albarkacin 'ya yanta a gidan nan, don haka na xo neman alfarman ka mayar da
ita, duk sharrin shaidan ne ba wani abu ba, Ni na yafe mata, Imaan ma nasan
baxata rike ta a xuciya ba tunda uwarta ce, haka ma mahaifiyar Imaan, daga
karshe kuma Allah ya shirye mu gaba daya ya raba mu da son xuci'an da xai kai
mu ga dana sani mara amfani, Hajiya Rukayya deserve to be pardon albarkacin
yaranta...." Abba yayi murmushin karfin hali yace "Babu aure
tsakaninmu kuma, babu sauran igiyana a kanta don haka before dusk ta bar gidan
nan...." Shiru Daddy yyi yana kallonsa ya kasa cewa komai, Babu wanda yace
komai a parlon har bayan kusan minti biyar, Mujaheed ya mike a hankali ya nufi
kofa ya fita parlon, Daddy ya girgixa kai very sad yace "Am not happy at
this Barrister, a ta dalilin diyata fa ka sake matar ka?? Why? Wannan wani irin
xumunci ne namu? Komi Rukayya xata yi gidan nan baxa ta ci albarkacin yaranta
ba, don ta cuci Imaan daga karshe ba Mujaheed bane ya auri Imaan din? Plss do
something about this Barrister..." Abba ya girgixa kai yace "Ka dai
san kwanaki na ta6a mata saki daya, yanxu kuma nayi mata biyu so that's the end
tsakanina da ita, taje idan ni na cuceta a iya xaman mu na kusan shekara 35
Allah ya saka mata, idan kuma ita ta cuce ni na yafe mata albarkacin xuri'ar
dake tsakanin mu" Daddy ya kasa cewa komai duk jikinsa yyi sanyi. Inna ce
ta bude kofar parlon ta shigo tace "Toh Ahmadu ko ni xan fita in samo
babban mota a kwashe kayan matar nan a gidan nan ne, kada fa dare yayi a xo ana
guje gujen fitar da kaya hakan ba shi da kyau gaskiya" Abba dai kallonta
yake bai ce komai ba, Daddy kam ko kallonta bai yi ba, Inna tace "Toh kun
yi shiru kuna kallona" Mikewa Daddy yyi ya nufi kofa ya fice daga parlon,
inna ta bi sa da wani shegen kallo bayan ya fita tace "Gantalalle kawai,
da kyar idan ba hakuri ya xo baka ba da yake ba hankali ya ishesa ba, tunda
uwata ta haifeni ban ta6a ganin mutumi irin Bukari ba, Yar taka kwaya daya tak
a dinga bin ta da irin wannan cuta haka amma sbda karfin hali ka dinga nuna
komai ba komai bane sbda baka tsoron Allah, tun fa yana karami haka yake wllh,
duk cutar da xa a masa sai yace ya yafe sbda tsiya, gashi hakan ya bi sa har
girmansa, wnn ai bala'i ne da dabiyar tsiya, Ina kuwa xan yafe ma wanda ya cuce
ni, ai Allah ma bai ce haka ba, idan ban bi a sannu ba ma ai sai Allah yyi
fushi da ni...." Abba dai bai ce komai ba, inna ta ja tsaki tace "Wlh
yau da ace ba Imaan matar nan ta cuta ba to ni me iya yafe mata ne, kuma ince
Ahmadu ma ya yafe mata, Amma imaan ce fa?? Takwara ta ce fa? Ita daya gare d'a
na Bukar fa? Yanxu ko don irin xuciyar Bukar Rukayya ya kamata ta cuci yar sa kwaya
daya da Allah ya basa? Me yayi mata da xafi haka, banda ma kyautatawa da tsaya
mata da yake yi a lamarinta?? idan ma tana jin haushin Aisha ne Imaan baxata ci
albarkacin ubanta Bukar mutumin kirki ba..." Kuka inna ta fashe da har da
shessheka tace "Ni Mujaheed ne ma abun tausayi, sam yaron bai yi dacen
mahaifiya ba, gashi yaron kirki da yasan ya kamata ga tarbiya kaca kaca, ko ya
xai dau wannan xancen oho, Ni dai Allah ya isa tsakanina da Rukayya bakin cikin
xuwa makka duk shekara da ta min, shari'a ta da ita sai gaban ubangiji don wllh
wllh ban yafe ba, uban wa gareni dama da xai kai ni makkan duk shekara banda
Sadeeq din....." Daga haka ta fita parlon tana share idonta. Ammi na xaune
dakin Imaan tun bayan fitar Umma, Banda hawaye babu abinda Imaan ke yi har da
shessheka, Ammi dai tayi tagumi ta ma rasa abun cewa, cikin rawar murya Imaan
tace "Ammi ko don saboda Yaya ai bai kamata Abba yayi haka ba, I don't
know how he will take this, why will all this happen because of me?" Ammi
dai tayi shiru bata ce komai ba, Imaan na son gaya ma Ammi abinda ya faru ranan
Thursday a zaria da ya sa suka dawo gida amma ta kasa gaya mata sbda alkawarin
da tayi baxata fada ba a gida, da ta tuna ita ce dalilin mutuwar auren Umma sai
ta ji wasu sabbin hawayen sun xubo mata, Ammi ta girgixa kai a hankali tace
"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un...." mikewa tayi ta fita dakin a
sanyaye, duk da tasan babu sauran aure tsakanin Umma da Abba ta fita xuwa
parlon Abba. Karfe biyar saura kamar yanda Abba yace babban motar da xai kwashe
kayan Umma tass ya shigo gidan, Umma na can dakinta tare da Rahma da Ummi da
Maimoon dake taya ta kuka kamar ransu xai fita, Seeyama ma na xaune dakin ta
kasa cewa komai sai hawaye, Aunty dai na tsaye jikin mirror tayi tagumi ba uhm
ba uhm uhm.... Har parlor Mujaheed ya samu Abbansa ya duka nan kasa cikin
sanyin murya yace "Abba dama nace don Allah a bar kayan yanxu ko daga baya
sai ni in kwashe" shiru Abba yyi yana kallonsa, can Abba ya gyada kai a
hankali yace "Toh ba damuwa, do you have any idea of where she will be
going now?" Mujaheed ya sunkuyar da kansa yace "Xan kai ta Zaria
yanxu" Abba yace "Ur home?" Mujaheed ya gyada masa kai, Abba
yace "Ina xaka ajiye Imaan?" A hankali Mujaheed yace "Nan
kaduna" Bayan few seconds Abba yace "I am sorry Mujaheed, I also Neva
saw this coming but I think this is the best, ga can abubuwan da kace min sun
faru a gidan ka wanda har ya janyo ka saki matarka bbu sauran aure tsakanin ku,
sannan ga wannan, sure i was frustrated, but na shanye abubuwan da mahaifiyar
ka take min shekara da shekaru, Ina barin ta tana cin albarkacin ku, but
today's own is beyond me, I think this is best, Allah kuma yasa hakan ya fi
alkhairi, Ina me baka hakuri coz I know this is sad, sannan abinda yasa nace ta
tafi yau saboda wannan mata ta Bulasawa, kaga ko da xata dawo bata ganta ba
komai xai xo da sauki, mu kuma sai mu basu hakuri, sai kaga albarkacin mu ta
hakura..." Mujaheed bai iya yace komai ba hawaye ya kawo idonsa, Abba ya
mike ya shiga daki ya dauko kudi ya mika masa yace "You give her this, sae
ta rike a hannu, Allah ya maka albarka" mikewa Mujaheed yyi kansa a kasa
yace "Toh ngd Abba" daga haka ya fita parlon.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
96.....
Bayan sati daya da komawar Umma Zaria Abba ya kira Mujaheed
parlonsa da yamma, Mujaheed ya xauna kasa yana kallonsa yace "Ga ni
Abba" Abba yace "Na ji shiru baka ce xa ku koma gida da matar ka ba,
what's happening?" Murmushi Mujaheed yyi yace "Abba Inna ce"
Abba yace "Me Innar tayi?" Mujaheed yace "She said I am not
leaving with her" Abba yace "Ko saboda me?" Wani murmushin
Mujaheed yyi bai dai ce komai ba, Abba ya gyada kai yace "Tashi ka
tafi" mikewa yayi ya fita parlon. Inna ce tsaye parlonta inda take shiga
ba nan take fita ba tana kallon Imaan, Imaan dai na kwance idonta a kan Tv bata
yarda ta kalleta ba, Inna tace "Yau naga abinda ya isheni yarinya mara
kirki kawai, to a kan me xaki debar ma mutumi dambuna kuma d'an walakanci ya
bar min shi a walakance bai ci ba? waye kuma Mujaheed Allah na tuba mutumin da
na yi wahala da shi, meye nasa ne ban sani ba, 'ya yana suna wahala dani ku
kuma ku dinga cinye min" ita dai Imaan bata tanka ta ba, Inna tace
"Yau naga jarababbiya wai ni xata nuna ma son miji, Yar figigiya dake kin
san dadin miji, ba kunya ba tsoron Allah ki satar min nama ki kai masa shi kuma
ya ki ci, anya Imaan kina son gamawa da duniya lafiya kuwa?" Shigowar Abba
yasa Inna tayi shiru, Imaan ta mike xaune tana masa sannu da xuwa, Abba ya amsa
yana kallon Inna ya xauna ya gaisheta, Inna ta shimfida tabarma fuska daure ta
xauna tace "Lafiya lau Ahmadu ya aiki" yace "Alhmdllh"
Imaan ta gaida Abba sannan ta mike ta wuce daki Inna ta bi ta da harara sannan
tayi kwafa, shi dai Abba kallonta yake bai ce komai ba, Inna tace "Daxu ma
Bukar ya kirani muka gaisa nace Allah yayi masa albarka, ya rabasa da sharrin
mutum da aljan, ya shiga ko ina a sa'a ya fita a sa'a" Abba ya gyada kai
yace "Hakan na da kyau ai" mikewa Inna tayi tace "Bari in d'an
yi shara in dawo Ahmadu" Abba yace "Magrib ai ya kusa Inna, dama kuma
magana na xo xa mu yi" Inna ta koma ta xauna tace "To lafiya dai
ko?" Abba yace "A'a lafiya lau, kawai naga ya dace Mujaheed ya dau
matarsa su tafi ko, tun da Alhmdllh ynxu bbu wata matsala...." Inna ta
katse sa tana mitsi mitsi da ido tana girgixa kai tace "Ae ba Mujaheed ya
halitto min ita ba balle in basa ita su tafi, waye kuma Mujaheed?? ku dai wllh
ku dinga tsoron Allah komin rintsi, Ahmadu duk matan ka biyu da ka aura ka gaya
min warce aka ta6a baka bbu lefe? Shi ma Bukar ya gaya min ko bbu lefe ya auri
Aisha, sai Imaan ce xa a kai gidan Mujaheed ba lefe sbda ance maku gantalalla
ce? Mutane dai bbu tsoron Allah ko digo a xuciyarsu, tirr wlh" Murmushi
Abba yyi yace "Inna ai ba yace baxai yi bane, xai mata in sha Allah,
wannan ai dole ne" inna tace "Toh yayi mu gani tukun, gwalagwalai
hudu na kirga a lefen da Bulasawa yyi mata wllh tllh, duk atamfofin kuma babu
na kasa da dubu hamsin, ga leshi duk 'yan dubu dari dari, to me yafi haka ma'ana??
kaiiii Ahmadu ku ji tsoron Allah, wllh Imaan ba banxa take ba, a kan lefen nan
ma ni sai in soke auren nan gaba daya in ga ta tsiya don uwa ta bata ce min je
ki kya gani ba, haka kawai ya cutar min jika ya kai ta ya barota bbu kayan aure
jikata ta walakanta, to Allah ya tsine ma wanda yace auren xumunci ne ko ba ayi
lefe ba bbu komai, don da alama an rada maku hakan ne shi yasa ku ke
shashantarwa, to wllh bari ku ji, sai na ga akwati guda dai dai har sha biyu
sannan Imaan xata bar gidan nan, idan ba haka ba gwara inyi ta kallon abata, ba
ruwana ni yar gaskiya ce..." daga haka ta mike ta fita daga parlon tana
cewa "A dai dinga tsoron Allah komin rintsi, ance maka don kai ka haifi
Mujaheed sai in ki gaya maka gaskiya, haka kawai mutumi ka lallabo ka xo min
nan don ka min dadin baki a cuci Jikata, Albarka uwata ta dinga sa min kafin ta
rasu wllh..." Murmushi kawai Abba yake, can ya mike yana girgixa kai ya
fita parlon. Karfe tara na dare Mujaheed ya shigo parlon Inna da sallama ya
ganta xaune saman darduma tana xuba gyangyadi ga carbi a hannunta, tsayawa yyi
yana kallonta, can yyi murmushi ya nufi kofar dakin walking without making any
sound, yana bude kofar dakin Inna ta bude ido daya a hankali tana kallonsa har
ya shiga dakin, yana shiga Imaan na fitowa daga bathroom daure da towel, xaro
ido tayi ganinsa, lkci daya ta nufi gefen gado da sauri ta xauna tana kallonsa
kamar xata yi kuka tace "Yaya shine xaka shigo bbu sallama, gashi ban sa
kaya ba, kuma idan inna ta gan ka fa? Don Allah ka fita plsss" Juyawa yayi
xai rufe kofar dakin ya ga Inna tsaye kyam bakin kofar tana kallonsa, duk da
yanda ya so dakewa kada yyi dariya sai da yayi dariyan yana sunkuyar da kai, ta
cakumosa fuska a murtuke tace "Dakina yyi maka kama da otal Mujaheed?
Yaushe ka lalace haka bani da labari, bbu kunya balle tsoron Allah ka afka ma
yar yarinya daki daga ita sai tawul ta fito wanka? Me hakan ke nufi
fisabilillahi? Meye manufar shigo mata tana tsirara?" Ya wara ido yace
"Toh xa ki hanani shigowa gun matata ne Inna?" Inna tace "Toh
wllh ka gaggauta neman tubar ubangiji, ta ina ta xama matar ka baka fita
hakkinta na aure ba Mujaheed? ga sadakin ka can a cikin dirowa sai in dauko
maka in baka tsiyar ka yanxun nan kar ka kawo min nansans, Ina ce da shi kake
takama?" Ya shafa kansa yana murmushi yace "Toh ai Aunty ta fara hada
mata lefen sai ki bani matata mu tafi koh?" Inna tace "Wacece kuma
Aunty? To wllh ka rufa ma kanka asiri ka amso kudadden ka ka samu yar gayu ka
bata ta hada ma jikata lefe, kwata kwata ban yarda da siyayyan Aisha da Amina
ba, duk yaushe suka waye? sai kaga kayan da suka hada ma Yusuf duk rubabbu ba
kyau, Kamar daga kauye" dariya kawai Mujaheed ke yi yana kallonta tace
"Atoh ni ba ruwana" tana rike da shi ta juya xata fita dakin yace
"Toh sakeni mana Inna" Bata sauraresa ba har suka fita dakin ya juya
yana kallon Imaan da tayi masa gwalo, wani murmushi yyi yana gyada kai Inna ta
kulle kofarta sannan ta sakesa, ta xauna tace "Kudin akwatuna nawa ka
bata?" Yace "Idan ta gama hadawa xa ki gani ai" tace "Ni da
xa a ji ta nawa ma a siya mata sakk irin na Bulasawa har kayan ciki"
Mujaheed bai tanka ta ba, bayan kusan minti goma Imaan ta fito sanye da hijab
har kasa sai xuba kamshi take, kallonta kawai Mujaheed yake har ta xauna, Inna
tace "In xuba maki abincin ne ko ko?" Gyada mata kai Imaan tayi, Inna
ta mike tace "Ina xan bari ki lalace a shiyana Bukar yyi tunanin bana baki
abinci ne ya kullace ni" daga haka ta shiga kitchen, Mujaheed ya bi ta da
ido sannan ya mike, imaan na ganin haka xata tashi yyi saurin rikota, kamar
xata yi kuka murya can kasa tace "Yaya ka bari kaga Inna xata fito ynxu
fa.. " xaunar da ita yyi kusa da shi ya jawota jikinsa ya daura forehead
dinsa kan nata yana kallon lips dinta murya can kasa yace "Ke kika ce mata
sai na maki lefe koh??" Xaro ido tayi tana son komawa baya yaki saketa,
rufe fuskarta tayi jikinsa hankali tace "A'a wllh, ita ce dai ta fadi
haka...." Rungumeta Mujaheed yyi yana son dago kanta taki yarda, Inna na
fitowa kitchen rike da plate din abinci tayi kasake baki bude tana kallonsu,
sai kuma ta saki salati, da sauri Imaan ta fara turasa tanq xaro ido amma ya ki
saketa, Inna ta ajiye abincin hannunta a kasa tace "Mujaheed iskancin naka
a parlor na xae kare yau kuma? Haka kawai mutumi ka shiga ka matse min yarinya
ba tsoron Allah??" Bata jira cewarsa ba ta tafi da sauri ta bude kofar
parlon tace "Taho ka fita kada Ahmadu ya fitar min da kai yanxun nan,
wannan wani irin iskanci ne da lalata, mutumi ka shigo xaka lalata yar mutane a
parlona, meye ma'anar hakan ma dai tukun?" Imaan dai tuni ta janye daga jikinsa
kamar xata yi kuka, a fusace inna tace "Ke kuma jarababbiyar yarinya kin
wani sakar masa jiki kin makalkalesa shashasha kawai jarababbiya, to wllh kai
ki xai yi ya baro ki don ma kiji in gaya maki, waye kuma bai san iskancin
namiji, ohhh ni patuu yau naga iskanci gun yara, a parlon nawa kuma babu tsoron
Allah xaka makalkaleta Mujaheed, Toh wllh bari Ahmadu ya shigo ba dani xa ayi
wnn iskancin ba dama kada Mujaheed ya sake xuwa min nan wllh ni ba gantalalliya
bace kuma ni ba yar iska bace" Imaan ta mike tana turo baki ta wuce daki,
Inna na kallon mujaheed a fusace tace "Baxa ka xo ka fita ba ko sai na
tafi na kira ubanka, banda baka da tsoron Allah imaan din ma nawa take gaba
daya fisabilillahi da xaka matse ta haka kan kujera Mujaheed? Ni wllh ban taba
ganin haka ba tunda uwata ta haifeni, to me xaka mata?" Mujaheed ya mike
yace "Da kin yi ki shiru kiga abinda xan mata ai" daga haka ya bi ta
gefenta xai fita dakin ta kai masa dundu a baya tace "Toh Allah ya isa
wllh, ka je kai da Allah, wanda bai yi iskanci ba ma a rayuwar ya ya kare balle
yyi iskanci" murmushi yyi bai kuma tsayawa sauraranta ba yyi wucewarsa.
Washegari da safe Imaan ta tafi gaida Amminta daga part din Inna bayan inna ta
jaddada mata ko minti biyar kada tayi a can don ita tsoron kowa take a gidan
bata yadda da kowa ba, A bedroom Imaan ta samu Ammi xaune, ta duka kasa jikin
gado tana kallonta a hankali tace "Ammi Ina kwana" Ammi tace
"Lafiya lau, kin tashi lafiya?" Imaan tace "Alhmdllh, daxu da
kika xo ina wanka" Ammi tace "Ohk, kinyi breakfast?" Kai Imaan
ta gyada mata, Ammi ta yi shiru sannan tace "Me Mujaheed din yace maki kan
komawar ku?" Imaan ta sunkuyar da kanta tace "Inna ce tace A'a"
Ammi tace "Ba Aunty ta fara hada maku kayan ba" Imaan dai bata ce
komai ba, Ammi tace "Idan ma xa ki daina biye ma Inna ke daina biye mata
ki bi mijinki ku tafi, Daddy ma yayi magana jiya" Kai kawai Imaan ta gyada
mata, Ammi tace "Ki tafi kitchen ki debi abinci, idan kuma shayi xa ki
hada sai ki hada, ko in soya maki kwai?" Imaan tace "Ammi nayi breakfast
fa" Ammi tace "Toh shikenan" Shiru ne ya biyo baya, Ammi tace
"Kina ji na?" Daga kai Imaan tayi ta kalleta tace "Ina ji
Ammi" Ammi tace "Bana son ki saka duk abubuwan da suka faru a ranki,
no matter what you've got to respect ur mother in law, in ma tana son ki in ma
bata son ki, duk wani abu na kyautata da kika san ya kamata ki dinga mata
albarkacin d'an ta da kike aure yanxu, kaninnsa ma gaba daya ko suna sonki, ko
basa son ki kiyi masu abinda ya kamata, babu ruwan ki da abinda suka maki a
baya duk wannan ya wuce, kuma nasan baki riko, lkci lkci sai ki ce ma Mujaheed
din ya kai ki ki gaisheta a can Zaria, just that you have to be very prayerful,
never get tired of praying domin addu'a shine makamin mumini, mijin ki kuma
kiyi masa biyayya yanda ya kamata, nasan ba sai na tsaya maki wani bayani a kan
aure ba you are educated Imaan, kin san komai, sai dai kawai kamar yanda kike
yi a nan gida haka nake son ki ci gaba da kasancewa cikin kamshi da tsafta,
sannan ki dinga kama jiki don wani lkcn na sanki da shegen son jiki, ko yaya ne
ki dinga aikin da baxai takura ki ba, kin dai ga yanda nake barin gida na a ko
da yaushe very neat, try to keep ur home clean kuma ya kasance cikin kamshi ko
da yaushe, duk da nasan ki da kokarin gyaran daki da wankin bandaki, but put in
more effort daughter, Allah ubangiji ya albarkaci auren ki, ya baku xaman
lafiya me dorewa, da hakurin xama da juna.... Kasa cewa komai Imaan tayi kanta
a kasa hawaye na sauka idonta, Bude kofar dakin aka yi Ammi ta kalli direction
din ta ga Inna tsaye bakin kofar, Ammi ta sauka saman gadon tace "Sannu
Inna" Inna tace "Sannu, me kike kitsa mata tun daxu bata dawo ba
Aisha??" Murmushi Ammi tayi tace "Kawai nasiha nake mata Inna"
inna tace "Ai kullum cikin yi mata nake" tana fadin haka ta kalli
Imaan tace "Tashi mu tafi, nasiha kuma wanne ne ban maki ba tun da kika
dawo wajena idan ba gulmar uwarki bane ya tashi" Imaan ta kalli Ammi a
sanyaye, da fillanci Ammi tace mata ta tashi ta tafi, inna ta saki baki tana
kallonta, mikewa Imaan tayi ta nufi kofa, Inna tace "Ba ruwana da
munafurci wllh" daga haka ta bi bayan Imaan suka fita, bayan sun fita
apartment din Inna na kallon Imaan tace "Me ta ce maki wai?" Imaan ta
turo baki tace "Toh Ina ruwanki?" Da yamma Inna ta dinga bin Imaan da
kallo ganin yanda ta shirya cikin riga da skirt har da shafa powder, Jin shiru
bata fito ba bayan ta shiga daki Inna ta mike ta bi bayanta a hankali ta leka
cikin dakin, a duke ta sameta jikin gado waya kare kunnenta, Inna ta buda baki
a sanyaye tana kallonta, Da sauri Imaan ta katse wayar hannunta ta ajiye tace
"Daddy ne fa nake kira" Inna ta karasa ta dau wayarta tana kallo
kamar xata yi kuka tace "In dai Mujaheed kika kira da wayata ke da Allah,
ba ruwana" Imaan ta mike ta fice daga dakin tace "Ai dai ba ke kika
saka katin ba Daddy ne ya saka maki naga" Maimoon ce ta shigo parlon tana
kallon Imaan tace "Abba na kiran ki Imaan" Inna tace "Ya dawo
ne?" Maimoon tace "Ehh ya dawo yanxu" Inna tace "Toh su
kuma gantalallun nan da suka tafi raka katuwa Rukayya basu dawo bane?"
Maimoon tace "Ehh kila xa su yi sati daya a can" Inna na tafe hannu
tace "Toh maza maza su dawo don rukayya Bata da tarbiyar da xata yi ma
yaran nan kada ta kai min jikoki ta barosu in shiga uku...." Imaan ta dau
Hijab dinta ta saka ta bi bayan Maimoon suka fita parlon, Abba na xaune parlor
hannunsa rike da remote Imaan ta shiga parlon ta xauna kasa ta sunkuyar da
kanta tace "Ina yini Abba?" Abba yace "Lafiya lau Mamana"
Imaan tace "Ya aiki?" Yace "Alhmdllh" Bude kofar aka yi
Mujaheed ya shigo da sallama, suna hada ido Imaan ta sunkuyar da kanta tana
wasa da fingers dinta, Mujaheed ya xauna kasa a hankali yace "Barka da
dawowa Abba" Abba yace "Yauwa, ya aiki?" Yace
"Alhmdllh" Abba yace "Maa sha Allah, kana ji na Muhd?" Mujaheed
ya kallesa yace "Ina ji Abba" Abba yace "Ka dau matar ka ku wuce
gida yanxu, Allah ya ba ku xaman lafiya... na yarda xaka rike Imaan yanda ya
kamata don nasan tarbiyar da nayi maka, so I need not to say much, Kai dai kayi
kokari ka rike min ita da amana, sai kuma ayi ta hakuri, daga nan yanxu ku tafi
ku yi ma Hajiya Aisha sallama da Amina sai ku wuce ba sai kun je gun inna
ba" Mujaheed ya kalli Imaan da ta rufe fuskarta ta fara hawaye, ya d'an yi
murmushi cikin sanyin murya yace "Toh nagode Abba, Allah ya kara
girma" Abba yace "Ameen, Allah maku albarka, ya baku xaman
lafiya" Mujaheed ya amsa da Ameen ya mike a sanyaye yana kallon Imaan da
ta ki motsi, Murmushi Abba yyi yace "To tashi ku je Mamana" imaan ta
mike da kyar tana share hawayen dake sakko mata da hijab ta bi bayan Mujaheed
da ya nufi kofa suka fita parlon.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
97.....
Gun Aunty suka fara wucewa a bedroom dinta, Mujaheed ya xauna
gefenta yace "Aunty xa mu wuce" Aunty tayi murmushi tace "Toh
maa sha Allah, Allah ya bada xaman lafiya ya kawo kazantar daki" murmushi
Mujaheed yyi ya mike Imaan dai na durkushe kasa, Aunty ta nuna mata gefenta
tace "Dawo nan daughter" Mikewa Imaan tayi tana share hawayen idonta
ta dawo kusa da Aunty ta xauna, Aunty ta kalli Mujaheed tace "Toh sai ka
bamu waje koh?" Juyawa yayi ya fita dakin yana murmushi. Nasiha me ratsa
jiki game da xamantakewar aure Aunty ta dinga yi mata tana bata shawarwarin da
xa su amfaneta, Imaan dai ta rufe fuskarta jikin Aunty hawaye na sauka idonta,
Aunty ta dago kanta daga karshe tana kallon kwayar idonta tana murmushi tace
"Allah ya albarkaci auren ki my daughter, ya kawo mana 'yan biyu da
wuri" Imaan ta sauke idonta kasa hawaye na xuba idonta, Aunty ta mike ta
dagota tace "Toh mu je yana jiran ki a waje" tana rike da hannunta
suka fita dakin, Maimoon dake parlor ta mike ta rungume Imaan a hankali tace
"Soon idan Maryam ta dawo xa mu je mu gan ki kin ji sis?" Imaan ta
gyada mata kai hawaye wasu na bin wasu a idonta, Aunty na rike da ita suka nufi
kofar fita tace "An kai maki duk kayan ki can gidan, a ko da yaushe ki
xamo cikin kamshi duk da nasan ki ba baya ba, sannan ki xama mai tattala komai
naki da na mijin ki, kin ji?" Kai kawai Imaan ke gyada mata, ganin
Mujaheed tsaye jikin flower Aunty tace "Toh ga daughter na amana Muhd,
though bani da fargaba nasan xaka rike min ita yanda ya kamata, sai kuma ayi ta
hakuri, Allah ya baku xaman lafiya" ya sauke kansa kasa yace "In sha
Allah Aunty, nagode" Aunty tace "Xa ku je kuyi ma Ammi sallama
koh?" Yace "Ehh" Aunty tace "Ohk to sai kun fito"
Mujaheed na gaba imaan na biye da shi har suka isa part din su, shi ya fara
shiga parlon da sallama sannan ta bi bayansa walking slowly, juyawa yyi ya kama
hannunta ganin ta makale bakin kofa ta warce da sauri, jin an bude kofa ya nufi
kujera, Ammi ta fito daga bedroom dinta tana kallonsu, ya xauna kansa a kasa
yace "Ina yini Ammi?" Tace "Lafiya qlau Mujaheed, ya aiki"
yace "Aiki Alhmdllh" Imaan dai na tsaye bata bude fuskarta ba har
lkcn, murya can kasa Mujaheed yace "Dama xa mu wuce ne yanxu Ammi"
Ammi tace "Toh Allah ya kiyaye hanya" A hankali yace "Ameen mun
gode" kallon Imaan da taki bude fuskarta tana shessheka yyi ya sauke kansa
sannan ya mike yace "To mun tafi" Ammi tace "Allah ya sanya
alkhairi, ya bada xaman lafiya...." Imaan ta nufi Ammi hawaye na sauka
idonta, Ammi tayi murmushi tace "Ji shashanci...." Rungumeta Imaan
tayi ta fashe da kuka, Ammi bata iya ta ce komai ba, Mujaheed ya juya a hankali ya fita daga parlon, Ammi
ta dago kanta tana kallonta, lkci daya jikinta yyi sanyi tace "Ki xama me
biyayya ga mijinki kinji Imaan, Allah ya albarkaci auren ku, ya baku xuri'a
dayyaba, nasan baxa ki bani kunya ba" Kuka kawai Imaan take bata iya ta
amsa mata ba, Ammi tayi karfin halin kin barin tayi hawayen ita ma ta kama
hannun Imaan har bakin kofa tace "Allah ya tsare" daga haka ta sake
ta Imaan ta fita daga parlon still crying, Parking space ta tadda Mujaheed
tsaye ya rungume hannayensa ya kafeta da ido, kin karasawa gun sa tayi ta
tsaya, ya bude mota sannan ya nufeta ya kamo hannunta ya bude front seat ta
shiga ya rufe motar, ya xaga ya shiga maxaunin driver yyi horn mai gadi ya bude
masa gate ya fita gidan da motar, yana hawa saman titi ya kamo hannunta a
hankali cikin sanyin murya yace "Ki daina kukan nan haka plss, tare da
yayan ki fa kike" Kamar ya kara tunxurata yin kukan hakan yasa yayi shiru,
har ya tsaya gun masu siyar da fruits ya siya ya dawo motar Imaan bata bude
fuskarta ba, ya ci gaba da driving dinsa, bayan kusan minti goma ta xame
hannunta a hankali daga fuskarta tana kallon titin gabanta, da sauri ta kallesa
tana goge idonta tace "Ina kuma xa mu je yaya?" Ya kalleta murya can
kasa yace "Zaria xa mu je" kallonsa ta dinga yi ko kiftawa babu, ya
kamo hannunta cikin sanyin murya yace "Xa mu je mu gaida Umma" Imaan
dai tayi shiru bata ce komai ba, and the rest of the journey was very silent
har suka isa garin Zaria, horn yyi bakin gate, sabon Mai gadi da ya sa a gidan
ya fito ya bude gate din ya shiga da motar yayi parking, imaan dai gabanta sai
faduwa yake sosai, ya kashe motar ya sauka ita ma ta bude side dinta a hankali
ta sauka tana bin gidan da kallo, Rahama ce ta fito daga cikin parlor ganinsa
ta nufesa da sauri cike da murnan ganinsa tace "Sannu da xuwa Yaya....
Mujaheed yace "Yauwa sannu" tunda Rahama ta kalli Imaan bata sake
kallonta ba ta amshi ledan hannun yayan nata ta wuce ciki, Rufe motar yyi yana
kallon Imaan yace "Mu je" ta sunkuyar da kai bata ce komai ba ya kama
hannunta suka nufi entrance din parlon, ko ba a fada masa ba he notice duk a
tsorace Imaan take, though shi ma dai karfin hali kawai yake don bai nuna ba
har suka shiga parlon, xaunar da ita saman kujera yyi sannan shi ma ya xauna,
sosai xuciyar imaan ke bugawa, yana kallonta murya can kasa yace "Relax
plss imaan..." Tayi masa murmushin karfin hali tana karanto addu'a a
xuciyarta, Ummi ta leko daga kitchen ta fito tana murmushi tace "Welcome
Yaya" yace "Thank you, Umma fa?" Ummi tace "She's
upstairs" Bata rufe baki ba sai ga Umma, Imaan ta daga kai suna hada ido
ta sunkuyar da kanta da sauri, Umma ta karasa shigowa cikin parlon ta xauna,
Imaan ta xamo kasa ba tare da ta yadda sun hada ido da ita ba murya can kasa
tace "Ina yini Umma" Umma bata kalleta ba tace "Lafiya lau, Alhmdllh"
Mujaheed yyi kasa da kai yace "Ina yini Umma" Umma tace "Lafiya
lau ya gida" yace "Alhmdllh" tace "Ya aiki fa" yace
"Alhmdllh Umma" Umma tace "To madallah" kallon Ummi tayi
tace "Kin gama girkin ne?" Ummi ta nufi kitchen tace "A'a na
kusa dai" Mujaheed na kallon Umman tasa yace "Aunty Mariya ta koma
ne?" Umma tace "Aa taje kasuwa xata dawo" Mujaheed yace
"Ohk..." Ummi ta dawo rike da tray mai dauke da table water daya da
goran coke daya da cup ta ajiye kusa da Mujaheed, kallonta kawai Mujaheed yake
har ta mike xata wuce Umma tace "Ruwan daya ya rage a gidan?" Ummi
bata ce komai ba ta xumburo baki ta koma kitchen sai ga ta ta dawo da wani
table water guda daya ta ajiye kan tray kusa da Mujaheed ta wuce, Umma tace
"Ya su Maimoon fa?" Mujaheed yace "Suna lafiya" Umma tace
"Daxu Yusuf ya xo, bai jima da wucewa ba ma, shekaranjiya ma ya xo"
Mujaheed ya mike yace "Ohk, ban yi la'asar ba Umma, xan je in yi
sllh" sosai gaban Imaan ya fadi jin xai fita ya barta ita kadai, ta dinga
kallonsa bata dai ce komai ba, Umma tace "Toh ka tafi masallaci, ita baxa
tayi sllhn ba?" Mujaheed ya kalli Imaan yace "Kin yi sllh ai?"
Girgixa kai tayi da sauri duk da tayi a gida, Umma tace "Toh ta tafi
sama" mikewa Imaan tayi ta nufi stairs xuciyarta na bugawa, Mujaheed ya bi
ta da ido sannan ya kalli Umma dake kallonsa yace "Sai na dawo Umma"
Umma tace "Toh sai ka dawo" daga haka ya fita parlon. Imaan ta bude
daya daga dakunan ta shiga, sosai gabanta ya fadi ganin jakunkunan Umma a dakin
wato dai dakin Umma ta shiga, tana shawaran xata fita daga dakin aka bude kofa
sai ga Umma ta shigo, kasa kwakkwaran motsi tayi inda take tsaye, kallo daya
Umma tayi mata ta dau wayarta dake gaban mirror ta fita dakin, Imaan ta sauke
wani ajiyar xuciya har lkcn gabanta bai bar faduwa ba, darduman da ta gani
shimfide kasa a dakin ta nufa ta xauna a kai tana ci gaba da karanto addu'o'i a
ranta, ta fi minti goma xaune dakin aka bude kofa, kanwar Umma Hajiya Mariya ta
shigo dakin, da fara'a take kallon Imaan tace "Ashe amarya ce a gidan yau,
sannun ku da xuwa" Imaan ta kirkiri murmushi tace "Ina yini
Mama" Hajiya Mariya tace "Lafiya lau Imaan, ya ku ka baro mutan
gidan?" Imaan tace "Alhmdllh" Hajiya Mariya tace "Toh
madallah, Allah ubangiji ya sanya albarka a auren nan, ya bada xuri'a
dayyaba" Imaan ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, Hajiya Mariya ta ajiye
handbag din hannunta ta fita dakin. Imaan na ta xaune dakin har shidda saura na
yamma, Rahma ta bude kofar dakin tana kallonta tace "Ance ki sakko ki ci
abinci" daga haka ta juya ta wuce, a hankali Imaan ta mike ta dauke pray
mat din ta linke ta ajiye sannan ta nufi kofa ta fita walking slowly har ta isa
downstairs, Mujaheed na xaune parlon da Umma dake dibar masa abinci a plate,
Hajiya Mariya ma na xaune parlon tana answering din call, Imaan ta karaso
parlon kanta a kasa ta xauna a kasa jikin kujera, kallonta kawai Mujaheed yake,
Umma ta ajiye masa abinci kusa da shi, ta dau wani plate din ta xuba wani ta
kalli Imaan, kafin tace komai Mujaheed na kallonta yace "Ga abincin
ki" mikewa Imaan tayi ta nufi Umma ta duka ta dau abincin a hankali tace
"Nagode" sannan ta koma ta xauna duk da ba yunwa ta ke ji ba, hira
kawai Mujaheed ke yi da kanwar mum dinsa, Imaan sai juya abincin gabanta take,
Hajiya Mariya tace "Toh ko xa ki wuce dinning ki ci abincin Imaan?"
Imaan tayi murmushi tana kallon direction din dinning din, Hajiya Mariya tace
"Tashi ki je can ki xauna kin ji" mikewa Imaan tayi ta dau abincin da
ke cike da nama ta wuce dinning ta xauna, tana ta xaune can bayan ta d'an ci
abincin da xata ci, Hira kawai Mujaheed yake da Hajiya Mariya amma gaba daya
hankalinsa na kan Ummar sa da tayi shiru bata cewa komai, can kuma ta mike ta
wuce sama ya bi ta da kallo, jin ana kiran Magrib ya mike yace "Xan je
masallaci in dawo mum" Hajiya Mariya tace "Toh sai ka dawo" ya
kalli imaan sannan ya nufi kofa ya fita, Hajiya Mariya ta mike ta dau plates
dake parlon ta kai kitchen ta fito tana kallon Imaan daga inda take xaune tace
"Tashi kema kiyi sllh Imaan" Imaan tace "Toh" daga haka ta
mike, sbda dadewan da tayi xaune a dinning din sai taji kafarta ya d'an rike
mata, haka dai ta daure ta wuce sama, wani dakin daban ta bude ta shiga bandaki
tayi alwala, ta fito ta xauna bakin gado, ta kusa minti biyar a xaune aka bude
kofar dakin Ummi na tsaye bakin kofa tace "Ance ga darduma can kije kiyi
sllh" Mikewa Imaan tayi ta fita dakin tana tafiya a hankali saboda
kafarta, dakin Umma ta bude ta shiga da sallama murya can kasa, taga darduman a
shimfide ba kowa dakin, ta hau saman darduman ta tada sllhn, tana ta azkar
bayan ta idar da sllh Hajiya Mariya ta shigo dakin tace "Imaan ke Mujaheed
ke jira xa ku wuce" A hankali Imaan tace "Toh" sannan ta mike ta
dauke darduman ta linke ta ajiye, Hajiya Mariya tace "Sai ayi ta hakuri,
Allah ya ba ku xaman lafiya" imaan bata iya tace mata komai ganin yanda
take tafiya Hajiya Mariya tace "Me ya samu kafar kuma" kamar xata yi
kuka tace "Ciwo yake son ya min" Hajiya Mariya tace "Ayya sannu,
kun xo da drugs din ki ne?" Imaan ta girgixa mata kai, kama hannunta
Hajiya Mariya tayi suka fita dakin, tun da suka sakko mujaheed ke kallonsu haka
ma Umma, Hajiya Mariya tace "Wai ciwon kafa take Mujaheed, sai kun fita
xaka siya mata magani ko akwai a gida?" Yana kallon Imaan yace "Xa mu
siya idan mun fita" Daga haka ya mike ya nufeta yace "Yaushe ya fara
maki ciwon?" imaan tace "Daxu" yace "Allah ya sauwake"
Komawa gun Umma yayi ya durkusa yace "Xa mu koma kaduna umma, in sha Allah
xan xo jibi" Umma tace "Toh Allah ubangiji ya kiyaye hanya ya tsare,
Allah ya maka albarka" yace "Ameen Umma ngd" har bakin mota suka
rakasu gaba daya, Hajiya Mariya na rike da hannun Imaan dake dingishi ta bude
mata front seat ta shiga Imaan ta ce ma Umma sai da safe, Umma tace "Allah
ya tashe mu lafiya" Hajiya Mariya ta rufe motar, Umma na kallon Mujaheed
tace "Ko a kawo maku aboniki ne?" Yace "Toh Umma" juyawa
tayi ta koma cikin gida sai ga ta ta dawo da kwalban man xafin gaba daya ta
mika masa ya amsa yace "Mun gode sai da safe" daga haka ya shiga
front seat Mai gadi ya bude masa gate ya ja motar sisters dinsa na masa Allah
ya kiyaye hanya, sai da ya kusa barin layin yyi parking yana kallon Imaan yace
"Sosai kafar ke maki ciwo?" Ta girgixa masa kai tace "Yana dai
yi min ciwo" ya dau man xafin ya bude yace "Bari in shafa maki kafin
mu kai kaduna in siya maki wanda kike shafawa" Bata ce komai ba ta daga
hijab din jikinta da skirt tana yatsine fuska ta juya tana facing dinsa ta daga
masa kafar, ya debi man xafin yana shafa mata a legs dinta tana masa kukan
shagwaba tana rike hannunsa wai xafi, murmushi kawai yake yana kallonta shi dai
bai ce mata komai ba har ya gama shafa mata ta sauke kafarta kasa yace
"Sorry wife" ta make kafada tace "Ko dai lil sis" kallonta
yyi yace "Koh?" Tace "Ehh" ya gyada mata kai yana murmushi
yace "Gaskiya ne, come closer in shafa maki sauran na hannuna a jikin ki"
Bai jira cewarta ba ya jawota ya saka hannunsa a hijab dinta ya daga rigar
jikinta ya shiga shafa mata both hands dinsa a warm tummy dinta gently in a
circular motion, ta xaro ido tana son komawa baya ya ki barin tayi hakan yana
kallon fuskarta to see her reaction, da farko kasa cewa komai tayi, can kuma ta
rike duk hannunsa kamar xata yi kuka tace "Wllh bana son irin haka yaya,
don Allah stop it" Bai saurareta ba har sai da ya kyaleta don kansa yana
murmushi, ta turo baki xuciyarta na bugawa har lkcn tana jin kamar hannunsa na
jikinta, driving din ya ci gaba da yi yana satan kallonta yana murmushi. Har
suka shiga garin kaduna Imaan bacci take tun bayan da suka baro Zaria, yayi
parking a wani babban pharmacy yana kallonta ganin yanda take bacci hankali kwance
don ya gyara mata kujeran motar, bai tasheta ba ya sauka motar ya rufe sannan
ya shiga pharmacy din, duk drugs dinta ya siya mata da na shafawa sannan ya
biya kudin ya fito, ya sameta tana bacci har lkcn, rufe motar da yyi bayan ya
shiga ne ya tada ta, ta dinga bin inda suke da kallo, yana murmushi yace
"Kin gama baccin ki na daren yau kuma yarinya, sae kuma gobe...." Ta
gyara xamanta tace "Where are we now?" Yace "Kaduna" daga
haka ya tada motar suka bar haraban pharmacy din... Gun masu gashin kaji yayi
parking yana kallonta yace "Do you care for some?" Tace "Meye
shi?" Yar dariya yyi yace "Kazan kika manta yau?" ta make kafada
tace "Ni dai a koshe nake" yace "A'a kin taba ganin inda amarya
ta kwana bata ci kaza ba?" imaan ta wani hade rai tace "Ni ba Amarya
bace" yace "Xa ki san ke amarya ce yau" daga haka ya sauka motar
ta bi sa da kallo, guda daya ya siya sannan ya hada da chill fresh milk da suke
siyarwa a wajen, yana dawowa cikin mota ya mika mata, ta ki amsa ta wani daure
fuska, ya ajiye yana murmushi bai ce mata komai ba ya tada motar, har suka isa
gida fuskarta a daure yake, Mai gadi ya bude masa gate bayan yyi horn ya shiga
gidan yyi parking, ya juya yana kallonta, hawaye ya gani makale idonta, sauka
yyi motar ya xaga ta side dinta ya bude motar ya kama hannunta ta fito daga
motar hawayen dake idonta ya sauko kasa, jawota yyi jikinsa a hankali yace
"Yayah ne fa Imaan"
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
98......
Imaan dai bata ce masa komai ba ta sauke kanta kasa a
hankali, yana murmushi ya ja dogon hancinta ta turo baki ta dauke kai, ledan
dake cikin motar ya dauko ya kulle motar sannan ya kama hannunta suka nufi
entrance din gidan, da makulli ya bude kofar ya shiga tana biye da shi a baya,
banda kamshi na turaren wuta me dadi bbu abinda ke tashi a parlon dake dauke da
new furnitures kamar ba a ta6a rayuwa ciki ba, komai na parlon sabo ne, yana rike da hannunta suka isa tsakar parlon
ya ajiye ledan hannunsa ganin taki yarda ta daga kanta, ya kai bakinsa kunnenta
yace "Baxa ki kalli gidan ki ba kanwata" Ita dai bata ce masa komai ba,
yana facing dinta ya dago kanta a hankali yace "Imaan" shiru tayi
tana kallonsa, ya sa finger dinsa ya share hawayen idonta yana murmushi ya kama
hannunta suka wuce upstairs, bedroom dinta ya bude mata yana kallonta yace
"Ur room" kallon dakin ta dinga tana tsaye bakin kofa, ya shigar da
ita ciki ta lumshe ido ta bude jin daddadan kamshin dake tashi dakin, I don't
want to talk about how expensive foreign furnitures da Daddy ya xuba ma tillon
yar tasa, kudi ne ba na wasa ba ya kashe a dakin Imaan, ko yar governor sai
haka, lol, ganin ta kasa cewa komai Mujaheed ya juya ya fita dakin, Imaan ta
dinga bin babban bedroom din da kallo wasu sabbin hawaye suka kawo idonta amma
na farin cikin abinda mahaifinta yayi mata, a sanyaye ta nufi kofar da ta gani
cikin dakin ta bude a hankali taga bandaki ne babba, ta sauke kanta kasa ta
juya ta fito daki, hijab din jikinta ta cire ta linke ta ajiye ta bude press
taga gogaggun kayanta me yawa da sleeping dresses har inner wears, rufe gun
kayan tayi ta koma bandaki ta dauro alwala ta fito ta dau sabon darduma dake
linke kan stool din mirror, babu kalan turaren da babu gaban mirror din, sai
lotions dinta da take shafawa da hair cream, ta shimfida darduman hannunta
sannan ta tada sllhn Isha, ta jima xaune kan darduma bayan ta idar da sllh tana
addu'a daga karshe ta mike har xata cire kayan jikinta sai kuma ta kalli kofar
dakin, turo baki tayi ta tafi ta sa makulli ta dawo ta cire kayan ta linke ta
ajiye ta shiga bathroom, babu abinda babu na bukata a cikin bathroom din tun
daga sponge, soap da take amfani da, shower gel, toothpaste, toothbrush, hatta
washing machine sai da Daddy ya siya mata aka sa a bathroom, ta hada ruwan xafi
a bucket da ta gani tayi wanka, ta wanke bakinta da Listerine sannan ta dau
brand new towel da ta gani a bandakin ta daura alwala ta dauro ta fito. Bata
wani dau lkci xaune gaban mirror tana shafe shafen turare ba ta mike ta fiddo
kayan baccinta a press ta saka, ta dau hijab tasa ta hau saman gado ta shige
cikin duvet ta rufe idonta, Har bacci ya fara daukanta taji ana knocking, ta
mike xaune ta wani hade rai tace "Waye wannan?" Mujaheed yace
"Waye koh? to bude ki amshi drugs din ki..." Tace "I am not
feeling pain anywhere" murmushi yayi yace "I know... but you need to
take them" Kamar xata yi kuka tace "Wllh Yaya bana jin ciwo, kuma ni
bacci nake ji, gobe xan sha" ya hade rai yace "Imaan open this door
now" ta marairaice ttace "Yaya wllh am feeling okay" yace
"Idan kika bari na bude kofar da kai na xan baki mamaki" tace
"Wayyoo Yaya ba sai in sha gobe ba nace" yace "Ohk jira in samo
makulli in dawo yanxu, Allah da gaske sai nayi shock din ki" xaro ido tayi
tana kallon kofar, jin shiru ta mike gabanta na faduwa, murya can kasa tace
"Yaya?" Taji shiru bai amsa ba, kara kiransa tayi ta ji bai amsa ba
ta nufi kofar a hankali ta murda makullin dake jiki ta bude kofar, cafkota yyi
ta fasa ihu a tsorace tace "Wayyo Yaya wllh ka ban tsoro" yace
"Da me yasa kika rufe kofar?" Ta marairaice tace "Saboda Ina jin
bacci" yana rike da ita suka xauna gefen gado yana kallonta yace "But
Ain't you hungry?" Kai ta gyada masa gabanta na faduwa tana kallonsa, ya
d'an yi murmushi yace "Toh amma sai ki ci kazan ki ko kadan ne, bari in
dauko" da har xata ce A'a sai kuma ta kalli kofa, da sauri tace
"Toh..." kallonta ya dinga yi kafin ya mike yana wani murmushi ya isa
kofar ya cire makullin jiki ya fita dakin, ta xaro ido tana bin sa da kallo
kamar xata fashe da kuka, ba a dau lkci ba ya dawo da plate dauke kaza sai
fresh milk with cup, ya ajiye su saman lallausan carpet dake dakin ya xauna
yana kallonta yace "Ko in xo in dauko ki?" A hankali tace "Yaya
wllh na koshi da gaske" yace "Ehh just tsoka daya xa ki ci sai ki sha
madaran" shiru tayi tana kallonsa kamar xata yi kuka, duk da dariyar da
take basa ya hade rai yace "Baxa ki sakko ba" xamowa kasa tayi a
hankali ta xauna tana facing dinsa ya dau tsoka daya ya kai bakinta ta sa hannu
xata amsa, ya mata wani kallo ya ki bata, haka nan ta bude bakin ya sa mata
naman ta kauda kai tana taunawa da kyar kamar warce ke taunar magani, shi dai
kallonta kawai yake, tana girgixa tace "Allah Yaya baya rai na yau, kamar
fa xan yi amai nake ji" Yana murmushi yace "Toh cinye na bakin ki sai
ki sha madaran shkkn" da kyar ta hadiye na bakinta ya bata fresh milk din
ta sha shi ma kadan tana yatsine fuska, ya ajiye su gefe ya mike ya dau darduma
ya shimfida yana kallonta yace "je ki wanke bakin ki Let pray" mikewa
tayi ta hau saman gado ta kwanta xata rufa da duvet tace "Ni dai nayi sllh
tun daxu, good night" Yace "Ai ban ce baki yi ba, come down my frnd
kiyi abinda nace maki" ta xaro ido tace "Yaya har shafa'i wllh nayi,
kawai wutr ne dai banyi ba tunda xan yi sllh cikin dare, wllh bacci nake ji
yaya" Ya nufi gadon ta mike da sauri tana komawa baya, yce "Sakko ki
rufa ma kanki asiri kiyi wutr dinki don ba yin sllhn nan na cikin dare xa ki yi
ba yau" ta hade rai tace"Saboda me?" Bai bata amsa ba ganin xai
cafkota da sauri ta sakko kasa daga kan gadon, ya dau hijab dinta ya mika mata
ta amsa tana kallonsa hawaye cike idonta ta tafi bandaki ta wanke bakinta ta
fito. Tun da suka idar da sllh ya juya yake kallonta ta ki yarda ta kallesa,
yyi murmushi ya matsa dab da ita, a hankali ya kai hannunsa saman goshinta
praying for the best in their married life, sun jima a haka daga bisani ya mike
yace "Saura drugs din ki" ta bi sa da kallo har ya fita dakin ta
tashi ta koma kan gado ta kwanta tayi lamo, yana dawowa rike da ledan drugs din
da glass cup dauke da ruwa ya kashe wutan dakin, ta mike xaune a hankali tace
"Yaya me yasa ka kashe??" Kunna kananun wuta mara haske sosai yyi ya
iso saman gadon ya xauna gefe ya ballar mata gaba daya Magungunan ya mika mata
da glass cup din ruwan, ta amsa ta kai baki ta shanye, ya karbi cup din ya
ajiye kasa, ya bude tube din da take shafawa a kafa yace "Saura
wannan" make kafada tayi tace "Ni dai wanda ka shafa min a mota ma
yyi, ai kafar ya daina min ciwo" ya daure fuska yace "Take off that
hijab in shafa maki in tafi in kwanta i am feeling sleepy" ta kallesa tace
"Tafiya xaka yi ka kwanta?" Yace "Ehh, or did you have anything
for me" girgixa masa kai tayi ta cire Hijab din, da sauri kuma ta rufe
jikinta tace "Ni dai ka kashe wutan kawai idan xaka fita sai ka kunna min
mara hasken" yyi murmushi yace "Yau kuma ni ake boye ma kafar?"
Bai jira cewarta ba ya kashe switch din dake jikin bango kusa da gado ya dawo
kusa da ita, ta daga rigar jikinta xuwa gwiwa, ya bude tube din ya fara shafa
mata lotion din a legs dinta xuwa toes tana kwance, ya fi minti goma yana shafa
mata ya kai fuskarsa nata jin tayi shiru, murya can kasa yace "Bayan
fa?" Ta bude ido tace "Har da shi?" Yace "Ehh" mikewa
xaune tayi ta sauke rigan kasa tayi
kwanta saman pillow, ya debi lotion din ya fara shafa mata tun daga
shoulders dinta har xuwa waist, ta wani turo baki kamar yana ganinta tace
"Ni dai Yaya da karfi xaka shafa min bana son kana min a hankali" ya
kai bakinsa kunnenta yace "Why?" Ta dauke kai tace "A'a ni bana
so dama ai bance yana min ciwo ba..." Yana murmushi murya can kasa yace
"Ohk bari in daina yi a hankalin" ta xaro ido tace "Toh ai kuma
ni bance ka karya min bayana ba, ka yi a hankalin" Bata kuma cewa komai ba
idonta a rufe, Lkci daya ta juyo jin gaba daya shafa magani a baya na neman
canxa salo tana kokarin mayar da rigarta sama tace "Yaya kawai ka kunna
wutan I am now feeling better ya isa haka ka tafi ka kwanta" kamo hannunta
yayi ya kwanta gefenta ya rufe bakinta kamar me rada yace "ohk bari in
shafa maki sauran a tummy din ki kamar daxu..." Bai bata chance din cewa
komai ba ya fara shafa mata hannunsa a ciki, turasa ta dinga yi jikinta na 6ari
tana cewa "Ni wllh bana so yaya ka bari" lkci daya ta ji Yaya fa
kamar ba shi ba, ta fara kokarin mikewa tana kokuwa da shi, ta dade bata yi
rikicewan da tayi a lkcn ba ganin ba sarki sai Allah ta galla masa cizo da
karfi amma ko gezau, hakan yasa ta dinga kiransa iya voice dinta, shi kuma ya
rufe bakin, tsoro yasa numfashinta ya dinga daga nan kuma bata kuma sanin komai
ba. Ray din rana da ya sauka kan fuskarta ya sa ta bude ido a hankali ta sauke
kan Ac dake dakin, kalle kallen dakin ta shiga yi as if trying to recall
something, dai dai nan aka bude kofar dakin suka yi ido hudu da Mujaheed lkci
daya ya sauke idonsa kasa ya kullo kofar, ta mike xaune da kyar, ta dafe kanta
tace "Yaya Ina jin xaxxabi, my head is aching" Ya iso kusa da ita ya
xauna gefenta still ya ki kallonta yace "Kiyi sllh sai kiyi breakfast in
baki magani" ta xaro ido ta kalli agogo taga karfe takwas ya kusa a
hankali tace "Sllh kuma Yaya, me yasa baka tasheni da asuba ba..."
Komawa tayi ta kwanta saman pillow tace "and my body is weak, xaxxabi nake
ji" Ya mike ya shiga bathroom ta bi sa da kallo kanta na sara mata, kara
kallon agogo tayi ta mike xaune tana son tashi amma taji kamar idan ta tashi
xata fadi ga ciwo da bayanta ke mata, fitowa yayi bathroom din yace "Ga
warm water a kettle kije kiyi alwala" Yana fadin haka ya iso gabanta ya
kama hannunta trying not to look at her in the eyes, sosai yaji jikinta yyi
dumi, Imaan dai sai kallonsa take, Lkci daya ta xame hannunta ta fasa ihu tana
komawa baya tana kallonsa, rikota yyi cikin sanyin murya yace "Stay still
Imaan" girgixa masa kai ta dinga yi jikinta na bari tace "Wayyo Allah
na, don Allah ka sakeni yaya...." ya saketa yace "Toh alwala xa ki yi
ai" ta rufe fuskarta da pillow tana kuka sosai tana kiran inna, juyawa yyi
ya fita dakin ya kulle mata kofar. Ba karamin wahala imaan ta ba Mujaheed ba
ranan, though yasan dole xata daga masa hankali amma bai yi tunanin xai kai
haka ba, sai a lkcn yasan raki yafi yawa a ciwon da take yi a gida, bai ta6a
ganin mai raki irin Imaan ba, duk ta sa shi ma ya dinga jin kamar xaxxabi sai
rufesa, duk abinda yasan xai mata ta samu relieve na ciwon baya da take ta ce
masa yyi.. amma Imaan taki bari ya huta da rakinta, damuwarsa abincin da ta ki
ci tun safe, gashi duk ta ishesa da kuka ita ya maida ta gida, a haka dai ya
yini yana fama kamar Nanny har washegari, nan ma kuma ta daura daga inda ta
tsaya jiya, though da Xaxxabi sosai ta tashi ranan, sure yasan she is in pain
but ko kadan bata da juriya, karfe sha biyu ya fita pharmacy ya siyo ruwan drip
da xai kara mata, bayan ya saka mata ruwan shine ta samu tayi ta bacci har
kusan yamma. Yana xaune parlor ya jinginar da kansa da kujera har bacci ya soma
daukansa a haka aka danna bell, bude ido yyi ya mike ya isa kofar ya bude,
Maimoon ce tsaye da basket da ke dauke da abinci tana murmushi tace "Ina
yini Yaya?" Ya shafa kansa yace "Lafiya lau, how are you?" Tace
"I am fine, Inna ce tace in kawo ma Imaan abinci amma fa wai ban da kai,
tace bata baka ba ko ka ci" tana magana tana dariya, ya d'an yi murmushi
yace "Toh shiga ki ajiye mata" Yana fadin haka ya bata hanya ta shiga
parlor ta ajiye abincin tace "Tana Ina?" Yace "She's sleeping
upstairs" tace "Inna ta ban sako in gaya mata fa" yace
"Bacci take yi..." Maimoon na murmushi tace "Toh shkkn sai da
safe" yace "Jira in dauko maki transport" tace "A'a driver
ne ya kawo ni" yace "Toh ki gaida Aunty and everyone" tace
"In sha Allah" daga haka ta fita parlon ya kulle kofa, Yana son xuwa
sama amma yana tsoron tashin hankalin Imaan, ya fi minti sha biyar xaune daga
karshe ya mike ya wuce sama, a hankali ya bude kofar dakin, ya ganta xaune ta
jingina da gado hawaye na sakkowa idonta... Ya sauke idonsa ya kulle kofar ya
karasa kusa da ita, ta hade kanta da gwiwa tana shessheka, har ransa ya dinga
jin tausayinta, cikin sanyin murya yace "I am sorry Imaan, na fa ce ki yi
hakuru..." Ta fashe da kuka tace "Ni bana so, kuma wllh sai na fada
ka da Inna" murmushi yyi ya dago kanta ya jawota jikinsa tana kuka sosai,
yace "Toh na ji ki gaya ma Inna in har xa ki hakura" ita dai bata ce
komai tana shessheka.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
*Albishirinku 'yan uwa*
Shin ko kun San zaku iya magance mafi yawan cututtukan da
suka addabi al'umma yanzu cikin sauki?
Sinadarin _Stemcell total care_ yayi fice wajen magance
matsalolin diabetes, BP, asthma, sickler, cancer, stroke, rashin haihuwa,
fibroid, infection da duk wata matsala da ta danganci lafiyar Al'umma.
Ba wannan kadai ba, akwai coffee na double root Wanda ke
inganta duk wani abu da ya shafi rayuwar
aure ga maza da Mata, inganta qwayoyin haihuwa da dai sauransu.
Akwai sinadarin rage tumbi da dai sauransu.
*Domin neman qarin bayani ku tuntubi wannan lambar
07068136856*
Sai an gwada akan san na kwarai.
99.....
Mujaheed ya sauka kasa ya debar mata abincin da Maimoon ta
kawo yana kallonta yace "Come and eat plss" ta make kafada ba tare da
ta kallesa ba tace "Ni baxan ci ba" daukan abincin yyi ya dawo gefen
gadon ya xauna yana kallonta cikin kwantar da murya yace "Haba wife, ki ci
ko kadan ne don Allah" matsawa tayi daga kusa da shi, ya ajiye abincin
yace "Toh me xa ki ci?" Ta goge idonta a hankali tace "Ni gida
xan tafi gun Ammina" ya d'an yi murmushi yace "Ita ma gaya mata xa
kiyi?" Kallonsa tayi da sauri, lkci daya suka dauke kai a tare, Imaan ta
rufe fuskarta da pillow hawaye ya kawo idonta, a hankali ya dawo kusa da ita ya
dagota ya rungumeta ya lumshe ido murya can kasa yace "Toh ki ci ko kadan
ne gobe xan kai ki gida in sha Allah" Bai jira cewarta ba ya dau abincin
da spoon ya debi tuwon ya kai mata baki, ta girgixa kai cikin sanyin murya tace
"Ni bana son tuwo ba" cikin lallami yace "Toh me xa ki ci?"
Tace "Shinkafa..." ya ajiye abincin ya mike ya dau hijab dinta ya
mika mata yace "To sa mu je in siya maki" mikewa tayi a hankali ta
amshi hijab din tasa ya kama hannunta tana biye da shi walking very slowly,
steps din nata yake kallo har suka fito dakin yace "Ko in dauke ki, you
can't walk?" Bai jira cewarta ba ya dauketa kamr little baby, ta rikesa da
sauri tace "Meye haka Yaya? Xan fadi plss" sosai gabanta ya fadi
memory din shekaranjiya na dawo mata jin ynda ya riketa, ta ki yarda su hada
ido, parking space ya ajiyeta yana murmushi yace "My weightless
wife..." Ta turo baki tace "Ni ka daina ce min wife dinka" ya
wara idonsa yace "Toh me ya rage? Ko sai mun sake abun shekaranjiya?"
Tsabar yanda xuciyarta ya buga sai da ta jingina da mota da sauri tana
kallonsa, ya sauke kansa yana murmushi, lkci daya ta fashe da kuka sosai, ya
xaro ido yace "A'a toh yi hakuri wasa nake maki..." Ta juya ta kife
kanta da mota tana shessheka, ya juyo da ita ya bude front seat ya shigar da
ita ta xauna ya rufe motar sannan ya xaga maxaunin driver ya shiga, ya dago
kanta yace "It's a promise baxan sake ba Imaan, sai idan ke kika sameni
har daki..." Yana murmushi ya karasa fadin haka, Ita dai bata ce masa
komai ba a ranta kuwa cewa tayi ashe har abada kuwa in dai ita xata je dakinsa
ta samesa, yace "Kuma ni ma sai na maki shagwaba yanda nake so kafin na
yadda" Tabe baki tayi ya kalleta ta gefen ido don sarai yasan tunanin da
take, ya wani murmushi yana gyada kai, murya can kasa tace "Is that a
promise?" Ya d'an bude ido yace "Suree" Bata ce komai ba amma
har ranta taji dadin promise din nan. tafiya yake amma gaba daya tunaninsa na
waje daban, the memory was just still fresh, that night be an unforgettable one
to him, bai san lkcn da yyi wani murmushi ba, ya kamo hannunta a hankali ba
tare da ya kalleta ba yace "Imaan" ita dai idonta na kan glass din
mota tana kallon waje ko kiftawa babu, nan ko tunani take me yasa ta kasa
recalling gaba daya abubuwan da suka faru shekaranjiya, tasan dai ta tashi
cikin daren but ba komai ta tuna ba, all she could remember was the pain, she
was seriously in pain all over daga baya kuma bata san ya aka yi ba, bata san
lkcn da ta koma bacci ba, jin bata amsa ba Mujaheed ya sake kiranta a hankali,
da sauri ta juyo, suna hada ido a tare suke sauke kai ya mayar da idonsa kan
titi ita ma ta ci gaba da kallon inda take kallo gabanta na faduwa, cikin sanyin
murya yace "Allah ya maki albarka..., I am proud of you" ita dai bata
ce masa komai ba, har suka kawo wajen cin abinci yayi parking yace "I will
be back soon" Yana fita ta bi sa da kallo gabanta na faduwa don har
xuciyarta take tsoronsa ynxu, tsoro me tsanani, har dai ya shiga cikin eatry
din, ta jinginar da kai da kujera ita dai fa memory din da ta kasa cirewa ranta
was just the moment da ta dinga jin unbearable ail and after that bata kuma
sanin komai ba, Bayan kusan minti goma ya fito rike da take away daya a
hannunsa, ta sauke idonta daga kallonsa har ya shigo motar ya tada suka bar
haraban eatry din. Suna isa gida a parlon ya sa ta xauna ya bata abinci ta dau
spoon tana juyawa a hankali, shi kuma ya xauna saman kujera yana kallonta,
Kamar ana tilastata ta dinga cin abincin, daga karshe ta rufe ta tashi xata
wuce sama yace "Imaan" Bata juyo ba amma ta tsaya, yace "Baki ci
da yawa ba" tace "Na koshi" daga haka ta wuce sama ya bi ta da
ido, murmushi yyi shi kadai ya mike ya dauke abincin ya kai kitchen, Tun da
imaan ta fito wanka bayan isha ta gansa a dakinta ta xama restless, yace
"Are you sure baki kara ruwan sanyi a ruwan ba?" Ta hade rai bata
basa amsa ba, dama da hijab dinta har kasa ta fito sbda sanyi da take ji ta
tafi can karshen gadon ta xauna ta takure waje daya, yace "Baxa ki sa
kayan ba" shiru tayi masa ta wani hade rai, ya mike yace "Toh shkkn
na tafi" daga haka ya fita dakin yana sha kansa, ta tashi da sauri ta sa
kayan baccinta ta feshe jikinta da turare ta sa wani hijab din ta hau saman gado
ta kwanta ta rufe har kanta gabanta na faduwa, kafin karfe goma har tayi bacci,
a lkcn ya shigo dakin dakin rike da Magungunanta, ya xauna gefen gadon ya cire
duvet din a hankali ya kai hannu goshinta, a tsorace ta farka ta mike xaune da
sauri tana ja baya ta fashe da kuka tace "Don Allah yayi hakuri yaya"
yace "Magani xa ki sha Imaan" hannunta na rawa ta amshi maganin da
yake mike mata da ruwa ta sha, ya mike yace "To sai da safe" daga
haka ya fita dakin sai da taji ya shiga dakinsa ya rufe sannan taji hankalinta
ya kwanta ta koma a hankali ta kwanta tana sauke ajiyar xuciya. Da asuba bayan
Mujaheed ya dawo masallaci ya shigo tashinta ya ganta xaune saman darduma har
ta idar da sllh ga qur'ani gabanta tana karantawa cikin sanyin muryarta, yyi
murmushi ya xauna gefen gado yana kallonta ko kiftawan kirki bbu, sai da tayi
rabin suran da take karantawa sannan ta rufe qur'an din, amma bata yadda ta
kallesa ba, murya can kasa yace "I once told you kids dina baxa su samu
flaws in recitation of Al-quran ba kin tuna?" Sai a snn ta kallesa tayi
shiru, yyi murmushi yana shafa kansa yace "Kin gane me nake nufi
yanxu?" Ita dai kallonsa kawai take and she looks so confuse, ya sakko
kusa kusa da ita yace "Fatan kin tashi lafiya sweet wife?" Ta sauke
idonta bata ce komai ba ta hade rai, mikewa yyi ya fita dakin ta bi sa da
kallo. Can ta tashi ta dauke Quran din da darduman ta ajiye su inda ya kamata
sannan ta shiga bathroom ta hada ruwan wanka yanda taga yana yi mata tayi, ta
wanke baki ta fito, doguwar riga kawai ta saka bayan ta shafa mai ta fesa
turare ta kwanta. Misalin karfe takwas da wani abu danna bell da aka yi
downstairs ya farkar da ita, ta mike xaune jin dannawa ake ta yi ba kakkautawa
ta sauko daga saman gadon ta fita dakin dai dai lkcn da shi ma ya fito parlonsa,
ta sunkuyar da kai yace "Go and sleep I will check" Bata ce masa
komai ba ya fita ta bi bayansa, tsaye ta gansa yana lekan balcony din through
window, ganin ya ki matsawa daga jikin window din ta karasa downstairs har ta
iso bayansa dai dai lkcn da ya sake curtain din xai juyo suka kusa cin karo
jawota yyi jikinta, tayi lamo, murya can kasa tace "Waye?" Yace
"I think it's not necessary...." Sosai gabanta ya fadi jin abinda
yace ta daga kai tana kallonsa, ya ja ta xa su bar parlon. Ta fixge hannunta
tace "Who is it plss?" Shiru yayi yana kallonta kafin yace
"Kishiyar ki" ta buda ido tana kallonsa gabanta na faduwa, lkci daya
ta juya ta wuce sama ya bi ta da kallo yana murmushi sannan ya kara kallon
kofar da aka fara bubbuga da karfi maimakon bell da ake dannawa, ya koma gun
kofar ya tsaya yace "Who is that?" Da karfi tace "Ubanka ne,
nace ubanka ne..." dariya yyi yace "Toh kya kara tsufa a inda kike
tsaye kuwa, kawai da sassafe mutane basu tashi ba ki taho masu gida, ke haka
ake yi a garin ku?"
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
*Albishirinku 'yan uwa*
Shin ko kun San zaku iya magance mafi yawan cututtukan da
suka addabi al'umma yanzu cikin sauki?
Sinadarin _Stemcell total care_ yayi fice wajen magance
matsalolin diabetes, BP, asthma, sickler, cancer, stroke, rashin haihuwa,
fibroid, infection da duk wata matsala da ta danganci lafiyar Al'umma.
Ba wannan kadai ba, akwai coffee na double root Wanda ke
inganta duk wani abu da ya shafi rayuwar
aure ga maza da Mata, inganta qwayoyin haihuwa da dai sauransu.
Akwai sinadarin rage tumbi da dai sauransu.
*Domin neman qarin bayani ku tuntubi wannan lambar
07068136856*
Sai an gwada akan san na kwarai.
100...
A fusace inna tace "Ni dai duk wanda ya walakanta ni
kansa ya walakanta duniya da lahira, don ba banxa nake ba, ta yaya xa a barni a
gantale bakin shegen kofa daga xuwa abun arxiki?" Mujaheed na murmushi ya
bude kofar yace "Toh mu munce ki xo mana da sassafe ne balle a bar ki a
gantale" Bangajesa ta kusa yi ta shige parlon fuska daure, ya bi ta da
kallo yana dariya, ta cire Hijab din jikinta ta linke ta ajiye tana kare ma
parlon kallo tace "Idan ba dai ya xamar min dole in duba jikata ba uwar me
xai kawo ni gantalallen gidanka Mujaheed, me kake bani? wllh albarkacin Imaan
na xo gidan nan yau, don ubanta ya min abinda har in mutu baxan manta ba ya
rike ni da kyau, ka tafi ka kira min ita in ga jikata in kama hanya inyi
wucewata..." Ya dawo kusa da ita ya xauna yana murmushi yace "Oh ni
ba jikan ki bane?" Ta daga hannu sama da sauri tace "A'a ba ruwana da
wannan xancen, uban me dama na hada da kai?" Ya mike yace "Toh bari
in kira maki ita, kina ganinta ki tashi ki bar min gidana dama kar in sa mai
gadi ya fitar da ke" Bai jira cewarta ba ya wuce sama, xaune ya tadda
Imaan gefen gado tana kallon door din dakin, ita kanta bata san irin kwanciyar
da hankalinta yyi ba jin muryar Inna, don gaba daya tunaninta Safeenah ce kamar
yanda yace mata, ya karasa dakin ya xauna gefenta ta dauke kai, murmushi yayi
ya juyo da fuskarta a hankali yace "Ki sakko ku gaisa da kishiyar ki"
Yana fadin haka ya mike ya kama hannunta suna isa kofar dakin yace "Ko in
dauke ki?" Ta hade rai tace "Saboda me?" Daukarta yyi kamar
jiya, ta xaro ido ta rikesa tace "Yaya bana so da gaske ka ajiye ni
plss" bai saurareta ba har suka sauka downstairs, Inna na ganinsu ta yo
waje da ido ta mike da sauru tace "Nashiga uku, me ya sameta
Mujaheed??" Imaan na kokarin sauka tace "Don Allah Yaya ka ajiye ni plss"
ajiye ta yyi bayan sun shigo parlon yana kallon eye balls dinta, turo baki tayi
tana sauke rigarta da ya tattare, Inna ta koma ta xauna tayi tagumi, Imaan ta
karasa gunta tana murmushi ta xauna kusa da ita ta shige jikinta tace
"Sannu da xuwa Inna" Inna ta turata daga jikinta tace "A gaskiya
Imaan ba ki yi halina ba ko kadan, kwata kwata baki da jan aji, haka kawai
mutumi bai maki lefe ba ki dinga shigewa jikinsa salon ya cuce ki ya kai ki ya
baro ki, meye amfanin daukan ki da yayi ynxu?" Sosai ta ba Mujaheed da ya
xauna yana kallonta dariya, Imaan dai bata ce komai ba, Inna na nuna ta da
yatsa tace "Wato duk abubuwan da nake gaya maki baki ji ba kenan
koh?" Imaan ta turo baki tace "Ni nace maki ban ji ba?" Inna ta
matsa daga kusa da ita tace "Ba ruwana wllh, idan ba ni din ba dama waye
xai gaya maki gaskiyar da xai maki amfani, Bukar da Ahmadu da matansu duk sun
lalace babu tsoron Allah, kuma a gaskiya ni dai ban karya ba na fito gida yunwa
nake ji" Mikewa Imaan tayi ta nufi kitchen tana tafiya a hankali, Inna
tayi mitsi mitsi da ido tana bin ta da kallo tace "Me ya sami kafar
kuma?" Mujaheed ya mike ya isa kusa da ita ya duka dai dai gabanta yace
"Ke dai kin fiye sa ido, Ina ruwan ki da abinda ya samu kafarta" sake
baki tayi tana bin Imaan da kallo har ta shige kitchen, ya mike yana murmushi
ya bi bayanta xuwa kitchen din, tsaye ya ganta tana taran ruwa a bowl, ya isa
kusa da ita yace "Me xa ki yi?" Bata juyo ba tace "Tace bata yi
breakfast ba" Ya jawota jikinsa murya can kasa yace "Xa ki iya?"
Tana shakan kamshin sa tayi shiru, sai kuma ta gyada masa kai tace
"Uhm" daga haka ta janye jikinta ta debo Irish ta dau peeler ta fara
peeling dinsu, ya duka yana kallonta, shi ya taimaka mata ta gama soye soyen
just to keep and eye on her to make sure is fine, tana daura su kan tray ya
rungumeta ta baya, sosai gabanta ya fadi, tana kokarin barin wajen tace
"Bana so Yaya" murya can kasa yace "Baki son me?" matsawa
tayi daga kusa da shi ta hade rai, ya dinga kallonta yana murmushi, shi ya dau
breakfast din ya fita parlor, xaune ya tadda
Inna kana kujera tana ta xuba gyangyadi, yyi dariya ya isa kusa da ita
ya ajiye tray din hannunsa yace "Mutum baxai tsaya gidan yyi bacci ba
kawai ya xo gidan mutane da sassafe yayi ta gyangyadi...." da sauri ta
bude ido bai jira cewarta ba ya koma kitchen, tare da Imaan da taki fitowa suka
dawo parlon, gaba daya taki yarda ta kalli Inna, Inna dai sai kallonsu take ta
gefen ido tana bude Madara har suka wuce sama, sannan ta gyada kai tace
"Ikon Allah, da kyar idan 'yar nan ta Bukar ba jarababbiya bace"
gefen gado Mujaheed ya sa imaan ta xauna ya duka gabanta yana kallonta yace
"Toh ke me xa ki ci wife?" Ta dauke kai tace "Sai anjima"
ya mike yace "Ohk Ina xuwa" fita yayi dakin ta bi sa da kallo, ba a
dau lkci ba ya dawo da laptop dinsa da waya ya xauna gefenta ya jawota jikinsa
yace "Hope ba ki jin ciwo ko Ina yanxu?" Kai kawai ta gyada masa, ya
ci gaba da abinda yake a laptop din idonta na kan laptop din, sun fi 20 mins a
haka wayarsa ya fara ring, a tare suka kalli wayar, Sunan Safeenah ne ya fito a
screen din, imaan ta dinga kallon wayar bbu ko kiftawa, shi kansa Mujaheed
kallon wayar yake, can yyi silencing kiran ya maida idonsa kan laptop, kira ya
fi uku ya shigo wayarsa na Safeenah bayan first kiran, daga karshe ya kife
wayar Mujaheed still operating his laptop, can kuma ya mike ya dau laptop din
da wayarsa yana kallon Imaan da ta yi kwanciyar ta yace "Bari in tafi
wajen Inna" Bata ce komai ba ya nufi kofa ya fita, mikewa xaune tayi ta bi
sa da kallo haka nan taji gabanta na faduwa, Yana fita da kusan minti goma sai
ga Inna ta shigo dakin ta rike ha6a tace "Shi Mujaheed din yace maki kar
ku sakko kasa ku barni ni daya a parlor kamar shegiyar mayya?" Imaan tace
"Ba ya sauka ba shi inna" cike da masifa Inna tace "Ya sauka
ina? Ni kadai raina a parlor kamar tsohuwar mayya, dama wllh sai da Ahmadu yace
kada in je naki ji to gashi dai an walakanta masu ni, dama abinda ya guda kenan
ni ce bana jin magana" Imaan ta sauko saman gadon ta marairaice tace
"Inna ni fa kaina ne ke ciwo shi sa na xo na kwanta, wllh na xata Yaya
yana parlor" Inna ta kulle kofar ta karaso kan gadon murya can kasa tace
"Amma dai duk abubuwan da na gaya maki a gida kina aiki da su kuwa
Imaan??" Imaan tace "Na me kenan?" Inna tace "A dakin nan
Mujaheed ke kwana?" Imaan bata san lkcn da tayi murmushi ba ta girgixa kai
tace "Aa ba nan yake kwana ba" Inna tace "Toh kar ki kuskura sai
kin ga akwatuna kin ji?" Imaan tace "Toh" Inna tace "Atoh,
ko min dadin bakin da xai maki kuwa" Imaan ta gyada mata kai tana
murmushi, Inna tace "Kuma kina dai cin abinci koh naga duk kin fige?"
Imaan tace "Ehh Ina ci" Bude kofar dakin aka yi Mujaheed ya shigo,
Inna tace "Toh Ahmadu dai yace kada in dade, haka kawai kada in bata ran
d'a na, bari in je Imaan, in sha Allahu jibi xan xo..." A hankali Imaan
tace "Inna ki bari da yamma mana" Inna tace "A'a haka kawai, wa
gareni da xai gaya min gaskiya banda Ahmadun, ga Bukar ya xama abinda ya
xama" daga haka ta nufi kofa Imaan ta mike ta ki yarda ta kalli Mujaheed
dake kallonsu ta bi bayan Inna. Murmushi Mujaheed yyi ya bi bayansu yace
"Toh ni ne baxa ki ma sallama ba Inna?" Inna na sauka stairs tayi
kamar bata ji sa ba Imaan na biye da ita, tsaye ya gansu balcony Inna na mata
magana kasa kasa, tana ganinsa tayi shiru ta fara tafiya tana cewa "Toh ni
na tafi Imaan, Allah ubangiji yyi maki albarka, ai kin cika min ciki...."
dariya ta basa sosai ya bi ta ya kamo hannunta yace "Toh mu je in ajiye ki
a gida inna sai nima ki sa min albarkan" ta tabe baki bata dai ce komai
ba, imaan dai na tsaye har ya bude mata back seat, Inna ta kalli Imaan tace
"Fatan dai duk kin ji abubuwan da na gaya maki koh?" Imaan ta gyada
mata kai a hankali, Mujaheed yace "Dauko Hijab dinki mu je mu yi dropping
dinta" yi tayi kamar bata ji sa ba ta juya ta koma ciki, tana tsaye parlor
har ta ji fitar motarsa a compound din, sai da taji Mai gadi ya kulle gate
sannan ta wuce sama ta shiga parlonsa da sauri, tun da suka xo gidan ranan ne
ta fara shiga parlon, duk iya dubanta bata ga wayarsa ba, hakan yasa ta karasa
cikin bedroom dinsa, daddadan kamshi ke tashi dakin nasa dake very neat, ta
nufi saman gado ganin wayarsa ta dauka ta bude, call logs ta shiga, sosai
gabanta ya fadi tana kallon kiran safeenah da yayi picking, ta shiga details
don duba minutes din kiran aka bude kofar dakin, da sauri ta juya xuciyarta na
bugawa, kallonta ya tsaya yi sannan ya mika mata hannu alamar ta basa wayar,
sauke kanta tayi kasa bata motsa daga inda take ba, ya karasa ya karbi wayar a
hannunta sannan ya juya ya fita, Bata san lkcn da ta durkusa kasan dakin ba ta
hade kai da gwiwa sai dai taji kukan ma ya ki xuwa, ta fi minti goma a haka
sannan ta mike da kyar ta fita dakin ta koma nata, xaunawa tayi gefen gado har
sannan xuciyarta na bugawa. Imaan na tsaye kitchen tana wanke abubuwan da ta
6ata wajen hada ma inna breakfast ta ji shigowar motar mujaheed gidan, Bata
fito kitchen din ba sai da ta gama tsaftace ko ina sannan, xaune ta samesa
parlor ya jinginar da kansa da kujera, ya bi ta da kallo yace "Aunty na
gaishe ki" tace "Ohkk" sannan ta wuce sama, tsaf ta gyara
dakinta ta canxa bedsheet ta kunna turaren wuta dama tun da tayi wanka ta wanke
bandakin sama sama, duk da yunwar da ta fara ji sosai bata yadda ta sauka
parlor ba tayi kwanciyarta tayi lamo gaba daya taji hankalinta ya ki kwanciya,
Bude kofar dakin aka yi ta rufe ido da sauri kamar mai bacci, ya kulle kofar ya
karaso kusa da ita ya xauna gefenta ya kai fuskarsa dai dai nata yace "Kin
ma yi breakfast din kuwa Imaan?" Tana kokarin juya masa baya har lkcn
idonta a rufe tace "Uhm" dagota yyi ta bude ido fuska daure tace
"Bana son haka..." Bai bari ta rufe baki ba ya hade bakinsa da nata,
Turasa ta dinga yi amma ya ki sakinta, ya rungumeta sosai yana kissing duk
jikinta, ta fara girgixa masa kai kamar xata yi kuka tace "Yaya stop plss"
ko sauraranta bai yi ba yana bin ta a hankali kuma a nutse, sun dau lkci me
tsaho a haka ganin gaba daya ta sakar masa jiki ya bude lumsassun idonsa a
hankali yana kallonta, ita ma idonta a rufe suke yyi murmushi ya ja hancinta a
hankali yana shafa fuskarta yace "Imaan" turo baki tayi ta juya masa
baya ba tare da ta bude idon ba, ya mike xaune ya dagota ya rungumeta murya can
kasa yace "What are taking for breakfast?" Bata ce komai ba kuma bata
bude idon ba, ya mayar da ita ya kwanta yana murmushi ya mike ya fita dakin,
sai a sannan ta bude idonta a hankali. Har bacci ya fara dauketa Mujaheed ya
dawo dakin da take away din rice and stew ya ajiye abincin ya hau saman gadon
ya kai fuskarta yace "Imaan" Bude ido tayi da sauri suna hada ido ta
kauda kai ta mike xaune yace "Ga abinci ki ci, I am going to mosque
now" ta gyada masa kai ya mike ya fita, tana jin ya shiga dakinsa ta kalli
agogo taga sha biyu ya wuce, mikewa tayi ta wuce bathroom, ta hada ruwan xafi
sosai tayi wanka sannan ta dauro alwala ta fito, tana ta xaune kan darduma
bayan ta idar da sllh, ga abincin da ya ajiye mata bata ko bude ba, ya shigo
dakin sanye da kananun kaya yana kallon ledan takeaway din yace "But I
told you to eat first Imaan" ta jawo abincin tace "Yanxu xan ci"
ya xauna gefen gado yana kallonta yace "Did you take ur bath?" Ta
girgixa masa kai ba tare da ta kallesa ba ta bude abincin ta fara ci, ya mike
yace "idan kin gama you come downstairs" ta gyada masa kai ya fita
dakin, tana gama cin abincin ta mike ta fita da take away din xuwa parlor, tv
kadai ke aiki parlon ta karasa kitchen ta ajiye ledan hannunta ta fito, wayarsa
dake kan kujera ya fara ring ta karasa da sauri tana kallon screen din ta ga
Safeenah, still tayi ta kasa daina kallon phone din, jin ya bude kofa upstairs
ta tafi bayan kujera da sauri ta durkusa har ya sakko parlon ya dau wayar yana
duba screen din sannan ya daga ya kai kunne, daga daya bangaren cikin sanyin
murya Safeenah tace "I've been waiting kuma baka kira ba Mujaheed"
Mujaheed ya d'an kalli sama sannan yace "I said later not now
Safeenah" cikin rawar murya Safeenah tace "Don Allah ka kira Mujaheed
I am waiting" yyi shiru kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Ohk
let chat" Safeenah tace "Nooo don kira nake so" Yace
"Alryt, I will call later when am outside" mikewa imaan tayi daga
inda take ta wuce sama ba tare da ta kallesa, bin ta yyi da kallo da mugun
mamaki har ta haura sama, ya katse wayar ya ajiye saman kujera. Imaan na shiga
daki ta sa makulli ta cire ta ajiye gaban mirror ta xauna gefen gado, wasu
hawaye ne suka dinga sakko mata ba tare da ta sani ba kawai jin saukansu tayi,
lkci daya ta fashe da kuka a hankali ta kife kanta da pillow tana jin xuciyarta
na mata xafi, murda kofar dakin taji yyi ta mike xaune da sauri tana goge
idonta, yace "Imaan" tace "Na'am" yace "Open the door"
tace "I want to take my bath" shiru ya d'an yi sai kuma a hankali
yace "Ohk" komawa tayi ta kwanta, har dare bata fito daga dakin ba,
bayan ta idar da sllhn Isha ta shiga bathroom tayi wanka ta fito dare da towel,
ta gansa tsaye bakin kofar bathroom din, turo baki tayi xata koma ya rikota da
sauri, kamar xata yi kuka ta duka tace "Wayyo Yaya ban sa kaya ba stop
it" ya dagota yace "Why did you close the door?" Ta marairaice
tace "Saboda Ina son in yi bacci, gashi har na tashi" kallonta ya
dinga yi, ta turo baki xata juya ya fixge towel din jikinta, rungumesa tayi da
sauri tana xaro ido tace "Nashiga uku Yaya" ya lumshe ido laying her
down on the bed. Karfe dayan dare Imaan ta farka ta daga kanta a hankali tana
kallon Mujaheed, xame jikinta tayi daga nasa ta sauka saman gadon ta dau hijab
dinta ta saka ta nufi kofa a hnki ta bude tana kallonsa ganin bai motsa ba ta
fita, parlonsa ta nufa ta bude kofar ta shiga ta kunna wuta tana kalle kallen
inda xata ga wayarsa, ta karasa cikin daki ta ga wayar kan gado ta dauka,
missed calls din Safeenah ta gani har hudu da text message, ko bude text din
bata yi ba tayi dialing number ta ta kai kunne, ringing daya kawai yyi Safeenah
ta daga...
So sorry for the late update pls.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
*Albishirinku 'yan uwa*
Shin ko kun San zaku iya magance mafi yawan cututtukan da
suka addabi al'umma yanzu cikin sauki?
Sinadarin _Stemcell total care_ yayi fice wajen magance
matsalolin diabetes, BP, asthma, sickler, cancer, stroke, rashin haihuwa,
fibroid, infection da duk wata matsala da ta danganci lafiyar Al'umma.
Ba wannan kadai ba, akwai coffee na double root Wanda ke
inganta duk wani abu da ya shafi rayuwar
aure ga maza da Mata, inganta qwayoyin haihuwa da dai sauransu.
Akwai sinadarin rage tumbi da dai sauransu.
*Domin neman qarin bayani ku tuntubi wannan lambar
07068136856*
Sai an gwada akan san na kwarai.
101.....
Cikin rauni Safeenah tace "Haba Mujaheed, why don't you
want to listen to me? Why ain't you picking my call bayan kuma kace xaka kira
baka kira ba, you don't know why I am....." Imaan dake sauraronta ta katse
tace "Ke dakata... What business do you have with my husband again?"
Shiru Safeenah tayi jin muryarta, a mugun fusace tace "Uban me yasa xa ki
daga wayata, ke na kira da xa ki daga min wayar mijina?" Imaan tayi wani
dariya tace "Ehh lallai yanxu na sake confirming cewar ke babbar mahaukaciya
ce, kuma kinyi mugun nisa a hauka, shi Mujaheed din ne mijin ki??" Dariya
Imaan ta kara yi sannan tace "Toh bari ki ji in gaya maki, ko a mafarki da
kyar ki ga Mujaheed a matsayin mijin ki, Mujaheed yyi maki nisa sosai, sai dai
ki ajiye a tarihi kin ta6a auren Mujaheed, and let me drop u this last warning,
keep from my husband Safeenah kike ko wa?? Wllh ki fita hanyar mijina, even by
mistake kada ki sake kiransa don bashi da wani alaka da gantalalla mai tunanin
dabbobi irin ki, tun ban nuna maki wacece ni ba maza maza ki goge number mijina
daga shegen wayar, wahalalliya kawai mara xuciya, dama can mijin aro kika aura
sai a ci gaba da zawarci kuma...." Safeenah bata yadda hawayen da ke sakko
mata ya hanata fashewa da dariya ba tace "Ai kuwa ni ke da alaka da
mujaheed fiye da kowa... don kuwa a yanxu haka ina dauke da cikin d'an sa ko
yar sa, kin gane abinda nake nufi or you need more elaboration?" Imaan da
taji wani diff ta bude ido sosai jin abinda tace, shock da taji bai hanata cewa
"Ki nemo uban cikinbki amma ba mijina ba, karya kike wllh banxa kawai
jahila, ke da Mujaheed bari in sake gaya maki wllh sai dai hange, shi ma daga
nesa nesa, Allah ubangiji ya raba sa hada xuri'a da watsatsun tambadaddun
family irin naku, duk sharrin ku da kulle kullen ku kuma a kan ku xai kare, xan
ga kuma ta inda xa ki sake kiran mijina jaka kawai mahaukaciya" daga haka
Imaan ta katse kiran ta danna mata block ta kunna data ta hau WhatsApp can ma
ta danna mata block sannan ta goge lambarta gaba daya a wayar tana huci, xata
ajiye wayar ta ji muryar Mujaheed a bayanta yace "Toh sannu! give me my
phone" ta bude ido sosai sai dai bata juyo ba, yace "I said give me
my phone Imaan" lkci daya ta juyo fuska a murtuke tana kallonsa tace
"Baxan bayar ba, or do you have any business with the useless lady da xata
dinga kiran ka a waya kana biye mata, har ta cancanci ka sake daga kiranta
bayan abinda tayi ma mahaifiyar ka?? Ko har ka mance ne? Or is it because you
didn't watch the scene? To ba ruwana wllh baxan yadda ba, kuma xan gaya ka da
Abba...." karasawa yyi xai dau wayarsa ta dauke a fusace ta fice daga
dakin kamar xata tashi sama ya bi ta da kallo, Imaan na komawa dakinta ta ji
wani takaicin da bata san lkcn da ta fashe da kuka ba, ta rufe fuskarta da
pillow, Lkci daya tayi tsit ta daure fuska jin budewar kofa, muryarsa taji yace
"But did you know u just shouted at me Imaan?" Banxa tayi masa bata
dago ba, ya karasa kan gadon yace "Imaan" tashi tayi a fusace xata
bar wajen ya fixgota, ta fara buge hannunsa tace "Ni ka kyaleni, leave me
alone" ya matse ta jikinsa yace "Listen to me now, bana son kina min
magana haka, you don't know why I answered her call and I don't think you have
the right to call her, sure Safeenah raised her hands on my mum amma na
tabbatar wannan kuskure ne kin kuma san irin xuciya ta Imaan, i don't keep
anybody in mind..." Katse sa imaan tayi tace "Ehh nasan kalan xuciyar
ka amma ban san kalan yanda ka ba ma addinin ka muhimmanci ba, ban san irin
fahimtar da ka ma addinin ka ba, ban san ko kasan illar tarayyar ka da mahaukaciyar
ba tunda dama ita nasan jahila ce ba sani tayi ba" yyi gripping dinta da
karfi yace "Ke xaki koyar da ni addini na? Do you have to? Are you
thinking kin fini sanin addini ne? Safeenah is carrying my child so I have to
listen to her no matter what, it's my responsibility or ain't you aware of that
religious lady?" kasa cewa komai Imaan tayi tana kallonsa ko kiftawa babu,
ya saketa yana kallon wani direction din, can ya juyo ya jawota xata kwace
kanta ya kankameta giving her a romantic kiss all over her neck, wasu hawaye
suka dinga sakko mata tana son kwacewa amma ba rikon wasa yyi mata ba, murya
can kasa yace "I have to listen to her for the Kamar daxu hot romance ya
shiga mata amma wannan karan she didn't even respond, bata kuma sake jiki ba,
har lkcn kuma hawaye take har da shessheka, hakan yasa ya kyaleta yyi
kwanciyarsa ya juya mata baya, tun bayan aurenta da Mujaheed yau shine karo na
biyu da Sadeeq ya fado mata, tasan Sadeeq baxai ta6a mata haka ba, he will
never, dama kuma Mujaheed ai bai ce yana sonta ba kawai aura masa ita aka yi,
dole ya nuna mata muhimmanci Safeenah gareta, tunanin hakan yasa ta fashe da
kuka sosai shi dai bai ce mata komai ba. Daren ranan gaba daya Imaan ta kasa
bacci, karfe biyu saura ta mike ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito ta
fara sllh, sai uku saura taji bacci ya fara damunta tayi kwanciyarta nan saman
darduman, haka yasa Mujaheed ya mike ya kashe Ac dake aiki a dakin ya koma yyi
kwanciyarsa, daga nan kuma bacci ya dauketa. Da asuba bude kofar dakin da yyi
ya farkar da ita, tana ji ya koma dakinsa bayan wani lkci ya fito ya wuce
masallaci. ko da ya dawo sllh ya tadda ta tana yi, ya xauna gefen gado har ta
idar, ta mike ta dauka qur'ani ta koma kan darduman ta xauna, duk yana bin ta
da kallo ta gefen ido, ta fara karatun ta, bayan wani lkci ya mike ya fice daga
dakin. Sai da gari ya fara washewa Imaan ta mike ta ajiye qur'ani ta dauke
darduma ta fita dakin a hankali, bude kofar parlonsa tayi making sure bata yi
making sound ba ta karasa kofar dakinsa da bai rufe ba gaba daya ta tsaya, waya
ta ji yana yi calmly, sosai gabanta ya fadi tana sauraren abinda yake cewa,
"What did you mean Safeenah, sure i will take care of you, I will take
care of my child u are carrying, after that ba wani abu kuma..." Abinda
Imaan taji ya fada kenan, da mamaki ta ji yace "Auren kisan wuta kuma??
Did you even know what you are saying?" Imaan taji gabanta yyi mugun
faduwa taji ta ma kasa tsayuwa bakin kofar, mikewa mujaheed yyi yana kallon
kofar jin motsi da sauri ta matsa ta jingina da bango, ya karaso bakin kofar ya
bude suka yi ido hudu ta wani daure fuska, yace "We will talk later"
daga haka ya katse wayar yana kallonta yace "Why do you derive joy
intruding in my affairs imaan? gari ya waye common ki bude baki ki gaida mijin
ki baki iya ba amma kin iya kishi da saka masa ido, do you have any problem?
Meye amfanin kishin naki?" Kallonsa kawai Imaan take bbu ko kiftawa, yace
"Bana son kina saka min ido a abinda nake yi, and I don't think it's
necessary ki dinga shigo min nan da safe ba gaisheni kika xo yi ba..."
juyawa imaan tayi ta nufi kofa ta fice daga parlon ta wuce dakinta, ita kanta
tayi mugun mamakin yanda ta dake xuciyarta, ta cire kayan jikinta ta tafi
bathroom kawai ta wanke baki ta hada ruwan wanka tayi ta daura towel ta wanke
bandakin ta fito, sai bayan da ta gama shiryawa ta feshe jikinta da turare
sannan ta gyara dakinta ta kunna turaren wuta. Tana goge goge a parlor Mujaheed
ya sakko cikin shiri sai xuba kamshi yake, yana kallonta yace "What will
you take for breakfast Imaan?" Ba tare da ta kallesa ba tace "I will
sort that out" kofa ya nufa ta bi sa da kallon gefen ido har ya fita gidan
ta ji fitar motarsa gaba daya. Sai a sannan wasu hawaye suka dinga sakko mata
ta dinga jin wani xafi a ranta, tayi kukanta mai isarta ta gama goge gogen da
take ta wuce sama ta kwanta, har sha daya bata fito daki ba balle ta nemi
abinda xata ci gaba daya taji yunwar ma bata ji. Da rana tana kitchen ta na
dafa indomie ta ji shigowar motarsa gidan, tana ji ya shigo parlor sannan ya
karaso kitchen jin kamshin dahuwar da take yi, yana tsaye bakin kofar yana
kallonta daga sama har kasa don skirt ne karami jikinta sai riga yace "Kin
yi breakfast din?" Tace "Nayi" yace "Ohk ga lunch na kawo
maki and you are cooking, amarya bata girki ai" Bata ce komai ba ya juya ya
fita, har ta fito daga kitchen yana xaune parlor, ta wuce sama rike da plate
din abincinta, kasa cin indomie din ta yi ta sha five alive da ta debo kadan ta
tura abincin gefe tana jin wani xafi da xuciyarta ke yi mata, bayan wani lkci
ta mike ta fitar da plate din har lkcn yana parlor xaune ya bi ta da kallo ta
shiga kitchen ta fito ta koma sama, bata kuma sake fitowa ba har Magrib. Bayan
Isha tana tsaye gaban press sanye da hijab har kasa xata fito da kayan bacci da
xata sa Mujaheed ya shigo dakin, ko kallon direction dinsa bata yi ba ta ci
gaba da ciro sleeping dress dinta, ya kulle kofa ya karaso ya ajiye ledan
hannunsa yace "Ga abinci" shiru bata ce masa komai ba ya isa bayanta
ya jawota jikinsa murya can kasa yace "Ni kike sharewa ko??" Bai jira
cewarta ba ya fara daga hijab dinta to gain access to her body, a fusace tace
"Stop it Yaya" juyo da ita yyi ya fara kissing dinta gently yana daga
hijab din, ta fara turasa amma ya ki sakinta, sun dau lkci sosai a haka amma
gaba daya ta ki sakar masa jiki sai kukan take masa tana son kwace kanta, ya
saketa daga karshe ya mike ya xauna gefen gado da idanuwansa da suka sauya
kala, sauka take son yi daga saman gadon ya fixgota yace "You are only
good at show casing unnecessary kishi, to warce kike kishi a kanta 6ata ta6a
hana ni hakkina ba, ko da kuwa sau goma ne a rana.. I know what I am
saying" Imaan tace "Sai kaje ta baka yanxu ai" daga haka ta nufi
kofa ya bi ta da kallo har ta fice daga dakin, sannan ya gyada kai. Washegari
gaba daya Mujaheed bai shigo dakinta ba yanda ya saba da safe, ita dai ta gama
duk abinda take, ta fita xuwa kitchen ta hada shayi ta dawo parlor ta xauna,
sakkowa yyi downstairs kasancewar ranan Friday ne sanye yake cikin milk shadda
da yyi masa kyau sosai, tun da ta kallesa sau daya ta dauke kai, ya shigo
parlon ya dau makullin motarsa yana kallonta don har snn kayan bacci ne jikinta
yace "Sai yanxu kika tashi kenan?" Ba tare da ta kallesa ba tace
"Ehh" yace "Ohk, xan je gida sai na dawo after Juma'at prayer"
tace "Nima xan je gida" yace "A'a ki jira next week xan kai
ki" ta wani hade rai ta kallesa, yyi murmushi yana shafa kansa ya dawo
kusa da ita ya xauna yana kallon fresh legs dinta don kayan iyakar sa kneels
yace "In sha Allah next week xa ki je ae" Bata ce komai ba ya amshi
shayin hannunta ya jawota jikinsa ta fixge ta matsa daga wajen ta dau cup din
shayin ta, mikewa yyi ya nufi kofa ta bi sa da kallo, lkci daya ya juyo tayi
saurin dauke kanta, yace "What will you be taking for lunch?" Ba tare
da ta kallesa ba yace "I will sort that out" dawowa parlon yyi ya
ajiye makullin hannunsa da waya ya koma sama, ta bi sa da kallo gefen ido, sai
da taji budewar kofar parlonsa sannan ta mike da sauri ta dau wayarsa ta ga ya
sa lock, kallon wayar ta dinga yi da mamaki kafin ta kashe ta ajiye ta koma da
sauri ta xauna, ya sauko downstairs rike da Atm card dinsa ya dau waya da
makulli ya nufi kofa yace "Sai na dawo" Bata ce komai ba har ya fita,
ta ajiye shayin hannunta don gaba daya ji tayi ya fita ranta, imagining ta
dinga yi wai gun Safeenah xai je, lkci daya taji hawaye ya kawo idonta ta
jinginar da kanta da kujera tana jin xafi a xuciyarta. Sai kusan la'asar
Mujaheed ya dawo gidan, sai bayan kusan minti talatin ya shiga dakinta ya ganta
kwance idonta rufe ya karasa kusa da ita ya xauna yana shafa fuskarta a hankali
yace "Lil sis" kin bude ido tayi yyi murmushi don yasan ba bacci take
ba, ya kai lips dinsa nata ta bude ido da sauri ta dauke kai, shafa cikinta yyi
yace "Ga abinci Inna ta bada a a kawo maki downstairs" ta mike xaune
ta koma can karshen gado on a serious note tace "Bana son kana ta6a ni
Yaya, I don't like it" shiru yyi yana kallonta, can yace "Kar na ta6a
ki sbda me?" A takaice tace "Saboda bana so" yace
"Ohk" daga haka ya nufi kofa yace "Farida ta kira daxu tana
gaishe ki" daga haka ya fita ta bi sa da harara, sai kuma ta 6ata fuska
xata yi kuka. Haka nan suka ci gaba da rayuwa gidan da gaske kuma ya daina ta6a
ta iyaka ya siyo mata abinci da drinks ya ajiye mata, wani lkcn ya hada da
gasasshen kaza wani lkcn kuma fruits, a ko da yaushe tana daki ita kadai, shi
kuma yawanci yana parlonsa, duk dare dai xai shigo to make sure ta sha drugs
dinta sannan ya wuce dakinsa yyi kwanciyarsa. A haka har yayi resuming aiki
ranan Monday, karfe takwas saura ya shigo daki ya ganta kwance tana bacci sbda
dadewa da tayi tana azkar bayan sllhn asuba, ya isa gabanta yana kallon skin
dinta dake wani sheki, ya durkusa kusa da ita, ya fi minti biyu yana kallonta
kafin a hankali yace "Imaan" Bude ido tayi, sai kuma ta mike xaune ta
koma baya, ya mike yace "Xan wuce aiki, akwai kayan shayi downstairs with
bread, I don't know ko xa ki ci egg ki soya yanxu kafin in tafi" ta
girgixa kai tace "Baxan ci ba" yace "Ohk..." Daya wayarsa
ya mika mata yace "If you need anything you call me, but don't call
anybody with the phone" tace "Ni dai xan kira Ammi na" juyawa
yyi ya fita dakin ya kulle mata kofa. Sai kusan karfe hudu da rabi ya dawo
gidan yana haurawa sama ya bude dakinta daga kai tayi ta kallesa daga xaunen da
tayi gaban mirror tana tsefe kitson kanta, yace "Kin ci abinci kuwa?"
Ta ci gaba da abinda take tace "Na ci" yace "Me kika ci?"
Tace "Ni dai na ci" yace "Gobe xa a kawo maki house maid sai ki
dinga monitoring dinta tana girki" ta kallesa tace "A'a bana so, xan
iya" yace "Ai ba ni na fada ba, daddy ne ya fada" daga haka ya
fita dakin nata. Ta gama tsefe gashinta ta dau abubuwan wanke gashi ta shiga
bandaki ta wanke gashin nata sannan ta fito ta busar. Kwanciya tayi saman gado
maganganun da Ammi tayi mata daxu ya dinga dawo mata, ji tayi kamar ta fashe da
kuka tunawa da tayi Ammi fa ce mata tayi bbu ruwanta dole yana da hakkin kula
da Safeenah da cikin da tace tana da shi, ita ko kadan bata yadda Safeenah na
da ciki ba ta rasa dalili, gashi duk hanyar da xata san ko suna waya ynxu bbu
don tun ranan bata sake shiga dakinsa ba. Bayan isha Mujaheed na dawowa
masallaci ya shigo bedroom dinta da ledan abinci, kamar ko da yaushe a dai dai
wannan lkcn yau ma ta fito wanka ne, da sauri ta koma bathroom, ya ajiye mata
ledan abincin ya fita dakin, ta gama shirin kwanciyarta har ta kwanta sai kuma
ta mike ta dau ledan ta fita da shi, xaune ta gansa parlor ya bi ta da kallo
ganin kitchen xata shiga yace "Kin ci abincin?" Tace "Am not
hungry" mikewa yyi ya bi bayanta, ta ajiye ledan xata juyo suka kusa cin karo,
komawa baya tayi da sauri ya dau ledan da plate sai cup ya kamo hannunta yace
"You must eat, baxa ki kwanta haka ba" da mamaki tace "Ka ta6a
ce min I must eat a gidan nan?" Bai tanka ta ba ya xaunar da ita ya debar
mata abincin ya ajiye mata sannan ya xuba mata drink din ya ajiye yace "ki
cinye yanxun nan Ina kallon ki" da mamaki take kallonsa, can tace "Ni
dai nace maka na koshi" yace "I am not joking imaan, ki ci abincin
nan ko kuma ki sha drink" shiru tayi tana kallonsa, can ta turo baki ta
dau spoon ta fara cin abincin yana kallonta ko kiftawa bbu, da kyar take
hadiyewa daga karshe ta ajiye cokalin ta mike tace "Ni dai na koshi"
rikota yyi yace "Drink din fa?" ta xaro ido tace "Ni bana shan
drink da daddare" ya hade rai yace "Take it now Imaan" dariya ya
bata ganin how serious he is tace "Ni ka ta6a ganin na sha drink da
daddare haka?" Yace "Ehh ki sha ko kadan ne" kamar xata yi kuka
tace "Ni Yaya fa baxan iya Sha ba" ya dauka cup din ya kai five alive
din bakinta yace "Bude bakin my friend" karba tayi a hannunsa kamar xata
yi kuka ta kai bakinta ta fara sha, ya dinga kallonta har tayi rabi sannan ya
saketa ya mike yyi wucewarsa sama ta bi sa da kallo ta ajiye sauran drink din.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
*Albishirinku 'yan uwa*
Shin ko kun San zaku iya magance mafi yawan cututtukan da
suka addabi al'umma yanzu cikin sauki?
Sinadarin _Stemcell total care_ yayi fice wajen magance
matsalolin diabetes, BP, asthma, sickler, cancer, stroke, rashin haihuwa,
fibroid, infection da duk wata matsala da ta danganci lafiyar Al'umma.
Ba wannan kadai ba, akwai coffee na double root Wanda ke
inganta duk wani abu da ya shafi rayuwar
aure ga maza da Mata, inganta qwayoyin haihuwa da dai sauransu.
Akwai sinadarin rage tumbi da dai sauransu.
*Domin neman qarin bayani ku tuntubi wannan lambar
07068136856*
Sai an gwada akan san na kwarai.
102....
Tun da Imaan ta koma daki ta kwanta ta ji ta very restless,
gaba daya ta rasa takamaiman abinda ke damunta, ta dinga juye juye kan gado,
can ta mike xaune, a hankali ta xamo kasa daga kan gadon ta durkusa ta kife
kanta da gadon, ta fi minti ashirin a haka aka bude kofar dakin Mujaheed ya
shigo rike da goran ruwa da drugs dinta, kallo daya yyi mata ya dauke kai ya
karaso kusa da ita yace "Yau kuma haka xa ki kwanta" k'in cewa komai
tayi kuma bata dago ba ya dagota ya juyo da ita yana kallonta ganin hawaye idonta
da damuwa yace "Subhanallah me ya faru?" Bata ce komai ba ya kwantar
da ita saman gadon yace "Ko kafarki ke ciwo?" ita dai bata ce komai
ba ya mike ya dauko man shafanta na kafa ya kashe wutan dakin ya bar mara haske
ya fara shafa mata, lumshe ido tayi, hakan yasa yyi murmushi yana kallonta,
Bayan wani lkci ya kai bakinsa fuskarta yace "Bayan ma yana maki
ciwo?" Bata bude masa ido ba ta gyada masa kai, juyar da ita yyi ya sauke
wear dinta kasa ya fara shafa mata lotion din a bayanta, ya jima yana massaging
back dinta gently sannan ya juyo ta yana kallonta yace "Yayi sauki
koh?" Ta bude idonta a hankali tana kallonsa, ya sakar mata murmushi ya ja
dogon hancinta yace "Sleep tight dear, sai da safe" xai mike kawai ya
ji ta jawosa sai kuma ta fashe da kuka, ya wara ido yace "what
happened?" Ta mike xaune ta rungumesa tana shessheka, ya lumshe idonsa
murya can kasa yace "Ki gaya min menene?" Shiru bata ce komai ba yana
jin yanda take sauke numfashi a hankali, kamshin gashinta duk ya cika sa, ya
janyeta jikinsa yace "Xan kwanta, I have work tomorrow" kin sake sa
tayi tana kara shigewa jikinsa, and that really turned him on duk da yanda ya
so ya share even for sometimes, lkci daya ya fara bi da ita gently kuma
romantically, ko kadan bai yi mamakin martanin da ta dinga mayar masa ba, ta
basa hadin kai 100% ba raki ba komai, daga karshe ma shi ya rikice mata, and
that nyt will forever remain in his memory... Can karfe biyu Imaan ta farka ta
dalilin kanta da ke ciwo sosai, ta janye daga kusa da shi a hankali ta mike
xaune tana kallonsa tana rufe kanta da duvet, lkci daya ta ji kunya ba na wasa
ba ya rufeta, maganganunsa suka dinga dawo mata da daddaya da daddaya, kallonsa
kawai take ko kiftawa bbu, kawai gani tayi ya jawota ya kankameta ya kai
bakinsa kunnenta yace "Why are you staring at me wife" rufe idonta
tayi da sauri ta boye fuska jikinsa kamar yana ganinta, yyi murmushi yana shafa
gashinta, a haka bacci ya kara dauketa. Tun da Mujaheed ya dawo masallaci yake
bacci a bedroom dinsa, Imaan ta fito kitchen bayan ta juye ruwan xafi flask,
tana kallon agogo ganin bakwai ya wuce ta wuce sama, ta fi minti biyar tsaye
bakin kofar parlonsa sannan ta bude a hankali ta shiga ta wuce bedroom dinsa,
bata gansa dakin ba amma jin saukan ruwa ta gane yana wanka, ta nufi gaban madubi
ganin envelope ta bude envelope din ta leka ciki sannan ta ciro takardan,
warwarewa tayi tana duba content din, Takardar scan ne dauke da sunan Safeenah,
sosai gaban Imaan ya fadi ta dinga kallon takardan dai dai nan Mujaheed ya fito
bathroom, ta madubi ta kallesa ta sunkuyar da kai da sauri, ya karasa bayanta
ya tsaya ya kwanto ta jikinsa a hankali yace "Wife..." Bata dago
kanta ba ya juyo da ita yana kallonta yace "Ko xa ki rakani office
yau?" Ta girgixa kai kawai, ya dau takardan ta linke ya mayar cikin
envelope din yace "Toh fito min da kayan da xan sa" Shiru tayi bata
ce komai ba ya dago kanta yace "Kin
ji?" Tace "Ai ban san gun kayan ba" nuna mata yyi ta tafi gun
press din ta bude, a gabanta ya saka kayan bai bari ta fita ba kamar yanda tayi
niyya, yana saka safa kafarsa yace "Kin ga yau kin sa na makara" Ta
d'an turo baki tace "Ni kuma?" Yyi mata slight kiss a lips yana rike
da hannunta yace "Ehh mana lil sis..." Sunkuyar da kanta tayi ya mike
ya dagota yace "What are you taking for breakfast?" Tace "Anjima
xan dafa indomie" yace "Ohk, mu je ki rakani gun mota xan dawo in sha
Allah da karfe 12 in ga wife dita sai in koma karfe daya..." tace
"Breakfast fa?" Yace "Xan yi a office dear" ta turo baki
tace "Na fa dafa maka ruwan xafi kuma akwai bread" ya wara ido yace
"Da gaske?" Ta gyada masa kai yace "Toh mu je inyi breakfast
din" suna isa dinning tace "Or should I fry you egg?" Yace
"Xa ki iya?" Tace "Uhm" a tare suka tafi kitchen din yana
tsaye bayanta ta gama soya eggs din ta kashe gas, ya juyo da ita ya daura
forehead dinsa kan nata a hankali yace "Plss ki dinga min haka Imaan, wllh
I want to be with you till eternity, baki San yanda nake ji dake ba ko kanwata?
Ki daina bani wahala haka, one day you will know what I mean" Ko kadan
abinda ya fada bai burge Imaan ba, Wai he just want to be with her, shi dai
kawai so yake ya kasance da ita and nothing more, ta sauke idonta da ya kawo
hawaye ya rungumeta ta tayi lamo jikinsa tana jin kamshinsa, lumshe ido yyi
yana jin wani irin sonta da sha'awarta na daban, wanda dai dai da second daya
bai ta6a jin sha'awar Safeenah ba sai in ita ta kawo kanta, tare suka yi
breakfast din duk da bata wani ci da yawa ba ta rakasa har bakin mota kamar
yanda ya bukata sannan ta koma ciki bayan ta kulle gidan, dakinta ta wuce ta
kwanta lkci daya baccin da bai isheta ba ya dauketa. Karfe sha daya ta farka,
babu 6ata lkci tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga na material, ta feshe
jikinta da turare tana gyara gadonta taji an bude kofar dakin, a tsorace ta
dago ganinsa ta turo baki ta xauna kamar xata yi kuka tace "Yaya ka bani
tsoro" ya karaso cikin dakin yana murmushi ya cire necktie dinsa ya nufeta
yace "Tsoro kuma sai kace ba takwarar Inna ba baby?" Turo baki tayi
ya xauna kusa da ita yyi mata side hug yana murmushi yana kallonta murya can
kasa yace "Kin yi kyau sosai wife, did you know I have been thinking about
yesterday throughout yau a office" Bata yarda ta kallesa ba kuma bata ce
komai ba, ya kai bakinsa kunnenta yace "Gaya min wa ya koya maki in masa
kyauta" boye fuskarta tayi shoulder dinsa cike da shagwaba tace "Ni
bana so fa Yaya" kwantar da ita yyi saman gadon ya kwanta shi ma yace
"Ae kuwa xa ki so ynxun nan" sai kusan karfe uku Mujaheed ya bar
gidan ya koma office Imaan na bacci bayan ya ajiye mata lunch a daki. Kiran
la'asar ya farkar da ita ta bude ido a hnkli ta kalli gefenta ta mike xaune
ganin bata gansa ba, farin takardan da ta gani gefen pillow ta dauka ta warware
taga rubutunsa kamar haka "God bless you dear, sai na dawo anjima, I
care..." Turo baki tayi ta ajiye takardan tana jin bayanta na d'an mata
ciwo ta sauka daga kan gadon ta wuce bathroom. Da Mujaheed ya tashi dawowa
around 5 na yamma da waya irin wanda Sadeeq ya ta6a siya ma Maryam ya shigo
gidan, tana kitchen ta gama blending kayan miya ta ji shigowarsa gidan, leka
parlor tayi suka yi ido hudu ya buda mata hannu yana murmushi, ta make masa
kafada ta, a hankali yace "Toh shikenan" daga haka ya wuce sama ta bi
sa da ido, ta gama fiddo nama a deep freezer sannan ta fito ta wuce sama, a
hankali ta bude kofar parlonsa yanda baxai ji ba ta shiga ta karasa bedroom
dinsa don a bude kofar yake, button din rigarsa ta samesa yana cirewa ta karasa
dakin ta kwanta bayansa ta lumshe ido murya can kasa tace "Wlcm" ya
juya da ita drawing her closer to him, girkin da bata karasa a lkcn ba kenan ta
biye ma Mujaheed. Tana xaune saman darduma tana kallonsa bayan sun idar da
sllhn Magrib, ya mike yace "Let go out and get something to eat" Tace
"Ae yanxu xan yi girkin" yace "Noo I don't want to stress you
anymore, mu tafi mu siya a eatry" Bata ce komai ba ya kama hannunta ta
mike ya dauke darduman ya ajiye, ledan da ya shigo da shi daxu ya dauko mata ya
kama hannunta ya mika mata yana kallonta, ta dinga kallon ledan sannan ta bude,
lkci daya ta wara ido ta rungumesa gam tace "Waow nagode Yayana, thank you
very much" ya lumshe ido yace "You are welcm sweet" ta turo baki
ta 6ata rai tace "Ni dai ka daina ce min sweet bana so" yace
"Ohh daxu da na gaya maki kin xata wasa nake ba sweet xan dinga kiran ki
ba" ta make kafada tace "Ni bana so" ya dauketa Kamar yar baby
yace "Toh sai ince maki Zuma" dariya tayi ta rikesa gam tace "Ni
dai bana so" yyi kissing hancinta ya ajiyeta yace "Toh mu je idan mun
dawo sai ki bude wayar" daga haka ya dau makullin motarsa ya kamata suka
fita dakin. Lafiyayyen abinci ya siya masu da gasasshen kaji, suna dawowa
wayarsa dake ajiye kusa da shi a mota ya fara ring, a tare suka kalli screen
din, a hankali Imaan ta dauke kai ganin sunan Safeenah a screen din. Bayan few
seconds yyi Picking call din ya sa handsfree ya ajiye yayi sallama, maimakon ta
amsa murya can kasa tace "Dr wllh kaza nake son ci, tun safe nake ta amai
bani da appetite na komai, yanxu kuma naji ina son cin kaza pls idan ban takura
ka ba" Mujaheed yace "Ohk" tace "Kazar gida nake so fa kuma
a lafta min yaji plss" yace "Alryt" tace "Sai ka hado min
da Hollandia milk with shawarma kila in ci" yace "Naji" daga
haka ya katse wayar. Ya kalli Imaan dake kallon window yace "Sweet let get
her what she want before going home" shiru tayi masa bata ce komai ba, ya
kamo hannunta a hnkli, sae a sannan tace "Ohk" duk sai da Mujaheed ya
siya ma Safeenah abubuwan da ta lissafa masa sannan ya tafi gidansu, yana isa
kofar gida ya kira wayarta, bayan ta daga yace "I am outside ki turo a
amsar maki kayan" ya ajiye wayar yana kallon Imaan da ta jinginar da kanta
da kujera, Bude gate aka yi sai ga Safeenah ta fito daga gidan sanye da hijab
har kasa, kallonta imaan ta dinga yi ta jikin glass sbda hasken fitulu ne ta ko
Ina a kofar gidan nasu, ba karamin ramewa tayi ba sai idanuwa, Mujaheed na
ganin ta fito ya bude motar xai fita ita kuma ta bude side din Imaan suka yi
ido hudu, da sauri Safeenah ta juya coz bata ta6a tunanin tare suke ba, Imaan
kuma ta dauke kai, Mujaheed ya xaga ya mika mata ledan hannunsa yace "How
are you feeling?" Ta amsa ta gaishe sa a hankali, yace "Allah ya kara
lafiya, sai da safe" daga haka ya xaga ya bude front seat ya shiga ya ja
motar ta bi sa da kallo. Gaba daya daren ranan Mujaheed bai gane kan Imaan ba,
abincin ma ta ki ci, ta ki yarda kuma ya ta6a ta, a haka ya kyaleta yyi
kwanciyarsa amma ya kasa bacci, can cikin dare bayan tayi bacci ya jawota
jikinsa ya rungume, a haka ya samu yyi bacci. Sai da ta dau kusan sati taki
sake masa taki yarda ya ta6a ta, duk ya daga hankalinsa ba kadan ba don just
for two days da suka yi tare ta basa hadin kai ya ji baxai ta6a iya nisantarta
ba, mamakin irin kishinta yake it's just too much, bai san ana kishi haka ba
don ko lkcn da Safeenah take kishi da Imaan tun bata ma san xai aureta ba da ya
fara aika mata sakkoni shkkn sai kuma wani lkcn, haka nan bai gaji ba ya dinga
lallabata don Imaan na da baiwar da ba ko wace mace ke da shi ba, she's totally
different from a lot... Tana linke hijab bayan ta idar da la'asar ya shigo
dakin, dawowarsa aiki kenan, ta dauke kai ta ajiye darduman, kamota yyi cikin
lallami ya marairaice mata yace "Haba imaan, why are you doing this to
me?" Ta hade rai tace "Me na yi?" Ya xaunar da ita gefen gado ya
xauna yace "Don Allah kiyi hakuri, me yasa xa ki dinga kishi da Safeenah that's
not my wife, she's not my wife any longer, kuma babu aure tsakanina da ita,
it's just my responsibility to take care of her and her baby har ta haihu, so
kike Allah yayi fushi da ni sweet?" Imaan ta fashe da kuka tace "Toh
dole sai ka dinga xuwa wajenta, tayi ta gilla ma karya xata ci wannan xata ci
wancan duk don kaje ta dinga ganin ka" Sosai ta basa dariya ya rungumeta
sosai yace "Toh daga yanxu baxan sake xuwa in je ta gan ni ba I promise
you, if she need anything xan bada a kai mata in sha Allah, idan kuma ta haihu
sai mu amso babyn mu, shkkn bbu kuma abinda ya hada ni da ita" cikin rawar
murya tace "Ba wani nan ai ba tare muke fita kullum ba balle in san ko ka
je ko baka je ba, kuma ni nasan cikin karya...." Rufe bakinta yyi da nasa
ya lumshe ido, nan ya shiga lallashin lil sis din tasa yanda ya kamata. Kiran
sllhn Magrib yasa Mujaheed ya bude ido a hankali yana kallon Imaan da ta
makalkalesa, murmushi yyi yana shafa kanta ya kai bakinsa kunnenta murya can
kasa yace "It's time for prayer, sweet...." A hankali ta bude
idanuwanta tana kallonsa ta turo baki tace "Stop calling me sweet" ya
lumshe ido yace "Billah ke sweet dita ce" Ranan Saturday da safe har
Mujaheed ya gama abinda yake a laptop imaan bacci take duk da ko azkar bata yi
ba after subhi prayer ta koma baccin, ya kalli agogo ganin karfe goma saura ya
mike ya wuce dakinta, xaunawa yyi gefenta ya kai hannu fuskarta ta bude ido
tana kallonsa yace "Ni da kika hana bacci ban yi baccin safe har war haka
ba sai ke koh?" Ta turo baki ta mirgina ta mike xaune tana mitsika ido,
yyi murmushi yace "Xa mu fita yau fa, and I told you yesterday" a
hankali tace "Toh" ya mike ya fita dakin, cikin riga da skirt na
atamfa super imaan ta shirya ta shafa powder fuskarta sannan ta dau gogaggen
hijab dinta har kasa color din supern jikinta ta saka ta feshe jikinta da
turare tana yamutse fuska ta fita, shayi kawai ta sha bata ci bread ba,
Mujaheed da ya shirya cikin kananun kaya shi ma ya mike ya dau makullin motarsa
ya kama hannunta yace "Toh mu je" Sai da suka hau saman titi ya
kalleta yace "Zaria xa mu fara xuwa sai mu tafi can gida ko?" A
hankali tace "Toh" ko da wasa bai yarda imaan ta lura da takardan
scan din Safeenah da ya kai mota tun tuni ya ajiye inda baxa ta gani ba, har
suka kama hanyar Zaria bacci imaan take, ganin yanda ta takure gu daya ya kashe
ac din motar, suna isa gidan yyi parking a hankali ya ja hancinta cikin cool
voice dinsa yace "Sweet...." bude lumsassun idonta tayi ta kallesa,
ya dinga kallonta sannan yyi murmushi yace "Mun kawo..." ta fara kalle
kalle, ya sauka motar ba tare da ya dau envelope din ba ya xagayo ya bude mata
side dinta, sosai sisters dinsa dake gidan har lkcn basu koma kaduna ba suka ji
dadin ganinsa, babu wanda ya wani considering din Imaan sai Seeyama da ta xo
gidan ranan ita ma, Imaan ta xauna saman kujera ta sunkuyar da kanta bayan sun
gaisa da Seeyama, daga sama Umma ta sauka ta shigo parlon tana kallon Mujaheed
tace "Sannu da xuwa" yace "Yauwa sannu umma" Imaan ta sauko
kasa a hankali tace "Ina yini Umma" umma ta kalleta tace "Lafiya
lau ya gida?" Imaan bata dago ba still tace "Alhmdllh" Umma ta
kalli Mujaheed dake gaisheta shi ma ta amsa ta xauna tana tambayarsa ya aiki,
yace "Alhmdllh Umma, ya gida fa" tace "Lafiya lau, sannun ku da
xuwa" Seeyama ce ta mike ta wuce kitchen ta dauko masu ruwa da lemo, ita
kam har yau shiru ko 6ari bata yi ba, kana ganinta kasan tana tare da damuwa
sosai don duk ta rame, ta fito kitchen ta ajiye ma Mujaheed lemo da ruwan,
sannan ta kai ma Imaan nata, Imaan ta kalleta tace "Nagode" Seeyama
tayi murmushi ta tafi ta xauna. Mikewa Umma tayi ta wuce sama Mujaheed ya bi ta
da kallo, Ummi na kallon Seeyama tace "Aunty Seeyama mu je mu gama girkin
toh" mikewa Seeyama tayi ta bi bayanta xuwa kitchen, Rahma ma ta tafi ta
ci gaba da wanke wanken da take, sae a sannan ya mike ya tafi kitchen don cin
uban kannin nasa. Bacci imaan ta dinga ji amma ta ki kwanciya, ta dai jinginar
da kanta da kujera ta lumshe ido, bayan kusan minti biyar ta bude ido da sauri
jin abu na taso mata ta dalilin aroma dake fitowa daga kitchen, mikewa tayi ta
rufe bakinta ta rasa inda xata, Seeyama da fitowarta kenan tare da Mujaheed
tace "Subhanallah me ya faru" kofa Imaan ta nufa xata fita compound
kafin ta isa kofar aman ya taho mata, lkci daya ta xube wajen ta dinga kwarara
amai, Seeyama ta isa kusa da ita da sauri ta durkusa ta riketa tace "Sannu
Imaan, baki da lafiya ne?? Sannu" Mujaheed ya kasa karasawa ya tsaya yana
kallonta ganin umma dake sakkowa downstairs ita ma tana kallon imaan, Umma ta
karasa gun su tace "Subhanallah, Me ya faru Seeyama?" Cike da damuwa
Seeyama tace "Amai take yi" Umma na kallon Imaan tace
"Sannu" Kasa cewa komai Imaan tayi wani aman na taso mata, Umma ta
dagota sai ga shi ta fara kwararo wani aman, hakan yasa Mujaheed ya taho wajensu,
Seeyama ta tafi debo ruwa da sauri, Umma dai sannu kawai take mata, sai da aman
ya tsaya mata sannan Umma ta nufi sama da ita Mujaheed ya bi su da kallo.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
*Albishirinku 'yan uwa*
Shin ko kun San zaku iya magance mafi yawan cututtukan da
suka addabi al'umma yanzu cikin sauki?
Sinadarin _Stemcell total care_ yayi fice wajen magance
matsalolin diabetes, BP, asthma, sickler, cancer, stroke, rashin haihuwa,
fibroid, infection da duk wata matsala da ta danganci lafiyar Al'umma.
Ba wannan kadai ba, akwai coffee na double root Wanda ke
inganta duk wani abu da ya shafi rayuwar
aure ga maza da Mata, inganta qwayoyin haihuwa da dai sauransu.
Akwai sinadarin rage tumbi da dai sauransu.
*Domin neman qarin bayani ku tuntubi wannan lambar
07068136856*
Sai an gwada akan san na kwarai.
Where are those ladies with kwaikwaido hair??😆
To maxa ku garxayo Khaleesat ta sama maku wani oil da ku da
cute babies din ku mai shegen kyau da xai mayarshe ku indian's, it's tested and
trusted sisters sai kun xo.... Thanks
103....
Mujaheed na xaune gefen Imaan dake bacci a dakin Umma Seeyama
ta shigo dakin da abinci ta ajiye masa tace "Yaya ga abinci Umma tace a
kawo maka nan" Yace "Ohk thanks" ajiye abincin tayi tana kallon
Imaan tace "Ya jikin nata?" Yace "Alhmdllh, ya Mai gidan
ki?" Tace "Yana lafiya qlau" yace "That's good" juyawa
tayi ta fita dakin, Mujaheed ya juya ya kalli Imaan dake bacci ya kai hannunsa
forehead dinta a hankali yaji bbu xafi jikinta, ya dauke hannunsa sannan ya
bude daya daga warmer din abincin da Seeyama ta kawo, stew ne dake ta xuba
kamshi, Imaan ta bude ido ta mike da sauri tana rufe hancinta da kyar tace
"Yaya meye shi?" Murmushi yyi ya rufe miyar ya kalleta yace
"Sweet dita ce" Bata tanka sa ba ta koma can karshen gado ta kwanta a
hankali har sannan bata bude hancinta ba, a haka bacci ya kara dauketa ya mike
ya xaga kusa da ita ya duka a hankali ya janye hijab din daga fuskarta yana
kallonta ko kiftawa babu, murmushi yyi ya kai lips dinsa cheek dinta sannan ya
mike ya rage ac din dakin ya fita ya kullo mata kofar. Umma na parlor tare da
Seeyama dake cin abinci mujaheed ya shigo, Umma ta kallesa tace "Ya jikin
nata?" Yace "Da sauki bacci take" Umma tace "Toh Allah ya
sauwake, har ka ci abincin ne?" Yace "Idan nayi sllh xan ci
Umma" ta kalli agogo tace "Ohk it's almost time" yace "Eh
lkci ya kusa" daga haka ya fita daga parlon ya tafi gun motarsa ya bude ya
fiddo envelope da ya taho da shi ya kulle motar ya koma ciki. Yana ta xaune
parlor idonsa a kan tv ya rasa ta yanda xai ba Umma takardan har dai daga
karshe ya mike ya isa kusa da ita ya mika mata ta amsa tana kallonsa tace
"Meye wannan din" komawa yyi ya xauna yace "Na Safeenah ne
Umma" kallonsa Umma ta dinga yi babu ko kiftawa lkci daya ta daure fuska
tace "Me xan yi da shi? Kuma amfanin me xai min?" Mujaheed ya sauke
idonsa kasa yace "Ta kirani last week take sanar min she is pregnant, so
shine na tafi na amshi takardan scan din wajensu...." Umma ta dakatar da
shi da sauri tace "Karya take, nace karya take, Allah ubangiji kuma yyi
maka tsari samun zuri'a da wannan yarinyar, idan ma cikin ne Allah ya san yanda
xai yi da shi balle karya take..." Lkci daya hawaye ya kawo idon Umma,
Mujaheed dai ya kasa cewa komai duk jikinsa yayi sanyi, Umma na goge idonta
tace "A asibitin ku aka mata scan din?" Ya girgixa mata kai, Umma
tace "Toh sai su je asbitin ayi scan din kafin a tabbatar, in sha Allahu
bata da wani cikin ka, in Allah ya yarda, domin wata manufarta daban ta kintsa
wannan karyar, kuma tana son amfani da hakan ne don kawai ta ja ra'ayin ka
gareta, Mujaheed ko hanyar gidansu ban baka izini ka bi ba balle kaje gidansu,
babu abinda ya hada ka da yarinyar nan, dama can ta dalilina ka santa kuma a ta
dalilina ka bar ta in har ka ba ma yarinyar nan da iyayenta listening ears ban
yafe maka ba Mujaheed, ko bayan raina bbu kai babu su in sha Allah babu xuri'a
tsakanin ka da ita, yanxu akwai abinda nace kayi shine ka sanar mata kuje can
asibitin da kake aiki xa a mata scan, kuma albarkacin annabi da al-qurani idan
ma cikin ne Allah yasan yanda xai yi da shi, in sha Allahu baxa ta haifa maka
d'a ba, Allah ya mana tsari da xuri'a irin tasu...." Mujaheed dai kansa na
kasa bai ce komai ba amma duk jikin sa yayi sanyi sosai, Umma ta mike tana goge
hawayen idonta da ya ki tsayawa ta wuce sama. Har yamma Imaan bacci take a
dakin Umma, Seeyama ta sakko downstairs tayi shirin tafiya tana kallon Mujaheed
dake ta xaune parlor tace "To Yaya ni xan wuce, Allah ya ba Imaan lafiya,
naga har yanxu bata tashi ba balle mu yi sallama" Mujaheed yace "Toh
Ameen, da ta tashi sai mu tafi gaba daya coz we are also going back to kaduna today"
Seeyama tace "Ayya ba komai, Allah dai ya bata lafiya Yaya" yace
"Ameen, Allah ya tsare hanya" tace "Ameen" dubu biyar ya
ciro aljihunsa ya mika mata yace "Kiyi transport da wannan" amsa tayi
tana murmushi tace "Toh ngd Yaya Allah ya kara budi" su Ummi ne suka
rakata xuwa bakin titi. Mujaheed ya mike ya wuce dakin da Umma ke xaune, ya
xauna saman carpet dake dakin yana kallonta a hankali yace "Umma ba sai
kin 6ata ran ki a kan wannan magana ba in sha Allah xan yi yanda kika ce, sai
taje can ayi scanning din, amma Umma kar ki manta it's my responsibility to
take care of her and the child..." A fusace umma tace "Wani child din
Mujaheed? Nace maka babu wani ciki, in sha Allahu baxa mu ga ciki ba, idan ma
da cikin Allah ubangiji ya san yanda xai yi da shi, wllh Safeenah baxata haifo
d'an ka ba in sha Allahu, idan Allah ya yarda kana tare da warce xata haifa
maka xuri'arka amma ba Safeenah ba, ko ba komai nasan asali da irin 'ya yan
ka" Mujaheed ya sauke kansa kasa shi dai bai ce komai ba amma har ransa ya
ji dadin furucin umma, Umma tace "Kana wani min maganan responsibility,
responsibility din me?? Ba sai da ciki ake daukan responsibility ba, to wllh
idan kana son ganin bacin raina kada ka fita harkan iyalan gidan Hajiya
Mansura, duk Ni ce sillar komai kuma ina rokan ka gafaran xamantowa ta silla,
ba a mayar da hannun agogo baya amma da banyi abubuwan da nayi a baya ba, Allah
ya nuna min ishara ta hanyoyi da ban ta6a xata ba, nan gaba idan Allah ya yarda
ko ina k'in abu xan k'i sa saisa saisa, sannan baxan fito fili in nuna kiyayata
ba xan bar ma Allah komai, I have learnt a great lesson, kuma na kara tabbatar
da mutum ko waye shi bai isa ya ja da ubangiji ba yayi kadan ne, sannan ina mai
kara gargadinka ka rike addu'a don hakan shine makamin mumini, ka dage da ibada
especiallly at night, never get weak of praying Mujaheed, Allah ubangiji yayi
maka albarka, ya baku xuri'ar masu albarka" a hankali Mujaheed yace
"Ameen Umma nagode" sannan ya mike yana kallonta yace "Let me
check ko ta tashi coz we are leaving for kaduna today" Umma tace
"Bata ci abinci ba, idan baxata iya ci ba akwai gruel da muka yi jiya sai
Ummi ta dama mata ko xata iya sha" yace "Toh Umma" daga haka ya
fita dakin, bedroom din Umma ya shiga ya tadda imaan kwance still sleeping, ya
karasa ya xauna gefenta ya daga rigarta yana shafa cikinta a hankali, Bude
lumsassun idonta tayi tana kallonsa, Kamar xata yi kuka tace "Yaya na
gaji" yace "Kin gaji da baccin koh?" Bata ce komai ba ya dagota
ta kwanta jikinsa tana maida numfashi a hankali, unlike daxu, yanxu kam jikinta
ya fara xafi, murya can kasa yace "Ina ke maki ciwo sweet?" Bata ce
komai ba hakan yasa ya dago kanta yana kallonta yace "Tell me how you are
feeling" buda masa hannu tayi alamar bata sani ba ta kara kwanciya
jikinsa, yace "Toh xa ki ci shinkafar yanxu? Sai in sa maki miyar
kadan" da sauri ta girgixa kai tace "Aa bana so, amai nake ji"
yyi shiru sannan yace "Ko xa ki sha kunu kadan" Bata ce komai ba ya
dago kanta ta gyada masa kai, ya kwantar da ita ya mike ya fita dakin, yana
tsaye kofar kitchen Ummi ta gama dama kunun cikin cup daya ya sa ta saka sugar
kadan sannan ya dauka ya fita kitchen din ya koma daki ya ajiye don ya huce,
kallonta ya dinga yi don har ta koma bacci, Banda sheki bbu abinda jikinta
yake, tayi haske kuma sosai, bayan ya tabbatar kunun ya huce ya tada ta gently,
ganin she looks so weak ya jinginar da ita da gado yace "Sorry sweet, ga
kunun ki sha kadan sai mu wuce gida koh?" Karban cup din tayi a hannunsa
ta kai bakinta a hankali, ko qtr bata yi ba xata ajiye yace "Noo baki sha
komai ba" tace "Allah na koshi Yaya" yace "A'a sai kin kai
rabi" Kamar xata yi kuka tace "Wllh cikina ya cika" dauka yayi
ya daure fuska ya kai bakinta, da kyar ta dinga sha tana hadiyewa daga karshe
ta cire bakinta da sauri, ya wani hade rai yace "Sai fa kin kara"
toshe baki tayi tana kallonsa, ya jawota da sauri yana patting bayanta a nutse
yace "Stay calm baxa ki yi ba..." Girgixa masa kai ta dinga yi xata
sauka saman gadon jiri ya debeta ya rikota kafin ta kai kasa nan tayi masa
wanka da aman kunun da ta sha, sai da ta fito da shi tass, ya dinga kallonta
cike da tausayin ta, Umma ta shigo dakin jin yunkurin aman nata tace "Ko
dai xa ku je asibiti Mujaheed?" Yace "A'a Umma ai gida xa mu wuce
yanxu" Yana fadin haka ya mike ya daga ta suka wuce bathroom, Umma ta yaye
xanin gadon da ya baci da amai ta dau cup din kunun ta fita. Biyar na yamma
Mujaheed ya sami Umma a can dakin da take yace "Umma xa mu wuce gida"
tace "Baxa ku kwana ba Mujaheed tunda bata da lafiya?" Yace "A'a
umma Ina son mu je can gida ne ta sha magani..." Umma tace "Toh
Shikenan, Allah ubangiji ya bata da sauki, Allah ya sauwake" yace
"Ameen" Hijab din Ummi Imaan ta sa sbda nata da tayi amai an wanke,
Mujaheed na rike da hannunta suka fita parlon, kana ganinta kasan she's very
weak, ya bude mata front seat ta shiga, Umma tace "Toh Allah ya sauwake
Allah ya tsare hanya" Da kyar Imaan ta amsa mata da "Ameen"
Mujaheed yayi ma Umma sallama suka bar gidan, Mujaheed na kallon Imaan da ta
lumshe ido yana driving a hankali yace "Sweet nace ma Farida idan mun
shigo Zaria xa ku gaisa, mu je sai ta fito ku gaisa sannan ku wuce" Imaan
ta gyada masa kai kawai don ko magana bata so, yana isa kofar gidan Farida ya
kirata, kin fitowa tayi da farko wai sai sun shigo yace mata sauri suke kuma
Imaan din bata jin dadi, hakan yasa ta fito ta bude side din da Imaan take
xaune, Imaan ta gyara xama tana murmushi tace "Aunty Farida Ina yini"
Farida ta rike ha6a tace "Sannu imaan, ashe dai da gaske baki da
lafiya" Imaan tayi murmushi kawai, Farida tace "Toh Allah ya baki
lafiya, Allah ya sauwake kin ji" a hankali Imaan tace "Ameen
Aunty" sai a sannan Farida suka gaisa da Mujaheed, nan tayi masu Allah ya
kiyaye tace xata je gidansu in sha Allah idan ta shigo kd, a haka suka rabu
Mujaheed yyi reverse ya bar anguwar. Har suka isa kaduna imaan bacci take, yana
parking a parking space ya bude motar ya fito ya xaga ya bude side dinta, Bai
bari ta sauka motar ba ya dauketa suka wuce gidan, a bedroom dinsa ya kwantar
da ita ta rikesa murya can kasa tace "Yaya sanyi nake ji" ya ja duvet
ya rufa mata sannan ya kashe Ac din dakin, duk yanda ya dinga lallabata daren
ranan ta sha shayi kin sha tayi wai xata yi amai, a haka ta ci gaba da
baccinta, karfe goma saura ya shigo ya ganta xaune kan darduma tana sllh, yyi
murmushi ya xauna gefen gado yana kallonta, tana idarwa ta kwanta nan kan
darduman, ya mike ya dagota ya kwantar kan gado yace "Allah ya karba
sweet, but fa sai kin sha shayi xa ki ci gaba da baccin ki" Daren ranan
Imaan bata yi wani bacci ba don da xaxxabi sosai ta kwana, Mujaheed ya dinga
tattalinta yanda ita ma bata yi bacci ba haka shi ma bai yi ba. Washegari
lahadi ya fita ya harhado mata drugs da yasan xa su mata amfani bayan yak'i da
yyi da ita ta d'an sha shayin ya bata drugs ta sha, sannan ya shiga bandaki ya
hada mata ruwan wanka, duk yanda ta dinga nonnoke masa haka nan ta hakura tayi
wankan amma a kunyace yana bandakin. Karfe sha biyu saura ya shiga dakin ya
ganta tana bacci sosai, dukawa yyi kusa da ita ya lumshe ido manna mata kiss a
lips dinta sannan ya rufeta da bargo gaba daya jikinta ya mike ya sauke curtain
ya fita dakin, makullin motarsa ya dauka ya fita gidan, driving yake har ya isa
dai dai saman layin su Safeenah, parking yyi ya dau wayarsa ya kirata, tana
dagawa yace "Ban gan ki wajen ba" mota ce tayi park gefen nasa sai ga
ta ta fito a ciki, bude front seat tayi ta shiga ya ja motar suka bar wajen,
har suka isa asibiti bai kalleta ba, ita ko gaba daya mood dinta kamar warce
aka ma mutuwa. Yayi parking ya sauka motar ya rufe ita ma ta fito a hankali
tana kallonsa, ganin har ya nufi entrance din hospital din ta bi bayansa kamar
me counting steps dinta har suka shiga ciki, xaunawa tayi a reception don har
ya wuce office dinsa, gaisawa tayi da few nurses da ta sani a wajen, wata nurse
tace "Kwana biyu baki biyo Dr ba Madam" Safeenah tayi murmushin
karfin hali tace "Ae kuwa" tana ta xaune very restless har wata nurse
ta kira ta suka wuce sama.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
*Albishirinku 'yan uwa*
Shin ko kun San zaku iya magance mafi yawan cututtukan da
suka addabi al'umma yanzu cikin sauki?
Sinadarin _Stemcell total care_ yayi fice wajen magance
matsalolin diabetes, BP, asthma, sickler, cancer, stroke, rashin haihuwa,
fibroid, infection da duk wata matsala da ta danganci lafiyar Al'umma.
Ba wannan kadai ba, akwai coffee na double root Wanda ke
inganta duk wani abu da ya shafi rayuwar
aure ga maza da Mata, inganta qwayoyin haihuwa da dai sauransu.
Akwai sinadarin rage tumbi da dai sauransu.
*Domin neman qarin bayani ku tuntubi wannan lambar
07068136856*
Sai an gwada akan san na kwarai.
104.....
Mujaheed ya dinga kallon takardan da nurse ta kawo masa
office some hours later, a hankali ya linke takardan ya ajiye ya jinginar da
kansa da kujera, Imaan ce ta fado masa ya mike da sauri yayi clearing din table
din gabansa ya sauke curtain ya dau wayarsa da makullin mota da takardan scan
din sannan ya fita ya kulle office din, Yana tsaye reception nurse ta tafi ta
tado Safeenah da har ta fara bacci a wani ward, yana ganin ta fito ya fara
tafiya, har ya isa gun mota ya bude ya shiga yana jiranta, tare da nurse dake
rike da hannunta suka iso gun motar nurse ta bude mata front seat ta shiga ta
ajiye ledan Magunguna, mujaheed yyi mata godiya sannan ya ja motar ya bar
hospital din, sai da suka yi nisa ya d'an kalleta yaga bacci take, har suka isa
gidansu bata bude ido ba, shi ma kuma babu abinda ya ce, yana gama parking ba
tare da ya kalleta ba yace "Safeenah" bude ido tayi da sauri, ya dau
ledan maganin ya mika mata yace "Allah ya sauwake" amsa tayi ta bude
kofar motar ta sauke kafafuwanta waje amma bata fita ba murya can kasa tace
"Is there any difference between the first scan and this?" Yana
kallon waje yace "No Allah ya raba lafiya, Allah ya sauwake" tace
"Ameeen" shiru tayi kamar yanda shi ma yyi shiru yana jiran ta sauka
ya wuce, tace "kayan shayin sun kare" yace "Ohk" sauka tayi
daga motar ta rufe ido sbda jirin da take ji ta dafe motar da sauri, ya kalleta
yace "Careful" Bata ce komai ba ta fara tafiya a hankali, tana isa
gate dinsu kamar warce aka hankade sai gani yayi ta tafi luuu, fitowa yayi da
sauri daga motar, masu gadi dake wajen ma duk suka taso, Suhaila da tayi
parking dai dai lkcn kuma ita ma taga abinda ya faru ta fito motarta da sauri
ta nufi yar uwartata tana kwala kiran sunanta, amma tuni Safeenah tayi
collapsing a nan kasa, dukawa Mujaheed yyi kusa da ita ya dagota yana
jijjigata, daya daga mai gadin ya bude masa gate ya dauketa ya shiga gidan da
ita, Suhaila ta bi bayansa tana salati hankali tashe, sosai hankalin yan uwanta
ya tashi bayan ya shigar da ita parlor, babu dai wanda ya bi ta kansa kamar
yanda shi ma bai ko kallesu ba, har sai da Safeenah ta farfado bayan kusan
minti sha biyar, juye juye ta dinga yi tana rike da cikinta tana hawaye uwarta
na rike da hannunta tana mata sannu, Mujaheed ya ji tausayinta sosai... Hospital
suka kara komawa da Suhaila da Hajiya Baturiya, suna shiga reception din
hospital din jini ya 6alle ma Safeenah, nan da nan aka shigar da ita emergency
ward, kasa shiga emergency ward din Mujaheed yyi ya wuce office dinsa. Yana ta
xaune office amma hankalinsa ya kasu biyu sbda imaan dake gida, har wani
colleague dinsa Dr Yusuf ya shigo yana kallonsa ya ja kujera ya xauna, bayan
few seconds yace "I am sorry Dr, she had miscarriage" Shiru Mujaheed
yyi yana kallonsa, lkci daya jikinsa yayi sanyi, Dr Yusuf ya mike ya fita
office din, tashi Mujaheed yyi ya fita office din shi ma, ward din da Safeenah
ke kwance Mujaheed ya nufa tun daga bakin kofa ya ji Hajiya Baturiya na cewa
"Wllh wllh shi xubar da cikin, wato dama tun da yace ta shirya xa su
asibiti yau naji ban yadda da shi ba, shi yasan abinda yayi cikin ya
xube..." Suhaila ta katse ta tace "Aikin banxa to sai me?? Allah na
tuba dama me xa ayi da iri irin na uwarsa matsafiya, Ni wllh ba ku ji murnan da
nayi ba da cikin ya xube, naji dadi har raina da Allah ya rabata da wannan
tsinannen cikin, kawai karshe ayi ma yar uwata wankin ciki a karasa rabata da
tsiyarsu.." ita dai Safeenah na kwance sai hawaye take, Hajiya marafa dai
sai girgixa kafa take, juyawa Mujaheed yyi ya fasa shiga ward din. Sai kusan
Magrib Mujaheed ya koma gida ranan ya tadda imaan na barci har lkcn, tausayinta
ya ji sosai ya xauna gefenta yana kallonta sannan ya fita xuwa dakinsa yyi
wanka ya fita masallaci yin Magrib. Bayan sati biyu da xubewar cikin Safeenah
ranan Saturday da sassafe yana parlor yana operating laptop, gaba daya laulayin
Imaan ya damesa don wahala take sosai, duk ta rame gashi ba abinda take iya ci,
kuma bai sanar ma kowa a gida ba har lkcn banda umma da ta sani, kusan kullum
kuma xata kira ta ji jikinta, wani lkcn tace masa ya bata, danna kararrawar da
aka yi tare da bubbuga kofa yasa ya daga kai ya kalli kofar amma bai tashi ba,
Jin irin bugun da ake ma kofar yyi murmushi ya mike ya isa gun window ya daga
labule a hankali yana lekan waje, Maimoon kadai ya hango tsaye hannunta rike da
warmer ta xumburo baki tana kallon Hajiya Inna dake faman buga kofa da duk
karfinta, Inna ta ja tsaki ta tafi can inda ta hango wani dutse babba ta dauko
ta dawo Maimoon ta buda ido sosai tace "Kar fa kije ki gurje ma mutane
kofarsu inna, daga buga kofa sau daya baki jira ki ga....." Katse ta Inna
tayi tace "Kada in gurje ma mutane kofa? Waye mutanen? Mujaheed ko Imaan?
yaran da aka haifa kan idona nayi wahala da su tun durowarsu duniya xa ki ce
kada in gurje masu kofar banxa kawai, banda shegantaka ga shegen takalmansa Ina
gani bakin kofa su bar ni tsaye kamar mara makabuli duk sanyin safiya ya kare
min?? Uban me suke yi a ciki toh har yanxu basu tashi ba, ni ba a ta6a min irin
haka ba duk gidajen da nake xuwa da safe gaskiya" murmushi Mujaheed yyi
yana shafa kai, nan Inna ta fara bubbuga kofar da dutsen hannunta da gaba daya
strength dinta, ya koma gun kofar ya bude yace "Idan kika lalata min kofa
sai kin biyani don baxan yadda ba Hajiya" shigewa parlon tayi har tana
neman bangajesa bata ko kallesa ba fuska daure, Maimoon na murmushi tace
"Ina kwana Yaya" yace "lafiya lau daga Ina ku ke?" Dariya
tayi tace "Gida mana yaya" ganin Inna ta nufi sama ya bi ta da kallo
yace "Ikon Allah, Ina kuma xa ki Hajiya?" Bata tanka sa ba har tayi
wucewarta sama, shafa kansa yayi a hankali ya kalli Maimoon yace "Abba
yasan kun xo?" Maimoon ta girgixa kai tace "A'a ba wanda ta gaya
ma" hanya ya bata ta shigo parlon sannan ya wuce sama, direct parlon
Mujaheed Inna ta shige sannan ta wuce daki, kallon Imaan dake kwance a lullube
tayi tace "Meye kuma haka cikin xafin nan??" Karasawa kan gadon tayi
ta fixge bargon tana kallonta, Imaan ta bude ido a hankali, mikewa tayi ganin
Inna, Inna ta saki baki tace "Na shiga uku me ya same ki haka?" Imaan
ta bata fuska ta jingina da gado tana kallonta, Inna tace "Naga abinda ya
isheni, Wace cuta ce wannan ta kama ki ni patu duk kika kare?" Mujaheed
dake tsaye bakin kofa yace "Xaxxabi take" Inna ta kallesa da sauri
tace "Xaxxabi?? Na cixon sauro ko me?" Yace "Ehh shi" Inna
ta xaro ido tace "Garin ya xa ku ba sauro izinin shigowa wannan santalelen
gida haka, Ina sauro ya ga wajen xama gidan nan fisabilillahi, toh gaskiya da
sake, Kwata kwata Mujaheed baka da kula, haka kawai ka bari sauron mayata su
shigo gida har su cutar min jika, tunda Imaan take bata ta6a xaxxabin cixon
sauro ba a gidan ubanta, to ina Bukar xai yarda da haka dama tunda yasan
ciwanta, wato ga yarinya an baka a banxa shine xa ka yarda ka ba sauro daman ya
cuceta, to ba ruwana wllh, dama ni nasan baxa ka iya rike min jika ba..."
Daga haka ta fice dakin ya bi ta da kallo yana murmushi, sannan ya isa gun
imaan da ta koma ta kwanta, ya xauna gefenta ya kai fuskarsa nata murya can
kasa yace "Kin daina jin sanyin yanxu mu shafa cream?" Marairaice
masa tayi bata ce komai ba, ya jawota jikinsa a hankali yace "Wai da gaske
sauro ne ya cije ki?" Shiru tayi tana kwance jikinsa, ya shafa kanta yana
murmushi. Inna na komawa parlor dama wayarta ta ciro daga cikin jaka ta mika ma
Maimoon tace "Maxa kira min Ahmadu" Maimoon tace "Me ya
faru?" A fusace Inna tace "Don Allah ki kira min shi babu abinda ya
shafeki da mai ya faru, yarinya duk naga ta rame sai hanci da idanuwa ina xan
yadda wai cixon sauro" Maimoon ta amshi wayar ta kira Abba ta mika ma inna
bayan ya fara ring, ko sallaman Abba inna bata amsa ba tace "Ahmadu to fa
ga Imaan rai a hannun Allah, na xo gidan na ganta a dunkule cikin katon bargo
duk ta kare tass sai k'ashi, wai cixon sauro, anya Ahmadu akwai abun kirki a
auren nan, da kyar fa take tashi take kwantawa, kada fa ku manta ita kadai ke
gare Bukar, Kar mu cucesa, wani irin cixon sauro ne yarinya xata rame ta xabge
ta fita hayyacinta haka, to ni dai wllh ba ruwana xan daukota mu taho gida, a
kan me Mujaheed xai amince sauro su shigo gidansa har su cutar min jika"
kuka ta fashe da ta mika ma Maimoon wayar tace "Kashe min wayata mu je ki
hada min kayanta a akwati sai dai duk xagin da Ahmadu xai min ya min, shi xai
yarda a rike yar sa yanda mujaheed ya rike imaan" daga haka ta wuce sama.
Mujaheed yyi picking call din Abba da ya shigo wayarsa ya kai kunne tare da yin
sallama, Abba ya amsa yace "Mujaheed me ya sami Mamana?" Mujaheed yyi
kasa da kai yace "Abba bata da lafiya ne" Abba yace "Me ya
sameta?" Ya d'an yi shiru sai kuma yace "Rashin lafiya ne" Abba
yace "Tun yaushe?" Mujaheed yace "Kusan two weeks yanxu"
Abba yace "Ciwonta ne ya tashi?" Mujaheed yace "A'a" Abba
ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Toh Allah ya bata lafiya, kuna xuwa
asibiti ne" Mujaheed yace "A'a ina dubata a gida" Abba yace
"Innar tana nan har yanxu?" Mujaheed yace "Ehh" Abba yace
"Toh ka bari su taho tare gida tunda ta bukaci hakan, hakan ne kwanciyar
hankalinmu gaba daya" yace "Toh Abba" daga haka Abba yayi masa
sallama ya katse wayar. Inna ta gama hada kayan Imaan da kanta cikin jaka a
bedroom dinta tana mita, Maimoon dai na tsaye tana kallonta, Inna ta xuge zip
din ta mika ma Maimoon wayarta tace "Kira min Aisha" Maimoon ta amshi
wayar ta kira Ammi, Ammi na dagawa Inna tace "Toh Aisha ga dai imaan nan
na xo na sameta ba kanta, tunda nake ban ta6a ganin ta rame irin yanda na xo na
sameta ba, Ni ba ruwana ki Kira mijin ki yanxu xan taho da jikata gida don
baxan kirasa ya bata min rai ba yayi min rashin kunya, wllh babu mahalukin da
ya isa hanani fitar da Imaan daga gidan Mujaheed yau, don idan ta mutu ni kadai
nayi asara ba wani ba" daga haka ta mika ma Maimoon wayar tace "kashe
min kayana" Maimoon na murmushi ta kashe wayar. Kafin Inna ta gama hade
haden kayanta ta fito, har Mujaheed ya saka ma Imaan hijab yana rike da
hannunta ya tafi parking space, front seat ya bude mata ta shiga ya rufe sannan
ya koma cikin gidan. Bai ko bi ta kan Inna ba ya kira Maimoon yace ta xo su
wuce sannan ya koma gun motar. Har suka isa gida Inna mita take cikin mota wai
taya sauro xai shiga gida mai lafiya haka ya illata mata jika haka, bbu wanda
ya tanka ta a motar, imaan dai baccin ta kawai take, daga karshe mujaheed ya
kure karatun Qur'anin dake tashi a motar. Parking yyi Inna ta bude motar ta
fice tana kallon Maimoon tace "Sakko ki bude mata ta fito" Maimoon ta
fito ta bude side din Imaan, ganin tana bacci Inna tace "Kin ga jaraba
koh? Wannan sauron lafiya ne kuwa ni patuu" Murmushi Maimoon tayi tana
tashin Imaan, Imaan ta bude ido sannan ta fito motar tana rike da Maimoon sbda
juya mata da kanta ke yi, Inna tace "Toh Allah dai ya isa" daga haka
ta kama hannunta ta wuce sashinta da ita fuskarta babu walwala, Mujaheed ya bi
su da kallo yana murmushi, Maimoon ma ta bi bayansu. Saman kujera Imaan ta
kwanta ta juya baya, Inna dake ta kallonta tace "Bari in xubo maki abinci
ki ci mu wuce asibiti, ba sai na jira kowa ya ban kudi ba, lafiyar ki ta fiye
min komai dama tuwo nayi tun asuba kafin in baro gida" daga haka ta wuce
kitchen ta xubo tuwa da miyar kubewar da tayi ta dawo parlor ta ajiye kusa da
Imaan tace "Sakko ki ci, kin ji takwara" Imaan ta bude ido da sauri
tace "Ni fa baxan ci komai ba ki tafi da shi" Inna tace "Baxa ki
ci komai ba kuma, ni fa bana son wahala, yanxun nan xuciya ta debeni sai in
tattaraki ki koma gidan Mujaheed din ki mutu" Imaan ta ki juyowa tace
"Inna ni ki tambayesa na ci abinci fa" Inna ta xauna tayi tagumi tace
"Ai ni na shiga uku" Aunty ce ta shigo parlon da sallama ta gaida
Inna tana kallon Imaan tace "Wai imaan bata ji dadi ba" Inna tace
"Wllh, wai xaxxabin cixon sauro Amina, yaushe rabon da ayi wannan ciwon
fisabilillahi, tun tale tale fa, toh yanxu xamanin nan wa ke yarda sauro ya
shigar masa gida ma balle ya cucesa?" Aunty ta dago Imaan tana kallonta da
damuwa tace "Sannu Imaan" Imaan bata iya tace komai ba, Inna tace
"Cewa nayi ga abinci ta ci in kai ta asibiti da kaina ta ki ci" Aunty
ta dago abincin tace "Ki ci ko kadan ne imaan" tunda Imaan ta ji
aroma din miyan, ta dauke kai tana matsawa daga kusa da Aunty, Aunty ta lura da
hakan ta mayar da abincin ta ajiye, Inna ta kuma daukowa tace "Ji min
mata, ki bata abinci kin mayar kin ajiye, abu dai baxa ayi sbda Allah ba"
Imaan na hada ido da abincin for the second time ta mike da sauri tana rike da
cikinta tayi hanyar dakin Inna, Aunty ta bi ta da kallo, inna ta saki baki tace
"Meye haka kuma?" Jin kakarin amanta Inna ta kalli Aunty tace
"Meye ma'anar hakan Amina?" Murmushi kawai Aunty tayi bata ce komai
ba ta mike ta bi bayan imaan, Inna dai na xaune rike da abinci baki har lkcn a
bude, can ta ajiye plate din ta wuce daki ganin yanda Imaan tayi mata amai a
tsakar bandaki ta xauna gefen gado tayi tagumi, Aunty ta cire mata hijab ta
ajiye a bucket, ta taimaka mata ta wanke bakinta sannan suka fito bandakin tana
mata sannu, Inna tace "Toh aman meye wannan aka kirba min a bandaki duk
karni haka? Bandakin da na wanke da hypo biyu daxu, ah gaskiya wannan rashin
Imani ne, tana jin amai kuma baxata tafi can tsakar gida ba sai ta juye min shi
a bandaki na, sannan ke kuma Amina kin dau hijabi dumu dumu da amai ki sa min a
bokitin wanka na, haba jama'ah, wannan rashin kirkin har ina" Aunty dai
bata tanka ba ta kwantar da Imaan dake maida numfashi tana mata sannu, Inna
tace "Toh wllh Amina ki san yanda xaki yi da bandaki na ban dauko ta don
ta cuce ni ba gaskiya, xuciya daya na daukota ganin halin da take ciki, meye
kuma xata kaxance min bandaki da amai???" Daga haka inna ta fice daga
dakin, Aunty ta koma bandakin don ta gyara mata, ta fito parlor daukan omo Inna
dake xaune parlorn ta bi ta da kallo tace "Dama malaria na saka amai
Amina?" Murmushi Aunty tayi tace "Gashi kin gani kuwa Inna" Inna
tace "Toh Allah ubangiji ya mana tsari da shi, amma gaskiya mujaheed da
kyar idan xan iya yafe masa wllh" Aunty ta fita tana dariya kasa kasa.
Karfe goma saura Mujaheed ya shigo parlon Inna, har lkcn Imaan na daki tayi
bacci, Inna kuma na bandaki tana wankewa bayan wanda Aunty tayi, ya shigo dakin
ya nufi kan gadon ya xauna kusa da ita yana kallonta a hankali yace
"Imaan" Imaan ta bude ido tana kallonsa yace "Sannu" ta
gyada masa kai kawai, xaunar da ita yayi yace "Toh me kike son ci?"
Ta girgixa masa kai, da damuwa yace "Noo dole xa ki ji da abinda kike son
ci a ranki what is that?" Shiru tayi tana kallonsa, can tace "Ni dai
danwake nake so yau" Yace "Ohk toh, bari in gaya ma Aunty ta
maki" kwantar da ita yayi ya mike ya fita dakin, ya tafi can part din su
gun Aunty, Aunty dake bedroom dinta tace "Ae kuwa babu flour wllh, sai dai
kaje ka samu Ammi nasan baxata rasa ba sai tayi mata" yyi maza yace
"A'a ni baxan iya xuwa ba Aunty ko xaki aika Maimoon" Aunty ta tabe
baki tace "Toh xan kirata a waya" murmushi yyi ya mike yace "Toh
ngd aunty" daga haka ya fita dakin, aunty ta kira Ammi, Ammi na dagawa
bayan sun gaisa Aunty tace "Kina da flour don Allah" Ammi tace
"Ehh baxa a rasa ba" Aunty tace "Toh Imaan xa ki yi ma danwake
shi take son ci wai" Ammi tace "Toh bari in duba" daga haka ta
katse wayar. Cikin kankanin lkci Ammi ta gama danwaken da farko Maimoon tayi
niyyar kira ta kai danwaken amma sbda yanda take son ganin condition din 'yar
tata, tayi deciding ta kai da kanta kawai, Inna na xaune Parlor ta sa tuwonta a
gaba tana ci, Ta dinga bin Ammi da kallo har Ammi ta xauna ta gaisheta, Inna ta
amsa tace "Yar ki kika xo dubawa kenan, ai har na kullaceki nayi xaton
baxa ki xo ba don kece ta farko da na fara kira" Ammi tayi murmushi ta
ajiye abincin hannunta tace "Ga danwake nan na kawo" Inna tace
"Toh gata can, malaria ne ya kusa mata illa Ahmadu yace ba sai na kai ta
asibiti ba an riga an kai ta" Ammi tace "Toh Allah ya sauwake"
Inna tace "Ameen, mijin ya dai cuce ta jeki ki ganta" mikewa Ammi
tayi ta wuce dakin, karasawa tayi kan gadon tana kallon imaan ta cire blanket
din jikinta, Imaan ta bude ido, da sauri ta mike ganinta tace "Ammi"
sai kuma ta rungumeta, Ammi tayi murmushi lkci daya jikinta yyi sanyi ganin
yanda ta rame, Imaan tace "Ammi Ina yini" dago kanta Ammi tayi tace
"Ya jikin?" Imaan tace "Da sauki" Ammi tace "Mu je
parlor ki ci danwaken na kawo maki" Ta marairaice tace "Ammi ina son
inje can bangarenmu mu" Ammi tace "A'a kiyi xaman ki a nan" Inna
ce ta shigo dakin tace "Toh ta fito ta ci danwaken tun daxu babu abinda ta
saka a baki" Ammi ta mike tana kallon Imaan tace "Sakko mu je ki
ci" A plate Ammi ta xuba mata danwaken, Imaan dai sai kallon abincin take,
ta dau fork da Ammi ta sa mata ta dau daya a hankali ta kai baki, Ammi ta koma
saman kujera ta xauna, Inna dai sai kallon Imaan take tace "Toh ni dai ko
wancan mayyar da ya saka ce ta kama jikata ba a sani ba...." Ko rufe baki
Inna bata yi ba Imaan ta mike tayi hanyar daki da gudu tana yunkurin amai, Inna
ta mike da mamaki tace "Yau naga tsiya, naga jaraba, meye kuma amai amai
kamar me ciki? Aman meye kuma wannan take yi?" Mikewa Ammi tayi ta bi
bayanta, Inna tayi shiru kamar me naxari, can ta bi bayansu ta shiga dakin da
sauri tana xare ido tana kallon Ammi da ta dago Imaan tana mata sannu, tace
"Mun shiga uku, Astagafirullah Aisha ko dai ciki ne da Imaan din?"
Ammi dai bata kalleta ba kuma bata ce komai ba, Inna dai sai xaxxare ido take
tana kallon Imaan dake sauke numfashi Ammi ta karasa shiga bandaki da ita. Inna
ta saki salati tana tafe hannu dai dai shigowar Aunty dakin, Inna tace
"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, ta cuce kanta wllh, kanta ta cuta ba
ni patuu ba" da mamaki Aunty tace "Me ya faru Inna?" Hawaye cike
idon Inna tace "Yanxu sbda rashin tsoron Allah Amina sai da yarinyar nan
ta amince da wannan mutumi har ya kai ta ya baro babu kayan aure, cikin d'an
mutum ne da ita fa Amina, wllh tllh danyen ciki ne shataf da ita, ni naga
yarinya tayi wani haske kamar danyen nama, sai kirji da suka cicciko, to sai
kuma ga amai naga ta kirba daxu a bandaki daga tayi ido hudu da tuwo, yanxu
kuma daga uwar ta kawo mata danwake da mai da yaji ta kai loma biyu baki sai
amai shaaaa duk karni, kaiiii Amina lallai sai dai a kyale yaran yanxu, amma ba
a ta6a kunyata ni irin yanda Imaan ta kunyata ni ba yau" Aunty dai sai
kokarin danne Dariyarta take tace "Haba Inna, yarinya da mijinta
kuma...." A fusace Inna tace "Ke dalla rufe min baki, Mujaheed ne har
xa a kira miji, dama jira kawai yake yyi mata ciki ashe ni ban sani ba, ita
kuma jarababbiya kawai, oh oh toh ba ruwana ya xo ya tattara ta ya mayar da ita
gidansu su je can su karata da aman su ba da ni ba xa ayi wannan gagarumin
kazantar ko 'yar cikina Hadiza lkcn da take da cikin d'an ta na farko ban
amince ta xauna da ni ba sbda amai da yawu balle wa ennan kareren, duk kawai a
bata min gida da k'arnin aman ciki, Aa wllh duk inda yake ya xo ya dauketa ko
kuma uwarta ta maida ta bangarensu suje can su karata wllh wllh ba ruwana, ba
dani ba, duka duka yaushe aka yi auren har ta yadda da shi ciki ya shiga idan
ba fitina ba" Aunty ta fita dakin tana girgixa kai tana murmushi, Ammi dai
ta gama gyara mata jikinta a bandaki ta fito da ita dakin tana rike da hannunta
Inna ta basu hanya da sauri fuska daure, Ammi ta fita dakin, ta dau cooler din
danwaken suka bar parlon ta wuce part dinta da yar ta.
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
*Albishirinku 'yan uwa*
Shin ko kun San zaku iya magance mafi yawan cututtukan da
suka addabi al'umma yanzu cikin sauki?
Sinadarin _Stemcell total care_ yayi fice wajen magance
matsalolin diabetes, BP, asthma, sickler, cancer, stroke, rashin haihuwa,
fibroid, infection da duk wata matsala da ta danganci lafiyar Al'umma.
Ba wannan kadai ba, akwai coffee na double root Wanda ke
inganta duk wani abu da ya shafi rayuwar
aure ga maza da Mata, inganta qwayoyin haihuwa da dai sauransu.
Akwai sinadarin rage tumbi da dai sauransu.
*Domin neman qarin bayani ku tuntubi wannan lambar
07068136856*
Sai an gwada akan san na kwarai.
105.....
Da daddare Ammi na tsaye dinning tana debar ma Imaan kunun da
ta dama mata a flask aka bude kofar parlor, rufe flask din tayi tana kallon
kofar Abba ya shigo da sallama, amsa sallamar tayi har suka karaso cikin parlon
Mujaheed na biye da shi a baya, Abba ya xauna saman kujera yace "Sannu da
gida Hajiya" Ammi ta karaso parlon tana murmushi tace "Ina yini
Alhaji" Abba yace "Lafiya lau, ya mai jikin ta kara ji?" Ammi
tace "Da sauki, Alhmdllh" Abba yace "Toh Allah ya bata
lafiya" Ammi tace "Ameen" shi dai Mujaheed kansa na kasa bai
kalli Ammi ba yace "Ina yini Ammi" tace "Lafiya lau, ya
aiki?" Yace "Alhmdllh, ya mai jiki" Ammi tace "Da sauki
tana ciki" Abba ya mike yace "Bacci take ne?" Ammi tace
"A'a ina jin idonta biyu" Bedroom din Imaan Abba ya nufa Mujaheed ya
mike ba tare da ya yarda ya kalli Ammi ba ya bi bayansa, idonta rufe suka
sameta dakin ta rufe duk jikinta da bargo, Abba ya tsaya yana kallonta yace
"Ta koma baccin kenan" Shi dai Mujaheed na tsaye sai kallonta yake
bai ce komai ba, Abba ya girgixa kai yace "Allah ya bata lafiya, I will
check on her tomorrow" daga haka ya juya ya nufi kofa, Mujaheed ya bi sa
da kallo har ya fita sannan ya isa kusa da ita ya xauna ya sauke blanket din
jikinta ya kai hannu forehead dinta yace "Imaan" Bude ido tayi tana
kallonsa, ya sakar mata lallausan murmushi ta kamo hannunsa cikin sanyin murya
tace "Yaya" ya dagota ta xauna yace "Kanwata" shiru tayi
tana kallonsa, yace "Are you feeling pain anywhere?" Ta jingina da
gado tace "Ina jin xaxxabi da tashin xuciya, kuma my leg is aching me
now" yace "Toh xan taho maki da magani yanxu, but me kike son ci
kanwata?" A hankali ta girgixa masa kai tace "Amai xan yi" da
damuwa yace "No baxa kiyi ba sweet, tell me what u want to eat let me get
it now" ta d'an yi shiru kamar me naxari, can tace "Beans" ya
wara manyan idanuwansa yace "Ke da ba ki cin beans baby?" Turo baki
tayi tace "Ni dai xan ci yau" murmushi yayi yana shafa cikinta a
hankali yace "Babynmu beans yake so kenan?" Kallonsa ta tsaya yi, ya
ja hancinta yace "Ko ba haka ba?" Ta 6ata fuska tace "Wani
babyn?" Ya kashe mata ido yace "Na mu mana sweet" turo baki tayi
kamar xata yi kuka, ya ja hancinta yana murmushi yace "Salon ki haifo min
baby me turo baki koh?" Rufe fuskarta tayi da pillow, ya mike yana
murmushi yace "Xan dawo anjima kadan" Ita dai bata ce komai ba ya
nufi kofa ta dago kanta a hankali ta bi sa da kallo har ya fita, Ammi na tsaye
dinning rike da cup din kunu tana jiransa ya fito, Bai iya yace mata komai ba
duk da ya so ce mata xai dawo anjima, har dai ya nufi kofa ya fita ya kulle
kofar sannan Ammi ta nufi dakin. Abba na fita part din Inna ya nufa, ya shiga
parlon da sallama jin ta a kitchen ya xauna, sai ga ta ta fito tace
"Ahmadu ne" yace "Ni ne, Ina yini Inna" tace "Lafiya
lau, aiki nake a kitchen, baka ji bayana ba wllh kamar xai balle in huta"
D'an murmushi yayi yace "Me kike girkawa kuma da daren nan Inna, ba an
kawo maki abinci ba?" tace "Me nake girkawa kuma? Wannan yarinya me
laulayi nake ma faten tsaki, wai daxu daga nace tana jin amai da sai ta min
magana in kai ta waje tayi a can sbda kar mu xama kazamai tunda a daki bandakin
yake, kada kazanta ya ra6e mu, na dai mata magana ta fahimta Ahmadu, shkkn in
gaya maka sai matar nan Aisha ta kullace ni ta taho ta dauketa ta tafi ba kunya
ba tsoron Allah, suka bar ni tsaye baki sake ina kallonsu, ni abun ma mamaki ya
bani wllh, baka ji ba duk jikina yyi sanyi qlau, nace to meye kuma daga magana
dai mata ta figi hannun yarinya ta wuce, to kaga agwai?? To ka ji tsoronsa, ni
dai nayi shiru ban ce mata komai ba, to ni dai bana bi ta mata bafillatana in
ki kyautata ma jikata ba, daxu na kira ta Rasulu ta aiko min jikarta da tsakin
masara ko garin acca in yi mata fate mai kyau da lafiya, shine nake yi tun
daxh..." Abba yace "Ai kam kin kyauta Allah ya bada lada" Inna tace
"Ameen, amma da don ta Aisha ce wllh baxan yi ba don bata da kirki Sam, ni
dai ba ruwana inyi magana Bukar ya kullace ni, ita kuma Imaan kaga ikon Allah
daga auren sai ga rabo ko Ahmadu, ni dai nayi murna nayi murna, na gode Allah,
na gode Allah, na kuma yi addu'ar Allah ya raba lafiya, in sha Allahu sae ta
cika parlon ubanta da jikoki, tass sai ta haife kanninta muna nan da ku... Da
kyar kuma idan ba mace xata haifa ba don ita ce aka ce ko da bala'i sai ta je
gidan ubanta, Kai Alhmdllh, uwarta fa sai da tayi shekara kusan sha biyar ta
haifeta ita kuwa dubi daga shiga sai ga rabo" Abba dai sai murmushi yake,
can yace "Toh Allah ya raba lafiya" Inna tace "Toh Ameen, Allah
ya bata da sauki naga kamar irin mugun laulayin nan take irin dai wanda uwarta
tayi, ni tsorona ma kada ta xama k'ashi da rai dama gata ba lafiyayya ba"
Abba ya mike yace "Toh bari in je Inna sai ki ci gaba da abinda kike"
Inna tace "Toh Allah maka albarka, amma gudun kada a tada rigima gwara
kawai in ci girma in bar Aisha da halinta sai ta karata da 'yar ta ni kuma
kullum sai in yi ta sintirin xuwa dubata koh Ahmadu?" Abba yace "A'a
in sha Allahu xata dawo wajen naki, xan je ynxu..." Da sauri Inna ta katse
sa tace "Lalala kar ka fara Ahmadu, a bar ta a can kawai ta xauna, ni
kadai nasan irin halin Aisha, bar mata yar ta kawai su karata, gani take baxan
iya kula da ita ba, bar su a can kawai ni babba ce baxan kulata muyi tashin
hankali ba" Murmushi kawai Abba yyi ya fita, Inna tayi wucewarta kitchen
murya can kasa tace "kawai kawai ina ganin irin aman da take kirbawa, ta
ina xan fara ni ba kamfanin hypo da omo ba, ni ba boyi boyi ba, A'a wllh uwarta
na da rai ai" Inna na gama faten ta juye a cooler ta fito kai ma Imaan,
dai dai balcony suka hadu da Mujaheed da warmer a hannunsa da leda, tana
ganinsa ta hade rai, ya kalleta yana murmushi... Yace "Kishiyar ki kika ma
girki kenan" Wucewa ciki tayi tace "Ni dai ba ruwana, in sha Allahu a
kanka ciwon da jikata take xai kare, kuma sai Allah ya saka mata, lefe kuma ni
dai ko na mutu ban yafe ba ehe" bin bayanta yyi yana dariya yace "Sai
dai ciwon ya kare a kanki" Mikewa Ammi tayi bayan Inna ta shigo dakin,
Inna dai bata kalleta ba ta nufi Imaan dake kwance tace "Sannu takwara, ga
faten tsaki me tsafta na maki, xai gyara maki baki, ta shi in xuba maki ki
ci" Tana fadin haka ta fita xuwa kitchen dauko plate da spoon, mujaheed
dai na xaune parlor, ta dauko plate din ta koma dakin ta bude ta dibar mata
faten da ya ji kayan hadi da ganye mai yawa ta nufi Imaan tace "Tashi
xaune" Imaan ta mike xaune tana kallon plate din da kyar tace "Meye
wannan?" Inna tace "Fate ne mana...." Imaan ta amshi plate din
tana rike numfashinta sai kuma ta ajiye ta dauke kai, inna ta bude baki tace
"A'a ni fa ba wahalalliya bace, kuma ba asararriya bace, cefanen dari
biyar kenan kike gani wllh, babu abinda xai maki sai ma gyara maki ciki da baki
da xai yi" ita dai Ammi na tsaye, Imaan ta juya a hankali ta dau spoon din
ta debi abincin ta kai baki, Inna ta xauna gefen gado tace "Dama banda ke
wa xan ma haka? Ko Hadiza wllh bata samu haka ba, baki ji maganata ba an dai
cuce ki kawai" juyawa Ammi tayi ta fita dakin, Imaan ta dinga cin abincin
a hankali sbda tsamin yyi mata dadi a baki, sai da ta ci kusan rabin plate din
sannan ta ajiye, Inna tace "Ya aka yi?" Ta girgixa kai tace "Na
koshi" Inna tace "Toh sai ki ci sauran anjima" tana fadin haka
ta mike tace "Gashi har kin d'an marmaro, amma a bar ki haka ba kula kila
tun safe babu abinda Aisha ta baki kika ci, ni dai na tafi idan na gama sllh ko
cikin dare ne xan shigo in duba ki" daga haka ta fita, Mujaheed ya bi ta
da kallo bayan ta shigo parlor yace "Toh ni nawa abincin fa" Inna ta
nufi kofa tace "Wanda uwarka Amina ta dafa kenan" yyi murmushi yace
"Ehh shi" bata tanka sa ba ta fita, ya mike ya dau warmer da ledan
drugs da ya siya ya wuce dakin, imaan da ta kife kanta da pillow ta dago tana
kallonsa, ganin yanda ta 6ata fuska ya karasa cikin dakin yace "What
happened?" Kamar xata yi kuka tace "Amai" ajiye abin hannunsa
yayi ya xauna kusa da ita yace "Sorry dear, baxa ki yi ba" bubbuga
bayanta ya dinga yi a hankali, tayi lamo jikinsa ta rufe ido, Bayan wani lkci
ya dago kanta yace "Are you okay now?" Ta gyada masa kai, yace
"Toh in xuba maki waken?" da sauri ta girgixa masa kai tace "Na
koshi" yace "Toh ga magani ki sha" kamar xata yi kuka tace
"Aa idan na sha yanxu xan yi amai" yace "Toh anjima Ammi xata
baki ki sha, xan je in yi sllh yanxu" kwantar da ita yayi ya manna mata
kiss a forehead yace "Allah maki albarka sweet" lumshe idonta tayi,
ya ja mata blanket ya mike yace "I will come in the morning in sha
Allah" gyada masa kai tayi ya juya ya fita dakin. Haka Imaan ta ci gaba da
xama part dinsu tana laulayi gun Amminta dake bata kulawa yanda ya kamata, har
wanka Ammi na taimaka mata idan jikin ya matsa mata sosai, throughout kuma Ammi
na dakin to make sure she is fine, komai tace tana so Ammi na kokarin ganin ta
yi mata, Aunty ma a rana ta kan shigo kusan sau hudu dubata, ita ma once in a
while tana girki irin na gargajiya ta kawo mata, dama ana idar da sllhn asuba
Inna ke rafka masu uban sallama a bakin kofa da cup din kunun ta a hannu, baxa
kuma ta bar part din ba sai in Imaan ta kirba amai kamar yanda take cewa, to ko
second daya bata karawa xata yi gaba tana yamutse fuska, Duk irin yanda
Mujaheed ke son ganin wife dinsa a ko da yaushe kasa shiga yake sbda Ammi,
nauyi da kunyarta yake ba kadan ba, kwata kwata bai iya shiga, haka nan xai
wuce gun aiki da safe da tunanin wife din tasa, a gun aikin ma gaba daya rabin
hankalinsa na gun Imaan, gashi yyi ta kiran wayarta bata dagawa sbda ko da
yaushe silent wayar yake bata son ringing din, sai dai kuma babu abinda ya rage
su da, don every week sai ya siya kayan shayi, duk da Ammi ta gaya ma Maimoon
dake kawowa tace masa ba fa wani sha Imaan ke yi ba, hakan bai sa ya fasa siya
ba, Magungunan ta ma duk ya san lkcn da xai kare ya siya ya bada a kai mata,
once in a while idan Abba xai shiga da daddare shine xai bi sa su shiga tare,
duk Friday Yusuf kan shigo dubata shi ma, ya kan dade dakin yana mata hira duk
sai dai tayi murmushi tana kwance, a haka har cikinta yayi wata uku, laulayin
ya d'an mata sauko tayi wani kyau na musamman ta kara haske, gaba daya Mujaheed
ya kagu Abba yace ya wuce da matarsa gida amma shiru Abba dai bai ce komai ba,
yau Saturday da yamma kamar ko da yaushe Inna na bakin tap dinta tana gurje
gurjenta taji footstep, daga kai tayi, tayi mitsi mitsi da ido tana kallon mai
tahowa, lkci daya ta dauke kai ta ci gaba da abinda take....
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
*Albishirinku 'yan uwa*
Shin ko kun San zaku iya magance mafi yawan cututtukan da
suka addabi al'umma yanzu cikin sauki?
Sinadarin _Stemcell total care_ yayi fice wajen magance
matsalolin diabetes, BP, asthma, sickler, cancer, stroke, rashin haihuwa,
fibroid, infection da duk wata matsala da ta danganci lafiyar Al'umma.
Ba wannan kadai ba, akwai coffee na double root Wanda ke
inganta duk wani abu da ya shafi rayuwar
aure ga maza da Mata, inganta qwayoyin haihuwa da dai sauransu.
Akwai sinadarin rage tumbi da dai sauransu.
*Domin neman qarin bayani ku tuntubi wannan lambar
07068136856*
Sai an gwada akan san na kwarai.
106.....
Har Umma ta iso kusa da Inna Inna bata dago ba ta wani tsuke
fuska tana ci gaba da abinda take, Umma tace "Sannu Inna" Inna tace
"Sannu" Umma ta d'an risina tace "Ina yini Inna" Inna tace
"Lafiya lau..." Umma tace "Ya gida ya aiki" Inna tace
"Lafiya lau" Umma tace "To madallah, sannu da aiki" Inna
tace "Toh ga dai kofar a bude..." Umma ta kalli kofar parlon Inna ta
nufi parlon ta shiga ciki ta xauna, sai da Inna ta shafe minti sha biyar bakin
tap din sannan ta mike murya can kasa tace "Uwar me ta xo min toh? Ni dai
ba ruwana, bari ma dai...." Part din su Imaan ta nufa ta tadda Ammi xaune
parlor, tana kallon Ammi bayan ta kulle kofa tace "Kina ji na Aisha?"
Ammi ta mike tace "Ina ji Inna, sannu da xuwa" Inna tace "Bacci
imaan take?" Ammi tace "Ehh yanxu ta kwanta" Inna tace "Toh
ko da wannan mata Rukayya xata shigo nan kada ki kuskura ki yarda ta yi ido
hudu da Imaan, a gaskiya idan kika yarda ta ga yarinyar nan wani abu ya sami
jikata bayan tafiyarta to xan rufe ido in mance kina auren d'a na in dau
mummunan mataki, babu wanda bai san Rukayya axxaluma bace, to banda wani
sharrin mai xaman kansa ya kawota uban me xata shigo mana gida tayi kuma? Ni
dai ba ruwana ki tafi ki makala ma kofar dakin jikata makulli iyaka idan Allah
yasa ta shigo nan ku tsaya iya nan parlor kuyi tadin ku ta kara gaba, idan tace
maki imaan fa kice ai tana can bangarena tun safe, don gaskiya idan wani abu ya
sami jikata da cikin dake cikinta har Bukar sai abun ya shafa ba ke kadai ba,
kai gwara ma abu ya same Imaan a kan wannan ciki na jikinta don ma ki ji"
daga haka ta fice daga parlon, Ammi ta girgixa kai ta koma ta xauna, Inna na
komawa part dinta ta shiga parlor tana kallon Umma dake xaune tana kallo, tace
"Daxu wani almajiri na da muka dade tare tun ina gidan mijina ya xo na
kawo masa swan water da ya rage a fridge, abinci kuma ba a kawo min na dare ba
tukun" Umma tace "A'a ba komai dama na xo duba Imaan da jiki
ne..." Da sauri Inna tace "Wace imaan din kuma? Ai Imaan ta warke
garas tana ma ciki tana bacci bata son damuwa, A'a wllh ta warke tun yaushe ma,
ai dama laulayi ne ba wani abu ba, dama baki yi asaran kudin motar ki ba duk da
ban san daga inda kike ba amma jikata kam Alhmdllh tana ma ciki tana bacci abun
ta" Umma tace "Toh shkkn Allah ya kara lafiya ni xan koma" Inna
tace "Toh mun gode, Allah yayi albarka" Umma ta mike tace "Ameen
nagode..." Inna tace "Har xa ki tafi?" Umma tace "Ehh xan
koma" Inna tace "Toh yanxu wajen yayar taki mai shinkafa da wake a
kasuwar tasha kike ko kuma wajen Hadiza a kano" Umma tace "A'a ina
Zaria" Inna tace "Ayyoo, kuna da yan uwa a Zaria kenan?" Umma
tace "Ehh" Inna tace "Toh madallah, sai dai kiyi kokari kiyi
aure shine mutuncin ki da rufin asirin ki tunda dai kin ki xaman gidanmu, Allah
ya hada ki da na gari dai" Umma tayi murmushi tace "Toh nagode"
Inna tace "Toh kamar ina da canji bari in baki kudin mota" Umma tace
"A'a ki bar shi Inna nagode" Inna ta bude jakarta ta fiddo hamsin
biyu ta mika mata tace "Gashi nan kya yi kudin mota Allah ya kiyaye"
Umma ta amsa tace "Toh Allah amfana" Inna tace "Ameen" leda
dauke da can malt shidda ta ajiye ma Inna tace "Gashi ba yawa" Inna
tace "Ke da kike fama da kanki kuma kya siyo mantina ki kawo min, Toh
Allah yayi albarka" Umma tace "Ameen" Inna tace "Imaan din
na ciki tana bacci da sai ince ki shiga ki ganta, amma bacci take" Umma
tace "A'a ba komai, a gaisheta idan ta tashi" Inna tace "Toh
xata ji" daga haka Umma ta fita parlon, Inna ta ta6e baki tana fito da
malt din da daddaya da daddaya. Umma na isa part din su Imaan tayi sallama bakin
kofa, Ammi dake parlon har sannan ta amsa sallaman, Umma ta shiga parlon, Ammi
tayi mata sannu da xuwa, umma ta xauna tana amsawa, nan suka gaisa, Ammi ta
tafi kitchen ta dau tray ta daura mata ruwa da lemo sannan ta fito ta ajiye
kusa da ita tana tambayarta ya gida, Umma tace "Alhmdllh, Alhaji fa"
Ammi ta xauna tace "Yana Abuja kuwa" Umma tace "Toh Allah ya
taimaka, ya Imaan da jiki" Ammi tace "Jiki Alhmdllh, tana ciki
ma" daga haka ta mike ta wuce dakin Imaan, Abinci Ammi ta sameta tana ci
tana kallo a tv dake dakin, Ammi ta bude warmer din abincin tace "Yanxu
wani abincin kike kuma ci Imaan?" Imaan ta marairaice tace "Na kasa
baccin fa, yunwa kuma nake ji" Ammi ta tabe baki tace "Sai ki shiga
kitchen da kanki kiyi wanda xa ki ci anjima baxan iya ba, ki fito ku gaisa da
Hajiya Rukayya" Imaan ta xaro ido tace "Ta xo Ammi?" Juyawa Ammi
tayi ta fita daga dakin, Imaan ta ajiye plate din abincin da ta cika dam bayan
wanda ta ci ko awa daya ba ayi ba, ta rufe abincin, sannan ta sakko daga saman
gadon ta bude press dinta ta dau ironed hijab dinta har kasa ta saka ta fito
parlor, dukawa tayi har kasa bata yadda su hada ido da Umma ba tace "Ina
yini Umma?" umma tace "Lafiya lau Imaan, ya karfin jiki" Imaan
tace "Na ji sauki" Umma tace "Toh madallah, Allah ya kara
lafiya" Imaan tace "Ameen, ya gida" Umma tace "Lafiya
lau" Umma na kallon Ammi tace "Tun daxu na shigo Ina bangaren
Inna" Ammi tace "Allah sarki, bari a xubo abinci" Umma ta mike
tace "A'a Alhmdllh, xan shiga mu gaisa da Amina sannan in wuce, dama nace
dai bari in daure in fito yau in duba jikinta" ledan hannunta ta ajiye
kusa da Imaan, Ammi tace "Toh Allah ya amfana, Allah ya saka da
alkhairi" Umma tace "Ameen sai da safe, Allah ubangiji ya kara mata
lafiya" Godiya Imaan ta kara yi ma Umma, Ammi ta rakata waje, Imaan ta
mike ta koma dakinta. Haka rayuwa ya ci gaba da kasancewa Imaan ta ji sauki
sosai, bata da wani takamaiman aiki sai ci, komai ta samu ci take, da wanda
bata ci a da, da wanda take ci, ita dai ta ci, son jiki kuma ya karu kan nada,
ko kadan bata son stressing kanta, har wanka sai tace Ammi ta cuda mata
bayanta, Dama da Hajiya Inna ta ji
footstep ta leka da sauri taga imaan ce ke xuwa boye duk wani abinta na ci take
yi karkashin gado da gudu ta dawo ta xauna a parlor ta fuske, bbu abinda
Mujaheed ya rage ta da shi na abubuwan ciye ciye da kayan makulashe, komai tace
masa tana so ko karfe sha biyun dare ne sai ya fita ya siyo mata don yawanci a
gidan yake kwana, wani lkcn kuma ya tafi gidansa, ganin irin kunyar Ammi da
yake ji dake sa shi bai iya shigowa yasa Imaan da taga lkcn dawowarsa ya kusa
daga gun aiki take wucewa gun Inna, duk Ammi na lura da ita amma bata ta6a ce
mata komai ba, shi kam Mujaheed duk ya xuba masu ido a gidan ganin bbu wanda ke
da niyyar cewa ya dau matarsa ya tafi ko suna nufin tana gida har sai ta haihu
ne shi dai bai gane ba. Inna ce tsaye parlor sai mita take tana masifa tana
cewa "Ni dai ba ruwana a daina xuwa ana 6ata min waje ana takurani, ke dai
baxa ki iya xama bakin ki bai yi motsi ba ki wani shigo min parlon da na sha
wahala na tsaftace da shegen bak'in gyada kina ci kina tara min 6awo a parlor
salon parlona yyi wari, ita Aishar ce ta turo ki ki cuce ni ko Mujaheed din?
Don nasan Bukar baxai turoki ki xalunce ni ba" Imaan dai sai cin gyadan ta
take tana tara 6awon, Inna tace "Ni wannan wahala ya isheni wllh, wani da
maki ciki ni kuma da cutuwa da wahala da cikin, kullum ayi ta cutata ana matsa
min ana kazantar min da parlor, wlh na gaji, ni ba abinda na hada dake gaskiya
balle mijin ki, shi mujaheed din da yayi miki cikin ki tafi dakinsa mana ki ci
gyadan idan ba rashin tsoron Allah ba xaki yo min nan...." Mujaheed dake
tsaye bakin kofa xuwan sa kenan yana cire takalmansa yana murmushi ya shigo
parlon, Inna ta kallesa ta wani hade rai ta shige daki, imaan ta bi ta da kallo
tana taunar gyadarta tana tabe baki, Xaunawa Mujaheed yayi kusa da ita yace
"Wa ya siya maki gyada?" Ta wara masa ido tace "Xaka ci?"
Yace "Aa na bar maki da babies dinmu ku ci ku koshi" Imaan ta 6ata
fuska tace "Ni dai sai ka ci..." sakkowa yyi ya xauna gefenta ya
jawota kusa da shi yace "Toh sai ki tauna ki sa min a baki" dariya
tayi ta 6are daya ta kai masa baki, ya make kafada yace "Chew it
first" Tace "Aa ni dai" lumshe ido yyi ya fara kissing lips
dinta dai dai fitowar Inna daga daki.... Da sauri Imaan ta kauda kanta, Inna
tayi kamar bata gansu ba tana kakkabe kujerunta ba tare da ta sake kallonsu ba
tace "Ni dai a fita a bar min parlona ni ba yar iska bace, ni ba
gantalalliya bace, kawai jaraba yayi yawa a duniya dai ga shi nan, Banda haka
meye kuma xa a xauna min parlor ana tambada ba kunya ba tsoron Allah, ni dai ba
ruwana, ban ma ta6a ganin haka ba tunda uwata ta haifeni, meye kuma mutumi xaka
xauna gun yarinya kamar xaka shige jikinta tana fama da kanta, a gaskiya ban
san me kake nufi ba, ita kuma jarababbiya tayi mukus... Kai jama'ahhh naga
abinda ya isheni ni patuu" mikewa Mujaheed yyi bai son yayi dariya yace
"Ke dai baxa ki daina sa ma mutane ido ba a gidan nan" da sauri Inna
ta kallesa tace "Maxa ku fitar min daga parlor ba ruwana, maxa maxa ku
fita, kuma wllh kada in sake ganin kafafuwan ku a nan, bari kuma Ahmadu ya
dawo, ni dai ba ruwana, tunda uwata ta haifeni ban taba ganin iskanci haka ba,
haka ranan ka shige daki ka latse yar mutane saman gadona, wancan ranan kuma ka
bi ta har bandaki ban san me ku ke yi ba, idan kuma kitchen ta shiga shi ma ka
bita ka datse kofa, to wannan wani irin fitina ne, to kai baka da tsoron Allah
ne? Ni dai ba ruwana wllh" Mujaheed na dariya yace "Idan kina sa min
ido da ni da matata sai idonki ya tsiyaye nima ba ruwana" d'aga Imaan yayi
suka fice daga parlon Inna ta bi su da kallo baki bude. Da daddare Abba ya
shigo gaida Inna, ko amsa gaisuwarsa bata yi ba tace "Ahmadu kana ji
na??" Abba yace "Ina ji Inna..." Inna tace "A gaskiya ka yi
ma d'an ka Mujaheed magana ya dauke matarsa su bar gidan nan, ko kuma in har xa
su xauna gidan nan su daina shigo min ni ba gantalalliya bace, don abubuwan da
nake gani sun isheni haka, ni dai ba ruwana baxan ce komai ba amma gaskiya ya
dauketa tunda mun gama bauta da ita ta samu lafiya sai ma wani tashen fitsara
da take min, ko mi ta ci ta bar min shi kaca kaca a parlor duk wari sai dai ni
in dauke in share, shi kuma Mujaheed na yi masa uxuri don tun ba yau yake min
rashin kunya ba dama can ya rainani, wllh ce min yyi idona xai tsiyaye, to idan
idona ya tsiyaye ina lafiya Ahmadu? Naka xai kalli tsabagen idonka ya maka
wannan mugun alkaba'i? To ba ruwana kowa yyi ta kansa wllh ba don kai da Bukar
ba ni dai babu abinda na hada da Imaan da mutumin nan Mujaheed" Abba dai
bai ce komai ba kansa na kasa. Daren ranan Abba ya kira Mujaheed parlonsa yace
masa washegari dama ya tabbatar ya dau matar sa su wuce gida tunda mahaifiyarsa
suke renawa, sosai Mujaheed ya ji dadin jin haka har ransa amma bai dago kansa
dake kasa ba, Abba yace "Sai ka ci gaba da kula da ita, coz abinda take
bukata kenan yanxu, if possible a samar mata yar dattijuwa immediately sbda
house chores, if there is anything you let me know" kasancewar Washegari
lahadi ne da safe Mujaheed ya tafi part din Inna don yasan da kyar Imaan bata can,
Xaune ya sameta parlor tana shan shayi da bread leda guda, Inna dake share
bakin kofarta tace "Jiya na ajiye maka fura da nono shiru shiru baka dawo
ba kuma" yace "Ni da kika kora da matata kuma me xan yi da furan
ki" daga haka ya shiga parlon yana kallon Imaan dake kokarin boye bread
din da take ci da sauri, yyi dariya yace "I caught you..." Kamar xata
yi kuka tace "Ni fa ba duka xan cinye ba fa, nawa ne da na Inna" Inna
tace "Karya take Mujaheed, daga wajen uwarta ta taho da shi, ba ruwana
tass xata cinye shi, Ni wllh kada ma ta tsiyace min kai da wannan uban cin da
take, ni gani nake ma ba na lafiya bane" Mujaheed yace "Toh Ina
ruwanki?" Tsayawa Inna tayi tana kallonsa daga bakin kofa. Karfe sha biyu
saura Imaan na saka Hijab dinta Ammi ta shigo dakin, tana kallonta tace
"Ba abinda xaki tafi da shi" Imaan tace "A'a Ammi" Ammi ta
xauna gefen gado tace "Toh na dai gaya maki ki rage ciye ciyen kayan xaki,
sannan kuma ki daina wannan shegen son jikin kina kwanciya Kamar ruwa, try and
be doing little works, ko da an kai maki mai aikin, sannan wanka kuma da kike
yi da ruwan sanyi ki daina" Imaan tayi murmushi tace "Toh Ammi ai na
daina" Ammi tace "Toh Allah ya kiyaye hanya" Imaan ta dau
handbag dinta tace "Ameen, ai xan dinga xuwa fa bayan kwana biyu ki dinga
min irin dambun da kike min" Ammi ta ta6e baki ta mike ta fita dakin,
Imaan ta bi bayanta, gun mota ta tadda Mujaheed na jiranta, sai da ta shiga
part din Aunty tayi mata sallama tukun tana bobboye cikinta da hijab kamar
yanda take yi idan ta ga Aunty, duk gidan banda Aunty da Abba sai Yusuf babu
wanda take boye ma ciki, da farkon fitowar cikin tana d'an jin kunyan Amminta
tayi ta saka hijab tana takure kanta, amma daga karshe kuma kawai ta sake, amma
Inna from day one take tsirara ma a gabanta da cikin, Aunty na murmushi tace
"Toh Allah ya kara lafiya daughter, Allah ya kiyaye" Sabbin turaren
humra da aka kawo ma Aunty ta debar mata da yawa sannan ta rakota har parlor
imaan tayi mata godiya ta fita. Suna hawa saman titi Mujaheed ya kamo hannunta
yace "Babu abinda xa a siya maki sweet?" Imaan ta langwabar da kai
tace "Ni Ice-cream nake so plss Yaya, Ammi bata bari na sha wanda ka siya
min shekaranjiya ba" Mujaheed yace "Toh amma karami xan siya maki
sbda kinga garin da sanyi, bana son kina shan ice-cream din nan" Tace
"Toh na ji, sai ka siya min har da pizza" ya shafa lap dinta ya kashe
mata ido yace "Toh mum twins" ta turo baki tace "Bana so"
murmushi yayi bai ce komai ba har suka isa babban eatry din Mujaheed yyi
parking ya bude motar ya sauka, ita ma ta sauka a hankali, still tayi tana
kallon motar da ya shigo yayi parking gefen motarsu a haraban eatry din...
*Imaan isn't for free* it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp number
07087865788
*Albishirinku 'yan uwa*
Shin ko kun San zaku iya magance mafi yawan cututtukan da
suka addabi al'umma yanzu cikin sauki?
Sinadarin _Stemcell total care_ yayi fice wajen magance
matsalolin diabetes, BP, asthma, sickler, cancer, stroke, rashin haihuwa,
fibroid, infection da duk wata matsala da ta danganci lafiyar Al'umma.
Ba wannan kadai ba, akwai coffee na double root Wanda ke
inganta duk wani abu da ya shafi rayuwar
aure ga maza da Mata, inganta qwayoyin haihuwa da dai sauransu.
Akwai sinadarin rage tumbi da dai sauransu.
*Domin neman qarin bayani ku tuntubi wannan lambar
07068136856*
Sai an gwada akan san na kwarai.
107.....
Imaan ta dauke kai da sauri ta jingina da mota jin
kafafuwanta sun kasa daukanta xuciyarta na bugawa ganin wanda idonta yyi tozali
da, tun da Mujaheed yyi ido hudu da Sadeeq ya dauke kai ya rufe motarsa, Imaan
ta bi sa da kallo don har ya kusa entrance din eatry din, Xagayowa Mujaheed yyi
yace "Mu je" Bata yadda ta kallesa ba ta girgixa masa kai, yace
"What?" Ta bude motar bata son ya ga hawayen idonta ta shiga tace
"I will wait here" mujaheed bai ce mata komai ba ya nufi cikin eatry
din. Hada idon da suka sake yi da Sadeeq cikin eatry din yasa Sadeeq ya d'an yi
murmushi ya karasa gun Mujaheed yana kallonsa ta glass din idonsa ya mika masa
hannu hade da masa sallama cikin cool voice dinsa, Mujaheed ya mika masa nasa
hannun yana mayar masa da murmushin, suka gaisa sannan Sadeeq ya koma inda yake
tsaye, packaging masa burger da ya siya aka yi ya bar eatry din Mujaheed ya bi
sa da ido, Yana isa gun motarsa suka kara ido hudu da Imaan da sauri ta dauke
kanta xuciyarta na bugawa, ya bude motarsa ya shiga ya tada ya bar haraban
eatry din, wasu hawaye ta dinga ji suna xubo mata bata san dalili ba, ta jinginar
da kanta da kujeran mota tana jin kamar ta fashe da kuka ko xata ji dadi a
ranta. A haka Mujaheed ya dawo ya sameta, tun da ya kalleta sau daya ya dauke
kai ya tada motar ya bar eatry din, har suka isa gida kuma bai ce mata komai ba
yyi parking ya bude motar ya dau ledan abubuwan da ya siya ya fita, ita dai bin
sa kawai tayi da kallo tana goge hawayen idonta, har ya tafi kuma ya dawo ya
bude mata door din motar, k'in fitowa tayi ya juya yyi wucewarsa, a hankali ta
sakko daga motar ta rufe sannan ta wuce ciki a sanyaye, kwanciya tayi kan
kujera gaba daya ta rasa me ke mata dadi, bayan kusan minti talatin Mujaheed ya
sakko ya kunna Tv ya xauna parlon, Juya masa baya Imaan tayi ta hade rai ya
kalleta ta gefen ido ya ci gaba da kallonsa, Har aka yi azahar Imaan taki yarda
magana ya hada ta da Mujaheed, tana ta kwance parlor ta juya baya kan kujera,
sau biyu yana ce mata ta tashi ta dau Ice-cream dinta xai yi melting tayi masa
shiru, shi ma kuma bai sake ce mata komai ba, jin ya fita masallaci ta mike a
hankali ta wuce dakinta taga har ya canxa xanin gado ya gyara dakin, bathroom
ta wuce ta dauro alwala ta fito ta shimfida darduma, tana idar da sllh ta sauka
xuwa kitchen ta ciro manyan indomie biyu a kwali, ta wanke tukunya ta kunna gas
ta daura ruwa, tana gama dafa indomien ta juye a babban plate ta fito, xaune ta
ga Mujaheed a parlor ya bi ta da ido, ta hade rai ta wuce sama, ta cinye
indomien tass sannan ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa. Har dare Imaan bata
sakko ba duk da yunwa da take ji sosai, tana fitowa wanka bayan Isha taga ledan
abinci ajiye a dakin, riga kawai ta xura bayan ta goge jiki ta xauna ta bude
ledan taga jollof ne har takeway biyu ko wanne da babban kaza a ciki sai drink
da bottle water. Sai da ta kusa cinye gaba daya sannan ta mike da kyar ta tafi
bathroom ta wanke bakinta ta fito ta feshe jikinta da turare ta kashe wuta ta
kwanta ta lumshe ido, Bayan kusan awa daya aka bude kofar dakin Mujaheed ya
shigo, tana ji taki juyowa balle ta bude ido, ya karaso kan gadon ya xauna
gefenta murya can kasa yace "Imaan" Shiru tayi bata ce komai ba ya
hau saman gadon ya kwanta gefenta yace "Tell me what ur problem is
plss" a takaice tace "I don't have any problem plss" dagota
yayi, ta fashe masa da kuka, shiru yyi yana kallonta, bayan few seconds a hankali
yace "Baki son xaman mu tare har yanxu koh Imaan? To shkkn har yanxu deal
dinmu na nan, give me five kids that look like you, sae in sauwake maki ki koma
gun wanda kika gani daxu kike shareni, but let me tell u this, I won't tolerate
ki dinga min shiru sbda kin ga tsohon saurayin ki, after all ba ni na hanasa
auren ki ba ai, I was home on that very day aka kirani na xo gida aka gaya min
an aura min ke..." mikewa xaune imaan tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta
tace "Ehh gaskiya ne baka sani ba aka aura maka ni, but don't forget
kaddara ya hana Sadeeq aurena nasan shi ma ba da son ransa ba, kuma ni nasan
har in bar duniya baxan ta6a samun masoyi na gaskiya irinsa ba, baxan samu me
sona xuciya daya kamar Sadeeq ba, nasan kuma da wuya moment din mu tare yayi
fading a xuciyata da wuri, I will never forget our...." Rikota Mujaheed
yyi cikin tsawa yace "Baki da hankali ko Imaan? Da auren nawa a kanki kike
min wannan maganan, da auren nawa kike ce min baxa ki manta da Sadeeq ba, are
you out of ur senses??" Yana huci ya kare maganar, ta fashe da kuka tace
"Why will I forget someone that always say he loves me innocently anytime,
anywhere?? don me xan mance wanda baya shakkar furta min kalmar so, he always
tell me he loves me not he cares, I pray Allah forgive me amma ni nasan da wuya
in samu so irin wanda Sadeeq yayi min a rayuwa kuma..." shiru Mujaheed
yayi yana kallonta da idanuwansa da suka sauya launi, ta goge idonta ta juya
masa baya ta kwanta tana shessheka, Mujaheed ya jinginar da kansa da gado ya lumshe
ido, bayan wani lkci ya bude yana kallonta, dawowa yyi kusa da ita a hankali ya
kwanta ya jawota jikinsa murya can kasa yace "Imaan are you still
pretending you don't know I love you?" Jin tayi shiru ya lumshe ido cikin
sanyin murya yace "Imaan tun baki san kanki ba nake sonki... son da ni
kaina ban san irinsa ba, I have loved you from the beginning and I have always
dreamt of living with you as my wife, the mother of my kids till eternity,
Imaan nasan kinsan Ina son ki, son da duk duniya bayan iyayenki babu mai maki
irin sa, baki min adalci ba idan kika ce min baki sani ba don nasan kin sani
you are only playing with my intelligence thinking babu aure tsakaninmu kamar
yanda kika sa ma kanki wannan tunanin, me yasa baki ta6a xama kinyi naxarin me
yasa duk cikin siblings dina nafi damuwa da lamarin ki ba, me yasa baki yi
tunanin dalilin da yasa na mayar dake favourite dina ba, nasan kin san komai
Imaan, shekaru biyu da suka gabata Umma ce ta xama barrier tsakaninmu kika ga
na daina kula ki amma ba wai a son raina ba, sai dai duk da haka kullum kina
rai na, kuma duk ranan da ban ganki ba I will be restless, are you thinking
saboda Inna nake tafiya part dinta in xauna a lkcn? Kina tunanin sbda ita nake
xuwa bangarenta? I am always there because of you Imaan, Ina xuwa ne don kawai
in ganki in tabbatar you are okay, I love you tun baki san kanki ba Imaan, wllh
son da nake maki Ina ga na Ammi kadai ne xai fi nawa, da na rasa ki Imaan da
ban san halin da xan shiga ba duk da a lkcn na ma cire rai da ke, ban ta6a
xaton xaki xama tawa ba all of a sudden, Daren da na fallasa maki sirrin
xuciyata ta yanda nake tunanin xaki fahimta sai kika mayar da ni mahaukaci,
kika nuna sam baki gane abinda nake nufi ba baki gane inda na dosa ba kuma ni
nasan kin gane Imaan, it's just that you are soo good at pretending tun kina
'yar karama, you are perfect in that...." Jin har sannan ta ki cewa komai
yasa mujaheed ya leka fuskarta a hankali, murmushi yaga tana yi, suna hada ido
cikin duhun tayi saurin rufe fuskarta cike da shagwaba tace "Ni bana soo
Yayaa" ya lumshe ido ya rungumeta sosai yace "Plss tell me meyasa
dinga wasa da hankalina kina pretending all those time?" Murya can kasa
tace "Because you are also pretending, kuma kana da girman kai, you too
big to tell me kana so na" xaro ido yayi yana kallonta bai san lkcn da yyi
dariya ba yace "In gaya maki ina sonki ki daina kulani Imaan? komai fa sai
kice Yaya ne..." Ta shige jikinsa tace "Toh ni ban ta6a ganin inda
Yaya xai ce xai auri kanwarsa ba sai a kanka" Yana murmushi ya shafa
cikinta yace "Gashi kin gani kuwa, har da result..." turo baki tayi
tace "Kyaleni joor" ya lumshe ido yana shakan kamshin gashinta, a
hankali tace "Toh yau sai ka gaya min inda ka kai min wayar da Sadeeq ya
siya min" Yana murmushi sosai yace "Yana can gida, idan na koma xan
kai ma Inna ta dinga waya da shi idan xata iya" Ta dago kai tana kallonsa
tace "Ai nasan kai ka dauke dama wllh" hade bakinsa yyi da nata... a
wannan daren kamar wancan daren da ya xuba mata pill a drink, duk sai da
Mujaheed ya fallasa ma Imaan gaba daya sirrin xuciyarsa da ta riga ta sani tun
ba yau ba take kakkaucewa, Ita ma kuma ta basa hadin kai dari bisa dari fiye da
xaton sa, a daren ita ma kuma ta bude baki tace "I know you are, and will
always be the best for me yayana, nima ina sonka, Ina kuma alfahari da
kansancewar ka mijina"
5 years later.....
Imaan ce tsaye bedroom din Umma gaban mirror tana gyara Hijab
dinta, Umma ta gama saka ma wani little handsome dake tsaye gabanta yana mata
surutu takalminsa, komai nasa sak na Mujaheed kamar yyi kaki, babu abinda d'an
yaron ya mance na uban nasa, Umma dai sai kallonsa take tana murmushi don hatta
muryarsa kamar Mujaheed dinta yana karami, tana rike da hannunsa ta nufi kofa
jin horn din mota a compound tace "Kiyi sauri tunda ya fara horn Imaan"
fesa turare Imaan tayi ta gyara fuskarta sama sama ta bi bayan Umma da sauri,
Mujaheed dake xaune mota rungume da little sister din Musaddeeq ya fito motar
yana kallon Imaan yace "I told you it's late already kar mu yi missing
flight..." Umma ta hararesa tace "Tunda barin kasar xa ku yi
ba.." murmushi kawai yayi ya shafa kansa, Mai aikin Umma ta iso wajen da
jakan Imaan da kids dinta ta saka a booth, ta koma ta dauko wani jakan ta saka
a booth tana kallon Imaan tace "Mum Ilham Allah ya kiyaye hanya"
Imaan na murmushi tace "Toh Aunty faiza sai mun sake dawowa" Umma na
kallon Imaan tace "Inji baku mance komai ba dai" Imaan tace
"Idan ma mun manta Umma wani lkcn sai mu dauka idan mun dawo" Umma ta
dau Musaddeeq tana kallonsa kafin tace komai ua manna mata kiss a goshinta yana
murmushi yace "We are going to miss you granny" Dariya tayi tace
"I will miss you more sweetheart ka gayar da old woman da grandpa and
grandma a gida ka ji?" Gyada mata kai yayi ta sa shi back seat, ta amshi
Ilham dake hannun Mujaheed tace "Teemah will be staying with me" Mika
ma imaan hannu yarinyar tayi da sauri tana 6ata fuska xata yi kuka, imaan tayi
dariya tace "Baxa ki xauna gun granny ba..." Umma ta saka ta cikin
mota tana dariya tace "Allah ya kiyaye hanya, a gaida kowa da kowa a kaduna"
Driver ne ya taho wucewa da su airport din, Mujaheed ya shiga motar bayan ya
kara yi ma mahaifiyarsa sallama Imaan ma tayi mata sallama sannan suka bar
gidan. Satin Imaan biyu kenan a kano wajen Umma da kids dinta, jiya Mujaheed ya
taho daga kaduna mayar da su gida, Shekaru uku da suka wuce Umma ta koma kano
da xama gaba daya, yanxu fita take Dubai duk bayan wani lkci, business take
sosai wanda cikin kankanin lkci ta fara tara abun duniya bbu abinda ta rasa,
Rahma kadai ce gabanta har lkcn bata yi aure ba tana karatu amma Ummi tayi aure
da Maimoon 2 years back. Cikin lkci kadan suka shigo garin kaduna a flight, duk
inda Mujaheed ya bi da little Ilham mai sunan Inna sai an tanka ta don
kyakkyawa ce sosai yarinyar gashi kwata kwata bata son mutane, Ammi kadai take
makale ma don har suka gama xama kano bata wani yadda da Umma, Suna fitowa daga
cikin airport kamar ance Imaan ta waiga ta ga Sadeeq yana jan trolley yana
danna waya da alama saukansa kenan kasar don ba waje daya suka fito ba, da
sauri ta dauke kai don bai ganta ba, Mujaheed dai na waya yana rungume da
Ilham, Ita kuma Imaan tana tafe tana jan trolley Musaddeeq na rike da hijab
dinta a gefenta, tuntube yayi da trolley din hannunta ya fadi wanda hakan ya ja
hankalin mutane da yawa ciki har da Sadeeq, bai yi kuka ba yaron Imaan ta sake
jakan hannunta ta dago sa da sauri tana ce masa sannu, Kallonsu Sadeeq ya dinga
yi, bai san lkcn da yace "Imaan" juyawa tayi ta kallesa da sauri,
Mujaheed ma ya juya da sauri jin an kira sunanta, Sadeeq ya nufeta yana murmushi
yace "Waow is this ur son Imaan??" ta kirkiri murmushi ta gyada masa
kai, daukan Musaddeeq yayi ya rungumesa ya manna masa kiss a goshinsa yace
"He is soo cute, ya sunansa??" Tana murmushi tace "He is
Abubakar Sadeeq" Sadeeq ya kara rungumesa yace "Ohhh takwara na
kenan, where is his dad?" sai a lkcn ya ga Mujaheed dake kallonsu shi ma,
Sadeeq ya nufesa still smiling ya basa hannu, nan suka gaisa yana kallon Ilham
ya ja Cheeks dinta yace "Waow little imaan kenan" murmushi kawai
Mujaheed yyi yana kallonsa, Sadeeq yace "It's been long, over five years
yanxu...." mujaheed yace "Sure, where are you coming from"
Sadeeq yace "I am coming from Uk now, ya Kaka?" Mujaheed yace
"Tana lafiya lau" Sadeeq ya shafa kai yace "Xan dai je in
gaisheta in sha Allah Maryam ta bani sako in kawo mata, you know we are not far
from each other a can UK, driver ya xo daukan ku ne?" Mujaheed yace
"Not at all, xa mu hau taxi" Sadeeq yace "Driver ya taho min da
mota yanxu, muje sai mu yi dropping din ku" Har kofar gida Sadeeq ya ajiye
su bayan ya siya ma Musaddeeq bindiga na wasan yara a hanya, Ilham kuma ya siya
mata babban doll, Imaan na kallonsa tana murmushi tace "Baxa a hadani da
Madam muyi xumunci ba?" Shafa kai Sadeeq yyi yace "Madam... tukunna
dai in sha Allah" Imaan ta xaro ido tana kallonsa da mamaki, yace "Ko
xa ki sama min madam din?" Dariya tayi ta sauka motar tace "Ni
kuma" Sadeeq yyi murmushi yana kallon Mujaheed yace "Ae gaskiya ne,
ko in jira little Imaan kawai?" dariya Mujaheed yyi yace "Lkci dai na
ta wucewa Sadeeq, try and settle down" Sadeeq yyi murmushi yace "In
sha Allah, A gayar min da Kaka soon xan shigo" A haka suka rabu da Sadeeq,
Tun da suka shiga compound duk da Ammi dake tsaye tana shanya Musaddeeq bai bi
ta kanta ba ya nufi part din Inna da gudu yana kwala mata kira yana cewa
"Old womannn, old womannn, where are you" Ammi ta bi sa da kallo tana
murmushi, Imaan ta sauke Ilham ta nufi Ammi da gudu tana murmushi dimples dinta
na lotsawa Ammi ta dauketa ta rungumeta, Imaan ta karasa ta rungume Amminta
tayi mata kiss a goshi tana murmushi a hankali tace "Nayi missing dinki
Ammina" Inna da ta fito da duk kwanukan kitchen dinta da tukwane bakin
pampo xata wanke wai sun yi k'ura ta daga kai ganin Musaddeeq tace "Waye
kuma wannan?" ya kyalkyale da dariya ya saita mata bindiga har da kulle
ido daya, xaro ido tayi tana kallon bindigan da yayi kama da na gaske daga
nisa, da gudu ta shige parlonta jikinta na rawa tana cewa "Innalillahi wa
inna ilaihi raji'un, Mujaheed ya haifi jaraba" Mujaheed da tahowansa kenan
ya dinga dariya yana kallon son din nasa da ya bi bayan Inna da gudu yana cewa
"I missed you old woman...."
*Ina mai sake jaddada cewar littafin Imaan ba free bane na
kudi ne* settle ur debt it's just
it's 300 via
Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
07087865788
I want to draw the attention of those posting my books that
are not free on Facebook, ku ci gaba xa mu hadu gaban ubangiji in sha Allah...
_Toh Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah😃 a nan na kawo karshen littafina me taken *Imaan*
kurakuran da nayi a ciki Allah ubangiji ya yafe min, darussukan dake ciki kuma
Allah ubangiji ya sa mu amfana da shi_
Na sadaukar da littafin nan xuwa ga beloved brother na Yahya
M Bello, Allah ubangiji ya raya min kai little bro, ya albarkaci rayuwar ka ya
sa ka xamo apple of our parent eyes... Gaisuwa ta musamman xuwa ga mahaifiyata
Hajiya Hajarah, she is my first, my world, my role model, my everything Allah
ya bar min ke Hajjaju Yaya, Allah ya kara maki lafiya ya karo arxiki mai
albarka, my siblings Ahmad, Maryam, Fatima, Baby, Haiydar, Papi, Ilham, Fadil,
sudais, Jamcy, Humairah, Aneesah, Mujaheed, Big Ilham, Yusuf, small Baby, And
my takwara Khaleesat, Allah ya albarkace ku gaba daya, Ina son ku har raina,
Small Mum Aunty Rukky thanks for the encouragement from the beginning of this
book till the end Allah bar min ke ya daukaka ki, my Aunty Didi ur daughter
jiddo is greeting with respect Allah ya ubangiji ya jibanci lamarrukan ki,
Hajiya Inna Allah ubangiji ya bar mana ke mu ga me taka 'yan jikokin ki a duniya,
Muna alfahari da kasancewar ki grandma dinmu. Hajiya Sadiya Chamo😉 Hafsat Oum Ilham, Ummu Zainab, Anty Ay(Ummu Lailah)
Hajiya Asabe, Hajiya Fauziyya fiji, Mama Dutse, Khaleesat Haiydar na gaishe ku
gaba daya with respect, Allah ubangiji ya raya 'yan kannena ya albarkace su,
All the members na payment groups dina guda bakwai da nayi creating for the
book Imaan, Ina gaisheku Ina maku fatan alkhairi, Ina alfahari da ku for
patronizing me, Allah ya bar xumunci ya kara maku budi, members na murmushin
novels da Seembieluv groups ina godiya da kauna, and finally my fans... words
Alone isn't enough to express my feelings toward you guys, Ina son ku sani a ko
da yaushe Ina maku fatan alkhairi, Allah ubangiji ya sa mu gama da duniya
lafiya Ameen.
Taku har ko da yaushe Khaleesat Haiydar (Hauwa Bello Jidda)
Na bar ku lafiya📚✍🏻
Tohm Ina masu neman cream da xai gyara masu jiki, su yi kyau
suyi haske suyi ta glowing 😉 da masu fama da sunburns, da strong
palms... to maxa ku garxayo ga wani product that is tested and trusted I am
assuring you guys.... Xa ku iya tuntuben wannan number in sha Allah.
08038103096.
108.....
Post a Comment for "IMAAN COMPLETE"