Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

TANTIRANCI KO KARUWANCI COMPLETE

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me .on Wattpad @rahamanalele*

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 1

*Alhamdulillah Alhamdulillah💃🏻 nagodema Allah daya bani ikwan dawowa ya bani damar kawo muku wannan labari nawa wato 💁🏻 TANTIRANCI KO KARUWANCI.* 🤫

*Yanayin me d'aukar hankali ne. Tafiyar abar dubawa ce. Karatun abin tunani ne. Ina san nayi amfani da Wannan damar wajen rokwan masoya littattafaina wato ƳAN MATA way'anda nayi musu ba dai-dai ba kan SAMAREEN BANAH part 2 da LEEKITAN ZUCHIYA dana hanesu karantawa. Toh ga dama tazo gareku. Zanso kubud'e kunnuwanku👂🏼 da ware idanuwanku👀 dan Wannan littafin mallakinku ne. Na sadaukar dashi ga duk BUDURWAR da zata karanta. Sannan Inayi muku fatan kukai qarshensa da lafiya. Kamar yanda kuke yimin addu'ar gamawa cikin nasara. Rahma nalele dai🤷🏻 takuce y'an hannuna. (Auntyn luv)*😍

 

 

 

 

 

Waige waige yakeyi acikin layin nasu. Sam bazai wacce shekaru ashirin da biyar ba. Yaro ne kyakkyawa ajin farko wanda kallo d'aya zaka mai kasan ya had'u tako ta'ina.

Ya tara abubuwa kamar haka..Tantiranci. Wayewar zamana. Ilimi. Iya wanka...

ABDUL D'AN KASADA  kenan me karatu...

Abokansa ne suka sakamai wannan sunan ashekara biyu kad'al kuma ya bishi..

 

ABDUL ya rasa abubuwa uku arayuwarsa..

Ya rasa soyayyar Mahaifiyarsa da y'an uwansa.

Sam mahaifiyarsa Mama Saude bata qaunarsa arayuwarta. Bata da abun qi kamarsa a rayuwa.

Tunda ABDUL ya tashi bai tab'a ganin ranar daya zauna shida ita sukayi magana irinta uwa da d'a ba.

Kullum cikin cikin hantaransa take da nuna masa tsana. Kai baqin hali dai iri iri ba wanda ABDUL baya gani agun Mahaifiyar tasa..

Kaf cikin gidansu da unguwarsu ba wanda baisan da zaman qiyayyar da Mahaifiyar tasa take masa ba. Hatta abokansa suna mamakin irin tsanar da Mahaifiyar tasa take masa.

   ABDUL yana da aboki AMEER.

AMEER layinsu d'aya da ABDUL

Saidai AMEER iyayansa masu kud'in gaske ne. Sam bazaka tab'a had'a gidansu AMEER danasu ABDUL ba.

Saboda gidansu ABDUL shine gidan talakawa na biyar acikin unguwar tasu.

 

AMEER tun tasowarsa arayuwa yake da rashin ji. Sam AMEER baya ganin kowa da gashi.

Ya rigada yayi suna wajen rashin mutunci..

Ga satan kud'in iyayensa da shaye shayen tsiya dabin mata kamar d'an akuya.

Sam bazakiso had'a Y'arki aure da AMEER ba..

Gashi su biyu kacal iyayensu suka Haifa shida qanwarsa Abida.

Suna sansu suna qaunarsu shiyasa yake amfani da Wannan damar yake iskancin dayaga dama..

 

Azahirin Gaskiya iyayensa suna matuƙar qoqari kan ya kintsu..

Dan basu san halaiyarsa kaf. Dan ko kad'an baiyiyo halinsu ba

Kasancewarsu nagari. Kawai sun yarda bata yanda Allah baya jarabtar bawansa.

Hakan yasa suke mai addu'a babu dare Babu ranah

 

Bambancin rashin jin AMEER da ABDUL abu biyu ne

Sam shi ABDUL baya bin mata baya aikata zina.. Sannan idan abinka zaikai shekara agaban ABDUL bazai tab'a d'aukar maka shi ba. Ma'ana anan baya sata baya aikata zina.

Saidai fa duk rashin mutuncin AMEER ABDUL yafishi. Dan shi idan yace yes baya dawowa yace no

Idan yace saiya aikata abu to Wallahi saiya aikata kodako abin nan zai kaisa ga caji office ne.

Sam ABDUL bashi da tsoro.

 

 

Gidansu ABDUL gidan yawa ne gidane irin gidan family house d'innan

Akwalla ba akasara ba yawan mutanan gidan zasukai su d'ari..

Gidan babban gida ne wanda yayi suna acikin unguwar. Suna kiran gidan da GIDAN YAWA. Saboda tsabar yawansu..

 

Alhaji Ali me katifa shike da mallakin gidan.

Yana da yara Ashirin da d'aya aduniya dukkansu maza.

Kuma kaf d'insu sunyi aure kuma agidan suke zaune da matansu da yaransu. Kasancewar gidan babban gida kowa idan yatashi auransa yankan wani shashi yake anan cikin gidan ya gina ya zauna da iyalinsa...

 

Mama Saude Ƴa ce ga qanwar Alhaji Ali yar autarsu. Amma ta rasu shekarun baya da suka wucce wajen haihuwan qanwar Mama Sauden wato ZAINAB.

 

Toh tunkan Mahaifiyar tata tarasu Alhaji Ali yake san Y'a mace kasancewar duk yaransa Ashirin da d'ayan nan duk maza ne.

Hakan yasa ya d'auki Saude tun tana qarama ya kawota gabansa wajen matarsa Hajjiya Ladi wacce kaf y'an gidan suke kiranta da Hajjiya Kakah.

Ita ta raineta har takai munzalin aure. sai alhaji Alin ya Aurar da ita ga d'ansa Shehu..

Shine suke zaune suma agidan har tasamu cikin ABDUL ta haifesa wanda tunda ta haifesa take nuna masa tsana dan qiri qiri qin shayar dashi tayi. Wai nononta nayi mata ciwo idan takai masa nonon bakinsa jitake kamar kan nononta zai gutsire.. Jin hakan sai Hajjiya Kakah ta d'auki ABDUL tashayar dashi da madara irin ta yara kamarsa awannan lokacin..

Kowa agidan Gani yake anya kuwa Saude itace ta haifi ABDUL.

Saboda sunga yanda take nuna mai tsana da tsangwama kala kala..

 

 

ABDUL ya tashi a nutse bashi da kwaramniya irin ta yara marasa ji..

Saidai daga lokacin dayakai shekara Ashirin da uku aduniya daga lokacin ABDUL yazama TANTIRIN d'an iska.. Ammafa injisu da fad'a😳 (saidai me karatu kagyara zama muji shin da gaske ne ko akwai sab'ani cikin maganar tasu)

 

Lokaci d'aya kuma ya juye yazama hakan.

Saboda tunda ABDUL ya gama karatu zai fara aiki a companyn abokin babansa wato mahaifi ga abokinsa AMEER kasancewar business ya karanta. shikenan fa kamai ya jagule ma ABDUL d'in alokacin..

An rasa tayaya meyasa hakan yajuye masa..

 

Bashi da abokanaye sai y'an iska. Y'an daba. Y'an shaye shaye masu jaye jayen magana.

Masu aikata lefuka TANTIRAI dai kawai.😳😳😳

Toh alokacin ne AMEER ya kulla abokantaka da ABDUL kuma ABDUL ya yarda..

 

 

Hajjiya Kakah tatara malamai kan suyi mata istahara ko Allah zai basu haske kan lamarin nasa.. Sai malaman suka bata tabbaci akan asiri akama ABDUL d'in kuma wallahi mugun asiri ne..

Makaryar asirin shine ranar da za'a d'aura ma ABDUL d'in aure.

Dazaran an d'aura masa Aure to ba makawa wannan asirin ya karye kenan..🤔

 

Tunda Hajjiya Kakah taji hakan hankalinta ya tashi dan tasan me dai hankali bazai tab'a d'aukar y'arsa yaba ABDUL ba.

Nan tashiga ba ABDUL magungunan tsari da karya sammu amma kamar bata basa dan ba abinda yake canjawa.

 

Saita fara kici kicin neman wacce tadace dashi a dangi..

Saidai kaf iyayen yaran da sunji za'a had'a y'ay'ansu Aure da ABDUL nan suke tsalle su dira suce su bazasu yarda a d'aurama yaransu aure da ABDUL ba..

Saboda sunyi duba da yanda TANTIRANCINSA yake qara habb'aka..

 

Lokacin da mahaifin ABDUL yaji wannan batu har kuka sanda yayi saboda baqin cikin abin da sukace..

Amma daga baya dayayi duba da irin tsanar da Saude Mahaifiyar ABDUL d'in da take masa saiya share komai... Dan Inda ace bata nuna tsana agaresa da zasuji kunyar fad'in hakan.

Danshi dai kaf cikin y'ay'an nasa bashi da abinso kamar ABDUL d'in.

Kullum cikin yimai addu'ar kintsuwa yake. Tare da yimai nasiha akan ya kintsu.

Saboda har sakin Saude yayi kan tsanar da takema ABDUL danta dena ta y'antar dashi kamar yanda ta y'antar da sauran yaranta amma taqi.. Haka dai Hajjiya Kakah ta bashi hak'uri ya maida ita d'akinsa awannan lokaci..

 

Sam Hajjiya Kakah bata dena nemama ABDUL maganin tsari ba. Haka addu'ar babu dare babu rana haka take mai kan Allah ya karya lamarin dan tasan tunda dangi suka hanata y'ay'ansu danta aurama ABDUL d'in tatabbatar bare dai bame bata y'arsa danta Aura masa asirin ya karye.

 

 

Tunda asirin ya kama ABDUL shikenan ya dena ganin mutuncin kowa agidan saina Hajjiya Kakah da mahaifinsa da qanwar mahaifiyarsa wato AUNTY ZAINAB...

 

AUNTY ZAINAB qanwace ga mama Saude idan me karatu ya koma baya kamar yanda na fad'a muku..

 

Mama Saude tana da shekara goma sha biyar aduniya aka mata aure.

Kuma tana shiga d'akin nata tasamu cikin ABDUL.

Lokacin data haifi ABDUL lokacin shekarun ZAINAB qanwarta biyar aduniya..

  Dake ZAINAB itama Alhaji Ali ya dawo da ita gun Hajjiya Kakah saiya kasance tunda ZAINAB ta qilla ido🤪 taga ABDUL sai taji ba wanda take so kamarsa..

Bini bini tana naniqe da ABDUL..

Tun a lokacin kowa agidan ya fara mamakin qaunar da ZAINAB takema ABDUL..

Idan taga ABDUL na kuka  nan itama zata hau kuka wiwi har sai Hajjiya Kakah tayi nasarar shawo kan kukan ABDUL d'in..

 

Toh wannan shine silar faruwar shaquwar ABDUL da ZAINAB AUNTYNSA..

 

Tunkan ABDUL yayi wayo yasan ZAINAB me qaunarsa ce..

 

ZAINAB bata iya san abu  ba arayuwarta.. Dan idan tatashi san abu sanshi take gabaki d'aya kuma da gaske..

Haka kuma bata iya qin abu ba. Idan taqi abu taqishi kenan har abada..

 

ZAINAB tana matuqar jin tsanar Ƴar uwar tata mama Saude aranta..

Saboda qiyayyar da takema ABDUL shine dalilin dayasa itama take jin qiyayyarta aranta..

 

Hankalin ZAINAB yayi matuqar tashi dataji wani sirrin Y'ar uwar tata akan ABDUL.. Wannan yasa taqara qaunar ABDUL a ranta da qarin jin tsanar Y'ar uwar tata...

 

Tunda mama Saude tagane qanwar tata taji sirrin nata shikenan suka samu rashin jituwa..

Dama ita ZAINAB tanajin qiyayyar yayar tata akan tsanar dataga tana nunama ABDUL d'in

Saidai koda wasa bata tab'a nuna mata afuska ba..

Sanda taji wannan sirrin nata tukunna tadena ganinta da mutunci tafito da tsanar da take mata afili har kowa ya gane hakan

 

Mama Saude ranta na b'aqi da yanda ZAINAB d'in tadena ganin mutuncin nata.

Saidai ta share tunda ta gane barazanarta tayi tasiri akan ZAINAB d'in dan gaya mata tayi idan har tatona mata asirin nan nata kowa yaji ya sani wallahi saita kashe ABDUL kotawata hanya saidai itama a kasheta..

 

Jin hakan shiyasa ZAINAB rufa mata asirin  saboda tatabbatar a irin qiyayyar da Sauden takema ABDUL d'in ba makawa zata kashe shin. Saidai ko a kashetan dan Wallahi zata aikata hakan kamar yanda tace..

 

Ita kuma tana qaunar ABDUL d'in dan duk wani abu dazai tab'a mata ABDUL d'in ya shiga damuwa ko ciwo ya kamasa ba sanshi take ba hakan ne yasata yin shuru da bakinta kawai tazubama sarautar Allah ido dan tasan dole Allah saiya tona mata asirin da bata san kowa yasani.

 

 

Hakan ya faru ne ana saura wata biyar Auran ZAINAB d'in

ZAINAB takamu da san wani Salisu d'an gaye haka. Yana santa sosai kasancewarta abin san kowane d'a namiji.

Danta kasance kyakkyawa ajin farko. Tatara duk wani abu da d'a namiji yake so ajikin mace..

Farace sul sul gwanin ban sha'awa

 

ABDUL yakan zauna yata kallanta lokacin yana qarami yace. Wai AUNTY ZAINAB dani dake wayafi wani kyau ne..

Murmushi kawai take yi dan shi ABDUL wankan tarwad'a ne bazaka kirasa fari ba kuma bazaka kirasa baqi ba.

Kalansa abinso. Ga fatarsa kogaggiya dan gaskiya mahaifinsa yayi qoqari sosai wajen ganin ya kyautata rayuwar ABDUL d'in..

Dan sam ABDUL ba abinda yake nema ya rasa agun mahaifin nasa.

Daga kayan sawa na wanka irin na yaran zamani. kud'in makaranta har d'an dai kud'in kashewa ba wanda ABDUL yayi missing arayuwarsa har yagama karatunsa yasamu nasarar amshe takaddarsa cikin nasara.

Gashi dai bawai suna dashi bane kawai wadatar zuci ne irin na mahaifin nasa da qaunar da yake masa..

Haka wajen Hajjiya Kakah bata yima ABDUL rowar duk wani abu nata naci da y'ay'anta suke bata..

Dan haka sam ABDUL bai tashi ta kwad'ayi irin na yara ba..

 

 

 

ZAINAB sanda ta Auri Salisu tagane tantirin d'an iska ne manemin mata d'an shaye shaye..

Tayi kuka tayi kuka lokacin data gane hakan

Saboda tasan bazata iya rayuwa babu shi ba.

Dan tana mai wani so ne wanda yafi qarfin akirasa da MASEEFAR SO

 

Baya dawowa gida sai qarfe goma sha d'aya ko sha  biyu na dare..

Sannan abuge yake dawo mata..

Wani lokacin ya mata dukan tsiya idan tana masa fad'a kan yadena abunda yake yi. Sai yace wai tayi mai rashin kunya dan haka sai ya hauta da duka..

Idan washe gari tayi kuma saiya hau bata hak'uri

Ahaka zaita lallab'ata har ta hak'ura

 

Ahaka ahaka har tadena hak'uri. da zaran ya daketa sai tayo GIDAN YAWA.

Haka zai zo bikwanta idan yadawo hayyacinsa..

Sam Hajjiya Kakah bata bashi ita saita ciccimishi

Daga baya tagane idan tana mai fad'a ran ZAINAB d'in na b'aci. sai kawai tadena yimai

Idan ZAINAB d'in ta gudo cemata take tazauna idan yazo tafiya da ita tabishi ba saima tayi mata sallama ba..

 

Sarai ZAINAB tagane gatse tayi mata amma bata damuwa dazaran yazo ko tana d'an jamishi aji kad'an ya lallameta Saidai Hajjiya Kakah tanemeta ta rasa😂 tabi mijinta..

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.**.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*🤱🏻¸* *.¸¸.**.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 2

 

 

Sam Salisu bai qare ZAINAB da komai na rayuwa ba.

Komai yanayi mata na rayuwa hakan ne yake sawa kaganta fes kamar wata y'ar tsana. Fatarta  kullum agoge take. Tana dai jin dad'in rayuwa na kayan more rayuwa..

  Matsalarta biyuce arayuwa. Na farko shine bin matan da mijin nata yakeyi da shaye shayen daya keyi. Na biyu shine rashin haihuwanta. Dan yanxu haka watanta tara da auren nasu amma uwar mijinta dake bata santa haka tabi tasata agaba wai bata haihuwa dan maseefa kamar shekara taran tayi ba wata tara ba..😊

 

 

___Wannan shine labarin ABDUL D'AN KASADA  da mahaifiyarsa Mama Saude da AUNTYNSA ZAINAB da kakarsa Hajjiya Kakah.

 

 

*****************************

Andawo labari..

 

ABDUL na gama waige wai gensa ya fad'a gidan AUNTYN tasa ZAINAB kasancewar anan bayan layin nasu gidan nata yake sam gidanta baiyi nisa da gidan nasu ba..

 

Da sauri ya fad'a falan nata da sallama sam bata jishi ba. Sai hakan ya bashi damar b'oyewa cikin wani lungu anan cikin falan nata...

   Gam gagam.. Zainab taji ana buga mata ƙofar falan nata kamar za'a b'alla.. Da mamaki tafito daga kitchen d'inta tana me yarfe hannu da qarema y'an sandan biyu  kallo daga sama har qasa tace.. "Lafiya. meya faru..

Afusace d'aya daga cikinsu yace..."ABDUL D'AN KASADA mukazo nema.. "ABDUL.. Ta maimaita da mamaki. Kana taciga da cewa. Toh baizo nan ba.

"Kinga malama karki raina mana hankali. Dama ance kece kike b'oyesa anan gidan. To bari kiji idan kullum kin saba b'oyesa yau baki isa b'oyesa ba dan lefinsa me girma ne..

Wallahi sai mun shiga ko'ina lungu da sak'o nacikin gidan nan mun zak'ulo shi d'an iska Yaro kawai..

 

   Dama na gaya muku arayuwar Zainab bata da abin so kamar ABDUL. Kuma duk yanda kuke da ita idan zakaci mutuncin ABDUL nan zata sab'a maka. Sun shaqu iya shaquwa ita dashi. Kowa yasan da wannan shaquwar dake tsakaninsu..

  Dan haka nan take taji ranta ya b'aci da titsiyan da suka sakata agaba suna masu yi mata.. Dan haka cikin tab'e baki tace.. "Rainin hankali kuma na nawa. Ainad'e da raina muku hankali. Tunda nace muku baizo ba aisaiku ba wandanku iska ku qara gaba.

Wane ma rainin hankali ne wannan zaku shigomin gida ina matar Aure kanku tsaye batare da sallama na baku izini ba. Haka dukar takoya muku. To Wallahi baku isa ku shiga ko'ina acikin gidana kucajemin shi ba.

Tunda wanda kuke nema nagaya muku baizo nan d'in ba.

Baku da hurumin daza ku shigarmin gida ina matar Aure mijina baya nan kuhau cajemin shi haka siddan ba..

Dan haka saiku qara gaba tunkan na kulla muku wani sharrin dazaku rasa aikinku dan kunsan ba wanda yakai mace iya sharri. Bare ni kuma da nake matar aure wacce kuka fad'oma cikin gida kamar wasu dabbobi. Taqarashe zancan nata da turo d'an kwalinta gaba alamar duk rashin mutuncin da suke tafe dashi nata yafi nasu.. Dan tasha zuwa wajen y'an sanda ana artabu da ita akan ABDUL d'in.. Sam ZAINAB bata tsoran y'an sanda.

 

Da matuqar b'acin rai sukace mata haka tace.. Tace haka tace!!!

Rai b'ace suka ficce daga gidan suna masu cewa wallahi saidai in kwana zaiyi agidan amma indai zai fito suna nan suna jiransa akofar gidan nata..

Jan tsaki tayi da cewa.. "Aikin banza.. Tana fad'in hakan ta koma falanta da zama kan kujera mecin mutum biyu tana meci gaba da cewa.. Wato shi ABDUL bazai dena jawoma kansa magana ba ko. Wai har sai yaushe zai dena abubuwan nan ne..

Kai amma mama Saude tacuci rayuwarsa. D'aga hannunta sama tayi🤲🏻 daci gaba da cewa.

 Ina rokwanka ALLAH dakayi gaggawar warware Wannan kullin. Kaifa kace muroqeka zaka biya mana buqatunmu. Gashi dare da rana aikina kenan wajan rokwanka kan way'annan al'amuran😭..

 

  ABDUL d'in dake inda yake b'oye fittowa yayi da nufota yana cewa.. "Kici gaba dayi min addu'a MY AUNTY insha Allah zan zama yanda kike so.

  Kallansa tayi a d'an tsorace dan bata san da gaske yazo gidan ba.. Taja numfashi da cewa. "Wai dama da gaske kashigo ne ban sani ba..

"Eh. Har nayi miki sallama naji shuru alamar kina kitchen.

"ABDUL kama kanka fad'a kadena aikata abubuwan nan dan Allah.

  "AUNTY zan dena insha Allah..

"Toh yanxu gayamin meya faru suka biyoka. "Kawai AUNTY kishare. "Idan naqi sharewa fah. Wai har sai yaushe zaka gane raina na mugun b'aci idan naga ka aikata wani abu wanda akema kallan Allah wadai. Har sai yaushe zaka gane ina jin ciwo araina idan naga ankawo qararka ko anzo da niyar kamaka.

   Kallanta ABDUL yayi cikin wani hali yace.. "Nasan kina jin b'acin ran dajin ciwo aranki MY AUNTY. Amma nima ina iya qoqarina wajen Ganin ban baki kunya ba. Kuma nasan kema kinsan da hakan..

Wata shegiyar harara ZAINAB ta galla masa da cewa.. "Wane qoqari kakeyi ABDUL. K'ok'arin ba'a cikakken sati sai anzo nemanka. Koko qoqarin qara qirqiran tantiranci.😡

Shuru yayi mata..

Ganin hakan sai yasata jan numfashi da tashi taje ta duba abincinta tadawo kamar zatayi kuka taci gaba da cewa.. Dan Allah Dan Annabi ABDUL kaji tausayina ni me qaunarka. Ka duba qaunar da nake maka kadena jawoma kanka magana..

  Kawar da kallansa daga gareta yayi da cewa. "Toh.

"Yauwa ABDUL kokai fah.

Yanxu bani labarin me yasa suke nemanka..

  "AUNTY kinsan bana gujema hukuma akan duk wani lefi da nasan bani na aikata ba.

"Kana nufin yanxuma kai ka aikata lefin kenan.

 D'aga mata kai yayi akunyace..

Murmushin yaqe ZAINAB tayi dacigaba da cewa.. Toh ina jinka meya faru..

   "Wani Alhaji ne yazo wucce wajen majalisarnu shine fa ya wani fitto yana zaginmu wai y'an iskan yara marasa tarbiya iyayenmu basu iya aihuwa ba. Tunda suka haifa y'an daba y'an wiwi way'anda basu san darajar na gaba dasu ba. Kawai AUNTY ki share dan yayi mana zagin cin mutunci. Kinsan kuma ni bazan iya jurewa ba. Musamman danaga ba abinda muka masa haka kawai ya fitto ya fara b'arar mana da kalamai.. Dan haka ina tashi na d'aga Addata da niyar sauke mai aka dan ya San dasuwa yake. Amma sai Allah ya temakesa ya kauce nasamesa a kafad'a. Yankan bai wani shigesa ba. Dan haka na qara d'aga sandar na sauke mai a damatsan hannunsa. Nanma naga bata shigesa ba. Saina qara d'agawa da niyar nayi mai me gabaki d'aya. Sai Allah ya temakesa abokan nawa sukace in barsa haka saboda yarigada ya sume MY AUNTY...

Shine fa muka tafi muka barsa agun... Toh da alama jama'a sun gammu ne shiyasa yanxu da muke kan hanya dan zuwa duba AMEER jami'an tsoran sukaso Ram damu. Sai kuma muka ankare dasu. Hakan yasa muka watse ni nayo nan

Jan numfashi ZAINAB tare da girgiza kanta hawaye ya zubo mata. Aduk duniya ba macen datake jin tsanarta kamar Yayarta Saude mahaifiyar ABDUL d'in..

Dan duk itace tajama ABDUL d'in wannan matsalar.

ABDUL da ko jini yagani ajikin mutum yana zuba hankalinsa tashi yake. Amma yanzu da kansa yake yankan mutum har yazo yana fad'a ba wani jin komai aransa..

 

AUNTY kidena kuka nasan amin da ciwo ace yau naka ya lalace.. AUNTY nima bansan ya akayi nazama haka ba. AUNTY ina tashi natsinci kaina cikin wannan bala'in. Kina dai gani duk da iskancina bana wasa da ibada.. Kuma rokwan Allah nake kan ya dawo dani daidai yanda nake da danutsuwa dan kawai naga farin cikinki... ABDUL yakai qershen zancen nasa da damuwa akan fuskarsa..

 

Goge fuskarta ZAINAB tayi dacewa.. "Nadena ABDUL, Kuma nasan duk abinda kakeyi badasan ranka kake ba.

Nasan kasan baka kyautawa.

Nidai fatana kadinga ragewa kadena kodan kaba maqiyanka kunya..

Akan idona kwanaki Hajjiya Kakah taso yimaka aure da yaran dangi amma fur iyayensu sukaqi saboda wannan halin da kake ciki. Kaga da ace kai nutsattsene ba iyayen da zasu qika. Saboda katara komai da ƴa mace take buqata agun d'a namiji...

 

Kallanta ABDUL yayi da tab'e baki yace.. "Itama Hajjiya Kakah da rikici. Banda haka miye nawani yimin aure ina qaramin Yaro haka, tukunna mah. Inkai matar ina.🤔

Kai wani aikin sai tsofaffi.

 

Ita dai ZAINAB shuru tamai. Danta fuskanci sam baisan meyake faruwa akan batun da ita tasani na yanda Hajjiya Kakah tagaya mata wai asirine yake d'awainiya dashi ba..

 

Tashi tayi taje ta sauke abincinta da zubomai tana mai cewa... "Kaga mutuniyarka nayi wato shinkafa da miya da salat...

  "Aunty nifa bazanci ba!!! harsai kingaya min dalilin dayasa Hajjiya kaka taso yimin aure batare da sanina ba.. Kumama wai acikin dangi. Dangin da take da tabbacin basu sona.

  "Haba ABDUL abinda nasani Shifa nagayama. Zanqi gaya maka wani batu ne wanda ya dace kasani... Ko kad'an bansan wani dalilinta ba..

"Nayarda saidai kinsan bana cin abincin gidanki.

" Yauwa meyasa baka san cin abincin gidana. Tunda aka kawoni daqer kakesan ruwan gidana.

    "Kwantar da hankalinki bafa wani abu bane kawai naga mijin naki ne d'an rainin hankali ne. Saiya dingama mutane wani kallo haka haka. Kamar wani abu nake zuwa yimasa agida..

Wallahi kija masa kunne yadena yimin wannan d'an iskan kallan idan ya ganni dake.. Idan ba haka ba toh..

   "Idan ba haka ba tome😳... ZAINAB tafad'i atsorace.. Dan bata san iskancin ABDUL d'in ya tab'a mijinta dan tasan sarai idan yace zaiyima mutum abu Wallahi saiyayi hankalinsa yake kwantawa...

    "Idan ba haka ba wallahi zan yanke masa kunne d'aya..

Musamman idan ya qara dukanki shima saina nad'a masa na jaki Wallahi. Haka kawai Dan iskanci saiya dinga garoki gida cikin dare kamar wata taya...

  "Ba garoni yake ba nice nake zuwa dan ganin damata. Wallahi Salisu bai tab'a cewa naje gidanmu.. Sannan dan Allah bani san katab'amin lafiyar miji. Dan wallahi idan naga kunansa a yanke narantse saina sab'a maka. Sai nayi maka abinda baka tab'a tunani ba.

Saboda kasan ina mutuwar san mijina.. ABDUL ina qaunar mijina kasan sarai ban iya so ba. Haka ban iya qin abu ba.

Karka aikatama mijina wani abun dazaisa naqika..

   "Wallahi kozaki mutu idan ya aikata ba dai dai ba agabana saina mishi hukunci daidai da abunda yayi..

  ZAINAB najin hakan tasaka kuka wiwi. Aiko yana ganin hakan yaci gaba da cewa kawai AUNTY ZAINAB ki matse. Najenye tunda kina san abinki. Amma wallahi kija masa kunne yadena yimin wannan kallan iskancin

   Sauke ajiyar zuciya ZAINAB tayi da sakin murmushi tace. "Yau ce ranah tafarko danaga kafara sauke abu idan kad'auka da zafi. "Eh yanxun ma dan naga kukanki ne.. "To yanxu kabi ta k'ofar baya kaficce daga gidan nan tunkan suqara shigowa. Dan kasan yau asabar Salisu yana dawowa iyanxu yayi wanka ya yayi gidansu daga nan ya wucce yawan nasa na fama.

 kuma kasan yana ganinsu zaune kofar gida ce musu zaiyi sushigo su caje gidan kasan tsoran y'an sanda yake ba d'an kad'an ba..

Tashi ABDUL yayi da murmushi yana cewa. "Sai AUNTYNA takaina.. Har abada bazan mance qaunar da kikemin ba. Insha Allah shekaru masu zuwa idan nadena wannan abubuwan nayi Aure sunan y'ata tafari AUNTY ZAINAB 😃..

Murmushi tayi da cewa "Allah  ya kaimu lokacin ina maraba da zuwan little zainab.. Tana fad'in hakan ne tana bud'e masa wata k'ofarta tabaya wacce zata sadasa da layin nasu cikin sauqi basai yayi wani zagaye ba..

Ficce yayi yana tafiya irinta gogaggun tantirai d'innan.

Murmushi kawai tayi da kulle kofar tadawo falanta da soma cin abincin data zubomai tana zancen zuci dayi mai fatan alkairi arayuwarsa..

 

Can kuma saita fara tunanin karfa yayar tata tayi abinda tasaba yimai idan y'an sanda na nemansa..😳

Aiko nan tafara kallan agogo tana Allah Allah mijin nata ya dawo tayi gidan nasu...

 

 

®🔳◾◼official Auntyn Luv.💋

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.**.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*🤱🏻¸* *.¸¸.**.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 3

 

Can taga kodai tad'auki gyalanta taje ne. Ita Wallahi bata san abinda zai dinga kai ABDUL hannun folisawa. Dan haka d'aukar wayarta tayi takira mijin nata tagayamai yayi sauri ya dawo gida ba lafiya.. 😂 dan imba haka tace mai ba zabai dawo ba..

 

ABDUL ko yana shiga gidan nasu shashin  Hajjiya Kakah yayi. Aiko tana ganinsa tarufesa da fad'a tana me cewa.. Me kuma yanxu yayi y'an sanda sukazo nemansa a gaggauce..

Murmushi yayi mata da fad'a mata komai daya faru sam ABDUL bai iya b'oye abu ba. Idan dai katambayesa gaskiya zai gaya maka babu wani kunbiya kunbiya..

 

  "Ai shikenan. Ka kyauta. Kaidai kam Allah yayi wadaranka. Shegen Yaro me jaye kayen masifa da bala'i. Ahaka zaka qare rayuwarka da yawan b'el b'el. Yawan shaye shaye da aiki irin na y'an daban. Da rayuwa irinta qaskantattu.. Mama Saude Mahaifiyarsa ce me wannan furucin dan dama taga shigowarsa shine tabiyo bayansa taji me zai gayama Hajjiya Kakah. Kamar yanda idan ya aikata wani abun take biyosa ta qare masa tanadi.

 

Idan da sabo Hajjiya Kakah da jama'ar gidan sunyi sabo da mugayen kalaman da mama Saude take gayama ABDUL, sam ABDUL bai tab'a ganin ranar da mahaifiyar tasa tafad'i alkairi akansa ba.

Kuma idan zata mishi zagin duniyar nan da kalamai na b'acin rai ABDUL baya tab'a bud'e baki yayi mata wani magana ko wani kwun kwuni..

  Dan shi gaisuwa ce kawai take had'asa da ita. Idan ta amsa ya wucceta idan bata amsa bama ya wucceta..

 

Ran Hajjiya Kakah ya b'aci kamar yanda ako da yaushe ranta yake b'aci idan mama Sauden tayima ABDUL mugayen maganganu na qara tab'arb'arewar rayuwa.

 Dan haka afusace tace da ita... "Amma ko ke Saude Allah yayi wadaran baqin halinki.. Anya kuwa ke kika haifi ABDUL da kike jifansa da mugayen maganganu🤔. Ni wannan abu naban ammaki dan ban tab'a ganin muguwar uwa irinki ba..

   "Ai dama haka zakice mana Hajjiya Kakah. Wannan d'an bura'uban Yaro ne. In banda jaye jayen magana ba abinda ya iya yi. Sannan idan nazo ina yi masa fad'a kibi kihauni da bala'i.. Toh wallahi kamar yanda nasaba saina kira numbar y'an sandan nagaya musu gashi ya dawo yana gida suzo su kamasa matsiyaci kawai.. Mama Sauden takatse Hajjiya Kakah da fad'in hakan tana me warga hannaye gefe da gefe irin na mafad'aciyar mace nan. Sannan ta tazaro wayarta daga rigar mama takira numbar y'an sandan da sukaje gidan ZAINAB d'azu. Dama idan hakan ta kasance tana da numbarsu..  Nanko tace dasu ga ABDUL d'in ya dawo gida suzo su kamasa suci ubansa da kyau..

 

Nan mutanan gidan da suka firfito jin abinda yake wakana kamar yanda idan hakan tafara sukeyi. Nan suka rangad'a bud'a da sheqewa da dariya suna masu cewa.. "Sai Mama Saude.. Aikinki na kyau. Irinki jama'a suke so mace me danqa d'anta ga hukuma..

Sai suka kalli ABDUL Wanda dama idan hakan tafaru baya nuna komai ko ajikinsa🤷🏻 dan yasaba da baqin halin uwar tasa.. Kuma ko ana ha maza ha mata yasan AUNTYNSA ZAINAB ko AMEER ko babansa ko Hajjiya Kakah ko maman AMEER zasu fito dashi.😄. Kai abokansu ma bazasu iya zama batare dasun fito dashi ba...

 

Nan suka qaremai kallo da cewa Kaidai ABDUL kana sha'aninka. Dan koka aikata lefi ana fito dakai aikai d'an gatan ZAINAB da Hajjiya Kakah ne. Banda kai wazasuma hakan..

 

"Eh... Ku fad'i kanku tsaye ku qara da wayyo. Idan zai shiga sau d'ari zamu fitto dashi sau d'ari..

  Nan gabaki d'ayansu suka juyo da kallansu game basu amsar.. Sunsan sarai sai ZAINAB itace me basu amsa daidai da kalamansu.

 

Ta watsa musu wani mugun kallo hannayenta riqe da qugunta ta kalli yayar tata da wani matsiyacin kallo na nuna tsantsar tsana. Kana tacigaba da cewa...

Akwai ranar da nadamar duniya zata saukar miki akan baqin halin da kike nunama ABDUL; kuma ranar bazata tab'a amfanarki ba. Dan alokacin lokaci ya rigada ya qure miki.. Idan har ina raye ni dakaina zan hana ABDUL yafe miki...

Da sauri ABDUL ya kalli ZAINAB da cewa.. "AUNTY Mahaifiyata ce fah..😳

  Kowa agun sanda ya kallesa..

ZAINAB tayi murmushin yaqe da cewa... "Eh. Mahaifiyarka ce. Amma ni kuma ai yayata ce..

Kana da damar da zaka kanani fad'in mata kalaman danayi niya ne..

  "aa kawai dai gani nayi koda tayi min abinda yafi hakan zan iya yafe mata.

Murmushin yaqen ZAINAB taqara yi da cewa.. "Awannan ranah na tabbatar bazaka tab'a yafe mata ba musamman idan nace maka karka yafe matan....

Zaiyi magana cikin sauri da fusata Mama Saude tace.. "ALLAH ya tsareni da zuwan wannan ranah. Har abada bazan tab'a Neman gafarar ABDUL ba.. Dan banga uwar uban abinda nayi masa Wanda zaisa namemi yafiyarsa ba..

 Kaji min y'ar iskar yarinya ba dama kizo kiga ina zartar da hukunci akan ABDUL saiki hauni da magana kamar wata sa'arki.. Wallahi kishiga taitayinki. Kinsan dai banda uwarmu haihuwa tazo mata da Hutu kinsan ke saidai kizo aqanwata ta shidda..

Kan ZAINAB tabata amsa saiga y'an sandar nan sun iso gidan da Farin ciki.

Ba b'ata lokaci suka tasa qeyar ABDUL suna masu godema Mama Sauden da jinjina mata.. Ita ko sai washare baki takeyi irin tayi abinda ranta keso..

   ZAINAB ta qara yimata kallan tsana taja tsaki da shigewa falan Hajjiya Kakah ta banko ƙofar falan a fusace. Ji kake garam..

Nan mutan gidan suka sheqe da dariya harda tafawa. Kana sai kowa ta koma shashinta..

 

Mama Saude ko zuwa wajen window na Hajjiya Kakah tayi ta lab'e kamar yanda tasaba atunaninta ko ZAINAB zata gayama Hajjiya Kakah wannan sirrin nata..

 

 

 

 

AMEER na zaune kan dining na falan Dadynsa yana cin abinci. Sai wani abokinsu yakirasa ya shaida masa y'an sanda sun tafi da ABDUL fah..

Nan AMEER ya furzar da abincin dake bakinsa ya tashi jikinsa na rawa yahau tambayar me kuma ABDUL d'in yayi..

Nan abokin nasu ya kwashe komai ya gaya masa.

Aiko sai AMEER yayi jifa da wayarsa yana me kutuntuma ashar. Fad'i yake.. "Wallahi qarya ne bazai yuhu ba.

Akan wane dalili mutumin zai fito ya zagesu Sannan a kullemin ABDUL wallahi alhajin nan ya jama kansa bala'i.. Sai munje har gidan munyi mai b'alli b'alli..

 

A rikice momynsa da Dady suka tashi daga kan kujerar da suke tare da qarasowa wajensa suna masu tambayarsa me kuma ya faru..

 

Nan cikin raini ya kashe komai ya gaya musu..

 

  "Toh bani san tashin hankali. Kawai zansan yanda za'ayi ABDUL d'in ya fito..

Amma bani san kaje gidan alhajin ka dad'a jawo mana wata fitinar. Dadynsa ya fad'i hakan cikin damuwa. Yana tuna tantiranci irin na ABDUL da AMEER...

  Kallan raini AMEER d'in yama Dadyn nasa da cewa.. "Kasan ya tab'o manyan yara. Dan haka wallahi saina hukuntashi.. Kaima kasan baka isa hanani aikata abinda nace zanyi ba.. Yana fad'in hakan ya d'auki wayarsa da ficcewa daga falan zuwa cikin motarsa yana me neman numbar ZAINAB. AUNTYN su

 

Suko da kallo sukabi AMEER d'in

Momynsa tace. "Kasan AMEER zai aikata abinda yace.. Dan haka ka hanzarta kaje ka fidda ABDUL d'in kasan shine kad'ai zai iya gayama AMEER yabar abinda zaiyi agidan Alhajin ya kuma barin.. Bacin haka kasan taurin kan AMEER ba Wanda ya isa dashi.

   Jan numfashi Dadyn yayi cikin tausayin kansu. Kullum acikin tashin hankali suke tunda AMEER yayi wayo kullum cikin jamusu magana yake. Kuma basu isa dashi ba. Duk da cewar suna iya qoqarinsu na ganin sun bashi hakk'insa Wanda ya rataya akansu.

    

    "Kumafa haka ne. Dadyn ya fad'i hakan da saurin ficcewa daga falan..

Ita kuma momyn ta koma kan kujeta tare da godema Allah da qaddarar basu AMEER d'in da yayi matsayin d'a..

   Ahaka Abida tafito daga d'akinta tasameta dan dama tana sallah ne lokacin amma taji komai daya wakana tsakaninsu da yayan nata..

Ita dai bata san abinda yakeyi. Shiyasa sam bata shiri dashi.. Amma tarasa dalilin da yasa take san ABDUL, dan indai akansa AMEER yake hauka bata damuwa sosai..

 

 

 

Anan ko hawaye Hajjiya Kakah tashare dacema ZAINAB "Yanxu ya zamuyi kinga sun tafi dashi. Wallahi bani san ya kwana acan

Itama ZAINAB d'in share hawayen tayi da bata amsa wajen cewa... "Yanda muka saba haka zamuyi Hajjiya Kakah..

  Kiran wayar AMEER ne ya shigo wayarta tad'auka da cewa.. "AMEER sun tafi da ABDUL

Yace mata.. "Kwantar da hankalinki AUNTY ZAINAB yau d'innan zai fito.

Murmushi ZAINAB tayi dacewa "toh.. Kana takashe wayar..

 

 

"Yanxu zuwanka sitetion d'innan nawa D'AN KASADA...

Kallan DPOn folisawan ABDUL yayi da cewa.. "72 (Saba'in da biyu) ..

Kallansa sosai d'an sandan yayi da cewa.. "Kadai tuna anya baikai saba'in da uku ba..

  Wani daga cikin y'an sandan ne yace.. "Oga ina tayashi lissafi yau saba'in da biyun ne kamar yanda yace..

  "Ok kai shi ciki ka kulle yau dakwai cin kaza banqararriya..

  Dariya kowa acikinsu yayi kana sukayi ciki da ABDUL

Bayan sun kullesa sun dawo kallansu ogan nasu yayi daci gaba da cewa. "Anjima kad'an zakuga baban AMEER d'in nan yazo fito dashi. Kai yaran nan suna abinda suke so..

  Wani acikinsu ya amshe da cewa.. "Suna kam abinda suke so. Mudai fatanmu kakarb'i kud'i da yawa gunsa dan kasan konawa kacemai baka zaiyi.

  "Ai kuyi shuru kawai. Tunda nace muku yau akwai cin kaza ai akwai cin ne..😄😄

Dariya suka qara sawa daci gaba da gwalmar Dadyn AMEER..

   Ahaka yazo ya samesu kamar yandako sukayi harsashe..

Nan suka fara ciniki inda ogan nasu yake cewa.. "Gaskiya alhaji lefin da yaran nan ya aikata wannan karan me girma ne..

Dan Alhaji sabo yayima aika aika..

 

®🔳◾◼official Auntyn Luv.

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.*🙆🏻*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*🙆🏼¸* *.¸¸.**.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`•🤱🏻

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 4

 

Dadyn yace "Nidai yanxu koma miye kuyi hakuri. Yaran yanxu ne mun haifesu bamu haifi halinsu ba. Kuduba AMEER d'ana kuga duk danginmu ba'a tab'a yin TANTIRI kamarsa ba, ko labari banjiyo irin hakan ba, kowa yasan da zaman hali irin nawa dana mahaifiyarsa sam bai yiyo halin d'aya daga cikinmu ba, to kunga ai dole sai munayi muna kai zuciyarmu nesa, dan haka dan Allah kubani bellin ABDUL kamar yanda kuka saba,

"Zamu baka belinsa Alhaji kamar yanda muka saba baka dan mutuncinka da kuke gani, amma dan Allah kudinga qara jamusu kunne dan ba abu bane me kyau ace kullum kaine wajen y'an sanda. Yanxu zaka iya bamu dubu Hamsin, DPO ya fad'i hakan da tsaida Kallansa ga Dadyn AMEER d'in.

Shuru Dadyn AMEER yayi, can yace zan iya baku indai zaku bani shi.

Nan suka bashi takadda ya cike ya basu kud'in sannan suka sako ABDUL.

 

Dadyn yana tuqin motar tasa yana kallan ABDUL lokaci lokaci, Can dai ya faka motar tashi kan hanya ya tsaida kallan nasa kan Abdul d'in yace.. "Na rasa dalilin dayasa nake jin qaunarka cikin raina fiye da AMEER, ina sanka ABDUL sosai cikin raina, yauma bata canja zani ba zan wara rokwanka a karon babu adadi kan kagyara rayuwarka kozaka iya gyaramin rayuwar d'ana, hak'ik'a ina rokwan Allah kan ya kintsar daku amma nasan yana jina kuma lokaci ya bani nasan zai kintsar daku. Kasani nasani AMEER bayajin maganar kowa sai taka, idan mukace mai gashi baya kalla amma idan kai kace mai gashi yana kalla, nasani Allah ne ya d'oraka akansa dan ban tab'a ganin wanda AMEER yake so kamarka ba, da wannan nake rokwanka daka kintsu ko shima zai kintsu, AMEER yafika aikata abubuwan ashsha nasani' dan ina kallo ina kuma ji ana kawomin qara,  kai idan ka aika tsiya kana dawowa kayi nadama kayi dana sani, amma AMEER bayijin komai bare yayi nadama, kai Yaro ne kin tsattse wanda kazama abin kwatance kaf faɗin unguwar nan tamu, hankalina ya tashi matuqa danaga ka tab'arb'are lokaci d'aya, dan Allah ABDUL ka dawo da rayuwarka kamar tada dan nasamu yanda nake wajen d'ana.

 

Kallansa ABDUL yayi cikin jin tausayinsa hak'ik'a yana jin tausayin dattijan aransa yana san shi yana qaunarsa kamar yanda yake jin mahaifinsa aransa da kakarsa da kuma AUNTYNSA ZAINAB.

 

"Kaci gaba dayi mana addu'a Dady insha Allah zan gyara rayuwata albarkacin addu'ar da kuke mana, Wallahi bana jin dad'i abubuwan da muke aikatawa, na kanyi nadama ayayin dana aikata, Dady har kuka nakeyi cikin dare, na rasa mafari na rasa dalili na rasa meyasa hakan ta kasance dani,

Zan gyaru zan gyaru nayi maka aik'awari Dadyna.... ABDUL yakai qarshen zancensa da zubda hawaye.

Ai nan take qaunarsa taqara cafkar zuciyar Dadyn, nan ya rungumesa yana cewa. "Nagode my son Allah yayi muku alkarka dena hawaye,  nasan zaka dawo yanda kake da, yanxu kira AMEER ka dakatar dashi zuwa gidan Alhajin daka yanka dan yace saiyaje yayimai aika aika.

 Zare jikinsa ABDUL yayi batare dayace komai ba yahau kiran number na AMEER' Yana d'auka Yace dashi.. "Dan uwa kashare batun zuwa gidan Alhajin nan pls, dan baqaramin b'arma nayi mai ba.

 

 

AMEER dake cikin motarsa bakin wani keb'abb'an shago yana jiran abokansu su fito daga shagwan dan sun shiga siya masu kayan maye ne. Sai kawai yaga kiran wayar ABDUL..

Nan ya d'auka bayan yaji abinda Abdul d'in yace mai sai yayi murmushi dacewa.. "Saifa naje dan yasan suwa ya tsaya yana zagi.

ABDUL yaja numfashi da cewa. "Tunda nace maka kashare ka share mana

"Na share d'an uwa.

"Yauwa to yanxu kana ina.

"Ina wajen shagwan Ali nasa su Abba tab'are su siya mana harka.

"Yayi, yanzu ina kan hanyata tazuwa gida kasameni cikin d'akina..

"Ok babu matsala sai munxo.

 

Sai ABDUL ya kashe wayar da kallan Dady yace. "Komai ya wucce Dady, bashi ba zuwa gidan, ka kwantar da hankalinka, "toh naji dad'i my son Allah yayi muku albarka, "ameen  ABDUL yace sai Dadyn yaja motar suka bar kan haryar.

 

Akofar gidan nasu Dadyn ya saukesa, Nanko ya shiga cikin gidan nasu dajin wani nishaɗi, irin yanxu akazo aka fitar dashi daga gidan yanxu kuma aka dawo dashi.

 

Direct d'akin Hajjiya Kakah yayi, nanko yaganta ita da ZAINAB sunyi jugum amma suna ganinsa nan suka saki fara'a ZAINAB tatashi da sauri takama hannunsa.... Saidai nan take tayi saurin sake hannun nasa, shima cikin tsoro yajanye hannun nasa harda b'oyesa a bayansa.

ZAINAB tace "Jikinka  shocking yakeyi ABDUL.

 Murmushi yayi da cewa.  "aa Aunty nakine yake shocking d'in, dan daga jikinki ya fito.

Nan ZAINAB tahau kallan jikinta atsorace tana dube dube da cewa "dan Allah da gaske kakeyi, pls karka tsoratar dani.

Murmushi ya qarayi da faɗin. "Toh jeki tab'a Hajjiya Kakah mugani.

Nan tatab'a Hajjiya Kakah amma bataji komai ba, hakan ne yasata sakin ajiyar zuciya ta hararesa da cewa, "kasan Allah na d'auka da gaske kakeyi,

Murmushi dai ya qara sakar mata da basu labarin Dadyn AMEER ne ya fito dashi, Nanko suka dad'a yimai nasiha ya nuna yajisu dayin shashinsa' mama Saude ta sauke labulan windanta zuciyarta cike da dakaicin yanda ana kamasa yake fitowa, kwafa ta iya yi kawai dan ba yanda zatayi..

 

Shiko ABDUL bayan ya shiga d'akin nasa fad'awa kan katifarsa yayi Wanda take yashe a qasa kan kafet, d'akin natsaf dashi irin na mazaje masu tsafta. Ba komai a d'akin daga katifar sai kayan kallo sai durowa sai tarin littattafan addini dana turawa komai dai a kintse tsaf gwanin ban sha'awa. Kafet d'innan tas dashi sai tashin kamshin d'aki yake..

Nan yaja wayarsa ya bud'e data dan yaga wata wainar ake toyawa a yanar gizo, saidai bai kaiga nisa a dube duben nasa ba' wani wan mahaifinsa me suna Baba Shehu mafad'ici, suna kiransa da Baba. Nan ya banko ƙofar ABDUL d'in afusace kamar zai tashi sama yahau ce dashi... "Kai dai kam kai dai kam anyi yaran banza yaran hofi mara mutunci wanda baisan mutuncin mutane ba, yanxu ba wanda ya isa ya gaya maka kenan kaji, lokaci d'aya ka maida kanka d'an iska d'an bura'uba me shaye shaye tantiri, angaya ma yanxu rayuwar dakasa agaba rayuwace me kyau, kabi ka raina kowa baka ganin kowa da gashi dan tsabar tantirancewa, to wallahi bari kaji' nagaji dajin magana akanka atareni kan hanya ana gayamin, duk randa kaqara aikata wani abu Wallahi saika bar gidan nan dan ba gidan ubanka bane gidan ubanmu ne, cewa yayi kowa ya yanka ya gida babamu yayi ba bare kace gidan ubanka ne. Idan ka gagari kowa ni bazaka gagareni ba.  Yana faɗin hakan ya juya ya tafi afusacen yana meci gaba da surutan takaici.

 

Cije bakinsa ABDUL yayi cikin b'acin rai yake cewa a bayyane.. "Ammafa mutumin nan ya raina ni, ya dace na gyara tunaninsa dan yasan dawa yake, yasan ABDUL d'in daya sani da bashi bane yanzu.. Yana zuwa nan a zancensa yayi shuru yana tunanin wane hukunci ya dace yayi masa dan yasan TANTIRANCINSA ba irin na yara qanana bane.🤔..

 

 

By AUNTYN LUV💋

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.**.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*🤱🏻¸* *.¸¸.**.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 5

 

Yana cikin tunanin ne AMEER ya shigo shi da wasu abokansu biyu..

"D'an uwa naso naje na daddatsa alhajin nan Wallahi.. AMEER ya fad'i hakan yana me kwanciya kan katifar ABDUL d'in.

"Kawai ka share d'an uwa idan halinsa ne zai sake mana wata ranah ai. Ni yanzu Kasan waye nake san nayima b'alli b'alli... ABDUL yakai qarshen zancensa da maida hankalinsa gabaki d'aya ga AMEER.

 Murmushi AMEER yayi da cewa.. "aa saika fad'a.

"Wannan yayan baban nawa mana Baba Shehu.

Wallahi AMEER yau ina san namai b'alli b'alli yanda idan na had'a ido dashi saiya sunkuyar da kansa.

  Dariya abokan nasu sukayi har suna had'a baki wajen cewa. "Ai dama ya dace kayimai tun da dad'ewa. Idan mukayi duba da yanda yake shiga maka hanci da duqunqune. ya dace ka facoshi dan kagyara tunaninsa😀..

   Murmushin mugunta AMEER yayi da cewa.. "Kuje ku sace mai shi kukaisa d'akin tsaro dan dama ni haushinsa nake ji.

ABDUL yace. "Hakan yayi sosai. Maza kuje dan yau ina san ya gane shayi ruwa ne...

Aiko ba musu abokan nasu suka ficce dan aiwatar da abinda sukace masu.

   Nan ABDUL da AMEER suka dinga hirarsu irinta abokai irinsu. Zasu sha kayan maye ne ABDUL yaji ankira sallar la'asar dan haka da qarfi da yaji ya hana AMEER shan kayan mayen yace sai sunje sunyi sallah..

 

Jama'a dadama suna mamakin TANTIRANCIN ABDUL.. Dan duk tantirancinsa baya wasa da sallah. Dashi ake sallah a masallaci.

Idan kaganshi da AMEER a masallacin to dama katabbatar shine ya saka AMEER d'in agaba dan shima yayi sallar akan lokaci..

 

AMEER yafi ganewa tarukus sallat.

Ya had'a Azahar da la'asar magrib i'sha.

 Toh yanxu dai ya d'an fara ragewa.  Saboda d'orasa kan hanya da ABDUL yake..

 

Bayan an idar da sallah abokan nasu suka sanar dasu kan sunfa kama Baba Shehun. Yana can d'akin tsaron nasu.

Toh ABDUL yace musu kana suka koma d'akin ABDUL d'in suka d'an maki kayan shaye shayen nasu suka b'ilgire...

  Basu suka tashi ba sai lokacin sallar magrib.

 

 

 

Qarfe taran dare ABDUL ya nufi d'akin tsaro.. D'akin tsaro wani d'aki ne da AMEER ya ware musu nan cikin gidansu ta ƙofar baya..

Anan suke hukunta mutanan da suke musu shishshigi cikin al'amuransu...

Suna shiga da mutum cikin d'akin ne bayan sun fitar dashi daga hayyacinsa.

Haka lokacin da zasu fitta dakai nan ma saisun fitar dakai daga hayyacinka. Dankarka gane inda aka kawoka..

 

Ahankali AMEER ya bud'e d'akin da shiga cikinsa.

Baba Shehu ne zaune d'aure jikin wata kujera anrufe idansa da wani yadi. Sai mutsul mutsul yake alamar yana san kunce kansa.

 

Murmushi ABDUL yayi da qarasowa garesa ya  kunce mai yadin da suka d'aure mai idon.

Aiko nan Baba Shehu ya kalli ABDUL da mamaki yana me qarema d'akin kallo.. Tas d'akin yake. dan har da gado da kayan kallo da toilet aciki. d'akin dai yayi kamar na ajiye baqi..

Shidai yasan bayan ya gama zagin ABDUL kasuwa ya nufa. Saidai yana kan hanyarsa ta dawowa ne ya karyo kwanar layinsu dake wajen ba cukowar mutane sai kawai yaji an makesa aka. Toh shine bai tashi tsintar kansa ba sai anan ido lullub'e.

 

Da qarin mamaki yace.. "Kai dan ubaka me nakeyi anan. Waya kawoni nan. Me zaka min nan d'in....

   Janyo wata kujera ABDUL yayi da wata zanbad'ediyar dodunarsa a hannu ya zauna yana me kallan Baba Shehun yace.. "Nagane kai idan katashi tambayar mutum baka masa tambaya d'aya saika jera mai uku masu ma'ana d'aya..

  Amsar d'aya ce.👌🏻 kawai nasa yara sun kawo min kai nan ne dan in gayama fad'anka gareni yayi yawa..

    Cikin mamaki Baba Shehu yace "Ni zaka nunama TANTIRANCI Abdullahi. Ni wan mahaifinka wanda muka fito ciki d'aya. Ashe TANTIRANCIN naka ya shahara haka ban sani ba.

 

Tashi ABDUL yayi da fara tsula mishi bulalar nan🤔 . da farko yaso nuna jarumta irinta iyaye. Daga bisani kuma dayaga bazai iya jurewa ba kawai sai yahau ihu yana neman temako amma ABDUL bai sarara masa ba..

  Fad'i yake Wallahi na tuba bazan qara yi maka fad'a bare zagi ba. dan Allah kayi hakuri...

Ina ABDUL yasaka aransa saiyayi masa lilis..

Dan haka ko saurararsa baiyi ba yaci gaba da zanesa yana mai ihu daneman d'oki..🤔

 

Gefe guda momyn AMEER dake falo suna hira sai taji kamar ana ihu.

Itafa tana yawan jin kukan mutane a gidan nata. Amma bata gane daga ina kukan yake fitowa.

Kallan AMEER tayi Wanda yake aikin murmushin aikin da ABDUL keyi. Tace "waini daga ina kukan nan yake fitowa ne. Lokaci lokaci ina yawan ji. Saidai bana gane daga inda yake fitowa.

Abida taja numfashi tace. "Nima ina yawan ji lokaci lokaci haka..

   " D'an d'aure fuska AMEER yayi cikin rashin ladabi yace. "Tayaya ni zan sani.

"Ai lura nayi kamar idan kana cikin gidan ne ko Abdul idan yana nan nake jiyo hakan.

  Shuru AMEER yayi. Tabbas tayi gaskiya. Dan haka tsarin nasu yake. Idan shine yake hukunta mutanan ABDUL zama yake dasu momyn yana d'auke hankakinsu da hira. Haka idan ABDUL d'in ne yake hukuncin shine yake zama kamar yanda yake tare dasu yanxu..

Ahankali yanxu yace da ita. "Ba mamaki ko makwaftammu ne. Amma nan gidan ina iyamu kenan waye zaizo yana mana kuka a gida..

  Momyn taja numfashi da cewa. "Ba mamaki kam ko hakan ne. to Allah ya kyauta.

Abida tace amiin..

 

 

Ko'ina na jikin Babah Shehu sanda ya zanu. Dan baqaramin duka ABDUL yayi masa ba.

Kuka kam babah Shehu yasha. Bai tab'a tunanin tantirancin ABDUL yakai haka ba. Nan take tsoranshi ya zagaye jinin jikinsa.

Kallo d'aya zakamai kasan saiya d'auki sati biyu yana jinyar kansa.

 

 ABDUL kiran AMEER yayi yace mishi ya gama mai b'alli b'allin. Dan haka ya fitto suyi gaba dan ana jiransu ne.

Shi kansa AMEER ya tsorata da dukan rashin mutuncin da ABDUL d'in yama babah shehun. Hakan ne ya tabbatar masa da cewa lalle lefin nashi bana yau bane ya dad'e yana tarasa...

Haka suka qara kullesa bayan sun d'irga masa ruwa daniyarsu na sai gobe zasu sakesa..

 

Direct gidan wani Alhaji sukayi. Wanda yake basu hudar ibilis ta maye suje su rabama mutanansa.

 

Yana ganinsu ya saki murmushi da cewa. "Saiku yarana. Nafara tunanin zan fara turaku Lagos kuna rabama manyan mutanan kayan namu.

   AMEER yayi murmushi bayan sun zauna kan kuje mecin mutum uku yace. "Aini banda matsala ko ina zaka turamu zan baka had'in kai Alhaji matuqar zaka saki bakin aljihu yanda nake so. Matsalar d'ayace shine ABDUL.

AMEER yakai qarshen zancen da kallan ABDUL wanda ya d'ora kafa d'aya kan d'aya yana me qarema falan kallo cikin wani salo kamar lokacin yasan falan..

   Alhajin yaja numfashi tabbas AMEER baida matsala ABDUL ne yake da matsalar. Dan idan yace bazaiyi abu ba. Toh bazai yi ba. Koda ko zaka sakar mishi bakin aljihu. Sam kud'i basa gaban ABDUL. Dan baya wani abu dasu.

Kasancewar baya huld'a da mata kamar yanda AMEER yakeyi.

Tara kud'insa kawai ABDUL yake a banki. Idan  ya fuskanci masu buqata saiyaje ya ciro ya basu.

Ko idan AMEER d'in yana da buqata ya basa.

Ko shi kansa idan yana san shiga kasuwa yama kansa shopping na kayan sawa da wasu al'amuran na rayuwa wanda bazai zama lalle mahaifinsa yayi masa ba.. Wannan shine kawai amfanin da kud'in sukema ABDUL.

 

Kallansa dakyau Alhajin yayi da cewa.. "Toh kaji abinda d'an uwanka AMEER yace' Allah yasa kaima kace min hakan.

  "Iya tsawan wane lokaci zamu d'auka a Lagos d'in. ABDUL ya fad'a cikin san sani.

"Eh bazaku wucce wata d'aya ba. Alhajin ya bashi amsa cikin tabbaci..

 

Tashi ABDUL yayi da d'aukar feroz dake kan table d'in gabansu yana cewa. "Babu matsala. Kawai muna buqatar kabamu miliyan d'aya. Mu raba. Idan yayi maka toh. Idan baiyi ba. Bana tunanin zamuje can. Yana zuwa nan a zancensa ya kalli AMEER daci gaba da cewa. Koya kagani d'an uwa..

  Jan numfashi AMEER yayi da cewa "Sosai hakan yayi...

Murmushi Alhajin yayi da fad'in. "Idan dan wannan ne babu damuwa. Zan iya baku fiyema da hakan. Idan har baku bani matsala ba..

 

Murmushi ABDUL da qarasawa kusa da Alhajin yace. "Bar batun samun matsala Alhaji, Dan bama kawo maka ita, Amma koda hakan tafaru wallahi saika bamu kud'inmu dan kasan ba kullum ake kwana a gado ba, ABDUL na fad'in hakan ya kalli AMEER damai alamar ya tashi su tafi, sannan ya ficce daga falan..

  Da kallo alhajin ya bishi. Gaskiya yaran ya had'u. Yana magana da izza. Babu tsoro ko shakko cikin idansa. Yana jin daɗin harka da yaran. Zai jure duk wani b'acin rai dazai fuskanta daga garesu. Dan ba qaramin samu yake dasu ba..

  Tashi AMEER yayi da Murmushi kan fuskarsa yana kallan Alhajin ganin yabi bayan ABDUL da kallo yace.. "ABDUL kenan ake gaya maka Alhaji. Sam bashi da tsora akan komai' kana dai gani na rigashi shiga  tantiranci amma yafini sanin yanda ake tafiya da irinku. Hmm yanxu dai Ina buqatar dubu ishirin' zan iya samu.

Murmushi Alhajin yayi dace masa.. "Zaka samu mana.

Nanya zuge wata jaka ya bashi dubu Ashirin d'in. Kana yabar falan zuwa cikin motarsu inda ABDUL yake..

 

Bayan ya shiga ABDUL yaja motar kallansa ABDUL d'in yayi da cewa. "Sanda ka karb'i wasu kud'i gunsa ko.

"Eh mana. Na hannuna ne bazasu kaini jin dad'in da nake san ji yau a club ba.

  "Yayi kyau hakan. Yanxu muhucce direct club d'inne ko akwai inda zamu.

 "aa mu wucce kawai kasan nayi fad'a da Amina bare muje na ganta..

Shuru ABDUL yayi mai dacigaba da tukin motar.

 

 

By AUNTYN LUV 💋

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.*🙆🏻*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆🏼*.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`•🤱🏻

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 6

 

 

RMC shine sunan club d'in da sukaje. Club ne wanda ya amsa sunansa. Club ne wanda sai d'an wane da wane ne suke iya zuwa wajen. Yaranmu yaran musulmai matasa yaran manyan masu kud'inmu su sukafi yawa awajen. Matan musulmammu basu da yawa. Haka bazaka tab'a bambance suwaye musulman a matan suwaye arnan amatan ba. Saboda duk shigarsu d'aya ne. Dan rigunan dake jikinsu iya mama kawai ya rufe musu. Sai wani d'an gajeran wando wanda ake kira da 3kwata. Babu tarbiya ga duk yaran matan da suke wajen. Dan kallo d'aya zaka musu kabasu suna da karuwai. Kawai KARUWANCI suke mazan na nuna musu tantiranci.

 

ABDUL baya kula mata ko kad'an. Sam y'a mace bata tab'a birgesa. Bai tab'a yima y'a mace kallo kallan sha'awa ba. Shidai barshi da TANTIRANCINSA yasha magungunan maye dasu kwaya yasha giya ya b'ingire nan yata makar bacci.

 

Amma banda AMEER. AMEER TANTIRANCI ne a iya sarrafa mace. Ya iya aikata zina masha'a kala kala da mata. sam wannan hali nashi yana ba ABDUL mamaki.

Yakan ce mishi kai baka gajiya da harka da mata ne. Ya kan bashi amsa da. Ai y'a mace ba abar gajiya bace. Halittace dan d'a namiji. Kaima dan baka tab'a jin mace bane shiyasa kake faɗin hakan. Watoh abokina kana da matsala da gabanka. Wallahi ABDUL baka da lafiya. Dalilina na faɗin hakan ko shine' idan mutum zai kana yana harka da mace akan idanka bakajin komai aranka. Sha'awa bata lullub'aka. Ya kamata kaje ka nemi magani. Idan baka zuwa nema ni zan nema maka.

ABDUL yakanyi murmushi yace da dashi. aa basai ka nema min ba. Dan abin ko sha'awa baya bani. Jin tsanar abin nake idan naga kana aikatawa. Ba mamaki gaba idan kayi aure ka fara aikata na sunna idan kazo bani labari naji sha'awan wannan cikin raina. Amma yanxu ba abinda zai sani neman magani ga cutar da bata dame ni ba.

Dariya AMEER yakeyi da zaran ABDUL ya bashi wannan amsar. Fad'i yake aransa ABDUL wawane tawajen wannan harkar. Dan acewarsa bai san rayuwa dakyau ba. Mata ai sunyi sosai arayuwa. Y'a mace wata abace wacce sai da ita namiji zai iya yin rayuwa...

 

Yauma bata canja zani ba kamar kullum. Suna isa shiga cikin club d'in sukayi. Saiga wasu mata biyu sukazo suka rungumi AMEER. Fad'i suke "wlcm sweetheart. Munyi missing naka. Nan ya qara jansu jikinsa yahau kissing nasu yana nuna musu shima yayi missing nasu fah.

AMEER danya kafa kai ga qirjin mace yana wasa dashi gaban y'an club d'in ba wani abu bane awajensa. Dan duk abinda yaga damar yi dasu akan idan jama'a yakeyi. basai ya bari sun keb'ance ba.

Duk clubs d'in da suke zuwa yana da matan da yake harka dasu.

 

San ABDUL suke. ƙaunarsa suke. san kasancewa dashi suke. Saboda shurunsa. Ajinsa. Iya kalamansa. Sanyin muryarsa. Kallansa. Wankan da yake d'auka. Ƙamshinsa.

Yafi AMEER sanin rayuwa. Inda ace shine da iskancin AMEER ba makawa har gida matan zasu dinga binsa. Dama ance kabar mutum shuru shuru..

 

ABDUL yasha drink da kayan shaye shaye kala kala

Bayan sun keb'ance cikin wani d'akin haya wajan bacci. Nanya b'ingire yata maka baccinsa. yayin da AMEER yaketa aikata masha'a da waƴannan mata.

Aqarshe dai sai kwana sukayi awajen. Dake ABDUL ya saba da sallah kan lokaci nan ana kiran sallar asuba ya bud'e idansa. Saidai yayi mummunan gani. Dan ganin AMEER yayi da waƴannan matan babu tufafi jikinsu ya wani rungumesu alamar sunyi sun gaji bacci yayi awannan gaba dasu. Sanda ABDUL ya rintse idansa shi dai bayi san wannan d'abi'a ta AMEER.

Tashi yayi da jan tsaki ya shiga toilet d'in d'akin ya tsaftace kansa da nufar masallacin da yake da tabbaci akwai awajen. Amma fa sanda yahau motarsu yaje can dan tsakaninsu da nisa.

Can wajen bakwai ya dawo still yanda ya barsu haka ya qara ganinsu.

Hakan yasa ya d'akama AMEER duka afusace yana cewa. "Dallah tashi kayi wankan sarki kayi sallah.

Da nauyin bacci a idan AMEER d'in ya kallesa da cewa. "Please kabarni zuwa 9 kaga ban wani samu bacci ba.

 

"Naga mene🙁. Dama ka tsaya kana aikata sab'an Allah wane bacci zakayi kan lokaci bare har kayi ibada kan lokaci.

Kaga ni gida zan tafi ga dubu goma nan nasan zata maka amfani.. ABDUL ya faɗi da wulga mishi kud'in ya d'auki kin motar tasu ya ficce yana hararar matan da suka tashi sanadin tashinsa da yayi.

"Gaskiya sweetheart ABDUL baiyi ba a rayuwa. D'aya daga cikin matan tafad'i hakan tana me qara shegewa jikin AMEER d'in. Murmushi yayi mata da cewa. "Barshi zaiyi nan gaba.

 

 

 

ABDUL ko yana shiga gidansu ganin y'an gidan yayi kaf ɗinsu zaune a tsakar gidan kowa yayi tagumi da nuna damuwa. Kamar anyi mutuwa agidan.

Ya kalli Hajjiya Kakah yana cewa. "Lafiya meya faru naga kamar anyi mutuwa agidan,

Jan numfashi tayi cike da damuwa tace "hmm kai dai bari. Ai Babanku ne Baba Shehu tun jiya daya ficce daga gidan nan ba'a qara ganinsa ba. Tun adaran da misalin qarfe goma sha d'aya ake ta nemansa amma shuru. Yanxu ma anyi duban duniya babushi babu dalilinsa. Andai kaima y'an sanda cigiyarsa. yanxu ma babanka yake cewa zaije gidan radio namma ya basu cigiyar..

  Tab'e baki AMEER yayi da kama hannunta yace. "Kwantar da hankalinki Hajjiya Kakah. Yanxu bari nayi wanka naje na nemo miki shi. Nayi alqawarin kayo yake zan kawo miki shi aduk halin da yake ciki.

Shafa kansa tayi cikin so da ƙauna tace. "Na gode maza jeka kayi d'an albarka.

Murmushi ya sakar mata da tashi yayi d'akinsa.

Mamansa taja tsaki da binshi da wata muguwar harara.

 

Bayan yayi wanka ya kintsa kansa da share d'akin nasa saiya saka turera sannan ya nufi gidansu AMEER d'akin tsaran nasu ya kunce Baba Shehun. Nan ko ya zube qasa agajiye. Fad'i yake. "Zansha ruwa. Zan sha ruwa ABDUL.

Murmushi ABDUL yayi da bashi ruwan.

Kallo d'aya zakama tsowan kasan ya zanu ya daku ya zama abin tausayi.

 Bayan ya gama shan ruwan nan yahau sambatu wajen cewa. "Nayi nadama Abdullahi nayi nadama. Bazan qara yi maka fad'a ba. Dan Allah dan soyayyarka da Annabi ka sauni ka fiddani daga mugun d'akin nan. Na tuba bazan sake shiga harkarka ba. Kayi duk abinda kaga zakayi. Wallahi bazan sake maka magana ba.

 

Murmushi dai ABDUL ya qara yimai da cewa. "Zan fiddakai yanxu saboda san da nakema Hajjiya Kakah. Amma ba cikin hayyacinka zan fiddakai ba. Sannan zan qara ja maka kunne kan batun shiga harkata. Wallahi idan kaqara shiga harkata sainayi maka abinda yafi wannan. Dan yanke maka kunne zanyi da karya maka qafa yanda bazaka tab'a muruwa ba.

  "Bazanma sake ba. Nidai dan Allah kafidda ni yunwa nake ji..

ABDUL na jin hakan ya wani daki qeyarsa nan ya sume. Saiya kira abokansa way'anda suka kawo maishi. yace suzo su fittar dashi.

 

Nanko baifi minti biyar ba suka zo suka fitta dashi ta k'ofar bayan. ABDUL na gaba suna binsa a baya. Ahaka har suka iso dashi cikin gidan nasu.

Nan jama'ar gidan sukayi kansu da salati ganin yanda suka kawosa baya hayyacinsa.

Tambayarsa suke a'ina ya samosa. Waye yayi mai wannan duka.

Sudai abokan tafiyarsu sukayi bayan sun diresa. Shiko ABDUL ce musu yayi akan titi ya gansa yanxu shine yasa suka d'aukosa.

Nan suka hau sheqa masa ruwa dan ya farfad'o.

ABDUL na ganin hakan yayi d'akinsa yana murmushin mugunta.

 

Dama da alwalarsa dan Allah nan ya tada sallar warha. Raka'a hud'u yake yi ya sallame ba mamaki ko shiyasa yake da nutsuwa duk da TANTIRANCI irin nasa..

Yana sallamewa ZAINAB ta shigo d'akin nasa da damuwa tace dashi. "Hmm kaga shegen dukan da akama Baba Shehu kuwa.

D'a mata kai ABDUL yayi.

Ta shagwab'e fuska daci gaba da cewa. Yanxu dai ya farfad'o har yana cin abinci. Anyi anyi dashi ya fad'i wanda yamai wannan duka amma yaqi. Nifa tun jiyan da suka gayamin ya b'ace nakasa bacci. Yanxu hankalina ya tashi danaga wannan aika aikan da aka mai.

  Murmushi ABDUL yayi da cewa. "Kawai AUNTY ki share. Dan idan ya qara shiga harkata narantse abinda zan masa saiyafi haka.

  Waro ido 😨 ZAINAB tayi cike da mamaki tace. "Yanxu dama kai ka b'oyesa kamai wannan shegen dukan.

"Eh' wani abu ne...

"Wani abu ne mana. Haba ABDUL wan mahaifinka ne fah. Bafa qaninsa bane. Wato abin naka qara gaba gaba yake ko.

  "aa kinga malama dakata.🏻 bafa wa'azi nanemi kiyimin ba. Yazo ya hauni da fad'a jiya kamar wani d'an cikinsa. Shine ni kuma nayi masa hukunci. Gayamin' shin hakan danayi yazama lefi. Idan ya zama lefi saiki gayamin🙁..

  Galla masa wata muguwar harara ZAINAB tayi da cewa "amma ko kaban mamaki. Iskanci hauka ne dazaka mai wannan dukan kamar kasamu d'anka.

  "Wato ZAINAB na lura kingama rainani. Karfa ki manta baifi shekaru biyu kika bani ba. Akan wane dalili zaki dinga hauni da fad'a kamar wani d'anki. Dallah malama fitanmin daga d'aki tunkan na mangareki. ABDUL ya katseta da faɗin hakan a fusace..

   Da qarin mamaki tace "Zama ka iya cewa komai ABDUL. Saidai duk lalacewa ni'ai qanwar mahaifiyarka ce. Haka kuma dole na gaya maka gaskiya. Wallahi babu tarbiya ga yaran dazai daki wan mahaifinsa.

 

  "Wato nine banda tarbiya.

"Nidai bance ba.

"Wallahi idan baki fitar min daga d'aki ba na rantse da Allah zan miki dukan tsiya. Dan ba kiranki nayi ba. Haka kawai zakizo ki wani hauni da fad'a kamar wani d'an..

 

Fitta ZAINAB tayi tana me girgiza kai. Ta sani tunda suka fara hakan yanxu tana biye masa za'a jisu. Duk da shak'uwar dake tsakaninsu da qaunar da sukema juna hakan baya hanasu kaurewa da fad'a. Musamman idan yayi abinda bai dace ba idan tazo tana masa fad'a nan suke kaurewa. Dan ABDUL ya tsani tamai fad'a. ganinsa bata kai ba. Tunda tsirarsu ba wani yawa bane. To data gane hakan sai take binsa da lallami. Idan har zatamai fad'an da lallami zai saurareta su wanye lafiya. Amma idan tace zatayi da zafi da kuma raini nan take ake jin kansu.

Damma mutanan gidan basu shiga harkar fad'an nasu. Dan ko sun shiga yanzu zasuji kunya.

 

D'akin Hajjiya Kakah tayi tana fad'i aranta. Gaskiya Yayarta ta cutar da ABDUL a rayuwa. Yaron daya tashi da nutsuwa nutsuwar da kowa yake kwatancensa. Amma lokaci d'aya ya juye ya koma TANTIRI.

Kuka sosai tadingayi a d'akin tana qara jin tsanar yayar tata aranta...

Hajjiya Kakah ko tunaninta kuka take kan dukan da akama Baba Shehu dan haka saita dinga rarrashinta..

 

Ya sani sarai sai tayi kuka a d'akin Hajjiya Kakah. Dan hakan takeyi aduk lokacin daya aikata wani abu tayi mai fad'a yahauta da nashi fad'an.. Dan haka saiyaja tsaki. Sam baya san ya dinga b'ata mata rai ko kad'an.

 Kai dole yaje ya bata hak'uri. Ya fad'i hakan a ransa batare daya tashi ba.

 

Itako bayan tagama kukanta dama da tana d'auke da matsalarta ta gidanta tana san sanar da Hajjiya Kakah.

Dan haka gyara zama tayi da cewa ma Hajjiya Kakan. "Kakah gaskiya nagaji da Auran Salisu. Dan abin nasa gaba gaba yake yi. Yanxu dawo min gida yakeyi yana me wankan tsarki. Na gama gane tsabar iskancin da yakeyi. Gashi ban ragesa da komai ba. Ina jin tsoran yaje ya jajib'o cuta yazo ya saka min. 

 

Jan numfashi Hajjiya Kakah tayi da cewa. "Kina da gaskiyà. Amma kafin nan ki qara saka mishi ido muga.

"Nifa na gaji ne.

"Waya gaya miki ana gajiya da Aure. Kije ki qara saka mishi ido idan kika qara tabbatar da zarginki sai kizo kinsan duk bazai gagara ba.

"Toh. ZAINAB tace mata.

Kan Hajjiya Kakan taqara magana saiga ABDUL ya shigo da zama kusa da Hajjiya Kakan ya kalli ZAINAB yace. "Auntyna kiyi hak'uri da sa'insar data shiga tsakaninmu d'azu. Sam bani san na dinga b'ata miki rai.

  Murmushi ZAINAB tayi dama tasan sai yazo ya bata hak'uri. Dan haka sai tace. "Kashare kawai dan komai ya wucce. fatana karka sake.

  "Zanyi qoqari sosai wajen ganin na danne zuciyata dazaran ya sake min.

 

  Hajjiya Kakah tace. "Magana akan me kuke ne.

"Bai shafeki ba Kakah ni kingama fitata. Ya bata amsa da murmushi ya ficce daga falan..

ZAINAB tayi murmushi ita dai tana san taga ABDUL ya dawo kamar da..

 

Wannan kenan.

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.*🙆🏻*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆🏼*.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`•🤱🏻

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 7

 

Tafiya suke cikin nutsuwa da karairaya irinta yara yaran mata masu aji daji da kansu. RAHMA da UMMA kenan me karatu. RAHMA suna kiranta da RAHEEMAT. UMMA kuma suna kiranta da UMMAKATI.

 

 Wani kaya ne a jikinsu wanda kallo d'aya zaka mai idan kai me tarbiya ne kayi Allah wadai da wannan kaya. Ankwan riga da siket sukayi ammafa d'inkin walak'antaccen d'inki ne. Ya matse jikinsu matuqa. Ya fidda musu da tsuraicinmu sosai abin gwanin ban sha'awa ga tantiran yara irinsu. Ga yara masu tarbiya ko abin babu kyan gani sam.

 

Wanda yayi musu d'inkin yayaye musu maya irin shomiyo back d'innan.  Siket d'in kuma ya matse musu tsaf tsaf daga qasa yayi musu wani tsagu wanda ya kusa zuwa musu cinya. Kan nan nasu yasha attach. Wato gashin duki. Anyi musu wani kitso dashi wanda kallo d'aya zakama kan nasu kasan wacce tayi musu kitsan ba qaramin kaya ta had'asu dashi ba.

Kafar nan tasu tasha sarqa irinta indiyawa d'auke da wasu takalma masu tsinin tsiya.

Wani figigin gyale ne suka yafa akan nasu hannunsu d'auke da y'ar fus.

Fuskar nan tasha fante fanten kwalliyar zamani.

Sai zuba qamshi suke me kwantar da zuciya.

  Kwata kwata yaran RAHEEMAT da UMMAKATI basaji  ko kad'an.

 

UMMAKATI ta kalli RAHEEMAT da cewa. "Mu tsaya anan gaskiya na gaji. Bara na kirasu na gaya musu su qaraso nan dan mun gaji.

   RAHEEMAT tace "nima da yanxu zance miki nagaji mu tsaya.

"Hello Alhaji muna kan layinsu Amal ku qaraso bazamu samu damar qarasowa inda kuke ba....

Daga can b'angaran akace mata. "Owkie gamu nan toh. Sai tace  "muna jira pls karku barmu kan hanya dan kuka wucce minti biyu wuccewa gida zamuyi dan dama a gajiye muke.. Tana fad'in hakan ta kashe wayar tata.

Dama akwai wani d'an dakali jikin wani gida inda suke tsayan. Dan haka sai suka zauna kan dakalin.

RAHEEMAT tace. "Musan yanda zamuyi mu cajesu maƙudai da yawa. "Tab ai basai kince ba. Ko kin manta muna da anko kusan 10 a gabammu, "Na d'auka kin manta ne.

"Yanxu RAHEEMAT yazamuyi da Alhaji tukur. Kinga ke yake so ke kuma kinqi bashi had'in kai, "Dallah kibar batunsa' wazaiyi wani harka dashi kalan yaje ya zubama mutane majina.😂

Dariya UMMAKATI ta kwashe da ita tace. Shegiya RAHEEMAT kina san abin hannunsa amma baki san abinda shi yake so.

Dan Allah gaya min. Nifa na kasa gane yanda kikeyi da maza basu d'anaki kike amshe kud'insu,

  Murmushi RAHEEMAT tayi da cewa. "Ai karatun ba'a b'oye nake yinsa ba. Bare kice ina b'oye miki wani abun. Akan idanki nake yin komai. Toh me kuma kike buƙatar sani.

Jan numfashi UMMAKATI tayi da fad'in. "Abin ne da d'aure.

Kai yake.

Kan RAHEEMAT tabata amsa saiga wata fitinanniyar mota ta parka gabansu. Wani alhaji ya fitto ak'alla zai kai shekara arba'in. Saidai kallo d'aya zaka mai kasan ya jiƙu da nera.

Ƙarasowa garesu yayi da murmushi yana cewa. "Yan mata adan gari. Idan babu ku babu gari. Idan kunyi yawa gari ya b'aci. Zaku iya shiga cikin mota mu zanta.

 Ba musu bayan sun kallesa da murmushi suka shige cikin motar. Sai shima ya koma cikin motar.

Su biyu ne dama. Dashi da wani da yake zaune a baya. To dama RAHMA bayan tashiga. Ita kuma UMMA ta shiga gaba. Shi kuma ya zauna wajensa na mazaunin direba.

 

RAHMA rungumar na bayan tayi tana cewa. "Nayi missing naka alhajina. Jiya fa har mafarkinka nayi.

Nan jibgegen mutumin data kira da Alhajin nata wanda shima zai iya kaiwa shekara arba'in d'in ya sakar mata murmushi da kiss gefan kuncinta yace mata. "Nima haka Baby. Da fatan yau dai zaki bani had'in kai.

Zare jikin tayi da Kallansa tace. "Mezai hana. Kawai kai dai kajira lokaci. "Ina nan ina jira Baby. Fatana dai yau nacimma burina.

"Karka damu zaka samu abinda kake so fiye da tunaninka. "toh Yanxu nawa kike buqata na baki dan nasan UMMA bazata buqaci kud'i ke kiƙi buƙata ba.

"Dubu Hamsin ne ba yawa Alhajina.

"Owkie. Nan ya zaro bandir d'in hamsin hamshin na dubu hamshin cikin ajjihunsa ya bata.

Tako karb'a a yangance.

Yayinda itama UMMA ta karb'e Hamsin d'in daga wajen nata gwanin na gabansu RAHMAN.

 

Sanda suka b'ata tunaninsu wajen shafe shafe sannan suka ficce daga motar dayi musu alqawarin cikin dare zasuxo club su had'e..

Shegun Alhazawan bada san ransu suka barsu ba. Dan yaran suna b'ata tunaninsu Sosai. Gashi yau har tsawan sati biyu kenan sun kasa cin galaba akansu. Sai tatsarsu suke kamar makilin😁.

 

Sun had'u dasu ne a bikin wani abokinsu daya Auri qawarsu Amal. Bikin daya wucce sati uku daya gabata

 

Sanda UMMAKATI ta tabbatar motar tasu tayi nisa saita kalli RAHEEMAT ta shege da dariya tace.. "Ko banza dai munci dubu d'ari  jikinsu a had'uwarmu dasu a sati uku kacal.👌🏻

RAHEEMAT tace. "Alamu sun nuna suna san nuna mana kud'i zallah. Dan musake dasu. Hmm zasu gane basu da wayo.

     "Nifa ban damu na bada kai komai ya faru ba. UMMAKATI tafad'i hakan tana me tusa kud'inta cikin y'ar fus tata. "Aike wawiya ce shiyasa. "Bana san iskanci fah RAHEEMAT..

"Toh kayi hak'uri.

Haka suna tafiya suna hira har suka iso unguwarsu layin zana. Layin d'an ƙarfalla suka shiga inda anan ne gidan iyayen nasu yake.

Makwaftan juna suke. dan gidansu manne yake da jikin juna.

Idan akace maka a gidajen suke saika rabka salati dan jin kansu yafi k'arfin kace anan suke.

Gidaje ne irin na da way'anda suka gaji ainun. Dake kunsan mutanan da akwai su da gini me inganci komun babunka gidanka zai ibi shekara da shekaru yana da kyensa. wannan dalilin ne yasa sudai gidajen basu fad'i ba amma suna buqatar kulawa.

 

Gidansu RAHMA babban gida ne wanda ya tara mutane da yawa ba gidan haya bane gidan dangi ne.

Dan jama'ar gidan suna da yawa.

Alhaji jamilu shike da mallakin gidan. Yana da mata hud'u kuma ko wacce tana da yara sama da biyar. RAHMA y'ar autace ga matarsa ta fari

Tana da yayu sama da goma sha biyar. Haka qanne ma.

Azahirin gaskiya saida RAHMA tazama budurwa itama tafad'a rashin ji. Itama ba'asan dalili ba.

RAHMA bata da kunya tunda tashiga wannan rashin jin. Bata ganin mutuncin yayunta maza da matan ko kad'an.

Ita dai idan bata shiga harkarka ba toh karka kuskura kashiga tata.

Gata qaramar yarinya. Amma sai rashin jin maganar tsiya. Sam RAHMA bata san fad'a. Idan yayunta zasu mata fad'a nan ake jin kansu. Dake matan sunfi mazan shekaru hakan ne yasa yawancinsu suke d'akin mazajansu.

Mazan kuma samari ne kuma ko wannansu baisa aransa zaiyi aure nan kusa ba. Kasancewar suna da ra'ayin yin gidajen kansu kafin auran. Toh rayuwarce babu dole suke bin abin a hankali dan sucimma burinsu yanda ya dace.

Yanzu dai y'an matan gidan basufi su bakwai ba harda RAHMAN

Qannansu masu tasowa kuma  basufi su biyar ba. Sai qananun way'anda ba'ama magana akansu.

 

Kamar yanda nace muku auta ce a d'akinsu. Dama mahaifiyarsu su shidda ta haifa. Maza biyar itace mace a cikinsu.

Hakan yasa uwar da uban suka d'au san duniya suka d'ora akanta.

Musamman dayake sanda mahaifiyar tata takai kusan shekara tara kafin ta samu cikinta. Dan har tafidda rai da samun wani cikin. Ganin irin wannan dad'ewar da tayi..

 

Dama ita da yarintarta majin nata yayo mata kishiyoyinta. Hakan yasa suke tsufewa a tare.

Toh lokacin da suka ganta da cikin RAHMA da ganin irin d'okin da mijin nasu yake tayata. Sai suka d'auki tsana tun daga lokacin suka d'ora mata.

 

Toh ashe wasa saban fari. Dan tunda RAHMA tazo duniya ubanta ke nuna tsantsar qauna a gareta. Gashi sunan mahaifiyarsa ya saka mata. Yana kiranta da mamana. Nan zuciyar sauran matan nasa tacika da baqin ciki da takaicin wannan qauna da yake ma RAHMA..

Ganin ai suma gashi suna haifan yara matan amma baya nuna ƙaunarsa garesu kamar RAHMA

 

Tafe a hankali maman RAHMA tagane irin qiyayyar da sukema RAHMAN. Hakan yasa taja y'arta ajiki ta nuna mata qauna bata san abinda zai tab'a mata ita.

  Wannan yasa RAHMA tatashi da shagwab'a. Amma bata da raini.

Lokacin data fara zama budurwa lokacin ne qaddarar rashin ji tasauka a kanta.

Dama yayunta basu saba da dukanta ba. Dan ko tayi musu lefi zasu hukuntata nan mahaifiyar tata take hanasu. Haka mahaifin nasu.

Saifa RAHMA tazama kamar kwai cikin y'ay'an gidan. Shiyasa data zama marajin magana ba wanda take tsoro ko shakku cikin yayun nata maza da mata.

Kowa ma cikin tsoran tab'ata yake idan yaji ta aikata abu.

 

Mahaifiyarta da mahaifinta sunyi nadamar sakar mata da sukayi. Gani suke wannan dalilin ne yasa ta lalace yanzu.

Dama ance icce tun yana d'anye ake iya tankwarasa bawai saiya bushe ba. Dan idan ya bushe baka ba tankwarasa yanda kake so.

 

Gata fara kyakkyawa abinta. RAHMA san kowa in wanda ya rasa. Bata cika jiki sosai ba. Dan tana d'aya daga cikin matan da ake kira da masu karuwan jiki.

 

Tana da iliminta daidai gwargwado. Musamman na addini. Dan bata da ilimin bako can dan secondary kawai tagama tace ta gaji da karatun.

 

RAHMA bafa wanda ya isa da ita a gidan ayanxu.

Komai taga damaryi yin kayanta take. Musamman data fahimci har yanxu da santa da qaunarta cikin zuciyar iyayen nata.

 

RAHMA ta iya yawan dare sosai fah😨

Dan ficcewa take taje tayi sharholiyarta ita da qawarta UMMAKATI

 

Kaf cikin gidan nasu kishiyoyun mamanta da yayunta da qannanta cewa suke duk fitan da takeyi KARUWANCI take zuwayi ita da qawar tata UMMAKATI..

   Kome tafita siya cewa suke karuwanci take zuwayi

Tsana dai kam da tsanarta cikin zuciyar y'an uwan nata

 

 

UMMAKATI ko dama can ita gidansu bame sawa bame hanawa.

Babanta ya rasu. Maman dama su biyu ta Haifa da yayanta. Yayanta Yarone me hankali da nutsuwa. Yanxu haka yana skull acan garin bauchi

Toh maman nasu irin iyayen nan ne masu San abin duniya. Idan dai UMMAKATI zata kawo mata kud'i bata damu ba ko kwana zatayi a waje...

 

Kaf unguwar ba wanda baisan RAHMA da UMMAKATI ba wajen rashin ji. Wasu sun yarda KARUWANCI suke. Wasunsu kuma sukan qaryata hakan.

 

Wannan shine labarin RAHMA (RAHEEMAT) da UMMA (UMMAKATI)👍🏻..

 

 

 

 

 

RAHMA na shiga cikin gidan nasu da mamanta taci karo a tsakar gidan tana surfan wake. Sauran kishiyoyinta na aikinsu irin na gida.

Maman ta kalleta kallan harara Tace. "Daga ina kike. Kan tabata amsa sai Nura  Yayanta wanda ya fitto daga d'akinsu na samari yace.. "Haba mama kya tambayeta daga ina take ai kema kinsan daga KARUWANCIN take' injisu da fad'a...

Bud'ar bakin RAHMA ke da wiya sai cewa tayi.. "Uwarka ce take daga KARUWANCI bani ba.😚

Saurin kallanta duk sukayi cike da mamakinta😨 maman nasu ta kama baki tace "RAHEEMAT rashin kunyar taci dama takai haka. Wato nice nake daga KARUWANCI bake ba ko.

Saita turo baki gaba da shigewa d'akinsu na y'an mata.

Aiko maman bata barta ba sanda taci gaba da cewa. Kaf zuri'armu ba wanda yayi karuwanci kuma insha Allah bazan gani akanki ba.. Tana kawowa nan a zancen nata ta maida kallanta ga yayan nata daci gaba da cewa. Matsayinka na d'an uwanta bai dace ka fad'in mata hakan ba. Koda ko kaji y'an uwanta na fad'in mata hakan.

 

Kwafa yayi dajan numfashi ya ficce daga gidan batare dayace mata komai ba.

  Aiko fitarsa ke da wiya kishiyoyinta suka tuntsure da dariya. Alamar sunji dad'in abinda ya faru..

 

Shuru maman tayi musu kamar bata fahimci me sukewa dariyan ba.

 

Ganin hakan sai d'aya daga cikinsu ta biyun tace. "Hmm Allah ya kyauta. Yarinya tun tana qarama akabi aka sangartata ai dole ta fand'are ta lalace tayi abinda ranta keso... Cikin sauri ta uku ta katseta da cewa. "Eh mana. Ai gashinan suna ganin ishara' mu yaran namu daba'a nuna musu ƙaunar ba ai gasu sune kintsattsu itako sai aikin bin maza.

Ta hud'un tace. "Hmm Allah ya kyauta. Ni addu'a ma nake mata Allah ya fitto mata da miji tayi Aure ko zata kintsu.

   Aiko ta biyun data uku suna jin abinda ta hud'un ta fad'a suka sheqe da dariya har suna had'a baki wajen cewa. "Kinjiki da yaudarar kai. "In banda abinki a ina kika tab'a ganin irinsu sun sami mazaje. Ai sai dai y'an iska irinsu. Kinga ko idan tasamu d'an iska irinta ai babu maganar kintsuwa.

 "Kumafa haka ne. Toh Allah ya shiryeta.. Tabasu amsa da fad'in hakan tana murmusawa.

 

Ita dai maman RAHMA ta tafasa tabace musu ba. Ashe RAHMA na jinsu dan haka da rashin kunya tafito danta rama maganganun da suka gayama mahaifiyar tata. Gashi dama ba kowa agidan da alama yaran gidan sun tafi islamiyar data sauwakema kanta. Bare fad'a ya kaure tsakaninta da y'ay'ansu matan.

 

A wulaqance ta kallesu harda turo d'ankwali gaba tace.....

 

 

😃😃😃😃😃

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.*🙆🏻*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆🏼*.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`•🤱🏻

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 8

 

"Eh ba'a nunama yaran naku qaunar ba. Saboda ba sansu ake ba. Baqin cikinku saidai ya kasheku danni mahaifina yake qauna fiye da dukkan y'ay'anku. Haka zuciyar taku zatata zama da baqin har qarshen rayuwa indai akaina ne. Tana kawowa nan azancenta saita maida kallanta ga amaryar baban tasu taci gaba da cewa.. Ke kuma da kike wani batu kan kina San nayi aure kozan kintsu aiba nice zakima wannan fatan ba. Y'arki Haleema zakima wannan fatan. Ko angaya miki na rasa masoya ne. Kawai nawa halin ne ya fitto fili. kuma insha Allah abinda kuke fata bazai tab'a faruwa a rayuwata ba. Kuma wallahi tallahi kufita daga harkar mahaifiyata. Dan ba sa'arku bace. Tayi muku nisan da har abada bazaku cimma ba. Mijinta yana santa fiye daku yana qaunarta fiye da tunaninku. Jama'ar unguwa suna qaunarta saboda kyawun halinta. Wannan dalilin shiyasa kuke kishi da ita saboda baqin hali da hassa irin taku.. Ku yanxu baku jin kunyar kanku kuzo gidan mata ku aure mata miji sannan kudinga mata munafunci da hassada kala kala da nuna mata kishi qiri qiri..

   "Ke RAHEEMAT miye haka ne. Banace miki karki qara tofa bakinki idan suna magana akaina ba. Ko sa'o'inki ne. Mahaifiyarta ta katseta da fad'in hakan.

Kallan mahaifiyar tata tayi da takaici tace. "Wallahi bazan dena tofa tawa ba. Muddin zasu nemi gaya miki magana saina gaya musu suma. Tana fad'in hakan ta koma d'akin nasu tana qunquni..

 

Dama sun saba da rashin kunyarta dan haka basu wani damu da amsar data basu ba. Saima ta hud'un ce daga cikinsu tatab'e baki da cewa. "Ko jimina ta nutsa kanta a tab'o ba'a kirata kaza ba. Sharrinki saidai ya tsaya akanki dan dake dama can ya dace. Halimata dai duk hassadarki baki fad'in wani sharri akanta. Dan bata da d'abi'a irin taki. Danko a dangin ubanta basu ajiye abin fad'a irin naki ba bare danginmu. Kingako ko kad'an bazanga lalata akanta ba... Tana kawowa nan azancenta sauran suka tafa harda shewa suna masu cewa. "Ke kike kulata. Aimu uwarta ce sa'ar yinmu. Y'ay'anmu kuwa sune sa'o'in yinta....

 

"Da gaske... RAHMA ta fad'i hakan bayan qara fitowa da tayi. Taci gaba da cewa.. Wallahi nice dai dai daku ba uwata. Ku kanku kunsan baku isheni kalloba bare yaranku suyi daidai dani. Kuci gana da shiga harkar uwata ni kuma zanci gaba da d'ora aya akan inda na tsaya.. Tana fad'in hakan ta qara komawa d'akin nasu.

 

Nan suka hau rera waqa suna masuci gaba da aikace aikacensu. Dan sun lura yau bazata gaji wajen basu amsar dukkan abinda zasuce ba. Gashi yaransu basu nan bare su shigar musu. _(Rahma Nalele tace way'annan anyi iyayen banza😌)_

 

 

 

 

Shiko ABDUL bayan AMEER ya dawo daga wannan Club d'in sun had'e kiran gaggawa ne ya riskesu daga ogansu. Wato wannan Alhajin dake basu hodar ibilis dan su rabama mutanansa.

 

Bayan sunje garesan gaya musu yayi dama garin Jos yake San turasu yanxu dan su kaima wani hodar. Saboda gobe yake San barin garin Jos d'in.

 

Nan suka karb'i hodan suka sassaka cikin wani burgujejen wadan sirrinsu wanda duk mayincin y'an sanda ko sojoji basu tab'a gane da wani mugun abu jikin wandunan nasu ba. Dan tunani zasuyi kan sun saka wandunan ne dan ado irin na samarin yanxu.

 

Bayan ya basu kud'i da adireshin inda zasu sauka babu b'ata lokaci nan suka shirya gudu gudu suka bar garin nasu wato Kaduna.

 

Dake jos da Kaduna basu da wani nisa gab da magrib suka iso.

Wanda zasu bama hodar tun a tasha ya taresu yakai su masaukinsa wato hotel na Sharna.

 

Bayan sun basa sakwan nasa wanka sukayi sukaci abinci kana sukayi sallah AMEER yacema mutumin yana so ya had'asu da wani yaransa ya d'an kaisu club na garin jos d'in suga ya suke irin tasu yanawar..😊

Babu musu yace musu zai had'asu da wani yaransa Abba. ai summa sanshi. Nan da sha d'aya zaizo saiya rakasu. Sam basu da matsala da hakan. Dan yasan zai kaisu inda ya dace dasu. Murmushi suka mai dan sunji dad'in yanda ya fahimcesu..

 

 

 

 

 

Da misalin qarfe tara na dare rahma da umma ne zaune kan dakalin kofar gidansu rahman suna zance da samarinsu.

  Ita dai rahma hira take da wani alhaji bala acan bayan layinsu yake. Yana da yara da yawa sosai dan matansa biyu ne. Yana matuqar san rahma sosai. Yayinda matanshi da yaransa suka tsaneta sosai.

Ko kad'an rahma ba sanshi take ba tana dai kulasa ne dan qiyayyar da matan nasa da yaran nasa suke nuna mata.

 

To yanzu kallanta yayi cikin wani salo irin nasu na manya yace. "Haba ƴar budurwata. Ya kike so nayi da rayuwata ne. Kina ganin yanda sanki da qaunarki suke shirin zautar dani. Had'e da jefani cikin wani hali. amma kike batun wai nabar batun turowa gidanku sai nan gaba. haba my luv' baki San akan sanki zan iya rasa rayuwata ba...

 

Kallansa Rahma tayi.. Sam bashi da kyen fuska. Saidai Yana da kwarjini sosai. Ko kad'an batayi mamakin kalamansa ba. dan  tasaba da hira da manya irinsu. Dan haka ashagwaɓe tace dashi. "Haba Alhajina. Ya dace kasan idan babu kai bazan iya rayuwa ba. Murmushinka dariyarka kalamanta nutsuwarka qamshinka suna ɓata tunanina. Suna sani zama na musamman dab inta tunaninka. Sam basa barin mafarkina dan bibiyata suke wajen haskomin kyakkyawar fuskarka.

Ina yawaita tuna wata rana danayi mafarkin gani cikin d'akinka ka jawoni zuwa gareka tare da sumbatar kyakkyawar yarinyar dana haifa maka wacce take d'auke a hannuna. alamu sun nuna idan nazama mata a gareka zakaji dani fiye da tunanin me tunani.. Takai qarshen zancen nata da rufe fuskarta wai adole taji kunyar gayamai hakan datayi..🙈😂

 

Aiko wawan dajin hakan nan ya washare baki yana me nuna jin dad'in abinda tace mai. Shidai Yana san yarinyar dan ta'iya hira me narkar da zuciya.

Ahankali yace. "Zanji dake fiye da tunaninki indai kika Aureni. Yanzu bud'an fuskar nagani dan bani San nadinga missing d'in ganinta..

 

A shagwaɓe tacire hannun nata daga fuskar tata tayimai fari da ido tare da cewa. "Komai nawa an halicceshi dominka ne. dan haka bazan hana kyakkyawar fuskarka kallan tawa fuskar ba.

Da murmushi yace. "Na godema Allah daya had'amu cikin qauna.

 

 Tashi tayi tana cewa "Allah abin godiya. Na fara jin bacci Alhajina. Yanxu sai munyi waya bara naje naga wancen kona minti biyar ne naje na kwanta dan zuciya na buqatar tunaninka.

"Amma ai babu gama hirar ba my luv. Baki bani amsar abinda nake bibiyarki dashi ba.

"Alhaji kenan. Nace maka baka da matsala da zuciyata. Ka qaramin lokaci zanyi maka magana bye...

Tana gayamai hakan ta nufi wajen wani saurayin nata daya d'auki lokaci yana jiranta.

Nanta bud'e gaban motarsa tashiga da Kallansa rai b'ace tace. "Minti biyar na baka ka gaya min abin daya kawoka.

Jan numfashi saurayin yayi da cewa.. "Har tsawan wane lokaci zaki d'auka kina me kula wancen mutumin ne...

Qara tsaida kallanta tayi akansa da harara tace "ban sani ba. Kaga malam bacci nakeji in kasan baka da abin cewa naqara gaba.

 

"Haba my dear. Ya dace kimin afuwa kan abinda ya faru tsakaninmu mana. Bai dace kidinga hukuntani yanda kikaga dama ba. Nace miki ba budurwata bace ai yadace ki yarda ko.

"Wallahi Abbas kayi qarya ka had'ani kishi da wannan kucakar yarinyar. Ya za'ayi mu tashi layi d'aya ni da ita. Tasanni na santa kawai kana tare dani saina ganku tare kace bazance budurwaka bace..

   "Kinsan Allah da gaske tambayata qanwata Anisa tayi kan tana gida ne. shine na tsaya bata amsa..

Jan numfashi RAHMA tayi da ficce daga motar  tana nufar gidansu da cewa. "Toh nayarda yanzu. sai gobe idan kazo dan yanxu ina da abinyi.

 Binta da kallo yayi tare da girgiza kansa wallahi daba dan yana qaunarta ba. Da haƙura da ita zaiyi. Dan shi ya kasa fahimtar inda tasa gaba. Shin tana sanshi bata sanshi Shifa bai sani ba. Amma kuma nuna kishin da tayi kan aminan layin nasu akansa alamu ne naso. Dan haka zai qara hak'uri har yacimma burinsa akanta.

 

 

Can wajen sha d'aya da mintina kwalliya sosai rahma tayi Cikin shigar riga da wando kayan sun matseta ainun. Rigar ja ce. Yayin da wandan yake biqi. Kan nan an tubkesa da ribom. Sai d'aukar qamshi take. Kamar yanda suka saba idan sunyi wannan shiga saka doguwar riga suke a saman shigar. Dan haka yanzuma d'aukar doguwar rigar tayi tasaka. Y'an uwan mata na d'akin nasu suna kallanta ta d'auki y'ar jakarta da wayarta zata fitta ne d'aya daga cikinsu taja tsaki da cewa. "Aikin banza. Idan dai zuwa karuwanci abinyi ne yarinya taci gaba. Muna nan da ita zatazo mana d'auke da cuta cikin nadama lokacin bame kallanta.

Har RAHMA takai ƙofar fittan juyo da kallan ga wacce tayi maganar tace da ita. "Idan ban shiga harkarki ba ummi kidena shiga tawa harkar. Sannan KARUWANCI ai uwarki ce takoya min.

 

"aa uwarki dai' badai tawa ba Wallahi. Dan tamu bata ajiye abin fad'a ba bare ya bibiyi y'ay'anta.

Rahma tayi murmushi da cewa. "Sanine dai bakiyi ba. Amma yanxu kije kiyi binkice dakyau' wallahi uwarki Lantana sau shidda tana yin cikin shege ubanta Kakanki shine sheida. maza jeki gun tsowan ya baki cikakken tarihi dan ba qaramin qoqari mahaifiyata tayi ba' wajen lallashin mahaifinmu kan yayi haƙuri ya karɓi tayin da Kakan naki yayi masa naya temakesa ya rufa masa asiri ya Aureta.. Na lura bakisan nasan da zaman wannan ba. Dan kema kanki baki sani ba. Dan haka maza garzaya kije kijiyo da kunnanki kozaki dena saka damuwar qaramar karuwa kamar ni😀..

 

Ummi y'ace ga matar Baban nasu ta uku. Dan haka tana jin wannan kalami na RAHMA sam bata bari ta ida ƙarshen zancen nata da numfashi ba. nan tayi tsalle ta kifama RAHMA mari wai dan me zata fad'in mata hakan.😂

 

Aiko nan RAHMA ta'ajiye y'ar jakarta gefe tayi kukan kura ta damqi wiyan ummi nan fad'a ya kauri.. Duk da cewar bata da wani qiba amma duk tafi y'an uwan nata ƙarfi. Hakan yasa tasamu nasarar kayar da ummin duk da yayarta ce haka tahau ruwan cikinta tadinga falla mata Mari tana cewa sainaci ubanki shegiya dan uwarki menayi miki dazaki fallamin mari. Daga fad'ar magana nabaki amsa saiki maran. Haka tadinga marinta tana naushinta damma itama ummin tana d'an kare kanta da ƙoƙarinta nasan taga tatashi.

Sauran ƴan uwan nasu ko sai ihu suke suna kiran sunan iyayen nasu..

 

Kankace kwab'o kowa agidan har mazan waƴanda suke gidan alokacin duk suncika d'akin daqer suka iya d'aga RAHMA akan ummi suna masu neman jin ba'asin meya jawo fad'an..

Dake Ummi irin mutanan nan ne masu saurin kuka. Nan kicin kuka tahau maida musu yanda fad'an nasu ya faro..

Sun juyo da niyar jin tabakin RAHMA amma me😀. Sam sun nemi RAHMA sama ko qasa babu ita babu dalilinta ta ficce tun sa'adda ummin tafara magana..

 

Mazan girgiza kansu kawai sukayi da komawa shashinsu dan basu da abin cewa indai lamari akan RAHMA ne..

  Nan maman ummin tadinga sauke masifarta da bala'inta kan duk qarya RAHMA tafad'ama ummin kar hakan ya dameta zuri'arsu kaf bame yawan tazubar bare ciki insha Allah Saidai sugani akanta.

Haka sauran kishiyoyin suka dinga bata hak'uri akan karta damu da wannan..

 

Ita dai Maman RAHMA komawa d'akinta tayi da turo musu ƙofa. Hakan ko ya qara musu takaici. Da kwafa sukabar d'akin yaran bayan sun gama lallashin ummin...

 

addu'ar da maman RAHMA tasaba mata yanxu ma ita d'in tasake mata. Kan Allah ya kare mata y'ar tata daga fad'awa tarkwan zina.

 

Bayanda batayi ba kan RAHMAN sudena yawan dare ita da umma amma abin ya gagara. Ko an kulle gida durqa ta Katanga takeyi su had'e da UMMAKATI..

Har kwad'o Babansu yasama ƙofar tasu da niyar idan yafito sallar asuba ya bud'esu amma sha Allah idan ya fitto sallar asuban ganin kofar tasun yake abud'e.

Saidai Komin dare suna dawowa gida. Basa kwana a wajen..

Ita dai taji aranta y'ar tata bata aikata zina. Saidai koma me sukeyi tana rokwan Allah ya shiryar mata da ita.

 

 

By AUNTYN LUV💋

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.*🙆🏻*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆🏼*.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`•🤱🏻

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 9

 

RAHMA bayan tayi nasarar d'aukar jakarta fakar idan Mahaifiyarta tayi taficce ganin tasaki baki tana jin abinda ummi kece musu..

 

Tafawa sukayi ita da UMMAKATI sukayi saurin yin kan layinsu.

Anan suka tsaya suka jira me adaidaitan da yake zuwa d'aukarsu dan kaisu duk clubs d'in da sukace mai. Ba qaramin kud'i suke bashi ba shiyasa yake musu yanda suke so..

 

Basu wani b'ata lokaci agunba yako zo ya d'aukesu.

Direct 01'11 Ya kaisu. Sunan club d'in kenan.

 

Club d'in manyan mutane ne Alhazawa. Waƴanda sukaci suka tadakai. Akwai yara matasa masu ji da kansu awajen yaran manya masu kud'i way'anda kallo d'aya zaka musu kasan eh lalle wajen ya dace dasu.

 

Tun a adaidaitasahun suka cire dogayan rigunan dake jikinsu suka saka cikin jakunkunan su  kamar yanda suka saba.

 

A ƙaƙidar wajen idan zaka shiga zasu baka hula kasaka. Dan haka su RAHMA na zuwa wajen suka basu hular wacce ake kira da fosinkaf🕵🏻 nan suka karb'a da sawa suka shige abinsu dan dama sun saba...

 

Kallo d'aya ABDUL yama RAHMA ya kawar da fuskarsa. Saboda jin faɗuwar gaban da ƙirjinsa yayi akanta.

Yarinyar tana da kyau sosai. Tatara abubuwan da kowane d'a namiji yake buqata agun mace.

       Rintse idansa yayi bayan ya harararo hakan sai yaji ransa ya b'aci da ganinta haka. Sai yaji sam baiji dad'in ganinta awajen ba.

 

Qara maida Kallansa gareta yayi akaro na biyu. Komai na halittarta ya bayyana. Ga yanayin  halinta ma ya bayyana kansa. Yarinyar zatayi rashin kunya. Sannan ba makawa shagwaɓabɓiya ce.

 

"Sam baki dace da nan wajen ba. Ya fad'i hakan a bayyane yana me qara kawar da ganin nasa daga garetan daci gaba da shan drink d'insa dan yau kwata kwata baya sha'awan shan giya.

Yayinda AMEER yake can nesa dashi yanata aikin b'ata tunanin wata yarinya..

 

 

Suko basu wani sha wahalar ganin way'annan su Alhajin da suka basu kud'i d'azu ba. Dan tunda sukace zasu had'u awajen tofa zasu had'un ne.

Da shagwaɓe RAHMA da UMMA sukaje suka d'ane cinyoyin su Alhajin suna masu kissing nasu a wiya kumatu da shafa jikinsu.

Nan Alhazawan suka fara rikicewa da qara maqalesu.

 

Sunyi shaye shaye San ransu.

Matse matse dai kam da shafe shafe da tsotse tsotse ba wanda basu shashi ba.

Rahma tana sane sarai bata bari ta bugu Sosai ba. Dan kar shirinta ya lalace

 

Hankalin su Alhajin ya tashi dan sha'awan yaran ta lullub'esu. Dan haka nan suka buqaci dasu keb'ance. Haka ko akayi. Dan nufar wajen keb'ancewa sukayi. Wasu d'akuna ne na alfarma suna bu'de musu suka shiga..

RAHMA da Alhajinta UMMA ma da nata Alhajin..

Amma d'ak'unan nasu ajikin juna suke.

Hmm suna shiga nan su Alhajin suka hau neman jikinsu. Kawai burinsu su cimma burinsu na biya buqatarsu sha'awarsu data lillib'esu akansu

 

RAHMA takalli Alhajin da fararan idanta tace. "Nifa a qaqidata sai munsha drink sannan zamu fara harka Alhajina. Ta fad'i hakan da alamun maye tattare da ita..

Murmushi ya kasar mata da bud'e wani furiji dan ya d'auko drink d'in... Sai tayi amfani da wannan damar ta zira hannunta cikin Jakarta ta lalubo wata kwaya ta b'oye cikin hannunta kana da maida kallanta garesa tana murmushi ganin Yana zuba musu a cup. Nan tatashi taje ta karb'i nata da juyawa tajefa kwayar kana ta juyo lokacin zaikai nasa baki kenan saita karb'a daci gaba da cewa.  Lallema' yazaka zubamin da yawa naka kad'an.

Murmushi ya sakar mata cikin shauqi yace.. "Sweety aike kika buqata' kinga ko dole naki yafi nawa yawa.

 

   "aa kadai yimin wayo. Aljanun kaina basu San abu me yawa. Dan haka bani naka ka karb'i nawa. Takai qarshen zancen da karɓar nasa tabashi nata.

Nan ya karb'a zai sha tayi saurin saka masa hannu a baki daci gaba da cewa. Saina baka izini...

Shuru yayi mata yana wani lumshe ido da bud'esu cikin shauƙi. Tare da kafama na fulaninta ido..

Sanda tad'an ɓatamai lokaci kana tabashi umarnin sha..

Nan ya shanye ba wani batun musu.

Yana ajiye cup d'in ya wani cakumeta yana qoqarin rab'ata da rigarta. Saidai bugawan da kansa yayi shiyasa shi sakinta da dafe kansa.

Taku rugumosa ta zaunar dashi kan gadan d'akin ta shige jikinsa tana d'aukarsu photo shida ita..

Sam baya hayyacinsa sai qoqarin kai kansa ga qirjinta yake. Itako sai aikin d'aukarsu photan take a wayarta tana me d'an kare fuskarta yanda baza'a ganeta ba..

 

 

A waje ko abinda yake faruwa shine.. Wani Yaro ne maqale da budurwar AMEER wacce yake bala'in jin daɗin harka da ita..

Kai idan AMEER kansu ke da wiya sai AMEER d'in ya tashi da nufarsu ya hankad'e wannan saurari yana muzufai da cewa.. "Kutumar uba😨. Kai d'an gidan uban waye daza kazo kana harka da Babyna..

Nan jikin yarinyar yahau rawa dan tafi kowa sanin TANTIRANCI irin na AMEER. Dan ansha fad'a dashi akanta. Sam batayi tunanin zasuzo wannan club d'in ba. Tomema ya kawosu Jos..

 

"Sunana Amar miye dan nayi harka da ita. Saurayin ya fad'a hakan afusace cike da nuna isa da taqama tare da dukan qirjin AMEER d'in..

Kan kace kwabo nan sai fad'a ya kaure tsakaninsu.

Dan AMEER cukumesa yayi dasan ta kwaɓe.🤔

 

 Aiko ta kwaɓe. 😳

Dan ABDUL na gajiya da ganin damban da suke an rabasu sunƙi rabuwa sai kawai ya tashi da zafin nama yaje ya shiga tsakaninsu da rabasu da qarfin tsiya.

Amma sai saurayin nan ya koma kan Abdul waime zaisa ya shiga fad'an nasu an kasa dashi ne.

ABDUL ya kallesa da mamakin yanda yake dakan ƙirjinsa yace.. " Dafa katsaya iya kai dashi. Kar kayi kuskuran dawowa kaina. Danna fika TANTIRANCI..

Sam saurayin nan bai saurari jan kunnan da ABDUL yake masa. Sai qara dukan ƙirjinsa yake irin shi waye..

Aiko ya nuna masa koshi waye. Dan ɗaga hannu yayi ya d'auke sa da wani matsiyacin mari. Kanya dawo cikin hankalinsa ya zari wata babbar kwalbar giya ya rotsa masa akai🙆🏼..

 

Gabaki d'aya y'an wajen sanda suka d'ora hannu aka🙆🏻♂🙆🏼 musulman ciki suka rabka salati suna ihu da fad'in "sai oga.

Ganin yanda nan take jini ya wanke kan wannan saurayi. alama ƙarara tanuna kan nasa ya fashe😨..

   ABDUL ya kallesa da murmushi ya gyaɗa kansa da cewa. "Kai ƙaramin d'an iska ne. Baka iya TANTIRANCI ba. Kaje garinmu Kaduna ka tambaya waye ABDUL D'AN KASADA za'a gaya maka waye ABDUL waye kuma AMEER...

 

Murmushi AMEER yayi da dafa kafaɗar ABDUL yace "aikinka yayi kyau ɗan uwa. Nima bari na qarasa shi. Nan AMEER ya ɗauki wata kwalbar zai qara roɗa masan🙆🏻 sai budurwar ta riqe hannun AMEER d'in cikin tashin hankali tace.. "Kayi min rai AMEER ka barshi haka. Na rantse da Allah bani da abinso kamar ka. Dan kai daban kake cikin mazaje. kayi hak'uri kabarshi dan wallahi yau itace had'uwarmu tafarko.

   " Da gaske. Ya katseta da faɗin hakan. Saita d'aga masa kai alamar tabbatarwa. Saiyaci gaba da cewa. Tome yasa kika min ƙarya. Kikace zaki ƙauyanku harna ɗauki maƙudan kuɗi na baki dan kiyima iyayenki tsaraba. Dama nan ne ƙauyen naku. dama duk abinda kike gayamin qaryane. Dama ashe ke munafuka ce.

 

  "Na rantse maka da Allah nan ne garin mu. Ba'a ƙauye muke ba. wannan nasan nayi maka  k'arya dan nasamu kud'i da yawa wajenka. Kuma ganina da kayi anan na rantse maka sabo da zuwa ne yasani kasa jurewa sanda nazo nan. Shine fa ya ganni anan d'in kuma na rantse maka ba abin daya shiga tsakanina dashi..

   Harara AMEER ya galla mata da janye hannunsa yana mai maida Kallansa ga wajen da saurayin yake. Saidai babu shi babu dalilinsa.

 

 ABDUL ya sakar mai murmushi da cewa. "Ai wani abokinsa yayi gaba dashi.

Tsaki AMEER yaja da dangwarar da kwalbar. yana niyar cewa wani abu' sai sukaji jiniyar motar folisawa..😳

 

Wanda ya kawosu wajen yace. "ABDUL akwai matsala fa.. Yaran daka daka ɗane ga wani hamshad'in me kud'i wato Alhaji Yaro nera. Shima yau shine karansa na farko zuwa wajen nan. Dan ban tab'a ganinsa anan ba. Ba mamaki yanxun su suka kira Y'an Sandan nan kan suzo su kamaku..

 

ABDUL ya dafa kafaɗar shi yace.. "Zuwa hannun y'an sanda baya damuna. Bani tsoran su ko kad'an. Kuma banyi nadamar abinda nayi masa ba. Kuma zaban gudu dan tsoran su kamani bah....

  AMEER yace "aa ABDUL bamu tab'a zuwa garin nan ba. Ya dace mu tafi badan tsoro ba. Dan kasan babu jin tsoran nasu cikin ranmu.

 

Ba yanda basuyi da ABDUL kan subar wajen ba. Amma yace bazai bar wajen ba. Dan bai dad'e da zuwa ba.

Suna cikin hakan ne sai suka tsinci wani rikicin shashin da Alhazawan suke nasu harkar. Wasu samari biya ne washe a ƙasa an kwak'ule musu ido da yanke musu harshe.

Nan hankalin ABDUL dasu AMEER ya tashi dan duk iskancinsu basa kisa.

Jama'ar wajen na ganin hakan kowa ya farayin takansa.

Dama su ABDUL da mashing biyu sukazo wajen dan haka sai suka nufi wajen mashing d'insu🤣

 

 

Su RAHMA ko basu San wainar da ake toyawa ba.

Dan alokacin RAHMA tagama ɗaukar photan da take d'auka Kenan. Saita hankad'e Alhajin nata.

 dama kansa ya gama d'aukar cajin maganin data sakamai wanda yasha a drink. Nan bacci me ƙarfin gaske yayi awan gaba dashi

Itama baccin takeji. Gashi mayen magungunan datasha ya fara cafkarta. Nan tatashi da murmushi tana layi takira wayar UMMAKATI wacce ita kam tarigada tabada kai dan lokacin ma suna kan harkar ne.

Aiko nan suka tsaya da harkar tad'auki wayar cikin sanyin jiki tana cewa.. "Ya akayi ne.

RAHMA tayi murmushi tace "shegiya maiyar maza. mara aji ta wannan wajen. Nina gama da Alhajina. yanzu zan tafi gida ma had'e washe gari.

"Yayi toh. Amma ki kula da kanki dannaji tafara cafkarki. Allah ma yasa wawan nan yana nan ya maida ke gidan akan lokaci. Umma tafad'i hakan cikin maye k'arara. Dan ita tashayu da yawa..

 

RAHMA tace "Ina zaije. Kedai kiji dad'in kawai bye sai mun had'u.. Tana faɗin hakan ta kashe wayar.

Nan tad'auki jakarta da fitowa tana y'ar waqarta amake alamar duniya tayi mata dad'i. Ta tabbatar zata caji Alhajin da yawa idan Allah ya kaisu gobe. Imba haka ba tace mai zata watsa hotonan yanar gizo kowa ya gani yaga abin da yake aikatawa danta lura kamar wani babba ne.

 

Saidai me😳 tana fitowa ta tsinci maganar an fasama Yaron Alhaji Ya'u kai. sannan ga gawar wasu matasa biyu an kashesu wajen kwak'ule musu ido👀 da yanke musu harshe..

Wata qawarsu Yahanasu ce take bata labarin. Nan RAHMA tad'an wastsake duk da dai bata gama dawowa normal ba. Amma sosai tayi qoqarin guduwa ta k'ofar bayan hotel d'in inda taga kowa nabi a rikice..

 

Sam bataga me kekenafaf nasu ba. Dan haka k'afa menaci ban baki ba😂 haka tana layi tana zabga gudun cetan ran kar a kwak'ule mata ido.. Dan duk rashin jinta tana da tsoro tafannin harka ta kwak'ule ido.

 

Hankalin RAHMA ya tashi ainun. Ga dare duk motar data tara bame tsayawa. kasancewar yanxu rayuwar babu yarda..

 

Lokacin ko su ABDUL suna Shirin hawa mashinan da sukazo dasu kenan..

Dama shi da AMEER ne a d'aya. D'ayan kuma wanda ya rakosun ne yahau.

Nan suka tada mashinan sukabi ta bayan hotel d'in  ta inda RAHMA tabi...

 

 

Harsun wucceta ABDUL ya dawo da baya ya kalleta yaga a make take. Alamar kwaya tafara aiki akanta. Gashi duk yanda taso data bar wajen bame temakwanta. Dan kowa takansa yake. Gashi dare ba kowa bane zai saurari tsayar dashi da takeyi. Babu makawa taqara lokaci nan y'an sanda zasuyi awan gaba da ita.

Dan haka cema AMEER yayi ya koma mashing d'in wannan wanda ya rakosun. Zai temaketa.

AMEER yace. "Kayi hauka ne dazaka temaketa bayan baka santa ba.

Wanda ya rakosu yace. "Gaskiya ABDUL muyi sauri mubar wajen nan karsuzo tanan suyi gaba damu.

Jin hakan yasa yace ma AMEER... "Please d'an uwa kakoma mashing nasa dan Wallahi bazan iya barinta haka ba. Sam zuciyata taqi yarda da hakan..

Jin abinda yace sai AMEER ya sauka daga mashing d'in ya koma na wanda ya rakosun. ABDUL ya matsa kusa da ita amake take matuqa.

Sai haki take alamar tayi gudun tayi gudun tagaji. Sam batama San me suke cewa ba.

 

  "Ke dallah kihau na rage miki hanya.. Yace da ita hakan a fusace..

Kallansa tayi idanta na juyawa tace.. "Dalla kadena min tsawa. 

"Zan tafi na barki inyaso sai suzo su kamaki kyayi musu layin rashin kunyar  dakyau aikin San dai dai suke da mata irinku..

Tsaki taja.' sam bata da niyar hawa mashing d'in..

 

 Ganin hakan sai ran ABDUL ya b'aci. Ya d'aga hannu ya falleta da mari cikin tsawa yace zaki hau kosaina miki dukan tsiya.😡

Abinka da illar maye. Nan tarikice tahau da sauri AMEER kyalkyale da dariya dan basu tafi ba suna San suga tafiyarsu..

 

Yanda ABDUL yaja mashin d'in sanda yabata tsoro. Nanta qanqamesa GAM tana cewa "to kayi ahankali mana.😚

Banza yayi da ita.

Suna barin wajen kuwa y'an sanda suka dira awajen. Allah dai ya karesu da sunyi gaba dasu.

 

Sanda sukayi nisa da wajen ABDUL yace dasu AMEER suyi hotel d'in kawai basai sun rakasa kaita unguwar tasu ba. zai iya gane hotel d'in tunda yaga sunansa koya b'ace zai tambaya. Sun yarda da abinda yace ganin hotel d'in ba wani b'oyayye bane.

 

Tana rike qam dashi tana masa kwatancen gidan nasu bacci nasan kamata. Sai tace nan tace cen idan sunje tace banan bane.😂..

 

daga qarshe dai ABDUL daya gaji tsayawa yayi da mashin d'in ya juyo da kallansa gareta ya qara bata wani marin nan tad'an dawo hayyacinta tafara mai kwatancen daidai tana mitar idan ya qara marinta Allah saita rama. Daqer da sid'in goshi ta iya kawosu k'ofar gidan nasu lafiya. Dan sai sambatu takeyi.

 

Bayan ta sauka ta kallesa duk daba ganin fuskarsa takeyi sosai ba kasancewar ba wuta sai  tace dashi.. "Wallahi saina rama marin daka dinga d'irka min. Allah ya kaimu gobe saina nemo duk inda kake na rama.

Girgiza kai ABDUL yayi. Yau dai rana nayi yaji tsanar shaye shaye. Sam batayi kyau da yanayin ba. Haka kawai yaji ransa ya b'aci da ita. Dan haka Ahankali cikin sanyayyiyar muryarsa yace. "Ya dace kishiga gida danna tabbatar da cewa gidanku na kawoki.

Harararsa tayi da cewa... "Idan ba gidanmu bane gidanku ne. Tana fad'in hakan taja tsaki da barin shi nan tashige gidan nasu a hankali cikin sanda..

ALLAH sarki Babanta da Mamanta suna zauren gidan cikin duhu suna jiran ganin dawowarta. Aiko sai ganinta sukayi cikin sanda ta shige d'akinsu.

Maman ta kalli Baban nata tace kaga ta wucce saimu kulle gidan muje mu kwanta ai.. Tafad'i hakan da damuwa

Murmushin yaqe yayi mata da kulle gidan suka nufi nasu makwancin tare da tunanin wane mataki zakuma su d'auka akanta.

 

Itako sanda ta kwanta a  katifarta sannan ta tuna da UMMAKATI.🤔

 

By AUNTYN LUV💋`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.*🙆🏻*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆🏼*.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`•🤱🏻

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 10

 

*Kuyi hakuri sisters n brothers bani da lafiya ne*

 

 

Tana cikin tunanin ne saiga kiran UMMAKATIN ya shigo wayarta. Cikin lumshe ido da wani hali tad'auka da cewa.. "Yanxu nake shirin kiranki. 

UMMAKATI ta sauke ajiyar zuciya da fad'in. "Da fatan dai kinkai gida lafiya, duk hankalina ya tashi danaji wani abokin Alhajin nan ya kirasa yana gaya masa abubuwan da suka faru, nan gabana ya fad'i yace min karna damu ai koda anyi wanda yafi hakan bincike bazai zo inda muke ba, shine nace bara ke nakira naji ko kinkai gida lafiya.

  Jan numfashi RAHMA tayi da cewa. "Nakai gida lafiya dan yanxu haka ma ina kwance ne. "Toh bari na barki sai mun had'e da safe dan dak'ar nake miki magana. "Eh, ai naji hakan, sai da safe.

RAHMA na fad'in hakan takashe wayar dajan bargo tana lumshe ido cikin matuqar jin bacci.

 

 

Shiko ABDUL sanda ya tabbatar da nan ne gidansu sannan ya kad'a kan mashing d'in yabar layin nasu.

Bai wani sha wahalar gane hotel d'in ba, dan wani police ya tambaya ya mai kwantance ammafa sanda ya bashi kud'i, Allah ya kyauta.

 

AMEER ya kallesa bayan shigowarsa d'akin da aka saukesu yace. "Ka kaita lafiya. "Eh. Ammafa yarinyar bata da kunya. Wallahi da qanwata ce baqaramin wahala zatasha aguna ba.

Dariya AMEER yayi da qara jan bargwan jikinsa yace. "Ai sufar yanayinta ya bayyana kansa. Zatayi shagwaɓa da rashin kunya wannan babu makawa😀.

 

Sanda ABDUL yayi sallah raka'a biyu ya rok'i Allah kan ya kintsar dasu sannan ya saka qaunarsa cikin zuciyar mahaifiyarsa kana ya kwanta. Wannan itace addu'ar ABDUL ako-da yaushe.

 

 

Eh, gaskiya RAHMA bata wani damu da sallah akan lokaci ba can ba🙁, Zatayi ammafa ba akan lokaci ba, kuma hakan ya faro asaline lokacin data fara fanɗarawa.

Yanxu haka sallar asuba sai kusan qarfe bakwai da rabi tahau yinta, dan anyi mata tashin duniya taqi Tashi, bayan ta'idar ne sai tanufi wajen mahaifinta danta gaida shi, saidai da damuwa ko akan fuskarsa ya amsa mata yana meci gaba da cewa. "Yanxu Mamana ban isa na gaya miki magana kiji ba kenan ko, duk abinda nake gaya miki baya shiga kunnanki ko,

Ahankali ta ɗago da fararan idanta tace. "Tome kuma nayi yanzu, nifa banyi komai ba, "ina nufin jiya da kika dawo ƙarfe ukun dare ina kikaje.

 Sosa ƙeya tayi da cewa birthday ɗin wata ƙawarmu mukaje nida UMMAKATI, Wallahi Baba tana sa kirki sosai yarinyar.... "Wane birthday ɗin arziƙine za'a yisa cikin dare, wato baza dai kiji abinda nake gaya miki ba ko. Kina dai ganin yanda kowa yake nuna miki tsana agidan nan amma kinkasayin hankali ko.

"Toh kayi hak'uri Babana bazan sake ba kaji, Allah bazan sake ba. Ta katse shi da faɗin hakan cikin raunin murya da shagwaɓa.

Hmm haka dama al'amuran suke, cikin ƴaƴanka dole kafi San wani, kafi ƙaunarsa, kamar yanda na gaya muku mahaifin RAHMA yana bala'in santa da ƙaunarta, koda ya shirya mata faɗa fata fata tana bashi hak'uri yake haƙura.

Dama shi irin iyayen nan ne  waƴannan basu zafi kuma basa duka, Sam  baya duka ko kaɗan, dan haka cikin saka mata albarka dayi mata fatan kintsuwa yace taje Allah yayi mata albarka..

 

Dataje gaida mamanta ko muguwar harara ta auna mata tace "gidan uban wa kikaje jiya dahar kika kai ƙarfe uku na dare. Wato bazaki dena yawan dare ba ko, wato sam ke ba'a isa dake bako.

  Turo baki waje RAHMA tayi da cewa, "Toh kiyi hak'uri bazan sake ba.

"Toh kiyi hak'uri bazan sake ba,🙁 maman ta mai-mai ta abinda tace cikin takaicinta kana taci gaba da cewa.. Wallahi RAHEEMAT kima kanki fad'a, idan yau mune gobe bamu bane, yanxu ke ko kishin kanki bakyayi ace cikin gidanku ke kad'aice kika fitta zakka, kowa baya sanki baya qaunarki kuma baki damu ba.

  "Toh ai y'an uwan nawa ne kad'ai basu sona, muta nan gari suna sona suna qaunata Wallahi dan baki fitta zuwa wajejen da nake zuwa ne dasai kin sha mamakin yanda ake ƙaunar ƴarki...

Saurin bige mata baki maman tayi afusace tace, "Allah yamin tsari da yawan gurare irin naki yawan gantali, nan har wani abun arziƙi ne ace jama'ar wasu gune suke ƙaunarki ba danginki y'an'uwanki ba, yanxu ko mutuwa kikayi ke dai kam wannan mala'ikan rubuta kyawawan d'abi'un mutane bazai samu kyawawa daga wajen y'an uwanki ba sai munana,

Wallahi RAHEEMAT kima kanki fad'a ki canja hali, yanzu bazaki San darajar fad'an da nake miki ba har sai kinga babu raina tukunna zaki san darajarsa, Yanxu maza ficce min daga d'aki mutuniyar banza kafin nayi boll dake..

Turo baki taqarayi gaba da ficce daga d'akin mahaifiyar tata dan RAHMA ta tsani fad'a a rayuwarta..

Subaiba yarinyar matar babansu ta hud'u ta kalleta da kyalkyalewa da dariya tace. "Hmm Allah ya kyauta. Tana fad'in hakan taci gaba da karatun novel nata na online na wannan marubuciyar UMMU BASHEER wato *KE HASKE CE* labarin yana mata dad'i sosai..

Amma me😳 sam batayi tsambani ba saiji tayi fauuuu🙁 RAHMA ta fallata da mari, kanta saita tunaninta nan taqara kai mata wani Marin gauuu kamar tasamu jikin dotse😨.

Kan kace me🤔 nan fad'a ya kaure tsakaninsu kamar a filin dambe. Dake Subaiba ma ba'a barta a baya ba wajen qarfi nanta kwashe RAHMA sai ganinta kawai nayi a qasa.

A rayuwar rahama sam ta tasani a kadata a fad'a dan haka bata ba Suwaiban damar hawa ruwan cikinta ba, nan tayi kukan kura ta d'aga Subaiwan daga ƙasa ta nunama Allah ta nanata da ƙasa,

Habawa nan suka dinga birgima a ƙasa suna masu yakushin juna da kaima juna juka kowane iri.

Subaiwa ta d'auki wani takalmi me tsini ta kwantarawa RAHMA aka, zahiri taji zafi sosai hakan yasa tayi saurin rarumo wani takalmin itama me tsini na ummi ta kwantara mata itama aka, saidai nata yazo da akasi dan a goshi ta kwantara mata, nan wajen ya d'an fashe jini ya fara zuba, amma saboda shed'an ya kad'a musu ganga nan sukaci gaba da faɗan Cikin jin matuƙar ƙiyayyar juna.

 

Dake ba kowa a d'akin su suke amansu suke lashewa.😀

 

Can matar baban nasu ta uku tazo waccewa ta d'akin nasu, nan taji ana gurnani da nishi irin na wahalar nan saita leƙa taga meke faruwa😂. Ai nan taga Suwaiba kan RAHMA tana kici kicin kwaye mata fuska.😨. Bata samu dai nasara ba dan wani juye RAHMA tayi da ita wanda yasa nan take itama ta haye ruwan cikinta tahau falla mata mari da make mata baki tana cewa... "Dan uwarki wa kikema dariya"

 

Salati Iyami tasaka tana cewa jama'a kuzo zasu kashe kansu🙆🏼

 

Kan ka kace me🙁 nan jama'ar gidan sukayo d'akin. Still wannan karan ma daqer aka d'aga RAHMA daga ruwan cikin Suwaiba.

Da kuka RAHMA take bada labarin wai dariya Subaiwan tayi mata dan kawai taga ta shigo d'akin da b'acin rai,  Kowa salati ya kamayi awajen suna masu cewa "Yanzu ke dan tayi miki dariya shine kika hauta da fad'a haka kamar ba Yayarki ba😨

Murgud'a musu baki RAHMA tayi da barin gidan gabaki d'aya tayi gidansu UMMAKATI

 

Maman UMMAKATI na ganin RAHMA tasakar mata murmushi da cewa "Ha'a, yana ganki ke d'aya ina ƙawar taki.

RAHMA ta kalleta da b'acin rai tace "Bata dawo bane.

"Eh, aina zata tana gidanku anan takwana.

"aa acan na barota hotel d'in Sharna" "Ok, ba mamaki ki ganta yanxu.

Shuru RAHMA tayi mata. Jin hakan sai yasata lura da yanayinta, nanta gano kamar akwai abinda ya faru da ita yanxu, dan haka sai taci gaba da cewa, Me ya faru ne naga kamar antab'amin ke. Cikin qara turo baki RAHMA tace "Ba Subaiba bace daga ganina na fitto daga d'akin mamammu kawai saita hau yimin Dariya.

"Wato ita dai Suwaiba bata San zaman lafiya sam, banda haka miye nayi miki dariya. "Aunty ki barta kawai zan gyara mata zama dan Wallahi wata rana Allah b'allata zanyi.

"Ki daiyi hak'uri dan sun rasa yanda zasuyi dake ne shiyasa baqin ciki yake kamasu har su dinga neman tsokanarki, ki barsu kawai kidena shiga harkarsu.

Shuru RAHMA tayi dan da gaske ranta ya b'aci da dariyar da Suwaiban tayi mata.

 

Can saiga UMMAKATI ta shigo gidan, da Murmushi ta kalli RAHMA da cewa. "Yeee qawata ammafa gaskiya alhajin nan bashi da dama.

mamanta ta kalleta tace "Wane Alhaji.

Maida kallanta kanta tayi da matsawa kusa da ita tace. "Wani ne mana  mama, yana da kirki sosai, kinga har dubu ishirin yaban yace na baki.

Nan maman tata ta waro ido cikin murna ta amshe kud'in daga hannun UMMAKATIN tana cewa "Kai ammako nagode Allah ya saka masa.

Tashi UMMAKATI tayi da kama hannun RAHMA tace "zomuje dakina mana kiji, nan ko RAHMA tabita d'akin nata wanda yake d'auke da qaramin gado da katifa sai kayayyakinta na sawa, bayan sun zauna kan gadan zuge Jakarta tayi da fito da wani kud'in ta nunama RAHMA tana cigaba da cewa, duk shi yaban, wato RAHEEMAT Alhajin nan yayi, gaya min ya kika gaya da naki.

Jan numfashi RAHMA da cewa "Ni sai yanxu ma na tuna dashi, ban karb'i ko sisi agunsa ba, amma yanxu bara ki gani.

Nan RAHMA ta lalubo numbarsa ta tura masa waƴannan hotunan nan tana me gaya masa gaskiya taji dad'in harka dashi cikin wannan dare, ga hotunan data d'aukesu nan sai maimaita kallansu take, Dan Allah yayi hak'uri tatafi batare data tsaya ya dawo hayyacinsa ba bare ya bata wani abu, amma yanxu tasamu nutsuwa ga A/C num nata nan tana buqatar ya turo mata da dubu d'ari yanxu zatayi wani abu ne da ita..

 

Lokacin da sakwan ya iske wannan Alhaji a fusace ya kira RAHMAN yana ce mata, "Ke qaramar y'ar iska, karki nemi ki raina min hankali, danna gama tunani tsaf na gayane babu wani abu daya shiga tsakanina dake har zuwa lokacin da bacci yayi awan gaba dani, dan haka babu abinda zan turo miki dashi..

"Gaske.... Ta katse shi da faɗin hakan tana me murmuwa tare da yima UMMAKATI sigina cikin wani salo taci gaba da cewa, Babu abinda zai hanaka turomin da kud'in dana buqata, eh da gaske babu abinda ya shiga tsakanina dakai, saboda ina da wayo, nasan sarai abinda kake nema aguna ba abu bane na banza, wannan dalilin yasa nayi amfani da damata danna b'ata tunaninka, wato kayi kuskuran neman harka dani, hotunan dana turo maka idan baka turomin da kud'in da nake buqata ba Wallahi nan take zan turasu yanar gizo kowa ya gani ya abinda babban mutum kamarka yake aikatawa.....

"aa aa dakata, kin san koni waye da kike shirin aikata hakan agareni, zan turo miki da kud'in da kika buqata yanxu sai dai daga shi babu ni babu ke, Ya kai qarshen zancen gumi na tsattsafo masa.

Dariyar mugunta RAHMA tayi da cewa. "Wannan ne dai kuma kayi qarya, dan zan nemeka aduk lokacin da nake bukar kud'i, na barka lafiya sai naji shigowar sakwan.. Tana fad'a mishi hakan ta kashe wayar da kallan UMMAKATI wacce ta zuba mata ido kawai tana kallanta. RAHMA ta kalleta da cigaba da cewa, abin ya birgeki ko, hmm Wallahi kima kanki fad'a kidena bama mazaje kanki kamar wata shashasha, dan tatse miki komai zasuyi kije gidan mijinki da saura,  ni tanadin danama mijin Aure na babban danadi ne, dan zanyi mai mugun bazata nanuna masa BARIKI IYAWA CE, in sashi qaryata kalaman da y'an uwa suke fad'a na wai karauwanci nake yi,

    Toh waima tayaya mahaifiyata tana min addu'a dare da ranah ace addu'arta baza tayi tasiri a akaina ba, kawai nafi yarda da cewa ni d'in bani jin magana amma tawajen aikata zina zan karema Mahaifiyata wannan mutuncin, dan mijin Aure na yayi mata kallan mutunci,

 

Jan numfashi UMMAKATI tayi da cewa, "zanyi k'ok'ari sosai wajen ganin na zama kamarki, kuma insha Allah zan dena bama maza kaina, dan gaskiya ne idan naci gaba a haka ba makawa bazan kaima mijin Aure na abin kirki ba,  yanxu dai yunwa nake ji dan ban tsaya na karya a hotel d'in ba, bara naje na dafa indomie da kwai ko naji qarfin jikina.

"Owkie, ki dafa dani dan nayi fad'a da Suwaiba,

 yanxu," wannan yasa bazanci abincin gidan ba,

"Toh shikenan bara na dafa mana, UMMAKATI tafad'i da tafi ta nufi kitchen d'insu.

 

Nan RAHMA ta baje kan gadan nata tashiga tunanin ABDUL, k'amshinsa ya tsaya mata arai, tana lokacin data rungumesa ta baya ba qaramin dad'i taji ba, kowane lungu da sak'o na jikinsa qamshinsa ne ke fitta, gaskiya koma waye shi ya had'u, yana da tsafta da aji, ga muryarsa me sanyi, saidaifa yana da saurin hannu, bazata tab'a manta marikan da dinga dirka mata ba, "Harfa sau biyu ya maran, wallahi Allah ya qara had'ani dashi ba abinda zai hanani ramawa, Ta faɗi hakan a bayyane batare da tasan ta fad'i a bayyanan ba,

 

By AUNTYN LUV💋

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.*🙆🏻*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆🏼*.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`•🤱🏻

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 11

 

Suko su ABDUL gari na Wayewa suka hau shirin barin garin na jos, wanda sukazo garin dan shi ya nuna buqatarsa nasan harka dasu, har yana nuna musu zai iya biyansu fiye da yanda ogansu wanda ya turasu wajensa yake biyansu,

 Saidai baisan yaran suna da wayo me yawa ba, hakan yasa sukace mai ya tintib'i ogan nasu idan ya amince su dinga harka dashi zasuyi dashi sam basu da matsala da hakan, yace muku zai tintib'eshin...

 

Bayan sun iso garin Nasu na kaduna kallan AMEER ABDUL yayi da cewa. "Duniya ta cika da rashin gaskiya, ka duba ogammu ya yarda da wannan mutumin amma yana san ya saye dan mu bijire masa mu koma aiki dashi.

AMEER yace "Bar banza mana, ya d'auka mu yara ne, san kud'in kawai mukasa a gaba bama duba mutuntuka.

ABDUL yace "Na yanke shawarar gobe kawai mu antaya garin na Lagos mu aiwatar masa da aikinsa koya kagani.

"Hakan yayi saimu fara shiri tun daga yau.

 

 

Da dare ne da misalin qarfe d'aya da rabi na dare mijin Salisu ZAINAB ya dawo gida a d'an bige, da alama watace can wajen iskancin nasu ta b'ata masa rai, dan haka sai kawai yazo ya sauke akan ZAINAB d'in....

Tana kwance har bacci ya fara kamata kasancewar yau kwata kwata bata jin daɗin jikinta, kawai basai yahauta da duka baji ba gani ba, wai dan iskanci tanaji yana sallama amma tayi biris dashi, toh dama gaskiya ZAINAB bata tab'a yin bacci idan har Salisu bai dawo ba, to da wannan yayi amfani yake ganin kamar yau iskanci take ji, shine yace bara ya sauke mata shi😀...

Sai d'auketa yake da mari yana kai mata naushi kamar ya had'u da saransa.

Ba qaramin wahala yake san bata a wannan dare ba, dan haka sai tayi yanda tayi ta ficce daga bedroom d'in, taci nasarar d'aukar wani hijabinta afalo tayi saurin bud'e kofa ta ficce.

Haka jiri na ibanta cikin daran nan haka tayo gidansu tana me addu'ar Allah yasa kartayi gamo da aljanu, dan tunda take gujema mijin nata bata tab'a guduwa cikin nisan dare haka ba.

ALLAH ya sota lokacin ABDUL suka dawo daga yawan nasu daran.

Saidai bai bugu sosai kamar yanda ya saba buguwa ba, saboda yayi alk'awarin denawa gabaki d'aya ahankali-ahankali, saboda ganin RAHMA da Yayi cikin wannan yanayi,

 

Dama Hajjiya Kakah tasakama y'an gidan dokar kar taji wani cikinsu ya kullema ABDUL ƙofar gida, wannan dalilin shiyasa ABDUL baya fargabar dawowa akowane lokaci, dan yasan k'ofar a bud'e take,

Ta kusa isowa kofar gidan nasu kenan saiga su ABDUL sun tsaida motarsu a kofar gidansu AMEER,

Nan suka fito da mamaki suna kallanta kallan tuhuma, AMEER ya bugu sosai dan haka saiya rufe baki da waro ido waje yace.. "Kai ka kai kai🤭, AUNTY ZAINAB me kikeyi acikin wannan daran haka, baki tsoran aljana takama ki😨, kut.. waya miki duka haka naga fuskarki ta kumbura,

Zainab ta kallesa dakyau ganin jini a rigarsa, shima ABDUL ga jinin ajikinsa tace, "yanaga jini a jikinku, meya faru daku.

 

Lumshe ido AMEER d'in dai yayi da bud'ewa yana layi irin na bugaggu yace da ita... "Al'ada muke😨 yana faɗin hakan sai kuma ya waro ido da maida kallansa ga ABDUL yaci gaba da cewa, aa ina nufin fyed'e mukayima mata,

Da sauri ZAINAB ta waro ido😳 nan take taji qarfi yazo mata, cikin tashin hankali tace "what,😳 fyeɗe...

Da sauri ABDUL ya make bakin AMEER d'in tare da waro nasa idan yana cewa, "kai😳.. Wallahi AUNTY qarya yake yi,

AMEER yayi dariya yace, "wallahi AUNTY qarya nake yi.

Maida kallanta tayi ga ABDUL tace,  "toh gayamin, meya sameku da har jini ya tab'a jikinku,

Yace, "wasu ne sukayi fad'a harda yanke yanke shine muka rabasu,

Jan numfashi ZAINAB cikin rashin yarda dan ganin duk abuge suke ba mamaki ko duk qarya suka sharara mata, amma Allah ya kaimu gobe zata jisu ne ai, dan haka saita ce dasu "Allah ya shiryeku... Tana fad'in hakan ta shige gidan nasu, sanda ta b'ata lokaci tana bugama Hajjiya Kakah kofa kafin ta bud'e, tana ganin itace dama tasan abinda ya korota, dan haka nan tabata hanya ta wucce ciki.

 

ABDUL ko da bacci a idansa shiyasa daya kulle gidan nasu kawai shashinsa yayi baibi takan AUNTYN tasu..

 

 

Haka acikin wannan dare ma RAHMA da UMMAKATI a jos  dai-dai wannan lokaci suma suka dawo daga yawan nasu daran, saidai basu shirya had'uwa da kowa ba kawai dai sunje sharholiyarsu ne, yawan rawa da shaye shaye, ba qaramin buguwa sukayi ba, wasu samarinsu ne suka kawosu har gida,

Dama iyayen RAHMA sunsan bazata dena dan furucin da tayi agaresu ba, amma suna mata kyakkyawan zaton zata dena, wannan yasa suka qara k'aimi cikin addu'o'in da suke mata, 

Aikinsu kenan hana kansu bacci har sai sunji dawowarta,

 

 

 

Washe gari a Kaduna bayan ABDUL ya kintsa d'akinsa wanka yayi ya feshe jikinsa da turara ya nufi d'akin Hajjiya Kakah danya karya, anan yaga manyan iyayan nasu maza sun saka Hajjiya Kakah da ZAINAB a gaba suna jin abinda ZAINAB d'in take gaya musu kan abinda mijin nata yake mata,

Qare mata kallo ya shiga yi, gaskiya ba qarya ta bugu sosai dan ga shaida nan ta nuna kan fuskarta duk ya kunbora mata fuskar.

 

sosai ABDUL ya nutsu ya gane duk abinda take fad'i akan mijin nata, hmm ransa ya b'aci matuqa, sam baya san abinda zai tab'a mishi lafiyar kakarsa babansa ZAINAB d'in, danko mamansa babin takanta yake ba, wannan dalilin yasa yaci alwashin yau saiya koyama mijin nata hankali, badai ya iya dukan mata ba, to shi kuma ya iya dukan maza,

 

Dan haka shuru yayi abinsa ya jawo kwanan sha me d'auke da kunun gyaɗa gefe guda kuma ga wani fulas me d'auke da ƙosai me zafi, dan haka nan ya koma kan kujera ya hauci dan yasan nasa ne.

Lokaci lokaci sukan had'a ido da Babah Shehu sai kaga Baba Shehun yayi saurin kawar da kallan nasa yana me nuna alamun tsoro.

Murmushi kawai yake yi yana cewa aransa na saka maka tsorona Baba Shehu, dan haka sai haƙuri..

 

 

 

Bayan ya gamaci gidansu AMEER ya nufa ananya gansa d'akinsa yanata sharar bacci hankali kwance, AMEER yana kyau daidai nashi, yana da wani jiki wanda mata masu aji suke so wato kamar dai yanda ABDUL ya haɗe....

Kallan agogwan hannunsa ABDUL yayi yaga k'arfe takwas ne da minti arba'in da d'aya ne, dan ya d'akama AMEER d'in duka yana me cewa, Dallah tashi d'an iska, qilama ko sallar asuba bakayi ba.

Tashi AMEER yayi yana murza ido yace "Allah nayi, dan Dady ne yazo yasani agaba.

"Wallahi AMEER kama kanka fad'a yanxu sallar ce har sai anwani zo an saka a gaba"

"Kawai ka share abokina, yanxu dai ya take ne, har yanxu tafiyar tamu nanan ne kodai zamu bari sai gobe"

"Idan kana san abari sai goben ai sai'a bari, kaga nima nasamu damar cin uban mijin AUNTY ZAINAB dakyau"

 Waro ido😳 AMEER yayi da wastsakewa sosai yace, "Yauwa kamar jiya naganta cikin dare kamar ma magana tashiga tsakanina da ita ko"

   Murmushi ABDUL ya mai da cewa, "Kawai guy ka kwafsa abar batun kawai, nan AMEER ya mararrarcema ABDUL kan dan Allah ya gaya masa me yace ne a cikin daran,

Share shi da batun ABDUL yayi ya shiga kiran abokansu cikin wayarsa ya shaida masu yana san sunemo masa mijin AUNTYNSA ZAINAB aduk inda yake sukai  masa shi d'akin huronsu, Nan suka amsa mai da ladabi kan yanxu ko zasu nemosa.

 

AMEER yace "Yau Salisu zaici ubansa" Murmushi ABDUL yayi da faɗin "kadai bari"

 

Sallama Abida tayi tashiga d'akin da tira abincin kayyawan AMEER ta dire a kan wani tebur anan cikin d'akin ta kalli ABDUL tace "Ya ABDUL ina kwana" "Lafiya my dear kin tashi lafiya"

"Lafiya lau, ga breakfast nan momy ta had'a harda kai tana tunanin ko zakaci.

"Wayyo momy data bari, dan yanxu na gama karyawa d'akin Hajjiya Kakah, yanxu zubama AMEER nasa kitafi da sauran. "Toh, tace mai cikin ladabi ta aiwatar da abinda yasatan.

 

Bayan tatafi ne AMEER ya kalli ABDUL yace, "kaga wani group da aka sakani ciki, waishi YARA MASU AJI, ya kai qarshe zancen nasa da nunama ABDUL d'in gaban wayar tasa dan ya gani.

ABDUL ya karb'i wayar da cewa, Nima d'azu naga ansani ciki, da alama y'an group d'in zasuyi surutu.

"Au, haba kana  ciki ashe, AMEER ya fad'i yana me janyo abin Karin nasa.

Bashi wayar ABDUL da bashi amsa wajen cewa duba kaga, ni ina ganin ma yanxu fitta daga cikinsa, dan bani san group d'in da aka cika surutu da yawa.

Bayan AMEER yaga ABDUL na ciki ya gane wanda ya sasu cikin group d'in, wani abokin ABDUL ne wanda sukayi fad'a dashi kwanaki, amma yanxu sun shirya saidai basu cika harka dashi kamar da yanda suke ba, to shine fa yaketa wani shish-shige musu, sun gane yana san  su dawo harka dashi kamar da ne, kuma ya nuna musu yayi nadama sosai, dan haka yanxu cema ABDUL AMEER yayi "kawai ɗan'uwa kashe, jeeboy ne ya bud'e group d'in yasamu, please karka fitta dan zaiga kamar basu  kwata kwata bamu san wata wuld'a dashi ne,

 Kan ABDUL ya bashi amsa sai kiran abokan nasu ya shigo wayar ABDUL d'in ya d'auka yana me cewa, "kun kai min shi d'akin ne.

Nan suka bashi tabbacin hakan, dan haka saiya kashe wayar da tashi yana cigaba da cewa , sunkai min shi AMEER bari naje namai yanda bazai qara tab'amin lafiyar my AUNTY ba,

Murmushi AMEER yayi kawai sai ABDUL d'in ya ficce.

 

 

Yana nan zaune kan wannan dai kujerar da aka d'aure Baba Shehu wancan lokacin to abinda aka masa shima haka aka masa, sun d'auresa tamau fuskar nan tashi a rufe ruf.

 Nan Abdul ya bud'e mai fuskar tare da watsa mishi ruwan sanyi bayan ya farfad'o ya sakar mai murmushi da cewa, "Mema sunanka"

Da matuƙar tsoro Salisu ya haɗiye yawu yace "Me make faruwa ne, me zaka min, suwaye suka kawoni nan, 

 falla masa mari ABDUL yayi yace "Ya za'ayi ina tambayarka kaima kana tambayata.

  _Na shiga uku ni Salisu, meya shigo dani hannun ABDUL D'AN KASADA, TANTIRI a y'an daba,_ Salisu ya fad'i hakan aransa da matuqar tashin hankali, afikiko cewa yayi, "Sunana Salisu"

"Toh miye dangantakar ka dani"

"Babu wata dangantaka, nidai nasan ina Auran ƙanwar Babarka ZAINAB"

  "Masha Allah, " Zanso naji dalilin dayasa kake dukar Auntyna ZAINAB dahar kake bari take baro gidanka cikin dare batare da hakan ya dameka ba"

 Gumi ne ya karyoma Salisu, tabbas yau me rabasa da ABDUL sai Allah, dan yafi kowa sanin TANTIRANCI irin nasa da AMEER tun yana zuwa wajen ZAINAB zance.

 

Cikin muryar rauni yace "A gaskiya bani da wani dailin dayake sawa nake aikata mata hakan"....

"Da gaske😀! ABDUL ya katseshi da fad'in hakan.

  Shuru Salisu yamai, shima ABDUL d'in shurun yayi yana kallansa kawai.

Can sai Salisun yace "Kamin aikin gafara Wallahi na tuba bazan sake aikata mata hakan ba, idan na sake aikatawa kamin duk abinda zakamin.

Murmushi ABDUL yayi da cewa, "wato Salisu, giya da kwaya da kayan maye suna da matuqar dad'i ga wanda yake shansu, suna saka mutum cikin nishad'i da annushuwa adai dai lokacin daya shasu, bayan kana shansu kana had'awa da iskanci wanda kawai ganin damarka ne yake saka kake dukan ZAINAB badan ka bugu ba, kana dukanta ne dan jin daɗin kanka badan buguwa ba, kana dukanta ne dan cin zalinta ba dan buguwa ba.

 Bazaka nunamin shaye shaye ba, saboda yanxu idan nagaya maka giyar da nake sha da kwayar da nake sha mamaki kasheka zaiyi, amma hakan baya sani dukan kowa sam babuma wani sinadarin da yake saka mutum duka acikin kayan maye, duk wanda kaga yana duka yayi dan qarin samun nishad'in kansa ne.

Ba abinda zai hanani hukunta yau  kan dukan daka mata a daran jiya, ABDUL na fad'in hakan nan ya hau zane Salisu yana ihu saiya make masa baki.

 

Sanda ya tabbatar ya masa dukan gobe ka k'ara sannan yabar dukan nasa,

Sai ya zaro wata qaramar wuqa me kaifi ya kama kunnansa na dama zai gutsire masa kunnan aiko nan Salisu ya kwalla wata qara da salati yana masa magiyar karya gutsire masa kunnansa dan soyayyarsa da manzan Allah😂..

 

Jin ya ambaci manzan Allah saiya fasa gutsire masan amma  sanda ya d'an tsagasa masa shi, nan take ko Salisu ya sume, ABDUL murmushin mugunta ya qara yi da yayyafa masa ruwa ya farfad'o da gumin azaba, nan ya dinga hawaye yana rokwarsa kan ya barsa haka, Wallahi yayi nadama ba kuma zai sake ba, dan Allah karya qara masa wani abun,

 Kauda kallansa yayi daga kansa yace, "Idan na qara maka wani abu mutuwa zakayi ba suma ba, dan haka bazan qara maka komai ba, dan ina San ganin AUNTYNA cikin farin ciki, idanko na kasheka bazan yafema kaina ba,

Kaci sa'a zamuyi tafiya gobe, dan haka zan kunceka a goben, daba dan haka ba Wallahi sai kayi sati biyu ina baka shaqi iskar waje ba. Yana faɗin hakan ya kulle masa baki da ficcewa daga d'akin.

 

 

 

 

Anan jos ko haka su RAHMA ma suka tashi sukaga anjefasu cikin wannan group d'in da aka jefa su ABDUL. Sam basu san wanda ya bud'e group d'in ba, amma su k'awarsu Aliya itace tasasu,

Group d'in yazo da farin jini awajen RAHMA da UMMAKATI, musamman jama'ar cikin group d'in, duk wanda aka sashi ciki sanda yaji shauqin san group d'in,

Gabaki d'aya y'an group d'in basu wucce su saba'in ba, amma kaf ci babu wani meji acikinsu.

Duk marasa ji ne aka had'a cikin group d'in,

Wanda ya bud'e group d'in yayi qoqari sosai dan group d'in ya dace da  mutunan da suke cikinsa.😂

 

"YARA MASU AJI. RAHMA ta fad'i cikin jin daɗin sunan group d'in,

Da san mutane da yawa acikin group d'in kuma duk masu aji ne irinsu.

Wannan dalilin yasa ta fantsama cikin group d'in tafara zuba hira kamar me, kan kace kwab'o nan Yawancin way'anda suke online acikin group d'in suka santa, wayanda ko dama sun Santa nan hira tafara aikinta, haka ma umma kati nan sukayi qawaye maza da mata,

 

Dama suna d'akinsu Rahma na y'an matan gidan ne UMMAKATI ta kalli RAHMA tace "Alama tanuna kinji dad'in group d'in nan. Murmushi RAHMA tayi da bata amsa tace, da farko danaga group d'in wallahi gabana ya fad'i, dana shiga cikinsa naga dake aciki ga kuma qawayenmu sai naji group d'in ya kwanta min arai, kuma ki lura yaran masu ajine cikin group d'in bakiga kowa ya sake ba.

UMMAKATI taja numfashi tace, " ammafa gaskiya naji wani iri a jikina kamar wani abu zai faru damu acikin group d'in"

"Ke dalla tafi can matsoraciya, ba wani abinda zai faru damu insha Allah" RAHMA tafad'i hakan da ajiye wayarta bayan ta kashe datan ta..

 

By AUNTYN LUV 💋

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.*🙆🏻*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆🏼*.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`•🤱🏻

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 12

 

*Read more 12 nayi muku danna wanke kaina agareku y'an hannuna*😂

 

 

Jan numfashi UMMAKATI tayi da cewa, "To shike nan Allah ya dafa mana", "Amiin, RAHMA tace mata

 

 

 

Direct gidansu ABDUL yayi, anan yaga ZAINAB ta ritsashi d'akin Hajjiya Kakah tana me tambayarsa meya faru dasu jiya taga jini ajikinsu, kodai da gaske fyaɗen sukama mata kamar yanda AMEER yace.

  Kallanta ABDUL yayi da ɗan  murmushi yace, "Allah da gaske ba fyaɗe mukama mata ba, wasu ne suke fad'a muka rabasu, dake faɗan na wuk'ane shiyasa kikaga jini ajikinmu, kuma Aunty kinsan duk rashin jina bana kula mata, dan Allah kiyarda da abin dana gaya miki

 "Owkie, na fahimta, amma dan Allah kudena faɗace-faɗacen nan da yawan dare, wallahi bashi da amfani dan Allah kuma kanku fad'a"

  "Yayi Auntyna, insha zamu rage, am yaushe zaki koma gidanki"

"Abdul nagaji da iskancin Salisu bazan iya da abinda yake min ba, nina hak'ura da Auran dashi, kana dai gani har yanxu bai biyoni ba, inda dane iyanxu yana gidan nan tun safe zaka gansa yazo ba Hajjiya Kakah haƙuri, amma yau dake yana jin iskanci kaga har yanxu baizo ba,

  "Aunty gaya min har yanxu kina san mijinki, Ya katseta da faɗin hakan

Cikin wani hali tayi shuru tana tunani, can tace "Ina sanshi har yanxu ABDUL, ina san rayuwa dashi, Amman wannan shine zai kasance karo na qarshe dazan qara zuwa gida saboda matsalata dashi.

Damma su Babah Shehu sun qara bani hak'uri ne kan na koma idan yazo dan suga kozai canja halinsa, banda hakan nina cema Hajjiya Kakah kawai suraba Auran d'azu.

  "Toh kiyi hak'uri insha Allah zai canja miki, ina tabbatar miki da hakan, dan yana sanki, zabai so rabuwa dake ba, musamman idan yaji abinda kikacema Hajjiya Kakah d'azun.

"Toh Allah yasa, yanzu ina zakaje,  "kawai na dawo gida ne.

"Hakan yayi"

"Yauwa dama ina san nagaya miki zamu Lagos gobe nida AMEER, bazamu wucce sati biyu ba zamu dawo"

"Lagos kuma, ABDUL me zakuje kuyi a Lagos" "AUNTY wani aiki oganmu yasamu, ba wani dad'ewa zamuyi ba" "Wai waye wannan ogan naku ne dazai dinga turaku gari gari kuma wane aiki kuke masa" ZAINAB ta tambayesa cike dasan jin abinda zaice mata

 Tashi yayi yana bata amsa da, "Bawani aiki bane Auntyna, kawai ki share basai kinji ba" "Ban gane in share ba, idan wani mugun abun yake saku kuyi fa, ai kaga na nuna muku illarsa.

"Toh nidai bazan gaya miki ba, dan ba wani mugun abun bane, kuma ma aunty yanzufa na girma ba wani abu dazan aikata wanda za'a kirasa da mugun abu.

   "Amma ABDUL kana....

"Amma ABDUL me, dan Allah karkice min baki san naje Lagos d'in nan, dan ina san zuwa, musamman ma da ban tab'a zuwa ba, ABDUL yayi saurin katseta da faɗin hakan.

Shuru tayi mai ganin hakan sai ya sulale yabar mata d'akin, dan yasan halinta sarai bata san yawan yawan nan da ogansu yake turasuyi.

 

 

Sanda yayi sallar warha sannan ya baje kan katifarsa ya bud'e data yana san ganin me duniyar yanar gizan take ciki...

 Sannu a hankali yake bin hirarrakin da y'an group d'in nan da aka sashi sukayi, "kai amma wannan yarinyar tacika surutu, ka duba yanda taketa sakar zance kamar wata aku....

"Kai dawa kakeyin magana, AMEER ya katse shi da faɗin hakan yana me kwanciya shima akan katifar tashi. Murmushi  ABDUL yayi dace mai, "Sam banyi tsammanin abayyane nake zancen ba, hirarrakin da y'an group d'in nan sukayi nake gani...

"Akwai wata RAHEEMAT da UMMAKATI sunfiya surutu kai musamman ma RAHEEMAT d'in.. AMEER ya qara katseshi da faɗin hakan

ABDUL yace "eh, naga tafi kowa magana, wannan da alama idan tabar group d'in surutun sauran zai ragu,

AMEER yace "kwarai da gaske, yanxu dama nazo na gaya maka ne munyi da oga kan jirgi zamubi gobe qarfe bakwai, dan haka saika tashi muje muyi ciki cikin samu.

 

 

Sun samu yanda suke so dan haka qarfe taran dare ABDUL yaje ya saki Salisu, amma kafin ya sake shi sanda yaja mishi kunne Wallahi ya dawo yasamu labarin ya qara dakar masa Aunty saiya mishi abinda yafi hakan, Salisu najin hakan yace ya yarda, nan ABDUL ya make qeyarsa nan take ko ya sume, saiya kira abokansa kan su fidda shi su kaisa can gidansu,

 

Haka ko akayi dan gidansu Salisun suka kaisa suna masu cewa wai ganinsa sukayi a yashe kan hanya, suna gaya muku hakan suka barsu da d'ansu.

 

Nanko ZAINAB sai zaman jiransa takeyi, can dataga baida niyar zuwa saita kunne idanta bacci yayi awan gaba da ita.

 

 

Su RAHMA ko awannan ranah bikin wata qawarsu Salima sukaje, biki ne na yara yaran mata irinsu, yaran da suka amsa sunansu wayayyu, duk wanda kagan shi a wannan biki toh ka tabbatar wani ne TANTIRI ko watace MARA JI.

Bad'ala dai iri iri anyi awajen fatyn nan, dan maza da mata ne suka haɗe suka cure waje guda aketa dirkar rawa,  ba sallah ba salati sai tashin muryar Arna kakeji tana rera musu waqa, RAHMA ta iya rawa ba lefi shiyasa mazajen wajen sukefi liqe mata wajen rawan.

 

Basu suka dawo gida ba sai wajen qarfe goma da rabi na dare

Duk sai warin giya sukeyi,  hakan yasa RAHMA tayi wanka agidansu UMMAKATI tasaka wani kayan kana tayi gidansu.

Girgiza kai maman tayi dacewa "Allah ya shiryamin ke kidena yawace yawacen nan da kikeyi, Wani Yayanta dake tare da maman yace "Ameen,

RAHMA da sanyin jiki daje ta shige jikin maman nata tace, "Wallahi mama zan dena dan Allah kayi hak'uri kinji, tace " Ya zanyi dake RAHEEMAT, ai tsakanina dake addu'a ce, Allah Yayi miki albarka, dan dadai hankali na bazan jefeki da mugayan maganganu wanda zasu qara fanɗarar min dake ba.

 

 

Washe gari Daqer da siɗin goshi Hajjiya Kakah ta harda da tafiyar dasu ABDUL zasuyi, dan kuka tasama ABDUL tana cewa saiya gaya mata aikin da ogansun yake turasu yi gari gari, shidai bai gaya mata ba amma Yayi qoqari sosai wajen shawo kanta, nan tayi musu fatan alkairi suka antaya airport sai garin abuja, anan suka qara yankar tikiti zuwa kudu Lagos,

 

 

Bayan tafiyar su ABDUL iyayen Salisu ne sukazo bikon ZAINAB suna masu gaya musu wai Salisun baya jin daɗi ne, wani hatsabibi aka samu  yayi mai dukan tsiya shekaran jiya😂 yanxu haka ma yana gida ana jinyarsa.

Jin hakan sai yasa hankalin Hajjiya Kakah ya tashi ita da ZAINAB nan suka bar batun wani biko tace da ZAINAB tashirya ta koma d'akinta tayi jinyar mijinta.

Haka ko akayi, haka ZAINAB ta koma gidan aka kawo mata Salisun ba lefi jikin nasa da d'an sauqi,

Amma tayi mamakin yanda yana cikin ciwo amma yake wani janta da hira har yana bata hak'uri kan bazai sake aikata mata abinda yake aikata mata ba, dan Allah tayafe mai.

ZAINAB taji dad'i sosai hakan yasa tayafe mai suka rungume juna cikin so da qauna,

 

 

 

 

******

Su ABDUL sun sauka lafiya anan sukaga wasu sunzo daukarsu, ba lefi dan hotel d'in da suka saukesu ya had'u irin sosai d'in nan, anan bayan sunci abinci sunyi sallah hutawa suka hau yi.

 

Akalla sanda suka kai kwana uku kafin wani ya basu hodar dafara yimusu jagora zuwa ga waƴanda zasu bama.

 

Idan dai hodar iblis tashiga hannun ABDUL da AMEER  duk iya kwafkwafinka baka isa ka ganeta a jikinsu ba.

Saboda kayan da suke sawa na musamman ne ajikin nasu yayin harkar, dan idan hodar nan takai akwati uku irin wanda ake saka hodar aciki tsaf suke sakawa jikin wannan kayan nasu.

 

Wannan dalilin yasa sam ogansu baya kawo matsala awajensu.

 

Haka wannan ɗan jagoran ya dinga sadasu da manya manyan sheɗanu a harkar suna masu basu hodar, su kansu duk da sun d'auki shekaru a harkar sanda salan su ABDUL ya birgesu, suka dinga mamakin yanda suke Yawo da hodar a jikinsu amma babu wanda zai kawo cewa akwai hodar jikinsu bare ayi ram dasu.

 

Su ABDUL suna san kwarewa a harkar, dan haka bayan sun gama rabama mutanan ogan nasu hodar sai suka shige jikin sheɗanun nan suka nuna musu suna san qara kwarewa a harkar kafin su tafi, jin hakan ko yama waƴannan dad'i dan haka nan suka d'orasu akan tasu harkar,

Gaskiya da wahala dan nasu ba irin nasu ABDUL bane, dan ankusa kamasu lokacin da zasu kaima wani babban mutum da irin salan ba mutana sai kuma Allah ya kare. Nan suka qara tabbatar da cewa Nash salan daban yake dana kowa.

Sun dai yanke shawarar wata biyu zasuyi su dawo gida.

 

 

 

 

Ayanxu watansu d'aya a garin na Lagos, Toh suna harkar aikin nasu suna kuma yawan daran nasu na bin club, gaskiya club a garin Lagos ba qaramin yawa bane dasu, gasu gurare ne masu kyau sosai da tsari, ba lefi su ABDUL suna jin dad'in garin sosai, dan sun qara samun wayewa fatarsu ta qara gogewa, dan wahalar da suke sha bata yawo arana bace,

 

 AMEER dolensa yabar batu akan harka da mata, dan matan nan ba irin na arewa bane, haka y'an garin suka gaya masa, suna masu tabbatar masa da cewa zai iya d'aukar cuta idan har bai kula ba, dan matan ba gaya masa zasuyi ba, ABDUL najin hakan ya kalli AMEER d'in da cewa, saika hak'uri mukoma gida ka d'ora aya tunda lamarin ya zamar maka jiki.....

 

 

______________________________

Suna dai hira cikin wannan group d'in amma ABDUL sama sama yake magana ciki,  kuma shi yana magana da maza y'an uwansa ne, sam wata magana bata tab'a had'asa da wata mace a group d'in ba, amma kunga AMEER har yayi sabo da RAHMA da UMMAKATI hira suke kamar sunsan juna....

 

 

 

Kaf RAHMA a y'an group d'in nan ba way'anda bata sani ba, tasan way'anda sufa fiye magana aciki, tasan way'anda basa magana, tasan mazan da suke magana idan sunga mata na hira, tasan mazan da suke magana idan sukaga maza y'an uwansu na hira, to tagane AMEER yana san hira da mata, gashi ya iya hirar dasu, sai kuma ABDUL, tagane sam mata basa gabansa, dan bata tab'a ganin ranar da Magana tashiga tsakaninsa da wata mace cikin group d'in ba, ta lura ko maganar zaiyi yanayi ne da maza y'an uwansa, gashi matan way'anda suka sanshi y'an garin nasu na kaduna sai suta masa shishshigi wajen d'ura maganarsu akan maganar da yakeyi da mazan y'an uwansa, sam bai tab'a ba wata mace amsa ba,  alamar dai abayyane take, kaf y'an group d'in Suna masa kallan me aji, musamman idan sukaga yanda wasunsu suke shige masa.

RAHMA faɗi take aranta gaskiya mutumin nan yanaji da kansa, ka duba yanda ake binsa yana wani share mutane,  su kuma dan tsabar zubar da aji ahakan suke qara shige masa, RAHMA takanja tsaki cikin b'acin rai aduk sanda taga ana binsa yana wani share mutane....

 

 

******

Yau da misalin qarfe goma da rabi na safe RAHMA tabud'e datanta inda taci karo da wani sak'o da aka tura mata ta prvt anan WhatsApp, nan ko ta share ring groups da dama, group d'in YARA MASU AJEEY yana d'aya daga cikin way'anda taturama,

Toh alokacin ABDUL yana online, dan haka akan idansa taturo da sakwan, nan yabi yana karantawa, irin sakwan nan ne da ake alaqanta manzan Allah dashi ace idan baka tura ma group kaza ba wani abu zai faru dakai, ko kuma ace wani ya fad'i maganar banza akan manzan Allah ga yanda abin ya kasance dashi, ko kuma ga wata tataka qur'ani tana me nunawa musulmai dan ransu ya b'aci,  sam ABDUL baya bin takan way'annan zancikan, dan haka karan farko maganarsa da wata mace a online bama a cikin wannan d'in ba yayima RAHMA magana akan wannan sakwan data turo wajen cewa, _Bai dace kudinga irin wannan post d'in ba RAHMAT, ya dace da'aka turo miki kijama wanda ya turo miki kunne wajen karya qara turo miki, amma bawai yasaki yad'a abinda aka b'ata  manzan Allah akansa ba, ya dace kima karatun kyakkyawar fahimta kigane kawai b'atanci ne irin na yahudawa dan kawai sudinga amfani damu wajen yad'a manufofinsu, na gaya miki gaskiya ne dan bana san kiraqa shere ring ma kowa._

Shuru RAHMA tayi bayan ta gama karanta abinda yace mata, azahirin gaskiya sai yanxu tagane turawan bashi da amfani, har zata sharesa sai kuma tace mai _Naji nagode_

 

 

 

Ahankali Ahankali ABDUL da RAHMA suke d'an magana, can da tafiya tayi nisa sai suka zama kamar abokai, dan idan RAHMA taga ABDUL na hira da maza y'an uwansa shiga takeyi ayi hirar da ita, haka shima idan yaga tana hira da abokan nasa yana shiga ayi hirar dashi sab'anin da da'idan yaga tana hira dasu baya shiga

 

 

 

 

Yau saura kwana biyu su ABDUL subar garin na Lagos, dan sun qara wata d'aya akan wata biyun da sukayi niya,

Toh yau d'in ta kasance Asabar da misalin qarfe goma sha d'aya, ABDUL ne da abokansa suke hira cikin group d'in harda RAHMA da UMMAKATI da qawarsu Yahanasu, k'arfin hirar dai akan  Yahanasun ce da wani surayinta dake nan cikin group d'in,

Toh ana wasa ne irin na wasa😀 Amma mezai faru😳, dama su takwas ne suke hirar, sai wanda ya bud'e group d'in yace "Yau ranar masoyace ta duk duniya, dan haka Dan Allah mu da muke online ayanxu mud'an tab'a wasan soyayya, mukuma tura group group dan muji comments d'in da za'ayi kan suwaye sukafi iya soyayya acikinmu, dan haka kowa ya zab'i budurwarsa acikinmu muyu wasan soyayyar yanzu dan a tantance,

 

 UMMAKATI tace, "kaji ka da wani zance, idan mukayi hakan miye fa'idarka,

Kanya bata amsa sai RAHMA tace, "koma dai miye fa'idarsa ai wasa ne, miye dan munyi wasan soyayya cikin group, nidai na tabbatar koda waye aka had'ani  sai mun cinyeku a soyayya🙈 ta fad'i hakan da kai qarshen zancenta da saka wannan birin me rufe fuska🙈👈🏻

 

Kowa dariya yama zancen nata,😀 Yahanasu qawarsu tace "um um RAHMA bar cika baki fa😀,

Tace "Allah da gaske nake kuma a fara a gani"

 

AMEER yace "toni na zab'i Yahanasu, sai Wanda ya bud'e group d'in yace, "ni kuma na zab'i UMMAKATI, ABDUL yayi murmushi duk da cewar gabansa ya fad'a amma haka ya share yace, "Nina zaɓi RAHEEMAT,

sai sauran biyun kasancewarsu dukkansu maza sai sukace, "Toh mune y'an sa ido👀 masu tantancewa, dan haka a kafta,

 

Nan wanda ya bud'e group d'in yace da UMMAKATI, "tun ranar dana fara ganinki ban qara samun kwanciyar hankali a rayuwata ba, wato UMMAKATI kin tafi da zuciyata, kin b'ata tunanin kwakwalwata, jina nake tamkar wanda bashi da hankaki, na kasa nutsuwa, na kasa samun kwanciyar hankali dan Allah kice kina sona kin yarda dani a soyayya...

 Jan numfashi UMMAKATI tayi da kallan RAHMA dake suna d'akin UMMAKATIN ne dama itama RAHMAN kallanta tayi nan take suka kwashe da dariya😆, RAHMA tace, "Dalla kibashi amsa.

Ahankali ko UMMAKATI tahau bashi amsa wajen cewa, "Hak'ik'a nima zuciyata bata dare da nutsuwa tun ranar dana had'a ido dakai, jeboy ina sanka ina qaunarka da fatan zamu gina rayuwarmu rayuwa irinta cikakkun masoya....

 

Sai AMEER ya karb'a yana cema Yahanasu, "wato matata ayanda nake samun farin ciki agunki bana tananin akwai wani wanda yake samun irin hakan agun matarsa, gaskiya babu qarya ina MASEEFAR sanki da qaunarki, dake kad'ai zan iya rayuwa ina fatan har a gidan aljanna ki kasance matata,

Murmushi Yahanasu tayi da cewa "Nima haka Abban Anisa, ina fatan qara zama matarka a gidan aljanna, ina sanka mijina ina qaunarka dan kaci gaba daji dani har bayan qarshen rayuwa bama qarshenta,

"Zanji dake matata nidai kawai kiyarda dani, "nayarda dakai mijina...

 

 

Ayanzu ABDUL da RAHMA ne suka rage aji irin nasu salan,

Sam ABDUL baisan me zaice ba, saboda shi bai iya soyayya ba, dan haka Ahankali ya kalli AMEER dake gefansa yana mai murmushin mugunta dan yasan indai ci akan soyayya to ABDUL dai bazai ci bah, dan bai iyata ba, baima san ya ake yinta,

Bayan ya gama fuskantar murmushin mugunta AMEER yake masa sai kawai yayi qaramin post ga RAHMA kamar haka, yace da ita "Kin tabbatar kina sona.

RAHMA taja numfashi tace dashi "Sosai ma kuwa, ina sanka ABDUL

Yace "toh muyi Aure mana.😊

RAHMA tace "zanyi farin ciki da hakan,

Yace "toh waye waliyinki

Tace "Ni kowama ya zama waniyi na.

Yace "kin amince, tace "kwarai ma kuwa na amince,

 ABDUL yace to turomin da A/C number naki naturo miki da sadaki yazu.

Nan gaban RAHMA ya fad'i ta kalli UMMAKATI, itama UMMAKATIN kallanta takeyi ad'an tsorace irin me yake shirin faruwa ne😳.

Nan dai RAHMA ta tura masa da account number nata.

Shuru group d'in ya d'auka suna masu kallan ikwan Allah, nan RAHMA taga sakwan shigowar kud'i wayarta.

 

"Dubu shittin😳.. RAHMA ta bad'a a bayyane tana me kallan UMMAKATI daci gaba da cewa, sadakina ya turan da dubu sittin..

UMMAKATI ta waro ido tace, "Harya turo miki ne.

RAHMA tace "gashi ko nagaya miki.

"Owkie, ai sai kice masa ya shigo kuci gaba muga k'arshen naku salan.

 

RAHMA tace da ABDUL "My dear naga sak'on sadakina dubu sittin ya shigo yanxu. Anya baiyi yawa ba, kasanfa albarkar Aure suke buqata.

 

Murmushi ABDUL yayi da d'agama AMEER gira wanda ya saki baki yana kallan ABDUL d'in da qurama wayarsa ido yana san ganin ikwan Allah,

 

ABDUL yace... "Haba my Baby, sam baiyi yawa ba, Yanxu dai acikin Suleiman da Usman masu saka ido cikin wannan wasan namu wa kika zab'a ya zama waliyinki.

   RAHMA tace "Na zaɓi Usman daya zama waliyina saboda nasan shi anan bayan layinmu yake.

ABDUL yace "gud hakan Yayi, nima na zab'i Suleiman dan shima yaran unguwarmu ne, yanxu sai kowa ya shaida dan yanxu za'a d'aura Auran namu..

 

Nan AMEER da jeeboy wanda ya bud'e group d'in suka ce sune shedu amma a jira sauran y'an group d'in suzo sai'a d'aura Auran,

ABDUL yace aa kawai a d'aura in yaso in sukazo saga komai..

 

Nan kamar wasa fa😳 suka d'aura Auran ABDUL da RAHMA, kowa ya shaida da auran. Kan kace kwabo nan su RAHMA suka cinye wasan.

Waliyansu suka basu making da yawa.

Yahanasu tace "RAHMA kin cika baki gashi salan naku ya cinye namu,

Yanzu wasa ya qare sai mujira comment d'in y'an group..

 

Aiko y'an group d'in suna zuwa nan suka dinga comments akan Auran nasu.

Wata acikinsu ana cemata Ashanty tawaro ido😳 a tsorace ganin abinda ya faru a group d'in tace, "Wallahi Auran gaske kukayi ABDUL da RAHMA kuje ku tambayi malamai na tabbatar zasu tabbatar muku da hakan, lallema, meya kaiku wannan kwamacalar😀.

Dake RAHMA tana online har lokaci nan tawaro ido itama waje tace, "What.. Aure na a group😨, ke dalla dakata malama wasa muke fah😀,

Ashanty tace "Wallahi bazan rantse miki a banza ba Wallahi tallahi  kuje wajen malamai ku tambayesu na tabbatar ke matar ABDUL ce yanzu😂

 

Tashi RAHMA tayi a rikice cikin tashin hankali takalli UMMAKATI tace, "Tunani yana san hautsinewa, kwakwalwata tana san rikicewa, wai me Ashanty take gaya min ne.😨

  UMMAKATI taja numfashi tace "abun abin a duba ne RAHEEMAT, nima yanxu hankalina ya tashi dajin abinda tace,

"Aurena ni RAHMA a group😨 RAHMA ta fad'i hakan cikin san fashewa da kuka, dan Wallahi ta tsorata sosai.

Nan ta d'auki gyalanta sai gidansu, a tsakar gidan taga mamanta na murja taliya, nan tazube ajikinta tana cewa, "Mama nashiga uku🙆🏼 Wallahi wasa muke yi bada gaske bane, dan Allah ki gaya min kice min wasa ne.

Maman ta kalleta da damuwa tace, "menene ya faru. Cikin kuka hannu aka RAHMA tace da itace. Aure aka d'aura min yanxu a cikin group kuma Wallahi DAGA WASA muka faru ni da shi, amma yanzu kinji wata Ashaty tace Wallahi Auran gaske mukayi, wai ba'a wasa da Aure....

Nan maman tatashi da zareta daga jikinta tadafe qirji tace "RAHEEMAT Aure ba abin wasa bane, tabbas yarinyar tafad'a muku gaskiya, shi kenan sai yazo ya d'auke ki ai kun kyauta... Maman takai qarshen zancen nata da murmushin yaqe.

 

Nan cikin RAHMA yad'au k'ogi ta qara d'ora hannu aka🙆🏼 ta kwalla k'ara tare da rushewa da kuka wiwi🤣 tana cewa "Na shiga uku an d'aura Aure na a group.....

Nanko take jama'ar gidan suka firfito maza da matan suna masu zaro ido da cewa me sukaji tana cewa, nan maman RAHMAN ta kora musu bayani kamar yanda tafad'a mata, basai kishiyoyin maman nata suka dafe qirji tare da qafa gwalalo ido har suna had'a baki wajen cewa "Munshiga uku😳, Aure, kuma Auran RAHMAN koba natan ba,

 

Mamanta tatabbatar musu da natan dai take nufi, nan suka hau salati suka wari rikice ba shiri ko waccen su tayi d'akinta tana cije yatsa, fad'i suke aransu tayaya hakan ta kasance, bayan bokansu yayi musu aiki akan ita da Aure har abada,  idanko tayi to asirin da suka mata zai koma kan y'ay'ansu mata.

Nan suka dinga safa da marwa Suna kai kawo alamar ya zasuyi...

 

Hmmm, ita dai RAHMA in banda kuka ba abinda takeyi, duk ƴan uwan nata mata sakata suka agaba suna kallanta, mazan ko waƴanda suke gida girgiza kai sukayi da cewa "Allah shi qara.. Suna faɗin hakan suka koma kan abubuwan da sukeyi.

 

Hawaye dumu dumu a fuskar RAHMA ta lalubo numbar ABDUL danta kirasa...

 

 

 

Suko anan AMEER ne ya rikice dan nan take yahau kiraye kirayen numbers d'in mutane yana tambayarsu shin ana yin auran wasa🙁

Kowa tabbatar mishi yakeyi da cewa ba'ayin auran wasa, dan addinin musuluncin ba abin wasa bane..

 ABDUL na jinsa sam bai wani damu ba. Saki ne dai idan tace ya saketa zai iya sakin nata dan dama ai shi mata bawai sun damesa bane🙅🏻.

 Suna cikin hakan saiga kiran RAHMA ya shigo wayar ABDUL, ba suna dan dama bawai Yayi seven num natan bane.

 

Sam bai zaci ita bace ya d'auka, saijinta yayi cikin kuka tana cewa, "Haba ABDUL ya zakamin haka, kasan ba'a wasa da Aure kace muyi..... Ta qarashe da qara volume d'in kukanta.

Shuru ABDUL yayi, da farko dai kukan nata ya taɓa  zuciyarsa, na biyu yana san tuno a inda yasan muryar tata, abu na uku bai taɓa jin wani yanayi agame da y'a mace ba kamar yanda yaji yanxu, ji yayi yana san taci gaba da magana, sannan kuma baya san taci gaba da kukan da takeyi,

Cikin sanyin murya yace, "Ina magana da RAHMA ne" afusace tace mai "Idan bada ita kike magana ba dawa kuke tsammanin kana magana adai-dai wannan lokacin, kawai so nake naji kace ka sakeni saki uku.....

 

"Da gaske...

Ya katseta da faɗin hakan dan yanzu ya gane muryarta sosai, itace dai yarinyar nan daya temaka a garin jos, tabbas kunnansa bazai manta da muryarta ba, Allah ya temaketa tamai rashin kunya ya nuna mata kuranta, dan haka cigaba yayi da cewa, idan naƙi sakin naki me zakiyi.

"Nemoka zanyi aduk inda kake, na cakume maka wiya wallahi ko kafi waye qoqari sai furta kalmar saki agareni.

"Yayi malama🏻 hakan yayi sosai👌🏻. Nayi miki alƙawarin nine zan kawo miki kaina har kofar gudanku danki aiwatar da abinda kikace agareni, idan kuma bakiyi ba, ni kuma zan kama hannunki nasaki amota na kawoki garinmu matsayin matar Aure nah?...

"Kayi kaɗan, Wallahi ƙaryarka tasha ƙarya, RAHMA ta katseshi da faɗin hakan tame tashi daga inda tare daci gaba da cewa, kana san ka nunamin kai TANTIRI ko, to bari kaji wallahi nafika TANTIRANCI, idan ka isa kai d'an halak ne kazo ƙofar gidan namu ba abinda zai hanani tabbatar maka da abinda nace maka, Ina garin Jos layin d'an k'arfalla, duk wanda ka tambaya wacece RAHEEMAT zai kawoka har kofar gidammu.

"Toh shi kenan, insha Allah nayi miki Alk'awarin zanzo, zamu bar garin Lagos yau  idan muka koma garinmu Kaduna nayi miki alqawari kwana d'aya zanyi a kadunan na duro garin naku, wallahi sai naga qarshen TANTIRANCIN KI...

  "Kodai naga qarshen naka ba, Allah ya kawoka kasan dawa kike wannan maganar, tana faɗin hakan ta kashe wayarta da kallan mahaifiyarta ta qara rushewa da kuka, tana meci gaba da cewa "nidai na shiga uku wallahi da wasa muka faru dashi😭.

Murmushi mahaifiyar tata tayi mata dayin d'akinta tana me neman number na mahaifinta tagaya masa abinda yake faruwa,

 

Itako RAHMA d'akinsu ta shige cikin tashin hankali, dan taji a jikinta ABDUL ya bambanta da samarin da take harka dasu, sam bataji wani alamun tashin hankali daga garesa ba, saima magana da yake mata cikin wani izza kamar wani tantiri, toh wallahi duk TANTIRANCINSA tafisa, yazo zaisha mamakinta...

 

 

ABDUL ajiye wayarsa yayi gefe yana murmushi, wallahi zai koyama yarinyar nan hankali, Allah ya kaisa gareta lafiya...

Kallansa kawai AMEER yayi ganin murmushi ma yakeyi, irin na wani abun da yake damunsa.....

 

 

 

 

Ina jiran comments

Muje zuwa y'an hannuna👐🏻. Karfa ku manta wannan labarin true life story ne, ku biyoni kuji yanda labarin zai kasance, shin da gaske Suna da Aure koko babu shi, By AUNTYN LUV 💋takuce....

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.*🙆🏻*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆🏼*.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`•🤱🏻

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 13

 

 

Sai yace dashi, "ABDUL ya dace muje mu tambayi malamai kan wannan batu, wallahi duk hankalina ya tashi"

"Hankalinka ya kwanta d'an uwa, Wallahi sam banji wani damuwa araina ba, ina san kaima kacire damuwar aranka" ABDUL ya katse AMEER da faɗin hakan.

Sai AMEER d'in yaja numfashi yace, "Yanxu ayau zasu bar garin nan kenan" "Eh, kawai mutafi yau d'in, dama ai ba jiran wani abu muke ba" Abdul ya qara katse shi wajen qara bashi amsa.

 

Haka ko akayi dan awannan lokacin suka had'a kayansu sukayi airport dan barin garin na Lagos...

 

 

 

_______

Sallah kawai RAHMA takeyi awannan ranah bacin haka ba wani abu da takeyi sai aikin tunani da kuka.

UMMAKATI tayi mata lallashin duniyar nan amma ko kallanta batayi ba, daga qarshe ma barinma UMMAKATIN tayi gidan nasu tayi gidansu UMMAKATIN, anan UMMAKATIN take qara gayama maman RAHMAN yanda abin ya faru, shuru kawai maman tayi tana nazari, ganin hakan sai UMMAKATI takoma gidansu tare daci gaba da bama RAHMA baki.

 

 

Ba kowa agidan nasu yanxu dan duk yaran gidan sun fatta da alama kowa yana da wajen zuwa ne, sai ya kasance daga maman RAHMA sai kishiyoyinta, nan tafito sanye da hijab danta leqa makwaftansu barka anyi aihuwa.

Sanda ta lek'a duk d'akunan kishiyoyin nata tace musu bara ta leqa makwafta barka, dama itace bata leqa ba.

 

Cikin jin daɗin zata fitta alokacin da suke buk'ata nan suka amsa mata da kulawa, tana fitta ko nan suka had'e a d'akin Lantana wato ta uku dan itace uwar sharri.

Iyami ta kalli  Lantana tace, "Mun shiga uku, yanxu ya zamuyi, ina jin tsoran karfa abinda mukama RAHMA ya dawo kan y'ay'anmu kamar yanda boka ya shaida mana muddin aka d'aura Auranta asirin kan y'ay'anmu zai dawo.

Asabe tace "hmmm, aini duk narasa nutsuwata, hankalina duk ya tashi, Lantana kisama mana mafita dan kinsan yace idan ya dawo kan y'ay'anmu zasu aikata TANTIRANCIN dayafi na RAHAMAN, kinga tunkan hakan tafaru dan Allah muyanke abin daya dace.

Lantana taja numfashi tace "mafita d'ayace garemu yanxu, itace mukoma wajen bokan mu gaya masa komai, na tabbatar zai temakemu.

Iyami tace "amma yau zamuje garesa ko. "aa saurin me kikeyi ne, mudai bari citta maje tunda kunga ranar ne sunan Hauwa'u zamu fitta gabaki d'ayanmu, amma idan mukace zamu yau ai bazai yuhuba, sam babansu bayarda zaiyi mu ficce mu uku a alokaci d'aya ba, tambayarmu zai fara yi ina zamu mu uku haka kamar anyi mutuwa, amma kunga wannan dake sunan K'anwarsa ne zai barmu kunga daga can saimu sulale mubar maman nata muje garesa koya kuka gani.

Asabe tace "Zancenki hakk'un, mu bari sai cittan maje......

 

Gabaki d'aya wannan zancikan nasu akan kunnan maman RAHMA sukayi, dan tana fitta taci karo da Larai wata makwafciyarsu tafito daga gidan da zata shiga danyin barkan, saita tambayeta ina zata tace zata leqa gidanne tayima Furera barka, Sai Larai tace mata ai bata nan Fureran sunje asibiti da jaririya za'a mata allura kuma yanxu fitansu kenan saidai tabari idan tadawo tayi mata.

To shine maman RAHMA tadawo gidan nasu sai taga shigar iyami d'akin Lantana dajin abinda suke faɗi..

Har wani jiri ne taji yana iyabanta, ahankali dai tadafe bango ta shige d'akinta tana mamakin mugun hali irin na mutane, dan Kawai mahaifin yarinya na santa shikenan sai suje su aikata mata asiri, Innalillahiwainna'ilaihirraji'un duniya tazo qarshe. Nan hawayen baqin ciki ya zubo mata ta share tana tunanin me zatayi itako tarama abinda suka mata, nan tadinga tunani kala kala daga qarshe tayanke shawarar Auran RAHMAN shine kawai abinda zai wanke mata baqin cikin da suka d'auki shekara da shekaru suna bata, tasani Auran ABDUL d'in da RAHMAN akwai gyara cikinsa dan sadaki ya dace ya kasance a hannun mahaifinta ne ba'a hannunta ba, bari dai tabari ubanta ya dawo susan nayi,  saidai bazata tab'a bari wannan damar ta wucceta ba, dan zatayi amfani da ita ne wajen ganin tadatse dukkan wani makircin da suka kullama RAHMANTA, tabbas dole ABDUL d'in ya zama miji ga RAHMAN, dan kawo qarshensu,.

 

 

Baban RAHMA nadawowa yahau tambayar maman RAHMAN kan wane batu ne take gayamai d'azu a waya, zaunar dashi tayi da bashi ruwa me sanyi sannan ta zaiyane masa komai, amma bata gaya mai abinda su Lantana sukama RAHMAN ba, saidai ta gyara zama ta tsaida dukkan nutsuwarta garesa tace dashi, "ni abin danaga ya dace anan shine, na lura Auran RAHEEMAT shine abinda ya dace, zai bamu farin ciki da nutsuwa da kwanciyar hankali, ko'a tarihi ban tab'a cin karo da yarinya maraji kamar RAHEEMAT ba, dan haka na yanke shawarar koda ace Auran nasu bai d'auru ba ak'ara d'aura musu wani. wallahi dama ni nagaji da halin RAHEEMAT.

Jan numfashi Baban RAHMAN yayi yace, "Banji dad'in wannan lamari ba, sam banji dad'insa ba, amma yanda kikace hakan za'ayi, saidai yanxu fara kiramin ita RAHMAN taban number na yaran na kirasa naji yanda suka d'aura Auran, idan da gyara sai kawai a gyara musu idan bai d'auru ba zanji tabakin yaran idan yana da ra'ayinta saina d'aura masa ita.

"Hakan yayi, maman tafad'i hakan tana me lalubar num na RAHMA danta kirata.

RAHMA na kwance gadan UMMAKATI sai aikin rahawaye take tana tsinewa ABDUL aranta, sai ganin kiran mahaifiyar tata tayi, bayan ta d'auka gaya mata tayi tazo gida yanxu tana nemanta, RAHMA najin hakan tatashi tayi gidan nasu, anan d'akin maman nata taga mahaifin nata, yace tabashi number na ABDUL, tana turo baki tabashi numbar ABDUL d'in, nan yace mata to tatashi taje dama numbar kawai zai karb'a, bayan ta fitta nan yakira ABDUL, lokacin suna  airport basu samu jirji ba, saidai masu aikin wajen sun basu tabbacin gobe zasu samu me tafiya arewa qarfe shidda na safe. Dan haka sai suka nufo dawowa hotel d'in da suka sauka cikin jin haushi, bayan ABDUL ya d'auki wayar tasa ahankali yake gaisar da baban RAHMAN da tambayarsa waye shi, nan ya gayama ABDUL d'in shi mahaifin RAHMA ne, yana san jin yanda suka d'aura Auran nasu, nan ba b'ata lokaci ABDUL ya gaya masa yanda suka d'aura, murmushi baban RAHMA yayi yace mai yazo jos ya samesa, Amman yana rokwansa alfarma yazo da iyayensa maza dan yana so su qara tabbatar da lamarin saboda wani dalili nashi.

Nan cikin ladabi ABDUL ya amsa mai da cewa indai ya dawo daga Lagos zaizo insha Allah da iyayen nasa.

Sosai ABDUL ya kwanta aran mahaifin RAHMA, haka kawai yaji yana san yaran, yana fatan yazo garesa lafiya yaji waye shi.

 

 

 

 

Washe gari ko su ABDUL suka bar garin na Lagos, sun sauka a Abuja lafiya, saidai sanda sukayi kwana d'aya anan, washe garima sanda suka kai wajen qarfe biyar kana sukaje tasha suka hau motar Kaduna, lokacin da suka iso Kaduna qarfe goma sha d'aya na dare ne,  ABDUL baiyi shashin Hajjiya Kakah ba, shashinsa yayi da zubewa kan katifarsa cikin jin daɗin yanda suka dawo lafiya, AMEER ne dai iyayensa suka san ya dawo, saboda bud'e gidan da sukaji anyi, nan sukayi kansa da fad'a wai akan meyasa zaiyi tafiya bai gaya musu ba, me yasa sam bai d'aukesu a bakin komai bane, karfa ya manta sufa iyayensa ne.

Shuru yayi musu kawai yana jinsu, sanda suka gama yace dasu Shifa yanzu ba Yaro bane, danya girma, sudena saka masa ido akan al'amuransa, tafiya ce dai yayi kuma bai gaya musu ba wani abu ne, yana gaya musu hakan yayi shashinsa cikin b'acin rai, dan sosai ransa ya b'aci da faɗan nasu garesa. (Allah ya shirya)...

 

 

 

Washe gari bayan ABDUL yayi wanka ya kintsa d'akinsa zuwa wajen mahaifiyarsa yayi ya gaisheta, saidai daqer ta'amsa masa, shidai ajiye mata tsarabarta yayi ya qara gaba  shashin Hajjiya Kakah dan taganshi cikin yi mata bazata,

Anan yaga mahaifinsa, yako ji daɗin hakan,

Hajjiya Kakah taji dad'in ganinsa sosai, bayan sun gama gaisawa yayi breakfast kana ya sasu agaba ya kwashe komai daya faru tsakaninsa da RAHMA ya gaya musu, ya qara da gaya musu yanda sukayi da babanta.

Murna sosai Hajjiya Kakah tayi, nan tahau tunanin Allah yasa ko Auran nasu bai d'auru ba a sake d'aura wani, dan bazata manta da abinda malamai suka gaya mata kan tantirancin ABDUL d'in ba, na muddin aka mai Aure ba makawa duk asirin dake jikinsa zai karye...

Nan cikin zumuɗi Hajjiya Kakah tace da ABDUL d'in, "Dani za'a garin Jos d'in, zamu kwana gidan Hajjiya Saratu qawata, nasan zataji dad'i sosai dan rabona da ita yau shekara Hud'u kenan, cikakkiyar aminiyata ce aika santa tana kawomin ziyara,

Shuru ABDUL yayi yana san tunota, tabbas ya ganeta dan tun yana Yaro yake ganinta tana kawoma Hajjiya Kakan ziyara, amma shi bai tab'a ganin Hajjiya Kakan takai mata ziyaran ba, dan haka kallanta yayi da cewa, "Naganeta, dama kamar baki tab'a kai mata ziyara ba ko"

Murmushi tayi da bashi amsa, "Eh, sau biyu na tab'a kai mata ziraya, Auranta da aihuwarta ta fari, tasan lafiya bata isheni ba shiyasa bata damuwa da zuwana.

 "Ok, Allah yabar qauna,

Mahaifinsa yace "gaskiya banji dad'in faruwar lamarin nan ba ABDUL, sam baku kyauta ba, dan ba'a wasa da addini, addini ba abin wasa bane, dan haka ku kiyaye nan gaba.

Cikin ladabi ABDUL yace mai, "Toh zamu kiyaye.

"Yanxu zan kira su Baba Shehu mu zanta yanda mukayi zan gaya maka da daddare.

"Toh, ABDUL yace mai da maida kallansa ga Hajjiya Kakah yaci gaba da cewa, Yanxu bara naje gidan AUNTY ZAINAB na gaisheta.

"Toh, adawo lafiya, Allah yay maka albarka, 

"Ameen yace mata da ficcewa daga falan...

 

 

Sanda ya shiga gidansu AMEER ya gaishe da iyayensa sannan yay gidan ZAINAB d'in, Ya ganta a falo kwance kan kujera da alama zazzab'i ne yake san kamata danta dukunkune cikin wani qaramin  tsaftacaccen bargwanta, d'akin nata sai tashin qamshin turare yake, ZAINAB tana da tsafta fiye da tunanin me tunani,

Tana ganinsa tayi qarfin halin tashi cikin murna take mai sannu da zuwa, Ahankali ya amsa mata yana me mata kallan wurillar san gano me yake damunta,

Ta tsargu da kallan da yake mata dan haka cikin alkarewa dashi tace, "Amai da gudawa nakeyi, ina ganin shi yake san sakamin zazzab'i,

Shuru yayi mata, itama sai tayi shurun,.

Can ya d'auke idansa daga fallanta yace "Aunty ko har yanxu kina da matsala da mijin naki ne, naga haskenki ya ragu. Gashi kinyi wata rama, akwai abin dake damunki ne.

Murmushi tayi mai da cewa, "wallahi ABDUL ban tab'a jin dad'in mu'amala ta rayuwa da Salisu irin na wannan karan ba, sam baya san b'acin raina ayanzu, sannan ya rage yawan daran dayake yi, kawai matsalata da danginsa ne ayanzu, ABDUL mahaifiyarsa aihuwa take so kamar me, gashi ni har yanzu aihuwar batazo gareni ba, qannansa zuwa gareni suke sumin rashin kunya akan hakan, kuma ba dama nayi magana dan nan take take zuwa tawankeni soso da sabulu, ABDUL ina san na haihuwa wallahi ina san yara, gashi yanzu tace mai wai dole ya qara Aure, ABDUL zanyi rayuwa da kishiya wallahi bana san hakan, bana san kishiya na tsaneta, haka kawai ina zamana da mijina sai tacemai yayi aure yayi min kishiya kuma kishiyarma y'ar uwarsa wacce take santa, wane baqin ciki zan gani, sam yarinyar bata da kunya bata da kamun kai, ina sha'awar rayuwa da mijina ni kad'ai, danna tara duk wani abu da d'a namiji yake buqata agun mace. ZAINAB takai qarshen zancenta da zubo da hawaye.

ABDUL yaja numfashi da kallanta yana me cewa, "Kiyi hak'uri my Aunty, komai yayi farko zaiyi qarshe, kuma kisaka azuciyarki haihuwa ta Allah ce, shi yasan me yake nufi da hakan daya hanaki yanzu da kike buqata, kinemi zab'inshi banaki ba kiga dai dai, na tabbatar zaki haihu Auntyna, zaki haifamin k'anne masu kyau kamarki, Wallahi Aunty zaki haihu, karki damu da abinda suke faɗi, dan basu tara sani da Allah ba, fatana kisaka Allahn agabanki ya isan miki kinji Auntyna. Ya qarashe maganar da sakar mata murmushi.

Murmushin itama tayi mai da cewa, "toh nagode, ya garin na Lagos kun dawo lafiya.

"Lafiya muka dawo Auntyna, saidai nazo miki da wani batu, nan ABDUL ya kwashe komai ya gaya mata na Auransa da RAHMA, sanda gaban ZAINAB ya fad'i, kuma bazatace ga dalilin faɗuwan gaban nata ba, ita dai taji dad'in lamarin dan dama rokwan Allah take kan ya kawo mata ranar Auran ABDUL d'in, dan asirin dake d'awainiya da shi ya karye, ahankali tace, "Gaskiya naji dad'in hakan, kuma idan aka tabbatar maka da cewar auren naku nanan dan Allah karka saketa, haka kawai naji ina santa, kai anya ma kuwa badani za'a garin na Jos d'in ba, dama ban tab'a zuwa ba, gashi ina fatan na had'u da wata marubuciya acen (RAHMA NALELE).

 

"Aunty baki jin daɗin jikinki, dan Allah karkice zaki kibari har gida zan kawo miki ita idan komai ya dai-daita.

Tace "amma zanso ayi komai agabana ai.

Yace "Kawai Aunty kishare, dan komai dazai faru zan gaya miki kamar akan idanki akayi.

Murmushi kawai ZAINAB tamai.

 

 

 

 

Kasancewar Dadyn AMEER amini ne ga Baban ABDUL nan ya gaya masa komai na Auran ABDUL d'in da RAHMA, yayi mamaki sosai dan haka yace goben dashi za'aje dama yana san ganin wani d'an uwansa,

 

Saiya kama mutum biyar ne zasu Hajjiya Kakah da baban ABDUL da Baba Shehu da qaninsa da Dadyn AMEER sai ABDUL da AMEER cukutan na bakwai,

    washe gari ko da qarfe shidda suka antayo garin na jos, da motarsu suka tafi, da motar su AMEER da motar Dadynsa

Hajjiya Kakah dai motarsu AMEER tahau, su Baba Shehu ko motar Dadyn AMEER d'in suka hau.

 Saidai sanda ABDUL yakira Baban RAHMA yazo ya kaisu gidan nashi, dan bazai iya gane gidan ba,  kasancewar ranar daya kai RAHMA gidan da daddare ne, kuma daqer ta'iya kawosu gidan.

 

Abin mamaki baban RAHMA d'an uwa ne ga Dadyn AMEER, shine wanda Dadyn AMEER d'in yake faɗin zai duba,

Wannan abu ya basu mamaki sosai dan Dadyn AMEER yana kawoma baban RAHMAN ziyara lokaci lokaci, haka shima yana kai masa ziyarar lokaci lokacin. Dan y'an uwan juna ne na gaske ba gaji gare gaji gare ba, dan kakansu d'aya, shiya haifi iyayansu maza, Dadyn AMEER yana temakwan Baban RAHMA sosai arayuwa, hakan yasa baban RAHMA yake sanshi da qaunarsa.

 

A d'akin d'aya daga cikin y'ay'ansa ya saukesu, dama maman RAHMA tayi musu abinci nan da sukayi sallah sukaci sosai dan ta'iya abinci ba d'an kad'an ba.

Babu b'ata lokaci suka buqaci ABDUL da AMEER dasu qara musu bayanin yanda suka d'aura Auran,

Nan ko suka koro musu bayanin komai, gaskiya basu d'aura Auran dai dai yanda ake so ba, Auran yana buqatar gyara, musamman yanda sadakin baizo ta hannun mahaifin RAHMAN ba,  wannan dalilin yasa dole Auran nasu yana buqatar gyara,

Nasiha sosai sukama ABDUL da AMEER kan karsu sake aikata ganganci irin wannan, sannan mahaifin RAHMA ya kallali ABDUL cikin so da qauna, yace "A zahirin gaskiya qaunarka tashiga raina, haka kawai naji ina qaunarka ina san na baka Auran RAHMA, duk da cewar ina da sani akan rashin jinka kai da AMEER abakin Dadynsa, dama kai ne dai ban sani ba, amma nasan AMEER sosai shima ya sanni dan ina zuwa gidansu lokaci lokaci kaima mahaifinsa ziyara, naso ace auran nan naku ya d'auru yanda akeyi, da wallahi bazance maka kasaki RaHMA ba, dan dakai tadace, b'cos aduniya banga mutumin daya tsayama RAHMA arai take kuka sanadinsa ba, amma kai kasaka mata tsoro aranta faɗi take tashiga uku ta abo ruwan dafa kanta dan kayi furucin bazaka saketa ba, da bakinta take gayama mahaifiyarta hakan, yanzu inasan nasan labarinka idan na gamsu nayi maka alqawarin baka Auran RAHMA.

Jan numfashi Hajjiya Kakah tayi tace da AMEER da ABDUL d'in su fitta daga d'akin zatayi magana da Baban RAHMAN.

Nanko su ABDUL d'in suka fitta,  Yayan RAHMA Usman ya gansu suka gaishesa da kulawa yace suzo su shiga d'akinsa, nan suka shiga d'akin nasa dajin dad'in yanda yayi masu.

 

Hajjiya Kakah ko gyara zama tayi ta karanto ma mahaifin RAHMA Komai akan ABDUL bata b'oye masa Komai ba.

Nan ko ya jinjina lamarin nasa, musamman ma asirin dayaji yana d'awainiya dashi da tsanar da mahaifiyarsa take masa.

Kan yayi magana maman RAHMA taja numfashi da gyara nata zaman ta gaya musu rashin ji irin na RAHMA, daga qarshe ta qara da cewa, "Nima inaji a jikina idan aka d'aurama RAHMA Aure ba makawa duk wani rashin ji nata zaiyi sauqi, dan haka ina bada shawarar a had'a AURAN ABDUL da RAHMA dan ina kyautata zatan yin hakan zai kawo haske arayuwarsu.

 

Kowa awajen tattara nutsuwarsa waje guda yayi yaga dacewar shawarar tata, dan haka Baban RAHMA yace ya amince da Auran nasu, yanzu bara ya kira aminansa a d'aura Auran yanzu ba wani batun b'ata lokaci.

Nan ya ficce yaje ya kira aminan nasa, Hajjiya Kakah da maman RAHMA suka fitta daga d'akin Dadyn AMEER ya bada sadaki dubu saba'in batare da b'ata lokaci ba nan take aka D'aura  Auran Abdullahi (ABDUL) da Rahma (RAHEEMAT)

 

Kowa cikinsu ya shaida wannan Aure, saidai me zai faru,🤔 tunda aka d'aura Auran ABDUL dake d'akin Usman ya fara jin wata hajijiya akansa, kamar ana kunce masa wasu notika a kansa, ya tashi yana rik'e kan nasa cikin wani hali yana cewa, "Kaina zan mutu, wayyo kaina zan mutu, kan AMEER da Usman suyimai wani abu tuni ya faɗa qasa sumamme. Nan cikin tashin hankali suka hau yayyafa mishi ruwa amma ina sam ko alamar motsi babu ga ABDUL, hankalinsu ya dad'a tashi nan sukayo d'akin da iyayen nasu suke suka fad'a musu ABDUL fa ya fad'i yanzun nan.

Hajjiya Kakah tace "Ai dama nasan hakan saita faru, kunga aikin asirin ko.

nan iyayen sukayi d'akin suna masu salati, saidai wani abu daya qara d'aure musu kai wanda ya furgitasu shine jini suka gani yana fittowa ta bakin ABDUL d'in da hankinsa tare da wani abu kore haka babu kyan gani.

Jinin sosai yake fitta fa😨.. wanda kallo d'aya zaka mai kasan idan har ya dad'e a hakan ba makawa mutuwa zaiyi, gashi shi ba motsi yake ba, amma haka jinin yake fitta daga jikinsa,

 

Ga RAHMA ko itama ga yanda nata lamarin ya kasance, dan tana gidansu UMMAKATI kwance a gadan UMMAKATIN tana shirya wulak'ancin da zatama ABDUL, Dan taji mamanta na fad'in yau zasuzo suna kan hanya, to shinefa da'aka qara d'aura masu Auran taji gabanta ya yanke ya fad'i, nan  tatashi tayo tsakar gidan gidan hannunta dafe da qirji, ji tayi kamar an zare mata wani kayan nauyi akanta, nan take jiri ya abeta ta zube k'asa sumammiya,

Nanko maman UMMAKATI da UMMAKATIN sukayo kanta suna masu kiran sunanta, saidai ina tayi kamar babu rai ajikinta. Nan cikin tashin hankali maman UMMAKATI tahau yayyafa mata ruwa, amma ko alamar farfad'owa babu ga RAHMA itama, dan haka tace da UMMAKATI taje gidansu RAHMAN tagayama mamanta abin dayake faruwa

 

Lokacin data shiga gidan lokacin Usman da AMEER suke fitto da ABDUL ranga ranga dan sashi cikin mota su kaishi asibiti, 

Babu b'ata lokaci nan tagaya musu RAHMA tafad'i kuma sunsa mata ruwa taqi farfad'owa.

Haka hankalinsu ya qara tashi suka tambayeta meya jawo mata fad'uwan, tace ita dai ganinta tayi ta fitto daga d'aki hannunta dafe da qirji daga haka saita fad'i..

Nan ko su AMEER sukayi gidansu UMMAKATIN suka d'auko RAHMAN itama suka sata a mota sai asibiti,

 

Matanity sunan asibitin da suka kaisu, kasancewar yafi kusa dasu, anan cikin gaggawa doctors suka hau yi musu binkicen gaggawa, ABDUL dai ya zubda jini sosai dan haka yana buqatar jini, babu b'ata lokaci haka sukazo suka gaya musu suna buqatar jini nan cikin gaggawa,

Baban ABDUL yace shi mahaifinsa ne ad'auki jininsa.

 

Abin mamaki😳 da'aka gwada jinin Baban ABDUL d'in saiya nunama doctor jininsu ba d'aya bane🙅🏻.

Baban ABDUL yace wannan zancen banza ne ai ABDUL d'ansa ne dan haka dole jininsu ya zama d'aya, dole yanzu su ibi jininsa su saka mai dan yana san d'ansa baya san ya mutu su'ibi jinin cikin gaggawa a saka masa yana san ganin d'ansa araye, su kuma sukace baza su iba  ba, dan Komai yana da qaqida, idan dai yana san agwada jininsa dana ABDUL d'in ne sai'a gwada dan ashare mai tantama, aga d'ansa ne ko ba d'ansa ba.

Aiko yana jin hakan yace ya yarda agwada.

 

Doctor ya gwada jinin ABDUL dana Baban ABDUL d'in ya nuna masa ABDUL ba d'ansa bane🙅🏻...

Lokacin da doctorn yake gayama baban ABDUL d'in jirine ya nemi ibansa Allah dai ya kare aka taresa bai faɗi ba,

Dadyn AMEER yace a ibi jininsa a sakama ABDUL d'in saboda karsu rasa shi,

Doctor yana gwada jinin nasa yaga daidai yake dana ABDUL d'in, yaqara dai yimai babban gwaji wanda zai bada komai, nan sakamako ya bashi tabbaci kan ABDUL d'an Dadyn AMEER ne🤔

Doctor da mamaki ya kalli Dadyn AMEER bayan ya ibi jinin ya sakama ABDUL d'in yace dashi yasamesa a office d'insa,

Bayan Dadyn AMEER yaje garesa cemai yayi  "Abin yaban mamaki, dan binkice ya nuna majinyacin d'anka, kuma gashi wancen mutumin yace d'ansa ne,  koda yake binkice ya nuna ba d'ansa bane, Kai ne ubansa.

Cikin waro ido😳 Dadyn AMEER yace "Ban gane me kake nufi ba doctor, kana nufin ABDUL D'ANA ne.....

D'aga masa kai doctor yayi cikin tabbatarwa da cewa,  "Haka dai binkice ya nuna"

Tashi Dadyn AMEER yayi dayin waje yaje ya kamo hannun AMEER yace "Doctor wannan shine d'ana, kuma Wallahi da mahaifiyarsa kad'ai natab'a mu'amala ta rayuwar Aure,

Doctor ya kalli AMEER Sosai yace "Gaskiya abin da rikitarwa, amma bara na gwada jinin shi wannan d'in nagani.

Shuru Dadyn AMEER yayi masa,

Haka sukayi d'akin gwaji da AMEER, shi kuma Dadyn yazo ya gayama su Baban ABDUL ada😀 cewa gafa abinda doctor yace, wai ABDUL d'ansa ne, tayaya hakan tafaru, bayan shi bai tab'ayin mata biyu, kuma mu'amala ta Aure bata tab'a had'asa da wata y'a mace bayan matarsa ba.

Wannan abu yaba kowa mamaki.

 

Nan Baban ABDUL yakira  doctorn yacemai ya gwada jininsa dana AMEER yaga d'ansa ne..

Baban RAHMA yace me hakan yake nufi, yace kawai yaji aransa cikin Abdul da Ameer dole d'aya ya kasance d'ansa dan ƙaunar da yake musu bata wasa bace.

  Baba Shehu yace wannan ba hujja ba, Dadyn AMEER yace aa ayi dai yanda yace...

 

Abin dai da kulle kai yake,🤔 dan bincike ya nuna ABDUL ɗane ga Dadyn  AMEER, sannan AMEER ɗane ga Baban ABDUL..

 

Komai ya hautsine, dan gabaki d'ayansu sun shiga rud'u, hankalinsu ya bala'in tashi, tabbas akwai abin daya faru, kuma matansu su zasu gaya masu Komai,

 

ALLAH yasa suna da hankali ba irin mata ba, dan wani sab'ani bai shiga tsakaninsu a wannan lokaci ba,

 

Yau ce ranah tafarko da AMEER yayi nadamar abinda yake aikatama iyayen nasa arayuwa, dan tunkan asan bakin zaran zancen ya kama qafar Dadynsa ya fashe da kuka yana cewa Dady ka yafemin abinda nadinga aikata maka arayuwa, nasan koma wane labari za'a bada nan gaba nasan bazai kasance me kyau bane agareni, kaga farta min dan Allah, ashe duk wannan abun da nake maka ashe ni ba d'anka bane....

Hawaye ne ya zuboma Dadyn nasa da duk wanda yake wajen... sai rahma nalele tatsaida hannunta daga rubutun, da takema masoyan nata, tana me hararo abubuwan da zasu faru nan gaba...😀

 

 

By Rahma Nalele Auntyn luv💋

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.*🙆🏻*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆🏼*.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`•🤱🏻

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 14

 

*Masoyana ina dad'a baku hak'uri, lafiyace bata isheni ba, rahma nalele dai takuce ƴan hannuna*💋

 

D'agasa Dadyn yayi da rungumarsa yace "kai d'ana ne AMEER, hakan bazai tab'a canjawa ba" kuka sosai AMEER yakeyi yana cewa, "ka gafarta min Dady nayi nadama"

 

Kowa sai share hawaye yakeyi awajen tare da girgiza kai da tayin mamakin lamarin,

 

RAHMA tasamu kanta sanadin temakwan data samu wajen doctor, amma tatashi da mutuwar jiki, hutu take buqata sosai dan ji take kamar anlakad'a mata dukan tsiya,

 

ABDUL dai bazai samu kansa nan kusa ba, dan doctor ya tabbatar musu saiya kai awa Ashirin da hud'u zai farfad'o, ahakan ma zato yake yi, wannan dalilin shiyasa su Dadyn komawa gidansu RAHMA da RAHMAN.

Anan sukaba Hajjiya Kakah labarin abinda yake faruwa, nan take ko hankalin Hajjiya Kakah ya tashi, fad'i take, "nidai dan Allah dan annabi karku rabani da ABDUL, danya zama jinin jikina, idan bana ganinsa hankalina baya kwanciya,

 

Dady murmushi yayi mata kawai, ashe ba banza ba yake matuƙar ƙaunar ABDUL, tabbas kuma miye ya faru ba qaramin abu bane, Allah dai ya maidasu gida lafiya su zanta da matansu...

 

Haka sukaje suka kama hotel d'in Sharna suna masu addu'ar Allah yasa ABDUL ya farfad'o cikin gaggawa su koma gida dan su kawar da  damuwa.

 

Hajjiya Kakah ko gidan Hajjiya Saratu tayi aminiyarta, aiko tasamu tarba mekyau agunta dan rasa inda zata sata tayi dan farin ciki, haka ta cika mata gabanta da kayan ci dana marmari, Hajjiya Kakah bata iya cin komai saboda damuwar dake cinta arai, wallahi bata san arabata da ABDUL dan tafi kowa sanin san ƴaƴa irin na Dadyn AMEER..

Nan ta gyara zama bata b'oye ma aminiyar tata komai ba tagaya mata damuwar dake damunta yanzu, dama ance abokin kuka shi ake gayama mutuwa, aiko Hankalin Hajjiya Saratu ya tashi, dan itama tasan ƙaunar da Hajjiya Kakah takema ABDUL, sam baza taso a rabata dashi ba, nan tadinga kwantar mata da hankali wajen nuna mata ABDUL bazai iya yada ita ba, dan yana matuqar qaunarta. Hajjiya Kakah ta gamsu da maganar Hajjiya Saratu, dan da wiya kam ABDUL ya iya yada ita.

D'akinta Hajjiya Saratu tabarma Hajjiya Kakah dan takwana cikinsa.

 

 

 

 

Dake maman RAHMA tasan RAHMAN tana fashin sallah sam batabi takanta dan tatashi tayi sallar la'asar bangariba i'sha ba, haka tabarta tadinga sharara bacci abinta, sai wajen karfe taran dare sannan ta iya tashi, amma tatashi da qarfin jiki sosai, dake a d'akin maman nata tayi baccin hakan yasa data tashi ta kalli maman nata tace, "Mama ruwan wanka,

"Au kin tashi ne, aidama nasan zaki buqata bara naje na juye miki dan dana gama tuwa na d'ora miki tuntuni, ina da tabbacin yama tafasa yanzu" maman nata ta bata amsa tana me tashi dan zuwa juye mata.

RAHMA tayi murmushi da cewa "Yauwa nagode mamana"

 

Bayan tayi wankan d'akinsu na y'an mata tayi dan saka kaya, ba kowa a d'akin da alama duk y'an uwan nata sun ficce wajen samarinsu, haka ta canja kayan ta koma d'akin maman nata dan taci abinci, tana cikin cin ne ta kalli maman nata tace, "Wallahi mamah sai nake jina kamar wata sabowa, gabaki d'aya jikina ya canja, kamar an d'auke min wani kaya me d'auyi akaina, sam ban tab'a jin hakan a gareni ba"

Maman taja numfashi tace, "Ai dama haka ne, wata ranah duk sai kaji kamar an zare maka wani abu ajikinka, dama ina san gaya miki maganar yaran nan ABDUL wanda kukayi Aure a group, nan take gaban RAHMA ya fad'i ita sai yanzu ma tatuna da batunsa, cikin sauri ta katse mahaifiyar tata da cewa, "Eh, meya faru,

Tace "ai d'azu iyayensa ne suka dawo dake gida daga asibiti" shima yana asibitin, nan anan ya fad'i.

"Ok,  ashe sune iyayen nasa, wai mema ya jawo min fad'uwan ne dahar aka kaini asibitin"

"Oho, ina zan sani, UMMAKATI dai tace kawai ganinki tayi kin fito hannu dafe da qirji sai kuma kika fad'i"

"O, na tuna, tabbas anyi haka, dan haka kawai naji gabana ya yanke ya fad'i, sannan kuma dana fitto tsakar gidan sai naji jiri ya kamani, daga haka bansan meya faru ba, yanzu dai gaya min mama, ba dai wani batun Aure tsakani na dashi ko"

  "Ai kunyi kuskure RAHEEMAT, Aure ya kwullu tsakaninku ke dashi, wallahi yanzu ABDUL mijinki ne, maman ta fad'in mata hakan dan tace bazata gaya mata cewar wani Auran aka d'aura mata dashi ba, dan tana san taqara tabbatar mata da cewa musulinci ba abin wasa bane.

  Aiko nan take RAHMA ta zare hannunta daga cikin miyar tuwan da take ci, hankalinta tashe tace, "Na shiga uku ni RAHMA, wallahi bana sanshi, danna tabbatar bazai zamo d'aya daga cikin mazajen danake fatan na Aura ba, kuma ma ni yanzu ban shiryama kaina Auran yanzu ba, wallahi tallahi saiya sakeni danni ban shirya zaman Aure dashi ba.

   Murmushin takaici maman nata tayi mata da cewa, "hmmm RAHEEMAT kenan, sam baki da hankali, kidai bi duniya ahankali dan ABDUL ya fiki rashin ji, yafiki TANTIRANCI ayanda naji labarinsa wajen kakarsa, sannan bazan so ya sake ki ba, dan ɗan uwanki ne, yaro ne ga ɗan uwan mahaifinki Alhaji Aminu wanda yake zama a garin Kaduna aikin sanshi sasoi dan yana zuwa nan kawo mai ziyara kamar yanda shima yake zuwa mai,  wallahi RAHMA ki rufama kanki asiri karki bari aji kanki tsakaninki dashi, dan Auranki dashi babban rufin asiri ne, kuma ni haka kawai naji ƙaunarsa araina, ina san shi ina san kiyi rayuwa dashi, bana san naji kin tayar da wata fitina atsakaninku idan har kina san ganin farin ciki na, idan kuma baki so kiyi duk abinda zakiyi.

  "Gaskiya mama saidai kiyafe min, wallahi ina ji araina bazan iya zama da igiyarsa akaina ba, dan kwata kwata banji ina sanshi ba, haka bazan tauyema zuciyata hakk'inta wajen rayuwa da wanda bata so ba, nidai kawai zance mai ya sakeni dan bana sanshi....

Ai bata ida zancen nata da numfashi ba nan maman ta make mata baki saiji kake gab🙁.

Aiko nan RAHMA tafashe da kuka da ture kwanukan abincin dake gabanta taficce daga d'akin tayi d'akin kwanansu.

 

Dama kishiyoyin maman nata yauce ranar da suka shirya zasu gun boka, sai kuma akayi rashin sa'a gidan qanwar baban RAHMAN da zasuje sunan taje asibiti dan ama jaririya allura sai likita ya riqesu wai jiririyar bata da ishash shan lafiya, dan haka an d'aga suna, Lantana tace to subarta ita taje wajen bokan duk abin da ake ciki in tadawo saita gaya musu,

Sun yarda da hakan, haka ta shiryama maman RAHMAN qarya wai zata duba mahaifiyarta jiki ya tashi, haka ya barta taje, toh bayan taje wajen  bokan gaya mata yayi yanzu haka asirin ya koma kan y'ay'ansu, kuma makaryar asirin shine mutuwar Auran RAHMAN, muddin Auranta ya mutu toba makawa asirin zai karya, shi yanzu ba abinda zai iya yi musu akai dan san da yaja musu kunne,  hankalin Lantana tashe tazo ta gaya musu, hankalinsu suma ya tashi sosai, nan dai suka d'aura aniyar kashe Auran RAHMAN kota halin qaqa...

 

Toh bayan dawowar Lantanan ne su ABDUL sukazo, toh sun kasa gane me yake faruwa sukaga baqi agidan nasu dan baban RAHMAN bai gaya musu zuwan nasu ba, suna tunanin magana dai ake akan Auran RAHMAN, sun dai kasa gane me yake faruwa, dan haka sai kowaccensu take a ankare tana me fatan tasan me yake faruwa, shine fa jin kukan Rahma da sukayi da shiganta d'akinsu na kwana sai kowaccensu tayi zarab ta shige d'akin cikin munafunci suka hau tambayan RAHMAN meya faru da ita take kuka, sam RAHMA bata gane munafunci ne ya kawosu ba, haka tasaki baki ta gaya musu wai Auranta da wannan yaran nan yana nan, ita kuma bata sanshi, aiko suna jin hakan suka hau zugata kan karta yarda da auran,  dan bai dace ace Auranta  yazo a haka ba,

Lantana tace "Ai munga wasu baqi sunzo wajen Babanku d'azu, harda Alhaji Aminu d'an uwan mahaifinki, kaidai baqin sune iyayen mijin naki"

Shuru RAHMA tayi mata, jin hakan sai Iyami ta amshe da cewa, "Kin manta Har da samari biyu, bashine har d'aya daga cikinsu ya fad'i jini ya dinga fitta ba"

Asabe tace "Haka ne, ina ga acikin samarin biyu qila da mijin nata a ciki ko" takai qarshen zancen da zubama RAHMAN ido cikin san suji tabakinta dan tabasu haske a hikimance,

Aiko RAHMA share hawayenta tayi dace musu, "eh, wanda ya fad'in shine mukayi Auran dashi dan shine naji mamana tace yana asibiti, kuma ma ɗane ga Alhaji Aminun d'an uwan baban namu"

Suna jin hakan sai suka dafe qirji, baqin ciki ya qara cika zuciyarsu, saboda sanin da sukama Dadyn AMEER shine me kud'i aduk cikin Y'an uwan baban su RAHMAN, Tab Wallahi da sake,🤔 wai bindiga a ruwa, ai dole Susan yanda zasuyi su raba Auran dan sam RAHMAN bata dace da Yaransa ba, y'ay'ansu sune suka dace dashi,

Nan suka dinga zugata kan karta yarda sam bai dace tana babbar yarinya kamarta Auranta yazo a haka ba,

Ji RAHMA tayi bata da masoya alokacin sai su, haka tadinga d'aukar zugarsu tana qara jin tsanar ABDUL cikin ranta..

 

 

 

Washe gari da qarfe 1:30pm Dady  harda Hajjiya Kakah suna tare da ABDUL, har zuwa wannan lokaci bai farfad'o ba, hakan yasa sukayi masallaci danyin sallah, lokacin yayi daidai da sulalewar RAHMA daga gidansu tayo asibitin dan karb'ar takaddar sakinta gurin ABDUL d'in, nan tayi tambaya aka nuna mata d'akin da ABDUL d'in yake,

Hajjiya Kakah tagani a dukkin k'ofar tana sallah ita da Hajjiya Saratu qawarta, sai tayi saurin shigewa d'akin tana me wara ido dan taga ABDUL d'in.

Aiko tagansa kwance kan wani tsaftataccen gado hannunsa d'auke da  robar qarin jini, gabanta ne ya fad'i, haka kawai taji wani yanayi yayi ram da zuciyarta, nan ta zuba masa ido tana me kallansa sama da qasa tare da mamakin kyau irin nasa, gay d'in ya had'u iya had'uwa dan ya tara abubuwan da kowace mace take buqata agun mijin Auranta, matsalar dai itace, ita ba yanzu tayi niyar yin Aure ba, kuma ABDUL yayi mata yaro, dan tana san Auran namijin daya zarce mata a shekaru Sosai, sam bata fatan ta Auri sa'anta ko wanda ya d'an girme mata da irin shekara d'aya haka ko biyu, to ABDUL ya cika duk wani abu da take buqata agun mijin Auranta saidai shekarunsa baza su wucce nata ba, wannan kad'ai ya isa ta iya sashi sakinta, dan aganinta idan ta Auri sa'anta bazata samu cikakkiyar kulawar data dace ba.

  Jan numfashi tayi tare da matsawa garesa hancinta na bin k'amshin jikinsa, tare da tunanin a ina tasan qamshin.

Ahankali ta kara hancinta ga qirjinsa ta shaqi qamshin dakyau nan tatuna ajikin wannan saurayin daya dinga marinta tatab'a jin wannan qamshin, da gaske turaran yana da dad'in qamshi, haka ta d'ago da fuskarta dan d'auke kanta daga qirjin nashi, karab suka had'a ido, gabanta yayi mummunan fad'uwa, nan tayi saurin qarasa janye jikinta a rikice, cikin in ina tace, "Dama, da, mah, nabi qamshin turaranka ne dan naji kamar na tab'a jin irinsa jikin wani.

Shuru ABDUL yayi mata idansa nakan fuskarta, _Yarinyar tana da kyau_ ya qara faɗin hakan akaro na biyu cikin ransa,

 

Ganin yayi mata shuru yana kallanta sai taci gaba da cewa, takaddata nazo karb'a,  sam ban shirya zaman Aure yanzu ba, dan haka saika bani takaddata dan Wallahi bazanyi rayuwar aure da sa'ana ba.

Ayanzu daga qasa ABDUL ya fara kallanta har zuwa sama, rigace da wando a jikinta, girar iya cikinta ta tsaya, sai wandan dogo har qasa, sai wani d'an figigin gyale data yane kanta dashi, ga alama ta nuna kitsan dake kanta kitsan qari ne, gashin ciko yayi aikinsa a kan, dan yasa kan ya cika tam irin na yara yaran mata masu aji mara ji kamarta, kayan sun matseta matuqa, dan sun bayyanar da sirrin halittarta, nan take wani abu ya caki zuciyar ABDUL, sam batayi kama da y'ar musulmai ba, dan shigar ita zata tabbatar maka da hakan.

Ahankali ya kawar da kallansa daga gareta tari ya kamasa sosai, nan ta rikice tad'auki ruwan swan wata dake wajen  ta bud'e ba tare da tunanin komai ba ta d'ago da kansa tare da kwafa masa bakin goran, a nufinta yasha.

Nan ABDUL ya lumshe idansa sakamakwan jiyo qamshin jikinta da yayi, kad'an yasha ruwan saita maida masa da kan nasa kan filo a hankali, sannan ta maida ruwan gefe tare da maida kallanta garesa taci gaba da cewa, Sannu, Allah ya qara lafiya.

Shuru dai yayi mata, ita dai RAHMA haka take, sam bata san taga mutum bashi da lafiya, yanzu saita rikice, y'an uwanta sunyi mata wannan shedar dan ko tayi fad'a yanzu dakai taga baka da lafiya jikinta sanyi yakeyi, nan zata zuba maka ido tana mejin tausayinka, idan kuma bakuyi faɗa ba, haka zata zauna dare dakai tatace maka sannu cikin kulawa.

Yan zumma zubama ABDUL ido tayi cikin tausayawa, tunani take bai dace tayi masa maganar saki yanzu ba, ya dace tabarshi ya samu lafiya saita karb'i abinta....

"Zaki iya kira min doctor"

ABDUL ya katse  tunaninta da faɗin hakan.

Nan taficce daga d'akin tayi inda take tunanin ganin doctorn,

Hajjiya Kakah taga fitowanta amma zatanta ko ma'aikatan wajen ne, musamman da bataga fuskarta ba.

Rahma tagayama doctorn ABDUL na San ganinsa, nanko ya tashi da murmushi akan fuskarsa yana tambayarta yanzu ya farka, eh tace mai, akan idanta ya shiga d'akin da ABDUL d'in yake, ganin hakan sai tabar asibitin tana me fad'i aranta bara dai tabari ya samu lafiyan, saiya bata takaddarta.

 

Doctor ya duba ABDUL sosai yaga baida matsala ayanzu, sam baya buqatar komai, dan jini ya wadaci jikin nasa, ma'ana dai ansamu yanda ake so,

Dan haka kiran Hajjiya Kakah yayi ya gaya mata jikin nasa yayi kyau sosai, ko yanzu za'a iya sallamarsa, tunda ba anan suke ba, amma zai  basa magunguna Wanda zai shasu tsawan sati biyu. Saidai sukula dashi sosai dazaran sunga wani canja agunsa su maidashi asibiti,

Murna sosai Hajjiya Kakah tayi, nan tazauna kusa da ABDUL d'in tana me shafa fuskarsa cikin san taji ko jikin nasa da d'umi, Hajjiya Saratu tayimai sannu yayi mata murmushi da tashi yana kallan Hajjiya Kakah yace, "Kakah yunwa nake ji, zanso nayi wanka na wanke baki sainaci abinci.

Kan Hajjiya Kakah tace wani abu, saiga su Dady sun shigo d'akin suna masu murmushi ganin ya farka, nan suka mai sannu Hajjiya kaka tagaya musu abinda yace, sai sukace bara sukarb'i sallama suje can hotel d'in da suka sauka sai yayi wankan yaci abincin idan suka qara ganawa da iyayen  RAHMAN sa tafi yau tunda da sauran lokaci,

 

Haka ko akayi, sun karb'i sallama AMEER ya kama hannun ABDUL ya sakashi cikin mota suka rankaya Sharna...

Wanka da ruwa me zafin gaske ABDUL yayi, ya tsaftace bakinsa da saban buroshin da makilin d'in daya gani cikin toilet d'in, sai yayi alwala ya saka kayan da Dadyn AMEER ya siya masa akan hanya lokacin da suke tawowa hotel d'in, kana ya rama sallolin dake kansa, sannan yaci abincin, haka kawai yake jinsa wani fayau haka, kamar an zare masa wasu kaya masu nauyi akansa, sanda su Dady suka tabbatar yad'an huta kana suka rankaya gidansu RAHMA, anan suke gaya mai an qara d'aura musu Aure shi da RAHMAN, amma ita RAHMAN bata san qara d'aurawa akayi ba, dan haka suna san jin ta bakinsa yana da ra'ayinta yana santa koko baya ra'ayinta Susan nayi tun yanzu.

Kunyarsu ta kama ABDUL matuqa, dan haka ce musu yayi shi ai d'ansu ne, bazai tab'a ƙalubantar duk wani abu dazasu zartar akansa ba, zai rayu da ita rayuwar da zasuji dad'inta, insha Allah baza'a tab'a samun matsala daga garesa ba.

Wannan kalami nasa ya qara saka qaunarsa a cikin zuciyarsu, nan suka saka masa albarka wajen yi musu fatan alkairi.

Sai maman RAHMAN ta roqi alfarma kan sud'an bar mata RAHMAN na d'an wani lokaci kad'an dan akwai shirye shiryen da zatayi mata, sai Dady yayi murmushi yace mata karta wahalar da kanta wajen yi mata wani abu, yana da wani gida daya gama gidawa danya koma saboda yana san qara Aure, kuma ba abinda baisa ba agidan, zai barma ABDUL gidan sai su zauna a gidan, dan haka karta damu yasaka komai na rayuwa agidan ba abin buqata sai kayan kitchen irin nasu na mata da kayan abinci, shi kuma wannan ba matsala bane akone lokaci za'a iya siya..

Murmushi tayi da cewa, toh angode amma duk da haka ad'an bata lokaci, kona wata d'aya ne, tayi alqawarin bazata qara ko kwana d'aya ba zata saka y'an uwa da abokan arziqi su kayo RAHMAN, dan Allah ita dai tana neman alfarmar.

Sunce mata toh ba komai Allah ya kawosu lafiya,

ABDUL yayi mamaki Dadyn AMEER sosai, Allah dai ya sakamai da alkairi dan yana nuna masa qauna akowane lokaci, hakankali ya kalli AMEER sai yaga hawaye na zuboma masa, da damuwa ABDUL ya tab'asa yana ce mishi lafiya, saurin goge hawayen yayi dacemai ba komai.

Shuru kowa yayi, dan ABDUL dai baisan me yake faruwa ba.

Nan dai dukkansu suka tashi dayima baban RAHMAN sallama sukayi mota, sai maman RAHMA ta tsaida ABDUL a zaure tana ta gaya masa irin tsanar da y'an uwan nata suke mata, da abinda kishiyoyin nata sukama RAHMAN, ta qara da cemai dan Allah karya saki RAHMAN idan tabuqaci hakan, tana san RAHMAN tayi rayuwar aure me d'orewa, dan Allah ya rik'e mata y'arta amana wajen qoqarin gyara mata rayuwa, ta lura shi kad'aine zai iya da ita, kuma tagaya masa komai ne dan tana san ganin qarshen makircin kiyoyin nata nan kusa,

ABDUL ya tabbatar mata bazai tab'a sakin RAHMAN danta buqaci hakan ba, zaiyi qoqari sosai wajen ganin yaba maqiyanta mamaki.

Maman taji dad'in furucin nasa sosai, tayi mai godiya dace mai ya tsaya taturo masa ita su gaisa ai baya tafi batare daya ganta ba, Har zaice mata ai d'azu tazo asibiti gunsa sai kuma ya fasa dan inda tasan taje garesa d'azun bazatace mai yanzu ya tsaya taturo masa ita ba.

 

RAHMA tana yatsina baki tayo zauran gidan nasu, ta kallesa sosai,  _yafi d'azu kyau_ ta fad'i hakan aranta, a fili ko ce masa tayi, "Kawai kabani takaddata dan nagaya maka nifa basan Auran nan nake ba. Kuma gaskiya ni bana sanka kawai kaban takaddata.

ABDUL yayi murmushi yace "Nima sam bana sanki, dan bakiyimin ba, bakya d'aya daga cikin jerin Matan da nake so, sam baki taka ko farcen qafarsu a zubi me kyau ba, zan gaya miki wata gaskiga wallahi duk wanda kikaji yace miki kin cika mace kyakkyawa me aji, to wallahi qarya yake miki, dan ke mummunace abar ƴama cikin mutane, farkoma kije ki fara kallan kanki a madubi, sam bakiyi kama da ƴaƴan musulmai ba, kalli wani qazantaccen gashi da kika wani kasa akanki, wanda kike da tabbacin musulinci baice ki saka shi ba, kalli kayan dake jikinki, kallo d'aya me tarbiya zai miki ya gane sam ba ƴar musulmai bace, kin matse jiki gabaki d'aya kina nunama maza suzo ga haja kin bud'e, mata wayayyu irinki a harka irin wannan basa fitowa sununa haka' saidai sufito a nunasu, sam baki iya KARUWANCI ba, dan inda nine a matsayinki bazan dinga fitowa da kaya ajikina ba, kawai karuwancin zan saka a gaba, in fito da kayan da duk maseefar sheɗani idan ya ganni saiya shagaltu da kallona, wato da bireziya  zan fito da d'an qaramin wando in nunama duniya ni TANTIRIYAR KARUWACE, abu na qarshe dazan gaya miki anan shine, Babu batun saki tsakanina dake, zan rayuwa dake rayuwa irin ta ma'Aurata da kalamai irin nasu badan ina sanki ba, saidan nanuna miki kuranki na baki isa kisani sakinki.. Yana faɗin hakan ya nemi ficcewa daga zauran, saidai ina.... Zuciyar RAHMA tacika tayi FAM da muggan kalaman daya jefeta dasu, dan haka shan gabansa tayi da cukume masa gaban riga tana wani fitta wani numfashi na baqin rai tace da shi, "Kai ka isa kazo har cikin gidamu kajefeni da muggan kalamai sannan kayi tunanin zaka fitta batare danace maka komai ba, eh, naji na yarda baka sona kamar yanda nima bani sanka bani qaunarka, batu kuma akan saka gashi danayi akaina, gani nayi ai kaina ne ba naka ba, kuma kai baka isa ka hanani sakawa ba, KARUWANCI kuma ai sani ne bakayi ba, ni tantiriyace a harkar, dan na zubba ciki sau goma sha shidda, bazan iya Yawo da kayan irin wanda ka fad'i yanzu da rana ba, dan kirana za'ayi da mahaukaciya ba tantiriyar karuwa ba, amma ina yawan bin club cikin dare kuma tsirara nake yawa gaban maza da mata sune zasu tabbatar maka da cewar ni ba qaramar tantiriya bace, wallahi kokafi waye qoqari saika sakeni dan rantsuwata bazata tab'a tafiya a banza ba"....

"Da gaske" ya katseta da faɗin hakan yana me dalla mata fararan idansa cikin nata, nan ko take kwarjininsa ya make ta, taji wani abu na fitowa daga idansa yana shiga nata, nan bata san ya akayi ba saijin hannunta tayi yana sakin rigarsa data cukume, cikin sauri ta  kawar da fuskarta daga kallansa,

ABDUL yayi murmushi da janyota jikinsa... Nan ta kallesa a furgice, ya qara sakar mata murmushi da da zare d'an figigin gyalan data yana kanta dashi, nanko take kitsan dake kan nata ya qara bayyana, kitsone yafi dubu amma sam bai bashi sha'awa ba, ya tab'e baki daci gaba da cewa, Bana san mutum me qarya a rayuwa, idan da gaske ne abinda kikace, meyasa ranar dana ganki a club ban ganki a yanda kika fad'i yanzu ba, kawai ganin qaramin iskancinki nayi wanda kika zauna kan cinyar wani Alhaji yana me lalubar qirjinki kina me hanasa, shin tantiriya karuwa me yawo tsirara gaban maza da mata ya dace ta hana abukin iskancinta jikinta wannan lokacin da hankalin kowa bai tafi kansu ba".

Hararar tsana RAHMA ta galla masa da cewa, "Wato kaine wanda nake nema wanda ya dinga wanka min mari kamar yasamu jakarsa ko"

"Eh, nine mana, har kikace zaki nemoni ki rama abinki ba"

Wata hararar ta qara galla masa da cewa "Babu abinda zai hanani ramawa yanzu kuwa"

    "ai dama ni bance karki rama ba, saidai idan kika min d'aya atake zan miki uku waƴanda sukafi naki"

 "Wallahi na tsaneka ABDUL karkayi kuskuran barin akawo maka ni cikin gidanka, dan zanyi maka wani kisa ne irin wanda matan yanzu suke yima mazajensu da zaran anyi musu Auran dole.

Murmushi ya qara sakar mata da cewa, "common my Baby, zanso hakan kuwa, dan dama ni nagaji da rayuwar, amma gaya min, wane irin kisa zaki min aciki, zakimin irin wanda wasu matan sukeyi na sakama amzajensu guba ne cikin abin cinsu, koko zakimin irin wanda wasu matan sukeyi na dannama mazajansu fillo yayin da suke bacci, koko zakimin irin wanda wasu matan sukeyi nayima mazajen nasu yankan rago, koko cakamin wuqa zakiyi, koko Dakar wani shashi zakiyi cikin jikin nawa wanda zai baki damar gamawa dani"

 

"Babu d'aya da zanyi maka cikin waƴannan, dan nawa salan na musamman ne, salo ne na yara yaran mata masu aji yaran zamani, kisan zamani zanyi maka ABDUL" RAHMA tabashi amsa cike daqarin jin tsanarsa cikin ranta.

 

Qara jawota jikinsa yayi da cewa, kince na zamani zakimin ko, to ai nagano kowane iri zakimin, kina nufin ki kama gabana ki gille min da wuƙa ko".... Cikin sauri RAHMA tawaro ido😳 da girgiza masa kai a tsorace,

hakan sai ya qara tabbatarma da ABDUL ba tantama ko kusa RAHMA bata san kan iskanci ba🤣 kawai tsiwar da rashin kunyar ce ta iya, dan haka kai mata kiss yayi ga bakinta ya tsotsa da sakewa yaci gaba da cewa, ina jiran zuwanki gidana my Baby, sannan ina san wannan tsiwar taki irin sosai d'innan.

 

Yana faɗin mata hakan ya sake da ratsawa ta gefanta ya ficce daga zauran.

 

Tunda RAHMA take bata tab'a cin karo da d'an iska irin ABDUL ba, sam bata tab'a had'a baki da wani katan garde ba, takanyi dai kiss d'in na gefe da gefe sam ƴamar bakin mutane take, amma gashi yau ya had'a bakinsa da nata cikin lokacin da takejin kamar ta shaqesa dan tsana, batayi aune ba, saijin hawaye tayi ya zubo mata, nan tafashe da kuka wiwi ta koma gidan nasu tana cewa "Wallahi saiya sakeni😭😭😭....

 

 

ABDUL ko saurin shigewa motarsu yayi, ganin shi suke jira ashe tuntuni.

Haka suka d'auki hanyar kaduna cikin addu'ar Allah ya saukesu lafiya.

Aiko sun isa lafiya anan ba tare da b'ata lokaci ba, baban ABDUL da Dadyn AMEER suka had'a kan matansu sukayi asibiti dukkansu, sam basu gaya musu abinda yasa sukace sushirya zasu asibitin ba, haka ABDUL sam bai san me yake faruwa ba, sanda yaga an zuqi jininsa dana mahaifiyarsa da jinin AMEER dana momynsa harda na babansa dana Dadyn AMEER d'in, sannan ya kalli AMEER yace, "Wai meyake faruwa ne" gwajin me za'ama jininmu" shuru AMEER yayi masa, ganin hakan sai yayi shuru ya zubama sarautar Allah ido.

 

Sun shafe sama da awa d'aya a asibitin kana doctor yabama kowan nansu sakamako, bincike dai ya nuna ABDUL shine d'an Dadyn AMEER kuma momyn AMEER d'in ita ce mahaifiyarsa, haka AMEER ɗan baban ABDUL ne kuma maman ABDUL d'in itace mahaifiyarsa,

 

Tashi ABDUL yayi cikin matuqar mamaki, tare da kallan kowannansu da furgici baiyi aune ba, nan yaji jiri na kamasa, yayi baya luuuu kamar zai fad'i sai Dady da babansa sukayi saurin taro shi, cikin matuƙar kulawa.

Dake da Hajjiya Kakah akaje asibitin tana qara jin sakamakwan ta rabka salati, AMEER ko sai jinsa sukayi a qasa ya yanke jiki ya fad'i sumamme, hankalin mama Saude ya tashi sosai, sam batayi zatan gwajin tantancewa za'ayi tsaninsu ba, da Wallahi bazata yarda ayi mata ba,

 lalle zataci uban ZAINAB dan ba makawa itace tatona mana asiri, Wallahi bame rabata da ita sai Allah...

Andai samu AMEER ya farfad'o, dan haka basu tsaya wani jin ba'asi kan lamarin a cikin asibitin ba, dan Dadyn AMEER cewa yayi subari su dawo gida su tattauna, amma yana so Dan Allah suzo gidansa ayi maganar anan, dan anan ne zasufi samun sakewa,

Kowa yayi na'am da zancen nasa

 

Sunyi faking a ƙofar gidansu ABDUL kenan saiga ZAINAB  ta iso wajen tana kuka wiwi,

Nan suka firfito suna masu tambayarta meya faru, ko anyi mutuwa ne😨... Ita dai shuru tayi musu daci gaba da kukanta.

Mama Saude ta galla mata wata muguwar harara tace, "Dan ubanki yanzu kika fara kuka, bani zaki tonama asiri ba, Wallahi sainayi miki illah a rayuwa, kowa maida hankalinsa kanta yayi yana nazarin kalmominta,

Ganin hakan sai ABDUL yaje ya kama hannun ZAINAB d'in yace.. "Aunty koma me yake damunki ina san kiyi hak'uri dashi, Aunty ina cikin tashin hankali, halin da nake ciki ayanzu na tabbatar yafi damuwar da kike d'auke da ita.

Tace "aa ABDUL, wallahi nafika shiga damuwa da tashin hankali ayanzu, dan Aurena ne ya mutu😭, yau Salisu yayi min saki uku ABDUL ya zanyi, wallahi ina san mijina.

Dafe kai ABDUL yayi da cije bakinsa ya zare hannunsa daga nata wannan jirin ya qara kamasa, zai fad'i still Dady da Babansa suka qara taresa.

Su Hajjiya Kakah ko salati suka rabka,

ABDUL kallanta yakeyi cike da tausayi, nan take wani zazzafan zazzab'i ya kama sa, ya lumshe idansa cikin wani hali,  ganin hakan sai Babansa ada da Dadynsa ayanzu suka riƙesa kowannansu niyarsa ya kaisa cikin gidansa.

Dan dukkansu hanyar gidansu suka nufa dashi.

Nan Hajjiya Kakah ta kallesu a kid'ime sai alokacin suka lura da yanda suka riqesa da niyar dake cikin zuciyoyinsu.

Ahankali cikin sanyin jiki baban ABDUL ya sake shi hawaye ya zubo masa yace da Dadyn, "Gidanka zakayi dashi ko nayi gidammu dashi,

Rintse idansa Dadyn yayi, gaskiya bazai iya yima abokin nasa kawaici akan ABDUL ba, Wallahi tun yanzu zai d'auke d'ansa, dan haka saiya bud'e idansa yace, "Kayi hak'uri abokina, ina san ainihin d'ana ya kwana cikin gidana yau kuma a d'akina...

 

ZAINAB najin haka tawaro ido😳 da barin kukan nata tace... "Shike nan Yayata yau asirinki ya tonu, dama wannan ne kike tunanin nina tona miki asiri, ko kad'an ni ban gayama kowa wannan sirrin naki ba, Allah ne dai ya tona miki asirin bani ba...

 

Shidai Dadyn AMEER gidansa ya nufa da ABDUL momyn AMEER tabi bayanshi.

Baban ABDUL ya share hawayensa, da kallan AMEER yace, "Ayanzu nine mahaifinka AMEER, shin zaka yarda dani, ka karb'e ahaka,

Kallansa AMEER d'in yayi da matsawa kusa dashi yace, "nayi nadama arayuwata, kuma ban tab'a yinta ba sai jiya da yau, kai mahaifina ne, kuma na yarda da hakan, zan bika duk inda kasa qasa, bazan tab'a guje maka ba,

Rungumarsa baban nasa yayi tare dajan hannunsa yayi gidan nasu dashi, anan wani d'akinsa ya zaunar dashi..

 

Anan waje ko, kasa shiga gidan nasu Hajjiya Kakah da ZAINAB sukayi, ita dai ZAINAB bata jin zata shiga gidan batare data qara ganin ABDUL ba, dan tana hango yanda yake lumshe ido da alama bayajin daɗin jikinsa Sosai, dan haka barin Hajjiya Kakah tayi anan tayi gidan Dadyn..

 

Anan falo taga sun kwantar da ABDUL, kansa na bisa cinyar momy yayinda Dadyn ya maida hankalinsa kan ABDUL d'in gabaki d'aya yana meyi masa sannu, hawaye ya zuboma ZAINAB, takai hannunta ga goshinsa nan taji zafi zau, tasan ABDUL bai iya ciwo ba, musamman idan wannan zazzab'in ne yayi ram dashi, dan tacema Abida takawo mata ruwan zafi,

Momy tace "dawai yanzu na kira doctor zaizo ya dubasa,

ZAINAB tace, "Ya saba irin wannan zazzab'in momy, kuma yana samun saukarsa da wuri idan aka gasa masa jikinsa da ruwan d'umi.

Shuru momyn tayi mata, haka Abida takawo ruwan da tawul d'in, nan ko ZAINAB tadinga goge masa jikin nasa, momyn na tayata, dan momyn tace mata tabari amma taqi,

ABDUL najinsu, sakin ZAINAB d'in ya tsaya masa arai matuqa, sannan  ba wacce yake hangowa aransa yanzu sai Hajjiya Kakah, danya hango tashin hankali agareta lokacin dataga Dadyn yayiyo gidansa dashi. Ga mahaifinsa shima ya shiga tashin hankali, dan yaga zubar hawayensa.

 

 

 

By AUNTYN LUV 💋

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.*🙆🏻*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆🏼*.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`•🤱🏻

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 15

 

*true 15 Read more* 🙁🏻 masoyana..

 

*Sadaukarwa ga UMMU BAHEER na gode da kawomin ziyara da kikayi, sanki daban yake araina, & Qawar arziqi RAHEENAT MAMOUDOU, ina yinki sosai masoyiyar asali*

 

 

Sanda ZAINAB ta tabbatar zazzab'in ya d'an sauka masa, sannan ta barsa, basufi minti biyar a haka ba sai gasu Hajjiya Kakah gabaki d'aya y'an gidan nasu, nan Dadyn AMEER da momynsa ada suka maida hankalinsu garesu.

Hajjiya Kakah tace, "Babu me sauran nutsuwa agaremu imba munji meya faru tsakaninku aka samu canjin y'ay'anku ba.

Momy taja numfashi tace, "gaskiya ni bazance nasan ya abin yake ba, ma'ana ni bansan meya faru ba, dan tun zuwan AMEER duniya nasanshi matsayin d'ana..

Dady yace "Nima dai haka, sam bani da wani sani akan lamarin.

Baban Abdul yace, "Nima haka, Wallahi bansan komai ba"

Mama Saude tace "Nima haka, ban san komai ba...

Da sauri ZAINAB ta kalleta tace, Qarya kike Aunty, kinfi kowa sanin abin daya faru, Wallahi ko kaffara bazanyi babu wanda yasan meya faru cikinku saike"

Cikin b'acin rai Kakan baban ABDUL wato baban babansa ya kalli mama Saude da cewa, "ke Saude ba wasa bane ya kawomu nan wajen, idan kina da sani kan wannan lamari ki warware mana zare da abawa, bani san shashancin banza,

Cikin wani hali mama Sauden ta kalli Dadyn AMEER hawaye ya zubo mata, tace, "Aduniya bani da abin so kamarka Ibrahim, ina sanka ina qaunarka, Bani da wani buri cikin raina saina Auranka.

 

Abin daya faru shekarun baya shine.

 

Tun tasowata dana ƴallah ido naganka Ibrahim shike nan nakamu da sanka da qaunarka, Nasan bazaka manta da wata ranah danazo na sameka nace maka ina sanka ba, saika watsan qasa a ido kace kai baka da ra'ayin mata biyu, kuma kana matuqar san matarka, baka san b'acin ranta, saboda kayi imani ba abun data tsana kamar kishiya, kana san matarka bazaka tab'a yimata kishiya ba, Sannan kai bazaka iya cin amanar abokin ka ba, wato mijina, danya yarda dakai fiye da tunanin me tunani.

Abin yayi min ciwo matuqa, saina saka araina saina aure ka kota halin qaqa, haka nida qawata Firdausi muka dinga bin malamai da bokaye kan su karkato min da hankalinka  zuwa gareni, ka Aure ni, sannan karabu da matarka, dan ba wata wacce na tsana a duniya kamarki Hafsat.. Mama Saude ta d'an tsaya anan da kallan momy, kana taci gaba da cewa, duk yawan bin malaman da mukeyi fad'a mana suke Akwai Aure tsakanina dakai, saidai batun rabuwa tsakaninka da Hafsat matarka babu shi, dan tazama wani jigo arayuwarka, kana jinta aranka fiye da komai a rayuwarka.

 

Ban wani damu da batunta ba, dan nasaka araina muddin na shigo gidanka koda bata fitta ba, alqawari ne saidai tayi rayuwar kunci.

Ana cikin haka sai Baba Ali wato Yayan Mahaifiyata gashi da ransa me mutu ba, tanuna Kakan ABDUL ada na wajen uba sai taci gaba da cewa, Ya bijiro da batun Aure na da kai Abduraman, tanuna baban ABDUL ada, kana taci gaba da cewa, wai yaga soyayyarmu tayi qarfi da yawa dan haka ya yanke shawarar d'aura mana Aure nan da wata biyu awancen lokacin.

Jin abin dayace ya bala'in tayar min da hankali, dama shiya had'amu yace yana san mu had'e kammu, dan zaiyi sha'awar ganinmu matsayin ma'Aurata, sam  bamu bashi kunya ba, muka fara soyayya, to zuwanka unguwar nan ne Ibrahim yasa na fara sanka, gashi tunda kazo saiya kasance baka da amini sai Abdulrahaman.

 

Saina zanta da qawata Firdausi kan ya zamuyi kenan, sai tace min akwai wani boka aikinsa kamar yankan wuqa ne, kuma yana da gaskiya idan zamu samu biyan buqata zai gaya mana, idamma bazamu samu ba duk zai gaya mana, dan haka kawai muje wajansa yayi mana aiki ya rufe bakin Baba Ali kan Aurena da d'ansa, sannan yasa kai Abdulrahaman ka haukace a sona da qaunata, sannan ka rabu hafsat

Munje wajen bokan,  ya kuma tabbatar mana abun da muke nema bazamu samu ba, dan Hafsat matarka da kai kanka baku wasa da ibada, koda anyi muku aikin bazaiyi tasiri akanku ba, saidai idan za'a kashe hasat d'inne toh shine zamu samu biyan buqata, wannan shine gaskiyar zance.

Har kuka sanda nayi, jin abinda yace, gaskiya duk baqin hali na bazan iya kashe raiba, wannan yasa na qara jin tsanar hafsat Sosai, saboda nayi tunanin da baka santa da yawa zaka iya aurena dan nima babu abunda bana dashi wanda dai zaisa maza su soni.

 

Haka nayi hakuri na Auri Abdulrahaman, saidai me🤔.. Wata ranah haihuwa tatashi min aka kaini asibitin dan samar min temakwan gaggawa, sai kwasam saiga Hafsat itama an kawota ranga ranga, sai aka had'amu a d'aki d'aya, amma an ratsa labule tsakaninmu.

Lokacin dana fahimci hafsat ce, sai naji raina yayi min dad'i, nan sheɗan ya kitsamin idan na haihu lafiya itama ta haihu muka samu abu d'aya nacanja na bar mata nawa na d'auki nata, hakan ne zai wanke min zuciya daga tsanar da nake mata, dan zata raini nawa cikin so da qauna, yayinda zan raini nata cikin gana masa azaba.

 

Aiko haka akayi, ninafara haihuwa,  sai itama ta biyo bayana, dama nurse biyu ne akanmu, da wacce take kanta da wacce take kaina.

Nan naji wacce take kanta tana fad'inma wacce take kaina, wai tasamu namiji itama, amma tana zubda jini Sosai gashi tafitta daga haiyacinta bara taje ta kira doctor.. Toh tawan tace mata, 

Nan farin ciki ya cika zuciyata, na cire sark'ar zinaran dake wiyana na miqama nurse d'in, cikin muryar qasa qasa nace mata na bata, saidai inaso tayimin canjin Baby tsakanina da waccar matar, na nuna mata hafsat da baki.

Aiko nan ta amshe Sark'ar ta saka a ajjihunta, cikin sauri ta d'auko ABDUL ta ajiyemin shi gefena, kana ta d'auki AMEER takai shi gefen hafsat d'in, sam hafsat bata sani ba. Dan da gaske bata cikin hayyacinta.

Haka y'an uwa da abokan arziƙi suka sakani gaba kan naba ABDUL nono nayi musu qarya kan nonona nayimin ciwo,  sam ban shayar da ABDUL ba, Hajjiya Kakah itace shaida dan da kanta tashayar da ABDUL madarar yara.

Bani da abun ƙi kamar ABDUL, wallahi har cikin qarqashin zuciyata tsanar ABDUL nake kamar yanda nake jin tsanar mahaifiyarsa, tun awannan lokacin nafara ganin kaidina, dan Hajjiya Kakah san ABDUL take fiye da tunanin me tunani, haka ƙanwata ZAINAB bata da abun so kamar ABDUL,

 

Lokacin da ABDUL ya gama karatunsa naji lokacin da babansa yake cemai zaiyi maka magana dan ya fara aiki a companyn ka, hankali ya tashi, musamman idan nayi duba da yanda nawa d'an AMEER yake gararamba agari, sam babu maraji a fad'in unguwar nan tamu kamarsa

Nan zuciyata tacika da baqin cikin kintsuwa da ladabin ABDUL, kowa yabansa yakeyi cikin  unguwar nan bama a cikin gidammu ba.

 

Sai kawai nasamu Firdausi nace mata muje wajen bokan nan ya b'atamin rayuwar ABDUL..... Mama Saude na zuwa nan azancenta Hajjiya Kakah tad'auki salati tare da fashewa da kuka, nan yaranta suka hau lallashinta. Itama mama Sauden hawaye ne ya zubo mata alokacin, amma ahakan taci gaba da cewa, munje wajen bokan yayima ABDUL asiri kan ya dena ganin mutuncin kowa, ya dinga yawan dare da raye raye, yaji aduniya ba abinda yake masa dad'i kamar harka irin ta dabanci, sai nacema bokan ba dama ya zama mazinaci ya dinga yima yaran mutane ciki, sai yace min ai makaryar asirin shine, idan har zai kusanci wata y'a mace to ba makawa komai zai karye, ko kuma idan har aka d'aura masa Aure shima nan take asirin zai karye, kuma idan ya karye zai fitta jini idan ba'a bashi temakwan gaggawa ba za'a iya rasa shi nan take, ma'a dai anan shine, bazai iya yimana asirin da zai iya saka ABDUL d'in ya dinga aikata zina ba.

 

Haka muka dawo gida tun daga wannan lokaci rayuwar ABDUL tacanja.

 

Wata ranah muna hirar da qawata Firdausi a d'akina, ashe ZAINAB najinmu, hankalinta ya tashi matuqa, sanda takasa hak'uri tabayyana agaremu tanuna mana taji komai, ganin hakan yasa nace mata wallahi idan tatona min asiri wallahi saina kashe ABDUL kota halin qaqa.

Ayanda na nuna mata tayarda zan iya kashe shin, wannan yasa jikinta yayi sanyi dani.

Wannan shine mafarin dayasa take jin tsanata cikin ranta, wannan yasa bata jin komai aranta idan tamin rashin kunya, nagama gane cewa ZAINAB bata da abun tsana a duniya kamarni, hakan yasa taqara san ABDUL waidan naji zafi,

Haka qananun abubuwa suka dinga faruwa tsakanina da ita duk akan ABDUL d'in, dan da wiya idan taganni awaje ga kuma ABDUL batayi min wani abun dazai b'ata min rai ba.

Mama Saude na zuwa nan ta kalli kowa a falan, taga kowa ita ya zubama ido, sai taci gaba da cewa, Wannan shine  labarin komai, shine abin daya faru, kuma wallahi a yanxu nayi nadama sosai, dan Allah kuyafemin...

 

 

"Kan uba😳.. Momy tafad'i hakan daci gaba da cewa, Wallahi qaryarki tasha qarya Saude, kinyi qarya kice min kinyi nadama ayanxu in yafe miki, na haifi d'an nawa, kimin canji da naki, ki nunama nawa tsana da hantara, ni kuma ina nan ina rainon naki, bani san kukan AMEER, bana san b'acin ransa, bani san wani abu ya tab'a min shi, duk wani abu da AMEER zai nuna yace yana so, saina siya masa, na rungumesa matsayin d'ana, naci kashinsa naci fitsarinsa, ashe ba d'ana bane, nawan yana can yana fuskantar wata rayuwa, yau ranah d'aya, lokaci d'aya, kizo kice min in yafe miki saboda kece ishash-shiya ko....

To wallahi bari kiji saina makaki a kotu na kashe ko miliyan nawa ne kan abimin hakk'ina,

Da sauri mama Saude ta kalleta zatayi magana sai momyn tayi saurin katseta da hannu🏻 daci gaba da cewa, wallahi idan kika k'ara min wata magana anan sainaci bura'ubanki a falan nan, an gaya miki kishi haukane, kalleni da kyau daga sama har qasa, kin san dai nafiki TANTIRANCI akan komai, babu abinda zai hanani d'aukar mataki akanki, baqar munafuka, azzaluma, me mugun baqin hali....

 

Kowa a falan shuru yayi, Dadyn ABDUL da Baban AMEER dafe kansu sukayi, kowa da tunanin dayake yi, shi dai Dadyn ABDUL yayi farin cikin yanda ABDUL yake d'ansa, sannan zai yafema mama Saude saboda abokinsa wato baban AMEER ayanzu, shiko baban AMEER tunanin hukuncin da zaima mama Saude yakeyi dan tabbas ta aikata babban lefi.

 

Hajjiya Kakah da ZAINAB kuka suketayi jama'ar gidan nasu suna masu basu hak'uri.

Y'ay'an Hajjiya Kakah su Baba Shehu ko girgiza kai kawai sukeyi suna mamakin baqin hali irin na mama Saude.

 

AMEER ko, kuka yakeyi bana wasa ba, gabaki d'aya jin duniyar yakeyi babu dad'i, haka yaji tsanar mahaifiyar tasa, sannan yaji qaunar mahaifinsa.

 

Shiko oga ABDUL shuru yayi kawai yana kallan mama Saude, tunani yake akan baqin hali irin nata, gani yake babu me mugun hali irin nata aduk fad'in duniya, nan take ya qara san Baban AMEER ayanzu da Hajjiya Kakah da ZAINAB, gefe guda kuma yaji qaunar mahaifinsa da momynsa sosai cikin ransa,

 

Haƙurin duniyar nan kaf y'an gidansu Hajjiya Kakah sun bama Dady da momy, sun kuma nemamma mama Saude afuwa dansu yafe mata.

Dady kam yayafe mata momy ce dai tayi shuru.

Hajjiya Kakah ta roqi alfarmar ABDUL ya koma gidansu, tasaba dashi sosai dan Allah karsu rabata dashi.

 

Murmushi Dady da momy sukayi mata da cewa gaskiya saidai tayi haƙuri, dan bazasu iya bata ABDUL ba, dan sunji sanshi da qaunarsa fiye da kowa ayanzu, sannan babu adalci cikin tafiyar idan har suka d'aukesa ayanzu suka Bata shi, momy ta tabbatar mata da cewa ABDUL nata ne, bazai iya rayuwa babu ita ba, dan haka ta kwantar da hankalinta bame rabata dashi, dan zai dinga zuwa yana gaisheta akai akai.

 

Hajjiya Kakah tayarda da zancensu,

Shima baban AMEER ya gamsu da zancen nasu, haka kowa a wajen baiyi zato ba, saiji sukayi baban AMEER d'in ya dan qarama mama Saude saki har uku....🤦🏻

 

Kowa sanda yaji ba dad'i abinda yayi, amma da sukayi dubu da abinda ta'aikata sai kowa ya goge jin tausayinta a ransa.

 

Kuka kam mama Saude tayi shi kamar idanta zai fitta, ba wanda yace mata tayi hakuri, haka kowa ya barta tadinga rizgar abinta.

 

Dady ya roqi baban AMEER kan yayi hak'uri ya bar masa AMEER dan ya had'asu waje guda ya rainesu.

Murmushi baban AMEER d'in yayi da cewa, "Ibrahim kenan, baka san yanda nake jin ABDUL bane a raina, da kaji yanda nake jinsa da baka rabani dashi ba, yanxu kuma naji qaunar AMEER sosai araina, zanso kabarni nima na rayu dashi yaji dad'in mahaifinsa na ainihi shima"...

 

Tashi ABDUL yayi daga kwancen da yake, ya kalli Baban AMEER d'in babansa ada😭 yace dashi, "Baba, zanji dad'in rayuwa da AMEER cikin gidan nan, idan baya ciki Dadyna da momyna ayanzu bazasu samu kwanciyar hankali na gabaki d'aya kamar yanda ya dace ba, dan Allah Babana, dan Annabi kabar AMEER yayi rayuwa dani.

  Kama hannunsa baban yayi da cewa, "ABDUL zan bar maka AMEER anan gidan har zuwa lokacin da za'a kawo maka matarka ka kakoma gidanka wanda mahaifinka ya baka.

Cikin farin ciki ABDUL yace, "Nagode Babana, zanci gaba da sanka da qaunarka har iya qarshen rayuwa". "Nima haka ABDUL, Allah ya albarkanci rayuwarku.

"Ameen ABDUL yace mai da kallan momy yana cigaba da cewa, momyna  zanso kiyafema maman AMEER duk abinda tayi miki arayuwa da wanda tafad'a miki da wanda ma bata fad'a miki ba.

"ABDUL bazan iya yafe mata ba, nadai ji bazan makata a kotu ba, kamar yanda kowa anan ya rokwan mata alfarma, amma batu akan yafiya babu shi tsakanina da ita. Momy tabashi amsa wajen fad'in hakan.

Ahankali ABDUL ya tashi yaje gareta da durqusawa gabanta yace, "momy, Allah yana san bayinsa masu yafiya, dan Allah momy dan....

Katse shi momyn tayi wajen kama hannunsa tace, "Ayanzu duk duniya bana jin akwai maganar wanda zanji kamar taka ABDUL, saboda ƙaunarka da soyayyarka datayi min mugun kamu ayanzu, ABDUL wallahi najika araina fiye da komai a rayuwata, ina san amatsayina na mahaifiyarka daka barni karka matsamin kan dole saina yafe mata, idan dai kai zaka yafe mata to kayafe mata, amma karka qara sani ciki...

Murmushi yaqe ABDUL Yayi, dayi mata kiss a hannu ya dawo da hankalinsa kan mama Sauden zaiyi magana Zainab ta kallesa da cewa, "A matsayina na masoyiyarka bana san naji kace kayafema mama Saude.

Ta faɗinma ABDUL d'in hakan tana me d'auke idanta daga kallansa.

Murmushi ya sakar mata da cewa, "me yasa.

Tace "haka kawai

Yace "Nayi niyar yafe mata saboda Hajjiya Kakah da d'an uwana AMEER...

"Ni kuma nace ban yarda ba, ta katseshi da fad'in hakan.

Nan ko falan ya hargitse kan Abdul yace wani abu, kowa afalan yayi kan ZAINAB d'in suna masu cewa bai dace tace haka ba, tayaya yayi niya sannan ta hanasa, babu ruwanta tabarshi yayafe mata.

 

ZAINAB najin haka tatashi da niyar barin gidan gabaki d'aya, nan ABDUL d'in yayi saurin shan gabanta, idansu ya haɗe da juna, zahiri sunji wani yanayi, amma suka share wajen d'auke idan nasu daga kallan junan. ABDUL yace, "Aunty ina san na yafe mata, dan Allah kibarni.

Ta kallesa da cewa. "Na gaya maka, a matsayina na masoyiyarka ban yarda ka yafe mata ba.

Yace "Haba mana my Aunty, yaushe kika koyi baqin hali.

Tace, "yanzu, yanzu na koya ABDUL, fatana karka yafe mata, idan kuma kamatsa kan saika yafe mata , Wallahi babu ni babu kai.🙅🏻

Waro ido 😳 ABDUL yayi da cewa, "Me yayi zafi Auntyna, sam bazan iya wannan yafiyar ba idan har zatayi sanadin rabani dake,

Kawai zan jira lokacin zuwan ranar da zakice na yafe mata na yafe matan,  ina fatan hakan yayi miki, murmushi tayi mai da gyaɗa masa kai alamar eh yayi mata.

Shima murmushin yayi mata da cewa ta koma ta zauna.

 

Matar Baba Shehu ta kalli ABDUL d'in tace "Yanzu ABDUL baka yafe mata ba kenan, murmushi ya qarayi dace mata, "Gaskiya nayi niyar yafe matan, amma Kuma bani san wani sab'ani ya shiga tsakanina da Auntyna, dan haka zan jira zuwan lokacin da zata yarjemin saina yafe mata.

Mijin Hajjiya Kakah yace "Hakan yayi kyau, itama Hajjiya Kakan taji dad'in hakan, dan zaka gane ne hakan ne da yanda take gyaɗa kanta,😃

 

Masha Allah komai ya bayyana kowa yasan waye shi, nan sukayi addu'a suka shafa kowa na gidan nasu sukabar falan dan nufar nasu gidan..

Kunsan dai mama Saude bata ba komawa shashinta, haka tayi shashin Hajjiya Kakah dan itace dolanta, aiko d'aki guda ta bata tace mata tayi duk abinda zatayi a cikinsa, karta gangaro mata nata dana ZAINAB, taje can taci baqin halinta.

Haka mama Saude tana ganin y'any'anta lokacin da take kwashe kayanta suna kuka haka tabar musu shashin ubansu, Sam baban nasu Bai damu ba dama akwai wata bazawara data sakamai gaba kan tana sanshi zaije su daidaita ya Aureta kawai dan dama yaga zatayi hankali da nutsuwa.

 

 

Anan ko ya rage daga ABDUL sai AMEER zai Dadynsu da momy da qanwarsu Abida.

Haka Dady ya rungumi AMEER yace mai yana sanshi har gobe, dan Allah baya san  ya saka wani abu aransa, yaci gaba da d'aukarsu matsayin iyayensa,

Haka AMEER d'in yaje ya kama qafar momy ya nemi gafararta, tayafe mai itama tace mai ya kwantar da hankalinsa har yanzu shi d'anta ne, dan yasha nononta baza tatab'a goge hakan ba.

ABDUL yayi murna sosai dajin hakan,

 

Doctorn da yake zuwa duba lafiyan Dady yazo ya duba ABDUL awannan lokacin, dan dama shine wanda momy takira, ya basa mugunguna dace musu gobe idan baiji qarfin jikinsa ba to sukawosa asibiti...

 

 

Haka ko akayi, washe gari ABDUL ya tashi da qarfin jikinsa, haka yaje ya gaida Hajjiya Kakah da Auntyn tasa Zainab, kana yaje ya d'an kwashe kayansa masu amfani a d'akinsa na gidan yakai gidan nasu, sauran kuma ya barma yaran gidan,

 

Dady yaso bama ABDUL wani d'aki dake jikin na AMEER dan yafi girma da tsari, sai momy tace mai aa yabar ABDUL d'in su dinga kwana a d'akin AMEER d'in kwana nawa ne ABDUL d'in zai bar gidan, ya koma nasa da iyalinsa, aiko Dadyn yaji shawarartata...

 

 

 

 

****Rayuwar fa tacanja musu, dan ABDUL yana ganin soyayya zallah agun iyayen nasa, sanshi suke qaunarsa suke kamar su cinyesa, sam basu san suga baya tare dasu, Bai yada Hajjiya Kakah da baban AMEER  ba, dan yana kai musu ziyara akai akai,  saika rantse ma bai bar gidan ba.

 

Babu wani batun TANTIRANCI yanzu agun AMEER da ABDUL,

Sun canja rayuwarsu

Dan dama ABDUL kun sani komai yanayi ne ba'a san ransa ba.

Yanzu ko baya yin komai na rashin ji.

Dama shaye shaye ne yaso yimasa illa kan anya zai iya denawa kuwa, da Dadyn ya fuskanci shine matsalar sai yaje neman musu magani,

Aiko yaci sa'a awannan karon, danya had'u da wani malami ya basa wani rubutu wanda aka rubuta Ayaturkursiyu qafa d'ari uku da fatiha qafa  hamshin da qasar shuri, yace mai idan dai suka sha bazasu qara sha'awar shaye shaye ba.

Aiko haka akayi, tunda ya basu suka sha basu qara jin sha'awar shaye shaye ba,

 

 

A sati uku kacal fah🤔. Suka zama mutanan kirki Kuma kowa a unguwar tasu ya shaida hakan. Saboda yanda d'abi'unsu ya canja, kai bazaka tab'a cewa AMEER ne da ABDUL ba.

Sun gayama ogansu me basu hodar iblis cewar sunbar harkar, aiko ogan nasu yaji haushinsu sosai, saidai ba yanda ya iya dasu, haka yayi hak'uri yana me addu'ar samun wasu kamarsu...

 

 

Yanzu haka ABDUL ya bama Dadynsa takaddar gama makarantarsa, har dadyn ya kaisa companynsa inda ya bashi matsayi me girma dan yaji dad'in yin aikin yanda bazai wani sha wahala ba, haka AMEER ma, shima ya basa aikinyi a companyn amma yana qasa da ABDUL sosai, kasan cewar karatunsa baiyi zurfi kamar na ABDUL d'in ba.  Sam kadaddarsa batakai ma a d'aukesa ba, amma ya Dadyn zaiyi, dole ya bashi aikinyi, dan ba irin faman da baiyi dashi a rayuwa kan yayi karatu yanda ya dace ba, amma AMEER yaqi yi.

Aiko yaji haushin matsayin da aka bashi, yayi takaicin rashin maida hankalinsa kan karatu dabaiyi ba.

Ammafa bawai ina nufin yaji baqin cikin matsayin da aka bama ABDUL bane, aa kod'an, dan AMEER ƙaunar ABDUL yake da zuciya d'aya.

 

 

ZAINAB ko zaman iddarta takeyi da wani qudari aranta. So take tagama iddar ta gayama ABDUL udirinta, wallahi tana san mijinta kamar yanda shima yake santa.

Ta gayama ABDUL mahaifiyarsa ce tazo gidan nata tasa Salisun agana kan dole saiyayi mata saki uku kota tsine masa, dan ita sam bata yarda da zainab d'in ba, bata santa dan haka ya saketa, tafi san shi da y'ar uwarsa, haka yana hawaye yace mata shi bazai iya sakin zainab ba,  tacemai saiya saketa ko yanzu ta d'aga mai nono da tsinuwa, shidai shuru yayi mata, ganin hakan saita fashe da kuka tana cewa wai b'oye masa takeyi ZAINAB d'in ce tazo har gidanta tayi mata zagin cin mutunci, tofa shine yana jin hakan sai yayi mata saki ukun.

Hak'uri dai ABDUL ya bata.

Yanzu haka kullum sai Salisun yazo gidan nasu bata hakuri, wai ya gane gaskiya ashe sharri mahaifiyar tasa tayi mata, dan Allah tasan yanda zatayi su kara zama ma'Aurata, Wallahi zai bata mamaki wajen bata kulawa, dan yanzu bashi da abinso kamarta.

Haka kullum yake zuwa yake b'ata tunaninta,

Hajjiya Kakah tayi mai zagin duniya yaqi dena zuwa, ABDUL yana lura da lamarin nasu sosai, kawai dai ya zubama auntyn tashi ido yaga ya zasuyi tunda saki uku ne...

 

Ita dai ZAINAB taji hud'ubar mijin nata, addu'a take tagama idda lafiya ta tunkari ABDUL da udirinta..

 

 

 

 

 

 

___Yanzu haka ABDUL da AMEER suna zaune ne a d'akinsu sun dawo daga aiki har sunyi wanka suna hutawa.. Abdul karatun littafin ANIL yakeyi na sanin d'abi'un mata da yanda suke rayuwa, Sai AMEER ya kalli Abdul d'in yace mai, "Nifa aure nake sanyi, idan dai ana san na kintsu gabaki d'aya, kaga tunda abin nan ya faru ban qara jin mace ba, ABDUL hakurina yana san qarewa..

ABDUL yayi murmushi yace.. "Ni har katuno min da RAHMA, kona tana wane hali ne yanzu oho.

AMEER yace, "bani jinta yanzu cikin group.

"Eh, naji momy na cewa, wai mamanta ta kwace wayarta, ABDUL ya bama AMEER amsa da faɗin hakan.

Sai AMEER d'in yaja numfashi yace, "yanzu jibi za'a kawo maka ita ko.

ABDUL ya waro ido yace. "Waya gaya maka,

Yace "naji Dady da momy suna maganar ne jiya lokacin kana bedroom..

ABDUL ya tab'e baki yace, "Hmm, AMEER yarinyar bata da kunya, tsiwa yayi mata yawa, amma ba komai zan canja tunaninta.

AMEER yace, "koma me zaka canja mata ka canja mata, yanzu ni dai me zanyi.

"Kawai kaje wajen Dady da Babah, ka gaya musu kai aure kake so"

"ABDUL Kona gaya muku bani da wacce zan kawo musu matsayin itace zab'ina, kana dai gani duk waƴanda nasansu duk a harkar bariki ne, Kuma gaskiya ba wacce zankai gidana cikin matsayin matar Aurena.

"Kaga illar iskanci kenan, wallahi da'ace da yanda zanyi dakai awannan lokacin da kake aikata masha'ar, dana dinga hanaka yanzu kaga amfanin hakan

Amman Ba damuwa, muzaga gari kawai idan kaga wacce tayi maka saiku kwalle kawai,

"aa zandai bari akawo maka RAHEEMAT, ba mamaki naci karo da dai dai dani cikin qawayenta, ko yayunta ko qannanta.

"Ok, hakan yayi...

 

 

 

 

______Labarin RAHMA ko shine, bayan rabuwarta da ABDUL tunaninsa ne ya dinga ram da zuciyarta, haka take tuno yanda suke cacar bakin nan dashi, idan tazo inda ya bata kiss rintse idanta takeyi,🤔 tarasa wannan wata irin masifa ce, kwata kwata bata da wani tunani sai hakan, data gayama UMMAKATI ce mata tayi tafara sanshi ne, sanda RAHMA takusa fasama UMMAKATI kai dan taji zafin amsar data bata matuqa, akan me dan kawai tana tunanin mutum zata wani cemata wai ta fara sanshi ne.

 

Sunyi haka da kwana biyu mamanta ta karb'e wayarta, aiko RAHMA tashiga damuwa da tashin hankali, dan taje tasai wata, maman ta qara kwacewa tace idan taqara ganinta da waya saita tsine mata..

Jin hakan sai yasa RAHMA hak'ura da batun wayar.

 

Wani magani me zaqi mamanta take bata dame bauru, haka zakaga RAHMA ta amshe bakinta shuru  tana sha.

Sarai tasan maganin mata maman nata take bata, dan indai maganin mata ne ba wanda bata sanshi ba agun UMMAKATI, hakan yasa bata qin karb'a, fad'i take aranta zata sha, ammafa ba ABDUL bane zai moreta, wallahi koyafi waye qoqari takardarta zai bata taje ta Auri wanda ya dace da ita.

 

Haka maman take mata turaran jiki da dilka dan ta'iya sosai, kullum saita mata dilka, kuma tabata maganin mata.

Ita kanta RAHMA tasan duk wanda yayi gigin kusantarta, idan bai zauce ba toko komai zai tsaya masa arai...

 

Tunda asirin kan RAHMA ya karye shikenan tadena yawan dare,  UMMAKATI tarasa meyasa RAHMA tadena yawan dare, har tambayarta tayi, tako ce mata ita haka kawai taji bata san yawan, ƙila kodan da igiyar Aure ne akanta shiyasa taji ta tsani yawan daran..

Haka UMMAKATI take tafiya abinta, saidai yau taje gobe taqi zuwa, da haka da haka itama taji bata san zuwan.

Ammafa suna d'anci gaba da shaye shaye. Dan wannan abu mugun abu ne.

 

Haka zasuje inda suke siya su suyo abinsu su maka a d'akin UMMAKATI su b'ingire nan suta makar bacci, sam maman UMMAKATI bata da matsala dasu.

 

Itako maman RAHMA neman RAHMAN takeyi ta rasa, tayi mata fad'an duniya kan yanzu bafa da bane, da take da damar zuwa duk inda taga dama, yanzu da igiyar Aure akanta, duk taku d'aya idan tayi tsinuwace take aiki akanta, dan haka ta kiyaye, amma ina.. RAHMA ficcewarta takeyi abinta.

Hakan yasa maman take addu'ar Allah yakaita kwanakin dasuka rage mata dan takaita d'akin nata ta huta.

 

Ana cikin haka sai y'ay'an kishiyoyin nata suka fara aikata rashin ji irin na RAHMAN,🤔 abin kamar wasa sai gashi har sun fara yawan dare irin nata, babansu ya kirasu ya tsawatar musu ammafa abun ya fassara, hankalin iyayen nasu mata ya tashi matuqa, haka suma suka dinga kiran yaran suna musu fad'a, amma ina.. Tafiya sai tafiya take, wannan ya tabbatar musu da cewa lalle kam asirin ya koma kan y'ay'an nasu, dan gashi nan ita RAHMAN tadena su Kuma sun karb'a.

 

 

Nan suka saka RAHMA a gaba cikin wayo da hikima irin tasu ta manya, wai tabasu number na ABDUL su kirasa sunsan me zasuce masa ya saketa.

Nan tabasu labarin ai wayarta tana wajen mamanta ta kwace mata, kuma ita bata riqe numbar tasa akanta ba, amma bara taduba a wayar UMMAKATI, bazata rasa numbar tashi ba, dan group d'aya suke.

Suna jin hakan suka zuba mata ido tana duba numbar a wayar UMMAKATIN

Saidai anyi rashin sa'a, dan tayi duban duniya a WhatsApp d'in UMMAKATIN bataga wannan group d'in ba, saida UMMAKATIN tazo take gaya mata ai tunda maman nata ta karb'e wayarta tafitta daga group d'in.

Jin hakan shiyasa RAHMA sanar dasu yanzu ba inda zata samu number nashi sai gun babanta ko mamanta, Kuma ko taje garesu ba bata zasuyi ba,

 

Baqin ciki haka ya qara kamasu, basu samu yanda suke so ba, amma sunci gaba da zugata sosai wai karta yarda duk yanda za'ayi ta karb'i takaddanta, koda kuwa ankaita gidan nasa ne,

 

Hakafa kan RAHMA ya kulle tadinga kallansu matsayin masoyanta ayanzu, tasa aranta mamanta ce maqiyiyarta, tunda taqi bata goyen baya kan lamarin...

 

Ita dai maman nata kallansu take, duk da bata fahimci me yasa yanzu suka had'e da RAHMAN ba, tasan dai koma dai miye munafunci ne...

 

 

 

 

To yanzu haka jibi ne za'akai Rahman kaduna gidan mijin nata ABDUL,

Ba irin kayan kitchen d'in da maman nata bata siya mata ba, dan dama itace kad'ai y'arta mace, tanadin duniyar nan ita takema, dan duk sana'ar da maman takeyi tattalama RAHMA kud'in take..

 

 

_____Yau dangi suka had'u dan kaita garin na kaduna, kaf y'an uwanta mata ba wacce tace bazata ba, kowa so yake aje dashi,

Haka y'an uwan momy da sukazo d'auka suka dire kayan lefenta akwati shidda manya manya, kayane na yara yaran mata, masu tsada da aji, dan momy da kanta taje kasuwa tayo mata siyayyar..

 

Haka ganin kayan ya qara baqanta ran kishiyoyin maman nata, bayan kowa ya gama gani mamanta cewa tayi atafin mata da kayan dan ba'ayi zuwa biyu ba,

Nasiha ba irin wacce mahaifin RAHMA baiyi mata ba, mamanta ko kiran Abdul tayi tace mai idan RAHMAN tamai wani abu ya gaya mata, dan tsine mata zatayi tabi duniya, musamman idan taganta da takaddar saki kuma ya kasance itace tayi sanadin sakin, gaban RAHMA ya fad'i Sosai dajin furucin mahaifiyar tata, tanaji ABDUL d'in yace mata ba damuwa zai gaya mata duk komai dazata mai.

Murmushi maman RAHMAN tayi da kashe wayar dan dama tana san ta jefama RAHMAN tsaro ne aranta, kuma taga tsoran muraran akan fuskar tata..

 

 haka aka saka RAHMA a mota zuciyarta cike da tunanin zancikan mahaifiyar tata,

Haka Y'an uwa da abokan arziqi sukayi garin na Kaduna da ita.

Aiko sunga kaduna garin gwamna, kari me kyan mafasali.

Anan gidan momy suka sauka,

Bayan sun huta sun danqa mata amanar RAHMAN, sai tasa wata y'ar uwarta tayi musu jagora zuwa gidan RAHMAN dan akaita d'akinta in yaso sai su dawo gidan nata su kwana ammafa ba agidan amarya ba😃.

 

Haka ko akayi, gida dai ko hasidin iza hasada bai isa kushe wannan gida ba,

Gida fah yayi kyau irin sosai d'innan, aljannar duniya ake gaya muku.

Saidai fa part biyu ne, Kuma duk iri d'aya ne.

Kowa yana gani cewa yake lalle RAHEEMAT zaki zauna da kishiya,  hmm shuruma amsane inji RAHMA, dan sam batacema kowa qala ba tunda ta gaisar da surukar tata wato momy.

UMMAKATI ce dai take basu amsa wajen cewa, lallema, ai qawata ba ita ba kishiya.

Hakan yake sawa bakinsu yin shuru

 

Babban falo biyu ne da RAHMA sai 2 bedroom, 1 nata 2 na yara, Kuma ko wanne da toilet a ciki,

Sai babban dining da babban kitchen.. Kai komai dai masha Allah,

Dukka falan biyu ko wanne da kalan adansa, d'aya anyi masa kwalliyar ruwan duka da biki, d'aya Kuma kalan ganye turarre da wanda bai turu ba, hanyace tako da ina wacce zata iya sadaka da ko'ina.

Sai shashin ABDUL d'in a tsakiyar part d'in RAHMAN da wancen part d'in daba'a bud'e ba.

Daga falokan RAHMA kana hango kitchen d'inta dan ba'a katangesa da gini ba, an katangesa da gilashi ne, me matuqar kyau da kyalli, zaka hango wanda yake ciki da abinda yake girkawa..

 

Tsakar gidan ko, bishiyoyi har biyu ne aciki, ga makeken wajen wanda na zamani, harda wajen shaƙatawa me birgewa,

Kai gida dai yayi kyau Masha Allah, wannan kalma ita ce kalmar da kowa yake furtawa a bakinsa.

 

Nan kishiyoyin mamanta dake dasu akazo, suka rikice hankalinsu ya tashi, baqin ciki da hassada ya kamasu, me lura ne Kawai zai iya gane cewa Suna cikin wani hali.

Haka kusan qarfe goma na dare direbobi suka  koma gidan Dady dasu,.

Amma RAHMA ta riqe UMMAKATI sam taqi yarda atafi da ita, tace anan zata kwana in yaso da safe ta koma gidan Dadyn atafi jos d'in da ita....

 

 

 

Nanko su ABDUL suna tare da ZAINAB sun sata gaba wai itace zata rakasu gidan amarya dan yanzu basa da abokanaye😂

ZAINAB tace sun rainata, bazataje ba, ai idda takeyi mezaisa tafitta, haka suka dinga lallab'ata har dai ta amince,

 

Kusan goma da rabi  haka suka nufi gidan ABDUL d'in da ita.

 

Sun samu ba kowa a gidan daga RAHMA sai UMMAKATI..

Nan AMEER ya ajiye musu kaza da madara ZAINAB tashiga yima ABDUL da RAHMA nasiha akan zaman Aure..

Sanda tagama tsaf RAHMA ta d'ago da kanta ta kalle ta, gaskiya matar kyakkyawa ce, saidai haka kawai taji bata santa aranta, Kuma bazatace ga dalilinta ba,

Haka dai tasakar mata murmushi itama ZAINAB d'in ta sakar mata murmushin gabanta na bugawa, tun da safe take jin faɗuwar gaban nata, yanzu ganin RAHMAN sai abun ya qara tsananta aranta...  Haka ko shakka babu itama RAHMA tanajin faɗuwar gaban,

 

Haka dai ZAINAB suka ficce da AMEER sukabar ABDUL da kulle gidan..

 

ABDUL dawowa yayi bedroom d'in RAHMAN  ya kalli UMMAKATI yace, "Sunnu qawarmu, murmushi UMMAKATI tayi da cemai, "Yauwa sannu angonmu. Tana faɗin hakan taficce daga d'akin tayi d'akin dake jikin na RAHMAN ta kwanta dan tabasu waje su gana, bacci takeji sosai dan haka saita kwanta kan gadan dake cikin d'akin, dan babu abinda babu ad'akin.

 

ABDUL na ganin UMMAKATI ta fitta ya d'ane gadan ya ritsa RAHMA acan k'urya suna masu jin numfashin juna, ahankali yace da ita, "Yau ga RAHMA a gidan ABDUL matsayin matar Aurensa,🤔 toyau zaki kashe nin ne koko sai ankwana biyu.

Harararra RAHMA tayi da cewa "Saurin me kakeyi, kajira lokaci mana.

Yace "Ai d'okin mutuwar nakeyi, pls gayamin yaushe kika shirya kashenin. Jan numfashi  RAHMA tayi sakamakwan hamshin turaransa dake bugarta, cikin wani halin tace, "Gaskiya bazan iya kashe raina ba koda na kiyashi ne, bare Kuma na mutum mutumin ma wanda yazo a matsayin mijina, dan Allah ABDUL mu tsaya mu fuskanci gaskiya, Wallahi bana san Auran nan, kasake ni na kama gabana, tunkan aji kaina dakai.

"RAHMA ina san aji kaina dake, wallahi babu batun saki tsakanina dake, idan zaki kwantar da hankalinki ki kwantar da hankalinki kifara sona nima na fara sanki mu Gina rayuwa me ban sha'awa. Danni a tsarin Aure babu saki aciki.

 

Wata muguwar harara tagalla masa, ya kama hannunta, nan take sukaji wani shock, sukayi saurin kallan juna, sai kuma suka share, haka yahau shafa hannunta yana me jin laushi kamar na Auntynsa ZAINAB, nan ya dinga bin jikinta da kallo ganin yanda ta qara kyau sosai kamar wata ba'indiya, sai wani qamshi ne yake fitta daga jikinta, ga lallan da aka mata ya dace da fatar tata,

Wata doguwar riga ce a jikinta me matuqar kyau ta let, gata ja, abin saiya bada kala, tana jinsa ya janye mata d'an gyalan data saka akanta, nan gashin kanta ya baiyana abin gwanin ban sha'awara, babu wannan tsinan nan kitsan nan dake kanta, wanda baya bashi sha'awa, batayi  kitso ba, amma kan yasha gyara sosai...

 

Da sauri ta make masa hannu tace "malam ya isheka da tab'a ni, Kuma wallahi saika sakeni danni basanka nake ba.

Sauka daga gadan ABDUL yayi yana cewa, "toh dama wayake sanki, mummuna dake sauran maza, sakin ki ne dai bazanyi ba, haka zaki zauna kita jiramin gida kinga babu wani batu na zuwa KARUWANCI kenan.

 

"Wallahi baka isa ba, kayi kad'an, ba zaman da zanyi na jira maka gida, aduk lokacin danaga damar fitta fittata zanyi sai naga abinda zaka min, batu na mummuna  daka kira dashi kuwa kaine mummuna bani ba, kaje ka kalli kanka a nadubi shizai baka wannan amsar,

Sanna ka kwantar da hankalinka KARUWANCI har anan bazan fasa yinsa ba, akwai clubs da yawa dana sansu anan, zanje garesu ba abinda zai canja dan ko'ina naje mazajen da nake harka dasu biyoni suke, dan ba abu bane me sauqi su iya  rabuwa da abubuwan da suke samu daga gareni...

 

Amsar tabama ABDUL haushi matuqa🤣 dan haka RAHMA sai ganinsa kawai tayi a ganta ya wani d'auketa da mari, yana cewa, "da Aurena akanki kike fad'in min wannan maganar.

Nan tsoransa ya kama RAHMA tadafe kunce had'e da fashewa da kuka, a shagwab'e tace mai, "Allah ya isan min mugu azzalimi, wato babu dad'i ni kayimin maganar KARUWANCI dan kawai na baka amsa saika maran,

Aiko nan ya qara falleta da wani marin dan da gasken gaske ransa ya b'aci Sosai.

Haka takasa ramawa sai kukanta data qara volume d'insa.

 

Nan kuma ABDUL yayi tunani irinsu RAHMA duka bazai biyu dasu ba, bazai qara tab'a lafiyarta, kawai zaiyi qoqari yayi mata illah a so, ya dasa mata sanshi da qaunarsa cikin ranta, ba makawa zai samu yanda yake so akanta, dan yana da sani akan irinsu basu iya san abu ba, haka basu iya qinsa ba, ya karanta a littafin wani marubuci ANIL wanda yake fayyacema mutane halayya mutum iri iri musamman mata.

 

Irin su RAHMA SO shine abu me sauqi wanda zai yake narkar da zuciyarsu nan kusa, shine abun da yake canja halayyarsu cikin qauki.

Haka ABDUL ya zuba mata ido tana kukan abin dariya abin takaici, dan kukan yana tafiya da wani salo ne, kamar shagwaɓa-shagwaɓa haka..

 

Haka ABDUL ya tattara tunaninsa kaf idan har yana san yayi maganinta nan kusa dole ya dinga amfani da jikinta yanda zai dinga kashe mata jiki takasa komai, Daga nan idan tafiya tai tafiya dole komai ya canja...

 

Haka ya janyota jikinsa tana turesa ya nuna mata qarfi, haka ta hak'uri ya kwantar da kanta bisa ƙirjinsa, ta cikin kunanta yahau bata hakuri, ahankali ahankali yake bata hak'urin kamar masoya, faɗi yake.

"Na tuba na tuba my Baby, bazan qara tab'a lafiyar jikinki ba my dear, dan Allah kiyafemin.

Dake babu abunda yake ran RAHMA sai saki, nan tace, "zan yafe maka idan har zaka ban takaddar sakina yanzu.

 

Dake ya shirya yimata wayo tako wane fanni sai ce mata yayi, "zan baki amma ba Yanzu ba, dan bani san mamanki ta tsine miki yanzu, kina dai jin abinda tafad'a d'azu, yanzu abinda za'ayi shine, kiban lokaci mukai irin nan da shekara d'aya saina baki takardarki na kuma tabbatar ma da mamanku baki da lefi kawai nayi ra'ayin baki takaddar ne.

Amma Idan na  baki yanzu akwai matsala, ko kina buqatar na baki mamanki ta tsine miki kibi duniya ne.

 

Da sauri RAHMA ta girgiza masa kai tace "Na yarda da wannan shawarar, amma babu ruwanka dani, zakayi rayuwarka inyi tawa bame shiga harkar kowa,

ABDUL yaja numfashi, yace "Gaskiya hakan bazai yuhu ba, dole zamu dinga shiga harkar juna, kamar yanda mata da miji sukeyi, idan har bamu so a gane shirinmu.

Kinga zamu dinga wasa irin na ma'Aurata, zamu dinga kwana gado d'aya, danni ban iya kwana ni kad'ai a d'aki ba, idan nakwana ni kad'ai a d'aki washe gari ganina ake a sume, wannan yasa muke kwana d'aki d'aya nida AMEER.

Kinga kuma mu ma'aurata ne, su momy najin na tashi a sume zasu gane bama kwana d'aki d'aya, kinga daga wannan lokacin asirinmu zai tonu, dan haka dole tun daga yau mu fara kwana d'aki d'aya, amma babu wani abu dazai shiga tsakanina dake, saidai hakan ya zama sirri tsakaninmu, karki gayama kowa ciki ko harda UMMAKATI.

 

Shuru RAHMA tayi tana tunani, can ta d'ago da fararan idanta ta kallesa tace, "Toh kai meyasa kake sumewa idan kakwana kai d'aya.

  Yace "wani aljani ne yake zuwa ya sumar dani,

RAHMA ta waro ido tace "Aljani,  yace mata "Eh, amma baya zuwa idan yaga ina tare da wani.

Tayi shuru tana ji aranta tayarda ne koko taqi yarda, can dai tayanke shawarar tayarda tunda shekara d'aya ne, shike nan sai ya bata ta kaddarta bame zarginsu, ta tsallake tsinuwar mahaifiyarta kenan..

 

Haka tace mai, "Na amince, amma babu batun wani abu dazai  shiga tsakanina dakai.

Murmushi ABDUL yayi, yana fad'i aransa, Gaskiya yaso ya kwafsa, ashe yarinyar wawiyace haka bai sani ba, hmm Wallahi har ciki sai yayi mata danya qara karya lagwan maqiyanta, a filiko cewa yayi, "Babu Abin da zai shiga tsakanina dake my Baby, sai abu d'aya,

Ahankali taca mai. "Toh miye shi.

Nan ya kai d'anyatsansa kan leb'enta ya hau shafawa yana cewa, "tun ranar dana miki kiss, bakinki ya shiga raina, dan Allah badan ni ba, ina buqatar kiyimin wannan alfarmar, na dinga yi miki shi aduk lokacin dana so.

A shagwaɓe tace mai "Nidai gaskiya ban yarda ba,

"Haba my Baby, tsoran me kike ji, bayan babu soyayya tsakaninmu bare kiyi tunanin zanyi miki wayo.

Jin hakan dayace sai tace mai, Toh tayarda.

 

(Rahma Nalele tace kinyi kuskure RAHMA, dama tasan duk masu sunan basu cika wayo ba Amma bata tunanin harda ita😂)

 

ABDUL najin hakan yaji wani dad'i aransa, nan batayi aune ba ya haɗa bakinta da nashi yana aika mata dame zafi, nan ko yaji almamun gangan jikinta ya fara karb'a.

Bai bari lamarin ya fara yimasa illah ba, nan yadena yimata, aiko ta tsinci kanta da qara shigewa jikinsa.

Sanda ya tabbatar komai nata ya dawo yace.. "Toh yanzu zanso muyi al'awala muyi sallar godiya ga Allah, kana muci abinci muje mu kwanta ko.

D'aga masa kai kawai rahama ta iya yi.

Ganin hakan ya qara tabbatar masa da lamarin ya shigeta, sai yaci gaba da cewa, ki maidani abokinki yanzu babu wani batun fad'a tsakaninmu.

Nanma qara d'aga mishi kai tayi,

 

Haka yayi shashinsa yana murmushin mugunta, itako har cikin zuciyarta bata d'auka duk shukata yayi ba,

 

Sanda tayo alwalar Sannan tayi tunanin ai tunda bawai zaman auran zasuyi sak ba, bai kamata suyi sallar ba,

Dayazo tagayamai hakan cemata yayi wannan ba matsala bane karta damu, ko sunyi ba wani abu bane.

Haka suka gabatar da sallar har ya dafa kanta yayi mata addu'o'i, daya fara yi mata tambaya akan yanda take wankan tsarki da sallarta daqer take bashi amsa.

Hakan ya qara tabbatar mishi da cewa kai ba wani abu da RAHMA tasani akan iskanci.. Dan da kunya cikin amsoshin da take bashi.

Bayan ya gama yi mata tambayoyin ne ta kafesa da ido tana tambayarsa meye dalilinsa nayi mata tambayoyin, yace kawai yayi mata ne, zatayi magana ya d'auke hankalinta wajen saka mata kaza abaki,

 

Haka ya dinga bata tanaci a shagwaɓe, sanda ta k'oshi tace mai ya isheta,

Nan yace mata to bara ya kaima UMMAKATI d'ayar kazar dake biyu ne,

Nan RAHMA ta waro ido, ita sai yanzu mah tatuna da wata UMMAKATI,

Ya kalleta kad'an yace "Kin manta da ita ko.

D'aga masa kai tayi da cewa, "Kuma ban san me yasa ba,

 

Murmushi yayi da shafar fuskarta yace "ina jiranki a d'akina idan kinyi wanka,

"Toh tace mai.

Saiya ficce,

ya tarar da UMMAKATIN har tayi bacci, haka ya ajiye mata kazar da sauran madarar da RAHMA tashan yayi shashinsa yana mamakin RAHMA, tabbas zatayi sauqin kai idan ya'iya bi da ita...

 

 

Sanda RAHMA tayi wanda tasa wasu kayan bacci riga da wando masu laushi, sam basu bayyana komai na jikinta ba, amma sun mata kyau matuqa, haka ta tubke gashinta tasaka turare tayi d'akin da UMMAKATI take, taga baccinta take sai kawai taqara gyara mata bargo, taja mata ƙofa tayi shashin ABDUL d'in,

 

Gaskiya shashin nasa yayi kyau matuqa, acan bedroom nasa tasamesa kan gadansa yana danne danne a waya.

Ya d'ago shanyayyun idansa ya zuba mata, tayi kyau sosai cikin kayan, ya fad'i aransa.

Bata wani jira cewarsa ba ta haye gadan tad'an matsa gefensa takwanta dajan bargo,

Murmushi ABDUL yayi bai kulata ba, sanda yagama abinda yakeyi cikin wayar tasa kana shima ya shiga bargwan ya rungumota jikinsa tare da sakar mata kiss a kumatu, zatayi magana, yayi saurin taranta wajen cewa "karki damu ina da tsoro ne, haka nake ma AMEER.

Cikin sauri tace "Toh ai ni ba AMEER bace,

Yace "Nasani, nidai kiyi hak'uri idan bana jin jikin mutum mafarkai nake masu abin tsoro.

Shuru tamai

A haka bacci yayi awan gaba dasu

 

 

Asuba nayi ABDUL ya tashi, gaskiya yaji dad'in baccin nasu, yayi alwala ya tasheta kana yayi masallaci. Dan ABDUL bai saba sallah a gida ba,

 

 

Qarfe tara momy taturo musu da binci me rai da lafiya,

Dukkansu ukun suka had'e a dining danyin  breakfast d'in, wato ABDUL RAHMA & UMMAKATI.

AMEER ne ya kira ABDUL yana gaya masa irin missing d'insa da yayi. Dan ya roqesa yazo yanzu suyi breakfast tare.

AMEER yace mai ai yaci nasa, momy ta cika masa ciki tam, Saidai yazo ya gansa kawai.

Toh ABDUL yace mai

 

Sunako cikin ci saiga shi yazo, bayan sun gaisa kallan kallo ne ya shiga tsakanin AMEER da UMMAKATI, itafa tunda tagansa jiya taji ya kware mata, nan taji tana sanshi tana qaunarsa,

 

Shiko AMEER bai wani jita a jiyan ba, amma yanzu ganinta sai yaji tayi masa, dan tana da kyau sosai, kuma komai nata abun dubawa ne ga namiji.

 

Nan baiyi qasa a gwiwa ba yacema RAHMA, "ina san ki bani qawarki UMMAKATI,

RAHMA tayi murmushi tace, "qawata tana da tsada, dan haka sai kabi wasu sharad'od'i.

"Gaya min zan bisu danna mallaketa.

ABDUL yace. "Haba my dear, darajata ayimai afuwa abashi ba tare da wani sharad'i ba.

RAHMA tace "toh na bashi ita, amma yayi ahankali, dan ta'iya b'oye zuciya idan tasace ta, musamman idan taraina me zuciyar...

Kallan UMMAKATI AMEER yayi yace, "Abar san kuwa, wai haka abin yake"

Murmushi tamai da cewa, "Da wiya RAHMA tagaya maka magana ba daidai ba"

"Idan ko haka ne, zan shigo da zafina, dan bani buqatar arainani, bare a b'oye min zuciya inda bazan ganta ba.

Tace "hmm! Ƙofar a bud'e take, idamma da gudu zaka shigo bada zafi ba zaka taddani kuma insha Allah bazan raina rigar jikinka ba bare kai kanka.

 

Wannan shine mafarin soyayyar AMEER da UMMAKATI..

 

 

Haka a wannan ranah y'an uwan RAHMA da kishiyoyin mamanta suka dawo jos, 

Wai ance sabo tushen wawa, RAHMA da UMMAKATI har kukan rabuwa da juna sukayi.

 

 

 

 

___ABDUL sai wayo yakema RAHMA da hankali yana amfani da rashin wayan nata yana dasa mata qaunarsa cikin ranta,

Sam ba abinda yake shiga tsakaninsa da ita, Amma idan kaga yanda Suke wasa da juna saika d'auka komai na Aure ya shiga tsakaninsu.

ABDUL yayi nasarar b'ata tunanin RAHMA danta sake dashi,

Danko ta sake dashi, dan tana mai girki suci tare, sannan wajen kwanciya tasaba dajin d'umin jikinsa, da alama shima ya saba dajin d'umin jikin nata, babu fad'a tsakaninsu yanzu, komai zasuyi sunayi ne da gaskiya.

Dan bazan manta ba, kwana uku da Auransu haka RAHMA tagaya ma ABDUL itafa tana shan giya kuma wallahi yanzu ji take idan batasha ba bazata samu nutsuwa ba, ABDUL yace mata gaskiya bata kyau da  maye, zaije wajen Dadynsa ya karb'ar mata wani rubutu insha Allah idan tasha zata tsani shaye shaye.

Haka ko akayi, yaje wajen Dady ya nuna masa yana san yaba wani abokinsu wannan rubutun daya basu shida AMEER, dan Allah ya bashi dan yana san rayuwarsa ta kintsu,

Dadyn bai wani tsaya yimai wani binkice ba, haka yaje wajen malamin daya bashi nasu ABDUL d'in yasa shi rubuta mai wani, kwana uku tsakani Dadyn ya kira ABDUL d'in ya bashi rubutun, aiko ABDUL yaji dad'i, hakan, Haka yasa RAHMA a gaba ya bata tasha,

Bayan tasha da kwana biyu haka taji ta tsani shaye shaye,  wannan yasa taqara sakewa da ABDUL d'in.

 

 

 

 

 

Yau ZAINAB ta fitta daga iddarta,  sai kiran Abdul take awaya kan yazo tana san magana dashi,

Bayan yazo keb'ancewa sukayi a d'akin AMEER na gidan dan ya dawo gidan nasu da zama,

Toh baya d'akin hakan yasa ZAINAB saka ABDUL a gaba tace, "Nasan zakaji wani iri kan batun dazan gaya maka yanzu, gaskiya ABDUL ina san na koma gidan mijina, shine muka yanke shawarar nayi Auran kisan wuta, saidai bansan wanda zan Aura wanda zai cikamin Alƙawari ba, hakan yasa nayi zurfi a tunani na gane kaine zaka cika min alƙawarin, ABDUL ina san ka Aureni na tsawan wata d'aya saika sakeni na kuma d'akin mijina, amma da shara d'in ba wani abu dazai faru tsakanina dakai, na San kana san farin ciki na, dan Allah ABDUL ka kyautata min rayuwa na koma gidan mijina naji dad'in rayuwar.

 

Sake baki ABDUL yayi yana kallanta, sam y'a mace wani zubin bata da hankali, banda haka me ZAINAB take gani agun Salisu wanda yake sawa take sanshi, wallahi ya tsani Salisu tsana me tsanani, dama fata yake mata Allah ya kashe shi ta Auri wani mekyan hali ya kula da ita kulawa tahar qarshen rayuwa, duk da cewar yasan tana matuƙar san Salisun  amma sam basu dace da juna ba, wallah za taci gaba da shan wahala ne kawai a gidansa, dan bazai canja mata halinsa ba duk dad'in baki yake mata, amma taqi ganewa, yanzu idan ya gaya mata gaskiya ba jinsa zatayi ba, kuma idan yace mata bazai iya yin Auran kisan wutan ba neman wani zatayi suyi, danya santa sarai idan ta kwallafa rai kan abinda tayi niya saita cimma burinta hankalinta yake kwanciya, hmm ya zaiyi, haka shi kuma tashi qaddarar take na Auran mata amma basu cin amarci ranar farko,

 zai yarda kawai idan akayi Auran komai ma ya kwab'e qila dama shine da raban bata Baby... Yana kawowa nan a tunaninsa ya sakar mata murmushi da cewa, "La AUNTY😀, ai baki da matsala da wannan, na yarda da tunaninki.

Cikin murna ta sakar mai kiss a hannu dayimai godiya. Haka ta ficce daga d'akin yabi surarta da kallo, yana hararo cikin ita da RAHMA dawa zaifi jin daɗin Luv..

 

Haka suka shirya batun Aure, Hajjiya Kakah da baban AMEER da momy da Dady da AMEER sunyi matuƙar mamaki da ABDUL da ZAINAB suka sakasu a gaba kan suna san junansu,

 

Toya zasuyi, ita dai momy takira ABDUL tayimai fad'a kan ya hak'ura da batun Auran, dan shi yaro, zama da mata biyu ba abu bane me sauqi,  ABDUL kiss ya sakarma momyn nashi ahannu yace shifa yana san Auntynsa, kawai tayi mai addu'a komai zaizo mishi da sauqi, sannan baya san RAHMA tasani, momyn ta hararesa tace saita gaya mata, nan ya marairaice mata kan karta gaya mata shida kansa zai gaya mata,

 

 

Haka ABDUL yasaka Dadynsa a gaba kan yana san ayi musu auran cikin wannan watan da suke ciki, hmm Aure fa🤔 ya shiga tsakanin ABDUL da ZAINAB,

Yau jumma'atu babbar ranah aka d'aura Auran ZAINAB da ABDUL,🙁

 

 

Bayan ABDUL da AMEER sun dawo daga wajen d'aurin Auren kallan RAHMA ABDUL yayi yace da ita, "my dear yaufa na qara zama ango.....

Dama akwai kofin gilashi a hannun RAHMAN zata bama AMEER ruwa aiko saita sake kofin a qasa ta dafe kirji tace, "Ango. Ango wane iri, 😳

 

Haka kawai ABDUL ya tsinci kansa da faɗuwar gaba, amma haka ya d'aure cikin tsoro yahau ce mata,  "Auntyna ZAINAB na Aura yau, anjima ma za'a kawota nan gidan, bakiga wasu mata sunzo mata jeran kitchen ba, me yasa naga kin yada cup, wani abu ne...

Ai bai ida zancensa da numfashi ba, nan ta rushe da kuka tayi bedroom nata da gudu tahau tattara kayanta..

 

ABDUL ya kalli AMEER daci gaba da cewa, Kaga Wata sabuwa, 😨

AMEER ya tashi yaje ya saka takalminsa yana cewa, "Hmm yanzu zaka fara fuskantar wata rayuwa, kai kasan mata biyu kuwa🤔.

AMEER na fad'in mishi hakan ya ficce daga falan yana tuno tashin hankalin daya hango a fuskar RAHMAN.

 

 

ABDUL ko dafe kansa yayi, shi wallahi sai yanzu ya tuna yayima RAHMA illah, ya gama jefa mata sanshi da qaunarsa, kuma fa gaskiya shima fa yana santa...😌

 

Ahankali jiki a sanyaye ya  bita bedroom d'in nata, nan yaga tana kuka Sosai tana had'a kayanta,

Cikin mutuwar jik yace, "Banyi tunanin zakiji wani abu aranki ba....

 

Da wata muguwar harara ta kallesa wanda santa gabansa ya fad'i🤣, tace, "Kacuci rayuwata ABDUL, kayi min wayo ka jefamin sanka da qaunarka cikin zuciyata, sannan ka zaga bayan fage kai da munafukar Auntyn taka ka Aureta dan kagama raina min hankali ko,

 Toh wallahi baka isa ba, saika sakeni dan bazan zauna da kishiya ba, kuma ko kasake nin yanzu ko karka sakenin yanzu ba abinda zai hanani tafiya garinmu jos cikin gidammu.

 

ABDUL ya sosa qeya yace, "Dan Allah kiyi hak'uri, kiyi hak'uri mu gina wata sabuwar rayuwa, Wallahi ina sanki,  yanzu na tuna idan bake bazan iya rayuwa ba....

"Da gaske.. Ta katse shi da faɗin hakan, ya d'aga mata kai, cikin qarin jin haushinsa taci gaba da cewa, nima idan babu kai bazan iya rayuwa ba, amma na gwammace nabar rayuwar dana rayu da kishiya..

Tana faɗin hakan ta bangaje shi ta wucce da d'an akwatinta, tana cigaba da cewa WALLAHI SAI KA SAKETA ZAN RAYU DAKAI....

 

ABDUL yana jin fatanta daga gidan, nan zuciyarsa tafara hango masa fuskar ZAINAB data RAHMAN, "Tabd'ijan... Shine abun dayace a bayyane, dan gaskiya bazai iya sakin ZAINAB ba, dan dama ya dad'e yana jin wani yanayi ajikinsa idan yana tare da ita, babu makawa wannan shine yanayin, itama yana santa yana san rayuwa da ita, ammafa gaskiya bazai iya rayuwa babu RAHMA ba, dan yana sane da saban da yayi da, jikinta, murmushinta, shagwaɓarta, maganarta,

"Common my Baby na shirya tsaftatacciyar  rayuwar aure dake, babu abinda zai kaiki garin jos ba tare da cikina ba?

ABDUL ya qara fad'in hakan a bayyane da ficcewa daga gidan da gudu dan zuwa tarota.🤥

 

 

Muje zuwa y'an hannuna, nidai rahama na shirya bama mutane haske kan iya zama da kishiya😌 badan nasan komai ba, Saidan nasan abinda nasani kad'an👌🏻 haka👈🏻...

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.*🙆🏻*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆🏼*.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`•🤱🏻

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 16

 

*Nayi kuskuran rubuta suna gareki UMMU BASHEER wajen sadaukarwa a page 15, ina miki fatan alkairi aduk inda kike y'ar uwar azziqi, nagode da kawomin ziyara Allah ya saka da alkairi, haka y'ar uwa RAHEENAT MAMOUDOU, ina tayaki addu'a kan Allah yaba mumcy lafiya ya kare mana ita ya azultata da lafiya me d'orewa; ga dukkan musulmai gabaki d'aya*

 

 

 

 

Dake unguwar manya ce, sam bataci karo da kowa ba, haka layin yake shuru ba irin hargowar nan irinta unguwar talakawa, haka take tafe tana jan akwatinta tana kuka sosai.

Ahaka ya cimmata, yasha gabanta yana ce mata, "Dan Allah my Baby ki saurareni, kizo muje gida kiji abinda zan gaya miki.

Nan ta kallesa idanta jajir tace, "Bazan saurarekan ba, Sannan bazan koma gidan ba, kafita daga harkata tunkan nayi maka abinda baka tab'a tunani ba...

Bai bari takai qarshen zancen nata da numfashi ba, yayi qoqarin rabata da akwatin nata, nanko fad'a ya kaure tana ja yana ja...

Yace "a matsayina na mijinki ban yarje miki ki qara koda taku d'ayane daga inda kike dan tafiya gidanku ba.

Tace "koka yarje kokar ka yarje saina tafi gidammu kaje can ka rayu da Auntynka....

Sam basuyi Aune ba sai ganin momy sukayi ta tsaida motarta a gabansu, dama gidan nasu take san zuwa danta lallashi RAHMA kan Auran ABDUL d'in, bata san tatada hankalinta shiyasa tataso yanzu tunkan a kawo ZAINAB d'in...

Kallansu tayi da mamaki tace "Ha'a, me yake faruwa daku kuke jani in jaka akan titi.

Kallanta sukayi tare da sakin akwatin. Sai tahau qare musu kallo tana nazartarsu, RAHEEMAT ina zaki da akwati haka a daidai wannan lokacin, gashi Kuma fuskarki a jeme da alama kuka kikayi koma kina kan yin kukan. Momy ta qara yin magana a karo na biyu tare da bayyanar da mamaki akan fuskarta.

Nan RAHMA taturo baki gaba, ta qara fashewa da kuka tana cema momyn, "Garinmu zan tafi, wallahi bazan iya zama da kishiya ba, ace Aurena ko shekara banyi ba yaje yayo min kishiya, kuma ma yarasa wacce zai Auromin sai Auntynsa ZAINAB wacce yake matuqar so, wacce duk sanda zamu zauna dashi dan hira saiya sako min hirarta da yanda yake santa, gaskiya ni takaddata zai bani bazan zauna dashi ba. Ta qarashe zancen nata da qara volume d'in kukanta.

 

Momy ta kama baki, sam batayi zatan RAHMAN zatayi kishi haka ba, gaskiya tayi mamakinta matuqa, kuma ta qara jin qaunarta aranta dan ance baka da masoyi sai me san d'anka.

Haka tamaida kallanta ga ABDUL taga duk yayi wani iri, nan tausayinsa ya kamata, wato tunkan ma akawo ZAINAB d'in ya fara fuskantar wata rayuwa...

 

"Momy kice wani abu mana.. ABDUL ya faɗi hakan cikin wani hali yana me kallan momyn..

 

"Maza ku wucce muje gidan naku, momyn tace dasu hakan tana me jan motarta zuwa gidan nasu.

 

RAHMA takallesa ganin yayi saurin jan akwatin nata tace, "Wallahi zanyi maganinka ne idan har kanace sai naci gaba da rayuwa dakai"

   "Bakomai my Baby idan har zan dinga ganin kyakkyawar fuskarki ako da yaushe bazan damu da wata rayuwa dazan fuskanta daga gareki ba.

 Galla masa harara tayi dayin kwafa ta wucceshi yabi bayanta da kallo, komai nata abin burgewa ne kamar dai yanda Auntyn tasa ZAINAB take.

"Kai zansha fara da wannan yarinyar fah🤔" ya fad'i hakan a bayyane..

 

Anan falan RAHMAN suke zaune su ukun, momy ta kalli RAHMA tace, "ƳAta gayamin miye matsalarki.

Cikin shagwaɓa tace, "Ni momy a yanzu matsalata d'ayace, shine yabani takaddata, bazan iya rayuwa dashi da Auntynsa ZAINAB ba, momy kasheni ABDUL yake sanyi tunkan kwana na su qare, banda haka ki dubafa momy, ban shekara cikin gidansa ba yayomin kishiya, kuma bai tashi gayamin ba sai ranar daza'a kawota matsayin matarsa, Sannan ya rasa wacce zai Auran sai wacce kullum take cikin bakinsa, sannan yace bazance yaban takaddar saki na ba.

Momy tayi murmushi da kallan ABDUL tace, "To kai kaji lefinka, sam baka kyauta ba, kuma mune manyan masu lefi gareta da muka yarje maka yi mata kishiya bayan bata wani dad'e a gidanka ba, Sannan baka tashi gaya mata ba sai randa za'a kawo mata kishiyar, dan haka bata takaddar sakinta...

Abdul yayi saurin kallan momyn tashi, yace, "Nasan nayi lefi momy, dan Allah ayafe min, ina san matata ina san rayuwa da ita...

"Ni yanzu bana sanka, tunda da kana sona da bakayo min kishiyar ba.. RAHMA ta katseshi da faɗin hakan a fusace kamar zata sheqa masa mari.

 Shidai sunkuyar dakai yayi, yadai san ko sama da qasa zata had'e bazai bada takaddar sakin nata ba.

 

Momy ta girgiza kai, gaskiya RAHMA nada kishi, wannan idan batayi a hankali ba ZAINAB zata garata idan taso mugunta.

 

Ahankali momy ta rungumota jikinta tace, kwantar da hankalinki y'ata, badai sakinki kikeso yayi ba, d'aga mata kai tayi, sai momyn taci gaba da cewa, Yanzu zansashi ya sakeki amma sai kin ban amsa biyu kacal.

Ahankali RAHMA tace "Ina jinki momy, wata amsa ce.

 

"Yauwa my daughter, amsa ta farko da zaki ban itace, yanzu idan ya sake ki me zaki gayama iyayenki da jama'ar gari.

"Momy zan gaya musu ni nace ya sakeni dan bazan iya zama da kishiyar da Yayi min ba,

Momy tace "Gud.. Tambaya ta biyu, idan sukace yanzu akan kishiya kika kashe auranki me kuma zaki iya ce musu.

"Zance muku Eh, dan ban shirya zama da ita cikin lokaci qanqani haka ba.

  "Gud my daughter, idan sukace miki meyasa kikace haka me zakice musu.

  Shuru RAHMA tayi, can tace, "Gaskiya babu abinda zan iya ce musu.

   "Kinga kenan zasu miki kallan wiwiya, wacce take da mugun kishi, Sannan wacce kishiya tafi qarfinta, dan kawai mijinki ya Auro miki ita, sai kika ficce daga gidan kika bar mata.

Toh a matsayina na mahaifiyar ABDUL ina baki shawara daki nutsu ki zauna a d'akin mijinki lafiya, ki kama Allah da Manzansa, kima mijinki ladabi da biyayya, kisama ranki har yanzu kina rayuwa ne da mijinki ba tare da wata kishiya ba, idan har kina san ayi miki kallan ishashshiyar mace kenan, wacce tafi qarfin kishiyarta, toh dole  sai kinyi hak'uri my daughter, kin sama zuciyarki dangana, Sannan ina san kibama ABDUL farin ciki, danna yarda da qaunar da yake miki, ina sanki dashi, ina san nayuwa dake matsayin surukata, dan Allah dan annabi ki goge tunanin barin gidan ABDUL, wallahi my daughter kun dace da juna ke dashi, ina rokwan wannan alfarmar daki bar wannan batu ya shige kinji my daughter,

 

Shuru RAHMA tayi tana tunanin zancikan momyn, tabbas idan tatafi za'ace ZAINAB d'in tafi qarfinta, gwara ta zauna a d'akinta ta nuna ma ZAINAB d'in bata kai matsayin daza tatafi gidansu saboda ita ba...

Ahankali tace da momyn, "Toh momy zanyi yanda kikace insha Allah,

"Yauwa y'ata ko kefa, Sannan daga yanzu idan wani abu ya faru tsakaninku ina san kifara zuwa ki gayamin ko kikarani awaya kafin kiyi tunanin tafiya garin naku kinji.

"Toh momy zanyi yanda kikace.

"Madallah, Yanzu bari na koma gida nasan ana can ana jirana. Momy ta faɗi hakan tana me tashi da kallan ABDUL taci gaba da cewa, Kazo gida ka sameni duk dare.

Toh ABDUL yace mata da tashi danyi mata rakiya...

 

Sanda yaga k'ulewar motar tata daga layin nasu sannan ya dawo gidan, baiga RAHMA a falan ba sai acan bedroom d'inta tana maida kayanta dirowa, yaje ya rungumeta ta baya nan ko tazare kanta daga jikinsa ta waro masa fararan idanta tace, "Kakama kanka malam, kar kaga dan Momy ta hanani tafiya kayi tunanin komai ya wucce ne, aa komai bai wucce ba dan Wallahi bazaka min kishiya abansa ba, dan haka daga yau karka qara shiga harkata, dan idan kaqara shiga zanyi maka abinda baka tuna....

Bai barata ta qara ba ya jawota gabaki d'aya jikinsa ya matse mata makin maganar wajen aika mata da wani shock kiss, Wanda ya kashe mata jiki lokaci d'aya.

Haka tadinga mai mutsul mutsul bai barta ba sanda ya tabbatar ya gama kashe mata jiki tsaf...

Sannan ya zaunar da ita gefan gado ya durqusa a gabanta yace "Dagaske nake, bazan iya rayuwa babu ke ba, bansan yaushe ne, wata rana ne, awane lokaci ne, na fara qaunarki ba, dan Allah me sona kiyi min afuwa ki yafemin bazan qara miki kishiya ba har qarshen rayuwa.

Ya fad'i hakan yana me sake mata hannu da kama kunnuwansa alamar ban hak'uri.

Kawar da fuskarta tayi hawaye ya zubo mata, cikin shagwaɓa tace.  "Haka kawai naji zuciya na magana akanka, dana saurari maganar tata dakyau sai nagane zaurance take min kan ba wani namji dazan so sama dakai aduk fad'in duniya nan, shine na shirya zan gaya maka dan mu sake rayuwa, sai kawai kazo min da batun kayi min kishiya.. Nidai bana santa bana qaunarta bana san Auntyn nan taka kwata kwata..... Ta qarashe maganar da fashewa da kuka sosai..

Rungumarta yayi yahau rarrashinta yana cewa, "ni naki ne ke kad'ai my Baby, dan kece matar ABDUL ta farko, sam bai isa canja hakan ba, zan baki farin ciki Babyna, dan na tabbatar Aunty ZAINAB bazata tab'a shiga soyayyata Dake ba, common my Baby kwantar da hakanlinki dan MASEEFAR SONKi fah, bazan tab'a fifita wata mace akanki ba.

Yana zuwa nan a zancensa takallesa tace "Ka tabbatar, d'aga mata kai yayi, alamar tabbatarwa, nan ta shige masa sosai fiye da yanda ya rungumeta har tana sakin ajiyar zuciya...

 

Sun d'auki lokaci ahaka suna masu jin ɗumin juna, suna niyar raba jikinsu dana junan ne suka jiyo masu kawo amarya Suna kwad'a sallama, ABDUL ya raba jikinsa da nata ya sakar mata kiss a kumatu yace, "Baby tashi jiki dasu, kinsan yanzu kin zama babba, an kawo miki ita ne dan a danqa miki amanarta, dan Allah my Baby kisaki ranki karsu gane kinyi kuka kinji.

Murmushin yaqe tasakar mai, ganin hakan saiya ficce ta cikin d'akin nata ta wata kofa da zata sadashi da shashinsa kai tsaye.

Haka RAHMA tasaka wani hijabinta ta fitto falan tana gaishesu,

Ba wasu bane y'an gidansu ZAINAB d'in ne, haka suka musu nasiha kana sukace duk da ZAINAB ta girmi RAHMA dole taba RAHMAN girmanta na matsayinta na uwargidanta, saidai kuma kar hakan yaba RAHMA damar yimata abinda taga dama.

Haka dai suka gama yimusu nasihar data dace kana sukaje suka kai ZAINAB d'in d'akinta suka gyara mata kitchen kamar dai yanda akama RAHMA, dan itama Dady ya sawwake mata komai sai kayan kitchen d'in...

 Haka suka watse suka bar ZAINAB itama a gidan, kamar yanda dangin RAHMA suma suka watse suka barta a gidan...

 

ABDUL nufan shi shashinsa wata qaramar wayarsa ya d'auka ya ficce daga gidan dan zuwa wajen AMEER su d'an tattauna..

 

Ya samesa a gidansu d'akin ABDUL d'in nada yana kwance da alama yana huta gajiya ne.

Yana ko ganinsa ya tashi yana cewa, "D'an uwa ya kaji da mutuniyar taka.

 

Yace "Hmm, dake akwai so, ban wani sha wahala Sosai ba, dan Allah AMEER ya ake zama da mata biyu, wallahi bansan ya abun yake ba, kaga soyayyar ma kawai ina daurewa ne ba iyata nayi ba.

Dariya sosai AMEER yamai yace "baka san yanda akeyi ba kayi, kawai malam kashare ka matse kazama babban mutum, karka fifita kowa a cikinsu, komai zakayi kayi dan Allah, hakan zaisa ka zauna lafiya dasu,

Kaga mubar batunka mu kama nawa, d'azu fitowata daga gidanka maman UMMAKATI ta kirani tana gayamin na turo iyayena kan batun Auran namu da ita UMMAKATIN idan soyayyar tamu ta gaskiya ce..

Da sauri ABDUL ya waro ido, cikin murna yace, "Wow d'an uwa na tayaka murna, na tayaka murna sosai fah, yanzu ka gayama su Baba ne..

"Eh, na gaya musu dawowata yanzu, har suna min tsiyar wai kodan naga an qara baka mata ne yau shine na kira maman UMMAKATIN, nan nace musu wallahi ita ta kirani ni ban kirata ba, sukace to Allah ya kaimu gobe zasu, anan na roqesu kan asaka musu rana dan Wallahi Auran nake so da sauri🙈.

ABDUL yayi murmushi yace, "Hakan yayi ai, gaskiya nayi murna sosai dajin hakan, kaima zaka zama ango kasha ni'imar Aure kenan.

Murmushi AMEER yamai da cewa, "Yanzu dai zaka d'au hutun office ko,

"Kai dai bari, ina san naji Babyna dakyau yau, ga Aunty zainab, kaidai kamin addu'a kawai.😃

AMEER ya tintsire da dariya yace, "na kasa yarda dacewarka na wai har yanzu babu abin daya shiga tsakaninka da RAHMA.

"Ka yarda AMEER, wallahi bazan maka qarya ba, inda naji abinda kake ji na tababatar dole kyallin amarci ya bayyana gareni, kuma kasan da d'okina zan gaya maka danna huta da gorinka.

"Ok... Toh Allah yaji qan RAHMA yau, amma naji baqin cikin yanda za'ama Auntyna PDP.

ABDUL yayi murmushi dan bai gayama AMEER Auran isan wuta ne tsakaninsu shi da ZAINAB d'in kamar yanda da yarda da Hakan ba.

Dan haka ce masa yayi "Yauwa, ina san na gaya maka ina san a satomin Salisu yanzu, zanyi mishi  wasu tambayoyine.

AMEER yace "har naji gabana ya fad'i, ince yau kuma ka dawo da d'abi'un namu ne😂.

ABDUL yayi murmushi yace, "Ko kad'an, kawai dai ina san nayi mishi tambayayoyin ne.

"Ok, yanzu saimu nemi su Abba tab'are, nasan kan kabar nan sun cika maka aiki.

Haka ko sukayi suka kira abokan nasu masu d'auko musu mutanan ada, suka gaya musu udirinsu, nan ko cikin giramamawa suka amsa masu..

 

Haka ko ABDUL baibar d'akin AMEER d'in ba suka kirasa sukace sun cika aiki,

Da sauri ko Abdul yayi gidansu ta kofar baya ya shige d'akin da yake da tabbacin Salisun yana ciki, ya samesa zaune kan wannan dai kujerar sunyi mai  d'aurin nasu da suka saba, ABDUL ya kunce shi da yayyafa mai ruwa, bayan ya dawo hayyacinsa jan wata kujera ABDUL yayi ya zauna a gafansa suna masu kallan juna...

 

"ABDUL me kuma ya faru, me zaka min bayan ka canja ayanzu baka aikata wannan harkar. Salisu ya faɗi hakan cikin wani hali.

Jan numfashi ABDUL yayi da cewa, "ba abinda zan maka, kawai ina so ne yanzu ka fad'i abinda zan gaya maka a record d'in wayana,

Salisu ban Auri ZAINAB danna saketa takoma gidanka ba, na Aureta ne dan nayi tsaftataccen zaman Aure da ita, dan ina san farin cikinta, idan har na saketa ta koma gidanka bazaka canja mata kamar yanda kake mata dad'in baki ayanzu ba, wallahi baka san ZAINAB Salisu, baka san rayuwar aure da ita yanda ya dace, Nine na gane hakan, hakan yasa nayi maka mummunar tsana, dan ita sanka take gabaki d'aya, kuma kafi kowa sanin bata iya SO ba, idan zataso abu sanshi take gabaki d'aya kuma da gaske mezaisa baza ka mata adalci kabarta tasamu wanda ya dace da ita ba, sai kawai ka lallab'o kana b'ata mata tunani dan tsabar baqin hali da mugunta irin taka.

     Yanzu dai zan kunna record nawa, ina san kace baka santa baka qaunarta dama yaudararta kawai kakeyi, dan kana da wacce kake SO kake qauna watoh Y'ar uwarka, amma ita san jikinta kawai kakeyi shiyasa kake san cigaba da rayuwa da ita, kuma zakayi maganar ne kamar kana gayama wani abokinka...

 

Cikin baqin ciki da b'acin rai Salisu yace, "ABDUL mumafa TANTIRANCIN nan mun iyashi, banga dalilin da zaisa na fad'i hakan bayan nasan qarya ne ba, ina san ZAINAB ina qaunarta fiye da tunanin me tunani, akan wane dalili zaka saka min magana a baki kace saina furta. Gaskiya bazai yuhu ba, dan ina san matata ina kuma san rayuwa da ita, Sannan na canja halina ina kyautata zatan zataji dad'in rayuwar Aure dani ayanzu dan ban tab'a jin qaunarta kamar wannan lokacin ba,..

 

"Yayi, gaskiya taurin kanka zai kaika ya baroka, ABDUL ya katse shi da faɗin hakan yana me cibaga da cewa, Ayanzu dai ZAINAB matata ce? ina santa ina qaunarta fiye da yanda kake zato, zanyi rayuwa da ita, rayuwar da har tamutu bazatayi Allah wadai da ita ba, bayan tsanarka da nakeji azuciyata ayanzu harda kishinta cikin raina, wallahi idan kayi kuskuran san rabani da ita ba abinda zai hanani kasheka, kuma yanzu zan kunna record kayi abinda nace maka, tunkan na illartar da rayuwarka....

ABDUL na fad'in hakan ya kunna wajan recording a wayarsa ya matsar da wayar gaban Salisun yayi masa alama da ido kan yafara magana.

 

Aiko cikin baqin ciki dajin tsanar ABDUL d'in aransa ya fara cewa, "Aliyu nifa basan ZAINAB nake yi ba, kawai ina san jikinta ne, yaudararta kawai nakeyi, y'ar uwata nake so nake san Aura in gida rayuwa me inganci da ita...

 Yana zuwa nan a zancensa ABDUL ya d'auke wayarsa da seven d'in recording d'in..

Sai Salisu ya fashe da kuka, wallahi yana san matarsa matuqa da gaske, ZAINAB tayi arayuwa.

Sam ABDUL baibi takan kukansa ba ya make masa qeya nan take ko ya sume, Abdul yayi murmushin mugunta ya kira waƴanda suka kawo mai shi yace su fidda shi can kan hanya ko sukai shi gidansu.

Toh sukace mai

Sannan Abdul d'in ya koma wajen AMEER zuciyarsa cike da farin ciki..

 

 

 

Sai kusan qarfe tara ABDUL da AMEER sukazo gidan,  shashin RAHMA sukayi direct sai dai sunga shashin nata akulle da alama tayi bacci ne dan sunga wutan shashin nata duk a kashe. ABDUL yacema AMEER su ajiyema RAHMAN tata kazar a falansa da safe tayi amfani da ita.

 

Zainab na kwance kan kujera da wani littafi a hannunta tana karantawa waice *YA FARU AKAN KAI NAH*, da alama Rahma nalele su biyu kad'ai tabawa karantawa, wato ita da NUFAISAT marigajiya mata a gidan ADAMS LEEKITAN ZUCHIYA, Dan AMEER yaga sabo ne ajerin littattafanta sam baisan da zaman wannan ba. Kasancewar shi ma'abucin bibiyar littattafanta...

 

 

"Aunty karatu kikeyi ne a daidai wannan lokacin kamar ba amarya ba.

ZAINAB ta harari AMEER me wannan farucin tace, "Eh, karatu nake, ya zanyi da marubuciyar tarigada ta kalle tunani, anya ko yau zan iya bacci batare dana karance shi tsaf ba.

 

Kan AMEER ya bata amsa sai ABDUL ya kwace littafin daga hannun nata yana fad'in, "Gaskiya Aunty ina san lafiyarki, ya dace yau muganki kan gado lullub'e cikin bargo dan huta gajiyar biki.

"ABDUL littafin ya shiga raina ne dan Allah kabani na qarasa.

"Tab, nifa yau ango ne, kawai ki hak'ura sai Allah ya kaimu gobe.

Kan tayi magana AMEER yace, "Aunty ga wannan kici zai miki dad'i sosai, ya fad'i hakan da ajiye mata ledar kazarta guda da babbar madara, kana ya nufi haryar fitta yana cigaba da cewa,  Zoka kulle gidan ABDUL bazan zauna hirar ba dan kasan  momy na nema na.

Toh ABDUL yace mai suka ficce daga falan, sai ZAINAB tabi ledar da kallo..

ABDUL na dawowa ya ganta a kofar shashinta ta nad'e hannayenta tana cemai, "Kasan bawai Auran gaskiya mukayi ba, meyasa kuka siyamin kaza kuma har kana cewa kai ango ne yau.

Murmushi ABDUL yayi mata da faɗin, "Aunty kenan, idan nacema AMEER karya siya kazar zai zargi wani abu, wannan yasa na barsa ya siya, Sannan ai ba qarya na fad'i ba, ni angowa ne ko kina da damar canja hakan ne.🤷🏻

Hararar tayi, saiya jata zuwa bedroom nata, sannan ya zaunar da ita gefan gado ya kama hannuwanta daci gaba da cewa, Aunty ki kwanta kiyi bacci, baccin nutsuwa danya harfar miki da kwanciyar hankali, dan bana san kifara tsorata da batun shirinmu dake tun yanzu.

Gyaɗa masa kai tayi da cewa, "Babu tsoro cikin zuciyata ABDUL, dan nasan bazaka tab'a bani kunya ba, maza kaje ka duba RAHMA dan naga kamar tana cikin wani hali d'azu da aka had'amu danyi mana nasiha.

   Kiss ya sakar mata a hannun nata da tashi ya ficce daga d'akin,

Sai tabi bayansa da kallo..

 

Direct shashinsa ya nufa sanda yayi wanka yayi sallah raka'a biyu kan Allah ya had'a masa kansu Sannan ya kawo masa sauqi kan dukkan lamuransa Sannan ya koma shashin ZAINAB d'in, lokacin tana cikin bargo bacci nasan d'aukarta, ahankali ya zauna kusa da ita yad'an yaye mata bargon suka had'a ido, nan sukaji wani iri haka a zuciyarsu, ganin tunda suke basu tab'a ganin juna cikin kayan bacci ba

Ahankali ABDUL yake ce mata "Aunty ina neman wata alfarma agunki, dan Allah zan kwana d'akin RAHMA dan batajin dad'i sosai, ina fatan zaki yarje min da kore mugun tunani daga zuciya..

Tashi ZAINAB tayi da qara tsaida idanta akansa, tace "Har ka manta da cewa Auran kisan wuta ne tsakaninmu, me zaisa ka tsaya b'ata lokacinka wajen tambayata dan zaka kwana a d'akin RAHMA,

"Duk da haka Aunty da rashin dacewa idan ban tambayeki ba, kawai dai yanzu inaso naji kin amince min koko aa.

"Na amince maka ABDUL daga nan har zuwa ranar  da alƙawarinmu zai cika kaban takaddar saki nah..

Kama hannunta yayi cikin farin ciki yace, "Aunty bayan kyau da kike min, har muryarki dad'i take min, dan Allah zan iya yimiki kiss a kumatu, dan Allah karkice min aa👏🏻

Murmushi tamai da d'aga masa kai, haka yakai bakinsa ga kumatunta ya manna mata me sanyi kana ya saki hannunta da tashi har yakai k'ofar fitta, sai tayi saurin tsayar dashi wajen cewa, "Yanzu kuma haka kawai naji wani iri araina, gaskiya da ciwo ace ranar farkon auranka mijinka yaje ya kwana da kishiyarka, koda yake bai dace ma naji wani abu ba, dan idan nabari ya bayyana ma' sai a zargeni, ta qarashe furucin da murmushi..

Junyowa yayi da cewa, "Shiyasa nace ki kauda mugun tunani daga zuciya.

"Sai da safe ABDUL kajamin k'ofa.

"Yauwa Aunty na tuna, ga wayata ki shiga wani folder MRE, zakiga wani audio me suna Salisu, wani sak'one wani ya turan d'azu, zakiji dad'in hirar Sosai, gobe kya bani wayar.

Cikin murmushi ZAINAB ta karb'a tana cewa, "Watoh danya kasance yana da sunan sahibina shine harka yanke kan zanji dad'insa sosai ko,

Murmushin yaqe ABDUL yayi mata da ficcewa daga room d'in yaja mata k'ofar yana me murmushin mugunta..

 

 

Ta kofar cikin falansa yasamu ya shiga shashin RAHMA, tana can kwance kan gadanta cikin bargo idanta biyu da alama ta kasa yin baccin ne.

  Suna had'a ido ta wani galla mai harara, saiya sakar mata murmushi, babu b'ata lokaci ya haye gadan ya shige cikin bargon nata da rungumota yana cewa, "Nazo tayaki baccin ne, tunda yau kin sallamani, sam bazan iya bacci babu ke a tare dani ba,

Daqarfin tsiya RAHMA ta kwace kanta tatashi da kunna ainihin wutar d'akin me haske tana me waro mai ido cikin mamaki tace, "Ina toh kabaro Aunty Amarya.

Abdul ya tab'e baki irin bai wani damun nan ba yace, "Na barota a part d'inta mata, Sannan na gaya mata ni yau a d'akin uwargida zan kwana, dake kinsan bata da matsala haka tace min ba damuwa...

"Ƙarya ne... RAHMA ta katse shi da faɗin hakan tana me harararsa, kana taci gaba da cewa, ba kishiyar da zatace ta hak'ura da kwanan farkwan Auranta mijinta yaje ga kishiyarata, kaga bana so, karka jamin wani abu, dan Allah katashi kaje d'akin amaryarka...

"Wallahi ba inda zani, musamman yanda kika qaryatani, ni ba surutu bane ya kawo ni, nazo ne mukwanta muyi bacci bayan na karb'i hakk'ina daya rataya akanki...

Qara waro ido RAHMA tayi, musamman yanda taga yayi wani kicin kicin da fuska

Ahankali tace "ABDUL dan Allah ka rufamin asiri ka tashi ka koma shashinta, dan babu kyau haka, bana san katashi cikin mutanan nan da suke tashi da shanyayyun jiki, dan rashin adalci da basuma matansu, dan Allah badan niba ka tashi kaje gareta  kaji mijina, abin alfahari na. Ta qarashe zancen nata da shagwaɓe mishi.

 

Murmushi yayi da zubama rigar jikinta ido, tayi mata kyau sosai, riga da wando ne na bacci tasaka, amma sun manne mata jiki Sosai,

 

 shima ahankalin yace mata, "My Baby lallashina kike yi.

D'aga masa kai dayi da cewa, "Eh mana, tunda na lura sheɗan nasan buga maka ganga.

Tashin shima yayi da matsawa kusa da ita sosai ya rungumeta suna jin numfashin juna yace da ita, "Wallahi Baby yau saikin ban hakk'ina, gwara ma ki saki jikinki na tafiyar dake a hankali.

 

Tsoro ne ya kama RAHMA, nan hawaye ya rubo mata, tace "ABDUL abinda kake shirin aikatawa ba qaramin abu bane.

Lashe mata hawayen yahauyi da aika nata da wani shu'umin kiss a wiya, nan ta rumtse idanta jin yana san rabata da rigar jikinta...

Da sauri taci gaba da cewa, Ina jin tsoro.

Hmm ABDUL bai kulata ba ganin na fulaninta sun rikita shi kwarar da gaske.

 

Gaskiya ABDUL ya nunama RAHMA ƘAUNA awannan dare,

Ya nuna mata SO kamar bazai barta darai ba, dan ji yake kamar ya cinyeta d'anye.

 

Taci kukanta ta more dan yayi mata abinda tun take arayuwarta bata tab'a jin irinsa ba.

 

Sosai yayi mamakin lamarin🤔, Wai ya abin yake, yafa samu RAHMA a cikakkiyar mace😀, sam bata tab'a sanin wani d'a namiji ba.

Kai gaskiya ya godema Allah daya kare mai ita daga fad'awa takwan zina..

Sosai fa ya qara santa, ya qara qaunarta, wannan dare ba abunda ya iya yi sai tattalinta, tana mai masifa yana manne mata,🤣 ganinta shi mugu ne, dan ba irin hak'urin da bata bashi ba amma yaqi barinta, sanda ya sumar da ita Sannan hankalinsa ya kwanta,

Shidai yana jinta tana Allah ya saka mata yaqi kula zancikan nata, daqer da sid'in goshi yasamu ta yarda ya tayata gasa jikinta har tayi wankan tsarki ya canja musu zalin gadan suka koma gadan,

Sanda ya tabbatar bacci yayi awan gaba da ita Sannan ya jawota jikinsa yana qarajin qaunarta aransa.

 

 

Asuba ta gari Rahman-Abdul... Da baccin nutsuwa. Zainab-Abdul da baccin tashin hankali😊

 

 

 

 

Rahma nalele nagaida y'an hannunta,🏻

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.*🙆🏻*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆🏼*.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`•🤱🏻

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 17

 

 

Itako ZAINAB lokacin dataji abinda Salisu ya fad'i akanta ji tayi kamar zata mutu dan baqin ciki, haka tayi kuka tayi kuka ta godema Allah, sam takasa samun nutsuwa, hakan yasa tayo alwala tayi lafula raka'a biyu ta roki Allah ya saka mata yaudararta da Salisun yayi, haka taji a duniya ba Wanda ta tsana sai shi,

Bacci dai haka ya d'auke sama sama ana ko kiran sallar asubayi tatashi...

Lokacin yayi daidai da tashin ABDUL ma,

Sanda ya mannama RAHMA kiss kana ya tashi yayi shashinsa.

Bayan yayi alwala canja kaya yayi ya dawo shashin RAHMAN ya hau ja mata hanci ahankali ahankali, aiko nanta bud'e mai manyan idan nata, yace "My baby lokacin sallah yayi zaki iya zuwa toilet kona kaiki, harararsa tayi da miqewa tana qoqarin tashi taji zafi a gabanta, nan tace "wash!.

Da sauri ya d'ane gadan yana tambayata lafiya.

Cikin kuka tace, "Ba gabana ne yake min zafi ba,

Yana jin hakan yace, Ayya.. am so sowie my baby, bazan sake yi miki irin hakan ba kinji, shuru tamai... Jin hakan sai yayi murmushi da sunkutarta sai toilet

 

Daya fitto shashin ZAINAB ya nufa, tun daga nesa ya gane tatashi, dan haka juyawa yayi zuwa waje dan tafiya masallaci.

 

Qarfe bakwai ya dawo gidan direct shashinsa ya nufa, ba wani b'ata lokaci ya shiga wanka ya fito ya shirya kansa, nan ko shigar tasa tayi mai kyau tamkar Forean Yaro, ABDUL yana san saka suit, shigar tana birgesa Sosai, Sannan tana dacewa dashi, hakan yasa yake nace ma wankan.

 

Ya san yau ba wani batun breakfast gun mutuniyar tasa, dan haka bai wani damu ba dayaga dining d'in babu komai.

 A shashinta can ya ganota a bedroom tana aikin kwalliya,

    Yace "Ko baki tsaya b'atama kan lokaci wajen kwalliya ba, my Baby kyau kike dashi,  shuru RAHMA tamai, ganin hakan saiya qaraso gareta ya d'an duqa ya rungumeta da bata kiss a wiya yaci gaba da cewa, toh fushin dani na miye, wallahi ko kimin kyakkyawan murmushinki kona qara maimaita miki daran namu na jiya yanzu.....

Da sauri RAHMA ta waro idanta da kallansa ta jikin madubin tace, "Tab, anya kana da imani kuwa.

"A dai kan sanki bana dashi, kawai kiyimin kafin kiga aiki da cikawa.

"Haushinka nake ji, musamman idan natuna irin tarin rokwanka dana dingayi awannan lokacin, amma kayi murus dani kamar babu qaunata ko kad'an cikin ranka.

"Bamfa tab'a aikatawa ba Baby, kinga ko dole nashiga wani yanayi na rikicewa nakasa sauraran rokwanki, musamman idan nayi duba da yanda kike da dad'i abin kamar karya qare......

Saurin rufe idanta🙈 RAHMA tayi dan taji matuƙar kunyar zancen nasa.

  Kimin dariya Baby, dan Wallahi da gaske nake idan kikaqi min bazan barki haka ayanzu ba.. Ya  fad'i hakan yana me zare hannunta daga fuskar tata, nan ko ta kallesa tacikin Mirro d'in ta sakar mai murmushi tare da manna masa kiss a hannu tace, "Na qara sanka mijina, amma dan Allah ka iya dani wajen taraiyata da Auntyn ka, dan nasan baqamin kishi zanyi ba.

"Karki damu, zanyi iya qoqari wajen kiyayewa,

"Madallah, kayi hak'uri yau banda lafiyar dazan iya had'a maka wani abu dan kaci.

"Karki damu, ai nine naja ciwan, zan duba Aunty zainab ba mamaki ko ta iya yin wani abu, sannan kiyi sauri ki shirya ki sameni a falona, zan d'an muku nasiha, bayan  fitata kuma, zan turo miki Aunty Salma ta duba lafiyarki kinji".  "Toh ba damuwa.

Haka ya qara sakar mata kiss yabar d'akin zuwa shashin ZAINAB.

 

Ya sameta a kitchen tana had'a coffee, ya tsaya yana qare mata kallo, tayi mai kyau sosai, ZAINAB badai san gaye ba, ya godema Allah daya basa mata masu san ado da kwalliya..

 

Ahankali ta juyo ta kallesa, dan qamshin turaransa ya fallasasa, yayi mata kyau sosai kamar karta dena kallanshi

Ta qaraso inda yake dacewa, "ABDUL duniyar tak'i yimin dad'i ayau, ta kasa sani sukuni, sai b'atan tunani take, sam tunani mekyau ya kasa ziyartar zuciyata, gashi sai bani sakwanni take, wallahi sakwannin ba masu dad'i bane.... Tana zuwa nan a zancenta, hawaye ya zubo mata, taci gaba da cewa, Wai shin har kaina na tsana ne koko shi kad'ai kawai na tsana,

yau naji maraici cikin raina ABDUL, da'ace mahaifiyata na raye, danaje gareta na rungumeta na fashe mata da kuka na bata labarin komai na kwanta kan cinyarta ta lallasheni kona samu sukuni, amma amma amma.....

Saurin katseta ABDUL yayi wajen karb'ar cup d'in hannunta ya ajiye gefe ya kama hannunta da rungumarta yana cewa, "kibar sambatu my Aunty, kibar batu akan maraici, ki share magana akan Salisu, ki tsaida tunaninki kan Soyayya, ni kuma na nuna miki wata rayuwa

 

Ina sanki ZAINAB, ina qaunarki ZAINAB, ina san rayuwa dake ZAINAB, danna gane shaƙuwar dake  tsakaninmu shaƙuwa ce me illah, idan muka rabu da juna zamu fad'a cikin wani hali

 

Bana SO, bana qaunar naga kin qara shiga damuwa saboda Salisu, Yakai qarshen zancen nasa da raba jikinsu dana juna yana me sakar mata murmushi

 

Itama Murmushin tamai tace, "Yanzu sai muje wajen su Dady mu gaya musu gaskiyar niyar yin Auran namu, sai kabani takaddata na roqi Allah ya fittomin da Wanda zai dace dani.

 

Murmushi ABDUL ya qara mata yace, "Kafin nan muje falo nayi muku nasiha ke da RAHMA.

Tace "Toh me zaisa kayi hakan,  yace "Saboda dama ni ban Aureki danna sake ki ba, na Aureki ne dan nayi rayuwar Aure dake.

Waro ido😳 ZAINAB tayi da cewa, "ABDUL me kake san cemin.

"Ina san ce miki, ina san in rayu dake matsiyin matata, ina san kicire wani batun na cewar ke Auntyna ce, ki Karb'e matsayin mijin auranki..

  "Tab bazai yuhuba,😠 ta katse shi da faɗin hakan tana me d'aure fuska.

   Sai yayi murmushi da janyota jikinsa, nan ko ta ware idanta gabaki d'aya suna masu kallan kwayar idan juna dajin numfashin junan, gaban ZAINAB yahau faɗuwa, sai ya qara sakar mata murmushi ya maida  kalansa ga leb'anta Wanda yasha jambaki, Yace, "Gaya min, kina sona koko baki sona.

Cikin rikicewa tahau cewa, "am aa, ina nufin ina sanka ABDUL amma ba irin wannan san ba...

"Da gaske... ya katse ta da fad'in hakan, yana meci gaba da cewa, Babu saki tsakanina dake ZAINAB, Sannan ina so ki juya wancan SON da kike min ya koma irin wannan da nake buqata, Ahankali tace, "Bana jin zai yuhu dan bansan ta'ina zan fara ba,

"Ki fara tako ta ina, dan ina san yin wata rayuwa dake, ya faɗi hakan dakai bakinsa cikin nata yahau aika mata da Wanda bata tab'a jinsa ba.

Nan ta rintse idanta yayi mata san ransa kana ya saketa da cewa, Bud'e idanki mana my Aunty, bafa abu bane na qarewa, so nake mufara soyayya"😃

 

Shuru ZAINAB tamai daqin bud'e idan nata, ya sakar mata kiss a wiya nan ta bud'e idan da sauri, sai ya d'aga mata gira daci gaba da cewa, Inafa jiranki a falona, yana faɗin hakan ya d'auki coffee d'in data had'a ya ficce daga kitchen d'in dan zuwa falan nasa.

 

Yana zuwa RAHMA na zuwa, nan tashiga kallansa tana me k'arema bakinsa kallo, jambakin ZAINAB yayi mai aiki kaca kaca😂, nan gabanta ya fad'i hankalinta ya tashi, cikin wani hali na kishi ta qaraso garesa ta dangwani jambakin bakin nasa a yatsanta ta nunamai.. gam gaban ABDUL ya faɗi..

Ganin yaqi ce mata komai sai ta juya shashinta da gudu tana sakin kuka😌

 

"Innalillahi.. Yace dadafe  kansa🤦🏻..

Daidai nan ZAINAB ta shigo falan, ta kallesa da cewa, "meya faru kake innalillahi..

Ahankali ya cire ahannun nasa daga goshin nasa ya kalleta da wani hali ya nuna mata bakinsa da cewa, "Zoki goge min,

Ta hararesa tace, "Ni nace ka shafa.

"Amma ai bakin ki ne ya shafa min ko.

"Amma ai bani nace ka shafa ba, tafad'i hakan dayi mishi wani shu'umin murmushi Wanda yajishi har cikin ransa kana tajuya kuma ta koma shashinta tana cewa, idan Uwar gidan tawa tazo ka kira ni dan zanje na qara had'a coffee agoge cikin sauri karta gani ta zargi ZAINAB....😀

 

 

 

By Auntyn luv,  pls commente n share Ring ga masoya, me yafi birgeki

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.*🙆🏻*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆🏼*.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`•🤱🏻

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 18

 

"Ai ta gani, Abdul ya faɗi hakan abayyane, ZAINAB bata jishi ba, dan tayi gaba..

 

Falan ZAINAB d'in yayi ya d'auki wayarsa sannan ya dawo shashin nasa yayi Bedroom d'insa.

   Ya tsaya gaban madubinsa yana kallan yanda jambakin ya kama mai bakin nashi, gashi nan b'aro b'aro kam ba wani maganar rufa rufa, nan yasa tishu ya goge kana Yayi shashin RAHMAN,  ya sameta tana kukan kamar ammata dukkan tsiya, zaiyi magana ta katse shi da sauri wajen d'aga mishi hannu tace, "Karka cemin komai malam, dama ka shirya cimin fuska ne shiyasa kace naje nasameka ko. cikin sanyayyiyar murya yace, "Kiyi hak'uri my Baby, ban zaci hakan zai miki ciwo sosai ba, kallansa tayi da b'acin tace, "Ban gane baka zaci hakan ba, yace "kwantar da hankalinki mana, dana shiga d'akin ZAINAB ganin jambakin nayi kan gadanta, shine nace bara na shafa na tabbatar da kalolin kishinki, ganin naga na farko nace bara naga na biyu, na uku ma yana zuwa, kuma dukkanku na shirya yi muku hakan, saidai kowa da irin nata salan, cikin ke da Aunty zainab ina san gane wacece tafi kishi, amma yanzu na canja ra'ayi tunda naga hakan yasaki kuka dan Allah kiyafe min banyi hakan danna b'ata miki rai sosai haka ba.

Jan numfashi RAHMA tayi da cewa, "kawai karka sake aikata hakan, dan idan kasake ZUCIYATA bugawa zatayi, yanzu ma bakaji  yanda bugawan nata ya canja bane, dan Allah mijina karka qarayimin irin hakan.

Murmushi ABDUL yayi da rungumarta yace, "bazan sake ba my Baby, yanzu tashi muje falan nawa ko. "Toh, tace mai,

 

Haka suka fito abin gwanin ban sha'awa gaskiya, kallo d'aya zaka musu ka hango dacewarsu, ABDUL ya gane tafiyar RAHMAN ta canja, hakan yasa ya d'auketa kamar wata baby bai direta a ko'ina ba sai'a falan nasa, yana sauketa kan kujera ya sakar mata kiss a goshi yace, "Baby tafiyarki ta canja, bara na kira Aunty salma ta dubaki, gyaɗa masa kai tayi ya qara sakar mata kiss a kumatu.

Nan ko ya kira Aunty Salma wata ma'aikaciyar jinya ce, qanwar momynsa, bayan ta tabbatar mishi tana zuwa saiya kira ZAINAB yace mata tazo RAHMAN tazo.

 

ZAINAB ta shigo falan hannunta d'auke da coffee, daga yanayin zaman da ABDUL Yayi da RAHMA tasan akwai so me girma a tsakaninsu, haka kawai taji wani iri aranta haka, bayan ta zauna kallan RAHMAN tayi da murmushi tace, Barka da fitowa, RAHMA tayi mata banza, ZAINAB bataji haushi ba taci gaba da cewa, An tashi lafiya.

Anan ne RAHMAN tace "Lafiya lau, dan ita fa gaskiya bata qaunar ZAINAB, Sannan bazata iya b'oye mata hakan ba.

 

ABDUL yayi gyaran murya ya kalli RAHMA yace, "my Baby ga my dear Auntyna wacce kike yawan jin labarinta a bakina kimma santa, ayau tazama abokiyar zamanki, da fatan zaki qarb'eta hannu biyu danna samu nutsuwa da kwanciyar hankali.

Rahma taja numfashi da kallansa cikin murmushin yaqe tace, "Naganta, kuma Allah ya bamu zaman lafiya.

"Ameen, ABDUL yace da kallan ZAINAB yaci gaba da cewa, Auntyna kinga dai RAHMA, duk da cewar nasan kin santa, ina so ku had'e kanku dan Allah nasamu nutsuwa da kwanciyar hankali, nasan kin girmi RAHMA, amma ayanzu a al'adance tana da wani girma awajenki, zanso kibata girman, sannan ke RAHMA bani san hakan yasa ki rainata, kaf cikinku na d'aura aniyar bama kowa hakk'inta, bama kowa damarta, bama kowa farin ciki, nutsuwa da kwanciyar hankali, dan Allah dan Allah dan annabi badan niba, ku had'e kanku ku zauna lafiya.. Ya qarashe zancen nashi yana me kallansu dukkansu biyun da nazartarsu yanayinsu.

 

ZAINAB tace, "Toh Allah ya bamu zaman lafiya,

Abdul d'in yace "Ameen my Aunty, yanzu zan raba muku kwana, zanyi kwana uku a d'akinki kamar yanda shari'a tace, sannan na dawo d'akin RAHMA nayi kwana biyu, daga lokacin saina fara kwana bibbiyu a d'akin kowaccenku, ina fatan dai kunyi na'am da hakan.

Dukkansu sukace hakan yayi, Sannan yaci gaba da cewa batu akan girki kuwa, na bama kowa damar tayi abinda ranta keso da rana da daddare, amma da safe ina san kowacce ran girkinta ta had'a mana breakfast dukkanmu mu had'u muci.

Toh sukace mai

 

Abdul ya maida kallansa ga ZAINAB yace, "Aunty yunwa nake ji, zanso ki had'amin wani abu naci kanna fitta, "Toh ZAINAB tace da tashi tabar falan, dama ta zaqu tabar falan dan jinta take kamar akan qaya.

Tunaninta ne ya bata inda sito d'in nasu yake, babu abinda babu komai na buqata tasamu harda kayan gwari, ga furiji me d'auke da naman rabo abin dai yayi mata daidai, tsarin gidan yayi ba qarya,

Nanta yanki nama ta had'a farfesu, da d'auko dankali ta fere ta soya shi da kwai, akwai wani ganyen tie d'inta da take sha wato KHAIMA, shi tasaka mai, ta shirya komai a taftace, dake gas ne shiyasa tagama komai da sauri, tazo falan nasa tajera mai akan dining,

Har a lokacin suna tare da RAHMA, wani film d'in RAHMA SADAU suke kalla waishi shuga naija, film d'in yana tafi da hankalinsu.

Cikin farin ciki ABDUL yake godema ZAINAB d'in, dan yaga saurin gama girkin nata.

Haka ya tashi yana cema RAHMA tatashi suje suci su ukun, tace bata jin yunwa, abin yaba ABDUL mamaki matuqa, dan yasan bataci komai ba. Hmm ya gane akwai kishi cikin tafiyar tata, dan haka bai matsa mata ba, haka yaje dining d'in, ZAINAB ta zuba mai komai zatabar wajen ya kama hannunta yace, "Haba my Aunty, saiku barni ni kad'ai kan dining, bayan yanzu nagama yi muku magana, zauna Kawai muci tare dan nasan kema kina jin yunwar,  murmushi ZAINAB tayi mai da cewa, "Toh bara na d'auko plate, haka taje ta d'auko plate ta zuba itama suka hauci tare.

ABDUL ya kasa jurewa, yace "Aunty girkin nan yayi dad'i fa, ZAINAB tayi murmushi ba tare da tace komai ba, RAHMA taja tsaki a ciki ciki, tatashi tabar falan sam basuma san tabar falan ba.

 

Tana zuwa part d'inta tayi jifa da wayarta tana cewa, "Wato harda wani cewa girkin nata yayi dad'i, yanzu dani na d'aure nayi mai aida nawa zai yaba kamar yanda ya saba, haka kawai taji hawaye ya zubo mata, cikin sauri tashare jin ana mata sallama, tana bud'e kofar tata taga Aunty salma ce, saita sakar mata murmushi tana meyi mata barka da zuwa.

Bayan sun gaisa dubata tayi taga dai ABDUL d'in baiyi b'arna sosai ba, saita bata magunguna tace tasha na kwana biyar, cikin girmamawa RAHMAN ta karb'a aunty Salman tatafi dan tace sauri take bazata iya leqawa gun ZAINAB ba saita qara zuwa.

 

Shiko ABDUL daya gama maida kallansa gun da RAHMA take yayi, sai yaga bata nan, yace da ZAINAB "Aunty ina RAHMA tayi, tace "ban san lokacin data tashi ba, inaga tana part d'inta.

Shuru yayi mata da tashi zai d'auki jakarsa sai ta rigasa tana cigaba da cewa, Muje nayi maka rakiya zuwa mota bana barka katafi haka kai d'aya ba. Murmushi yayi da shafan gefan fuskarta yace, "Zamu kyau da soyayya Aunty,

Dan Allah ki karb'eni matsayin mijinki, ina san nayi rayuwa dake.

Murmushin itama tayi da cewa, "Yazanyi dakai ABDUL, tunda kace min babu saki tsakanina dakai nasama zuciyata dangana, zan rayu dakai rayuwa irinta ma'Aurata.

"Toh nagode sosai, yanzu bara nama RAHMA sallama saina fito ko.

"Hakan yayi afito lafiya.

 

Ya samu RAHMA kwance kan kujera cikin tunani, ya sakar mata kiss a baki yana cewa, "tunanin me kikeyi my dear,

Tace "Tunani nake yanzu har kwana uku zakayi bani ba jinka kusa dani musamman yayin bacci.

"Zanyi kewarki matata fiye da yanda zakiyi tawa, dan nayi sabo dake sosai, ki cire damuwa kamar yau ne zan dawo d'akinki, fatana ki kulamin da kanki Sosai, dan bana san naji wani abu ya samarmin ke kinji,

D'aga mai kai tayi alamar taji, sai taqara da cewa, Aunty salma tazo ta dubani yanzu, kaga har magunguna tabani, "Yauwa ta kyauta, shine bata shigo ciki ba,  "wai tace sauri takeyi, idan ta qara zuwa taga Auntyn taka,

"Ok, bara to naje, dan Allah kici abinci yanzu, bana san zamanki da yunwa, Sannan banji dad'in yanda kikaqi ci d'azu ba, bayan kuma nayi muku magana, tace "Toh kayi hak'uri bazan sake ba, kuma yanzu zan tashi na had'a coffee dacin kazata tajiya, "Hakan yayi,

"Ina maka fatan alkairi ka dawo lafiya kamar yanda zaka fitta lafiya, Allah ya kare min kai,

Yaji dad'in addu'arta sosai, haka ya amsa mata da ameen ya qara sakar mata kiss ya ficce da farin ciki, 

 

ZAINAB na tsaye jikin motarsa yana zuwa ta bashi jakarsa dayi mai murmushi tace, "Toh adawo lafiya mijin Auntynsa,

Murmushin shima yayi mata da cewa, "Toh Allah yasa matar qaninta,..

 

 

 

 

A office ko zama na musamman ABDUL yayi yana tunanin yanda zai tafiyar da matan nasa, AMEER ya dafa kafaɗarsa yace, "Wai tunanin me kakeyi ne, ABDUL yace "Hmm ina tunanin yanda zan tafiyar da soyayyata da ZAINAB ne, Wallahi AMEER ina san iya soyayya saboda ita, ina san na rikitata akan sona, tayi min wani so Wanda bata tab'a yima wani irinsa ba.

AMEER yayi murmushi yace, "Ina uwar gidan tamu kake magana kan AUNTY ZAINAB, "ABDUL ya lumshe ido dan tuno mishi da RAHMA da yayi, yace "tana nan, sam bana ta ita, dan muna kulle tunanin juna nida ita, nayi imani bazan iya rayuwa babu RAHMA ba, yanzu dai damuwata ZAINAB ce, ina san yimata soyayya irinta yara yaran zamani.

AMEER yace  "Wannan ai ba matsala bane, kawai zama zakayi RAMADAN, kata b'ata tunaninta kaga me zai biyo baya.

Da mamaki ABDUL yace waye RAMADAN.

AMEER yaja kujera ya zauna, yace "RAMADAN wani jarumi ne cikin wani littafi SAMARIN BANAH na RAHAMA MUH'MD RUFA'I NALELE, in gaya maka Auntynsa yake aura kamar yanda ka Auri Aunty zainab, zan soka da satar soyayyar RAMADAN, na tabbatar zaka samu farin ciki me d'orewa kai da Aunty zainab

Dan idan kaga yanda yake b'ata tunanin Auntyn tasa SAILUVAH abin zai tsuma zuciyarka matuqa, haka abokansa da nasu matan soyayyarsu suma abin adubace, wato FAWAS da KHAMIS

ABDUL yayi murmushi yace "a ina zan samu littafin.

ABDUL yace "buɗe Bluetooth na wayarka na tura maka document d'in littafin, Wallahi tun daga farkwan fara karatun naka zakasan akwai soyayya cikin tafiyar labarin.

  ABDUL yace, "Idan kaso abu komai ma zaka iya faɗa akansa, Allah dai yasa ba b'atan tunani kayi ba.

 

Murmushi AMEER yayi yace "Saika karanta zaka yarda bawai na faɗin maka hakan danna b'ata tunaninka bane, aa iyakar gaskiyar na gaya maka, yauwa na tuna idan ni ban b'ata tunaninka ba junior zai b'ata maka tunanin.

ABDUL yace "kuma waye, yace "shima acikin labarin yake.

Shuru ABDUL yamai.

 

Aiko yana turamai littafin nan ya bud'e yahau karantawa, dan babu aiki gabansa alokacin, dad'in littafin ya fara tsuma shi, daqer ya iya ajiye wayar tasa yana hararo yanda zai tafiyar da tashi Auntyn..

 

 

Qarfe takwas da rabi na dare ya dawo gidan, bayan yayi shashinsa yayi wanka part d'in Rahma yayi tacikin part d'insa, ya ganta tana bacci hankali kwance, da alama ma Yanzu baccin ya d'auketa dan jikinta bai sake sosai ba, haka ya bata kiss a goshi da qara ja mata bargo yayo shashin ZAINAB.

 

Tana kan kujera tana kallo itama dai dad'an baccin a idan nata,

Ya zauna kusa da ita tamai Wlcm cikin murmushi tace, "Nayi farin ciki da dawowarka, yace "Nima nayi farin ciki da ganinki cikin k'oshin lafiya,

"Muje kaci abinci dan na tabbatar kana tare da yunwa,

"Haka abin yake, kamar ko Kin sani, ina jin yunwa sosai

 

Bayan yaci abincin umartarta yayi da suyi  sallah raka'a biyu, bayan sun idar ya dafa kanta yayi mata addu'a, da tambayarta yanda take ibadarta da wankan tsarki, ZAINAB ta cire kunya ta gaya masa. Komai daidai ta faɗin masa.

Daga nan tashi yayi yace "Aunty kizo d'akina ki tayani kwana mana,  gaban ZAINAB ya faɗi, tace mai, "aa zan kwanta anan basai nazo d'akinka ba, kaga kowa ai yana da d'akinsa,  yace "matata  ba haka take min ba, dan kullum zuwa d'akina take tana tayani kwana, dan haka kema dole ki dinga zuwa tayani idan ba haka ba, nakai qararki gun kaka malam dan ina jin lokacin dayake ce miki kidinga min ladabi da biyayya. Yana faɗin hakan ya ficce daga room d'in yana cewa aransa duk wayanki malama saina maidake abu d'aya ni dake.

 

ZAINAB tasan me zuwan nata zai haifar, tasan sarai ABDUL iskanci zai mata zallah, danya yaye kunya ya maida ita yanda yake so cikin haske ba wani abu bane, dan dama can ba kunyar bace dashi.

 

Tana da tabbacin zai iya zuwa wajen kaka malam wato wan mahaifiyarsu Alhaji Ali mijin Hajjiya Kakah ya gaya masa kamar yanda ya fad'i yanzu, ita halin ABDUL ai saidai tasanar da wani, dan haka zata kiyaye, dan ayanzu ba yanda zatayi dashi, igiyarta na gunsa sai yanda yaga damar yi da ita, "wayyo ni ZAINAB yau zan kwana d'aki d'aya da ABDUL matsayin mijina, ta fad'i hakan a bayyane tare da tashi tahau canja kaya dan dama da wankanta, wata rigar bacci tasa iya karta gwiwa, ammafa  tabayyanar da Komai na halittarta, dan rigar tabi jikinta ainu, tana da tabbacin kallo d'aya ABDUL zai mata sha'awa ta baibayesa.

 

Ta shigo falansa kenan sukaci karo da RAHMA tazo d'aukar ruwa, RAHMA akwai ta dasan shan ruwan dare, dan yanzu haka ma farkawanta kenan ta duba taga ruwanta ya qare shine tayo falan ABDUL d'in ta bud'e furijinsa tad'auki ruwan, shine ta juyo zata koma d'akinta sukaci karo da ZAINAB....

 

Ita abin dayaja hankalin ZAINAB agun RAHMA shine ƙamshin turaranta, ita kuma RAHMA abin dayaja  hankalinta agun ZAINAB d'in shine shigar da tayi.

 

ZAINAB ta had'iye yawu cikin jin wani iri haka tace, "Ruwa kikazo d'auka ne.

RAHMA tayi ƙofar dazata sadata da part d'inta tana cewa, "Eh, saidai safe..

ZAINAB tabi bayanta da kallo kana tanufi bedroom d'in Abdul d'in da sallama tana cewa "Nashigo,

ABDUL ya saki baki yana kallanta, gaskiya shigar tata taburgesa, sanda ya lumshe ido ya tashi yace, "Aunty ai kin shigo, kawai kullemun k'ofa. Ya fad'i hakan yana me qarasawa gareta, sanda ta kulle ƙofar yahau qara  kallanta daga sama har qasa yana meci gaba da cewa, Aunty kinyi kyau sosai a shigar nan, zanso kidinga yimin irinta, dan wankan ya shigeni sosai, Aunty kinga cinyarki kuwa😃 kinga qugunki kuwa, kinga yanda rigar tazauna ajikinki kamar dama danke akayi..

 

_Saifa nazama y'ar iska zan zauna da ABDUL lafiya_ ZAINAB tafad'i hakan aranta cikin matuƙar jin kunyar zancen nasa...

 

Bata ankare ba saijinta tayi ajikinsa yana aika mata da irin na d'azu da safe, wato shu'umin kiss d'in nasa.

 

Cikin lokaci qanqani komai ya fara wanzuwa, sannu a hankali ABDUL yayima ZAINAB abinda Salisunta yake mata cikin dare, saidai nasa salon yazo mata da bambanci mai tarin yawa, salon ABDUL d'in me tsayawa arai ne, dan yayi mata irin wanda bata tab'a tunanin jin irinsa ba, har sanda takasa jurewa tasakar mai kuka,

Wannan abu daya faru tsakaninsu ya tsaya aransu matuƙa, kowa yana da tarin tambayoyi cikin ransa azuciya _Dama Aunty zainab haka take_

_Dama ABDUL haka yake_

 

Wannan tambayar ita suketa yima kansu.

Gaskiya ABDUL yaji dad'in raya sunnar da ita, tsakaninta da RAHMA kad'an ne, dan jin dayama RAHMA bajin dazai iya mantawa nan kusa bane, gaskiyar magana itace zai qara tantancewa tsakaninsu wacece tafi bashi nutsuwa yafi jin daɗinta a dararrakin nasu, kansa ya kulle yana dai gani kamar yafi jin daɗin RAHMA, amma dake yanzu yana tare da ZAINAB sai yake ganin kamar ba wacce tafi kowa a cikinsu, kai dole asamu bambanci, zai tantance ne, wannan tunanin yaketayi ZAINAB na maqale a ƙirjinsa,

Itako ZAINAB wata soyayyar ABDUL d'ince tayi ram da zuciyarta, ashe Salisu ba abin daya sani wajen iyawa da mace, ga qanin bayansa yafisa iya tafiyar da mace, Gaskiya iyawa irin wannan tana qara zazzafar qauna tsakanin ma'Aurata, bata san lokacin data sakar ma ABDUL d'in kiss a kumatu ba, ya kalleta sai taci kunya ta kamata, ta rintse idanta, yayi murmushi da cewa,  "Nimafa na qara sanka da qaunarki AUNTYNA.. Shuru ZAINAB tamai,

   Ahaka ko bacci yayi awan gaba dasu.

 

 

RAHMA ko kasa jure yanda taga ZAINAB tayi, dan sai zirga zirga take a room nata tana jan tsaki dayin magana ita kad'ai kamar wata zararriya.. Fad'i take. "Lallema matar nan su take ta nuna min karuwanci ni da gidan mijina, ka duba shigar da tayi kamar wata shahararriya a iskanci, ni zata nunama saka qananan kaya, nasan duk inda namiji yakai da abinsa bai isa shareta cikin wannan shigar ba, tab lallema🤔, wato so take ta kwace min miji, wallahi bata isa ba, ina san mijina idan iskanci takeji nina fita iyawa, kuma muzuba mu gani, dama dan tun da farko ba sanshi nake ba shiyasa sam ban damu tayin shiga irin wannan ba amma yanzu tunda nasan dad'insa zan nuna mata ita qaramar ƴar iska ce... Hakan take fad'i a bayyane tana jan tsaki, nan taqara jin tsanar ZAINAB aranta, haka acikin daran tajawo dukkan akwatinanta na kananun kaya wanda take tarawa dan yima majin Auranta tanadi, da wanda take sawa agidansu kaf ba wanda tabari, kayane masu yawan gaske dan a kashi d'ari talatin zaka cire shine kayanta namu na gida su atamfa da leshi su material, duk sauran kananun kaya ne. Sai kayan Auranta da aka mata sune kad'ai na arziqi kuma ko 1 bata ɗinka ba

Dan masifar kishi irin na RAHAMA alokacin ta shirya kayan da lokutan da zata dinga saka ko Wanne, ba ita tasamu yin bacci ba sai kusan qarfe 2 na dare, dan ma tasamu tayi lafula raka'a hud'u dan gaisar da ubangijinta, dan tunda asirin jikinta ya karye tadawo tayin ibadarta akan lokaci, haka lafular tana qoqarin yi idan taga da hali.

 

 

Washe gari tunda asuba da ZAINAB tayi nasarar yin shashinta bata qara yarda ta had'u da ABDUL ba, wata kunyar ABDUL d'in takeji kamar me, musamman idan tana tuno da yanda daran nasu ya kaya, idan tatuno da yanda takemai kukan dad'i rintse idanta takeyi gam kamar taga wani abun tsoro.

Dama shi yasan za'ayi hakan tsakaninsa da ita, dan tunda ya shiga toilet ya fito yaga babu ita yasan me yasata gudu.

"Hmm su Aunty zainab kenan, 😂 taji irin wanda bata tab'a jiba, gaskiya RAMADAN kayi gaskiya akwai wani sirri tsakanin soyayyar macen data girme maka, ashe ba banza ba ka mannema AUNTY LUUVAH a SAMAREEN BANAH.. ABDUL ya faɗi hakan lokacin daya gama shiryawa dan fittowa tafiya office.

 

Yaga breakfast kan dining nan ya shiga tunanin wayayi cikinsu, ZAINAB ce dashi hakan yana nufin itace tayi kenan, toh Yaushe tayi, ya tambaya kansa, shashin RAHMA yayi yaji tana wanka, ya tsaya a bakin k'ofar toilet d'in yana cewa, "My Baby kiyi sauri ki fito na ganki dan nayi missing d'inki sosai fa. Gashi ina jin yunwa zanso ina ganinki ina breakfast dan abin zaiyi min Sweet matuqa..

RAHMA tayi murmushi dacemai, "kaje dining d'in ka jirani yanzu zan fito,  Yace "Kin tabbatar, tace "Allah bazan dad'e ba...

Jin hakan saiya fitta daga d'akin yayi shashin ZAINAB, saidai ya duba ko ina bai ganta ba, ashe tana can wajen shaqatawar gidan, anan ya hangota ta windan falanta.

Aiko nufar wajen yayi yaje ya ritsata yana cewa, "My dear Aunty me kikayi anan da sassafe haka,  ZAINAB taja numfashi daqer ta iya cemai, "kawai naji sha'awar san ganin furanni ne.

"Amma ai yadace ki tsaya kiji da mijinki kafin ki keb'ance dan ganin nasu ko.

"Toh nayi lefi amin afuwa.

"Aunty Ki kalleni naji dad'i mana, ya zaki dinga min magana ba tare da kallan fuskata ba!

Murmushi ZAINAB tayi cikin gajiyawa ta kallesa, yayi kyau sosai, bata ankare ba saiji tayi ya rungumeta, yana meci gaba da cewa, ina sanki Auntyna, Sannan naji dad'in yanda komai ya faru tsakaninmu ba tare da d'aukar lokaci ba.

  "Saimu godema Allah, yanzu muje kaci abinci kar yayi sanyi.

Haka suka jero abin gwanin ban sha'awa har zuwa dining d'in,

ZAINAB taci gaba da cewa "har yanzu uwar gida bata fitto ba, yace "Yanzu zata fito, mud'an jirata kad'an...

 

Shuru tamai, shiko sai kallanta yake yana tuno irin sambatun data dinga mai jiya cikin daran nasu.

Nan ta ankate da kallan dayake mata ta wani galla mai harara tace, "Wai kallan na miye ne.. Yayi murmushi da cewa, "Kawai ina tuno kukan da kika dinga min ne, tare da sambatu, Oh su Aunty dama haka kike😀 baki iya jurewa.

 

ZAINAB taji kunya ta kamata🙈, kamar qasa ta tsage ta shige ciki, nan ta sunkuyar da kanta da dafe kan nata, tace "idan kana tuna min zan hana idanka ganin fuskata.

Cikin sauri yace, "toh na bari yanzu bud'emin naganta, amma batun denawa saikinyi da gaske, dan lamarin da tsayawa arai yake matuqa.....

Kan ZAINAB tace wani saiga RAHMA ta fito daga shashinta cikin wata shegiyar shiga🤔.. Wankan abin a kalla ne, wankan abin ayi tunani akansa ne, wankan ya dace ya tsaya aran masoyi...

 

Dake hankalin ABDUL yana kan yaga tafitowar tata, dan da gaske yana san ganinta, dan haka yana jin tatab'a kofar da zata sadata da falan nasa yakai kallansa wajen, yayi ko kyakkyawan gani😨..

 

Gata fara, kyakkyawa me kyan fasali, jikin RAHMA jikine wanda mutane suke kiransa da karuwan jiki, duk wankan data d'auka dolene yayi mata kyau.

 

Wata baqar riga tasaka me kwantawa ajiki talafe yanda komai na jikin mutum zai bayyana, hatta shatan kan Brest nata sanda ya bayyana, sai tasaka jan wando wanda ya tsuketa daga qasa, shi dai bazaka kirasa da 3kwata ba, Sannan baza kace masa dogo ba,

Ya dai tsaya mata a sangalalin qafarta, Sannan tasaka wani takalmi me d'an tsini ja, saita tubke gashinta da jan ribom, sannan ta d'aure kan da wani gyale me kalan baqi da ja, daga yanayin yanda tayi d'aurin nan zaga gane wayayyiyace a iya ado da kwalliya

Fuskar nan tata tasha fante fanten kwalliyar zamani.

Tun daga nesa suke jiyo qamshin turaranta.

Kallo d'aya ZAINAB tayi mata tad'auke kanta, saboda jin wata bugawa da zuciyarta tayi, nan take taji wani masifaffan kishi yazo mata.. Ganinta bai dace RAHMAN tayi wannan shigar ba, tunda tasan ai ba girkinta bane.

 

Har ga Allah ABDUL baisan lokacin daya tashi ya nufi RAHMA ba, da gaske tab'ata mai tunani, sanda ya gansa gabanta ya rungumeta sannan ya samu nutsuwa, faɗi yake, "My baby kinyi kyau sosai,

RAHMA tasaki murmushi da sakar masa jikinta ganin yana bata kiss tako ta'ina😨😨😨

 

ZAINAB ta qara kawar da kallanta akaro na biyu, ranta ya qara mata zafi matuqa, wata zuciyar tana gaya mata tatashi tabar musu falan kawai, wata kuma gaya mata take aa kidai zauna kiga iya gudun ruwansu, Kai ina tashin shine zai fiye mata alkairi, dan jikinta ya fara rawa, _kai kishi masifa_ ta fad'i hakan aranta tare da niyar tashi...

 

 

 

By Auntyn luv, comments & follow me on wattpad @ rahamanalele,💋

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.*🙆🏻*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆🏼*.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`•🤱🏻

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 19

 

*true 10 read more*

Nagode sosai da nuna  ƙaunarku gareni sister, Auntyn luv takuce.

 

 

Har tatashi sai kuma wata zuciyar tace mata zauna dai, haka takoma ta zauna ammafa sam taqi yarda ta qara kallansu a karo na uku.

RAHMA ta mintsine shi a gefan ciki, nan ya dawo hankalinsa, a shagwab'e tace "Yunwa nake ji Sha kallona.

"Nima haka my Baby, ganinki ne ya rikitani har na mance dajin yunwar tawa, amma yanzu najita muje muci ko.

Murmushi tamai, ahaka hannunsa cikin nata suka qaraso dining d'in,

Sanda suka zauna ABDUL ya ankare da ZAINAB, nan ko yaji wani iri haka, musamman dayaga yanayinta ya canja ba kamar yanda suke dashi kafin zuwan RAHMAN ba.

Sharewa yayi yaqi kallan kowa a cikinsu ya fara cin abincinsa...

Zuciyar RAHMA tawanke tas taji dad'in hakan daya faru, dan haka sam bata jira ZAINAB d'in tafara yimata magana ba saita kalleta da b'oye jin daɗin nata tace, "Aunty zainab Yau yana ganki haka kamar baki da lafiya.

ZAINAB tamata kallan kishi me tafe da tsana tace, "Wallahi RAHMA sam banijin dad'in jikina, sakamakwan rashin baccin daban samu nayi jiya ba.

RAHMA tace "Ayya, meya hanaki yin baccin, bayan yanzu ba lokaci bane na sauro bare nayi tunanin ko sune suka hanaki

 

ZAINAB tayi mata murmushin mugunta tace, "Hmm, kedai bari, babu ruwan sauro dan ABDUL ne ya hanani yin baccin, gaskiya mijinki jarumi ne matuƙa.

  ZAINAB takai qarshen zancen nata da kallan ABDUL wanda yayi saurin kallanta da mamakin amsar databa RAHMAN, saita sakar mai murmushi tare da d'aga masa gira.

Ba yanda zaiyi dan haka mayar mata da murmushin yayi..

 

RAHMA tayi shuru tana juya maganar data gaya matan a kwakwalwarta, nan tashiga magana da zuciya... _Lallema matar nan, wato saima tafito ta nuna min ABDUL ya raya sunna da ita ko_ afiliko sakin murmushi tayi dacewa "Ayya dole naganki haka, damma ba Wannan bane cin amarcinki na farko da saiya kwantar dake, musamman idan nayi duba da yanda nawa daran ya kaya dashi, wallahi Aunty da kina nan lokacin da sai kin tausayamin.

 

ZAINAB tagane RAHMAN ta ganota ta faɗin mata hakan ne danta b'ata ranta, shiyasa tayi saurin bata amsa da fad'in hakan, wato dai yarinyar ta shirya zama da ita kenan, idanko haka ne suzuba su gani.

Ahankali ta kalli RAHMAN da murmushi tace, "Aiko dazan tausaya miki, duk daya kasance bana nan nasan kinyi fama, yanzu dai kimin fatan samun sauqi nan kusa.

Rahma taja numfashi tace, "karki damu, dan zaki warware nan kusa, abin da mamaki matuƙa da jikinki ya jijjiga haka, dan ganin ai wannan ba shine karo na farko ba...

Kan ZAINAB ta qara cewa wani abu ABDUL ya tashi da d'aukar jakarsa da wayarsa ya kallesu dukkansu biyun yace, "malamai gwalmar tawa ta isa haka🏻, dama ina san gaya muku nadaukar mana me gadi da wanda zai dinga bama furanni ruwa da tsaftace harabar gidan, dan haka duk wacce take da girki ita zata dinga basu abinci safe ranah dare, Sannan shi me gadin yana da mata zata dinga zuwa muku cefane da aikan da kuke buqata, itama a za'a dinga biyanta ne kamar yanda na zanta dashi megadin ya tabbatar min da cewa haka sukeyi, dan kar y'an aikin suyi yawa, shin kuna ganin hakan yayi kodai kawai mu hutashar da ita na d'aukar muku y'an aiki,.

Zainab tace, "Ina ganin hakan yayi, idan dai tagaske zata iya jure zuwa yi mana cefanan da aikace aikacen namu.

Abdul ya kalli Rahma ta gyad'a masa kai da cewa, "zancen aunty gaskiya ne, allah yasa matanan kwarai ne.

"Ameen zainab da Abdul sukace, abdul ya qara da cewa, ni zan tafi sai Allah ya dawo dani,

ZAINAB tace "tunda nice dakai aisaika tsaya nayi maka rakiya ko.

Murmushi yayi mata da sakar mata kiss a kumatu yace, "aa, kiyi zamanki my Aunty, ke da bakya jin daɗi, ya faɗi hakan da shafar gefan fuskar RAHMA yaci gaba da cewa, ki kula da kanki my Baby, Sannan kisha maganinki pls karki manta wani abu ya samar min ke.

Murmushi RAHMA ta sakar mai da d'aga mai kai alamar taji.

Ganin hakan saiya janye hannunsa da barin falan yana mamakin hirar data shiga tsakaninsu biyu, shi inda namace ne, bazai yarda akai hira irin wannan dashi haka ba,  haka ya shiga motarsa yabar gidan da tunani sosai cikin ransa.

 

 

Suko tunda ya fitta ba wacce ta qara yima y'ar uwarta magana, haka suka gama cin komai duk suka tashi sukayi shashinsu.

 

ZAINAB da gaske taji tsanar RAHMA aranta kamar yanda itama RAHMAN taji tata aran nata, sun shirya zaman kishi sosai cikin ransu, bari mugani ko zasu iya jurewa..

 

 

ABDUL bayan ya samu sarari a office cigaba da karanta labarin SAMAREEN BANAH yayi, salan soyayyar XEE da KHAMIS tafara tafiya da imaninsa, haka yana shagaltuwa sosai cikin tunani idan yazo kan salon soyayyar SAILUVAH da RAMADAN, gaskiya ya qara samun wata makafa acikin labarin, ayanzu bayajin zai samu wata matsala cikin soyayyarsa da ZAINAB.

 

 

Akwana ukun da ABDUL yayi da ZAINAB ya murjeta san ranshi, ita kuma ta qara sanshi matuqa da gaske, taji aranta bata da sauran abin so Yanzu sama da shi.

 

RAHMA ta qare tunaninta gabaki d'aya ta kuma lura da ZAINAB gabaki d'aya cikin kwana ukun da tayi da ABDUL, taga tsanarta a kwayar idan ZAINAB d'in, amma dake tana da wayo sam bai zama lalle wani ya gane hakan ba, tagane so take takwace mata ABDUL da karfi da yaji, dan tunda taga shigar da ita RAHMAN tayi ranar shi kenan itama tafarayi.

Ran RAHMA ya b'aci matuqa da gaske ganinta mezaisa tayi abinda taga tayi, kujimin RAHMA fah🤔, saikace ba ita tafara ganin tayi Sannan tad'auko yi ba. Koda yake dama dana da niyar farawa tunda tagane san ABDUL d'in yayi ram da zuciyarta, kuma dad'i da qari ma shine yanda tagane shi d'inma yana mutuwar santa.

 

Ayau takarb'i girkinta  tagare tunaninta tsaf bazata qara yarda  ZAINAB taga wankanta na qananun kaya ba.

Dan haka ba shiri ayau d'in takira Abida qanwar ABDUL d'in ta ibi kayan Auranta kala goma tace tarakata wajen telan da yake mata d'inki ya d'inka mata su, danta yaba yanda yakema Abidan d'inki, haka RAHMAN tatambayi ABDUL zuwa wajen telan yace bazata ba, dan baiyarda da lafiyarta ba, kawai tabari sai tasamu sauqi sosai.

Rahama najin hakan tahau rokwansa Allah da Annabi yabarta bazasu wucce minti goma ba,

Jin hakan yace toh taje.

RAHMA tasamu yanda take so dan Ahmad kat ne wajen d'inki, nan yasa yarinyar aikinsa ta gwada masa RAHMAN, ya tabbatar mata bata da matsala da kayanta dan Abida tasa ce bazai mata wasa irinna teloli ba.

Haka tace mai tagode zata turo Abidan da kud'in nasa gobe, yace mata ba damuwa.

 

 

Suna dawowa gida Abida tatafi, nan ko RAHMAN tahau girki tana qare tunaninta dan tasaka aranta zatayi komai ma majinta wanda saiyafi na ZAINAB, zata jajirce tazama itace tauraruwarsa.

Bayan tagama tayi wanka ta shirya cikin dai qananun kayan, saita wadata kanta da turare da d'akunanta kana tayi sallar isha tazauna zaman jiran mijin nata.

 

 

Itama ZAINAB tana cikin qananun kayan, itama fa tashirya b'ata tunanin mijinta koran girkinta ne koba ran girkinta ba.

 

Yanzu ya dawo, direct shashin RAHMA yayi da murmushi kan fuskarsa, haka kawai yaji yana murna dadawowarsa d'akinta.

Ba qaramin d'adi namiji yake jiba idan ya dawo gida matarsa tazo cikin kyakkyawar shiga me tafe da qamshi ta rungumesa.

Haka RAHMA tayi yanzu harda tsallen murna wai adole taga dawowar mijinta lafiya, yanda ta maqalesa kad'ai ya isa ya tabbatar maka akwai so da qaunarsa cikin zuciyarta, yaji dad'in yanda take farin ciki da ganinsa, ya kalleta cike da so da qauna yace, "Wai murnar tamiye ne haka, ta wani waro mai fararan idanta tace, "Kai, baka san tarin farin cikin dake raina bane yau, towai mema zaisa bazanyi farin cikin da dawowar mijina d'akina ba, bayan na d'auki ba kwana d'aya ba, ba biyu ba, har uku bana dare dajin d'umin jikinsa.

 

Baka san jin ɗumin jikin miji wani babban sirri bane, yana qara so, yana qara qauna, yana saka kewa, kewar da bata da daɗi azuciya, ya kan saka tunani a kwakwalwa, tunanin dake saurin wargaza kwakwalwar, yana harfar da tashin hankali, tashin hankalin da baya kwanciya tadad'i muddin baka ji d'umin ba, bana samun nutsuwa ko kad'an tunda ka ƙauracema shinfid'ata masoyina, ina sanka mijina, mezaisa bazan kasance cikin farin ciki idan na ganka ka dawo gareni ba, Kawai kagayamin meyasa ka tambayata hakan, bayan ina da damar da zan nuna murnar fiyema da wannan...

 

Murmushi ABDUL yayi da bata kiss yace, "kawai naga nayau na musamman ne, shin nayi lefi ne danna tambaya. "aa bakayi lefi ba, amma yadace kasan dole yanzu naqara sanin darajarka, yanzu dai muje na tayaka  rage kayan jikinka yanda zakaji dad'in hutawa dakyau.

"Hakan yayi Babyna.

"Toh d'aukeni muje shashin naka qafata namin ciwo, tafad'i hakan da shagwaɓa.

Waro ido yayi da cewa, "Baby, ciwan qafa kuma😳.

D'aga masa kai tayi da faɗin, "ina nufin ciwan qafa a soyayya,😀 dan idan ka d'aukeni zanji dad'in hakan sosai..

Murmushi yayi da d'aukarta yana cewa, "Zanyi miki duk abinda kike so, dan ji nake kamar na cinyeki da salanki, ina yinki Sosai asoyayya matata...

 

Bayan sun isa shashin nasa taya sa cire kayansa tayi, Sannan takai bakinta ga kunnansa tace, "Sha kallona, zanso na temaka maka wajen yin wanka, dan Allah Baby karkace aa, ina san nawanke ka da hannuna ne.

Yanyota jikinsa yayi suka fad'a a gado yace, "Bayan farin cikin da kike na dawowata d'akinki danayi na lura akwai abubuwan da kika shirya da yawa dan bani farin ciki, gayamin hakan yana nufin me. "Hakan baya nufin komai mijina, shin baka yarda dani bane. "Nayarda dake matata ammafa bazan barki ba saikin gayamin wani abun dangane da wannan sauyin.

   "Bazan iya maka qarya ba mijina, kawai na shirya baka dukkan farin ciki ne danna kwace ka agun Auntynka Zainab, danna lura so take ta kwacemin kai, shine na yanke shawarar hanata wannan damar, muddin ladabi da biyayya da kyautatawa zasu kaini ga samun nasara, zanyi maka su danna malleke zuciyarka aso ni kad'ai, bazan b'oye maka ba, ina qaunarka mijina, kuma ka shirya wata rana na zuwa dazaka nunani kace nice TAURARUWAR ZUCHIYATA...

 

"Hmm, idanko haka ne saiki dage, danna lura dukkan ku kun shirya mallake zuciyar tawa, hmm bazance miki komai ba, saidai bazan manta daduk wani abu da zakimin ba... Wannan shine satar amsar dazan baki..

Murmushi tamai da d'agasa, suka shiga toilet d'in, da gaske tayasa wankan tayi, ba qarya yafa qara santa, dan wannan wani sirri ne babba ga ma'Aurata sudinga temakama junansu wajen yin wanka..

 

Bayan ya kintsa kansa shashin ZAINAB yayi danya duba lafiyarta.

 

Abun yana tab'a zuciyar miji, idan zaibar d'akinki, ki sakamai kukan kirsa cewar baki san tafiyarsa.

 

Hakan ZAINAB tayi, nan ko take Abdul ya rikice yahau lallashinta wajen cewa, "Aunty ba ina nan ba, dan Allah kisa aranki ban barki ba ina tare dake, hakan zaisa ZUCIYATA ta zauna cikin nustuwa, AUNTY ABDUL d'inki bazai tab'a barinki ba, dan kinyi rayuwa dani tun muna qanana, gani yau matsayin mijinki, wannan wane rashin sa'a ne da zaisa na barki, AUNTY nasan hakan da ciwo, amma yazanyi dakaina, tana can tana d'aukin ganina ayau, tana farin cikin nadawo gareta yau, gashi ke kina min kukan baki san rabuwarki dani,  kawai tashi muje mu kwana gabaki d'aya, nasan RAHMA zata yarda, Sannan zanfi samun nutsuwar hakan sosai araina, dadai nabarki cikin wannan halin, maza tashi, Nasan zata yarda da hakan..

ZAINAB ta waro ido da harararsa tace, "Na shaƙeka idan ka kwatanta yin hakan, kai baka san dajin ciwo cikin zuciyar kishiya yayin da take ganin mijinta da kishiyar tata suna aikata kowace irin mu'amala ba, zanji araina tamkar na mutu idan naganka da RAHMA a gado d'aya, dan haka jeka kawai sai Allah ya tashemu jeka jeka saida safe ina maka fatan alkairi. Takai qarshen zancen nata da nuna masa hanyar waje,

Murmushi ABDUL yayi, bai qara cewa komai ba ya ficce mata daga d'akin harda ja mata ƙofa😀.

 

 

Ayau ABDUL ya tantance tsakanin RAHMA da ZAINAB wacece gwanarsa ta fannin raya sunnah, hmm bazaice komai ba, zai barma zuciyarsa wannan sirrin, yana rokwan Allah daya hanesa nuna bambanci tsakaninsu su biyun, yasani lamari na soyayya kamar yanda ayanzu yake katanta mutum bai isa yace zaiyi komai daidai ga matansa ba, saidai ya kamanta, to shima kamantawan yake fatan yayi abin daya dace, ya San kansa bazai iya ƙin nuna wacece fitacciyar gwanar tasa yayin da suke tare dukkansu ba, yasan zai iya nunawa koda bai shirya yin hakan, dan ance abar zuciya da abinda take so, wannan shine yake damunsa yake kuma rokwan Allah daya hanesa fitowa zahiri ya nuna gwanar tasa cikin su, dan yana san had'in kansu.

Amma zai bama kowacce cikinsu hakk'inta a soyayyar, saidai hakan zai kasance  akeb'ance dan kiyayewa.

 

 

Washe gari bayan ya kintsa kansa suna kan dining sai bin kowaccensu da kallo yake yana nazarinsu, ZAINAB tana sanye da qananun kaya riga da wando, kayan sun bayyanar da komai na halittarta Sosai, yayin da RAHMA take sanye da less ɗinkin riga da siket, kasancewarsa kalar ja nanya haskata, ga shi ya zauna a jikinta cif da cif, dama ai kunsan RAHMA bata saka kayan da yayi mata yawa saidai inna bacci ne.

Haka kawai yaji shauƙi aransa yana san yagansu da cikinsa, musamman RAHMA baisan meyasa tunanin hakan yafi karkata akanta ba, musamman idan yayi duba da yanda ZAINAB tafi buqatan hakan.

 

 

 

ABDUL na fitta RAHMA takira Abida tabata kud'in d'inkin telan nata danta kai masa kamar yanda sukayi alƙawari, dama agun ABDUL d'in zata karb'a shiyasa bata bashi jiyan ba.

 

 

Asatin ko yagama d'inka mata, nan taqara iban wasu tabashi dan yayi mata yanda takeso d'inkunan nasa sunyi ba qarya.

 

 

ZAINAB ta lura RAHMA tadena saka qananun kaya, sai hakan yayi mata dad'i sosai amma duk da haka tana takaicin yanda idan tayi shigar tamu ta hausawa ABDUL d'in yake shagaltuwa da kalanta.

Sam ZAINAB d'in ta kasa gane RAHMAN, takasa gane komai nata, musamman in dai magana akan ado da kwalliya ne saidai ama RAHMAN rashin kunya, badai kakadata ba, ita hakan ajininta yake, dan duk shigar da zatayi tasan me zata saka wanda zai tafi da wannan shiga, hakan ne yake sawa komai nata yake fitta daban dana ZAINAB d'in, Sannan batu na saka qananun kaya ba irin shigar da RAHMA batayima ABDUL d'in, ammafa sai dare yayi, ABDUL har Allah Allah yake ya dawo gida ran girkinta dan yaga wankan data mai, bama girkinta ba kona ZAINAB d'inne..

Sannan yaji dad'in yanda take sakawa da daddare, ganinsa hakan yafi mai, dan yana da tabbacin shi kad'ai zai ganta, amma idan da safe ne gani yake kowa ma ganinta zaiyi, dan wata shigar idan tayi shi kansa kunya kamasa takeyi, ya rasa meya had'ata dasan qananun kaya, saita sakamai wata riga da kad'an tafi rigar mama, wandon da kad'an yafi d'an kamfai, kai lamarin RAHMA saishi dayayi mata farin sani a yanzu, dan yana da tabbacin ba wanda zai gaya masa RAHMA ayanzu, wallahi ko iyayanta ko aminiyarta UMMAKATI basu isa gaya masa wacece RAHMA ayanzu ba.

Yayi sabo da komai nata sabo irin wanda idan yayi gigin barinta bazai iya rayuwa ba kwata kwata, zahiri yana san ZAINAB yana qaunarta dan itama nata salan yana tafiya da imaninsa, yana dai fatan rayuwa da matan nasa rayuwa tahar qarshen rayuwa...

Yana kiyaye kansa sosai yayin da suke tare gabaki d'ayansu, sam baicika magana yanzu ba, dan ya lura idan yace zai dinga kula hira dasu a lokaci d'aya dole sugane wacce hankalinsa yafi karkata akanta, wannan dalilin yasa sam baya wani hira dasu sosai idan har ya tabbatar suna dare waje d'aya kenan.

 

 

Bayan wata takwas sun saba da rayuwar da  sukeyi,  tsakanin RAHMA da ZAINAB sun yarda sufa kishiyoyin juna ne, ayanzu ko wani sha'ani za'ayi agidan momy, ko wani nata ya aihu ko biki zanso kuga nasu salan a kishi🤔, kowacce kicinsu so take taga kowa na dangin ABDUL d'in yazama itace yake kulawa ba y'ar uwarta ba, saka kaya wannan idan zasuyi dan zuwa taro kowa cikinsu tunani take, wane kaya wacce zatasa bana fa san tafini kyau🤔, sam basa fitta unguwa a tare, kowacce fittarta take daban daban,  hakan yasa Momy tasan zama suke zaman kishi, har kiransu tayi kan su had'e kansu su zauna lafiya, sukace mata toh, sam basujita ba, hankalin dai momyn ya kwanta ne ganin suna ba d'anta kulawa sosai, kishin nasu kishin san mallakar mijin nasu ne🤔, dan Momy tagani da idanta cikinsu ba wacce take san ganin b'acin ran ABDUL d'in..

 

Momy fa tafi qaunar RAHMA, tafi santa nesa ba kusa, tana dai San ZAINAB amma sama sama haka, dan tana tuna abinda yayarta tayi mata wato mama Saude, wannan yasa sam bata wani jin qaunar ZAINAB d'in aranta kamar yanda take jin na RAHMA.

ABDUL ya gane hakan ne dan duk zuwansa gidan nasu dazaiyi zata tambayi lafiyar RAHMA sau goma bata tambayi ZAINAB ba, abin yana damunsa har yayi mata magana ranar yake cewa momy me yasa baki tambayar Aunty Zainab sai RAHMA, bata b'oye masa ba, tace saboda ina tuna abinda yayarta tayi min ne, hakan yasa bani wani jinta araina, yace momy ZAINAB na da kirki tana sona sosai musamman ayanzu dana gane bata da abin so sama dani, dan Allah momy kidauki RAHMA da ZAINAB abu d'aya, dan bana san tagane baki wani yi da ita, murmushi momy tayi mai tace, ai ganewa ne bakayi ba, tuni ZAINAB tagane ban wani damu da ita, tagane nafi san RAHMA da ita, kuma tasan dalilin dayasa ni nuna mata hakan, bani san ka qara min magana akan ZAINAB, dan bazan sota yanda kake so ba, shuru ABDUL yayi, dan yasan bazai iya juya wannan ra'ayin nata ba..

 

 

 

 

 

Ya batun mama Saude da AMEER ne, AMEER ya d'auki halin da ABDUL ya d'auka tsakaninsa da ita, baya shiga harkarta, gaisuwa ce tsakaninsu shi da ita, yana bata kud'i masu yawa idan ya d'auki albashinsa, haka babansa ma yana basa, sam AMEER baya zama suyi hira shida ita, gashi duk cikin y'ay'anta ayanzu tafi san shi da qaunarsa, idan yana hira da Hajjiya Kakah saita dinga saka musu baki, dazaran yaga hakan saiya tashi sam baya san tadinga shige masa.

Tagane manufarsa tsaf, yana gaisheta da bata abin hannunsa ne dan bayanda zaiyi da ita tunda dai itace mahaifiyarsa, banda haka ta gane baya san wata mu'amala tadinga shiga tsakaninsa da ita.

 

Ya rungumi qannansa hannu biyu yana kyautata musu suna qaunarsa sosai kamar yanda suke qaunar ABDUL, ga Hajjiya Kakah da mahaifinsa sanshi suke sosai wannan yasa hankalinsa kwanciya, Sannan Momy da Dadynsa ada sam basu nunamai komai, musamman da yanzu ABDUL yabar gidan qara jansa ajikinsu suke sosai,

 

Babansa yayi ya Auri wannan bazawarar data liqe masa, mama Saude tayi kuka tayi kuka kamar ranta zai fitta, anan ne tausayinta ya kama AMEER amma sam bai nuna mata ba.

Ga amaryar dai tana da hankali amma tana nunama mama Sauden wasu abubuwa wanda suke sa ranta b'aci, AMEER ya lura da hakan, dan haka yaqi sakewa da ita kamar yanda take nuna masa tana san ya dinga sakewa da itan, maganar gaskiya AMEER kishin mahaifiyarsa ne yasashi qin sakewa da amaryar baban nashi, Mama Saude tagane hakan, hakan yasa taqara san AMEER d'in, ayanxu Aure takesan tayi, saidai babu wanda ya tab'a zuwa da niyar Auran nata.

 

 

 

 

 

Ayau jumma'atu babbar ranah aka d'aura Auran AMEER da UMMAKATI a garin jos.

Ba yanda RAHMA batayi da ABDUL ba kan ya kaita jos bikin, amma yaqi kaita, har kuka tayi amma yaqi sauraranta, ZAINAB tayi mamakin hakan sosai, dan lokacin da take qara tambayarsa suna tare a dining ne. Tace mai ya dace kabarta taje ABDUL, qawarta ce fah, kuma aminiyarta, dan Allah kabarta, sam ABDUL baisan lokacin daya kalli ZAINAB d'in yace mata, Auntyna kibarta Kawai, dan bana san tayi nisa dani ne, kwana uku take nema na bata ba kwana d'aya ba, zataje jos amma sai lokaci yayi, ZAINAB najin haka tayi shuru, tagane ya faɗin mata hakan ne da cikakkiyar gaskiyarsa.

 

 

Ajikin gidan ABDUL akwai wani makeken gida, qila girmansa yazo d'aya dana Abdul, tunkan bikin AMEER me gidan yama Dadyn ABDUL tallan gidan, saboda zasu bar Nigeria zuwa Gana, ba b'ata lokaci ko Dady ya siya, yasa akama gidan gyara sosai ya danqama AMEER gidan, yace ya bashi duniya da lahira, AMEER har kukan farin ciki sanda yayi, ya qara yarda sanshi da qaunarsa a jikin Dadyn yake, sam bazai iya barinsa ba, ABDUL ya tayasa murna sosai, qarin jin daɗinsa shine yanda zasu rayu waje d'aya, makwaftan juna..

 

Toh acikin gidan y'an uwan maman UMMAKATI sukama UMMAKATIN jeren kayanta tun ana biki saura kwana biyu, ba lefi sunyi qoqari matuqa, yayan UMMAKATI yamata kaya na bajinta duk da kasancewarsa d'an makaranta, gaskiya yayi qoqari matuqa, haka mamanta ma ba'a barta abaya ba, tayi abinda uwa takema y'arta yayin Auranta,

Ayau jumma'an da aka d'aura auran ayau d'in danginsu Hajjiya Kakah da qanwar momy sukazo d'aukar amarya, y'an uwan RAHMA biyu wato y'an matan gidansu sa'o'inta sun biyo UMMAKATI dan sukaganta, duk da matuniyar fad'ansu ce sunyi kewarta sosai, musamman da rayuwa ta juya musu, yanzu iskanci yinsa suke fiye da yanda RAHMAN tayi nata, yanzu dansu kwana a waje da maza ba wani abu bane, wata d'aya da tafiyar RAHMA kaduna ummi tayi ciki,😳 Mahaifiyarta na kici kicin zubarwa saiga Suwaiba da nata cikin, nan itama mahaifiyarta tashiga tashin hankali suka had'e a d'akin iyami suna tattauna me zasuyi akan lamarin, gashi dai RAHMA shuru ba amo ba labari, da alama tana cikin kwanciyar hankali, qilama ta yarda da mijin nata, yanzu dole su share batunta sunemo mafutar yanda zasuyi...

Sam sun manta Maman RAHMA na gidan suke wannan batu, aiko ajiye wanke wankenta tayi, tayi d'akin Iyamin ta kallesu dukkansu ukun, wato Iyami Asabe Lantana, ta girgiza tace, Rayuwa kenan, duk abinda zakayi idan bazaka dinga tuna Allah ba toko zakaga ba daidai ba, kunata jifan y'ata RAHMA da mugun kaba'i kan karuwace, karuwanci take zuwa, ba mara kunya y'ar iska kamarta, yau gashi kuma naku y'ay'an sun zama haka, har qari sukayi kan abinda ita batayi ba, gasu sunje sun jajib'o muku ciki, cikin da kuka dinga fatan agani ajikin RAHMAN, gashi yau shine ajikin y'ay'anku, shiyasa akace idan zaka gida ramun mugunta ka ginashi karya wucce tsayinka, kunje kumma y'ata asiri saboda baqin hali irin naku, saboda kawai mahaifinta yana santa, yanzu gashi asirin ya koma kan y'ay'anku fiye da yanda kuke zato, RAHMA dai tana d'akin mijinta, kwanciyar hankali kuma shike sawa aji mutum shuru a d'akinsa, RAHMA nacen tana zama da mijinta lafiya da abokiyar zamanta, kullum jifanta nake da addu'ar kuma nasan bazata faɗi qasa banza ba, Allah karaba mumini da baqin hali irin naku, tana gaya musu hakan ta ficce daga  d'akin takomo wajen wanke wanken ta....

 

Nan ko Kunya ta kamasu, suka rasa inda zasusa kansu, tare da mamakin ya akayi  tasan summa RAHMAN asiri, nan suka watse kowa tayi d'akinta

 

 

Haka suka tasa y'ay'an nasu agaba suna masu zaginsu, ahakan dai  sukaje suka bada kud'i aka zubar masu da cikin, ko sati ba ayi ba, saiga jamila y'ar asabe itama da nata cikin, nan itama uwarta tasata gaba zuwa wajen doctor dan acire, docton yace nata cikin baiyi kwari ba dan haka magani kawai zai bata tasha cikin ya fitta, to abin yazo da qarar kwana, nanko tana sha jini ya b'alle mata cikin dare, ba'a wayi gari da ita da rai ba, dan tace ga agrinku nan,

Nan ko fad'a ya kaure tsakanin Asabe da Lantana da iyami, suka dinga tonama kansu asiri, anan yaran gidan kaf da mahaifinsu suka san dama asiri sukama RAHMA, itadai Asabe faɗi take Lantana da iyami suncuceta da suka kaita wajen boka yama RAHMA asiri ga asiri ya koma kan y'arta wacce tafi so jamila gashi harya kaita ga Qatar kwana.

Sukuma faɗi suke ai bajanta sukayi ba, da yardarta da amincewarta sukaje wajen bokan..

 

Abin dai babu dad'in ji, dan har makwafta da sukazo jajen mutuwar jamila sanda sukaji batun, (Toh Allah ya kyauta, maman RAHMA tafad'i hakan)

 

Haka akayi arba'in d'in jamila RAHMA bata san ta mutu ba, dan babanta yace kar'a gaya mata, duk ran da tazo taji komai, haka yayun RAHMA sukayi nadamar tsanarta da sukayi arayuwa, yanzu santa ya kama zuciyarsu...

 

Toh shine fa yanzu ummi da Suwaiba suka nace sai anje kai amarya UMMAKATI dasu, dansuga y'ar uwar tasu RAHMAN, haka kawai ayanzu suke santa..

 

 

Sun sauka a garin Kaduna lafiya,  direct gidansu AMEER sukayi, wato gidan babansa, Hajjiya Kakah tayima UMMAKATI nasiha sosai, da akakai UMMAKATI wajen mama Saude fashewa da kuka mama Sauden tayi, kome tatuna oho🤔, haka dai tadaure ta karb'i amanar da aka bata ta UMMAKATIN, sannan akayi gidan momy da ita, Momy ma tayi mata nasiha sosai alokacin aka kaita gidanta, gida yayi kyau sosai, saidai shima irin na RAHMA ne, part biyu ne, dana UMMAKATIN dana abokiyar Zamanta me zuwa😃 idan Allah yayi.

 

RAHMA sai sauri take tasaka kaya taje gidan UMMAKATIN dan zance yazo mata yanzu gun matar me gadinsu cewar ankawo UMMAKATIN,

 

Tana kici cikin saka hijab saiga su sun shigo falanta ummi da Suwaiba, dake RAHMA a falan take saurin juyowa tayi ga kallansu.....

Ahaka tad'an tsaya shuru tana kallansu, aiko kan tace wani abu sunje da gudu sun rungumeta cikin murna da farin cikin ganinta, kallo d'aya RAHMA tayi musu taga qaunarta cikin kwayar idansu ba kamar da, da take ganin ƙiyayyarta a kwayar idan nasu ba.

A hakan dai ta nuna musu ƙauna wajen qara rungumesu.

 

Toya zakayi danaka😌 naka naka ne daɗin zama ne dai sai bare, haka suka zauna kan kuje tahau yi musu kallan mamaki, ta kasa hak'uri tace, "Ummi Suwaiba, yau kune da nuna min ƙauna, har kuna tsallan murna da gani na...

Suna jin abinda tace suka fashe da kuka, babu b'ata lokaci suka kwashe komai daya faru bayan barinta garin jos suka gaya mata, suka qara da cewa, "RAHMA kiyafe mana nuna miki tsanar da mukayi, ashe iyayenmu sune suka jefaki cikin wannan halin da kika tsinci kanki aciki.

Nan hankalin RAHMA ya tashi, cikin kuka tace, "Wallahi Ummi Suwaiba bana komai a iskanci, barni dai da shaye shaye, amma ban tab'a aikata zina ba, ayanzu mijina shine shedata, shine wanda zai faɗi kuyarda, gaskiya naji baqin cikin yanda kukayi ciki, musamman yanda jamila tamutu sanadinsa.

Kuka sosai RAHMA tadinga yi suna tayata, ba abinda take tunowa sai fuskar jamila yarinya me hankali acikinsu, sam bata magana sai in takama, duk tafisu ilimi, gaskiya mahaifiyarta tacutar da rayuwarta, da bata kaita gun doctor ya bata magani ba qila da har yanzu tana raye, koda yake dama shine sanadinta, bame canja hakan.

 

Nan RAHMA taqara rungumesu cikin jin tausayinsu, haka suka gaya mata sufa yunwa sukeji, dan basuci abinci a gidan momyn da Hajjiya Kakah ba, saboda d'okin da sukema kansu nasan ganinta.

Murmushin jin daɗi tasakar musu, nan tatashi da cire hijabinta tashiga kitchen had'a masu me dad'i, bata basu had'in data ma mijinta ba, kasancewar yau itace dashi, nasu daban tayi musu...

Aiko sunji dad'in kazar data gasa musu, had'e da dankalin data soya musu me d'auke da kifi, dama sunsan duk da rashin jin da RAHMAN tayi ta tsaya ta koyi girki Sosai wajen mamanta dan maman nata ba baya bace wajen iya girkin, duk tafi iyayen nasu.

Sanda RAHMA ta tabbatar sunci sun k'oshi Sannan tajasu zuwa gidan UMMAKATIN..

 

 

Wata runguma RAHMAN tama UMMAKATI, suka tafa suna masu murnar ganin juna, RAHMA ta kama baki tace, "wato ƙawancenmu bame rabuwa bane arayuwa, abu kamar wasa gashi mun qara had'awa matsayin makwaftan juna, waƴanda suka auri y'an uwan juna, gaskiya mu masu sa'a ne.😃

UMMAKATI tace, "Hmm, ai ina dad'a godema Allah daya bani AMEER, wanda bazai rabani da y'ar uwata ba.

RAHMA ta kalli shashin da aka kulle irin na UMMAKATIN, tace "Wato kema sai ammiki kishiya ko, UMMAKATI tab'ata fuska tace, "Bazaima soma yimin ba, danna shirya zama dashi, na shirya mallakarsa, wallahi RAHMA ba boka ba malam.

RAHMA ta harareta tace, "Dalla can,😏 ai tunda ABDUL yayi min kema sai ammiki, gwarama ki kwantar da hankalinki ayi miki mu had'e kai mununa mah kishiyoyin basu isa samun mazajenmu yanda suke so ba.

 

UMMAKATI tace, "Lallema, wallahi bazan kwantar da hankalina AMEER yamin kishiya ba, bare har na fara tunanin b'amb'arar mijina jikinta,  kai RAHMA bar batun nan kawai, dan jin sunanta ma abin takaici ne...

RAHMA najin haka tayi murmushi, tana hango fuskar AMEER, kallo d'aya zaka mai kasan zaiso mata over😆. Ita tadad'e da gane hakan..

Amma zataga ikwan Allah, badai UMMAKATIN tacika baki ba...

 

 

Y'an kawo amarya anan gidan UMMAKATIN sukace zasu kwana.

Yayinda Ummi da Suwaiba sukace a gidan RAHMA zasu kwana, RAHMAN ko taji dad'in hakan, harta yanke shawarar zata kwana tare dasu saidai ABDUL yayi hak'uri da ita yau, tunda gobe zasu koma bazata barsu haka su kwana su biyu kuma a d'akinta ba, idan tayi musu gaskiya bata kyauta musu ba, gwara taje ta kwana dasu susha hira suji dad'i...

 

 

 

Qarfe takwas ABDUL ya dawo gidan, yana shiga part d'inta ta rungumesa kamar dama jiransa take, nan yahau kiss d'inta cikin so da qauna, daqer ta ankarar dashi y'an uwanta na falan fah🤥,

Juyawa yayi ya kallesu cikin shauqi yace, "Sannunku.

Suka sakar mai murmushi cike da sha'awar yanda yake ƙaunar y'ar uwar tasu suka cemai, "Yauwa sannu.

Yace "daku akazo kawo mana amaryar tamu ne.

Suwaiba tace, "Eh..

Yace "Hakan yayi kyau, yasu mamana da sauran y'an gidan.

"Suna lafiya, Ummi ta amsa mishi.

Ahankali ya rad'ama RAHMA tabiyosa part d'insa a kunne.

Bayan ta bishi ta tayasa rage kayan jikinsa, wanka ya shiga namma tatayasa yi, bayan sun fito still taqara tayasa kintsa kansa, yaci abinci, kana ta zauna kan cinyarsa tafara mai magana cike da shagwab'a. "Sha kallona, dama ina san kabarni yau ranah d'aya naje na kwana da y'an uwana, kaga mun dad'e bamu had'u ba.

Murmushi ya sakar mata da jan hancinta yace, "har abada bazan iya bama kowa damar kwana dake ba, bayan kece dani, dan haka hak'uri zakiyi mukwana abinmu kamar yanda muka saba.

B'ata fuska RAHMA tayi tace, "gaskiya bazai yuhu ba.

Yace "da gaske... Ta d'aga mai kai, yayi murmushi daci gaba da cewa, toh shikenan tashi kije, na kira ZAINAB ta tayani kwanan ai ba wani abu bane.

RAHMA najin hakan ta qara murtuqe fuska tace, "shima bazai yuhu ba.

ABDUL ya harareta yace, "wannan ne kuma baki isa ba, ko kije ki musu sai da safe ko kuma naje na kira ZAINAB.

RAHMA ta shagwaɓe mai kan ita dai yayi hak'uri yabarta sannan karya kira ZAINAB. Yace tama sam bazai yuhu ba,

Tace "Yanzu tsakani da Allah kaga dacewar na barsu nazo na tare dakai.

ƙin kulata yayi ya hau yimata wani abun daban, ba shiri ta dakatar dashi ganin ya fara burkitata, tace mai bara taje tayi musu saida safe.

Tare suka tashi yana cewa muje ingaya musu da kaina, ta gallamar hararar wasa tace, "kayi dai zamanka kar jin kunyar tayimin yawa.

Yace "Wallahi da gaske nake tare zamuje dan bani san su zargeki.

Jin hakan yasa ta yarda sukayo shashin nata tare.

 

Sunko samesu suna kallo, ya kalli Suwaiba yace, "K'annena kuyi hak'uri ina buqatar matata zan d'auke muku ita zuwa gobe da safe, dafatan babu damuwa, tace mai, "Lah, babu komai, Allah ya tashemu lafiya,

RAHMA tace, "toh idan kungama kallansa gafa d'akuna nan kowanne zaku iya shiga ku kwanta, idan kuna buqatar wani abu kumin waya gata jikin bango, "Toh, sukace mata...

Saita shiga d'akinta tad'auko kayan baccinta ABDUL ya kama hannunta cike da ƙauna suka bar falan,

Nan ko suka bisu da kallo cike da sha'awarsu, "Gaskiya mijinta na santa sosai, Ummi tafad'i hakan dajan numfashi, Suwaiba tayi murmushi tace, "ai kallo d'aya zaki mai kigane yana ƙaunarta over, mudai iyayenmu sun cucemu da suka aikata mata wannan abu, gashi ita bai mata illa ba mu yazo yana mana, shiyasa akace idan zaka gina ramun mugunta ginasa daidai tsawanka, gudun kaga ka abka kakasa fittowa,

wallahi ummi yanzu haka gabana ƙaiƙayi yakemin, yana buqatar namiji matuqa.

Hawaye ya zuboma Ummi ta share tace, "hmm kedai abar kaza cikin gashinta,

 

 

ABDUL ya nace bazai bar RAHMA takwana dasu bane dan bai manta da yanda suke qinta ba, kamar yanda mahaifiyarta tagaya masa, yana san ya nuna musu akwai so da qauna matuqa tsakaninsa da RAHMA...

 

Barin RAHMAN yayi a room nasa yaje duba ZAINAB, sanda ya tabbatar da lafiyarta sannan ya dawo ga RAHMAN, lokacin tacanja kaya zuwa na bacci, shigar ta shigesa Sosai, nan dai sukayi kallo sama sama dake hankalinsa yana kanna fulaninta, baija lokacin wajen ram dasu ba...

 

 

 

 

Washe gari kan RAHMA tafitto daga part d'in Abdul Suwaiba da ummi suka gama mata komai na gyaran d'aki, duk da d'akin ba datti bane dashi amma da suka qara gyara mata ya qara kyau sosai, tajiko daɗin hakan da suka mata, tare suka shiga kitchen suka had'a breakfast,

Takaima ABDUL da ZAINAB nasu dining d'insa, kana takasa nasu ita da y'an uwan nata a dining d'inta..

 

ABDUL yaji haushin qin ganinta da baiyi a dining d'in nasa ba, dama bata tsaya tayasa wankan safe ba bare aje maganar shiri, dan haka daya tashi tafitta daga gidan ko bin takanta baiyi ba,

 

Dan tariga da ta shagwaɓasa akan komai, komai ita take masa, idan kaga yana yin abu to katabbatar tare sukeyi.

Sam ZAINAB bata san da hakan ba, ita bata wani shagwaɓasa akan komai, sam tunaninta baima kai wajen ba.

Dan inda yakai wajen da zata dinga masa koda ko batada ra'ayin hakan.

 

RAHMA bata yarda da fushinsa, dan tana mai abu idan taga ya b'ata masa rai nan take shawo kan matsalar tun da wurri, shiyasa da yanzu ya ficce baibi takanta ba, sai tayi saurin keb'ancewa takirasa tana basa hak'uri dan tasan lefinta, daqer ya saurareta, ita dai data samu ta samu kansa kashe wayar tayi tana mamakin baqin hali irin nasa🤔 ita da y'an uwanta ya dinga nuna mata qiri qiri saidai tabarsu tazo garesa bayan ba dad'ewa zasuyi ba...

 

 

Haka dai ta had'a samu sha tara ta arziqi, atamfa bibbiyu tabasu, da leshi d'add'aya, sai kayan kwalliya dan tana dasu wadatattu a akwatin auranta, ABDUL ya kirata yace taje bedroom nasa ya ajiye mata dubu hamshin tabasu, tamai godiya haka taje tad'auko musu, qarfe biyu na rana nayi sukaje gidansu AMEER anan motocin da suka kawosu sukayi layi, ba b'ata lokaci nan suka shige dan komawa garin nasu jos..

 

 

 

Yau dai takama AMEER da UMMAKATI zasu angwance, hmm.. Mezai faru, bayan ABDUL ya ajiye ma UMMAKATI kazar amarci da madara yayi musu sallama yayi gidansa, daqer da sid'in goshi AMEER ya iya barin sukayi sallar godiya ga Allah har yayi mata tambayoyin da suka dace tabashi amsa dan itama duk rashin jinta tana da d'an sani akan addini, dan tare suka gama islamiya da RAHMA.

Kallo d'aya zakama AMEER kasan ahannu yake, tunkan sukai qarshen cin kazar tasu yahau nuna mata alamu, hankalin UMMAKATI ya tashi matuqa, haka dai tasaka kayan bacci tabishi d'akinsa kamar yanda ya umarceta da zuwa, AMEER jarumin na mijine, dan daga yanayin yanda yake sarrafata kad'ai tatabbatar da hakan, komai nasa daban yake da mazan da take harka dasu, da tafiya tai tafiya sai kawai AMEER yaga rami a bud'e, "kan uba... Ya faɗi hakan😆 duk da baya cikin hankalinsa, amma ya gane dan yasha hoda matan da dasu tab'a sanin namiji ba, dake UMMAKATIN tayi shaye shayen maganin mata yajita fiye da kowace y'a mace da yake watsewa dasu, yasani dama dole asamu bambanci, dan darajar matar Aure da karuwai bazai tab'a zama d'aya ba....

 

Daqer AMEER ya iya barin UMMAKATI, bayan yaje ya tsaftace kansa dawowa yayi kanta ya zuba mata ido yace, "Ke wane d'an bura uban ne ya hudamin ke awaje.

Dama gaban UMMAKATI bugawa yake yi, dan tunda taji yace bura uba,🤣 tasan sarai ya gane ita ba cikakkiyar mace bace.

Ahankali tace, "dan Allah AMEER kayi hak'uri..

Yace "inyi hakuri dame. Tace "Kayi hak'uri kawai....

Ai bai bari takai qarshen zancen nata da numfashi ba ya wani falleta da mari.. nan cikin tashin hankali taci gaba da cewa, Wallahi fyeɗe akamin🙆🏼..

AMEER yana san UMMAKATI musamman yanda tabashi wanda bai tab'a jin irinsa gun wata y'a mace ba,  dan haka ahankali yace mata, "gayamin waye yayi miki hakan..

Kallansa tayi taga idansa ya juya ya koma ja saita qara burkicewa tahau inda indar sanin abinda zatace mai...

 

 

 

_¶Follow_

_¶Share_

_¶Vote_

AUNTYN LUV💋

`´-`´-

“˜•

¸ª_`

*.¸¸.**.¸¸.*🙆🏻*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*  

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆🏼*.¸¸*

`´-`´-

“˜•

¸ª_`•🤱🏻

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

      A true life story

*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Page 20

 

 

"Dama dama, dama ana saura wata d'aya bikinmu nafito unguwa zuwa gidan wata qawarmu, to dake ban tashi dawowa ba sai dare akan hayar dawowar tawa wasu y'an iska suka kamani, har wani gida suka kaini, mutum biyu acikinsu sukamin fyeɗen, haka suka yadani bakin wani layi sai wani abokin yayana ne yaganni ya dawo dani gida, sanda nakai sati uku ina kwance a asibiti, Allah yasa ba ciki, mamana tace zata gaya maka, saina dinga rokwanta kan karta gaya maka dan nasan zakace bazaka Aureni ba, gashi ni bani da abin so kamarka, bani da abinda nake qauna sama dakai, dan Allah dan annabi AMEER karka juyamin baya ka rabu dani, Wallahi ina sanka, ina qaunarka bazan iya rayuwa babu kai ba, dan soyayyarka da manzan Allah kaji qaina karayu dani, wallahi ni marainiyace a soyayya, bani da kowa sai kai, idan kabarni bame iya rainon ZUCHIYATA, UMMAKATI takai qarshen zancenta da rushewa da kuka wiwi, kuka take kamar ranta zai fitta, duk da kukan akwai na kirsa saidai ta tsorata sosai da ganin yanayinsa, kuma wallahi har zuciyarta qaunarsa take, qaunar san zama dashi take, qaunar san rayuwa dashi take, qaunar san mutuwa dashi take...😭

 

Kowane namiji aduniya yana da tausayi saidai idan baki shirya mai kalaman dazaisa yaji tausayinki ba, musamman idan da akwai so, dole zuciya ta karb'i sakwan koda kuwa zata shiga wani yanayi bayan karb'ar sakwan.

 

Dan haka jan numfashi AMEER yayi da rintse idansa, yau rana d'aya, yaji ya tsani aikata zina, yana maseefar san UMMAKATI yaji ciwo da zafi aransa Sosai daya ganta tazo mai ahaka, nan kwakwalwarsa tahau tuno mai matan daya dinga watsewa dasu, tunani ya shiga yi kan ya mazajen auransu zasuji idan suka gansu a bud'e, yasan zasuji abinda yaji yau, gaskiya yayi nadama arayuwarsa, yayi nadama matuqa, nan tsanar zina ta dirsu a zuciyarsa, ya bud'e idansa yana me qarema kyakkyawar furkarta kallo, sam tunanin rabuwa da itama baizo masa kwakwalwa ba, dan yana mata wani so, musamman dayau yaji ainihin hak'ik'aninta, dan haka hawa kan gadan yayi ya kama fuskarta wacce take cab'a cab'a da hawaye, ga tsoransa nan mararan kwance a fuskar tata, Ahankali yahau lashe mata hawayen da aika mata da wasu shu'uman kiss,sanda ya mata san ransa kana yace, "wallahi my dear dazanga way'anda sukamin wannan b'arnar, wallahi daba abinda zai hanani kashesu da hannuna, naji kishinki matuqa, Sannan nayi miki afuwa, bana san wannan kukan dan haka ki dakatar dashi..

Murmushin jin daɗi UMMAKATI tayi da rungumarsa tana cewa, "Nagode da fahimtata da kayi mijina, naji na qara sanka da qaunarka

AMEER yayi murmushi dan ya dad'e da gane ba qaramin so take mai ba.

Haka ya temaka mata taje tayi wanka ta dawo ya rungume abarsa,

 

Hajjiya Kakah da momy da RAHMA su suka aika musu da abin kari da safe, abincin har yawa yayi musu, kallo d'aya zaka musu subaka sha'awa, dan amarcin ya baiyana garesu lokaci d'aya..

 

 

AMEER da UMMAKATI suna jin daɗin rayuwarsu sosai

Saidai Asati biyun Amarcin nasu kallo d'aya zakama UMMAKATI kasan ta fad'a ta rame, Dan AMEER murjeta yake kullum ba d'aga qafa, sam baya gajiya da ita, ta lura zatasha fama da shi sosai, duk yawan iskancinta tagane AMEER TANTIRAI ne kan harkar, idan sunayi duk da tasan baqar wahala take sha amma ji take kamar karsu dena..

 

 

 

 

*********

Wata biyu da auran AMEER da UMMAKATI ciki ya bayyana ajikin ZAINAB😃, ABDUL ya gane hakan ne yau da Duke zaune shida ita, dake itace dashi. Kusan qarfe goma na dare suna kallo, kawai saitata shi da gudu tayi toilet tadinga sharara amai, yabita cikin sauri yana mata sannu cikin tausayawa.. "Aunty wai me yake damunki ne, naga kwana biyun nan baki cika jin daɗin jikinki ba, daga kice kanki na miki ciwo saikice zazzab'i na damunki ko ciwan baya wai meyake faruwa ne.

Shuru ZAINAB tamai sanda ta tsaftace bakinta sannan tajuyo ta kallesa cikin wani hali tace, "Wallahi ABDUL nima bansan me yake damuna ba, gaya maka ne banyi ba, yau tun safe nake amai duk abinda naci saina amayar dashi,

ABDUL ya waro ido yace, "shine baki gayamin tuntuni ba,

"Kayi hakuri abin bai wani dameni sosai bane.

Jawota jikinsa yayi ya sakar mata kiss a kumatu yace, "Kodai nayi miki abinda sahibinki Salisu ya kasayi miki shine..

ZAINAB ta waro ido tace, "Me kenan.. Yace "Ciki mana.. Harararsa tayi da cewa, "Bana jin shine. Yace "Aunty ki yarda shine, dan duk wata alama tabayyana kanta gareki, bari ma na qara tabbatar wa , danna karanta shafin mata masu ciki da yanda yanayinsu yake a cikin littafin ANIL Wanda nake da tabbacin babu qarya cikin bayanansa. Yakai qarshen zancen nasa da zuge zip d'in gaban rigarta yana me qarema na fulaninta kallo, sun qara girma ainun, kallo d'aya zaka musu kasan da walakin goro a miya, nan sha'awa ta kamasa sanda ya biya buqatarsa hankalinsa ya kwanta, nan ya qara maida hankalinsa a kanta yaci gaba da cewa, Wallahi Aunty ciki ne dake, dan har jin daɗin da nake samu daga gareki ya canja, gobe ki shirya nakaiki asibiti anan zaki tabbatar da abinda nake gaya miki,  ZAINAB najin hakan ta rungumesa, cikin farin ciki take cewa, "Tunkan muje naji farin ciki ya mamaye zuciyata, Allah ya tabbatar min da alkairi, wallahi harna qara sanka mijina, shafa kanta ABDUL yahauyi cikin shauqin santa yace, "Nima haka my Aunty..

 

Washe gari tun da asuba yaje ya gayama RAHMA tayi breakfast dan ZAINAB bata jin daɗi, nan ko RAHMA ta shiga damuwa tace mai me yake damunta, yace saidai yakaita asubiti sunji komai, tadaiyi breakfast d'in da wurri, toh tace mai,

 

Haka taje tahad'a musu tazo da jera komai akan dining d'insa kana tadawo shashinta tashiga wanka.

Bata wani dad'e da barin wajen dining d'in nasa ba suka fito daga d'akunasu shida ZAINAB d'in, cikin kulawa yace mata bara yaje ya kira RAHMAN suyi break d'in cikin sauri, toh ZAINAB tace mai dajan kujerar wajen d'aya tazauna zaman jiransu.

 

Hmm RAHMA na zaune gaban madubi tagama make-up kenan, saita tuna da shan maganinta na kullum, wato maganin hana ɗaukar ciki🤔, tayi tunanin tare da ita za'aje asibitin ne, shiyasata jawo durowarta tad'auko maganin ta b'alli ɗaya kamar yanda tasaba tana me faɗi aranta gwara tasha yanzun dan bata san tamanta shan maganin, musamman ayanzu da batasan yaushe zasu dawo ba, dama akwai ruwa agefanta dan haka saita zuba a cup, hannunta ɗaya ɗauke da maganin ɗayan kuma ɗauke da cup ɗin ruwan, zatasha kenan ABDUL ya shigo ɗakin.. Aiko nan tasake cup ɗin da maganin zuwa qasa.. Danta tsorata sosai da ganinsa, yau kuma wace ƙaddarace tazo mata haka, sam tamanta dazai iya shigowa akowane lokaci.

 

Wannan shine abinda RAHMA take aikatawa a b'oye ba wanda yasani, daga ita sai matar megadin gidan nasu data bata shawarar yin hakan...

 

ABDUL ya ƙaraso ahankali ya durƙusa ya ɗauki maganin, ya qare masa kallo a kwayar, kana ya maida kallansa gareta, nan tahau girgiza masa kai atsoracen, ya kalli durowar data buɗe yaga maganin da gidansa, ba ɓata lokaci nan ya ɗauki kwaninsa maganin yahau karantawa azuci, nan ya waro ido cikin tashin hankali ya kalleta yace, "Baby..😨 Maganin hana ɗaukar ciki kike sha.. Ya faɗi da sanyin murya..

 

Hawaye ne ya zuboma RAHMA, nan zuciya tafara tuno mata wata hira da sukayi shi da ita...

 

 _Baby ina san naganki da cikina, inasan yara da yawa, bansan wane farin ciki zanji ba idan naganki da cikina, alokacin murmushi tayi mai tace, nima na damu naganni da cikin nan naga farin cikin dazan ganka ciki, ya mata murmushin shima da bata amsa, zan dad'a qoqari dan naga kamar bana dagewa, ta waromai ido da cewa, wallahi kana dagewa dan Allah karka qara k'aimi, danna tabbatar  idan kak'ara kaimin kwantar dani zaka dingayi, ya rungumeta cike da qauna yace, Allah ya bamu masu albarka nan kusa, ta amsa mai da ameen_

 

Ayanzu kasa bashi amsa tayi, yaqara cewa, Tambayarki nake Baby, maganin hana ɗaukar ciki dama kike sha.

 

D'aga masa kai tayi alamar eh, da kuma girgiza masa kan alamar aa..

Yaci gaba da cewa, Toh wanne zan d'auka aciki, eh ko aa.

Ahankali tahau cewa, "Dan Allah kayi hak'uri wallahi bada niyar wani abu nake sha ba, ina Sha ne dan bani san na haihu yanzu, ina san nakai shekara huɗu haka kafin nayi cikin, kuma wallahi shawara akaban....

Ai bata idda zancenta da numfashi ba.. Ya ɗauke da wani shegen mari, takallesa a furgice hannu dafe da kuncin, tunda take a duniya bata taɓa ganin ɓacin ransa irin na yau ba, har idansa wani kad'awa yayi yakoma shi ba jaba shiba baqi ba... Haka ya nunata da yatsa yace, "Wallahi tallahi ba abin da zai hanani hukuntaki, dan kinyi min abinda tunda nake arayuwa ban tab'a jin ciwansa lokaci d'aya kamar Yanzu ba, badai ciki bane baki so yanzu, baki san haihuwa dani ko..

Da sauri ta katse shi da cewa, "wallahi ina san haihuwa dakai ABDUL, Narantse maka da Allah bawai ina sha dan karna aihu dakai bane...

Yace, "Dagaske...

Ta ɗagamai kai alamar tabbatarwa, yayi murmushin takaici daci gaba da cewa, Har azuciyata naso ganinki da ciki kafin zuwan na Aunty zainab, duk da nasan tafiki buqatar hakan, amma shikenan,  tunda haka kika zab'ar mana ni dake, zaki rayu ke kad'ai a haka, har zuwa shekarun da kikesan suyi kiyi cikin, idan lokacin yayi saikimin magana, nayi alƙawarin danne zuciyata, da ɗaukar mata hutu a soyayyarki  harzuwa lokacin, zan rayu da ZAINAB, na bata soyayyata gabaki d'aya da abin dake cikinta, daga yau bani san na qara ganinki a shinfid'ata, har sai lokacin dakika d'aukar mana ya cika, idanko naganki kitabbatar aranar zan nuna miki ni TANTIRI NE.

 

Ayanzu muna jiranki kizo muyi breakfast... Yana fad'in mata hakan yabar mata room d'inta,

Rahma tasaka hannu aka🙆🏼. Ta rushe da kuka wiwi😭 harda kiran wayyo Allahnta..🙁 Wallahi ta yarda da ainihin gaskiyarsa yake gaya mata kalaman, tunda take dashi bata tab'a ganin b'acin ransa irin nayau ba..

 

Haka tayi kuka tayi kuka tagodema Allah kana taje ta wanke fuskarta tafitto, suna zaune zaman jiranta, ABDUL yana danna waya ZAINAB ko kafama ƙofar da RAHMAN zata fitto ido tayi, tana san taga wankan nata dakyau irin tun daga sama har qasan kamar yanda tasaba,  aiko RAHMAN na fitowa suna had'a ido.

Da wani hali ZAINAB tad'auke kallan nata daga gareta, tana me faɗi aranta shegiya ita kowane kaya tasa wai saiyayi mata kyau ne,😊 kome yasa yau kuma batayi kwalliya oho...

 

Ita dai RAHMA da sanyin jiki ta qarasa dining d'in, ZAINAB tatashi ta zuba musu, bayan ta zauna ne ta kalli RAHMAN a karo na biyu tace, "Y'ar uwa ina kwana, Ahankali RAHMAN tace "Lafiya..

ZAINAB bata qara cewa komai ba tabi sawun ABDUL itama tafara cin abincinta.

RAHMA ko sai juya cokali take sam takasa cin abincin, ABDUL yana lura da ita, duk da cewar tunda tafitto bai kalleta ba, ZAINAB ko tayi mamakin hakan, dan tafi kowa sanin yanda idan RAHMAN tafitto yake shagaltuwa da kallanta.

 

Murmushin mugunta ABDUL yayi ya matsa kusa da ZAINAB sosai ya karɓi lokalin hannunta yana cewa, "My Aunty zan fara baki kulawa Yanzu tunkan atabbatar miki.

ZAINAB tayi murmushi da cewa, "bakaji yanda nake jin daɗin abincin nan bane, dan Allah bani cokalina na qarasa cinyewa, jiya ban iya cin komai ba, dan duk abinda na dafa bana iyaci, kuma aina gaya maka.

Kiss ya sakar mata a kumatu yace, "Ai ba hanaki cigaba daci zanyi ba, kawai zan temaka miki ne, yakai qarshen zancen da bata farfesun naman rago a baki.

ZAINAB ta lumshe ido tace, "gaskiya naji dad'i, dama hannuna ya gaji dakai komo, ABDUL yayi murmushi, "Kai Aunty banda qarya fa, tace "wallahi da gaske nake, yace "Ai tunda ina kusa dake daga Yanzu har zuwa randa zaki haihu zan dinga baki komai har sai kince ya isa..

Kiss tasakar mai a gefan kumatun shima tace, "nako gode my dear...

Murmushi ya dad'a yi mata daci gaba da bata Tana me jin daɗi, tunaninta duk d'okin cikin ne yasashi bata kulawa agaban RAHMA, hakan ya mata dad'i over.. Bata san shi da biyu ya bata kulawar ba, yayi hakan nr danya b'ata ran RAHMAN...

 

Aiko RAHMA ta shaqa dan bata tab'a jin masifar kishi irin nayau ba, hawaye yaso zubo mata tayi saurin mayar dashi, har zata tashi tabar musu wajen sai kuma tafasa, dan bata san ZAINAB tazargi taji haushin kulawar daya bata ne yasata tashi tabar musu wajen..

 

Sanda ZAINAB d'in tace mai ta k'oshi Sannan ya barta, ya tashi da d'aukar wayarsa ya kama hannunta ahankali ya d'agata yana cewa, "kidinga kulamin da kanki sosai my Aunty koda bana nan.. Tayi murmushi dace mai toh, tad'auki gyalanta dake gefe, dama da shirinta na zuwa asibitin da zasu tafito, haka hannunsa cikin nata suka ficce daga falan... Ko bin takan RAHMA basuyi ba..

 

RAHMAN na ganin ficcewarsu tasaki kukan dake cinta azuciya wanda takasayi a gabansu,😭 nan tayi watsi da dukkan kayan dake kan dining d'in, saiji kake fas fafas fas..😳 kasan cewar kayan duk tangaran ne🙁..

ZAINAB da ABDUL sunyi karar fasowar kayan... Amma ba wanda yayi magana cikinsu, tunanintu ko wajen matar megadi ne wani abu ya fashe. Sanda sukazo bakin ƙofar motar ABDUL d'in ya tuna bai d'auko mukullin motar tashi ba. Da kulawa ya kalli ZAINAB d'in yace ta jira shi Yanzu ya d'auko kin yana kan dining anan ya manta dashi, ta gyaɗa maka kai alamar toh...

 

Yana zuwa falan nasa yaga aikin da RAHMAN tayu🤔, yaga komai nakan dining d'in tayi watsi da shi, ashe k'arar da sukaji zubowar kayan ne, ya kalleta tana dai zaune inda take, zuciyar nan tacika tayi fam, sai zubar da hawaye take, ABDUL ya cije baki yana me qara bin kayan da kallo har dai yaci karo da mukullin motar tasa, ya d'auka daniyar ficce, aiko nan RAHMA taqara volume d'in kukan nata, bai juyo ba bare tayi tunanin zaiji tausayinta, ficcewarsa yayi yana me qara sakawa aransa kad'an tagani Wallahi sai yayi maganinta, tunda ya kwana da sanin ba qaramin so take masa da kishinsa ba, badai magani take sha ba, zaima dawo yaji y'ar iskar data bata shawarar, wallahi saiya kulleta koma wacece.

Haka ya bud'e motar tashi ZAINAB tashiga cikin farin ciki, megadi ya bud'e musu get sukabar gidan...

 

RAHMA najin fitarsu tatashi tahau zaga falan hawaye na zubo mata ga Zuciya na d'aukar zafi, cikin sauri tayi falanta da wata muguwar qara tace... "Uwani..

Nan matar megadi tashigo falan da sauri tana cewa. "Hajjiya gani, Allah yasa lafiya dan baki tab'a min irin wannan kiran ba..

RAHMA ta harareta tace, "Inafa lafiya, kin had'ani masifa da mijina, yau yaga maganin da kike siyomin, tunda nake arayuwata ban tab'a ganin b'acin ransa irin nayau ba, dan haka ina jinki mecece mafuta tunda kece kika bani shawarar shan maganin badan na tambayeki ba, saidan azarb'ab'i irin naki, toh wallahi kisani idan nashiga tashin hankalin dayafi wanda nake ciki ayanzu, kitabbatar kema saikin d'and'ani kud'arki..

Uwani ta waro ido, duk da ranta yayi fari, wato burinta ya kusa cika

 

 

 

 

 

 

 

Wai me yake faruwa ne🤔 jama'a.

Toh koma dai menene nidake dakai munsan rayuwa bata tafiya haka batare da matsala ta kusantota ba.

 

_¶Share_

_¶Vote_

_¶Follow_

AUNTYN LUV taku ce💋

l

 

 

 

 

'´-'´- “˜• ¸ª_'

 

*.¸¸.**.¸¸.*🙆*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*

 

 

 

 

 *TANTIRANCI KO KARUWANCI*

 

 

 

 

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆*.¸¸*

 

'´-'´- “˜• ¸ª_'•🤱🏻

 

 

 

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

 

A true life story

 

 

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

 

 

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ

 

Page 21

 

10 read more..🙁

 

Tace, "Innalillahiwainna'ilaihirraji'un, ashe shiyasa nagansa yau kamar yana cikin damuwa kamar kuma baya cikinta, lokacin daya fito tare da Hajjiya ZAINAB naga yana murmushi, lokacin daya qara dawowa nan ya fitowa naga kamar akwai abinda yake damunsa, Hajjiya kiyi hak'uri, dama dole wata ranah ya gani, kawai ki sanar dashi ke bakina sha bane dan wani abu, kina Shane dan kawai kisamu hutu kafin zuwan aihuwar taki, wallahi Hajjiya karki tsorata dan ayanda kike Yanzu yadace kid'an huta kafin ki haihu, dan Aihuwa ba dad'i bace, wahalace tsagwaranta, kinga zata hanaki soyayya da mijinki, zata hanaki sakewa akan komai, wallahi karki tsorata dan...

 

RAHMA bata barta ta qarasa ba ta katseta da cewa, "Kinga da Allah malama dakata, koyaushe maganar da kike gayamin kenan, inda karatu ne yaci ace na haddace shi, nidai nayi nadamar bin shawararki danayi, mijina yana san ganina da cikinsa amma nazo na biyema shirmammun maganganunki kamar wacce kanta ya kulle, kitashi kibani waje bani san ganinki, sannan Wallahi ki kuka dakanki dan bazan shiga masifar ni d'aya ba...

 

Jiki a sanyaye Uwani tatashi zata fitta sai RAHMAN taci gaba da cewa, kafin ki fitta kije falansa wajen dining ki gyara wajen ya b'aci..

 

"Toh  Uwani tace mata, haka ta nufi falan nasa tana zancen zuci, wato tunda take agidan bata tab'a shiga falan ABDUL d'in ba, gaskiya yau RAHMAN tana cikin wani hali, dan tasan da tana cikin hankalinta bazata sata zuwa ba, dan ita ko d'akinta bedroom nata bata bari tashigan mata, toh bare falan megida, dama ZAINAB ce take barinta ta shiga duk inda take so shashinta..

 

Haka dai Uwani tadinga bin falan da kallo, wato dai kud'i yana wajen masu shi, falan ABDUL d'in ya burgeta ainun.. Haka ta kashe kayan da RAHMAN ta zubda tas, ta goge wajen sosai, kana taje ta gayama RAHMAN tagama.

 

Nan RAHMAN taje ta kulle mai shashin nasa dake suna da kin shashin nasa ita da ZAINAB..  Haka tadawo ta d'auki gyalanta sai gidan UMMAKATI..

 

Suko su ABDUL bayan sun isa asibitin doctor ya tabbatar musu ZAINAB d'in na d'auke da ciki wata uku harda sati d'aya. Nanko ZAINAB tatashi tayi tsallan murna da mannama ABDUL kiss a kumatu, kana ta durk'usa tayima Allah suddada tana gode masa da kyautar daya bata, kana ta tashi taqara mannama ABDUL kiss duk ta rikice, da alama farin cikin yana san yayi mata yawa, ABDUL ya tashi ya kalleta da d'an murna ya rungumrta da cewa, "AUNTY na tayaki murna sosai, yanda yazo miki da lafiya ina miki fatan ki haifesa da lafiyar. Ta kallesa da murmushi tace, "Wallahi ABDUL bantab'a jina cikin farin ciki irin nayau ba, gaskiya kai jarumi ne, ka bani abinda ban tab'a tunani ba, yace ki godema Allah my Aunty..

 

Murmushi tayi da fad'in, "Allah shine abin godiya..

 

Haka doctor ya dinga kallansu da sha'awa, sanda suka gama murnar tasu shima ya nuna musu tashi murnar, da gaya musu tun yanzu zata fara zuwa awu, ABDUL yace ba damuwa, haka ya dawo ya sauketa a ƙofar gidan nasu, yayi office d'insa ZUCHIYA cike da tunanin RAHMA..

 

Bayan RAHMA tagama ba UMMAKATI labarin komai kallanta UMMAKATIN tahauyi kamar a lokacin tasan RAHMAN...

 

Cikin damuwa tace.. "Ammako RAHEEMAT kinban mamaki, wane irin sakarci ne wannan da zaki dinga afka kwayar hana d'aukar ciki a cikinki bayan kinsan baki tab'a haihuwa ba, kuma kina da kishiya kuma kishiyar nan kinsan ba zaman dad'i kukeyi ke da ita ba, zama kuke zaman kishi, kina da tabbacin tad'aura aniyar kwace miki mijinki, baya ga haka bata da wani buri saina ganin taga kunsamu sab'ani ke da shi, dake kanki ya kulle sai kawai kika manta da duk waƴannan abubuwan kika dinga shan maganin dan toshewar basira, Sannan kikaqi gayama kowa kika dinga sha'aniki, yanzu ke tsakaninki da Allah kimma kanki adalci,😏

 

Muma bar batun ABDUL Dan shi baida asara danga zahiri ya fara nuna miki alamu gaban kishiya, Dan Allah kimma kanki adalci...

 

 

 

Hawaye ya zubo ma RAHMA, tace, wallahi nayi nadama UMMAKATI, sai yanzu kaina ya bud'e, yanzu fa yayi min iyaka da d'akinsa, wallahi UMMAKATI ina san mijina, ina san rayuwa dashi, ina san kulawar da yake ban, ina san ABDUL fiye kaina, gashi ya shirya baqanta raina, d'azu ji nayi kamar zan mutu ganin kulawar dayake ba ZAINAB d'in..

 

Dan ALLAH kiban shawara ban saba fad'a dashi haka ba, fad'anmu baya wucce mintuna mun shirya amma yanzu kinga na kirasa yaqi d'aga min waya..

 

UMMAKATI tatab'e baki😏 tace, "Wallahi ni kodan saboda kishiya bazan sha maganin hana d'aukar ciki ba, bare ina uwar gida ina kallo amarya tazo ta rigani aihuwa, ga kishiyarki makira munafuka, na natabbatar saita baki wahala dan bazata hanasa bata kulawa agaban naki ba, wallahi kodan kiji ciwo saita dinga jansa, dama ai abin nema ne ya samu.

 

RAHMA ta share hawayenta tace, "Hmm Ƙanwar dai mahaifiyar mijinki ce.

 

UMMAKATI tace "Toh saime,😏 nifa bana santa, dama dai batazo a kishiyarki bace da zan sota.

 

Sam UMMAKATI bata shiri da ZAINAB, sai tazo gidan sau d'ari ta wucce shashin ZAINAB tashige shashin RAHMA bata leqa ZAINAB d'in ba, ita har tafi RAHMA kishin ma, tsakaninta da ZAINAB gaisuwa ne idan sunci karo a hanya, kuma har a zuciyar UMMAKATI bata san ZAINAB, ita hakan ajininta yake, idan akama y'ar uwarta kishiya ko qawarta toko ba ita ba wannan kishiyar koma wacece, UMMAKATI tana da kishi sosai Allah dai ya qare b'acin rana🙁, Dan shi kansa AMEER yana kiyaye mata akan kishi, dan ko irin wannan wasan na kishiya baya yi mata, gashi sai tsotseta yake sam taqi yin k'iba soboda masifarsa, lokaci lokaci yakanyi tunanin dole ya qara Aure Dan ya sauk'ak'a mata da futunarsa Dan yasan ba qaramin qoqari sosai takeyi dashi ba.

 

RAHMA taja numfashi tace, "Ni dai yanzu mecece mafita, jan numfashin itama UMMAKATIN tayi tace, "Mafita d'aya ce RAHEEMAT, shine kisan yanda zakiyi kishawo kan mijinki, ki nuna masa kinyi nadama, Dan fad'a da miji ba qaramin babban tashin hankali bane, ni dama can ba san matar megadin nan taku nake ba, haka kawai naji bata kwanta min arai ba, shegiya ashe tana tare da mugun tunani, gashi ta nuna akanki, yanzu qara kiransa muji kozai d'auka.

 

RAHMA ta d'auki wayarta ta qara kiran ABDUL d'in.. Lokacin ya isa office d'insa kenan yaga qara shigowar kiran wayar tata, wato a karo na goma sha uku, zai d'aga kenan AMEER ya shigo office d'in nasa hannunsa d'auke da wasu takaddu yana cewa, "Yau kayi latti sosai, alamar tanuna yau uwar gidace dakai, d'aga masa hannu Abdul yayi alamar ya d'an dakata da maganar tasa ya amsa kiran RAHMAN...

 

Bayan ya d'auki wayar ahankali yace, "Baby bafa wani abu bane ya sameni da zaki dinga kirana haka, RAHMA taja numfashi Wallahi jin muryarsa kad'ai tana saukar mata da nutsuwa, cikin kuka tace mai, "Dan Allah mijina kayi min afuwa wallahi bazan qara ba, dan nayi nadama, sharrin shed'an ne, wallahi ayanzu kaina ya bud'e na hankalta kwarai da gaske, dan Allah kajenye udirinka, dan ZUCHIYA bazata iya d'auka ba, kayi duba da kyawawan halin da musulinci ya koyar damu, afuwa, yafiya, tausayi, ba d'an adam d'in da baya kuskure arayuwa, Wallahi mijina zaka rasani idan har baka sanyayama zuciyarka ruwan sanyi ba😭... Takai qarshen zancen nata da qara volume d'in kukanta..

 

Murmushi ABDUL yayi, idan dai surutu ne ba wanda RAHMA bata iya ba, amma ta farnin wayo da tunanin sanin abin daya dace sai ahankali..

 

Cije bakinsa yayi dan baya san kukan nata yace, "Yanzu Baby idan na rasaki nayi yaya kenan da rayuwa, hmm zaki iya kirana amma karki qara min magana kan wannan matsalar, Dan bazan saurareki ba, wallahi Baby ba abinda zai hanani hukuntaki, kuma bana tunanin zan jenye udirina, ki kulamin da kanki dan yanzu bazan iya kula dake ba, zanji da amaryata da cikinta har Allah ya sauketa lafiya..

 

RAHMA najin hakan ta qara rushewa da kuka, Dan haka d'if ya kwashe wayar tasa dayin wurgi da ita cikin takaici.. AMEER ya tare wayar ya kallesa da damuwa yace, "meya faru ne haka kayi jifa da wayarka, ABDUL ya tashi da juyama AMEER baya yana kallan window yace, "Wallahi AMEER Rahma bata da hankali, shan maganin hana d'aukar ciki tadinga yi ban sani ba saiyau da Allah ya nunamin, AMEER ina san RAHMA Sosai ina san ganinta da cikina kamar yanda na gaya maka, amma dake wawiyace haka tadinga min b'arna ban sani ba, wai ba tunaninta bane, shawara aka bata, wallahi idan mahaifarta tasamu matsala AMEER na rantse da Allah me kankat zanyi mata, tunda nake arayuwata ban tab'a jin ciwan wani abu da akamin lokaci d'aya irin wannan ba. Santa nake over, tsaftatacciyar rayuwa nake sanyi da ita me d'orewa, amma ba komai, danna shirya koya mata hankali, tasan ciki da haihuwa dad'i ne dasu...

 

 

 

AMEER ya rabka salati yace, "kut😳. Maganin hana d'aukar ciki, Allah yasa ba UMMAKATI bace tabata shawarar, Dan Wallahi idan itace sainayi mata abinda har tamutu bazata tab'a mantawa dashi ba, ABDUL ina san yara nasan arawar kan UMMAKATI zata iya basu shawarar susha maganin... Kai bari in kirata yanzu.. kan uba🤥.. AMEER ya fad'i hakan hankalinsa tashe da lalubar num na UMMAKATI, Dan shi kad'ai yasan kansa akan san yara, yana san haihuwa matuqa, qilama yafi ABDUL d'in so.

 

UMMAKATI na lallashin RAHMA Dan taji duk abinda ABDUL yace mata.. Sai ganin kiran AMEER tayi, haka tad'auka atsora ce Dan taji faɗuwar gaba matuƙa..

 

Tace "Hello my dear kakai office lafiya... "Dakata da Allah, ya katseta da faɗin hakan, tare da cigaba da cewa, Wato maganin hana d'aukar ciki kukesha ke da RAHMA ko..

 

Cikin sauri da waro ido da cewa, "Wallahi wallahi ban tab'a shan maganin hana d'aukar ciki ba, yace "Toh meyasa kikaba RAHEEMAT shawarar shan maganin Dan tsabar mugunta.. Tace "wallahi bani na bata shawara ba, matar megidansu ce Uwani tabata shawarar shan maganin, Kuma wallahi ga RAHEEMAT d'in ka tambayeta ni bamma san kalar maganin hana d'aukar ciki ba, sakasancewar bata gaya min tana sha ba sai yanzu...

 

AMEER yaja numfashi yace, "hmma idamma kina sha zan kamaki ne, Wallahi ki kuka da kanki wannan ranar... Murmushi tayi da cewa, "inafa buqatar jin kwanka cikin marata, idan yazo kyakkyawan ƴanƴasa zanyi masa dan in nuna maka farin cikin kasancewarsa tare dani, Dan Allah ka yarda dani mijina bazan tab'a aikata maka hakan ba, itama kanta ya kulle ne, Dan bazan manta da hirarrakin da mukeyi da ita kan yanda tadamu tayi ciki Dan taga farin cikin da ABDUL zai shiga ba, dan Allah my dear ka kwantar masa da hankali yayafe mata dan tana cikin wani hali matuƙa...

 

Murmushi AMEER yayi da cewa, "yanda kike so haka za'ayi, amma yad'au zafi sosai, danya gayamin bai tab'a jin ciwan wani abu lokaci d'aya irin wannan ba, zan sashi ya sauka ammafa sai a hankali... Yana gaya mata hakan ya kashe wayar da kallan ABDUL Wanda tunda ya juyamai baya bai qara juyowa ba, ahakan AMEER ya gaya masa yanda sukayi da UMMAKATIN,..

 

Aiko afusace ABDUL ya juyo ya kalli AMEER yana cewa.. "Kan uba😳 MATAR MEGADI.. AMEER ya d'aga masa kai alamar tabbatarwa.. Nan ABDUL ya zari mukullin motarsa da wayar tasa ya ficce daga office d'in.. AMEER ya dafe kai, yasan ABDUL bai iya d'aukar abu da sauqi ba wani lokacin,....

 

***********

 

Abin daya faru shine, Auran ZAINAB da sati uku tazo gidansu Dan gaisar da Hajjiya Kakah, toh sun samu sab'ani dan fitar Hajjiya Kakan kenan taje asibiti kamar yanda tasaba zuwa ana duba lafiyarta..

 

ZAINAB ta zauna tana hutawa, kawai sai mama Saude tashigo falan da sanyin jiki, kallo d'aya ZAINAB tayi mata tausayinta ya kamata, duk ta canja ta kod'e kamar ba ita ba, Hajjiya Kakah tabata labarin yanda kishiyar tata take nuna mata wasu abubuwa danta dinga baqanta mata, tasani sune suke damunta suka hanata nutsuwa, dama kallo d'aya tama matar baban AMEER d'in tasan ba qaramar wayayyiya bace, hmm ita tasani dan ita tajama kanta, da bata aikata baqin halin data dinga nunama ABDUL ba ai da Auran nata bai mutu ba....

 

Katse ma ZAINAB d'in tunani tayi da cewa, "k'anwata kiyafe min, Dan nayi nadama, ina cikin wani hali matuƙa.. Ta faɗi hakan da rushewa da kuka, nan tausayinta ya qara kama ZAINAB, sai taci gaba da cewa, Rayuwar babu dad'i kwata kwata, yanzu Aure nake sanyi ko nasamu sa'ida cikin al'amurana.

 

ZAINAB taja numfashi tace, ba komai nayafe miki Aunty, kuma kidena kuka insha Allah zakiyi Aure nan kusa..

 

Mama Saude ta share hawayenta tace, "Nagode ZAINAB, ayanzu ke kad'ai kika ragemin, kiji tasayina ki sake dani kona samu kwanciyar hankali, ZAINAB tayi murmushi da kama hannunta tace, "Karki damu Auntyna, ina sanki dama ni halinki na tsana, insha Allah zakiga canji atare dani..

 

Murmushin yaqe mama Saude tayi mata....

 

Toh tun daga ranar ZAINAB take kula mama Saude, ranar taqara zuwa duba Hajjiya Kakan mama Saude ta kalleta da murmushi tace "niko ina san muyi wata magana dake, amma ina jin tsoran ku zaki fahimceni.

 

ZAINAB tace, "aa, faɗi ina jinki Aunty..

 

Mama Saude ta gyara zama ganin bakowa ad'akin dan Hajjiya Kakah alokacin ma ta shiga makewayi...

 

Tace, "wani tunani nayi, naga kedai ba Haihuwa kike ba, kuma daga dukkan alamu ABDUL yana san haihuwa, dan naji ranar suna hira da AMEER yake cema AMEER d'in wai yana san yaga RAHMA da ciki, AMEER yace mishi toh Aunty Zainab fa, sai yace mishi eh kema yana san ki samu amma gaskiya yafi ya fara ganin RAHMA dashi tukunna dan yana da wani udiri aransa nasan yima y'an uwanta bazata....

 

Toh me kika fahimta anan, alamu sun nuna ABDUL yafi san RAHMA dake, kuma wallahi duk ran da RAHMA tasamu ciki babu makawa sai ABDUL ya juya miki baya, bar ganin yanzu yana wani ji dake, dazaran RAHMA tasamu ciki zaki fara fuskantar matsala dashi, zai juya miki baya matuƙa, zai dena baki kulawa a soyayyarku, ya dace ki zauna kiyi tunani, namiji dai ko ciki d'aya kuka fito dashi saiya nuna miki iyakarki, to bare mijinki, Wanda yake ganin aqarqashin ikwansa kike,..

 

ZAINAB tayi shuru cikin tunani.. Can tace, "Aunty bana tunanin ABDUL zai juyamin baya koya wulaqantani koya min wani abu dan kawai matarsa tasamu ciki ni ban samu ba, Aunty ABDUL yana sona, yana qaunata fiye da tunanin me tunani, na qara gane hakan ne ayanzu dana zama mata a garesa, aunty dan Allah kibar wannan zancen karki b'atamin tunani....

 

Mama Saude tayi murmushi tace, "Hmm yaro yaro ne baisan wuta sai in ya taka ta, ZAINAB har yanzu da quruciya atare dake, ina gaya miki wannan maganar ne dan nasan ayanzu babu wani batun kunbiya kunbiya tsakanina dake, Wallahi bazaki tab'a fuskantar matsala da ABDUL ba har qarshen rayuwa idan dai babu ciki ajikin RAHMA, idanko RAHMA tasamu ciki zakice nagaya miki, dan zakiga abubuwa iri iri, ke kinsan yanda d'a yake kuwa, ke kinsan yanda uba yake jin soyayyar d'ansa kuwa, ki kalla yanda idan kaza ta y'any'ashe y'ay'anta idan kika zo gareta zaki tab'asu take binki da caki, toh dabba ma kenan tasan soyayyar d'anta bare mutum, ZAINAB ko kiyarda ko karki yarda kan ABDUL rawa yake kan  yasamu ciki, wallahi da kunnena naji yana gayama AMEER wai yafisan yaga RAHMA tafara yin ciki kafin ke... Mama Saude na zuwa nan a zancenta ta zubo da hawaye, cikin kuka taci gaba dacewa, Wallahi haka kawai nake sanki ayanzu ZAINAB, sam bana san ki fuskanci kowace irin matsala arayuwa, musamman idan nayi duba da yanda ke kad'ai kika ragemin, bani da sauran masoya ayanzu sama dake..

 

ZAINAB ta fara share mata hawaye cikin tunani, tunani take tabbas zancen yayar tata gaskiya ne, amma zuciyarta taqi yarda ABDUL zai iya juya mata baya idan RAHMA tasamu ciki, Ahankali ta qara tsaida kallanta akan Mama Sauden tace, "Aunty to mecece shawararki, Mama Saude tayi murmushin jin daɗi, tace,  "shawara d'ayace, kisan yanda zakiyi kija ra'ayin matar megadin gidankun nan da kike aikota kawoma Hajjiya Kakah kayan alatu, kibata maganin hana d'aukar ciki kice taje ta rinjayi RAHMAN tabata dacewar yanzu kai ya waye maza basu san haihuwa da wuri, ta tsaya ta mori soyayyar amarci kafin tayi, kinga idan akaci sa'a taji zancenta, nasan idan tad'auki shekara d'aya tana sha dole mahaifarta talalace, kamar yanda naji ana faɗi a gari, kinga ita babu ke babu, ba asiri kika mata ba bare ki d'aukarma kanki zunufi, Sannan ba samun cikin tayi kika zubar mata ba bare nanma ki d'aukarma kan naki zunufin..

 

Wannan itace shawarar dazan baki, kuma itace mafitta agareki...

 

ZAINAB taja numfashi tace, "koma dai miye dole nad'auki alhakinta idan nayi mata hakan, sam bazanga daidai ba tunda na manta Allah nanan, kawai Aunty mubar batun nan, yarinyar bata tab'amin komai ba, sai kishin dai dake shiga tsakanina da ita, kuma wannan akowane gida akwaishi saidai in babu kishiyar..

 

Mama Saude tatashi tana cewa, "ZAINAB kima kanki faɗa, shawara mekyau na baki, dan ina da tabbacin RAHMA na samun ciki bayan Abdul ya juya miki baya uwarsa Momy cewa zatayi ya sakeki dan baki da amfani, dama dai kingani ba wani sanki take ba, shikenan Saiki dawo gida muzama zawarawa biyu, kije kiyi tunani.... Tana faɗin mata hakan taficce daga d'akin...

 

ZAINAB tayi shuru, itafa Gaskiya tanasan ABDUL, Yayi mata 💯 arayuwa, komai nasa daban ne, tana sanshi tana san qarashe rayuwa dashi, tabbas mutuwa zatayi ram da ita idan har momyn nasa tasa ya saketa...

 

Haka ZAINAB ta koma gidanta koda wasa bata gayama Hajjiya Kakah hirar tasu ba,

 

Ta d'auki kwana biyu tana tunanin zancikan mama Sauden, dama ta kwana da sanin ABDUL yafi san RAHMA a soyayya fiye da ita, duk da yana qoqari sosai wajen kare kansa dan karta gane hakan.

 

Nan sheɗan ya buga mata ganga kan zancen da mama Saude tagaya mata gaskiya ne, kawai taje wajen matar megadin nasu tayi yanda tace mata...

 

Nan ko babu b'ata lokaci ZAINAB tayi wajen matar megadin nasu, tagaya mata udirinta,

 

Uwani tanuna alamar tsoro, tace "Ranki ya dad'e bazan iya ba gaskiya, dan na lura me gidan yana santa sosai kamar yanda yake sanki, ina tsoran randa zai sani itama tasan yaudararta nayi na shiga uku..

 

ZAINAB tace, "common Uwani, saikace ba y'ar gari ba, bata yanda za'ayi tasani bare shi megidan namu yasani, saidai inke zaki gaya musu.

 

Zan baki kud'i me yawa har dubu d'ari fa...

 

Nan Uwani ta waro ido😳.. Tace "Ranki ya dad'e dubu d'ari, ZAINAB tayi murmushi tace "Eh, dubu d'ari idan kinyarda ba. sannan idan muka samu nasara tad'auki shekara tana sha, zan qara miki wata dubu d'arin..

 

Cikin sauri Uwani ta had'iye yawu tace, na amince, wallahi na amince..

 

 

 

Nan Uwani taje d'akin RAHMA ta sameta tana karatu tace.. "Hajjiya karatu kike ne, RAHMA tace mata "Eh..

 

Saita zauna tace, "Dama inasan magana dake ne.

 

RAHMA ta'ajiye littafin hannun nata wato. *MATAR KAMAL* littafin rahama muh'md rufa'i Nalele, wannan karan ita kuma tabama karantawa..😂

 

Tace "ina jinki Uwani...

 

Uwani ta gaya zama tace, "dama shawara zan baki, ganin danayi megidan nan yafi sanki fiye da ZAINAB, me zaisa baza kiyi abinda zaisa ya qara sanki ba.

 

Rahma tayi murmushi tace, "hmm, Uwani kenan, Uwani sarkin tsegumi, kawai bani insha, ba wani batun kunbiya kunbiya gayamin abinda kike san gayamin dan bani san yawan magana.

 

Uwani tayi murmushi tace, "Dad'ina dake Hajjiya saurin gano mutum, dama ce miki zanyi, mezai hana kiyi tsarin iyali na shekara d'aya, wannan zai qara muku zazzafar ƙauna tsakaninki da mijinki, dan duk wata soyayya me tsayawa azuciya taqi fitta ta dad'i soyayyar amarci ce, Wallahi idan kika aihu yanzu shike nan kin shigo sahunmu masu y'ay'a, kinyi bankwana da soyayya har abada, mijinki zai dena ji dake, ke kanki idan akace kiyi soyayyar bazaki iya ba, saboda koyaushe tunaninki zai dinga tsayawa ne akan y'ay'anki, shikenan baki da aikinyi sai dattalin yara, amma idan kika qara shekaru kad'an yanzu kafin ki haihu koda kin haihun mijinki binki zai dingayi kamar jela, saboda ya rigada Yayi sabo da soyayyarki, saikiga ke kina tattalin yaranki shi kuma yana tattakinki, kinga kenan kinci riba biyu, ibar soyayyar amarci data haihuwa, dan Wallahi da gaske nake miki ba soyayya me tsayawa aran miji sai soyayyar amarci, idan kun dad'e kunayi kigani lokacin da kika aihu, idanko baku d'auki lokaci ba kunayi ba, shikenan saidai kiyi zaman hakuri da mijinki,

 

Ni dai nagaya miki hakan ne dan nagani agidan da muka fara aiki kafin muzo nan, sannan kuma zan gaya miki wannan amana, naji da kunnena kishiyarki ZAINAB tana fad'ama qawarta ranar nan, wai ita bazata haihu yanzu ba, dan tana san taci riba biyu..

 

Kunsan da ƙuruciya agun RAHMA, nan babu tunanin komai taji maganar Uwani,  musamman dataji ZAINAB ma tafad'i hakan, bayan taba Uwani taje ta siyo mata maganin tunanin ABDUL ne ya fad'o mata, Wanda kullum maganar kenan Baby ina qoqari amma har yanzu nakasa ganinki ciki, shuru tayi tana tunanin tasha ne kodai karta sha, candai kanta ya qara kulliyawa sai kawai ta share tace ai shekara d'aya ne, kuma dama ita bata da burin yin ciki awannan lokacin, bata san daga yin Auranta aganta da ciki, tana san tayi irin shekara uku ko huɗu kafin tayi cikin, amma idan cikin yazo mata taza taƙi karb'arsa ba, zata karb'esa hannu bibbiyu dan ganin farin cikin ABDUL, yanzu dai ta d'auki shawarar Uwani..

 

Amma maganin na kullum take sha, dan tayi binkice an tabbatar mata wannan baida matsala sosai..

 

Kowa da manufarsa cikin wannan abu...

 

Mama Saude ta bama ZAINAB wannan shawarar ne dan tana riqe da ita na hana yafe mata da tace ABDUL kar yayi, shiyasa tayi amfani da wannan damar dan tasan dole wata rana ABDUL yasani, idan kuma yasani dole zai canjama ZAINAB d'in, dan dagaske taji yana gayama AMEER cewar yafi san yaga RAHMA da ciki kafin ita, manufar dai mama Saude anan itace, ZAINAB da ABDUL su samu sab'ani ko tayaya, idan hakan bai yuhu ba zata shirya kashe mata Auren taga yaya zatayi🤔..

 

Megadin gidansu ZAINAB d'in kuwa ba kowa bane face d'an uwa ga Lantana kishiyar maman RAHMA,

 

Dan takanas ta kano Lantana taje qauyensu tace zata barma d'an uwan nata filinta na gado anan qauyen nasu wanda ta gajesa agun iyayensu kasancewar iyayen nasu sun rasu, da'aka raba gadan nasu to ita bata saida nata ba, shine tace mai indai zai mata abinda take so zata bar masa filin nata..

 

Toh kunsan mutumin qauye, ba kowa bane cikinsu yake da wadataccen tunani, dan haka nan yace mata menene abin da take so, tace mai so take yaje gidan RAHEEMAT a kaduna shida matarsa matsayin masu gadi, so take kota halin qaqa ya kashema RAHMAN Aure, babu b'ata lokaci tagaya masa asirin da suka ma RAHMAN da yanda ya koma kan y'ay'ansu, dan haka ya gayama matarsa komai dan suyi aikin tare..

 

Nan yace mata ba komai, ai wannan me sauqi ne, musamman yanda ba Wanda yasanshi agarin jos da kadunan, dan bai tab'a kawuma Lantanan ziyara ba, bare RAHMA tasanshi ko mahaifiyarta..

 

Nan Lantana tabashi adireshin komai, dan ta tambayi Baban su RAHMA cikin wayo da dabara, kan tana san wata rana takai mata ziyara dan tanemi yafiyarta, toh shine fa ya bata, dan yasan dama bai zama lalle tasan gidan nata ba duk da sunje bikin,..

 

Hakan yasa d'an uwan Lantanan shiryawa shida matarsa sukazo Kaduna suka rab'e jikin gidan ABDUL, daya fitto suka dinga rokwansa Allah da Annabi yad'aukesu aiki, daga qauye suke ainihi sun shigo birni ne dan aikatau, aikin ba irin Wanda basu iya ba, yanzu gidan da suke aikin ne megidan ya rasu, kasancewar bai tab'a haihuwa ba shine matarsa tace bata buqatar wani aiki yanzu, shine ta sallamesu...

 

Yanzu sun rasa inda zasu dosa

 

Nan tausayinsu ya kama ABDUL, yace sudawo gobe, zaiyi shawara da matansa..

 

Dama alokacin Dady yace zai samar ma ABDUL d'in megadi, dan haka nan batare da b'ata lokaci ba ABDUL ya kira Dadyn yace yayi hakuri ga wasu sunzo mishi suna buqatar gadin, dan haka idan yama Wanda yace zaituro masa magana toya bashi hakuri dan yasan waƴannan sunfi shi buqata.

 

Duk da hankalin Dady ba wani kwanta dasu amma haka dai yace mishi toh badawa..

 

Washe gari ko da safe kamar yanda ABDUL d'in ya gaya musu su dawo, bayan ya fitto daga masallaci ganin d'an uwan Lantanan yayi a kofar gidan nasa, nan ya tsaya yayi masa tambayoyi sosai kana yace zasu iya zuwa anjima su fara aikin, dama akwai wani shima zaizo yau d'in, zai dinga ba furanni ruwa da tsaftace harabar gidan...

 

Idan me karatu be manta ba, ya dace ya tuno ranar da ABDUL yake gayama su RAHMA zuwan megadin da matarsa..

 

Wannan shine mafarin dayasa d'an Uwan Lantana fara gadi agidansu RAHMAN..

 

Ko yaushe shida matarsa cikin kulla yanda zasu raba ABDUL da RAHMAN suke, amma duk a banza, dan RAHMA taqi sakewa dasu yanda suke so, ganin sun sake da ZAINAB..

 

Da aka kwan biyu, y'ar uwarsa Lantana ta kirasa awaya tana tambayarsa ya taji shuru, ce mata yayi abinda takeso zai d'auki lokaci, kawai tabar batun, dan shidai yasan bazai bar garin Kadunan batare daya cika mata burinta ba, wannan yasa Lantana tunanin kodai bazai iya bane, kodai ya canja shawara ne yasa shi ce mata hakan, wannan tunanin da tayi shiyasa watsar da lamarin, har ta karaya, tagayama su Iyami tace Auran RAHMA fa bazai kashuba, dan haka subar batun saka rai akan d'an uwanta, yanzu Susan yanda zasuyi da y'ay'ansu...

 

Wannan yasa abaya sukayi furucin yanzu ta y'ay'ansu suke..

 

Toh shine fa da ZAINAB tazoma da matar me gadin wannan batu sai hakan ya mata dad'i wato sun samu mafitta kenan,

 

Wannan shine abin daya faru me karatu

 

*******************************

 

Lokacin da ABDUL ya sauke ZAINAB agida bayan dawowarsu daga asibiti.. ZAINAB d'in ko zama batayi ba, Uwani tazo ta gaya mata yau ABDUL yaga maganin da RAHMA take sha..

 

Nan ZAINAB ta waro ido😳 tace "Garin yaya..

 

Uwani tatab'e baki tace, "Bata dai gayamin yanda akayi ya gani ba, amma tana cikin tashin hankali matuƙa, dan lokacin da takemin maganar kallo d'aya zaki mata kisan taci kuka...

 

Nan ZAINAB tafad'a tunanin🤔 ashe shi yasa d'azu ya bata wannan kulawar a gaban RAHMAN, shiyasa lokacin daya fitto daga d'akin RAHMAN taga kamar ransa a b'ace yake, to ita yanzu ya zatayi, tayi hakan ne dan bata haihuwa, yanzu ga ciki a jikinta, me zatayi kenan..

 

Ahankali ta kalli Uwani tace, "Gaskiya Uwani akwai babbar matsala,😌 dan yanzu haka ina d'auke da ciki..

 

Uwani ta waro ido tace, "innalillahi.. Acikin yaudarar danama RAHMAN nace mata baki shirya haihuwa yanzu ba..

 

ZAINAB tace, "Yanzu dai jeki shashinku idan na samo mafitta zan mini magana..

 

Uwani tatashi ta fitta, tana qara gayama mijinta hak'arsu takusan cimma ruwa, dan Auran RAHMA zai mutu nan kusa, musamman idan tayi kuskuran gayama ABDUL cewa itace tabata shawara....

 

Shiko ABDUL fitowarsa daga office d'insa bayan ya shiga motarsa kiran y'an sanda yayi yace su biyosa gidansu zasu kamamai wata mata. Ta bama matarsa shawarar shan maganin hana d'aukar ciki, yasa so su hukunta mai ita, Nanko sukace mai gasu nan zuwa...

 

Yana parking motarsa a kofar gidan nasa kamar ance UMMAKATI ta kalli windownta, nan tagansa da fitowar da yayi a fusace, nan tace da RAHMA.. "Ke d'ago kiga ABDUL ya dawo gida yanzu..

 

RAHMA tatashi cikin wani yanayi ta kalli windown nata, taga da gaske ne, aiko Cikin sauri tazari gyalanta taficce daga falan,

 

UMMAKATI nace mata tatsaya su qarasa yanda zasu shawo kan matsalar, ko kulata batayi ba ta ficce daga gidan, niyarta taje ta bashi hakuri ido da ido ko Allah zaisa ya sauko mata....

 

ABDUL na shiga gidan ya kalli megadin cikin b'acin rai yace.. "Ina matarka, yace "Tana ciki.. "Kirata.. Ya gaya mai hakan cikin sauri..

 

Nan d'an Uwan Lantana ya shiga kwad'ama matarsa Uwani kira,

 

Tana fittowa ABDUL ya watsa mata wani shegen kallo yace, "Kece kika bama Matata shawarar shan maganin hana d'aukar ciki ko...

 

Kan Uwani tayi magana saiga RAHMA ta shigo.. ABDUL ya kalleta da mugun kallo, yace, "Daga ina kike.. Kawar da kallanta tayi daga garesa tace, "Daga gun UMMAKATI..

 

Saiya maida kallan nasa kan Uwani yace.. "Magana nake miki kinyi min shuru..

 

Still yanzumma kan tayi magana ZAINAB tafito.. ABDUL kamar zai tsinkama Uwani mari yaci gaba da cewa, Wai ba magana nake miki ba..

 

Cikin ƙarfin hali Uwani tasosa qeya tace, "Ranka ya dad'e ni ban bama RAHEEMAT shawarar shan maganin hana d'aukar ciki ba, hauka nake dazan bata wannan muguwar shawarar😨....

 

RAHMA tawaro dukkan idanta tace... "Mene, me kike cewa, kina so kice bake bace kikazo har d'akina kika bani shawarar..

 

Uwani tagirgiza mata kai, tace, "Haba Hajjiya RAHEEMAT, idan kina so mubar muku gidanku ne saimu bar muku, amma ai bakya lanqayamin sharri kan abin da banjiba ban gani ba,

 

Nan numfashin RAHMA yafara sama sama ta kalli ABDUL wanda ayanzu ya maida kalansa gareta hawaye ya zubo mata tace.. "Na rantse da Allah mijina bazan qara munafurtarka akaro na biyu ba, wallahi itace tazo har d'akina tabani shawarar badan nace mata ina san hakan ba, dan ko a mafarki ban tab'a tunanin shan maganin hana d'aukar ciki ba, Amma tazo ta b'atan tunani, dan Allah kayarda dani, wallahi gaskiya nake gaya maka.

 

Nan ABDUL ya shiga tunanin kicin RAHMAN da Uwani waye me gaskiya, can yace wani abu sai Uwani ta kama baki tace.. "Kan uba😨.. Lalle me iya zama daku jama'ar birni saiya shirya. Dan kinga na rufa miki asiri, idan kin mata bara na tuna miki, da kunnena naji kuna magana da wata qawarki, kina gaya mata bazaki haihu da ABDUL ba, dan ba sanshi kike ba, dukiyarshi kike so, ke inda hali ma zaki iya kawar dashi, har qawar taki tana cewa aikinki nakyau, kikace mata ai kinfi qarfin haka, koba haka akayi ba😳.. Uwani takai qarshen zancenta da gwalaloma RAHMAN ido...

 

Wato idan tashin hankali yama mutum yawa harna qurar jikinsa me basa magana d'aukewa take nad'an wani lokaci..

 

Tota RAHMA kam tad'auke awannan lokacin, yayin da zuciyar ZAINAB tahau bugawa, dan tasan wannan ƙarin Uwani ne, sam RAHMAN bazata aikata hakan ba, haka kawai taji bataji dad'in hakan ba..

 

Tunda RAHMA take arayuwarta bata tab'a cin karo da annamimiya irin Uwani ba, nan takasa magana, ta qara kai kallanta ga ABDUL ta girgiza mai kai, tace "Qarya take min, ban aikata hakan ba, wallahi bamuyi wannan hirar da kowace qawata ba.

 

Kan ABDUL ya hautsine ya kasa gane lamarin,

 

Dan haka Ahankali Cikin sanyin murya yace da ita, "Baby... wai me Uwani take gaya min ne, ZUCIYATA tafara buqawa, Baby ni zaki kauda, kuma da gasken baki san aihuwa dani...

 

Ai kan yakai qarshen zancensa da numfashi RAHMA tatafi ƙasa luuu zata faɗi sumammiya.🤔 nan cikin sauri ya tarota ta zube jikinsa, kwayar idansu ta hud'u da juna, tace, "Wallahi Tallahi ban tab'a tunanin shan magani dan hana d'aukar ciki ba, ita tazo min da shawarar, kuma wallahi duk abinda tafad'i yanzun akaina duk qarya ne.

 

Ni banyi hira makamanciyar haka da kowa ba, qawata d'ayace UMMAKATI, idan nayi mata sharri kan wannan batu zanci amanarta, dan itama bata tashi sanin komai ba sai yanzu..

 

Atare suka lumshe ido shi da ita, yana bud'e nasa idan dan san cewa wani abu, sai kawai ya ganta a sume...

 

Nan yahau jijjigata yana kiran sunanta, amma ina tayi nisa asuman..

 

Daidai nan folisawa biyu suka shigo gidan.

 

ZAINAB tayi kitchen d'inta da gudu dan ibo ruwa a yayyafa ma RAHMAN..

 

ABDUL ya kalli folisawan yace sutafi kawai, danga matar da zasu kama nan tayi magana kan sharri aka mata kan batun da yaso su kamata dan shi..

 

Nan sukamai murmushi sukace.. Hakan bazai yuhuba sam, dole zasu tafi da ita acanne za'a tabbatar da gaskiyar zancenta....

 

Baice musu komai ba, danshi ayanzu tatashin RAHMA yake,  ZAINAB na kawo ruwan yahau yayyafa mata amma RAHMA taqi tashi..

 

Hankalin ZAINAB ya tashi matuƙa, gani take duk ita tajawo wannan tashin hankalin..

 

Lokacin da Uwani ta fuskanci y'an sandan tafiya da ita zasuyi ihu tasa musu, tana rokwarsu Allah da annabi karsu tafi da ita zata faɗi gaskiya...

 

ZAINAB najin hakan Cikinta ya d'uru ruwa.. ABDUL ko kallan Uwanin yayi da mamaki da tunani, ZAINAB ta kallesa tace "Dan Allah karkasa a kulleta, ya kalli ZAINAB d'in yace, "Aunty idan ya tabbata tunanin RAHMA yabata tasha maganin ko sun kulle Uwani dole zasu saketa, idan ko Tunanin Uwanin ne tabama RAHMA Wallahi bazan barta ba Aunty..

 

ZAINAB ta d'ora hannu aka🙆 tace "Mun shiga uku,

 

baice mata komai ba ya kinkimi RAHMA sai mota, addu'a yake cikin ransa Allah yasa RAHMAN ta farfad'o, wallahi da gaske yana ji aransa zai iya binta idan mutuwa tayi😭.. Kamar yanda ADAMS ya tafi NUFAISAT ta bishi a LEEKITAN ZUCHIYA😂

 

Haka folisawan nan sukayi gaba da Uwani tana kuka tana cewa zata faɗi gaskiya..

 

ZAINAB tace "wallahi Uwani idan kika tab'oni Cikin zancenki saina miki abinda harki mutu bazaki manta dani ba.

 

Folisawan basu bari Uwanin ta saurareta ba haka suka ficce da ita..

 

D'an uwan Lantana mijinta ko tunda yaga folisawan yayi sauri ya fad'a makewayin part d'insu, kunsan mutumin qauye da tsoran fulisawa😂

 

Nan akabar ZAINAB da safa da marya a harabar gidan

 

Tana me tunanin kodai takira ABDUL ta gaya masa Uwani maqaryaciya ce, duk abin data faɗi kan RAHMA qarya take.. Dan koda ta sakota Cikin zancen hakan ya tafi akan duk qaryar tata ne🤔...

 

_¶Share_

 

_¶Vote_

 

_¶Comment_

 

_¶Follow_

 

AUNTYN LUV💋

 

'´-'´- “˜• ¸ª_'

*.¸¸.**.¸¸.*🙆*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*

 

 

 *TANTIRANCI KO KARUWANCI*

 

 

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆*.¸¸*

'´-'´- “˜• ¸ª_'•🤱🏻

 

 

{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫

 

 

A true life story

 

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..

 

 

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ

Page 22

*To yazanyi daku🙁 nayi muku 16 read more* Sannan amin haƙuri wani abu ne ya shige min gaba..

Kai bazata kirasa ba, abin daya dace shine tabi bayan su Uwani ta tsoratar da ita,

Aiko da gudu tayi d'akinta tad'auko gyalanta tabi bayansu, basuyi nisa ba, dan haka nan ta tsaidasu tana me gaya musu dan Allah zatayi magana da Uwanin na minti d'aya.. d'aya daga Cikin folisawan yace mata hakan bazai yuhuba, Dan ya sab'ama doka, tayi dai hakuri sukai ofishinsu.

Nan tahau basu hak'uri, sukace toh takira ABDUL tukunna, tace dan Allah dai suyi hak'uri.

Haka badan sunso ba suka bata Uwanin.

Bayan sun d'an matsa gefe ZAINAB d'in cemata tayi.. "Wallahi Uwani idan kikace nice nace kibama RAHMA magani saina qaryataki, na kuma ce a kulleki a gidan yari har zuwa qarshen rayuwarki dan baqaramin qazafi kika min bah, duka zaki dinga ci ba dare ba ranah ga aiyukan gidan yarin masu matuqar wahala, dan haka sai kisan me zakice musu, kindai san nan ba qauye bane, duk abinda nagaya muku zartar da hukunci zasuyi akanki, Dan haka kikiyaye idan har kina so nasa ABDUL yace susakeki..

Hawaye ya zuboma Uwani, cikin matuƙar tsoro tace, "zan kiyaye, indai zakisa a sakeni..

Zainab najin hakan tanufi folisawan dace musu tagode, sannan sukayi gaba da Uwanin, ita kuma ta juyo gidan nasu hankalinta ad'an kwance..

Dame gadin nasu taci karo zai gudu hannunsa d'auke da kayansa, tace, "Aha, kai kuma miye haka, ina zaka da kaya kamar wani dillali.

Yace "guduwa zanyi, ganin y'an sanda sun tafi da  Uwani, kar suzo nima su tafi dani..

ZAINAB tayi dariya tace, "Da Allah kakoma ciki, ashe inaganinka kamar wani wayayye ashe abin ba haka yake ba, Uwani ko kwana bazatayi a wajensu ba! zansa ABDUL yace su saketa, yanzu idan katafi me hakan yake nufi.

D'an uwan Lantana yaja numfashi yace, "toh bara na koma, aina d'auka zasuzo su tafi dani ne.

ZAINAB ta wuccesa tana cewa, "aa, ka kwantar da hankalinka..

ABDUL da RAHMA ko gasu a asibiti..

Doctor yace RAHMAN ta samu suman ne sakamakwan jin wani abu daya furgitata da yawa, ABDUL yace mai haka ne,

Doctorn yace.. "idan hakan taqara faruwa da ita gaskiya zuciyarta zata karb'a hakan kuma zaisa zuciyar takamu da ciwo nan take

Dan haka ABDUL ka kiyaye idan har kana san ganinta da lafiya, ayanzu dai zata iya farfad'owa akowane lokaci, amma dan Allah kasan maganganun da zaka gaya mata kwawawa dan susa hankalinta kwanciya.

Sannan mun duba maka mahaifar tata, anyi mata hoto zuwa anjima idan sakamako ya fitto zamu gaya maka komai.

ABDUL yace, " Nagode sosai doctor, Allah ya kaimu fitowar sakamakwan lafiya..

"Ameen.. doctorn yace da barin d'akin yana me sha'awarsa da matan nasa, d'azu ya kawo ZAINAB yanzu kuma ya kawo RAHMA, duk matan nasa kwawawa dasu, kuma duk sun dace dashi..

ABDUL d'in ko zama yayi ya zubama RAHMA ido burinsa kawai yaga tatashi...

Wayarsa tayi qara yana dubawa yaga AMEER ne, nan ya d'auka da gaya masa yana asibiti ne tare da RAHMA.

AMEER yace masa meya faru, waye ba lafiya,

ABDUL ya gaya mai komai daya faru.

AMEER ya rintse idansa yace shi baiyarda da maganar Uwani ba, gwara da folisawan suka tafi da ita acan ta gaya musu gaskiya, Allah yabama RAHMAN lafiya, dama abin dayasa yanzu ya kirasa wasu takaddu ne Dady ya turo su yanzu yana buqatar saka hannunsa, dan za'a fitarma da wani kayansa ne wanda company ta had'amai.

ABDUL yace. "saidai kakawo min takaddun nan na saka hannun, Dan bazan iya tafiya na barta ita kad'ai ba, sannan Bana san ka gayama su Dadyn komai

AMEER yace "Toh, ba damuwa gani nan zuwa..

 

Kan AMEER d'in yazo doctor ya kawoma ABDUL sakamakwan lafiyar mahaifar RAHMAN, nutsuwa sosai ABDUL yayi ya karanta komai, binkicen ya nuna mai maganin bai fara mata illa ba, kuma akwai tabbaciwar zata iya samun ciki ako wane lokaci, dan maganin da take sha baya san tsallake, idan har ta tsallake sha tofa ciki zai iya shigarta akowane lokaci..

Har sallah raka'a biyu sanda ABDUL yayi a d'akin dan farin ciki da murna, amma duk da hakan saiya koya ma RAHMAN hankali dan nan gaba.

Bayan AMEER yazo ABDUL ya saka mai hannun kan takaddun fitar AMEER d'in keda wiya RAHMAN ta farfad'o..

Lokacin ABDUL yana bakin windown d'akin yana kallan harabar asibitin, wato dai ya juyama RAHMAN baya..

RAHMA tadinga qarema bayansa kallo can dai saita rushe da kuka, aiko da sauri ABDUL ya juyo ya matso gareta yana cewa, "Kukan kuma na miye my dear, ya kamata kisan yanzu kina Cikin wani hali, lafiyarki kawai nake fatan Allah ya tsayar miki da ita..

Ƙin kulasa RAHMA tayi taci gaba da kukanta..

Ganin hakan saiya d'agota ya rungumeta yaci gaba da cewa, my Baby zan iya jure komai agareki amma banda rashin lafiyarki da kukanki, dan Allah kiyi hak'uri zuciyarki tasamu nutsuwa yanzu, bana fatan na qara ganinki Cikin halin dana ganki d'azu.

Cikin shashsheƙa tace, "Bata yanda za'ayi nasamu nutsuwa da kwanciyar hankali bayan bansan awane matsayi nake yanzu acikin zuciyarka ba, nayi rantsuwa da Allah Uwani sharri tamin, kaji tausayin zuciyar dake sanka da ƙaunarka, ka yarda dani mijina, karka bani takaddata dan bazan iya rayuwa da wani namiji bayan kai ba, na gayama gaskiya ne, dan bana san na yaudari kaina.

ABDUL ya d'ago da fuskarta idansa cikin nata yace, koda kinyimin abinda yafi haka matata bazan tab'a sakinki ba, koda zaki zamar min matar jaraba bazan iya baki takaddar saki ba, zan iya jure komai cikinsu amma bazan iya jure ganinki babu igiyata akanki ba, idan kina wannan tunanin to kidena.

Shuru RAHMA tamai, saiya maidata kan gadan ya kwantar ya ficce daga d'akin dan kiran doctor yana me godiya ga Allah aransa daya tasheta.

Doctor daya qara dubata yace mai yanzu komai nata norma zasu iya tafiya.

Haka suka karb'i sallama suka baro asibitin,

RAHMA ta lura har a lokacin bai wani sake mata ba, hakan yasa zuciyarta taqi barinta cikin nutsuwa.

Yana sauketa a gidan wayarsa tayi qara, folisawan ne suke gayamai yazo yanzu yaji, dan Uwanin tafad'i gaskiya.

Aiko nan yayi ofishin nasu.

Bayan ya isa Ogansu yasa aka kira Uwanin, kallo d'aya ABDUL ya mata ya d'auke fuskarsa, wato taci duka ba d'an kad'an ba, duk fuskar nan ta kumbure, sai hawaye take abin gwanin ban tausayi, ogansu yace da ita, "Ga ABDUL yazo Saiki gaya mai da bakin ki..

Watoh lokacin da suka fara bin Uwani da lallami dan tafad'in masu gaskiya qin cewa komai tayi, ganin ashe ba dukkanta zasuyi ba tambayarta zasuyi, bata san dukkan yana biyowa baya ba.

Da suka fara dukkan nata rikicewa tayi, nan tagaya musu itace taba RAHMAN shawarar shan maganin.

Haka yanzu cikin zubar hawaye tace da ABDUL, "Wallahi nice naba RAHMA shawarar shan maganin hana d'aukar ciki, amma yanzo nayi nadama Dan Allah kasa a sakeni,

ABDUL ya maida kallansa kanta a karo na biyu, ya qare mata kallo tun daga sama har qasa, kana yace, "Menene dalilinki na bata shawarar, Uwani tamai shuru da sunkuyar da kanta qasa, ABDUL yaja numfashi da maida kallansa kan folisawan yaci gaba da cewa, Tana da dalilin daya sata bata wannan muguwar shawarar, Dan haka inaso kumaida ita ciki kuqara cin ubanta dakyau zata gaya muku Gaskiya...

Ai kan folisawan suyi Magana Uwani ta durqusa gaban ABDUL arikice tace, "kamin rai Alhaji, wallahi zan fad'a maka gaskiya.

ABDUL yace "Toh gaya min, ina jinki.

Uwani tace, "dama can munzo ne Dan mu kashema RAHMAN Aure, watoh ka saketa kota halin qaqa, dan mijina d'an uwane ga kishiyar maman RAHMAN, haka tazo har qauyenmu tace tabashi filinta na gadansu da aka raba musu kasancewar iyayen nasu sun rasu, Amma sai in har yazo nan garin Kaduna ya kashema RAHMA Aure, dan sunyi mata asiri ne danta dinga yawan gantali a duniya kartayi Aure har qarshen rayuwarta, toh gashi yanzu da tayi Auran asirin ya koma kan y'ay'ansu kuma makaryar asirin shine mutuwar Auran RAHMAN, idan har Auranta ya mutu to asirin zai karye.

Wannan shine yasa mukazo gidanka gadi danmu aiwatar da udirinmu, to munyi munyi bamuci nasara ba, shine na b'ollo da bata shawarar shan maganin hana d'aukar ciki, Dan nasan duk ran daka gani zai zamar muku tashin hankali qilama ka iya sakinta, shine d'azu na qara maka da cewa naji tana magana da K'awarta wai bata sanka, dukiyarka take so, wallahi duk na faɗin maka hakan ne danka saketa, Wallahi sharri nayi mata..

Hankalinsa ABDUL ya tashi matuƙa dajin waƴannan zancikan nata, damma ta b'oye mai zancen ZAINAB kenan🤔 Saboda tayi tunanin idan tasakota cikin zance ba mamaki ZAINAB d'in taqaryatata, ta kuma aiwatar da abin data gaya mata d'azu..

ABDUL ya tashi da matuƙar jin mamaki yace, "Yanzu kina nufin kishiyar maman RAHMA itace ta turoku gadi gidana dan ku kashema RAHMA Aure, shine kukayi amfani da wannan damar na bata magani danna saketa ko..

Taga mai kai tayi cikin tabbatarwa.

Yaci gaba da cewa, Wato dai duk abinda kika fad'a akan RAHMAN qaryane ko.

Namma d'aga mai kan tayi da cewa, "Wallahi qarya nake mata, dan Allah dan annabi kayafemin banzan qara ba

ABDUL yayi murmushi da kallan folisawan yace, "zaku iya saketa mu tafi,

Ogansu yace mai, "Mezai hana ABDUL, kawai saka mana hannu zakayi, Ammafa yadace kabar mana ita muje mu kamo mijin nata mu horasu ko zasu kiyaye gaba.

Nan cikin Uwani ya murd'a, hankalinta kuma ya tashi, nan Cikin tahau basu hak'uri..

ABDUL yace "Ku barta, abin dai da suka so bazai yuhu ba, tunda gashi asirinsu ya tonu, Yanzu Kuban takaddar nasa hannun.

Haka suka bashi ya saka musu hannun da sallamarsu suka bashi uwanin yace ta shiga mota sutafi..

Bayan sun iso gidan kallan megadin yayi wato d'an uwan Lantana ya watsa masa kud'in albashinsu yace. "Ina so ka tattara kayanku yanzu ku barmin gidana.

Ba musu dama shi ya Riga yayi shirinsa dan haka kallan Uwani yayi yace mata tashiga ta kwaso kayanta, aiko jiki na rawa taje ta ibo kayan nata suka ficce daga gidan..

ABDUL ya koma mota yayi shuru yana tunanin lamarin da abin daya dace yayi, candai daya samu mafitta saiya juya kan motarsa ya koma office...

ZAINAB na ganin yabar harabar gidan ta sake labulan windownta da kiran wayar Uwani, tana tambayarta meta gayama y'an sandan, cikin wani hali Uwani ta kwashe komai ta gayama ZAINAB d'in..

Aiko kyakkyawar ajiyar zuciya ZAINAB tasake tare da kashe wayar, gaskiya tayi nadamar abin data aikatama RAHMA, yau da asirinta ya toni ya zatayi..

RAHMA zazzab'i ne yake san rufeta, hakan yasa ta kwanta kan kujerarta me cin mutum uku, zuciya cike da tunani..

Tana cikin tunanin ne UMMAKATI ta shigo mata.

Ta kalleta da tausayawa tace, "Dan Allah RAHMA ki sauqaqama kanki, kar kisa wannan qaramar maganar takaiki da kwanciya, AMEER ya gayamin kuna asibiti d'azu, to ina shirin tawowa sai kuma naga dawowarku, Allah ya qara lafiya, Dan Allah ki sauk'ak'ama kanki..

RAHMA tad'an tashi da kallan UMMAKATIN ta kwashe komai daya faru tsakaninta da Uwanin d'axu tagaya mata..

Dan tsabar takaici da baqin cikin sharrin dataji Uwanin tayi mata, sanda hakan yasa UMMAKATIN zubda hawaye.. Tace, wallahi daba dan naga fitansu d'azu ba, danaje na jawota yanzu naci ubanta..

RAHMA tace, "kinga fitansu d'azu fa kikace, UMMAKATI tace mata, "eh naga fitansu, harda kayansu, ABDUL d'in ne naga ya dawo da Uwanin, naga ya watsama megadin naku kud'i sai kuma naga fitarsu..

RAHMA tace, "Qila ya koresu ne. Tace, "aikam, yanda naga fitansu ba fitan dawowa bane.

Dan Allah RAHMA ki kwantar da hankalinki, bani san tashin hankalinki, nasan baki iya shiga damuwa ba, abu k'ank'ani yakan iya jagula miki lissafi, me yawa yazo bai jagula miki ba..

RAHMA tayi mata murmushin yaqe kawai batare da tace mata komai ba..

Koda ABDUL ya dawo da daddare dama girkin RAHMA ne, lafiyarta kawai ya duba yaga tana normal saiya yayi shashinsa..

Tunani tashigayi tabisa d'akin nasa ne kamar yanda tasaba koko tabarsa tunda yasa mata doka, shuru tayi tana tunanin, candai ta yanke shawarar binsa.

A hankali tatura ƙofar tasa tashigo, nan taji zubar ruwa da alama wanka ya shiga, ya b'ata lokaci sosai kafin ya fitto, kallan juna sukayi, ya galla mata harara da cewa, "dokata nanan akanki, abinci dai idan kikamin kibarshi inda kika saba kaiwa, bacin hakan bana tunanin akwai wani abu dazai dinga shiga tsakanina dake, dan haka ki tashi kibar min d'akina, ai kina da naki d'akin ko.. Yakai ƙarshen zancen da watsa mata wani kallo..

Hawaye ya zubo mata ta kalleta sai yayi saurin d'auke kansa, ahankali tatashi taficce daga d'akin.

ABDUL ya rintse idansa abayyane yake cewa "anya kuwa zan iya jurema kaina wannan hukuncin dana faro shi kuwa my Baby..

RAHMA dai kuka tadingayi tsakaninta da Allah a d'akinta, koda wasa bata tab'a tunanin zata shiga wani hali akan namiji ba, sallah raka'a biyu tayi tasha magana takwanta.

Itako ZAINAB yunwa takeji dan duk abincin data dafa saita kasa ci, ayanzu dai ba abinda take jin sha'awa sai breakfast d'in da RAHMA ta had'a musu d'azu da safe, kallan agogo ZAINAB d'in tayi taga qarfe goma da rabi na dare.. Ahankali cikin sand'a tayo falan ABDUL duba dining ko Allah zaisa RAHMAN bata kwashe kayan ba, duk da tana tare da sanin bata yanda za'ayi taga kayan breakfast d'in awajen tunna safe..

Karaf suka had'a ido da ABDUL dake kan dining d'in, nan ya zuba mata ido yana nazarinta, ganin yanda tashigo falan da sand'a... Cikin in eh na tace, "a dama kana nan..

Yace "Aunty me kika fito yi awannan lokacin.

ZAINAB ta Sosa kai hawaye ya zubo mata cikin damuwa tace.. "ABDUL na rasa yanda zanyi, yunwa nake ji tun rana, komai na dafa bana iya cinsa, gashi cikina zai k'ogi yake min, ba abinda nake san ci ayanzu sai breakfast d'in da RAHMA ta had'a mana d'azu..

Cikin damuwa ABDUL ya tashi yazo ya kama hannunta yakaita har kan dining d'in, yace "Aunty kema kinsan abincin safe bazaita zama anan har wannan lokacin ba, yanzu dai ga tuwan shinkafa miyar egushi & farfesu, ki gwadaci ko Babyn nawa zai so su..

Dama tunkan yayi magana ƙamshin abincin ya cika hancinta, nan ta saka tuwannan a gaba dama malmala uku ne, ABDUL yaci d'aya, RAHMA ce zataci d'aya d'ayan kuma tabari gobe tayi d'umamansa, dan Allah yayi RAHMAN dasan d'umamen turo.. To koci batayi ba, haka ZAINAB tacinye malmala biyun nan, ABDUL yadinga binta da kallo, gaskiya kam tana jin yunwa, dan ba kowa bane zai iya cinye malmala biyu nan take, yasani RAHMA bataci ba, kuma taqi cin ne dan ya gaya mata dokarsa nanan akanta..

ZAINAB tace, gaskiya naji dad'in abincin nan, Allah ya sakama RAHMA da alkairi.

Ameen ABDUL yace mata.

Sai tasha ruwa tamai saida safe ta ficce daga falan..

ABDUL yabi bayanta da kallo, "ALLAH ya saukeki lafiya my Auntyna, ya faɗi hakan a bayyane..

Shi da RAHMA baccin nasu baiyi musu dad'i ba ko kaɗan, dan basu saba da hakan ba, dan ita RAHMA abin har san zama mata ciwo yaso yi, d'an kwana biyun nata da take riritashi da mijin nata yanzu yazo ya saka mata doka, wannan yasa tatashi da ciwan kai, duk da tana da tabbacin shima bai isa kwana babu tunaninta ba, amma tasani dole nata yafi damunta..

Bata san shiya fita shiga damuwa ba, kawai danne zuciyarsa yayi irinta y'ay'a maza, yanzu haka suna kan dining suna jiran fitowarta, dan tagama shirya komai na breakfast, saidai sunfi minti goma sha biyar suna jiranta har yanzu bata fittowa..

ZAINAB ta qosa taci abincin, dan haka iban nata tayi tahauci ABDUL yaja kujera baya yayi shashin RAHMAN..

Ganinta yayi a falo tana kallo cikin kyakkyawar shigarta na kayanmu na gida.. ABDUL ya galla mata harara yace.. "Wato kin manta ke muke jira ko..

RAHMA ta turo baki gaba tace, "daga yau kudena jirana, dan bazan qara yin break daku ba..

Yace "Da gaske..

Ta d'aga mai kai alamar tabbatarwa..

Ƙarasowa gareta yayi ya d'agata tsaye, idansa cikin nata yaci gaba da cewa.. Baki isa ki karyamin dokata ba, wannan ra'ayina ne nasan karyawa da matana da safe, kuma babu canji akan wannan ra'ayin nawa, dan haka wucce muje, idan kika qara yimin irin hakan zan d'auki mataki akanki, idan kuma kika nuna min ban isa ba, ai mahaifiyarki taban damar sanar da ita komai idan kikaqi yimin ladabi da biyayya acikin zaman takewar Auran namu....

Rai b'ace RAHMA tajanye kanta daga rikwan da yayi mata, hawaye ya zubo mata, ta nufi hanyar falan nasa, har takai ƙofa sai yayi saurin cigaba da cewa.. Kinga dakata malama, har saikin nunama kishiya kina fad'a da mijinki, ki duba yanda fuskarki take d'auke da hawaye da takaici, amma kike san zuwa inda kishiya take ahaka...

Tsayawa cak RAHMA tayi. Batare data juyo ba, ta share hawayen nata, sannan ta tsaya tsayuwar jiran qarasowarsa gareta.. ABDUL yayi murmushi, wato rashin jituwar tasa babu dad'i ko kaɗan, zanso kuga yanda ayanzu zuciyarsa tayi masa sanadin ganin hawayen nata..

Bayan ya iso gareta kama hannunta yayi ta fuzge da gallamai wata shegiyar harara, me d'auke da taikaci zallah, shima ya galla mata tasa, haka badan taso ba, tasakar mai hannun, saiya sakar mata kiss a kumatu yaci gaba da cewa, ashe haka kike kyau da harara, nan cikin qarin jin takaicinsa taqara gallamai hararar.

Bai rama ba amma ya qara kama hannun nata a karo na biyu, suka shiga falan nasa a tare..

ZAINAB tayi musu kallo d'aya ta d'auke kanta.

Ahankali tace da RAHMAN ina kwana, itama RAHMAN ahankalin ta amsa mata da lafiya

Daga haka dama ba wata hira tsakaninsu. Dan haka ABDUL na fara cin abincin saiya fara cakalar ZAINAB da magana.. "Aunty, zakiyi kyau da girman ciki, kidinga zama daqer tashi daqer, abin zai ban sha'awa matuƙa.. Zancen nasa yaba ZAINAB dariya, sanda tayi dariyarta san ranta tace, "Nifa zabanyi girman ciki ba, dan kaga yanzu wata uku harda sati d'aya amma ko alama bai nuna ba.

ABDUL yakai hannunsa kan cikin nata ya wani lumshe ido cikin nuna soyayyarsa ga cikin Sannan ya bud'e idan yace, "Allah ya fitomin dakai lafiya my Baby, macece ko namiji ne ban sani ba, amma zanso ki haifamin mace me kama dake sak, na saka mata kyakkyawan suna, sunan dazai dace da ita.

ZAINAB tayi murmushi tace, "Ameen my dear ameen, Allah ya saukenin lafiya dan ina ji a jikina kamar macen zan baka.

Murmushi yayi da sakarma cikin nata kiss, taji wani dad'i ya kamata, RAHMA ko rintse idanta tayi da maida hawayen dake san kawo mata farmaki

Nan bata ankare ba saiji tayi ABDUL d'in nayin waya da Momy, yana gaya mata ta kusa samun jika. RAHMA najin yanda momyn take nunamai farin cikinta, sannan ba wacce tazo bakinta sai RAHMAN, tambayarsa take RAHMA ce me cikin ko, yace mata aa Aunty Zainab ce.. Dake Momyn neman jikan take daga wajen kowannansu, hakan yasa taqara nunamai farin cikinta, ta kuma gaya masa anjima tana nan zuwa duba ZAINAB d'in.

Cikin murmushi yace mata toh Allah ya kawoki Momy.. Yana faɗin hakan ya kashe wayar, bai kira Dadynsa ba, dan yasan momyn zata gaya masa..

RAHMA tatashi tace ta koshi da kallan ABDUL d'in, taci gaba da cewa, "Allah ya dawo min dakai lafiya.

Ya sakar mata murmushi tare da tashin shima ya sakar mata kiss a kumatu yace, "ameen my dear, ki kula da kanki dakyau kinji..

Batace mai komai ba tabar falan, ZAINAB ta kalli abincin da taci, ko cikakken cokali uku batayi ba, tace da ABDUL.. "My dear. RAHMA fa bataci abincin nan da yawa ba.

Yace "eh, nagani, qila bata jin yunwar ne.

Tace, "Lalle kam ba mamaki.

RAHMA na komawa shashinta zama na musamman tayi, tahau tunanin ABDUL so yake ya kasheta tunkan kwanta ya qare..

Qarfe biyu na ranah momy tazo gidan nasu.. Ta nunama ZAINAB farin cikinta sosai, ZAINAB tayi mamakin hakan kuwa, dan yanda Momy ta nuna mata farin cikin nata kamar itace tasamu cikin..

Momyn tagane kamar RAHMA tana da damuwa, dan taga ta faɗa kad'an, ma'ana taɗan rame, da gaske daga jiya zuwa yau tad'an fad'a, tambayar duniya ba wacce Momyn batama RAHMAN kan tagaya mata meyake damunta ba amma RAHMA tace mata ba komai..

Haka Momyn tatafi zuciya da zargi..

Rayuwar gidan gabaki d'aya tacanja musu,  ABDUL yaqi dawoma RAHMA daidai, tun RAHMAN na kuka Yanzu har tafara sabawa dacin mutuncin da yake mata agaban ZAINAB, dan idan zasuyi breakfast sau dubu sai ABDUL ya bama ZAINAB kulawa sau dubun nan, kuma kallo d'aya zakama kulawar Kasan bata Allah bace, kasan ta baqanta ran RAHMA ce..

Ayanzu tun abin na damunta har yazo ya dena damunta..

Tsakaninta dashi gaisuwa ce da dafa mai abinci, sai idan tana buqatar kud'i tacemai zata d'auka cikin dirowarsa, bayan hakan ba wani abu da yake shiga tsakaninsu..

Gashi dai yanzu cikin ZAINAB wata shidda.

Bata da abinci sai girkin RAHMA, sam RAHMA bata san abincinta ne kawai ZAINAB take iya ci yazauna a cikinta ba, ABDUL ne kad'ai ya sani. Dan duk daran duniya ran da RAHMA ta karb'i girki tare da ZAINAB ABDUL yake cin abincin dare.. Kuma koda wasa RAHMA bata tab'a sani.. Ita dai tasan cin abincin nasa ya qaru, bakamar yanda suka saba ci tare ba.. Yanzu duk yawan abinci idan ta kai masa dining da daddare cinyewa yake, bata san tare sukeci da ZAINAB ba.🤣

Tsaf ZAINAB tasan tun ranar da ABDUL ya kori su Uwani har yau babu shiri tsakaninsa da RAHMA, tana tare da sanin basa kwana d'aki d'aya..

Gashi dukkansu sai ramewa suke, dan kallo d'aya zaka musu kasan basa tare da nutsuwa, wannan kad'ai ya isa tabbatar maka baqaramin qauna sukema junasu ba, ran ZAINAB ya b'aci matuƙa da gane hakan da tayi..

Fatar RAHMA ta goge ta qara haske saidai jiki kam babu shi, dan d'an jikin nata ya zube, kai kallo d'aya zaka mata kasan tana da damuwa.

Haka shima ABDUL, nasa zubewan har yafi na RAHMAN kaɗan haka👌🏻, dan shi har Dadynsa da Momynsa da Babansa ada da Hajjiya Kakah sanda suka sashi gaba kan yagaya musu meyake damunsa..

Amsar d'ayace yake ce musu ba komai, idan kuma sun matsa yace musu taifot da maleriya ne yake damunsa.. To sunfi yarda da hakan, Momy ko tayi tayi RAHMA tagaya mata matsalarta amma taqi.. Abin na damun Momyn matuƙa..

UMMAKATI ce tasan komai dayake faruwa tsakaninsu itama tayi tayi da RAHMAN kan ta qara komawa d'akin ABDUL da daddare koda zai mata rashin mutunci gwara ta jure ta mannemai su kwana gado d'aya tasan daga nan sai sauke dokar tasa amma fur RAHMA tace mata baza taje ba, itama Yanzu tayi zuciya, Wallahi saidai su mutu a haka, dadai ta qara zuwa d'akinsa..

UMMAKATI ta tab'e baki tace aiko zaku mutu ahakan, gashi nan sai qarewa kuke atsaye, ni a labarin masoya ma ban tab'a jin naku ba, zuciya naso amma gangar jiki taqi nuna hakan...

Shuru RAHMA tayi mata..

____________________

Toh yau dai tun safe RAHMA ta d'aura aniyar bin ta bakin UMMAKATI, dake ya kasance girkinta ne, bazata iya da wannan rayuwar ba, dan ita me lafiyace, bazai yuhu takashe kanta tun tana qanqanuwarta ba, dan haka wallahi yau duk bala'i sai ABDUL ya sauke mata wannan tsananniyar dokar tasa..

Bayan ya dawo gidan ya duba lafiyarsu shashinsa yayi, dan haka sai tatashi daga kan gadanta ta shiga toilet ta qara yin wanka tacanja kayan bacci, Ta mulke jikinta da humrarta me dad'in qamshi..

Sannan ta nufo shashin nasa.. Cak ta tsaya a bakin ƙofar da zata sadata da falan nasa, sakamakwan jin muryarsa da tayi da ZAINAB..

Kallan agogwan wayarta tayi, taga sha d'aya saura minti biyar wato goma da minti hamshin da biyar. 10:55pm.

"Ranar girkina, ZAINAB da ABDUL afalo suna hira, me hakan yake nufi, hakan yana nufin duk ran girkina abinda sukeyi kenan..

Ahankali ta durƙusa ta leqasu ta qasan ƙofar kasancewar ƙofar a bud'e take, da alama daya shigo dubata d'azu bai rufe ba..

Nanko tagansu zaune a dining kowannansu gabansa d'auke da plate d'in abincin data girka, da alama ABDUL d'in ya gama cin nasa ne, dan hannunsa d'auke yake da waya, yana dannawa yana kuma biyema hirar tasu, ZAINAB ko sai afa abincin take bakinta tana sakin y'ar dariya..

da alama hirar da sukeyi tana musu dad'i matuqa..

RAHMA na niyar janye kanta taga ABDUL d'in ya juyo da kallansa ga kofar da take Kallan nasu, sanda yad'an shagala kad'an da kallan kofar kana ya d'auke idansa daga kan kofar..

Dake kan RAHMAN a qasa yake hakan bai bama ABDUL d'in damar ganinta ba, dama shi qamshinta ya jiyo, aduk inda yaji qamshin nata to tana kusa wato tazo waje..

Yana da tabbacin kodai tazo d'aukar ruwa nata yaqare ko tazo d'aukar wani abu, jin suna tare shida ZAINAB hakan yasata juyawa, amma tabbas ko kaffara bazaiyi ba, yasan tanufa falan nasa...

Ahankali RAHMA tajanye kanta, hawaye ya zubo mata d'aya nabin d'aya, haka ta koma d'akinta.. Haba sai yanzu tagane, ashe ABDUL bashi d'aya yakecin abincin da take girka mai ba, shiyasa take ganin yana cinye komai baya ragewa, dake ZAINAB d'in ta iya wayo da plate d'inta take zuwa, wato taci aciki idan tagama tatafi da plate d'in nata dan karta gane..

Toh yau tagani Allah ya kaisu gobe zata nuna musu iyakarsu... Dama tana jin haushin ZAINAB dajin tsanarta aranta, dan bayan cin kashin da ABDUL yake mata a gabanta na nuna kulawarsa ga cikin nata, idan ABDUL d'in ya fitta office ZAINAB d'in fitowa take ta baje a habar gidan da y'ar taburmarta tata turo ciki gaba,🤣 sai RAHMAN take gani kamar ZAINAB d'in ita take turoma cikin, dan tana zama ne a fuskar windown RAHMAN, hakan yana qara b'ata ran RAHMA sosai, dan tayi imani da biyu ZAINAB d'in take zama a harabar gidan, imba da biyu ba tadinga shiga ciki wajen shaƙatawar gidan mana.

RAHMA tayi ma ZAINAB muguwar fahimta kan hakan, dan ZAINAB tana fitowa ne dan batajin daɗin zaman d'akin, idan kuma tace zata shiga wajen shaƙatawan gidan bata jin dad'in ƙamshin furannin wajen... Hak'ik'a cikin nata me tsurfa ne matuƙa, me saurin fusata zaiga kamar iyayi takeyi.. Toh RAHMA tayi amfani da wannan damar tayi rantsuwa ba abin dazai hanata had'a musu bom💣 gobe...

Haka tagoge hawayenta tayi sallah raka'a biyu dayin addu'o'inta na yau da kullum sannan ta haye gadanta taja bargo...

Har ABDUL ya gama shirinsa na fitta office RAHMA bata bud'e ƙofarta ba, dayazo dining ganin dining d'in yayi wayam,😄 sai ZAINAB dake zaune tana hammar jiran abinci, cikin wani hali ya nufi shashin RAHMAN, Nanko yaganta zaune a tsakiyar falanta ta baje tana breakfast d'inta hankali kwance, Farfesun naman rago tayi, gefe guda kuma kunun gyaɗa ne da alale, ta d'ago da kallanta garesa saita wurga mai wata muguwar harara, taci gaba da cin kayanta.

ABDUL yace, "Me hakan yake nufi, taqara kallansa da wata muguwar hararar tace, "hakan yana nufin nadena yimaka abinci, nadena had'a muku breakfast, nadena girka maka abincin dare...

Cikin Sauri ya katseta da cewa, "wannan zancen banza ne, Wallahi kinyi kad'an, ai zaman Aure aka kawoki yi, bazan gaban kanki ba...

"Da gaske.. Ta katse shi da faɗin hakan, kana taci gaba da cewa, Ashe kana sane da zaman Aure aka kawoni kike min abinda ranka keso, ka hanani kusantar shinfid'anka, ka hanani jin daɗin rayuwata, kullum cikin ƙirƙiro abubuwan da zaka baqanta raina kake, ka maidani banza kishiyatace mutum agareka, toh wasan ya tsaya a haka, yau zanga me zai tsallakeka daga fad'awa tarkona, musamman idan natuna cin amanar daka d'auki wata uku kana min, Wallahi bazan qara dafa maka abinci kazauna kai da ZAINAB kuna ci kana jifana da zazafan kalamai ba..

ABDUL ya harareta da d'aukar kanun gyaɗan gabanta da alalan ya ficce dashi daga falan ya kaima ZAINAB, yadawo ya d'auke farfesun gaban nata nan ma yakaima ZAINAB d'in yanace da ZAINAB d'in "Aunty yau RAHMA rikici take ji, wai bazata qara dafa mana abinci ba, Wallahi duk damuwata kece, Yanzu idan tadena ya zamuyi.

ZAINAB ta waro ido tace, "Na shiga uku ni ZAINAB, aiko babu yanda za'ayi saidai inje na rok'eta dan yanzu nafara san girkinta, dan Allah mijina kasan yanda zakayi da ita, wallahi akwai babbar matsala idan tadenayi...

ABDUL yace, "Kwantar da hankalinki my Aunty, zansan yanda zanyi da ita, Yanzu ga waƴannan dan naga yau kin tashi dajin yunwar sosai..

Murmushi ZAINAB tayi tace, "ashe ka gane, amma kai me zakaci.

"Aunty karki damu dani, zansha Lipton a office Yanzu zuwa ranah sai kisan abin da zaki girka min..

Tace "amma naso dadai ka karyan hakan zaifi tsari matuƙa..

Kanya bata amsa sai hango RAHMA yayi tana shiga motar daya siya musu dan zuwa anguwa cikin shigar doguwar riga, da alama tama direban Magana tuntuni, shiyasa tana zuwa tashiga ya jata dan ga get d'inma a bud'e yake, wato direban yama saban megadin nasu Magana ya bud'emai kenan..

Cikin sauri ya kira direban awaya yace dashi ina zai kai RAHMA yace mai tace gidan momy zai kaita, shuru ABDUL yayi da kashe wayar yana tunanin kalmomin data gayamai d'azu, tashi yayi da sakarma ZAINAB kiss a goshi yayi mata sallama, sanda ya shiga motarsa yabar harabar gidan kana ya kira RAHMAN a wayarta kira hau uku bata d'aga ba, ana hud'un ne ta d'aga dacemai, "Haba mijina, bafa wani abu bane zai faru dani kike min kira haka, ABDUL yayi murmushi danya tuna ranar daya gaya mata hakan.. Sai yace, "Zan gargad'eki ne kan kada kiyi kuskuran gayama momy kinsha maganin hana d'aukar ciki..

RAHMA tayi murmushi da cewa, "Haba my dear, saikace bani da wayo, aiko a mafarki bazan yaga mata hakan ba, dan nasan makomata awajenta, kawai abin dazai kaini wajenta daban ne, sannan kar kayi tunanin ba akanki bane, wallahi akanka ne da matarka ZAINAB, zaka san ka sakamin dokar shekara hud'u.. Ta faɗi hakan da kashe wayarta tana murmushi..

ABDUL yayi shuru cikin tunani, "Wai me yarinyar nan tashiryamin yau ne, ya faɗi hakan a bayyane, kana ya lumshe idonsa dan tuno da kwalliyarta da tayi, tayi kyau sosai, cikin shigar doguwar rigar, abu ja yana matuqar haskata, ga bakin nan nata yasha jambaki abin gwanin ban sha'awa..

Murmushi yayi daci gaba da cewa, wallahi nima baby nagaji da horaki haka, na gaji da hora kaina, kije ki dawo mu shirya Wallahi nagaji..

RAHMA ko tana zuwa gidan momy tarushe mata kuka, Hankalin momyn ya tashi matuqa, nan tahau cewa "dama ni nasan akwai abin dake damunki, gashi Yanzu daya ciyoki ai kinzo gayamin,  toh menene gayamin hankalina dama a tashe yake..

RAHMA tace.. "Momy na haƙura da zaman Aure da ABDUL, na hakura nabar masa ZAINAB..

Momy tace.. "Wai meya faruwa ne..

RAHMA ta gyara zama, fuska jab'e jab'e da hawaye tace, "Wato tunda ABDUL ya Aura ZAINAB da wata uku nafara fuskantar matsala dashi, kullum cikin hantarata yake wai ban iya komai ba, toh ban wani damu ba alokacin, tunanina nad'an wani lokaci ne, Ashe abin ba haka yake ba, lokacin da ZAINAB tasamu ciki shikenan ya juyamin baya gabaki d'aya, kullum cikin yimin habaici yake a gabanta tana me min dariya, wai bana aihuwa, menene menene, cinkashi dai ba irin Wanda ABDUL da ZAINAB basa min..

Sai ZAINAB d'in ta fito harabar gidan tazo daidai kofata tata turomin ciki, tana zunkud'omin tana min waqa, ban san menama ABDUL yadena sona ba, idan zai ganta sau d'ari tana min hakan baya ce mata tadena min..

Daga qarshe dai yanzu yau rabona dashi wata huɗu kenan, yace karna qara zuwa dakinsa, aikina shine na dinga dafama ZAINAB abinci dashi suna ci har zuwa randa zata haihu ta yaye.. Allah momy bazan miki qarya ba, watana huɗu kenan ina yi musu girki ba dare ba dara, idan dare yayi suta hira da dariya har qarfe goma sha d'ayan dare, kana suje su kwanta.

Toh momy nikam na gaji, ABDUL da ZAINAB baza su kasheni kwanana bai qare ba, zan tafi gidanmu yazauna dame haihuwa, har yana cewa sai dai in mutu da sanshi da ƙaunarsa amma bazai dawo dasan da yake min ba, dan yanzu babu wata madubin dubawarsa sai ZAINAB.. RAHMA takai qarshen zancen nata da qara volume d'in kukanta..🤔

Momy ta kama baki cikin matuƙar mamaki. Batace da RAHMAN komai ba ta lalubo numbar wayar ABDUL takirasa, yana d'auka tace mai yazo maza maza yanzu shi da ZAINAB tana kiransu.

Toh yace mata..

Sannan momyn tahau rarrashin RAHMAN kan tayi hakuri zata cicci musu, ai samun ciki ba hauka bane..

Basu wani d'auki lokaci ba, saiga ABDUL d'in da ZAINAB, da alama ya biya gidan nasu ne ya d'aukota..

Momy ta dinga binsu da kallan harara, suna zama ta kalli ABDUL tace, "Kai kam kai kam anyi mutumin banza, dama kasan bazaka iya rikesu da amana ba kasa aka qara yi maka wani auran, samun ciki hauka ne daza kusa yarinyar mutane a gaba da gori kala kala, inda ba'a aihuwa ku za'a haifeku ne, aa saboda tsabar baqin hali irin naku saikusa yarinyar mutane a gaba.

ABDUL ya kalli ZAINAB itama ta kallesa, saiya maida kallansa ga momyn yace, "Momy ban gane me kike fad'a ba..

Momy tamai dakuwa, tace "kaci gidanku, ABDUL ya saukar da kansa qasa, sai taci gaba da cewa, wato ashe tunda ka Auri Zainab kike ganawa marainiyar Allah RAHMA azaba, ya d'ago dakan nasa cikin sauri ya kalli momyn saita qara galla mai harara, saiya qara sunkuyar dakan nasa, ganin hakan sai taci gaba da cewa, yo marainiyar Allah mana, tana da kowa anan ne, ashe dama haka kake, ashe dama kwantaccen kaine dakai, har macece zata burkita maka kai kakasa adalci tsakanin matanka, samun ciki haukane da tunda ZAINAB tasamu ciki kike gorantama RAHMAN, sannan dake ke babbar banza ce shashasha Saiki dinga zuwa ƙofar d'akinta kina turo mata cikin.. Momyn takai qarshen zancen da kallan ZAINAB wacce tayi saurin kallan momyn, aiko nan momyn ta wulga mata tata hararar daci gaba da cewa, Nasan RAHMA bazata muku qarya ba, dama ana ganinku kowa yasan zaku dinga mata wayo, haka kuka dinga cutar da ita ba dare ba rana tana meyi muku aiki kamar wata baiwa..

Watoh kullum ita take muku girki kukama k'afa ku cinye ku zauna kuta hira har ran girkinta ba kunya ba jin tsoran Allah kuta sheqa dariya cikin dare..

Toh baku isa ba, yanda kuke da y'anci haka take dashi, wallahi na qara jin kunyi mata makamanciyar irin wannan ranku idan yayi dubu saiya b'ata..

ABDUL ya rintse idansa ya bud'e da kallan momyn yace, "Dan Allah momy kiyi haƙuri, mun tuba bazamu sake mata komai ba..

Momy ta qara gallamai harara tace, "wato dai da gaske hakan kuke mata.

ABDUL ya cije baki da cewa, "Eh, haka ne, amma dan Allah kiyi hak'uri..

Momy tayi murmushi tace "Aibani zaka bama haƙuri ba, ita zaka bama haƙuri..

ABDUL ya kalli RAHMA tamai gwalo, dake tana gaban momyn ne bazata ganta ba, sai yace da ita, "Kiyi hakuri dan Allah bazamu sake qara aikata miki hakan ba.

RAHMA taturo baki, tace, "Badan kaga ina sanka bane shiyasa kake min komai, kasan bayanda zanyi da zuciyata akan sanka, nayafe muku idan kuka qara cutar dani kuje kuda Allah.. Takai qarshen zancen da fashewa da kuka.

ABDUL ya zuba mata ido, ashe kowace mace tana da nata sharrin, Wallahi ko'a mafarki baiyi zatan zata iya aikata hakan ba.

Nan momy tajawota jikinta tahau rarrashinta, ZAINAB tabisu da kallo.

ABDUL yace, "Kiyi haƙuri my dear, baza muqara aikata miki komai ba, dan Allah ki tashi mu koma gida ina da aiki a office..

Cikin fusata Momy tace.. "Bazata tashin ba, bazata koma gidan naku ba, sai tayi wata d'aya anan, kuje can kuci baqin halinku, amma anan zata zauna tad'anyi ƙiba ta murmure, in yaso saiku samu y'ar aikin da zata dinga yimuku girki..

ABDUL ya dafe kai yace, "dan Allah Momy kiyi min rai, ina buqatarta kusa dani matuƙa, bazan iya rayuwa babu ita kusa dani ba, Dan Allah kiyi wannan shine na farko kuma na qarshe, Nayi miki alƙawarin bazamu qara aikata mata komai ba.

Momy tace, "ku kuka sani, kutashi kubani waje, wallahi bazata bar gidan nan ba sai tayi wata d'aya anan..

ABDUL zai qara yin Magana momyn ta katseshi daci gaba da cewa, Kaga ABDUL kafitta daga idona in rufe, bana san munafuncin banza munafuncin hofi, da kasan bazaka iya rayuwa babu ita kusa dakai ba kadinga gana mata azaba, wacce mace ce zata d'auki abinda ita tad'auka, dan haka kafita daga idona sannan kutashi ko fittan min daga gida tunkan ranku ya zugunduma ya b'aci..

Saurin tashi ZAINAB tayi ta ficce daga falan zuciya cike da tunanin meyasa RAHMA tayi musu wannan sharrin🤔.

Shiko ABDUL matsawa kusa da momyn yayi ya kama qafarta yace, "Wallahi momy bazan miki qarya ba, na rantse miki da Allah bazan samu cikakken nutsuwa ba idan har RAHMA bata tare dani, momy ganinta kawai yana kwantar min da hankali..

Momy ta qara gallamai harara tace, "Duk kasan da wannan shine ka mata iyaka da shiga d'akinka, ta kasan ce bata da wani amfani a gareka sai tayi muku girki kuta sheqa dariya.

ABDUL ya saki qafar momyn da rintse idansa ya bud'e da cewa "Ni dai kiyi hak'uri ki bani matata, ya faɗi hakan kamar zai mata kuka, momy tayi murmushi tace, "wallahi Allah bazan baka ita ba, sai tayi wata d'ayan dana iban maka, dan haka kata shi kabi matarka me ciki, itama Allah zai bata cikin..

A hankali ABDUL ya tashi ya ficce daga falan, acikin motarsa yaga ZAINAB, ya tada motar yana cewa "Yanzu abincin wa zaki dinga ci my Aunty..

Tace kawai zan dinga qoqarin cin Wanda ya samu, zan gayama Hajjiya tadinga aiko min da duk abin datayi, nasan hakan zai temaka min sosai, kuma ma wata qawata ta gayamin hakan bazai d'aure min ba, insha Allah na fitta daga watan nan duk tsurfar zata iya barina..

ABDUL ya sakar mata kiss a kumatu yace, Sannan kiyi hak'uri da qaryar da RAHMA tayi miki,. ZAINAB tayi murmushi tace, "Ba Komai, kar Wannan ya dame ka..

Haka dai ABDUL ya sauke ZAINAB agida yayi office d'insa zuciyarsa cike da tunanin RAHMA..

Momy ko qara jan RAHMA jikinta tayi cikin lallashi take ce mata "ki kwantar da hankalinki bara Abida tadawo daga skull kibata kin d'akin naki ta ibo miki kayanki na sawa ko kala goma ne...

"Toh, RAHMA tace mata.

Aiko Abida na dawowa RAHMAN taba ta kin d'in dakin nata, dayi mata kwantancen inda zataga kayan nata..

Aiko babu b'ata lokaci nan taje ta ibo mata tadawo.

D'akinta momy taba RAHMA, anan zata dinga kwana har wata 1 d'in tayi.

Aranar RAHMA ta gayama UMMAKATI komai a waya, UMMAKATI zaginta tadinga yi kan baidace tayi haka ba.

RAHMA ta kashe wayarta tana ce mata ai sai tayi..

Momy tace RAHMA ta zauna agidan ne dan tayi tunanin kodai ZAINAB ta mallake ABDUL da maganin mata ne, shiyasa ya juyama RAHMAN baya, wannan tunanin da tayi shiyasata cema ABDUL d'in bazata koma ba sai nan da wata d'aya, tanaso tayi amfani da wannan ne wajen gyarata da ingantattun magungunan mata, dan ba qaramin tausayin RAHMAN bane ya kamata, dama ai dole ZAINAB tafi RAHMAN sanin irin waƴannan abubuwan,

sam momy bata san yanzu duniya ta canja ba, bata san RAHMA zata iya sanin magungunan mata qila fiye da ZAINAB d'in ba, dan tana karatun littattafan hausa, tana kallo a film dajin hirarrakin bakin mutane, bare kuma da take tare da UMMAKATI, UMMAKATI boss ce akan harkar, azahirin gaskiya tun gyaran da maman RAHMA tayima RAHMAN na bikinta RAHMA bata qara shan wasu magunguna ba, saidai tana dagema dashan kayan marmari, da zuma musamman yanzu da basa shiri da ABDUL, tana so idan ya shigo hannu yasan yayi missing d'inta ba d'an kad'an ba..

ABDUL ya shiga damuwa sosai da RAHMAN bata kusa dashi, dama dan yana ganinta ne shiyasa ya iya jurema kansa dokar tasa akanta, yanzu da baya ganinta duk ya fitta daga hayyacinsa...

Yanzu kullum sau biyu yake zuwa gidansu momy, kuma RAHMA tagane danya dinga ganinta yake zuwa, dan haka sai take killace kanta idan taji yazo,

Amma tana leqensa batare daya ganta ba.

Da gaske momy take gyara RAHMA, Ita kanta RAHMAN tasan idan ya shigo hannu bame rabata dashi sai Allah..

Ashe tantiriya ce Momy akan harkar magungunan mata, RAHMA ce kad'ai tasan wannan, kuma da kanta take had'awa, ammafa tana da qawa HADIZA SALISU M SHAFIF, Wato fitacciyar marubuciyar nan wacce ta rubuta TATTALIN SO, DA MATAR SO, ba mamaki ita ta koyama momyn had'a magungunan...

Hankalin RAHMA kwance Yanzu, bata ganin ABDUL da ZAINAB bare ABDUL d'in yata jifanta da makaman yaqin nasa idan yaga ZAINAB kusa dashi, har wata qiba RAHMAN tayi, hakan ya qara tabbatarma da momy ba qaramin cutar da RAHMAN sukeyi ba..

Yau kwanan RAHMAN goma sha shidda, ya rage mata saura kwana goma sha huɗu takoma d'akinta, toh ayau d'in UMMAKATI taqara karo mata ziyara a karo na uku dan ba'a kwana uku zaka ganta..

Suna zaune akan gadan momy, dan lokacin da UMMAKATI tazo gidan alokacin momyn ta fitta wai zata kasuwa.

Abida bata nan tana makarantar islamiya, dake yau lahadi ba skull..

UMMAKATI ta kalli RAHMA tace, "Sai wani kyau kike, wai miye sirrin ne, RAHMA tace, "hmm kedai abar kaza cikin gashinta, wallahi UMMAKATI ina gaya miki baki yarda wallahi Momy kat ce akan sanin sirrin riqe miki, badai tace miki idan kika aihu ita zata d'aukeki wankan gida ba, to kijira zuwan lokacin zakiji abinda nakeji yanzu haka, dan ko na gaya miki ba fahimta zakiyi ba, abin da zan iya ce miki d'aya ne ina buqatar jina jikin mijina yanzu, wallahi ina buqatar hakan..

UMMAKATI taja numfashi da kallan d'an cikinta daya fara tasowa tace, "Yanzu dai bani abubuwan da kike rage min..

RAHMA ta galla mata harara tace, "ke wata irin futunanniyace, yaza'ayi kina da ciki kidinga shan maganin mata, wallahi ina gargad'inki daki dena sha, dan yanama yara illah.

UMMAKATI tace "da karatu ne dana dad'e da haddace shi cikin kwakwalwata, kinga malama in zaki bani kibani, dan naji daɗin Wanda kikaban ranar, AMEER kamar zai cinyeni, kuma duk qarya ne da ake cewa wai idan mace tana da ciki kar tasha maganin mata.

RAHMA tace "Kinsan Allah da gaske ne, zaki dai iya sha amma sai idan cikin naki bai wucce wata biyu ba, amma idan har yakai hud'u haƙurin shiyafi dacewa, nidai yau ban rage miki Komai ba, dan yanzu sani take agaba na shanye komai a gaban nata.

UMMAKATI taja tsaki da zuge Jakarta ta d'auko wani cingom ta miqama RAHMAN tace, "Ina so ranar da zaki koma gida, kici wannan cingom d'in tunda safe, kada ki ciresa daga bakinki harsai kin tsotse zaqin tas.

RAHMA ta karb'a da cewa, kuna dai so ABDUL ya haukacemin, amma a ina kike samu wannan..

Tace "Yanzu daga kasuwa nake, shine na biya tawajen shagwan Sadeeq, yafa kawo harka da yawa kingansu nan cikin jakata amma bazan baki ba, sai Kin dawo kin gaya min yanda kuka kaya da ABDUL..

Wallahi RAHMA ban tab'a cin karo da futunan ne irin AMEER ba, nayi imani har ga Allah koda ya qara Aure ba wacce zata iya dashi saini, ni nasan karatunsa, ni kadaice me ganewa, idan yayi rashin sa'a ya Auri wacce bata ganemai ba gaskiya za'a samu matsala.

RAHMA tace, "Dan Allah kiraba kanki da tunanin zuwan kishiya.

UMMAKATI tayi dariya, tace "Kwantar da hankalinki ƴar uwa, ni nasan idan ina tare da AMEER bazai tab'a qara Aure ba, babu boka babu malam, kawai na gaya miki hakan ne dan koda yayi babu wacce zata iya dashi, bare ta gane karatunsa.... Kan RAHMA tabata amsa sai ganin shigowar motar ABDUL tayi ta window.

UMMAKATI tayi dariya da tashi tana cigaba da cewa, wallahi tafiya zanyi, yau gaki ga ABDUL, kuma babu kowa a gidan, zanga Yau yaza kiyi.

RAHMA tace "ai kina fitta zan kulle ƙofa.

UMMAKATI tayi murmushi bayan ta nad'a gyalanta, ta d'auki jakarta da qara zama gefan gadan tana cewa, "Toh bara na bari idan ya shigo na fitta.

RAHMA ta harareta...

Nan ABDUL ya shigo d'akin suka gaisa da UMMAKATIN tatashi tana cewa, "ABDUL yau gidan ba kowa, in nine kai guduwa zanyi da matata, tunda Dady ya baka wannan damar tuntuni..

ABDUL yayi murmushi yace, "Dan Allah da gaske ba kowa, UMMAKATI tace "Wallahi ba kowa, momy ta fitta, Abida kuma tana islamiya, yace "hakan yayi, saita ficce tana ma RAHMA dariya..

 

ABDUL ya haye kan gadan ya ritsa RAHMAN can jikin bango ya kama fuskarta yace, "Na yafe miki sharrin da kika shararamin wajen momy, Sannan qin d'aga wayata ma da bakyayi shima na yafe miki, amma wallahi idan yau baki gayama momy zaki dawo gida ba, nasantse miki da Allah idan kika shigo annuna saikin yabama aya zaqinta.. Haba my Baby, yanzu ke ko tausayina bakyaji, ki duba duk na rame sanadinki, bana iya yin bacci cikin kwanciyar hankali, kullum cikin tunaninki nake, dan Allah dan soyayyarki da manzan Allah ki dawo gida yau, kidawo kiji dani, kidawo najiki wallahi nayi missing d'inki over...

RAHMA ta harare shi tace, "Toni me yasa kiqi min uzuri, ka dinga jefani cikin tunani, kullum ziciyata sai tayi kukan rashinka kusa dani, amma kaqi yimin adalci, dan haka nima bazanyi maka adalci ba, kuma zan gayama Momy ta qara maka wata d'aya, wallahi da gaske nake, kuma bara tadawo kaji, kasan tana jin maganata, saidai kawai kaji tace maka saina qara wata d'aya, badai kafi san AUNTYNKA ZAINAB dani ba..

"Da gaske kike..

Ya katseta da faɗin hakan, saita d'aga mai kai, babu b'ata lokaci ya had'a bakinsa danata yahau bata wani shu'umin kiss, dama yasha jambaki, hakan yama Abdul sweet sosai.. Dake dama zuciyar RAHMAN da muradin ABDUL d'in nan kanta ya kunce..

Tafiya tai tafiya sun kusan cimma burunsu, ABDUL yaga shigowar motar direban gidan da alama ya dawo da Abida ne daga islamiya.

Nan cikin sauri suka gyara kansu, RAHMA tayi saurin goge masa janbakin da yake bakinsa, suka qurama juna ido, ahankali ya janye hannunsa daga na fulaninta yace "my dear Yanzu kin yarda gabaki d'ayanmu muna buqatar junanmu, RAHMA ta d'aga masa kai da cewa, "Nidai yau bazan iya bacci ba😭.. Takai qarshen zancen da zubda hawaye..

ABDUL ya sakar mata kiss yace, "nima haka, yanzu idan Abida ta shigo kice mata zaki supermarket siyayya, tazo ta rakaki, kinga sai na kama mana d'aki a hotel MZM, saimu bar Abidan a mota har mu fito nasan bazata gayama momy ba..

RAHMA ta d'aga mai kai alamar toh..

Aiko Abidan na shigowa RAHMAN tagaya mata hakan

Abida tace, "Aunty!, kuma Ya ABDUL ne zai kaimu,

ABDUL ya harari Abidan yace "eh nine zan kaiku wani abu ne, Abida tayi murmushi tace, "Ya ABDUL kenan, nidai bazan yarda aci amanar momy dani ba, dan haka ba inda zanje..

ABDUL tashi yayi tare da kama hannunta, yace "Haba my sister, haba y'ar Autar momy, kinsan fa ina san matata, dan Allah ki duba qaunar kasancewa da juna da mukema junan namu, ki rufa min asiri naje nayi hira da matata a hotel na d'an wani lokaci, Saiki jiramu amota, dan Allah qanwata karkice aa kinji..

Abida ta kallesu duk jikinsu yayi sanyi, faɗi take aranta, wannan wata irin maseefa ce, mata da mijinta suje hotel hira bayan ga gidansu.. Ai duk ABDUL d'in ne yaja,...

Haka dai Abida ta yarda amma da sharad'in badai suje hotel ba saidai suje gidansu ta jirasu a harabar gidan nasu har su fitto..

ABDUL yayi murmushi yace ya yarda, dama ZAINAB tana gidan Hajjiya Kakah, shi kenan bame ganinsu sai me gadin gidan nasu...

Haka suka shirya suka ficce daga gidan suka yo gidan ABDUL d'in..

Falan nata duk yayi qora, ganin haka ABDUL yajata part d'insa..

Hmm Allah yasa Abida na harabar gidan cikin mota tana jin waqa, daba dan haka ba!😨 data dinga jiyo ihun ABDUL,

Dan baqaramin shiga hannun RAHMA yayi ba😨..

Komai yacanja mai, daga qarshe dai haka yabarta badan yaso, Saidan kukan data dinga mai, dan yau bai mata da wasa ba..

Kamar zai cinyeta haka dai tayi wanka a daddafe..

Gabaki d'aya sai jikinta yahau yimata ciwo.

Bayan sun suturta kansu, zaunar da ita kan cinyarsa yayi, yace "Baby akwai babbar matsala, dan soyayyarki da manzan Allah karki barni arayuwa, nayi missing Komai naki dan Allah kada kiyarda kikai wata agidan momy, dan Allah dan Allah dan Allah kinji👏🏻.

RAHMA tasakar mai dukkan hannayenta awiyansa, takai bakinta cikin nasa, tamai san ranta, kana tace, "Nayi nadamar baka had'in kai yanzu, dan bai dace ba, ya dace na hukuntaka kamar yanda ka hukuntani, amma yazanyi da zuciyata, zanyi maka qoqari matuqa wajen ganin nadawo gareka nan kusa, aiduk kai kajawo, yace "aa my dear duk kishiyoyin mamanki su suka jawo, kuma bayanda zanyi dasu dan amatsayin iyaye suke gareki.

RAHMA ta waro ido tace "sha kallo, me kake nufi da faɗin hakan da kayi.

" Abin danake nufi bashi da wani mahimmanci Yanzu, amma dai na gayama mamanki komai, kuma baba mahaifinki ya d'auki matakin daya dace, nasan mama bazata gaya miki komai ba, amma, ina fatan kisamu juna biyu nan kusa da kaina zan kaiki gidan naku kigaida maman..

Kiss tasakar mai a kumatu da cewa, "Toh naji wannan, yanzu gaya min kana sona fiye da komai a rayuwarka...

ABDUL ya rungumeta yace, "Na rantse miki da Allah ina sanki fiye da kowace y'a mace a soyayyah, tafana yau kiyatani kwana.

Tashi tayi da murmushi kan fuskarta tace, "Nidai bazan ba momy kunya ba, dan haka kaga futata....

Tana fitowa taci karo da ZAINAB a falan nasa, sukama juna Kallan kallo, ZAINAB tace, "Sannu, da fatan kin dawo lafiya, RAHMA taja numfashi tace, "eh, lafiya nadawo, amma lokacin da momy ta ibam min baiyi ba, idan har yacika zan dawo ai.

ABDUL ya fitto da murmushi kan fuskarsa ya kalli ZAINAB yace, "Wlcm da dawowa my Aunty, kinganta nan taqi yarda tazauna wai bazata bama momy kunya ba, gaskiya ina buqatar matata dan Allah Aunty kishirya da daddare muje muba Momyn hak'uri tabani ita, dan nafi yarda da ganinku ku biyu a lokaci d'aya, Aunty wallahi rashinta ne yake sani qara ramewa..

ZAINAB ta had'iye wani mugun yawu tare jan numfashi tace, "Zan shirya, Allah yasa momyn tabamu ita..

RAHMA tagallama ZAINAB d'in harara batare da sun ganta ba, tayi waje abinta..

Wallahi ita har tamanta tana da kishiya, gashi zuwanta harya b'ata mata farin cikinta..

ABDUL yama ZAINAB d'in kiss yabi bayan RAHMAN da sauri.. ZAINAB tabishi da kallo, ta lura yana cikin farin ciki Sosai, tome sukayi yasashi farin cikin haka.🤔

Abida na ganin fitowansu tace aranta, ya Abdul kenan, wannan dai bazan hira bane, zaman aikata aikin lada ne..😂

Aiko daya shiga motar sanda ya juya ya kama hannun Abidan ya Bata kiss da cewa, "Godiya me yawa my qanwa, Allah ya baki miji me sanki kamar yanda nake ƙaunar Auntynki RAHMA..

Abida tayi murmushi tace, "Ameen brother, Yanzu saika kaimu supermarket d'inko.. Yace, "ai yau ranar Hutu ce, ko ina kike buqata zan kaiku...

Kan Abidan tayi Magana wayar RAHMA tad'auki ruru, tana dubawa taga UMMAKATI ce, nan tad'auka da cewa, "Allah ya rabaki da zaman jikin window, UMMAKATI tayi murmushi tace, "Ba ameen ba, kice har yaci amarcin tunkan kikai wata d'ayan, kai wannan wata irin sa'ace, ashe yaji shawarata..

RAHMA tayi murmushi tace, "Kinfa san Ina san mijina, dan haka bayanda zanyi da zuciyata wajen b'atamin tunaninta da yakeyi, kalma d'aya yace dani! yayi min wayo..

ABDUL ya kalleta da

murmushi itama tamaida mishi murmushin, baice da ita komai ba yaci gaba da tuqinsa.

UMMAKATI ta kwashe da dariya tace, "Yanzu dai kindawo gabaki d'ayan ne ko yaya..

RAHMA tace, "Hmm umm, kinsan bazan ba momy kunya ba, yanzu dai zan kira anjima, tace mata toh da kashe wayar..

Haka ABDUL ya kaisu supermarket suka d'auki abinda ransu ke so, ya d'aukarma ZAINAB abubuwan daya san tana buqata, kana yazo ya sauke su a ƙofar gidan nasu, koda wasa bai shiga dasu ciki ba, daqer ya iya barin RAHMA tabar cikin motar dan sai janta da magana yake, tana fitta ko yayi wajen Hajjiya Kakah..

Yaci sa'a AMEER yana gidan dan haka hirar tasu tayi sweet matuƙa.

Momy tambayarsu tayi daga ina suke, sukace mata daga supermarket, tace me yasa basu tafi da direba ba, suka ce mata kawai sunyi sha'awar hawa napap ne, jinsu kawai tayi, dan bata yarda ba, tafi yarda da kawai sunyi sha'awar tafiyar qafa ne.

_¶Share_

_¶Vote_

_¶Comment_

_¶Follow_

AUNTYN LUV💋

 

'´-'´- “˜• ¸ª_'

*.¸¸.**.¸¸.*🙆*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*

 

 

*TANTIRANCI KO KARUWANCI*

 

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆*.¸¸*

'´-'´- “˜• ¸ª_'•🤱🏻

 

 

Written by Rahma Nalele

 

 

🤦🏻Sardaunah...

 

 

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ

Page 23

*15 read more, Sannan sadaukarwa ga MASOYA ZAINAB*🙁

*Sannan ina kira ga jan hankali ga marubutan film, daku dena satar min labari kuna juyamin yanda ranku keso, idan zakuyi tasar kudinga sata kawai kai tsaye, ni nasan kaina nasan kalamai na, dan haka dole nagane aduk inda najisu. Nawa ba irin naku bane, da qirqira acikin tafiyar me haɗe da baiwa, ba fariya nayi ba, amma zanfi jin daɗi idan kukace dani Rahma bamu kawai muyi film da labarinki, amma bawai kudinga rainamin hankali wajen bibiyata na tura muku da kaina bansan ku bane, Eh, zan kama suna, YUSUF kake ko wa🤔, labarina na MASIFAR SO ka sacemin kayi film dashi kuma na gani, me suna Fateema ko Zara, bayan na bama wani d'an uwana zaiyi film dashi, sannan akwai wani ma wai shi Aliyu, kasace min labarina na ƳAR ƘAUYE KO ƳAR BIRNI ka siyarma da wani, amma dake ina saka sunana cikin cikin labarin hakan yasa ya gane bakai bane ka rubuta, ya kuma nemi wasu littattafaina a online, danya gane rubutun online ne, ahaka ya samu numbata ya kuma kirani ya gayamin, kaje kai da Allah, dama ai bai zama lalle dole abar mana labaranmu ba, tunda a online muke rubutawa, amma ai yadace mutane kudinga jin tsoran Allah, sannan zan faɗi na qarshen da yake San sace min SAMAREEN BANAH, wai adole shi me gaskiya ya kirani rami rami yake gayamin wai ogansa A ZANZO zai siya ya maidashi season film, ashe qarya yake yake min😨 dan da tafiya tai tafiya saina dena jinsa, zan gama binkice akanka na tabbatar da gaskiya ai, nidai idan mutum zai saci novel nawa ya sata kawai kai tsaya yadena ma abin kwaskwari mah*.

Dare ko nayi Abdul da Zainab sukazo suka saka Momy agaba kan tabasu Rahma, amma sam taqi yarje musu, tace sai tayi wata d'ayan nan datace musa.

Kasancewar momy bama'abociyar fitta unguwa ba, tun fitan da tayi narar bata qara fitta ba, hakan baima ABDUL sweet ba, yana ji yana gani Rahma tafi qarfin kai annunsa gareta, suna dai waya susha soyayyarsu abin dai abin dakaici, dan suna gama wayar suke shiga wani yanayi..

Toh yau dai ranar tacika Rahma tadawo d'akinta, ABDUL murna kamar me, sosai ZAINAB ta danne zuciyarta dan in bata danneta ba gaskiya zasu samu rashin fahimta tsakaninta ABDUL d'in..

Sai wani rawar kai yake abin dai abin jin daɗi ga RAHMA ga ZAINAB abin takaici..

Amma fa ranar girkin RAHMAN yake nuna rawar kan, gaskiya yana qoqari sosai wajen bama ko wacce hakk'inta

Yanda suke rayuwarsu haka suka cigaba da tafiya da ita.. Ammafa akwai canji..

ZAINAB tagane ABDUL yafi qaunar RAHMA fiye da ita.

Ta hango wani so da ayanzu yakema RAHMAN Wanda baki bazai iya furtawa ba.

RAHMA ta mallake ABDUL fiye da tunanin me tunani..

Kar me karatu yayi tunanin maganin mata ne kawai yasata mallakarsa aa taqara da wasu abubuwa guda uku..

Ta qara yawan shagwaɓarta garesa, ta qara qirqiro wata fasaha yayin da suke raya sunna, ta fahimci akoda yaushe ABDUL yana san ganinta cikin kwalliya da tsafta da ƙamshi... Saita qara k'aimi sosai wajen san wadata kanta dasu.

Sannan ta d'an shiga jikin ZAINAB kad'an danta san wasu sirrika nata.

Ta gane ZAINAB tana da tsafta sosai, saitayi amfani da wannan damar tasaka aranta Saita fita tsafta..

Idan RAHMA ta tsaftace d'akinta saitafi kowane lungu da tsak'o ta wadatashi da qamshi..

Sab'anin ZAINAB da inta tsaftace ko ina bata tsayawa bama kanta walaha wajen bin ko'ina tabashi qamshi..

RAHMA tagane ZAINAB ta iya girki.

Saita sama ranta zata iya girki fiye da yanda ita ZAINAB d'in ta'iya, duk da abin ya nuna kansa a zahiri ba wacce bata iya girkin ba acikinsu, amma dan maseefa haka RAHMA tasa aranta saita iya fiye da ita, hakan yasa kullum cikin karance karancen girki gala gala take.. Da namu na gida dana larabawa dana turawa, kowanne RAHMA neman qarin ilimi take akansa.. Wani abun idan ta girka maka, saika rantse aljanace.

RAHMA ta lura ZAINAB tana da hak'uri da kawaici da nuna komai ba komai ba koda ko komai d'innan zai sata kuka a d'aki, sam bazata nuna maka ba..

Sai RAHMA ta fara kwaikwayan way'annan halayan nata, idan yau ZAINAB cikinta na mata ciwo, ko wani laulayi irin dai na masu ciki wanda bai taka kara ya karya ba, sai RAHMA ta danne zuciyarta tataba ZAINAB d'in kulawa tana taya Abdul musamman idan a gabansa ne, koda yake koda a bayan idansa ne haka take bata kulawar, Ammafa idan har ta fahimci bata jin daɗi, wata rana har barin ABDUL take ya kwana a d'akin ZAINAB d'in idan hakan yazo aran girkinta, kuma gashi ZAINAB d'in na buqatar kulawa.

 

Duk wani hali na ZAINAB wanda RAHMA take ganin ABDUL yana san ZAINAB dansu, yana yabanta akansu, yana jin daɗin yanda take dasu, sanda RAHMAN tayi yaqi da zuciyarta ta koyesu, sai yake ganin RAHMAN ma dasu..

ZAINAB tagane RAHMA ayanzu sosai, ta gane so take ta qarashe mallake ABDUL Cikin wayo da dabara.

Kuma ko kad'an hakan bai sab'awa haddini ba, dan ambaki damar da zaki dasa ƙaunarki da soyayarki acikin zuciyar mijinki, babu boka babu malam, ke dai duk abin da zakiyi kiya dan Allah, kar ki kuskara ki aikata abin da kike da tabbacin cutarwa ne ga y'ar uwarki..

A tunani da hankali irin na ZAINAB tayi zama na musamman tayi tunani me zurfi ta lura tayi imani har ga Allah RAHMA bata tab'a aikata mata wani abu na cutarwa ba..

Sannan tayi imani RAHMA tana yin komai ga ABDUL ne dan yafi santa fiye da ita ZAINAB d'in..

ZAINAB tayi tunani idan taso Allah da manzansa bai dace ta zargi RAHMA kan soyayyar da ABDUL yake mata ba, dan tana bin dukkan wasu matakan daya dace yasota dansu mataken da basa kaucema hanya.

Tasan RAHMA na kishinta sosai ba wai bata kishinta ba, amma tana mata kishin ne irin wanda ya dace..

A lura irin tata tagane ABDUL yana san RAHMA ne dan shagwaɓarta, yana san RAHMA ne dan iya girkinta, yana san RAHMA ne dan tsaftarta da san qamshinta, uwa uba ABDUL yana san RAHMA ne dan yana jin daɗin raya sunna da ita..

ZAINAB ta fahimci dukkan waƴannan abubuwan ba wanda ABDUL baya san RAHMA dansu..

Wannan shi ake kira da kishi, ba kishin yaran yanzu ba, kishin da suke na hauka da bin bokaye da malaman tsubbo, wannan kirane na Rahma muh'md Rufa'i Nalele, idan zakiyi kishi kiyi kishin abinda kika da tabbatar yana jan hankalin mijinki agun kishiyarki, sai kiyi qoqarin iya wanda yafi nata, wanda zai jawo miki hankalinsa fiye da yanda yake jan hankalinsa agun abokiyar zaman taki, wannan shi Momy ta gayama RAHMA lokacin da zata bar gidanta, tace RAHMA ki zama me lura da abin dayake jan hankalin mijinki ga abokiyar zamanki, Sannan ki zama me b'oye kishi, ki zama me kishi akan duk wani abu da kikasan me kyau ne wanda abokiyar zamanki takeyi, to ki kwaikwayeta, kiyi qaqarin ganin kinyi wanda yafi nata, sannan kiji tsoran Allah kadda ki tab'a aikata mata mugun abu, kadda ki kuskara kibi shawarar qawayen banza, duk abinda aka baki akace miki ba'a bama me kishiya ammake ambaki kada kiyi amfani da shi, duk abinda kikasan idan kinyi amfani dashi cutarwa ne ga y'ar uwarki kadda kiyi amfani shi dan Allah RAHMA kinji.

Alokacin jikin RAHMA yayi sanyi ta kuma saka aranta bazata tab'a aikatama ZAINAB wani mugun abu ba....

Abu d'aya ne yake tsayama ZAINAB arai.. Wanda take zargin RAHMA danshi, shine, wai meyasa ABDUL baya nuna jin daɗinsa idan yana raya sunna da ita ko idan ya gama yi da ita, amma idan har yana raya sunnar da RAHMA kowa washe gari saiya gane yana cikin farin ciki bama ita ba..

Tayima RAHMA da ABDUL d'in labe wata rana tajiyo yanda yake burkicewa yayin da suke aikata sunnar..

Tasani ba kishiyar da bata san maganin mata ba, kuma itama tana cikin sahun matan da suke shan maganin matan. Masu kyau masu tsada masu inganci, amma meyasa ita baya burkice mata kamar RAHMAN..

Sau biyar kenan tana musu lab'en wannan ne ya tabbatar mata da cewa abin nasu na kullum ne, wato koda yaushe suka had'u had'uwa irin wannan sai sun burkicema juna.

Kai dole akwai wani abu da RAHMAN tayi masa wanda yake sashi burkicewa..

Amma banda haka ai idan shan maganin ne itama tana sha, ya dace itama ya dinga burkice mata, tasani idan har ya fara burkice mata akan hakan, ba makawa zata samu kaso casa'in ita a irin soyayyar da yakema RAHMAN..

Dan ba abinda takeyi wanda ita batayi..

Saidai na RAHMAN yafi nata.. Amma duk abinda RAHMA takeyi itama tanayi.

Kawai bazata iya jurewa bane kan saita iya fiye dana RAHMAN, kamar RAHMAN takeyi.

Wannan shine abun da yake damun ZAINAB, amma duk sauran basa damunta, damuwarta shine kawai yanzu ABDUL yadinga jinta yayin raya sunna fiye da RAHMA..

Abin da ZAINAB bata gane ba shine, ko kad'an ba abinda RAHMA tayima ABDUL dangane da batun maganin mata, dan RAHMA sam bata wani damu da shaye shayen maganin matan ba, amma ance tunran gini tunran zane..

_Babban sirri ne gareku yara yaran mata, koda ace iyayenki basu miki ba, ke kima kanki. Kisa a rubuta miki suratul Yusuf da suratul maryam awance miki da ruwan kankana ki zauna da bisminllahi ki shanye, Sannan kisa a rubuta miki suratul Alrahaman itama awanke miki da ruwan kankanar ki shanye, kisa amiki dahuwar kaza da nonon raƙumi da garin rid'i ki cinye.. Ko da wannan kad'ai kika tsaya Wallahi kinfi qarfin wulaqantawar miji akan raya sunna, koda kina da abokiyar zama saidai idan ta kauce hanya wajen shan maganin matan, wato anyimata tsufface tsufface da asirce asirce shine zai sa kiga mijinki ya canja miki, amma maganar gamsuwa koda yaje ya jita ahakan da tasha kayan tsufface tsuffacen, zaiji aransa yafi samun qamsuwa agunki, hankalinsa dai yana kanki, koda ya juya miki baya bazai iya share rayawa dake ba,_

Toh RAHMA mamanta duk tamata hakan, tunkan akaita d'akin mijin nata..

Momy kuma tazo ta qara mata da kayan dake dake na saiwowi da ganyayyaki, sam momy bata ba RAHMA wani abu wanda take da tabbacin zai cutar da ZAINAB azaman takewar auran nasu ba, ita dai taba RAHMA magungunan mata ingantattu way'anda zai bata zaman lafiya tsakaninta da mijinta..

Wanda ko ita RAHMAN zata iya shansu ba tare da niyar ta cutar da ZAINAB d'in ba,

Momy tana san ZAINAB bawai bata santa ba, amma ita tafi qaunar RAHMA fiye da ita, haka kawai taji hakan aranta, kuma wannan yana d'aya daga cikin ƙaddarar ZAINAB, dan idan da wacce momy zataso to abayan ZAINAB take, amma dake rayuwar ba haka take ba, bakai ne da kanka ba, Allah ne dakai, to dan haka sai kayi hakuri da dukkan ƙaddarar da tazo maka, zaka iya iyawa da komai amma bazaka iya iyawa da zuciyarka ba, shiyasa akace kadinga neman tsari daga sharrin zuciya

Mudawo kan ABDUL..

Haka shima ABDUL idan da wacce zaiso abayan ZAINAB take, amma kunga yanda yafi qaunar RAHMA fiye da ZAINAB d'in, wannan wani abu ne da yake faruwa da yawancin mutane, idan aka samu rashin fahimta sai zaman lafiya yaqi samuwa, ZAINAB tana da hankali da kuma saurin fahimtar abu, tasan sarai ABDUL yafi qaunar RAHMA da ita Amma wannan ba wani abu bane da zata saka aranta wanda zaizo ya dameta.. Ko ciki d'aya kuka fitto da mutum zakaji aranka kafi san wani dashi, wannan ba wani abu bane, dan yana faruwa arayuwa, bare kuma rayuwarta da ABDUL, tasan sun shaqu da Abdul, shaƙuwa ce tsakaninta da ABDUL ba soyayya ba, tagane ABDUL yana rayuwa ne da ita rayuwa irinta waƴanda suka shaƙu da juna, shaƙuwa daban soyayya daban.. Tun farko tasani babu soyayyar Aure tsakaninta da ABDUL, soyayyar y'an uwan taka ce tsakaninta dashi da kuma shaƙuwa.. RAHMA kuwa tare tagansu da ABDUL d'in, tasan soyayya ce tasa suka kai har  lokacin da ABDUL ya Aureta, tasan bata san ya suka fara al'amuransu ba amma tasan sun faro SO ne bata hanya irin tata ba.

Wannan yasa ayanzu bata zargin soyayyar da ABDUL yakema RAHMAN..

Ita ta godema Allah ma da ahakan yake santa yake ƙaunarta, ayau idan tafito tace wani abu na raini kona wulaqanci ya shiga tsakaninta da ABDUL Wallahi tayi mishi qarya, yana da wayo sosai yana matuƙar qoqari wajen ganin ya bata hakk'inta...

**********

Wata biyu da dawowar RAHMA gidan daga gidan momy tasamu ciki, sam bata san da zaman cikin ba, haka ABDUL shima bai san dashi ba, dan laulayi bai fara kamata ba...

Yau da misalin qarfe biyu na ranah ZAINAB ta Haihu, tasamu y'arta mace kyakkyawa da ita, yarinyar tayo kamar ABDUL sak, sam batayo kamar ZAINAB d'in ba, abin yama Abdul sweet Sosai, dangi kowa da kowa sai murna yake..

Yarinyar tazo da farin jini Sosai.. Dan kowa nuna qaunarta yake da gaske har cikin ranta..

Musamman RAHMA yarinyar tashiga ranta sosai,

Momy direct daga asibiti ta d'auki ZAINAB d'in wankan gida.

Abin yama Abdul dad'i sosai dan dama yana san yaga momyn tana ba ZAINAB d'in kulawarta... Wallahi yaji dad'i har cikin ransa..

Yayin da ran mama Saude yayi mata baqi qirin, sam bata so momy ta d'auki ZAINAB d'in ba.

Hajjiya Kakah ko taji daɗin hakan.

Kullum RAHMA da UMMAKATI qarfarsu na gidan momy.

Ana gobe suna ABDUL ya keb'ance da momy yana yi mata kame kame..

Ta kallesa a nazarce tace, "Wai me yake damunka ne Abdul, ka tasoni daga cikin mutane ka kuma yimin shuru kaqi gaya min komai.

Ahankali kamar me rad'a yace "Momy kinsan sunan dana sakama yarinyar..

Momy tayi murmushi tace "aa saika fad'a.

Sosa qeya yayi da cewa, "Momy sunan RAHMA nasaka mata..

Da sauri momy ta waro ido😳, Tace "Kana nufin sunan kishiya ka danqarama y'ar kishiya😨.

ABDUL ya d'auke kai da d'aga mata gira alamar tabbatarwa..

Sai momy tasaki salati daci gaba da cewa, Toh yanzu kiran me kamin.

Ya juyo ya kalleta da d'an murmushi yace, "So nake kice ma ZAINAB d'in Dady ne yace yana san sunan asa mata, shi kenan.

Momy ta hararesa, bai bari tace wani abu ba ya sakar mata kiss a hannu da barin wajen...

Momy tayi shuru, tab gaskiya ABDUL yanzu yana ji da RAHMA, tafad'i hakan aranta..

Da suka keb'e da ZAINAB d'in Momy kama hannunta tayi tace, "ashe sunan yarinyar RAHMA... Gaban ZAINAB ya tsinke ya faɗi, ta tattaro dukkan jarumtarta tace, "Yanzu dai nake ji momy, kuma sunan yayi, RAHMA zataji dad'in hakan, ammata takwara, gaskiya nayi farin ciki dajin hakan..

Dake momy babbace, murmushi tayi danta gane ZAINAB d'in tafad'i hakan ne kawai amma dole bazataji dad'i ba, karo na biyu kenan Momyn taji qaunar ZAINAB d'in aranta, wato nuna ƙaunarta da tayi ga Abdul lokacin yana matsayin d'an mama Saude, da kuma yanzu da ABDUL d'in ya sakama y'arta sunan kishiya tanuna bata damu ba, gaskiya momy taji qaunarta aranta Sosai.

Hakan yasa ta saki hannunta tace, "Allah ya miki albarka, yasa ki gama da duniya lafiya..

"Ameen ZAINAB tace mata..

ZAINAB qoqarin tayi sosai nasan ganin ABDUL... Suna had'uwa ta galla mai harara tace, "watoh sunan y'ata RAHMA, sunan kishiya ka sakama y'ata, gaya min miye dalilinka..

ABDUL yayi k'irmishishi da idansa yace, "kawai Aunty naga sunan ya dace da ita ne, kuma ayanda naga kina san RAHMA baki nuna komai akanta hakan ne yabani qarfin gwiwar saka mata sunan..

Qara galla mai harara tayi, tace, "toh baka isa ba, dan kowace zuciya tana da kishi, nuna ina san RAHMA bashine zai baka damar saka ma y'ata sunanta ba, dan haka ina buqatar ka canjama y'ata suna da sunan mahaifiyata, danna lura kafi qaunar RAHMA dani, kafi santa fiye dani, bandamu ba amma kada kushiga hakk'ina, wannan baya cikin jerin adalci..

Yace "da gaske..

Ta d'auke kanta daga kallansa ranta a mugun b'ace, saiya ƙaraso gabanta ya karb'i little Rahman, ya kwantar da ita ya juyo da kama hannun ZAINAB d'in, idansu cikin na juna, suna masu jin numfashin juna, yaci gaba da cewa, Aunty tunaninki ban sani ba, tunaninki ban san me kikama RAHMA ba, da haɗin kanki Uwani tabama RAHMA maganin hana d'aukar ciki.. ZAINAB ta waro ido😳, ya sakar mata murmushi daci gaba da cewa, Aunty kinsan meyasa ban kulaki ba, kinsan me yasa ban nuna miki nasani ba, saboda na duba qaunar da kika nunamin tun muna yara, ina da tabbacin hakan ba tunaninki bane, zai iya yuhuwa qawace tasaki aikata ma RAHMAN Hakan, Aunty shaƙuwa daban soyayya daban, na shaƙu dake, bani san ganin b'acin ranki, bana san ganin wani ya b'ata miki, har zane mijinki na tab'ayi dan ya dami ZUCIYATA da irin abubuwan da yake miki,

Shaƙuwa ce ta haifar da soyayyar da ayanzu mukema junanmu ni dake, RAHMA ko tun ganin farko danayi mata a club, ZUCIYATA takamu da santa da qaunarta, wannan sirrin ZUCHIYATA ne ban tab'a tunanin zan gaya miki ba, kawai ina so Aunty kisa aranki ina sanki fiye da yanda nake san RAHMA, hakan zai haifar miki da kwanciyar hankali, danke TAURARUWATA CE, ita kuma rayuwata ce,

Nayi imani idan har na rasaki arayuwa rayuwar bazata tab'a min dad'i yanda nake so ba, dan bazan tab'a mantawa dake ba,

Amma maganar Gaskiya idan har narasa RAHMA ina kyautata zatan nima za'a iya rasani, bana so kisa aranki nafi qaunar RAHMA akanki, idan har kika saka hakan bazaki tab'a zama lafiya ba, wallahi wallahi wallahi Aunty ina sanki ina kuma san cigaba da rayuwa dake, dan Allah dan annabi karki kalli qaunar da nakema RAHMA, dan bazan iya b'oye miki ba, ina mata wani so... Aunty mubar batun ahaka, kawai na sakama ƴarki sunan RAHMA ne dan koda bata haihu nan gaba ba, zata rayu cikin farin ciki da kwanciyar hankali da yarda a zuciyarta mijinta yana santa da qaunarta tunda har gashi yamata takwara a d'akin kishiyarta, wannan zai temaka mata sosai wajen ganin bata damuwa da rashin aihuwar ba, sannan nayi hakan da biyu ne, dan na gwada adalcinki, idan kika kawo min qorafi kan meyasa nayi miki hakan, na tuno miki abinda kika mata, idan ko kikayi shuru toko na tabbatar kina sane da abinda kika mata, kuma yana damunki zuciya..

Jikin ZAINAB yayi sanyi, ashe yana ganinta da abun bai tab'a gaya mata ba, to waye ya gaya masa, cikin sanyin jikin hawaye ya zubo mata, tace, "ABDUL dan Allah ka....

Saurin katseta yayi da cewa, "Haba my Aunty, idan da wacce zanso abayanki take, dan kin nunamin dukkan ƙauna, amma dake ZUCHIYA gidan shirrice, kinga yanda tafifita soyayyar RAHMA akan taki, kawai kisa aranki ina sanki fiye da RAHMA, Sannan kin fad'i a jarabawar nan taki, haka ina so kibar zubar da wannan hawayen naki, dan nasan kin dad'e dayin nadama, Aunty bana san ganin hawayenki dan Allah kidena bana so... Yakai qarshen zancen da rungumarta, runguma irin wacce kallo d'aya zaka mata kasan akwai so..

Daidai nan RAHMA ta shigo d'akin, aiko tayi mummunan gani, har zata turmuqe fuska saita tuna yanzu ba da bane, koda zata gansu suna aikata aikin lada nuna kishi akan hakan fad'uwa ne...

Dake ABDUL d'in ne yake kallan ƙofar shigowar shine yasan da shigowarta, sam ZAINAB bata san da shigowarta ba dan ita juyama ƙofar baya tayi....

 

Cikin murmushin yaqe RAHMAN ta juya idanta da galla mai hararar wasa tace, "Ya kamata ka sakar min y'ar uwa haka, kar momy tazo kasata jin kunya...

Sarai ABDUL ya gane taji kishin hakan ne, amma yana jin daɗin yanda take qin nunawa, danya lura tunda tadawo daga gidan momy tadena nuna kishin nata, kamar yanda ZAINAB d'in take qoqarin qin nunawa..

Aiko da sauri ZAINAB ta raba jikinta da nashi jin muryar RAHMAN? Tajuyo takalleta da murmushi tace, "banso kika gammu cikin wannan yana yin ba.

RAHMA tace, "Lallema Aunty, ai wannan ba komai bane, kadda ki manta mijinmu ne fah, dama kunun kanwa momy tace na kawo miki.. Rahma takai qarshen zancen da ajiye mata fulas d'in dake hannunta da Kofi... Zata fitta ABDUL ya kama hannunta yana qarema lallan hannun nata kallo, can yace, "Lallan nan yayi kyau sosai Baby, zanso naga irinsa a hannun Me jego...

RAHMA tayi murmushi jin daɗi dama tayi danya gani ya yaba ne, Gaskiya tana san mijin nata, yana bata kwarin gwiwa sosai wajen yaba dukkan wani abu daza tayi ko tayi, koda yake har ZAINAB d'in ma yana yaba mata wannan d'abi'ar tashi ba akanta kad'ai take ba..

Cikin murmushin tace, "Ai meyin lallan me jegwan taso fara yima, amma dake tashiga wanka sai nace tafara min..

Yayi murmushi yace, "Yayi kyau sosai, kice mata tazo tamata tafitto daga wankan.

"Toh, RAHMA tace mai da ficcewa.

ZAINAB ta sakar mai murmushi shima ya sakar mata daci gaba da cewa, "Aunty zanje gida na d'an huta kinga yau ko office banje ba, amma Dady yayimin uzuri, Sannan ina so ki manta da komai, sunan Yarinyata dai RAHMA kuma bazan canja mata sunan kamar yanda kika faɗi d'azu ba...

Murmushi ZAINAB taqara yi da cewa, "Gaskiya naji kunya, aiban san jarabawa ka rubutamin ba dana sani Wallahi ba abinda zai hanani ci.. Dan Allah mijina kayafemin da yafiyar RAHMA dan bazan iya gaya mata nice nasa abata magani ba,

Tashi yayi da ficcewa yana cewa, "Aunty mun yafe miki...

Anyi suna yarinya dai taci sunan RAHMA.. Suna kiranta da RAHEEMAT kamar yanda dangin RAHMA ke kiranta da Hakan..

RAHMA kamar tayi me, dan jin daɗi, haka awannan ranar taje kasuwa ta kashe kud'i sosai wajen siyama yarinyar kaya... Aiko ta siyama yarinyar kaya na gani na fad'a, dan kowa yaga kayan saiya yaba..

Kaya dai kam ba irin wanda me jego bata samu ba,

AMEER da UMMAKATI ma summa me jegwan kaya da Babynta...

Wannan rana RAHMA ta nunama Abdul jin daɗinta.. Yanzu haka suna kwance ne a gado.. Dake qarfe goma sha d'aya da rabi ne na dare.. Takallesa a hankali, tace "sha kallona, gaskiya bani da bakin gode maka, nayi murna naji farin ciki dayimin takwara da kayi, yace "komai zan iya yi miki my Baby, ammafa kidena murnar dan kema idan kika haifamin mace sunan ZAINAB zansa mata, dan nadad'e dayi mata alƙawarin idan har nayi Aure na haifi mace sunanta zan sakama Babyna, toh dake yanzu itace ta Haifa shiyasa nasa sunanki..

RAHMA ta qara qanqamesa tace, "murna dai bazan denata ba, sannan bazanji komai ba idan na Haifa kasa sunan ZAINAB d'in, dan nasan ni kafara yima..

Had'e bakinsa da nata yayi nan suka fad'a wani abu daban...

Dake sunan agidan momy akayi, hakan yasa tunda Mama Saude taje sunan bata qara zuwa gidan ba, gashi tana so ta zuga ZAINAB babu dama..

Amma tasa aranta zata zugata idan tazo musu yawan arba'in..

A wankan gidan da momy ta d'auko ZAINAB yi mata, ba qaramin gyara momyn tama ZAINAB d'in ba, duk da zuciyarta na hanata kan kar Abdul ya qara botsarema RAHMA amma haka dai ta d'aure tama ZAINAB d'in abin daya dace..

Aiko ZAINAB taji dad'in hakan, tana da tabbacin gamuwarta da ABDUL saiya raina kansa..

Abin da ZAINAB bata sani ba shine, tafi RAHMA qarfin jini, shiyasa duk shaye shayen daza tayi basa bin jikinta kamar yanda suke bin jikin RAHMA, wannan yasa komin k'ank'antar magani idan RAHMA zatasha zai mata amfani nan take amma ZAINAB sai tasha biyunsa kafin yayi mata amfanin rabin na RAHMAN..

_Mata da yawa suna shan magungunan mata amma suna kawo qorafin baya yi musu, toh abin da baku sani ba shine jininku yana da qarfi, bai zama lalle idan yama wanda jininsa baya da ƙarfi kuma yayi muku irin nasa ba, aa da bambanci, irinku ana so ku riqe yawan shan kayan marmari kayan ruwa, kamar amisali idan zakuci abincin safe kufara da shan Zuma cokali d'aya, haka da rana ma, amma idan zakuci abincin dare to kuci da yamma, bayan magrib saiku sha kayan marmari musamman kankana da abarba da ayaba suna saurin bama megida saƙo.. zasufi baku abinda kuke nema nan kusa, wannan sako ne daga Rahma muh'md rufa'i nalele_

 

Hakan yasa koda ZAINAB tadawo gida taga dai canji awajen ABDUL amma ba kamar yanda take tunani ba, kai gaskiya taga rikicewarsa harya kasa haƙuri sanda ya tambaye ta, "wallahi najiki cakwai kamar baki Aihu ba, Aunty me kikasha ne, nasanfa akwai wasu magunguna waisu maganin mata, yakai qarshen zancen nasa da murmushi tare da qara shige mata.

ZAINAB kasa basa amsa tayi, dan dad'i, dole tadage da shan magungunan mata fiye dada, qila ya iya burkice mata fiye da yanda yake burkicema RAHMA...

*wato idan tunanin mutum ya tashi d'aukewa har basirarsa tafiya take*

Mama Saude bata samu galaba akan Zainab Wannan karan ba, dan duk yanda taso data zugata danta taji qiyayyar RAHMA abin ya faskara, ta lura idan ta matsa mata ZAINAB d'in zata iya ganota, hakan yasa ta haƙura, badan taso ba,

____________________________

Laulayi ya kusanto RAHMA, har yafi na ZAINAB, amma ita tana iya cin abincin da take girkawa, saidai amai da ciwo ba irin wanda RAHMA bata fuskanta..

Abin ya faro ne sati d'aya da dawowar ZAINAB gida daga wankan gida..

Ranar lahadi ABDUL yana gida yayi wanka ya shirya yafito dan d'aukarsu zuwa wajen shaƙatawa, har sun fitto harabar gidan, sai RAHMA ta shaqi hamshin turaran da me bama fulayoyinsu ruwa ya saka, nan cikinta ya murd'a ta durkushe awajen dama little Rahma na hannunta, ABDUL yayi saurin karb'arta ya miqama ZAINAB ya durkusan yana tambayarta lapia, aikan ya rufe baki tawankesa da amai.. Gashi farar shadda yasaka,🙁 nan yace, "Haba my Baby, lefin me nayi miki dazaki kwararamin amai hak...

Aikan ya qarasa taqara kwarara masa wani, aiko da sauri ya tashi yayi fate d'insa da gudu, ZAINAB tayi dariya tare da durkusawa zata kama hannun RAHMAN bata kai ga hakan ba itama tawanke da aman..

Zainab tatashi Allah yasa bai shiga idan little Raheemat ba, itama part d'inta tayi tana nadamar zuwa kusa da ita da tayi..

Daqer RAHMA tatashi tayi part d'inta da shiga toilet, anan tacire kayan jikinta gabaki d'aya tasakarma kanta ruwa, sanda ta qara yin wanka tafitto tacanja kaya ta feshe jikinta da turaranta Sannan ta zauna bakin gado tana tunanin mezaisa daga jin qamshin turaran me bama fulayoyinsu ruwa tafara sakar amai.

Sanda ta huta sannan ta fitto falanta, anan taga ZAINAB riqe da little d'inta, ABDUL na gefe duk sunyi wankan suma sun canja kaya, ABDUL ya harareta yace,  "nabar miki kayan nawa suna toilet ke zaki wanke da hannunki ko injin ban yarda kisa ya wanke min ba..

RAHMA tayi murmushi tace,  "Dan Allah kuyi haƙuri, nima bansan meyasa daga jin ƙamshin turaran me bama fulayoyi ruwa nafara sakar amai ba..

ABDUL ya tsaida kallansa ga cikinta, itama ZAINAB haka, har suna had'a baki wajen cewa, "Yaushe rabanki da al'ada..

RAHMA tafara tunani tace "yau ina ga wata biyu da sati biyu kenan..

ABDUL ya kalli ZAINAB ya rad'a mata wani abu a kunne dayi mai murmushi da gyaɗa masa kai, RAHMA tana kallansu, haka dai suka tashi suka ficce daga gidan direct asibiti sukayi, RAHMA tayi mamaki matuƙa, musamman da taga dan ita sukazo asibitin, dan sai dubata ake.

Doctor ya kira ABDUL ya shaida masa tana d'auke da ciki wata biyu da sati biyu..

Murna ta kama ABDUL, farin ciki ya bayyana garesa, yayima Allah godiya.. da nutsuwa ya fito daga office d'in doctor d'in, kallo d'aya ZAINAB tamai tasan yana cikin farin ciki, haka RAHMAN ma, Nan ya gaya musu doctorn gaya masa yayi RAHMA na d'auke da ciki, kunya ta kama RAHMA ta sunkuyar da kanta qasa tana murmushi tare da wasa da zoban hannunta, ABDUL ya kalli ZAINAB ya d'aga mata gira tasaki murmushi cikin jin daɗi takama hannunsa tace, "Na tayaka murna sosai my dear..

Sam ABDUL bai nuna d'okinsa Sosai ba, dan yasan idan ya nuna saisa jikin ZAINAB yin sanyi, dan bai manta da lokacin da ita tasamu ba, yana tare da sanin bai wani nuna d'ukinsa sosai ba...

Ammafa da suka dawo gida ya keb'ance da RAHMAN, kamar zai cinyeta dan nuna mata farin cikinsa.. Sai sakarma cikin nata kiss yake, RAHMA tayarda ba qaramin so mijin nata yake mata ba, tun daga wannan lokaci tasa aranta zata qara kwaimi sosai wajen faranta ransa akan komai..

UMMAKATI da Momy Dady su Hajjiya Kakah sunyi farin ciki da samun cikin RAHMAN..

*WATA ƘADDARA😭*

Yau watan ZAINAB uku da haihuwa..

Sai hakan yayi daidai da watan Haihuwan UMMAKATI, wato yau ko gobe dai ana sakama UMMAKATIN rai da zuwan haihuwan..

RAHMA watanta uku da sati d'aya kenan da samun cikinta

Wata ƙawar ZAINAB me suna Asiya itace takawoma ZAINAB d'in ziyara awannan rana.

Asiya irin yaran nan ne marasa ji, masu yawan biye biyen malamai da bokaye..

Toh yau datazo ta tarar da ABDUL a gida baya jin daɗi ko fitta office baiyi ba, amma yanzu jikin da sauƙi, dama da safe ne jikin yafi matsa masa, haka kawai ya tashi da zazzab'in, sai hakan yazo a girkin RAHMA, saiya kasance tafi bashi kulawa fiye da ZAINAB, suna zaune ne dukkan a falan nasa, ZAINAB na gefe hannunta d'auke da Raheemat yayin da RAHMA take kusa da ABDUL tad'an shige masa jiki haka Amma ba Sosai ba,

Sai Asiya takira ZAINAB a waya, cewar gata a shashinta tazo kuma bata ganta ba, sai ZAINAB d'in tace mata, tana falan ABDUL taqaraso falan tagaishe shi dan bashi da lafiya...

Toh Asiya tace mata, ta qaraso falan ABDUL d'in ta gaishesa, RAHMA ta gaisheta ta amsa, sannan suka bar falan ita da ZAINAB d'in. Aiko barinsu falan kamar daman RAHMA jiran hakan take, nanta qarasa shigewa jikin ABDUL d'in... Ya kalleta da d'an murmushi irin na mara lafiya yace, "My dear, zan iya shafa miki wannan zazzab'in fah, dan kin shige jikina da yawa.. RAHMA tamai murmushi tace "Ai dama haka nake so, so nake na rabaka da ciwan, dan yanzu na saba da ciwuka kala kala, yace, "Amma ai ni kike bari da jinya, nidai yanzu kiraba kanki da jikina karki jaza mana jinya biyu..

Tace, "hmm ai saikayi.

Zura hannunsa yayi ga cikinta yana shafarwa ahaka har bacci yayi awan gaba dashi..

Asiya ta kalli ZAINAB tace, "kedai kima kanki fad'a wallahi ZAINAB kima kanki fad'a, dan ko makawo ne ya shigo gidan nan ya shafa yasan wannan shegiyar yarinyar ta mallake miki miji, yanzu ki duba yanda take wani maƙale dashi, yanzu ke tsakaninki da Allah bakiji kishi ba..

ZAINAB ta kalli Asiya da mamaki, tace, "Ikwan Allah, to ba matarsa bace, miye danta zauna kusa dashi, kefa mu rayuwarmu daban take da sauran kishiyoyi.. Idan kece da girki ABDUL gabaki d'aya hankalinsa akanki yake, haka cikin ni ko RAHMAN Wanda take dashi tattara hankalinmu muke gabaki d'aya akansa,

Wannan ai ba wani abu bane.

Asiya taja numfashi tace, ammako ni ZAINAB kina bani mamaki, wai har sai yaushe zaki gane kishiya abokiyar gabanki ce, ahar sai yashe zaki gane yarinyar nan tarigada ta gama da ABDUL.

ZAINAB tace, "Dan Allah Asiya mubar batun maganar ABDUL da RAHMA, nifa gaskiya bazan b'oye miki ba, ban cika san ki kawomin ziyara ba, danke kina da mummunar fahimta, yanzu kawai ki gaya min meya kawo ki..

Asiya ta cije baki tace, "wato ZAINAB nizaki wulaqanta dan nazo gidanki ko, ZAINAB tace "haba qawata, kema kinsan wannan ba halina bane, toh kiyi hak'uri idan ranki ya b'aci, yanzu gayamin meya kawoki...

Asiya ta qara cije baki ta zuge Jakarta ta fiddo da wata kwalba me d'auke da wani had'in maganin mata, tace, "Maganin mata na kawo miki, wannan maganin idan kikayi amfani dashi ABDUL gigicewa zaiyi akanki, matar data had'a wannan maganin tace karmu kuskura mu siyarma dame kishiya, toh naga ranar kin kawomin kukan kina san had'in maganin mata wanda zai gigita ABDUL, shiyasa da yanzu nasamu wannan ba wacce tafad'omin arai sai ke..

Da sauri ZAINAB ta karb'i kwalbar tana cewa, "Ammafa qawata nagode miki, saidai kince kar me kishiya tayi amfani dashi.

Asiya tatashi tana gyara gyalanta tace, "hmm Allah ya shiryeki ZAINAB, kika san ita me take sha, ai idan kikaji ance ga maganin mata amma kar'a bama me kishiya to kimaida kanki bame kishiya ba, kiyi amfani da maganin zakiga yanda hankalin miji Zai karkata ya dawo kanki,

Kud'in maganin dubu Ashirin da biyar ne, lakata zaki dingayi duk bayan sati d'aya kina sakawa a gabanki, wallahi na tabbatar saikin nemeni, dan mai bada maganin baya bada maganin banza..

ZAINAB tace "namiji ne me had'in maganin,

Cikin sauri Asiya ta gyara zancenta da cewa macece..

Haka ZAINAB tashiga d'akinta ta laloma Asiya kud'inta cif tabata, sannan tayi gaba..

Washe gari Abdul ya samu sauqi toh dama ya shiga girkin ZAINAB..

Dare nayi bayan sallar isha'i ZAINAB tasaka magani..

Tunda tasaka taji yanda maganin yake bin jikinta tasan ba qaramin mekyau bane.. Maganin yayi over, nan take ya ciko mata dakomai na gabanta fiye dada..

ABDUL na shigowa hannunta ya wani gigice mata..

Ran ZAINAB yayi mata fari kwal dan tunda take dashi bata tab'a ganin gigicewarsa irin na wannan rana ba,

Ga ABDUL ko bai tab'a jinsa cikin jin daɗi irin na wannan rana ba.

Sai Kallan ZAINAB d'in yake zuciyarsa na gaya masa akwai abin datayi, dan shi tunda yazo duniya bai tab'a jin wannan mafificin daɗi haka ba..

Ko kad'an ABDUL baiji dad'in fitta daga girkin ZAINAB da yayi ba..

Hankalinsa yayi mugun tashi tayaji RAHMA tadawo salam🙁..

Kamar ba RAHMANSA ba, washe gari ma abin dayaji jiya akanta haka ya qaraji agareta, ya koma girkin ZAINAB yaji abin dayaji ranar, yaji dad'in kamar qara yawa yake agareta..🤔

Kwana takwas kenan yana jin wannan canji, ZAINAB cakwai👳 RAHMA salam🙁,

Yau da yake d'akin Zainab kallanta yayi da cewa, "Aunty, wai me kika sha ne dan Allah, ta kallesa da murmushin wasa tace "Ban sani ba.

Shuru yayi mata, "Gaskiya akwai babbar matsala, ya faɗi hakan a bayyane, batare dayasan ya faɗi hakan a bayyanan ba.

ZAINAB tayi dariya tace, "Me kace"

Yace "Cewa nayi bazan iya rayuwa babu ke ba.

Dad'i ya qara kama ZAINAB, tace "Faɗi dai gaskiya, dan da farko ba haka kace ba..

Tashi yayi daga d'akin ya bar mata, direct part d'in RAHMA yayi, ya ganta zaune gefan gado tana nemo kayan bacci da alama wanka tayi, saiya qaraso kusa da ita ya tadata tsaye yace, "My dear, yanzu kike wanka qarfe gama sha biyu saura fa, bayan d'azu nazo naganki kina bacci..

RAHMA tace, "aa, k'aik'ayi naji jikina namin shine naje na qara yin wankan, wallahi bakaji yanda naji dad'in jiki nawa yanzu ba..

ABDUL ya karb'i rigar baccin dake hannunta ya tayata sawa, kana ya zaunar da ita gefan gadan yana Kallan cikinta, sai girma yake, gaskiya zatafi Aunty Zainab girman ciki ya faɗi hakan aransa..

Afili ko kama hannunta yayi yana murzawa yace da ita.. "Gaskiyà akwai babbar matsala my Baby,

RAHMA ta waro ido tace, "Wata irin matsala, ABDUL ya qura mata ido yana tunani, candai yace, "Wallahi baby banajin dad'in raya sunna dake.

Ayanzu nafi jin daɗin Aunty Zainab fiye dake.

My dear bazan iya b'oye miki ba, bana san wannan canjin dayazo gareki, pls kigyaramin kanka gaskiya akwai matsala, kuma ki fahimceni, kinsan ni me ƙaunarki ne, babu wani batun kunbiya kunbiya tsakanina dake, dan Allah kimin maganin abun, kinsan na saba dake, bazan iya zuba miki ido haka ba, dan haka bana so abin yayi nisa gaskiya, dan zai zama cutarwa ne agareni..

Ainan take cikin RAHMA ya d'ori ruwa, tadanne, hankalinta ya tashi kamar tafashe da kuka, haka dai tamai kiss a gefan kumatu tace, "Nagode me SONA, hak'ik'a kacika masoyin asali, insha Allah zakaji canji, amma Allah zan rok'a yakawo min canjin, dan Wallahi banyi komai ba kaji wannan canjin..

Rungumarta yayi dan takasa jurewa sanda hawaye ya zubo mata..

Sanda ya tabbatar ya kwantar da ita, yaja mata bargo, sannan ya koma shashin nasa inda ZAINAB take..

RAHMA ko bata iya bacci ba a wannan dare..

Washe gari suna breakfast sai Kallan ZAINAB take tana zargin anya ba wani abun tasha wanda yasa ABDUL d'in jinta babu dad'in ba..

Tana cikin tunanin ya shafi gefan fuskarta yace, "Tunanin na miye haka..

Murmushi ta sakar mai zata bashi amsa sai Zainab tayi karab tace "Ai kaima kasan ba wani tunanin da zatayi sai naka, idanko ba naka takeyi ba to tana tunanin Haihuwa ne.

RAHMA ta sakar mata murmushin itama, tace, "Aunty duk baki canka ba, dan awannan lokacin tunanin mamana nake, takai qarshen zancen da kallan ABDUL... Sannan a shagwaɓe taci gaba da cewa, Dan Allah mijina kakaini wajen mamana naganta, bazan iya jure qin ganinta a wannan lokacin ba, idan ban manta ba nad'auki kusan shekara biyu kenan rabona da dangina..

ABDUL ya d'auke kallansa akanta jin yaji wani iri haka, shagwaɓarta fami takema zuciyarsa wajen hankad'o masa qaunarta..

Cikin nutsuwa yace, "Toh ki shirya gobe zan kaiki, dama ina jiran na ganki da ciki ne saina kaiki...

Murna ta kama RAHMA Sosai, kantayi magana saiga kiran wayar AMEER ya shigo wayar ABDUL, yana d'auka yace mishi gasu a asibiti UMMAKATI ta Haihu tasamu y'arta Mace..

Murna sosai ABDUL yayi Sannan ya gayama su RAHMA, ai ba b'ata lokaci sukace ya jirasu su shirya yanzu ya saukesu a asibitin,

Toh yace musu,

Haka suka tashi suka bar abincin da suke ci yabisu da kallo, dama little Raheemat tana hannunsa, saiya maida hankalinsa akanta kawai.

Aiko sunga y'ar UMMAKATI kyakkyawa da ita kana kallanta kaga AMEER..

Dama anan sukazo suka tarar da momy dasu mama Saude harda su Dady..

Da aka gayama maman UMMAKATI haihuwar rokwan alfarma tayi gun baban AMEER da momy kan sukawo mata itta wankan gida dan Allah, ƙafarta na mata ciwo ne bazata iya zuwa ba.

Momy ta fahimci maman UMMAKATIN Sosai take buqatar a bata UMMAKATIN dan wankan gidan.. Hakan yasa tajanye d'aukarta da tayi niya tace mata insha Allah gobe zasu kawo mata ita garin jos d'in..

Hakan baima AMEER dad'i ba.

Amma yazaiyi.

RAHMA ko dama goben ABDUL yace mata zai kaita can d'in sai hakan yazo a daidai..

Aiko tare dukkansu sukayo garin jos d'in harda ZAINAB..

Zanso kuga yanda yayun RAHMA da qannanta yanda suka nuna murnarsu da ganinta, sai sha'awarta suke ganin ta qara kyau tayi b'ulb'ul da ita, ga cikinta yayi mata kyau sosai..

Kishiyoyin mamanta ko ba qaramin baqin ciki sukaji da ganinta hakan ba, musamman cikin da suka ganta dashi..

RAHMA tayi mamakin ganin gyaran da akama gidansu ta tambayi mamanta waye ya gyara musu gidan.. Tace ABDUL ne ya turo ma da Yayanta Usman kud'i yace dan Allah agyara gidan, kuma lokaci lokaci yana aiko musu da kayan abinci, saidai kawai sugani ance musu daga Kaduna ne inji ABDUL..

Haka gidansu UMMAKATI ma shiya bada a gyara musu, kuma har itama yaje turoma da kayan abincin..

RAHMA tayi murna sosai dajin hakan.. Nan tashiga yima ABDUL d'in godiya ya harareta,

Saita kalli yayunta tafashe musu da kuka tana neman yafiyarsu kan rashin kunyar datayi musu da rashin jin maganarsu da batayi..

Sun yafe mata anan suke qara shaida mata ashe duk kwalla kwallan su Iyami ne, suka qara da bata labarin d'an uwan Lantana dayazo gadi gidansu..

Sukace mata ABDUL ne ya gayama babansu komai,

Aiko ran RAHMA ya b'aci matuqa tace bazata tab'a yafema matan baban nata ba..

Nan suka gaya mata ai dukkansu baban nasu ya musu saki bibbiyu, kuma ya gaya musu idan suka qara yungurin yimata wani abu  Wallahi abakin auransu, dan zai qarasa musu Sauran igiyarsu d'ayar datayi saura...

Jin hakan yasa RAHMA yin shuru..

Kama hotel d'in Sharna ABDUL yayi musu shida ZAINAB, AMEER ma anan ya kama d'aki, kwanansu d'aya sukabar garin jos d'in amma kallo d'aya zakama ABDUL kasan ya bar RAHMA a garin ne kawai dan ba yanda zaiyi..

Amma yadai ce mata ana yin suna tashirya zaizo ya d'auketa....

Kwana biyu da zuwan su RAHMA garin jos, RAHMAN tacire kunya ta gayama mamanta matsalarta, wacce mijinta ya gaya mata, dake RAHMA mamanta wayayyiyace, tajata ajiki sosai tun tana gida duk wani sirrin RAHMAN bata b'oye mata, har lokacin data kamu da wannan ƙaddarar, bata dena gayama maman nata abin dayake damunta ba.

Yanzu ma da maman nata taji wannan batu murmushi tayi tace "natab'a fuskantar wannan matsalar RAHEEMAT, sanda nayi shekara ina shan magunguna amma abanza ban dawowama mijina dai dai ba,

Hawaye ya zuboma RAHMA tace, "Yanzu shi kenan bazan dawo daidai ba..

Maman tata taqarayin murmushi tace, "aa zaki dawo daidai, akwai wani bafulatani a saban garin narabi, zanje gobe na karb'o miki saiwar daya bani wancen lokacin na dafa nake sha na kwana uku, Allah dai yasa yana nan bai mutu ba..

RAHMA tace ameen,

Aiko washe gari maman RAHMA taje wajensa, taci sa'a yana nan da ransa, ya bata saiwar, tabashi d'ari biyu, ya bata naira d'ari, dan shi baya tsawwalawa wajen saka kud'i akan maganinsa..

Nan maman tata ta dawo gida, babu b'ata lokaci tadafa mata, ta bata tadinga sha, sannan still ta qara sawa aka rubuta mata suratul maryam da Yusuf aka wanke da ruwan kankana tashanye tas, shi kenan abinda maman tabama RAHMA amma nan RAHMA taji canji ajikinta..

Yawo kam RAHMA tasha shi a garin jos, duk yawancin qawayensu way'anda sukayi Aure sanda taje gidansu, UMMAKATI kamar tadinga binta haka taji idan tadawo tana bata labarin inda taje..

Kaf y'an uwanta duk sanda RAHMA taje gidansu, kuma masha Allah duk tasamu canji daga garesu, dan sun nuna mata qauna matuƙa..

ABDUL duk kiran dazaima RAHMAN saitace mishi tana gida kaza, duk da ayanzu yana matuƙar ji da ZAINAB amma hankalinsa yana kan RAHMAN, shi tunaninsa cikinsa, yana ganin yawan fitan da takeyi karyaje ya jawo cikin ya zube😂 har wajen doctor yaje ya gaya mai yace masa ya kwantar da hankalinsa ba abinda zai samu cikin nata

Hakan yasa hankalinsa kwanciya..

 

Ranar suna yarinya taci sunan momy.. Suna kiranta da mamy..

Sosai momy taji dad'in karar da AMEER yayi mata, hakan yasa taqara sanshi sosai aranta.

Kuma babansa ne da Hajjiya Kakah sukace asaka sunan Momyn, har mama Saude tatashi zatayi bori Hajjiya Kakah tadakatar da ita da cewa Momy fa tashayar da AMEER, bashi da abin dazai saka mata..

ABDUL sai shiri yake washe garin sunan zaije ya d'auko RAHMA da momynsa, dan momyn nasa tun ana washe gari suna taqara dawowa jos d'in

Saidai dayazo garin jos d'in qememe RAHMA taqi binsa wai saita qara sati d'aya..

Momy kuma tace dole ya barta,

Haka badan yaso ba ya barta yanata harararta..

UMMAKATIN ko taji daɗin wannan wankan gida, dan ba qaramin gyarata mamanta takeyi ba..

RAHMA na qara yin sati d'ayan ABDUL bai qara ko kwana d'aya ba yazo ya d'auketa..

Koda yajita yasamu canji sosai. Tadawo mai yanda take da, amma fa batun jin daɗi yanzu yana yin ZAINAB dan yanzu ZAINAB d'in kat ce a harkar, har d'aukar zuwan kwananta yake, amma azuciya, batun gamsuwa kuma yafi samun gamsuwa agun RAHMA...

UMMAKATI tadawo Kaduna daga wankan gidan, amma saidai wata y'ar iskar budurwar mijinta AMEER tayi mata b'arna🙁

Zaku gane b'arnar kuci gaba da bina ni Rahma muh'md Rufa'i nalele..

RAHMA da ZAINAB suna cikin tafiyar da zaman nasu a haka, sai kawai ZAINAB tafara fuskantar wata matsala a gabanta,😳

Abin ya faro ne wata rana ranar asabar, taje tsugunno kawai sai taga abu kamar balanbalo ya zazzago mata🤔, tasa hannu zata jawo taji wata azab'a zafi wanda bata tab'a jin irinsa ba, toh dama ranar, ranar girkinta ne, ABDUL daya zo jinta kamar yanda ya saba sai yaga abun, hankalinsa ya tashi ya tambayeta menene wannan, tace itama bata sani ba,

Habawa washe gari nayi ZAINAB taje tsugunno basai taga wasu abu kamar nama ne hanta ce oho🤔 sai fito mata suke, hankali tashe ZAINAB ta gayama ABDUL tayi asibiti.

Doctor ya dubata yace ai tasamu kansar mahaifa ne, kuma shi bai tab'a ganin irin nata ba, dan haka akwai abinda tasaka awajen daya jawo mata hakan.

Hankalin ZAINAB ya tashi matuƙa..

Tun a asibitin tafara kuka.

Haka dai doctor yabata wasu magunguna yace taje tasha, yanzu an mata hoton mahaifar da wasu gwaje gwaje idan sakamakwan yafito gobe tazo ta karb'a..

ABDUL daya tambayeta me doctor yace mata bata bashi cikakkiyar amsa ba, komai ya kwab'ema ZAINAB, abin gwanin ban tausayi, gashi takasa gayama kowa.

Washe data koma shuru doctorn yayi mata, yaqi bata sakamakwan yace sai ta kira ABDUL tukunna,

Ba musu takira ABDUL, lokacin yana office, dayaji abinda tace ba shiri yayo asibitin, lokacin da doctor ya bashi sakamakwan gwajin tunanin ABDUL kusan tarwatsewa yakusa yi.😨

Cikin tashin hankali ya kalli ZAINAB da doctor d'in yace "Dan Allah doctor karkasa jinana yahau, kamin bayani yanda zan fahimta, karka fara tabbatar min da cewa abin dana karanta awannan takaddar gaskiya ne..

Doctor ya tashi cikin lallashi ya dafa kafaɗar ABDUL d'in Cikin sanyayyiyar murya yace dashi, "Wallahi ABDUL abin daka gani jikin wannan fefar gaskiya ne, nasan kai musulmi ne me yarda da ƙaddara ina so kayarda Allah ne me kowa me kuma komai, shiya baka ZAINAB shi zai d'auketa aduk lokacin daya so..

Aiko ABDUL na tashi ya kalli ZAINAB nan ya faɗi qasa sumamme...

Abin da ZAINAB bata sani ba shine, maganin da Asiya tabata, boka ne ya had'ama Asiyan, Sannan da mugunta yake saka cutar jikin maganin dancinma wani buri nasa..

ZAINAB tayi zarab zata d'auki sakamakwan ta karanta doctor d'in ya rigata d'auka.. Ta kallesa

da mad'aukakiyar damuwa tace, "Dan Allah kabani na karanta.. Doctor d'in bai kulata ba nan ya kira ma'aikatansa suka d'auke ABDUL daga office d'in dan basa temakwan gaggawa...

ZAINAB ta nacema doctor d'in saiya bata takaddar ta karanta amma k'ememe yaqi bata... Ya kalleta da cewa, "zan baki ki karanta ZAINAB, amma sai in har ABDUL ya yarda, sannan kafin nan kigaya min me kike sakawa a gabanki wanda yajawo miki wannan matsalar, cikin kuka sosai ZAINAB tace, "Wani maganin mata ne wata qawata tabani, doctor d'in yace "Yanzu maganin yana nan, tace "eh yana nan, yace taje maza tad'auko mai yanzu ya gani..

Aiko ba musu nan ZAINAB tayi gida taje tad'auko mai maganin.

A binkicen da doctorn yayi ya gane sinadaran da akayi amfani dasu wajen had'a maganin sinadarai ne masu matuƙar illah..

Suna saka kansar mahaifa, suna tsittsinka hanji mutum, suna hana aihuwa, sannan uwa uba bazai tab'a barin mutum yayi rayuwa me tsawoba..

 

Kuka sosai ZAINAB tayi dajin wannan bayanin nasa, tayi nadamar yin amfani da wannan magani Sosai, da kud'inta tasiyama kanta bala'i🙆.

Har dai yanzu yaqi bata ta karanta takaddar..

Daqer da sid'in goshi aka samu ABDUL ya farfad'o, zanso kuga yanda ABDUL yake kuka kamar wani qaramin yaro,😭 ZAINAB tayi tayi ya gaya mata me yasa shi kukan amma yaqi kulata,

Can data damesa baisan lokacin daya d'a hannu ya tsinketa da mari ba..

A gigice ZAINAB ta kallesa hannu dafe da kuncin nata tace, "AB ABDUL ni ka ma ra.. Ta faɗi maganar cikin in ina..

Ya kalleta cikin sanyin jiki yace, "Aunty kiyi hak'uri bansan meyasa na mare ki ba...

Tace "ban damu da Marin ba, nafi damuwa da kukunka.

Ya girgiza mata kai da kallan doctor yace, "ina fatan bata karanta sakamakwan ba..

Doctor ya d'aga masa kai yace, "ban bata ba Abdul, ai bazan bata ba harsai ka yarda,

ABDUL yayi shuru yana tuno karanta sakamakwan gwajin nata da yayi.

Sakamakwan ya nuna sakamakwan saka wani abu da takeyi a gabanta ya harfar mata da wani ciwo me ƙari wanda ya d'auki lokaci yana gutsuttsure mata a mahaifa, wanda yasa mahaifar kamuwa da kansa, kuma yake cinye mahaifar, ayanzu cutar ta shafi hanjin cikinta, kwata kwata bazatayi wani tsawan rayuwa ayanzu ba, binkicen ya nuna daqer takai wata d'aya nan gaba araye, dukko maganin da zatasha arayuwa..

Wannan shine yasa ABDUL sumewa dan bai shirya ma rayuwarsa rayuwa babu ita ba..

Wannan shine yasa ABDUL kuka wiwi...

ZAINAB ta nace sai an bata takaddar ta karanta.. Abdul yayi mata dabara wajen ce mata kansace takama mahaifar tata, idan har bata shan magani akan lokacin zai iya rasata, wannan shine abin daya sashi kuka..

ZAINAB najin hakan hankalinta ya qara tashi, doctorn ya rubuta mata maganin dazata dinga sha, wanda zai temaka mata ayanzu..

Sanda ya tabbatar tayi waje Sannan ya gayama ABDUL maganin da take amfani dashi, da irin cututtukan dake jikin maganin..

Shuru kawai ABDUL yayi, ya karb'i takaddar sakamakwan.. Dacema ya duba mai tasa lafiyar, babu ko b'ata lokaci nanya hau dubasa, harda yi masa hoto, yace mai ya dawo gobe ya karb'i sakamakwan.

ABDUL toh yace masa da zuwa motarsa, anan cikinta yaga ZAINAB d'in tanata rizgar kuka..

Da daqer ya iya kaisu gida lafiya..

Yaje d'akinsa ya b'oye takaddar..

Yana zama yaji zazzab'i ya kamasa abu kamar wasa ZAINAB da RAHMA suka kasa gane kansa,

Ba shiri suka koma dashi asibiti..

Akalla ABDUL yakai sati uku yana kwance a asibitin, danya saka abin aransa matuƙa, ga kuka, koyaushe idansa cikin hawaye..

Duk da doctor ya tabbatar masa shi baya ɗauke da wata cuta, dan ga sakamakwan gwajin dayayi masa nan ya nuna sam bashi da wata cuta, dama mafi akasari yafi yima matan illah..

Dady Momy Hajjiya Kakah babansa ada RAHMA ZAINAB d'in ba irin magiyar dabasu masa ba kan ya gaya masu me yake damunsa amma yaqi..

Ciwan nasa yafi tashi idan ya kalli ZAINAB..

Lura da hakan da doctor yayi ne yace da ZAINAB d'in tadena shiga d'akin da yake..

Daqer dai aka samu kan ABDUL..

Ana dawowa dashi gida ciwo ya tasarma ZAINAB. Nan itama aka kaita asibitin, doctor ayanzu bazai iya b'oyema kowa ba, dan haka nantake ya gayama su Dady abin dayake damun ZAINAB d'in..

Hankalin kowa ya tashi, musamman UMMAKATI da tafi kowa sanin maganin mata😨

RAHMA tasa kuka wiwa bata tab'a zatan zata so ZAINAB a rayuwarta ba, haka kawai ayanzu taji tausayinta ya cika zuciyarta, zatabar  d'akin kenan ZAINAB d'in tayi saurin rik'o hannunta, tace dasu Hajjiya Kakah Dan Allah sufita xatayi magana da ABDUL da RAHMA

Suna fitta ta kalli RAHMA da tutsetsen cikinta wanda yake San fitta watan gaba da zasu shiga, tace da ita, "RAHMA ba rayuwa zanyi ba, azahiri bani da abin qi kamarki, amma ayanzu banda abar so kamarki, dan nasan bame riqe min Rahma amana amarki, tunda kina matuƙar ƙaunar mahaifinta, ga amanar little Raheemat nan nabaki a hannunki, dan Allah kiyi rayuwa da ita rayuwa irin wacce zakiyi da y'ay'an da kika harfa a cikinki, sannan kiyafemin dan nice naba Uwani maganin hana d'aukar ciki tabaki dan atunanina bana haihuwa, dan Allah kiyafemin.

Kuka sosai RAHMA takeyi tana cewa, "Nayafe miki Aunty Zainab wallahi na yafe duk abin da kika min, dawanda nasani dawanda ban sani, nima ki yafe min idan nayi miki wani, kiyafe min sharrin dana miki wajen Momy, dan Allah kadda ki mutu wallahi nima ina sanki Aunty Zainab karki mutu..

ZAINAB tace "Nayafe miki, da sakin hannunta takama na Abdul taci gaba da cewa, "dan Allah ka yafe min dukkan abin dana maka arayuwa ABDUL, hawaye ya zuboma ABDUL yace "Aunty bakimin komai ba, idan ma kinyimin na yafe miki, nima kiyafe min.

Tace "na yafe maka ABDUL, wallahi na yafe maka, na aikata hakan ne dan nima ka dinga samun jin daɗi agareni, ashe idan wani yayi rawa yaci nasara wani idan yayi fad'uwa zaiyi..

ABDUL ya qara zubo da hawaye, yace "Aunty dakin zauna ayanda kike, dana rayu dake rayuwa me tsawo, kuma kin kasa yima kanki adalci dan ina gaya miki ina samun nutsuwa da kwanciyar hankali agunki..

Aunty me yasa kikamin haka, Aunty ban nuna miki cewa bana jin daɗin rayuwa dake ba, Aunty baki San ina qaunarki ba, Aunty dan Allah karki mutu kizauna muci gaba da rayuwa...

ZAINAB ta share hawaye, tace, "wannan ƙalubale ne gareku mata, maganin mata yafi yima mace illa fiye da ɗa namiji,

Kuna dai gani kud'i na nasiyama kaina masifa, damuwar tamiye ne, da zaki sa aranki sai mijin ki yajiki fiye da kishiyarki, karkiyi abinda kikaga yayima wata akan komai, mata musauqaqama kamma da shaye shayen magungunan da basu da inganci, musamman na sawa, kan yayima mijinki illa sau d'aya kya zaiyi miki sau dubu.

ABDUL ya sakarma hannunta kiss, yace "Aunty kibar sambatu, kibar batu akan wannan lamarin, nidai fatana kitashi, Aunty baki da mugun hali, kina da tausayi, kina da kirki, gaki da saurin fahimta, komai d'aukarsa kike da sauƙi, wannan yasa nake qaunarki.. Aunty ina San rayuwa dake kitashi pls karki mutu......

Kamar jiransa ZAINAB take ya rufe baki, nan tahau salati, RAHMA ta qara waro ido, ABDUL ko shuru yayi ya zuba mata ido. Nan ba tare da b'ata lokaci ba ZAINAB tace ga garinku nan, wato rai yayi halinsa...😭😭😭😭😭😭😭

ABDUL ya rintse idansa hawaye ya zuboma mai, yace"shikenan Aunty kin tafi, yana faɗin hakan ya tashi jikinsa a sanyaye yabar d'akin..

RAHMA ta zuba mata ido, dama dama, dama tana da hali, datace ad'auki ran abin dake cikinta abar ZAINAB d'in araye, ashe baka sanin kana qaunar mutum sai kaga ya shiga wani,

ABDUL fitansa kanya qarasa wajensu Momy nanya faɗi qasa sumamme, sukayo kansa Cikin sauri,

RAHMA ta rufema ZAINAB ido tafito tana bin bango, nan ta kallesu tace, "Kubar shi, dan dole ya faɗi, Aunty Zainab dai tatafi bazata dawo ba..

Aiko nan suka hau salati. Hawaye ya zuboma AMEER yace, "Innalillahiwainna'ilaihirraji'un..

_¶Share_

_¶Vote_

_¶Comment_

_¶Follow_

AUNTYN LUV yau babu kiss bare dariya y'an hanuna👐🏻

 

´-'´- “˜• ¸ª_'

*.¸¸.**.¸¸.*🙆*.¸¸* *.¸¸.*.¸¸.*

 

 *TANTIRANCI KO KARUWANCI*

 

*.¸¸.* *.¸¸* ¸¸.*¸* *.¸¸.*🙆*.¸¸*

'´-'´- “˜• ¸ª_'•🤱🏻

 

 

Written by Rahma Nalele.

 

 

Sardaunah

 

 

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ

Page 24..

*😄😄😄😄 ina qaunarku MASOYA na*

16 read more nayi muku

*****************************

Kowane me rai dole yasan akwai ranar mutuwarsa, ZAINAB dai tatafi kuma bazata dawo ba, ABDUL bai tab'a tunanin yana San ZAINAB sosai haka ba, sanda ta rasu sannan ya San baqaramin So yake mata ba...

Toh ya zaiyi kowa zaman jiran tasa yake.

Hajjiya Kakah mama Saude Baban ABDUL ada Dady & Momy yan uwan arziqi, qawayen arziqi, masu saka ido marasa saka ido duk sunyi kukan rashin ZAINAB, dan ZAINAB mutum ce, kowa addu'ar Samar mata rahama yake..

Momy ce ta d'auki little Raheemat dan bata kulawar data dace..

Anyi uku anyi bakwai anyi arba'in, yanzu zaman kewa ake.

Kwanar goma dayin arba'in d'in ZAINAB ciwan daquda ya kama RAHMA..

Dake cikin dare ne ya tasar mata kusan qarfe d'aya, hakan yasa ABDUL Cikin tsoro matuqa, musamman kukan da RAHMAN take tana cewa, "ABDUL zan mutu, ABDUL zan mutu, dan Allah katemakeni, Yace "bazaki mutu ba my dear, idan kika mutu nima fa binki zanyi, ta qanqamesa tana sakar salati.. Ai ba shiri ABDUL yayi asibiti da ita, duk zuciyarsa a jagule take, yanzu idan itama ta mutu ya zaiyi😭😭..

Alwala ya d'auro a asibitin ya hau sallar nafula yana rokwan Allah ya saukarmai da ita lafiya, Sannan yabar mai ita surayu cikin inuwa d'aya..😭

Azaba kam RAHMA tashata, dan ba ita tasamu kanta ba sai kusan qarfe biyar na asuba, ta haifo kyakkyawan d'anta namiji, kallo d'aya zaka mai kasan ABDUL ne, dan kamar tasu tayi yawa kamar am tsaga kara.

Ma'aikatan asibitin na gayama ABDUL ta haihu tasamu d'a namiji yanzu haka tana d'akin Hutu ba qaramar ajiyar zuciya ABDUL yasake ba..

Yaje ya kama hannunta ya sumbata yace "Gashi dai baki mutu ba my

Baby, tayi mai murmushi tace, "Gaskiya Allah ya sakama iyayenmu da alkairi, wallahi sha kallo, haihuwa da zafi matuƙa, da gaske ji nake kamar bazan rayu ba, gaskiya bazan qara yin ciki ba, ta kai qarshen zancen nata da shagwaɓa..

ABDUL yayi murmushi da faɗin, "Ai yanzu kika fara my Baby, me akayi da maza, tunda Aunty Zainab bata nan, wannan alƙawari ne sai kin bani yara goma sha hud'u, little Raheemat tazama ta sha biyar..

RAHMA ta waro ido, tace "14 Babys..

Yace "Yeah, sunyi kad'an ne, tace "Yawa dai, ina ma lefin kaqara samun biyu nan gama, kaga 4 ai sun ishemu..

Yace "Ina, Wallahi da gaske nake miki yara goma sha biyar nake fatan Allah ya bani..

RAHMA tayi shuru tana tuno azabar data sha..

Saidai gashi ganin d'an nata ya wanke mata zafin fitowar tasa da taji..

ABDUL kamar ya cinye yaran nasa haka yake ji aransa dan qauna, yaran yazo da kyau ba lefi..

ABDUL ya kalli RAHMA da katse mata tunanin nata yace, "Wato duk girman wannan Cikin naki dama 1 zaki bani,

RAHMA tayi murmushi da cewa, "Toba gashi na baka kyakkyawa ba, me kamarka fa sak na haifo maka.

"Haka ne my dear, nagodema Allah Sosai daya bani shi, Allah ya qara sawa kibani Baby girl nan da 1 year..

RAHMA tayi shuru, yaci gaba da cewa, kinqi cewa komai, tace "Toh mezance..

Yace "kice ameen kawai, idan kuma kikaqi cewa sainayima kaina addu'ar Allah ya bani damar qara Aure nan da wata uku...

RAHMA ta kallesa da sauri, tare da wurga masa harara, tace, "me kace, da sauri ya rufe bakinsa da hannu yana girgiza mata kai alamar baice komai ba.

Cikin shagwaɓa taci gaba da cewa, "idan akan haihuwa ne zaka min kishiya, insha Allah bazaka tab'a yimin ba, ayanzu na cire tsoronta Allah yata bani ko ashirin ne zan baka mijina..

Ya shafa gefan fuskarta yace, "Yauwa nagode nutsuwata...

 

Ba qaramin mamaki su momy sukaji ba da ABDUL ya kirasu yana gaya masu ta haihu, ai ba shiri momy da Hajjiya Kakah sukayi asibitin.

Anan sukaga AMEER da UMMAKATI, hannun AMEER d'in d'auke da yaran.

Da gaske yanda little Raheemat tazo da farin jini haka yaran shima yazo da farin jinin..

Dady da baban AMEER sunyi murna sosai da zuwan yaran duniya.

Dangi y'an uwa da abokan arziqi sunyi murna sosai..

Haka y'an uwan RAHMA ma sunyi murna, momy ta gayama maman RAHMA zata d'auketa wankan gida, duk da maman RAHMA taso ace itace zata mata wankan, amma haka tanunama momyn kara tace mata babu komai ai..

Da yamma aka sallamesu daga asibitin, aiko direct gidan momyn akayi da ita,

Wannan zuwan nata ma ad'akin momy ta sauka.

Gaskiya ABDUL baiji dad'in wannan wankan gida ba, yanzu shi d'aya zai dinga kwana a gidan nasa kenan, gashi idan zai kalli shashin ZAINAB sau dubu saiya tuno da ita sau dubun nan..

Gaskiya kewarta tana damunsa, ayanda yake ji aransa bazai iya cigaba da zama a gidan ba..

Washe gari haka yaje ya gayama Dadynsa cewar shifa gaskiya bazai iya zama agidan nasa ba, gaskiya ZAINAB tana yawan damun zuciyarsa, musamman idan yana kallan shashinta..

Dady ya fahimci ABDUL d'in sosai, yace ya bashi nan da sati d'aya zai duba masa wani waje mekyau saisu koma can. Aiko da murna Abdul ya rungumi Dadyn nasa yana meyi mai godiya..

Y'an uwan RAHMA sunzo qannanta da yayun nata.. Tayi ko murna sosai da ganinsu..

Ranar suna yaro dai yaci sunan mahaifin ABDUL wato Dady.. Suna kiransa da Abba.

RAHMA tasamu kaya sosai bana wasa ba, damma mutuwar ZAINAB bata bar zukatan mutane ba, da tabbas datafi samun farin ciki awannan aihuwar tata..

Kwana uku da suna y'an uwanta suka koma jos, tare da sha tara ta arziqin da momy tayi musu da ita kanta RAHMAN..

Dady ya Samar ma ABDUL wani fili me mugun kyau gashi cikin jerin unguwannin manya..

Dake filin yana da girman gaske, Dady ya umarci AMEER daya siye rabin filin, aiko AMEER ya siya, sai aka yankarma ABDUL nasa babu b'ata lokaci aka hau ginawa,

Ita dai RAHMA Abdul ya kawo mata zanan wasu gidaje guda 5 yace tazab'i wanda yafi mata kyau, aiko tazab'i wanda yafi mata kyau d'in, ta tambayesa meyasa ya kawo mata yace ta zab'a..

Ahankali ya kama hannunta ya zauna a gefan gadan momyn, yace "My baby, bazan iya cigaba da rayuwa acikin gidanmu ba, saboda ina yawan tuna Aunty Zainab, tunaninta na damun ZUCIYATA matuƙa, hakan yasa na gayama Dady kuma ya fahimceni harya nemamin wani fili, Ammafa yana da nisa da gidanmu sosai, saidai wajen yayi kyau, yanzu haka ma'aikata jirana suke nakai musu wannan zanan da kika zab'a, na tabbatar gina wajen bazai d'auki lokaci ba.

RAHMA najin haka hawaye ya zubo mata, tace "yanzu zan rayu ni kad'ai kenan, yanzu zan rayu babu kowa kusa dani kenan, gaskiya bazan tashi daga gidan ba, haka kawai ka rabani da UMMAKATI, gasu Momy suna kawo min ziyara shi kenan ba wanda zan dinga gani, nidai bazan koma ko'ina ba..

Abdul ya kama fuskarta ya sakar mata kiss, cikin matuƙar ƙaunar ta yace, "my dear dole mubar wannan gidamu, idan har kina San ganina cikin nutsuwata akowane lokaci, wannan daga ZUCIYATA yake, har abada bazan tab'a sauya wannan ra'ayin nawa ba, kisama zuciyarki nutsuwa kiyi tunani, su Momy bazasu iya barin ki dan kinyi nisa dasu ba, bare kuma UMMAKATI, na tabbatar wata rana ma gida wani nasu gidan zasuyi a jikin namun, muci gaba da rayuwa yanda muka faru, ma'ana, filin mun rabasa biyu ne nida AMEER, kinga ko dole wata ranah sudawo garemu.

RAHMA zatayi magana yayi saurin katseta wajen cigaba da cewa.. Bana San ki b'atamin tunani, dan Allah kibarni nabi umarnin zuciyata, zanji haushinki matuƙa idan kikaqi bani goyan baya..

Cikin kuka me tafe da shagwaɓa tace, "Shikenan mijina, dole naso duk wani abu da kakeso, wallahi ko a daji zaka ajiyeni ba kowa kusa dani zanyi maka ladabi da biyayya na zauna bazan tab'a baka kunya ba..

Aiko yana jin hakan ya rungumeta yana mejin dad'i aransa, nan d'umin jikinta ya fara cigarsa, ya fara tunani yanda yayi missing d'inta, kwana takwas kenan rabansa dajin d'umin jikin nata..

Hakan yasa yaƙi raba kansa da jikin nata akan lokaci, har sanda Momy tazo tagansu a haka.

Tace "ABDUL tashi ka fitta...

Da sauri ya raba kansa da jikin nata suka maida kallansu ga momyn.

Ta wurga mai harara daci gaba da cewa, Nace ka tashi ka fitta ko..

Aiko ba musu ya ficce daga d'akin..

RAHMA ta sunkuyar da kai..

Momy ta qaraso gareta ta kwantar da Abba dake little Raheemat ma na bayanta ta kwantar da ita, Sannan ta kalli RAHMAN taci gaba da cewa, Kima kanki fad'a RAHMA, shi namiji ba ruwansa, yanzu zai siyeki da Dadyn baki ya qara yimiki wani cikin tunkan kiyi arba'in...

Da sauri RAHMA ta d'ago da kanta ta kalli momyn, saiko momyn ta gyaɗa mata kai daci gaba da cewa, Da gaske nake gaya miki, dan haka ki kula kinji..

"Toh, RAHMA tace mata..

Tun daga wannan rana basu qara jin rumin juna ba, har tayi arba'in.

Gyara kam RAHMA tasha shi, musamman da ayanzu momy taga babu ZAINAB.

Kwana uku dayin arba'in d'in RAHMA, ABDUL yazo yasa momy agaba wai tabashi RAHMA dan Allah zata rakasa gidan wani abokinsu, yayi masa alqawarin yau zasuje masa..

Momy tayi murmushi danta gane manufarsa tsaf, ta lura shifa matarsa yake buqata, dama tana lura da take takensa..

Dan haka cikin lallami tace dashi, "Kayi hak'uri ABDUL, kaga munyi magana da Dadynka d'azu yace kawai RAHMA tazauna anan tunda ankusa gama saban gidan naku, kaga daga nan tana tashi sai kawai akaita can d'in, munga rashin tsari akan ta qara komawa tsowan gidanku Sannan kuma lokaci qanqani ku kuma tashi..

ABDUL ya waro ido, yace "Tab, momy kinsan ko zasu kai wata d'aya nan gaba kafin sugama komai.

Momy tace, "eh, munyi magana da Dadyn naka ai, har nake cemai wata d'aya ai kamar yau ne, dan Allah karka bani kunya yaran kirki, ka qara haƙuri wata d'aya kamar yau ne..

ABDUL yaja numfashi yace, "Allah yaji qan ZAINAB, da yanzu tana nan na tabbatar da bazan damu sosai ba.

Momy tace, "Ameen, ai dama haka ne.😄

Har ABDUL ya tashi da niyar barin falan sai Momy taji tausayinsa ya kamata, dan haka cikin sauri tace.. "ha'a, ina yanzu zakuje gidan abokin naka.

Cikin jin daɗi ya juyo da sauri yace mata, "Eh,

Tace, "To, zauna bara na kira maka ita..

Yace "Toh..

Dama RAHMA a kintsanta take, dan sun shirya komai ta waya tsakaninta da ABDUL d'in, itama tana buqatar mijin nata matuƙa, shiyasa koda wasa bata mai musu ba..

Momy ta shigo tace mata taje ta raka mijin nata unguwa, amma baza taje da Abba ba, taje zataji dashi, karta kwaso mai sanyi.

Hakan yayima RAHMA daɗi sosai, dama Abba baya kuka da ranah sai cikin dare yake damun muta ne.

Haka dai tasakarma little Raheemat kiss a goshi ta ficce daga d'akin..

Momy tabisu da kallo ta window, yaran suna bata sha'awa matuƙa, dacewarsu a ma'Aurata abin abin sha'awa ne..

Direct tsowan gidansu suka nufa, tunkan komai ya fara wakana UMMAKATI takira RAHMA awaya tace, "amma kam kedai anyi futunanniyar mata, yanzu haƙurin kika kasa yi sanda kika biye masa kuka zo jin daɗin juna ko..

RAHMA tayi dariya tace, "Ke dai kam bazaki dena gwalma ba, Allah zan gayama AMEER yace miki kidena zaman window kinama mutane sa ido.

UMMAKATI tace, "Ayya y'ar uwata, kema kinsan daga yau bazan qara yi muku ba, abinda barina zakuyi kuyi gaba, UMMAKATI tafad'i hakan cikin sanyi, dan har kuka sanda tayi da AMEER yake gaya mata su RAHMAN zasu tashi daga gidan..

Itama cikin sanyi RAHMA tace, "Dan Allah karki min kuka ki hanani bama mijina kulawata da qarfina, nasan yanda muka faro zama tare haka qarshen zai kasance, ABDUL ya gayamin shima AMEER d'in zai fara ginin nasa nan kusa..

UMMAKATI tace amma ai badani kad'ai zai zauna a gidan kamar yanda ABDUL ya bayya dake kad'ai yake San qarashe rayuwarsa ba..

RAHMA ta waro ido tace "ban gane me kike nufi ba, yauwa dama na lura a y'an kwana kin nan akwai abin dayake damunki, pls gaya min y'ar uwata, kinsan bamu saba b'oyema juna komai ba..

Hawaye ya zuba UMMAKATI, tace "bama ABDUL kulawa ayanzu, idan kika tashi tafiya ki biyo zan gaya miki komai, idan kuma dare yayi kuna sauri kar momy ta ganeku ki bari gobe ai zanzo zan gaya miki komai..

"Toh, RAHMA tace mata da kashe wayar..

ABDUL ya rungumeta yana tambaya me suke cewa..

RAHMA tace "sha kallo, kamar UMMAKATI tana da damuwa.

Ya had'e bakina da nata na d'an wani lokaci kana ya sake yana cewa, "ai dole ta tsinki kanta cikin damuwa, Hajara wasa ce.

RAHMA tace "wacece Hajara.

Yace, budurwar AMEER ce, AMEER yana yinta kafin ya kamu da qaunar UMMAKATI, yanzu sundawo da soyayarsu, ba mamaki UMMAKATIN ta gane hakan ne shiyasata shiga damuwa, Wallahi my dear ba shawarar daban bama AMEER kan ya rabu da ita ba amma yaqi, bana San mu'amularsa da yarinyar kwata kwata, dan bana santa, na bashi shawarar yabarta ya samu wata amma yaqi, ke dai kice mata tata addu'a kawai, amma fa Hajara sheɗaniya ce...

Shuru RAHMA tayi, jikinta kuma yayi sanyi, nan tafad'a tunani, tare dajin tsanar Hajarar.. Amma tana farajin sakwannin da ABDUL d'in yake aika mata dashi nan qarfin jikinta ya dawo, tayi saurin kawai da tunanin nata...

 

Gaskiya mijinta yayi missing d'inta sosai, dan ba qaramin wahala ya bata ba..

Sanda sukayi sallar isha'i sannan suka nufi gidan momy.

Aiko kallo d'aya tayi muku tasan suna d'auke da mafifin farin ciki, musamman ABDUL, kana ganinsa zaka tabbatar yana cikin farin ciki..

Washe gari ko UMMAKATI tazo suka zauna a d'akin momy ita da RAHMA..

Ta kalli RAHMA tace, "Gaskiyar magana itace, tunda na dawo daga wankan gida nafara fuskantar wasu canjin halaye daga AMEER, baya dawowa gida akan lokaci, bai cika cin abinci yanda ya dace ba, Sannan hira tsakanina dashi tayi ƙaranci, ya dena bani kulawar daya saba bani, sannan lokaci lokaci yana zama cikin tunani, akwai abinda yake damunsa amma ya kasa gayamin,

Kullum cikin bibiyar duk wani mutsinsa nake idan har yadawo gida, RAHMA so nake na gane me yake faruwa, amma nakasa gane komai, bantashi gane abin dayake damunsa ba sai acikin satin nan, dama ina lura dashi da yanda yake kaffa kaffa da wayarsa, ko d'auka nayi bada niyar yi mishi wani abu cikin wayar ba nan zakiga yahauni da maseefa, wai baya San ayanzu na dinga d'aukar masa waya, RAHMA nasaka a cikin zuciyata Wallahi saina duba naga meyake sawa yake tashi da fad'a idan na d'auki wayar tasa, Kullum cikin fakwansa nake kan in d'auki wayar, amma bana samun nasara, dan ayanzu haka ba abinda yake da kusanci da AMEER kamar wayarsa..

Shekaran jiya waccan nasamu nasarar d'aukar wayar tasa yana bacci, nan na dinga binkice a wayar, nagano yana soyayya da wata wai ita Hajara, RAHMA ayanda na fahimci soyayyarsu ba qaramin so sukema junansu ba, kamar ma yafi qaunarta akan qaunar da yake min, ashe itace damuwarsa, inta k'aice miki yanzu haka wai acikin satin nan zaikai sadakinta, RAHMA idan hakan ta kasance hauka zanyi, ina matuƙar San mijina bani San ganinsa da kishiyata, dan Allah RAHMA kiban shawara kinga ke kad'aice dani anan.. UMMAKATI takai qarshen zancen nata da fashewa da kuka wiwi...

RAHMA da saurin kuka nan hawaye ya zubo mata, ta kama hannun UMMAKATIN tace, "Bar kuka y'ar uwata, nasan tunda na iya zama da kishiya kema zaki iya, karki tab'a sawa aranki baza amiki kishiya ba, kishiya abokiyar zama ce, ga wanda ya fahimceta, maganar gaskiya bazan karyar miki da zuciya wajen gaya miki qarya da yaudara ba, bazan gaya miki AMEER bazai miki kishiya ba, bazan yaudareki wajen lallashinki kan babu wata saike a wajen AMEER ba,

Tabbas UMMAKATI AMEER zai ƙara Aure dan naji d'azu su momy na maganar, acewarsu gobe zasu kai sadaki.

A furgice UMMAKATI ta qara tsaida kallanta ga RAHMA, tace, "na shiga uku, wallahi ba qaramin so nake ma AMEER ba, ina sanshi bana San ganinsa da kowace mace saini.

RAHMA taqara damqe hannunta tace, "Karki bani kunya UMMAKATI, karki karyar min da zuciya akan farin sanin danayi miki wajen jajircewa akan komai, meyasa nake ganin tsoran kishiya a kwayar idanki, meyasa kike jin tsoranta, meyasa meyasa UMMAKATI, kina San nunamin ke raguwace, kai amma banyi tsamanin hakan ba, duk matar da take jin tsoran kishiya bata yarda da kanta ba, duk matar da takejin tsoran kishiya ita d'in banza ce, duk matar da take jin tsoran kishiya kishiyar tafi bata wahala a rayuwa, tafi mallake mijin nasu nan take, tafi yarda da cewa dama basan uwar gidan tasa yake ba ya Aureta, bata iya komai bane yasa ya aureta..

Duk macen da take jin tsoran kishiya Wallahi UMMAKATI kigaya mata ita ba mace bace kawai rako mata tayi.

Shawarar dazan baki kawai ki riqe Allah ba wani batun zuwa wajen boka ko malam akan kishiyarki, karki kuskura ki cuceta koda wasa dan hakan zai hana miki mallakar mijinki, duk abinda zakiyi kiyi dan Allah, sannan shawara ta qarshe dazan baki itace, tunda ke me shegen kishi ce, kadda kiyarda a had'a muku gida, kice masa ya raba muku gida, wannan shine mataki na farko da zakibi dan samun cikakkiyar nutsuwa.

UMMAKATI taja numfashi tace, "naji duk abinda kikace, kuma insha Allah bazan nuna ma AMEER damuwata Sosai ba, saidai zan d'an janye masa, tunda na fahimci baya San nasan komai, sannan agaskiya koda zansa a raba mana gida saina zauna da ita na samu sani akan iya zama da ita, kana nace masa ya raba mana gida..

RAHMA ta rungumeta tace "Yauwa y'ar uwata, gaskiya naji daɗin yanda kikaji maganata, Sannan duk da haka kirage damuwa kinga sai ramewa kike, wani gani zaiyi sam baki jin daɗin rayuwan Auran naki, dan Allah kisaki ranki kar kishiyar taki tazo ta ganki ahaka, taji daɗin hakan tasamu ƙarfin gwiwar yi miki abin dataga dama..

Goge hawayenta UMMAKATI tayi tace, "zan rage damuwa musamman danaji kinfad'a hakan, amma na saba da futunar AMEER inaga dai bazan tab'a yin qiba yanda nake so ba arayu.

RAHMA tace, "zakiyi, musamman idan kika cire damuwar komai..

Aiko da gaske ne washe gari su Dady suka kai sadakin Hajara budurwar AMEER.

Sannan ba tare da b'ata lokaci ba sukace asa musu ranah a lokacin, toh mahaifan Hajara dama neman kai suke da ita dan haka nan suka saka musu ranah nan da wata uku.

Sudai su Dady godiya sukayi suka bar gidansu Hajaran, sam yarinyar bata kwanta musu arai ba, dan sunyi binkice an gaya musu yarinyar bata jin magana, da suka kira AMEER suka gaya mai ce musu yayi ai dane bata jin maganar amma yanzu ta kintsu, shi dai dan Allah karsu hanasa Auranta, jin hakan da sukaji sai suka sakama abin albarka...

Cikin wayo da dabara AMEER yazo yana ma UMMAKATI maganar wajen ce mata zai canja mata kayan d'aki dan yaga duk sun d'an jeme, UMMAKATI takalli kayan d'akin nata tayi murmushi dayin bedroom d'inta batare data kulasa ba.

Tana zuwa bedroom d'in takira RAHMA ta gaya mata abin daya ce, RAHMA tace tayarda karta nuna mai tasan komai.

Aiko haka UMMAKATI tayi, ta dawo falo tace mai ya kamata ya canja mata komai harda kayan kitchen da kayan bedroom nata.

AMEER yayi shuru yana hararo kud'in da zai kashe mata..

Can dai dayake yana qaunarta yace yanda kikeso haka za'ayi.

Ginin ABDUL ya kammala, komai yayi yanda ake so, gidan ya had'u iyakar had'uwa, tsayawa magana akan gidan b'ata lokaci ne, me karatu kaidai gano gidan a idanka kawai.

Gidan zaman mace d'aya ne, dama fa ABDUL banda ra'ayin tara mata..

Yau dai RAHMA takoma saban gidanta.

Yawancin komai na Cikin gidan sababbi ne.

RAHMA kusan shid'ewa tayi ganin ita kad'ai zata zauna a gidan, koda zai mata kishiya saidai yaje can ya Samar mata wani gidan ya sata...

Gaskiyà taji dad'in ganin gidan nata bad'an kad'an ba.

Gaskiya dole ta qara San mijinta, dan yayi mata komai a rayuwa.

Bayan kowa ya watse ambarta daga sai d'anta dan little Raheemat tana wajen momy wai sai tayi wayo sosai za'a kawo mata ita.

Bayan ta gama girki wadata gidan tayi da turare, sannan ta shiga wanka tayima d'anta ma, tagyara kanta sosai, dan shigar qananun kaya tayi, kallo d'aya zakama shigar ka kauda ido, dan ABDUL ne kawai yake da hakk'in tsaida idansa akai,

Haka d'anta ma tasaka mai kaya me tsari, tafashe jikin nasu da turare suka kwanta,

ABDUL bai dawo gidan da wurri ba, sai can wajen qarfe tara na daran.

Gaskiya yana San RAHMA sosai, tasan sirrin riqe miji sosai, tsaftarta da qamshinta Suna qara masa qaunarta, bare kuma sauran...

Haka ya dinga bin gidan da kallo kowane lungu da sak'o na falukan gidan biyu komai ya zauna a mazauninsa, ko ina tashin qamshi yake, baibi takanta ba sanda yayi shashinsa yayi wanka ya shirya kansa Sannan yayo sashin nata.

Dama tana ankare da shigowarsa dan taji dawowarsa, dan haka yana shiga bedroom d'in nata ta wani mai make hug, abin ya bada kala danya shiga ABDUL sosai, farin ciki ya kamasa, nan suka fara b'ata tunanin juna, sanda suka gama ma junan nasu welcome sannan suka saki junan, RAHMA ta kama sannunsa suka zauna a gefan gado cikin sanyi da shagwaɓa tace dashi, "sha kallo, gaskiya na gode da sakani da kayi cikin wannan gidan, Allah ya qara bud'i kafi haka kafi hakan akowane yanayi, gaskiya bansan dame zan saka maka ba wajen nuna ƙaunar da kakeyi agareni..

Ya sakar mata kiss da cewa, "Kawai kici gaba da sona, ki zama me yima so hudima akan soyayyata, Sannan kiyi qoqarin jan qaunata a ranki tafi kusanci da komai a rayuwarki, watoh matata ina miki wani so wanda duk abin da zan miki bazanji komai ba, fatana ki d'aure kita bani yara masu kamata masu kamarki..

RAHMA tashige jikinsa tace "insha Allah my dear, zanyi komai da kace dani.

Yace "Madallah my Baby, yaro na yayi bacci ne.

Tace "eh, amma cikin dare zai tashi kaji irin kukan da yake mana.

ABDUL ya waro ido yace, "pls barmin wannan fatan, insha Allah bazai tashi ba sai asuba tayi. Tace "hmm, zamu gani, yanzu dai tashi muje muci abinci, dan nima banci ba kai nake jira

"Owkie, tashi muje ni kaina zan ciyar dake.

Haka suka jero abin gwanin ban sha'awa, aiko tana cinyarsa yana bata abincin tana bashi,

Wajen baccinsu rikicewar ABDUL d'in sanda tayi yawa, ita dai RAHMA godiya ga Allah Kawai takeyi..

********

Komai sanda AMEER ya canjama UMMAKATI, dayazo yana kame kamen gaya mata Auran nasa katse shi tayi da cewa, "Aure zakayi AMEER, kishiya kake San kamin, kawai so nake naji mena rageka dashi. AMEER ya rintse ido ya bud'e yace, "Wallahi ba abin da kika rageni dashi, kawai haka kawai nake ji araina idan ban Auri Hajara ba mutuwa zanyi, dan Allah matata kimin kyakkyawar fahimta, bana San na fuskanci tashin hankali daga gareki.

UMMAKATI tace, "Yanzu Yaushe ne bikin

Yace "Yau saura kwana. Shidda, ga kud'i dubu d'ari na baki na fad'ar kishiya, dan Allah dan annabi ki kwantar da hankalinki bazan tab'a canja miki daga yanda kika sanni ba..

Murmushi UMMAKATI karb'ar kud'in tayi, kana tace, "Allah ya bamu zaman lafiya, amma ina da sharad'i guda d'aya, wata shidda zanyi da amaryar taka ka raba mana gida, ina da kishi matuqa, kuma dama an baka damar rabama matanka gida idan har kana da hali, musamman idan sukaqi zaman lafiya..

AMEER yace baki da matsala da wannan.

Aiko kwana shidda nayi aka d'aurama AMEER aure da Hajarar.

Hajara makirar yarinya ce, akan cikar burinta zata iya yin komai, budurwar AMEER ce ada, suna lalatarsu awancan lokacin, AMEER yana jin dad'in harka da ita, yarinyar tayimai tako ta ina,

Wata ranah ya fitto zaije office kwasam suka had'u da juna, bayan sun gaisa yayi wuccewarsa itama haka,

Tun daga lokacin Hajara tace bata da mijin Aure sai AMEER, haka tadinga yawan bin malamai wai danta zama matarsa, aiko tasamu sa'a dan mutanan nata suna fara aiki akan AMEER d'in yaji aduniya ba wacce yake so da qauna kamarta, dama lokacin UMMAKATI tana jos taje wankan gida, shikenan AMEER ya fara zagawa wajen Hajara, ahaka ahaka tadinga jansa jikinta sosai, tana yimai girki, har gidansa take biyosa tunda UMMAKATI bata nan, illa sosai Hajara tama zuciyar AMEER lokacin da UMMAKATI taje wankan gida.

Haka masoya tayi qarfi tsakaninsu harya furta mata zai aureta, gashi yanzu tazama mata a garesa🤔....

Su RAHMA ana tare da UMMAKATI ana bata baki, Sosai RAHMA tayi nasarar danne kishin UMMAKATI awannan ranah.

Dare yayi aka kawo amarya shashinta, can dangin Hajarar suka kawoma UMMAKATIN ita wai amana,

UMMAKATI ta kallesu tace, "Yanzu tsakaninku da Allah bakuji kunyar kawomin wannan katotuwar budurwa kuce wai kun bani amanarta ba.🤔 d'aya daga cikin dangin Hajara tace, "keko baiwar Allah miye dan mun baki amanarta, mukaga ai haka akeyi...

UMMAKATI tace, "aa Wallahi yanzu kai ya waye, ba'a karb'ar amanar kishiya, nasan wane hali y'arku take dashi, haka kawai ku danqa min amanarta, komai taje ta aikata yazama alhak'i akaina, aa aa wallahi bazai yuhu ba, kudai je kukai y'arku shashinta, Allah ya bamu zaman lafiya amanace dai bazan karb'a ba, dan amana wata kayace ake had'a mutum da ita, bare ta kishiya..

Nan take jikinsu yayi sanyi, RAHMA ta harari UMMAKATI tace dasu, "Toh Allah ya basu zaman lafiya, dan zaman lafiyan ake nema.

Jin abinda RAHMA tace suka ce ameen da tashi suka koma shashin Hajaran

RAHMA ta kalli UMMAKATI tace, "Amma ke banza ce wallahi kin kwafsa, yanzu basai su fara tunanin ko ke muguwa bace akwai abinda kike aikatawa shiyasaki qin karb'ar amanar tata.

UMMAKATI tace, "wallahi saidai suce hakan, amma bazan tab'a karb'ar amanar kishiya ba, ki kalleta katotuwa da ita ace ambaki amanarta, suje dai can da amanarsu..

RAHMA tayi shuru, yanzu ta fahimci UMMAKATIN gaskiya amana kowace iri ce kayace, bare kuma ta kishiya.

Haka ABDUL da AMEER sukazo, ABDUL dai bai shiga gidan ba, danya gayama AMEER shidai bazai shiga kaima amarya kaza da hannunsa ba, dan shi da gaske yaje baya San Hajara, yafi San UMMAKATI, dama dai wata ya Aura to dazai iya kai mata..

Murmushi AMEER yayi kawai, dan dama yasan Hajara da ABDUL basa jituwa.

ABDUL ya kira RAHMA a waya yace tafito su tafi, tace bazai shigo ba, yace mata eh.

Haka taqara lallashin UMMAKATI ta d'auki Yaranta taficce tana ma AMEER saida safe..

Shima bin bayanta yayi danya kulle gidan, amma yana dawowa, UMMAKATI taqi bud'emai kofa, yayi kwankwasawar duniya taqi bud'e mai.

Tana jinsa yayi shashin amaryar, kuka ya kufce mata, yau ita me cika bakin AMEER bazai mata kishiya ba amma gashi yayi mata yau, kuma zai kwana a d'akinta, yayi mata abin dayake yi mata.

Nan UMMAKATI na kuka mamy y'arta na tayata, daga qarshe da taga kukan bashine mafita ba, sai kawai tashiga toilet taqa yin wanka, tama y'arta sukabi lafiyar gado ZUCHIYA cike da tunani...

Nanko ABDUL Kallan RAHMA yayi yana tuqin motar tasa yace, "Naga jikinki yayi sanyi, wani abu ne.

Itama ta kallesa, tace, "Wallahi my dear UMMAKATI ta tsayamin arai, tana da kishi sosai ina tunanin anya zata iya yin abin daya dace kuwa.

ABDUL ya tab'e baki yace, "idan taji babu daɗi zata iya, tunda ke kika iya aikowa ma zai iya, dama ina San neman wata alfarma agareki, yau naga wata Baby wajen d'auko Hajaran da mukayi, dan Allah my dear kibarni na qara Aure dan Babyn tayi min over, amma fa bata kaiki kyau da tsari ba, saidai kinsan ance zuciya da abin datake so..

RAHMA tagallamai hararar gaske, tace "zanfa iya k'onaku kai da ita.

Yace, "Toh idan kika k'ona mu kiyi rayuwa dawa, tace "Aina haife me kama dakai, Sannan still Aunty Zainab tabani me kama dakai, sai kawai na rayu da yarana.

ABDUL yayi murmushi yace, "Magana ta gaskiya ayanzu dai bani da ra'ayin zama da mata biyu, amma idan kika saki layi daga sabon danayima komai naki, ba makawa zaki ganki da kishiya kwatsam.

"Tace nifa bana tsoran kishiya, matar dama take tsoran kishiya haushinta nake ji, nabaka umarni jeka yomin kishiya, ina dai zuciyar taka guda d'aya ce, haka ma ruhinka guda ne, dan haka mu zuba nida amaryar taka idan kayi muga wacece zata mallaki abubuwan nan biyu, wato ZUCHIYAR da RUHIN naka.

ABDUL ya qara yin murmushi yace, "Habawa yarinya, wato dan kinga kin mallake zuciyar tawa da ruhin nawa shine ya baki damar cika baki ko, tace "eh, yace "zan gyara tunaninki, dan saidai kawai kiji ance and'aura min aure da wata, tace, "ni kuma nayi maka alƙawarin bazan yimi buri ba, amma kai da kanka zaka San da bambanci, har kafara kawo k'orafin amaryar taka, daga qarshe ka qara sanin darajata..

Dai dai nan yayi parking d'in motarsa a gidan nasu, saiko ga wayarsa tad'auki qara, suka kalli wayar shida RAHMAN babu suna, yana d'aga wayar yaji muryar wata budurwa tana cewa, "sunana Balkisu, naganka a wajen d'aukar amarya Hajara, dan Allah ina so kazama abokina, ABDUL ya kalli RAHMA yana cewa, "Banji me kikace ba.. Ya faɗi hakan da karama RAHMA wayar tashi a kunnanta, nanko budurwar me suna Balkisu ta qara maimaita kalaman nata.

Gaban RAHMA ya tsinke ya fad'i, nan take tashin hankali ya bayyana akan fuskarta qarara, cikin sanyi tace da ita, "Toh kiyi hak'uri mijina baya abota da mata, dafatan kin fahimta.

Balkisu najin muryar RAHMA jikinta yayi sanyi haka kunya ta kamata, ABDUL yamaida wayar tasa kunnansa yace, "kiyi hak'uri Balkisu bana abota da mata, dan qawata d'aya ce matata,..

Balkisu najin hakan takashe wayar.. Daidai nan RAHMA tafita daga motar..

ABDUL yayi murmushi dan ganin yana kiranta taqi kulasa,

Acan bedroom yacim mata tana kwantar da Abba, fuskar nan tayi kicin kicin da ita, Yace, "Aha, mara jin tsoran kishiyace take fushi da mijinta haka Dan kawai buduwa takirasa tace tana San abota dashi, RAHMA ta kallesa da saurin d'auke fushin dake kan fuskar tata, zatayi magana yayi saurin katseta wajen cigaba da cewa, karki gayamin qarya, Ninasan har ƙarshen rayuwarki bazaki tab'a iya b'oye kishinki akaina ba, koda zakiyi hakan nad'an wani lokaci ne. Yakai qarshen zancen nasa da jawota jikinsa yaci gaba da cewa, A ra'ayin kaina dai bazanyi miki kishiya ba my Baby, dan bakyayin kyau da ita, dan haka sakar min fuskar naji dad'i, fushinki yana damun zuciyata.. Qara rungumesa RAHMA tayi, "tace nabar cika baki my dear, ayanzu nagane koda bana jin tsoran kishiya kishinka wani hattane acikin jikina..

Yayi murmushi da cewa aransa SOYAYYA tana da dad'i...

AMEER ko yasan wannan kam dama hanya abud'e take, yadai ji dad'in amaryar tasa amma UMMAKATI kankat ce agunsa, hakan yasa asuba nayi ya qarayin shashin UMMAKATIN, bugun ƙofar tasa ce tasata tashi, tana jan tsaki haka tatashi taje ta bud'e kofar, yana ganinta ya rungumeta, yana gaya mata kalamai masu dad'i wai yayi missing d'inta, ita dai shuru tamai ahaka dai yabarta yaje masallaci, itako tashiga tunanin gaskiya mijin nata na santa, danta hango qaunar tata akwayar idansa yanzu..

Tashiga toilet tayo alwala tayi sallah

Sosai fa UMMAKATI tadanne zuciyarta tadinga musu abin kari harna tsawan kwana bakwai, ahakan tagane AMEER d'in baya wani ji da amaryar tasa, dan irin wannan d'ukin ko kad'an bai nuna mata ba, Hajara ko tsaf ta fahimci AMEER yana qaunar UMMAKATI sosai, tayi alk'awarin saita datse wannan qauna dayake mata.

 

Hankalin UMMAKATI ya d'an kwanta ganin Hajara ba wata kishiyar ayi kishi da ita bace.

Dan UMMAKATIN tafi Hajaran kyau da tsari na halitta..

Bata San abun ba daga nan yake ba.

A lura irinta Hajara tagane UMMAKATI bata da tsafta sosai, irin dai kadaran d'innan kadaham,

Sannan bata cika bama AMEER d'in kulawa Sosai, irin ta maida kanta baiwa agaresa, sam bata mai hakan.

dake girkin nasu ahad'e yake hakan yasa Hajara ganewa UMMAKATIN bata wani iya girki ba.

Hajara data gane ta lura da wannan abubuwan saita maida kanta me tsafta fiye da UMMAKATIN, dama tad'an iya girkinta dan tafi UMMAKATIN saita qara lura Sosai wajen San taga tafi yanda take a iyawan.

Daga qarshe saita maida AMEER kamar wani sarki, kan yace iyi kaza Hajara tayi, ko kad'an bazaka tab'a had'a biyayyar da Hajara takema AMEER da wacce UMMAKATI take masa ba,

Ayanzu Hajara ta shagwaɓa AMEER sosai da salanta..

Duk ran girkinta sai AMEER ya zage yaci abinci San ransa, ranar girkin UMMAKATI kuma sai kaga yaci kad'an,

Ya yarda yanzu yasan dad'i, ashe abaya kawai yana iya cin abincin UMMAKATIN ne.

Haka duk ran girkin Hajara saiya dawo gida da huri, kuma baya fitta office da wuri,

Alamadai tanunama UMMAKATI AMEER yana yin Hajara sosai

Kuma idan tafiya tai tafiya ahakan zata zama banza agidan. Tunda ta mishi magana itama ya dinga dawo mata gida akan lokaci bai dena ba, sannan tayi mai magana kan itama ya dinga cin abincinta da yawa kamar yanda yake cin na Hajara amma baijita ba, dan yanda ya saba ci kad'an haka yaciga dacin kad'an d'in,

Ayanzu jin daɗin AMEER d'aya ne wanda yake samu agun UMMAKATI shine tafi Hajara kwarewa aharka ta kwanciya, sannan tafita sweet, sam babu had'i, wannan yasa yake daurewa yake bama kowacce hakk'inta cikinsu, ya sani dai dole hankalinsa yafi karkata gun Hajara ayanzu tunda ya gane tafi UMMAKATI iya girki kuma tafita tsafta, tafita ji dashi.

Amma har a zuciyarsa shidai yafi qaunar UMMAKATI akan Hajara, dan yana ganin Hajara amatsayin watsattsiyar mace tunda a harkar bariki suka had'u, haka kawai yaji UMMAKATI tafi kwanta masa arai fiye da Hajaran, amma duk da haka shidai bazai iya da zuciyarsa ba, yasan dole tafi karkata gun wacce tafi kyautata masa acikinsu, yanzu ya gane abubuwa da dama, ya gane wani abun baka ganesa sai kana da mata biyu, banda haka shi har a zuciyarsa bai tab'a ganin qazantar UMMAKATI ba sai yanzu dayaga tsaftar Hajara, Sannan bai tab'a lura UMMAKATI bata iya girki ba sanda yaji girkin Hajara, ya yarda mata biyu suna da amfani agun d'a namiji Sosai🙈....

Duk da wannan Hankalin Hajara yaqi kwanciya, itafa burinta tazama sarauniya agidan, tazama itace me fad'a aji agidan, sam bata jin daɗin ganin qaunar da AMEER yakema UMMAKATI, tafi so taga ya tsaneta ya d'aukaka darajarta fiye data UMMAKATIN, tana so taga yana kyarar UMMAKATIN kamar karya sannan ya dena qaunar y'arta,

Sam bata jin daɗin yanda yake bama kowa hakk'inta acikinsu, burinta kawai yadinga ji da ita tazama tauraruwarsa.

Hakan yasa watan ta biyu agidan tasamu nasarar fitta unguwa, taje wajen malaminta ya bata maganin mata masu zafi, Sannan tace dashi aikin zai mata Wanda zaisa AMEER yadena ganin kyawun fuskar UMMAKATI, sa'ilin nan kuma yaji baya San ganinta kusa dashi, wato ya dinga kyararta da hantararta kamar karya, Sannan ta lura AMEER d'in yana matuqar San mamy tana so acire soyayyar da yake ma mamyn tajuye takoma qiyayya..

Malamin nata ya tabbatar mata duk abin datake so zai mata, matsalar dai ta kud'i ce.

Dama Hajara tasan zai buqaci kud'in, dan haka dasu tatafi, nan ya mata had'e had'e wanda zataba AMEER d'in yaci a abinci, da wanda zata ba mamy itama taci a abincin, saina UMMAKATI ita basai an bata naci ba, yace kawai zai mata aiki.

Burin Hajara ya cika, dan ayanzu AMEER ko kad'an baya San ganin fuskar UMMAKATI, haka yanzu ya dena ƙaunar mamy, tana ganinsa zataje wajensa saikaga yahau zare mata ido da fad'ace fad'ace, abin ya fara damun UMMAKATI, da tayi tunanin ashe haka kishiyar take, irin bata wani ga tashin hankalin da take tunanin gani ba, ashe tashin hankalin yana gaba

Gashi ko yanzu tafara fuskantarsa

AMEER yadena shiga d'akinta, tsakaninsa da ita ajiye mata kud'i kozatayi wasu buqatun, ya tattare hankalinsa gabaki d'aya ya maida kan Hajara, UMMAKATI bata jin dariyarsa sai'a shashin Hajara.

Gashi kusan Kullum saiya dawo da ranah yin harka wajen Hajaran,

Kwata kwata fa ya fitta daga harkar UMMAKATI da y'arta🤔

Bata fuskantar kyara da walaqancinsa sai idan suna breakfast da Dinah, Anan zaita hararar UMMAKATIN sam baya San ya fiya ganinta, gashi suta wasa da dariya shida Hajara, mamy na fara yin kuka irin na yara zai dakama UMMAKATI tsawa yace tatashi tabar wajen baya San hayaniya.

Ganin haka sai UMMAKATI tadena zuwa aci abincin tare da ita, sannan tadena ma girkin dasu, saita dafa ita da y'arta suci su koshi,

Haka zaka ganta Kullum cikin kuka ba dare ba ranah.

Matsalar tasu d'aya ce UMMAKATI da AMEER Suna wasa da ibada, idan suka shiga matsala basa maida hankali wajen yin addu'a, wannan yasa asirin Hajara saurin yin RAM dasu..

Dena yin girkin da UMMAKATI tayi ba qaramin dad'i yama Hajara da AMEER ba,  shi AMEER dama basan ganinta yake ba, itako Hajara qara zage damtse tayi wajen nuna masa itace madubin dubawarsa..

UMMAKATI bata faɗin matsalarta ga kowa sai tafiya tai tafiya taga bayanda zatayi, sab'anin RAHMA da abu na samunta tana d'an haƙuri dashi na wani d'an lokaci zata fitto tafad'a dan tasamu nutsuwa.

Yanzu haka sanda AMEER ya manta dawata shirgi wai ita UMMAKATI agidan sannan UMMAKATIN tatari RAHMA dazancen tana kuka kamar ranta zai fitta.

RAHMA tabata shawarar tatafi jos na d'an wani lokaci, tabarsa da Hajaran duk daran dad'ewa dole ai yadawo ya nemeta,

sannan ta gane zancen UMMAKATIN tsaf ta gano duk da sakacinta, dan inda ta iya girki kuma tafi Hajara tsafta dole wasu al'amuran su ragun mata, dan haka ayanzu idan taje jos ba zama zatayi ba, dole dinga koyan girki agun way'anda take da tabbacin sun iya..

Sannan dole tayi yaqi da zuciyarta wajen dena yin qiwa dole tazama me cikakkiyar tsanta. Sannan zata gayama mamanta tasa ayi mata rubutun suratul Yusuf da maryam awanke abata tasha...

UMMAKATI ta yarda da shawarar RAHMA kuma tashirya d'aura d'ammara da tsafta da iya girki..

Daga gidan RAHMA gidansu Hajjiya Kakah tayi da gidan momy, tayi musu sallama kan zata jos, tunaninsu zata ziyara ne hakan yasa suka dinga mata fatan kaiwa jos d'in lafiya..

Bayan tadawo had'a kayanta tayi tsaf takira AMEER d'in awaya kira biyar bai d'auka ba sai'ana shidda tukun ya d'auka.. Taja numfashi tace mai zata jos ne duba jikin mamanta, yace mata saita dawo, akwai kud'i awajen Hajara taje ta karb'a idan tana da buqata, tace mai bata buqata ta kashe wayarta, dama tayima direbansu magana kan zai kaita jos d'in, dan haka yana dawowa daga gayama iyayensa sukayo jos.

Sun sauka lafiya, UMMAKATI bata b'oye ma mamanta komai ba tagaya mata, nan maman tace mata tatashi suje wajen wani malami aikinsa kamar yankan wuqa ne, nan zai janyo mata hankalin AMEER d'in,

UMMAKATI tace mata ita har ta koma ga Allah bazata tab'a bin malamai ko bokaye ba, dan haka kawai maman nata tabar zancen zuwa wajen malamin.

Dake RAHMA takira mamanta ta gaya mata komai dayake faruwa da UMMAKATIN hakan yasa maman nata taja UMMAKATIN ajikinta tana koya mata girki da wasu abubuwan jawo hankalin me gida..

Sam UMMAKATI bata damu da sallah akan lokaci ba, bare azo wani batun nafula, maman RAHMA ta lura da ita sosai hakan yasa take mata wa'azi kanyin sallah akan lokaci, tace mata duk matar da take sallah akan lokaci Wallahi tafi qarfin kishiyarta, aiko UMMAKATI tacanja yanzu, lokacin sallah nayi take tashi tayi, sannan ba lefi ta iya girki sosai fiye da yanda Hajaran ta'iya, Batu na tsafta ko, yanzu UMMAKATI ji take ba wanda yafita tsafta..

Kimanin wata takwas kenan raban UMMAKATI da AMEER

Tunda UMMAKATI tabar Kaduna AMEER ya fara fuskantar matsala daga wajen Hajara, ashe duk abin datake mai naganin idan UMMAKATIN ne, yanzu da bata nan komai yayi sanyi, tsaftarta ta ragu, iya girkinta ya rago, haka wani ji dashi da takeyi duk ta rage..

Sannan ya lura tana fitta batare da saninsa ba, lokacin daya gane hakan tunaninsa basa yayi iskanci da maza take zuwa yi..

Nan zarginta yayi ram da zuciyarsa, tunda dama yasan halinta, nan kishi ya fara d'awainiya da zuciyarsa, sam AMEER bashi da nutsuwa yanzu, gashi tunda UMMAKATI tadawo yin sallah akan lokaci taketa jefansa da addu'a kan Allah ya karkato mata da hankalinsa, idanko haka ne ai dole ya tsinci Kansa cikin kewarta, shiyama rasa meyake damunsa, duk jinsa yake kamar bashi ba, ya rasa ya akayi ya auri Hajaran ya rasa meyasa UMMAKATI tatafi jos..

Lokacin da yake gayama ABDUL matsalarsa ABDUL d'in basa shawara yayi kan ya rige ibadarsa sosai,sannan ya rage yin bacci, ma'ana yadinga tashi sallar dare yana me gayama Allah buqatunsa...

Aiko AMEER ya d'auki shawarar ABDUL, tunda ya fara sallar dare Hajara tafara fitta d'aga ransa,

Haka kewar UMMAKATI tadami zuciyarsa.

Ganin bazai iya ba haka yacire kunya yayo jos.

Hak'uri sosai yadinga ba maman UMMAKATI kafin tayarda ya gana da UMMAKATIN.

Sanda ya zubarma da UMMAKATIN Hawaye Sannan tayarda ta saurareshi,

Yafi sati a garin jos yana bibiyarta da lallashi tayi hak'uri tabishi ta koma d'akinta, UMMAKATI nasan AMEER sosai hakan yasa tausayinsa kmaa zuciyarta ta yarda zata bishi.. Amma da sharad'in zai raba musu gida ita da Hajaran, yace dama ai ankusa gama ginin da yakeyi jikin gidan ABDUL wanda suke ciki yanzu..

Hakan yama UMMAKATI dad'i Sosai.

Dama tsakanin miji da mata sai Allah,.

Komai dai ya dawo kamar ba'ayi ba,.

Dan yanzu UMMAKATI tasharema AMEER tantamarsa akanta, ya gane yanzu tana da tsafta sosai, kuma ta iya girki bad'an kad'an ba,

Dama yasan bamai iyawa dashi sai ita.

Yanzu fa UMMAKATI ta dawo da ƙaunar da AMEER d'in yake mata,

Hankalin Hajara ya tashi, ta qara komawa wajen malaminta yayi mata had'e had'e, yanzu dai ya bata wani magani yace  taba UMMAKATIN taci a abinci ita y'arta, idan tayi hakan UMMAKATI da AMEER har abada, dan zai mata saki uku, sannan ko zai rayu da y'arta har abada bazai tab'a qaunar y'ar ba..

Saidai kash kan Hajara tadawo daga wajen malamin nata ankwashe kayan UMMAKATI tsaf akai saban gidan da AMEER d'in ya gida, wato gidan da yake kusa da jikin nasu RAHMA..

Hajara na dawowa UMMAKATI taje tayi mata sallama kan yaudai AMEER ya raba musu gida

Hajara ta waro ido tace, "Aunty UMMAKATI ban gane me kike San cemin ba,

Tace "Dama nace ma AMEER zai raba mana gida komin daran dad'ewa, shine yanzu da aka gama wani gininsa acan kusa da gidan ABDUL muka shirya nizan koma can, to dama yau zan koma tun d'azuma aka kwashe kayana, dama zaman jiran dawowarki nake nayi miki sallama...

Hajara najin haka tace "kutumar bura uba... Aiko bazai yuhu ba, Wallahi bazai tab'a sab'uwa a raba mana gida ba, yanda zan zauna anan kema haka zaki zauna anan.

UMMAKATI tamata Kallan banza ta nunata da yatsa, tace, "ke ki shiga taitayinki, dan kinga ina barinki bashi zaisa kidinga min abinda kikaga dama ba, idan kin i'sa cikin uwarki da ubanki ki hanni tarewa awancan gidan, ni kuma nayi miki alqawarin nabar miki AMEER kenan har qarshen rayuwa..

Hajara tace haka kikace, toh bara yazo kiga ikwan Allah..

Aikan UMMAKATI ta rufe baki saiga AMEER ya shigo, da wani qarfin gwiwa Hajara tace, "AMEER Wallahi saidai mu tare tare, bazai tab'a yuhuwa kabarni anan kakai UMMAKATI saban gida ba...

Hajara bata San yanzu haushinta AMEER yakeji ba, dan haka cikin tsawa yace mata bata isa b tayi kad'an.

Zata kawo masa wargi ya faffalleta da mari, me UMMAKATI zatayi imba dariya ba.

Tatofama Hajaran yawo taficcewarta Daga gidan..

Nan fad'a ya shiga tsakanin AMEER da Hajara, har AMEER d'in yamata saki d'aya...

Wannan rana batama Hajara dad'i ba haka dai ta'ibi kayanta tayi gidansu, AMEER ya kulle gidansa..

Dama acan saban gidan UMMAKATIN masu mata gyara RAHMA da Abida da ummi qanwar AMEER ne wato y'a ga mama Saude sune suke shirya mata gidan nata, basu suka gama komai ba sai kusan bakwai na dare..

Dama RAHMA tana aikin tana leqawa gidanta dan had'ama ABDUL abinda zaici, ahaka ahaka harta gama komai, dan haka yanzu tana dawowa wanka tayi tama d'anta nan ABDUL d'in ya dawo yagansu tsaf...

*************

Komai ya canja, rayuwar tasu a yanzu tayi dad'i, babu fad'a babu tashin hankali,

Hajara dai AMEER yasa mota tazo tsowan gidan nasa ta kwashe kayan ta ya aika mata dashi. Da cikwan sakinta, dan dama shi bai San ya akayi ya Aureta ba..

ABDUL ko shuru kake jinsa shida RAHMA, dan yanzu hakama d'auke take da wani cikinsa dan tana yaye Abba tasamu ciki,

Momy dai ita ta d'auki Abban tace idan cikin RAHMAN yayi kwari a kawo mata little Raheemat tunda ita tayi wayo..

Aiko cikin nata nayin kwari suka amsota.

Haka UMMAKATI itama dai tana dawowa saban gidan tasamu ciki, saidai wannan karan RAHMA ta rigata samun cikin..

Wata ranah mama Saude ta fitto zata wajen wani malami dan ya raba auran baban AMEER da amaryarsa mota tabi takanta ta karya mata wiya, sam bata wucce minti talatin ba tace ga garinku nan rai yayi halinsa,

ABDUL yaji mutuwarta sosai aransa, nan yayi mata sallah raka'a biyu dayin furucin yayafe mata komai da tayi masa a rayuwa.

AMEER yayi kuka hakama Hajjiya..

Wata uku da rasuwarta RAHMA ta aihu tasamu yarinyarta mace me kama da ita sak, nan aka saka mata suna ZAINAB, suna kiranta da Aunty Zainab..

Wata biyu da haihuwan RAHMA UMMAKATI ma ta haihu taqara samun mace, aka saka mata sunan Hajjiya Kakah...

Dan da sunan mama Saude za'a saka mata sai mijin Hajjiya kaka yace aa Adai saka Hajjiya Kaka😄 wai atunaninsa kar yarinyar tayo baqin halin mama Saude..

AMEER murmushi kawai yayi dan gane manufarsa, amma yasa ransa gaba idan UMMAKATIN ta qara haihuwa sunan mama Sauden zaisa, dan ance uwa uwace, koda yaya take...

Dadyn ABDUL ya qara aure kamar yanda yake da niya, dan San haihuwa ce yasashi auran, saidai tunda ya auro matar bata samu cikin ba ashe bata haihuwa, momy dai dama bata kulasa da wani batu na kishi ba, hakan yasa hankalinsa ya qara karkata akanta, wato dai momyn itace tauraruwarsa.

Wani ana kiransa da Aliyu shine ya fito auran Abida qanwar ABDUL, mutumin kirki anyi Auranta dashi an kaita gidanta lafiya sai muce Allah bada zaman lafiyar.

Zumunci tsakanin RAHMA da UMMAKATI abin ba'a cewa komai, dan sun riqi junansu da amana, sam basu d'ora rayuwarsu kan munafurci ko hassada ba.

UMMAKATI ta yarda jarabar AMEER qaruwa takeyi, hakan yasa tasakama zuciyarta salama tafara rokwan Allah ya fitto mata da abokiyar zama tagari wacce AMEER d'in zai gani ya aura amma ya raba musu gida..

Aiko yasamu wata wai ita Nazira, yarinya me hankali da nutsuwa, bai b'oyema UMMAKATI ba yace zaiyi aure ne danta dinga samun sauƙin wasu al'amuran.

Yanda ta nuna mai babu komai abin ya masa dad'i, haka AMEER ya qara aure ya Auri Nazira.

Ya raba musu gida, amma kallo d'aya zakama ruyuwar auran nasa kasan yanaji da UMMAKATI...

Daqer aka samu wani malami ya iya karya asirin dake d'awainiya da y'an uwan RAHMA..

Ayanzu duk sun samu mazajen aure amma babu kamar mijin RAHMA a mazajen nasu, wato ABDUL

UMMAKATI Yaranta biyar ayanzu, mata hud'u maza biyu.

RAHMA ko Yaranta takwas, maza shidda mata biyu.

Dan ita tana yayewa take qara samun ciki, UMMAKATI ko tana d'an samun hutu kafin taqara yin ciki,

Kishiyar UMMAKATI Yaranta biyu, tasamu matsala da mahaifa..

Momy ji da RAHMA take Sosai ganin yanda su basu samu aihuwar sosai ba amma gashi ita sai Haifa musu jikoki take.

Abida ma ba'a barta abaya ba, Yaranta uku, biyu maza d'aya mace.

Y'an AMEER na wajen mama Saude ma sai aurar dasu baban nasu yake.

Rayuwar dai tana tafiya yanda ake so...

***************

RAHMA ko ta mallake ABDUL, ko motsi baya yi akan wani batu wai shi qara Aure..

San matarsa yake kamar me, qaunarta yake kamar me, jinta yake kamar me, qaunarta tayi mai mugun illah

Tana zaune awajen shaqatawar gidan, yayin da little Raheemat take gefe da littattafan makarantarta tana tilawa, Abba da Aunty Zainab dasauran yaran basa nan suna wajen momy, little Raheemat d'ince agida, sam bata yarda tayi nisa da RAHMA, saboda ƙaunar da take nuna mata fiye da sauran yaran..

ABDUL ya nufi wajen yana me rufema RAHMAN ido tabaya..

Yace, "My Baby, my dear, madubin dubawata, nutsuwata, kwanciyar hankali na, tauraruwata, haske me haskaka zuciyata, rayuwata, farin ciki na, abin kwanciyar hankali na, ZUMA TA!.... Na tawo miki da tsaraba me girma yau..

RAHMA ta zare hannunsa daga fuskarta, tajuyo dashi gabanta ya zauna, tace, "Bani tsarabar bana San jan rai, yace saikin rufe idanki, ta rufe, ya sakar mata kiss daidai setin bakinta kana ya saka mata mukullin mota a hannunta, tana bud'e idanta tayi arba da mukullin, nan farin ciki ya kamata, ABDUL ya tashi da ware hannayensa alamar ta rungumesa, aiko cikin sauri tatashi ta rungumesan, runguwa wacce kallo d'aya zaka mata kasan akwai SO, kallo d'aya zaka musu kasan sun jik'u a so, kallo d'aya zaka musu kasan suna matuƙar ƙaunar juna, kallo d'aya zaka musu kasan idan suka rabu da juna za'a samu matsala me girma..

"Ina sanka mijina, ina ƙaunarka mijina, ina farin ciki da kasancewata dakai mijina, ina godema Allah daya bani kai amatsayin mijina, ina fatan kaiwa ƙarshen rayuwa dakai mijina, ina San mutuwa dakai mijina, ina san na qara zama matarka a gidan aljanna mijina, ina rokwan Allah daya barni dakai mijina..

ABDUL yace,"ina yinki matata, ina ji dake farin ciki na , ina alfahari dake uwar y'ay'a, dan Allah kici gaba da sona daji dani da qaunata kinji nutsuwata.

"Insha Allah baka da matsala da hakan mijina.. RAHMA tafad'a da ksi masa kiss..

Little Raheemat tatashi tsaye ta hard'e hannaye, cikin shigar riga da wando, yarinya y'ar shekara goma sha takwas..  Ta kallesu tace, "Dady, ina San nasan wata irin rayuwa kayi da AUNTY ZAINAB..

RAHMA da ABDUL suka saki juna da maida hankalinsu gareta, suka zuba mata ido, taci gaba da cewa, ina nufin waccar Auntyn taka ta hoton falanmu wacce kace katab'a auranta.. Shin kasota kamar yanda kake San momyna, takai ƙarshen zancen nata da Kallan RAHMA wacce take kira da momynta..

ABDUL ya kalli RAHMA danshi baisan da zaman Raheemat d'in awajen ba.

Kana ya dawo da kallansa gareta, ya qaraso gareta, tare da kama hannunta, yace "Na so Aunty Zainab, munyi soyayya tsakanina da ita me tsayawa arai..

"Amma dai baka sota kamar yanda kake San momyna ba ko. Tafad'i hakan da saurin katse shi.

Yayi murmushi da niyar bata amsa, sai RAHMA ta amshe zancen da cewa, "wai meyasaki yin wannan tambayar, tace "momy nayi tambayar ne dan ganin ƙaunar da Dady yake miki bata wasa bace, ban tab'a ganin ranar da kuka samu sab'ani dashi ba, nafi ganinku cikin qaunar juna, sai nake mamakin anya Dady yaso wata y'a mace kuwa arayuwarsa bayan ke, saina fara tunanin Aunty Zainab d'insa wacce kukace itama uwa ce agareni, kuma ya tab'a Auranta, sai nake tunanin to wata rayuwa Dadyn yayi da ita gaki kusa dashi, anya yasota yanda ya dace kuwa...

RAHMA ta ƙaraso gareta itama ta kama hannunta tace, Dadynki yaso Aunty Zainab fiye dasan da kika tashi kikaga yana yimin..

Little Raheemat tayi murmushi da sakarma ABDUL kiss a kumatu, da RAHMAN itama a kumatun, sanda ta d'auki jakarta tace dasu,"Gaskiya Dady ka iya soyayya, Sannan momyna kema gwanace wajen sace ZUCHIYA, tafad'i hakan da barin wajen shaqatawar..

ABDUL ya kalli RAHMA da sanyin jiki, tace, "karka damu mijina idan dai kaga me suna ZAINAB kuka kakamu da qaunarta ka Auro ita..

Little ZAINAB ce ta shigo wajen shaqatawar da gudu, tana cewa, "Tab, Momy kishiya kikeso Dady yayi miki😨..

RAHMA tace eh, amma me sunanki...

Little ZAINAB tace, "idan ko hakane, akwai wata qarawata da take San Dadyn nawa, kuma sunammu d'aya..😄

RAHMA ta harareta tace "toh ba qawarki nake buqata ba, qawar wata nake buqata..

ABDUL ya tashi da kama hunnun little Zainab din yace, "Muje my dear ki nuna min gidansu, da sauri RAHMA tace, "dan Allah karki rakasa nifa mamanki ce...

ABDUL yayi murmushi yace, "Muje kawai kinyi yarinyata

Har sunkusa zuwa get little Raheemat ta fitto ta dakama Zainab tsawa tace, "Idan kika kaisa babu mu babu ke, shi kenan sai qawar taki tazama momynki da y'an uwanki.

RAHMA tayi murmushi, little ZAINAB ta kalli ABDUL tace, "Dady kaji abinda aunty Raheemat tace, ABDUL yace "naji, karki damu zomu tafi.

Tace "kai ina Dady kaidai kaje..

ABDUL ya kalli little Raheemat ya harareta, yace, "zanyi maganinku ne,

RAHMA tayi dariya da barin wajen.

Little Raheemat tace "Allah Dady idan kama Momy kishiya sai kullum daran dangi zamu dingama kishiyar, harsai kace tatafi gidansu.. Tana faɗin hakan takoma ciki..

Little Zainab ta d'aga masa gira da cewa "da gaske take Dady,..

ABDUL kenan yaja yaransa jikinsa idan kukaga yanda hira da wasa dasu kamar wasu sa'o'insa, Saidai duk da haka suna jin tsoransa Sosai dan idan sukayi lefi baqaramin hukuntasu yake ba, musamman idan magana akan karatu ne..

Alhamdulillah

Me yafi tab'a zuciyarki cikin wannan labarin

Meyafi baki sha'awa

Meyafi burgeki

Me yafi jan hankalinki

Rahma nalele ta qayatar dake

Alhamdulillah

Alhamdulillah

 

 

 

anan nakawo ƙarshen labarina na TANTIRANCI KO KARUWANCI, Wanda zan canja mai suna da HALIN WASU MUTANAN, da wannan suna zaka gansa a wattpad nawa Sannan a YouTube ma da wannan sunan zaka gansa.

"Godiya tatabbata ga Allah me kowa me komai daya bani ikwan kawo muku qarshen wannan labari nawa lafiya, nasan ni dakai dake bamu tab'a bama kammu zan kawo ƙarshen labarin nan anan ba.

Wallahi wani tunani ne yake d'awainiya da zuciyata, idan nace zan barshi nakai qarshen labarin nan kamar yanda yake, gaskiya wannan tunanin nawa zai iya barina, sannan bugu da qari wani gidan radio sun buqaci dana rubuta musu wani labari, na kuma amsa musu, wannan ma yasa nayi saurin kai qarshen wannan labari..

Ina miqa sakwan gaisuwata ga MASOYA na a duk inda suke.

musamman y'an group nawa,

Duniyar marubuta

 

 


Post a Comment for "TANTIRANCI KO KARUWANCI COMPLETE"