Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

GIMBIYA BALARABA COMPLETE


 *đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ


~*Binta Umar*~

~*[MAMAN ABDUL WAHABU*~]

~*Mrs Ahamad gwadabe*~

_Bissimillahi rahamanir rahimi_ 

_DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI_

 ~*WANNAN LITTAFIN QAGGE NE DA GA NI BINTA WANDA YAGA YAYI DAIDAI DA RAYUWARSHI A RASHIN SANI NE*~

 

 

1. SARAN BOYE COMPLETE
2. GIDAN UNCLE COMPLETE
3. KWAI CIKIN KAYA BOOK TWO COMPLETE
4. WUTSIYAR RAKUMI COMPLETE
5. GOBE NA COMPLETE
6. ZAN FASA KWAI COMPLETE
7. MY UNCLE COMPLETE 
8. HEEDAYAH COMPLETE
9. SIRADIN RAYUWA COMPLETE
10. MIN QALB COMPLETE
11. KWARATA COMPLETE

 

~*_WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU KACAL IN KANA BUKATA SAI KAYI MAGANA*~

08089965176

 

 

*INA ALFAHARI DA MASOYA NA MASU SON RUBUTU NA ALLAH YAKARA KAUNA TA DAN ALLAH*😘

 

 

_ban yadda wani ko wata ya joya min littafi ba batare da izini na ba Ayi hattara_

 

 

 

~*DEDIGATED TO: MY FAN'S*~

 

 

 

 

*🅿1*

 

 

 

Ba kajin komai a gurin sai busa gami da sarewa da sawun doki kowa a gurinshi kokari yake yaga wucewar sarki *Almustapah* ma Adalin sarki kenan Wanda Al'umarshi take jin dadin mulkinshi gami da Adalcin A tsakanin talaka da mai kudi babu Wanda ya ware a ciki kowa nashi ne ,

 

 

 

Gurin ya karade da hayaniya can jama'ar dake gurin suka fara jiyo wata Murya cikin Lasifiqa Ana cewa jama'a Ku dakata Ku nutsu kafin fitowar mai martaba sarki mai Adalci yanzu Yarima Mai jiran gado zai fito tare da ta wagarshi Allah yaja da ran Yarima *Almansor* takawar ka Lafiya ,gaba salamin baya Salamun Dan sarki jikan sarki sarauta gadarta kukayi bata haya bace wannan tsantsan tace a jini take

 

Ba fade sai faman zabga kirari yake yi har yanzu bamuga fitowar Yarima Al'mansor ba ni kaina na qago in ga waye wannan Yarima n ,da ake tai wa kirari haka lailai sarauta ikon Allah masu Abu da Abunsu!

 

 

Bakin shi yaqi yin shiru har ila yau zabga kirari yake gami da banbadanci ga Yarima Amma shiru kakeji tamkar an shuka dosa Wanda a keyi dominshi babu Alamarsa,

 

 

Wani mugun tsaki *Balaraba* taja  A fili tace Aikin banza Kawai Mtsss  gaskiya wannan ma Dan rainin hankali ne kawai ya fito shine sai ya tsaya bata mana lokaci dubi fa time tafada tana kallon Agogon dake daure a hannuta gami da kallon kawarta Bushira wacce suke zaune a tare A wata katuwar rumfa cikin "yan Uwansu dalibai da'Alama Saukar Alk'urani Sukayi ganin tarin Alluna gami da kyauttuka a zube a gurin,gefen maza daban na mata daban hakanan gurin zaman malamai daban ,gurin zaman iyayen yara daban gurin zaman manyan baki daban ,sai wani guri keban tacce Wanda a ka tanadar wa da mai martaba domin zama shida Mai jiran gado Wato yarima gurin yasha shinfidu iri iri na Alfarma ga wasu bayi biyu a tsaye a bayan kujerun hannuwansu riqe da wasu tafka tafkan mafitai suna fiffita tun kafin Masu sarautar su zauna a gurin,

 

 

Bashira tace wallahi kuwa dama naji rade radin cewa ae mugun girman kai ne dashi Yariman shiyasa ban so Malam Idiris ya kawo saukar fadar sarkin ba yafi kawai dacewa sarkin yaro makaranta mu karbi Allunan mu sabida kin San sha'ani da masu sarauta a kwai matsala ,

 

 

Tsaki Balaraba tayi a karo na biyu cikin gadara tace wallahi Dan kar in tashi in yi tafiya ta Abin ya zama laifi gurin Malamai dama mutum yayi kaurin suna komai sai ace kai ,da tafiya ta zanyi babu wani banzan da zan tsaya batawa kaina lokaci a kanshi sauka ce dai nayi nasan nayi ae ba lailai bane sai na karbi Allon ba,

 

 

Ke Balaraba! Bushira tafada cikin mamaki tace kardai maimar taba kike zagi kin San dai nan ba gurin gadara ba ne gami da girman kai Dan haka ki iya bakinki,wallahi ,kasa kasa Balaraba ta karashe zancan tana waiwayawa bayanta domin dogarawa ne ke waye dasu ko wanne riqe da gora Kansu yasha tafka tafkan rawani idonsu ranbade da kwalli sai zarewa sukeyi

 

 

Babu wani tsoro ko kadan a Furucin ta tace ke rabu dani Dan Allah shikkenan sai in zauna a kan wani ina batawa kaina lokaci sanin kanki ne fa su Sadiya suna can na jira na kin san basu da kowa sai ni nasan suna can a takure ,shikkenan sai in zauna wani ya bata min lokaci,nifa ba da sarki nake ba,ke kin San da Wanda nake yi tafada tana wani ciccije baki!

 

 

Bushira tace wallahi balaraba ki rage wannan zafin kan naki sai ki riqa Abu cikin gadara  tamkar wata "yar wani ki yi tunanin nan fa gidan masu mulki kika shigo wallahi ni dai babu ruwana to!!

 

 

Mtsss ke nifa wallahi babu Wanda zan ji tsoro uwata da ubana kawai zan ji tsoro sai Allah da Annabi Amma babu wani mahalokin da ya isa yana kashi ina kashi in ji tsoro ni babu ruwana da wani sarautarsa,

 

 

 

Shiru Bushira tayi ganin Balaraba tana faman daga murya dama dama tayi kaurin suna a makarantar ,bata karacewa mata komai ba,

 

 

 

Can suka kara jin busa gami da sarewa wannan bafaden dake tsaye bakin katowar kofar da Mai martaba za fito yayi saurin zubewa a gurin kanshi a qasa gami da dunqule hannunshi Alamar jinjina, cikin banba danci yace Allah yaja da ran Yarima *Almansur* sarki mai farin baya baka fito ba sai da ka shirya mai takalmin karfe wannan haka yake sarautar ma suna taci in kana guri ,Dan gidan Fulani Dan gidan zainaba Dan gidan Fadim......

 

 

 

Tsitt! Bafaden yayi sakamakon da katar dashi da Wanda a keyiwa banbadanci yayi,

 

 

Nayi ta kokarin in ga fuskar sa Amma ina nakasa gani sakamakon tarin jama'ar da ta take masa baya da yawa daga cikinsu Abokannanshi ne sai "yan uwanshi da kyar da jibin goshi na hango bayanshi sakamakon sunkuyawa da bafaden dake take masa baya yayi domin tattare masa rigar da yake sanye da ita domin samun damar zama cikin kujerar Alfarmar da a katanadar dominshi.

 

 

 

Wannan bafade da yake ta zuba kirari yakara dawo wa kusa dashi fadi yake tuba nake yi *Jimina* A gafarci na Tuba!!

 

 

 

Wani Abokinshi mai suna Shahid ya kalle shi yace kaje ya yafe maka Amma ka kiyaye gaba kasan sarai ba ya son wannan Abinda kake yi masa saunawa naji yana hanaka"

 

 

 

Sunkuyawa yayi yace tuba nake ranka yadade bazan karaba ,In sha Allahu,

 

 

Daga Kai shahid yayi yayi masa Alama da ya tafi,

 

 

 

Tunda ga can nesa balaraba take ta faman daga kai domin hango Dan mulki sunan da tasa masa kenan ,Amma ta Gaza ganinshi, takasa daurewa sai tamike tsaye cikin wayancewa tana gyara daurin zaninta gami da gyara zaman hijab dinta,

 

 

 

Da kyar ta hango shi ba sosai ba sabida yadda fadawa suka kewayeshi kuma da a kwai taxara mai yawa a tsakaninsu da inda take zaune,

 

 

 

Idan ba'idonta ne yake mata gizo ba sai taga Yariman da a ke tawani zuzutashi yaro kankani, tabbas ko ita ta girmi wancan yaron tafada cikin zuciyarta gami da komawa ta zauna tana tabe baki,

 

 

 

 

 

~*BINTA UMAR ABBALE*~

 

 

 

 

_MARUBUCIYAR_

 

_*NANA KHADIJA*_

 

_*YARO DA KUDI*_

 

_*GIMBIYA BALARABA*_

📚📚📚📚

 

😘

 

 

 

 

 

*_Acigabah da gashi_*đŸ»

[04/05, 02:50] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

 

 

🧝🧝🧝🧝🧝

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

🧝🧝🧝🧝🧝

 

 

 

*đŸ»Writting by*

 

~*[Binta Umar*]~

~*MAMAN ABDUL WAHABU*~

 

 

~*MRS AHAMAD GWADABE*~😘

 

 

 

_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE DARI BIYU KACAL IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_

08089965176

 

 

 

*🅿2*

 

 

Ko min ti biyar bai yi da zama a gurin ba mai martaba sarki Almustaph yafito tare da mutananshi ,nan da nan guri ya nutsu ,fadawa ne a bayanshi cikin Nutsuwa ya riqa ratsa mutune fuskarsa a sake yana karbar gaisuwa,

 

 

Ya na zama wani bafade ya gyara masa zaman Alkyabbaur dake jikinshi ,da sauri yaje ya zauna jikinsu na rawa gami da yin gurfene sai kace wani mai nai man gafara,

 

 

Cikin Nutsuwa mai gabatarwa ya mike ,yayi gyaran murya cikin lasifiqa yace Masha Allah ,Alhamdullhi yanzu zamu fara gudanar da wannan taron sakamakon fitowar mai martaba Allah yaja da ranka ya kara maka lafiya gami da Adalci,

 

 

 

To Masha yanzu zamu saurari jawabin sarki mai Adalchi kafin jawabin Manyan baki da malamai da iyayen yara"

 

 

 

Cikin kamala da dattako mai martaba ya mike tsaye ,wani bafade ya karoso gurin hannunshi riqe da wata zungureriyar lasika ya sai ta ta daidai bakin sa ,

 

 

Sarki ya bude taro da Addu'a cikin Lafazin sa mai kyau da lumana yayiwa dalibai nasiha da iyayen su sabida jajircewarsu gurin ganin "yayansu sun samu ilimi in gan tacce.

 

 

Kana ya kuma ya zauna ,gurin zamanshi cikin nutsuwa da qasaita irin ta sarautar da ta Amsa sunanta,

 

 

Da dai dai da dai dai malamai da masu jawabi gami da iyayen yara kowa yayi nasa jawabin sannan mai gabatarwa yayi gyaran Murya yace "yanzu zamu kira daya daga cikin dalibanmu masu hazaqa zata yi mana karatu kafin mai martaba ya mikewa ko wanne Allonshi muna wa kowa fatan Alkairi gami da ko mawa gida lafiya"

 

 

 

Muna bukatar

*BALARABA AYUBA TANKO*

Tafito nan ,mai gabatarwa yafada cikin lasifiqar,

 

 

 

Hankalin kowa ya koma kan taron Matan dake zaune can cikin wata katuwar Runfa a ke 6ance a gurin,

 

 

 

Shiru Balaraba tayi gabanta yana faduwa domin Sam bata taba tsammanin ita ce zatayi karatu ba,

 

Gaskiya duk rashin kunyarta tana jin nauyin  ratsa dubban mazan dake zaune a gurin ,gani take ma baza ta iya karatun ba domin ita kam ta tsani kallo wallahi,

 

 

Bushira ce take zungurinta ,tana jinta tayi mata banza,

 

 

Mai gabatarwa yakara maimaita  Balaraba Ayuba tanko ta fito ,mana"

 

 

 

Shiru taqi fitowa,

 

 

Dago kansa yayi cikin ginshira yana bin ilahirin jama'ar dake gurin da kallo cikin izza ,ya dinga karade tarin "yan matan da Kallo so yake yaga ta inda wannan yarinyar zata fito ,wacce tun dazu a ke shalar tafito tayi kunnen Uwar shegu da jama'a,

 

 

 

*Wai ina BALARABA AYUBA TANKO TAKE NE*?

 

mai gabatarwa yaqara mai maitawa A Dan Fusace,

 

 

 

Ko gama rufe bakin sa bai yi ba ta mike tsaye tana gyara zaman hijab din ta sosai ,kana ta gyara zaman glass din dake fuskarta ,tafara ratsa Jama'a domin zuwa gurin da 'a tanadar domin ita din

 

 

 

Tun da tafito cikin jama'a sosai hankalin mutane ya koma kanta, banda Almansor ,domin kallo da yayi mata ya kauda kai yana Jan tsaki,

 

 

 

Taje ta tsaya gami da gyara lasifiqar sosai ,tayi gyaran murya cikin Nutsuwa ,tafara kwararo karatun Al'kurani mai girma tamkar wata balarabiyar kasar Saudiya yadda take fitar da harafi dallah dallah take bawa kowa nashi hakkin ga wata murya mai dadin sauraro gami da kashe jiki

 

 

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*😘

 

 

 

_MARUBUCIYAR_

 

*NANA KHADIJA*

 

*YARO DA KUDI*

 

*GIMBIYA BALARABA*

 

📚📚📚📚

 

 

 

 

*đŸ»,,,,,,,,*

[04/05, 02:50] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

 

 

🧝🧝🧝🧝🧝

*đŸŸGIMBIYABALARABA*đŸŸ

🧝🧝🧝🧝🧝

 

 

 

*đŸ»WRITTEN BY*

*Binta Umar*

~*MAMAN ABDUL WAHABU*~

 

 

~*MRS AHAMAD GWADABE*~😍

 

 

 

_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN NUMBAR*_

08089965176

 

 

 

*🅿3*

 

 

 

Shiru gurin ya dauka jikin duk Wanda yake gurin ya Mace sakamakon karatun Al'kur'ani mai girma da yake ratsa gurin.

 

 

Sai da ta karanta Ayoyi goma na farkon Suratul bakara ,kana tarufe da Addua'a cikin Nutsuwa a je lasifiqar Hannuta ,a ma'ajiyarta tafara kokarin barin gurin

 

 

Ida nun mutane sukai caaaa! A kanta Sai tafiyarta tafara hardewa tamkar zata fadi.

 

 

 

Cikin isa Ya dago kanshi dalilin Da yasa Abokinshi Shahid ya takura masa da Magana kasa kasa wai lallai sai ya kalli ita wannan mai karatun

 

 

 

Yana ya mutse Fuska gami da Limshe ido yabi bayanta da kallo domin baiyi nasarar ganin Fuskarta ba ,Wata irin ingarmar Mace ya hango game tsawo ga qiba dai dai Misali ga wani Uban Sharp Wanda sai da yafito ta cikin hijab din a nagani ,Sakamakon yadda Allah ya wadata ta dasu ,kafarta ya kalla cikin bakin takalmi Fara Tass tass da'ita ,Da'a lama jikin ma haka take

 

 

Ajiyar zuciya ya sauke yayi saurin dauke idonsa daga kanta,jin zuciyarsa tana darsa masa wani Abu,A rayuwarshi yana son farar Mace kasan cewarshi Mai dun fata .Sai tarin kyau Wanda Allah yayi masa

 

 

Shiyasa yake son Farar Mace inji hausawa Alkyabbar Mata,

 

 

 

 

Shahid ya zungure shi kadan yace"yaya ka ganta Yarinyar tayi fa wallahi irin kallar ka gata zata dace da Sarauta dubi zubin tsarin jikinta dagani A kwai qasaita"

 

 

 

 

Gyaran Murya yayi kadan "yace "yar wane sarki ce ? Waye Babanta a garin nan ? Da kake hada ni da'ita haka kawai daganin Sarkin Fawa sai Miya tayi zaqi!

Yafada Cikin izgili gami da qasaita Wanda hakan yazame masa jiki,

 

Shiru Shahid yayi sabida yasan halin Abokinshi Dan daukar zafi ne yace"yanzu dai mubar maganar sai muntashi daga nan"

 

 

Ta6e baki Sarki! Yayi dake haka yanwancin suke kiransa dashi Sabida isa da takamar da yake da'ita wacce shi kanshi sarki Almustapa  baya yi a Matsayinshi na sarkin ,shi da kanshi yake kiran Almansor din da Sarki zamu'iya cewa shine ma yasa masa sunan Sabida yadda yakeyi din tun yana yaro. To shine fa Abokanshi suke kiranshi da sunanan ,cikin gida kuwa da yarima suke kiranshi.

 

 

 

Mai gabatarwa yakara fitowa a karo na biyu ,bayan Maryam taje ta zauna Cikin nutsuwa yace'Alhmdullhi mun saurari karatu daga bakin Dalibar mu Maryam Ayuba tanko dalibar datayi fice tayi zarra cikin Makaranta sabida hazaqarta da tsaftarta biyyarta Nutsuwarta Tabbas Muna Alfahari da ita Kuma munai mata fatan Alkairi gami da samun miji nagari.

 

 

Yanzu batare da bata Lokaci ba Mai martaba sarki Mai adalci Uban talakawa Mai tausayin Al'umma ,zai fito ya rarrabawa ko wanne Alonshi gami da sauran kyautittikan da muka tanada ga dalibanmu da Suka Sauke Al'kurani mai girma kimanin Mutum Dari Uku da sha bakwai Muna fatan wata shekarar dalibai na kasa zasu bada himma da jajijrcewa Musamu ninkin waddanda muka yaye Allah yakarawa Mai Martaba Lafiya da Imani,yafada gami da aje lasifiqar ya bar gurin a nutse .

 

 

Gurin yayi tsitt! Mai Martaba yayi gyaran Murya Cikin Abin Maganar ,Wanda yana zaune gurin zamanshi wani bafade yake riqe dashi,

 

 

Ya dauki Allon Farko

 

Sunan *BALARABA AYUBA TANKO* yagani jiki yace'Alhmdullhi.

 

 

 

*Balaraba Ayuba tanko*

 

 

Wannan karon ba tayi nawar fitowa ba ta mike tafara ratsa jama'a a karo na biyu Cikin qasaitarta da yanayin tafiyarta ta durfafin inda  Mai martaba yake zaune

 

 

Idon Mutane yayi caaaa! A kanta kamar dazu ,tsaki taja a ranta tace wallahi na tsani kallo ko kadan"

 

 

 

Ta kasan idonshi yake kare mata kallo har tazo ta durqusa kusa da Mai martaba gami da gaidashi Cikin Nutsuwa,

 

 

Yayi saurin dauke idonshi daga kanta ganin ta dago kai ba yaso taga yana kallonta duk da cewar ta kasan idonshi ne idan ba mai kurrala ba ma babu Wanda zai fahimci ita yake kallo ciki ko harda ita balaraba n.

 

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

 

 

_MARUBUCIYAR_

 

*NANA KHADJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

📚📚📚📚

*đŸ»,,,,,,,,,*

[04/05, 02:51] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

 

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

 

 

 

*đŸ»Writting by*

~*Binta Umar*~

 

~*MAMAN ABDUL WAHABU*~

 

 

~*MRS AHAMAD GWADABE*~

 

 

 

_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI SAI KA TUNTUBI WANNAN  NUMBAR*_

08089965176

 

 

 

*🅿4*

 

 

 

Mai martaba ya Maka mata Alo gami da kyautitikan ta na musamman ,Masu photo da video sai aikinsu suke a gurin.

 

 

Sannan ta mike hannuta riqe da Allon Fuskarta cike da Walwala,Mai martaba ya kara lasifiqa a bakinshi yace" Ma haifin wannan Yarinya mai Albarka yafito a kwai kyauta ta musamman da na tanadar domin ku iyayen yara"

 

 

Raurau rau idanunin Balaraba yayi jin Furucin Maimartaba sai ta fara kokarin mayar da kwallar da tataro a kwarmin idonta domin bata son zubowarta anan.

 

Tana tsaye masu hotona da Video sai daukarta a keyi.

 

 

Mai gabatarwa ya Mike yaje yatari lasiqa yace"Allah yaja da ran sarki mai Adalci wannan yarinyar marainiyace Ubanta ya rasu shekuru goma da suka wuce ita kanta batayi wayo ba Mahaifiyarta ma haka yanzu shekarunta uku da rasuwa sai ita da qqnnenta Guda biyu"

 

 

 

Mai martaba yayi gyaran Murya cike da tausayin Balaraba"yace Allah ya jikansu da Rahama to yanzu muna bukatar waliyyinta yafito domin ya karbar mata Abinda muka tanadar mata"

 

 

 

 

Diri Diri Maigabatarwa yayi yana waige wai ko zaiga Sallau ,Amma ko Alamarsa bai gani ba cikin mutuwar jiki yakara tarar Lasifiqa yace Allah shi taimaki sarki sarakuna ae wakilin nata bai samu damar halartar taron ba"

 

 

 

 

Girgiza kai Maimarta yayi yana Nazarin wani Abu kana yagara Murya A nutse yace"ina bukatar *Sarki!! Yarima Almansor yafito na wakiltashi ga wannan yarinyar mai tarin Albarka*

 

 

 

Yana zaune a hakimce yaji wannan Furucin na Maimartaba sai yaji faduwar gaba kadan Amma kwata kwata Fuskarshi bata nuna ba ,shifa ba kowane kare da doki yake so Maimartaba ya riqa Alaqantashi dashi ba yanzu fisabillahi inashi ina jera kafada da kafada da wancan "yar gidan fukara'u wacce ba'asan Matsayin taba.

 

 

A nutse ya mike cike da qasai ta gami da izza kamar yadda ya zame masa jiki ya karasa kusa da da maimartaba gami da mika gaisuwa domin yana mutukar girmama Mahaifin nashi sosai da sosai baya son bacin ranshi ko kadan shine yasa ma duk Abinda maimarta ba yace baya musawa ko dako Abin baiyi masa ba,

 

 

 

Cikin nutsuwa Mai Martaba ya mike tsaye wani bafade biye dashi a bayanshi riqe da tarin mukulai da wasu takkadu cikin Ambulan,

 

 

Maimartaba ya karbi Mukuuli guda biyu ya mika Sarki!! daya na gida ne da yake ginasu can bayan gari sabida irin haka daya kuma na wani katafaran shago ne cikin wata kasuwa datayi shura cikin jahar tasu nan ma ya mika mata a karo na biyu ko wanne da takkadunshi na mallaka hade da sa hannun shi maimartaba.

 

 

 

A nutse Sarki! Ya karba gami da karasawa in da take tsaye gabanta na dukan Uku Uku,

 

 

 

Da sauri wani bafade ya karaso gurin ya kara lasifiqa bakin Sarki! Domin yasan zaiyi magana dole.

 

 

 

Gyaran Murya yayi yana duba takkadar farko,

 

 

Ya Mika mata Cikin Wani irin Voice yace  Maimartaba Sarki Almustapah ya Mallakawa Balaraba Ayuba tanko daya daga cikin gidajensa na bayan gari halak malak sakamakon kokarinta da tayi gurin saukar Alku'ani maigirma Allah yaja da ran sarki Yakara maka Lafiya Balaraba na godiya,yafada yana Dan ya mutse fuskarsa kadan gami da mika Mata takkadun ,Akwain guri ya dauki kabbara gami da kirari ga sarki Almustaph Masu photo da vidio suka fara Aikinsu ,duk wani Masoyin Balaraba a gurin ya tayata murna makiyanta kuwa tamkar su mutu.

Sallau wanda ke can rabe jikin katanga ji yake kamar yaje ya cinnawa kanshi wuta ya huta da wannan bakin ciki

 

 

 

Ta sanya hannu biyu ta karba fuskarta cike da walwala Amma taki yadda ko kadan ta kalli Fuskarsa haka masu photo suka riqa daukarsu.

 

 

 

Kamar yadda ya mika mata takkadar farko haka ya mika mata tabiyu hade da Dan mukkulin shagon da yin bayani domin kowa ya shaida

 

Zubewa Sallau yayi gumi ya tsinke masa yana mamakin yanzu Balaraba ce ta mallaki shago cikin kasuwar sha tambaya Wanda shiga wannan kasuwar sai wane da wane domin kasuwa ce ta masu kudi ,nuffashin sa ya riqa fita sama sama tamkar zai bar gangar jikinshi tsabar bakin ciki ae bai gama dawowa daga dimuwar da ya shiga ba yajiyo muryar Sarki!! Yace "Ni Almansor Almustapah na baiwa Balaraba Ayuba tanko kujarar Maka sakamakon hazakarta da kokarin ta muna fatan sauran dalibai zasu kara zage damtse gurin jajircewa da bada himma a kan karatu muna fatan wata shekarar daliban dazasu sauke Alku'ani mai girma su ninka na yanzu.

 

Yana gama fadar haka ya Fara kokarin barin gurin cikin ginshera wacce tazame masa jiki cikin kasaita yaje ya zauna gurin zamanshi  yana kallon kowa daidai.

 

Gefe guda yana mamakin yarinyar da Girman kanta ganin ko kallon in da yake taqiyi ko dame take taqama oho!

 

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

 

_MARUBUCIYAR_

 

*NANA KHADIJA*

 

*YARO DA KUDI*

 

*GIMBIYA BALARABA*

 

📚📚📚📚✍đŸ»

[04/05, 02:51] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

 

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

 

 

 

 

*đŸ»writteng by*

*Binta Umar*

~*MAMAN ABDUL WAHABU*~

 

 

~*MRS AHAMAD GWADABE*~

 

 

 

_WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU_

08089965176

 

 

 

*🅿5*

 

 

 

Daya bayan daya dalibai suka riqa fitowa suna karbar Allonsu hannun maimartaba kamar yadda yayiwa Balaraba kyauta haka ya riqa yiwa kowa daidai da Matsayinshi.

 

 

 

Sulaiman Ahamad shine yasamu kyauta kwatankwacin ta Balaraba  nan shima Sarki! Almansor ya bashi kyautar kujerar maka kamar yadda yabawa Balaraba,

 

 

 

Guri ya hautsine kowa yana taya nashi murna gami da karbar Allon ana sanya Albarka ,nan kaf dalibain da malamai gami da iyayen yara suka jero reras gaban sarki masu photo suka riqa daukarsu domin tarihi .

 

 

Sarki ya jiro wasu takkadu ya mikwa shugaban Makarantar wato Arrama Malam Idiris yace" ni Almustaph na malakawa wannan Makaranta Filina dake hayin diga halak malak kuma Na dauki nauyin ginashi da izinin Allah muna fatan zaku kara zage damtse gurin kula da tarbiyar yara da basu ilimi mai amfani.

 

 

 

Allahu Akubar Allahu Akubar Allahu Akubar

 

 

Guri ya hautsine da Akabbar Malam idirs ya zube gaban sarki tamkar zaifashe da kuka sabida dadi sai zanba godiya yakeyi

 

 

 

 

Kankace komai guri ya karade da busa irin ta gidan sarauta mai taken jinjina game sarki.

 

 

 

 

Sarki Almustaph ya mike da Alama gida Ai shiga Aikuwa fadawa suka baza manyan riguna domin take masa baya.

 

 

 

Dama A Al'ada sai sarki ya tashi sannan kowa yake tashi sabida girmamawa,

 

 

 

Mikewa Sarki!! Yayi tare da tawagarshi domin bin bayan Mahaifinshi ,wan an Dan kanzagin bafaden ya soma Aikinshi na banbadanci har ya Manta da gargadinsa na dazu

 

Busar da ake masa daban take da wacce a kewa maimartaba domin kanaji tasa yadda take tafiya slow tana tafiya da Yanayinshi na taqama!!

 

Gyara kintsi Dan sarki jikan sarki nan gani nan bari dawisu sarkin Ado dawinsun ma dole ya saurara Maka Farar Aniya Farar zuciya Farar Alkyabba  Dan gado masu sarautar gaskiya arziqinku bai rufe muku ido ba Allah dai ja da kwana Dan sarki jikan sarki!

 

Tuni guri ya kacame Kiowa  yanaso yayi ido hudu da wannan Dan sarki da'aketa wasa shi haka Mussaman Matan dake gurin da masu saukar da "yan kallo.

 

 

Balaraba na gefe duk tururrubin da'ake gurin gami da hayaniyar baisa ta zuwa gurin da yake kokarin wucewa ba sai zabga tsaki takeyi yana kallon bushira sai faman kutsawa take wai lallai sai ta ganshi.

 

 

Gefe can taja ta tsaya domin yadda a ke bangajeta gashi Sam Sam bata son hayaniya da jira da tana da damar tafiya da tayi tafiyarta wallahi domin kwata kwata bata son batawa kanta lokaci sanin da tayi cewar kannanta nacan na jiranta a gida,

 

To ganin yadda makarantar ta karramata a matsayinta na daliba ta farko yasa bataso ta watsa musu kasa a ido

 

 

Duk a zaton ta Sulaiman Ahamad shine na farko ganin yadda yake da kokari domin ko musa bakace shine yake cinyewa Amma Abin Mamaki sai taji sunanta a farko ,Tabbas ta yadda da kanta tunda Ita kanta tasan tana da masifar kokari domin wani sa'in itakewa "yan ajinsu kari idan malami bai shigo ba ita dai kyaleta da rashin kunyarta da gadara gami da takama gashi ita kuma ba "yar gidan kowa ba!

 

 

 

 

Da kyar bushira ta hangi Sarki! Daga can nesa sai ta riqa mamakin ganinshi jin Balaraba nace da ita ae yaro ne Lallai Balaraba da son girma take cikin zuciyarta tace gaskiya yana da kyau wai!! Dole yaji dakanshi duk da cewa bai fiye haske ba amma kalar fatarshi abin kwatance ce ga wani uban saje da yabi ya kewaye fuskarshi a tsare hade da mitsitsin bakinshi idonshi Manya farare tas dasu sun Dan risina kadan bazaka taba gane girmansu ba sai ya bude masu duka Amma idan ka kalli saman fatar idonshi zaka gane yana da Manyan idanuwa a sabila da dimun'da'iman idan nashi a lumshe yake ba yadda ya bude su sabida shi kanshi yasan Allah yayi masa baiwarsu .

 

 

 

Tun kan ta karaso gurin Balaraba take zabga mata harara tace"wallahi Sam Sam ba kuyi ba kun zubar mana da qima kuna mata kuriqa rububin zuwa kallon wancan waishi Dan sarki Mtssss Wallahi babu da Namijin da zanyiwa wannan rawar jikin ba'a haifeshi ba tafada a zafafe tanaji tamkar taje ta gaggaurawa matan dake rububin zuwa ganin shi.

 

 

 

 

Kallonta Bushira tayi tana Mamakin Balarabar da yadda ta dauki kanta ita ba "yar kowa ba I dillalin kashi.

 

 

Tace"laifi ne Dan munje ke tunda bazaki ba ae shikkenan ,humm gaskiya ya hadu duk da banganshi sosai ba tabbas nasan yana da mugun kyau.

 

 

 

Tsaki Balaraba taja tace kyawunshi din baza bai dameni ba ni nan Sam Sam kyauwun wani Namji bazai rude ni ba ko wata sarautarsa  tafada tana girgiza jiki gami da ji da kanta

 

 

 

Dariya Bushira tayi kadan tace" Wallahi wannan Abinda kekeyi yana mutukar bani Mamaki  wai ko Dan kinga kina da kyau ne?

 

 

Banza Balaraba tayi mata tana hura hanci!

 

 

 

Bushira tacigaba dacewa Dan kinsan bazaki taba samun kamarshi bane a matsayin Miji shiyasa kike ta wannan Abin"

 

 

 

"Wani kallon Tara shaura kwata Balaraba tayiwa bushira tana ya mutse Fuska tace " Billahillazi kika sake yimin wannan Furucin sai na fasa miki baki ae kin San zan iya ko"!

 

 

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

 

_MARUBUCIYAR_

 

 

*NANA KHADIJA*

 

*YARO DA KUDI*

 

*GIMBIYA BALARABA*

 

📚📚📚📚📚

[04/05, 02:52] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

 

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

 

 

 

 

*đŸ»Written by*

_*Binta Umar*_

~*MAMAN ABDUL WAHABU*~

 

 

~*MRS AHAMAD GWADABE*~

 

 

 

 

_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN*_

08089965176

 

 

 

*🅿6*

 

 

Bushira tace"idan baki fasa basa min baki ba kya tsoran Allah Mtss ke daga anyi magana sai kiriqa nunawa mutane gadara Aikin kawai!

 

 

Shiru Balaraba tayi mata ganin rantaya baci Sam bata son bacin ran Bushiran sabida ita kadai ce ta iya zama da ita take jure halinta ,tace"Ai sai ki shige mutafi ni wallahi nagaji da tsayuwar gurin nan wai sai yaushe za'a tashi tunda dai Maimartaba ya tafi ba shikkenan ba kowa sai ya yi nasa guri" Tafada tana wani daga  kai!

 

 

 

"Sai dai ke kiyi tafi Amma ni bazan biki ba ke kullum ba kya gudun Abin Magana duk da halinki Amma haka A ka karramaki gurin nan gashi kina nema ki watsawa mutane qasa a ido"Bushiran tafada tana dauke kai daga kanta

 

 

Gaba tayi kawai ta kyaleta tsaye a gurin tace "Sai kin tawo ae wallahi bazan zauna ina bata lokaci Na ba kinsan su Sadiya nacan A takure babu Mai basu Abinc......kafin ta karasa Sallau ya tari gabanta Cikin yaqe yace"diyata yarinyar Albarka ina Alfahari dake"

 

 

 

Gabanta ya fadi!! Sai ta dake tace"Kawu Ashe kazo gurin saukar banganka ba sai yanzu"

 

 

 

Washe hakoransa yayi yace"ae nazu tuntuni a gaban idona Maimartaba ya fito duk ina kallonshi har ya koma cikin gida yafada yana ta dariya Mara dalili domin kana ganin yadda yakeyi kasan karfin hali kawai yake

 

 

 

"Allah sarki Kawu wato kazo Ashe Amma kanajin lokacin da Maimartaba yake fadin ina waliyyina yake yafito domin ya karbar min kyautittika Na kayi shiro ko? Tana sane tayi mashi Magana domin taga Halin da zai shiga sanin da tayi basu da Makiyi sama dashi da iyalinshi duk da yana Amatsayin wan Mahaifinta.

 

 

Duk sai ya diririce Sabida yasan yarinyar "yar zafin kai ce duk da cewar bata masa rashin kunya Amma yana shakkar ta yasan kallonsa kawai takeyi gashi shi kullum nuna mata yake Ubanta ne shi tunda ba ran Mahaifinta, Amma duk wani hakkinta yakasa daukewa Asali ma da hadin bakinsa A ke muzguna musu a gidan ita da "yan Uwanta.

 

 

Sai ya hau dudduba jikinsa yace"dube ni fa Balaraba babu sutturar Arziqi kunya nakeji shiyasa ban fito ba"yafada bakinshi na rawa kai daganin yadda ya yi maganar kasan tsari ne kawai da Rashin gaskiya

 

 

Bata ce komai ba kawai ta hau duba kayan jikinshi.

 

 

Tace"Kawu kenan kowa ae da sandar hannunsa yake kai duka maye laifin tufafinka yanzu gaskiya banji dadi ba wallahi ni kai dai a guri kowa da "yan Uwanshi da iyayenshi ban dani duk su Kawu Habu da Kawu Maman da Kawu Salisu babu Wanda yazo gurin

Harsu  Safiya da Mabaruka ma haka ai shikkenan tafada tana daga kafada ,

 

 

 

Duk sai ya rasa Abin fada Sabida babu gaskiya yace"kin San wa "yan nan basa son Zumunchi kowane shege sai yace kasuwa zai tafi su kuma su Safiya da kike magana a kan su kin sansu da shegen son kudi kamar jaraba suna can suna Aikin A wara da kulelensu kamar ko da yaushe"

 

"To Kawu ina Uwa da Iya su mai yasa basu zo ba? Tafada domin taji mai zai ce domin tasan bata bakinta takeyi sabida tasan bazuwa zasuyi ba Lokacin da sukaji Labarin saukar cewa suka dinga yi ae saukar zuqu ce wannan.

 

Yace "ke ma dai Balaraba kin san wa"yannan tsinannun Matan baza su zo ba su Neman kudinsu ya fiye musu komai ki rabu da waddanan "yan hassadar ,yafada yana kokarin karbar Allon hannunta gami da kyautitikan hankalinshi na kan Mukkalan gidan da shagon sai faman washe baki yakeyi

 

 

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

_MARUBUCIYAR_

 

*NANA KHADIJA*

 

*YARO DA KUDI*

 

*GIMBIYA BALARABA*

 

 

📚📚📚📚📚📚

[04/05, 02:52] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

 

 

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

 

 

 

*đŸ»Written by*

*Binta Umar*

~*MAMAN ABDUL WAHABU*~

 

 

*MRS AHAMAD GWADABE*

 

 

_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA 200 IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN*_

08089965176

 

 

*🅿7*

 

 

_Bissimillahi_

 

 

 

Sakar mishi tayi tana bin shi da kallo ganin yadda jikinshi yake rawa Humm Kawu kenan tariga ta Fahimchi Abinda yake wa

 

Yace"Diyar Albarka gaskiya ina Alfahari dake da Dan Uwana Ayuba da ya hafeki Allah yajikanshi ya gafarta masa

 

 

"Ameen Balaraba tace taci gaba dacewa Kawu Naji kayiwa babanmu Addu'a banda Mamana"

 

 

Bata Fuska Kawu yayi yace "Allah yajikanta itama daga haka yaja bakinshi yayi shiru ita tarasa wace irin qiyyaya Kawu yakewa Mama ta duk da bata raye.

 

 

 

Yace"ae sai mutafi ko gaskiya naji Farin ciki sosai Balaraba zakije Makka Aikin Hajji mu Na zaune,

 

 

Dariya tayi tace "Kawu kenan kar kadamu Nabar maka kaje kai kawai Tafada babu damuwa tattare da'ita.

 

 

 

Wani farin ciki ne ya ziyarce shi A zucci yace "ja'ira mai kama da tsohowar Karuwa ae ko baki bani ba baki isa kije Makka ba in dai INA raye a doran duniyar nan.

 

 

A zahiri kuwa yariqa washe baki tamkar me sai shi mata Albarka yake kamar babu gobe.

 

 

 

Jin shi kawai Balaraba takeyi domin tafi kowa sanin waye Kawu.

 

Haka suka ran kaya suka nufi gida Kawu sai hirarraki yake mata Na babu gyara babu dalili.

 

 

 

Wani gida Nafara hangowa cikin wani surqoqin lungu Wanda kwatoci sukayi wa yawa gasunan duk sun bi hanya babu kyawun gani gefe ga tarin bola da tarkace da wata tsiya ce yara duk sun Tara kayan gwangwan da Alama yaran Layin suna fita Sana'ar gwangwan domin ga Alamu nan tarin robobin qarafuna da buhunhuna.

 

 

 

Haka sukai ta tsallake  shirgin gurin Kafin su shiga cikin gidan da babu kofar arziqi duk ta lauye ko tsayuwa batayi da kafarta sai an kare da dotse ko kujera,Kawu sai zage zage take yi kafin ya shiga gidan fadi yake shegu tsinannu "yayan Allah bani duk sun zo sun cika mana layi da kayan sata "yan iskan yara kawai"

 

 

Wani kallo Balaraba taiwa Kawun Mai kama da Harara tace"Haba Kawu wannan zage zagen bashi da Amfani Shiyasa suka rai naka ina ruwanka dasu ,sai La'antarsu kake yi ta'ina zasuyi Albarka kar ka Manta fa harda su Babaye da Walidi cikinsu shikkenan tunda ka hadasu ka zage babu ta yadda zasuyi Albarka ,Neman halak dinsu sukeyi yafi suje su dauki Na wani " ta qarashe maganar Cikin bacin rai!

 

 

Gyaran Murya yayi ko kunya babu domin shi yanzu lallaba Balaraban yakeyi so yake ya kwace mata duk Abinda ta samu gurin saukar.

Yace"Rabu dasu diyar Albarka kinji ko shige muje ciki Ae ke kaman Dan Uwana yayi sa'ar Haihuwa ba wa"yannan "yan iskan ba"

 

Yaran dake gurin suka kwashe da dariya suna nunashi da hannu domin dai dama yaran duk sun rai nashi sakamakon zubar da Mutunchin shi da yakeyi gurin in sunje gwangwan dinsu sun dawo yabi yana kar6e musu kudi.

 

Balaraba taja tsaki ta shige ta barshi gurin tace"ae kaga Abinda nake gudar maka nan gashinan sun mai da kai mahaukaci"

 

 

Walidi ne yafito a guje su ka ci karo da Balaraba yayi mata wata bangaza tamkar zai yadda ita kasa,yayi gaba ko saurararta bai yi ba.

 

Da sauri ta jawo hannunsa ta zabga Masa Marika hagu da dama tace" Dan Uwarka ni sa'arka ce zaka bangaje ni ka huce ko kallo ban isheka ba ko ka ga INA shiga sabgarku ne"?

 

 

Kuka Walidi yafashe dashi yayi cikin gida da gudu yana cewa"Allah ya isa ban yafe ba Shegiya "yar Karuwa"

 

 

 

Wani Bacin rai! Ya dirar wa Balaraba tayi cikin gidan A fusace yau sai taga da Wanda walidi yake taqama Lallai yau za'ayi rigima gidan nan domin tagaji da irin cin zarafin da yaran suke mata.

 

 

Da sauri Kawu yabi bayansu yana zagin Walidi ta Uwa ta Uwa ba

 

 

Uwa" Na zaune kan kujera "yar tsuguno tana wanki dake sana'ar tace kenan wankau Walidi ya shigo yana burara ihu tamkar Wanda a ka yanka ,Sai tambayarsa take menene da qyar yace waccan "yar karuwar ce ra mareni hagu da dama inaji ma ido na yafashe yafada tana rintse ido daya cikin sharri

 

 

Cikin Sababi! Da tashin Hankali! Uwa ta Mike tana gyara daurin zaninta tace "Lallai Yau zaci kambu a gidan nan Wallahi tallahi bazan lamunci wata "yar iska ta riqa dakar Min "yaya ba bara ta shigo inji meye dalil......kafin ta karasa tajiyo Muryar Kawu yana ta Surfawa Walidi zagi!

Abin Mamaki!

 

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

 

 

_MARUBUCIYAR_

 

*NANA KHADIJA*

 

*YARO DA KUDI*

 

*GIMBIYA BALARABA*

 

 

📚📚📚📚📚

[04/05, 02:52] +234 808 996 5176: 🧝🧝🧝🧝🧝🧝

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

 

 

 

*đŸ»writting by*

*Binta Umar*

_*MAMAN ABUDL WAHABU*_

 

 

*MRS AHAMAD GWADABE*

 

 

_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE 200 IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN*_

 

 

 

*🅿8*

 

 

"Yau kuma da Abinda kashigo da shi kenan Malam me walidi yayi maka kake ta surfa masa zagi haka? Kar dai a ce tarewa mutsiyaciyar yarinyar nan kake Balaraba"

Tafada tana nuna Balaraba dake jikin rijiya tana kallonta.

 

 

 

Kawu ya gyara tsayuwa gami da riqe Abubuwan dake hannunsa da kyau ,ya kalli "Uwa yace"Laifi ne Dan Na tare mata Yarinyar kirki haka ka wai kin bata yaranki kin sangar tasu basa ganin kowa da mutumchi a gidan nan yanzu a ce kamar Balaraba ita Walidi zai zage yayi ta zagi kina kallonshi kice in yi shiru"

 

 

Mugun Mamaki ne ya kama Uwa jin Abinda Kawu yake fada Lallai a kwai lauje cikin nadi kawun da yake zama a zagi Balaraba da ita da iyayenta da qannenta yau shine yake tare mata fada.

 

Ta gyara tsayuwa gami da gyara daurin dankwalinta ta kalli kawun tace Au! Ashe kai ma tafara baka cin hanci cewa zakayi kafara cin kudin zina da sata

Tafada tana wani girgiza jiki cike da Neman fitina,

 

 

 

Kifta mata ido Kawu yayi ganin har ta hasala

 

Duk Balaraba Na kallonshi.

 

Aiko dake "Uwa tasan Halin Mijinta nan da nan ta dago Abinda yake nufi kifta mata idon da yayi

[04/05, 02:54] +234 808 996 5176: 🧝🧝🧝🧝🧝🧝

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

 

 

 

*đŸ»writting By*

*Binta Umar*

_*MAMAN ABDUL WAHABU*_

 

 

 

*🅿9*

 

 

"Ke kuwa Uwa wane irin Abu mai muni yarinyar nan tayi miki ? Kike jifan ta da Mummunan Al'kaba'i haka me yayi zafi kema fa kin haifa"

Iya take fada bayan fitowarta daga dakin ta tana tsaye ruqe da ha6a tana kallon Uwa cikin Mamaki

 

Kafin Uwa tace komai sai gasu Mabaruka sun shigo a guje ko wanne hannushi ruqe da Farin botiki Wanda suke zuba Awarar da suke Siyarwa da kwai suna kaiwa kasuwanni

 

Sai wasan banza suke suna dariya kamar wasu shashashai ko wacce taci janbaki gami da wani katon A cuci a kawunansu.

 

 

Sai suka tsaya ganin Iyayen nasu a tsaye dagani Fada a keyi.

 

 

Uwa tace "Yawwa "yayan Albarka dama tunda naji shiru nace Lallai yau Awara zata qare Allah dai yayi muku Albarka Ya Baku miji nagari duk Dan bakinciki sai ya mutu ehe!!

Tafada tana kallon gefan da Iya ke tsaye tana kallonsu,

 

 

Shamsiyya tace"wai meye ne ? Naga duk kunyi wani cirko cirko tafada tanawa Balaraba Wani Dan iskan kallo.

 

 

Uwa tace"Wannan mai ido a tsakar kan ce take zagina bay an ta mari Walidi shine babanku yake cewa wai laifin walidi ne  kan nayi mata magana Shine yar Ubanta tafito zata tare mata .

Tafada gami da zama kan kujerar da tatashi ta ciga da wankinta tana sakin habaici ga Iya.

Mabaruka ta kalli Kawu sallau Mahaifinsu ,Cikin Raini da rashin kunya tace "Haba Kawu yanzu har ka fi son bare da Jininka yanzu a gabanka wannan jakar! Take zagin Maihafiyarmu baka ce komai iyi!? Kawai sai ta aje botikin Awarar a Fusace tayi kan Balaraba gadan gadan!

 

Dama sun saba dambe Dan su Shamsiyya basu da Hankali in dai Abu ya hadaka dasu Abu kadan sai a fara dambatuwa.

 

Balaraba tayi saurin kaucewa daga jikin rijiya ta tari Shamsiyya tun kafin ta karaso suka kacame da kokawa Abin Mamaki!!

 

Mabaruka tafara daukar Abubuwa tana dukan Balarabar dashi ganin ta kayar da Shamsiyya tana duka .

Sai dura mata Ashar Mabaruka take ta Uwa ta Uba.

 

Iya ta shiga tsakani tana rabawa gami da ruqe Balaraba Amma Ina!! Balaraba taqi rukuwa domin dama in tai zuciya fadanta baya rabuwa.

 

Shiko Kawu sallau barin gurin yayi yana tsitstsinewa su Shamsiyya a zuciyarsa domin babu Halin yayi a fili sabida tsoran Masifar Uwa.

 

 

Uwa dataga Ana cutar "yarta sai kawai ta daga ruwan daudar da take wanki dashi cikin roba ta kwararawa Balaraba a jiki tundaga tsakiyar kanta har zuwa qafarta tana ta zabga Mata zagi gami da mugun fata!!

 

 

Da kyar Iya ta janye Balaraba daga kan shamsiyya tana bata hakuri gami da yi mata Fada,

 

 

Shamsiyya da tasamu ta mike sai taciga ba da zagin Balaraba tana jin fan ta da kwanonisu Na cin Abinci Wanda suke gefe Dan qazanta har yanzu ba'a wanke ba qudaje sai bi suke gami da ruwan wanki da Uwa ! take kwara musu

 

 

Har tasamu nasar jifanta a kanta gurin ya tasa ,cewa"take Wallahi sai naga bayanki Dan Uwarki karuwa Uwar tamu zaki dinga zagi shegiya wacce ba'a san Asalinta ba"

 

 

Bakinci tamkar ya kashe Balaraba sai tafashe da kuka, a gurin su Sadiya da Shamsu kannanta suna taya dawowarsu kenan daga makarantar Allo,yara duk sun cika gidan,

 

 

Iya ta janye Balaraba ta kai ta dakinta  tana rarrashi tace"ko da yaushe ina fada miki ki daina Daka ta tasu Mabaruka su ba hankali garesu ba gashi yau a cikin farin ciki kike kinyi saukar Alku'ani mai girma Amma zaki bata wayonki Dan Allah ki daina kulasu.

 

 

 

Cikin kuka tace"iya kinajin zagin da suke min fa wai mai Na tsarewa Uwa ita da yaranta suka tsane ni ,nifa basa bani ci basa bani sha komai bi nakewa kaina ni nake fita in nema in ciyar da kaina da kannena to gaskiya nagaji zan siyar da gado Na kawai in bar musu gidan gwara inje in kama haya sai yafi min"

 

 

"Aa Balaraba kina nufin zaman kanki zakiyi bazai yihuba dama yaya Lafiyar kura kullum cikin yi miki sharri suke duk Wanda yaji cewar kin gama daki shikkenan sai zancensu ya tabbata ,ki kara hakuri kinji ko kwana nawane zaki yi Aurenki .

 

 

 

"Aa Iya ki kyaleni kawai "tafada tana share hawaye.

 

 

Iya tace"Aiko bazan kyaleki ba Balaraba yin hakan yana nuna cewar cin Amanar Dan Uwana Ayuba ,Sam baicancanci haka ba bayan haka kuma zumunchi bai CE haka ba

 

 

 

Share hawaye tayi ta kalli su Sadiya da shamsu Wanda suke zaune sun zuba mata ido suma suna share hawaye,tace "kunci Abinci"?

 

 

Girgiza kai sukai Alamun A'a.

 

Mikewa tayi ta karbi mukullin dakinta gurin iya tace"Ku taso Ku je Ku siyo indomee sai in dafa muku kafin in daura girki"

 

 

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

_MARUBUCIYAR_

 

*NANA KHADIJA*

 

*YARO DA KUDI*

 

*GIMBIYA BALARABA*

📚📚📚📚

08089965176

[04/05, 03:04] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

 

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

 

 

 

*đŸ»writting by*

*Binta Umar*

_*MAMAN ABDUL WAHABU*_

 

 

 

~*MRS AHAMAD GWADABE*~

 

 

*🅿10*

 

 

Dakinsu Na gado ,ta bude musu ,suka shiga ,tana jin su Mabaruka da Shamsiyya ,sai zaginta sukeyi har yanzu ,sai tayi musu banza,

 

Tafito da kudi gudar Dari biyar Sabuwa dal! Tabawa Sadiya ,dake tafi  Isyaku ,wayo ,tace maza taje ta siyo musu indome guda hudu ,sai ta dafa musu kafin ta Dora musu Abincin dare.

Cikin Farin ciki Sadiya ta kar6a ,ta tafi kantin Abbah ,dake bakin layinsu siyowa Sai Murna takeyi dake yarinyar ,tana son. Indomee sosai ,shiyasa kullum said tayiwa Aunty tasu Addu'a in tayi Sallah,sabida duk Abinda suke Nema tana musu .

 

*wannan kenan*

 

 

*ASALIN LABARIN*

 

 ___________________

 

 

Malam Tanko  Makeri

Shine Ai nihin sunasa ,Wanda jama'a suke kuranshi dashi ,Amma A salin sunansa dayyabu " to tun yana yaro Mahaifinshi ya sanya masa Tanko kasancewar sunan Mahaifinshi ne dashi

Shiyasa sunan ya buya idan ba Tanko Makeri kace ba babu Wanda zai gane.

 

 

Mutum ne shi Wanda Allah yayi masa baiwa  da Fasa ta qere qere duk Abinda ya kalla sau daya to in sha Allahu nan take zai qera makashi ,tamkar daga kamfani

 

 

Shi kadai Mahaifinshi ya haifa ya koma ga Allah.

 

Shi kuma tun tasowarsa mutum ne mai Auri saki  ,Matarshi ta Farko Lantana itace Uwarsu Kawu Sallau da Kawu Maman ,Matarshi ta biyu "yayanta duk mata ne su biyar ,haka ta zubesu gaban Lantana ,tayi tafiyarta ,Lokacin da Auran ya Mutu.

 

 

Lantana wata irin mace ce mai zuciyar kafurai bata da imani ko miskala zarratin,ita ke daura yaranta a kan mumun dabi'a

 

Idan Tanko ya fita sana'arsa sai ta daurawa "yayan kishiyarta ,mata talla ,tace duk inda zasuje suje su siyar mata tallah har da daddare daura musu take ,idan suka qi kuwa tasa Sallau ya Zane su.

 

Tun Tanko bai Sani ba har yazo ya sani ,yayi tai mata fada,budar bakinta sai cewa tayi itafa baza ta zauna da gurda gurda "yan mata gida daya ba batare da ta more su ba idan baya so ta daura musu tallata to yayi musu Aure,

 

Dake Tanko Jan wuya ne a gidanshi ,ya tsawar mata ,yace "gidansa takyale masa yara suyi karatu ,tukkuna idan Miji ya fito ai za'ai musu Auran.

 

 

Lantana taqi ji ,Tanko yana sa kafa yana fita zata fafaki yaran da faratin tallah ,suna kuka suke tafiya,

 

 

Karshe Suka yanke shawarar guduwa gurin Uwarsu,

 

 

Aiko ranar da Asubah suka fito dukkaninsu suna labewa suna jiran babansu ya fita sallah su gudu

 

 

Tanko ya fito kamar yadda ya saba ,ya tsaya shagon su Sallau ,domin tashinsu ,suje massalaci ,daga bakin kofa ya tsaya gami da bubbuga kyauran ,ya wucewarsa

 

 

Su sallau ko sunajinsa ,da suka fahimci ya kauce daga gurin sai suka cigaba da baccinsu ,dakin sai tsami ne yake tashi ,sabida ,dama bawata tsaftace dasu ba ,sai su fi sati basiyi wanka ba.

 

 

 

Su Atika kuwa bayan sun tabbatar da wucewar babansu ,sai suka fito sadaf sadaf zasu gudu.

 

 

Abin Mamaki ! Sukayi gware da Tanko ya dawo domin daukar chazbah ,

 

Sai ya kara haske fitilar dake hannunsa yana kallonsu daya bayan daya,ga Atika riqe da katuwar jaka.

 

 

Yace"INA zakuje ne"?

 

Sai suka fashe da kuka dikanninsu ,

 

Kukan da yayi sanadiyar Farkawar Lantana daga Barci duk da tana cikin Uwar dakinta,

 

Tafito da sauri jin kukan da soro ,tana Addu'a Allah yasa ba daya daga cikin "yayanta bane ya mutu ,kanta ko Dan kwali babu.

 

 

Me za ta gani su Atika ne tsaye riqe da jaka suna zabga kuka ,ga babansu a tsay"

 

 

Tace"Malam Lafiya dai in ce ko "? Wa"yan nan shashashan yaran sun tashe ni daga bacci"

 

 

Ko sauraronta bai yi ba ,ya cigaba da tambayar su Atika ina zasuje da Asubar nan.

 

 

Atika tace "babah mungaji da Azabar da ake gana mana ,zamu tafi gurin babarmu,

 

 

Lantana tayi salati kamar gaske tace"Au!sharri zaku kullamin gurin Ubanku "ooo ! Ni Lantana Na hadu da "yayan zamani,

Sai ta hau kwala Sallau kira.

"Sallau" Sallaau!! Sallau"!!

 

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

 

_MARUBUCIYAR_

 

 

*NANA KHADIJA*

 

 

*YARO DA KUDI*

 

 

*GIMBIYA BALARABA*

 

📚📚📚📚

_in kana bukatar cigabansi ga number nan_

08089965176

[04/05, 03:05] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

 

 

 

*đŸ»writting by*

*Binta Umar*

_*MAMAN ABDUL WAHABU*_

 

 

 

_Bissimillahi _Rahamanir rahim_

 

 

*🅿11*

 

 

Sallau ya taso a fusace Sallau ,yafito gami da cewa "wai menene kin tashe ni ina bacci"

 

 

Sai tafashe da kuka tana nuna su Atika da hannu tace"ga sunan suna kulla min sharri a gurin Ubanku ,har da zagina"

 

 

Ai ko sallau ya yi tsalle ya gaurawa Atika Mari yana zaginta ta Uwa ta Uba,kwata kwata bai lura da Malam Tanko dake tsaye a gurin ba.

 

 

Tanko yace"yanzu Lantana yaushe yaran nan suka zage ki Dan sharri" to tunda Abin ya zama haka zan dauke yaran nan daga hannunki ,ya mai da idonsa kan Sallau dake tsaye yace"kaji kunya sallau ,da zaka din ga biyewa Uwarka da duk Abinda tace da kai , Allah ya shirye ka,ya mai da idonsa kan su Atika yace su koma ciki ,kafin yadawo daga masallaci.

 

Yana fita Sallau ya riqa zaginsu shi da Lantana,sukayi masu shiru ,Lantana tace baza su koma ba cikin gidan ba tunda suka fito sun fito kenan ,sai subari Ubansu mai daure musu gindi ya dawo sannan.

 

 

 

Bayan Sun fito daga Massalaci Tanko ya tsaya shida Amininsa yake fada masa halin da a ke ciki.

 

Budar bakin Malam iliyasu yace"mai zai hana muha da Atika da Yunusa mana ina ganin hakan zaifi.

 

Malam Tanko yaji dadi hakan ,ai nan suka tsayar da Magana.

 

Bayan sun karya da kansa ya fita dasu yasa su a mota ban da Atika domin yafada halin da ake ciki.

Tana kuka suka rabu da "yan Uwanta.

 

 

****

 

Lantana kamar ta mutu jin cewar Atika zata Auri yunusa Dan gidan Malam iliyasi ,ita San samunta yaran suyi tazama babu Aure sabida tsabar qiyyaya.

 

 

 

Ranar daurin Aure Abin sai yabawa jama'ar dake gurin Mamaki jin ana daurawa Uba da "ya Aure.

 

Da Labari ya iski Lantana gurin daurin Auren tafito tamkar mahaukaciya tariqa dure duren Ashar

Da kyar su Sallau suka jata suka mayar da ita gida.

Tace"Yanzu Sallau Abinda Malam zai yimin kenan ,ya muna furce ni ,Ashe Aure zai yi ban sani ba niko mai zan yiwa Malam in wuce bakin cikin da ya kunsa min"

Sai ta fashe da kuka har dasu fyatar majina.

 

Sallau yace"ki rabu dashi Lantana,mune maganin Matar tasa wallahi ,tunda tasa ki zubar da hawaye Sai mun hanata zaman lafiya"

Maman yace "kwarai kuwa sai mun daukar miki fansa a kanta"

 

Sai tai ta shi musu Albarka ,tace"ai dama nasan zaku share min hawaye shi kuma Malam din zai shigo ya same ni wallahi"

 

 

****

 

Lantana babu irin cin mutumchin da bata yiwa Malam Tanko ba ,ya share ta ,kawai bai kulata ba ya cigaba da hidimarsa,

 

 

Gidan Malam Ilayisu nan a ka kai Atika,sosai Tanko yayi mata kayan daki babu laifi ,nan ma da labari ya iski lantana ,tai ta zuba ruwan bala'i a gidan ,tana cewa Tanko ya kwashe dukiyar "yayanta yayiwa wata banza kayan daki ,ai "yaya maza sune "yaya

A takaice dai ranar Lantana bata barsu sun rintsa ba.

 

Ashe Abu Na gaba,

Sabida kayan dakin Amaryar Malam Tanko iri daya ne da Na Atika ,da Alama duk shi yayi musu.

 

 

 

Wata makociyarsu tazo tana tsoguntawa Lantana ,Aikuwa "yan jeran nafita ,suka shiga dakin Amaryar ita dasu Sallau ,duka wargitsa shi,gami da debo kwata suka yaba jikin gadon da tsakiyar dakin ,sannan suka dinga kuza ruwa a tsakiyar gadon da dakin,sai da suka jiqa katifar jagab sannan suka futa daga dakin ,gami da barinshi a bude.

 

 

Ko da "yan kawo Amarya suka zo Lantana Na kuryar dakinta ta tasa redio tana ji ,tana jin shigowarsu sai ta rage redio n tayi lif tana jiran me zai faru.

 

 

 

Abin Mamaki gami da daure kai dak in suka gani a bude ,suna San ya kafafunsu ciki suka ga Abin mamaki ,Komai a fashe ga katifa jagab dakin yana ta warin kwata,

 

Matar Liman ,ta ce"innalilahi wa'ina ilayi rajiun"! Ai ba haka muka bar dakin nan ba,kai! Jama'a wai kishi hauka ne?

 

Lantana Na jiyo Abinda take cewa sai tafito a fusace tana gyara daurin zaninta ,Dan kwali a hannu,

Ta nuna Matar liman da hannu tace"ke Shattu bana son munafurci da kankanba ,ehe! Duk wata kutun gwila da kuka hada naji labari da sanya hannuku gurin bawa Malam ,waccan Mutsiyaciyar yarinyar tsintaciyya wacce ba'a San daga in da take ba ,wato ni za ai wa rufa rufa ,an lullube kura da fatar Akuya ,an dauko Mayya an kawo min gida salon tazo ta leshe ni da "yaya Na,to wallahi baza ta sabu ba ehe!! Tafada tana buga cinya cike da neman tashin hankali!

 

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

 

_MARUBUCIYAR_

 

*NANA KHADIJA*

 

*YARO DA KUDI*

 

*GIMBIYA BALARABA*

 

 

_IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN_

08089965176

[04/05, 03:05] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

 

 

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

 

 

*đŸ»writting by*

_*BINTA UMAR*_

*Maman Abdul Wahabu*

 

 

 

 

_Up_

          _up_

                     _up_

*BINTA UMAR FAN'S*

 

_INA MUGUN YINKU SOSAI DA SOSAI INA JIN DADIN YADDA KUKE KAUNAR NOVELS DINA ,NAGODE DA GOYAN BAYANKU DARI BISA DARI_

 

_*HAKIKA BANI DA BAKIN DA ZAN YI AMFANI DA SHI GURIN GODE MUKU ,SAI DAI IN CE ALLAH YABARMU TARE ,ALLAH YABAR KAUNA TA DAN ALLAH*_

 

 

 

*"YAN QUNGIYAR ZAMANI WRTERS ASSOCIATION*

 

_INA YINKU OVER ,MUSSAMAN ,RAEL SHAXXI  ,HUSAIN 8K "YAR MUTAN ARKALLAH ,HAFSAT SISI ,HALINKU YANA BURGE NI HALINKU ABIN KOYI NE_

 

 

*ALLAH YAQARA DAUKAKA ZAMANI*

 

 

*🅿11*

 

 

Shattu tace"kinga lantana mu ba tashin hankali ne ya kawo mu ba Alkairi ne ya kawo mu duk dai wannan da yayi nagari kan shi," takarashe magana tana kama hannun Amaryar Malam Tanko

Da nufin shigar dai ita cikin dak in'

 

 

Mutanen dake ciki suna ta faman tsane ruwan dake kwance gurin ,suka ce "Aa shattu yanzu in kinshigo da ita nan ina guri ,ki kai ta makota tukkuna mugama gyara gurin.

Duk abinda mutum yayi kansa.

 

 

Shatu tace "to bara muje gidan Baba Laraba I Dan kun gama sai kuzo Ku fada,

 

 

 

Da sauri Lantana ta tare hanya tana buga cinyarta tace"Ahayye nanaye Akin bur in ji tusa ,dole Dan ace da Mijin iya baba ni warki CE daidai da qungun kowace shegiya,ihe! Muna fukar Banza kawai!

 

 

Shattu tace"wai Lantana Lafiyarki kalau kuwa kishi fa ba hauka bane"A tunani Na zaki dauki Suwaibah a matsayin "yarki tunda kin San kome ya faru da rayuwarta"

 

 

 

 

"Ke!! Dakata shatu" Lantana tafada ta na turo dauri gaban go shi

 

Tace"dadin baki zaki yi min Dan bake a kaiwa kishiyar ba.

 

 

Baki San yanda  zafin Abin yake bane shiyasa kike shishshigi a kan Maganar,

Nafada Na kara fada ni Lantana,in dai ina raye babu macan da ita sa in zauna da ita ,ko wacece kuwa"

Ta karashe maganar tana buga cinya.

 

Shatu kawai sai taja hannu Suwaiba ,wacce take ta kuka tsora ya cika ta,dama tuntuni take jin labarin matar a bakin mutan gari.

 

 

 

Lantana ta koma ta zauna ,gami da kunne redion ta tasaka kasat din wakokin bar mana coge tana ta zubda habaici a gidan,jira kawai take su tanka ayi wace za'ayi

 

 

Su dai sukayi mata shiru suna Aikinsu,

 

Bayan da suka gama ne daya ta tafi domin Kiran shattu ta shigo da Amarya dakinta.

 

 

To can kuwa gwaggo laraba ta sanya Suwaibah a gaba tana ta yi mata fada tace"duk Abinda lantana zatayi babu ruwanki da'ita idan mijinku ya fita kine mi izinin zuwa nan gudun fitinar laraba ,sai miyi zamanmu idan ya dawo sai ki koma,

Kinji ko?

 

 

Suwaibah ta daga kai tana zubar da hawaye gami da tuno Dan ginta da "yan Uwanta ,Rayuwa kenan

 

 

 

Kafin su watse sai da shatu takara yi mata fada sosai San nan tafito ta tafi

 

 

 

Lantana Na zaune tsakar gida tana jiran shigowar ,malam Tanko ,Domin yau ko me za'ayi sai dai ayi taci Alwaashin bazai kwana da Amaryarsa ba tunda ya munafurce ta,

 

Sallau ya shigo fudun! Fudun! Dashi kayan jikinsa duk datti tsabar kazanta jikinshi in banda tsami babu Abinda yake yi

 

 

Ya zauna kusa da Babarta sa gami da cewa"lantana me kikeyi har yanzu baki je kin kwanta ba ,goma fa ta wuce yanzu"

 

 

Tace"INA jiran babanku ya shi go Ayi wacce za'ayi"

 

 

Yace"to Ina Abinci Na"?

 

 

Lantana tace "kaga sallau !!wane irin Abinci kuma ,zan baka? Da girmanka da komai ,ni yau ban yi girki ba,ka kyale ni inji da Abinda ,ya dame ni"

 

 

 

"Gaskiya dole in yi Aure nima nagaji da wannan Abin da a ke mana a gidan nan Abinci ma sai a hanaka"

Dubi Yunusa dake shi Ubanshi yana sonshi ai yayi masa Aure ya bashi Abin yi da gurin zama,Amma mu muna zaune, gaskiya da sake ,bari Baban ya shigo yasan wacce zaiyi, shikkenan sai mu zauna muna kallonshi yana Aure Aure ,duk kudinshi su kare ta nan gurin. Sai bayan ya mutu mu tashi a tutar babu"

 

 

 

Lantana ta gyara zama tace"Yo dama ai tuntuni nake fada muku Ku San Abin yi wallahi domin Malam baya tataku ,kaima kaje ka nemo matar Aure ,ihe! Duk in da kudi suke yafito dasu yai maka kuma dole ya baka jari da gurin Zama"

 

 

 

Sallau yace "ai Abinda zan yi keanan kuma zan fara binkicen a dakarsa ta waccan dakin nasa da baya son Abude nasan da a kwai Abubuwansa a ciki masu Amfani ,zan bi dare Na sacesu ,a kan ya Qarar dasu a banza ba mu mori ko kwabo ba"

 

 

 

Wata dariya Lantana ta fara yi cike da Farin ciki tace"shiyasa nake son ka Sallau ,ai kai ne maganainsa wallahi"

 

 

 

Sallau tace"wai har an kawo masa Amaryar ne"?

 

 

 

Dakin Suwaiba lantana ta kalla tana zabgawa harara ,tamkar da mutum take tace"tana ciki tana jinka munafukar banza!

 

 

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

 

_MARUBUCIYAR_

 

*NANA KHADIJA*

 

*YARO DA KUDI*

 

*GIMBIYA BALARABA*

📚📚📚📚

_in kana bukatar cigabansi ga numbar nan_

08089965176

[04/05, 03:08] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

 

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

 

 

*đŸ»writting by*

_*BINTA UMAR*_

*Maman Abdul Wahabu*

 

 

_RABBI SHARALI SADARI WAYYASIRLI AMRI WA'ALAL UQUDATUN MIN LISANI YAFQAHU KAULI_

 

 

 

*🅿13*

 

 

 

Tashi sallau yayi yaje ya dinga buga kyauran  dakin ,cikin sigar rashin mutumci ,yana zagin Suwaiba Matar mahaifinshi

 

Lantana tace" kayi min daidai ni dama nasan zaku share min hawaye Na"

 

 

 

Sallau yaciga ba da ciwa Suwaibah mutumci yace"Tsintacciya wace tafito yawon karuwanci ,Dole sai kin koma garinku ,Na gado mai sifar bararoji nan ba Nijar bace ,kin zo zaki lashe mu mayya kawai"

 

 

Suwaiba Na ciki tana kukan wannan cin mutumchi da ,salau ya ke sirfa mata!

 

Motsi yaji daga waje ,yayi saurin barin kofar ,Suwaibah yaje ya zauna kusa da lantana ,duk a zatonsa malam tanko ne,

 

Maman ne ya shi go fudun! Fudun! Yadawo daga yawonshi Na gidan kallo

Ya zauna bakin rijiya,yana hamma yace Lantana ina Abinci na?

 

 

 

Ban dashi!! Lantana tafada a zafafe tacigaba da cewa"gantalalle gama yawon Na ka zaka tambaye ni Abinci ai ko ina dashi bazan bayar ba"

 

 

Maman yace"to kar ki bayar mana ai nasan in da yake zanje in diba"

 

 

Tace"zagina zakayi ne Maman" wato baza ka dai Na yi min rashin kunya ba ko kana gananin Abinda mahaifinku yayi min"

 

 

 

"To me zan miki "yafada babu damuwa a fuskarsa yacigaba da cewa "karkari kawai duk abinda matarshi tayi min ko tayi miki in Zane ta ciki da waje"

 

 

 

Lantana tayi dariya gami da gyara zama tace" yawwa Dan arziqi irin albarka ,dama haka nakeso nasan kuna sona ,sabida haka. Mutaro mu takura mata kamar yadda mukaiwa wa"yancan yaran suka gudu ,har sai tagaji itama ta gudu da kafarta.

 

 

Sabida Azabar mu

 

 

Tace "kai kuma Sallau kabi dare da rana ka kwashe duk wani Abu da yake taqama dashi mu boye, domin baza mu tashi a tutar babu ba"

 

 

Sallau yace ai ba sai kin fada ba Lantana"

 

Dariya Maman yayi yace"gaskiya Lantana kin San ta kan Mugunta"

 

Ita ma dariyar ta sheqe da ita tana gyara zama tamkar wata sabuwar mahaukaciya tace" ai duk a gurina kuka koya"

 

Tace"bara Na kawo muku Abinci "yayan Albarka"

 

Ta mike tayi kchin tana sambatu kamar tababbiya

 

 

Suwaibah Na makale jikin kofarta tana jinsu ,Da duk Abinda suke kullawa,tausayin Malam tanko ya kama ta,sai tace"in sha Allahu Allah bazai Baku iko ba"

 

 

Goma da dara bi Tanko ya shi go gidansa,ya kulle gidan ,

 

 

Abin mamaki Su Sallau ya gani zaune sun kewaye uwarsu kamar masu Neman gafara

 

 

Yayi sallama

Suka Amsa ,ban da Lantana tana can tana kallon Abinda yake hannunsa!

 

 

Sallau yace Barka da dare?

 

"Barka kadai" Tanko yafada yana kokarin shiga dakin Amaryarshi

 

 

Sai  lantana ta mike taje ta tari hanya ,cikin Neman tashin hankali tace"Malam baka isa ba fa"

 

 

Cikin nutsuwa Tanko yake kallonta ,Tamkar mahaukaciya yace"lafiyarki kalau kuwa lantana"

 

 

Rasss!! Nake tafada gami da buga cinya!

 

Tace "bani ledar hannunka ,tafada kamar wata Uwarsa!

 

 

Abin yabawa Tanko mamaki ,da yake tanko ba ya son raini ko kadan yace"bazan baki ba Lantana ranki zai yi mummunan baci idan baki kauce kin bani hanya ba"

 

 

Ta buga cinya! Cikin rashin mutumci da rashin kunya tace "bacin rai Na yaushe kuma ,Tanko kajima baka bata min ba,har kaje ka daura Aure batare da sanina ba sabida tsabar muna furci da Annamimanci kuma karasa wazaka Aura sai mayya kuma karuwa wacce ba'san daga in da take ba"

To sai dai kazaba ko ni ko ita ihee!!!!

 

 

 

 

 

Wani bacin rai ne ya turnike Tanko ,wai shi Lantana take zagi a gaban yaransa da matarsa,kawai sai ya fidda hannu ya tsinka mata mari ,ya hankade ta ,tafadi a gurin ya shige dakin Amaryarshi ya mai da kofa ya rufe gamma!!

 

 

Kuka Lantana ta rusa tana dukan kofar dakin da kafarta gami da zagin suwaibah ta uwa ta uba,makota Na jinta,

 

 

 

Sallau ya taso yana kokarin janye ta daga gurin tana fincikewa tace"sallau kaga yadda Malam ya fasa min hanci jini Na zuba ko"

 

 

 

Da sauri sallau ya lalubi Cocilan din shi da yake yawo da ita a Aljihu yana haska fuskar Mahaifiyar tashi

 

 

Ai kuwa ya sata habo gurin marin gashinan jini yana zuba a hancinta.

 

Da sauri yace"Maman zo kaga n"

 

Maman ya taso a fusace ya karaso gurin.yana dubawa

 

 

Tabbas jini ne yake fita a hancin mahaifiyar tasu,

 

Ganin yadda Maman yake huci yasa Lantana kara lanjarewa tana kuka sabida ta San halin Maman da bakar zuciya!

 

Suka janye ta daga bakin kofar suna rarrashinta ,nan suka yi mata Alkwarin daukar mata fansa a kan Suwaibah tunda duk a dalilinta Malam tanko ya zubar mata da jini ,Abinda bai taba faruwa ba ,

To suma sun dauki Alkwarin sai sun zubarwa da Suwaibah Joni

 

 

*******

 

Tun daga ranar Su Sallau suka matsawa Suwaibah in har suna gidan bata isa ta fito ba sai su hau jifanta ko su sanya mata kafa tafadi ,ko du zuba karkashi kofar dakinta da ta fito tafadi kasa,

Su kuma Na gefe Na faman kyalkyala mata dariya

 

Ko idan tayi girgi ,suje su kwashe su cinye tai magana su zageta

 

Ranar Sallau ya dauki cokali mai ya tsu ya kai mata jifa a goshin ta,bayan ta fito daga ban daki,ai kuwa kan kace kwabo jini ya tsinke sai ta saki butar hannunta,ta dafe gurin tana jin wani mugun zafi

 

 

 

Lantana dake zaune kan kujera "yar tsuguno tana tsintar shinkafa ta kyalkyale da dariya,tace kayi min daidai Sallau!!

 

 

 

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

 

_MARUBUCIYAR_

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

📚📚📚📚

_in kana bukatar cigabanshi ga number nan_

08089965176

[04/05, 03:09] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

 

 

 

*đŸ»Writting by*

_*BINTA UMAR*_

*MAMAN ABDUL WAHABU*

 

 

_BISSIMILLAHI RAHAMANIR RAHIM_

 

 

*🅿14*

 

 

 

Suwibah ta dago kai tana kallon Sallau ,dake tsaye , zuba mata ido yana jiran ta tanka masa ,yayi mata wankin babban bargo!

Tafi minti biyar tana kallonshi ta gaza furta ko kalma daya,sabida tana tunin yin magana ,a yadda suke su kadai a gidan zasu iya yi mata duka,

 

Sai kawai ta wuce shi ta nufi dakinta jini Na diga a goshinta,

 

Suka kwashe da dariya suna nuna ta da hannu Lantana kamar ta tuntsira kasa Dan dariya

Tace "in kin sa kiyi magana mana"

Maman yace"wallahi Na dauka ma ramawa zatayi da naga tana kallonka.

Sallau ya zabura! Yace ta rama? Lallai da ta tarowa kanta Masifa tana cikin gidan Uban nawa"

 

Lantana tace "duk Ku rabu da ita a kwai Abinda zamu kulla mata idan an kwana biya"

"Zo kaji" tafada tana yafito sallau da hannunta

 

 

Rada tayi masa wacce ko Maman dake gurin a zaune bai jiba.

Su LA fashe da dariya murya kasa kasa ,Sallau yace"gaskiya Lantana dole a Sara miki'

Lantana tace ba dole ba! ai ni duk Wanda yaci tuwo miya ya sha dani

 

Ko da Malam tanko ya dawo yaga  goshin suwaibah a fashe yayi tambayar duniya yaya haka tafaru taqi fada masa,sai ya rabu da ita kawai ya samo mata magani ,ta sha ta kwanta nan da nan bacci ya dauke ta,kwananan tana yawan yin bacci tarasa meye dalili.

 

 

*****

 

To haka rayuwa tai ta tafiya har cikin suwaibah ya fito ,lantana ta daga hankalinta,sosai Amma da ta tuno Abinda suka shiryawa cikn ita da sallau sai hankalinta ya kwanta.

 

 

Cikin suwaibah Na da wata tara tana dab da haihuwa ko yau ko gobe, ta fito zata ban daki ,da kyar take taka kasa sabida tsabar nauyin da cikin yayi mata bayan haka kuma Mararta Na mata ciwo

 

 

Ta juya baya tana jawo ruwa a rijiya Sallau ya fito daga dakin mahaifiyarsa ya hankade ta ,tayi taga taga zata Afka cikin rijiyar tayi saurin dafa bango ,Amma INA!! Santsin gurin ya kwashe tafadi ,gurin  rigijff!!

Cikinta ya bugu da murfin rijiyar dake jin gine jikin bango Duk yayi tsatsa ,dalili kenan da yasa yaqi zama a rijiyar shine Lantana ta jin gine shi gurin

 

 

Suwaibah ta kwala ka!! Tana fadin wayyo Allah cikina

*innaliliahi wa inna ilaiyi rajiun*

Lantana tafito a suk wane tana fadin "ke lafiya ne kike yi mana ihu?

 

Sai taga nta zube bakin rijya gurin wanke wankensu,

 

Cikin zuciyarta tace Sallau ya cika ai ki kenan

 

Suwaiba ta dinga daga mata hannu Alamar ta temake ta,

Tabe baki lantana tayi "tace Abinda ya dame ki kenan ,nima lokacin da nake haihuwa babu wacce take te makamin ,sabida haka kije can ki karata,ta koma cikin dakinta,tana waqe waqe.

 

Sallau ma ficewa yayi daga gidan babu Abinda ya dame shi.

 

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

 

_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMIBIYA BALARABA*

📚📚📚📚

_in kana bukatar ci gabanshi ga number  nan_

08089965176

[04/05, 03:09] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

 

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

 

 

 

*đŸ»Written by*

_*BINTA UMAR*_

*MAMAN ABDUL WAHABU*

 

 

 

 

_MALUKAL MULKI ZULJALALI WAL IKIRAM_

 

 

 

*🅿15*

 

 

 

 

Suwaibah ta ruqe cikin ta tana fidda numfashi Sama Sama ,sai ko karin tashi take yi a gurin ta kasa ,sai kawai ta koma ta kwanta tana salati gami da Addu'oi tana fatan idan mutuwarta ce tazo to Allah yasa ta cika da Kalmar shahada.

 

Murqususu take tana jin wani mugun ciwon Mara kwankwason ta tamkar ya balle daga jikinta,tun tana iya yin Addu'ar afili har ta gazayi ta dawo yi a zuciyarta

 

Lantana tafito daga dakinta hannunta riqe da bota da Alama ban daki zata shiga,

Sai taga Suwaibah kwance a bakin rariyar Bandaki kamar ma bata numfashi,

Wani farin ciki ya kamata ,ta karaso gurin ta daki cikin Suwaibah da kafar ta tana dariya ,tace" shegiya "Yar mutsiyata "yar dadi miji ,yanzu shi malam din ai sai yazo ya karbar miki haihuwar ,shida ya dirka miki cikin,in sha Allahu dake da duk Dan da zaki Haifa sai kun muto kowa ya huta da jaraba"

   Tafada tana kara dukan cikin a karo Na biyu ganin suwaibah bata motsa bah.

 

Nan ma shiru

 

Sai ta daga botar dake hannunta ta kwara mata ruwan ciki.

 

Suwaibah tasaki Ajiyar zuciya Wanda yayi dai dai da tsinkewar jini ,a jikinta kwarara yafara bin rariya

 

Gaban Lantana ya fadi ,ganin yadda jini yabi bin makwarara tamkar Wanda a ka kwance famfo ,tayi sauri ta tsallake Suwaibah ta shiga bandaki tayi uzirinta ,tafito da sauri ta shige dakinta ,tabar Suwaibah ,Akwan ce Rai a hannun Allah.

 

 

Atika ta shigo gidan Cikin Sallama ita ma da nata tsohun cikin,dama tare suke jerawa ,kusan kullum ta kanzo gidansu gurin suwaibah ,si ta hirarrakinsu duk a kan Haihuwa, Lantana tai tajin haushi tana zubarmusu da habaici,basa kulata

 

 

*innalilahi wa'ina ilaihi rajiun*!!

 

Shine Abinda Atika tafada ta yi kan suwaibah tana kokarin tashin ta ,Amma ina!!ina takasa sakamokon yadda jikin Suwaibah ya shika bubu kwari wuya ya langwabe,

Bakinta a bushe tace"Atika mutuwa zanyi ki cewa babanku ya gafarce ni bani da rabon kumawa ga Dan gina  ,Dan Allah duk Abinda Na haifa ki riqe min shi a hannunki Na baki Amanarshi

 

 

Atika ta fashe da kuka tace"bazaki mutu ba in sha Allahu zaki goya danki da hannuki"

 

Suwaibah ta rimtse ido tana cije baki! Cikin Wahala jin wani Abu da yake kokarin dannowa ta kasanta ,ta riqa sakin Nushi a galabaice!!

 

Atika ta kwantar da ita a gurun ta mike cikin zafin Nama tayi dakin Lantana da Sauri.

 

Tana zaune kan tabarma da mifici a hannunta ,ta ware wakokin bar mana coge cikin redion ta sai ji take cike da Nishadi tana bin wakar cikin kwarewa ,tamkar ita ce ta rerata.

 

 

Atika taga labule fuskarta jike da ruwan hawaye Ciki tashin Hankali tace"Lantana ki kawo temako Dan girman Allah,ga suwaibah can zata haihu jini yana kwarara a jikinta"

 

 

 

Lantana  tayi mata kwallon banza tace"ke Fice min A daki munafukar banza da wofi ni ce nai Mata cikin zaki zo kice in temaka mata kowa ai da haka ya haihu,lokacin da nake haihuwa Uwarki! Ta taya ni ne"?

 

 

Da sauri Atika ta fita daga dakin tana Mamakin Rashin Imanin Lantana

 

Ta yi hanyar waje da sauri domin taje ta kira Gwaggo Shattu matar Liman,

 

 

Ita ko Lantana tana jin ficeawr Atika daga gidan ,sai ta mike ta je ta daga labulenta tana keqen Suwaibah a kwance har yanzu batasan Wanda ke kanta ba

 

Taja tsaki!! Ta saki labulen ta har da sake gyarashi sosai ta zauna ta cigaba da jin wakokinta,babu Abinda ya dameta.

 

 

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

 

_MARUBUCIYAR_

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

📚📚📚📚

08089965176

[04/05, 03:10] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

 

 

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

 

 

 

*đŸ»writting by*

*BINTA UMAR*

_MAMAN ABDUL WAHABU_

 

 

 

_*ZAMANI WRTES ASSOCIATON*_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

 

_*ALLAH KAI MANA MAGANIN ABINDA YA DAME MU  ,MUGUN JI DA MUGUN GANI ALLAH KA TSARE MU*_

 

 

 

*🅿16*

 

 

_Bissimillahi_

 

 

 

Gwaggo shatu da Atika suka shigo cikin tashin hankali, Haryanzu suwaibah Na kwance bakin rariya, jini Na fita ta kasanta, Numfashinta sai kaiwa yake yana kawowa,tana ganin zuwan gwago shatu ,ta daga mata hannu tana motsa bakinta,da sauri Gwaggo ta karasa gurin da take kwance ta dago,sosai tana nanata innaliliahi a fili tace"Atika maza zo ki kama min ita mu shiga daki haihu zatai yanzu,

 

 

Atika tazo suka kama suwaiba suka shiga da'ita dakinta sai nishi! Take cikin garari da Tsabar wahala ga kan da yafito ya Amma tsabar galabaita ya hanshi yunkurin fitowa ,ita ma Suwaiba duk wani qarfinta ya kare nishin wahala kawai take,

 

 

Lantana Na dakinta sake da labule tana jin wake-waken ta babu Abinda ya dame ta

 

 

 

Gwaggo tace"Atika jeki karbo Rubutun gurin Malam Nasan yanzu ya gama"

 

 

Atika Na kuka ta fita daga dakin tana tausawa Suwaibah ganin yadda take shan wuya ,tace dama haka mata suke wahala gurin haihuwa, ita sai tafara jin tsoran ranar da tata zata zo

 

 

Ta Na fita suka ci karo da Sallau ya shigo gidan ,saura kadan ya buge ta ta kauce,

Sallau ya ja ya tsaya yana dura mata Ashar!! Yace"ni ba wanki bane da bazaki gaishe ni ba"

 

 

Tace"Sallau suwaibah babu Lafiya zata haihu kaje ka kira babanmu"

 

 

Dariya Sallau ya fashe dashi cikin mugunta yace "Allah yasa ta mutu in dai sai naje Na kirashi ne ai kema kinsan gurin Aikinshi kije ki kirashi,mana"

Yayi wucewarsa ciki ya barta tsaye,

 

Sai ta fita da sauri tana share hawaye tana tur! Da Bakin Hali irin Na lantana da yaranta,

 

 

 

Tuni Malam ya kammala rubutun Na kuda ya fito da kanshi ,ganin yara zasu bata masa lokaci,sai ya hangi Lantana ya tsaya ta karaso,ta gaishe shi,yasan Rubutun zata karba sai ya mika mata yace maza a je bata in sha Allahu zata sauka lafiya"

 

Atika ta kar6i rubutun ta Na godiya,har ta joya zata tafi sai ta tsaya ta ce"Malam Babanmu yana gurin Aiki bai San halin da ake ciki ba"

 

 

"Ashsha""! Malam yafada yana jinjina Kai yace"yanzo zan tashi yara suje su fada masa ko in je da kai na,kedai maza jeki kai rubutun"

 

 

Da sauri Atika tatafi tana taiwa Suwaibah Addu'a Allah ya sauke ta Lafiya

 

 

 

Gwaggo shattu sai gumi take sharbawa ganin duk iya bakin kokarinta tayi Akan Suwaiba tayi wani yunkuri!! Ko yaron ya fado Ta kasayi Asabili da qarfinta ya kare, ita dai tana kwance Batasan wace duniyar take ba,sosai Gwaggo ta firgita,ganin yadda jini yake fita har yanzu gashi ba a haihuba,tabbas fitar jini ga mace mai naquda hadari ne,ba'aso Anfison in mace ta haihu sai jinin ya fita,duk da a lokacin da qaracin wayewar kai,Gwaggo shatu ta fahimci Suwaibah tana cikin hadari ba karami ba shiyasa ta tsinke da Almarin ,sai addu'oi take tofa mata,ta mike ta fita domin baza ta iya aikin ita daya ba,tanajin tsoran fita taje ta kira unguwar zoma, Sai ta daga labulen dakin Lantana,

 

 

Lantana ta rage Karfin Redion ta ,tana mata wani kallo gami da ya mutse fuska

 

 

 

"Lantana kiji tsoran Allah kiji tsoran ranar kumawarki ga Allah ,Lantana meye duniya,kishiyarki Na naquda kika bari har ta gala baita batare da kin je kin sanar ba duk Wanda yayi nagari kanshi"

 

 

 

Lantana ta harziqa!! Tace"kinga shattu banason kinibibi kunsan Yarinyar baza ta iya haihuwa da kanta ba kuka kulla mata Aure duk domin ku bata min rai!, to Ta Allah ba taku ba,Sai kije ki nemi Wanda yayi mata cikin yazo ya karbi haihuwar Amman ni karki kuma saka ni a lamarin Ehee!!!!

 

Sallau dake gefe yana cin wake da shinkafa cikin Langa,ya fashe da dariya,jin Abinda Uwartasa tace wai aje a nemi Wanda yayi mata cikin yace "in banda Abin baba Mu kadai mun isheshi "yayan Asali ba sai yaje ya hada jininshi da bara gurbi ba"

 

Lantana tace"ai Abinda Akeso ya gane kenan yaqi yagane sabida muna fukai sun zigashi"

 

 

 

Sallamar Atika ce ta sa Gwaggo shattu bata tanka musu ba sai tasaki labulen dakin da sauri ta karbi rubutun hannun Atika,suna rige-rigen shiga dakin Suwaiba

 

 

 

Abin Mamaki jinjiri ne kwance cikin jini yana motsi Igiyar cibiya ta sarqe masa wuya,ga shi mahaifar bata fado ba

 

 

Da sauri Shattu taje ta dauke shi gami da since masa zaran cibiyar ta sanya reza ta yanke gami da daurewa,tana tai wai Allah tasbihi,ta mika wa Atika yaron ,taje tadago Suwaiba tana kokarin bata rubutun domin asamu mabiya ta fado sai taga Suwaibah ta koma Sharaf! Ta kwanta ,Rai yayi Halinshi!!

 

 

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

 

 

_MARUBUCIYAR_

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

📚📚📚

08089965176

[04/05, 03:13] +234 808 996 5176: 🧝🧝🧝🧝🧝🧝

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

🧝🧝🧝🧝🧝🧝

 

 

 

 

*đŸ»Writting by*

_Binta Umar_

*Maman Abdul Wahabu*

 

 

_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION*_đŸ€đŸ»

 

 

*🅿17*

 

 

_Bissimillahi_

 

 

*inalillahi Wa inna ilaiyi rajiun!*

 

Shine Abinda Gwaggo Shatu take Fada, Jikin sai rawa yake yi ta kalli ,Atika dake tsaye a gurin gabanta yana Faduwa! Tace "Suwaibah ta rigamu gidan gaskiy...

Kafin ta karasa Malam Tanko ya daga Labulen Dakin cikin tashin hankali,

Ya ga Suwaiba Kwance a kasa lullube da Zani ,da Sauri ya dauke Zani yana kiran Sunanta,Gwaggo Shatu ta fashe da Kuka! Tace"Malam Suwaiba Babu Allah ya raba ganawa"

 

*Innalillahi Wa'ina ilaihi rajiun*

 

 

Malam Tanko ya fada Bakinshi sai rawa yake yi Da Sauri ya Fita daga dakin ya tsaya kofar Dakin Lantana,Daga Waje yace"Lantana ki fito ,Suwaibah Allah ya karbi Abinshi, Burinki ya cika"

Yana gama Maganar Yayi waje Cikin Zafin Nama,Bakinshi dauke da Addu'oi Ga Suwaiba Matar Arziqi

 

 

Da Sauri Lantana ta bankada Labule,ta fito kamar gaske ta tsaya tsakar gidan Tafashe da ihu! "Wayyo Mun shiga Uku! Ihu! Take Sosai Sai kace Mahaukaciya ,Cikin Ziciyarta Sai murna take

 

Nan Makota suka dinga Shigowa Cikin tashin Hankali ,Masu kuka nayi masu salati nayi ,kar dai Lantana taji Labari

 

 

Malam Suka shi go dashi da Liman da Sauran dattawan Unguwa,

 

A ka sutturce Suwaiba a ka kai ta gidanta Na gaskiya, Sosai mutuwar ta ta ba zuqatan Mutane banda Lantana da yaran ta

 

 

 

Bakin ciki Kamar yakashe Lantana Lokacin da ta Fahimci Da Namiji Suwaibah ta haifa,suka riqa tsara yadda zasu kashe jinjirin ita dasu Sallau,Fahimtar Hakan yasa Malam Tanko ,daukar jinjirin Bayan kwana ba kwai ya Miqashi ga Gwaggo Shattu ,yace ya bata Amana

 

Gwaggo tace ta karba Allah ya tayata riqo ,A lokanci A kwai qan warta da take Shayarwa sai ta bata,Jaririn Wanda yaci Sunan Ayuba,da zumar in ta yayashi Sai ya dawo Hannuta,

 

 

 

Lantana taji ciwon Abinda Malam Tanko yayi ,nan ta Sanyashi a gaba ta rika cin mutumcinsa bai ce Mata komai ba

 

 

To A taikaice dai rikon Ayuba ya dawo Hannu Gwaggo Shatu yana da Shekara Uku ,Sharasa Bakwai a duniya Allah ya dauki Ran Malam Tanko Sakamakon Rashin Lafiya tafarar daya,

 

Ayuba ya shaqu da Mahaifinshi Sosai Shiyasa Yaji Dacin Mutuwarsa,inda Kiyyaya da tsana gami da tsangwama,ce Tsakaninsa da "Yan Uwansa don ko da  a kazo rabon Gado Sallau da Lantana ,Cewa Sukayi Ayuba Bashi da gadon Ubansu Domin Ba Dan Halak! Bane ,Sai da Malam Liman ya tsaya tsayin Daka A kan Lamarin Sannan A ka fitarwa da Ayuba gadonsa a gidan Ubansa.

Duk Rayuwarshi gidan Liman yake yin ta ,inda ya kasance *Yaro* mai zafin Nema,a wancan lokacin duk Abinda ya ta6a sai ya zama kudi.

 

Sallau ya sakoshi a gaba Da bakin ciki da hassada ,duk inda yasan yana zuwa Nemansa sai ya je ya batashi.

[04/05, 03:14] +234 808 996 5176: đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»

 

 

*đŸ»Writting by*

_Binta Umar_

*MAMAN ABDUL WAHABU*

 

_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION*_đŸ€đŸ»

 

*🅿18*

 

_Bissimillahi_

 

 

 

A lokacin Sallau yayi Aure inda ya Auri "Yar yayar  Lantana Mai Suna Fatsima suna kiranta da (Uwa!) Yarinya ce Mara kunya inda bata ganin girman kowa ,babba da Yaro ,Har Mahaifiyarta fito Na fito take da ita,Bata da Aiki sai yawon tallace Tallace to har a kayi Auran Uwa Na fita kofar gida ta dasa kasko Na suyar Awara gefe ga gyada nan cikin Faratin A quq-qulle a leda marau da tubes! Haka take Tara matasa ai ta shirme ,idan har kan dillanci tazo nan ma tana tabawa

A takaice ita ce take ciyar da Sallau domin shi ya zauna zuciyarsa A mace yaqi ya fita ya nema ,Gwara Maman shi ya kan fita yayi buge bugensa ya samu Na kashewa,ita ko Lantana Kasuwanni take bi tana tallan zogale da kuli ,Da wannan suke Samun Abinda zasu kai bakinsu.

 

To shiyasa daga Lantana Har Sallau! Suka taso Ayuba a gaba da kyashi gami da hassada,Wanda hausawa sukance (Hassada ga mai rabo taki ce)

 

Ayuba ya shaku da "Yar Uwarshi Atika ,domin duk wani Sirrin shi tasani ita da Gwaggo Shatu marikiyar shi ,

 

Haka ya cigaba da Rayuwa ,tare da Kiyyaya da tsangwama gurin "Yan Uwanshi,Amma duk da Haka shi bai fasa Zumunci da su ba,

 

 

 

Hafsatu ita ce Ayuba ya Amince da tazama Uwar "Yayanshi, Domin ya yaba da tarbiyar ta gami da nutsuwa da kamun kai,"Yar Makotan Su Atika ce Yayarshi Ita ma haifinta ya rasu,to haka dai Malam Liman ya tsaya Masa tsayin daka ganin Tabbatuwar Auran

 

Nan ta tare gidansu ,Bangaran shi Na gado,Uwa da Lantana suka ce dawa Allah ya hadasu,suka sanya ta a gaba Babu irin Muguntar da basai Mata,yarinyar duk ta kwar zane,kullum cikin Aikin Awarar Uwa take tamkar ita take Auranta,inda Allah ya tai maketa ma ,Lantana,bata yini a gida Sai Yamma take dawowa daga zarar ta dawo ,zatai ta kwala Mata kira tana zagi! Tai ta sanya ta Aikin Wahala ,ko da ta Samu ciki basu bar ta ta huta ba, Kullum idan Ayuba ya shi go gidan yaga irin wahalar da take sha,sai bakin ciki ya kamashi gashi bashi da Bakin Magana,Lantana ta tsigale shi, Kullum in sun shiga daki yai ta Rarrashin ta yace"tayi hakuri Shima ba yason Wannan Wahalar da take sha Da yana da Hali da sai ya kama mata Haya ko daki guda ne,to Babu Hali domin duk wasu hanyoyin Samunsa Sallau ya shiga ya fita ,ya rabashi dasu da Asiri da kuma Ziga ga Mutane ,cewar kar Wanda ta hada hurda dashi domin ko ba Dan gari ba ne,Zai cuce su ya gudu

 

To Lokacin A kwai qarancin Ilimi gami da Wayewa Sai Jama'a suka dinga gudun Ayuba,

Tunda ga Lokacin ya dai na sana'a sai dai ya fita tayi buge bugensa ya dawo gida

 

A lokacin Uwa! Tana da Yara Biyu Namiji da Mace'Iro da Shamsiyya, To iro tun yana shekara Uku ya iya yawon Talla kusfa kusfa,haka zata kasa masa a faran ti tun Safe ,ba bu Maganar zuwa makaranta

Haka ake Zaman doya da Manja a gidan Domin Maman ma ya yi Aure shima Matarshi Na gidan , Mai suna Halima inda ta kasance mace mai sauqi hali gami da Hankali ,kwata kwata bata kaunar Abinda Su Lantana sukewa Hafsatu Matar Ayuba ,sai ta riqa Jan ta a jiki tana tausar ta,nan ko Uwa!! Tace dawa Allah ya hada su ,shiga fita Dari sai ta Zubda musu Ha baici ta dauki gaba da Halima ,duk dai a kan tana kula Hafsatu,ita ko Lantana dama Macace mai mugun kwadayi kasan cewar Maman duk ya fisu Samu yasa bata son Laifin sa ko Na Matarshi shiyasa ta kyale ta take Kula Hafsatun Dan kar ta dai Na bata Abinci da kayan dadi in Maman ya siyo Domin ,shi kwata kwata ya Manta da wata Lantana ta Matarshi yake,in Anyi Magana yace ai tana fita Nema taci da Kan ta,shima yanzu Nauyi yayi masa yawa.

 

*Allah ka azirtamu da "Yaya masu Albarka ,duk Dan da zai zame mana fitina a rayuwarmu Allah kar ka bamu,Allah ka sa mufi qarfin zuciyoyinmu*

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

_MARUBUCIYAR_

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

08089965176

[04/05, 03:14] +234 808 996 5176: đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»

*đŸŸGIMBIYA BALARABAđŸŸ*

đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»

 

 

 

*đŸ»Writing by*

_Binta Umar_

*MAMAN ABDUL WAHABU*

 

 

_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION*_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

*🅿19*

 

 

 

_Bissimillahi_

 

 

 

Cikin Hafsatu ya isa Haihuwa , Halima Matar ,Maman ce ta tsaya Mata a gidan Lokacin Gwaggo Shatu babu Lafiya Abinka da jikin girma, Iya" Atika ita ce ta karbi Haihuwar ,su Lokacin Domin Lantana ta tafi tallanta Hakanan Uwa! Na waje tana Soyar Awara Tamkar ba matan Aure ba

Cikin ikon Allah ta haifi diyar ta Mace Sak! Mahaifinta Kamar an tsaga kara dashi Fara tas!! Ga hanci har baka, Ayuba ya ruqa Murna ,A take yayi wa jaririya huduba da Sunan Mahaifiyarshi, wato Suwaibah ,sai ya ke ce Mata Balaraba kasancewar An haifeta ranar Laraba

 

Ko da Lantana ta dawo taga jaririya tace ,Haushi Kamar ya kashe ta ganin Baiwa da kyau da Allah yayi mata ga Hafsatu Lafiya lau,ita San samun ta Hafsatun ta mutu kamar yadda Suwaibah ma ta Mutu , A ranar kwana tayi tana zage-zage Kamar ba tsohuwa ba,

 

Ita ko Uwa!! Tsabar kyashi bai bar ta ba ma ballan ta ta shi go ta ga Abinda Hafsatu ta Haifa ,ta dai tura Iro gulma! Domin yaje ya gano mata ,Aiko Yaron ya dawo Yana Fada mata kyawun "Yar jinjinyar ,Bakin ciki kamar ya kasheta,ta waiwaya ta kalli Yarinyar ta Shamsiyya,a zaune ,duqun duqun!! Daga ita sai karamin ,Wando ga Wani Uban zarni! Da take yi,Yarinyar Baqa ce Sosai gashi Mummuna Dan Har Iro yafi ta kyau tunda shi ya Dan dauko kammanin Mahaifinshi,ito ko Shamsiyya Kamarsu daya da Uwarta!

 

Nan taci Alwashin Sake Haihuwa ,Domin tana Zaune Wata baza tazo tafi ta "Yaya a gidan Ba, kuma in sha Allah ita ma sai ta haifi Fari ,sabida Sallau yana da Haske dai-dai gwargwado

 

*Ni ko nace kuji ni da Uwa! Da tsabar jahilci don Allah*đŸ€Ł

 

 

Har a kayi Suna Uwa! Da Lantana basu leqa sun ga Abinda a ka Haifa ba,Balle  Sallau" Wanda ya tsiri gaba! Da Ayuba babu gaira babu dalili ganin yadda yayi komai Na Haihuwa ,Hatta hakika, biyu ya yankawa Maijego,shine yake Bakin ciki ,yana tunanin a ina ya samu kudin da yayi wannan Hidimar

****

Kafin Hafsatu tayi Ar'ba'in Uwa! Ta samu Ciki sai tun qaho take tana hora hanci  ita zata haihu ,Shiga Dari fita Dari sai ta yadda Habaici tamkar Wacce bata taba Haihuwa ba ,Ita ko Hafsatu bata ce Mata komai ,in tagama Ai kace Aikacen ta ,sai ta tafi bangaran  ,Suyi zamansu Har Magari ba

 

 

*Balaraba* ta saba da Halima Sosai in Kusan Kullum tana Hannunta ,in ko bata gurinta tana can gidan ,Iya Atika, Haka jama'a suke Kaunar ta daga An fita da ita kowa son ta dauke ta yake,Sabida farin jinin ta, Uwa! Ko babu shiri ta bazama, Gurin Malamai a kan Yarinyar ,Wai a Sanya Mata Bakin jini a ida nun Jama'a kuma a saka Ta ta fandare ta zama ga gararriya, Malamin nata yaga Tsubbu bace Tsubbacan Sa ya yi Mata Baya nin Yadda zata yi da kayan Aikin da ya bata Mutukar ta kuskure to babu Makawa "Yayanta zasu Lalace domin Aikin kansu Zai kuma,

 

 

Haka ta dawo gida tana Haki ga tsohon Ciki a jikinta, Sai da ta bari dare yayi Sosai kowa ya shige dakinshi ,sannan ta Fito ta daga Manyan dutsinan da suke girgi dashi ta tona Gurin da Wuqa yayi zurfi Sosai ,sannan ta saka Wasu Manya Manyan Layu! Guda biyu ,tayi Sauri ta Mayar da kasar gurin ta Binne ,sannan ta Dora dotsen a kai.

 

Ashe tayi shuka a idon Makwarwa Domin dai tun lokacin da tafito ,Halima ta ganta ita ma ta ta shine domin  Zuwa ban daki  har ta fito sai ta  Ja da baya ,ta labe jikin kofar ta ganin  Uwa!! A Gurfa ne a gaban Murhu ta dage tana To na wa.

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

 

_MARUBUCIYAR_

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

08089965176

[04/05, 03:14] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

 

đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»

 

 

*đŸ»Writting by*

_Binta Umar_

*Maman Abdul Wahabu*

 

 

 

_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION*_

 

 

 

*🅿20*

 

 

 

_Bissimillahi_

 

 

 

Uwa! Na gama binne Layun ta Mike ,tana karkade jikinta sai wai ge wai ge take Na rashin Gaskiya, tayi Sauri ta shige dakin ta

 

 

Ita ko Halima sai ta bari ta dai najin Motsin Uwa! Daga dakin ta,Sannan ta fito a hankali,ta aje botar hannunta gefe ,ta Dauke katon dutsen ,sannan ta sa Wuqa tafara tone Abinda Uwa ta Binne! A gurin

Can ta tonu Layu  daure jikin Wani Jan yanki, tayi Bissilimih gami da sanya Hannunta ta dauke ta aje gefe ,ta fara mai da kasar gurun tana Rufewa,Tsaf ta Gyara gurin ,ta mike tana Addu'oi ta dauki Layun ,ta je ta aje a gurin ta,Sannan ta dawo tayi Uzirin ta dama Abinda ya tashe ta kenan,

Jin Motsin bude kofar ban daki ne yasa Uwa futowa da Sauri ,Tana kallon Bakin Murhu,Ajiyar Zuciya ta Sauke ganin Babu Abinda ya faru yadda ta bar gurin haka yake, Kallon- kallo sukayi ita da Halima,Sai ta buga tsaki ,ta joya ta shige dakin ta ban ko kofa!

 

 

Girgiza kai! Halima tayi kawai,tana Mamakin Zuciyar Uwa Tamkar ta kafurai, A fili tace Allah ya shirye ki Uwa!"

 

Ta shige dakin ta ita ma

 

 

Safiya nayi Uwa! Ta fito ta aza tukunyar Awara ,A wuta ta dinga Hura huta Sosai sabida Malam yace Mata ,In ta binne layun ta saka Wuta sosai a gurin yadda Aikin zai fi saurin kamawa, Ai kuwa haka tayi sai Faman Saka ice take, duk a kokarin ta Na taga *Balaraba* ta lalace,

*Allah ka sa muda ce*

 

Can Bangaran Halima kuwa ,babu Wanda ta fadawa Abinda ya faru ,kawai Safiya nayi ta boye Layun Cikin Hijab din ta ,ta fita daga gidan,kai tsaye gidansu ta nufa,dama kusa ne,ta sanya kannenta ,suka kwance Layun ,tare da yi musu futsari Sannan tace ,su jefa a Masai!

 

Ai kuwa haka yaran sukayi Abinda ta Umar cesu, Nan ta rarraba musu Goma-Goma suka tafi suna Murna,

 

Maihaifiyar ta take Tambayar ta Mai nene"?

 

Nan ta warware mata komai

 

Tace "Gaskiya Uwa! Bata da imani Wallahi narasa Abunda Hafsatu ta tsare mata,Bai wuce ita tayiwa Asiri ba"

 

 

Halima tace"Tabbas ita za tayi wa ,in sha Allahu sai dai sharrin ta ya bi ta,tunda ita ba ta nufe ta da shi ba,

 

*****

 

Wannan Shine sanadiyar Lalacewar Iro ,Uwa!Na zuba Ido taji an ce Balaraba tafara sace-sace sai Hakan tafaru kan Dan ta Iro, Kwatsam! Suna Zaune daf da Magariba dukkaninsu a tsakar gida har Lantana ,ta dawo daga yawon Tallanta, Tafito da ciniki tana lissafawa Sallau! Ma shigowar sa kenan ,yana gyara tsayuwar Kekensa, Ita Kuma Tana Aikin Awara Wacce Shamsiyya take Zama gidin bishiya tana Soyawa da daddare,

 

 

Kawai! Suka ji ihu! Ana barawo barawo Kafin suyi Wani yunkuri! Iro yafado gidan Yana Haki! Gashi sai Warin ganye! Yake yi,idonshi yayi ja,da gudu ya shiga dakin Lantana ya kulle ,

 

Matasa ne suka shi go sun kai su goma ko wannesu riqe da Abin duka! Suka Zagin Iro ! Wai sai ya fito sun dake shi,

 

Lantana ta Mike a zabure! Tana gyara daurin Zaninta bayan ta Kwashe kananun kudinta da ta baza a kasa tana qirgawa ta boye cikin ,Wani burgujejen Sket din ta Mai Aljihuna,Wanda take sanyashi a ciki kafin ta daura Zani, takarasa In da suke tsaye Suna Hayaniya! Sallau Sai Rarrashin su yake Sabida ,dama shi tuntuni yaji Labarin Abinda Dan shi yake Aikatawa.

 

Tace"Ku tsinannu! "Yayan Mutsiya ta, Mai jika Na yayi muku ,kuka biyo shi da Abin duka sai kace ,Wanda kuka kama shi da kayan Wani!

 

 

Daya daga cikinsu, Yace "ke! Tsohuwa Kar ki rainawa mutane Hankali mana! Eh! A kwai tsinanne irin Iro! barawo Mai kwatar Wayoyin Mutane, Kinga Wannan Yaron ya fizgewa Waya,yanzu An ai keshi ya kai chaji ,Sabida haka kushiga Ku fito dashi ,Billahillazi Ku mu balla kofar! Mu Saba masa Kammani,dama ya ishe mu da Sace-Sace' A Unguwa babu dama a Aiki Yara da kudi ,sai ya kwace.

*BINTA UMAR ABBALE*

 

 

_MARUBUCIYAR_

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

08089965176

[04/05, 03:15] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

 

đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

 

 

*đŸ»Writting By*

_Binta Umar_

*MAMAN ABDUL WAHABU*

 

 

_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION*_

 

 

 

 

*🅿21*

 

 

 

"Sai dai idan kune barayi To kaji"! Lantana tafadi Maganar Kamar zata kaiwa Yaron Duka! Taci gaba da Cewa  "Nasan Halin jikana baya Sata ,haka Kawai zaku kala Masa Sharri, Mutsiya ta"

Wani Yaro Da suke kira Umaruru Dan zafin Kai Ne ,Sosai Bai Saurari Kowa ba Yayi Hanyar Dakin da yake Hango iro tun dazu yana Leqo da kai ta taga, Ya daki Kofar dakin da kafarshi daya,ta bude wai sunan an San ya Mata Sakata , Ya kamo Iro suka fito ,Yana turjewa, Nan Mata San suka yo kansa ko wanne da Abin duka ,suka fara jibgarshi suna Tambayar inda ya kai Wayar da ya kwace

 

Nan Uwa! Tafa sa ihu! Tayi kan su Tana tutturesu Wai kar su kashe Mata da! Su fadi ko nawa ne kudin Wayar Zata biya su

 

Lantana ta rika dura Musu Ashar tana bangaje su Lallai sai ta shiga tsakiya ta Hanasu dukan iro

 

 

Umaruru ya Sanya Hannu daya ta ture ta tafadi a gurin ,Amma duk da Haka bata dai Na Zaginsu ba gami da Yi Musu mugun Baki

 

 

Shi ko Sallau Shiru yayi yana kallonsu yana tsaye jikin bango yasan ko yace Suyi Hakuri ba za su hakura ba ,Sabida yasan Dama sun Dade sunaso su kama iron, Shi tsoro yake Ma kar su hada dashi,

 

Halima da Hafsatu suka fito suna rokarsu suyi hakuri ,Amma Ina!! Sam sun ki hakura sai dukanshi suke Suna Tambayar inda ya kai Wayar Mutane, Amma Yaki Magana Sabida tsabar Taurin Kai!!

Makota cike da gidan suna Kallon ikon Allah ,dayawa daga cikinsu cewa suke Alhakin Hafsatu ne ya fara kama Uwa!

 

 

Uwa! Ko Na can tana zagi Sallau Cikin Rashin kunya tace"So lubiyo Namijin hotiho ,kana tsaye a shigo har gida ana dukan Dan ka ka kasa tabuka komai, kai dai kayi Asara Wallahi

 

 

 

*Balaraba* ce ta shi go gidan Jikinta Sanye da kayan Makarantar Isilamiyya Riga da wando da Hijabi ,Kafadar ta sakale da jakar buhu ,Wacce ta sanya Alkur'ani hade da Sauran Littatafan Addini.

 

 

Da kyar! Ta samu ta Ku tsa cikin Mutane ta isa gurinsu,Hsnkalinta Nakan su Umaruru ,Ganin suna dukan Iro babu Imani gashi kowa yayi shiru,

 

Lantana Ta kalleta ta Watsar Tace"Kunga barauniya nan ita zaku doka Ba iro ba domin ita ke min satar "Yan kudade na idan naje Tallah Na dawo ko tausayi Na,bata ji Sabida tsabar Rashin Imani"

Ta karashe Maganar tana mikewa Tsaye

Dukan ninsu suka joyo suna Kallon *Balaraba* jin Abinda Lantana take fada a kan ta,

 

Hakan yaba Iro da mar tserewa da gudu yayi Waje hanci a fashe yana jini ,ga jikinshi yayi budu budu Rigar da yake sanye da ita ma ta yage! Tsabar Wahala

 

 

Umaruru Yace"

*Balaraba* kin  dawo daga Makarantar"?

 

"Eh Umaruru Balaraba ta fada cikin Nutsuwa

 

 

Umaruru ya Kalli Lantana ,yace" Wallahi kuji tsoran Allah da ranar Lahira tsohuwa ,Ku dinga fadin Alkairi a kan Dan Wani *Balaraba* yarinyar kirki ce,Domin ba 'a taba kamata da kayan Sata b.....

 

Uwa ta katse shi ta hanyar Cewa"Dole kafadi haka mana Munafiki Allah ta Allah ,sabida kana kama ta ka latse a lungu da sako ,Ai mun San duk Abinda yake Faruwa ,Babu Abinda bamu Sani ba" Ehee!!

 

Kuka Mai cin Rai Hafsatu ta fashe dashi ,ta shige dakin ta da gudu,ita ko *Balaraba* Tana tsaye Babu Cikin dakiya idon ta tar! Duk da a lokacin tana da kananun Shekaru ta Gama gane Bata Da babbar Makiyya kamar Uwa!

 

 

 

 

_BINTA UMAR ABBALE_

 

 

*MARUBUCIYAR*

 

 

*NANA KHADIJA*

 

*YARO DA KUDI*

 

*GIMBIYA BALARABA*

08089965176

[04/05, 03:15] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

 

đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»

 

 

 

 

        *by*

_BINTA UMAR_

 

*MAMAN ABDUL WAHABU*

 

 

 

_ZAMANI WRITES ASSOCIATION_

 

 

 

*🅿22*

 

 

 

Uwa!

ta cigaba da cewa "dama duk wannan yawon da take yi da sunan zuwa makaranta ,mun san iskanci take tafiya tunda dama "yar nagada ce ,sabida haka kufadi kudin wayar ku a biya ku domin ana da abin da za'a biya,

Ta karashe maganar cikin kuri! da cika baki,sabida tasan bata da wasu kudi idan ba jarin a wararta ba,

Umaruru mamaki ya cika shi jin abinda uwa take fada,sai ya girgiza kai kawai yana mamakin sharrin wasu matan ,shiyasa a kace ko shedan yana gudun sharrin mace,

Balaraba kuwa tana tsaye babu damuwa a tare da ita domin in da sabo yaci ace tasaba da irin kiyyar da suke nuna ma ita da iyayenta, shiyasa abin baya damunta da yake yarinya ce mai taurin zuciya ,sai dai abin yai ta damun mahaifiyar ta,itama babu abinda take iya yi idan ba kuka ba.

 

 

 

Umaruru ya kalli uwa! dake tsaye tana hura hanci! yace"kudin wayar nan dubu bakwai da dari biyar ne ,sabida haka tilas a biya ,hakan kuma ba ya na nufin cewar in muga iro baza mu damka shi ga hukuma ba,tundadai kowa ya shaida da hakan.

 

 

Sallau yayi saurin tarar sa yana kwantar da kai yace"umaruru kuyi hakuri a kashe magana anan don Allah za muyi masa fada ,in sha Allah bazai kara ba.

 

 

Uwa

Kuwa da taji maganar dubu bakwai gabanta ya yanke ya fadi sabida tasan dudu-du jarin a wararta bai kai na dubu uku ba,kuma dashi take joyawa suna cin abinci sai tafara sake-saken yadda zatayi,

 

 

"Tun yaushe kake fadar haka,cewar zaka ja kunnesa naji labari cewar ai kai yake kawowa kudin kuke rabawa shiyasa kake daure masa gindi

 

Sallau ya gigice sai rantse rantsa yake yace"ni ko kwabo baya bani ban sani ba ko uwarsa yake kawowa gatanan a gabanku ni babu ruwana"

 

Dama umaruru ya fadi maganar ne domin ya tsoratar da shi.

 

 

Cikin uwa! ya duri ruwa sabida tasan idan suka gane tana karbar wani abu daga hannun iro itama ba kyaleta zasuyi ba,

Tayi sauri ta katse sallau dake basu hakuri,cikin rashin kunya tace"dallah malam matsa kabawa mutane guri solobiyo kawai,kai umaruru nawa kace ma kudin wayar,? tafadi maganar sai kace wacce zata iya biya

 

 

"Dubu bakwai dari biyar ne"

 

Ta kalli Lantana wacce tunda zu ta kasa furta ko a sabida taji ana maganar biyan kudin waya, ita kam bata da ko kwabo ba zata bayar ba.

 

 

"Lantana ki fito da kudin nan danaga kina lissafawa a biyasu kudinsu ,tunda dai kema iro yana mora miki kullum da daddare sai kin ce ya siyo miki balangu ko kifi"

 

Lantana tayi tsuru-tsuru tana motsa baki ,da kyar! tace "mai nake dashi "yannan ! da zan bayar so kike na rusa jarina"

 

 

Cikin rashin mutumchi Uwa tace "Lantana dole fa kifito da kudin jikinki ko kinqi ko kinso wallahi domin bazan bari su kashemin da ba,ehee"!!

 

Da kyar! Lantana ta kwance zaninta tana daga zaune ,sai surutai take tafito da "yan ashirin ashirin da "yan goma goma ,kwata kwata a kudin babu hamsin ko daya

 

Uwa tazo ta kwashi kudin da sauri ,tafara lissafawa,

 

*Balaraba ko na tsaye cikinta kamar ya kulle dan dariya sai boye dariyar take dan kar ta fito amma INA! sai da ta subuce mata ta zauna kasan gurin tana yi tana kallon Lantana dake faman share gumi! Sai tsine-tsine take,wai sam bata yadda ba kalawa Iro sata a kayi

 

 

,Aiko Lantana ta dauki wata sanda da suke tone kwatarsu idan ta toshe ta kaiwa Balaraba duka da ita tana faman zaginta ta uwa ta uba.

 

 

Balaraba ta mike da sauri ta shige dakinsu tana jiyo Lantana kamar mahaukaciya tana ta dura mata ashar tamkar ba tsohuwa ba.

 

 

To da kyar! dai Uwa ta samu ta hada dubu uku da dari biyu,domin kudin gun Lantana ko dari biyar basu kai ba,ta mikawa Umaruru gami da cewa"gashinan Abinda ya samu kenan,Shamsiyya bata dawo daga tallaba,kuje kubawa mai wayar hakuri idan an kwana biyu za'a cika masa kudinsa,domin Allah ya hore abin da za'a biya

 

 

Umaruru ya karbi kudin yana lissafawa tsaf!

Yace "kifadi ranar da zaki ciko kudin kawai bama son jeka ka dawo"

 

Tabe baki tayi tace"ku dawo rana ita yau zan Baku kudinku"

 

 

"To Allah ya kaimu kar muzo kice wani abu fa"

 

 

"Mtssss nifa nace kudawo Ku karba ,akin banza akin wofi,Uwa! tafada a zafafe ,bakin cikinta yadda ta rusa jarinta yanzu kafin ya tashi ma aiki ne

 

 

Umaruru yaja ta wagarshi suka fice daga gidan,suna fita Uwa tace dawa Allah ya hada ta duk wanda ya kwana ya tashi a gidan sai taci masa mutumchi kar dai Sallau yaji labari,

Simi-Simi ya kama hanya zai shige daki ,tayi saurin janyo masa riga gar wuyanta ya yage ,tace"kama hanya ka fita ka nemo mana abinda zamu ci ehe! wallahi baza ka shigarmin daki ka zauna min ka kashe min  katifa babu abinda kake min sai dai in nema ,in ci da kai in ci da "yayanka"

 

Bai ce mata komai ba ,ya fizge rigarshi gami da gyara wuyanta in da ta yaga masa,ya sakai ya fice daga gidan babu abinda ya dameshi,can mahadarsu ya nufa,abokanshi na Zane suna ta faman karta! (Caca) nan ya zauna cikinsu a ka fara yi dashi.

 

 

 

 

_ina so Ku fahimci ko wane marubuci da nasa salon,gaskiya ni babu yadda za'ayi in yi rubutu batare da na fadi jogon labari ba ,domin shine ginshin fara karatu, So dan Allah kuyi hakuri kuci gaba da bina a yadda nake za azo in da kuke so_

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

_MARUBUCIYAR_

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

[04/05, 03:17] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

 

 

đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»

*đŸŸGIMBIYA BALARABA*đŸŸ

đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»

 

 

           *By*

_BINTA UMAR_

 

*Maman Abdul Wahabu*

 

 

_ZAMANI WRITES ASSOCIATION_

 

 

 

*🅿23*

 

 

 

_Bissimillahi_

 

 

 

To haka rayuwa take, Ayuba ya yi ta fafutukar naman abinda zai rufawa kanshi,asiri ,yayin da "yan uwanshi suka tasa shi a gaba har sai dai suka ga ya kwanta, ba ya iyayin komai da kanshi sai dai ayi masa,gashi lokacin nauyi yayi masa yawa dalili kuwa yayarshi Atika mijinta ya rasu,sai ta dawo gidan ta zauna dakinsu na gado ita da "yan uwanta ,da suke can garinsu ,suna aure,a lokacin Balaraba na da shekara goma sha uku, sai kanwar ta ,wato sadiya, tana da shekara tara,sai qaramin kaninsu Usuman dan shekara bakwai.

Sosai Ayuba yake ciwo an rasa gane kan ciwon anyi na asibitin har an hakura ,sai aka dawo yin na hausa,sabida yadda kafarsa guda ta kumbura take fitar da ruwa abin babu dadi , wani mai maganin hausa da yazo ya dubashi ,yace jifansa a kai (Asiri) sabida haka kar a kara yin maganin asibiti domin zai kara rikita ciwon,cikin ikon Allah ya hada magani ya bashi nasha da wanka gami da shafawa, a kafar,sai a ka fara samun saukin abun, domin wani lokacin yakan tashi da kan shi yafito waje yana dafa bango,

Tunda yafara wannan ciwon tsakanin Sallau da Lantana da Uwa babu wanda yazo ya duba shi ballan tana yace dashi sannu ,gwara Mamman shi yazo dalilin tursasawar matarshi Halimatu,

 

Lantana tace yadda uwarka ta tafi tabarka haka kai ma zaka tafi kabar naka "yayan gyyar tsiya arna a idi, kullum in zata fita yawon tallanta sai ta tsaya a tsakar gida tayi surutai ,sannan take tafiya ,tana fatan Allah yasa kafin ta dawo ta tarar ya mutu kowa ya huta

 

 

Allah mai yadda yaso a sanda yaso ,an kwanta da Ayuba lafiya daran alamis ,domin kafin yayi bacci ma sun dade da matarshi da yayarshi Atika ,gami da "yayanshi suna hira,ashe ta bankwana ce, da asubah Hafsatu ta rika tashin sa taji shiru ,sabida ta saba duk asubar fari shi yake riga kowa tashi a gidan,shiyasa ta gigice ta fice daga dakin da sauri,tayi dakin Iya Atika,ta daga labulen ta ce"Iya fito kiga babansu Sadiya yaki tashi,

 

Da sauri Iya ta mike daga kan dadduma ta fito tana salati a zuciyar ta domin dama jikinta ya bata ,tunda ta kwanta take munanan mafarkai,

 

Ta shiga dakin gami da zama kusa da qanin nata ,tana kallon yadda idon shi suka kakkafe tasan lallai Ayuba ya amsa kiran Ubangiji, salati take tana sallallami ,Hafsatu tace "Iya ya mutu ko"?

 

Iya Atika tarasa mai zata ce mata sai kawai ta kama hanya zata fita daga dakin tana sharar hawaye,

Kafin ta daga labule,taji abu ya fadi, rigif!! wanda yayi dai-dai da farkawar *Balaraba* daga bacci a furgice! Iya ta dawo dakin da sauri tana Salati ganin yadda Hafsatu tafadi kan Ayuba dake kwance,

 

 

Tana daga ta taga ta kwanta yaraf! alamun babu rai! a jikinta,

 

*INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN*

 

Abinda Iya tafada kenan,

 

Balaraba ta mike tsaye a zabure tana kallon iyayen ta biyu a kwance ,dukkaninsu babu rai! tace"Iya mai nene Iya kar kice min babana ya mutu,! Iya ki tashi Umma na kin ga tafadi, a kasa, sai ta fita waje da gudu bata saurari abinda Iya take fada mata ba,

 

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

 

_MARUBUCIYAR_

 

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

08089965176

[04/05, 03:17] +234 808 996 5176: đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»

 

*GIMBIYA BALARABA*

 

đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»đŸ§đŸ»

 

 

 

 

           *By*

_BINTA UMAR_

*MAMAN ABDUL WAHABU*

 

 

 

_BISIMILLAHIR RAHAMANIR-RAHIM_

 

 

 

*Page*

*24*

 

 

 

Lantana dake tsugune bakin rijiya tana daura alwala,ta juyo da sauri ganin Balaraba ta fito da gudu daga dakinsu tana ihu,sai ta mike tsaye gami da sakin botar hannuta,tace"ke Balaraba kina hauka ne,dan ubanki ko Ayuba ne ya mutu abinda zakiyi kenan,shashasha mara hankal....

Kafin Lantana ta karasa maganar ,Iya ta tare ta ,da cewar "to ai zan ce ya kare Ayuba da Hafsatu ,sun koma ga Allah,wanda yake ganin zai zauna jiran duniyar gashinan ga tanan.

Lantana ta zabura ,cikin rawar jiki tace "me kika ce Atika, kina nufin Ayuba ya mutu"?

 

Iya tafashe da kukan da yake cin zuciyarta tun dazu,tace "ai ba'a wasa da mutuwa Lantana ,leqa ki gani,

 

 

Jikinta na rawa ta nufi dakinsu Ayuba,

 

Ai kuwa abinda ta gani ya daga mata hankali sosai ,babu Ayuba babu Hafsatu, Lantana ta furgita sosai ,sai ta fito da sauri,ta fasa wani ihu! da ya ta da mutan gidan gaba dayansu har da makota,

 

Kankace kwabo gida ya cika da jama'a ana ta kokawa da wannan mutuwar mai abin mamaki.

 

 

Balaraba kuwa ta dai na kuka sai dai na zuci idanun ta sunyi mici mici kallon kowa kawai take,takama kanne ta da ke kuka ta rungume itama tana kukan zucci.

 

 

Uwa da Lantana kai har da Sallau , mutuwar nan ta gigitasu ta firgitasu,sosai jikinsu yayi sanyi,amma abin mamaki ana yin sadaqar uku ,shikkenan ,suka watsar,mussaman ,yanda suka ga irin mutanan Ayuba ,suna kawo taimako, sai Sallau yayi uwa yayi makarbiya yace"ai shine wakilin yaran, sai Iya tayi da gaske sannan yake barinta ta karbi sadakar,komai idonshi na kai,ita ko Balaraba ,in an bata ,sai ta mikawa Iya,Ashe Sallau duk yana lura,sai yaga babu idon Iya sai yayi ta zuga Balaraba wai ta karbi kudin ta tabashi ,ya aje mata sabida in tazo yin aure shi zai yi Mata kayan gado,

 

Kwata kwata Balaraba bata sauraronshi,sabida tasan ko ta bashi kudin zuwa zai yi yayi caca dasu kamar yadda yayi ,da wa"yanda ya karba ,yamma nayi ya lura,an dai na zuwa sai ya yayi tafiyarshi,mahadarsu,ta "yan caca

 

 

 

Rayuwa kenan Balaraba ,ita ce tazama uwa da uban Sadiya da Usuman ,tun bayan rasuwar iyayensu,ita ce cinsu ita ce shansu, kudin makarantarsu,da nata,

 

 

Bayan rasuwar iyayensu da kwana arba'in ,Balaraba ta hada "yan kudin da suka samu ita da "yan uwanta, ta shiga kasuwa ,ta siyo kuloli da farantai ,hade da manyan tukwane, tazo ta dira abincin siyarwa, a lokacin shekarun ta basu wuce sha shida ba, dake yarinya ce mai girman jiki ,shiyasa in ka kalle ta zakayi tunanin ta zarta haka, Balaraba tana da kyau sosai ,tana da diri na jiki, fara ce tas! Dan idan tayi kwalliya ta fita baza ka taba cewa a wannan gidan take rayuwa ba,tana da kirki sosai abin ta bai rufe mata ido ba domin ko abinci tayi kafin ta fita dashi duk wanda ya kwana ya tashi a gidan takan zuba masa ,sannan yaran da suke fitar mata dashi su dauka a kura, su kai mata bakin kasuwar,(sha tambaya) anan take siyar da abincin ta,wanda da an fita dashi yake karewa,wani ma sabida kawai yazo ya gan ta yasa yake zuwa cin abincin ,rumfa ce da  ita, sosai komai a tsare ,a kwai yaran da suke yi mata wanke wanke da goge goge,tana zaune aikin ta kawai in mutum yazo siya ,ta hada mishi duk abinda yakeso,domin babu abinda babu,wani abin ma idan ba tayi a gida,ba to a kwai mata masu girka mata anan su hada komai tsaf! In kasuwa ta tashi ta basu hakkinsu,

 

duk wannan ,bai hanata karatu ba, yanzu haka ta kammala scondry scoohl , gashi tayi saukar Alkur'ani mai'girma,

 

Iro yana mutukar son Balaraba, yayin da ita kuma tayi masa wata muguwar tsana,sabida halinshi,yanan bai sauya ba,

 

 

Shamsiyya da Mabaruka dama sai sufi kwana da kwanaki basa magana da ita sai dai in zasu ari wani abin a hannunta kamar kayan kwalliya ko mayafi ko takalmi,wataran har kayan sawa suke ara,in zasuyi zance

 

 

Ita ko Balaraba in ta basu bata kar6a in sun dawo mata dashi sai tace su riqe ta bar musu.

 

 

Amma hakan baya hanasu zaginta gami da ai batata in zata fita,sana'ar ta si ta zinden ta ,suna yi mata dariya,wai zata tafi yawon iskanci ,cikin kasuwa, Balaraba bata sauraronsu sabida bata daukesu masu hankali ba daga su har uwarsu.

 

 

Sallau ko tsoran ta yake ji ,kwata kwata bayason laifin ta, sabida bata masa koro in yazo maula gurinta, haka zata dauki dubu biyu ko uku ta bashi

Shiyasa kullum cikin tsinewa su Shamsiyya yake.

 

*wannan kenan*

 

Kadan daga cikin halayen Balaraba

 

 

Macace mai mutukar son girma bata son rai ni ko kadan,kuma bata son harkar qaranta,ko sitturunta babu kanana,duk manya ne ,shiyasa mutane da dama suke mata kallo mace mai girman kai da izza! sabida bata dariya ,sai ta kama kan kaga dariyar ta zaka dade,a kwai samari wadanda suka amsa sunansu a cikin unguwar amma tsoran tun karar ta suke da wani zan ce sabida kwarjin da take dashi

 

Ko cikin kasuwar da take sana'ar ta akwai manya manya mutane da suke son ta amma sun kasa furtawa, sabida kwarjini ,sai kace mai bakin Aljani a jiki.

Sai dai a gani da ido amma babu fuska,

 

*Wannan shine jigon labarin*

 

 

 

_in sha Allah zan cigabah bayan Allah in Allah yasa muna Raye_

 

 

*Yanzu a ka fara labarin gimbiya Balaraba*

 

 

~*Sadaukarwa*~

 

~*Maraici*~

 

~*Soyayya*~

~*Bakin kishi*~

 

~*Mulki*~

 

~*Izza*~

 

~*Takama*~

~*Sadaukarwa*~

 

 

_DUK A CIKIN WANNAN LITTAFIN ,WATO GIMBIYA BALARABA_.

 

 

*BINTA UMAR ABBALE*

 

_MARUBUCIYAR_

 

*NANA KHADIJA*

 

*YARO DA KUDI*

 

*GIMBIYA BALARABA*

 

08089965176..

[13/06, 14:43] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

 

 

 *GIMBIYA BALARABA*

 

 

 

           *NA*

_BINTA UMAR ABBALE_

 

 

 

 

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

 

 

 

 

*25*

 

 

Cikin bacin rai Balaraba ta fita daga gidan Uwa naji Mabaruka tana zaginta sabida nai man fitina amma sabida ta daure musu gindi suyi abinda suka ga dama shiyasa batace komai ba ita take kara ingiza "yar tata cewar tayi duk abinda ta gadama babu mai takura mata gidan ubanta ne

 

 

 

Kicibus sukayi da Sallau ya dawo daga majalisarsu, sai ya tareta yana washe baki tamkar zai fadi yace"dama sai sauri nakeyi ina addu'ar Allah yasa baki fita ba"

 

 

 

A nutse ta ke kallonshi bakinshi duk yayi gaja gaja da dattin goro jikinshi in banda warin taba da ganye babu abinda yakeyi, zuciyarta sai tashi take.

 

 

 

 

Da kyar ta gai dashi  ta bude jakarta sabida tasan abinda yakewa  ta ciro gudar dari biyar ta mika masa

 

 

 

Jiki na rawa ya sanya hannu ya karba  yace"Allah yayi miki albarka Balaraba, ai ni kin fimin wadan can shegun "yan iska kawai Wanda ba 'acin ko kwabonsu uwarsu kawai suka sani ni mai zanyi dasu shegu "yayan asara"

 

 

 

 

Mamaki  da tsananin takaici ne ya kama Balaraba, jin irin zagin da yake ma "yayanshi, wai sai yaushe Kawu Sallau zai yi hankali ne.?

 

 

 

 

Cikin bacin rai tace"gaskiya Kawu abinda kake ba dai-dai bane dan Allah ka daina zagin "yayanka kanai musu mugun baki,  sam abinda kakeyi bai dace ba"

 

 

 

"Rabu dasu shegu tsinannu jiya ina ganin Shamsiyya ta shi go da dubu uku ta bawa uwarta babu yanda banyi da ita ba tabani ko Dari biyu ce amma sabida batada mutumci taki, ni mai zanyi dasu"

 

 

 

 

Takaici bai bar Balaraba tace komai ba kawai ta wuce tabarshi tsaye a gurin yana zage-zage da alama kwakwalrwarshi ta soma samun matsala

 

 

 

 

Tun kafin ta karasa bakin titi mai Napep din dake kaita ya karaso dama tayi mamaki rashin zuwansa da wuri abinda ba ya yi sabida yasan lokacin fitarta,shiyasa itama tayi mishi uziri kila wani abin ne ya tsare shi

 

 

 

 

Cikin mutumci suka gaisa dashi,ta Shiva ta zauna cikin nutsuwa 

Shi kuma ya dauki hanyar zuwa kasuwar sha tambaya

 

 

 

 

Danja ce ta tsayar dasu dai-dai babban titin da zai sadaka da kasuwar, Balaraba ta kalli agogon dake daure a hannuta karfe goma shaura lallai yau ta makara da yawa, ranta ya baci ganin yadda masu mashina da motoci gami da motocin haya kowa yayi cirko cirko a cikin mota, kawai sai ta ziro kanta waje domin ganin abinda yake faruwa a gurin gashi danja ta sakesu amma kowa ya tsaya da abin hawarshi

 

 

Motoci ta gani manya manya irin na gidan sarauta sun tawo a jere daga daga dayan titin wanda zai sadaka da gidan sarki Almustapah, wani mai sai da pure water taji yana cewa  na kusa dashi "Sarki Almansor ne zai wuce shiyasa  humm masu abu da abunsu"

 

 

 

 

Motarshi na karasowa ya sauke  glass din motar gami da ziro kanshi waje ya daga sannunshi, kan kace kabo gurin ya kaure da hayaniya wasu sai kokarin fitowa suke daga abun hawansu duk dan suyi tozali dashi, abin mamaki har da mata "yan mata da masu aure duk sun fito suna daga masa hannu

 

 

 

 

 

Balaraba na hakimce cikin Napep din ranta in yayi dubu ya baci  domin mai Napep din nata ma yayi ficewarsa, can ta hangoshi cikin jama'a sai kurdawa yakeyi wai lallai sai yaganshi

 

 

 

 

Sai da motar da yake ciki ta shige sannan a kafara samun saukin cinko San da a kasamu a titin

 

 

 

Mai Napep din ya dawo sai washe baki yakeyi ya ce "ranki shidade kowa na rubibin zuwa ya ga Sarki Almansor ke kina zaune cikin mota, yau dai nayi tozali da Sarki sarkin kyauta da karamci, Allah yaja zamanin masarautar Sarki Almusta......

"Kaga Ashiru"

Balaraba ta katseshi a fusace

 

Ta cigaba da cewa "idan ban ba danci zakayi to kaje kasameshi inda yake, dan tsabar wulakanci da rainin hankali a kan zai wuce kawai sai a dakatar da mutane, sabida ba'a damu da damuwar kowa ba, wato in mutum wani uziri mai karfi ya fito dashi shikkenan shi abin ya shafa sabida rashin imani, dubi time dan Allah munfi karfin rabin awa a tsaye a titi, sabida an rainawa mutane hankali, Mtsss dan Allah ni kai ni inda na nufa, Allah ka tsaremu da irin wannan mulki"

Ta karashe maganar a zafafe!

 

 

 

 

Cikin mamaki Ashiru mai Napep yaja Napep din yana satar kallonta ta cikin mirrow din din Napep din nashi, mamakin karfin halinta yakeyi da yadda take magana cikin gadara gami da takama ita ba "yar kowan kowa ba sai mugun bacin rai,a zuciyarsa yace" wallahi kika sake kika fadi wata magana akan masaurar garin nan sai kin kare rayuwarki a kurku ko kuma mutan gari suyi kuli kulin kubara dake in basu kashe ki ba ma, yana so ya fada mata haka a fili amma sabida yadda take masa mugun kwarjini yasa ya yi gum da bakinshi sai satar kallonta yakeyi

Ganin yadda tayi wani kicin-kicin da fuska.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

_Binta Umar Abbale_

08089965176

[17/06, 02:59] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

[16/06/2019 9:50 PM] Binta Umar Abbale: đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 *GIMBIYA BALARABA*

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

               *NA*

_BINTA UMAR ABBALE_

 

 

 

 

*MARUBUCIYAR*

```NANA KHADIJA

```YARO DA KUDI```

````GIMBIYA BALARABA```

08089965176

 

 

 

 

```BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

 

 

 

 

*🅿26*

 

 

 

 

 

_____ Sha daya saura  minti biyar Balaraba ta shiga kasuwar lokacin costomas dinta sun cika gurin, da ka dubesu zaka san sun ci sun ta da kai, sabida kudi, Balaraba ta shiga gurin cikin tafiyarta da qasaita kamar wata basarakiya, fuskarta babu walwala ta din ga bin gurin da kalo sabida kwata-kwata bata san kazanta ko kadan, wasu "yan mata ne guda uku suna kai wa da kawowa kokarinsu su sallami duk Wanda yake gurin cikin nutsuwa suke komai.

[16/06/2019 10:25 PM] Binta Umar Abbale: Ta nemi wata kujera ta zauna tana duba wayarta, bata so ta shiga inda mutanan suke sabida ta lura da motar Alhji Yusuf a gurin mutumin ya takura mata, babu irin korar karan da batayi mishi ba a gurin amma sabuda tsabar bakin naci yaki hakura da dai na zuwa cin abinci

 

 

 

 

Tana zaune tana kallon mutane na kaiwa da kawowa cikin kasuwar kowa yafito nema,a fili tace"Allah ka bamu sa'a

 

 

 

Wani al'amajiri ta hango kusa da wata me kosai sai ta kirashi da hannunta,

 

 

Da sauri yaron ya taso har yana hadawa da gudu,

 

 

Gudar dari biyar ta ciro cikin pose din ta ta mika masa, gami da cewa"je ka bawa mai kosai kace ta yi muku sadaka in jini"

 

 

 

Hannunshi yana karkarwa ya karba, yana godiya sosai, ya wuce da Sauri

 

 

 

 

 

 

Iyani, mai kosai soya kosai kawai takeyi tana addu'ar Allah yasa kar tayi mata bandaro gashi sha daya na safe har ta wuce ji take tamkar ta dora hannu a ka taita kurma ihu sanin da tayi in kosai nan yayi kwantai bata da yadda zatayi a gida sabida tabar marayun"yayanta,

 

 

 

 

Almajirin yace"Iyani gashi in Gimbiya wai ki mana sadaka da kosan ki"

 

 

 

Da sauri Iyani ta dago kanta tana kallon Yaron jin ya abanci Gimbiya tasan  babu mai wannan sunan sai mutuniyarta Balaraba

 

 

 

 

Gudar dari biyar ta gani hannun Yaron sabuwa dal

 

 

 

Tayi saurin kallon rumfar Balaraba,aiko suka hada ido Balaraba ta dago mata hannu fuskarta a sake

 

 

 

 

Iyani ta washe baki tace"Uwar dakina ashe kinzo tun dazu nake tambayar Hauwa'u tace baki karaso ba, kila kina kan hanya, yau kin makara gaskiya"

 

 

 

 

Fuska a sake tace"wallahi kuwa kinga mun hadu da gosolow a hanya,wai Yaron sarki zai wuce shine fa a ka kashe hanya"

 

 

 

 

 

"A'a lallai ai a kashe hanya,cewa zakiyi masu garin ne za su wuce"

Iyani tafada tana tsamo kosai cikin matsami

 

 

 

 

Tsaki Balaraba ta ja bata kara cewa komai ba ta bar Iyani tana 6a6atun surutunta.

 

 

 

 

 

Nan almajirai sukayi dan dazo suna karbar sadaka,ganin haka yasa Balaraba ta kira daya daga cikinsu tace ya shiga kasuwa gurin Delu mai kunu ya karbo na dari biyar shima irin Wanda take daurawa a Leda

 

 

 

Da gudu Yaron ya ruga ya shiga cikin kasuwa sai murna yakeyi

 

 

 

 

Girgiza kai tayi kawai a fili tace"lallai ko wane Yaro da irin tarbiyarshi, Allah ka shirya mana zuri'armu

 

 

 

 

 

 

Alhaji Yusif ne ya fito yana ta raba ido so yake ya ga inda mutuniyar tashi take sabuda yanzu ya tambayi daya daga cikin yaran ta tace masa sai yanzu ta karaso

 

 

 

 

 

Yana sanye da wata muguwar shadda wa gambari mai uban tsada taji sitati sai motsi take yi kanshi da hula zanna bukar kana ganinshi kasan dan birni ne kuma akwai daloli yana da kyau dai-dai misali irin mutanan ne masu qiba amma ba sosai ba

 

 

 

 

 

Tana kallonshi yana dube dube tai masa banza,sai ta fito da wayarta ma tana dubawa,

 

 

 

 

Kamar ance ya kalli gefan damanshi sai ya ganta zaune cikin kujera

 

 

 

Ya kasa boye farin cikinsa sai ya saki dariya,har sai da hakoranshi tas daya yana sanye da hakorin magana, kana ganinshi kasan Alhajin Allah ne.

 

 

 

 

 

 

*🖋YANZU MUKA FARA*

[18/06, 22:42] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

[18/06/2019 3:01 PM] Binta Umar Abbale: [18/06/2019 2:08 PM] Binta Umar Abbale: đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

_*GIMBIYA BALARABA*_

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

              _*NA*_

_®BINTA UMAR ABBALE_

 

 

 

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

08089965176

 

 

 

📚 Zamani writes AssociationđŸ€đŸ»

 

 

 

*Al hayyu Al kayyumu ya Allah*

 

 

 

*🅿27*

 

 

 

_________Kicin-kicin da fuska tayi gami da dauke kanta ta cigaba da danna wayarta tamkar bata san da wata hallita ba a tsaye a kanta.

 

 

 

Gyaran murya yayi fuskarsa dauke da murmushi mai kayatarwa yace"ranki shidade Gimbiyata gaisuwa daban take sarauniyar zuciyar Yusif zuciya takice na baki ki yadda kikeso da ita" 

 

Kanta a kasa tana danna waya har ila yau takasa dago kai ta kalleshi ballantana tabashi gurin zama

 

 

 

Murmushi yayi yace"ko zan iya zama, tun dazu nake nan gurin ina sauraron zuwanki naji shiru, sai yanzu Hauwa'u ta ce dani kinzo"

 

 

Dago kanta tayi ta zuba masa idanunta masu rikita masa lissafi, tace"ajiya kabani da zakazo kana nema da sanyin safiyar Allah"

 

 

 

 

Dariya ya saki mai tattare da shauqi gami da so da kauna sam bai ji haushin kalaman ta ba.

 

 

 

Ya zauna kujerar da take fuskantar ta yace"e mana baki san na baki amanar zuciyata ba"

 

 

 

 

Mtssss taja kawai ta maida hankalinta kan wayarta gami da duddubawa,ta bawa banza ajiyar Yusuf.

 

 

 

 

Murmushi ne,kwance a kayatacciyar fuskarsa kwata-kwata yarinyar bata bashi haushi asali ma, wani sabon so da kaunarta ne ya mamaye zuciyarsa

 

 

 

Kawai ya zuba mata ido kawai bai ce mata komai ba

 

 

 

Harara ta ban ka masa gami da cewa"bai yuwa kazo ka tasani a gaba kana kallo tamkar Wanda ya samu madubi, ni kam bana son kallo wallahi"

 

 

 

 

Har yanzu da murmushi a fuskarsa yace" ke kin fi madubi a gurina tunda kullum dake nake kwana nake tashi a zuciyata,Gimbiya kinki ki amince dani, Why"

Yafada muryarshi na karkarwa

 

 

 

 

A nutse tace"wace irin amince zan yi maka ne? bayan kasan kai kafi qarfina, ko ni sam bana sha'awar auran namiji mai dukiya ko mulki,talaka zan aura dai-dai dani,nafada maka tuntuni"

 

 

 

 

 

"Wai me yasa kike magana irin na jahilai ne,Gimbiya, kituna (Annabi Muhammad Slw) ya auri mace mai tsananin dukiya kuma bazawara, kinga kenan babu laifi cikin abin,namiji ya auri mace mai dukiya,ko mace ta auri namiji mai kudi ko mulki,wannan maganar taki bata da tushe ballantana makama"

 

 

 

 

Shiru tayi sabida bata da abin cewa

 

 

 

 

Yace"kinyi min shiru Gimbiya"

 

 

Wayar ta kashe ta kalleshi fuskarta babu yabo babu fallasa tace"shikkenan kaje kawai zamuyi maganar ko a waya ne,kaga nan cikin kasuwa ne bana son kallon da mutane ke mana"

 

 

 

 

 

"Ok baki dauki maganar da muhimanci ba shiyasa kikace zamuyi a waya wannan ba dai-dai ba ne, me makon kice min inzo gida in sameki, zai fi ai"

Ya karashe maganar yana karyar da wuya,cikin nashi salon.

 

 

 

 

Wani irin kallo tayi masa mai kama da harara wanda hakan ya zame mata jiki shiyasa mutane suke mata kallon mace mai girman kai gami da izza da takama,

 

 

 

 

 

"Ban ga dalilin da zaisa in gayyace ka gidanmu ba,babu wata kyakykyawar magana a tsakanina da kai,kabari tukkuna sai an kwana biyu"

 

 

 

 

 

Girgiza kai yayi kawai ya mike tsaye yana kallon agogon hannushi yace"duk abinda kikace haka za'ayi Gimbiyata ina jiran kiran wayarki"

 

 

 

 

 

"Ok a sauka lafiya"

Tafada gami da latsa wayar hannuta,

 

 

 

Har ya wuce ya dawo fuskarsa a sake yace"yau baki da sako gurin Mama kilishi"?

 

 

 

 

Murmushi ne ya subuce mata bata shirya ba,tun sanda ta ga hotan matar a wayarshi taji tana mutukar kaunarta,sosai shiyasa duk lokacin ya zo cin abinci take hada mashi waina(masa) sabida ya fada  Mama tanason wainar shinkafa, shiyasa kullum take hada masa da yawa ya kai mata,Mama kilishi har tasan da zaman  Gimbiya Balaraba,

[18/06/2019 3:02 PM] Binta Umar Abbale: Mikewa tayi a nutse  ya bita da wani mayataccan kallo,duk tana kallonshi, kawai sai taja ta tsaya gami da cewa"kayi gaba ganinan zan kawo maka sakon har gurin da ka aje motarka"

 

 

 

 

"Menene hujjarki ta fadar haka,? Kina nufin in wuce gaba ke kya biyo ni daga baya, ban yadda ba"?

Yafada gami da bin ta da wank kallo mai dauke da so da kauna

 

 

 

Gaba tayi kawai bata saurare shi ba sabida ta riga ta San mugun nacin sa

 

 

 

Bayanta ya bi yana kare mata kallo ji yakeyi in bai auri yarinyar rayuwarshi zata  shiga garari,

 

 

 

 

Hauwa tasa ta hada mata komai cikin wani take away na mussaman an nan nadeshi da wata Leda mai kyalli a sanya leda mai zurfi, ta fito  rike da ledar a hannunta,ta mika masa, "gashi a kai mata ace ina gaidata da kyau"

 

 

 

 

 

Cikin murumushi ya karbi ledar har yana kokarin hadawa da hannuta tayi saurin zare hannunta ledar ta kusa faduwa kasa, sai harararshi take

 

Basarwa yayi yace"zataji insha'Allahu, kizo ki rakani gurin motana"

 

 

 

Share shi tayi ta kawai ta koma gurin zamanta, ta zauna gami da dora kafa daya kan daya, babu abinda ya dameta.

 

 

 

 

Girgiza kai kawai yayi ya wuce,ya na mamakin izza da mulki na yarinyar ya lura abin a jikinta yake,ko shi da yake dan saurata ba ya yin irin abinda take,asalima sam bayaso a san cewa yana da alaqa da masarautar garin, sai dai dayawa daga cikin abokanshi in sun ganshi cikin kasuwar sai su riqa mamakin mai yakawoshi har dai suka fahimci gurin Balaraba yake zuwa, to babu irin maganar da ba'a fada masa ba a kan Balarabar amma yayi kunnan uwar shegu da jama'a sabida shiyasan wacece Balaraba a cikin zuciyarsa.

 

 

 

 

 

 

*🖋YANZU MUKA FARA*

[20/06, 05:57] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

 

[6/19, 12:18] Binta Umar Abbale: [đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

_*GIMBIYA BALARABA*_

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

                 *NA*

_®BINTA UMAR ABBALE_

 

 

 

 

 

*MARUBUCIYA*

```Nana Khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

 

Zamani writes

AssociationđŸ€đŸ»

 

 

 BISIMILLAHIR

 RAHAMANIR RAHIM

 

 

 

 

🅿28

 

 

_______ Biyar  saura Ashiru mai Napep ya zo daukarta dama lokacin suke tashi sai da tabbatar su Hauwa sun tsaftace mata gurin komai an wanke an ajeshi in da ya dace sannan ta bawa ko wacce hakkinta sukayi sallama cikin mutumci, Ashiru ya dauketa suka bar kasuwa mutane sai zindanta sukeyi mussaman wadanda suka kawo mata maganar banza a kasuwar ta ci musu mutumci,shiyasa sam basa iyayin munafurce-munafurcensu a gaban idanta sai sun ga bata guri

[6/19, 20:48] Binta Umar Abbale: Abin mamaki suna zuwa dai-dai danja kamar dazu suka tadda uban gosolow gashi yamma tayi duk "yan kasuwa kowa yana kokarin komawa gida, amma an dakatar da jama'a , cikin mamaki Balaraba tace " wai me yake faruwa ne?

 

 

 

kallonta yayi ta cikin mudubin Napep din yana shakkar abinda zai fada mata,yace "ai Sarki Almansor ne  ya dawo, ashe sun je daurin aure can gwarzo, maimarta bai samu damar halarta ba sai ya wakiltashi dashi da mai girma waziri Rayyanu"

 

 

 

 

Tsaki taja tace"Allah ya kyauta, gaskiya an shiga hakkin jama'a dayawa wallahi, daga zai wuce sai a dakatar da jama'a sabida takama da sarauta,sam wannan bazai iya mulkin garin nan ba"

ta karashe maganar tana tabe baki

 

 

 

 

"yar dariya Ashiru yayi yana satar kallonta gefe guda kuma yana jin tsoran maganar da zai fada mata, amma sai ya dake yace" nura Gimbiya sam Sarki Almansor baya burgeki,kuma baki fahimce shi bane mutum ne shi mai sauqin  kai gami da iya mu amula da jama'a yana da tausayin nakasa dashi sosai, matsalarshi kawai muskilanci shiyasa mutane suke masa kallon mutum mai girman kai da izza"

 

 

 

 

shiru tayi masa batace komai ba, sabida ta lura da Ashiru yayi nisa da kaunar Sarki!

 

 

 

 

wayarta tafito da ita tana dubawa ranta a bace, ta najin yadda motoci suke gudu kan titi dago kanta tayi tana ya muste fuska, cikin rashin dace idanunsu suka hadu dana juna, cikin sakon daya ya gane ko wacece,sai yayi saurin kauda kanshi gami da gyara kwanciya cikin motar

 

 

 

tabe baki tayi ta kauda kanta,ko daga bacci ta tashi zata iya ganeshi sabida ranar saukarsu ta kare masa kallo, shiyasa in taga ana rububin ganinshi sai tai ta jin haushi sabida ita sam bata ganin kyawunshi da mutane suke zuzutawa

 

 

 

bayan motarshi ta wuce sauran motocin suka dinga wucewa a jere har suka kare,sai sannan a kabawa jama'a damar wucewa,

 

 

 

 

 

Agogon dake daure a hannunta ta kalla biyar da rabi sun samu kosan rabin awa a tsaye a titi, giriza kai kawai tayi a zuciyarta tace idan tasan wannan bacin ran zata samu da babu abinda zai kaita fitowa wallahi

 

 

 

 

Sabida haka ana tsaka da kiran sallahr magariba ta karaso gida, tun daga nesa ta hango Shamsiyya na suyar doya da kwai  matasan unguwar duk sun kewayeta

 

 

 

 

 

tana karasowa gurin warin taba ya sata saurin toshe hanci tana kauda kai, da kyar ta samu ta ratsa ta tsakiyarsu tana kokarin shiga gida,

 

 

 

 

 

Iro ne ya tare mata hanya yana wani washe baki yace"Kanwata kin dawo kenan?

 

 

Sama-sama ta kalleshi tana kokarin wucewa tace"e wallahi"

 

 

 

ganin tana kokarin wucewa tabarsha a gurin yasa ya kira sunanta,

 

 

tsayawa tayi tana kallonshi yace"tuntuni nake so muyi wata mahimiyar magana dake dama"

 

 

 

sabida sanin da tayiwa Iro da kafirin nacin tsiya yasa tace masa"yanzu dai lokacin sallah ne kaga isha'i ta kusa yi gashi banyi magariba ba kabari sai anjima sai muyi maganar ko"?

 

 

 

 

Washe baki yayi wasu jajayen hakora suka bayyana Balaraba tayi saurin dauke kanta zuciyarta ta wani mugun tashi,lallai Iro ya bata rayuwarsa

 

 

 

 

yace"babu damuwa ai zamu hadu anjima,yau bazan fiya yawon dare ba, watakila ma a gida zan kwana"

 

 

 

 

ko saurarsa batayi ba tayi saurin shigewa cikin gidan sabida yadda taji zuciyarta tana tashi warin tabar wiwi da ganye duk sun cika soran gidan.

 

 

 

 

 

 

*Muje zuwa*

[21/06, 18:40] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

              ∆∆∆∆∆∆

               _*GIMBIYA BALARABA*_

             ∆∆∆∆∆∆

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                 _*Na*_

_®BINTA UMAR ABBALE_

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

 

 

Zamani Writes AssociationđŸ€đŸ»

 

 

 

 

 

```Bisimillahir rahamanir rahim```

 

 

 

 

*🅿29*

 

 

 

 

 ______ "Salamu alaikum"

Balaraba tayi sallama cikin gidan nasu, babu wanda ya amsa mata,duk da cewa dukkaninsu suna zaune a tsakar gidan, har Lantana ma domin ita ma bata dade da dawo wa daga yawon tallata ba, tana zaune ta mike kafa kan tabarma tana lissafa kudin cinikinta, ita kuma  Uwa na gaban murhu tana soya a wara dake bayan tayi ta safe wacce Mabaruka take dauka to da yamma ma sai ta kara dora kasko, bata tashi sai wajan karfe goma na dare, ita kuma Shamsiyya a waje take soya doya da kwai,

 

 

 

Iya ce ta fito daga ban daki hannuta rike da buta ta tace"Balaraba kin dawo kenan"

 

 

 

Tana kokarin bude kofar dakinsu tace"e wallahi Iya, ya gida"?

 

 

 

"Lafiya kalau ai tun dazu nake cewa shiru baki shigo ba gashi ba kya kawai magariba"

 

 

 

"Wallahi kuwa lokacin da zan fita muka hadu da cinkoso a titi haka ma yanzu abinda ya tsai dani kenan, ga mariba ta wuce ban yi sallah ba"

 

 

 

 

"Ai kuwa sai ki yi harama yin sallah sabida kin san sallahr magariba lokacin ta kurarre ne"

 Iya tafada ta kokarin daura Alwala

 

 

 

 

 

Lantana ta hau surutai na ha baici, tanayi tana tauna goro babu abinda ya dameta,

 

 

 

Iya da Balaraba suna jinta babu wanda ya tanka mata a tsakaninsu

 

 

 

 

Uwa tace"ke ma dai Lantana da wata magana kike wanda a ka rai na shi za'a fadawa haka ya yarda,mu babu abinda za'a rufe mana duk abinda mutum yakeyi muna da labarinshi,

 

 

 

 

Sadiya matar Kawu Maman ce ta fito daga wurin ta, ta dan tsinci magan ganun da Uwa take a kan Balaraba, tace"ke dai  Uwa kinyi a sara wallahi, ki tsaya kina shirme da "yar cikin ki, ki tsaya ki gama kashe wutar dake gabanki mana, amma kin bi kin sanya yarinuar nan a gaba kullum da irin sharrin da zaki kulla mata,kuma kullum kina cin arziqinta duk abinda kikeyi a na sani, haihuwa ce kema kinyi,duk abinda kasowa kanka to ka sowa dan uwanka, amma gaskiya abinda kikeyi ba kya kyautawa wallahi"

 

 

 

 

Saura kadan Uwa ta kifar da kaskon tuyar awarar ta wanda yake cike da mai gefe ga uban a wara nan cikin roba ok

 

 

 

Tayi kan Sadiya da masifa "ke kinga sarkin kinibibi da kankan ba, kwadayayya kawai, au! sabida in ta taje yawon iskancinta ta dawo tana kawo miki ajiyar kudi kuyi raba dai-dai shine kika fito zaki tare mata, iyi, to bari kiji babu ruwanki da ni da " yayana wallahi, bakinki ya sari dayan kashi,duk cikin zuri'ata ban haifi lalatattu ba ehe! ke da baki san ciwon haihuwa sai ki fadi haka, in kinyi zuciya yau ki haihu banza juya wacce bata haihuwa kawai"

Uwa ta kare maganar tana buga cinya bakinta duk ya tara yawu sabida sabida tsabar jaraba da masifa

 

 

 

 

 

Sadiya tayi wani murmushi mai ciwo ta kalli Uwa tace"Babu abinda yake damunki sai jahinci, wannan "yayan naki da kike magana a kansu,ni a gurina da haihuwarsu gwara babu,sabida zasu iya yi miki sanadin shiga wuta, sabida haka babu abinda zan ce yanzu sai dai in ce Allah ya shirye ki, kuma Balaraba da kike wanna tada jijiyar wuya a kanta tafi karfin ki daga ke har " yayan ki"

 

 

 

 

 

 

da mara Uwa taci ta dinga cusawa Sadiya zagi gami da gore-gore tace "karya kike ki ce wancan mutsuyaciyat yarinyar tafi qarfina wallahi sai dai idan banga dama ba,ke dai kawai kice kina yi min bakin ciki kawai ganin ke baki haihu ba,

 

 

 

 

Lantana na zaune tana jinsu uffan bata ce ba, dama in suna fadansu bata saka musu baki, Iya kuwa sauri takeyi ta idar da sallaha tafito,

 

 

 

 

Balaraba ma sa taji abin yayi yawa tafito ta kama Matar Kawu da yake haka take kiranta dashi, tana bata hakuri da kyar ta mayar da ita gurunta, tafito ta daura alwala,  kowa yayi shiru, sai Uwa ce kawai take zage-zage ga yara nan sunyi cirko-cirko suna kallonta taqi tazo ta sallamesu,

 

 

 

 

Walidi ne ya shigo gidan kafadar sa rataye da wani katon buhu cike da robobi da gwangwanaye da kwalebe gami buhun-buhuna, ya tadda Uwarshi tana ta sirfa asahar sai kace ba magujiya

 

 

 

 

 

 

Ya na wani ciccije baki yace" ke kuma Uwa wai menene? tun daga waje a ke jiyu masifarki ke dawa ye ne ehee!!

Ya karashe maganar yana cije baki

 

 

 

 

 

 

Tana kokarin zama kan kujerat suyar a warar ta tace"yo ni da waye ne in ba wacan "yar iskar yarinyar ba, ita kuma waccan juyar mai zaman kashe wando ta fito tana min maganar banza, sabida bata san darajar haihuwa ba take fadin wai da hai huwarku gwara babu, shine nake ci mata mutunci,domin ina raye babu mahalukin da ya isa ya tabaku in kyaleshi ko da ko sarkin garinan ne Almusfah"

 

 

 

 

 

 

Bai tsaya ya gama sauraran abinda take cewa ba, ya nufi gurin Sadiya gadan- gadan, yana wani irin zagi irin na marasa tarbiya, ya daki kofar gurin da karfi abinka da kofar da babu kwari sai ga ta tabude da kanta, kokari yake ya  shiga gurin, Iya tana tareshi yace"dallah iya saurara mana, wannan matar har ta isa ta ai bata mu ko tafada mana magana dan Uwarta! yau sai na farke mata ciki da kwalaba wallahi,ki kyauce kawai na afka mata, sai na nuna mata waye ni, yawa kike Iya!!!

 

 

 

 

 

 

"Walidi wato ni ban isa in fada maka kaji bako, yanzu Matar wan mahaifinkan naka zaka cakawa kwalaba,iyi yaushe ka zama haka"

Iya tafada tana rirriqeshi

 

 

 

 

 

Matar Kawu ce tafito jikinta sanye da hijabi hannunta rike da carbi da alama bata dade da idar da sallah ba

 

 

 

Tace"Iya sake shi gani na fito yazo ya caka min kwalabar, in ya cika shi mara kunya ne, yau zasu ga gatana daga shi har Uwarshi"

 

 

 

 

 

kafin Iya ta ankara Walidi ya kwace daga hannuta, ya nufi inda ya jibge buhun shi na gwan-gwan ya ciro kwalbar maltina guda ya basa ta a kasa yayi kan Sadiya cikin zafin zuciya!

 

 

 

 

 

 

 

 

*YANZU A KA FARA*đŸ»

[22/06, 15:16] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

              ∆∆∆∆∆∆

               _*GIMBIYA BALARABA*_

             ∆∆∆∆∆∆

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                 _*Na*_

_®BINTA UMAR ABBALE_

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

 

 

Zamani Writes AssociationđŸ€đŸ»

 

 

 

 

 

*🅿30*

 

 

 

 

 ______Da gudu Balaraba ta  kara so gurin tace"wai kai Walidi me yake damunka ne,? wane irin zafin zuciya gare ka, kanaso ka aikata aikin da nasani a rayuwarka, ni in dai a kai na kuke wannan abin zan tafi in bar gidan sai ku sake a ciki, amma duk tsiya nan ne tushe na, kuma da nan nake gadara,ni wannan masifar ta ishe ni wallahi"

 

 

 

 

Jin furucin da Balaraba tayi yasa Lantana ta mike a zabure ta nufi inda a ke rigimar tace" kai Walidi ka kiyaye ni wallahi, wato kanaso ka jawo mana musiba,ko bisimillah ka caka mata kwalba mugani,wato uwarka tana daure maka gindi ka yi abinda kaga dama,ai uban naka zai shigo ya same ni, ehee"!

 

 

 

 

Ta kalli Balaraba dake tsaye tace"ke kuma da kike cewa zaki bar gidan,gidan ubanki zaki je, kinaso ki kara nunawa duniya dama zaman kanki kikeyi ko, kina min bakin cikin abinda kike bani kullum ta Allah to babu inda zaki je,kina nan kina cigaba da samo min kudi ehee!!

Lantana ta karashe maganar tana gyara daurin zaninta

 

 

 

 

Tsaki Balaraba taja kawai ta bar gurin  domin cigaba da tsayuwarta a gurin zai ya janyowa ta zagi Lantana ko ta gaya mata magana,shi yasa tabar gurin ranta  a bace

 

 

 

 

 

Uwa kuwa jin abinda Lantana tace yasa ta dinga ga ya mata bakaken maganganu, tace"wallahi Lantana sai tau na kara tabbarwa cewar ke muguwar kwadayayyi yace, wato duk abinda nake miki ba kya gani, ai sai kije ki tayi"

 

 

Shiru Lantana tayi mata sabida tasan masifar jarabarta, ta mike taje ta dauki buta ta shiga ban daki, batare da ta saurari cin mutucin da take mata ba,

 

 

 

*Wannan kenan*

 

 

 

 

*GIDAN SARKI*

 

 

 

 

 

Yana zaune a lambu dake shashen shi, wasu dogarawa masu manya-manyan riguna da manyan rawani, su biyu suna tsaye a kanshi, daya da wani katon mafici daya kuma a tsaye yana bin gurin da kallo, daga yaji motsin abu zai duba,

 

 

 

 

Shi kuma yana kishin gide kan wani tuntu ja da adon zane irin na sarautar garin, yana sanye da wata shadda milk colaur mai mugun tsada,wacce a kai wa dinkin "yar shara da dogan wando gaba da baya na rigar surfani ne irin mai dauke da alamun gidan saurata, duk kayanshi na zaman gida haka suke dai-dai da jallabiyoyinshi,a kwai tambarin sarauta, wani kara min littafi ne na addini a hannunshi yana dubawa, ta cikin farin tabarau din dake idanshi, duk wanda san  Sarki!Almansor ya kalleshi a yanzu ya san da akwai abinda yake damunshi,sabida walwalar shi ta ragu  kuzarinshi ya ragu duk da cewa dama tun fil'azal shi ba mutum ne mai fara'a da dariya ba, kafin ka ga dariyarshi sai kayi da gaske, sannan kullum fuskarshi a tamke take tamau, to a " yan kwanakin nan abin yakara karuwa wanda har sai da Mahaifiyar shi ta fuskanta, lokacin da ta tsirashi da tambaya yace mata babu komai, sam bata yadda da abinda yace ba,tafi zaton ko maganar da tayi mishi ce a kwanaki, take damunshi, sabida haka, tasa Jakadiya Shafa'atu mai mata hidama taje can shashensa ta kira mata shi,tunda takira wayarshi yaqi ya dauka, tasan halinshi da muguwar bakar zuciya da muskilanci, ba ai masa komai ba ma sai ya tsiri share mutane ko yayi kwana da kwana ki bai kula kowa ba, yanzu ma haka tun shekaran jiya da sukaje daurin aure gwarzo shida su Waziri bai kara fitowa daga shashensa ba, shi kadai yake rayuwarshi shida hadiman sa,

 

 

 

 

daya daga cikin wayoyinsa ne tayi kara,

 

 

 

cikin ginshera gami da kasaita ya karbi wayar daga hannun daya daga cikin fadawan nan guda biyu,ya kalli scerin din wayar yana ya mutse fuskarshi,

 

 

 

 

 

"Muddibo na!  sunan da ya gani kenan yana yawo ka screen din wayar

 

 

 

 

Wani murmushi ya saki wanda ya fito masa da kyawunsa da zatinsa,ganin sunan Abokinshi kuma dan Uwanshi amininshi, ba tare da bata lokaci ba ya daga wayar, cikin Yanayin muryarshi kasa-kasa yace"ya akai ne, ka shigo garin ne"?

 

 

 

 

 

 

 

 

*YANZU MUKA FARA*đŸ»

[23/06, 13:45] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

              ∆∆∆∆∆∆

               _*GIMBIYA BALARABA*_

             ∆∆∆∆∆∆

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                 _*Na*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

 

 

Zamani Writes Associatio

 

 

 

```Bisimillahir rahamanir rahim```

 

 

 

 

*🅿31*

 

________Daga 6angaran Maddibo yace"yau kwana na biyu da dawowa, nakira wayoyinka jiya shekaran jiya da jiya duk a rufe, ko jiya nazo gaisuwa fada ban gan ka ba, shine Fulani tace kana gurin ka kwana biyu a kulle ka ki saurarar kowa, hakane ko"?

 

 

 

 

 

Zakuda kafada yayi ranshi ya soma baci jin irin maganar da Maddibo ke masa sai kace wani ubansa,yace"Ubana ne kai da zaka turkeni kana tambaya,in kana bukatar ganina ai kasan in da nake, meye sai ka tsaya tambaye-tambaye, zan kashe wayata in magana zaka fadamin,

ya karashe maganar yana kokarin datse wayar, cikin zafin zuciya

 

 

 

 

Sanin halin sa da yayi na saurin daukar zafi yasa yace"zaka fara halin naka ko, daga magana sai hayaniya, baka tsaya ka saurare ni ba, dan Allah ka rage wannan zafin zuciyar taka"

 

 

 

Shiru yayi masa,

 

 

Maddibo ya cigaba da cewa "zan shigo in anjima, muyi wata magana, kwana biyu akwai abinda yake damuna wallahi"

 

 

 

Da kyar yace"ina sauraron ka,

 

bai saurari abinda Maddibo zai ce ba kawai ya kashe wayar,

 

 

Da sauri Dogari ya karbi wayar ya aje ta kusa dashi, ya koma ya tsaya inda yake

 

 

 

Ko minti biyar ba ai ba wani kiran ya kara shigowa daya wayar tasa, mika hannunsa yayi ya dauka sabida ba ya san irin abinda suke masa ko zama zai gyara duk sai su zabura suna dube-dube,wani lokacin in abin yayi yawa sai ya hanasu, to ko ya hanasu din ba sa dai nawa

 

 

 

 

Ummina! sunan da ya gani yana yawo kan scerin din wayar

 

 

sai da takusa tsinkewa sannan ya daga,

 

 

"Yayi maka kyau, Fulani tafada ranta a bace, ta cigabah da cewa, yau ni kake gwadawa halin naka ko, sabida kawai na yi maka fadan gaskiya,wato kai ba a isa ai maka fada ba ko,shikkenan kazo ina ne manka in kaga dama"

tana gama fadar maganarta ta kashe wayar bata saurari abinda zai ce ba

 

 

 

 

 

Ya fi minti biyar kanshi a kasa yana latsa wayar, zuciyarshi tana masa wani mugun zafi, sam Ummi takasa fahimtarsa da inda ya dosa, shi ba auran ne ba yaso ba, yarinyar da takawo masa a matsayin wacce take so ta zama matarshi kuma uwar "yayanshi itace sam bata kwanta masa ba, Halisa kwata-kwata bata cikin tsarin matan da yake so ya aura

 

 

 

 

Mikewa tsaye yayi, da sauri daya daga cikin hadimanshi ya gyara masa ta kalmanshi wasu masu gashi masu kalar ja da baki, saman su a rufe, ya zira cikin kafafunshi masu dauke da zara zaran ya tsu tamkar wanda bai taba taka kasa ba,Yadda yake tafiya sai ka zaci tausayin kasa yake ko baya san taka kasa, cikin kasaita yake tafiya, hakan ya zamar masa jiki tun yana yaro haka tafiyar shi take,

 

 

 

 

 

Mama Fulani na ki shingede a wata katuwar dadduma da wani katon tuntu, suna hira da Jakadiya Shafa'atu, tana yan ka mata lemon zaki,dake Fulani tana san shan kayan frut shiyasa kullum bata rabo dashi a gabanta,

 

 

 

 

 

 

Yayi sallama ya shiga cikin yanayin tafiyarshi ya karasa ciki sosai

 

 

 

Tunda ya shigo Shafa'atu tayi kasa da kanta,har sai da ya zauna sannan ta dago kanta,ta kai gaisuwa sannan ta mike ta bar dakin cikin ladabi

 

 

 

 

Mintuna goma tsakani babu wanda yace komai tsakanin Ummi da shi,

 

 

Gyaran murya yayi ya ce"Ummi an tashi lafiya"?

 

 

Shareshi tayi ta cigaba da shan lemonta

 

 

 

Matsawa yayi kusa da ita ya rike kafafunta, ya wani marairaice yace"Ummina an tashi lafiya"?

 

 

 

 

Harararsa tayi tace"sai yanzu kasan dani, zaka dameni da tambayar tashi lafiya, da ban tashi lafiya ba baza ka ganni ba"

 

 

 

Shiru yayi mata tunda shi maganar ma wahala take mishi, har yanzu kafafunta na rike a hannunshi

 

 

 

 

Tace"sakar min kafa mana"

 

 

kin saki yayi ya kara rikewa tamau

 

 

Tasan halin rigimarshi, shiyasa ta saki fuska kadan tace"Lafiya lou nake shikkenan ko"?

 

 

 

 

Gyara zama yayi sosai yana kallonta fuskarshi dauke da wani kayataccan murmushi wanda ita kadai ce take ganinshi, yace"Masha Allah Ummina,

 

 

 

"Me sa kaki daga waya ta kwana biyu jiya kuma na aiko kazo kaki zuwa,?

 

 

 

 

Kasa yayi da kansa sabida yasan halin Ummi da saurin fahimtar mutum,gashi shi sam bai iya karya ba, yace " Ummi bani da lafiya"

 

 

 

"Karya kakeyi"

Ummi tafada kai tsaye"

 

 

Baki ya bude yana kallon Ummin jin abinda tace saura kadan dariya ta subce masa,sabuda yasan halin Ummi ba ai mata karya

 

 

 

 

 

"Ko nai maka karya ne"?

Ummi tafada hankalinta kwance

 

 

 

" Baki ba Ummina"

yafada yana boye dariya

 

 

 

"Yawwa ko da naji, in ban yi karya ba, sai in ce yaji ka daka min sabida nai maka maganar Halisa ko"?

 

 

Shiru yayi

 

 

Tace" ko ba haka bane"?

 

 

"Hakane Ummi"

yafada babu wani boye-boye

 

 

 

Kallonshi take cike da mamaki tace"har yanzu kana nan a kan bakanka kenan"?

 

 

 

Zama ya gyara sosai yana fuskantar mahaifiyar tasa, domin maganar da yakeso ya da ita muhimanci ce, yace"Ummi ba wai ina kin Halisa bane, a'a ina kin halinta ne, Halisa bata da tarbiya sam bata cancanci ta zama matata Uwar "yayana ba kamar yadda kikeso, amma tunda kina so shikkenan sai ayi amma dukkanin abinda ya biyo baya babu ruwana"

 

 

 

 

Shiru tayi tana nazarin maganarahi, tasan Yaron ta da tunani da hangen nesa yana da nutsuwa, nutsuwarshi ce ma tasa Maimarta ba ba ya zartar da wani abu da ya shafe shi ko na menene sai ya nemi shawarar dan nasa

 

 

 

 

Cikin nutsuwa tace" duk na fahimci abunda kake nufi, ina so ka yi min biyyaya da dukkanin abinda na umarceka dashi, sabida kasan halin yadda nake rayuwa cikin kishiyoyina, da sauran matayen waziran Mahaifinka, mutukar kaki yadda da wannan abu to babu shakka zasuce nice na hanaka auran "yar uwarka, kasan halin mahaifin ka shi babu ruwanshi da kananun maganganu na gidan nan, sabida haka nake neman alfarma a gurinka ka daure ka aureta, na san yadda kake a tsaye duk fitinar Halisa sai tayi laushi, sabida nasan baza ka yadda da shirme ba"

Ummi ta karashe maganar tana sauke a jiyar zuciya

 

 

 

 

 

Shiru dakin yayi na tsawon minti biyu sannan yayi gyaran Murya yace" Ummi na amince da abinda kika umarce ni, zan auri Halisa domin in faranta miki rai, amma kin san ba zan yadda da kananun maganganu na cikin gidan nan ba, za'ayi rigima dani, mutukar naji wata magana ta biyo ba,domin ba zan lamunci wani ya zage min ke ba rayukan zasu baci, maganar Halisa ce, na kuma amince zan aureta shikkenan sai su bar maganar"

 

 

 

 

 

 

 

 

*Yanzu muka fara*

[26/06, 22:19] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ» đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

              ∆∆∆∆∆∆

               _*GIMBIYA BALARABA*_

             ∆∆∆∆∆∆

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                 _*Na*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

 

 

Zamani Writes AssociationđŸ€đŸ»

 

 

 

 

 

```Bisimillahir rahamanir rahim```

 

 

 

 *🅿32*

 

 

 

______Cikin nutsuwa Ummi tace"alhmdulilahi in sha Allahu babu abinda zai biyo baya sai alkairi,sai dai ina san ka rage zakin zuciyar nan taka kuma ka din ga fitowa cikin jama'a kwata-kwata  kwana kwana biyu na lura baka zaman fada ko zaka iya fadamin dalili"?

 

 

 

 

 

Yafi minti uku baice komai ba daga bisani ya dago kanshi yana kallon mahaifiyarshi yace"Ummi kin san halina bana ganin ana yin ba dai-dai ba in yi shiru duk ranar da mai martaba bai fita fada ba in ya wakiltani na lura su galadima basa su mussaman Baba waziri,Ummi su mulki ya dama sam ni bana sha'awar shi zaman fadar ma dan dai  Mai martaba yana so ne,shine dalilin da ya sa kawai bana son zama sabuda zakiga suna yin abunda bai dace ba, kuma ba'a isa ai magana ba"

 

 

 

 

Shiru Fulani tayi tana nazarin maganar dan nata tasan a kwai badakala a cikin gidan duk ranar da Mai martaba ya fadi ya mutu,domin dukkaninsu abinda suke wa kenan mulki, shiyasa suka tsaneta in banda tana da karfin arziki a gidan da tuni sun koreta babu irin jifan da basa mata tunda suka lura tana da ciki shikkenan ko wanne ya tashi hankalinsa, kishiyoyinta tamkar su mutu Asiri ko ta ina,in da Allah ya taimaka itama ba a kwance take ba maca ce mai addini da addu'a shiyasa duk asirinsu baya kamata ko ya kamata bayayin wani tasiri yake karyewa, a taikaice dai sai da cikin Almansor ya kai wata goma da wata goma sanan ta haifeshi lafiya sumul gida ya kace me da murna,da hayaniya sarki Almustap ya haifi da namiji kasancewar duk "yayanshi mata ne su goma sha uku uwargidanshi kawai ta haifi " yaya maza uku, kuma suka dinga mutuwa daya bayan daya, shine malamin ta yace mata kishiyar ta ce take kashe matasu sabuda tana so ta haifi danta wanda take so ya gaji kujerar mahaifiyarshi dole sai ta tashi tsaye, nan ta daga hankalinta ta dinga kiran malamai gami da "yan bori suna mata aiki a gidan, a kan duk dan da Mai martaba zai haifa in dai namiji ne to kawai ya mutu tun kafin yazo duniya,sosai take aiki da aljanu a gidan duk dan kar wata tazo ta haifi da namiji  Abin da bata sani ba shine sauran "yan uwan Maimartaba Almustapah basa so ya haifi da namiji sabuda gudun kar mulki ya koma hannunsa bayan babu shi.  Babu irin abinda basa yi na shirka domin ganin bayan Sarki dan su samu damar hayewa kujerar mulki

 

 

 

 

Fulani ita ce matar maimartaba ta uku lokacin da sarki ya aure ta sai a ka dinga surutai cewar ya auri " yar malaminshi kuma ba "yar sarauta ba ce,  nan kishiyoyin ta suka sanya ta a gaba lokacin tana bata da shekaru da yawa batafi shekara sha uku ba, da yake yarinya ce mai hankali sam bata musu rashin kunya in suna zaginta sai dai ta shige gurinta tayi kuka ta gayawa Allah damuwarta, kusan shekarar ta goma sha biyar a gidan,sannan Allah ya bata ciki da yake doguwar maca ce sai cikin ya boya in banda Maimartaba babu wanda ya sani a cikin gidan,sai ko jakadiyar ta mai suna Shafa'atu da yake ita take hidima da ita,

 

 

 

 

Cikin ikon Allah da lokacin haihuwa yazo ta haihu lafiya babu matsalar komai.Jakadiya Shafa'atu ce ta gyara jariri tsab ta kwantar dashi a wani kayataccan gado mai kyau irin na yara,sannan tazo ta taimakawa mejego itama ta shirya tamkar ba itace ta haihu ba,

Nan ta zube a gabanta tanayi mata sannu tace" ranki ya dade ki fadi abinda kike bukatar ci yanzu sai a kawo miki,sai ki kwanta ki huta"

 

 

 

Fulani ta sauke ajiyar zuciya kana kallonta kasan tana da damuwa tace"bana bukatar komai yanzu kawai kije fada ki kira min maimartaba"

Da sauri ta mike ta fita daga dakin domin cika umarnin da a ka bata,

 

 

 

 

 

Lokacin da ta isa fada cike take duk su Waziri Zayyanu da Galadima da Wamabai hade da dakatai duk suna gaban sarki a gurfa ne, ta karasa taje ta kwashi gaisuwa,sannan ta isar da sakon Uwar dakinta

nan fada tayi shiru kowa yana mamaki yarinya karama zata aiko kiran sarki,kowa jira yake yaga zai je ko bazai je ba, abin mamaki! maimartaba ya mike a nutse ya kalli mutanan gurin yace"zan shiga in fito yanzu a cigaba da tattauna maganar da muke kai insha Allahu in nadawo za'mu samu mafita"

yana gama fadar maganarshi ya wuce wasu dogarawa uku suka bi bayanshi suna baza babbar riga,tare da fadi takawar lafiya gaba salamun baya salamun Sarki mai adalci a fito lafiya, Jakadiya Shafa'atu ta bi bayasu itama tana nata kirarin.

 

 

 

 

 

Nan baki kofa suka tsaya bayan Maimartaba ya shiga bangaran Fulani

 

 

 

Tana zaune  ita kadai tana tunanin irin rikicin da zai tashi mutukar mutanan gida suka ji cewar ta haihu kuma da namiji wadanda basu san sa zaman cikin ba ma cewa zasuyi karya ne,ita tsoranta kar taje a sabauta mata yaro

 

 

 

Maimartaba yayi mamaki ganin ta tsaf tamkar bata haihu ba.Sannan ga yaronsa mai kama dashi mutuka tamkar an tsaga kara, a hannuta tana shayar dashi, sai ya karasa kusa da ita da sauri fuskarsa dauke da murmushi yace" Fulani mai halin manya mace ma kara da kawaici da kunya,yau na kara tabbatar wa cewa ke alkairi ce a gare ni"

 

 

 

 

A nutse ta mika masa jinjirin tana murmushi tace"gaskiya naji dadin wannan yabon da kayi min, yau Allah ya sauke ni lafiya kaga bawar da Allah yayi mana"

Hannu biyu yasa ya karbi jariri cikin farin ciki yace"masha Allah dukan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki da yayi min wannan bai wa Allah shine abin godiya"

Kunneshi ya kara dai-dai na dan nashi yayi masa hudu ba kamar yadda Annabi ya fada sannan ya kira shi da sunansa sau uku,  sai ya mike tsaye gami da rungumeshi ya ce zamuje fada dashi domin tasan da zuwansa"

 

 

 

Hankalin Fulani ya tashi amma sai ta dakewa zuciyarta tayi addu'a tasan babu abinda zai samu dan ta face da sanin ubangiji, nan Maimartaba ya fita da jinjirin a hannunshi fuskarshi dauke da walwala

 

 

 

Fada na cigaba da tafiya kawai suka ga sarki ya shigo rungume da yaro nan hankalin kowa ya tashi aka fara rige-rigen karbar yaron

 

 

 

Waziri Zayyanu ne yayi nasarar karbarshi daga hannun sarki lokacin da ya zauna yace"ranka shi dade a ina muka samu yaro mai kama da kai sak, sai kace an tsaga kara"

 

 

 

 

A nutse Maimartaba ya ce"yau Allah yayi min baiwarshi Allah ya sauki Fulani lafiya shine dalilin kirana"

 

 

 

 

Saura kadan Waziri ya yar da yaron jikinshi ya dinga karkarwa kafin kace kwabo gumi ya jika masa riga sai yafara mutsu mutsu da baki kwata-kwata ya rasa abinda zai ce, fada ta dauki murna kowa yana fadin albarkacin bakinsa wasu na boye damuwarsu ban da Waziri domin mikewa yayi ya bar fadar yana sabe babbar riga tamkar zai tashi sama haka shige gidansa dake cikin gidan sarautar,

 

 

 

Kafin kace kwabo Labari ya watsu cikin gidan, Uwar gidan Maimartaba ta turo Jakadiyar ta domin ta tabbatar sannan tasa a ka kira mata malaminta domin yayi mata binkice,

malamin yace"wannan yaron da a ka haifa ba zamu iya kashe shi ba sabuda yin haka zai janyo mana shiga hadari dani dake, amma abinda zamuyi masa guda daya ne zamu iya cire masa son mulki a cikin zuciyarsa sai dai yaga ana yi"

 

 

Tace"dama ai abinda nake so kenan kamar yadda ban hafi namiji ba haka bana so wata ta zo ta haifi namiji wanda zai gaji sarauta sabuda haka kawai a cire masa son mulki inda hali ma a sanya masa tsanar gidan nan ko a kada shi ina nufin ai masa kurciya kawai ya bar garin gaba daya"

 

"Zamuyi kokari iya iyawarmu ke dai duk abinda muka umarce ki kiyi kar ki fasa,yanzu dole zamuyi yanke-yanke kuma zamuyi kwanan bori in gari ya waye sai ayi sadake sadake zakiga abin mamaki"

 

 

 

 

Haka  suka dinga dauki ba dadi kan zuwan Sarki Almansor duniya dan ganin sun sabauta shi tun yana yaro amma da yake yana cikin kariyar Allah hade da addu'ar iyaye babu abinda ya sameshi dan gane da mugun abun da suke masa kullum cigaba yakeyi har kawowa yau da ake masa maganar aure.

 

 

*Wannan kenan*

 

 

Wayarshi ce tayi kara ya dauka yana dubawa. Maddibo2 sunan da ya gani kenan, a hankali ya daga yayi gyaran murya gami da cewa, ka shigo ne"?

 

 

Daga daya bangaran Maddibo yace"Eh gani a fada muna gaisawa da mai maimartaba yanzu zan shigo"

 

 

 

"Ok in bangaran Ummi"

 

 

"Shikkenan zan shigo yanzu dama ina so mu gaisa da ita wallahi"

 

 

"Sai ka shigo"

yafada yana kakarin kashe wayar

 

 

 

Ummi tace"kai da waye"

 

"Maddibo ne"

 

 

Murmushi tayi tace"ai shi babu ruwanshi wallahi na lura baya biyewa sauran "yan uwanshi,  ya kan zo lokaci zuwa lokaci muna gaisawa"

 

 

 

"Shiyasa muke shiri dashi sosai Ummi kin san bana shiri da mutum munafiki"

 

 

 

"Nan Maddibo ya shigo ya zube gaban Ummi yana kwasar gaisuwa.Cikin sakin fuska Ummi ta amsa masa tana tambayarsa mutanan gida,yace" Ummi ni yau kwanana biyu da dawo wallahi gidan ma sai jiya na shiga"

 

 

 

"Ayya to masha Allah, in ka kara shiga a mika min gaisuwa gurin iyayen naka"

 

 

 

"Zasuji in sha Allah Ummi"

 

 

Nan suka mike tare Ummi tana ta shi musu albarka tana musu fatan dorewar zumuncinsu

 

 

 

 

Ban garan Sa suka nufa suna tafiya suna hira yayin da hadiman da suke harabar gurin suka dinga kawo gaisuwa Maddibo ne kawai yake amsawa shiko uban gayyar tafiya kawai yake kansa a kasa tamkar wanda ba ya son kallon rana,

 

 

 

 

Wasu hadaddun kujeru suka zauna wanda suke kewaye da kayattacan falon wanda ya sha shimfido irin na gidan sarauta ga wasu manya-manyan tuntu can kan wani tudu shima ya sha shimfidu masu kyau, kafin ka hau sai ka taka matattakala nan yake zama in zai huta in baya son fita waje

 

 

 

 

 

Maddibo yace"na lura sam baka iya tarbar baki ba wallahi baka ji yadda makogaro na ya bushe ba, a ko ruwa ka bani in sha"

 

 

 

 

Wani irin kallo yayi masa yana ya mutse fuska yace"in har nine zan kawo maka ruwa zaka kwana a nan"

 

 

 

Dariya yayi ya mike yace"masifaffe kawai kar Allah ya sa ka bani,ai ina da kafafu"

 

 

 

Tsaki yaja yana lumshe ido yace"kasan kana da kafafu meye na magana"

Sabuda ka rai namin hankali ni zan kawo maka ruwa ko kar Allah ya sa ka sha"

 

 

Maddibo yace"dan Allah kar kadame ni da masifa ka tsaya ka saurari abinda nazo dashi, Yafada yana zama kusa dashi yana kokarin bude ruwan goran sake hannunsa

 

 

 

 

 

*Muje zuwa*

[28/06, 06:33] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

              ∆∆∆∆∆∆

               _*GIMBIYA BALARABA*_

             ∆∆∆∆∆∆

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                 _*Na*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

 

 

Zamani Writes AssociationđŸ€đŸ»

 

 

 

 

 

```Bisimillahir rahamanir rahim```

 

 

 

 

 

*🅿33*

 

 

 

 

 

 

_____Cikin  Yanayin maganar shi yace"Allah yasa magana ce me muhumanci, kazo kana wani damuna matsalata tafi taka"

 

 

 

 

Ajiye robar ruwan yayi bayan ya gama sha yace" magana ce mai muhumanci mana, tun kafin inyi tafiya naso mu zauna muyi maganar Allah bai nufa ba sai yanzu"

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya cigaba da cewa"akwai yarinyar da na hadu da ita wallahi a garin yawace-yawace na na resturant, kasan ni dai da son abinci mai dadi,kawai kwanaki  Buba ya dauke ni muka shiga kasuwa gurin wani abokinshi,  a lokacin yunwa duk ta ishe ni, dole tasa muka futo daga kasuwar domin mu samu abunda zamuci, kawai Buba yace a kwai gurun cin abinci mai kyau bakin kasuwar mu tsaya  muci ba sai mun futa wajan gari ba.Tunda muka shiga gurin idona yayi tozali da yarinyar naji duk duniya babu macan da ta dace da ni kamarta, yanzu abinda nakeso da kai kawai ka shige min gaba gurin neman auranta domin nikam nayi mata"

Maddibo ya karashe maganar tashi yana sauke ajiyar zuciya, fuskarshi cike da farin ciki da annushuwa.

 

 

 

 

 

Wani irin tsaki Sarki! yaja yana wa Maddibo wani irin kallo yace"Lallai ka rai namin hankali wallahi , duk ka gama ya wace ya wacen ka kazo ka kare a gurin mai tuwo-tuwo sabuda tsabar ka rai na ni kazo kace in shige maka gaba, kar Allah yasa ka aure ta din"

 

 

 

 

Maddibo ya karyar da kai kamar wani maraya yace"Kasan kuwa yadda nake son yarinyar nan, wato na kawo maka kuka na kai da nake tunanin zaka sharemin hawaye ka mara min baya  a kan al'amarin zaka sace min gwiwa, bai kamata kayi min haka ba, Alhaji"

 

 

 

 

"Kaga malam nifa ka fitar dani daga cikin wannan al'amarin haka kawai kai karasa wacce zaka ce kana so sai " yar tallah a bakin kasuwa, kai ka san "yayan tallan nan ba tarbiya ce da su ba, ka sani ma ko tana biye-biyen maza kawai kaje ka kwasowa kanka datti da karzuwa, ka bata mana zuri'a kar ka kara sani a cikin wannan shirmen naka"

 Cikin fusata!Madibbo ya dakatar da shi, yace"kayi karya kace wannan yarinyar tana da karzuwa ko karuwa ko kuma me zaman kanta,yarinya nutsatstsiya kamila, maitarbiya, sana'ar siyar da abinci da takeyi domin rufin asirin kanta ne sabuda na lura iyayenta basu wasu masu karfi bane, amma bari kaji duk izzar ka da takamar ka wannan yarinyar tafi ka, sabuda haka in kanaso mu shirya da kai kar ka kara ai bata min ita,sabuda zuciya ba zata iya jurewa ba"

 

 

 

Dariya Sarki!ya kama yi masa ba yana nunashi da hannu yace"amma ka bani kunya wallahi,yanzu a kan "yar towo-towo  kake wannan tada jijiyar wuyar"?

 

 

 

Shareshi Maddibo yayi.

 

 

Har yanzu da murmushi a fuskarsa yayi gyaran murya gami da kara gyara kwanciya cikin ginshera yace" zanso in ga wannan yarinyar, da dai ban yi niyyar zuwa ba amma ganin yadda ka hakikance a kanta yasa dole zanje na ganta,yanzu yaushe ka shirya tafiyar"

 

 

 

 

Sakin fuska yayi ya juyo yana kallon Sa yace"ai a inda ke sakar kwata-kwata yarinyar taki amince min zuwa gidansu, yanzu ma da kyar na karbi numbar wayarta wallahi, amma dole insa a buncika min gidansu"

 

 

 

 

Shiru Sarki!yayi yana nazarin maganarsa ji yake tamkar ya tsinka masa mari,sabuda yadda ya bashi haushi,gashi bashi da halin magana yanzu zai hayayyako masa da masifa ya lura abokin nasa ya yi nisa sosai kan son yarinyar,sai kawai ya masa shiru yana ji yana magana bai tan ka ba.

 

 

 

 

"Kayi min shiru ina ta magana ni kadai"

 

 

"Me kakeso in ce maka yanzu"

yafada hankalinshi a kan wayarshi, ya cigaba da cewa "kace yarinyar taki baka dama kaga kenan bata son ka sabuda haka sai ka hakura kawai,domim wahalar da kanka zakayi gurin macan da bata son ka"

 

 

 

Shiru Maddibo yayi yana jin tsoran fada masa maganar dake bakinsa,da kyar dai ya samu yace"abinda zamuyi kawai muje can gurin inda take sana'ar tata, kafin musamu gidan nasu"

 

 

 

 

 

"Wannan ne kuma baza ayi dani ba,kome zakayi sai dai kayi,in ka damu ka sa a duba maka gidan iyayenta,ni kuma nayi maka alkwari zan maka jagora insha'Allah"

ya karashe maganar batare da ya kalle shi ba

 

 

 

 

"Ai kuwa dole gobe na me adress dinta ko ta halin kaka ne"

 

 

Tabe baki yayi yace" yace mubar maganar haka, muyi wata wallahi raina baci yakeyi dan dai babu yadda zanyi da kai ne"

 

 

 

 

Dole tasa Maddibo barin maganar badan zuciyarsa naso ba suka shiga wata hirar daban.

Can wayar Sarki! ta yi kara,a nutse ya duba fuskar wayar,Halisa ce

 

 

dauke kansa yayi daga kan wayar har ta katse, wani kiran yakara shigowa a karo na biyu,nan ma ta katse bai dauka ba, Maddibo yace"matsala ta da kai kenan sai ai ta kiranka a waya dan tsabar wulakaci kaki dagawa"

 

 

 

A ya mutse yace"kasan ko wacece ne"?

 

 

"Sai kafada"

 

"Wannan shashashar yarinyar ce Halisa"

 

Dariya Maddibo yasa yace"wai kai har yanzu baka sallama mata bane"?

 

 

"Tsaki! yaja cikin damuwa yace" Zaman da ka ganni inayi gurin Ummi zancan take maimaita min wai dole sai na aureta,babu yadda na iya dole in yi musu biyyaya amma kai kanka kasan yarinyar bata burgeni sabuda dabi'unta duk babu masu kyau"

 

 

 

 

"Addu'a zakayi kasan dole ne muyi wa iyayenmu biyayya kan dukkanin abun da zasu zo mana dashi mutukar bai sabawa shari'a ba , amma ina ganin zaka iya da ita duk taurin kanta,tunda na lura ta sonka da yaw........Kafin Maddibo ya rufe bakinshi daya daga cikin, bayin dake tsaye bakin kofar shiga falon yayi sallama,ya zube nan bakin kofa kai a kasa yace" ranka shidade Gimbiya Halisa ce tazo da jamar'arta"

 

 

 

Shiru yayi kawai yana latse-latse a waya

 

 

Maddibo yace"je ka shigo dasu"

 

 

Da sauri ya mike gami da cewa"angama ranka shidade, Allah ya taimeka ,yanzu zan cika umarninka"

ya fuce da sauri!

 

 

 

 

Maddibo ya kalleshi a fakaice ya na kunshe dariya yace"kaga mutuniyar taka ko muna zan canta sai gata tazo,gashi bakace komai ba"

 

 

 

Uffan! bai ce ba masa ba har Gimbiya Halisa suka shigo ita da masu take mata baya.

 

 

 

 

 

*MUJE ZUWA*

[29/06, 05:20] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

              ∆∆∆∆∆∆

               _*GIMBIYA BALARABA*_

             ∆∆∆∆∆∆

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                 _*Na*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

 

 

Zamani Writes AssociationđŸ€đŸ»

 

 

 

 

 

```Bisimillahir rahamanir rahim```

 

 

 

*🅿34*

 

 

Cikin kasaita ta shigo falon kai tsaye in da yake zaune ta nufa,tana wata irin tafiya cike da izza da takama.

Nan jama'arta suka zube bakin kofa suna kwasar gaisuwa,daga bisani suka fuce daya bayan daya, Wani irin zama tayi kan kujerar tamkar zata shige jikinshi tace"Yayana ya kake? kwana biyu duk kasa hankalina ya tashi in na kira wayarka sai kaki amsa min, kasan ko yadda na damu da kai kuwa"

     Fuskarshi a hade yace"ki matsa daga kusa dani mutukar kina so in saurare ki da abunda kikq zo dashi,kin san bana son wannan dabi'ar taki  yana daya daga cikin abunda yasa sam ba kya burgeni"

       Jikinta a sanyaye tace"wai me yasa kake fadamin duk maganar da tazo bakinka,yanzu me ye laifin wanda yace yana sonka,kasan fa ban rasa masoya ba"

      Wani irin kallo yayi mata mai kama da harara cikin kasaita yace"ni ina ruwana da wasu masoyan ki  kin san kina da masoyan zaki makale dole kice sai ni zaki aura,kije ki zabi daya daga cikin masoyan naki ki aura zai fi miki alkairi"

 

 

 

 

Shiru tayi na minti biyu tana tunani tasan halinshi mugun dan wulakanci ne da girman kai,ya zama dole ta lallabashi tunda dai ita ke nema dole ta kwantar da kai har Allah yasa burinta ya cika.

      Kwantar da murya tayi tace"kayi hakuri insha Allah zan gyara,ni dai burina kawai ka dinga kulani kana daga waya ta idan na kira"

     Shareta yayi ya cigaba da duba wayarsa.

Maddibo ta kalla tace"Ya Maddibo ka sanya baki mana wallahi ina jin tsoran wulakancin abokinka kullum da irin kalar da zai min gashi zuciya ta takasa hakura dashi."

 

         Cikin dariya Maddibo yace"kar ki damu insha'Allah komai zai wuce,amma dole kiyi hakuri da halinshi domin ba ke kadai yake wa,so tun yanzu ya kamata ki gane wane irin namiji zaki aura"

    Ajiyar ta sauke tace"bakaji yadda nakeji a cikin zuciya ta ba amma babu komai"

 

       Cikin dariya gami da barkwanci Maddibo ya kalli abokin nasa yace"mutumina kana ji fa ya kamata ka aje wayar nan ku fuskanci juna da mutuniyar kafin zuwan lokacin"

 

        Hankalinshi na kan wayar yace"ba kaji abunda tace min ba yanzu,wai tana da masoya,kajifa wani zance dan Allah, tasan tana da masoya me yasa ta nace min, "yar rainin hankali kawai"

      "Ni dai nace kayi hakuri"

Halisa tafada muryar ta kasa kasa

   A ya  mutse yace"in ban hakura dake ba yaya zanyi,ai dole ki kuyi iya magana,domin ni bana son shirme"

  "to zan koya in sha Allah"

Nan dai ta lallabashi ya hakura suka cigaba da hira sama-sama, Maddibo yace"to ni zan wuce sai munyi magana a waya kafin gobe,insha Allah zan sa a duba min"

 

"Allah ya kaimu"

abinda yace kenan,Halisa tace"Ka gaida gida Maddibo a gaida su Mama"

 

 

 

Sosai Halisa ta dinga jansa da hira, wani ya amsa wani ya share ta,to inda sabo ta saba da haka,cikin zuciyarta tace a juri zuwa rafi wataran tulu zai fashe,yanzu ni burina kawai in ga na mallaka duk wulakancin ka zan jure

 

 

****

 

Maddibo da ne ga wazirin Sarki,inda Waziri ya kasance kani ga  Maimarta ba Sarki Almustapah,Uwarsu daya ubansu daya, Waziri yana da "yaya goma sha shida, bakwai mata sauran duk maza ne, matanshi hudu ko wacce tana da " yaya dashi, Waziri mutum ne shi mai bala'in san mulki sosai domin ji yakeyi tamkar ya kwace sarautar daga hannun dan uwanshi,kullum burinshi da kokarinshi yaya za'ayi taga sarautar ta dawo hannunshi, shida iyalinshi,shiyasa da yaga Maimartaba bai haifi da namiji ba,sai hankalinshi ya kwanta, yana jiran ranar da Maimartaba zai kwanta dama,ya gaje sarautar tunda shine namiji,cikin hukunci ubangiji Allah ya azurta Maimartaba da haihuwar Sarki!Almansor, in da ya zamo daya daya kwal cikin "yaya mata goma sha bakwai shi ya zama cikin na sha takwas, lokacin waziri kusan zaunce wa yayi,ya dinga shige sa fuce gurin ganin ya ga bayan Sarki!Almansor, Allah bai bashi iko ba,dan duk wani kulunboto da yake shiryawa sai ya koma kanshi ko kan iyalinshi,duk rabi" yayanshi maza sun zama "yan shaye-shaye in ka cire, Yusuf(Maddibo) duk ciki shine nutsatstse a cikinsu,shiyasa suka fi shiri da Sarki!Almansor kusan a tare suka yi makaranta komai iri daya suke sawa, duk inda daya yake dayan ma ba gurin, halayyarsu ce kawai bata zo daya ba,inda Sarki Almansor ya kasance mugun muskili wanda magana take masa wahala,sai ya kwana ya yini bai kula kowa ba har in dai ba kamawa tayi ba,shi kuwa Maddibo mugun saukin kai ne dashi gami da wasa da dariya, in ka ganshi sam baza kace yana da alaka da gidan sarauta ba,sabuda da kowa mu'amala yakeyi,babba da yaro,

          Tsakaninsu basa boyewa juna sirri duk abunda ya dami daya daga cikinsu, tsakaninsu suke warware matsalar basa taba yadda maganar ta futa waje, shiyasa kai tsaye Maddibo shi ya fara kawowa maganar Balaraba,

 

     Kiranshi da suna Sarki! da mutane keyi na gida da jama'ar gari ya samo a sali ne daga gurin mahaifinshi,shine take kiranshi da sunan tun yana yaro in yaga yana wata irin tafiya cike da kasaita, ko cin abuncin sa abin kallo ne,balle yadda yake magana, Yadda Maimartaba ya fuskanta abin a jininsa yake, shi kanshi yaron ya san ya fishi kasaita, shine dalilin da yasa yake kiranshi da sunan, mutanan gida suka kama hade da jama'ar gari

 

        Halisa kuwa " yar kanwarsu ce wacce ta kasan ce autarsu wato Fulani Mariya maca ce mai mutukar kirki da sanin ya kamata sam bata kin talaka kullum cikin jawo jama'a take gidanta, tana can tana auran sarkin garin Wani gari jaja Amare, tun Halisa tana yarinya rikonta ya dawo hannun, me babban daki, wato Uwargidan Sarki, ta hada da "yayan ta ta rike kamar gaske, tun ta so warta take mutuwar son Sarki!Almansor, tun tanayi a boye har abu ya fito fili kowa ya fahimta,har maimartaba, nan kuwa Me babban daki ta tsaya kai da fata tace lallai dole ne a kulla wannan al'amarin domin dorewar zumunci, Maimarta ba ma ya nuna yaddarsa, a kan al'amarin, Shi kuma wanda ake domishi ya nuna bayaso da kyar dai mahaifiyarshi ta lallabashi ya dadda gudun bakin mutanan gari

 

*Wannan shine kadan daga cikin tarihin abunda ya faru a baya*

 

 

*Cigaban Labari*

 

 

Da asubah Maddibo yasa drevar ya futa dashi suka shiga kasuwar sha tambaya,can gefan titi yasa drevar yayi parking din motar, yana kwance cikin motar yana kallon masu shigowa cikin kasuwar duk da cewa safiya ce,

      Wajan karfe takwas da rabi ya hangi Napep din Ashiru Balaraba na kokarin fitowa daga ciki yau tana cikin wata irin doguwar riga baka " yar saudia rigar taji adon duwatsu sosai da sosai tayi nan nade kanta da veil  kafarta sanye da wani takalmi mai tsayi mai igiyoyi,sai ta kara tsayi sosai takalmin shima baki ne sosai kafarta tayi kyau a cikin talakmin hannuta rike da wayarta da wata "yar karamar pose  ta tsaya suna magana da Ashiru

 

         Maddibo kuwa suma ne kawai bai yi ba lokacin da ya hangi fitowar ta sai ajiyar zuciya yake saukewa, yana wa Allah tasbihi cikin zuciyarsa yace" tabbas Allah ya aje baiwarsa gaskiya yarinyar ta hadu sosai,  dole maza su rika rikice wa a kanta, in da take burgeshi , kamun kai da rashin kwadayi gami da dogaro da kai shiyasa duk abunda a ka fada masa a kan ta yake kauda kai,sabuda yana ganin babu mahalukin da ya isa ya hanashi auranta,

        Ya na can yana tunani Ashiru yaja Napep dinshi ya na kokarin hawa titi,can ya hangoshi, da sauri ya bawa drevar Umarnin bin bayanshi duk in da ya nufa.

 

 

 

 

 

 

*Muje zuwa*

[30/06, 04:10] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

              ∆∆∆∆∆∆

               _*GIMBIYA BALARABA*_

             ∆∆∆∆∆∆

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                 _*Na*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

 

 

Zamani Writes AssociationđŸ€đŸ»

 

 

 

 

 

```Bisimillahir rahamanir rahim```

 

 

 

 

*🅿34*

 

 

 

Sosai Ashiru yake gudu a kan kwalta,kasancewar babu cinkoso sosai na ababan hawa, sauri yake shima ya isa gurin aikinsu, kawai sai yaga katuwar mota ta tari gabanshi, sai ya rage gudu, ya fara tafiya a hankali gabanshi yana faduwa!

      Cikin sauri drevar dake jan Maddibo ya yi parking din motar gefan titi ya fito,yana dagawa Ashiru hannu.

     Ashiru ya tsayar da Napep dinshi ya fito daga ciki duk hankalinshi a tashe,ganin mutum sanye da wasu manyan kaya ja da baki kanshi nade da wani katon abu,yana gani ya fahimci daga gidan sarauta ne,

     Hannu ya bashi suka gaisa yace"Yallabai ne yake son yin magana da kai"

 

   

 

Jiki na rawa Ashiru ya bi bayan dravar suka karasa inda yayi parking din motar, Maddibo ya mika masa hannu fuskarsa a sake yace"barka da asubah"

       Cikin dari-dari Ashiru ya mika masa hannu sukayi musabaha da juna,kana yace"barka dai yallabai,fatan katashi lafiya"

 

 

 

"Lafiya kalau Abokina"

Maddibo yafada fuskarshi dauke da murmushi ya cigaba da cewa"in baza ka damu ba inaso in nemi alfarma a gurinka"

      Jiki na kyarma Ashiru yace"babu damuwa Yallabai"

 

"Masha Allah, Menene alakar ka da Balaraba"?

    Cikin rawar baki yace" babu wata alaka a tsakaninmu kawai ina kaita bakin kasuwa kullum"

      "Ok shiga muje ka nuna min gidan su"

Maddibo yafada babu wata damuwa a tare dashi.

      Ashiru duk ya rude yace"Yallabai Allah dai yasa ba wani abun tayi muku ba,sabuda na fahimci bata kaunar Sarki!Almansor, in wani abu tayi muku, ku gafarce ta dan Allah, Balaraba marainiya ce bata da uwa babu uba,kusan itace take daukar nauyin gidansu"

      Ajiyar zuciya Maddibo ya sauke, wani irin tausayin Balaraba yana ratsa zuciyarsa.

Yace"Babu laifin da tayi mana, alkairi ne zai kai ni gidansu,ka kwantar da hankalin ka"

     Da kyar Ashiru ya je ya gyara parking a gefan titi kana ya sanya key ya kulle Napep din nasa, ya shiga motar suka kama hanya har unguwarsu Balaraba.

 

 

 

Sosai Maddibo yayi mamakin irin unguwar da Balaraban shi take rayuwa, wani irin lukuna masu dauke da dagwalan katoci ku ina kwata tabi hanya abun babu kyawun gani, hankalinshi bai kara tashi ba ma sai da yaga lokwan su Balaraba,mai tattare da tarkacan, kayan gwan-gwan ko ina gasu nan wasu a daure a buhun-huna wasu kuma a washe a hanya, in ban da wari babu abunda yake tashi a gurin,

    Kasa shiga ciki yayi sosai ya tsaya daga baya,  Ashiru yace"Yallabai ga gidan can, in da waccan budurwar take soya a wara to nan ne gidansu"

      Yara ne suka fara taruwa a gurin suna kallon Maddibo,wasu na rugawa gida da gudu suna fada cewa ga Sarki yazo, ai tuni Yara suka cika gurin,kasancewar Safiya ce wasu duk sun fito domin tafiya makaranta, da sauri ya juya, ya bar gurin drvar shi ya bi bayanshi yana  baza babbar riga, Ashiru  ma ya mara musu baya,cikin zuciyarshi yana mamakin abunda yasa wannan mutumin yake neman gidansu Balaraba,

      Maddibo ya shiga mota hankalinshi a tashe yana tunanin yadda za'ayi Sarki! ya iya shigowa wannan unguwar, shida yake da mutukar tsabta da mugun kyam-kyami! Wani lokacin in yaga abunda kyam-kyami, tsigar jikinshi ta dinga tashi kenan kuma kwana yake tsartar da yawu,ko ya yini bai ci abunci ba, yasan halinshi, sai dai kawai ya daukoshi suzo ba tare da yafada masa yadda yanayin gurin yake ba, kuma dole zuwan dare zasuyi, shawarar da ya yanke kenan cikin zuciyarsa.

 

 

 

Misalin karfe takwas shaura na dare, Maddibo na Shashen Sarki yana fama dashi ya tashi ya shirya, su tafi kar dare yayi, sai da ya gama yan garshi sannan ya mike ya shiga bedroom dinshi yayi wanka, ya fito a nutse ya tsaya gaban tafkeken dressing miroow dinshi wanda yake dauke da wasu mayuka masu tsada hade da manya-manya turarrika masu bala'in kamshi, da tsada.

      Mai ya dauka yana shafawa a lafiyayyir fatarshi, sai sheki takeyi ko fatar wata macan albarka, Sarki!yana da kyau na ban mamaki ba lokaci guda kake ganin kyawunshi ba, sai ka yi kamar minti biyar kana kallonshi,a san nan ne zaka rinka ganin zallar kyawunshi yana bayyana wanda har kaji baka san ka dauke idanka da kanshi, Wata irin fata ce dashi chacolet, ga ta a murje ga wani lafiyyan gashi da yabi jikinshi ya kwanta baki sidik dashi, hatta da ya tsun kafar a kwai su a kwance,hakanan gefe da gefan fuskarshi, nan ma yabi ya kwanta, an yi masa wani irin gyaran fuska wanda yafito masa da dogan hancinsa hade da karamin bakinshi,kasan habarshi gashin yafi yawa ya barshi yayi tsayi kadan, hakan yayi masa mugun kyau, Sarki!Bashi da fara'a sosai, haka in baka sanshi ba zakayi zaton yana da girman kai, gami da wulakanci sabuda,dabi'ar shi, amma in kayi mu'amala dashi sau daya zaka gane mutum ne shi mai mutukar kirki gami da saukin hali, baya son rai ni ko kadan, shiyasa basa shiri da Halisa sabuda ya fuskan ci halinta,

       Sarki!yana da wani abu da ya boye yake aikatawa babu wanda ya sani daga shi sai Ubangijinsa, cikin zuciyarsa baya son wannan abu da yakeyi, shiyasa kullum cikin rokan Allah yakeyi da ya  sa ya dai na.

 

 

 

 

Wata Muguwar shadda ya dauko wagambari blue coulor anyi mata ire-iren dinkin da ake masa, wanda hausawa suke kira"yar shara, wani irin aiki akayiwa rigar da zare kalar shaddar, gaba da baya,in banda maiko babu abunda take, ya dauki agogo na zallar azurfa ya daura a hannunshi, bayan ya fesa turaranshi na ka'ida, kai tsaye inda takalmanshi suke jere ya nufa.

     Anutse ya sanya wani takalmi shima mai bue colour duk jikinshi gashi, samanshi a rufe, duk dai ka na gani kasan na masu mulki ne,

 

       Cikin nutsuwa ya fiti falon inda Maddibo yake zaune yana sauraron fitowarshi, ya kalli agogon hannunshi yace"ka kyauta tun misalin karfe takwas da minti biyar ka shiga ciki, sai yanzu ka fito dubi time, fa"

Yafada yana nuna masa wani dan kareran agogo dake manne a bangon dakin, ya cigaba da cewa"yanzu har yaushe mukaje mu ka dawo,ka zauna kana wani feleke a daki sai kace wani mace"

     Fuskarshi ya shafa yana sosa Gemunshi,cikin sigar Zolaya yace"mutumin da zashi zance gun budurwa ai dole ya kimtsa duk da dai ni a matsayin dan rakiya zanje, kuma mai gabatar da kai kaga dole in tsaya in shirya sosai domin kada budurwar taka ta rai na mu, duba ka ganka dan Allah, duk kabi ka wani susuce, ni da zan maka jagora ma watakila in fika mutumci a gurunta"

        Da sauri Maddibo ya kalli jikinshi yana so yaga inda ya kakare wanda har zai sa Balaraba, tayi masa mummunan kallo,

       Shi kanshi sai da ya bawa kanshi dariya, ganin jallabiya ce a jikinshi tun ta dazu da safe, shaf ya manta da ana wata kwalliya in za'aje gurin budurwa shi dai burinshi kawai yaje yaga mutuniyar shi,

      Dariya yasa, sosai Sarki! yana taya shi, yacr"kasan Allah na manta da cewar wannan rigar ce a jikina,in banda ka tuna min,bari in shiga in canza kaya yanzu in fito"

      Tsaki!Sarki ya ja yana kokarin zama kan kujera, yace"Wallahi har na ka gara inje in ga yarinya nan da ka rude a kanta,

ka dai yi sauri lokaci yana tafiya"

      "Yanzu zan fito insha Allah"

Maddibo yafada yana kokarin shiga bedroom din domin shiryawa.

 

 

 

 

 

 

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[01/07, 17:43] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

              ∆∆∆∆∆∆

               _*GIMBIYA BALARABA*_

             ∆∆∆∆∆∆

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                 _*Na*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

 

 

Zamani Writes AssociationđŸ€đŸ»

 

 

 

 

 

```Bisimillahir rahamanir rahim```

 

 

 

*🅿35*

 

 

 

 Tsaf Maddibo ya fito cikin wani yadi mai santsi anyi masa wani irin dinki a gaban rigar ya dora falmaran ita ma duk jikinta surfani ne, ire-iren kayan Sarki! kenan, wannan ma da Maddibo ya sa sabbi ne dal,a ledarsu, kafarshi sany da takalmi kwatankwacin na kafar Sarki! yayi kyau babu laifi,amma bai kai Sarki!Almansor ba, haka suka fita daga farlon suna hira,cike da kasaita Sarki!yake tafiya, yayin da hadiman gurin  suke zubewa suna kwasar gaisuwa.

     Direba shi ne ya taso da sauri ya nufi wata katuwar mota cikin jerin motocin dake aje a gurin a je motocin  ya je ya bude yana sauraron karasowar su,

     Zubewa yayi kasa hannushi a dunkule yace"ranka shi dade barka da fitowa,Allah yaja zamanin ka, Sarki!me jiran gado"

     "Barka kadai Haladu, ya aiki"?

Yafada yana kokarin shiga motar,

 

" Alhamdulilahi ranka ya dade"

Haladu ya fada yana kallon Maddibo yace"barka da fitowa yallabai"

    Maddibo ya mika masa hannu cikin barkwanci da wasa da dariya suka gaisa,sannan ya shiga mota ya zauna kusa da mutumin nashi,

 

      Haladu ya kunna mota cikin nutsuwa suka fita daga gidan,

 

      Hira suke irin ta abokansu wanda sukai yi karatu tare, Maddibo yace"kaga Harisu Galadima yaran shi uku kasan da mata biyu ya fara,jiya munyi waya dashi yake ce min daya amaryar tashi ma ciki gareta, zai na hudu, shi kuwa Yakuba Buba" dama kasan ya riga kowa aure yanzu in banyi karya ba sai in ce maka zai haifi yara biyar,duk da cewa matarshi daya"

 

      A nutse yace"ka rabu da Harisu Galadima wannan ai mayen mata ne,ko ka manta lokacin muna skul yadda yakeyi in yaga mace,shege ji yakeyi kamar ya bita yayi mata fyade, in bai yi mace biyu ba me zai yi, muna nan da kai zakaji ance maka ya kara ta uku"

    Dariya sukayi duk su biyun har da tafawa.

Maddibo ya gyara zama yana fuskantar Sarki! yace"kai ai ni in na samu wannan yarinyar nagama dacewa wallahi,nake gaya maka yarinyar ta cika mace ta ko wanne fanni, bazan iya yi mata kishiya ba"

     Wani irin kallo yayi masa yace"yar towo-towo din ce kake wani cewa ta hada komai na mace wanda,kake so, kar fa ka mance cewar yarinyar "yar bakin kasuwa ce"

     Shan kunu Maddibo yayi yace"Yasin zanyi maka rashin mutumci, wallahi Balaraba tafi karfin wulakanci a gurinka,kar ka kara ce mata "Yar bakin kasuwa"

 

     Dariya ya sa har sai da dimful dinshi ya fito yace"Wallahi har ka tuna min da wata   mara kunyar yarinya kwanakin baya, da sukayi saukar al'kurani,makarantar tasu ta kawo saukar gaban sarki, Sunanta Balaraba, bazan taba mantawa da kallon banzan da tayi min ba, kai in ka gani sai kayi mamaki, lokacin kana can Swiziland, abun ya bani mamaki, sosai"

     Murmushi Maddibo yayi yace"nafada maka duk me wannan sunan ba karamar mace bace, mybe ka nuna mata halinka ne shiyasa ta nuna maka nasu halin"

 

      Tabe baki yayi yana dan sosa sumar kanshi wanda hakan ya zame masa jiki in dai zai yi magana sai yw sosa kanshi yace"me ya dameni da ita,kasan ni mata basa gabana,wallahi, kai ni fa zan iya kare rayuwata batare da wata mace ba"

 

 

"Wannan kuma mahaukaci zaka fadawa wanda bai san wanene kai ba"

 

Dariya yasa ya dan sosa kai yace"Wallahi nake gaya maka yarinyar nan wai a na cewa gani na fito, ita ta riga kowa tashi domin ta ganni ina lure da ita, daga baya kuma ta fara yimin kallon banza,sai kace wani sa'an ta"

     "Maddibo ya ce" ka ishemu da zan wata yarinya ko ka na ciki  ne, dan ban taba ganin ka ka zauna zance wata ba,ko Halisa bata da wannan matsayin"

     "Kai me zanyi da wannan yarinyar" yafada yana gyara fuska ya cigaba da cewa"kawai dai inai maka kwatance da ita ne, Allah yasa taka Balarabar ba irin halinsu daya da waccan din ba"

 

      "Zamuje ka ganta ne ai sam tawa daban take da kowa"

 

 

"Ok Shikkenan, Allah yasa"

 

Nan suka cigaba da hira har suka karasa Unguwarsu Balaraba,

 

    Maddibo ya kalli Haladu Direba yace"yi parking dai-dai can"

    da sauri Haladu yayi parking din motar inda a ka umarce shi,

 

A nutse ya dago kanshi yana bin unguwar da kallo, Kallon Maddibi yayi yace"wannan wace irin unguwa ce ka kawo mu, guri duk tarkace da kazanta, ko ina kango,da kwatoci, kasan bazan fito ba wallahi,kaje kasa a kira maka ita"

 

      Ajiyar zuciya Maddibo ya sauke  domin yasan dole za suyi haka dashi, yace"kake maganar kango duk gidajan jama'a ne, duk babu wani kango a cikin nan unguwar, wannan tarkacen kuma da kake gani yaran unguwar ne suke sana'ar gwan-gwan"

 

      Ya mutse fuska yayi yace"gaskiya Maddibo baka da kirki, yanzu da kasan a irin wannan unguwar budurwar taka take ka gayyoto ni,kamar baka san halayyata ba, kai yanzu ya dace"kazo ka nemi matar aure a irin wannan guri"?

    "Kaga bana son ka bata min rai dan Allah, kafito mu shiga ga lukon gidansu can,yanzu duhun dare ne babu wanda zai gane ka"

 

      "Billahillazi, babu inda zanje nayi iya yi na, in ka damu kai ka futa ka kurawo ta sai mu gaisa,amma bazan fita daga motar nan ba,haka kawai kwalabe su fasa min kafafu,kan wata shashashar budurwar ka wai ita Balaraba"

ya karashe maganar yana gyara kwanciya cikin motar babu abunda ya dame shi.

 

      Sanin halin taurin kai irin na Sarki! yasa Maddibo jan tsaki ya bude motar ya fita sabuda yasab duk nacin da zai masa bazai fito ba kamar yadda ya fada

 

Dariya Sarki! yasa bayan fitar Maddibo daga cikin motar yace"duk Abinda zakayi kayi amma bazan fita in cuci kai na ba"

 

 

Haladu Direba ya fito ya tsaya a bakin motar yana kalle-kalle, ganin fitowar  Maddibo, yasa ya karaso  Maddibo yace"ka tsaya kawai zan fito zan shiga gurin can"

 

"A fito lafiya yallabai"

 

Haladu ya koma bakin mota ya tsaya,

 

 Ganin motar gidan Sarauta yasa yara suka fara, taruwa

 

 

 

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[02/07, 14:47] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

              ∆∆∆∆∆∆

               _*GIMBIYA BALARABA*_

             ∆∆∆∆∆∆

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                 _*Na*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

 

 

Zamani Writes AssociationđŸ€đŸ»

 

 

 

 

 

```Bisimillahir rahamanir rahim```

 

 

 

 

 *🅿36*

 

 

Kasancewar babu wutar nepa a unguwar shiyasa yara basu ankara ba sosai, dabi'ar yaran cikin gari kenan in suka ga bak'o cikin mota zasu zo su tsaitsaya suna kallo wasunsu kuwa har zuwa suke su dinga taba motar suna dariya suna rugawa gida da gudu,Sarki!yana kwance cikin motar yana bin unguwar da kallo, cikin zuciyarsa yace"yanzu haka jama'ar dake cikinta suke rayuwa, wasu gidajan gasu nan duk babu kofofi, wasunsu an sanya musu buhu an kare sabuda kar a gano cikin gidan, a fili yace"da gani gurin zai yi sauro sabuda tarin shirgi da datti da kazanta, dole a kawowa unguwar a gaji,

Shi kadai yake wannan sake-saken cikin zuciyarsa, gefe guda kuma ya zaku yaga wannan yarinya da Maddibo ya makance a kanta.

 

 

 

 

 

A nutse Maddibo ya kutsa kansa cikin lungun su Balaraba wanda yake dauke da tarkace iri-iri haka ya dinga tsallake kananun langa-langa da robibi har ya karasa kofar gidansu Balaraba,inda yara da matasa suke tsaye kan Shamsiyya wacce take ta faman soya awara da kwai,

    Gefe guda ya ja ya tsaya ya kira wani yaro wanda yake tsaye kan Shamsiyya yana jira ta sallame shi,

   "Kai Salmanu ungo awarar taka, in sallame ka in huta"

Shamsiyya ce ta dago tana wa Salmanu magana,kawai sai ta ganshi ya nufi gurin wani mutum can gefe, fitilar wayarta ta kunna ta haske fuskar Maddibo tana wani ya mutse fuska tace"wancan wanene a tsaye a can ne"

   Da Sauri Walidi dake tsugune kusa da ita yana zukar wani abu a tsumma ya mike yana wani ciccije baki yace"yana ina ne yanzu in farde masa ciki"!

    "Gashi can naga ya kira Salmanu ko uban me zai yi masa oho! je ka gani"

 

Walidi na tafiya yana hada hanya ya nufi inda Maddibo ke tsaye tare da Salmanu

 

 

Matasan dake tsaye a gurin ne suka rufa masa baya suma cikin rashin tarbiya suke cewa"bari muje muga wane dan iska ne,yanzu mu kaddamar masa"!

 

 

Maddibo yana hangen zuwansu gurinsa sai ya gyara tsayuwarsa, har suka karaso gurin,suka tare Salmanu, cikin tsageranci Walidi yace"kai ina zaka ne? me wancan guy yace maka"?

 

Jiki na rawa Salmanu yace"Cewa yayi in kira masa Gimbiya ta gidanku"

 

 

"Kai!! dan uwarka wacece Gimbiya a gidanmu"?

Walidi yafada yana dukan kafadar yaron.

 

" Balaraba fa yake nufi"

Salmanu yafada jikinsa na rawa domin wani irin tsoran Walidi yake ji

    Cikin tsawa!Walidi yace "kai! kauce daga nan dan uwarka ko in yaga ka, yanzunan"

 

 

Da gudu Salmanu ya bar gurin,

 

Cikin wata irin tafiya Walidi  ya karasa kusa da maddibo ya tsaya yana masa wani irin kallo, duk da cewa a kwai duhu a gurin bai hana shi ganin irin kallon da yake masa ba.

 

"Kai waye ya baka izinin shigo mana lungu ehe,! mufa duk inda mukaga bakuwar fuska babu yadda, gurin wace Gimbiya kazo a lungun nan"

     Dariya ce taso takama Maddibo ganin yadda yaron yake wani ciccije baki yana wani tangadi tamkar zai kai masa duka, gashi sai warin ganye suke dukkaninsu, girgiza kai yayi gami da gyara tsayuwa yace"Sannuku "yan samari, ni bak'on alkairi ku kwantar da hankalin ku, Gurin Balaraba nazo"

 

 

Walidi ya gyara tsayuwar gami da zira hannu cikin aljuhun wandonsa ya fito da wata wayarsa wacce duk ta sha dauri ka da kyaure sabuda tsabar ganin duniya,ya kunna fitar wayar cikin sigar rashin mutumci ya dallare fuskar Maddibo da ita,

  Sai  wayar ta kusa faduwa sabuda razana da yayi, ganin Fuskar Sarki!Almansor da yayi, sabuda Maddibo suna dan yanayin kama da Sarki!amma ba sosai ba, sai dai duk inda jininka yake za'a ga kama ko yaya ne"

    Bakinshi na rawa yace"ranka ya dade, kace Balaraba kake son gani"?

 

"Kwarai kuwa"

Maddibo yafada fuskarshi a sake,

 

Washe baki Walidi yayi yace"ai kuwa bata dade da dawowa daga kasuwa ba, wallahi ai yaya ta ce, bari in shiga in kira maka ita"

 

Fuska a sake Maddibo yace"Ok nagode Abokina, kace"mata Yusuf ne"

 

 

"E ai insha Allahu zan yi mata bayani"

Walidi yafada gami da juyawa da sauri!

Maddibo yace"jimana"

 

Walidi ya dawo da sauri ya zube kasa bai sani ba,

Maddibo yace mike tsaye mana Abokina"

Cikin yake Walidi ya mike tsaye sam ya kasa hada ido da Maddibo sabuda tsabar kwarjin da yayi masa,

    Hannu ya zira cikin aljihu ya fito da kudi daurin "ya dari-dari guda uku ya mika masa, Hannu na kyarma Walidi ya karba yana ta zabga godiya,

   Gyaran murya yayi yace" ka dauki dauri daya ku raba da kai da abokanka, sauran dauri biyu ka bawa mutanan gida"

Godiya kawai Walidi yake bakinshi yaki rufuwa,sauran matasan dake gurin suka sanya ihu!suka bi bayan Walidi da gudu,

   Shamsiyya ta dago kanta tana kallonsu har suka karaso gurin basu bar ihun murna ba, ranta a bace! tace"kai wannan wane irin iskanc......kafin ta karasa maganar tata Walidi yazo yayi fatali da kaskon suyar awarar wanda yake cike taf da mai gami da awara cikin kwai,  da sauri! ta dauke kafafunta tana kurma ihu! sabuda yadda mai duk ya zuba a kafafunta, kafin ta dawo hayyacin ta Walidi ya daki! Katuwar rubar dake cike taf!da awara an soya ta gwanin sha'awa, duk ta watse a gurin cikin kasa da tarkacan kazanta, ihu! ta kurma ta mike da sauri tayi kan Walidi tana dura masa ashar! ba ta sani ba ta tsumbula kafarta cikin kaskon awarar  wanda ke dauke da ragowar mai da bai karasa zubewa ba, durkushewa tayi a gurin tana rike kafarata sosai ta kone, a kafafun da hannunta guda.

 

 

 

 

Cikin Ihu!da hargowa Walidi yq shiga gidan, sauran matasan dake biye dashi a baya suna tayashi,

Lantana ta mike da sauri! har sai da zanin jikinta ya sabule ya fadi kasa tayi saura daga ita sai dan tofi, Cikin gigita tace"shikkenan Walidi ya jawo mana musiba ooo ni Lantana!

    Uwa! ma fitowa tayi daga dakinta kanta babu ko dankwali,gabanta yana mugun faduwa tace"kai Walidi menene kake mana ihu! ne"?

 

Banza yayi musu ya nufi dakin Balaraba da gudu, yana fadin" Aunty Balaraba Gimbiya ta gidan sarki! ki fito kinyi babban kamu, daga yau nine zan zama yaronki, Allah ya yanke min wahala"

 

Tana zaune kan dadduma hannuta rike da carbi idar da sallahr ta kenan, taji shi yafado mata daki yana mata sambatu,

 

Jin abunda Walidi yake fada yasa Lantana, bankada labulen dakin Balaraba da sauri ta shiga har tana kokarin faduwa, tace"kai Walidu me kunne na yaji kana fada ne"?

 

 

 

 

*Muje zuwa*

 

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[03/07, 14:29] +234 808 996 5176: đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

       

       ∆∆∆∆∆∆  

        _*GIMBIYA BALARABA*_

        ∆∆∆∆∆∆

                 đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

             _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 

 

*MARUBCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

 

_*Zamani Writes Association*_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rahim```

 

 

 

*🅿37*

 

 

 

 

_*Almuminu,Almuhaiminu ya Allah*_

 

 

 

 

Wani kallo Walidi yayi wa Lantana irin nasu na marasa tarbiya yace"kinga Lantana duk wani zancan bakin ciki da hassada ya kare, ni daga yau wallahi na dai na biye muku ku cuce ni, Balaraba dai Allah ya rufa mata asiri,dan Sarkin garin nan shine yazo gurinta gashi can a waje"

    Lantana bata bari ta karasa jin zancan Walidi ba ta nufi hanyar waje tamkar zata kifa sabuda sauri,

     Iya ce tayi sauri ta tari gabanta tace"ina zakije haka Lantana dubi jikinki babu zani daka ke sai dan tofi"

 

"So nake inje in ganewa idona zancan da Walidi yazo dashi"

Lantana ta karashe maganar tamkar wata zautacciya

    Sadiya Matar Kawu tasa dariya tace"yanzu ke Lantana idan a kace ki futa haka sai ki futa,to in kin futa waje me zakiyi"?

 

Iya ta riko hannuta ta dawo da ita tsakar gida ta zaunar da ita kan tabarmar ta,sannan ta leka dakin Balaraba tace"me kike yi baki futo ba kije kiga ni ko waye"

 

 

A nutse tace"Iya babu inda zani ni domin ba muyi da wani zai zo gurina ba,sai dai idan wata Balarabar a ke nufi bani ba"

 

 

Walidi kamar ya dora hannu a ka yace"dan girman Allah aunty Balaraba kizo kije ku gaisa,kin san dai bazan miki karya ba, wallahi da gaske nake"

 

Shamsiyya ce ta shigo cikin gidan tana durawa Walidi zagi ta Uwa ta Uba, sai jan kafa takeyi, Mahaifiyar su ta gani tsaye bakin rijiya tayi shiru, kamar babu ita a gurin, cikin jin radadin zafin ciwo tace"Wallahi Uwa!yau sai nayiwa Walidi rashin mutumci, kinga yadda ya kona ni, yayi miki barna,gashi can duk ya zubar miki da awarar gaba daya"

 

 

Wani uban zagi Uwa!ta kurma tana kwalawa Walidi kira wanda yake dakin Balaraba yana tw zabga mata magiya kan ta taje gurin Maddibo.

 

 

"Wai me yake a cikin dakin waccan mutsiyaciyar ko tafara koya masa iskanci ne"

Shamsiyya tafada tana daga muryar ta dan Balarabar ta ji ta.

 

"Rabu da shashasha kwadayayye kawai,makarya cin banza da wofi wai dan Sarki ne yazo zance gurinta shine yazo yana yiwa mutane shirme"

 

 

"Kan Ubancan"!

Shamsiyya ta kurma wani uban zagi,ta cigaba da cewa" shine ya kona min jiki a kan waccan,wallahi bazan yadda ba,sai nayi musu wulakanci, wane dan Sarki kawai yace Farkanta ne ya biyo bayan ta meye ba mu sani ba"

ta karashe maganar tana buga cinyar ta

 

 

Lantada dake zaune kurum tun dazu bata ce uffan! ba tace"shiyasa ai nake so in futa in ci masa mutumci in koreshi, sabuda nasan babu wani mutum mai mutumci da zai zo gurin wannan lalatacciyar sai lalatacce, O ni Lantana,yanzu in da gaske ne dan Sarki ne yake son yarinyat nan ina zan sa kai na"

ta karashe maganar har da rike haba!

   Sadiya matar Kawu tace"Ko wane irin miji Balaraba zata aura, duk mulkinsa da dukiyarsa gami da nasabar sa, Lantana baki isa ki hana abunda Ubangiji ya tsara a kan ta ba,Balaraba dai ta zama murucin kan dotse wallahi,bakin cikinku babu in da zashi a kanta"

     Kuka Lantana tasa har da fyace majina tace"Ni kikewa rashin kunya Sadiya har kina kokarin zagina tsofai-tsofai da ni"

 

Uwa!ta tabe baki gami da cewa"muna furci dai dodo ya kanci meshi,ehe!! ai gashinan ke da kike daure mata gindi tana kokarin zaginki ,gaskiya naji dadin wannan abu"

   Sadiya matar Kawu dakinta ta shige tace"gaskiya ce ba kyaso Lantana dole in fada miki"

 

 

 

Ganin Nacin! da Walidi yake mata ya ki karewa yasa ta mikewa tsaya har yanzu tana cikin hijab dinta har kasa ta kalleshi gami da cewa"muje shikkenan ai sai ka sakar min mara in sake"

    Walidi ya washe baki gami da cewa"Yawwa matar Manya,aike yanzu kin zama kadara a gidan nan, ba irinsu wadancan "yan iskan ba"

Yana sane ya fada da karfi dan Shamsiyya taji,aiko ta ji shi, yana futowa ta dinga zaginsa, tana hadawa da Balarabar, shiru kawai Balaraba tayi mata,shi kuwa Walidi kallonta yayi shekeke!yace"mahaukaciya kawai a haka zaku shegu "yan iska, kawai"  Da gudu Shamsiyya tabishi tana zaginsa, kamar wata "yar maguzawa, Balaraba tayi saurin kaucewa tabata hanya, tana mamakin ta tamkar wata dabba haka take ganin Shamsiyya sam!bata da nutsuwa balle kamun kai.

   Tuni Walidi ya fuce daga gidan, sai ta tsaya bakin kofar gidan tana kalloshi yana tsaye can kusa Maddibo,ta dinga kurma masa zagi babu ji babu gani, sai da tayi mai isar ta sannan ta juya ta koma cikin gidan tana jan kafarta suka ci karo da Balaraba tana kokarin futowa,

   Kaucewa tayi ta bata hanya a karo na biyu,ganin tana nema ta bangaje ta, tsayawa tayi ta na mata wani dan banzan kallo tace" Haka zaki kare,karuwa kawai"

    Murmushi Balaraba tayi kawai ta  raba ta gefenta ta wuce tabar ta tsaye a gurin,tana cizon ya tsa taso ta tanka mata suyi kokawa kamar yadda suka saba shekarun baya da suka wuce.

 

 

Can gefe ta hango Walidi tsaye da Wani mutum a tsaye,sabuda haka kai tsaye inda suke ta nufa cikin nutsuwa.

 

Tunda ta fito ya nemi nutsuwarsa ya rasa har sai da Walidi ya fuskanta yayi saurin waiwayawa yana kallon bayanshi sai yaga Balaraba, washe baki yayi yace"Yallabai dama nace maka yanzu zata futo wallahi"

    Fuska a sake Maddibo yace"nagode Abokina"

hannu ya mika masa,Walidi ya saurin mika masa nasa sukayi musabaha yana mamakin mugun sauki kai irin na Mutumin,

     Tun kafin takaraso ta fahimci Yusuf ne, (dan anace) sunan da tasa masa kenan, sam bata taba zaton zai nemi gidansu ba, lallai ta yadda yana sonta da gaskiya kamar yadda yake fada,

     Fuskarta babu yabo babu fallasa ta karasa gurin.

Walidi yayi saurin wuce yana fadin "Yallabai a sauka lafiya, mungode sosai"

Hannu kawai Maddibo ya daga masa,duk ya rasa nutsuwarsa,dalilin futowar Mutuniyar tashi,

 

Anutse ta gaida shi, ya amsa yana mata wani kayataccan murmushi

 

"Ya akai ka kawo kanka gidanmu"?

kai tsaye tayi masa wannan tambayar.

 

Murmushi ne dauke a fuskarsa yace" ke kin dauka son da nake miki na gaibu ne? duk inda kike zan biki wannan shine soyayyar gaskiya"

   Murmushi ne a kwance a kayatacciyar fuskarta, tace"gaskiya kam yau na yadda da kai dari bisa dari"

 

Wani dadi gami da farin ciki ne suke ratsa zuciyar Maddibo,jin abunda tace, sam bai yi tunanin zai shawo kanta da wuri haka ba,

"Alhamdulillahi Gimbiya ta, yau ranar farin ciki ce a gurina,nagode da tarbar da kika yimin"

 

Shiru kawai tayi tana sakar masa murmushi mai kayatarwa.

  Gyaran murya yayi yana kallonta yace"tare muke da dan uwana kuma abokina aminina, yana can cikin mota, kizo muje ku gaisa dashi"

 

Wani irin kallo Balaraba tayi masa, tace"kamar yaya inzo muje mu gaisa,shi bai isa yazo nan din ba kamar yadda kazo har sai an bishi inda yake"

     A nutse yace"Mutumin nawa ne akwai tsirfa, baya son hayaniya, kinga yanayin unguwar taku"

ya karashe maganar yana son boye mata abunda yake da akwai,dan a zahirin gaskiya bazai iya futowa ya fada mata kyamkyamin ne ya hanashi zuwa inda take.

 Shiru tayi tana nazari, a cikin zuciyarta, a yanzu Maddibo ya wuce wulakanci a gurinta,mutumin da ya tako yazo har inda take duk da tarin arzikin da yake dashi,ita sam bata san yana da alaka da sarauta ba tunda bai taba fada mata ba,wannan dalilin ne kawai zai sa taje har inda abokinsa su gaisa kamar yadda ya fada din, baya ga haka kuwa, bai isa ta taka taje har inda yake ba.

 

A nutse ta kalli Maddibo tace"Muje kawai amma fa sabuda darajar ka, zani har mu gaisa dashi dan gaskiya ni babu wani mahalukin zai nuna min isa da mulki, idan ba mahalaccina ba"

 

 

Fuskarahi a sake yace"godiya nake Gimbiya ta gidan Maddibo"

Murmushi tayi tana wani fari da ido,suka jera a tare suna hira cikin fahintar juna, "yan yaran da Balaraba take rabawa naira biyar-biyar kullum in za tafita, suna zaune bakin hanya suna ta wasa, duk da dare ne kuma babu wadataccan haske,amma sai sa suka gane ta, nan suka rude," laaaaa Aunty Balarabamu, a dawo lafiya"

    "Allah yasa"

Balaraba tabisu tana amsa wa babu kyara ballantana hantara!

 

 

 

 

Wata katuwar Mota taga sun nufa, ga wanu mutum tsaye jikinta,jikinsa sanye da wasu jajayen kaya, irin na gidan Sarauta, cikin mamaki ta dinga bin Maddibo a nutse sam babu wata fargaba a tare da ita,

 

 

 

Sarki! Yana zaune cikin mota yana danne-danne cikin waya ranshi yayi mugun baci! ganin yadda Maddibo ya bawa banza ajiyarshi yana can yana zance da budurwarsa ya manta tare suke,wato da ma dan ya wulakanta shi ne yasa yazo ya takurashi dole sai  yayi masa rakiya,dole ya nuna masa bacin ransa,dan bazai yi zaman banza, cikin mota, sai kace mara abin yi"

  Kokarin bude motar yaji a nayi, sai ya gyara zama a nutse ya sanya hannushi ya bude motar ta ciki sabuda ya sanya mata sucurity dole sai shine zai bude,

Shan kunu! yayi domin yasan Maddibo ne, ya bude motar kawai ya dauke kansa, ya mayar da hankalinshi kan wayar dake hannusa

 

Balaraba na tsaye a bayan Maddibo duk taga abunda yayi, so take ta kalli fuskarsa, sosai babu haske sai hasken wayar hannunshi,

 

Cikin Dariya Maddibo yace"Mutumina kaji ni shiru ko, kasan halin Gimbiya tawa sai a hankali"

 

A fusace! Sarki! ya dago kanshi ya watsa masa wani kallo,kana yace"kaga Malam abunda ya dame ka ne wannan, dan tsabar rashin mutunci ka tafi kabar mutane zaune a cikin mota kamar wasu marasa abunyi, dubi time fa"

Yafada yana kallon haddadan agogon dake daure a hannushi, ya cigaba da cewa"tun misalin takwas da kwata duba fa sai yanzu ka dawo tara da minti ashirin da biyar, duk irin zancan da zakuyi da kai da "yar towo-towon naka ai yaci a ce ka tuna dani,tunda dai ni ba banza bane da zaka shanya ni kamar wani shashasha"

Ya karashe maganar cikin masiba!

 

 

Tunda Ya fara magana  gabanta ya dinga faduwa! ko cikin mafarki taji wannan muryar baza ta taba mance da me ita ba, Sarki! ne Yariman Sarki Almustapah Maimarta ba sarkin garin nasu mai adalci,

gabanta ya cigaba da dukan uku-uku jin sunan da yake kiranta dashi, wai "yar towo-towo.

 

 

 

 

 

 

*Muje zuwa*

 

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[05/07, 12:57] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

       

       ∆∆∆∆∆∆  

        _*GIMBIYA BALARABA*_

        ∆∆∆∆∆∆

                 đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

             _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 

 

*MARUBCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

 

_*Zamani Writes Association*_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rahim```

 

 

 

 

 

 

*🅿38*

 

 

 

 

 

 

                  *Real Bintu Batula*👄

 

Rai a bace Maddibo yake kallonsa, jikinsa duk yayi sanyi jin irin bak'aken  maganganun da Sarki! yake ya wa Balaraba, kwata-kwata ya rasa me zai ce masa, kallon Balaraba yayi jiki a sanyaye ya bude baki zai yi magana, tayi saurin tararsa,fuskarta babu yabo babu fallasa ta kalleshi a nutse tace"Kar ka bata ranka a kan abunda abokin ka ya fada a kaina, tabbas kamar yadda ya fada cewa ni "yar bakin kasuwa ce,haka abun yake, duk da nake " yar towo-towo ban taba nema a gurin uban kowa sabuda haka babu wani mahalukin mutum da ya isa yazo har kofar gidanmu yace zai ci mun mutumchi in kyaleshi komai kudinshi da mulkinshi wallahi"

 

 

A nutse ta kalli Sarki! dake zaune cikin mota yana jin duk abunda take cewa kwata-kwata bai yi mamakin jin abunda tace, Sabuda tun da tafara magana ya gane ko wacece, tabbas muryarta baza ta taba bace masa ba.

Wayarshi ya ke dubawa amma hankalinshi na kanta, duk da cewa a kwai duhu a gurin hakan bai hanashi kare mata kallo ba, ta kasan idonshi.

 

 

 

 

Cikin isa da gadara Balaraba ta kalleshi shekeke! tace"Idan ka isa kai wani ne ka aje wayar muyi magana da kai, bari kaji wani abu, ni Sunana Balaraba Ayuba Tanko kamar yadda kasani, kana ji na ko"? tafada tana hura hanci, kana ta cigaba da cewa, "kai kuma in har ban mance ba Kai ne Almansor Sarki! dan Sarkin Almustapah, hakane ko ba haka ba"?

tafada cikin sigar tambaya gashi ta tsare shi da ido, tana tsaye babu fargabar komai a tattare da ita, Cikin jarumta tacigaba da cewa" Wallahi baka isa kazo har kofar gidanmu ka ci mun mutumci ba, domin ni bani na kira ka ba"

 

 

 

Tsit!!!! gurin yayi Maddibo yana mamakin jarumta irin ta Balaraba,ko shi da yake Namiji bazai iya tsayawa gaban Almansor    har ya gaya masa magana irin wannan ba, sabuda  kwarjinin da Allah yayi masa.

 

 

 

 

A tsanake ya dago kanshi fuskarshi a murtuke, ko da wasa bai kalli inda take tsaye ba, murya a cunkushe yace"in kagama abunda kake kashigo mutafi,in kuma baka gama ba zan wuce kawai, sai katawo" "Wai me yake Faruwa ne,? tsakaninku naga kamar a kwai abunda kuke boya min, gaskiya banji dadin irin yadda kuka gaisa da junanku ba, abun bai min dadi ba"

Maddibo ya fada yana kallon Balaraba,

 

Murmushi tayi mai cike da takaici tace"Yusuf abokinka dan rainin hankali ne, wallahi ni kuma kasan bana daukar raini, ni "yar talaka ce, amma ban nema gurin wani ba sabuda haka babu mutumin da ya isa ya zage ni ban rama ba"

 

 

A fusace!Sarki ya bude murfin motar Balaraba na tsaye jiki tayi taga-taga kamar zata fadi,cikin tsoro ta matsa gefe,gabanta yana dukan uku-uku, duk da cewar babu wadataccan haske a gurin sai hasken farin wata, hakan bai hanata hango tsantsan bacin rai a fuskarsa ba,

ganin fitowarsa yasa Buba Direba dake can gefe a tsaya yayi saurin karaso gurin yana baza babbar riga, ya na zuwa ya zube a gurin gami da dunkule hannunsa alamun jin jina, yace"ranka shi dade, a kwai abunda za'ai maka ne"

 

Cikin wani irin murya yace"Babu abunda za'ayi Buba koma inda kake"

 

Buba ya mike da sauri, kanshi a kasa yace"Allah shi taimaki Yarima Sarki Allah ya ja Zamanin ka"

 

 

 

Da Sauri Balaraba ta dauke kanta, ganin ya maido da hankalinshi kanta, ya zuba mata ido, kawai yana kallo, Lokaci guda ta nemi nutsuwar ta tarasa jikinta yayi mugun sanyi, ganin shi tayi yana matsowa kusa da ita a hankali, fuskarshi a murtuke! jinsa daf da ita yasa ta jingina da jikin motar a karo na biyu, kamshin turaransa duk yq cika mata hanci, sai sa ya tsaya daf da ita sosai har numfashinsu yana haduwa, sannan ya kafe ta da idanunsa masu tsananin kaifi,da kassara jikin duk wata "ya mace me ji da kanta

 

 

 

 

A nutse a bude bakinsa yace" Duk abunda kikayi a yanzu, bazan yi mamaki ba sabuda nasan zakiyi abunda yafi haka" Wani irin kamshi  taji yana futa daga bakinshi, lokacin da yake mata magana, kanta ta sunkuyar kasa kagabanta na lugede tunda take, babu wani da Namiji da ya taba kusantar ta kamar haka, kokari kawai take ta kwaci kanta, amma babu hali,sabuda yadda ya yi bake-bake a gurin,duk tsahonta ya rufe ta.

 

 

Yayi tsawan Minti biyu kafin ya kara cewa komai kana ya cigaba da cewa" Babu mamaki duba da yanayin unguwar da kika taso a ciki, babu abunda yake damunki sai tsan-tsan jahilci, da gidadan ci , da Zama cikin maza, a cikin kasuwa, shashashar yarinya kawai, zan koya miki hankali, zaki nuna min da me kike gadara, da kikewa kanki kallon ke wata aba ce"

Yana gama fadin wannan maganar ya tattaro miyau, a bakinshi ya dai-dai ci fuskarta  ya tofa mata, ya dora mata da wani banzan kallo yace"ina sauraron ki da duk hukuncin da zaki dauka  a kaina"

 

 

 

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[06/07, 13:37] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

       

       ∆∆∆∆∆∆  

        _*GIMBIYA BALARABA*_

        ∆∆∆∆∆∆

                 đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

             _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 

 

 

 

 

*MARUBCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

 

_*Zamani Writes Association*_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rahim```

 

 

 

 

 

 

 

 *Real Bintu Batula👄*

 

 

 

 

 

 

*🅿39*

 

 

 

 

 

 

 

 

Hannu kawai ya dagawa Buba Dreba da sauri ya karaso gurin, Cikin nutsuwa ya mai da idonshi kan Maddibo yace"Ni zan wuce, naga alamar baka da ranar tafiya, ka kawoni gurin yarinyar mara tarbiyya tana neman ta zageni"

 

 

Cikin daga murya Balaraba tace,"to in na zageka me zaka yimin karkari kasa a daure ni to ka dade baka sa an daureni ba,kuma zakasan wanda ka tofawa miyau dinka,wallahi sai na rama kaji na rantse"

Cikin hayaniya take fadar maganar,hawaye yana kokarin zubo mata,

    Babu zato taji wani sabon yawu a fuskarta ya kara tofa mata a karo na biyu, baice komai ba ya shige mota Buba Direba ya shiga ya kunna mota suka bace daga gurin.

 

Maddibo kamar ya dora hannu aka domin takaici da Sarki! ya kunsa masa, ya dauko shi domin yazo ya gyara masa lamarinsa gurin Balaraba, yazo ya bata daya goma bata gyaru ba,yanzu yaya zaiyi?

    Cikin muguwar kunya gami da jin nauyi ya kalli Balaraba tana goge hawayen bak'in ciki,tana sane ta matse kukan batayi a gabansa ba,sabuda kar yaga gazawar ta, sai bayan ya tafi hawaye ya balle mata,kamar me tunda take a duniya babu mahalukin da ya taba yi mata tozarci irin na yau,dole ne ma sai ta rama wulakanci da mutumin nan yayi mata.

     "Kiyi hakuri dan girman Allah,Balaraba, hakan ba halinshi bane, dana san abunda zai faru a tsakanin ku da ban gayyato shi ba,dama da yaya ya yarda zaizo din,kiyi hakuri dole zan dauki mataki akan haka,sabuda ke kanki kiba da daraja da mukami cikin zuciyata"

     Fuskarta goge da hannuwanta duk biyun,fuskarta a hade tace" Ya kuke dashi,ma'ana menene alakar ka da gidan Sarki"?

 

 

 

Tsayuwa ya gyara sosai yana fuskantar ta, yace"Ni Sunana Yusuf kamar yadda kika sani, amma Mutan gida na kirana da Maddibo asali sunan kakanmu a gare ni shiyasa suke kirana da haka, Sarki Almustaph Wan mahaifina ne, Waziru Zayyanu"

    Da sauri Balaraba ta dago kai tana kallonsa cikin mamaki!

Ya cigaba da cewa"Sarki! Almansor dan Uwana ne na jini kuma aminina abokina tare mukai karatu dashi tare muke rufewa mu kashe, amma halin kowan daga cikinmu daban yake da na dan uwansa, yana da saukin kai sosai in ka fuskance ki, amma bashi da hakuri ko kadan in ka tabashi, Mugun muskiline,sosai shiyasa nayi mamakin abunda ya hadaku haka kuke fadawa junanku bak'aken maganganu, da alama s kwai abunda ya taba hadaku a baya"

 

   Shiru tayi na minti biyu ta kalleshi a nutse tace"kana kallonshi yayi min wulakanci har da tofa min miyau bakace komai ba, dama ka dauko shine domin yazo ya wulakantani ko, babu komai, Nagode"

Tana gama fadar maganarta ta kama hanya ta barshi tsaye a gurin,tafiya take kamar zata kifa jin zuciyarta take kamar zata kone sabuda tsabar turiri da take mata, da kyar ta kai kanta gidansu,

   Maddibo ko binta da kallo yayi har ta bace masa, jikinsa a sanyaye ya futo da waya ya kira daya daga cikin Direbobin cikin gidan Maimartaba Sarki Almustaph ya fada masa unguwar da yake,yace yazo yanzu-yanzu ya dauke shi

Yana nan a tsaye a gurin, Sallau Direba ya karaso gurin Lokacin goma da rabi na dare,da sauri ya bude motar ya fito ya budewa Maddibo ya shiga suka bar unguwar,

   Salihu Yana tukin mota yana mamakin me ya kawo Maddibo irin wannan unguwar, ya gaza hakuri ya yace"ranka shi dade nace Allah yasa lafiya, ko wani abune ya faru a unguwar ne"

 

"Lafiya kalau, nazo gurin wani abokina ne"

 

 

"Masha Allah Yallabai dafatan ka same shi lafiya"?

 

" Alhmdulilahi"

Maddibo ya fada yana jin zuciyarsa babu dadi,Sarki!

ya cuce shi, yanzu yaya zai yi ya shawon kan Balaraba,

 

 

 

 

Yana zaune a ka tafaran Falonshi shi kadai kwal, in banda karar AC babu abunda kakeji, yana zaune a wata kujera me cin mutum daya daga shi sai wando 3Quetar kafarshi daya kan daya kana kallon irin zaman da yayi kasan na masu mulki ne, Sigari yake zuka yana lumshe ido,zuciyarsa in banda zafi da turiri babu abunda take,jira kawai yake Maddibo ya shigo suyi ko wacce-wacce,domin yana ji yana gani bazai bari ya auri yarinya kamar wannan mara tarbiya ba babu yadda za'ayi ta shigo ta bata musu zuri'a.

 

 

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[07/07, 12:38] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

       ∆∆∆∆∆∆  

        _*GIMBIYA BALARABA*_

        ∆∆∆∆∆∆

                 đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

             _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 

 

*MARUBCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

 

_*Zamani Writes Association*_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

_*DEDICATED*_

           _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

             

    

 

 

 

*®REAL BINTU BATULA👄*

 

 

 

 

*🅿40*

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rahim```

 

 

 

 

Maddibo ne ya shigo falon cikin sallama,amma kana kallon fuskarsa kasan yana cikin bacin rai, kujerar dake fuskantar sa ya zauna sosai ya murtuke fuskarsa, yace" yace "Yanzu  abunda kayi  mun ka kyauta kenan, haka mukayi da kai ? a kan zakaje ka bata min lamarina a gurin yarinyar nan"

 

Hannu ya daga masa a fusace! ya mike zaune sosai ya gyara zamansa, yana kashe guntuwar tabar dake hannunshi cikin wani karamin plete wanda ke aje kan wani karamin teble dake gabanshi,   a ya mutse yace "me nayi maka, zaka zo kana min wani shan kunu,ni ban yi magana ba,kai ne zakayi magana, haka kawai ina zama kazo ka dauke ni la kaini an ci mun mutunci, wannan bayi ba ne"

Ya karashe maganar yana huci!

 

 

 

Kasa Maddibo yayi da muryar shi ganin yadda Sarki! ya ke hayaniya, yasan halin bakar zuciyarsa yanzu sai ayi batacciya shi dashi,shiyasa ya kwantar da kai, dama kuma (Annabi muhammadu slw) yafada cewa idan mutum biyu na fada,to daya yayi saurin saukar da zuciyarsa gudun abunda zai je ya dawo,idan duk zucoyoyi biyu suka dauki zafi a lokaci guda,to shedan zai samu abunda yakeso,a kansu, Allah kasa mu dace

 

 

"Yanzu a matsayin ka na namiji mai hankali a kanta ya kamata ka biye mata duk abunda tayi, wannan ni kawai ka ciwa mutumci wallahi"

 

 

 

"Ok " Ok wato ni ba kaga abunda tayi min ba,yariya karama tana nema ta zageni, abunda babu wanda ya taba yimin shi a rayuwa ta ita tayi min sabuda samun gurin kazo ka nai min wata maganar banza, Ok zan dauki mataki akanta mai tsauri wallahi sai inga yadda za'ayi ka aureta"

 

 

 

"Duk abunda zakace sai dai kace" auran yarinyar nan kamar nayi nagama,kuma duk abunda tayi maka kai ne ka jawo tayi maka, me ye ruwanka da sana'arta da har zaka dunga kiranta da "yar towo-towo wannan ai cin fuska ne, kuma a sanina da kai nasan wannan dabi'ar ba taka bace,kawai ka ara ka yafa ne"

 

 

 

 

A harzuke! Yace"an kira ta da "yar towo-towo din karya akai mata ne, in tayi wasa ma da " yar tasha za'a kira ta watarana"

 

 

Zare ido!  Maddibo yayi cikin mamaki yace"wai me yake damunka ne, kai me yarinyar nan tayi maka da zafi haka"?

 

 

 

Tsaki! yayi ya koma ya kwanta cikin kujera yana lumshe ido zuciyarsa sai zafi take

 

 

 

Maddibo yace"dan Allah kafada min meye alakar ka da yarinyar nan Balaraba naga alama kun san juna,ganin yadda kuka shaida juna da wuri"

 

 

 

Minti biyar bece komai ba,farlon yayi tsit! bakajin komai sai karar AC kadan-kadan,

 

Cikin Ginshera yace"Babu wani abu da ya hadani da ita, hasali ma ban taba ganinta ba,sai ranar saukar su, wacce sukayi ta wattanin baya da suka wuce, wannan shine ganina da ita na farko, tun daga ranar ban kara dora idona a kanta ba sai yau"

 

 

 

Cikin mamaki Maddibo yace"kana nufin kace min itace yarinyar da kake fada min dazu muna mota"

 

 

 

"Kwarai kuwa"

yafada idanunshi a lumshe, ya cigaba da cewa"tun ganina da ita na farko naji na tsaneta sabuda dabi'ointa na lura yarinyar tana da girman kai sosai, kai kanka kasan halina bana shiri mutum mai girman kai da nuna shi wani ne"

 

 

 

Girgiza kai Maddibo yayi yana cigaba da sauraronsa

 

 

 

Ya cigaba da cewa"babban abunda ya burgeni da ita shine, lokacin da aka kirata cikin jama'a a lokacin bukin saukar alkur'anin nasu, ta bude taro da addu'a, lokacin ta bani sha'awa sosai jin tana futar da kira'a sosai, hakan yasa, Maimartaba yayi mata kyauta nima nayi mata tawa"

 

Shiru yayi yana jan numfashi tsawon minti biyu baice komai ba, yana dan girgiza kansa, yaja tsaki kadan ya bude idonsa sosai wanda suke lumshe yace"inda na kara tabbar da cewar yarinyar nan bata da kirki,lokacin da zata karbi kyautar daga hannuna, in kaga irin kallon da tayi min irin na wulakanci sai ka rike baki,kwata-kwata kanta na wani gefe bataso ta kalli fuskata, ina nan da hotonan in kana bukata zan dauko maka kagani kai ma zakayi mamaki"

 

 

 

Shiru Maddibo yayi kawai yana sauraronsa

 

 

Shi kuma ya cigaba da cewa"a lokacin abun ya bani mamaki, ganin lokacin dana futo daga gida itace ta farko gurin mikewa domin ta ganni, kamar yadda jama'a suke yi  amma yanzu gata a gabana tana dauke kai, kawai na shareta amma abunda tayi mun ya bani mamaki, sosai, naje na zauna, Shahid ya nuna min irin hotonan da yayi mana ni da ita, a lokacin na kara ganin, wukantacan kallon da ta din ga yi min,shi kuma Shahid cewa yake wai mun dace da ita sabuda yana ganin kamar "yar wani ce a garim nan kuma yarinyar tana da kyau sabuda haka kawai in shi ga,raina ya baci sosai da maganar da yayi min, wannan shine dalilin batawar mu dashi,domin da muka shiga gida, ya dame ni da zancan ta, fada mukayi dashi sosai, shine dalilin da yasa kaga baka ganshi ba kwana biyu, to wannan shine,abunda ya hadani da ita, sabuda haka,naji bana kaunarta kai kasan halina,in naki mutum to nakishi har abada wallahi"

 

 

 

 

A nutse Maddibo yace"ni dai yanzu hakuri nake baka, maganar nan ta wuce kai kayi laifi,itama tayi laifi, sabuda haka sai ayi hakuri a yafi juna,amma gaskiya banji dadin tofa mata miyau da kayi ba"

 

 

 

"Ok yanzu hakuri kakeso inje in bata kome"?

 

A'a ni bance ba,kawai ka kiyaye ko da nan gaba zaku hadu,tunda dai kasan babu abunda zai hanani auranta,sai dai idan mutuwa nayi"

 

 

"Wannan kuma abunda ya shafe ka ne, wannan yarinyar bana fata in sake ganinta,har abada kai ma ina me baka shawara ka janye maganar auranta,zai fi maka alkairi,kanemi yariyar arziki domin samawa " yayan ka Uwa ta gari"

 

 

 

Cikin Sanyi murya Maddibo yace"Addu'a kawai zaka taya ni dashi a kanta, amma maganar gaskiya Allah ya jarrabe ni da kaunar ta, kuma kai ne kake mata kallon mara tarbiya Balaraba yarinya ce mai hankali da sanin ya kamata, abunda yasa ake mata kallon mara tarbiya dalilin sana'ar ta ne kawai"

 

 

 

"Ok me yasa baza ka hanata talla a cikin kasuwa, in dai da gaske  kana sonta,sai ka hanata fita kawai ka killace ta guri guda,kai kanka kasan al'adar cikin gidan nan, abu mawuyaci ne su yarda ka aure ta"

 

 

 

 

"Ko kowa yaki yarda da al'amarin Maimar taba zai lamunce min,sabuda kasan halinshi da saukin kai, mutukar a kayi buncike a kanta, a gano babu wani aibu, a tattare da ita, ba zai hana kulluwar al'amarin ba"

 

 

 

"Ok Allah ya bada sa'a"

Abunda yace kenan, ya koma ya kwanta cikin kujera

 

Shiru falo yayi kowa yana sake-sake cikin zuciyarsa,daga bisani Maddibo ya mike ya nufi wani bedroom dake falon domin ya yi wanka yayi shirin bacci

 

 

 

Shi kuwa Sarki! da alama a falon zai kwana domin dai bashi da alamar tashi ya shiga bed din yana kwance yana dacin rai, tunani kawai yakeyi kan Balaraba, wane irin mataki zai dauka a kanta, domin duk abunda yayi mata bai wuce ba sai yaga karshen rashin kunyar ta, sai dai wannan ya zama dalilin batawarsu da Maddibo

 

 

 

 

*Comment*

*Vote anda  Share*

[07/07, 22:32] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

           ^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

            ^^^^^^^^^

                   đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 *®REAL BINTU BATULA👄*

 

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*Zamani Writes Association*_đŸ€đŸ»

 

 

 

_*DEDIGATED*_

           _*TO*_

```{ RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

*🅿41*

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rahim```

 

 

 

Har karfe biyu na dare yana zaune a falo yana kallace-kallace,Maddibo ko tuntuni yayi bacci babu abunda ya dame shi,  wani film yake kalla tashar Sky Moveis, sai da yaga karshen film din sannan ya mike a nutse ya kashe kayan kallon ya nufi bedroom din nasa, kai tsaye toilet ya shiga yayi wanka gami da dauro al'wala, ya futo a nutse ya shirya, jikinshi, ya fesa turare sannan ya shimfida dadduma ya tada sallahr nafila kamar yadda ya saba,duk daran duniya, yana nan zaune kan abun sallah har aka fara kiran sallahr asubahi, ya mike tsaye hannushi rike da carbi ya sanya wani takalmi mai uban kyau,jikinshi duk wani gashi-gashi kana kallon takalmin kasan irin na masu mulki ne, futa yayi daga dakin nasa ya nufi kofa, har yq bude zai futa,sai ya tuna da Maddibo ya koma da baya, ya bude bedroom din da yaga ya shiga jiya, Maddibo na kwance bacci yake sosai,

    Kiran sunanshi yayi"Maddibo"

  Bude ido yayi dake bashi da nauyin bacci

 

"Ka tashi kayi sallah ni na tafi massalaci, sai kafito"

 

Bai tsaya ya saurari abunda Maddibo zai ce ba kawai ya fuce daga dakin

 

Yana futa suka ci karo da Maimarta ba ya futo tare suka jera har zuwa massalacin,

 

 

Bayan an idar da sallah suka gaisa, jama'a kowa yana so su gaisa da Maimarta ba, da yake in an idar da Sallah ya kan zauna a massalanci su gaisa da Jama'a ko kuma in da akwai daurin aure ko radin suna duk nan za'a gabatar kafin ya koma gida ya futo fada

 

Sarki ya na zaune kusa dashi Waziri yazo suka gaisa da dan uwanshi, da alama akwai maganar da yake so yayi, ganin haka yasa mutane suka fara futa da dai-dai da dai-dai,  gurin ya rage daga Maimarta ba,sai Waziri da Sarki! Sai Maddibo dake gefe guda yana lazimi

 

Kanshi a kasa yace"Allah shi taimake, dama akwai maganar da nake so muyi da kai, tuntuni wallahi sai yau, nace,ko zamuyi maganar kawai a huta Allah shi taimake ka"

 

 

 

Maimarta ba,yana zaune hannushi rike da wani carbi mai kyau sai kalli yake,lazimi yake, kallon kanin nasa yake, yana nazarinsa sabuda yafi kowa sanin waye Waziri, duk da girmansa sam bai san abunda ya dace ba gashi bai iya yanke hukunci ba,shiyasa ko wani abu a kakawo gaban fada,ba ya wakiltashi a kai, gwara ya wakilta Sarki!sabuda yana yin abu cikin hikima da adalci,

 

Gyaran murya yayi yana nuna masa carbi,alamar ya daka ta tukkuna, ya cika carbin

 

 

Tsit!gurin yayi har sai da ya kammala, sannan ya dago kanshi cikin nutsuwa yace"Wace irin magana ce, wannan wacce ka boye ta ka kasa fada gashi kullum muna zama a fada, da tuni an warware ta"

 

 

 

"Allah shi gafarta maka, ai wannan maganar bata shafi fada, ba ta shafi cikin gida ne,"

 

 

Girgiza kai Maimarta ba yayi tsawon minti biyu bece komai ba,daga bisani ya kalli Waziri yace"ka sameni a shashen Fulani sai mu tattauna maganar, Allaj ya warware mana"

 

 

"To" To Masha Allah, Allah ya kara nisan kwana  ai magana ce ta alkairi nasan kuma kai ma zakaji dadin ta"

 

 

Murmushi Maimarta ba yayi ya mika masa hannu suka musabaha, yace"ai tunda naga kana farin ciki nasan maganar ta shafe ka"

 

"Kwarai kuwa"

Waziri yafada shima yana murmushi, amma fa ta ciki na ciki

 

 

Sarki! ne ya matso sosai kusa da mahaifin nasa, kanshi a kasa yace"barka da asubah"

Hannunshi Maimarta ba ya riko fuskarshi a sake yace"kai kayi min laifi, kwana biyu baka zuwa fada,bazan karbi gaisuwar ka b

 

 

Sosa kai yayi na sabo,yayi kasa da kanshi yana murmushi yace"tuba nake ranka shi dade, tunda mukaje can gwarzo na dawo bana jin dadi jikina,wallahi"

 

"Me yasa baka kawo uzirin ka ba"

 

 

Shiru yayi sai faman sosa kai yake

 

 

 

Waziri Zayyanu yace"wannan sharme ne, mu me yasa muke futowa fada, kullum kuma ai tare mukaje can Garzon ko ba haka ba ne, wannan yana nuna mana cewar sam baza ka iya wakiltar jama'a ba.

Cikin fada ya karashe maganar,

 

 

A nutse Sarki ya dago kai yana kallonshi,ya wani hade fuska sam ba ya so yana shiga lamarin shi,shi kuma yaki ya gane,

    Ganin yadda Sarki! ya hade fuska ne yasa Waziri saurin sunkyar da kansa, sabuda wani irin kwarjini da Allah yayi masa,

 

Wannan abun da Waziri yayi masa yasa ya fasa gaida shi,kawai ya dauke kanshi,jira kawai yake Maimarta ba ya mike shima ya samu damar tafiya,

 Maddibo ne ya karaso kusa da Maimarta ba ya gai dashi, ya gaida Mahaifin shi Waziri Zayyanu,

 

Maimarta ba ya mike cikin nutsuwa, suma suka mike suka biyo bayanshi lokacin gari ya soma washe wa, Wasu fadawa ne guda Uku tsaye bakin massalacin sune suka rufa musu baya,har sai da Maimar taba,ya shiga Shashenshi,sannan kowa yayi nasa ban garan,

 

 

 

Sai wajejen Goma da wani abu sannan Waziri ya samu Maimar taba,bangaran Fulani, nan suka zauna a ke bantaccan falo wanda yake zama domin sirri irin wannan,

 

 

 

Gyara zama yayi sosai yace"ranka ya dade magana ce daga Sarkin garin Yalwa, kasan tare mukayi karatu dashi,sosai har yanzu alakar mu dashi tanan, to shine yake neman wata alfarma a gare ka, wato ya naso ya hada jini da kai, wai yarinyar shi Azima tana son Auran Almansor,, shine ya aiko min da sako, a kan hakan, Allah shi tai makeka kaji abunda yake tafe dani"

Waziri ya kare maganar yana sauke ajiyar zuciya

Kanshi a kasa yana sauraron abunda Maimar taba zai ce

 

 

Minti biyu a tsakani, Maimarta ba yace"wannan ba hurumi na ba ne,domin bazan iya tilas ta Sarki! ya je ya nemi auran yarinyar nan ba, abunda zakayi kawai ka nemi shi kafada masa zan can, sannan yarinyar tazo ya gan ta in yaga tayi masa shikkenan,ni dan addu'a ne, sai a hada da Halisa kawai"

 

 

 

 

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[08/07, 13:24] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

           ^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

            ^^^^^^^^^

                   đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 *®REAL BINTU BATULA👄*

 

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*Zamani Writes Association*_đŸ€đŸ»

 

 

 

_*DEDIGATED*_

           _*TO*_

```{ RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

*🅿42*

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rahim```

 

 

 

 

Shiru Waziri Zayyanu yayi na minti biyu kana ya dago kanshi yana kallon Maimartaba yace"Allah shi taimake ka ina ganin yaron nan zai bamu kunya domin kasan halinshi da baudaddan ra'ayi, ina ganin kai ne zaka tilas tashi ya amunce da buk'atar mu,domin lokacin maganar Halisa ma haka muka dinga dauki ba dadi a kansa, Zai iya bujerewa bukatar mu, Azo a samu matsala game da dan gartakarmu da Sarkin Yalwa, Maimar taba Sarki Alkassim"

 

 

 

Cikin Mamaki Maimarta ba yake kallon Waziri jin abunda yace, gyaran murya yayi a nutse yace"maganar in tilas ta Sarki! ya nemi auran yarinyar da kake magana sam! bata taso ba, domin babu wanda zai zauna masa da ita,sai shi,idan na tilas tashi yaje ya dauko yarinyar mutane, yazo yayi mata rikon sakainar kashi,in ce me? ko kai kace me, abunda nakeso ka fahimta shine, ba wai ina biye wa yaron da duk abunda yake so ba, ina neman zaman lafiya da kwanciyar hankali, ko yau Sarki! yace yana so ya auri mace hudu ni mai daura masa aure ne,sabuda nasan da amuncewar sa kuma ba kowa ne zai zauna masa da suba sai shi, sabuda haka ka aika ai maka kiranshi,sai ka zube masa maganar in ya amunce shikkenan nima na amunce, Allah ya tabbatar da alkairi"

Ya karashe maganar yana duba wani karamin littafin husunul-musul wanda yake karantawa shi kullum da safe,

 

 

 

Jikin Waziri Sanyi kalau ya dago kansa yana kallon Maimartaba yayi tunanin zai samu nasara gurinshi sai yaga sab'anin haka, a gurinshi, jiki a sanyaye yace"duk yadda kace haka za'ayi Allah shi taimake ka zan sanya a kira min shi yanzu kafin mu zauna a fada"

 

 

Cikin sakin fuska Maimarta ba ya mika masa hannu sukai musabaha yace"masha Allah, ina sauraron ka duk yadda kukayi dashi sai ka same ni a shashenan domin tattauna maganar"

 

 

"Insha Allahu, A tashi lafiya"

Waziri yafada  kanshi a kasa ya futa daga dakin.

 

 

 

 

Sarki! kuwa ko da ya koma bangaran shi, kai tsaye bedroom dinshi ya nufa domin wani irin bacci ne yake damunshi,  jallabiyar dake jikinshi kawai ya cire    baya son zafi ko kadan, shiyasa kafin ya kwanta sai da yakara karfin AC  sabuda baya son ya kwanta zafi ya ta dashi daga bacci, Kwanciya yayi kan bed dinshi,wanda yaji shimfudu na alfarma, wayoyinshi ya kunna ya zube su a gefanshi, nan take sakkoni suka da dinga shigowa, ko daya bai duba ba, kawai yana kwance ya zubawa rufin dakin ido, daka gani akwai abunda yake damun zuciyarshi, wanda shi kadai ne ya sanshi sai kuma mahallincin shi, wannan abu na damunshi, sosai in dai zai rufe idonshi da nufin yin bacci,sai Allah ya nuna masa wata mata, tana kuka sosai gata a durkushe a gabanshi ita da wata yarinya matashi budurwa itama tana kuka suna rokanshi wani abu,wanda ya kasa fahimtar menene shi,abun mamaki matar in ta tashi tafiya,cikin mafarkin sai ta zo ta hada hannunshi da wannan matashiyar yarinyar tace"ga amana na baka, daga haka sai ta tafi har ya daina ganinta, ita kuma wannan matashiyar yarinyar kuka take sosai tana kokarin kwace hannuta daga nasa, abun mamaki shi kuma sai ya rike hannun tamau! yaki saki a haka yake farkawa, in ya tashi yai taso ya tunano fuskar wannan matashiyar yarinyar amma sai ya kasa haka zai bi hannushi da kallo wanda ya rike nata, ya kan dade bai dai na jin dumin hannuta a nasa ba,

   Wannan mafarki yana damun rayuwar shi a kalla ya kai shekara biyar yana wannan mafarki, babu wanda ya sani da gashi sai mahaliccin sa, ko mahaifiyar shi bata sani ba,

 

Wayarshi ce ta dame shi da kara, a nutse ya  dauka yana dubawa Halisa ce,

kamar ya share ta,sai wata zuciyar tace"ka dauka kaji wane shirme zatai maka,

Cikin yanayin muryarshi yace"Assalamu alaikum"

 

Wata irin ajiyar zuciya Halisa tayi, cikin shagwaba tace"Habibi ka tashi lafiya"?

 

"Lafiya,kefa"?

 

" Nima lafiya lou, sai dai tunanin ka da ya uzzira min"

Halisa tafada tana mutso-mutso kan bed din ta, itafa ko muryar shi taji sai ta shiga wani hali, ballan tana ta kusance shi, ji take kamar ta rungume shi ta huta da abunda take ji a kansa

 

 

Muryar shi kasa-kasa yace"bacci zanyi yanzu in kina da abun fada ki fada ko na kashe waya ta"

 

 

 

Jin yanda yayi kasa da murya ya kara gigitata, makale wayar tayi a kunnen ta tace"cewa nayi fa gani ina kewar ka ina ma ina kusa da kai da nayi maka tausa"

 

 

Shiru yayi mata,kawai ranshi ya soma baci da shirmen da tafara yi masa, shiyasa suke fada kullum,sabuda shi ya tsani mace mara kamun kai

 

 

Shiru da taji yasa ta kara kwantar da murya tace"ka ga babu abunda nake yanzu nima a kwance nake,bacci yaki zuwa sabuda tunanin ka,ko inzo ne, in tayaka bacci"

 

 

 

"Gyaran Murya yayi yana lumshe ido yace"  Ke wai yaushe zakiyi hankali ne "?    Shiru tayi gabanta yana faduwa sabuda tasan halin dizginsa

 

 

Tsaki!yaja kasa-kasa ya cigaba da cewa

"wannan shirmen da kike sam baya burge ni, ni nafison ki kama kanki, ki zama cikakkiyar mace, sabuda rashin hankali ke yanzu in nace kizo sai kizo,Ok toum in kinzo kiyi min me"?

Yafada cikin sigar tambaya

 

 

Shiru tayi kawai takasa cewa komai

 

 

" Ba magana nake miki ba"

Yafada a fusace! sabuda ya tsani ya na magana ana shareshi

 

Bakinta na rawa tace"yi hakuri,ni ai na dauka, babu komai tunda auran juna zamuyi"

 

 

Jin abunda tace kawai sai ya kashe wayar ranshi a bace, yace"Shashashar Yarinya kawai, aje wayar yayi gefan shi, ya lumshe ido yana tasbihi cikin zuciyar shi, har bacci ya dauke shi

 

 

 

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[09/07, 13:33] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

           ^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

            ^^^^^^^^^

                   đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 *®REAL BINTU BATULA👄*

 

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*Zamani Writes Association*_đŸ€đŸ»

 

 

 

_*DEDIGATED*_

           _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

*🅿43*

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rahim```

 

 

 

 

Wannan,  mafarkin da yake ne, ya tasheshi firgigit! ya mike zaune sai hada uban gumi yake, na yau mafarkin yafi na kullum domin kukan da wannan matashiyar yariyar take yafi na ko yaushe, tunda yake ganinsu cikin mafarkin bai ta ba yi musu magana sai yau Allah ya bashi iko, bayan Mahaifiyar yarinyar ta tafi ganin kukan da matashiyar yariyar take yasa ya bude baki yace"tayi shiru, tabarwa Allah komai zai yi mata magani, duk da maganar da yayi hakan bai sa tayi shiru ba, sai ya mike da niyar tafiya sabuda cikin mafarkin kukan ta ya dameshi yana taba masa zuciya, wannan karon ma hannunta ya rike cikin nasa yana janta tana turjewa, sai ya daka mata wata irin tsawa, wacce tasa ta bude ido da sauri, tana kallonshi, fuskar da ya gani ce ta sashi furgita ya farka daga baccin hankalinshi a tashe,

 

 

Ya jima Zaune a gefan gado yana mamakin yariyar da yagi cikin mafarkinsa, sosai yake mamakin meye alakar shi da wannan mara kunyar yarinyar wato budurwar Maddibo, dama ita ce yake gani cikin mafarkin tsawon shekara biyar, Allah bai bashi ikon ganin fuskar ta ba sai yau, kusan minti ashirin yana zaune yana saka wa da kwancewa, nan Maddobo ya shigo ya same shi, hannushi dafe da kai, sai kace wani mai ciwon kai,

 

 

Kanshi ya tsaya yana gyara link din rigarshi yace"Lafiya tun dazu nake kiran wayarka shiru"

 

 

 

"Bacci nake"

abunda yace kenan

 

Cikin Nazari Maddibo yace"Bacci fa kace"?

 

 

dago kansa yayi yana masa wani irin kallo, a ya mutse yace"Karya nake kenen"

 

 

Murmushi Maddibo yayi yace"mai da wukar malam, ni zani gurin Gimbiya in ci abunci, ko injiraka ne"

 

 

 

A hasale yace"wallahi zamuyi fada dakai, kar ka kara sakoni cikin maganar ka da wannan yarinyar in kana son kanka da arziki, kai daka ga zaka iya kaje kayi, amma ni, kasan nafi karfin inci kazantar ta"

 

 

 

Daga kafada Maddibo yayi alamun abunda ya fada bai dame shi ba,yace"Ni kam zanci har da side kwano, sai na dawo"

 

 

Banza yayi masa har ya fuce daga dakin.

 

 

Maddibo na futa wasu bayi suka shigo Maza biyu mata biyu

 

 

Wani irin kallo ya watsa musu cikin tsawa yace"wane shegen ne yace ku shigo min daki,"?

 

 

Kasa sukayi da kansu dukkaninsu

 

 

Cikin tsawa ya cigaba da cewa"ni kuturo ne da komai sai kuce sai kunyi min, nace bana so, nace bana so, amma sabuda tsabar naci! kullum sai kunshigo min daki da sassafe! kufuce ku bani guri"

yafada cikin tsawa!

 

 

Zubewa sukai gabansa, kamar wasu masu neman gafara, wannan abun ya kara tunzura masa zuciya, a zafafe! yace"me kuma zanyi muku,, bakuji abunda nace ba?

 

 

Mariya ita ce baiwar shi wacce take kula da gyaran bangaran shi da da kai masa abunci da daukewa in ya kammala goge-goge da share-share,  ita ce tace

"Ranka ya dade don Allah kayi hakuri ka bari munai maka hidima a shashen ka, domin aikin mu ne,hakan ka gafarce mu, ranka ya dade, zamu maka gyare-gyare ne"

 

 

Wani kallo ya watsa mata, wanda yasa ta sunkuyar da kai kasa, babu shiri,domin idanunsa duka ya ware mata,tunda take dashi ba ta taba ganin ya bude idonshi haka ba, kullum a lumshe suke, ko kallon ka yake, baya budewa sosai kasa-kasa yake kallo.

 

 

Yace"kece Sarkin iyayi ko, wacce tafi kowa iyawa, kowa yayi shiru zaki damu mutane da magiya,Ok ku fuce min a daki, tukkuna inyi abunda zanyi in futa,sai kuyi abunda zakuyi"

Ya karashe maganar yana hararasu,sai kace su sukai masa laifi

 

Daya bayan daya suka fuce daga dakin, suka tsaitsaya a falo suna gulmarsa, kasa-kasa Mariya tace"yau da alama a kwai abunda yake damun Yallabai wannan masifa haka"

 

Wacce take kusa da ita tace"kuma hakan ba halinsa bane,shi dai kyaleshi da muskilanci gami da shariya"

 

Mariya tace"gaskiya akwai wani abu dake damunshi"

Haka dai sukayi cirko-cirko a falo suna magana kasa-kasa, gefe kuma suna jiram fitowarsa,domin su fara aikinsu

 

 

 

 

Yana kokarin mikewa ne  daya daga cikin wayoyinshi ta hau gyara, ko kallonta bai yi ba balle ya dauka, toilet ya nufa, cikin zuciyarsa sai mita yake, ya tsani kamarshi azo ace sai an masa komai, yana da lafiya da kuzari Allah ya hore masa sai ya tsaya an masa bauta, shi sai yake ganin wannan cutar kai ne, a rayuwar shi ya  tsani yaga ana wani jin tsoransa,kamar ayi masa sujjada, kamar dai yadda suke masa, shiyasa kullum cikin yi musu tsawa!yake, baya son wannan rawar jikin da suke masa, Sarki!bayason raini ko kadan, shiyasa abunda Balaraba tayi masa ya kasa bacewa a zuciyarsa,dalili kuwa shine tunda yake a rayuwarsa babu mahalukin da ya taba yi mishi abunda tayi

 

Toilet dinshi abun kallo ne, sosai in ka shiga baza kayi sha'awar futowa ba,domin har wani sanyi-sanyi yake,duk abunda mutum yake bukata a kwai a ciki

 

Jaccuzi kuwa har biyu ne a ciki, sabuda girman toilet din, a nutse ya shiga ya hada sabulai na mussaman yayi wanka, ya futo ya nannade jikinshi da towol ya dauki karami yana goge kanshi,

 

 

 

Kai tsaye dressing mirrow dinshi ya nufa, ya tsaya jikinshi a fara shafa mayukanshi masu kyau da tsada, ya taje sumarshi sai kyalli take,itama ya sanya mata mayuka, Kwantaccan gashin dake fuskarshi yake gyarawa sosai ya gyara Sajanshi ya tsaida gemunshi iya inda yake so, sai fuskar tafito tayi wani mugun kyau da haske,kalar fatarshi ta fito sosai,annuri ne kawai yake futa a fuskarshi,

 

Wayarshi ce take kara alamun kira,bai saurare ta ba,sai da ya futo da kayan da zai sanya,sannan ya zauna gefan gadon ya dauki wayar yana dubawa a nutse.

 

 

 Khalifa sunan da ya gani yana yawo kan fuskar wayar,

 

Khalifa dai yaron Waziri ne, kani ga Maddibo, kenan yaron bashi da kunya ko kadan shiyasa basa shiri da Sarki! ko kadan yanzu ma yayi mamakin ganin kiranshi, sai da yagama yangarshi sannan ya dauko,

 

"Assalamu alaikum"

 

 

Daga daya bangaran Khalifa yace"Yallabai barka da asubah"

 

"Barka kadai, Khalifa ya kake"?

 

" Lafiya yallabai, dama Baba  Waziri ne yace kazo yana neman ka"

 

 

Shiru yayi na tsawon minti uku,kana yace"Ok ya fita fada ko yana gida"?

 

 

"Yana gida"

 

"Ganinan zuwa"

Yafada yana kokarin kashe wayar,

 

 

Mamaki yake  kiran me Waziri yake masa Allah yasa alkairi ne,

 

 

Tsaf ya shirya cikin wani uban yadin filtex me ruwan sararin samaniya, an mishi dinki irin na sarauta sosai yayi masa kyau, kafarshi saye da takalmi irin nasu shima kalar kayan jikinshi, wayoyin shi ya diba ya futa daga dakin, suna tsaye sukaji futowarsa, da sauri sukayi kasa da kansu, ko kallonsu bai yi ba ya fuce daga falo, Wasu bayi maza su biyu suna tsaye bakin kofa,suka zube suna kwasar gaisuwa, yana tafiya yake amsawa, suka mike da sauri suka rufa masa baya

 

Duk wasu bayin dake kaiwa da kawowa a filin gurin tsayawa sukai suna gaidashi, har sai da ya wuce sannan kowa ya koma bakin aikinsa,

 

 

*Ikon Allah Sarauta da mulki sai mai shi*😇

 

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[10/07, 05:14] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

           ^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

            ^^^^^^^^^

                   đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 *®REAL BINTU BATULA👄*

 

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*Zamani Writes Association*_đŸ€đŸ»

 

 

 

_*DEDIGATED*_

           _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

*🅿44*

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rahim```

 

 

 

 

 

 Waziri na zaune a falo tare da uwar gidanshi, Hajiya Rahamatu, wato mahaifiyar su Modibbo, wacce suke kira da Mama, macace mai mutukar kirki da maida dan wani nata, tana da kara da kawaici,da kauda kai a kan abunda babu ruwanta, shiyasa kullum cikin tsawatar da "yayanta take, a kan su lura da duniya mussaman in taga suna jiji da kai da nuna su " yayan sarauta ne, kullum takance musu,babu wanda Allah ya ware tsakanin tsakin bayinsa,me mulki ko mara mulki talaka ko me kudi,sai wanda yafi bauta masa.

    Wani lokacin idan Waziri yana wani abun na son zuciya takan iya bakin kokarinta gurin ganin ta hanashi, haka zasuyi ta rigima dashi, Amaryar shi ce,halinsu yazo daya,duk wasu abubuwan da yake yi ita take ingizashi,yake da girmanshi da komai,bashi da gaskiya kullum cikin shirya manakisa yake.

 

 

A nutse Sarki! yayi sallama cikin falo,Mama ta amsa masa cikin sakin fuska, tana gyara masa gurin zama, fuskar sa ya saki sosai ya je ya zauna kasan kafafun ta kanshi a kasa yace"barka da asubah Mama"

 

 

Kanshi ta shafa tace"barka kadai, Almansor,yau sharabon da in sanya ka a idona"

 

 

Sosa kansa yayi irin na sabo yace"Yace Mama Ayi hakuri, a gafarce ni"

 

Dariya tayi kawai tace"ai nasan hali baka son mutane dama"

 

 

"Mama a dane wannan"

yafada yana sosa kansa

 

 

Wani irin kallo Waziri yayi masa yace"kema ai da neman magana kike wannan yaron da baya son jama'a ko kin manta da halinshi, wai kuma a haka akeso a bashi mulki"

 

 

 

Shiru Mama tayi jin abunda mijin nata yace, tasan yanzu zai kauce hanya

 

 

Girgiza kai kawai Sarki! yayi ya dago kanshi fuskarshi babu yabo babu fallasa yace"Khalifa ya kirani a waya dazu yace kana nema"

 

 

 

"Kwarai kuwa"

Waziri yafada yana gyara zamansa kan kujera

 

 

"To Masha Allah, ina sauraron ka"

 

 

Mikewa Mama tayi ta bar gurin dan ta barsu su sake suyi maganarsu amma tana mamakin abunda zai sa Waziri kiran Sarki! sabuda tasan basa jituwa ko kadan.

 

 

 

"Wato kana jina ko"?

 

 

"ina jin ka"

Yafada kai tsaye!

 

 

"Kasan abokina Maimarta ba Sarkin Yalwa, ko?   Cikin nutsuwa yace" Eh nasanshi "    "To shine ya ke neman alfarma a gurina da gurinka,  a kan yana so ka auri yarinyar shi Azima, ta nuna tana sonka, to shine na nake neman alfarma a gurinka, a matsayi na na Mahaifinka, kar ka bani kunya,  a gurin abokina kaje ka nemi yarinyar nan, insha Allahu baka da matsala da ita, yarinya ce nutsatstsiya"

 

 

 

Kanshi na kasa tsawon minti biyar bece komai ba, daga bisani ya dago kanshi, a nutse yace" Zanyi tunani akai"

 

 

"Zakayi tunani akai"?

Waziri ya maimaita maganar da yayi cikin sigar tambaya,

 

 

"Fuskarshi ya hade sosai ya dago kanshi yana kallon Waziri, yace" Allah ya taimake ka, wannan maganar da kazo min da ita tayi min tsauri dayawa dole ne inyi nazari a kanta, kabani nan da kwana biyu,duk abunda na yanke zan maka magana"

 

 

 

Kwantar da kai Waziri yayi sabuda yana nema, yace"A'a baza muyi haka da kai ba, Magajin Sarki, ka fada min kawai yanzu, wannan abun me sauki ne, a gurinka, domin kasan ko ba yau ba, dole zaka hada mata hudu,sabuda muna saka ran zaka gaji kujerar mahaifin ka"

 

 

Wadannan maganganun da Waziri yayi sun bashi mutukar mamaki, wai yau da bakinshi yake kiranshi da Magajin Sarki, lallai akwai wani abu dake zuciyar shi wanda yake boye wa,   Amma sabuda ya kyaleshi ya tafi yasa yace"Shikkenan na amunce da, Allah ya shige mana gaba,

 

 

Murmushi Waziri yayi yace"Allah yayi maka albarka Magajin Sarki, in sha Allahu zakaji dadin auran yarinyar, kaga sai a hada da Halisa ko"

 

 

"Duk abunda kuka yanke dai-dai ne a gurina"

yafada yana kokarin mikewa da niyar tafiya

 

 

Hannu ya mika masa suka yi sallama, Waziri sai shi masa albarka yakeyi, sai murna yake kamar ya ari baki, nan Sarki! ya barshi, cikin farin cikin amuncewar sa

 

 

 

******

 

*Balaraba* kuwa kwana tayi tana kuka a ranar kamar ranta zai futa, taji ciwon wulakancin da Sarki! yayi mata, wai ita yake kira "yar towo-towo " yar bakin kasuwa, tayi kukan rashin iyaye, tasan duk rashin su ne ya jawo mata wannan wulakancin, gashi tana shigowa gidan Lantana ta tare ta tana zagi, wai sai ta futo mata da kudin da ta samo, in ba haka ba, zata shiga gidan ba, nan su  Shamsiyya suka dinga ihu! suna dariya, tafi minti ashirin a tsaye a soro sai da Walidi ya shigo gidan, ya ga abunda yake faruwa,ya zage Lantana tas! har Uwa  bai bari ba duk ya hada ya dinga dura musu ashar, ya rike hannun Balaraba suka shiga ciki,  Su Sadiya da Usuman suna zaune, a tsakiyar dakin sai kuka sukeyi, babu haske,ga uban sauro sai tashi yake, a dakin, haka ta shiga takamasu ta rungume tana kuka, har sukayi bacci, kwata-kwata zaman gidan ya ishe ta, dole ne ta samawa kanta ma futa.

 Sam,  bata yi wani baccin arziki ba, da ta rufe ido sai ta hango shi lokacin da yake tofa mata miyau din bakinshi, bata jin bacin ran abunda Lantana tayi kamar wannan, sabuda tasaba, dashi,tunani kawai take, wace irin hanya zata bi ta rama abunda yai mata,

 

 

Tunda tayi sallahr asubah bata koma ba, tana zsune kan abun sallah tana lazimi, bacci yana fuxgar ta, kadan-kadan, ta jiyo muryar Lantana tana kwala mata kira,

"Balaraba, ke Balaraba"

Lantana tafada tana dukan kofar dakin kamar zata karya ta.

 

Tana jin ta tayi shiru har sai da ta ha'da carbi sannan ta mike a nutse taje ta bude kofar,

 

 

Lantana tayi mata wani kaskantaccan kallo, tace"au! kwana kikayi kina kuka naga idanunki sunyi jajazir!" tafada tana rike ha6a cikin mamaki!

 

 

"Me zanyi miki ki ke buga min kofa"

tafada kamar bata san abunda ya kawo ta ba,

 

 

"Au! tambaya ta kike me zaki min"?

Lantana tafada cikin mamaki! " to kudin gasara zaki bani"  ta karashe maganar tana gyara daurin zaninta

 

 

"Lantana yau bani da kudi, sai gobe"

 

"Baki isa ba wallahi"

Tafada cikin hayaniya da masifa

 

 

Rantsuwar da tayi ya mutukar bawa Balaraba,mamaki, ita ko yau batayi niyya bayar wa za taga inda wanda ya isa yasa ta bayar

 

 

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[11/07, 05:47] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

           ^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

            ^^^^^^^^^

                   đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 *®REAL BINTU BATULA👄*

 

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*Zamani Writes Association*_đŸ€đŸ»

 

 

 

_*DEDIGATED*_

           _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

*🅿45*

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rahim```

 

 

Kawu Sallau ne ya futo daga daki, hannushi rike da wata karamar redio yana kokarin dai-dai ta tasha, dake safiya ce , yana so ya saurari labarai, kofar dakin Balaraba ya nufa  inda Lantana take tsaye tana karewa Balaraba zagi, tace"Jiya kinfi awa daya a waje,kuma ance me mota ne mutumin da yazo gurin ki amma sabuda kin raina mana  hankali shine zakice baza ki bamu kudin gasara ba to ko  sai kin bayar sannan zaki futa daga gidanan kinji na gaya miki"

    Jin abunda Lantana tace  yasa Sallau saurin karasowa gurin yana rage karar redio dake hannushi yace"Lantana wai me yake faruwa ne, tun daga daki nake jiyo hayaniyar ki"

 

 

Gyara tsawuyar ta tayi tace"Yo in banda sharri irin na wannan yarinyar, da tsabar mugun abu, wai yau bata da kudin gasara wanda take bamu muna siya muna karyawa dashi, jiya fa Wani me mota ne yazo zance gurinta, ta dade a waje,kafin ta shigo gida"

 

 

Walidi ne ya bude kofar bandaki ya fito,hannushi rike da bota, da alama sai yanzu zai yi sallar asubah, a jiye botar yayi nan bakin rijiya ya nufi gurin da suke, ya kalli Lantana yana wani ciccije baki yace" Yawa! kike fa Lantana, Ehh wannan da kuke gani fa tafi karfin wulakanci a gurinku, kune mutsiya ta daga ke har ita Uwa!din, kudin gasarar banza da wofi, kullum da take baku kudin ai babu wanda ya taba gode mata, sai dai kullum ku bita da zagi! To wallahi kukayi wasa zan k'ona kudin da aka bani in baku, banzaye fattararru kawai!!

ya karashe maganar yana wani tangadi kamar zai buge Lantanar, da ssuri ta matsa gefe guda, Cikin mamaki tace"Ni kake zagi ko Walidi"

 

 

"Kinga Lantana"!

Walidi yafada yana nuna ta da yatsa

Ya cigaba da cewa" nifa a kan wannan zan iya kaddamar miki, gwara ki kauce kawai, Eh! ni dai na fada miki"

 

Shiru Lantana tayi tana zare ido, shi kuwa Sallau ko a jikinsa, duk irin rashin mutumci da Walidi yakewa mahaifiyar sa, a cewarsa ai itace ta jawo wa kanta,

   Washe baki yayi yana kallon Balaraba yace" "yar Albarka, sannu da kokari, kinji ko ki cigaba da hakuri damu, ni dai nasan ban miki wani laifi ba, sabuda haka zan tafi gurin me shayi, yanzu"

   Balaraba ta gane munufar sa, sabuda haka sai tace" Kawu kai ma yau sai dai kayi hakuri, domin bani da kudin da zan baka yau da gobe kayan Allah"

 

 

Murtuke fuska yayi, ya hau zuba mata ruwan ashar, yace"wato nima karyar zakiyi min kenan, in da gaske kike ki matsa in shiga cikin dakin naki in duba kaji ni da ja'irar yarinya ko"

Ya karashe maganar yana gyara babbar rigar shi

 

"Haba Baba, wannan ba yi bane, kai yanzu a kace ka shiga dakin sai ka shiga,gaskiya kai Lusari ne wallahi" Hahahahaha

Walidi ya karashe maganar yana kyalkyala dariya, ya zira hannu cikin aljihun wandon dake jikinshi wanda yayi dau'da sosai duk jirwaye, gudar dubu daya ya futo da ita ya mika masa yana cigaba da dariya kamar wani mahaukaci, ganin  Walidi ya futo da Dubu daya sabuwa dal! ya bawa Sallau yasa jikin Lantana kyarma, washe baki tayi ta matso kusa da Walidi, tace"Ashe da gaske ka keyi yaron nan, ai nace dama jarina yayi kasa, kaga yau sai in shiga kasuwa in siyo kuli-kuli, Allah dai yayi maka albarka d'an nan

 

Walidi yasa dariya yana nuna Lantana da hannunshi yace"ke dai Lantana in kika ga kudi duk sai ki shiririce, dube ki don Allah"

yafada yana dariya, ya cigaba da cewa"wannan kudin sun futo daga gurin mijin Balaraba insha'Allah in kin kwantar da kai,kullum zan dinga baki dari biyu, yanzu dai ga dubu daya ke ma sai kira jari kamar yadda kika fada,

 

Warce wa tayi daga hannusa, tana washe baki tace"da gaske kake dan nan"?

 

 

"Da gaske nake mana,ke dai ki dai na takurawa Balaraba a gidan nan"

 

"Yo ni dama ai bana takura mata,sai kaje ka nemi masu takura mata, to kaj!  in kaji ina mata fada to fadan gaskiya ne, ko ba haka bane Balaraba"

tafada tana kallonta

Girgiza kai kawai Balaraba tayi tana kokarin komawa daki

 

Jin hayaniya tayi yawa a tsakar gida yasa Uwa! futowa daga dakinta, yau ta makara bata tashi da wuri ba dalili jiya sun dade ita dasu Shamsiyya,da Maburuka suna lissafin kudi, har Sallau ya dawo daga mahadarsu ya taddasu suna lissafi,yayi-yayi su bashi dari biyu Uwa! ta hana shi "yayan nashi kuwa sai dariya suke masa, Shamsiyya ce me cewa" Baba zuciyar ka ta mutu, wallahi Allah ya wadaran Halinka" nan ya mike ya barsu ya shige daki yana ta zaginsu,su kuma sai dariya suke masa.

 

Ganin kudi tayi hannun mijinta cikin mamaki, ta bi bayanshi ganin yana kokarin futa daga gidan, yasa ta kwala masa kira"Sallau"

 

Da sauri ya juyo yana hararar ta, ta karaso gurin kanta babu dankwali daga ita sai daurin kirji tace"me nake gani a hannun ka kamar gudar dubu daya"

 

Da sauri ya zira ta a aljuhu yace"Kwarai kuwa menene"?

 

"Kamar yaya menene, a gidan ubanwa ka samu kudi,haka kuma kake kokarin futa batare da ka bamu kudin karin kummalo ba,tunda Allah yasa ka samu"

 

 

Banza yayi mata kawai ya kama hanya zai futa a karo na biyu, da sauri ta je ta tari gabanshi, tana hura hanci tace"karya kake wallahi, ka bani ko yanzu in tara maka mutane,domin na gaji da muguntar ka, wato sai da kasamu kudin kaje kaci banza kaci wofi,to baza ta sabuba,wai bunda a ruwa"

Tafada tana dukan cinyar ta

 

 

Sanin halin jarabar Uwa!yasa Sallau kallo inda Walidi yake tsaye yace"Zo kara bani da wannan mutsiyaciyar Uwar taka, mayyar kudi"

 

 

Dariya Walidi yake sosai ya karaso gurin yana wata irin tafiya yace"ai duk halinku daya da ita Baba, dubu daya ya ciro ya mika mata yace"kema gashinan kici albarkacin Balaraba"

  Da sauri Uwa ta karbi kudin daga hannun Walidi tace"karya kake inci albarkacin wata banza yarinya, wallahi"

 

"Ke dai kika sani, zaki iya yaga kudin yanzu, ai tunda kince karya ne"

 

Tafiyar ta tayi tana surutai gami da fadar bakaken magan-ganu ga Balaraba,

  Sallau ma fucewa yayi ya bar gidan, Lokacin Balaraba ta samu ta futo ta shiga bandaki, domin tayi wanka ganin rana tafara yi,

jan ruwa take a rijiya, Maburuka ta futo hannuta rike da bokiti, da kutto wande ke dauke da sabulu da soso, daga ita sai daurin kirji,wani irin kallo ta watsawa Balaraba, taja tsaki, yaje ta dangwarar da bokitin saura kadan ya fada kafar Balaraba, tayi saurin kaucewa, kawai bata saurare ta ba, ta dauki ruwan da taja cikin wani bokiti irin na roba ta shiga bandaki, nan ta jiyo Mabaruka na cewa, banza kawai, kina dauke da najasa kina shigarwa mutane,ban daki dole ne ma in kin futo in wanke bandakin domin bazan je in kwashi cuta ba"

 

 

Ranta ya ba'ci sosai jin abunda Marubuka take cewa a kanta, sauri-sauri take ta futo daga bandakin taci Uwarta, ta lura idan bata, tasar musu tsaye ba,zasu hanata shan ruwa a gidan,

Mabaruka na zaune a kan rijiya tana wake-wake cikin rashin kamun kai,

Balaraba ta futo daga bandakin, tayi kamar zata wuce, sai tai sauri ta dawo da baya,ta damki! wuyan Maburuka ta rike tamau, ta jawota sosai suka matsa daga jikin rijiyar, had'a ta da bango tayi ta makure ta sosai tace"wa kike zagi ne, mara kunya"

 

Kakari! Mabaruka take sosai tana son tayi magana takasa, idanunta sunyi jajazir,

Wani wawan mari Balaraba ta tsinka mata,wanda yasa jinta da ganin ta suka dauke na wucin gadi, tace"Ke baki kira kanki da najasa ba, zaki kira wani, bari kiji dan uwarki, duk irin iskancin da kikeyi a unguwar nan nasani, shegiya me bakin uwa, duk sharrin ku sai ya koma kanku,ni nafi karfin ku wallahi"

Hawaye ne, kawai yake zuba a idanun Mabaruka, jikinta sai kyarma! yake yau ta tsorata da Balaraba sosai,ashe haka take da karfi,sai kace me aljanu,

Cikin ikon Allah har yanzu babu wanda ya futo daga daki cikin mutan gida,

 

Kasa da muryar ta tayi tace"bani hakuri dan Uwarki ko in cire miki makogwaro yanzu-yanzu

 

 

Bakinta na rawa tace"Allah ya baki hakuri"

 

Sakinta tayi tana hararar ta tace"karyar rashin kunya kike yi yarinya,wallahi kika duk ranar da kika kara zagina sai naci miki uwa"!

 

Shiru Mabaruka tayi tana kallonta Har ta shige dakinta,

 

 

Cikin sauri-sauri take shiryawa ta tashi su Sadiya da Shamsu ta shiryasu cikin uniporm kamar kullum,  ruwan tea ta dafa musu,dake tanada kayan shayi a dakinta nan ta hada musu suka karya,suka futo a tare,a gurguje ta leka dakin Iya suka gaisa, tace"yau baki futo ba"

 

 

"Wallahi na tashi da zazzabi ne, tun dazu nake jin hayaniya a gidan, lafiya in ce ko"?

 

 

"Lafiya kalau"

Balaraba tafada ta cigaba da cewa" amma kin sha magani ko"?

 

 

"Ai cikin dare zazzabin ya rufe ni"

Iya tafada tana kara rufe jikinta,

 

"Insha Allahu zandawo da wuri sai muje chamis a duba ki"

 

"To sai kin dawo,kinji Allah yayi miki albarka"

 

 

"Ameen Iya nagode, in su Sadiya sundawo su zauna a gurin ki tunda babu isilamiyya yau"

 

 

"To shikkenan sai kin dawo"

 

 

 

Balaraba na futa taci karo da Walidi shida abokansa, da sauri ya taso ya zo ya karbi jakar hannunta, sai washe baki yakeyi, suka jera,har inda me Napep dinta yake,  tsayuwa in yazo daukar ta

 

 

 

Tunda ta futo matasan dake unguwar suke kallonta wasu su fadi alkairi,wasu su fadi sharri a kanta, babu abunda ya dame ta, ta shiga Napep, Walidi ya mika mata jakar ta, yana mata adawo lafiya

 

 

Suna futa daga unguwar ta kunna wayarta, ko minti biyu ba ai ba kira ya shigo, sai da ta kusa katsewa sannan ta daga,

 

Ajiyar zuciya ya sauke, muryar shi kasa-kasa yace"Allah ya taimaki Gimbiya ta"

 

 

Shiru tayi bata ce komai ba,

 

 

"Tuba nake gani tun misalin bakawai ina nan ina zaman jiran ki nazo in baki hakuri bisa laifin dan uwana yayi miki jiya"

 

 

 

Ajiyar zuciya tayi, tace "Yusuf halinka daban da kai da dan uwanka"

 

 

Murmushi yayi kamar yana kusa da ita, yace"Halinmu daya da dan uwana,shima dan dai baku fahimci juna bane, ta wani gefan ma yafi ni kyawun hali"

 

 

 

"Hummm, yanzu dai ina kan hanya, ganin zuwa sai muyi maganar" bata saurari abunda zai ce ba ta kashe wayar,

 

Tunani take wace hanyar zata bi domin ta dauki fansar abunda Sarki! yayi mata

 

 

 

 

_Muje zuwa My Fans😘_

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[11/07, 20:48] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

           ^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

            ^^^^^^^^^

                   đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 *®REAL BINTU BATULA👄*

 

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*Zamani Writes Association*_đŸ€đŸ»

 

 

 

_*DEDIGATED*_

           _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

*🅿46*

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rahim```

 

 

 

 

Tun kafin ta futo daga Napep din ta zuge jakarta ta futo da niqabi ta rufe fuskarta sabuda ganin kasuwar ta soma cika da jama'a wataran har kusan faduwa take sabuda idanun jama'a

 

Sai da takara jaddadawa Ashiru  akan kar ya wuce shida da rabi na yamma, bai zo ya dauke ta ba,domin bata so ta dinga kai wa Magariba a waje.

 

 

Duk da niqab din dake sanye a fuskarta hakan bai hana wasu gane ta ba, sabuda yanayin tafiyar ta, wasu suke gane ta, shiyasa bayan wucewar ta suka kama yi da ita,

 

Wani Alhaji Musa yace"wallahi na rasa yadda zanyi in tunkari yarinyar can, sabuda mugun kwarjinin da take min,gashi Allah ya jarrabe ni da sonta kamar me"

 

"Ai ba kai kadai ba"

wanda yake kusa dashi ya fada, ya cigaba da cewa"ni kaina kwarjini take min,wallahi ina mutukar son tsarin jikinta, da yanayin tafiyar ta, yarinyar fa tayi sosai, matsalar kawai "yar talakawa ce"

 

"Duk wannan ba matsala bace a gurina mutukar zan samu fuska a gurinta"

Alhaji Musa ya fada, yana jan numfashi, yace"kwanaki da muke zancan ta da Alhaji dan Yaro, yake fadamin,  wai Yusuf Maddibo ne yake neman ta,kasan Abokin Buba ne,shi kuma Buba kasan tare suke harkokinsu dashi,shine yake fada masa"

 

 

"Ai kaji abunda nake fada maka,wallahi yarinyar matar manya ce,sosai amma in kaga zaka iya shiga bisimillah,amma fa zaka sha wulakanci, domin shi ma Yusuf din, dan kore ne a gurinta har yanzu bata karbe shi ba"

 

"Duk wannan baya damuna,indai zan samu biyan bukata"

Alhaji Musa ya fada, nan suka cigaba da tattauna maganar,

 

 

 

Kafin ta shiga gurin nata sai da ta tsaya suka gaisa da Me kosai cikin mutumci, ta futo da dari biyar ta mika mata tace"gashi a rabawa yara kosai sadaka"

 

Almajiran dake zaune gurin suka dinga murna da farin ciki, dama dakon zuwanta sukeyi sabuda sun saba kullum tana sawa a raba musu kosai, nan suka dinga godiya gami da fatan alkairi

 

 

Anutse ta shiga ciki inda ta tarar da Su Hauwa'u suna ta kai wa da kawo wa komai tsaf duk wani costomas an bashi abunda yake bukata,  sama-sama suka gaisa da su, fuskarta babu walwala, kullum haka takeyi sabuda bata son wani ya kawo wargi a cikinsu,can gefe guda ta hango Yusuf zaune cikin kujera, ya zuba mata ido,kamar zai cinye ta,fuskarsa dauke da wani kayataccan murmushi, da sauri ta dauke kanta, ta nai wa Hauwa magana,

 

 

Reciptoin  ta futo ta zauna kan kujerar ta, kamar  ko da yaushe, tana kallon masu shige da fuce, a gurin.

 

 

Ganin ta futa yasa Maddibo mikewa a nutse ya bi bayanta, mutanan dake gurin suka bishi da kallo, ganin dukaninsu a gurin suka taddashi,gashi ya mike ya futa batare da yaci komai ba.

 

Zama yayi kujerar dake fuskantar ta fuskar shi dauke da murmushi har ila yau, yace"Ranki ya dade,barka da zuwa"

 

 

Sakin fuskarta tayi tace"kai ma ranka ya dade,fatan ka tashi lafiya"?

 

Bai yi tsammanin zata sakko da wuri haka ba, ganin yadda ranta ya ba'ci jiya, amma abin mamaki ko a fuska bata nuna masa ba,asali ma yau tafi kowane lokaci sakar masa jiki.

 

Yace"Lafiya kalau, na tashi ke fa"?

 

"Nima lafiya kalau"

tafada tana yi masa wani kayataccan murmushi.

 

"Hakuri nazo na bawa Gimbiya sarauniyar zuciya ta"

Yafada yana wani karyar da kai, gwanin tausayi

 

 

 

"Humm Yusuf kenan, wane hakuri zaka bani, ai kai ba kayi min laifin komai ba,wanda yayi laifi shi ya kamata yazo ya bada hakuri in ana so in huce, fushina"

Ta karashe maganar tana wani fari da ido.

 

 

Shiru yayi yana binta da kallo,cikin so da kauna, yace"Ayi masa afuwa,Gimbiya na ari bakinsa naci masa albasa, abunda yayi shi, shine yayi ni, A yafe masa"

 

 

 

Girgiza kai tayi tana tabe baki tace"in kaga na hakura to sai dai idan ka dauko shi ka kawo min shi nan yazo gurina a karo na biyu,wannan zuwan nasa ya zama na bada hakuri ne, a gurinshi, shine kawai zai sa na hakura,

 

 

 

Murmushi yayi yana gyada kai cikin zuciyar sa yace"lallai na kara tabbatar da cewar sarauta a jinin yarinyar nan yake,wato ta na nufi yaje ya dauko Sarki! a karo na biyu ya kawo mata cikin kasuwa, lallai lamarin Balaraba ya shallake tunanin sa, ko mutuwa zai yi baya tunanin Sarki! zai yadda yazo kasuwa gurin ta da zumar bata hakuri, sai dai idan zai rufe masa yaki fada masa gaskiya, amma domin ya nuna mata son ta dake cikin zuciyar sa  na gaske ne, yasa yace"duk wannan me sauki ne, mutumi na zai iya zuwa ya baki hakuri kamar yadda kike bukata,sabuda dan uwana yana mutukar son abunda nake so"

 

Harararsa tayi tana fari da ido tace"ni dashi wa kafi so"?

 

 

Dariya yasa yana kallonta yace"matsayin ki daban, nashi daban, a zuciya ta, amma bari ki fara ganin naki matsayin a gurina"

ya karashe maganar yana kokarin futo da wayarsa aljihu,

 

 

A nutse tace"me zakayi naga ka futo da waya"?

 

Kashe mata ido daya yayi ya sai ta Camara ta wayar shi ya hau daukar ta a hoto,

Da sauri ta sanya hannu tana kare fuskar ta domin yayi mata bazata,

 

"Kabari bana so dan Allah"

tafada tana kauda fuskar ta.

 

Sai da yai mata kusan goma sannan ya dai na

 

Shan kunu! tayi tana dauke fuska tace"ka dauki hotana ba da yarda ta ba zakaje ka nunawa abokan ka su kalli munina ko"?

 

 

Yana dariya kasa-kasa yace"babu wanda zan nunawa sai mutum daya"

 

"Wanene shi"

tafada cikin sigar tuhuma

 

 

"Mutumin ki ne"

 

Tabe baki tayi tace"har yanzu ban yadda da son da kake min ba har sai kaje ka kawo min shi nan sannan zan yarda da kai"

 

 

Wayar shi yake latsawa yana murmushi yace"bari kiga Zahiri,kafin in kawo miki shi bari in kira shi a waya sai kuyi magana"

Numbar Sarki! yafara lalube cikin wayar tasa

 

 

 

Shiru tayi kawai tana kallon shi,   duk layin da ya kira a kashe,  na ukun ne ya shiga,sai da ta kusa katsewa sannan yaji an daga wayar, da sauri ya bude handsfree ya mika mata,

 

Ta karbi wayar  cikin basar wa

 

 

Muryar shi taji kamar ta me bacci, yace"Assalamu alaikum"

 

Gabanta ne  ya fadi! jin muryar shi duk da kasa-kasa take bai hanata jin dadin ta ba,

 

Cikin jarumta! tace"Amin wa'alaikassalamu"

 

 

Jin muryar mace yasa shi sauri tashi zaune, dama a kwance yake a  kan wata katuwar Sofa, Mamaki yake, me ya kai wayar Maddibo hannun mace, kwata-kwata bai dauki muryar ta ba,

 

Gabanshi ya fadi kad'an,tunowar da yayi yanzu haka Maddibo yana gurin yarinyar nan me abunci, sabuda da zai tafi ya fada masa.

 

Muryar shi ya bude sosai sauti,da a mo suka bayyana, yace"Wacece keee? ina me wayar"?

 

 

kitttt!! ta kashe wayar ta mikawa Maddibo, cikin dauriya tace"kiranshi a waya bashi ne zai sai in hakura,kawai ka kawo min shi nan"

Tafada cikin bada umarni"

 

Girgiza kai yayi kawai yace"ta kwana gidan sauki insha Allah zan kawo miki shi nan"

 

Sakin jiki tayi suka cigaba da hira cikin nishadi cikin zuciyar ta kuwa murna take ta kusa daukar fansa a kan abunda Sarki! yayi mata.

*Ni ko nace anya zaki iya kuwa Balaraba,amma dai muje zuwa😀*

 

 

 

Bangaran Sarki! kuwa kashe wayar da tayi, yayi mutukar bata masa rai sosai,domin ya tsani yana waya a kashe masa, ranshi a mugun bace! ya fara kiran wayar, lokacin Maddibo ya kashe, sabuda ya san dole zai kara kira yaji ba'asi sabuda yasan Wayar sa ce,

 

 

 

 

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[13/07, 06:19] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

           ^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

            ^^^^^^^^^

                   đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

 *®REAL BINTU BATULA👄*

 

 

 

*MARUBUCIYAR*

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*Zamani Writes Association*_đŸ€đŸ»

 

 

 

_*DEDIGATED*_

           _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

*🅿47*

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rahim```

 

 

 

 

Sau uku yana kiran wayar bai dauka ba,gashi ta na ringin, amma sabuda tsabar rainin hankali irin na Maddibo yaki dagawa,kashewa wayar yayi ransa a bace, yanzu ya tabbatar da cewar Maddibo ya kira wayarsa ne domin ya bawa yarinyar tai masa wulakanci.

 

 

 

Sai kusan Sha biyu da rabi na rana Maddibo ya yi wa Balaraba sallama, har inda yayi parking din motarsa ya ta rakoshi, mutane suka dinga bunsu da kallo, wadanda suka san Maddibo suka dinga zubewa suna kwasar gaisuwa.

 

Balaraba, Zuciyar ta ta amunce da Maddibo sabuda kyawawan halayen sa,ta lura ya san abunda yake,a rayuwa, zata iya auransa, zata cigaba da addu'a Allah ya yi mata zab'i mafi alkairi a gareta,

amma duk da haka ta nan a kan bakanta, ba zata nuna masa yardar ta da wuri ba har sai ya kawo mata Sarki! tarama abunda yayi mata.

 

 

 

Sosai Sarki! ya nunawa Maddibo bac'in ransa a kan abunda yayi masa,  yace"dan tsabar rainin hankali,ka kira waya ka bawa wata, ina magana,a kashe min waya,kar ka k'ara yi min haka"

 

 

Ganin yadda Sarki! yake masa hayaniya yasa yayi masa shiru har sai da ya yi mai isarar sa,sannan Yace"in kagama fadan sai ka saurare ni"

 

Ko kallonsa baiyi ba, ya cigaba da karka'da kafar sa,

 

Maddibo yace" tabbas Na kira wayarka, kuma na bawa Balaraba, sabuda ina so in dai-dai ta alakar ku da ita, ni nakasa gane, wace irin gaba ce a tsakanin ku, yanzu da zan tawo ma tace in gaishe ka" Ya karashe maganar yana satar kallonsa, ganin ko kallonsa bai yi yasa ya cigaba da cewa"ga hotonan da nayi mata ma"nuna masa wayar yake, wai ya kalla, shi kuwa ya wani sha kunu yak'i kalla sai ma ya dauki tashi wayar dake gefe a jiye ya hau latsawa, Maddibo bai yi zuciya ba, yace"Mutumi na kalli nutsuwa da kamun kai gurin yarinyar nan dan Allah"

 

Kamar da dutse yake magana, Sarki! ya share shi,

 

Girgiza kai kawai yayi yana murmushi, ya aje wayar kan kujerar ya mike ya nufi bedroom din Sarki, domin yin wanka, badan baiyi da safe ba,kawai  shima yanayin sa kamar na Sarki! ne baya son zafi,kullum cikin wanka, duk da haka Sarki ya fishi, sabuda shi ko da sanyi ne, sai ya kunna AC sannan yake iya bacci.

 

 

 

Minti biyar da ta tashin Maddibo, ya dago kanshi yana kallon wayar Maddibo dake aje kusa dashi, a zuciyar shi, sai yaji yana son yaga hotan Yarinyar, har ya mika hannu zai dauki wayar wata zuciyar tace masa,me zakayi da hotanta, yarinyar da ta zage ka, kawai sai ya dauke hannushi yq cigaba da duba wayarsa yana jin wani abu cikin ransa a game da yarinyar,

 

Kasa hakura yayi ya mika hannushi a karo na biyu ya dauko wayar, ya fara dubawa,

 

Shagala yayi da kallon hotonan,Sosai yake kare mata so yake ya hango wani abu na aibu a tattare da ita bai hango ba, Jikinshi ne yayi sanyi, sosai tabbas wannan yarinyar itace wacce yake gani cikin mafarkin sa,  da sauri ya dauki wayar sa a gurguje a tura hotonan cikin wayar sa baya so Maddibo ya futo ya same shi yana duba masa waya,aikuwa motsin sa yaji yayi sauri ya mai da wayar ya aje inda take,Allah yasa ya gama turawa

 

 

Cikin jallabiya me yankakken hannu ya futo, ya zauna kusa dashi, da murmushi a fuskar sa yace"Mutumi na ina labari, ya kamata fa ka dai na wannan fushin domin auran Balaraba babu fashi" yafada yana dariya, ya cigaba da cewa"kai nifa daga yau na zama Balarabe,na Balaraba,kaga wanda zai yi mana wak'ar bukinmu ya huta"

 

Dariya ce ta sub'uce wa masa bai shirya ba, yace"Wallahi kasa ni nayi dariya, ban yi niyya ba naji haushin abunda kayi min d'azu"

 

Shima dariyar yake yace"ko dai naji haushin abunda kayi min jiya, haka kawai, zaka sanya ni a kwana, badan na buga sammako naje na wanke kaina ba, a gurin ta, da tuni sai dai in ga ana yi"

Gaskiya ina son yarinyar nan sosai, ka dubi Allah ka tayani sonta, ka sauke duk wani abu dake damun ka a kanta"

ya karashe maganar yana kwantar da kai.

 

 

Tab'e baki yayi hankalin shi na kan wayar sa yace"kai ka kyale ni don Allah, kowa yaji da tasa matsalar, meye alaka ta da ita,da zaka ce dole in saki jikina da ita, ni babu ruwana, tunda kana ganin zaka iya zama da ita,Allah ya sanya al'kairi amma a zuciya ta sam ba nai maka sha'awar ka aure ta"

 

 

"Meye dalilin ka na fadin haka"?

 

" Sabuda yarinyar bata da kunya" yafada kai tsaye, ya cigaba da cewa"sam baza ka iya da ita ba,a yanda kake salo-salo, wannan yarinyar, in ta fuskanci irin son da kake mata, wata rana sai ta sanya ka kuka"

 

 

"Ba dai Balaraba ba" Maddibo yafada da sauri yace"kaine kake ganin haka,sabuda rashin jituwar dake tsakanin ku amma nasan Balaraba, tana da ilimin zama da miji"

 

 

Murmushi yayi yana girgiza kai yace"Shikkenan,Allah ya sanya al'kairi, yanzu ta yaya zaka fara,kasan dai dole ka fuskanci kalubale,gurin manyan mu,mutukar sukayi bunkice suka fuskanci yarinyar "Yar.... Shiru yayi bai karasa ba, ganin Maddibo ya sha kunu! sai ya fashe da dariya yace" Gaskiya zanga irin love din da zaka dinga zubawa da yarinyar nan, na fuskanci ka zarme da yawa wallahi, ni ban ga abunda yake rud'ar ka ba,a gurin ta ba yaga hasken fata"

 

 

Ajiyar zuciya Maddibo ya sauke yace" babu wani farar fatar ta dake rud'ata kawai na duba nagartar ta ne, maganar ta yaya zan fara, me sauki ce, kai tsaye me Martaba zanje in samu da maganar,nasan abun zai zo da sauk'i dama matsalar na gurin Waziri,dole zai k'alubalanci abun"

 

 

"Yayi, har ka tuno min da maganar mu dashi d'azu da safe, kasan abokin shi Sarki Yalwa, ko"?

 

" Eh mana"

 

"Wai yariyar shi ce tace tana so in aure ta, in had'asu da Halisa, shine da kiran da yayi mun da safe"

 

 

"Dariya Maddibo yayi kad'an yace" ni narasa abunda yake damun wasu matan wallahi, kawai sai tace ka aure ta baka santa,baku taba mu'amala da ita ba, tayaya wannan abu zai faru"

 

 

 

"Humm kai ne kake ganin haka, nasan yarinyar ciki da waje, domin waccan shekarar tare mukayi aikin hajji da ita, kuma wata uku da suka wuce da naje Umara mun had'u da ita, sosai ta nace min kullum tare muke tafiya masallaci, sai dare take kyaleni ta tafi ma saukin su, safiya nayi zata zo ta dame ni, shine dalilin da yasa  ko sati daya ban cika ba na tattaro kaya na na gudo bata sani ba, sai dai ta shafa taji ba nanan, kai kanka kasan na tsani ta kura"

 

Dariya Maddibo yasa yace"Wallahi baka da kirki "Yan mata suna sonka kai kana k'insu ko zaka fad'a min dalili"

 

 

 

 

 

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[13/07, 20:43] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

  ^^^^^^^^°

   _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^

                  đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

                   _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®{REAL BINTU BATULA}👄*

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

_ZAMANI WRITES_

 _ASSOCIATION_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rashim```

 

 

 

*🅿48*

 

 

 

Maddibo ya cigaba da cewa "yanzu me kace kai akan al'amarin"?

 

 

" Kai ma kasan halin Baba Waziri,cewa nayi na amunce kawai,ba kaga yadda yake murna ba"

 

"Ya zakayi da rigimar Halisa"?

 

Tsaki! yaja yace" Halisa ba tafi karfi na ba,ina ruwana da rigimar ta tayi, ta gaji, ka manta cewa ba ni ne nace,ina son ta ba, ita wannan din da a ka k'akaba min, sam! ba tai min ba, Siririya ce, babu wani cikar arziki, ka san ba nason mace, haka, dukkanin su babu wacce tai min gwara-gwara ma Halisa tana da wasu abubuwan"

 

 

Dariya Maddibo yake sosai yace"kana kiran Tafida, da mayen mata,to kai da wane suna za'a kira ka"?

 

 

Shan kunu! yayi kamar ba shi ba yace"ai gaskiya ce, ganganci ne ka auri mace, wacca baza ka more ta ba,sai dai kai ta fama da kashi da jijiya, wallahi nake fad'a maka,wata macan ko me zaka bata, baza ta yi k'iba ba"

 

 

Cikin dariya Maddibo yace"kana daga zaune sai zaro magana kake, wallahi matan ka sun shiga uku, kai dai"

 

 

Tab'e baki yayi ya mik'e tsaye tsaye, yace"babu ruwana dasu a cikin su duk wacce tafi kyautata min itace taurarowa ta"

 

 

Mikewa Maddibo yayi yace" Zanje fada mu gaisa da Maimarta ba, idan naga da sukuni zan shigar da maganar Balaraba"

 

"Allah ya bada sa'a" Sarki yafada ya cigaba da cewa"nima wanka zan shiga zan futo yanzu"

 

 

 

Lokacin da Maddibo ya isa fada, bata cika sosai ba, daga Sarki sai Waziri da Wambai sai  Wasu fadawa su hud'u , Maimarta ba yana zaune kan kujerar shi, suna magana da Waziri, duk dai a kan Sarki! ne, Waziri yace"d'azu munyi magana dashi yace ya amunce, yanzu abunda zamuyi shine, zamu aika da takkada gayyata gare ta kan tazo su gaisa dashi, muna bukatar ta zauna tare damu, domin ta koyi irin al'adunmu sabuda kasancewar kowane gari da irin tasu sarautar"

 

Jin maganar da Waziri yake tasa Maddibo faduwar gaba! kalubale na farko kenan,

 

 

Cikin nutsuwa da dattako yayi sallama fadar kanshi a sunkuye ya zube! yana kwasar gaisuwa

 

 

Da murmushi a fuskar Maimarta ba yake amsa wa yace"da alamu akwai magana a bakin Ubana, Maddibo d'an Maddibo kuma Uban Maddibo"

 

 

Murumushi Maddibo yayi ya karasa gaban Maimarta ba kanshi a sunkuye,yace"Allah shi taimake ka, nazo muku da wata magana me muhimanchi ina fatan zaku karb'eta hannu biyu"

 

 

 

"Masha Allahu"

Maimarta ba yafada ya cigaba da cewa"nasan ko wace irin magana zats futo daga bakin ka mai muhumanchi ce Ubana,ina sauraron ka, tare da sauran iyayen naka"

Yafada yana kallonsu Waziri dake zaune duk sunyi shiru

 

Da sauri Wambai yace"kwarai kuwa Allah shi taimake ka, muna sauraron ka"

 

 

Shiru Waziri yayi irin na kara, amma ya k'agara Maddibo ya fad'i irin maganar da yazo da ita cikin fada wacce ya kasa fad'a masa ita a matsayin sa na wanda ya haife shi,

 

 

 

Cikin nutsuwa Maddibo yace"Allah shi taimake ka na samu matar aure insha Allahu, ina so a aika gidan su domin a tsayar da magana"

 

 

Kafin Maimarta ba yace komai, Waziri yace"  "yar wane Sarki ce a fad'in duniyar nan, ina fata bakaje kayi mana jajibe-jajiben " yayan bayin mu, ba wato talakawa"

 

 

 Shiru fada tayi, sabuda Waziri ya karya dokar fada,bai bari Maimarta ba yace komai ba, ya fara magana, daga baya da yage b'arnan da yayi, sai ya d'an runk'ufar da kanshi yace"Afuwa a gafarce ni ranka ya dade"

 

 

Minti biyar Maimarta ba bai ce komai ba, daga bisani ya d'ago kai a nutse yana kallon Maddibo yace"kaje ka cigaba da neman yarinyar zamu sa a je ayi bunkice, babu ruwan mu, da cewar "yar talaka ce,ko " yar mai kudi ce, ko "yar sarauta ce, duk wannan basa gaban mu, nagarta da kyawawan halaye shi zamu duba, Allah yasa za'ayi damu"

daga fadin haka,sai yayi shiru, amma fa fuskar shi babu walwala dalili Waziri ya b'ata masa  rai, sam! ya tsani halayen dan Uwan nashi kwata-kwata baya kaunar talakawa, tun jiya yake tunanin maganar da yayi masa akan Sarki! da d'iyar Sarkin Yalwa, yasan da akwai wani abu a b'oye wanda shi Wazirin yake son cika wa, amma koma meye ya barwa Allah domin  ya fisu sanin abunda yake lullub'e.

 

Cikin farin ciki Maddibo ya mik'e yana godiya, Maimarta ba ya dakatar dashi da hannu, yace"ka zauna a fada na lura tunda ka dawo baka zauna ba,kai ma ka koyi d'abi'un d'an uwanka, yau in ya zauna a fada gobe ba zai zauna ba"

 

 

Komawa yayi ya zauna gami da tankwashe kaf'a yace"Allah ya taimake ka"

 

 

"Ko kana da wani Uzirin ne"?

Maimarta ba yafada yana kallon shi

 

 

" A'a babu wani uziri a yanzu, ranka ya d'ade"

 

 

Shiru Maimarta ba yayi  yak'i sakin fuskar sa,sabuda abunda Waziri yayi ya bashi haushi, nan Wambai ya fahimta yace"Waziri ya na neman afuwa ranka ya dad'e"

 

 

A nutse yace"Ai ya nuna min bani ne uban d'anshi ba,tunda har ya kasa hakura in fad'i magana sai da ya fad'i tashi"

 

 

"Tuba nake, a busa kuskure ne,ranka ya dade a gafarce ni"

Waziri, yafada yana jin wani mugun bak'in ciki, a zuciyar sa, dole ne ma yasan yadda zai yi ya kawai da mutumin nan daga karagar mulki,tunda ba danshi kad'ai a ka hallice ta ba, shima yana da gadon sarauta kamar yadda yake da ita, babu yadda za'ayi ya dunga nuna masa mulki, amma babban abunda yake bashi mamaki da d'aure kai shine duk sanda yayi niyar aiwatar da wani abu a kansa,daga ya had'a ido dashi sai ya kasa, ya rasa wane irin kwarjini yake masa.

 

 

Haka fada tai ta tafiya, har lokacin sallahr la'asar, Maimartaba ya mike a nutse domin shiga masallaci,

 

 

 

Suna dawo wa fada Maimarta ya aika ai masa kiran Sarki!

 

 

Lokacin yana wani k'ayataccan lambu wanda yake hutawa, yana kishin gid'e kan wani lallausan kafet,da wani tumto mai kyau da taushi,anyi masa ado irin na sarauta, gefe ga kayan marmari nan burjik, amma ko daya bai dauka yaci ba, yau baya buk'atar kowa ya rab'eshi shi kad'ai ya ke zaune a gurin, wata irin iska na kad'awa mai dad'i, wayar shi ca hannu shi ya kura mata ido ko k'iftawa baya yi, *Niko da san ganin kwaf! sai na je lek'a a fakaice don kar ya gani,  😳 me zan gani ni Binta* hotonan Balaraba yake ta kallo, in yaga wanan  sai yaga wan can, ya kasa gajiya da kallonsu, fuskarshi nayi saurin kalla, naga wani irin annuri yana sauka tamkar wanda akai wa bushara da gidan aljanna.

 

 

 

*Tofa menene zai biyo baya, bayan wannan?*

 

 

*Muje zuwa my fans*😘

 

 

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[14/07, 22:56] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

  ^^^^^^^^°

   _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^

                  đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                   _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®{REAL BINTU BATULA}👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

_ZAMANI WRITES_

 _ASSOCIATION_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rashim```

 

 

 

*🅿49*

 

 

 

A nutse  Jakadan Maimarta ba ya karasa inda Sarki! yake kishingid'e kanshi a kasa yace"barka da hutawa ranka, ya dad'e.

Cikin k'asaita ya dago kanshi yana kallon Jakadan yace"barka kadai"

 

"Allah shi taimake ka Mainasara, dama Maimartaba ne yace" yana son ganin ka yanzu"

Shuru gurin na tsawan minti biyu, ya kara dago kanshi a karo na biyu,yace"kaje kace ganinan zuwa"

"To a tashi lafiya, ranka ya dad'e ko in tsaya mu tafi tare ne"?

Girgiza kai yayi kawai, hankalinshi na kan wayarshi, cikin nutsuwa Jakadan ya mike ya bar gurin,yana baza babbar rigar dake jikinshi,

Tsawan mintu goma yayi yana kallon cigaba da kallon hotunan Balaraba dake wayarsa,bayan zuwan  Jakadan Maimartaba, wani hotono duk cikin hotunan ya d'auki hankalinsa wanda ta sanya hannuwan ta ta rufe fuskar ta dasu, hoton ya dauk'i hankalin shi sosai sab'anin wanda fuskarta ta futo a ciki, sabuda haka kawai sai d'ora shi a fuskar wayar tashi,ba tare da yayi tunanin komai ba, ya jima yana k'arewa yatsun hannuta kallo wasu zara-zara dasu, inda suka yi wani jazir sakamakon k'unshin da tayi musu, ajiyar zuciya ya dinga saukewa, a kasalance ya mik'e tsaye ya sanya takalmansa, ya nufi fada, domin amsa kiran mahaifin nashi.

 

 

Cikin nutsuwa yayi sallama ya shiga, ya nemi guri ya zauna, ya kai gaisuwa ga mahaifin nasa,sannan d'aya bayan d'aya ya gaida su Waziri.

 

 

Shiru fad tayi kowa yana sauraron yaji abunda yasa Mamairtaba kiran Sarki!

 

 

Gyaran murya yayi yace"Munyi magana da baban ka Waziri, d'azu da safe, nace masa ya aika ai masa kiran ka ya nemi yaddar ka, a kan abun da yazo dashi, naji mutukar farin ciki a busa amincewar da akayi,ba tare da kaga yarinyar ba,kuma kayi k'okari gurin ganin ka kare martabar d'an uwana, naji dad'i da bin umarnin sa da kayi, yanzu abunda ya rage mana shine a sanya lokacin daurin aure domin baza mu tsayw jira ba, ga d'an uwanka ma yazo da maganar aure ya samu mata, amma dole za muyi bunkice akanta, ya fad'a mana yarinyar ba tada alak'a da sarauta, duk wannan bazai hana mu hanashi auran ta, sabuda haka na yanke hukunci a kan zaka zama jagora gurin bunkito mana Asalin yarinyar kafin magana tayi k'arfi, yanzu dai na bashi damar yaje ya cigaba da neman ta, Allah yasa za'ayi damu"

Maimartaba ya karashe maganar Cikin nutsuwa da dattako.

 

 

Shiru na tsawan minti biyu fada tayi shiru, Sarki! ya kasa cewa komai, tabbas mahaifin nasa ya d'ora masa nauyin mai wahala, wanda kuma yake ganin bazai tab'a bujere wa Umarnin shi, dole kamar yadda yake Umartar shi da yayi abu,wannan ma dole ya je ya cika Umarnin da ya bashi,

 

 

Wannan zan iya cewa sarar, Sarki! ce in kuna magana dashi, kafin ya baka amsa zai tsaya ne, yayi nazarin maganar da kafad'a masa daga bisani sai ya yanke hukunci,sam! baya yanke hukunci kai tsaye.

 

 

A nutse yace"insha Allahu zan iya bakin k'okarina gurin ganin na bunkita Asalin Yarinyar da Nasabarta, sannan da tarbiyar ta, Allah ya bani ikon bin Umarni, Allah ya taimake ka"

 

 

Murmushi ne kwance a fuskar Maimartaba, abunda d'an nashi yafad'a ya sashi farin ciki sosai, domin ya zaci zai bujire masa a kan Umarnin da ya bashi, duk da dai ya san d'an nashi yana masa biyyaya a kan duk abunda ya Umarce shi, ya san wannan abun da ya sashi mai tsauri ne, a matsayin sa na Yarima mai jiran gadon mulki, sabuda haka babu abunda zai cewa d'anshi sai dai yayi masa fatan alkairi a rayuwarsa,shima yana masa addu'a Allah ya bashi "yaya masu biyyaya kamarshi.

 

 

Nan suka cigaba da zama a fada, suna sauraron masu k'orafe-k'orafe daga jama'ar gari.

 

 

*Wannan kenan*

 

 

 

Yau da Wuri ta dawo gida, sabuda rashin lafiyar Iya, haka ta wuce Shamsiyya a k'ofar gida yara duk sun yanyame! ta kamar ko da yaushe, haka ta kewaye su ta shiga cikin gidan, karo suka kusa yi da Iro, tayi saurin bashi hanya, domin ya wuce, sai yaja ya tsaye yana mata wani kallo irin na " yan iska,

 

Kauda kanta tayi tana k'okarin shigewa cikin gidan, in ba zata manta ba sai tace yau tafi sati uku rabon da ta sanya shi a idon ta, yana can yawace-yawacen shi,

 

 

Tare mata hanya yayi ya wani zura hannu a cikin aljihun wandon jins dake jikinshi, wai shi lallai saurayi sai ya burge ta, abun sai ya so ya bata dariya, ta maze batai ba, k'ara had'e fuskar ta tayi tamau! tace"meye haka Iro zaka tare min hanya,don Allah kauce ka bani guri"

tafad'a tamkar itace take gaba da shi ba shi ba,

 

 

"Ank'i abaki hanya ki wuce " yar rainin hankali, ni zaki dinga yiwa yawo da hankali, ranar nan nace inaso muyi magana dake, sabuda tsabar kin mai dani albada! wanda bai san abun da yake ba, kika shanya ni a waje ina ta jiran ki futo ki kak'i, Ehh!! har na tsaga bulle na, na shigo cikin gidan, nan ma kika rufe k'ofar ki, sabuda kinga dodo, zai cinye ki, to bari kiji duk irin k'ina da kike to baki da miji sama dani, sabuda haka duk guje-gujen da kike zakiyi ki gama, maganar auranmu dake tayi nisa kece baki sani ba.

Ya karashe maganar yana matsowa kusa da ita.

 

Da sauri ta matsa gefe guda tana toshe hancin ta, domin tunda ya fara magana wani irin wari yake surnanowa yana futowa daga bakinshi, sam! bata son kallon fuskarshi sabuda yadda tayi bak'ikk'irin da ita, leb'anshi har da d'inki da goshin sa, gashi babu hakora uku a bakin shi, lokacin da ya matso kusa da ita kuwa wani irin tsami! taji me hawa ka, lokaci guda taji zuciyar ta wani irin mungun tashi,

 

Da kyar! tace"Iro bani hanya in wuce dan girman Allah kar kasani in a mayar da "yayan hanjina"

 

 

"Ke!! dan Uwarki me kike nufi? "

Yafad'a yana kara kusantar ta,

Ya cigaba da cewa"Lallai ma kin raina min hankali wato kina nufin wari nake shiyasa kike toshe hancin ki ko"?

 

Shiru Balaraba tayi har yanzu hannunta na hancin ta,

 

Wata irin raruma! ya kai mata ta goce! da sauri, yaje ya daki! karyayyar k'ofar gidan, dotsen da akasa a ka tokare ta yayi nasa guri, k'ofar ta rufe, yayi  kanta  gadan!gadan!

 

 

Ganin yayo kanta yasa da sauri ta nufi cikin gidan, sai ya sanya kafarsa ya tad'e ta tafadi! kasa, ya kai mata raruma! ta mike zumbur!  ta ingije shi ta nufi k'ofar futa, da gudu, sai ya k'ara sanya kaf'arsa ya tad'o ta a karo na biyu, nan Allah bai bashi nasarar kada ita ba, hannushi ya sanya ya tokare ta yana mata wani kallon irin na sha'awa hannu ya sanya ya fuzge mata mayafin ya jefar k'asa, a gigice ya kai hannusa jikinta, inda ita kuma Allah ya bata sa'a tayi nasarar fuzgo wata k'aramar wuk'a dake soke a k'ugunshi, hannushi ta daka! da ita cikin zafin nama! nan take Iro ya zube a gurin jini na futa a hannunshi sosai da sosai, saura kad'an d'an ya tsan shi k'arami ya guntule, ihu! yake kurmawa, wanda yasa mutanan  Cikin gidan futowa da gudu suka nufi inda suke jiyo Ihun!

 

 

Da Sauri Walidi ya bud'e k'ofar soran dalili shima yaji ihun, dama dawowar shi kenan,ya tsaya yana raba wasu yara fad'a wanda suka zo siyan a wara,

 

 

Ihu! Iri yake sosai kamar wani k'aramin Yaro, ga Balaraba a tsaye, babu mayafi babu d'ankwali, ga hannunta rik'e da wuk'a

 

 

Da yake a kwai sauran haske a garin bai duhu ba, yasa kowa ya fahimci abunda yake faruwa, Uwa! ce ta kurma wani uban ihu! gami da d'ora hannu a ka tana fad'in na shiga uku! na Lalace, ni Uwande! shikkenan zata kashe min yaro na wanda nake hutawa dashi, wallahi Balaraba sai na d'auki fansa a kanki"

Kafin kowa ya ankara tayi kan Balaraba da gudu ta danne ta tana duka ko ita, da yake Uwa! irin matan nan ne masu k'iba, kowa ya kasa daga ta daga kan Balaraba sai duka take, Lantana ko tana gefe d'aya tana k'ara ingiza Uwa!,kan taci uban Balaraba, a cewar ta abunda Balaraba takeyi musu samun guri ne,

 

A fusace!Walidi yayi kan mahaifiyar tasa wacce take k'okarin kwatar k'aramar  wuk'ar dake hannun Balaraba wai lallai sai ta cire mata ya tsa kamar yadda tayi wa iro,

 

Cikin tsawa! yace"Wallahi Uwa! in baki d'agata kin daina dukanta ba sai nayi miki aski da wannan askar dake, hannuna, kin san dai zan iya, ko, dan tsabar mugunta da kawai ki danne ta, kina duka, kamar baki san halin d'an iskan d'anki ba, saunawa nake kamashi ke kanki yana lek'a ki a band'aki in kina wanka, wallahi naji dad'in abunda Gimbiya tayi masa, shege dan iska"

Ya karasa maganar yana dukan k'afar iro wanda yake kwance a k'asa rik'e da dan ya tsa yana jale-jale sura kad'an ya cire, amma sabuda tsabar son mata, yana can yana kallon jikin Balaraba, wanda Uwa! ta tattare mata zani, duk rabin cinyoyin ta a waje, ji yake kamar ya shafa jikin ko yaji sauk'in Sha'awar dake damunshi

 

 

Ganin Walidi yana masifa yasa Lantana tayi k'us! da bakin ta, sabuda tana k'ula fucin d'ari biyun da yace zai bata gobe da safe, tasan tayi magana zai iya hana ta,

 

Itama Uwa! mikewa tayi daga kan Balaraba, tana wani irin huci! sai zaginta take ta Uwa ta Uba, tana nema mata bala'i gami da jafa'i,

Abunda yasa ta daina dukan Balaraba shine tasan tsaf! Walidi zai aikata abunda yace, shiyas ta d'agata badan ta hak'ura ba,

 

Cikin borin kunya Iro ya mike tsaye yana nuna Walidi dan ya tsa yace"ban tab'a sanin kai shege bane sai yau, ina matsayin d'an uwanka, wannan tayi yunk'urin kasheni ka goyi da bayan ta, to bari kaji wallahi da kai da ita duk ban kyaleku ba, sai nasa an tsaga min ku gida biyu,zakaci uwarka! k'aryar daba!! kake tawa dabar!! tafi taka"

 

A zafafe! Walidi yace"wa kake zagi! in ka isa kai wani ne k'ara zagina ka gani"

 

 

Cikin gadara Iro yace"Uwarka!! Ehh gshi na zage ka me zaka iya ne"!!

 

 

Da gudu Walidi yayi kanshi ya yar k'asa ya dinga dukanshi, Sai da yayi masa laga!laga sannan ya d'aga shi yana huci! ya tsaya kusa da Balaraba wacce ke tsaye kawai ta rasa ma wane irin tunani zataiyi wannan masifa har ina!

 

Yace"in ka isa ka k'ara shiga hurimin Balaraba, sai dai Uwarka ta haifi wani, ya karasa maganar yana cije baki!

 

 

Ihu! Uwa! take kurmawa  tana tsinewa Walidi, Iro ta kallah wanda yake kwance bai san in da hankalin shi yake ba, jini ne kawai yake futa ta hancinsa da bakins, da gudu ta karasa gurin da Lantana take tsaye, tace"Lantana a gabanki za'ayi kisan kai, sabuda ke butulo ce wato kin manta alkairin da yaron nan yake miki,kullum ya dawo daga tafiya kin dinga k'arb'e masa kud'adan sa, babun abunda zance dake sai dai ince Allah ya isa tsakanina dake Lantana" tana gama fad'ar haka ta shige cikin gidan da gudu domin ta d'ebo ruwa wanda zata zubawa Iro da alama suma yayi

 

Tana barin gurin Lantana tace"Yo ni me zan tsinana miki, kaji masharanciyar mace, ko zatai min sharri, yashe nake ganin Iro ma balle ya bani kud'i o ni Lantana Allah ya had'ani da suruka wacce bata k'auna ta"

 

Banza Walidi yayi mata,hankalin sa na kan Balaraba yana tausar ta, kawai sai saukar mai soyayye yaji a k'afafun shi ya waiwaya a zabure! Shamsiyya a tsaye a bakin k'ofar shigowa hannuta rik'e da abunda take tsamo a wara, sai muzurai! take sam! bashi taso mai ya sama ba Balaraba tayi niyyar watsa wa sai ya sauka a k'afarshi.

 

 

 

 

 

*Muje zuwa*

 

 

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[15/07, 22:39] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

  ^^^^^^^^°

   _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^

                  đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

                   _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®{REAL BINTU BATULA}👄*

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

_ZAMANI WRITES_

 _ASSOCIATION_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rashim```

 

 

 

*🅿50*

 

 

 

 Da sauri Balaraba ta sunkuya tana duba k'afarta guda wacce soyyayan mai yayi nasarar zuba  lokaci guda ya tsun kafarta suka tashi, sabuda nan  mai ya zuba  Walidi kuwa ko ta kan kafarshi bai yi ba, yayi kan Shamsiyya, da wani mahaukacin duka, da gudu tayi cikin gidan, domin tasan zai iya ji mata ciwo,

 

Duk suna tsaye a tsakar gidan ta shigo a guje ta nufi d'akinsu ta kulle kof'a tana zagin Walidi tace"dan Uwarka, ka manta ranar da ka k'onani akanta, wallahi naso ita man ya sama shegiya mai sufar aljanu"

 

K'wafa Walidi yayi kawai yace"sai dai in baza ki kara futowa ba amma billahillazi sai na k'one miki wannan bak'ar fuskar taki,wacce ta gaji da bilitin" d'akin Balaraba ya nufa yana k'okarin bude mata,

 

 

Lokacin da ta shigo cikin gidan kai tsaye d'akin Iya ta nufa, duk mutan gidan babu mai kula da ita, gwara ma matar Kawu wato Sadiya,ita kuma, bata zama,kusan kullum tana hanyar gidansu, tana jinyar mahaifiyar ta, Iya na kwance kan wata ya mutsetstsiyar kafita jikinta a rufe,da zani sai rarar d'ari take, Sadiya da Usuman suna zaune sun zabga uban tagumi, suna tsoran su futa Lantana ta dakesu domin haka take musu kullum shiyasa in suka dawo daga makaranta, har indai yayarsu bata dawo ba, to sai suyi zamansu gurin Iya, jikinsu yayi sanyi da rashin lafiyar Iya.

 

 

Shiga tayi d'akin cikin sallama Sadiya ta amsa, tace"  Yayarmu sannu da zuwa"

 

"Sannu Sadiya, kuna zaune ku kad'ai Iya bacci take ne"?

 

 

" Yanzu ta tashi taje tayi alwala ko sallah batai ba ta koma ta kwanta"

Sadiya tafad'a tana kallon yayar tata.

 

" Yayarmu kin dawo lafiya"?

Usuman yafada, hankalinshi na kan ta

 

 

"Lafiya lou Usuman, kayi karatu a makaranta ko"?

 

" Eh nayi yau ma an karb'i haddar da aka bamu"

 

"To ka dage da karatu ni kuma nayi maka alk'awarin zan siya maka keken hawa"

 

Murna yake sosai ya mik'e ya karaso inda take ya rik'e hannunta yace"nagode Yaya Allah ya biya miki bukatun ki"

 

 

"Ameen" Balaraba tace ta mayar da hankalin ta kan Iya, tace"Iya sannu  da jiki"

 

Kai kawai Iya ta iya d'agawa "Bari in d'auko miki hijab muje Chamis kinji"

 

 

D'aga kai ta kuma yi a karo na biyu.

da taimakon Balaraba Iya ta mike tasa mata hijab d'in ta rok'ota suka futo, Su Sadiya nan suka zauna jiran dawowar su

 

Kasancewar Walidi ya futa daga gidan yasa Lantana yi musu wani kallo shek'ek'e tace"munafurcin banza da wofi, zaki lanjare kice baki da lafiya, duk kuje ku gama munafurcin naku ku dawo ku same ni nice dai Lantana ban can zaba

 

 Babu wanda ya kulata cikinsu Uwa! lokacin tana band'aki, sai ita kad'ai a zaune a tsakar gidan, suna futa suka ci karo da Sallau ya dawo,tun daga bakin lungu a kasanar dashi abunda ya faru a gidan, cikin tashin hankali ya shigo gidan, 

 

Yaji dad'in ganin ta a sabuda haka sai ya ja tsaya yana surfa mata ashar yace"bantab'a sanin ke "yar daba bace sai yau, duk ikirarin da mutane suke a kan " yayana cewa suna harkar Daba! a she ba haka bane, duk abunda ya faru d'azu ina da labarin sa, to bari kiji wani abu da baki sani ba, duk k'iyayyar da kike wa Iro shine dai mijin ki ko kink'i ko kinso sabuda haka dole ne zakije har d'akinshi ki bashi,hakuri idan kuma kink'i sai dai kije ki nemi wasu iyayan bamu ba, domin ni nan da kika ganni sharri na yafi kala dubu,wallahi duk inda kika shiga,sai naje na b'ata miki suna"

Ya karashe maganar a zafafe!

 

Da kyar! Iya ta bud'e baki tace" haba Sallau bai kamata kafad'i wannan maganar ba,kamata yayi kabi ba'asi kafin ka yanke hukunci, me Iro yayi mata har ta d'auki mataki a kanshi, ni duk da akwance nake a d'aki bana jin dad'i hakan bai hanani na jiyo abunda yake faruwa ba, da Iro da Balaraba duk naka ne, in dai adalci ake"

 

"Ke Iya rufe min baki, bana son hauka, me zai yi mata kuwa? wanda har zata d'auki wuka ta cire masa d'an yatsa, wallahi sai kin biya kud'in magani yanzu-yanzu, domin yana can Chamis za'ai masa d'inki, duk abunda ya faru shi Iro da kanshi yaje ya fad'a min komai, ni sam banga wani laifi a nan ba, dan yayi yunkurin tab'a jikin ki sabuda shine mijinki, dama kuma addini ya hallata cewar namiji zai iya tab'a jikin matar da zai aura kafin auren domin ya san wace iri ce matar gudun abunda zai je ya dawo, sabuda haka bayan kin biya kud'in maganin shi zakije ki bashi hakuri har shagonshi, kamar yadda na fad'a a farko"

 

 

 

Cikin mamaki Balaraba take kallonshi, jin abubuwan da yake fad'a bata tab'a yadda Kawu Sallau mugun jahili ne ba irin yau, a wace mazahabar a ka yadda namiji ya kusanci mace kafin auransu, itakam bata tab'a jin wannan k'aulin ba,

 

 

Iya tace"to kayi hakuri mu dawo sai mu yi maganar in sha Allahu zata bi umarnin ka kamar yadda kake so"

 

 

Kaucewa yayi ya basu hanya yace"kuje ku dawo ku taddani ina nan ina jiran ku"

 

Suna futa shi kuma ya shige gidan yana zage-zage kamar wani mahaukaci, Lantana ta mik'e zaune tana taya shi zage-zage tace"ashe kaji abunda ya faru ko?

 

"E naji ai shi Iron yaje ya fad'amin, duk abunda ya faru,kuma ina shigowa unguwar ake ta tarata ana fad'amin"

 

 

"Hummm! kagani ai sai ka d'auki mataki akan ta in ba haka ba kuwa sai dai kazo ka tarar ta kashe mu,a gidan dan yarinyar ta zama abunda ta zama, a duniyar nan"

Nan Sallau ya zauna kusa da mahaifiyar tashi suna k'ara maimaita maganar,

 

Uwa!ce ta futo daga band'aki hannunta rik'e da buta, aje butar da sauri ganin d'akin Balaraba a bud'e tun dazu Walidi ya bud'e mata, lokacin da zata shigo,gidan sam ta manta bata kulle ba suka futa, kai tsaye d'akin ta nufa, Lantana ta mik'e da sauri tabi bayanta, shima Sallau d'in mikewa yayi ya rufa musu baya,

 

Bunkice suke mata sosai a cikin d'akin sunyi mata filla-filla da kayan sawar ta sun jefo waje, Lantana tace" yawwa Uwa! d'aga katifar nan ko anan take b'oye k'udi ki kwasa maganin dukan d'anki da tayi, aikuwa kafin Lantana ta rufe baki, Sallau ya d'aga katifar da sauri, babu komai k'asan katifar, ya mayar da ita ya aje, dama Balaraba bata wani ajiyar k'udi duk in ta samu na b'ukata ne shiyasa basa taruwa, mafi a kasari ma tafi ajiya cikin jakarta,kuma tana jikinta a rataye, haka suka k'araci bunkucen su basu ga komai ba, suka futo suna ta zagin ta,kamar mahaukata

 

 Babu abunda yake damun Iya illa zazzab'i na maleria nan me chamis din ya had'a mata magani yace"dole za'ai mata allura ta kwana uku, Balaraba duk ta biya kud'in me chamis din yace"Iya kinci abunci in ce ko"?

"Eh to ba sosai naci ba"

Iya tafad'a da kyar! yace "babu damuwa dama illar guda d'aya ce ayi miki allura bakici abunci ba, tunda kinci ko yaya ne shikkenan, nan ya had'a allura yayi mata, suka kamo hanya suka tawo gida,gurin wani mai balango da gurasa suka tsaya Balaraba ta sai mata gurasa da balangu,suka wuce gida, suna shiga soran gidan suka dinga jin hayaniya tana tashi a gidan, Iya tace" wannan masifa ta gidan nan Allah kayi mana maganinta,

"Humm Iya ki kyalesu suyi su gama insha Allahu na kusa barin gidan sai kowa ya huta tunda nice basa buk'ata, duk kuma wanda ya zalunce ni Allah zai saka min"

Balaraba tafada lokacin da suke shiga gidan, kayanta tafara cin karo dasu a watse a tsakar gida wasu a gurin rijiya wasu a kusa da shara, Cikin mamaki ta tsaya tana binsu da kallo, dawowar Mabaruka kenan daga talla, tana tsaye ita da Shamsiyya tana wassafa mata abunda ya faru, tsalle ta buga tayo kan Balaraba tace"Allah nagode maka,kullum mu ake kira karuwai, yau gashi yau Allah ya nuna mana karuwa a gidanmu,,zatayi zina da d'an gida, Huuuuuuuuu!!! tir dake da halinki shegiya karuwa"

tak'arashe maganar cikin ihu! dama hanya take nema wacce zata ci mutumcin Balaraba sabuda mak'ure ta da tayi a bango kwanaki,

kayanta dake watse tabi tana tumurmusawa da k'afafunta, babu abunda Balaraba tace, takama hannun Iya ta shigar da ita d'akinta,sannan ta futo su Sadiya na biye da bayanta, suka shiga d'aki, zama tayi gefan katifa ta zabga tagumi hannu bibbuyu, tunani take yaya zatayi da rayuwar ta da ta k'annenta, sai yanzu tafara jin rad'adi a kafarta, kallon k'afar tayi taga ta kara tasawa alamun k'ona, ita ba wannan ne abund ya dame ta ba yadda za'ayi su futa daga wannan jarabar itada "yan uwanta, shawarar da ta yanke kawai shine ta nemi gidan haya su bar gidan, shine mafuta duk wanda zai yi zargin ta, ya dad'e bai yi ba,dama kuma a cikin zargin mutane take, kullum, tun tana jiyo motsin da hayaniyar su Lantana ta a tsakar gida, taji shiru da alama kowa ya shiga d'akinshi, buta ta dauka ta futo tsakar gidan domin ta daura alwala, suka ci karo da Sallau ya shigo gidan afujajan, gabanta ne ya fad'i sai tafara karanta innalillahi a zuciyar ta, tsayawa yayi yace" yawwa dama d'azu gajiya nayi na futa sabuda abokai na suna jirana a waje gashi baki dawo ba, sabuda haka yanzu me ake ciki, ki kawo kud'in da nace ki bayar domin za a sai wa Iro magani yanzu"

 

"Kawu ina takkadun gida da shago na wanda Maimartaba da yaron shi ya bani gurin saukata"?

 

Gabanshi ne ya fad'i sosai sabuda tun lokacin da ya karb'i takaddun daga hannunta yaje ya sanya su a caca  lokaci guda a ka cinye shi cikin inda-inda yace" wannan maganar ki aje ta gefe guda domin bazan baki a hannun ki ba, sunan na adana miki"

 

"Kawu kaje na bar maka su, kayi hakuri ni a yanzu bani da wani k'udi da zan baka, wallahi"

tafad'a tana k'okarin shiga band'aki sabuda tasan tunda ta ganshi ya shigo afujajan tasan daga gurin caca yake, watakila an cinye shi ne ya tawo yana neman kud'i ruwa a jallo,tasan ko ta bashi k'udin gurin caca zai koma baba wani magani da zai sai wa Iro, tana jinshi yana zaginta ta shigewar ta band'aki, bayan ya gama zage-zagen nasa d'akin Lantana ya nufa sai kace zararre, cikin ikon Allah duk ya taddasu suna bacci, nan ya tsallake su ya shige k'uryar d'akin ya fara laluben inda, Uwa! take ajiyar kud'i Allah ya bashi sa'a ya ga wani k'aton banki, batare da b'ata lokaci ba ya fasa shi ya kud'i ne a ciki kimanin dubu bakwai, ya lissafa dubu biyar ya bar sauran dubu biyu, a watse a gurin ya tsallake yayi ficewar sa daga gidan.

 

 

 

 

*Muje zuwa*

 

```Shin Balaraba in ta bar gidan ina zata koma?```

 

 

```Idan Uwa! ta wayi gari taga bankin ta a fashe wace irin masifa ce zata biyo baya```?

 

 

```Ta yaya Sarki! zai fara bunkican Asalin Balaraba```?

 

 

``` Menene a zuciyar Sarki!dangane da Balaraba```?

 

 

```Maddibo ne mijin Balaraba ko Sarki!?```

 

 

*Duk wannan amsoshin suna gaba, ku cigaba da bina domin ganin wace irin waina za'a toya*

 

 

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[16/07, 21:17] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

  ^^^^^^^^°

   _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^

                  đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

                   _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®{REAL BINTU BATULA}👄*

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

_ZAMANI WRITES_

 _ASSOCIATION_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rashim```

 

 

 

*🅿51*

 

 

 

 

 Bayan ta idar da sallahr tayi addu'oin ta kamar yadda ta saba,  Usuman ne ya farka daga bacci ya fara kuka, " Yaya yunwa nakeji, abunda yaron ya fad'a, Sadiya ta hau tashi daga bacci,sam ta manta bata basu abunci ba suka kwanta bacci, Sadiya ta mik'e zaune tana mutsike ido, Balaraba tace"tashi kuci abunci,kinga Usuman ya tashi yana kuka,maza jeki dakin Iya ki dauko kular abuncin ku,da sauri Sadiya ta mike, ta nufi d'akin Iya,  Iya na kwance kan dadduma bayan ta idar da sallah wani bacci ne me dad'i yake fuzgarta, zazzab'in ya sauka domin har wani gumi take, Sadiya tayi sallama, d'akin Iya ta mik'e zaune tace"Lafiya Sadiya"?

 

Iya kular abuncin mu zan dauka"

Iya ta koma ta kwanta,tana cewa "in kin futa ki ja min k'ofar, nan Sadiya ta d'auki kular ta futa daga d'aki,

 

 

Bud'e kular Balaraba tayi tana duba abuncin, babu abunda yayi duk da yake dafa duka ce, har yanzu da zafinsa, nan ta zuba musu suka fara ci pure watar ta dauko musu guda biyu, Usuman yace" Yayarmu ke bazaki ci abuncin ba"?

 

"Zanci mana Usuman kai da kuci ku koshi" tafad'a cike da tausayin yaran,  bayan sun gama ta rakasu suka wanke hannuwan su,  suka dawo ta gyara musu kwanciya suka kwanta, nan ita kuma ta cigaba da had'a "yan kayanta da suka rage tana sakawa cikin a kwatu, domin taci alwashin barin gidan gobe daga yau ta bar kwana a gidan,

 

Sai wajan karfe d'aya saura na dare sannan ta kwanta, cikin ikon Allah a subar fari ta tashi daga bacci ta futo ta d'aura alwala ta koma d'aki da sauri  ganin ana iska sosai hadari ya had'u har an fara yayyafi, tanaji massalacin bayan gidansu sun tayar ta bisu sallah, bayan an idar da sallahr rayi addu'onta, ta cigaba da zama kan dadduma tana jan carbi kamar yadda ta saba, wajan karfe shida, ta fara jin motsin mutanan gidan, sun fara futowa, bacci ne yake fuzgar ta kad'an-kad'an sai taji hayaniyar Uwa! tana buga kyauran d'akinta ta tare wa Sallau hanyar wucewa tana kunzuma masa ashar! "Wallahi tallahi babu wanda zai yi min wannan d'anyan aikin sai kai,domin dama kasha auna fasa min asusu na,ina kama ka,shine jiya ka faki idona, sai da kabari nayi bacci kafasa ka kwashe min kud'i ,wallahi Sallau ko ni ko kai a gidannan domin bazan sha wahalar neman kud'i na ba,ka dinga bin dare kana sacewa, eheee! ba zata sab'uba bunduga a ruwa!

Ta karasa maganar tana tattaro wuyan rigarsa ta cukume shi,

 

 

" Shikkenan daga kin ga an fasa miki banki an kwasar miki kud'i sai kice nine sabuda kin raina ni duk b'arayin "yayanki bakya tuhumar kowa sai ni, to komai masifar ki dole ne ki sake ni,inje inyi alwala inyi sallah tunda ke baza kiyi ba,  baza ki hanani yi ba"

 

 

"Kai dallah! rufe min baki"

tafada tana kai hannuta dai-dai bakinsa kamar zata gwab'e ta cigaba da cewa"kai har kana da bakin da zaka fad'i wata magana a kan sallah, akwai babban makiyin Allah irinka, ai Sallau in kaga na cika ka agurun nan to tabbata ka futo min da kud'ina"

Tafad'a tana k'ara tattaro wuyan rigar sa, k'arfi yasa ya angije ta, tafad'i k'asa ragwajab! ya futo daga d'akin da sauri, ya nufi k'ofar futa daga gidan, da gudu ta biyo bayanshi tana huci! cikin tashin hankali da masifa tace" ni ka tunkud'e ko, har kasa na fad'i a gaban yara na, to yau zanga yanda za'ayi ka futa daga gidan nan mutukar ba kud'ina ka bani ba"

 

Mutan gidan duk sun futo suna kallon ikon Allah, Uwa! ta shak'e wuyan Sallau sai huci take, dama d'azu shammatar ta yayi ya ingije ta d'azu domin Uwa tana da mugun k'arfi sai kace doki haka take,

 

 

K'ifta ido yake kamar b'era a ruwan zafi, bakin sai karkarwa yake,ya rasa abun cewa, duk alamu na rashin gaskiya ya bayyana a tattare da shi.

 

 

"Ke dan ubanki sakar min wuyan d'ana kar ki kashe min shi ki cuce ni"

Lanatana tafad'a lokacin da ta karaso inda suke, cikin tashin hankali take k'okarin b'anbare hannun Uwa!daga wuyan Sallau,  doke hannun Uwa tayi, cikin rashin kunya tace"kinga Lantana, matsa dan Allah sam baki iya komai ba sai munafurci da kwad'ayi, in kinga na sake shi to sai ya futo min da k'udina ehee!"

 

 

Gefe guda Lantana ta matsa tana rik'e hannun ta domin taji zafin buge mata hannu da tayi

tace"shikkenan,to kashe shi ki huta mara kunyar yarinya kawai, a gidan ubanwa naje nayi k'wadayi da har kike kirana da haka"

 

 

"Sai kiyi kuma kanki a keji"

Uwa! tafad'a tana k'ara matse Sallau jikin garo

 

 

Walidi ne ya shigo gidan, tashin sa kenan daga bacci ya fara jiyo hayaniya sabuda haka a fusace ya shiga gidan, cikin mamaki yake bin iyayen nasa da kallo,

 

"Ke!dallah, wai menene haka, kuke sai kace wasu  yara,k'ananu, ke Uwa! sakar masa wuya" yafad'a cike da bada umarini kamar shine Ubansu,

 

 

"Walidi in kaga na saki wannan mutumin to sai ya futo min da kud'ina, da ya fasa min banki jiya da daddare ya kwashe min"

 

Sallau duk yayi tsuro-tsuro, gwanin tausayi

 

 

Wani irin kallo yayi wa mahaifin nasa yace"Kai! ya akai ka fasa mata banki ka kwashe mata k'udi? wallahi baba zuciyarka ta mutu, eh! ka cuce mu daka haife mu, ina tur! da futowa ta tsatstson ka!!

 

Kasa cewa komai Sallau yayi duk ya muzanta, jikinshi yayi sanyi k'alau sai ya sunkuyar da kai k'asa

 

 

"Walidi"

da sauri ya daga kai yana kallon inda yaji kiran

Balaraba ce tsaye k'ofar d'akinsu, hannu ta d'aga masa alamun yazo inda take, da sauri ya nufi inda take, " ya akayi Gimbiya"?

yafad'a yana murumshi,

 

"Nawa ne k'udin?

 

" Wane k'udin kike tambaya"?

 

"Na Uwa! mana,sai a biya ta ta sakar masa wuya"

tafad'a tana kallon inda suke tsaye, tana k'ara mamakin rashin mutumcin Uwa!

 

 

Wata mahaukaciyar dariya Walidi ya kwashe da ita, yace"kinga Gimbiya kar kishiga wannan cakwakiyar babu ruwanki sunfi kusa, tunda ki kaga yayi shiru to ya aikata ne"

 

 

"Ai ba cewa nayi zan shiga ba, a dai biya ta ta sake shi, tun misalin shida na safe suke abu d'aya yanzu har bakwai da rabi, yanzu kuma zaka ga yara sun fara shigowa siyan a wara, wannan ba mutumci ba ne"

 

Tab'e baki yayi yace"dubu biyar ne"

 

"Shikkenan zan futa yanzu, zanje banki zan ciro k'udi ka f'ada mata in nadawo zan bata magana ta wuce"

 

"Shikkenan Gimbiya, tunda kince zakiyi amma ni da dan tani ne da kin rabu dasu, ai gwara da tayi masa haka,gaba bazai kara aikata wa ba"

 

 

Lantana idonta a kansu, sai tab'e baki take tana cewa"munafukar banza da wofi kawai, kinibabbiya" kasa-kasa take maganar sabuda batason Walidi yaji

 

 

 

"Ke Uwa! sake shi za'a biya ki"

Walidi ya fad'a yana cije baki!

 

Hannu  daya ta mik'a masa tace"bani in rik'e a hannuna tukkuna"

 

"Dallah! ki sake shi za'a baki an fad'a miki"

yafad'a kamar zai kai mata duka,

Sakin sa tayi ta matsa gefe tana huci!

tace"ina kud'in suke, kai ma zan iya tsine maka akan k'udin wallahi"

 

Dariya yake mata yace" Yo ke Uwa! ai ko kin tsine min tsiniwar ki baza ta kamani ba, sabuda kema, baki bi naki iyayen ba, duk abunda kai sai am maka,Hahahahahahaha!

Ya karashe maganar yana wata dariya kamar shashasha.

 

Ya cigaba da cewa, "Gimbiya zata bayar a baki an jima"

 

Jin yace Balaraba zata bayar a bata yasa ta kwantar da hankalin ta ta wuce d'aki tana huci!

 

 

Sallau kuwa tunda ya samu ta sakeshi sai ya sulale ya futa daga gidan kafin kowa ya ankara,haka ya futa baiyi sallah ba.

 

 

Shamsiyya da Mabaruka har a ka gama masifar suna bacci sai da Uwa! ta shiga d'akin tana kwashe sauran kud'in tanayi tana zage-zage sannan ne suka tashi, Shamsiyya tace"wai menene ina bacci ina jin hayaniya a gidan sama-sama, na d'auka ma mafarki nake"

 

 

Nan Uwa! ta kwashe komai ta fad'a musu, suka had'u da ita suna zagin Baban na su.

 

 

 Balaraba kuwa wanka tayi a gurguje ta sanya doguwar riga ta atamfa, me kalar blue da yellow mayafi mai girma ta yafa ta sanya takalmi plate mai a don duwatsu, tayi kyau sosai duk da ba wata kwalliya tayi ta kuzo a gani ba, su Sadiya sun shirya tsaf cikin uniporm dinsu na makaranta, ta hada musu shayi mai kauri ta basu sannan ta dafa musu indomee cikin kula, tare suka futo ta kulle d'akin ta nufi d'akin Iya, tana kwance kan katifa, da alamar ta fara samun saukin jikin ta, suka gaisa cikin mutumci Balaraba tace"Iya jiki yayi sauk'i ko"

 

 

"Alhamdulilahi jiki yayi sauk'i Balaraba, Allah yayi miki albarka, ta cigaba da cewa, kin futo to Allah ya bada sa'a"

 

"Ameen Iya nagode, yanzu ba kasuwa zani ba,zanje in ciro kud'i a banki zan sa a fara neman min gidan haya, ko a bayan layi ne,domin bana so in yi nesa dake"

 

" Yanzu ashe baki bar wannan k'udirin naki ba, Balaraba"

Iya tafad'a cikin jimami

 

 

"Iya kiyi min addu'a kawai zaman gidan nan nagaji dashi wallahi,gwara in tafi in bar musu"

 

 

"Shikkenan Allah yasa haka shiyafi alkairi"

 

"Ameen sai nadawo"

Balaraba tafad'a tana k'okarin tafiya, ta jiyo mitar Lantana, ko waiwaya batai ba, ta futa daga gidan.

 

 

 

*****

Kwana yayi yana tunanin ta ina zai fara bunkican Asalin Balaraba, ga Moddibo yau yak'i kwana a shashen sa, ya gudu nasa sabuda tunda ya dawo nan yake kwana, dole gobe kafin ya futa,ya nemi Moddibo a kan al'amarin domin shi kam bai san ta inda zai fara ba, kwana yayi yana mafarkin da yasa bayi kullum, asubar fari ya tashi, yana had'a gumi, mafarkin yau yafi na kullum bashi tsoro, yau ganinshi yayi tare da yarinyar nan mai kama da budurwar Moddibo, yana tara da ita kamar matarsa, abunda bai tab'ayi ba kenan, tunda yake bai tab'a mafarkin wata "ya mace ba, ya san dai shi mutum ne mai yawan sha'awa shine dalilin da yasa ma yake yawaita azimi, domin tsare kanshi, kuma baya tab'a yadda ya keb'ance da mace ko wace iri ce mutukar ba muharramarsa bace, sosai ya ganshi a mafarkin tare da yarinyar suna mu'amula irin ta ma'aurata, jikinshi a mutukar sanyaye ya mik'e ya shiga toilet domin ya tsarkake jikinshi, dole sai yayi wanka, kamar yadda addini ya tanada, bayan ya gama ya d'aura alwala ya futo, jikinshi d'aure da wani k'aton towol mai kauri da tsane ruwa, wani k'arami ne a hannushi yana tsane kanshi dashi, farar  jallabiya mai yankakken hannu ya saka ajikinshi had'e da gajeran wando, ya sanya hula irin ta larabawa, a kanshi sai ya zama tamkar wani balaraben kasar Saudia,kalar fatarshi ta futo sosai, ya zura wani farin takalmi ruffafe mai mutuk'ar kyau a kyawawan k'afafunshi, ya nufi massalaci cikin nutsuwa.

 

 

 

 

*Muje zuwa*

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[17/07, 21:39] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

  ^^^^^^^^^^^

   _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^

                  đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

                   _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®{REAL BINTU BATULA}👄*

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

_ZAMANI WRITES_

 _ASSOCIATION_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rashim```

 

 

 

*🅿52*

 

 

 

Tare suka futo daga massalaci da Maimartaba, cikin nutsuwa suke tafiya tamkar wasu abokai yayin da wasu fadawa suke take musu, baya Waziri da Shamaki ne a bayansu, Shamaki ya kalli Waziri cikin sigar munafuci yace"Allah ya taimake ka, wai yaya kasake har haka tafaru? tuntuni tane fad'a maka wannan shak'uwar dake tsakanin Maimarta ba da yaron nan tayi yawa,kamata yayi ka d'auki mata, a matsayin ka na k'ani gare shi, ka lura da kyau, sam baya baka kulawa kamar yadda yake kula da d'anshi, ko wani abu ne ya faru, in ka lura Maimarta ba baya zartar da wani hukunci sai yasa anyi masa kiransa, kuma duk gaku a zaune a fada, kai da Ciroma da Galadima  baku da amfani, nine Shamakin Maimarta ba,nafi kowa sanin shi, tunda kusan kullum tare muke yini a fada, kwanciya bacci ne kawai yake rabamu da shi, ina mai tabbatar maka da cewar in bakai da gaske ba, sai dai kaga wannan Yaro wata rana yana mulkar ka, Allah shi taimakake kayi tunani kan maganar da nafad'a maka"

Shamaki ya k'arasa maganar yana sunkuyar da kai, cikin munafurci

 

 

Ajiyar zuciya Waziri yayi yana kallon Maimarta ba tare da Sarki! suna tafiya a nutse hatta da tafiyar su iri daya ce sai dai kasaitar Sarki! har tafi ta mahaifin nashi,

 

 

"Akwai abunda nake shiyarwa,domin

 Ni kaina wannan abu yana damuna Shamaki, tare nake so mu had'a baki da Ciroma amma yak'i bani goyan baya a kan k'udirina kansu,to amma yanzu na samo mafuta, kwananan buk'ata zata biya kan Yaron shiyasa duk wata giggiwa da yake nake d'aga masa k'afa sabuda nasa ta lokaci kad'ance, zai shafe a duniya kamar ba'ata b'ayin sa ba a doran duniya"

Waziri ya k'arasha maganar yana kallon su ganin yadda hadimai suke zubewa k'asa suna kwasar gaisuwa,wasu tun daga nesa in sun hangosu suke zubewa k'asa kansu a sunkuye, had'e da daga hannu, alamun girmamawa har sai Maimarta ba ya shige suke mike wa tsaye, wannan abu yana mugun b'atawa Waziri rai, shima suna gaishe suna bashi girma a matsayinsa na Waziri,amma baya gani, yafi son suyi masa gaisuwa wacce tafi ta Maimartaba da d'anshi Sarki!

 

 

Maganar da suke tattauna tsakanin Maimarta ba da Sarki! yana sanar dashi cewar zai fara bunkice da ya umarce shi, amma yana neman alfarmar ya barshi ya futa da Normal kaya,domin yin basaja, kuma bayaso a had'ashi da kowane bawa, in ba Direba ba, wato mai janshi a mota

 

Maimarta ba,yace"wannan tunanin naka yayi kyau sosai sabuda idanun jama'a wani ma in ya lura ga daga inda yasa ake bunkicen zai iya fad'in k'arya a kan yarinyar, dan haka duk in da ka tsara kaje kayi, Allah ya kiyaye hanya"

 

 

Sarki! yaji Dad'in amuncewar da Maimarta  ba yayi, domin a k'aidar masarautar su, basa futa da Tufafi dole sai na sarauta in kagansu da Normal tufafi to a cikin gida suke.

 

 

Tare suka shiga b'angaran Mama Fulani domin yau Maimarta ba a gurin ta yake, ta k'ofar baya ya shiga, shi kuma Sarki! ya shiga ta k'ofar da kowa yake shiga,

 

Tana zaune kan wata katuwar daddamu, ja mai adon fulawa, gefan tumtum ne manya-manya guda uku, gabanta kuwa shak'e da kayan marmari, tana sanye da wata lifaya mai tsananin kyau da tsad'a hannuta rik'e davwani k'aramin carbi mai kyau sai kyalli yake,  tayi kyau har tagaji Mama Fulani kenan mace mai karamci da karramawa, mace mai kaunar talakawa da nakassau, Jakadiya Shafa'atu ce zaune a gabanta,da mufuci a hannuta duk da safiya ce amma fiffita take mata, cikin sakin fuska tace"Shafa'atu wai ke bakya gajiya ne"?

 

" Yaya za'ayi in gaji da hidima da uwar d'akina"

Jakadiya Shafa'atu tafad'a tana sunkyar da kai,

 

Shiru Fulani tayi kawai tana mamakin karamcin Jakadiya Shafa'atu, macace mai dattako da sanin ya kamata, duk wasu munafurce munafurce da ake a gidan babu ruwanta, an sha had'a baki da ita, domin cutar da ita, tana kare ta, domin farat d'aya bata ce musu bazata yi ba, ko magani suka bata sukace ta sanya mata a abunci sai ta karb'a da yarjejeniyar zata aikata, tana ganin sunbar gurin zataje ta zubar,kuma tazo ta fad'a mata cewar ta dage da addu'a, tana da mak'iya sosai a gidan, ko Waziri yaso ya had'a kai da ita lokacin cikin Sarki! tak'i yadda , shiyasa sam batada farin jini a cikin "yan uwanta har kullum suna kiranta da munafuka, ta sha hak'o tarin layu da hade da bak'in gashi irin na bunsuru, a harabar shashen Fulani sai dai kawai taje ta k'ona, ko kuma ta kaisu can wajan dukonan gidan suyi masu futsari, a kwai lokacin da Uwar gidan Maimartaba ta aiko Jakadiyar ta da wata bak'ar kaza, an cire mata kai, sai digar jini take, gashi an farka cikinta, anzuba layo suma an d'inke su da bak'ar fata, an saka a cikin kazar an d'inke da bakin zare, can wani lambu taga ta nufa, sai ta bita a baya tana kallonta tana tona rami, mai zurfi tayi saurin sa kazar a ciki ta mayar da k'asar ta rufe gurin, sauri-sauri tabar shashan dan kar a ganta  ko gama futa batai ba  taje ta tone gurin ta futo da kazar, ta bude cikin ta ta zazzago layun, nan ta tara ice ta had'a ta kone su tass! yana mamakin rashin imani irin na Uwar gidan Sarki, wato Kululu mai d'akin kudu, haka suke kiranta

 

 

To duk irin wadan nan abubuwa suna faruwa, a cikin gidan, duk abunda Allah ya nuna mata irin wanda ake kullawa a gidan tana k'okarin ganin ta kare Uwar d'akin nata,

 

*Wannan shine karamacin Jakadiya shafa'atu a gurin  Mama Fulani*

 

 

Da sallama ya shiga d'akin.

"Barka da shigowa Magajin Sarki Allah ya ja zamanin Uban d'akina"

Jakadiya Shaf'atu ta fad'a kanta a k'asa,

A nutse ya zauna  gefan mahaifiyar tashi, yace"barka kadai, fatan kun tashi lafiya"?

 

"Lafiya lou alhamdulilahi"

tafad'a tana kokarin mikewa da niyyar futa dama indai ya shigo takan basu guri ne su gaisa, sosai sai bayan ya futa take dawowa,

 

 

Cikin sakewa suka gaisa da mahaifiyar tashi, tace" nasan da akwai abunda ya kawoka tunda naganka yanzu da safe, ina sauraron ka"

 

 

 

Fuskar shi a sake, yace"Mama lafiya lau, na shigo mu gaisa ne"

 

Harararsa tayi kad'an tace"yayi kyau, yau an tuna dani kenan, ai ina lissafawa, yau kwananka uku, rabon da ka shigo min nan tun sanda nayi maka maganar Halisa"

 

 

"Mama ba haka bane, wallahi Moddibo ne yake zuwa yana takura min shine yake hanani futowa"

 

 

"Babu ruwan Maddibo yaron arzik'i kullum sai ya shigo da safe mun gaisa, kwanaki ma da yaje can gurin yarinyar da zai aura,har abu ta bashi ya kawo min, kai ka tsaya  muskilanci, in anyi maka maganar aure sai ka tsiri kauracewa mutane"

 

 

"Mama kiyi hakuri maganar Halisa ta wuce, tunda na amunce,bayan itama Baba Waziri jiya mun zauna dashi, akan Maganar Azima" yar abokinshi Sarkin Yalwa, na kuma amunce zan aureta domin na faranta muku rai"

 

Sakin fuska tayi sosai tace"naji dad'in wannan abu,   Allah yayi maka albarka, ya taya ka rik'o"

 

 

"Ameen, ya rabbi"

Yafad'a ya da cewa, Mama har yaushe kuka saba da budurwar Moddibo da har take miki aike, haka"?

 

"Tun ranar da Moddibo ya fara sonta, nake da labarin ta a gurinshi, kuma itama tana da labarina, mutukar yaje, gurin sai ta bada abu an kawo min"

 

 

Shiru yayi na munti biyu yana nazarin maganar da tayi, A nutse yace"na lura kema kin yaba da yarinyar tunkafin ki ganta, Maimarta ba ma na lura ya son al'amarin, Moddibo ya b'oye muku wani abu wanda baya son ku sani a kan ta, yanzu halin da ake ciki Maimartaba ya turani bunkice a kanta"

 

 

"Gaskiya banaji yarinyar tana da wani aibu, domin har waya munayi da ita wani lokacin in yaje gurinta, ya kan kira waya ya bata yace mu gaisa,ko ga muryar ta nasan yarinya ce me kamun kai"

 

 

Shiru yayi, daga bisani yace"Mama yanzu ace kamar d'an nan gidan yaje ya auro "yar bakin kasuwa mai sai da abunci a titi, Mama wai Moddibo ya rasa yarinyar da zai so sai wannan yarinyar ni nafi kowa sanin wacece ita"

 

 

Murmushi fulani tayi tana girgiza kai tace"ta yaro kyau take bata k'arko, meye laifin ta ai ya fad'amin komai a kanta, yarinyar neman na kanta take, kaga na d'aya dai bata sata bata maita, bata zina, yanzu babban abunda za'a bunkita a kanta shine asalin ta Shikkenan, ai duk inda mutum yake yana tare da baiwar shi"

 

 

Tab'e baki yayi yace"gaskiya Mama yarinyar nan tana da fada! a gurinku, ke da Maimarta ba, shima lokaci guda ya amunce da maganar, ni kam banawa Moddibo sha'awar auran yarinyar"

 

 

Da murmushi a fuskar ta tace"D'a duk na kowa ne, kai dai kayi masa fatan alkairi kawai"

 

 

"To me nace yanzu, tunda yaji ya gani yana son ta a haka, Allah ya sanya alkairi"

 

"Ameen, abunda zakace kenan"

 

Hira sukayi  irin ta tsakanin d'a da uwa sannan yayi mata sallama ya futa,

 

 

*****

Karf'e takwas da rabi na dare, ya shirya tsaf cikin k'ananun kaya, riga  da wandon jins, masu kyau ya sanya farin galashi a idonshi, sai a gogo daya d'aura a hannushi na silvar ya tsunsa uku sanya da wasu manya-manya azurfa masu kyau da tambari irin na sarauta, wani bak'in takalmi ya sanya a kafarshi mai kyau da tsada, yayi wani mugun kyau sosai, duk wanda ya ganshi bazai gane Sarki! bane sabuda yadda k'uruciyar shi ta futo sosai d'an gemunshi ya kwanta yayi luf a fuskar shi sai shek'i yakeyi, babu wanda zai ganshi yace, shine sai wanda yayi masa farin sani, Turaranshi ya fesa wanda yake amfani dashi me suna (pure love) nan take d'akin ya d'ume gurin da k'amshi a nutse ya futa.

 

Buba Direba na jingine jikin mota, Sarki! ya futo sai yayi sauri ya b'ude masa motar tun kafin ya karaso, Cikin yanayin muryar shi yace"Malam buba, ba da wannan motar

zamu futa ba"

 

"Allah ya taimake ka, da wacce zamu futa"?

 

Wata bak'ar toyota ya nuna masa da hannunsa yace" muje a waccan"

 

Da sauri Buba Direba ya nufi inda motar take, yana buge ta, duk da tsaf take babu wata kurar arzki a jikinta nan ya bud'e masa ya shiga ya zauna cikin nutsuwa Buba yaja motar suka futa daga gidan.

 

 

 

 

 

 

*Comment*

*Vote and Share*

[18/07, 20:08] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

  ^^^^^^^^°

   _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^

                  đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

                   _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®{REAL BINTU BATULA}👄*

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

_ZAMANI WRITES_

 _ASSOCIATION_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rashim```

 

 

 

*🅿53*

 

 

 

 Sai bayan sun futa daga gidan ne, Buba ya d'an waiwayo A hankali yana kallon Sarki! dake kishin gid'e a bayan motar,yace"Allah ya taimake ka,ina muka nufa ne"?

 

A nutse yace"muje wannan unguwar da mukaje tare da Moddibo kwana uku da suka wuce,  Maimartaba ya umarce ni da bunkicen wani abu"

 

"To masha Allah ranka ya dad'e Allah ya bada sa'a"

Buba ya fad'a yana cigaba da tuk'in mota, a nutse.

 

 

Yau da wutar nepa a unguwar sabuda haka ko ina da akwai haske tar, can gefe guda Buba yayi parking din motar, yace"Yallab'ai gamu munzo"

 

 

A nutse ya dago kanshi yana bin gurin da kallo, wasu gugun! matasa ya hango sunfi su a shirin a bakin wani kanti, wasu na shan rake wasu na cin gyad'a mai b'awo, yayin da wasu suke cikin a wara, a wata k'atuwar takkada, sai hira ake suna dariya, cike da rashin kamun kai, ya dad'e yana nazirinsu, kafin ya bud'e mota ya futo a nutse, ya gyara zaman gilashin dake fuskarsa, Buba yayi saurin futowa shima, a nutse ya kalleshi yace"ka koma ka zauna cikin mota,Buba bana buk'atar rakiya"

 

Hannu ya d'aga alamun jinjija yace"a futo lafiya, ranka ya dad'e" ya koma cikin mota kamar yadda a ka umarce shi,

 

A hankali ya rik'a tsallake kwatoci masu d'auke da dagwalo na k'azanta, har ya k'arasa gurin wad'an nan matasan.

 

 

"Assalamu alaikum"

sallama ya fara yi musu, cikin muryarshi mai dad'in sauraro.

Hannu ya mik'a wa na kusa dashi yace"barka da dare abokina"

 

"Barka kadai" Salihu ya fad'a lokacin da yake mik'a masa hannun sukai gaisa, wani irin taushi yaji lokacin da hannusa ya had'u dana Sarki!

da sauri ya d'ago kanshi yana kallon fuskar Sarki!

gefe guda kuma wani mugun k'amshi ne ya cika musu hanci, shiyasa duk sukayi d'if! suka bar hayaniyar da suke suna kallo Sarki! dake tsaye,hannusa cikin na Salihu,

 

Gyaran murya yayi yace"Abokina in babu damuwa ina son in maka wasu tambayoyi"

 

 

Duk da Sarki! yayi basaja,domin kar a ganeshi, amma muryarshi taso ta tona masa asiri sabuda duk wanda yake cikin garin har in yana sauraron kafofin sadarwa,to muryarshi ba b'oyayyi b'ace mussaman da azimi,da lokacin aikin hajji, akwai wani Maudi'i yake gabatarwa na addini wanda kafafan sadarwa suke sawa kullum, wannan Maudi'i kuwa shi kad'ai yake gabatar dashi sai dai kawai, a tura shi Media, shiyasa Salihu ya furgita jin kamar Muryar Sarki! magajin Sarki, yace"babu komai in sha Allahu zan baka amsar abunda zaka tambaye ni mutukar na sani"

 

Fuskarshi a sake yace"muje can gurin maganar sirri ce"

 

Jiki a sanyaye Salihu ya mik'e ya bi bayan Sarki! sauran abokanshi suka bisu da kallo cikin mamaki,

 

Kai! wannan guy, d'in me ya kawoshi gurin Salihu, Allah yasa dai ba wani abun ya jawowa kansa ba"

Maganar daya daga cikin  matasan  dake gurin kenan, "To wa yasa ni mudai babu ruwan mu"

na kusa dashi yafad'a ya cigaba da shan raken sa.

 

 

 

Can wani gefe suka tsaya,wanda yake da k'arancin haske, A nutse Sarki! ya kalli Salihu yace"Abokina kasan wata yarinya Balaraba a nan unguwar"?

 

 

Shiru yayi na tsawan minti biyu yana tunani can yace"Eh na san wata a can lungun take" yafad'a yana nuna lungun gidansu Balaraba, ya cigaba da cewa, "amma gaskiya ba a fiye kiran ta da sunan ba sai a gidan su mu dai matasa muna kiranta da Gimbiya sabuda girman kanta, gashi ita ba " yar kowan kowa ba, a na tunanin ma Uwar da ta haifi baban ta Mayya ce"

 

 

Shiru Sarki! yayi yana nazarin maganar yaron, daga bisani yace" kasan gidan nasu ne,inaso ka rakani gurin baban ta"

 

 

"Nasan gidan mana"

Salihu yafad'a ya cigaba da cewa"k'anin ta Walidi abokina ne, Allah yasa kai ma ba wani abun tayi maka ba, dan jiya ma wanta Iro ta cirewa d'an yatsa guda, yanzu haka yana can kwance yana jinya"

 

 

Cikin mamaki Sarki! yace" garin yaya mace kamar wannan zata cirewa saurayi kamar ka d'an yatsa guda, dame ta cire masa"?

 

 

 

"Humm Wannan yarinyar ai inda kasan " yar daba haka take, da wuk'a take yawo, mu dai inda mukaji wai tana so shi yayan nata yayi lalata da ita dama kuma shine zai aure ta, shine da yak'i amuncewa ta futo da wuk'a ta yanke shi, muje in raka ka kaji a bakin mutan gidan nasu"

 

Cikin mamaki Sarki! yake bin bayan Sallau, yana al'ajibin abunda Salihu ya fad'a masa yanzu al'amarin yarinyar har ya kai haka

 

 

Yayi mamaki sosai da inda yaga yarinyar take rayuwa a rin wannan lugun mai tattare da k'azanta da bola amma take wa mutane kallon banza,

 

 

Shamsiyya na zaune a kujera "yar tsuguno tana lissafa cinikin a wara, ta bisu da kallo, da Sauri Sarki! ya dauke kanshi zuciyar shi na wani irin tashi, sabuda kauri gami da zarnin futsari da warin bola da ya cika masa hanci, hankici ya futo da shi yana d'an goge fuskarsa cikin basarwa, Salihu ya k'arasa kusa da ita yace" Shamsiyya babanku yana nan"?

 

"Bayanan menene"?

tafad'a kai tsaye

 

"Dama wannan guy din ne yake neman shi"

 

Da sauri ta mik'e ta karasa kusa da Sarki! cikin kwarkwasa tace"sannu ina wuni"?

 

Dauke kai yayi da sauri, sabuda wani irin k'auri da yaji tana yi yace"lafiya lou alhamdulilahi"

 

"Salihu yace " wai kana neman babanmu"

 

"Eh hakane"?

yafad'a ba tare da ya kalleta ba.

 

" Bayanan amma bari in sanya yaro ya kira maka shi yanzu"

tafad'a tana kokarin tafiya, sai wani murgud'a mazaunai take,wai dole sai ta burgeshi,

Tare suka jera da Salihu domin futa bakin lungu ko zata ga Walidi ta tura shi ya kira baban nasu domin tana ganin wannan bak'on nasa na alkairi ne.

 

 

 

Kanshi a kasa yayin da ya zuba hannuwansa duk biyun cikin aljihun jins d'in dake jikinshi,yana jimanta labarin da Salihu ya bashi a kan Balaraba, lallai in ko hakane yarinyar ba matar aure bace.

kanshi a kasa ya fara jiyo wani mugun k'amshin turare mai dad'in gaske, d'ago kansa yayi, karaf! suka had'a ido ta cikin gilashin dake idonshi yake kare mata kallo, a kwai hasken fitala tunda da wuta lokacin, d'auke kanta tayi cikin izza! da tak'ama take tafiya, tana sanye da wasu riga da wando pakistan ta masu kalar blue da pink da adon wasu manya-manyan stons masu shek'i ta yane kanta da wani mayafi wanda ya sakko kad'an ya rufe mata k'irjin ta amma duk da haka ana ganin tudunsu, wandon ma duk da burgujeje ne,amma bai hana bayyanuwar sharp dinta ba, masu gigita lafiyayyan namiji kai har wanda ma bai cika lafiya ba, in ya kalli duri da k'irar Balaraba sai yayi sha'awa, shima da sauri ya kauda kai, ya d'an sosa kansa kamar yadda ya saba, yace"Jimana "yan mata"

 

Tsayawa tayi tana shan k'amshi, gefe guda kuma tana tunanin a ina tasan wannan muryar.

 

Cikin Yanayin tafiyar shi ya karasa inda take tsaye tana masa wani kallo sama sa k'asa,tana tab'e baki, har ya k'araso ya tsaya dab da ita, tayi saurin matsawa baya, tace"Lafiya Malama"?

 

Gyara murya yayi ya k'ara yin k'asa da ita yace"amm" ina neman maigidan nan ne wanda kika futo daga ciki"

 

D'auke kai tayi ta d'an turo baki gaba, tace"bayanan" tana fad'a tayi gaba,tana d'aga kai sama, as,usul

 

"Ok yanzu a ina zan same shi a kwai abunda ya kawo ni, gurin shi"

yafad'a yana d'an daga muryar shi sabuda tayi masa nisa kad'an.

 

Tsayawa tayi tace"in zaka iya tsayuwa nan ka tsaya ka jira shi,yanzu zai dawo tunda tara tayi"ta k'arasa maganar tana k'okarin tafiya a karo na biyu, da sauri yace"d'an tsaya mana, "yan mata ai ban gama tambayar ba"

Wani irin kallo ta watsa masa,wanda yasa shi saurin dauke kai, "wai me zan maka ne, uhum? ka tambaye ni na baka amsa,sai me kaga ina da uziri ni,yi sauri kafad'i abunda zaka fad'a in wuce abuna"

Ranshi ne ya b'aci sosai! jin yadda take masa tsawa sai kace wani sa'an ta, lallai yarinyar nan baza ta canza ba, kanshi ya sosa kad'an yace"naji kince tara na dare tayi, ke ina zaki a matsayinki na "ya mace me kamun kai, babban abun mamaki ma kin ci uwar kwaliyya gami da turare mai dad'i me zai hana ki tsaya ki tayani hira kafin Baban yazo"

 

Wanini irin kallo take masa,wanda kana kallonsa kasan ta shirya wulak'anci, a ya tsine tace"baka da hurumi a kan abunda kake tambaya ta,haka kawai daka ganin sarkin fawa sai miya tayi zak'i, aikin banza kawai ni natsani munafurci wallahi, ka tambaya an baka amsa ka tsaya neman magana"

Wani irin d'aci-d'aci ya fara ji a bakinshi,tsigar jikinshi ta fara tashi, tunda yake a rayuwar shi babu "ya macan da ta tab'a ci masa mutumci irin wannan sai wannan yarinyar,

Daure zuciyar sa yayi kawai yana bin ta da kallo, tabbas ya gazgata abunda Salihu ya fad'a masa yanzu a kanta

 

 

Tun daga Nesa Shamsiyya ta hango Balaraba da Sarki! a tsaye, tamkar zata tashi sama haka ta k'araso gurin zuciyat ta tana tafarfasa, tace" ke dabbar Araf! mayyar maza, wato ke duk inda ki kaga namiji sai kin nuna masa ke karuwa ce ko, to bari kiji wannan da kike gani yafi k'arfin wallahi sai dai ki gani ki kyale, domin shi dai ba d'an iska bane irin ki"

Shamsiyya ta karashe maganar tamkat zata tsone mata ido

 

Abun mamaki sai yaga kawai Balaraba ta girgiza kai zata wuce ba tare da tacewa Shamsiyya komai ba, a zuciyarsa yace"wato wannan yarinyar rashin kunyar ta da rashin mutuncin ta akan mu yake" kallasa Shamsiyya tayi tana wani fari da ido ta jawo mayafin da Balaraba ta nannad'e kanta dashi Balaraba tayi saurin dafewa sanadin haka har sai da wayarta ta fad'i k'asa had'e da pose d'ita sabuda in ta cika, Shamsiyya zata iya cirr mata kuma babu hula  zai ga gashin ta, Shamsiyya tace"kaga wannan wallahi kar ka yadda da ita,sai ta lalata ka, dan muguwar makira ce ta iya kissa da kisisina duk da haka takewa maza irin ku masu kud'i"

 

A dake! yace"to ke wanene yace miki ni mai k'udi ne, sakar mata mayafi ta tafi"

yafad'a a cunkushe, dan yaji haushin abunda tayi Balaraba ko meye dalili oho

 

Sakar mata mayafin tayi tace"gayyar tsiya gayyar datti da najasa sai an dawo"

 

Wuce Balaraba tayi bata kallon gabanta, sabuda tsanani b'acin rai, karo sukaci da Sallau ya shigo lungun yana baza babbar riga sai kace wani limami  ya kalleta, a banza ce yace"wallahi in baki dawo da wuri ba zaki zo ki tadda mun kulle k'ofarmu domin baza mu tsaya jiran ki ba"

yana gama maganar sho ya shige bagaz-bagan,

 

Duk wad'annan maganganun da Sallau yayi kamar a gaban Sarki! yayi su dan yaji komai, haka Shamsiyya.

 

 

 

 

 

*Muje zuwa*

 

 

 

*Comeent vote and Share*

[19/07, 22:49] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

  ^^^^^^^^°

   _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^

                  đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

                   _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®{REAL BINTU BATULA}👄*

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

_ZAMANI WRITES_

 _ASSOCIATION_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rashim```

 

 

 

*🅿54*

 

 

 

 

Sai surutu Shamsiyya take masa, kanshi a k'asa  sam baya k'aunar ya kalli fuskar ta, haka Sallau ya same su, jiki na rawa yace"barka da zuwa"

 

 

D'ago kansa yayi a nutse ya kalli Sallau hannu ya mik'a masa yace"barka kadai Baba"

 

 

Washe baki Sallau yayi yace"yan samari nayi mamaki jin cewar nayi bak'o,gashi bangane fuskar ka ba"

 

 

Shamsiyya tana tsaye tana dariya tace"aikuwa nima nace bangane shi ba"

 

 

Shiru yayi na minti biyu ya kalli Shamsiyya a ya mutse yace"d'an bamu guri, zamuyi magana ne"

 

Yak'e tayi tana "yar dariya takama hanya zata huce Sallau yace" ai "yata  ce in taji babu komai" bana buk'atar taji"

yafad'a babu walawala a fuskar shi, wani kwarjini yayi wa Sallau sabuda haka sai ya kalli Shamsiyya yace ki shiga gida" Ko kunya babu ta shiga gida, sai ta mak'ale a soron gidan ta kasa kunne tana so taji, abunda ya kawo wannan guy addu'a take Allah yasa cewa zaiyi yana sonta,

 

 

A nutse Sarki! yace"wani abokina ne yaga "yar gidan nan shine muke bukince a kanta, ance mana kaine mahaifinta"

 

Washe hak'ura Sallau yayi yace"Eh duk "yayana ne, wacce kakw nufi a cikinsu"?

 

 

" Balaraba"

yafad'a kai tsaye

 

Murtuke fuska Sallau yayi yace"wannan lalatacciyar yarinyar kake nufi, yanzu nan ta futa yawon bariki, ai inaji ma ka ganta wata gansamemiyar mara kunya"

 

 

"Eh naga wata yarinya yanzu ta futa ko ita ce"?

 

" Babu shakka itace, shawarar da zan baka shine kaje ka fad'awa abokinka ya janye maganar auran ta domin ba d'iyar arzik'i bace, ni ne wan mahaifin ta, na santa ciki da waje jiya nan ta yankewa d'an uwanta ya tsa da wuk'a, sabuda haka in mata yake so yazo zan bashi d'aya daga cikin "yayana masu hankali da tarbiya"

 

 

Yafi minti biyar yana nazarin maganganun da Sallau ya fad'a masa, daga bisani yace"shikkenan dama abunda ya kawo ni kenan"

 

 

Sallau yace"to madallah, ka gayawa Abokinka cewar yazo ya duba d'aya daga cikin "yayana zan bashi, amma ya rabo da wannan yarinyar,in ba haka ba sai ta kashe shi"

 

 

Sarki! yace"za'afad'a masa, hannu ya zura cikin aljihun jins d'in dake jikinsa ya ciro kud'i kimanin dubo goma ya mik'a masa,

 

jiki na kyarma! ya warce kamar zai had'a da hannusa, saura k'adan ya tsuguna sabuda tsabar godiya da rawar jiki, nan Sarki! ya wuce ya barshi yana sambatu daf, da zai futa daga lungun sukayi karo da Balaraba, fad'uwa ta kusa yi yayi saurin rik'o hannuta, yana kallonta ta cikim gilashin dake idonsa, kallon kallo sukeyi da ita, fuskarta a had'e ta fuzge hannunta tana hararasa, tare da zabga tsaki tayi gaba, ji yayi bazai iya jurewa ba yasa ya tarota ta hanyar fuzgota ta dawo gabanshi, ya rik'e mata kafad'u da duk hannuwan shi sannan ya mannata da bango  fuskarsa daf da tata yace"wai ke dame kike tak'ama ne, mara kunya, dan ma kin samu zaki fad'i na taimake ki shine zakiyi min tsaki"  a tsiwan ce tace"anyi maka d'i... bata karasa ba ya rik'e bakin da ya tsunsa biyu ya murd'e leb'ubunan fuskarshi babu walwala yace"wai me kike da suna"? Balaraba kome? d'azu kafin ki futa kin min tsak'i yanzu ma haka, daga kawai an miki tambaya, zakina wa mutane, tsaki, wai ke kina tak'ama da kyau,ko dame kike tak'ama ne"? yafad'a yana zura hannun shi ta bayanta in da ya shafo tudun mazaunan ta a hannunsa, cikin sigar duniyan ci,  yace "ko da wannan kike tak'ama ne"?

 

Zabura! Balaraba tayi tana mutso-mutso, gashi har yanzu bai sakar mata baki ba, wani munafukin murmushi ya saki, yace" yarinya ko dame kike tak'ama bai dame ni ba, babu abunki wanda zai rud'ani kamar yadda yake rud'a wasu mazan, yanzu "yar uwarki tafad'a min wai inyi taka tsan-tsan dake, bata sani ba ni ko a k'afa aka d'aura min ke sai na kwance,na gudu"

yana gama fad'ar maganarshi ya sake tayi taga-taga zata fad'i sabuda rashin k'arfin jiki, shi kuma kamar walkiya ya b'ace daga gurin.

 

Kamar ta d'ora hannu aka haka takejin wani mugun d'aci a zuciyar ta, gabanta ne ya fad'i lokacin da ta tuno muryarsa sai taji kamar tasan mai irinta, tsugunawa tayi a gurin tana cusa fuskarta tsakanin k'afafunta tafashe da kuka wurjanjan! babban bak'in cikinta yadda wannan guy d'in ya samu nasara a kanta, gashi ta kasa gane fuskarsa duk da haske futula, tunda take a duniya babu namiji da ya tab'a kusantar ta kamar haka,sai shi har yayi nasarar tab'a mata jiki, bayan shi sai Sarki! ranar da suka zo tare da Moddibo, shima kuma bai yi a banza ba sai ta d'auki fansar abunda yayi mata, ta dad'e tana kuka a tsugune a gurun, daga bisani ta mik'e ta shiga gida, duk suna zaune a tsakar gida Sallau yana mayar musu da magana  abunda ya faru, amma k'iri-k'iri yak'i futo da k'udin, tanaji Uwa! tana cewa"ai yadda Shamsiyya take f'adamin mutumin da yazo yayi mata, sabuda haka ko ya sake dawo wa ka had'ashi da ita kawai, amma me za'ayi da waccan mutsiyaciyar yarinyar, nan sukai ta zagin Balaraba, gami da mata mugun baki, duk tana jinsu a d'aki, abunda ya hanata kwana a gidan da ta kama haya shine, babu fenti babu shara, yanzu futar da tayi ma kenan, domin tasa yara su share mata gidan, tunda anyi fenti da yamma, haka ta kwanta tasa su Sadiya da Usuman a gaba tana kuka tunda take bata tab'a kukan maraici ba sai yau

 

 

 

 

 

*Comeent Vote and Share*

[21/07, 06:17] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

  ^^^^^^^^°

   _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^

                  đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

                   _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®{REAL BINTU BATULA}👄*

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

_ZAMANI WRITES_

 _ASSOCIATION_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rashim```

 

 

 

*🅿55*

 

 

 

 Da wuri ta tashi tayi shirye-shiryen ta, tsaf ta shiryasu Usuman cikin kayan makaranta, ta had'a musu shayi, suka sha, itama ta had'a tasha, tana zaune gefan katifa, wayarta tafara k'ara tana dubawa taga Moddibo ne, sai ta kusa katsewa ta d'auka, ajiyar zuciya taji yana saukewa,sai ya bata tausayi , sallama tayi cikin muryar ta mai dad'in sauraro, yace"Gimbiya kin tashi lafiya"?

 

"Lafiya k'alau, kai fa"?

" Nima k'alau na tashi, jiya nai ta kiran wayar ki tun safe a kashe, gashi baki futo kasuwa ba"

 

Cikin nutsuwa tace"wallahi kuwa na kashe ne sabuda ina da uziri,nagode sosai"

 

 

" Wane uziri ne wannan, da alama kina cikin damuwa"

yafad'a da cikin tausayin ta gami da so da k'auna

 

A jiyar zuciya ta sauke, tace" yanzu zan fito zan kira sai muhad'u domin maganar ta wuce a fad'eta a waya"

 

 

"Ok toum in sha Allahu yanzu zan futo sai mu had'u, amma kicire damuwar komai a ranka kinji ko"

 

 

K'walla da take k'okarin zubo mata take k'okarin mayarwa tace" nagode Yusuf sai mun had'u"

kashe wayar tayi ta aje gefan katifa, ta cigaba da kurb'ar ruwan shayin ta, sha takeyi kawai amma zuciyarta babu dad'i,, tana jiyo hayaniyar mutan gidan a tsakar gida,, Uwa sai cinikin awara take babu abunda ya dameta

 

 

A nutse ta futo daga d'aki nta ta jawo k'ofar gami da sanya mata kwad'o, Lantana na tsaye bakin k'ofar futa hannunta rik'e da wani k'aramin buhu da alama kasuwa zata shiga, wani kallon banza ta watsawa Balaraba, ta ci gaba da magana da Uwa! dake zaune a kujera "yar tsugono tana faman soyawa a wara, gaishe su tayi, suka k'i amsa wa, tace" Matar Kawu Ina antashi lafiya"?

Sadiya dake sunkuye tana wanki bakin rijiya tace"lafiya lou Balaraba,kin futo"?

"Eh matar Kawu"

Balaraba tafad'a tana k'okarin barin gurin.

 

"Allah ya bada sa'a"

Matar Kawu tafad'a ta cigaba da wankin ta.

 

"Ameen" Balaraba tafad'a ta nufi kofar d'akin Iya.

 

Iya jiki yayi sauk'i suka gaisa a gurguje, ta aje mata kular abuncin su Sadiya tayi mata sallama ta futa.

 

 

Ashiru yana cikin Napep yana jiran futowar ta, dan haka tana shiga suka gaisa, cikin mutumci yaja Napep din suka bar Unguwar.

 

 

Daf da zasu shiga kasuwar wayar ta tayi kara, tana dubawa taga Modibbo ne, d'aga wa tayi tace" Ina titin jark'asa yanzu, zan tsaya dai-dai masu sai da lemo da a yaba sai kasame ni a nan"

 

"Ok gani nan zuwa"

Moddibo ya fad'a gami da kashe wayar.

 

 

Futa tayi daga Napep d'in ta sallami Ashiru,

 

Nik'ab d'inta ta futo dashi ta sakaye fuskar ta,sabuda zurga-zurgar jama'a duk da safiya ce, ko minti goma batayi ba, taga wata mota mai kyau tayi parking a gabanta, d'auke kai tayi domin tasan ba motar Moddibo bace, futowa yayi yana murmushi, yace"Gimbiya wannan shan k'amshin naki yana burge ni, gaskiya dole maza su dunga jin shakkar ki"

jin muryarsa yasa ta waigo da murmushi a fuskarta tace"barka da zuwa"

"Barka kadai Gimbiya,shigo mota mana" yafad'a yana bud'e mata k'ofar motar, tunda take bata tab'a shiga motarsa ba sai yau, sabuda haka a nutse ta shiga, ya mayar da murfin ya rufe, ya zagaya ya bud'e ya shiga shima,

 

 

 

"Maddibo ya kalleta a nutse yace" wannan nik'ab d'in yayi miki kyau Gimbiyata"

 

K'okarin cirewa take, tace"kaga ni ko ala dole nake sashi sabuda kallon da ake damuna dashi"

 

"Nima kinyi min gata"

yafad'a da murmushi a fuskarsa,ya cigaba da cewa"da zaki dinga sawa daga nan har lokacin auran mu"

 

 

Kallonsa take cikin nutsuwa tace"Yusuf da gaske kana sona"?

 

"Kwarai kuwa"

yafad'a cikin shauk'i yau gashi ga ita

 

 

Idanun ta ne ya fara tara ruwa tace"zaka iya aure na dani da k'anne na biyu wato Usuman da Sadiya"?

 

 

Cikin tausayi yace"kwarai kuwa, duk abunda kike so ina so balle Usuman da Sadiya Gimbiya ki kwantar da hankali, in sha Allahu zan rik'e ko da amana"

 

 

Hawaye ne ya fara zuba a fuskarta, taso ta danne kukan amma yak'i dannuwa, tace"Nagode sosai, inaji a rayuwata bani da mai k'aunata kamar ka, na auna ka sosai na lura tsakani da Allah kakeso na, ba wani abu nawa ne yake burgeka ba,shiyasa na yanke shawarar tsayar dakai a matsayin mijina kuma Uban "yayana, sabuda haka in ka shirya kawai ka futo muyi aure in huta da bala'in da nake ciki"

 

 

Shima kamar zai yi kukan yake rarrashin Gimbyar tasa duk hankalinsa ya tashi, yace"kinyi magana a kan gab'a Gimibiya, dama ke kad'ai nake jira ki amunce min naj dad'i insha Allahu zaki futq daga halin da kike ciki zan aure ki domin kyawun halinki,ba dan kyau da wani abu naki ba, ni ina sonki tsakani da Allah" ya karasa maganar jikinsa na kyarma, ji yake kamar ya yaye mata damuwar dake damunta.

 

Rarrashin ta yake har sai da ya ga damuwar da take ciki ta ragu, domin har dariya tai masa,sai suka cigaba da hirarsu cikin so da k'auna, yace"yau baza ki shiga kasuwa bane"? girgiza kao tayi tace"yau bazan shigaba,zan koma gida ne, domin a kwai sauran aiki da nabari, zan tare a sabon gidan da nakama haya" gabanshi ne ya fad'i yace"kamar yaya kin kama haya? haya wace iri"?

 

Sunkuyar da kai tayi tace"har gida mana"

 

Cikin mamaki yace" Gimbaya kin kama hayar gida, kikace min maganar babu dad'in ji, ke baki san yanzu sai ki zama abin kwantacce ba, ne, kamar ki budurwa kina zaman kanki,gaskiya ban amunce ba"

ya k'arashe maganar da b'acin rai a fuskarsa.

 

 

" Yanzu ya kakeso ayi ne"

tafad'a da damuwa a ranta, domin bata son tona asirin gidansu"

 

 

Sassauta murya yayi yace"ki bar maganar kama hayar gida kiyi hakuri ki koma gidanku ki cigaba da zama kamar yau ne komai zai huce"

 

 

"Shikkenan, zan bi maganar ka"

tafad'a cikin tausayawa kanta"

 

" Yawwa nagode Gimbiyata, yafad'a fuskarsa d'auke da murmushi najin dad'i

 

 

Wayarsa ce tayi k'ara yana dubawa yaga Sarki! ne, Balaraba ya kalla fuskarsa d'auke da murmushi yace"ga mutumin ki fa"

 

"Wanene"?

tafad'a cikin rashin sani

 

" Sarki ne"!

 

Shan kunu! tayi ta d'auke kanta, murmushi yayi kawai ya girgiza kai tana ji yana masa magana yana amsawa sama-sama, da alama wani abun yake tambayarsa, yana gama wayar ya kalleta yace" muje in kanki gida, yana can yana jirana yanzu"

 

" A ya mutse tace"gashi ni kuma bangaji da ganin ka ba, sai yaya kenan"?

 

Agogon hannunsa ya kalla da murmushi a fuskarsa yace"Kiyi hakuri in kin bani dama zan shigo da daddare mu k'ara gaisawa, yanzu  muhimin abu ne yasa ya kirani"

 

 

Tab'e baki tayi tace" wannam d'an rainin hankalin wallahi na tsane shi"

 

 

Cikin mamaki yake kallon ta fuskarsa ta janza da yanayin damuwa yace"har kike rantsewa Gimbiya yanzu d'an uwan nawa kika tsana"?

 

 

Tab'e baki tayi tace"ranin wayo ne dashi,wai shi d'an Sarki, nifa gaskiya ko aure mukai da kai bana buk'atarsa a gidanmu"

 

 

Shiru Moddibo yayi yana jimanta al'amarin yace"ya kamata ki rage wannan tsanar da kike yi masa domin wata rana zata iya zama so, kamar yadda Annabi Muhammadu (Slw) yafad'a

 

 

 

 

 

 

*Comeent Vote and Share*

[22/07, 02:06] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

  ^^^^^^^^°

   _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^

                  đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

                   _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®{REAL BINTU BATULA}👄*

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

_ZAMANI WRITES_

 _ASSOCIATION_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rashim```

 

 

 

*🅿56*

 

 

 

 Shiru tayi masa kawai, yace"muje in kai ki gida ki huta don Allah kar ki sake futowa waje,domin bana son rana tana dokar miki fuskarki mai kyau da kwarjini"

murmushi tayi kawai, yana "yar dariya ya kunna motar suka bar gurin, kafin suka k'arasa gidansu Balaraba kira ya shigo wayarsa, yana dubawa yaga mutuminsa ne, a fili yace" aiki ya had'ani da wanda baya son jira,Gimbiya d'auki wayar nan"yafad'a cike da bada umarni,aiko batare data duba wanene yake kira ba, kawai ta d'aga wayar gami da kara ta a kunne, tayi sallama cikin siririyar muryarta mai dad'in saurare, gabanshi ne ya fad'i jin muryarta, sai yayi d'iff, sallama ta k'ara yi tana duba fuskar wayar a karo na farko domin taga wanene, Magajin Sarki! sunan da tagani kenan, tasan ko waye, tsaki taja ta zata kashe wayar, yace"ke ina me wayar yake,ne ke dashi duk kun zama shashashai, dallah bashi wayar zamuyi magana, kuma ki kuka da kanki gurin yi min tsaki, kinyi min sau biyu kar ki kar ki sake kiyi na uku, wani tsakin ta k'ara ja a karo na biyu, ta mik'awa Moddibo wayar batare da tace komai ba, k'arba yayi da hannu d'aya, d'ayan kuma yana tuk'i dashi ya kara a kunnensa gami da fad'in " ya a kayi ne, ganinan fa a kan hanya"

"Kar Allah yasa kazo d'in"

Sarki! ya fad'a da rai a b'ace! ya cigaba da cewa "an d'ora min nauyi duk a kanka, tun safe na kiran wayarka dan wulak'anci,kana min hanya-hanya sabuda kana tare da wannan mara kunyar yarinyar da in kayi wasa sai ta lalata ka, kaja mata kunne da kyau duk ranar da ta kuskura ta kuma yimin tsaki, sai nasa an d'aure ta a na tsawon kwana uku, ba budurwar ka ba,ko mecece d'inka bai dame ni ba sai ta d'auki hukunci,tunda kai so ya rufe maka ido kana gani tana abu na rashin kamun kai ka kasa tsawatar mata"

yana gama fad'in haka ya kashe wayar yana wani irin huci! ji yake kamar yaje ya samu yarinyar ya koya mata hankali, ranar da suka fara zuwa gidansu shida Moddibo tayi masa tsaki, jiya tayi masa yau ma tayi masa uku kenan, mutukar ta kara wani to sai ta fuskanci hukunci,

 

Babu Abunda Moddibo yace, kawai aje wayar yayi gefansa, Balaraba ta kalleshi cikin bacin rai tace"na lura kana mutuk'ar tsoran mutumin nan dubi irin masifar da yake maka a waya tamkar wani mahaifin ka, kayi masa shiru, bakace komai ba, gaskiya ka canza tsari, domin ina gani ko aure ma mukayi duk abunda yace da kai shi zakayi"

ta k'arashe maganar tana zumb'ura baki,

 

Ajiyar zuciya ya sauke dai-dai lokacin da yake parking d'in motar a bakin hanya, yace"kin kasa gane, Sarki! Gimbiya, na fad'a miki halinshi ne haka, yana da saurin d'aukar zafi ga muskilanci a cikinsa in ban dani babu da wanda yake sakewa, nine shi shine ni, shiyasa nake so ku samu fahimtar juna ke dashi, amma ina neman alfarma a gurinki don Allah"

Ya fad'i maganar yana kallon ta sosai, ya cigaba da cewa"in banda kina da alak'a dani, da yau babu abunda zai hanaki ki kwana a rufe, domin babu abunda Sarki! ya tsana kamar kayi masa tsaki ko yayi magana ka share shi,to duk yadda kuke dashi zai nuna maka kuskuran ka, sabuda shi mutum ne mai mutuk'ar son girma da rashin son wasa, kullum a kame yake,in kika fahimce shi sosai zaku zauna lafiya,a hakane kike ganin kamar d'an wulak'anci ne,shi"

Jin abunda Maddibo yace a kan Sarki! yasa Balaraba ta k'udurta a ranta, zata dunga yi masa domin ta k'untata masa, amma ba zata nuna gabansa ba domin kar yace bata jin magana, yanzu ma kwantar da kai tayi tace"Yusuf ba wai ina gudunshi bane, ni kawai jinane bai had'u da nashi ba, tun ganin farko da nayi masa, amma domin faranta maka rai zanyi k'okarin sashi a zuciya ta"

 

Murmushi Moddibo yayi yace"yanzu abunda zaki nuna min nasan kin dai na, bari in kira wayarsa ki bashi hak'uri"

 

Girgiza kai tayi da murmushi a fuskarta tace"shikkenan ka kira shi"

Wayar ya d'auka fuskarshi a sake ya fara kiran Sarki!

 

Yana ji yak'i dagawa har sai da Moddibo ya kira sau uku,sannan ya d'auka,shiru yayi bece komai ba, jin alamun and'aga wayar yasa shi saurin mik'a mata wayar, kasa-kasa tayi da murya tace"Allah ya baka hakuri"

Wani irin yarrrr! yaji a jikinsa lokacin da yaji sanyayyiyar muryar ta, kashe wayar yayi da sauri, yana da ya sanin d'agawa domin muryarta ta yanzu ta tayar masa da wani mugun tsumi wanda ya dad'e a jikinsa, sam d'azu bai ji wannan yanayin ba sai yanzu, jikinshi ya fara takurewa guri guda,ganin yadda sandar girmanshi ta mik'e sosai abun  mamaki, innalilahi yake yaja cikin zuciyarsa, jikinshi ya fara rawa, mik'ewa yayi wayar ta fad'i kasa, ko ta kanta bai bi ba, ya nufi bedroom d'inshi domin duba magani, dama yana ajesu sabuda irin haka wata drowar yq bude ya dauko kwallin maganin ya bud'e ya ciri biyu ya watsa a bakinsa, da sauri ya je ya bud'e firji ya ciro robar ruwa irin na gora ya b'alle murfin ya kora maganin dake bakinsa,sai da ya shanye ruwan tas sannan ya yada robar a gurin ya kwanta kan bed, ruf da ciki,sai mutsu-mutsu yake shi kad'ai yasan halin da yake ciki.

 

A cikin wannan hali Moddibo ya shigo ya same shi, cikin mamaki ya tsaya yana kallonshi, yana ta murk'ususu kan bed gashi ruf da ciki ya rik'e cikinsa da duk hannuwanshi biyu, k'araso wa yayi kusa dashi yana kiran sunan shi, d'ago kai yayi yana kallonsa da ido jajazir, yace"lafiyan ka k'alau kuwa, dubi yadda ka turme she bedshirt sai kace wani yaro na shigo sai sallama nake kana nan kama mutsu-mutsu"

 

Harararsa yayi, ya mik'e zaune da k'yar! bai so ya shigo ya same shi cikin wannan halin ba,  a tsarge ya mik'e tsaye bai tsaya komai ba ya nufi toilet da sauri dan kar Maddibo ya ga halin da yake ciki.

Dariya Moddibo yasa yana binsa da kallo, a fili yace" Yo me zaka b'oye min naga komai, sai anyi magana kace,kai mace bata gabanka har da ciki kuri wai zaka iya zama da babu aure, da wataran sai dai azo a d'auki gawar ka"

Sarki! yana jinsa yayi masa banza,  jikinsa babu kuzari sosai ya had'a ruwan sanyi da zafi ya dunga kurmawa kansa, wai ko zaiji dad'i ya jima a toilet d'in sannan ya futo yana shan kunu dan kar Moddibo ya k'ara wata maganar a zuciyarsa kuwa ya k'udurta gobe zai tashi da azimi tunda abun hakane.

 

Wasu riga da wando ya d'auko irin na shan iska ya sanya a jikinsa, ya fesa turaren shi mai k'amshi, sannan yaje ya zauna, har yanzu fuskarshi babu walwala ya kalli Moddibo yana ya tsine fuska yace"sai yanzu ka ga damar zuwa kenan? kana can tana hure maka kunne ko mijin tace"

 

Zama Moddibo yayi kusa dashi yana wata dariya cikin jin dad'i yace"wallahi kamar ka sani kuwa yanzu ma da kyar! na tawo domin na kasa gajiya da kallon kyakykyawar fuskarta"

 

Wani irin kallo yayi masa yana jin kamar ya gaura masa mari, ya tsani yaga namiji na zumud'i a kan mace, cikin gatse yace"me yasa baka kwana a can ba"

 

" Yo kwana nawa ne"?

Maddibo yafad'a yana wani lumshe ido.

 

Wani iri Sarki! yaji a zuciyarsa jin abunda Moddibo yace, gyara fuska yayi yana d'an tab'e baki yace" bayan kak'i ka bada had'in kai,kana can tana hure maka kunne, tuntuni nake neman ka, in fad'a maka abunda na bunkito a kanta"

 

Gyara zama Moddibo yayi yace"ina sauraronka nasan dai duk abunda zaka bunkito to na alkairi ne,domin nasan Balaraba bata da aibu, wanda zai hanani auranta"

 

 

 

 

 

 

*Comment Vote and Share*

[22/07, 20:34] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

  ^^^^^^^^°

   _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^

                  đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

                   _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®{REAL BINTU BATULA}👄*

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

_ZAMANI WRITES_

 _ASSOCIATION_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rashim```

 

 

 

 

*🅿57*

 

 

 

 

" Yarinyar da kake son ka aura "yar daba ce"

Sarki! yafad'a kai tsaye

Sakin baki Moddibo yayi cikin mamaki yace"ban fahimci abunda kake nufi ba, "yar daba kamar yaya"?

 

" Ina nufi tana yawo da wuk'ak'e a jikinta tana sukan wanda ta gadama, a yanda na samu labari cewar ta cirewa d'an uwanta d'an ya tsa"

wani mugun b'acin rai ne ya ziyarci zuciyar Moddibo idanunsa suka k'ank'ance yace" yanzu kai bakaji kunyar fad'ar wannan kalmar ba,akan yarinya kamila irin Balaraba"

"Wace irin kunya kuma,ana maka maganar gaskiya wannan maganar ta futo ne daga bakin Ubanta k'arewa ma"

ya karasa maganar yana d'aga kafad'a alamun abun bai dame shi.

 

" Duk abunda a ka fad'a maka a kan Balaraba k'arya ne, mak'iyanta ne, kawai masu neman suga bayanta"

ya karashe maganar cikin jin haushi

 

Murmushin k'asaita yayi yace"shikkenan in anjima da daddare ka shirya muje unguwar tasu ka k'ara tambaya kaji, da kunnen ka"

"Ko bak fad'aba dama yau zani gurinta, nifa duk abunda za'a fad'a kan yarinyar nan sai dai a fad'a sai na aureta insha Allahu"

 

Ya mutse fuska yayi yace"Allah ya sanya alkairi"

nasan dai ni ake fad'awa magana"

 

Mik'iwa Moddibo yayi yana k'okarin futa yace"ai duk kai ka jawo kana nuna tsananin k'inka a kan yarinyar, ko d'azu da tayi maka tsak'i nace ta baka hakuri duk dan ku fahimci juna"

yana gama fad'ar maganarsa ya fuce daga d'akin, hakan da yayi ya tabbatar wa da Sarki! yayi fushi dashi, Moddib mutum ne mai tsananin hak'uri da kauda kai, ganin fushinsa sai an shirya sabuda zakai tayi masa abu yana hak'uri, amma in yayi fushi ana dad'ewa kafin a shawo kansa,

 

Balaraba kuwa can gidan da takama haya taje,ta tarar yaran da tasa suyi mata aiki sun gama suna k'okarin kulle gidan, ta k'arb'i mukulin ta sallame su,

 

 

Gidansu Bushira ta wuce  daganan in lokacin tashi daga makaranta tayi sai taje ta d'auko su Sadiya,

 

 

Cikin mamaki Bushira taga Balaraba a gidansu tace" hala yau b'atan kai kikayi"

Shareta Balaraba tayi tw shege ciki tana zabga sallama,babarsu Bushira ta amsa tana daga cikin d'aki,tace"kamar muryar Balaraba, Bushira tace"itace mana, "yar rainin hankali"

da murmushi a fuskarta ta shiga uwar d'akin inda mahaifiyarsu Bushira ke zaune a kan ledar d'aki tana ninke kayan sawarsu, tace"Balaraba idonki kenan"

 

Cikin dariya Balaraba tace"wallahi kuwa Baba ina wuni"?

 

"Lafiya kalau ya mutan gida,ya kasuwa"?

 

" Lafiyalou alhamdulilahi"

 

"Masha Allah" Baba tace tw cigaba da cewa"ko jiyw sai da mukayi zancan ki da mutuniyar taki, tace wai tunda kin gujeta itama bazata k'arw zuwa gidan ku ba"

 

Dariya tayi tana d'an hararar Bushira dake tsaye tana kallon Balarabar tace"Baba wallahi rashin lokaci ne kinga ina futa da sassafe shiyasa kuma bana dawowa sai yamma, ai ita tasan inda nake a kasuwar me yasa bata zuwa, in ta damu dani"

 

"Gaskiya kam laifin ta ne"

babarsu Bushira tafad'a tana kokarin mik'ewa kchin tq nufa domin kawo wa Balaraba abunci da ruwa,  Bushira ta shaga d'akin sosai tana kallon Balaraba yace"lallai hajiyata kina lokaci wannan jiki haka kinganki kuwa yadda kikayi wani uban kyau da alama babu abunda yake damunki"

 

Tab'e baki tayi tace"ke wannan ya dama, dallah ni ki zauna kiji abunda ya kawoni, neman shawarw nake"?

Zama Bushira tayi kusa da ita tace"tofa ta samu kenan"?

 

 

Ajiyat zuciya tayi cikin tausayin kanta tace"Bushira aure zanyi, nagaji da wannan gararanbar da nake"

 

Zare ido Bushira tayi tace"wane me sa'a ne yayi dace a zuciyar ki"

 

 

Lumshe ido tayi tana murmushi tace"Yusuf kenan mallakin zuciyata  fari mai farar aniya, mai kyawun zuciya"

 

Dariya Bushira ta kwashe dashi ta bata hannu sukq tafa, tace"a ina kuka had'u da wannan me sa'ar ke kuwa"

 

"Gurin sai da abunci"

 

Cikin mamaki Bushira tace"na tayaki murna aminyata,amma zanso in ganshi, wanda har ya iya mallakar wannan b'akar zuciyar taki,me shegen muskilanci"

 

Duka Balaraba ta kai mata, tana shan kunu tace"banason iskanci wallahi,shikkenan daka mutum ya kama kansa sai a dunga kiransa muskili ko d'an wulak'anci"

 

" Mubar wannan maganar mu koma waccan ta Yusuf d'in yaushe zaizo inzo mu had'u"

Bushira tafad'a tana kanne mata ido d'aya cikin sigar tsokana,

 

" Yau insha Allahu zaizo ki gama abunda kike sai muje gida tare"

 

Bushira tace"ai kuwa babu wani abu da zanyi yanzu kawai sai cin abunci sai wanka"  "shikkenan muci abunci sai mutafi amma zanje d'auki su Sadiya a makaranta Hira suke irin ta k'awaye Baba ta shigo da kwano mai murfi cike da abunci shinkafa da wake, da man k'uli soyyaye sai yaji a gefe, ta aje a tsakiyarsu Bushira ta mik'e da sauri ta lek'a waje ta kira yaro ta aike shi yq siyo musi lemo na kwalba had'e da ruwan pure watar,

 

Dawowa tayi ciki, ta zauna Balaraba ta bud'e kwanon abunci, dariya tasa tace"lallai yau nazo a sa'a irin wannan gara haka, gaskiya inason wake da shinkafa a rayuwata, Bushira tace"ai ke dama "yar k'auye ce,sai auki son gayu kina abu irin na gidadawa, wai wake da shin kafa ta6!

Balaraba tace" kema baki san dad'i ba ne"

 

Yaron ya kawo musu aiken sannan suka fara ci Balaraba taci sosai rabon da tayi k'oshi irin na yau har ta manta,  k'arfe d'aya saura sun shirya tsaf, Baba tai musu fatan alkairi suka futa,  babu nisa dama tsakanin gidansu Bushira da makarantar sabuda haka a k'asa suke tafiya, Balaraba tace" kin san wani abu kuwa Bushira"?

Bushira tace"sai kin fad'a"

"Humm kwanaki sai ga mutumin ki a k'ofar gidanmu"

 

"Wanene"?

Bushira tafad'a cikin rashin sani

 

" Sarki! Almansur"

 

Tsayawa Bushira tayi cikin mamaki tace"gurin wa yazo"?

 

" Gurina sukazo shi da Yusuf ya rakoshi"?

 

" Ke ban gane fa ba kiyi min bayani dalla-dalla, nan Balaraba ta kwashe komai tafad'a mata, Bushira tace"yanzu dai kice Yusuf d'in naki jinin sarauta ne kenan"?

d'aga kai Balaraba tayi alamun hakane

 

Bushira tace"gaskiya lamarin ki da akwai abun mamaki Balaraba, Allah ya sanya alkairi, yasa za'ayi damu, ina fatan baki masa rashin kirkin ki ba ko"?

 

 

"Kinsan sai nayi, sabuda in nace bana son mutum to har abada bana sonsa,  sai da na nuna masa bai isa ba, shine ya tofa min miyau d'insa, ni kuma na d'auki alwashin sai na rama"

 

Dariya Bushira tasa tace"a ina zaki ganshi balle ki rama"?

 

" Na fad'a muki fa yadda suke da Yusuf,watarana  dole mu had'u  Bushira tace"gaskiya zanso inga wannan game din naku ke dashi"

 

Balaraba tace"ni zanso ki gani wallahi ke kin san halina bana manta abu komai dad'ewarsa sai na rama"

 

Bushira tace" yaya mutan gidan ku sukayi da sukaji labari"?

"Basu sani ba tukkuna"

 

" Nasan zasu tada hankalinsu, "yan bak'in ciki kawai"

 

Dariya Balaraba tayi tace"sai dai suyi kuwa in dai nice"

Haka suka k'arasa makarantar suna hirarsu gwanin sha'awa

 

 

 

Daf da zasu shiga gidan suka ci karo da Walidi, ya futo daga lungunsu yace"yawwa Gimbiya dama ke nake jira, ki dawo,na kira wayar ki naji a kashe"

cikin tashin hankali yake maganar

 

Balaraba tace"menene ya faru"

 

" Yanzu Kawu ya tafi gurin me unguwa, da goro da alwa,wai yau da asubah a d'aura miki aure da Iro,kan sadaki dubu biyar"

 

Wani irin yammmm! taji a jikinta jin abunda Walidi yace Bushira tace"anya kaji dai-dai kuwa,ko Shamsiyya a ke nufi"?

 

" Ya zakice haka abunda a kayi a gabana, wai jiya wani babban mutum ne yazo gurinta,shine yake fad'awa Lantata tace"maza yaje ya siyi goro a d'aura auran da Iro sabuda taga alamun yarinyar jininta na masu kud'i ne"

 

 

Balaraba tsugunawa tayi a gurin jiri yana d'ibarta tarasa abunda zatace, Walidi yace"yanzu meye abun iyi ne"

Bushira tace"kaje anjima zamu kiraka" wucewa yayi yana fad'in ina saurare, ni da cewa nayi ko zata gudu ne kawai sabuda nasan tunda suka had'a wannan makircin babu abunda zai hana a daura auran"

 

"Hakane komai nufi ne na Allah babu wanda yasan mijinta sai Allah, kaje kawai zamuyi shawara"

 

Tafiya yayi, Bushira ta kamata ta mik'e tsaye suka shiga gida, zama sukayi gefan katifa Sadiya da Usuman suka nufi d'akin Iya domin cin abunci

 

 

Bushira tace"ana wata ga wata yanzu me kika yanke"

 

Wayarta ta d'auko cikin jaka tafara lalubar numbar Yusuf d'in ta fada masa halin da ake ciki, hankalinsa ya tashi sosai yace ta saurare shi zaizo kafin la'asar sukayi sallama

 

 

Yana gurin wani abokinshi wanda suke harkokinsu a tare a kasashen waje, lissafi suke na irin ribar da suka samu bayan dawowar shi daga Swiziland , hankali a tashe yayi masa sallama kai tsaye gida ya koma bai zame ko ina ba sai sashen Sarki!  suka had'u a farfajiyar gurin, yana tare da Buba Direba zasu fita wata jana'iza yanzu, wanda me Martaba ya wakiltashi, yana sanye da wata alkyabba mai kyau da walwali kanshi ned'i ne irin na sarauta, k'afarshi sanye da wani takalmi mai gashi-gashi yayi bala'in kyau in ka kalleshi sai ka k'ara kallonsa,wasu fadawa ne uku tsaye a bayanshi, tsayawa yayi yana kallon Moddibo har ya k'araso inda yake, fuskarsa ya kalla yaga kamar yana cikin damuwa, yace"har ka gama jin haushin nawa"?

 

" Muje mota,zamuyi magana"

 

Tab'e baki yayi kawai yq fara tafiya cikin kasaita, Moddibo yq rigashi zama ciki sabuda yanayin tafiyarsu ba d'aya bace, yana shiga Buba ya rufe motar, ya zagaya da sauri ya zauna a mazaunin sa, su kuma wad'an nan fadawan suka shiga mota guda suna bin bayan motar a nutse

 

Banyan sun d'an yi nisa da tafiya Sarki! ya kalleshi yaga duk a furgice! yace"kayi shiru wai menene"

 

"Balaraba za'ai wa aure"

yafad'a kamar zai rushe da kuka!

 

Wata dariya ce ta kama Sarki! ya dara yace"shine zakayi kuka lallai Moddibo yarinyar nan zata zautaka, sai me in anyi mata aure,? dama can Allah ya nufa ba matar ka bace"

Cikin damuwa da b'acin rai Moddibo yace" ba nafad'a maka damuwa ta bane domin ka b'ata min rai ba, na fad'a maka ne domin ka nema min mafuta"

 

 

"Ok toum yanzu me zanyi maka, dama ni bana son ka aureta sabuda haka babu wani mafuta da zan nema maka"

 

A nutse Moddibo ya juyo yana kallonsa yace"alfarma d'aya nake nema a gurin shine ka amunce min in kawo Balaraba shashen ka in b'oyeta kafin ka gama bunkice a kanta, dan girman Allah kaga daga mungama bunkice a kanta sai muje mu samu me Martaba mu fad'a masa halin da ake ciki,amma yanzu in muka bari a ka daura mata aure rayuwarta tana cikin ha tsari, nima zaku iya rasani, domin zuciyata zata iya mutuwa"

 

 

 

 

*Comment Vote and Share*

[23/07, 16:23] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

  ^^^^^^^^°

   _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^

                  đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

                   _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®{REAL BINTU BATULA}👄*

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

_ZAMANI WRITES_

 _ASSOCIATION_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rashim```

 

 

 

*🅿58*

 

 

 

 

 

Cikin mamaki yace"ban fahimci abunda kake nufi ba, kana nufin ka kawo min ita shashena ka aje, min kan wane dalili zaka had'ani da mace baliga irin wannan"

 

Cikin kwantar da kai Moddibo yace" ai a k'asa zata zauna, kai kana sama, duk abunda kake buk'ata da a kwai a saman ka,nasan in ba neman magana ba babu abunda zai sakko da kai k'asa"

 

 

"Shikkenan sabuda buk'atar ka sai in dai na zaman farlo sabuda ka aje " yar gwal,sai in takure kaina,kasan abunda bazai yi hu bane"

Ya k'arashe maganar yana masa wani kallo a d'age!

"Shikkenan to ka bata aron d'aki a saman mai d'auke da toilet, ni zan dinga kawo mata abunci,da komai na buk'ata,banaso ma ta futo balle masu yi maka hidima su ganta su zargi wani abun"

Ganin yadda Moddibo ya wani sukurkuce yasa yace"shikkenan" sakin fuska Moddibo yayi yace"nagode d'an uwana,na baka amanar ta ka kula min da ita don Allah"

Cikin shank'amshi yace"ban karb'i amana ba, gaskiya ga guri nan da ta zauna"

 

"Shikkenan hakama nagode"

Moddibo ya fad'a cikin farin ciki, ya cigaba da cewa yanzu, in mun dawo me zai hana mu tsaya a gidan nasu ko"?

 

 

Girgiza kai yayi kawai yayi shiru, hakan ya nunawa Moddibo bai yadda ba, shiru yayi bai sake maganar ba yana jin tsoron kar ya botsare masa, yasan halin kayansa.

 

 

 

****

Sai bayan sallahr la'asar suka dawo gida, Moddibo ko zama baiyi ba, ya k'ara futa shi kad'ai a mota,

 

 

Balaraba suna zaune ita da Bushira suna jiran zuwan Moddibo domin yayi mata waya yace gashi nan kan hanya, "yan kayanta ta had'a a k'aramar a kwatu, ta had'a nasu Sadiya da Usuman tanayi tana kukan bakin ciki da halin damuwar da take ciki, Bushira sai tausar zuciyarta take, Lantana ce yi sallama ta shigo d'akin tayi musu wani irin kallo,na raini da wulak'anci tace" Au kuka kikeyi, dan mugun hali, in ceko "yan gulma sun fad'a miki d'aurin auran ki da d'an uwanki ne,shine kike koke-koke banza,to ko kukan jini zakiyi sai dai kiyi munafuka kawai,ai da wannan lalatar da kike gwara ayi miki aure kar ki jawo mana abun kunya   a gari"

 

 

Haka Lantana ta k'araci zage-zagenta ta futa, basu ce mata komai ba, suna jiyo shewarsu Uwa da "yayanta a tsakar gida, sai zaginta suke, Iro ne ya shigo shima ya zauna anayi dashi,

 

 

Wayarta ce tayi k'ara Moddibo ne, ta d'aga wayar gami da karata a kunne, cikin sanyin murya tace" Yusuf, ka zo ne"?

 

"Eh ina cikin unguwarku, na bari ay sallahr Magariba duhu yayi sai in zo"

 

"Yawwa dama abunda nakeso ince kenan" tafad'a tana kokarin kashewar jin alamun za'a shigo d'akin, Iro ne ya shigo yana wani lasar baki, idonshi tar! a kan Balaraba, yace"amaryata ya akai ne"?

K'okarin tsallake Bushira yake yi yaje kusa da Balaraba yw zauna, Bushira tayi saurin janye k'afarta hakan yasa ya fad'i k'asa kamar wani soko, dama ga jiki babu k'wari  ya mik'e yana layi yace"ke tashi ki futa zani magana da amarya ta"Wari ne ya cika d'akin na tsamin hamta da warin ganye, zuciayarta taji tana wani irin tashi, Balaraba kuwa tuni ta toshe hancin ta, Bushira tace"kai in banda abunka Iro ai kamata yayi kai da zakazo gurin amaryar ka kaci kwalliya kazo kana k'amshi, ba wari ba, yanzu abunda za'ayi kaje kayi wanka kasa kaya masu kyau ka fesa turare in kanaso amaryar taka ta saurareka, jin abunda Bushira tace, yasa ya washe baki yana kallonta yace"kina nufin ta yanzu ta amunce dani"?

"Sosai kuwa"

Balaraba tanai masa murmushi kamar gaske

Futa yayi daga d'akin yana fad'in yanzu zanje kuwa in shek'awa amaryata kwalliya"

 

Yana futa suka fara dariya kasa-kasa Bushira tace"wannan ya kasance a mijinka ai ka shiga uku da wari da tsamin hammata"

 

 

Cikin takaici da damuwa Balaraba tace"rabu da shashasha mahaukaci kawai"

Dariya kawai Bushira take mata.

 

Sai bayan sallahr isha'i sannan Moddibo yazo, yana zaune cikin mota yana tunani,sai yaga gilmawar Walidi, ya sauke glass d'in mota yana kiransa, dawowa Walidi yayi ya tsaya, ganin fuskar Moddibo yasa ya washe baki yace"yallabai barka da zuwa"

 

"Barka kadai abokina"

Moddibo ya fad'a ya cigaba da cewa" kaje ka kiramin Gimbiya"

 

Da sauri Walidi ya tafi, lokacin duk sun watse a tsakar gidan babu kowa, sabuda haka da sauri ya shiga d'akin Balaraba tace"yawwa dama kai nake nema d'auki wannan a kwatun ka futa dashi, zakaga wani mutum da mota a bakin lungu" Walidi yace"ai shine ya aiko ni ma yanzu"  "Ok yi sauri ka kai masa" hannu biyu yasa ya d'auka ya futa da sauri,su kuma suka mik'e suna yafa mayafansu, Bushira ta rik'e hannun Sadiya, Balaraba ta rik'e hannun Usuman a haka suka futa daga gidan, lokacin babu mutane sosai a waje, sai yara k'ananu, sabuda haka basu fuskanci komai ba, nan Walidi ya bud'e bayan motar ya zura jakar ya mayar ya rufe ya tsaya yana hangowar zuwansu Balaraba, Moddibo yana ganin tawowar su ya bude mata kofa, su Sadiya tafara sakawa,  ta tsaya suna sallama da Bushira Moddibo ya zuro kanshi  suna gaisawa da Bushira, kud'i ya ciro wanda bai san adadinsu ba, ya mik'a mata, ya k'ara ciro wasu ya mik'awa Walidi dake ta washe baki, yace "ina neman alfarma a gareku da ku rufe wannan abu a tsakanin mu, in kukayi haka kunyi jahadi,bayan komai ya lafa zan muku kyauta ta mussaman"

 

 

Bushira tace"Babu komai Yallab'ai"

 

Godiya yayi musu ya kunna motar cikin sauri yaja motar, su kuma suka bar gurin cikin mamaki kyautar kud'in da yayi musu.

 

 

 

 

Shiru cikin motar babu wanda yace komai sai da suka hau titi sosai sannan Moddibo ya juyo fuskarasa d'auke da murmushi yace"Gimbiya wannan ce Sadiyar"?

 

 A hankali tace"Eh"

 

"Kai masha Allah kuna kama da ita amma ba sosai ba"

 

Murmushi tayi kad'an da damuwa a fuskarta tace"Yusuf ina ka shirya a jeni ne"?

 

Fuskarshi ya gyara yana kallonta ta cikin mudubin motar,yace"gidan mu mana amma kina keb'antaccan guri,wanda babu wanda zai san dake a gurin"

 

 

Ajiyar zuciya ta sauke hankalinta ya kwanta tace" nagode Yusuf Allah ya kara mana so da k'auna"

 

 

"Ameen gimbiya ta"

yafad'a yana kallon Usuman dake kwance kan cinyarta yace"yayi bacci kenan"

 

 

"Baccin dai yake so yayi" tafad'a tana shafa kansa

 

 

Girgiza kai yayi yace"yaran suna bani tausayi sosai, in sha Allahu maraicinku ya k'are"

 

 

Wasu hawaye masu zafi ta d'auke tace"godiya a gareka gwarzo na zuciya ta,a yanzu banda kowa banda komai sai kai, nice kai, kai ne ni"

 

 

 

Sosai Moddibo yaji dad'in wannan kalamin nata, wani irin nishad'i yake ji a zuciyarsa

 

 

 

Hanyar gidan Sarki yaga ya nufa, bata kawo komai a ranta ba, sai da ta gansu dai-dai kofar shiga cikin gidan sarautar yana kokarin shiga da Motar tace" me za muyi a nan"?

 

 

 

Fuska sake yace"bana ce miki k'ebantaccan guri zan kawo ki ba,kinga nan gidan babu wanda zai san kina ciki,

 

 

Shiru tayi kawai gabanta yana wata irin fad'uwa, wata doguwar kwalta dake shimfud'e a cikin gidan suke bi, a hankali yake jan motar har suka iso shashen Sarki! me gadin gurin ya bude masa get ya shiga da Motar,  gabanta ya dina fad'uwa wanda bata san dalili ba, duk inda ta kalla a gidan wasu irin tambari ne da zane-zane irin na sarauta anyi musu ado da wani abu mai kyalli,kasancewar a kwai haske tarwai a gurin, yasa taga hadiman dake kaiwa suna kawowa a gurin kowa da aikinshi,  gurin aje mota suka nufa, tana ciki motar ta zama "yar k'auye ganin wasu shirga-shirgan mota masu kyau irin na masu a mulki,a fake a gurin, shima gurin k'ayata shi da wata rumfa, mai mai d'auke da ado mai tsari, parking d'in motar yayi, da sauri wani fade ya bude masa ya futo ya tsaya ya jingina jikin motar, ya futo da waya,yana k'okarin kiran Sarki!

 

 

 

 

 

 

*_Muje zuwa_*

 

 

 

 

*Comment Vote and Share*

[24/07, 16:56] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

  ^^^^^^^^°

   _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^

                  đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

                   _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®{REAL BINTU BATULA}👄*

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

_ZAMANI WRITES_

 _ASSOCIATION_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rashim```

 

 

 

*🅿59*

 

 

 

 

Ya zaune a farlo cikin kujerar shi ta hutawa, wani k'aramin littafi ne a hannunshi irin na addini yana dubawa, idanunshi sanye da farin tabarau na k'ara k'arfin gani, yana cikin wasu kaya na shan iska, cikin nutsuwa yake duba littafin,sai yaji wayarshi dake can kan kujera tana k'ara, alamun an kirashi, mik'ewa yayi a nutse ya k'arasa inda wayar take yana dubawa Moddibo ne, a nutse ya daga, gami da yin sallama,

Moddibo yace" gani nan zan shigo da ita"

 

"Wacece" yafad'a cikin sigar tambaya.

 

Cikin mamaki Moddibo yace"har ka manta da maganar mu ta d'azu kenan"?

 

Shi sam! ya manta da sunyi wata magana dashi,sai yanzu  tsaki ya d'anja k'asa-k'asa yace"naman ta ni, ina fatan kaja mata kunne dai"

 

"Baka da matsala da ita insha Allah"

 

Kashe wayar yayi,ya ajeta kusa dashi ya cigaba da duba littafin dake hannunsa.

 

 

A nutse Moddibo ya kalli Balaraba dake tsaye duk jikinta yayi sanyi, cikin zuciyarta take cewa anya batayi ganganci ba kuwa,  ta guda daga gidansu,tabi wani namiji uwa duniya,duk tsiyar naka,shine naka amma tayi amanna da Moddibo ba zai cuceta ba.

 

Hannun Usuman ya kama, suka fara tafiya, cikin nutsuwa yake k'ara kwantar mata da hankali, ganin da yayi jikinta yayi sanyi k'alau.

 

Wata k'atuwar k'ofa me murfi biyu taga sun nufa, suna isa bakin k'ofar wasu bayi ne tsaye d'aya a gefe d'aya a gefe hannusu rik'e da wata sharb'ebiyar bulala, suna ganin Moddibo ne sai d'aya yayi saurin bud'e masa suka zub'e suna kwasar gaisuwa, a nutse ya amsa musu, suka gaida Balaraba, ta amsa a dake! sannan suka shiga ciki,

 

 

Ji tayi k'afarta ta nutse a cikin wani abu mai taushin gaske, da sauri ta kalli k'asa inda taga wani kwantaccan kafet ya mik'e samb'al har inda Sarki! yake zaune, wani mugun k'amshi ne ya ziyarci hancin ta,  lumshe ido tayi cikin jin d'adin k'amshin ta bud'e ido tana rarrabashi cikin katafaran farlon mai d'auke da set d'in kujeru uku, ko wanne da sentar teble d'inshi a tsakiya, a tishawa su Sadiya da Usuman suka fara, saboda sanyin air condition d'in dake farlo, wannan atishawar da yaran sukayi itace tasa ya d'ago kanshi cikin  isa yana kallonsu daga can bakin k'ofa, shi kuma Moddibo dama ya gano shi a can in da yake hutawa, a nutse yake tafiya domin zuwa gurin, Balaraba kuwa sam bata lura da mutum a gurin ba da suka shigo, shiyasa da taga Moddibo yayi wani gurin sai ta zage,jiki tana ta kalle-kallenta na k'auyanci.

 

 

Usuman ne ya rik'e mata hannu, yace"Yayarmu sanyi nake ji"

jikinsa sai b'ari yake, kallonsa tayi,taga da gaske sanyin yake ji, ta kalli Sadiya taga itama ta takure cikin hijabi,sai mutsu-mutsu take, rarraba ido take a farlon tana so taga inda Moddibo yake, yazo ya kashe musu wannan abun mesa sanyi, bata ganshi, ba dalili  yana isa gurin Sarki! ya saki wani labule me igiyoyi masu kyalli yana gudun kar yayi masa halin nasa har Balaraba ta gani shiyasa ya saki labulen,  duk iya laluben ta ba taga Moddibo ba, ga Usuman bayan atishawar da yakeyi har da tari sai k'warewa yake, sam! ta tsani matsalar "yan uwanta, kalle-kalle take a farlo ko zataga inda ake rage k'arfin fankar a cewar ta  can ta hango wasu abubuwa a manne jikin bango, kai tsaye can ta nufa, batare da b'ata lokaci ba ta sanya hannunta ta murd'a da k'afi! aikuww farlo ya d'ume da wani sauti!! dimmmmmmm! da gudu! ta matsa daga gurin tana zare ido,wanda yayi dai-dai da futowar su Moddibo da sauri ya k'araso inda suke, yayi saurin yaje ya saisaita komai, shi kuma Sarki! tun kafin ya k'araso gurin yake zabga mata harara,  yana k'araso gurin yayi mata wani banzan kallo cikin wani irin murya yace" ke bagidajiyar ina ne,uhumm! kawai zakiyi tad'aga mana hankali baki iya abuba kice zakiyi, ni wallahi bana son hauka"

yafad'a yana me zama cikin kujera tare da hard'r kafa d'aya kan d'aya

 

Sai da ta kusan suma,lokacin da taji muryar sa, hankalin ta ya tashi, sai ta nemi miyau ko d'aya ta rasa a bakinta, sunkuyar da kanta tayi cikin jin kunya, tana tunanin abunda yasa Moddibo ya kawo ta gurin mutumin da baya k'aunar ta, wata zuciyar tace"k'ila had'a baki sukayi dashi,domin ya wulak'an taki,dama namiji ba d'an goyo bane.

 

 Shiru farlo yayi Modibbo ya rasa dame zai fara,  Hannun Usuman ya rik'e da hannu d'aya, d'ayan hannun kuma ya rik'e Sadiya dashi ya kalli Balaraba yace"zo muje kinji Gimbiya"

 

 

D'ago kai tayi tana kallonsa fuskarta a murtuke tace"ina zamuje, Yusuf dama ka d'auko mu ne domin a tozartamu, ni banga gurin zama ba anan"

ta k'arasa maganar ta tana kokarin kama hannun Usuman dake cikin hannunsa,

 

Tayi-tayi ta k'wace hannun daga cikin nasa ta kasa, rarrashin ta yake kan tazo ya nuna mata d'aki a saman bene,amma fafur tak'i ita k'okarinta ya bar ta ta futa da "yan uwanta domin sai yanzu ta fahimci abunda yake nufi ya kawota gurinshi, domin yayi mata cin mutumci sam baza ta iya zama inuwa d'aya dashi ba.

 

 

 

Cikin k'asaita ya d'ago kansa yana kallon tababar da sukeyi, tsakaninsu ya kalli Moddibo yace"  Meya sa kafin ka kawota nan baka fad'ama ta ba,? nifa wannan hayaniyar da kuke ta ishe ni, babu dole in zata zauna ta zauna, kai da zaka taimake ta kaine kake wani rarrashin ta, in bata zauna wa ka kyaleta kawai malam taje duk inda zata je, dama ta saba"

 

 

Moddibo ya d'an harare shi,bai ce masa komai ba ya mayar da hankalinshi kanta yana rarrashi,

 

 

Wa d'annan yaran fa?

 a sharad'in  mu dama a zata zo min da yara ne"?

yafad'a yana binsu Sadiya da kallo.

 

 

Moddibo yace" Yan uwanta ne,itace uwarsu itace ubansu,zata zauna tare dasu insha Allah ko aure mukai muna tare dasu.

 

 

 

Tab'e baki yayi ya mayar da kansa k'asa yana duba littafin hannunsa.

 

Da k'yar Moddibo ya rarrashe ta,tare ta bishi sama, tare da sharad'in gobe zai canza mata gurin zama, sai da ya tabbatar da ya kwantar mata da hankali sannan ya sauko k'asa cikin sauri ya nufi k'ofar futa, ko kallon Sarki! baiyi ba, saboda ya bashi haushi d'azu abunda yayiwa Gimbiyarsa bai dace ba, 

 

Tab'e baki yayi kawai ya cigaba da abunda yake, yananan zaune Moddibo ya dawo hannusa nik'i-nik'i da manya-manyan ledoji, kamar yadda ya futa bai kulashi ba, haka da ya dawo kai tsaye sama ya nufa, inda Balaraba take.

 

 

 

Wajan minti ashirin ya sakko, yazo ya zauna kusa dashi ya dafe kansa da hannu guda yana sauke ajiyar zuciya,

 

 

Shareshi yayi shima tsawon minti goma babu wanda yace da d'an uwansa k'ala, Cikin jan nuffashi Moddibo yace"wallahi narasa wane irin hali ne da kai, kafin in kawo yarinyar nan sai da nafad'a maka kuma ka amunce, kan me yasa zaka ci mata mutumci, kowa ai da koyo ya iya,gaskiya banji dad'in abunda kayi mata ba"

 

 

 

Kamar da dotse yake magana yana jinsa yayi shiru.

 

 

K'wafa yayi kawai yana duba agogon hannusa yace"yanzu dai gata can babu abunda zata nema,komai na siyo mata in tsautsayi yasa ta sakko don Allah babu ruwanka da ita"

 

Hankalinsa na kan littafin hannunsa yace"sai ka fad'a mata nima babu ruwanta dani, haka kawai ni da gidana anzo ana kafa min doka"

 

 

" In dan ta ita ne sai ku shekara bata shiga harkar ka ba, nasan halin kowa a cikinku"

 

Aje littafin yayi yana wani murmushi mai d'auke da ma'anoni daban-daban ya fuskaci Moddibon sosai yace"wai dakata malam har tsawon wane lokaci ka d'auka zatayi anan, inaji fa kayi mata alk'awarin gobe zaka canza mata guri, kazama me baki biyu kenan"?

 

 

" Wannan kuma kai za'a tambaya tunda wuk'a da nama na hannunka, dole ne in kadamu kaje ka k'arasa bunkice a kanta idan kuma ka gama shikkenan sai kaje kasanar da me Martaba halin da ake ciki"

 

 

" Ni tuntuni nagama bunkice na a kanta kuma nafad'a maka, amma tunda kace haka insha Allahu gobe zan sanar masa da halin da ake ciki"

yafad'a yana d'an jan numfashi sannan ya cigaba da cewa" Yanzu wane amsa zaka bawa me Martaba in ya aika gidansu yarinyar nema maka auranta, a kaji cewar tana hannunka ka b'oye kana da amsar da zaka kare kanka"?

 

 

"Duk wannan me sauk'i nr tunda kafin in d'auko su sai da naje na sanar da me gari, yasan halin da ake ciki, kuma a ranar yace zai aika a kira masa shi me unguwar da aka had'a baki dashi da wan mahaifin nata Sallau, wata k'ila kana iya ganinsu gobe a fadar Sarki"

 

"Shikkenan Allah yasa haka shi yafi alkari, Allah ya baku zaman lafiya"

 

 

"Ameen ameen"

Moddibo yace cikin jin dad'in addu'ar da d'an uwan nasa yayi masa, hira suke sosai irin tasu, Sarki! yace"gobe da misalin k'arfe hud'u na yamma Gimbiya Azima zata kawo min ziyara"

 

 

Murmushi Moddibo yayi yace"kace muna da manyan bak'i"

 

Ya mutse fuska yayi kawai bai ce komai ba.

 

Moddibo yace"wai Halisa tasan halin da ake ciki kuwa? ma'ana tasan su biyu zaka aura lokaci guda"

 

 

Wani murmushi ya saki cikin k'asaita yace d'azunan muka gama rigima da ita anan,sai da nayi mata fata-fata sannan ta shiga hankalin ta kasan halina sarai bana son shirme"

 

 

Cikin dariya Moddibo yace"gaskiya ne, rigimar Halisa babu mai iyawa da ita sai kai, wai don Allah yanzu ka fara sonta kuwa, na lura kai sam ba'a gane cikinka ko kana son abu baka nunawa wai saboda me"?

 

 

Cikin yanayin maganar shi yace"kowa an fad'a maka irinka ne, da kake haukacewa kan mace, duba don Allah shiriritar da kake kan wannan kidahumar yarinyar wacce ko hankalin ki kirki bata dashi, ka zubar da girman ka ta gani, d'azu dakana bata hak'uri ji nayi kamar in tsinka maka mari dan haushi wallahi"

 

 

Dariya kawai Moddibo yake kyak'yatawa yace"malam bakasan dad'in soyyaya bane shiya kake wannan maganar, ina ganin in kane kuka ma sai kayi da dai ban san halinka bane shiyasa nake tambayar ka yaya kakejin Halisa a zuciyarka, dan gaskiya ni ina mutukar son Gimbiya ina tunanim zan iya rayuwa da ita ita kad'ai"

 

 

 

 

Sarki! yayi masa wani kallo a d'age yace"wannan tsarin ka ne, malam ni babu wata "ya mace da zanyi wa kuka a kan me, me zata bani? wallahi kuna bani mamaki, wai me kukeji ne in kuna rawar jiki akan mata, soyyayar banza duk shirme ce ni aganina"

 

 

Girgiza kai Moddibo yayi yace"gwara da kace kai a ganin ka, amma ina nan ina addu'ar Allah ya nuna min lokacin da zan ganka kanai wa mace "yar murya ni nasan komai daran dad'ewa wannan lokaci sai yazo

 

 

 

 

 

*Turka!Turka*

 

```WAI SARKI!! NE?```

                  *KO*

```MODDIBO NE?```

 

 

 

 

*Muje zuwa*

 

 

 

 

*Comment Vote anda Share*

[25/07, 16:36] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

  ^^^^^^^^°

   _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^

                  đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

                   _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®{REAL BINTU BATULA}👄*

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana khadija```

```Yaro da kudi```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

```{RAHAMA ALIYU}```

 

 

 

_ZAMANI WRITES_

 _ASSOCIATION_đŸ€đŸ»

 

 

 

 

```Bisimillahir-rahamanir-rashim```

 

 

 

*🅿60*

 

 

 

 

 

 "Lallai kuwa ashe zaka sha zama in har zaka tsaya jiran wannan lokacin da kake, fad'a, aini ko ina son mace bata isa in nuna mata ba, zahiri sai dai ta gani a ai kace, kai dai da kaga zaga iya kaje kayi"

 

Moddibo ya mik'e tsaye da niyyar tafiya, da murmushi a fuskar sa yace"wannan ciki bakin naka yana bani mamaki, amma dai zamu gani ai"

Hannu ya bashi sukayi sallama, ya futa.

 

Shi kuma kusan rabin kwana yayi a farlon nasa yana karance karance sai wajan uku shaura ya mik'e ya haura sama, toilet ya nufa ya d'auro alwala yayi nafila kamar yadda ya saba, yayi addu'oin sa, sai jingina jikin bed d'insa yana jsn carbi, bacci ya soma fuzgarsa, cikin bacci ya dinga jin motsi, kad'an-kad'an a bardar saman sa, mik'ewa yayi a nutse ya bud'e window yana duba gurin,   Sadiya ce a takure a  k'ofar d'akin da suke ciki ta bud'e ta futo ta tsuguna ta takure kanta cikin gwiwa jikinta sai rawa yake.

A nutse ya bud'e k'ofar d'akin nasa ya futo yazo ya tsaya kan yarinyar, sam bata san ma yazo gurin ba,  kallon cikin d'akin yayi haske tarr! da yake basu kashe futila ba, can ya hango Balaraba kan bed tana ta bacci abunta, gashin kanta duk ya hargitse, ga sharab'ar ta duk a waje, kasancewar riga da wando ne a jikinta irin cotton d'in nan rigar me dogon hannu ce tana da botora shi kuna wandon iya gwiwa ne, shiya duk wasu sassan jikin nata suke waje, sauri d'auke kansa yayi yana d'an ya mutse fuskarsa, ya mayar da idonsa kan Sadiya, cikin murya mai sanyi yace "Kee"

 

 

Da sauri yarinyar ta d'ago kanta tana kallonsa a furgice zata ruga da gudu cikin d'akin, sai yayi saurin damk'e hannunta, inda yaji zafi rad'au, da alama zazzab'i yarinyar take, k'okarin fuzge hannuta take cikin tsoro, yayi k'asa da murya sosai yace"me yasa kika futo nan uhumm"?

 

Shiru Sadiya tayi tana kuka, "Baki da lafiya ne"?

 

D'aga kai tayi tana zubar da hawaye

 

" ina yayar taki"?

yafad'a k'asa-k'asa

 

"Bacci take yi, na tashe ta tak'i tashi gashi ni tsoran d'akin nake yayi girma da yawa"

 

Bai ce komai ba, ya kama hannun yarinyar suka shiga d'akinshi ya futo da maganin zazzab'i ya ciro biyu yace"kinji abunci da zaki kwanta"? d'aga kai tayi, ruwa ya ciro mara sanyi ya mik'a mata maganin yace"maza sha kinji ko, yanzu za ki daina jin ciwon insha Allah"

 

Cikin daurewa Sadiya ta watsa maganin a baki ta had'a da ruwa ta shanya, yace "muje in raka ki ki kwanta, kar ki k'ara futowa sai da safe"

Tare suka futa hannusa rik'e da nata,    Balaraba na tsaye a bakin k'ofa kamar ta d'ora hannu a ka, tana kamar an tashe ta ta farka daga nannauyan baccin da ya d'auketa,wanda kafin tayi shi sai da ta shafa, saboda tunanin da yayi mata yawa, kawai sai ta duba taga k'ofa a bud'e babu Sadiya, ta mik'e a zabure! ta sauka k'asa, duk girman farlon ta dudduba bata ganta ba, da sauri ta dawo sama ta tsaya bakin k'ofar tarasa abunda zatayi, hawaye kawai sai ya k'wace mata, zuba kawai suke zuciyar ta sai sak'e-sak'e take mata.  kawai sai taga an bud'e k'ofa,  suna had'a ido yayi saurin kau da nasa dan bazai iya kallonta a yanayin da take ciki ba, kai babu d'an kwali, ga kayan jikinta sun futo mata da k'irar ta,  da sauri! tazo zata fuzge hannun Sadiya, tana kuka, gabanta sai fad'uwa yake tana addu'ar Allah yasa bai cutar mata da k'anwa ba, rik'e hannun yarinyar yayi tamau! yak'i saki yana son yaga iya gudun ruwan ta, hannuta tasa tana tureshi , kamar me ture dotse sam yak'i motsi cikin kuka tace"Allah ya isa tsakanina dakai, mugu azzalimi Allah sai ya saka mana, ka cuci marainiyar yarinya sai nayi shari'a da kai"

tana kuka tana dukan k'irjinsa take maganar.

 

Lokaci guda ya fahimci abunda take nufi, cikin tsantsar b'acin rai da damuwa ya fidda hannu ya tsinka mata mari,  zuciyar shi tana tafasa yace"me kike nufi ne da wannan maganar taki"?

 

"Duk abunda kake nufi shi nake nufi" tafad'a cikin hayaniya, abunka da dare, gari yayi tsittt! shi tsoransa ma kar hadiman sa suji tunda wasu, suna kwana a k'asa, wa ni k'ebantaccan guri, wanda yake da k'ofa w ciki da waje,  saboda haka sai ya sa k'irjinsa ya tura ta cikin d'akin ya shiga shima da Sadiya a hannusa yarinyar duk ta furgice! da sauri Balaraba ta mik'e tsaye, saboda fad'uwa tayi k'asa lokacin daya angiza ta, tayi kan Sadiya tana dukanta tana kuka, kamar wata mata hankali, tunkud'e ta yayi a karo na biyu ta kara fad'uwa k'asa yace"wallahi ki shiga hankalin ki, banza shashasha kawai kin saki baki kina bacci, saboda abunda kikazo yi kenan, kin bar yarinya ta futo da zazzab'i a jikinta,  dube ki don Allah"

yafad'a yana mata banzan kallo, ya cigaba da cewa"duk abunda kike tunanin nayi da ita to nayi d'in ,kema bazan barki ba, zan biyo dare inyi dake, kuma tunda kika shigo gidana babu ke babu futa kin shigo kenan, zanga k'arshen rashin kunyar ki"

Yana gama maganar sa ya fuce daga d'akin kamar walkiya.

 

Sadiya ta jawo tana kuka tana duba mata jiki, ita har ga Allah ta tsorata dashi, sam bayanin da yayi mata bai gamshe ta ba,

 

 

Yana komawa d'akinsa ya zauna bakin gado ya dafe kansa cikin damuwa, wannan yarinyar ta b'ata masa rai, ko neman mata yakeyi me zai tsinta jikin yarinya k'arama irin wannan, mik'ewa yayi da sauri yaje ya kunna CCTV Camara, ya sai ta komai, idon ya zuba mata sosai yana kallon yadda bakinta yake motsi, sai masifa takewa yarinyar tanayi tana kuka,

 

Wani murmushi ne ya k'wace masa ya girgiza kai kawai, shi mamakin yarinyar ma yake, da gaske zargin sa take yayi wani abu da yarinyar.

 

 

 

 

*Comment d'in da kuke min baya isa ta, in kun k'ara in k'ara yawan typing*

 

 

 

 

 

 

 

*Comment Vote and Share*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         *_TO_*

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

 

 

```BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM```

 

 

      

 

 

 

 

 

 

*🅿61*

Yana zaune yana kallonta cikin CCTV Camara ta zabga ta gumi dagani tana cikin damuwa, mik'ewa ya ga tayi tana gyarawa k'anan nata kwanciya, ta nufi toilet, da sauri ya d'auke kansa lokaci da ta juya baya tana tafiya, gabanshi ya dunga fad'uwa, idonsa k'urr! a k'ofar ban d'aki har ta futo da alamu alwala ta d'ora, yana kallo ta bud'e k'aramin a kwatunsu ta d'auko zanin atamfa da wani k'aton hijab tayi shirin yin sallah, can inda a ka tanadi daddumar sallah yaga ta nufa ta tada sallah,  agogon bango ya kalla, hud'u shaura minti ashirin, mik'ewa yayi shima a nutse a shiga toilet ya had'a ruwa, yayi wanka, sannan ya d'auro alwala, niko nace, ko wankan me yayi oho,da asubar fari shi da ba mata gareshi ba.

 

 

 

Sabuwar jallabiya fara kar, ita ya sanya a jikinsa, yaje ya kashe CCTV Camara, ta idar da sallahr tana zaune tana kallon gabas hannunta duk biyun a sama da alama addu'a take,  sai yaji yarinyar ta burge shi, da alamu me ibada ce,  Sallahar raka'atanin fajri ya tayar, bayan ya idar ya zauna yana jan jarbi har lokacin da a kafara kiran sallahar asubahi, sannan ya mik'e a nutse ya sauka k'asa, suka had'u da d'an rakiyar shi yana zaune a farlo yana jiransa, yana ganin sakkowar sa ya mik'e tsaye yana kwasar gaisuwa suka gaisa, a mutum ce, Sarki! ne a gaba shi a baya har suka isa masjid.

 

 

 

 

Balaraba kuwa ta dad'e kan abun sallah bayan idar da sallah asubahi tana rok'on Allah ya futar da su daga damuwar da duke ciki da ita da "yan uwanta ba, bacci ne ya dunga fuzgarta dan haka nan kan abun sallahr ta b'ungire bacci ya kwashe ta.

 

 

 

To bayan an idar da  sallah ne anyi gaishe-gaishe kowa yana so ya koma shashensa, Moddibo yake tambayar shi amanar da ya bashi, rasa abunda zai ce masa yayi kawai ya share shi, Moddibo yace" to tunda ka k'i fad'amin muje inga ya suka kwana"

A hasale Sarki! yace"ni wannan binbinin naka ne banaso wallahi, ni yanzu bacci nakeji jiya sam banyi baccin kirki ba kabi ka dameni da zan wata Balaraba, da ta hana mutane sakat!"

 

Cikin sanyi murya da sanyi jiki Moddibo yace"muje dai in ganta, wallahi jiya kwana nayi ina mafarkinsu ita da "yan uwanta, ina kaunarsu, a zuciyata kuma nakeji kamar bazan yi wani dogon zama dasu ba"

 

 

Cikin mamaki yake kallon Moddibo lallai yau ya gazgata da cewar Moddibo da gasken gaske! yake son Balaraba, bai tab'a jin tausayinsa ba irin na yau, tabbas ya yarda so bala'i ne.

 

Yace"kan wane dalili zaka dunga yadda zuciyar ka tana maka sak'e-sak'e na abu marasa kyau, na d'auka tuntuni ka daina irin wad'annan tunanin naka"

 

"Mubar maganar kawai Magajin Sarki ni kad'ai nasan abuda yake damun raina fa, jiya kwana nayi ina murk'ususu ciwon cikina ya tashi, kasan yadda yake min in ya motsa min"

 

 

 

Da sauri ya kalli fuskarsa yaga duk tayi zuru-zuru,  tabbas da gaske yake, yace"kayiwa girman Allah ka rage k'ulafun yarinyar nan, kar kaje ka tayar mana da hankali, kafi kowa sanin in ciwon ka ya tashi, babu me zaman lafiya, da kwanciyar hankali, ba kai kad'ai ne kake shan wahala ba harda mu gaba daya "

Girgiza kai Moddibo yayi yace"sam ba soyyayar da nakewa Balaraba bace zata tayar min da ciwon na ba sai dai rashin fahimtar dake tsakaninku da ita, Balaraba ba ta da kowa,a yanxu sai Ina so ka tayani sonta da kula da ita"

 

"Shikkenan zanyi yadda kace, amma don Allah kar ka jawo mana tashin hankali, Indin saboda bana sakin jiki da Balaraba ne, yasa kake wannan tunanin na dai na daga yau insha Allah"

 

Farin ciki ne ya kama Moddibo fuskarshi a sake suka shiga shashen Sarki! d'in zama yayi cikin kujera shi kuma Moddibo ya hau sama,d'akinsu Balaraba, tana zaune ta zanga tagumi cikin damuwa Sadiya da Usuman na zaune gefe-da gefen ta, yayi sallama ya shiga, dak'in dago kanta tayi cikin nutsuwa ta sauke a kansa har ya k'araso kusa da ita ya zauna da murmushi a fuskarshi, yace"barka da asubah sarauniyar zuciyar Yusuf Moddibo, zuciyata tana azabtuwa da so da k'aunarki Ina fatan kin tashi lafiya"?

 

Fuskarta d'auke da k'ayataccan murmushi ta sauko k'asa gami da sunkuyar da kai, tace " lafiya kalau na tashi Ina fatan kai ma ka tashi lafiya"?

 

 

"lafiya k'alau, ya kwanan bak'unta kuma"?

 

Shuru tayi kawai har yanzu da murmushi a fuskarta, yace" sakko muje k'asa Ku gaisa da mutumin ki"

 

 

B'ata fuska tayi, tace"ba Kaine kake gaba dashi ba,ai shine ya kamata yazo ya gaishe ni"

 

 

"Duk da nine nake gaba dashi amma girman shi yafi nawa, kuma a matsayin ki na matata uwar " yayana ya kamata ki d'aukeshi a matsayan magaji na tunda shak'ik'ina neshi, duk ranar da bana nan,shine zai mar miki uwa uba"

 

 

K'walla ce ta taro a idonta tace" wannan wace irin magana ce kake Yusufu ni dai ka daina min don Allah"

Kamar zata fashe da kuka ta k'arashe maganar.

 

Rarrashin ta ya fara yi cikin taushin murya har sai da yaga ta mayar da k'wallar sannan hankalinsa ya kwanta ya kalli su Sadiya gami da shafa kan Usuman yace"kun tashi lafiya"?

 

Kai a sunkuye Sadiya tace"Yaya Yusuf Ina kwana"?

 

Amsa yayi fuskarsa a sake, Usuman ma ya agaidashi a nutse ya amsa, Balaraba tace"Sadiya ai da zazzab'i ta kwana mybe ko b'akonta ne"

 

 

Hankalin sa a tashe ya jawo yarinyar yana tambayar ta, jikin nata, tace" Yaya Yusuf naji sauk'i abokinka wannan me kyau d'in yana da kirki shine ya bani magani nasha cikin dare"

Moddibo yace"sunanshi Sark! Ko ce masa Magajin Sarki! nasan zaiyi fiye da haka ma, saboda yana tausayi"

 

 

Kicin-kicin da fuska Balaraba tayi tace"ka gafarce ni Yusuf, ko maganar da zanyi maka zata b'ata maka rai, gaskiya kayi masa magana jiya cikin dare ya shigo d'akin nan, gaskiya ni ban yadda ba"

 

 

 

Wani iri yaji a zuciyar sa, jin abunda tace"me ya kawo Sarki! d'akin, ya san halin d'an uwanshi ba mane min mata bane,kuma bazai ci amanarsa ba, Sadiya tayi Sauri tace"A'a Yayarmu ya ganni a wajan d'akine shine ya bani magani nasha ya rakoni na kwanta yace kuma in daina futowa cikin dare"

 

Moddibo yace"yanzu naji,zance, kiyi hakuri Gimbiya babu abunda zai faru sai alkairi ba halin Sarki! bane abunda kike nufi"

 

d'an tab'e baki tayi kawai tayi shiru yace"Ku tashi mu sauka k'asa Ku gaisa sai Ku karya"

M'ikewa sukayi duka suka nufi k'ofa.

 

Karo sukaci dashi zai hau saman shima, ratse masa sukayi a baranda har ya k'arasa hawowa Mariya baiwarsa ce take bayansa da'alama gyare-gyare zatai masa Wanda takeyi kusan kullum duk safiya, murmushi ya sakarwa Sadiya, sam ! baki kalli inda  Balaraba take tsaye ba, ciki-ciki tace"Ina kwana"?

yaci albarkacin Yusuf Moddibo.

A dak'ile ya amsa, ya mik'awa Sadiya hannu, yarinya mai sauk'in kai da wayewa sai ta sanya hannuta cikin nasa tana yar dariya tace" Magajin Sarki ina kwana"?

Cikin mamaki yake kallonta sai kuma ya kalli Moddibo cikin tuhuma yasan shine zai fad'a mata wannan sunan, saboda ba kowa ne ya ke kiransa dashi ba,

 

Murmushi Moddibo yayi, shi kuma ya tab'e baki kawai yaja hannun Sadiya suka nufi d'akinsa, Sakin baki Balaraba tayi kawai tana kallon ikon Allah, shi kuma yana sane ya sakarwa yarinyar fuska duk Dan ya muzgunawa zuciyarta, saboda yana bala'in jin ciwon zargin da take masa a kan yarinyar,baya ga haka ma, yarinyar ta kwanta masa,tana da hankali da nutsuwa ba kamar  yayar ta ba.

 

 

 

 

 

 

*Comments Vote and Share*

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         *_TO_*

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

 

 

```BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM```

 

 

      

 

 

 

 

 

 

*🅿62*

 

 

 

 

K'asa suka sauka zuciyarta tana mata sak'e-sak'e kan zak'ewar da taga mutumin nata yayi kan Sadiya,sam bata yadda dashi ba, ganin yadda yake wa mutane wani irin kallo, kullum ido a lumshe kamar munafuki.

 

 Ko da suka sauka k'asa hadimai ne su wajan biyar maza biyu mata biyu suna aikin gyara falon,kowa da inda yake gyarawa, jikinsu sanye da wasu kaya iri d'aya masu kamar Uniform, wani k'amshi ne mai dad'i ya cika hancinta, wani ku-ku ne ya futo daga kchin hannusa dauke da wani tank'asheshan faranti cike da abubuwan ci, Balaraba tayi saurin kauda kanta domin bata so tayi k'auyanci irin na jiya, hannun Usuman ta kama suka ni bayan Moddibo,inda ya nufi

Wani k'ebantaccan guri a falon, yace da Usuman ya zauna, yaron ya zauna cikin wata k'aramar kujera mai taushi, zama tayi itama tana bin gurin da kallo gaskiya k'ayatuwar gurin ya burgeta sosai dagani gurin hutawa ne,

 

D'aya daga cikin hadiman dake aiki a gurin ne ya k'araso ya zube gaban Moddibo yace"ranka ya dad'e a kwai abunda za'ayi ne"?

 

A nutse Moddibo yace"ka kawo abun kari na mutum hud'u"

 

Cikin bin umarni ya mik'e daga gurin.

 

Cikin nutsuwa ta kalli Moddibo tace"ya kamata fa ka kira Sadiya haka"

 

" Yanzu zai sauko ai wanka ya hau yayi"

Shiru tayi kawai tana d'an ya mutse fuskar ta, tace"tsarin gurin nan ya burgeni Yusuf ina so abu White coulor" Murmushi yayi yace"lallai tsarin ku d'aya da mutum min in kin lura ai duk adon falon nasa white ne"

Shiru tayi tana da tasanin fad'ar maganar, minti biyu tsakani yace"zan shirya miki falon ki da wannan colour"

 

"Nagode"

Abunda tace kenan,tayi shiru kanta a kasa tana wasa da hannuta

 

Tsura mata ido yayi,kurum yana kallo, ta d'ago kai tana kallonsa suka sakarwa juna murmushi, tace"wannan kallon fa,Yusuf"?

 

 

Da murmushi a fuskar sa yace"kallon soyyaya ne Gimbiya zuciyata tana fad'a min akwai wani babban al'amari da zai faru a tsakanina dake"

 

Itama Murmushin take,tace"babban al'amari ai bai wuce na aure na da kai ba, dama ina so in tambaye ka a wace matsaya muka tsaya,nifa zama anan kamar a kan k'aya nake"

 

" Karki damu insha Allahu yanxu in na tashi daga nan gurin me Martaba zan wuce, za'ayi komai a gama cikin kwanciyar hankali"

 

Ajiyar zuciya ta sauke,ya cigaba da cewa"maganar gurin sai da abuncin ki ki bar wa su Hauwa'u su cigaba da samu a ciki, in sha Allahu xaki fara business in munyi aure"

 

Cikin murna da farin ciki take masa godiya,a bisa karamcin sa a gareta, tanaji a yanzu bata da babban masoyi kamar sa, zata dunga k'okarin danne damuwar ta duk Dan ta kwantr masa da hankali,  Salmanu ne, ya k'araso gurin hannunsa d'auke da wani faranti me fad'i ya aje a tsakiyar su, Moddibo yace"jeka abunka kaji" godiya Salmanu yayi ya bar gurin, Sauri-sauri yake ya gama abunda yake yaje ya fesawa abokinshi Dauda labari,shi Dauda yana b'angaran uwar gidan Sarki wato, Kulu,mai d'akin kudu, kenan Mama Kulu kenan,

 

A nutse suke karyawa ita dashi, kana ganinsu kasan masoyan asali ne,Wanda suka yarda da Kansu, Usuman na gefe yana karyawa shima.

 

 

Cikin nutsuwa yake sakkowa daga sama step by step hannunsa na rik'e dana Sadiya, yana sanye da wasu kaya na alfarma, masu tafe da wata alkyabba, kafarshi sanye da wani takalim me gidan ya tsa, babu nad'i a Kansa, duk da cewar shigar dake jikinsa ta nad'in ce amma bai yi ba, cewarshi ya gaji da kayan nauyi, sumarshi ya gyara,sosai da gemunshi, sai sheki yake,d'an k'aramin bakinsa mai d'auke da siraran lips Wanda suka d'an yi duhu kad'an, yayi Kyau kwantaccan gashi ya kewaye shi, as'usul idanunshi a lumshe kamar ko da yaushe,sai k'amshi yake zubawa, yana sakkowa  masu hidima a gurin suna zubewa suna kwasar gaisuwa, ko wanne munafurci fall a abakinsa saboda ganinsa da k'aramar yarinya "yar shekara goma, cikin yanayin tafiyarsa ya nufi, daining teble d'insa Wanda yake cike da abubuwan ci, dai-dai inda suke zaune yazo ya gifta Balaraba taji gabanta yana fad'uwa duk da cewar ba ta kalli fuskarsa ba,gefansa ta kalla, Yanayin kwarjinsa da yadda yake tafiya cikin k'asaita ya furgitata ko ba'afad'a an San d'an mulki ne shi saboda abun a jinsa yake, jin kamshin turaran sa yasa Moddibo saurin waiwayo wa sai yaga yana k'okarin zama kan kujerar daining d'in,  ga Sadiya ta zauna itama, ku-ku shi na tsaye gefe,yana jira ya dai-dai ta zamansa yafara had'a masa,abin kari.

Mik'ewa yayi ya bar Balaraba a gurin ya nufi inda Sarki! yake zaune, sukai yi magana sama-sama,batajin abunda suke cewa, saboda a kwai tazara a tsaksninsu can ta hango,Sadiya ta zage sai kwasar girki take, babu wani kamun kai sosai yarinyar ta bata haushi, Moddibo ne ya k'araso inda take,tayi saurin kauda kanta saboda wani lokacin shima haushinsa takeji in taga yana wa Sarki!rawar jiki.

"Gimbiya zanje in gaisa da mutan gida,zuwa yamma zan shigo sai muk'arasa maganar mu, don Allah ki cire fargar ba komai a ranki"

 

A sake tace"shikkenan sai ka dawo a gaishe min dasu"

 

"Zasuji insha Allahu"

Yafad'a yana k'okarin barin gurin.

 

Bayan futar Moddibo daga falo,sai yayi shiru saboda duk masu hidima a gurin sun gama sun futa,sai sautin AC ne kawai yake tashi, Usuman can gefe yake yana ta "yan wasaninsa, sai taji zaman gurin ya gundure ta, taja tsaki ya kai sau biyat r in ta d'aga kai ta hango Sadiya,na cin abunci ta sake sosai dashi tana masa hira har da dariya.

 

Sam! tak'i yarda su had'a ido dashi, a sace take k'are masa kallo yana cin abunci cikin nutsuwa, gashi fuskarsa a sake,yana sauraron hirar da Sadiya take masa,cikin zuciyar ta take ayyana irin dukan da zata yiwa Sadiya.

 

 

Taku! tafaraji k'was!k'was!k'was! irin na mace, takun takalmin ya d'auki hankalin ta har shi uban gayyar, da yake can inda yake zaune saitin k'ofar shigowa ne, shiyasa ya ga wacce ta shigo Gimbiya Halisa ce, Balaraba na zaune can wata kusuwar wa shiyasa bata ganta ba,

 

Halisa tana tare da wasu bayi guda biyu suna take mata baya, wanda suka tsaya bakin k'ofar shigowa, can inda ta hange shi zaune ta nufa fuskarta babu walwala,ganinshi zaune da wata,daga can nesa tana yiwa Sadiya kallon wata k'atuwar budurwa, shiyasa ta sha kunu,sosai tana tunanin me ya kawo mace har falonsa duk da tasan halinsa  ba ya Neman mata.

 

Giftawar ta Balaraba ta hanga,ta bita da kallo daga sama har k'asa, tana ganin yanayin shigarta ta gane," yar sarauta ce.

Sarki! kuwa d'auke kansa yayi daga kanta har ta k'araso gurin ta tsaya gami da d'ora hannuta kan kujerar da Sadiya take zaune tana mata wani kallo irin na raini tace"Habibi wannan yarinyar a ina ka samo ta,naga sam ba jinsin mu bace"

 

 

Banza yayi mata,kawai ya cigaba da cinsa abuncin sa a tsana ke,

 

K'ara maimata maganar tayi,ya d'ago kansa cikin jin haushin ta yace"ban sani ba, ki kauce daga kan mutane tunda ke baki da ladabi da sanin ya kamata"

 

Ganin ya hasala! yasa ta fara yak'e tace" tunda na shigo na ganka zaune da mace a guri guda naji hankalina ya tashi shiyasa na rasa nutsuwa ta, sai da na k'araso kuma naga ashe ma yarinya ce,amma dai duk da haka hankalina bai kwanta da ita ba,yarinya sai kace,me dubi yadda take k'walo ido kamar mayya"

Karaf! a kunnen Balaraba,dama taji abunda Halisa tace a farko Dan gane da Sadiya.

 

Ranta a b'ace ta futo daga inda take,ta tsaya a gurin tana kallon su, a cunkushe ta bud'e baki tayi magana, tace"ke! Sadiya baro gurin nan, kinji ko"

Duk hankalinsu ya koma kanta har shi,uban tafiyar, ganin fuskar yayar ta a murtuke ya fad'ar mata da gaba,sai ta fara yunk'urin mik'ewa tsaye domin ta cika umarnin ta, yayi saurin dafe hannun yarinyar ya hanata tafiya, ido ya zubawa Balarabar dake tsaye can gefe tana cika tana batsewa, ganin Sadiya tak'i tasowa yasa ta k'ara buga mata tsawa,a karo na biyu.

A nutse ya d'an daga muryarsa yace"tak'i zuwa d'in in kin isa kizo ki jata,da k'arfi mugani"

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*Comments Vote and Share*

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         *_TO_*

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

 

 

```BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM```

 

 

      

 

 

 

 

 

 

*🅿63*

 

 

 

 

Cike da karsashi,da jarumta ta durfafi inda suke fuskarta a had'e tamkar wacce bata tab'a dariya ba, tana zuwa tafara yunk'urin fuzge hannun Sadiya daga cikin nasa, a nutse ya d'ago kanshi tare da zuba mata idanunsa,ya bud'e tar! Gabanta ya buga! sai kace mai lak'ani a idonsa, duk gwiwarta ta sage! kanta ta sunkuyar k'asa domin bazata iya jurar k'alon k'wayar idonsa ba, amma duk da haka bata fasa k'okarin fuzge hannun Sadiyar ba saboda k'arfin Hali, rik'e hannun yayi tsaf! da tazo zata k'wace sai su had'a hannu, sai ya had'a da hannun nata ya matse,ganin abun nasa harda iskanci, yasa ta fuzge hannunta tana zabga masa harara, batare da tabari ya gane gazawar ta ba,ta kalli Sadiya,cikin fad'a tace"zan kama ki,wallahi tunda kike barin maza suna rik'e miki hannu" barin gurin tayi a fusace,ta kama hannun Usuman suka haura sama.

Kallo ya bita dashi, fuskarsa d'auke da murmushi, girgiza kai yayi kawai yana mamakin k'uruciyar ta, yanzu ya gane itama yarinya ce, sakin hannun Sadiya yayi dake zaune tana mayar da k'walar da ta taro a idonta,saboda tasan halin masifar yayarta

Yace"kwantar da hankalin ki kinji ko Halimatu, duk abunda tayi miki in mun had'u zan rama miki, tashi kije" mik'ewa tayi jikinta a sanyaye, ta haura sama

 

Sai sannan ya mai da hankalinsa kan Halisa dake tsaye, tana cika tana batsewa duk wani abu da ya faru tsakanisa da Balaraba ta gani mussaman had'a hannu da suka yi"

 

 

B'ata fuska yayi kad'an yace'' kin zama dogariya ne,wai duk gurin zaman nan bai miki ba sai dai ki tsaya a kai na"

 

 

Cikin fushi tace"ai banga fuska ba, tunda ka kawo wacce kakeso har gida,ita kuma wannan mai sifar karuwan fa"

 

 

Hararata yayi yace"ki iya bakin ki wallahi ranki zai mugun b'aci a kan wannan yarinyar matar Moddibo ce in sha,Allahu"

 

Wata dariya ta shek'e da ita,ta nemi guri ta zauna, cikin jin dad'i tace" gaskiya Ya Yusuf ya iya zab'e tsaf wannan zata yi masa wayo dubi idonta,don Allah,wai me ma ya kawota shashen ka ne, kuma meyasa har ka zauna da ita da k'anwarta guri guda"

ta k'arasa maganar da damuwa!

 

"Sai ki bari sai ya zo sai ki tambaye shi,amma yanzu ni bani da lokacin baki wannan amsosin naki"

 

 

Mik'ewa yayi daga gurin ya barta zaune,babu shiri ta mik'e tana bin bayansa har ya zauna kan wata kujera me  cin mutum d'aya, ta zauna a wacce take fuskantar sa, wata k'aramar drowar ya jawo k'asan kujerar ya futo da wani k'aramin littafi irin na addini yafara dubawa, tunda taga yayi wannan zaman tasan ba zai saurareta ba, duk abunda zatayi kuwa,dole ta jira ya kammala tukkuna, mintuna goma ta gaji da zaman gurin sai ta mik'e  ta fa kaici idonsa, ta hau sama tana laluben inda Balaraba take, cikin sa'a ta ga wani d'aki a cikin d'akunan dake barandar a bud'e,kai tsaye d'akin ta nufa cikin k'asaita  ta tura k'ofar da k'afarta,ta shiga babu sallama, Balaraba na zaune gefan gado ta cire hijab d'in, tana sanye da doguwar riga,cotton mai taushi,tana da yankakken hannu, sai tayi amfani da k'ara min hijab me hula, irin na Larabawa, tayi mugun kyau,kamar wata balarabiyar k'asar Oman, Halisa sai da Gabanta ya ganin ciki da k'asaitar Balaraba,fata luwai sai kace me rayuwa a kasar waje,ko ita albarka,ita da take rayuwa a cikin jin d'adi.

Dukkaninsu k'ofa suka kalla jin a bugo da k'arfi an shigo, dogarewa tayi bakin k'ofa tana watsa musu kallo, ta kalli Balaraba a k'asan kan ce,tace"zo ki rufe min k'ofar nan,ke me kama da "yayan bayi"!!

 

D'as!d'as!d'as! K'irjin Balaraba ya fara buga jin furucin Halisa, cikin sigar izgili da nuna ke awa! kuma baki isa ba,tace" a matsayin ki na wa! da har xaki bada umarni abi,ki bari sai kin kai matsayin zama cikkakun mutane sai ki bada umarni,amma dai yanzu baki isa ba"

 

"Ke ni kike fad'awa magana,har kike k'okarin zagina,munafukar Allah, ta'alah macuciya, an ga gidan sarauta an lallab'o, to bari kiji,shi kanshi Moddibo baza ki same shi ba,balle kuma Sarki! Wannan nawa ne ni d'aya"

Halisa ta k'arashe maganar tana dungurewa Balaraba kai, abunda Halisa bata sani ba shine ba'a nuna Balaraba da d'an yatsa,komai girman ka kuwa sai ta nuna maka ruwa ba,sa'an kwando bane,

Wani ba hagon mari ta tsinkawa Halisa a fusace! Sam!ba tayi tunanin abunda zai je ya dawo ba.

Ihu Halisa ta kurma! tayi kan Balaraba da duka sai zaginta take,abinka da sabo da fad'a tuni Balaraba ta tare ta,su kafara kokawa abun mamaki, nan Balaraba ta yar,da Halisa a k'asa, saboda ita bata iya fad'a ba,ga jikin Hutu,babu k'wari, sosai Halisa taji ciwon fad'uwar ta k'asa, ko da mik'e bata daddara ba,ta k'ara yin kan Balaraba a karo na biyu, tayi nasarar fuzge mata hijab d'in wuyanta ta cire hular kan nata,ta tattaro gashin kan Balaraba ta rik'e sai ja take,tana gaya mata maganganu na b'atanci kuma sai ta d'aure ta,tunda ta sake tayi kokawa da ita, Balaraba kuwa k'okarin kwatar kanta takeyi hannuta ta kama ta murd'e! da k'arfi, Halisa ta saki ihu,babu shiri ta sakar mata, kai tana duba hannunta tana cije baki, ki take kamar wacce tayi targad'e, ganin sunk'i su dai na fad'an yasa,Sadiya sauka k'asa da gudu, domin taje ta fad'awa Magajin Sarki, yana zaune,a inda yake,kanshi k'asa yana duba littafin hannun sa, ya ga Sadiya gabansa tana zare ido,d'ago kai yayi yana rufe littafin hannusa, yace"dukan ki tayi kike haki! haka"?

 

Girgiza kai tayi cikin tsoro tace" Yayarmu fad'a suke yi da wannan da tazo gun ka"

 

Falon yake bi da kallo, cikin mamaki, ina Neman Halisa,

 

M'ikewa yayi kawai ya rik'e hannun Sadiya suka nufi sama,

Yana tura k'ofar yaga abun mamaki da d'aure kai, Balaraba ce, rik'e da wuyan Halisa ta mak'ure a bango,ita kuma Halisa duk tayi wujiga-wujiga,sai k'okarin k'watar kanta take,ta kasa,idanunta duk sun firfito waje, k'arasawa yayi ciki har inda suke, batare da yace,komai ba ya fara, k'okarin b'anb'are hannun Balaraba dake wuyan Halisa, sanyi da taushin Hannunsa,suka sa ta dawo hayyacin ta, kallonsa tayi da idonta wanda suka kad'a saboda b'acin rai!

 

 

Hannunta ya matse cikin nasa,shima ya zuba mata idonsa,kamar yarda tayi masa, dafin! dake nasa idon ya fi nata,dole tasa, ta risinar da idonta, ta zare hannuta daga nasa ta koma gefe guda tana huci!

Halisa  kuwa zubewa tayi a gurin tana nufarfashi,na wahala! Dariya ce take cinsa ganin yadda Halisa tayi wurjanjan, cikin yanayin maganar sa yace"Halisa,da ilimin ki da komai kike kokawa sai kace a jahiliyya,in ita ta saba da dambe,ke sai ki biye mata,gwara ma da tayi miki duka"

Yafad'a babu damuwa a tare da shi.

 

Hawayen b'akin ciki ne ya fara zubowa Halisa,tace"abunda zaka ce kenan ko"?

 

"To me zan ce miki me ya kawo ki gurin ta,ko na aiko ne"?

 

Mik'ewa tayi tana gyara alkyabar jikinta,tace" zaka ce na fad'a maka wannan k'ask'antacciyar bata isa ta dake ni a banza,ba tana a matsayin baiwa ta,wallahi sai na wulak'antata"

 

 

Siririn murmushi ya saki iya leb'anshi ya d'an kalli Balaraba kad'an sai kuma ya kauda kansa,ganin ta babu hula,ga botiran rigar jikinta duk sun zube, saboda fad'a duk saman k'irjinta a waje, Ki yayi yanayin jikinsa na sauyawa, Matsalar shi kenan shi mutuk'ar zai ga wani shashe na jikin "ya mace shikkenan sai sha'awarsa ta motsa, ya cije leb'anshi na k'asa kad'an yace" Wannan tafi k'arfi ki Halisa,kika tab'a ta kin tab'a zuciyar Moddibo,ki bari zan mishi magana ya ja mata kunne"

Hannunta ya rik'e suka fara tafiya, domin barin d'akin,tace"wato ni ba zuciyar ka bace,kenan har zaka kasa d'aukar mataki a kanta dubi irin dukan da tayi min"

Kamar zai yi dariya, yace"muje k'asa in rarrashe ki, ko" mamaki sosai yake na k'arfin halin Balaraba, kizo har gida kina fad'a da masu gida, da alama dai yarinyar tana da aljanu.

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         *_TO_*

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

 

 

```BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM```

 

 

      

 

 

 

 

 

 

*🅿64*

 

 

 

 

Da harara Balaraba ta bisu dashi,har suka futa, Sadiya ta matso kusa da "yar uwarta tana wasa da hannuta tace" don Allah yayarmu ki daina fad'a da ita baki ga ita "yar Sarki bace,kar ki jawo a kulle mu,kinji tana cewa sai ta d'aure ki"

Ta k'arashe maganar tana sharar hawaye

 

Tsawa! ta buga mata tace"rufe min baki,duk bake kika jawo ba, wallahi duk sanda na k'ara ganin kinje gurin wancan mutumin sai ranki ya b'aci,ki ko kiranki yayi kar kije"

 

Kwanciya tayi kan gadon tana kuka,Usuman yana taya ta,ita kuma Balaraba sai fad'a take mata.

 

 

 

Ko da Sarki! suka sauka k'asa da Halisa, zamansa yayi a inda ya tashi,ta k'araci k'orafe-k'orafen ta,bai ce mata komai ba, haka ta mik'e tana niyyar tafiya ranta duk a b'ace! ya d'ago kai a tsanake yace"koma ki zauna zamuyi magana"

 

Komawa tayi ta zauna, ya aje littafin dake hannusa,fuskarsa babu yabo babu fallasa yace"kin san Gimbiya Azima,"yar Sarkin Yalwa"?

 

Gabanta ya fad'i! jin sunan wacce ya fad'a ita kuwa tasan Gimbiya Azima,domin abokiyar fad'anta ce, basa shiri ko k'adan dalili kowa yana ji da izza! gami da tak'ama.

 

 

 

Bakinta na rawa tace"Eh nasanta"

 

"Yawwa itace zata zama abokiyar zaman ki in Allah ya yarda"

 

Wani irin yarrrr! ta ji ajikinta lokacin da taji abunda yace mak'ogaron ta ya bushe k'amas, tace"ban fahimci abunda kake nufi ba"

 

 

Wani irin kallo yayi mata yace"kin San bana magana biyu, kije kiyi tunanin maganar dana fad'a miki"

 

 

Kuka ta fashe! dashi kamar wacce a ka aiko mata cewar uwarta ta mutu, tace"yaushe har a k'ulla wannan al'amarin ban sani ba,kuma mahaifiyata bata sani ba,Dan anga cewar ita macace shiyasa har ake abu batare da saninta ba,wannan ai yaudara ce"

Cikin kuka ta k'arashe maganar.

 

 

Ransa a mugun b'ace ya d'ago Kansa ya zuba mata idonsa,masu kwarjini,tuni tayi k'asa da kanta tana sharar hawaye

Yace"dukanin ku ke da ita Azimar babu zab'ina a ciki, ke kin kasance zab'in Mamana,ita ta kasance zab'in Waziri, duk zan aure ku ne ba dan inaso ba,sai dai n in cika umarnin magaba tana"

Shiru yayi na minti biyu ya cigaba da cewa na fad'a miki ne saboda ki sani kuma ki shirya, saboda kin fi kowa sanin halina bani da munafurci kuma bana san hayaniya, da fitina,wanda na lura ke haka halin ki yake tada zaune tsaye, idan anjima zata zo nan domin ta kawo min ziyara zan tara Ku guri guda dake da ita,ku fahimci junanku, kar wata b'araka ta futo daga gare ki, nasan halinki, in xaki kwantar da hankalin ki ki kwantar domin ke da ita ba da ku kad'ai zan zauna ba,kin fi kowa sanin yaya tsarin masaraurmu yake"

 

 

 

Kuka mara sauti Halisa take,lallai tana cikin tsaka mai wuya, yanzu ta tabbatar da cewar Baba Waziri baya k'aunarta tunda har ya had'a "yar abokinsa aure da masoyin ta,  ita da take burin taci  lokacinta ita dashi kafin ya kawo wata,tasan ta more kuma sunsha soyyaya, yanzu ko auran a kayi tilas su raba kwana ita da Azima.

 

 

 

 

Tunda ya gama maganar shi,ya kishin gid'e kan kujerar ya lumshe idonsa Allah kad'ai yasan abunda yake damunwa, yana jin kukan Halisa yak'i k'arewa ya bud'e idonsa wanda suka d'an yi ja kad'an, yace" kin cika min kunne fa da gunjin kuka, kije ki tambayi Baba Waziri yadda a kai haka ta faru tunda na lura ke baki da kunya, har kina cewa an yaudare ku"

Yadda ya fad'i maganar da yanayin b'acin rai! yasa ta gane tayi kuskure domin Sarki! mutum ne wanda baya saurin nuna b'acin ransa da wuri,  in ransa ya b'aci a yanayin maganar sa zaka gane, mik'ewa tayi ta nufi kujerar da yake zaune, ta rab'a jikinta a jikinta harda langwab'e kai, ta rik'e hannusa guda, d'aya, tayi k'asa da murya ta sosai tace" Allah ya huci zuciyar Habibi na, zuciya tana azabtuwa da so da k'aunar ka, shiyasa na rasa tunani na,lokacin da naji wannan maganar,ina kishin ka,mutuk'a bana k'aunar ko wace mace ta rab'eka sai ni,amma ina ganin burina bazai cika ba, Habibi nasan Azima ciki da waje,zata aure ka ne da wata manufa,a zuciyarta, gaskiya banso Azima zata kasance matarka ba, amma tunda haka Allah ya hukunta mama zan cigaba da tayaka addu'a"

 

 

Yanayin yadda tayi masa magana a nutse yasa yaji ta bashi tausayi, gyaran murya yayi gami da d'an gyara zaman sa,a nutse yace"ki koma inda kike mana, na hanaki irin wannan"

Muryar shi bata futa sosai yayi maganar,

Mik'ewa tsaye tayi tana gyara alkyabarta tace"tafiya ma zanyi,yanzu sai anjima zan shigo,da kamar k'arfe nawa zata zo"?

Tafad'a cikin sigar tambaya.

 

 

"Hud'u zuwa biyar na yamma"

 

 

"Shikkenan to"

Tafad'a a sab'ule jikinta babu kuzari ta futa daga falon

To,can gidansu Balaraba kuwa,babu wanda ya damu da rashin dawowar ta gida da wuri har wajan k'arfe tara da rabi na dare bata shigo gida ba, Iya hankalinta ya tashi ta futo ta nufi d'akin Sadiya matar Kawu suna maganar,can sai ga Sallau nan ya shigo fud'un-fud'un yana sab'a babbar riga, Iya ta tare shi cikin damuwa tace"Sallau har yanzu Balaraba bata shigo ba,babu ita babu yaran"

 

 

Da sauri ya kalli k'ofar d'akin nata, cikin mamaki yace"to ina ta tafi mutsiyaciyar yarinya,me shegen yawon tsiya,ai gwara in aurar da ita,kar ta jawo min masifa"

 

 

Lantana ce ta bankad'a labulen d'akinta ta futo da futular k'awai a hannunta, tace"wai zancan me nakeji ne"

 

 

"Wannan munafurkar ce bata shigo gida ba"

 

 

Lantana tace"Oho! dai a banza, duk inda ta shiga ta dawo,dole ace da mijin iya baba mune dai tilas d'inta, ehee"!!

 

 

Sallau yace"ai ko guduwa tayi bazan fasa abunda na shirya a kanta ba, sai na d'aura auranta da Iro"

 

 

Lanatana tace"kayi min dai-dai, da taje ta jawo mana abun fad'a"

 

Uwa! na daga cikin d'aki tana sako baki, bak'in ciki da b'acin rai yasa Matar Kawu komawa gurin ta, Iya ma d'akinta ta koma tana addu'ar Allah ya tsare mata su Balaraba duk inda suke.

 

 

 

Lantana Sallau Uwa su Shamsiiya baccin su sukai babu abunda ya dame su.

 

Sab'anin Iya da matar Kawu baccinsu rabi da rabi ne, saboda fargaba,

 

 

Asubar fari suka dunga jin bugu, a gigice Sallau ya diro daga gado,babu salati babu komai yaje ya zare sakata, yana hamma! Idonsa duk kwantsa abun k'yamk'yami! d'an aiken gidan me gari ne yazo, Sallau gabansa ya fad'i yace"lafiya dai ko"?

 

D'an aiken yace"me gari yace"kazo yanzu-yanzu me Martaba ya aiko yana neman ku"

 

Saura kad'an ya fad'i saboda razana da yayi,baki na rawa yace"me nayi ni Sallau"?

 

 

 

D'an aiken yace"Ai ba kai ka dai zakaje ba tare dashi zaku"

 

Ihu! ne kawai sallau ba kurma ba,ya shige gida cikin tashin hankali!

 

 

 

 

 

*Muje zuwa*

[02/08, 18:14] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

 

 

 

 

_*DEDIGATED*_

         *_TO_*

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

 

 

```BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM```

 

 

      

 

 

 

 

 

 

*🅿65*

 

 

 

 

Lantana ce ta futo daga d'aki hannunta rik'e da butar alola, taga Sallau ya shigo wurjajan, kafin tayi magana ya tare,ta yana cewa "Lantana masifa ta same ni ,yanzu aike ya same ni,cewar muzo ni da me gari wai  me Martaba yana neman mu"

 

Sakin butar tayi tafadi a gurin saura kad'an zaninta ya fad'i k'asa saboda tsorata da tayi,salati take tana sallalami, cikin tsora tace"Allah yasa ba wani laifin kayi ba"

 

 

Yace"yanzu dai zanje in ji, d'aki ya shiga yana tashin Uwa,ya fad'a mata halin da ake ciki,ko a jikinta ta koma tai kwanciyar ta

Wani kud'addan yadi ya d'auko ya sanya a jikinsa,ya d'auki wata daud'add'iyar hula ya kwafa a kansa ya futo da sauri,har yanzu Lantana na tsaye a tsakar gida,jikinta duk yayi sanyi, tarasa abunyi,ta kalli Sallau lokacin da ya futo,tace"Nifa inajin wannan shegiyar yarinyar nan ce ta ka k'arar ka gurin Sarki kasan ba kunya ce da ita ba"

 

 

" Ai in itace ma,kanta ta kai domin a gaban me Martaba zan zayyane masa abubuwan da take na fajirci"

 

 

Lantana tace"Kayi min dai-dai kar ka rage komai duk ka fad'a masa zinace-zinacen da takeyi"

Haka Sallau ya futa Lantana tana k'ara yi masa hud'uba.

 

 

 

 

Lokacin da suka isa fadar Sarki Almustafa a cike take, me Martaba yana sauraron k'urafe-k'urafen mutanan sa, sai da fada tayi sauk'i sannan me Martaba ya waiwayo kansu, suka k'ara mik'a gaisuwa, Sallau duk ya sare! da al'amarin ganin yadda me Martaba yake yanke hukunci cikin adalci a bawa me gaskiya,gaskiyar sa, mara gaskiya a bashi rashin gaskiyar sa,sai gumi! yake sharcewa,

 

 

 

Cikin nutsuwa me Martaba, ya d'ora idonsa a kan me gari, Halilu, yace"Halilu ya al'amura da fama da jama'a"?

 

Me gari Halilu yace"Alhamdulilahi Allah ya taimake ka"

 

"Masha Allahu"

me Martaba ya fad'a yace"kasan wancan yaron"?

Sallau da

Me gari Halilu su ka kalli inda me Martaba yake nuna was,

 

Walidi ne zaune cikin dugayen kaya kamar bashi ba,sai Moddibo dake gefan sa,a zaune,

 

 

Cike da furgici Sallau yace"Walidi me ya kawo ka nan"?

 

 

Wani dogari ya buga matsa tsawa,gami da cewa"gyara kintsi!! nan ba gurin shirme bane"

 

 

Shiru fada tayi,na minti biyar  me Martaba ya kalli me gari Halilu a karo na biyu yace"ina sauraron ka"

 

 

Sunkuyar da kai k'asa me gari yayi yace"k'warai kuwa Allah yaja zamanin ka,nasan wancan yaron farin sani domin yana d'aya daga cikin matasan gari na, yanzu haka ma muna tare da mahaifin sa,Allah ya taimake ka"

Ya k'arashe maganar yana sunkyar da kansa cikin ladabi,

 

 

"Alhamdulilahi"

me Martaba ya fad'a ya cigaba da cewa, " yaron nan yazo min da magana wacce naji bata kwanta min ba,wato kuna so ku had'a aure babu sanin kowa,hatta yarinyar da  kuke so kuywa aure bata sani ba,kuma bata amunce ba, shine nasa aka kira ku inji kan wane dalili zakuyi haka"?

 

 

Sallau yayi karaf! yace"Allah ya taimake ka wannan yarinyar da kake magana a kanta nine mahaifinta,saboda nine wan ubanta,nafi kowa sanin halinta muguwar karuwa ce,yawo take tana bin maza,ga shaye-shaye,kwanaki ma har ciki ta zubar,shine ni kuma nake tsoron kar Allah ya tambaye ni amanar da ya bani yasa kawai nace gwara inyi mata aure in huta, to sai a kayi sa'a kuma d'an uwanta wato yaron gurina Iro yace yana sonta zai aureta a haka duk da mugun halin nata, nayi murna da naji haka,shine banyi k'asa a gwiwa ba,naje na siyo alawa da goro, na kai gidan me gari domin a d'aura auran bata sani ba, Allah ya taimake ka yanzu zan can da nake maka ma, tunda ta samu labari,mun nemata mun rasa tunjiya bata kwana a gida"

 

 

 

Fada tayi shiru tana sauraron maganganun da Sallau yake, kowa yana jiran abunda me Martaba zai ce"

 

 

 

A nutse ya d'ora idonsa kan Walidi,yace"kaji abunda mahaifin ka yace a kan "yar uwarka"

 

 

Walidi ya gyara zama sosai yace"Allah ya baka nasara,a rayuwarka, duk abunda ma haifina ya fad'a ba gaskiya bane, gaskiyar magana Balaraba kintstsiyar yarinya ce me gurin zuciya, nan dai Walidi duk ya fayyacewa me Martaba abunda yake faruwa, ya cigaba da cewa,maganar cewar Balaraba ta gudu, an neme ta an rasa, hakane, Allah ya taimake ka,Balaraba ta hannun Moddibo, shine ya taimake ta ita da "yan uwanta guda biyu"

 

 

 

Kallo ya koma kan Yusuf Moddibo musamman Mahaifin sa Waziri Zaiyyanu

 

 

Me Martaba yace"hakane Moddibo"?

 

A nutse yace"k'warai kuwa Allah ya taimake ka,yarinyar tana hannuna kuma ina me farin cikin sanar dakai cewar itace yarinyar da na fad'a maka inaso in aura"

 

 

Cikin mamaki me Martaba yace"jeka d'auko min yarinyar,ka kawo min ita,yanzu zan sa a kira min d'an uwanka,Almansur,domin shi nasa yayi min bunkice a kanta,shi kuma muji ta bakinsa"

 

A nutse Moddibo ya mik'e ya na kai gaisuwa, ya futa daga fadar,

 

 

Sallau kuwa duk rigar jikinsa ta jik'e jagab! ganin reshe yana nema ya juye da mu jiya, babban abunda ya d'aga masa hankali shine ,jin da yayi wai Balaraba na gidanan,kuma wai wannan da yayi maganar shike san ta da aure ,lallai asirinsu ya tuno.

[03/08, 19:52] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

________________________

_*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_

________________________

 

 

 

 

 

_*DIDEGATED*_

       _*TO*_

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

 

 

_BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM_

 

 

 

 

*🅿66*

Jakada me Martaba ya bawa umarnin kiran Sarki! ba tare da b'ata lokaci ba,ya tafi  shiru fada tayi tamkar babu mutane a ciki, Sallau sai zufa yake sharcewa duk ya rasa yanda zai yi sai gyara hula yake, yana kalle-kalle a tsorace!

 

 

 

Lokacin da Moddibo yaje wa da Balaraba zan can halin da ake ciki,ta tsorata sosai da taji cewar me Martaba ne da kansa yake neman ta, jikinta yayi sanyi domin bata san abunda zai je ya dawo ba,tunda yace mata Sallau yana gurin,nan dai Moddibo ya rarrashe ta da ta kwantar da hankalinta insha Allahu k'arshen matsalarsu tazo,haka suka futo tare,da Sadiya da Usuman Balaraba na sanye da dogun hijabi har k'asa,

 

 

Yana zaune a inda yake ya hangi sakkowar su daga matattakalar bene, sai yayi sauri d'auke kansa yana jin wani abu a zuciyarsa, dake namiji ne me jarumta kwata-kwata fuskarsa bata nuna ba,

 

Tsayuwa yayi kusa dashi suna magana, ita kuma taja hannun su Sadiya sukayi gaba,

Bud'e k'ofa tayi suka kusa cin karo da Mariya wato baiwar shi, ta shigo kai a k'asa ta k'arasa inda yake zaune  ta zube gwiwa biyu tana gaishe su,sannan tace" Ranka ya dad'e Jakada na waje yana neman iso"

 

D'aga kai yayi kawai

 

Mik'ewa tayi ta futa da sauri, ko minti biyu ba ai ba Jakada ya shigi, cikin sallama, ya kwashi gaisuwa sannan ya fad'i sak'on me Martaba.

 

 

A nutse yace" A ce masa gani nan zuwa yanzu in sha Allah"

 

Mik'ewa Jakada yayi yace "A futo lafiya ranka ya dad'e"

 

 

Moddibo yace" Nafad'a maka kak'i yarda yanzu dai gashi kaji daga bakinsa ko"

 

A nutse ya mik'e tsaya ya d'an ya mutse fuskar sa kad'an yace"muje"

 

 

Moddibo ne ya bud'e k'ofar suka futa tare,Balaraba na tsaye a wani guri ta hangi futowar su, saurin dauke kanta tayi ganin yadda kyawun Sarki! ya dusashe na Moddibo,wani in rana ta daki fuskarsa yana muuni!sai taga shi wannan wani k'yalli da annuri fuskarsa take, tafiya yake cikin kasaita, tana kallon bakinsa daga inda take yana motsi da alama magana suke da Moddibo, ta lura tunda ya futo bayin da suke gurin suka bar abunda suke suna gaishe shi,

 

 

 

Ganin sun kusa zuwa inda take ne yasa tayi saurin kauda kanta,ta gyara yanayin fuskarta sosai gudun kar ya kawo wargi.

 

 

Moddibo yace"Yi hakuri Gimbiya kina tsaye kina jiranmu ko"

 

 

Murmushi tayi kawai ta basar, Sarki! kuwa wucewa yayi ya barsu a gurin, sai suka biyo bayansa.

 

 

Bayan sun dai-dai ta zamansu gaban me Martaba, ya kalli Balaraba sosai yana nazarin ta,a idonsa yake ganin kamar yasan fuskar, gyara murya yayi kalli Sallau da ya diririce a gurin duk alamun rashin gaskiya sun bayyana,a tare dashi,yace"Wannan itace yarinyar da kake magana akanta"?

 

Sallau ya d'aga kai cikin tsaguwa Sam yaki kallon gefen da Balaraba take, lokacin k'ankani me Martaba ya fahimci Sallau bashi da gaskiya,girgiza kai kawai yayi ya mayar da idonsa kan Sarki! Yace"Magajin Sarki ya labarin bunkicen da nasa kayi min kan wannan yarinyar dake zaune kusa da kai"

 

 

Cikin yanayin maganar sa ya ce"Allah ya baka nasara, a gafarce ni, nayi laifi saboda banzo na fad'a maka komai ba yau tsawon kwana biyu kenan, dama yau nakeso inzo in fad'a maka sai ga shi ka aiko,tuba nake ranka ya dad'e"

Galadima yace"me Martaba ya karb'i uzirin ka"

 

Moddibo ne ya kalleshi yana masa magiya da ido,dama kafin su futo sai da ya dunga lallab'ashi

 

 

Sarki! yayi gyaran murya a nutse yace"Allah ya taimake ka nayi bunkice sosai nagano wannan yarinyar bata da wani aibu yarinya ce me ladabi da biyayya da bin nagaba da ita,nayi bunkice sosai duk wani sharace-sharace da ake mata basu da tushe,anayi ne domin ganin tana futa kullum gurin sana'arta,wannan shine abunda na sani a game da ita,

Ya karasa maganar cikin nutsuwa.

 

 

Shiru na minti biyu me Martaba yayi gyaran murya hankali kwance yace" Nayi farin cikin jin wannan abu, wannan yarinyar tun kafin in ganta hankali na ya kwanta da ita,in sha Allahu tana tare damu ita da "yan uwanta, ni ne zan shige mata gaba,kan lamarinta, a yanzu yanzu zan d'aura mata aure da Yusuf Moddibo, saboda na yaba da nagartarsa gami da jajircewar sa kan lamarin ta, wannan shine hukuncin da na yanke"

 

 

"Alhamdulilahi-Alhamdulilahi, Abunda Moddibo yake ta fad'a kenan cikin zuciyarsa, Balaraba ma taji dad'in yadda abubuwa suka zo da sauk'i haka, duk wanda yake zaune a fadar yayi murna da wannan abu,in ka cire mutum biyu wato Sallau da Waziri Zayyanu,

 

 

Nan me Martaba ya umarci maga takarda da ya futa ya sanar a cikin gida,sannan ya tawo  da goro da Alawa domin, cika al'k'awarin da ya d'auka.

 

 

 

Shiru fada tayi bayan futar maga takarda,kowa da abunda yake sak'awa cikin zuciyarsa,kawai sai sukaji muryar Waziri Zayyanu cikin fushi!yace" wannan hukunci da me Martaba ya yanke bai yi ba, domin ni ne nake da hakki a kan yaronan don haka ban amunce ya auri wannan yarinyar ba,in ko ya aureta zai had'u sa fushina!

 

 

 

 

 

 

*Tofaaaaaa!*

 

 

*Fans kuna ina ne wa ya dace Balaraba ta aura, shin me zai biyo baya in me Martaba ya d'aura auran Moddibo da Balaraba, shin wane irin rikici ne zai faru kan hakan, yaya su Lantana zasuji jin cewar Balaraba tayi aure gidan sarauta, shine wanene mijin Balaraba???*

 

*SARKI! NE KO MODDIBO?*

[05/08, 00:16] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

________________________

_*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_

________________________

 

 

 

 

 

_*DIDEGATED*_

       _*TO*_

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

 

 

_BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM_

 

 

 

 

*🅿67*

 

 

 

 

Shiru fada tayi ana kallon kallo abunda Waziri ya fad'a ya girgiza jama'ar dake gurin. me Martaba bai tab'a yanke hukunci ba, a samu wani wanda zai ce be yi dai-dai ba, kowa yana jiran yaji abunda me Martaba zai ce, shiru yayi kawai yana jin damuwa da b'acin rai a zuciyarsa yau Waziri ya nuna masa cewar d'anshi Moddibo bashi da iko a kansa aure tunda ya riga ya yi niyyar d'aura shi a yanzu sai ya d'aura shi, saboda haka duk abunda Waziri yaga zaiyi yayi, yanzu yana sauraron dawowar maga takarda ne.

 

 

Mik'ewa Waziri yayi ya futa, ba tare da ya yiwa kowa sallama ba, me Martaba yaji ciwon abunda d'an uwansa yayi masa,amma sai yayi shiru kawai.

 

 

Mintuna goma da futar Waziri sai ga maga takarda nan ya dawo, yana tare da wani bawa a bayan shi, yana d'auke da d'aurin goro da kwalin alawa, Galadima ne ya matso ya kwance d'aurin goron da alawa, kansa a kasa yace"Allah ya taimake ka, Waziri tuba yake yayi abisa kuskure a gafarce shi"

 

Murmushi kawai me Martaba yayi ya kalli Sarki! dake zaune kanshi a k'asa yana jini b'acin rain abunda Waziri yayi wa mahaifin sa.

 

Kafin me Martaba yace wani abu Sarki! Ya fahimci abunda yake nufi, kamar ya sani kawai ya zura hannu cikin rigarsa ta ciki ya futo da kud'i zasu kai duba talatin  ko sama da haka, mik'ewa Moddibo yayi ya rik'e a hannusa, kasa-kasa yace"ka rik'e a hannuka ana d'aurawa sai ka bata sadakin ta"

 

Moddibo ya k'arba fuskar sa d'auke da murmushi kana ganinsa kasan na farin ciki ne.

 

Kafin kace kwabo fada ta cika da mutane, nan me Martaba ya Umarci babban limami a fara d'aura aure.

 

Alhamdulilahi-Alhamdulilahi an d'aura auran Moddibo da Balaraba kan sadaki dubu arb'ain da biyu, nan maga takarda ya fara rabon alawa da goro me Martaba ya Umarci Moddibo ya d'auke Balaraba su futa, haka kuwa a kayi, suka futa,suka bar Sarki! suna ta gaishe-gaishe da mutane

 

Jiki a sanyaye Balaraba ta dunga tafiya har suka isa shashen Sarki! gabanta sai fad'uwa yake tana jin kamar a kwai wani abu da zai faru.

 

 

Can fada kuwa komai yana tafiya dai-dai kana kallon Sallau kasan yana cikin wani mugun hali na d'imuwa yayi yunk'urin mik'ewa ya kasa saboda yadda yake jin jikinsa na rawa ji yake kamar kafarsa ba a jikin jikinsa take ba, nan me Martaba ya sallami kowa, mutanan da suka rage a ciki sune makusantan sa, sai Sallau da me gari Halilu da Walidi,  kyautar ban girma me Martaba yayi wa  Walidi, wanda tasa shi kusan sumewa a gurin ya dunga godiya, me Martaba yaja kunnen Sallau sosai, da sosai, sannan ya gargad'i me gari Halilu kan kar ya kuma aikata abu maka mancin haka, me gari Halilu ya bada hakuri kuma ya nemi afuwa, shi ko Sallau bud'ar bakinsa,sai yace"ranka ya dad'e maganar sauran yaran wato Sadiya da Usuman ina so abani su mu koma gida"

 

Sarki!! Ya d'ago da kansa cikin fushi! yace"Sadiya da Usuman zasu zauna gurin "yar uwarsu,kai ka tafi ka kad'ai"

Wani bafade ya kalli Sallau da jajayen idonsa yace"gyara kintsi dai!!! kayi na d'aya kayi na biyu kar ka sake kayi na uku,anan zan tub'e ka in zane maka jiki,ko zaka nunawa me Martaba abunda ya dace ne."

Girgiza kai Sallau yayi jikinsa na kyarma! cikin tsawa wannan bafade yace"ka nemi afuwar gurin me Martaba"

 

Jiki na rawa Sallau yace"Allah shi gafarta maka ina neman afuwa"

 

Saura kad'an Walidi ya saki dariya saboda yadda ya ga jikin mahaifin nasa yana rawa, murmushi me Martaba yayi yace"Allah yayi mana afuwa baki d'aya, wato malam Sallau maganar wad'annan yaran naka Sadiya da Usuman kayi hakuri kabar su gurin "yar uwarsu kaji ko, duk lokacin da kukayi sha'awar ganinsu za'a kawo muku su har gida,idan kuna sha'awar zuwa gurin su k'ofa a bud'e take muna maraba da ku baki d'aya"

me gari Halilu yace"godiya yake ranka ya dad'e"

Ganin babu yadda zai yi ne yasa ya fara yak'en dole yana godiya ga me Martaba, amma in zaka tona zuciyarsa a lokacin tafi garwashi zafi da turiri.

 

Nan me Martaba ya bada Umarni a kaisu gida tare da kayayyakin abinci buhu-buhu   mota guda a ka had'a musu na kayan masa rufi,Walidi kuwa in ya tuno da kyautarsa da akayi masa sai yaji kamar babu wanda ya fishi sa'a a rayuwa,gobe i yanzu yana cikin kasuwar sha tambaya yafara gudanar da kasuwancin sa.

 

 

 

 

Cikin tsananin b'acin rai! Waziri Zayyanu ya shiga b'angaran sa,sai a kayi sa'a duk "yayan shi maza na zaune a falo suna hira, nan suka ga shigowar mahaifin su hankalin sa a tashe, Khalifa ne yace" Allah yasa lafiya dai na ganka kana faman gumi!

Zama yayi cikin kujera yana cire rawanin dake nannad'e a kansa,yace"je ka kira min mahaifiyar ka"

Tafiya yayi kiranta, ya kalli sauran yaransa da kumfar baki yace" in dai nine na haife ku daga yau na rabaku da Moddibo har abada babu ni babu shi hakanan kuma babu ku babu shi"

Cikin rashin fahimta Ishak yace"ban fahimci me kake nufi ba Baba"

 

Zuwan mahaifiyar tasu ne ya dakatar da maganar da yake tazo ta zauna kusa da mijin nata,tana kallon fuskarsa tasan lallai yau an tab'oshi"

"Lafiya ranka ya dad'e"?

Ta fad'a cikin sigar tambaya.

 

Waziri yace" zaki ce min baki san abunda yake faruwa bane? kun had'a kai da d'anki kun munafurce ni, yaje ya d'auko yarinya da suka gama lalacewa da ita a waje ya kawo wa wannan mak'iyin nawa ya d'aura masa aure da ita"

 

"Duk maganar da kakeyi ban fahimce ka ba,domin kuwa ni ban San abunda yake faruwa ba"

 

Girgiza kai yayi kawai ya umarci d'aya daga cikin yaran dake zaune a gurin yaje ya kira Moddibo.

 

Hankalin kowa ya tashi a gurin saboda sun san halin mahaifin nasu bai iya b'acin rai ba.

 

Mintuna goma tsakani Moddibo suka shigo tare da Ishak d'an uwansa

 

Ko zama Waziri Zayyanu bai bari yayi ba,yace"Umarni na ne ni ne nasa a kira ka, saboda dalilai masu k'arfi,yanzu-yanzu nake so ka furta cewar ka saki wannan yarinyar da kasa aka d'aura maka aure da ita,idan kuma kak'i ni yanzu zan saki taka Uwar,saboda haka zab'i ya rage naka."

 

 

 

 

 

 

*Muje zuwa*

 

 

 

*Comment Vote and Share*

[05/08, 20:08] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

________________________

_*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_

________________________

 

 

 

 

 

_*DIDEGATED*_

       _*TO*_

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

 

 

_BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM_

 

 

 

 

*🅿68*

 

 

 

 

Dukaninsu sun furgita da jin furucin da mahaifin nasu yayi, ita kanta mahaifiyar tasu ta girgiza da furucin da mijin nata yayi,kuma tafi kowa sanin halinsa zai iya aikata duk abunda ya fad'a.

 

Modibbo ya shiga, tsaka me wuya bai tab'a tsammanin hukuncin da mahaifin nasa zai yanke ba kenan,iya tunanin sa yana ganin zaiyi fushi dashi daga baya ya sakko shi kuma sai ya nemi afuwar sa, tabbas Uwa-Uwa ce, babu ta yadda za'ayi ta sanadiyar sa ya rushe auran da aka d'aurashi sama da shekara talatin da wani abu,dole duk son da yake wa Balaraba ya rabu da ita ko da hakan zai yi sanadiyar rasa rayuwarsa, a kan mahaifiyar sa babu abunda ba zai iya ba.

Khalifa ne mara kunya sosai ya cikinsu  yace"Mu baza ka jawo mana b'acin rai!ba a cikin gida saboda haka kabi umarnin da a ka baka, idan ba haka ba zamu b'ata maka rai kuma zamu hana matar taka daka aura jin dad'in duniya,a kan mahaifiyar mu,babu abunda baza muyi ba"

Jin furcin da Khalifa yayi yasa Waziri umartar sa da yaje ya d'auko takarda sa biro, aikuwa da sauri ya tafi, ita kuwa Hajiya Kattime tana zaune tana kallon ikon Allah bakinta ya mutu, takasa fahimtar komai, a wannan badak'alar da take faruwa.

 

Khalifa ya dawo hannusa rik'e da farar takarda da biro ya zo ya mik'awa Moddibo, guda d'aya, d'ayar kuma yaje ya kai wa mahaifin nasu ganin Waziri ya d'ora biro jikin takkada yasa Moddibo saurin dakatar dashi, da hannu jikinshi na kyarma! yayin da gumi yake zuba a jikinsa, ya d'ora biyu jikin farar takarda  yayi rubutu kayi biyu,kamar haka.

 

_Ni Yusuf Moddibo na saki matata Balaraba Ayuba Tanko saki d'aya kacal, kan wani dalili guda d'aya, ina fatan Allah ya had'amu da ita a aljanar Firdausi_

 

Yana gama rubutuwa ya ninke takadar, zuciyarsa tana wani bugawa fatt!!fatt!fatt! Waziri Zaiyyanu ya mik'a masa hannu  yana nufin ya bashi takardar, a hankali ya karasa inda yake zaune ya mik'a masa, bud'e takardar yayi ya karanta ya mayar ya ninke ta ya aje ta gefe,wani takarda ya kara cirowa ya mik'awa Moddibo cikin bada Umarni yace"Saki uku zaka rubuta mata,saboda nasan halin wancan mutsiyacin zai iya turasasa ka ka mayar da ita,don haka ban yarda da saki d'aya ba"

Cikin tsantsar b'acin rai Hajiya Kattime tace"Wannan abunda kake tsantsar jahilci ne da son kai, Allah da kansa shi ya hallici saki,kuma ya umarci da ayi shi,amma kuma baya son ayi din,saboda haka tunda ka tursashi ya rubuta saki d'aya saboda son zuciyar ka to ka kyaleshi haka, ba lallai sai an saki mace saki uku ba take sakuwa,saki d'aya ma ya hallata"

Cikin tsawa Waziri yace"Zakayi abunda na saka ko sai ka gama jin hudubar da mahaifiyar taka take maka"

Ganin Moddibo ya tsaya yayi shiru da takarda a hannu yasa Waziri ya d'ora biron dake hannusa a jikin takarda ya fara rubutu.

 

Moddibo ya rik'e hannunsa jikinsa zafi rad'au! muryasa a shak'e yace"Baba Waziri ka gafarce ni, idan nayi maka,laifi, ni Yusuf Moddibo na saki Matata Balaraba saki uku"

"Innalilahi wa inna ilaihi rajiun"

Shine abunda Kattime take fad'a zuciyarta kamar tayi bunduga tarasa wane irin bakar zuciya ne da mijin nata.

Mik'a masa takardar yayi a karo na uku yace"rubuta min da hannun ka"

Ganin babu abunda yayi saura yasa Moddibo ya rubuta ya mik'a masa, ya bud'e ya karanta tsaf, cikin bada Umarni yace"Ka tafi da kanka kaje ka kaiwa wanda ya d'aura maka auran" Moddibo ya karb'i takardar ya kama hanya, yana tafiya yana had'a  hanya jiri yana kwasar sa,Allah yasa bangaran babu ma'aikata sosai, sai da ya futa harabar gidan sarautar sannan ya dai-dai ta nutsuwar shi,amma duk da haka duk Wanda ya kalleshi a lokacin yasan yana cikin tsananin damuwa, haka ya isa fada, lokacin ana shirye-shirye kiran sallaar magariba 

me Martaba ya futo kenan domin shiga gida suka ci karo da Moddibo, yana kallonsa ya gane da akwai matsala, kafin yace komai Moddibo ya mik'a masa takardar hannunsa, da sauri maga takarda ya karb'a ya bud'e  ya fara karantawa kamar haka.

 

_Ni Yusuf Waziri Zayyanu na saki matata Balaraba Ayuba Tanko saki uku,saboda wani dalili,ina rokon Allah ya had'amu da ita a aljanar Firdausi_

 

*Innalilahi wa innailaihi raji'un*

Kalmar da me Martaba yake ta maimai tawa kenan, kafin su ankara Moddibo ya zube a gurin yana wani irin murk'ususu, jini na fita ta baki ta hanci, ya rik'e cikinsa tamau! bakinsa na motsi,kalamar shahada kawai yake

Sarki! ne ya futo daga b'angaransa ya na d'aure da alwala,sai ya hango abunda yake faruwa saboda haka cikin sauri da sassarfa ya k'arasa gurin,lokaci mutane har sun taro, hankali a tashe ya tsuguna ya d'ora gwiwarsa a k'asa ya d'auki kan Moddibo ya d'ora a cinyarsa, cikin damuwa ya sanya gefen rigar shi yana goge masa jinin dake futa daga bakinsa, Moddibo ya rik'e hannunsa tamau!! wani hawaye yana zuba ta gefen fuskarsa, muryarsa bata futa sosai yace"Allah yayi bazan yi tsayin kwana ba, a duniya balle in rayu da yarinyar da zuciyata take mutukar so, d'an uwana ne kai ko na mutu kai na amunce da ka maye gurbi na gurin Balaraba, ka bata hakuri,ga tanan na bar maka amana son Balaraba wani b'angare ne na zuciyata na tabbata ko na rayu a duniyar nan to da soyayyarta zan mutu, Sarki! na baka amanar Balaraba"

Ya k'arashe maganar yana wata irin shak'uwa!

Cikin tashin hankali da damuwa me Martaba ya bada Umarni a dauko mota domin a tafi asibiti,Moddibo najin abunda ake sama-sama girgiza kai kawai yake domin shi yasan halin da yake ciki,,hannun me Martaba yake taso ya kama,ganin haka yasa Sarki!kamo hannun me Martaba ya had'a dana Moddibo, me Martaba ya rik'e hannun sosai yana kalmatussha hada, nan take Moddibo ya fara fad'a shima. "La'ilahaillallahu Muhammadur rasulullahi,sallalahu alaihi wassalam" Da wannan kalmar Moddibo ya cika, dai-dai lokacin da ake k'wala kiran sallahr magariba.

[07/08, 13:48] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

________________________

_*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_

________________________

 

 

 

 

 

_*DIDEGATED*_

       _*TO*_

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

 

 

_BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM_

 

 

 

 

*🅿69*

 

 

 

Wata irin ajiyar zuciya Sarki! ya saki lokacin da ya ji jikin Moddibo ya shika a jikinsa, sai yayi zaman dirshan a gurin had'e da rungume gawar yana wani irin kukan zuci idanunsa sunyi jajawur!kalmar innalilahi wa'ina ilaihi raji'un kawai yake maimaita wa cikin zuciyarsa.

 

Kafin kace kwabo mutuwar Moddibo ta watsu a cikin gidan,mutane kowa na futowa daga b'angaran sa cikin tashin hankali, lokacin da labarin ya iski Waziri bai yadda ba,sai da ya tura Khalifa domin yaje ya gani gaske ne,aikuwa Khalifa ya dawo cikin tashin hankali,ya tabbatarwa da Mahaifin nasu hakane.

 

 

Waziri ya shiga cikin tsananin rud'u da tashin hankali,a gigice ya futo kafarsa babu takalmi ya nufi fada,zuciyarsa na yi masa sak'e-sak'en cewa Sarki Almustafah shine ya kashe masa d'ansa saboda wani dalili nasa.

 

Lokacin da ya isa,gurin ana ta k'okarin cire gawar Moddibo daga jikin Sarki! Abun ya gagara domin ya rik'e shi tam! wasu hawaye na zubo masa masu tsananin rad'ad'i, cikin zuciyarsa yake cewa shikkenan na rasa d'an kuwa nagari shikkenan narasa amini me share min waye, me yasa mutuwa zata d'auki Moddibo ta barshi,shi a duniya shima tabbas bashi da wani amfani a cikinta.

 

me Martaba ne yake ta rarrashin sa kan ya sake shi a d'auke shi daga gurin,gashi lokacin sallah yayi,amma tamkar da dutse yake magana,kwata-kwata Sarki! baya fahimtar abunda yake cewa.

 

Waziri ne ya k'araso gurin idanunsa a kan gawar Moddibo,kurrr!! Yake kallonsa kamar wani zautacce yace"K'arya ne, babu wani munafurci da ban sani ba,a gidan nan duk wani abu a dake shirya min ni da "yayana nasan shi, saboda haka, ni sai nabi kadin jinin d'ana Yusuf Moddibo"

 

Cikin mamaki jama'ar dake gurin suke kallon Waziri jin irin maganar da yake fad'a,maganar tasa tayi kama da ta masu tab'in hankali. Babu wanda ya saurare shi, a cikin su, suka cigaba da bin umarin me Martaba, da k'yar suka samu suka b'anb'are Moddibo daga jikin Sarki! suka nufi fada dashi, domin killace shi tunda dai dole yayi kwanan keso.

Waziri ne ya bi bayan su yana gyara alkyabar dake jikinsa, yace"Ban yadda a aje min gawar d'ana anan ba, domin inaso in kaishi kabarinsa da duk sassan jikinsa gaba d'aya, idan aka aje min gawar d'ana a wannan fada ban yafe ba,domin wannan fada bata alkairi bace,bata tattare da komai sai shirka,da tsafi gami da shanye jinin mutane"

Jin irin kalaman da Waziri yake fad'a ne yasa wad'anda suke d'auke da gawar Moddibo suka dakata, me Martaba kuwa cikin karfin hali yace"Kuje Ku cika umarnin da na Baku"

Aikuwa sai suka shige ciki sosai suka aje Moddibo gefe, suka futo gami da tsayawa bakin Kofa,suna jiran Umarni na gaba, me Martaba ya kallesu a nutse yace"Ku tsaya nan gurin ban yadda kowa ya shiga inda yake ba,yanzu zan futo zan shiga sallah"

Nan suka amsa suna godiya

 

Me Martaba ya wuce Waziri a gurin yana zare ido.

 

Waziri kuwa duk ya rasa abunda yake damunsa duk wannan maganganun da yayi, yayi ne kan ya b'ata wa me Martaba rai sai yaga ko a fuskarshi be nuna ba, ya fahimci yana cikin tashin hankali,kuma yasan bata komai bace face ta rasuwar gudan jininsa,.

Shi yanzu sam bai damu da rasuwar Moddibo ba,burinsa kawai yaga ya rusa sarautar Sarki Almustafah,ya kafa tasa

B'angaran sa ya koma fud'un-fud'un yana tafiya yana zancan zucci.

 

Bayan idar da sallar ne limami ya sanar da rasuwar Moddibo ta lasifi k'a inda jama'ar gari suka ji suka shiga cikin tsananin d'imuwa da jin mutuwar bawan Allah Moddibo, mutumin da bai dauki kansa a komai ba, yana rayuwa dai-dai da kowa Moddibo in ka ganshi baza ka taba cewa yana da alak'a da sarauta ba.

 

 

Hajiya Kattime tayi kuka tayi Ala wadai da turr! da halin mijinta,babu tamtama shine yasa zuciyar Moddibo ta buga ya mutu lokaci guda, duk da cewar ita musulmace muka ta yadda duk kanin me rai mamaci ne,mutuwar Moddibo tana alak'a da mahaifinsa Waziri,shine sila.

 

 

Humm Rayuwa kenan, me Martaba ne da Sarki! suka wanke Moddibo tsaf suka suturtashi, suka kuma kwana dashi, har garin Allah ya waye.

 

 

Mutane damk'am a harabar gidan sarautar suna jira a futo da gawar Moddibo domin su sallah ce shi, kowa da irin abunda alkairin da yake fada a kansa.

 

 

Har waye war gari Waziri bai futo ba, kuma duk irin karatun da ake cikin gidan yana ji, domin malamai ne suka taro suna ta sauke wa Moddibo al'ikur ani.

 

 

Me martaba ne ya bada Umarni a je a kira Waziri dole ya zo kan gawar danshi kafin a d'auke shi, sannan ya umarci Sarki! kan yaje ya futo da Balaraba, itama tazo kan gawar mijinta kafin a d'auke shi.

 

 

Gabansa ne ya fad'i  domin kwata-kwata ya manta da Balaraba, nan take ya shiga wani yanayi da ya tuno da nauyin ta da Moddibo ya dora masa kafin rasuwar sa.

 

 

A nutse ya mike ya futa daga fadar,  wani bawansa yana take masa baya, kai tsaye shashensa ya nufa.

 

 

 

Balaraba kuwa tun lokacin da Moddibo ya kaisu daki ya ajesu, ta shiga cikin wani yanayi me wahalar fad'a motsi kad'an tayi zataji gabanta na faduwa,lokacin da Moddibo ya zo futa kiran sa tayi ta sanya kuka, tace"Yusuf a rayuwata bani da babban masoyi sama dakai da me Martaba, tabbas yanzu na kara tabbatar da soyyayar da kake min ta gaskiya, Yusuf na baka amanar kaina, saboda kazama jigo na rayuwa ta, ina rokan Allah ya amintar da ruhimu tare"

Hawaye ya share mata,yana wani murmushi Wanda ya kara masa kyau,ya kama duk hannuwanta ya rik'e a nasa cikin taushin murya yace" Gimbiya baki da matsala dani insha Allahu karshen kukan ki ya k'are a duniya,fatana dake kawai ki rik'e amana ta,kuma ki tayani addu'a  zanje in nemi yafiyar mahaifina, saboda na lura da halin da ya shiga lokacin daurin auran mu"

 

 

Wani hawayen ya kuma zubo mata,ba tare data goge ba tace"Yusuf inajin wani abu a zuciyarta a game da wannan al'amari, don Allah ka nemi afuwa gurin Baba Waziri, kan dukkanin abunda yazo maka dashi"

 

Damk'e hannunta yayi sosai cikin nasa,  da murmushi a fuskarsa yace" Insha Allahu komai zai zo da sauki, yanzu abunda zakiyi shine, kici abunci ki bawa su Sadiya suci su kwanta, ke kuma sai kiyi alwala kiyi sallah raka'a biyu ta nafila domin ki nema mana zab'i na Allah, yanzu zanje in dawo muyi hira me dad'i irin ta Ango da Amarya"

Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta.Ya mik'e tsaye  da murmushi a fuskarsa,ya kamo fuskarta ya manna mata kiss, rufe ido Balaraba tayi cikin jin kunya, fuskar ya saki, ya nufi hanyar futa yana waiwayenta, har ya bud'e kofa zai futa,ya tsaya yace"Gimbiya sai na dawo"

Bud'e ido tayi da sauri tana kallon kofar futa ko rigarsa bata gani ba,ya fuce.

 

 

Jiki a sanyaye ta mik'e ta nufi toilet ta dauro alwala tazo ta shimfid'a dadduma ta tada sallah kamar yadda Moddibo ya umarce ta.

 

Sosai ta yi addu'oi tana kuka tana rokan Allah,  bacci ne ya ci k'arfinta nan kan daddumar ta b'ingire bacci me nauyi ya d'auke ta,ba tare da taci komai ba,hakanan su Sadiya basu ci komai ba suma bacci ya kwashe su,

 

Humm baccin asara kenan baccin da Balaraba bata tab'a irinsa ba, ko sallahr asubah ba tayi ba, a tak'aice dai Balaraba bata da labarin rasuwar Moddibo domin bata tashi farkawa ba sai k'arfe bakwai da kwata  na safe.

[08/08, 04:57] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

________________________

_*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_

________________________

 

 

 

 

 

_*DIDEGATED*_

       _*TO*_

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

 

_*BISMILLAHI-RAHAMANI-RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿70*

Bugun k'ofar Sarki! ne ya tashe ta,ta mik'e zaune jikinta duk a mace,da k'yar ta mik'e tsaye ta nufi, K'ofa domin bud'ewa duk a tunaninta ko Moddobo ne, tayi mamakin baccin da ya kwashe ta,me cike da tarin mafarkai marasa kyau.Bud'e kofar tayi tana koma wa ciki ba tare da ta kalli me shigowa ba, shiga yayi d'akin sosai yana bin su da kallo daga ita har su Sadiya

 

Sai da ta zauna gefen gado tana kallon sa, gabanta ne ya fad'i lokacin da suka had'a ido da Sarki! Mutum me fararan idanu taga k'wayar idonsa ta rine tayi jajazur!

K'asa tayi da kanta,gabanta na dukan uku-uku! A nutse yace"Kinyi sallah"

 

Cikin wani irin yanayi ta kalleshi tana girgiza kai.

Alamun batai ba.

 

Ajiyar zuciya ya sauke k'asa-k'asa yace" Kiyi sallama ki sauko k'asa ki same ni, ina jiran ki"

 

Cikin k'arfin hali tace"Ina Moddibo"?

Yana k'okarin futa daga d'akin yace"Yana k'asa,zaki sauko ki same shi"

Futa yayi ba tare da ya saurari abunda zata ce ba.

 

Mamaki take me ya kawo shi d'akin ina Moddibo yake?,shine ya kamata ya shigo gurin ta ba Sarki! ba,bayan haka kuma taga kamar a kwai alamun rashin nutsuwa a tattare da Sarki!

Sauri-sauri tayi alwala ta futo ta tada sallah.Bayan ta idar tai addu'oi yanda ya sauwak'a ta mik'e har zata futa ta dawo tana duba su Usuman dake ta faman bacci, Ajiyar zuciya tayi ta tashi Sadiya domin tayi sallah,sai da taga Sadiya ta shiga toilet sannan ta futa daga d'akin.

 

 

Yana tsaye tsakiyar falon hannunshi goye a bayansa hankalinsa na sama ita kawai yake jira ta sauko, had'a ido sukayi a karo na biyu lokacin da take saukowa dukkaninsu suka d'auke kai,sai kace wasu surukai, bai jira sun jera ba, ya kama hanya zai futa, ita kuma sai ta tsaya a tana kallon sa,yace tazo kasa ta same shi zai futa kuma ina Moddibo yake?

Mutumin dake take masa baya ne yace"Allah ya kara miki lafiya, ai bayansa zaki ni, me Martaba ne yake neman ki"

Jin abunda yace yasa fad'uwar gabanta ya tsananta, babu kuzari tabi bayansa, kanta a k'asa

Tayi mamaki da ta dunga ganin mutane a harabar gidan kuma kowa ta kalli fuskarsa babu walwala gashi wasu daga ciki sai kallonta da k'yar dai suka isa fada, Sarki!ya tub'e takalmin sa ya shiga,ita kam tsayuwa tayi bakin Kofa sai da akai mata iso sannan,ita babban abunda ya d'aga mata hankali shine dandazon mutanan da ta gani shiya furgitata.

Me Martaba ne kad'ai cikin fadar sai gawar Moddibo dake cikin makara a killace, Balaraba na sanya k'afarta ciki taci karo da makara, fad'uwa ta kusa yi saboda tsorata da tayi,bango ta dafa da hannunta miyau din bakinta ya bushe tass!tamkar ba'a tab'a hallitarsa ba,a bakinta har wani shak'ewa take, zubewa tayi bakin k'ofa, tana shashsheka,shikkenan mafarkin da tayi kan Moddibo ya tabbata babu tamtama wannan Moddibo ne cikin makara,kamar yadda ta ganshi jiya cikin baccin ta, kamar zautacciya ta k'arasa kusa da Moddibo da rarrafe,ta sanya hannu ta d'aga mayafin da aka lullub'e masa fuska dashi, Silalewa tayi ta fad'i a gurin ta suma.

 

Da sauri Sarki!ya mik'e yaje ya janye makarar,cikin tashin hankali yake tunanin yaya zai da ita

 

Me Martaba,ne ya mik'o masa ruwa irin na gora,ragowa ne wanda ya sha ya rage yana aje a gefe, jikinshi na kyarma!ya karb'a ya gumtsa a bakinsa ya fesa mata a fuska, ta bud'e idonta zumbur zata mik'e a gigice!Sarki!ya dafe,hannunta dake rawa,karr!-karr! muryasa bata futa sosai ya kalli mahaifin nasa yace"Allah ya taimake ka, ya kamata a futa da Moddibo domin wannan kwata-kwata babu abunda zata iya yi masa na addu'a tunda bata cikin hayyacin ta,ina ganin zan shiga da ita gida gurin Mama dole sai tasa ido a kanta zata iya futa bata sani ba"

 

Me Martaba yace"Wannan shawarar taka itace shawara, kai ta cikin gida, idan ka shiga kai kiro min Hajiya Kattime da Mahaifiyar ka, su futo suyi bankwana da Yusufu domin za'akaishi gidansa na gaskiya"

 

"In sha Allah"

Sarki ya fad'a lokacin da yake mik'ewa yana rik'e hannun Balaraba da ta zama kamar wata zautacciya, yayi da ya sanin zuwan ta gurin, mik'ewa tayi tsaye kafafunta na rawa, sai kace me koyan tafiya,haka ta kuma komawa ta zube gurin,Suma ta k'ara yi a karo na biyu,wannan karon hankalin Sarki!ya tashi,sosai da sauri ya d'auko gorar ruwan a karo na biyu,ya gumtsa a bakinsa ya fesawa fuskarta babu alamun zata farfad'o kuma fesa mata yayi a karo na uku na shiru, mik'ewa yayi har yana kusa tuntub'e da k'afarta, hanyar futa ya nufa, cikin sauri, Shamaki na tsaye bakin k'ofar shigowa yaga futowar Sarki! da sauri yazo ya rissina Sarki! yace" Yanzu ka umarci jama'ar dake bakin hanya su matsa zan futo ya zuwa shashen Mama Fulani"

 

Shamaki yace"Angama ranka ya dad'e"

 

Minti uku Shamaki ya dawo yace"ranka ya dad'e  zaka iya futowa"

 

Hannu kawai ya d'aga masa ya koma ciki,

Balabara dake kwance ya hau tattaro wa da niyar d'aukar ta me Martaba na kallonsa, ya ciccib'eta cikin jarumta ya nufi k'ofar futa da ita kana ganinsa kasan yana cikin tsantsar damuwa dan dai shi mutum ne me tawakkali da mik'ewa Allah lamarinsa, cikin nutsuwa yake tafiya da ita,tana hannunsa yayi mata d'aukar jarirai, duk tsayin tazarar dake tsakanin fada da b'angaran Mama Fulani,bai damu ba, shi ko ya gaji ji yake maka tamkar yarinya k'arama ya d'auka,duk da cewar Balaraba tana da girman jiki kuma bata da rama, a jikinta.

Yana tafiya yana kallon fuskarta, wani irin tausayinta na ratsa masa zuciya, haka ya isa shashen mahaifiyar tashi, mutan dake gurin sam basu dame shi ba, burinsa kawai ya kai Balaraba gurin Mamanshi domin yana jin tsoron amanar Moddibo ta samu matsala, ganin shine yasa bayi dake shashen suka dunga sunkuyar da kansu har sai ya wuce sannan zasu d'ago Kansu

 

Wani k'aramin falo ya wanda zai sada ka da babban falon Mama Fulani,nan ya tarar dasu Mama Fulani Hajiya Kattime Halisa,  Hajiya Madabo mahaifiyar Halisa Gimbiya Azima, domin itama tun yammacin jiya tazo sai ta riski abunda yake faruwa, duk suna zazzaune kowa da carbi a hannu,idanunsu sunyi jajazur! bai saurare su ba ya wuce da Balaraba ciki, har bedroom d'in Mama Fulani, kwantar da ita yayi a makeken gadonta,ya nufi k'aramin firji dake d'akin,ruwa ya ciro me sanyi sosai ya bud'e ya fara tuttulawa a jikin Balaraba, wanda yayi dai-dai da shigowar Mama Fulani cikin tashin hankali,tace "Me yasa me ta"?

 

" Suma take Mama wannan yarinyar amanar Moddibo ne, Mama ki taimaka min kar tabi bayansa"

Yafad'a tamkar wanda baya cikin hanlalinsa, lallai na yarda da ake cewa komai girman mutum a gaban iyayensa Yaro ne.Rarrashin sa take ganin yadda ya tada hankalinsa, ragowar ruwan dake hannunsa ta karb'a ta yayya mata, cikin sa'a Balaraba ta bud'e ido tana sakin wata ajiyar zuciya,, kalle-kalle kawai take yayin da take jin wani irin ciwon kai!

Ajiyar zuciya ya sauke ganin ta dawo hayyacinta yayi saurin futa daga d'akin don kar ta ankara dashi a gurin, yana Futa k'aramin falon ya fad'a musu umarnin da me Martaba ya bayar, mik'ewa sukayi suka futo domin zuwa fada, tsakanin Halisa da Azima harara ce ke had'asu, Halisa wani bak'in kishi ne yake damun ta ganin yadda Habibinta ya rungomo Balaraba a jikinsa,sai kace Wanda ya dauko matarsa, itama Azima nata b'angaran haka abun yake domin kishin da taji lokacin da taganshi da Balaraba har yafi na Azima, kawai daurewa take,dan dai gidan mutuwa tazo.

 

 

 

 

 

*Gaskiya ina jin dad'in comment d'inku*😀

 

_*ANATARE IYA WUYA*_

❤❤❤❤❤❤❤❤

 

 

 

 

_Ina taya ku jimami  na rashin Moddibo Allah ya bamu hakurin jure rashin sa_

[09/08, 17:22] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

________________________

_*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_

________________________

 

 

 

 

 

_*DIDEGATED*_

       _*TO*_

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

 

_*BISMILLAHI-RAHAMANI-RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿71*

 

 

 

 

Cikin dauri Hajiya Kattime  tsuguna gaban gawar Moddibo tayi masa addu'a sosai gami da nema masa  afuwa gurin Allah,A fili tace"Yusuf ni mahaifiyar ka na yafe maka dukkanin abunda kayi min wanda na sani da Wanda ban sani ba,ina fatan Allah ya had'amu a aljanar firdausi"

"Ameen" Ameen"Abunda mutane ke cewa kenan.me Martaba ya aika ai kiran Waziri tun d'azu yak'i zuwa, haka me Martaba ya bada Umarnin d'aukar Moddibo a kai shi gidansa na gaskiya, Sarki!ne ya d'ora makarar gefen kafad'arsa Galadima a gefe sauran mutane suka taya su rikewa a ka futa da Moddibo futa ta har abada, sai bayan futa dashi ne zuciyar Hajiya Kattime ta karye sai ga hawaye na biyo kuncinta,nan jama'ar dake gurin suka dunga tausar zuciyarta,da k'yar dai suka koma Shashen Mama Fulani, inda take zaune gefen Balaraba wacce take ta rusa kuka kamar ranta zai futa, magana take so tayi amma takasa saboda yanda muryarta take sark'ewa, tsabar kukan da take.

Hajiya Kattime ce ta shigo d'akin saboda jikinta na bata wannan yarinyar da Sarki!ya shigo da ita, itace Balaraba.

 

 

Kallonta Mama Fulani take har ta k'araso ta zauna gefen gado, tace" Ina kyautata zaton wannan itace yarinyar da ake rigima a kanta ko"?

 

Mama Fulani tace"Itace kin ganta nan kuka take tak'i jin rarrashi"

 

Cikin dauriya  Hajiya Kattime ta matsa kusa da Balaraba ta rik'e mata hannuwa cikin tausayi da taushin harshe tace"Dole kiyi kukan rashin Moddibo, kiyi hakuri ki barwa Allah ikon shi, nice na haifi Moddibo ina ganin babu wanda zai kai ni jin zafin mutuwarsa, irin wannan ta farar d'aya, to da yake nasan kowa na hakane na hak'ura na barwa Allah mutuwa rigar kowa ce dole inda ya tafi zaki tafi zan tafi haka Mama Fulani zata tafi, saboda haka ina rokon ki ki yi shiru don Allah in ci Albarkacin Moddibo bana son ki jawowa kanki wata lalurar yanzu ke din kece zan dunga kallo a matsayin Yusuf d'ana, kiyi hakuri kiyi masa addu'a domin  ita yake bukata a gurin mu"

 

Cikin kuka Balaraba tace"Mama me yasa Yusuf zai yi min haka? bani da kowa sai shi,Yusuf shine gatana Allah ne gatana,gashi ya tafi ya barni lokaci guda,

*Innalilahi wa'inna ilahi rajiun* Ya Allah ka kawo min a gaji"

Ta k'arashe maganar tana jin tamkar numfashinta zai d'auke.

 

Wasu hawaye Mama Fulani ta goge na tausayin Balaraba sosai yarinyar ta bata tausayi.

 

 

Hajiya Kattime tace"Kar kiyi sab'o kinji ko, lokacinsa ne yayi dole ya amsa kiran da a kai masa"

 

Mama Fulani tace"Ki daina kukan rashin iyaye kinji ko mu zamu zame miki uwa da uba Insha Allah ba zaki maraici ba"

 

 

Cikin kuka da damuwa Balaraba tace"Nagode sosai kamar yadda kika fad'a Mama  nima zan muku biyyaya dai-dai gwargwado tamkar Ku ne kuka haife ni"

 

 

Hajiya Kattime tace"Yanzu ina "yan uwan naki"?

 

Sai sannan ta tuna dasu Sadiya,k'okarin saukowa take daga gadon cikin faduwar gaba, tabarsu su kad'ai bata san wane hali suke ciki ba.

 

Hajiya Kattime ta rik'eta tace" Bari aje a d'auko su,kinji ko kar ki futa cikin wannan halin"

 

Muryar ta na karkarwa tace"Suna can Shashen Sarki!nan muka kwana"

 

"Shikkenan bari in tura Mariya taje ta dauko su ki kwantar da hankalin ki"

Hajiya Kattime ta mike ta futa.

 

 

Mama Kuwa  k'ara kwantar wa da Balaraba hankali take,tana d'an yi mata tambayoyi cikin hikima,irin tasu ta manya,nan ta fuskanci yaran sun sha wahalar rayuwa kuma sun taso cikin maraici, lokaci guda taji sun shiga zuciyarta zata iyayin komai a Kansu.

 

 

 

 

Har akaje a ka dawo Waziri bai futo ba,yana shashen sa yana sak'e-sak'e mugun abu a zuciyarsa.

 

 

 

Cikin "yan Uwan Moddibo kuwa babu wanda ya futo aka zauna dashi sai Ishak duk shauran basu fito ba, suna can suna goyan bayan mahaifinsu,Wanda har aka share makoki babu shi babu dalilinsa.

 

 

Yau kwana takwas kenan da rasuwar Moddibo me Martaba yayi shirin zaman Fada, Hajiya Kulu me d'akin kudu tana kusa dashi, da yake yana shashenta, k'orafi kawai take masa na shashanci, duk wannan abunda take masa bashi ne a gabansa yana mamakin da har aka share makoki bata tab'a bud'ar baki tayi masa ta'aziyyar rasuwar Moddibo ba. Gyaran murya yayi yace" Duk wannan k'orafin naki bai karb'u ba a gurina saboda ke babbar me laifi ce,kinayi kamar baki San abunda yake faruwa ba a gidan, ke indai ba Matsalar "yayan ki bace babu matsalar da ta dame Ki, kina a matsayin matata Uwar " yayana na farko, kin tsaya kina rashin hankali, ya kamata ace kin nutsu kin San abunda kikeyi a rayuwar ki,saboda haka kar ki k'ara kawo min maganar Na'ja'atu nan saboda ban ga dalilin da zai sa kice dole in d'ebi kud'i masu nauyi har million uku in bata da sunan zata ja jari, Wanda nasan k'arya take, babu wani jari da zata ja zuwa zatayi ta b'arnatar dasu, ke da ita kuje ku sanja tuni"

Ya k'arasa maganar yana k'okarin mik'ewa da niyar futa.

Mik'ewa tayi itama da sauri tace"Allah ya ja zamanin Sarki, a duba maganar nan tawa, tunda kayiwa Na'ajatu aure bata tab'a zuwa tazo ta nemi alfarma a gurin ka ba sai wannan lokacin,kullum kana nuna min "yayana kamar ba kaine ka haifesu ba"

 

Wannan magana da Hajiya Kulu ta fad'a ta d'agawa me Martaba hankali,sosai tsayawa yayi yana kallonta da ransa a b'ace yace"Kar ki k'ara yi min magana makamanciyar wannan, duk sanda kika k'ara ranki sai ya b'aci, sosai daka ke har "yayan naki da kike ganin kamar bani ne na haife su ba"

Sunkuyar da kai tayi ranta yana suya sosai tace"Allah ya huci zuciyarka" Shiru yayi mata na minti biyu ya cigaba da cewa"Duk cikin "yayan naki wacece tazo tai min gaisuwar Moddibo, ko da yake ai ban isa ba,tunda bani da Iko dake dasu,sai abunda kika tsara musu shi zasuyi ai kun kyauta"

 

Cikin sauri tace"Allah ya gafarta maka, duk babu wanda be zo ba a cikinsu,duk sunje sun yiwa Waziri gaisuwa,ko wacce ta tafi gidanta gudun fad'an ka"

 

"Saboda haka kika tsara musu cewar Waziri ne Uban Yusuf bani bane shiyasa bani da matsayin da zasu zo su gaishe ni balle suyi min gaisuwa, sun kyauta"

Ya karashe  maganar cikin b'acin rai!

 

"Allah ya huci zuciyar ka"

Tafad'a muryarta na rawa ganin kwab'arta tana so tayi ruwa.

 

Har ya wuce zai tafi yaja ya tsaya yana kallonta yace"Nasan duk akan wa kike wannan abun wanda har kike nema ki sheganta min "yayana, duk cikin " yayan da na haifa  babu wanda na ware nace shi nafi so kowa ina sonshi tunda nine na haife shi, Almansur Sarki!shine d'ana namiji guda shine kuma magaji na   insha Allahu,saboda haka in zaki kwantar da hankalin ki ki kwantar da hankalin ki"

Yana gama fad'ar maganar shi ya futa a nutse.

 

 

Hajiya Kulu zaman durshen tayi kan kilishin dake malale tsakiyar d'akin wasu zafafen hawaye yana zubo mata, wai me yasa bata haifi d'a namiji bane?wai me yasa duk "yayanta suka zamo " yaya mata,? Ita kad'ai take tambayar zuciyarta, yanzu ta tabbata kenan Mama Fulani tayi nasara a kanta,tunda har ta haifi d'a namiji kuma takasa nasara akansa da ita kanta Mama Fulani, wata wawar ajiyar zuciya ta sauke ta mik'e zumbur!tana surutai falonta ta futa inda Hadiman ta ke zaune,suna jiran futowar ta, daga bakin Kofa ta tsaya ta kira Jakadiyarta me suna Ladi, suka shiga d'aki tare, wani irin zama tayi kan wani tuntu tace"Ladi duk wani shiru da k'uli da mukayi shekara da shekaru ina ganin duk sun karye,dole ne yanzu mu sake sabon lale,me zafi!domin inaji ina gani zamu zama "yan kallo a gidan nan dani da " yayana"

 

 

 

 

 

*Muje zuwa*

 

 

 

 

*Comment Vote and Share*

[13/08, 19:27] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

________________________

_*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_

________________________

 

 

 

 

 

_*DIDEGATED*_

       _*TO*_

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

_Alhamdulilahi, Ina taya d'aukacin alummar musulmi murna za gayowar wannan wata me albarka,ina fatan Allah ya nuna mana na shekarun gaba, ubangiji Allah ya shafe mana zunuban mu_

 

 

 

 

 

 

 

_____________________________

 

*đŸ™†đŸ»♂đŸ™†đŸ»BANI BANEđŸ™†đŸ»♂đŸ™†đŸ»*

            _(Zargina ake_)

 

~BY: MAMA QUEEN~

 

*đŸ’«DA BAZAR MU WRITER'S ASSOCIATION*đŸ’«

 

 

*NOTE*

Wannan book yana kunshe da abubuwa kala-kala kama daga cin amana,sark'akiya,rikitarwa dad'i sauransu.....

 

 

          _Wannan yana da banbamci domin kuwa killatacce ne duk Wanda ke buk'ata se ya biyoni ta number kamar haka_

 

Whatsap numbar

07061553385

*Karku bari abaku labari*

_________________________

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿72*

 

 

 

Jakadiya Ladi ta gyara zama sosai gaban uwar gijiyarta cikin sigar munafurci da iya kitifi tace"Allah ya taimaki uwar d'akina,dama abunda nake taso ki gane kin kasa fahimta,ai tuntuni ni na riga nasan abunda kikayi ya daina tasiri kan me Martaba,amma yanzu ga shawara"

 

Gyara zama Kulu tayi tace"Ina sauraranki tabbas nasan shawarar ki me kyau ce"

 

K'asa-k'asa Ladi tace"Me zai hana yanzu mu dawo kan shi d'an nasa wanda ya k'wallafawa rai,tunda dai,asiri baya cin mahaifiyat tasa kuma baya cin me Martaba, ina ganin haka shine abunda ya dace muyi"

 

Kulu ta sauke ajiyar zuciya tace "Wannan shawarar taki itace abunyi, ni in san samu ne ma dukaninsu inga basa motsi a duniyar nan,saboda basu da wani amfani"

 

Jakadiya Ladi tayi wani munafukin murmushi tace"Wannan aiki naki da kika d'auko me girma ne uwar d'akina,amma duk bazai gagara ba, a kwai wani d'an bori dake can lakwaja,shi zanje in d'auko zai yi miki aiki sosai,amma gaskiya dole za'a bawa aljanunsa me k'afa biyu sannan aiki zai ci"

 

 

Cikin gadara Kulu tace"Ko me k'afa hud'u suke so za'a nemo abashi indai bukata zata biya"

 

 

 

Ladi tace"Allah ya taimake ki kin san me ake nufi da me k'afa biyu kuwa"

 

Girgiza kai Kulu tayi cikin izgili!

 

Jakadija Ladi tace"Me k'afa biyu yana nufin mutum kamar ni da ke"

 

Babu wata fargaba Kulu tace"Ai shine nace miki ko k'afa hud'u suka nema ni zan basu domin buk'ata ta biya"

 

Ladi tace"Allah ya taimake ki nasan zaki iya ai,gobe idan Allah ya kaimu zan tafi in zo miki dashi, saboda haka sai a ta nadar masa masauki"

 

Kulu tace"Babu damuwa duk wannan tunda a kwai d'akuna nan b'angaran yanzu babban k'alubalen shine yadda za'ayi ya shigo gidan"

 

 

"Ranki ya dad'e zan bashi tufafi irin na hadimai na gidan nan sai ya sanya kawai in ya shigo su saje"

 

 

"Yawwa wannan shawarar taki tayi"

Kulu tafad'a tana gyara zamanta.

Nan suka zauna suna kullu yadda abun zai kasance .

 

 

****

Lokacin da me Martaba ya shiga fada ta cika sosai abun mamaki Sarki! Ya gani zaune gefen Galadima yaji dad'i sosai d'aya gefen ya kalla yana laluben Waziri babu shi babu Alamarsa.

[14/08, 14:56] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

________________________

_*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_

________________________

 

 

 

 

 

_*DIDEGATED*_

       _*TO*_

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*đŸ™†đŸ»♂đŸ™†đŸ»BANI BANEđŸ™†đŸ»♂đŸ™†đŸ»*

            _(Zargina ake_)

 

~BY: MAMA QUEEN~

 

*đŸ’«DA BAZAR MU WRITER'S ASSOCIATION*đŸ’«

 

 

*NOTE*

Wannan book yana kunshe da abubuwa kala-kala kama daga cin amana,sark'akiya,rikitarwa dad'i sauransu.....

 

 

          _Wannan yana da banbamci domin kuwa killatacce ne duk Wanda ke buk'ata se ya biyoni ta number kamar haka_

 

Whatsap numbar

07061553385

*Karku bari abaku labari*

 

 

 

 

_*BISIMILHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿73*

 

Zama yayi kan kujerarsa,  suka fara gaisawa da jama'ar dake zaune a fadar,bayan angama gaishe-gaishen ne, me Martaba ya umarci jakada ya je ya kira Waziri,cikin sauri ya tafi, wajan minti goma sai gashi ya dawo,ya zube gaban me Martaba kansa a sunkuye yana jin nauyin fad'a masa abunda Waziri yace"Sai da ya nisa tukkuna yace"Allah ya taimake ka yace"Ace maka bazai zo ba"

 

Shiru na minti goma me Martaba be ce komai ba, kawai a kafara gudanar da al'amuran da suka dace, kwata-kwata Sarki! baya jin dad'in zaman fadar saboda b'acin rai da damuwa da yake ciki,gashi ya fuskanci mahaifin nasa ma yana cikin damuwa ko ga yanayin fuskarsa  ma,ta nuna alamu, haka dai ya d'aure

har lokacin sallah azuhar yayi kowa ya mik'e domin yin sallah, tare suka fito daga massalaci da me Martaba, kai tsaye Shashen Mama Fulani suka nufa, suna tattauna,wasu muhimin abu da ya shafesu.

 

Mama Fulani na zaune a farlo ita da Jakadiya Shafa'atu, Sarkin k'ofa ne ya shigo ya sanar mata da shigowar me Martaba, kafin kace kwabo bayin dake gurin kowa yayi nasa guri,har Jakadiya Shafa'atu.

 

 

A nutse suka shigo Mama Fulani ta gyara masa gurin zama tanai masa barka da shigowa zama yayi sosai da murmushi a fuskarsa suka gaisa,duk b'acin ran da yake ciki idan yazo gareta sai yaji wata sa'ida a ransa.

 

Sarki!ya gaida mahaifiyar tasa a nutse, tace"Kai kuma sai yau ka shigo ko, kazo ka aje amanar taka baka zuwa dubata haka ake rik'e amana"

 

Sosa kai yayi irin na sabo yace"Afuwa Mama ni kaina bana cikin nutsuwa bani da lafiya"

 

Me Martaba yace"Dole ne kayi Magajin Sarki wannan rayuwar bata da tabbas babu komai a cikinta sai rud'u da tashin hankali"

Sarki!ya sauke ajiyar zuciya yace"Allah ka jik'an Moddibo"

 

Tare suka amsa da "Ameen"

 

Mik'ewa yayi yaje ya kwanta kan wata katuwar Sofa, ya lumshe idonsa wani irin bacci  yake ji.

 

Me Martaba yace"Yarinyar nan ai tana gurinki ko"

 

Mama Fulani tace"Tana cikin d'aki ita da "yan uwanta,gaskiya ina tausayawa rayuwarsu wallahi"

 

"Dole ai abun tausayi ne, shi yasa na yanke shawarar d'aura mata aure da Magajin Sarki tunda ta rasa miji me nagarta kamar Yusuf ina ganin shi Almustafa zai iya rik'eta amana"

 

Murmushi Mama tayi cikin k'arfin hali tace"Wannan hukuncin naka yayi Allah ya tabbatar da alkairi, amma ina hasashen rigimar da zataje ta dawo kasan dai rigimar k'anwarku Madabo ko"?

 

Me Martaba yayi gyaran murya a nutse yace"Barta wannan duk rigimar ta a bayan fage take kuma batayi a gabana sai bayan idona,na riga na yanke hukunci Almustafa zai Auri matar Yusuf Balaraba kenan zai kuma auri Halisa d'iyar k'anwata Madabo"

 

Duk irin maganganun da suke wakana tsakanin iyayen nasa yana ji yayi lamfu, shi kad'ai yasan abunda yake sak'awa a zuciyarsa

Bud'e ido yayi kad'an yana kallon iyayen nasa ya mik'e zaune, a nutse yace"Allah ya taimake ka maganar Azima fa"

 

 

Shiru Martaba yayi daga bisani yace"Maganar Azima tananan itama za'ayi tunda an yiwa mahaifinta Alk'awari kar ka damu, Zamu aika masa da wasik'a cewar ranar juma'a me zuwa za'a d'aura auran sai su shigo da shirinsu insha Allahu zaka had'a mata uku rana d'aya ina maka addu'a da fatan alkairi,insha Allahu zaka samu nasara a rayuwarka"

 

Godiya Sarki yayi yana girmama al'amarin mahaifin nasa,shi da kansa yake addu'ar Allah ya bashi ikon yin adalci tsakanin matansa,

 

Me martaba yace"Kaje ka kiramin ita yarinyar,ina so mu zauna da ita gaka gata gani ga mahaifiyar ka, domin in fad'a mata irin hukuncin da na yanke a kanku, bazan yi mata dole ba, a rayuwarta"

 

Mik'ewa yayi a nutse Mama tace"Tana cikin uwar d'aki takasa sakewa har yanzu"

 

Kai tsaye d'akin ya nufa, yana taka k'asa kamar me tausayinta.

[15/08, 05:41] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

________________________

_*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_

________________________

 

 

 

 

 

_*DIDEGATED*_

       _*TO*_

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*đŸ™†đŸ»♂đŸ™†đŸ»BANI BANEđŸ™†đŸ»♂đŸ™†đŸ»*

            _(Zargina ake_)

 

~BY: MAMA QUEEN~

 

*đŸ’«DA BAZAR MU WRITER'S ASSOCIATION*đŸ’«

 

 

*NOTE*

Wannan book yana kunshe da abubuwa kala-kala kama daga cin amana,sark'akiya,rikitarwa dad'i sauransu.....

 

 

          _Wannan yana da banbamci domin kuwa killatacce ne duk Wanda ke buk'ata se ya biyoni ta number kamar haka_

 

Whatsap numbar

07061553385

*Karku bari abaku labari*

 

 

 

 

_*BISIMILHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_

 

 

 

 

 

_*INA MIK'O GAISUWA TA GAMI DA FATAN ALKAIRI GARE KA*_

 

*_Adimin Haruna H Umar_*

*_Beneficial writers fan's_*

 

```INA MAKA ADDU'A DA ALLAH YA BAKA MACE TA GARIđŸ„°```

 

 

 

 

*🅿74*

 

 

 

 

A nutse ya bud'e k'ofar ya shiga bakinsa d'auke da sallama.

Wata irin fad'uwar gaba taji lokacin data tsinkayi muryarshi tana daga cikin toilet tana d'auro alwala, lokaci guda taji duk jikinta yayi sanyi wasu hawaye masu zafi suka fara zubuwa a idonta, cikin zuciyarta tace"Shikkenan yanzu zai zo ya dawo min da damuwa ta baya,wayyo Allan Moddibo, hawaye ne ya ke kwarara sosai a idonta mutuwar Moddibo ta dawo mata sabuwa dal!tunda taji muryar d'an uwansa Sarki!sai take ganin kamar zata ga Moddibo.

Jikin bangon band'akin ta jin gina tana share hawaye sai k'okarin dai-dai ta kanta take, amma ina dole fuskarta ta nuna alamun anyi kuka.

 

 

Murmushin k'asaita

ya saki lokacin da suka had'a ido da Sadiya dake zaune kan gado,tana wasa da wasu awarwaron Balaraba da ta cire ta aje kan drowar duk wani kwalliye-kwalliye ta daina sai kace me takaba kullum da hijab a jikinta da carbi,kai hatta da d'an kunne ta cire ta aje,gani take itama rayuwarta tazo k'arshe babu Yusuf Moddibo rayuwarta ba zatayi dad'i ba.

 

 

 

Da gudu Sadiya taje ta rungume shi tana dariya tace"Magajin Sarki!yau kwanana bakwai ban gan ka ba,wai ina ka shiga ne?ina Yusuf kullum yayarmu sai tayi kuka idan na tambayeta sai tace babu komai"

Lokaci guda duk tayi masa wannan tambayoyin.

 

Hannunta ya kama suka zauna cikin wata kujera ya d'ora Usuman a cinyarsa, yana shafa kan yaron  cikin tausayi,yace"Na fuskanci Halimatu kina da surutu da yawa, Ok kina son in sanya ki a makaranta ko"?

 

 

Cike da farin ciki ta d'aga kai, murmushi yayi kawai yana girgiza kai,yace"Kar ki damu insha'Allah a satin nan zaku fara zuwa school ke da d'an uwanki"

Tsalle ta buga na murna cike da farin ciki tace "Mun gode Magajin Sarki,Allah yasa kazama Sarkin mu"

Murmushi yake sosai yace"Ameen,in dai na zama Sarki kece Gimbiya ta" tsalle Sadiya take tana murna cike da k'uruciya Usuman sai taya ta yake,

 

Wata tsawa taji wacce tasa tayi saurin shiga taitayin ta d'akin yayi shiru, Balaraba ce ta futo daga toilet taga shashancin da Sadiya take ranta ya b'aci sosai, ta lura shi kuma sai biye mata yake,tana jinta ko gaida shi batayi ba saboda rashin hankali.

Fad'a sosai takewa yarinyar  kamar zata kai mata duka Sadiya har ta soma hawaye, ganin hawayen ne yasa ransa ya b'aci ina dalili ita ba'a hakura mata ba,ita zata takurawa wata.

Cikin wani irin voice me kashe jiki yace" Ya isa Malama"

 

Kallonsa tayi ta gefen ido tayi saurin kauda kanta, kasa-k'asa tace da Sadiyar taje ta gaida shi,

Simi-simi Sadiya taje ta tsuguna tana gaishe shi,ya amsa sama-sama suk hankalinsa na kan Balaraba dake k'okarin ta da sallah,

Rarrashin Sadiya yake har Balaraba ta idar da sallahr ta d'an waigo kad'an bata yarda sun had'a ido ba tace"Ina wuni"

 

Shiru yayi kawai yana rikitata da mayun idanunwansa masu sa kasala.

 

Jin bai amsa ba, ta kara maimaita gaisuwar.

 

Gyaran murya yayi a nutse yace"Lafiya, nake, yayi shiru na minti biyu kana ya cigaba da cewa"Me Martaba na neman ki yanzu"

Cikin fad'uwar gaba ta mik'e tsaye da sauri har tana k'okarin faduwa ta dalilin dogon hijab din dake jikinta

 

Bakinta na rawa tace"Allah yasa ba wani laifin nayi ba"

 

Shiru yayi mata yana binta da kallo ganin jikinta na tawa.

 

Had'e fuska yayi yace"Ji mana, kinga ki nutsu ba wani abun bane,naga kina ta wani rawar jiki, yawwa bayan nan kuma, Wad'an nan yaran da suke gaban ki ki bar ganin k'annan ki ne, to in kika cucesu sai Allah ya saka musu, na fad'a miki"

Yana gama maganar sa ya mik'e ya futa a nutse, bai tsaya kallonta ba balle ya saurari abunda zata ce,ita kuwa binsa tayi da kallo har ya fuce tana mamakin yanda yake mata magana cikin isa!da gadara, lallai ruwa ya daki babban zakara,

[16/08, 14:28] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

________________________

_*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_

________________________

 

 

 

 

 

_*DIDEGATED*_

       _*TO*_

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*đŸ™†đŸ»♂đŸ™†đŸ»BANI BANEđŸ™†đŸ»♂đŸ™†đŸ»*

            _(Zargina ake_)

 

~BY: MAMA QUEEN~

 

*đŸ’«DA BAZAR MU WRITER'S ASSOCIATION*đŸ’«

 

 

*NOTE*

Wannan book yana kunshe da abubuwa kala-kala kama daga cin amana,sark'akiya,rikitarwa dad'i sauransu.....

 

 

          _Wannan yana da banbamci domin kuwa killatacce ne duk Wanda ke buk'ata se ya biyoni ta number kamar haka_

 

Whatsap numbar

07061553385

*Karku bari abaku labari*

 

 

 

 

_*BISIMILHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿75*

 

 

 

Cikin nutsuwa, tabi bayansa, Yana gaba tana baya zuciyarta sai wani d'ar-d'ar take, me Martaba yana bala'in yi mata kwarjini don haka suna had'a idoshi ta sunkuyar da kanta a k'asa,gami da zubewa k'asan k'afafun Mama Fulani tana gaishe shi.

Cikin sakin fuska ya amsa yace"Sannu kinji ya k'okari,ya mukaji da rashin Moddibo kuma"?

Cikin rawar murya tace"Alhamdulilahi"

 

"Allah ya jik'an Yusuf"

Me Martaba ya fad'a,da amin suka amsa.

Sannan yayi shiru na minti biyu kana ya cigaba da cewa"Wato abunda yasa na kira ki, nan gurin shine, ina neman alfarma guda a gurin ki ina fatan zaki bani wannan alfarmar"

 

A nutse tace"Ai babu abunda zaku nema a gurina in kasa yi muku shi,Allah ya taimake ka"

 

Me martaba yaji dad'in lafazinta yace"Alhamdulilahi,Allah yayi miki albarka, ina son zan maye miki guribin Yusuf da Almustafa Sarki!kenan, ma'ana zan d'aura muku aure insha Allah rana ita yau, ina fatan ban shiga hakkin ki ba, ko idan ba kya sonsa ki fad'a kar ki rufe min,tamkar "yar cikina kike,domin bazan yi miki dole ba"

 

Cikin fad'uwar gaba, tace"Duk rin hukuncin da ka yanke a kaina, bani da ja akai domin ka isa dani,saboda haka na amince da zab'in ka"

 

Albarka me Martaba ya sa mata sosai sannan ya bata umarnin tafiya.

 

Balaraba ta mik'e a nutse ta bar gurin kai tsaye d'akin da ta futo ta koma.

Tana shiga ta zube kan daddumar da tayi sallah ta fara wani sabon kuka,tana tausayawa kanta,sam takasa cire Moddibo daga zuciyarta, yaya zatayi ta had'a soyyayarsa da ta kowa sam bata jin soyyayar Almustafa cikin zuciyarta,tana ganin bata da babban masoyi. Kamar Moddibo, kuka take sosai,da sosai.

 

Ganin kukan da yayar tasu take ne yak'i k'arewa yasa Sadiya ta kama hannun Usuman suka futa suna kuka suma.

 

 

Babu kowa a falo sai Sarki!dake kwance kan Sofa, yak'i komawa fada, saboda yana buk'atar hutu, sosai kwana biyu sam baya samun ishashan bacci,Moddibo na yawan fad'o masa a rai, mussaman idan ya tuna lokacin da ya had'a hannusa dana Balaraba yana fad'in, d'an uwana ga amana ta nan,wannan magana da Moddibo yayi masa tana tsaye a cikin ransa,

 

Hangosu yayi sun futo suna share hawaye ya mik'e da sauri yana ware lumsassun idonsa, Sadiya ta k'araso kusa dashi  cikin rawar murya tace"Magajin Sarki! ga yayarmu can tana kuka, kuma tak'i taci abunci tun safe take kuka, mu kam munci abunci mun k'oshi abunmu"

 

Jin da yayi Sadiya tace"Tana kuka sai yayi tunanin maganar da me Martaba ya fad'a matane ta sanya ta kuka, wato tanaso ta nuna masa cewar bata sonsa,amma takasa fad'a gaban me Martaba, ranshi yaji ya b'aci kad'an, cikin zuciyarsa yace "Babu ruwuna da ko tana so ko bata so,insha Allah sai na cikawa d'an uwana burinshi.

Mik'ewa yayi ya rik'e hannunwan su suka nufi d'akin da take ciki, tabbas bazai lamunci zama da yunwa ba

Tana kwance kan daddumar har yanzu kuka take ya k'ofar d'akin ya shiga,da sallama ciki-ciki, sam batasan da shigowarsa ba, yazo ya tsaya kanta,yana k'are mata kallo, inuwar mutum dogo ta gani akanta, tayi sauri d'ago da fuskarta wacce taji jage-jage da hawaye, had'a ido sukayi, yana mata wani kallon kurulla.

Da sauri ta mike zaune tana goge fuskarta da k'asan hijab dinta,hararasa take k'asa-k'asa ta takure jikinta cikin hijab tana sauke ajiyar zuciya.

 

Yafi minti biyar a tsaye a kanta yana nazarinta, gyaran Murya yayi ya kira sunanta cikin yanayin muryar shi, sunkuyar da kai tayi bata amsa ba.

Tsugunawa yayi kusa da ita ya d'ora gwiwarsa k'asa yana k'okarin d'ago fuskarta,da tafukan hannayensa,a zabure ta matsa gefe tana watsa masa harara,k'asa-k'asa, fuskarsa ya had'e sosai yace"Kukan me kike yi"?

 

Shiru tayi masa gabanta na faduwa saboda kusancinsu da shi yayi tsanini Wanda har hucin futar nuffashinsa tanaji ga k'amshin turaransa duk ya baibayeta.

 

Kaurara murya yayi yace"Wannan shine magana take da ta karshe mutuk'ar zan dunga yi miki magana kina raina min hankali, kinajin abunda nake cewa kinyi shiru ko"?

 

D'ago kanta tayi tana kallansa,cikin dauriya tace"Me ya dame ka da kukana"?

 

"Saboda ke amana ta ce"

Cikin mamaki ta kalleshi jin abunda ya fad'a.

 

"Anyway,nasan abunda yasa kike kuka saboda ance dake ki aure ni ne,shine dalili, ko"?

Yafad'a cikin sigar tambaya.

 

Shiru tayi tana takure jikinta,so take ya tashi daga kusa da ita duk a takure take.

 

Wani murmushi yayi yana d'an girgiza kansa cikin damuwa  abubuwan da suka da meshi yace" Tabbas kinyi rashin masoyi, mu kuma munyi rashin d'an uwa managarci hak'ika Moddibo ya taka muhimiyar rawa a rayuwar ki, tabbas duk abunda ya tafi ya bari a doran duniyar nan dole in d'ora daga inda ya tsaya, ko da me Martaba be yanke wannan hukuncin ba, ni ina da wannan kudirin na auranki araina saboda wasiyar da d'an uwana ya tafi da ita" Nuffashi ya sauke yayi shiru,gami da tsura mata ido, kana ya cigaba da cewa, mutuk'ar kikaga ba'ayi wannan auran ba,to sai dai in ke kika bujere,wa buk'atar mu,saboda haka, inason ki kwantar da hankalin ki a kaina ni ba,bak'on zafi bane duk irin zaman da kike so muyi ni dake haka zamuyi"

 

Tsitt!! D'akin yayi bakajin komai sai k'arar AC da sautin nuffashinsu, da k'yar ta d'ago kanta tana kallonsa,bata tab'a tsammanin ya iya kyawawan lafazai irin wannan, wani irin kwarjini yayi mata,wanda yasa tayi saurin kauda da kanta daga kansa, muryarta na rawa tace" Ka matsa daga kusa dani"

 

Girgiza kai yayi kawai yana sakin murmushi,yace"Sadiya tace"tun safe baki ci abunci ba,hakane"?

 

D'akin take bi da kallo tana neman su Sadiya,basa nan, gabanta ya fad'i ta zaci suna d'akin a tunaninta ko Sarki!yayi niyyar yi mata wani abu ganinsu zai sa ya fasa.

[17/08, 15:30] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

________________________

_*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_

________________________

 

 

 

 

 

_*DIDEGATED*_

       _*TO*_

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

 

_*BISMILLAHI-RAHAMANI-RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿76*

 

 

 

 

 

Ganin yadda take rarraba ido  yasa ya mik'e tsaye cikin nutsuwa yace"Ki futo falo kici abunci,ki sake da mutane, sannan ki cigaba da walwalarki,wannan zaman da kike cikin d'aki ke kad'ai duk bashi ne mafuta ba,a gareki, ita rayuwa ta duniyanan bata tabbata, ki sanya tawakkali a cikin zuciyarki, kisa a zuciyar ki cewa inda Moddibo ya tafi kema zaki tafi,domin can d'in shine tabbas,a garemu"

Yana gama maganar sa ya futa daga d'akin,a nutse.

 

Balaraba tayi mamakinsa mutuk'a sam bata tab'a tunanin mutum ne shi mai sauk'in kai haka ba,ga Ilimi da ikilashi,ta lura mutuwar Moddibo batasa ya furgice ba,duk da shak'uwarsu amma yana cikin nutsuwarshi, haka ake son mutum me tawakkali.

 

 

Wannan Nasiha da Sarki!yayi mata ta k'arfafa mata jiki sosai tanaji a zuciyarta cewa itama hakane idon lokacinta yayi dole tatafi babu tsumi babu dabara.

 

Allah kasa mu dace.

 

A nutse ta furo falo, taga su Sadiya na zaune kan wata k'atuwar dadduma suna cin "yayan itatuwa shi kuma yana kwance kan Sofa kamar d'azu idansa a lumshe,da alama bacci yake ji,

 

Babu kuzari a jikinta ta nufi wani keb'antaccan guri wanda aka tana da domin cin abunci ta zauna a nutse ta had'a dai-dai cikinta tayi bissimilah ta fara ci, duk abunda take yana kallonta ta k'asan idonsa dake mutum ne shi mai yalwar gashin ido shiyasa in ya lumshe idonsa sai kayi tunanin a rufe yake.

 

Mama ce ta futo daga wani d'aki cikin shiri tana sanye da wata lafiyyar lifaya wacce tayi mata kyau sosai, had'a ido sukayi da Balaraba tayi saurin yin k'asa da kanta, Mama Fulani tayi murmushi kunyar yarinyar tana burgeta sosai,tace" Yawwa ko kefa ai gwara da kika fito amma kin zauna cikin d'aki babu ci babu sha"

Sunkuyar da kai tayi cikin jin nauyi.

Ta kalli su Sadiya sun sake suna wasa,Usuman ta kira tace"Zo muje ka rakani wani guri"

Da sauri yaron ya tafi gurinta.Mama ta kalli Balaraba tace"Zamu shiga shashen Hajiya Kattime yanzu"

"To Mama a futo lafiya"

Balaraba tafad'a cikin girmamawa.

 

Har ta nufi k'ofa sai ta dakata ta juyo tana kallon Balaraba tace "Ki kula da Almustafa,in ya tashi daga baccin ki bashi abunci, na lura kwana biyu yana wasa da cikinsa,duk ya rame"

 

Balaraba tace"Insha Allahu Zanyi Mama,Agaida Hajiya.

 

"Zataji insha Allahu"

Mama tafad'a lokacin da take k'okarin futa.

 

Shiru yayi duk yana jin zantukan da sukeyi,har yanzu idonsa a lumshe yake yana kallonta duk abunda take, cin abinci take a nutse har ta kammala,ta goge bakinta, shiru tayi tana tunanin ta yaya za'ayi ta tasheshi daga bacci har ta bashi abunci, dole ne ta cika umarnin da aka bata.

 

 

Mik'ewa tayi ta nufi inda yake, ganin ta nufo gurinsa yasa ya rufe idon gaba d'aya ta k'araso tayi tsaye kansa tana kallon fuskarsa, tsigar jikinta taji tana tashi ganin wani zallah kyau da annuri da yake futa a fuskarsa, mai d'auke da zara-zaran gashin idon had'e da sanjensa Wanda ya kewaye d'an mitsitsin bakinsa, tsabar hutu da jin dad'i yasa tafarshi tayi wata irin kala, ita ba fara ba ita ba b'aka, hakika Allah yayi hallita a gurin, ko da take farar mace, tayi shawa'ar fatarshi ji take ina ma itace take da Irin fatar.

Hannusa ta kalla mai d'auke da zararan zaran yatsu ya d'ora kan cikinsa, tayi saurin kauda kanta tana tunanin ya zatayi ta tashe shi, cikin sa'a d'aya daga cikin wayoyinsa tafara k'ara, yanaji yayi shiru, kallon fuskar wayar tayi, Matata,sunan da tagani yana yawo kan screen ni d'in, katsewa tayi wani kiran ya k'ara shigowa wata zuciyar tace d'auki kiyi magana, kiji wacece,tunda dai ita iya saninta dashi tasan bashi da wata mata, sun kuya tayi zata d'auki wayar yayi saurin dafe wayar da hannusa, hannuwansu suka had'u guri guda. Yarrrrr!! Ya ji a jikinsa sai ya d'amke wayar a hannusa tare da hannuta,ya bud'e idonsa tarr! A kanta sukayi ido hud'u

Abunda yasa ya hanata d'aukar wayar shine gudun rigimar Halisa yasan itace saboda ringing din da yasa mata daban ne, yasan taji muryar mace, tashin hankali zasuyi

Zare hannuta take k'okarin yi ya rik'e ya had'a da nashi da wayar ya kara a kunne, cikin wani kasalalliyar murya yayi sallama.

Tana jiyo muryar Halisa tana fad'in Habibi ganinan shigowa Shashen Mama yanzu na futo shashanka Buba yace baka shigo ba tun da safe, da ka futa"

 

Kamar baya so yace "Sai kin shigo "

Kashe wayar yayi yana me kallon hannun Balaraba dake had'e da nashi, babu zato taji yace mene kika tsaya min aka, tun d'azu"

 

 

 

_*TSANTSAR BUTULCI*_

 

                  *_NA_*

_BINTA UMAR ABBALE_

*BINTUBATULA*👄

 

 

_Littifi mai dauke da darusa  gami da cin amana da  iri-iri, kar ku bari a Baku labari_

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

               ^^^^^^^^^^^^^^^^^^

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^

                          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

                    _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

 

_*MARUBUCIYAR*_

```Nana Khadija```

```Yaro Da kud'i```

```Gimbiya Balaraba```

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS*_

_*ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

________________________

_*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_

________________________

 

 

 

 

 

_*DIDEGATED*_

       _*TO*_

```RAHAMA ALIYU```

 

 

 

 

_*BISMILLAHI-RAHAMANI-RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿77*

 

 

 

 

Daburcewa tayi, tana k'okarin cire hannuta daga nasa, tace"Mama ce tace ka tashi kaci abunci yanzu"

 

Kallonta yake cikin nutsuwa yace"Mama batace ki tashe ni daga bacci ba, cewa tayi in dan na tashi ki bani,ai duk inajin abunda kuke fad'a"

 

Shiru tayi na minti biyu tace"Hakane, ko da yake dama hakkin ciyar da kai abunci ba akaina yake ba, ga matarka nan sai ta baka"

Tana gama fad'ar maganar takama hanya zata wuce,ya rik'e hannuta, yace"Ba ita aka umarta da ta bani abunci ba,ke a ka umarta da ki bani saboda haka,sai ki tsaya ki bani"

 

Cikin sanyi jiki tace"Wai me yasa kake son rik'e min hannu ne, nifa ba muharramar ka bace,abunda kake babu kyau,nasan ka sani kuma kana takewa"

Cikin d'an b'acin rai tayi masa maganar.

 

Hannunta ya saki,yana d'an sosa kansa irin na sabo, shi bada wata manufa yake tab'a jikinta,illa kawai irin sabon da Halisa tayi masa,n yawan kusantarsa,duk da yake itama baya wani zak'ewa iya kacinsa da ita ya rik'e mata hannu, ko kuma in zai mata magana ya d'an zungureta daga haka baya k'arawa,itace me zak'ewa da yawa yana tsawatar mata.

 

Ganin ya sakar mata hannu yasa ta wuce can inda kayan  abuncin suke ta fara had'a masa lafiyayyan towon shinkafa miyar taushe me d'auke da wadattacen nama,da man shanu, cikin wani had'addan plate ta had'a ta rufe da irinsa ta nufu in da yake zaune.

 

K'asa ya sauko ya jingina jikinsa jikin kujera, tazo ta aje masa ta koma ta d'auko lemo jus ta da ruwan roba nan ta aje kusa dashi, ta mik'e zata bar gurin,gyaran murya yayi a tsanake yace"Dawo ki zauna ki bani kamar yadda aka umarce ki"

 

Cikin Mamaki Balaraba ta juyo tana kallonsa, a dake tace"Ban gane abunda kake nufi ba"?

 

"Ai baki gama aikin ki ba, yafad'a yana kallon k'ofa jin kamar za'a shigo,kafin tayi wani tunani Halisa ta shigo da siririyar sallama taci uwar kwalliya tamkar wata sarauniya, turusss!! Tayi ganin Balaraba kan Habibinta, shi kuma yana kallonta, k'okarin dane abunda taji a zuciyarta tayi ta k'arasa kuda dashi, cikin wata irin tafiyar k'asaita

 

 

Balaraba kuwa saurin kauda kanta tayi, cikin zuciyarta tana wani irin jin haushin Halisa haka kawai.

 

Ta k'araso ta zauna kusa dashi har kafad'arsu tana gugar juna,cikin tsabar kwarkwasa ta gaishe ya amsa babu yabo babu fallasa, yace" Wannan kwaliyyar da kikayi ni kika yiwa ko kuwa"

 

Cikin jin dad'in yaba kwaliyyarta da yayi tace" Kai nayiwa gwarzon zuciyata me mulkin zuciyata"

 

Wani k'asaitaccan murmushi yayi yana kashe mata ido yace

"Nawa ne kud'inta in siya"

 

Fari da ido Halisa tayi tace" Bana buk'atar komai sai so da k'aunarka"

 

Ganin yanda suke hira ta soyyaya sun shareta yasa Balaraba barin gurin da rai a b'ace!

 

Kallo ya bita dashi har ta shige d'akin da take.

 

Ita kuwa Halisa bud'e a abunci tayi ta fara bashi abaki  sunayi suna hirar soyyaya ko da wasa bata yi masa zancan Balaraba ba saboda in gargad'in da yayi mata, kwanaki,a zuciyarta tace,kowa tasa ta fisheshi,ita k'okarinta taga ta mallake zuciyarsa ita kad'ai,don haka sai ta k'ara zage damtse tana ta shirya masa hira masu dad'i, sosai ya saki cikinsa yaci abuncin saboda dama neman me d'ebe masa kewa yake,bai samu ba.

 

 

 

********

 

 

To Sallau dai da k'yar ya koma gida tare da taimakon Mai gari da d'anshi Walidi,saboda tun a hanya ya jigata sai haki!yake tun lokacin da me Martaba ya fad'a masa cewar Balaraba zatayi aure a gidan shikkenan yaji zuciyarsa kamar ta dena aiki,sai haki!tsabar d'imuwa da tashin hankali sunyi masa katutu a k'ahon zuciya.

 

 

Duk suna zazzaune a tsakar gida suna jiran shigowar Sallau hankalinsu duk a tashe, kowa da abunda yake fad'a, akan Balaraba wai ita ta kai kararsa gurin Sarki!

 

 

A rirrik'e a ka shigo dashi Lantana ta tashi tana sallalami gami da salati dad'i take shikkenan,wannan "ya tasa anyi masa wannan bulala ta gidan sarki!Allah ya tsine miki Balaraba"

 

 

Ihu!Su Shamsiyya suke sukayi kan ubansu suka kakkamashi suka shiga d'aki dashi suna duba jikinsa sukaga babu wani k'warzane ko d'aya babu alamun duka a jikinsa.

 

 

Uwa!tace"Wai meye kake haka sai kace Wanda zai tada aljanu,tun safe munanan muna fargaba,gaka ka dawo kuma me makon kayi mana bayani kuma kazo kana wani nishi!sai kace kuturo"

 

Lantana tace"Ke rufe min baki shashasha kawai,bakya ganin halin da yake ciki,Allah yasa dai ba guba suka bashi yasha ko ya Ciba"

 

Walidi dake tsaye bakin k'ofa yasa dariya yana nuna Lantana da hannu yace"Babu wata guba da yaci,guba d'aya itace bak'ar zuciyarsa ya kusa had'iyewa saboda tsabar bakin ciki, Hahahahahaha"

Walidi ya shek'e da dariya babu abunda ya dame shi.

 

 

 

 

_*TSANTSAR BUTULCI*_

 

                  *_NA_*

_BINTA UMAR ABBALE_

*BINTUBATULA*👄

 

_littafin me cike da sark'akiya gami da cin amana, kar Ku bari a baku labarin_

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

             。。。。。。。。。。。。。。。

             _*GIMBIYA BALARABA*_ 

                đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

                   _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*BINTUBATULA👄*

 

 

_MARUBUCIAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

 

 

 

 

 

 

_*Zamani writers Association*_

________________________

*We are her to educate motivate and entertain aur Reades*

_________________________

 

 

 

*DIDEGATED*

          *to*

RAHAMA ALIYU

 

 

 

 

BISIMILLAHIR_RAHAMANIR RAHIM

 

 

*🅿78*

 

 

 

 

Wata k'atuwar harara Lantana ta makawa Walidi bakinta na kumfa tace" Walidi kayi asara wallahi ban san inda kaje ka samo wannan b'akar zuciyar taka ba, yanzu ubanka na halin rai da rayuwa shine kake masa dariya"

ta karashe maganar tata tana rik'e hab'a cikin mamaki!

 

Wata mahaukaciyar dariyar Walidi ya kara saki yace" Kaji Lantana da wani magana kuma, hahahahaha, ai bak'ar zuciyarki na gado, amma naji kina zancan ina na gado bakar zuciya, to ai kece kika gada mana ita, hahaha"

 

Ya k'arashe maganar da mahauaciyar dariyarsa, barin gurin yayi yana fad'in ni kam nayi nawa guri domin yau ina cikin farin ciki da annushwa sanadin Balaraba yau na "yantu na zama cikkaken mutum ehe duk d'an bak'in ciki sai dai ya mutu!

fucewarsa yayi ya barsu da baki a sake

 

Sallau kuwa tuni ya sharb'e a gurin bakinsa ya karkace miyau na dulala, da kyar ya d'aga hannusa guda yana kiran Lantana ta matsa kusa dashi tana salati, baki a mugud'e yace" Lantana muna cikin wani yanayi wannan yarinya da mukai wa rikon sakainar kashi, Allah ya rufa mata asiri tana gidan sarki za'a d'aura mata aure da d'an wazirin gar..... kafin y k'arasa maganarsa Lantana ta fahimci abunda yake nufi, wani uban ashar! ta kurma tamkar ba tsohuwa ba fad'i take, "Me nake shirin ji ni Lantana, Balaraba d'iyar Tanko itace zatayi aure gidan sarauta ni nawa jikokin na nan a zaune lallai da sake! tafad'a wata irin kumfa na futa daga bakinta tsabar tashin hankalin da take ciki sam yanzu rashin lafiyar Sallau din bata gabanba, tunanin ta ya koma gurin ganin yaya zatayi ta futo da Balaraba daga wannan gida ko ta halin k'aka ne.

 

 

Shamsiyya ce ta futo daga uwar dakinsu daga ita sai daurin kirji nonuwanta sun cika sun tun batsa sai kace wata matar gida goshinta sai kyalli yake. Lantana ta dube ta sama da kasa tace"Dube ki cikkakiyar mace wacce ta amsa sunanta na mace kina zaune a gida kina tsotsor tsamiyya waccan mutsiyciyar yarinyar ta shallake ki, ai ko ta halin k'aka sai kin zauna gidan sarauta kema"

Lantana ta karashe maganar kmar zautacciya

 

Shamsiyya tace"Wai hayaniyar me nake ji ne tun dazu ina bacci"

 

Nan Lantana ta kwashe duk abunda yake faruwa ta fada mata"

 

Wani irin k'yashi da bakin ciki da hassada ne suka dura a zuciyar Shamsiyya ,rashin abunyi ne yasa ta fashewa da kuka wurjanjan! ta kalli inda mahaifiyarta take zaune kamar mutum mutumi,sai kace wata gunki tace"Uwa! kina raye a duniya haka tafaru damu k'askantacciya ta fimu komai kullum.kina cewa zaki sabautata mata rayuwa, gashinan kina zaune taje ta auri dan gidan sarauta mu muna zaune"

"Wayyo na shiga uku na lalace"!

 

Sosai Shamsiyya take kurma ihi!

 

Wata wawar ajiyar zuciya Uwa! ta sauke zuciyarta cike da bakin ciki gami da hassada, a halin da ake ciki yanzu batasan yadda zata fara ba,amma ya zama dole ta bazama k'auyuka gurin malamai da bokaye, domin samawa kanta mafuta lallai maganar hauwa ta tabbata inda suke cewa dan hakin da ka raina shike tsone maka ido, a halin yanzu duk hankalin ya karkarta gurin ganin yaya za'ayi su sabauta Bawa Balaraba rayuwa ko ta mutu ko tai rai ko ta haukace cikin uku za ayi daya

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

             。。。。。。。。。。。。。。。

             _*GIMBIYA BALARABA*_ 

                đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

                   _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*BINTUBATULA👄*

 

 

_MARUBUCIAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

 

 

 

 

 

 

_*Zamani writers Association*_

________________________

*We are her to educate motivate and entertain aur Reades*

_________________________

 

 

 

*DIDEGATED*

          *to*

RAHAMA ALIYU

 

 

 

 

BISIMILLAHIR_RAHAMANIR RAHIM

 

 

 

 

 

 

  ``` Tunanin ka kamanin ka d'an uwa ka tsare kanka, Allah yai maka albarka, sai ka gyara makomar ka```

 

_*Wannan magana taka haka take fasihin mawak'i Musbahu m Ahamad*_

 

 

*Allah kasa mu dace*

 

 

 

*🅿79*

 

 

 

 

 

 

Da sauri Uwa!ta mik'e har zanin dake d'aure a jikinta yana k'okarin fad'uwa k'asa,  tayi saurin rikeshi ta tsallake Sallau da kwance magashiyan a dandaryar k'asa,sai nishi yake,d'akinta ta afka kamar mahaukaciya,taje ta zura rigarta ta yafo mayafi ta futo, tana kallon Shamsiyya tace"Maza jeki sako riga mu baza ma,domin zama bai gan mu ba"

 

Da sauri Shamsiyya ta shiga dakin domin sako riga.

 

Lantana ta kalli Uwa!dake tsaye tana zazzage kud'i a cikin banki irin na gwangwani,tana lissafawa, tace"Uwa!yanzu, waye zai kula da Sallau gashi a kwance, kin san nima futa zanyi,yau na tashi bani da ko kwabo"

 

Hararta Uwa!tayi tace"Ai yau dole ki hak'ura da zuwa ko ina ki tsaya ki kula da d'anki daga nan har zuwa lokacin da zan dawo, domin kema zaman jiyya ya kama ki"

 

Lantana ta karyar da kai gwanin tausayi tace"To tunda kince haka shikkenan zan zauna, nasan dai zaki sammin abunci da zansa a baki na"

 

 

Uwa!tace"Idan Shamsiyya ta dawo daga talla ta ciri dari biyu tayi cefa ne,ina da sauran garin kwaki,sai ta tuk'a muku teba,daga nan har dare,in kun ga bamu dawo ba to ku rufe Gida kawai domin in na futa yanzu sai inda mai ya tsaya"

 

Lantana tace"To to shikkenan ai,Allah dai ya bada sa'a, a samo nasara"

 

 

Uwa!tace"Ameen, ai in kana da kudinka komai me sauk'i ne, dama Dan me nake neman kud'in duk dan "yayana,saboda haka yau ranar sune"

 

Tafad'a tana lissafa kudinta sun kai kusan dubu goma sha bakwai.haka ta zufa basu cikin wata karamar jaka, ta rataya ta a kafad'a Shamsiyya ta futo daga daki.

 

Suna futa tsakar gida suka ci karo da Sadiya matar Kawu Mamman tana tsaye bakin k'ofar ta duk abunda yake faruwa a kunnenta.

 

 

Kallonsu tayi tana me tausaya musu,ganin suna nema su jefa kansu cikin halaka,tace"Uwa!kiji tsoron Allah, ki tuna akwai ranar tsayuwa, me Balaraba tayi miki kike nema ki jefa rayuwarta cikin musiba,ki sani da shi sharri d'an aike ne, zuwa yake ya dawo saboda haka Ina mai tunasar dake cewar babu abunda yake d'orewa a duniyar nan sai ikon Allah,duk sharrin ku gami da hassadar Ku a kan Balaraba,dukanin abunda Allah ya hukunta, a kanta na alkairi sai ya faru, babu makawa, sai dai Ku mutu da b'akin cik...... "Ke  Sadiya rufe min baki munafuka"

Uwa!ta fad'a a fusace!ta cigaba da cewa" Wato ke dan baki haihu ba,shine kike min bak'in ciki, a dukanin lamarina da "yayana, to bari kiji, yanzu na fara bin malamai akan " yayana, sai ki mutu,baki san bin malamai ma sai me kud'i ba, aikin banza kawai"

 

Shamsiyya ta rik'e hannun Uwa!tana fad'in "Don Allah k'yaleta munafuka ce zo mu tafi tana b'ata mana lokaci"

 

Futa sukayi suna zagin Sadiya, gami da kwashe mata albarka.

 

Ita kuwa Sadiya bayan futarsu girgiza kai tayi kawai ta shige d'akinta tana nema musu shiriyar Allah.

 

*Wannan kenan*

 

*********

 

Sosai Sarki!ya sakarwa Halisa fuska sukaiyi hira ta fahimta, abunda yasa ya saki jiki da ita,shine ya fad'a mata maganar auransa da Balaraba yaga ta Saki jikinta, bata nuna kishi ba, yaji dadin hakan sosai,kuma suna tare Azima ta kirashi a Waya, nan ma bata nuna b'acin ranta ba, ta burgeshi sosai, har wajan magariba suna tare da juna.

 

 

Balaraba na cikin d'aki shiru, zuciyarta duk babu dad'i gasu Sadiya masu d'ebe mata kewa suna can falo har yanzu basu shigo ba. Mik'ewa tayi a nutse ta futa daga d'akin.

 

 

Can ta hango su, wani keb'antaccan guri suna wasa babu abunda ya dame su

 

Kwata-kwata bata kalli inda suke zaune ba, ta nufi inda su Sadiya suke, tunda ta futo yake satar kallonta ta kasan idonsa, har Halisa ta fahimta,ranta ya b'aci amma ta danne, kawai bata nuna ba.

Mik'ewa yayi shima ya d'an kalli a gogon hannunsa bakwai shaura, Yace"Lokacin sallah yayi ya kamata, kije kiyi sallah ko" Halisa ta mik'e tsaye tana gyara zaman rigarta, tace"Idan nayi sallah zan dawo mu cigaba da hira, yau naji dadin hiraramu,babu fad'a bare hantara"

 

 A kasalance yace"Baki da abunyi ne,shiyasa kike wannan maganar, hirar haka ta isa, gobe ma bance kizo ba, domin nasan halinki"

 

Cikin shagwab'a tace"Me yasa"?

 

"Ba ranar ki bace gobe,zan zauna da Azima kamar yanda na zauna dake yau"

 

Tab'e baki tayi,amma bata yarda ya gani ba,tayi shiru da bakinta kawai bata sake magana ba.

 

 

Tsakaninsa da Balaraba ido ne,ko da tazo ta wuce su bata ce masa komai ba shima haka haka suka shige d'aki ita dasu Sadiya, su kuma suka futa tare.

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

             。。。。。。。。。。。。。。。

             _*GIMBIYA BALARABA*_ 

                đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

                   _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*BINTUBATULA👄*

 

 

_MARUBUCIAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

 

 

 

 

 

 

_*Zamani writers Association*_

________________________

*We are her to educate motivate and entertain aur Reades*

_________________________

 

 

 

*DIDEGATED*

          *to*

RAHAMA ALIYU

 

 

 

🎯🎯🎯🎯🎯🎯🎯

_*Soyayyar gaskiya*_

🎯🎯🎯🎯🎯🎯🎯

 

_Jin jina gare ki marubuciyar wannan littafin,( Mugirat Musa 66) Nagode da addu'ar ki a gare ni, Ina miki fatan alkairi a rayuwar ki,Ubangiji Allah ya biya miki buk'atanki na alkairi damu kanmu al'umar musulmi baki d'aya._

 

 

 

 

 

BISIMILLAHIR_RAHAMANIR RAHIM

 

 

 

 

*🅿80*

 

 

 

 

 Sai bayan sallahr Magariba Mama ta shigo, sun sha hira da Hajiya Kattime sosai,taji dadin ziyarar da Mama ta kaima ta,domin ta d'ebe mata kewa sosai, ko da Waziri ya futo daga turakarsa ya ganta,shan kunu yayi ya fucewarsa ba tare da ya amsa mata gaisuwarta ba, inda akwai wacce ya tsana a duniya,bai wuce Mama Fulani, da d'anta ba,wato Sarki! Ko da ya futa babu inda ya nufa sai sashen Hajiya Kulu me d'akin kudu wato Uwar gidan me Martaba kenan.

 

*****

 

Tana hakimce kan wata kujera me cin mutum d'aya k'afarta d'aya kan d'aya  bayi ne zagaye da ita suna fadanci, ita kuma sai zuba mulki take, Waziri yayi sallama ya shiga d'akin.

 

D'aya bayan d'ayan bayin da suka futa,bayan sun kwashi gaisuwa gurinsa.

 

Guri ya nema ya zauna yana fuskantar Hajiya Kulu sosai, suka gaisa cikin barkwanci kamar yarda suka saba, yace magana ce, nake tafe da ita"

 

Hajiya Kulu ta gyara zamanta tana kallonsa,tace"Ai tunda na ganka nasan akwai magana a bakin ka, kasan abokin kuka shi ake fad'awa mutuwa, nima dama ina neman ka"

 

 

Girgiza kai yayi, yaja wata ajiyar zuciya me zafi, yace"Mijinki yana samun nasara akaina ta ko wane hali,to wannan karon nayi rantsuwar sai dai ayi mutuwar kasko, ko ni ko shi,wallahi tallahi, mulki sai ya dawo hannu na,domin inaji ina gani, bazai bawa d'anshi mulki ba,ni ina zaune ban hau kurarar naji yaya take ba, ajiyar zuciya ya sauke,ya cigaba da cewa"Ina me tabbatar miki da cewar wannan karon idan ya tsananta to zan kawar dashi, daga duniyar nan,sai dai yaga ana mulki a k'iyama,idan yaje can"

Ya k'arashe maganar bakinsa na kumfa"

 

Hajiya Kulu,tace"Wannan maganar da kake tafe da ita,nima a kanta nake,a kintse nake,a shirye nake,zan mara maka baya gurin ganin burinmu ya cika,akansa ko d'ansa,domin kwata-kwata bana sha'awar mulki ya koma hannun wancan d'an shegiyar,ina me tabbatar maka da cewa kashinmu ya bushe"

 

 

"Bar wannan maganar Hajiya,domin in kina yin ta jikina har wani d'aukar zafi yake,yanzu ke wace shawarar kika yanke kan al'amarin domin inji shirinki,nasan kema dai ba daga baya ba gurin shirya mugunta"

 

 

Hajiya Kulu ta gyara zams sosai,ta kwashe masa duk abunda ta tsara,har da zuwan d'an bori, me suna Tsito, Waziri ya girgiza kai, gami da cewa"In yazo nine zan bashi masauki ina fatan dai ya iya aiki"

 

Hajiya Kulu tace"Idan kaji aiki ma d'aya kenan,Tsito k'arshe ne,duk wani aljani dakake ji da gani, yana aiki dashu,kuma in ka nemi kayi magana dasu zai kirasu kuyi magana, babu wata shirka da tsubbu da bai iya ba,mutuk'ar zaka'aje masa kayan aiki,zaka ga aiki da cikawa"

 

Gyad'a kai Waziri yayi cikin jin d'adi yace"Hak'ika wannan shine irin Wanda nake so, na samu,na lura yanda kike k'warzanta shi,har kashe mutum zai iya yi ko"?

 

 

Hajiya Kulu tayi dariya, har da dukan hannun kujerar da take kai, cikin annushuwa tace"K'aramin aiki kenan,ai nake fad'a maka,yanda nake jin labarinsa gurin Jakadiya tace,a rana in yasa kansa,zai iya bawa aljanunsa k'afa masu goma,su sha jini su k'oshi"

 

 

Waziri yayi murmushi yana ji a jikinsa buk'atarsa ta kusa biya, yace"Yaushe kika ce zai zo ne"?

 

 

"Gobe Jakadiya za taje ta d'aukoshi"

 

 

"Allah ya kaimu"

Waziri ya fad'a ya cigaba da cewa"Tabbas idan yayi mana aiki me kyau,zan yi masa muhimiyar kyauta,ta ban mamaki"

 

 

Hajiya Kulu tace"Kai dai kaje ka kwantar da hankalin ka kawai,ai buk'atarmu kamar ta biya ne"

 

 

Waziri ya mik'e tsaye, da niyyar tafiya, gaskiya yana cike da farin ciki, tabbas yasan Hajiya Kulu ba tun yau ba,makirar maca ce kuma muguwa ce,ta inna niha,duk hanyar mugunta,ta sani,sallama sukayi,ko wanne zuciyarsa fara tas, suna Allah-Allah gobe tayi D'an bori Tsito ya dura,a gidan, domin ya fara aiwatar da aikinsa.

 

 

****

Bayan sallahr Isha'i Mama ta aika Jakadiya Shafa'atu domin ta kira mata, Balaraba a cewar ta zaman kad'acin da Balaraba take,zai iya haddasa mata wani ciwon, babu yadda ta iya,  ta mik'e ta bi bayan Jakadiya,domin baza ta iya sab'awa umarnin Mama ba,lokacin su Sadiya sunyi bacci.

 

Sosai Mama take hira da ita tana dan janta a jiki,duk domin ta sake,tasa  Jakadajiya tana basu labarai na ban dariya,sai ga Balaraba,ta saki jiki sosai har tana dariya. duk abunda bata gane ba,a game da labarin da Jakadiya Shafa'atu take bayarwa sai ta tambaye ta,ita kuma ta fad'a mata, k'arshe dai Mama Fulani tayi musu shiru kawai tana kallonsu da murmushi a fuskarta,taji dad'in sakin fuskar da Balaraba tayi.

 

 

Yana kwance, cikin Sofa yayi lif kai baka ce a kwai mutum cikin d'akin ba,duk wannan abunda yake faruwa yana ji,tun futowar Balaraba, ya nemi nutsuwarsa ya rasa hatta baccin da ya rufe masa ido nemansa yayi ya rasa,ya lumshe ido kawai yana sauraron muryarta wacce ta kashe masa jiki, ashe haka yarinyar take da surutu,muryarta nada dad'i,abunda yake fad'a kenan cikin zuciyarsa.

 

Mama Fulani ce kawai tasan yana gurin,domin da futo ta ganshi a kwance har tayi masa maganar tafiya shashensa yace"Sai ad'an jima zai tafi"

 

Yanzu ma murya ta d'an daga kad'an tace"Magajin Sarki!"

 

Da sauri Balaraba ta kalli inda Mama take kallo,gabanta na fad'uwa yanzu da yana gurin ta saki jiki take,dariya sai kace wata shashahsa, k'asa tayi da idonta lokacin da ta hangi inuwarsa kwance kan kujera, dake gurin da yake babu wadataccen haske,ya k'ashe k'wai shiyasa lokacin da ta futo bata ganshi ba,

 

Jin muryar Mamansa yasa yayi gyaran murya,yana daga kwancen yace"Na'am Mamana"

 

 

Cikin tausasawa tace"Yau da alama dai nan zaka kwana,ko"?

 

Shiru na minti biyu,yace"Mama yau wani irin kad'aci nake ji wallahi,ki barni inyi kwanciyata nan,ina jin motsin ki"

 

 

Murmushi tayi cike da tausayinsa tace"Yau yarinyar tar ce kuma ta motsa maka"

 

Murmushi yayi wanda har sai da sukaji sautinsa,Balaraba taji wani yarrrrr! A jikinta. Yace"Dama ni kullum yaro ne,a gurin ki, tunda har yanzu banyi auran fari  ba,kuma ban haihu ba"

 

 

Shiru Mama tayi,kunya duk ta isheta Mama Fulani maca ce mai mutukar kunya a rayuwarta,

 

Jakadiya Shafa'atu tayi murmushi tana k'okarin mik'ewa tsaye tace"Lallai Uban d'akina dole kasa Fulani tayi shiru,saboda ka tab'o abunda baza ta iya magana akai ba,saboda kunya, kana maganar auran fari,kai kasha kurumin ka, mata uku zaka aura me yafi wannan dad'i"

 

Miskilin murmushi yayi iya leb'anshi yana satar kallon Balaraba shi yana ganin fuskarta sosai,itace takasa gano fuskarsa,sai dai zatinsa,

 

Jakadiya ta runk'umfa tana fad'in A tashi lafiya  Uwar d'akina"

 

Mama tace"Allah ya bamu alkairi"

 

Sarki!ta kalla kanta a k'asa tace"Yallab'ai a tashi lafiya"

 

Hannu kawai ya d'aga mata,maganar tana masa wahala,dama zuwa-zuwa ce, in yaga dama wataran haka zai ta hira,mussaman da Moddibo ko Mamansa

 Balaraba ma mik'ewa tayi ,tai wa Mama sallama, Mama tace"Har zaki shiga Balaraba, ko dan kinga Jakadiya ta tashi"

 

Girgiza kai tayi cikin jin nauyi tace"Ba haka bane Mama,ina so in d'an kwanta ne, naji kaina na ciwo kad'an watak'ila bacci ne"

 

 

"Ayya, to ki tabbatar kin sha magani kafin ki kwanta kinji ko"

Tafad'a cikin kulawa.

 

Balaraba tace"Insha Allah Mama, Allah ya bamu alkairi"

 

Mama tace"Ameeen

 

Balaraba ta wuce d'akinta a nutse, Idansa a k'asa sai ka rantse da cewar bacci yake saboda yadda ya lumshe su, amma duk wani motsin Balaraba yana gani har ta shige d'aki.

 

 

Ajiyar zuciya ya saki,yanayin jikinsa na sauyawa, ya rasa abunda yasa yake jin wani irin sauyi a jikinsa mutukar zai ga gilmawar ta,sai sha'awarsa ta motsa,yasan yanzu idan ba'ai wasa ba,kwana zaiyi yana mafarkai, shi kansa yasan mutum ne mai mutuk'ar Sha'awa, yana daurewa kawai,amma abun mamaki idan yana tare da Halisa baya shiga irin wannan yanayi

 

 

 

Shi kad'ai a kabari a k'aton falon, domin Mama ma ta shiga ciki, rage haske futular yayi ya gyara kwanciyarsa,bacci ya d'aukeshi, mai cike da mafarkai, mafarkin da ya dad'e bai yi ba,yau yayi Balaraba ya gani, tare da wannan matar suna cikin farin ciki da annushuwa,suka zo gurinsa, kamar kullum, matar ta kama hannusa dana Balaraba ta had'a guri guda, ta tafi tana waiwayensu, fuskarta cike da farin ciki har suka daina ganinta.

 

 

Balaraba ya kalla sai yaga tanai masa wani k'ayataccen murmushi, gashi ta rik'e hannunsa sosai,  taja hankalinsa cikin mafarkin, wanda yayi sanadin da yakasa daurewa ya rungume ta sosai yana kiss d'inta,  ji yake kamar gaske, jikinsa duk ya shiga babu abunda yake buk'ata lokacin sai Jima'i, sai da ya kai k'ololowa sannan ya farka cikin wani mugun yanayi jikinsa duk ya b'aci, still kamar yadda yake ganin girmansa cikin mafarkin haka take a fili, ta mik'e tsaye! Tana jiran hakkinta .

 

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿81*

 

 

 

 

 

Ya dad'e yana jin wani irin yanayi a jikinsa, wanda bai tab'a jin irinsa ba, da k'yar ya samu ya mik'e a jigace,   futa yayi daga shashen gaba d'aya, ya nufi nasa, lokacin ana kiraye-kirayen sallahr asubah, a gurguje yayi wanka gami da tsarkake jikinsa, ya futo ya zura jallabiya me yankakken hannu, wani takalmi mai kyau ya zura a k'afarsa ya futa, da nufin zuwa massalaci, domin gabatar da sallahr asubah.

 

 

*******

Uwa! da Shamsiyya ne zaune gaban wani mutumi zaune a kan  wani buzu, da wasu manya-manyan carbuna, gami da alluna irin na k'arfe a jijjigine a bango, yana sanye da riga da wando na wani yadi bulu, wanda akai wa d'inki "yar shara. Gabansa wani fefe ne k'aton gaske cike da yashi, yana zane-zane a ciki, shi kad'ai ya san abunda yake zanawa.

 

 

Yana ganinsu ya saki fuskarsa, sannu da zuwa kawai yake musu.

 

Suka nemi guri suka zauna suna gaisawa, amsawa yake, hankalinsa na kan Shamsiyya.

 

Yashin, da yake gabansa ya hau zanawa, tsawon minti biyar, ya d'ago kansa yana kallonsu yace" Na duba naga abunda yake tafe daku, ina fatan dukanin abunda aka umarce ku dashi zakuyi batare da kun bamu wahala ba"

 

 

Uwa! ta gyara zamanta sosai, tace"Allah ya gafarta maka, duk abunda aka umarce mu muyi zamu yi mutuk'ar buk'atarmu zata biya"

 

 

"To Masha Allah"

Arrama ya fad'a yana kallon Shamsiyya sai sid'e leb'e yake.

 

 

Gayan murya yayi, yace"Naga wata yarinya buduwar wa,gata anan"

Yafad'a yana nuna wani zane da yayi jikin yashin.

 

Uwa! ta k'walalo ido tana son ganin budurwar da ya fad'a

 

Murmushi yayi yace"Ai baza ki ganta ba, wannan aikinmu ne"

 

Uwa! tayi yak'e tace" Allah ya taimake ka"

 

Arrama ya cigaba da cewa "Wannan yarinyar da nagani, naganta kewaye da wasu taurari masu haske da d'aukaka, kuma na fahimci akanta kuka zo"

 

 

Shamsiyya ta gyad'a kai tana fad'in "Hakane Arrama, Balaraba sunanta.

 

Murmushi yayi, ya sid'i leb'ansa a karo na biyu yace" Itace Balaraba, gatanan cikin gidan sarauta, kewaye da dawakai da bayi, gatanan cikin shigar alfarma, kuma zata haifi "yaya maza sosai a gidan, ciki kuwa harda Sarki!"

Arrama ya k'arasa maganarsa yana duba ya shin dake gabansa.

 

 

Uwa! saura kad'an ta saki futsari saboda jin abunda Arrama yace, bakinta na rawa tace" Yanzu Allah ya taimake ka babu yadda za'ayi a rusa mata rayuwa,a sabauta mata rayuwa ta haukace, a maye gurbinta da Shamsiyya, gata a gabanka"

Ta k'arasa magana tana nuna masa Shamsiyya

 

 

Arrama, yayi wani bazawarin murmushi, yace"Akwai yadda za'ayi mana mutuk'ar zaku bi umarni kamar yadda na fad'a muku tun farkon zuwanku nan".  Shamsiyya tace"Insha Allah zamu bi umarni"

 

Arrama yace"To yanzu abunda za'ayi, ke zaki zauna a gurina tsawon kwana bakwai zan fara yi miki wankan magani, ke kuma"

Yafad'a yana kallon Uwa! yace"Ke kuma zan had'a miki wasu magunguna da zakuje kuyi amfani dashi duk rintsi kar ku wuce kwana bakwai ba Ku gabatar dasu ba, har indai kuka bi abunda nace muku, to buk'atarku zata biya"

 

 

Babu fargabar komai Uwa! tace"Ai dama mu domin buk'atarmu ta biya yasa muka zo gurin ka, zamu bi dokikin aiki insha Allah"

 

 

 

Malam ya janyo wata k'warya k'autawar gaske tana cike da d'aurikan magani, yw ciro k'ulli uku ya mayar da murfi ya rufe.

 

 

 

Kulli d'aya ya mik'a mata yace"Wannan duk yadda za'ayi aje a samu k'asar kabari Wanda aka bunne sabuwar gawa,a d'ebo damtsa uku, a had'a da wannan garin magani, aje har inda wannan yarinya Balaraba take, a barbad'a a hanyar ta ta wucewa, mutuk'ar ta tsallaka to zata had'u da ciwon me wahalar gaske, babu wanda ya san makarin wannan abu sai ni, zata dunga lalura a kasa gane kanta,da gidinta k'arshe ta haukace kowa ya huta"

 

Uwa! Ta karb'a tana hamdala, ya mik'a mata sauran d'auri kan maganin yace"Su kuma wannan a abunci ko abunsha za'a bata taci, sunansa shashatau,mutuk'ar taci zata mance wacece ita"

 

Hannu na rawa Uwa! Ta k'arb'a tana ta zabga godiya, tace"Arrama nawa ne abun sadaka"?

 

 

Arrama ya sosa kansa, yana satar kallon Shamsiyya, yace"Abun sadaka ai babu yawa,ki bada dubu goma sha hud'u, domin zan sissiyi kayan aiki a ciki,za'a bawa mutanan nan"

 

Uwa! Ta zuge jakarta ta futo da kud'i ta lissafa tsaf ta ciri dubo goma sha hud'u cikin dubo goma sha bakwai saura dubu uku,ta mik'awa Arrama.

 

Karb'a yayi yana washe baki,Lallai yau kakarsa ta yanke sa'a.

 

Uwa! Ta mik'e tana gyara lillib'inta, ta kalli Shamsiyya tace"Kiyi k'okarin bin umarnin da aka baki, domin mu samu buk'atarmu ta biya, a kan kari nasan Arrama bazai cuce ki ba"

 

"Zanyi k'okari, ke ma kiyi k'okarin aiwatar da aikin ki"

Shamsiyya tafad'a wa Uwa!

 

Sallama tayi musu ta futa daga zauran.

 

*****

Shamsiyya da Arrama a zaure.

 

 

 

 

 

 

Rashin comment d'inku yana bani mamaki wallahi gashi kuma kuna karantawa, shikkenan har indai baza ku gyara ba, zan daina ku kuma in mai dashi na kud'i dama can na kud'i ne, na sakarmu domin in faranta muku rai,

 ku gyara idan ba haka ba zan maida hankalina kan novel dina Tsantsar butulci, domin wannan nasan kud'i ake bani

 

 

_Nasan zakuji haushin magana ta, gaskiya ce, dole zan fi maida hankali kan book din Tsantsar butulci domin hakkin mutane dake kai na_

 

 

_Wannan kuma in nasamu time inyi typing yadda ya sawwak'

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿82*

 

 

 

 

 Wani munafukin  kallo Arrama yakewa Shamsiyya kallo irin na k'asan ido,  gyara zama yayi, yana d'an lasar leb'anshi,yace "Matso nan mu fara aikinmu"

 

Shamsiyya ta matsa kusa da Arrama sosai,idonta tar a kansa.

Shima kallonta yake cike da sha'awarta,yace"D'ora hannunki a kan yashin" Shamsiyya ta d'ora hannuta duk biyun kan tarin, yashin dake cikin fefe.

 

Minti biyu yace"Cire hannun naki"

Shamsiyya ta cire tana dubawa.

 

"Me kika gani"?

Arrama yafad'a hankalinsa na kanta.

 

" Babu abunda na gani"

Tafad'a tana k'ara dudduba hannuwan nata.

 

"Mugani"

Yafad'a idonsa a kanta kamar tsohon maye.

 

Shamsiyya ta nuna masa hannuwan ta, yayi wani bazawarin murmushi irin na yaudara, yace"Dama ke ai baza ki ga komai ba,sai dai a gane miki,nagano miki alkairi me tarin yawa,kuma kamar yarda kuka buk'ata  zaki auri wannan mutumin da "yar uwarki zata aura mutuk'ar kin bi umarni"

 

 

Shamsiyya ta gyara zama sosai fuskarta cike da farin ciki, tace"Nagode Arrama nasan dama zakayi k'olari a kaina,ni kuma nayi maka alk'awarin idan na auri d'an sarki zan kaika hajji da umara kuma zan siya maka gida me kyau"

 

 

Arrama yayi dariya yana lumshe idonsa, yace"Nagode k'warai da gaske, ya fad'a yana d'aukar wani allon k'arfe dake jingine a bango, ta wada, ya bud'e ya fara rubutu, sai da ya cika allon sannan, ya wanke cikin wata roba me fad'i, ya kalli Shamsiyya dake zaune, yace"Aiki na farko da zamu fara yanzu, zaki shiga wannan d'akin na bayana ki kwab'e kayan jikin ki Tass, ki shafe jikin ki da wannan rubutu,ki zauna haka tsawon awa uku,sai rubutun ya bi jikin ki sannan zaki mai da kayan ki"

 

 

Ba tare da wata damuwa ba, Shamsiyya ta mik'e da sauri ta karb'i robar da rubutun yake ciki,tace"Yanzu zan shiga kuwa,ai ni duk abunda akace nayi zanyi"

 

"Yawwa haka ake son mutum me bin umarni" Malam ya fad'a yana dantso wani garin magani a hannunsa,ya barbad'a a cikin rubutun,yana fad'in maza shiga ki fara'a aiki"

 

Shamsiyya ta bankad'a d'akin ta fad'a abunta, wasu irin tarkace ta gani a k'uk'utaccan d'akin, kamar bola,da wata ya mutsatsiyar katifa,a shimfid'e, ba abunda ta dame ta, ta tub'e kayanta tas, ta fara shafa ruwan rubutu kamar yadda a ka umarce ta.

 

 

 

Tun kafin ta gama shafawa tafara jin jiri na d'ibarta, da k'yar ta gama shafawa dan bayanta ma bai san anayi ba, ta b'ingire a gurin wawan bacci ya d'auketa.

 

 

Mintuna goma, Arrama ya mik'e yaje, ya saka sakata, a k'ofar d'akin,ya dawo da saurin ya shige d'akin da Shamsiyya take, da sauri ya saki a sabarin da ya ke, lullub'e d'akin, wani murmushi ya saki lokacin da yaga Shamsiyya,a kwance zigidir haihuwar uwarta, bata san in da kanta yake ba, Nonowan ta,ya kalla yaji wani zillo a k'asan sa, da Sauri ya cire "yar sharar dake jikinsa, ya zage ta zugen wandonsa, da sauri afka kan Shamsiyya, ya damk'i qirjinta, yana wani irin ihu, ya fara saduwa da ita, tamkar matarsa ta aure.

 

*Wa'iya zubillahi*

 

Sai da Arrama yayi awa hud'u a kan Shamsiyya yana lugudarta, bata san inda kanta yake ba, duk inda ya ga damar sarrafata bata motsi, ya gamsu iya gamsuwa, ya mik'e jikinsa da kuzari saboda ya zubar da duk abunda ya dame shi,a mararasa, kayansa ya zura ba tare da wani tsarkake jiki ba,ya futa daga d'akin, ya zauna kam buzunsa,ya cigaba da amsar bak'insa kamar yadda ya saba.

 

 

 

 

************

Tsito da Jakadiya Ladi.

 

Cikin yanayin maganarsa ta " yan daudu yace"Ladi kin nace dole sai naje,gidan nan nayi aiki,kin san fa gidan sarauta, wallahi duk abunda ya same ni, bazan k'yale ki ba" Ladi tace"Babu abunda zai faru sai alkairi, akwai shirin da zan maka yanzu,ga kaya nan na kawo maka,irin na hadiman gidan zaka saka a jikinka, muna shiga,gidan, shikkenan magana ta k'are"

 

 

Tsito yace"Babu damuwa tunda kince akwai kulawa, za muyi aiki yadda ya kamata"

Kayan ya karb'a ya Sanya a jikinsa tsaf ya saje da bayin gidan Sarki Almustafa, suka kama hanya suka tafi, Tsito duk jikinsa kayan aiki ne, wasu irin layu,da k'ananun k'ososhi,da wasu tarkace rakwacam,kana ganinsa kasan d'an bori ne.

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿83*

 

 

 

 

 

 Wani keb'antaccen d'aki a kaje Tsito,dake dare ne babu wanda, ya lura dashi a cikin bayin saboda sun san junansu duk yawansu.

 

A daran Hajiya Kulu da Waziri suka shiga gurinsa.

 

Ya cire kayan jikinsa yana zaune daga shi sai jan zani irin na sak'i ya d'aura a k'ugunsa,jikinsa duk layu da tarkacen kayan tsafi, wani k'ok'o ne a gabansa me k'urzunu-k'urzunu da wasu takarce a ciki, wasu ciyaye shi da jajayen yankuna,an suka musu allurai"

 

Da baya-da baya ya basu umarnin shiga d'akin,suna zama ya fara furje-furje wata kumfa na futowa daga bakinsa,sai ya mik'e tsaye yana wani irin tsalle yana zagaye su, bakajin komai sai sautin kayan aikin dake jikin k'afafunsa da hannayensa da wuyansa, kacacar-kacacar, wasu zan tuka yakeyi yana tumami a gurin, ya zayi zaman bori a gansu,duk kamaninsa sun sauya,kana ganinsa kasan bashi bane, Hajiya Kulu ta tsure tana had'iye yawu da k'yar,shi kuwa Waziri farin ciki yake yasan k'arshan wahalarsa ta k'are.

 

 

"Nine Aljani Mak'asudu, dan gidan sarki K'azaza,jikan Sarki Jajubu" Nine na gaji sarauta,sama da k'asa, Nine nake da Muk'ulin mulki a hannu na, nasan abunda yake zuciyoinku, duk biyun,saboda haka kun kawo kukanku inda za'a share muku hawaye.

 

 

Abunda sukaji d'an bori Tsito yana fad'a kenan.

 

 

Waziri yace"Allah ya ja zamanin ka, tabbas kaine ka gaji mulki gaba da baya, ko a cikin jinsun Ku,ma zuriarku daban take,da kowa muna fata wahalarmu tazo k'arshe"

 

 

"Ihuhuhuhuhu! Aljani Mak'asudu yayi,ya kyalkyale da dariya,yana Fad'in " Kasamu mulki ka gama, gobe ka kwana da shirin hawa kujerar sarauta,domin zan b'atar da d'an uwanka a duniya jininsa zan shanye tass!! Wannan mataki na farko, bayan na shanye jinin d'an uwanka, zaka bani jini bil'adamu k'afa shida bakwai kenan,,,wannan shine sakamako na"

 

Waziri yace"Duk za'ayi maka daga yau zuwa gobe zan kawo maka,bil'adamu kasa jini ka k'oshi.

 

 

Gyad'a kai Aljani Mak'asudu yayi, ya kalli Hajiya Kulu yace"Ke ma kije buk'atar ki ta biya, zamu sa, a tsugunar miki dashi wannan yaron da ya tsaya miki a zuciya, zakiyi yadda kike so ke da yaran ki, itama Uwar tasa duk wani abu da take ji dashi, zamu sauke mata shi,amma dole mubi a sannu saboda tsarin da yake jikinta,a shekarun baya mahaifinta ya bamu wahala sosai, dan haka dole mu d'auki fansa a kan jininsa"

 

 

Hajiya Kulu tace"Kar kaji komai Ubana, ka fad'i bukatar ka ni kuma zan baka abunda kake nema"

 

 

 

Aljani Mak'asudu yace"Ke ma zaki bani K'afa Uku shine muradi na"

 

 

Hajiya Kulu tace"Angama Ubana, duk Wanda. Kaga yayi maka cikin gidan nan mace ko namiji ko a cikin "yayana ne,kana iya shanye masa jini na baka"

 

 

Waziri shima yace"Wannan haka yake, nima ka zab'i Wanda kakeso cikin "yayana da bayina na baka, kasha jini yadda kake so"

 

 

Aljani Mak'asudu yace"Ku tashi ku tafi buk'atarku ta biya ta duniya"

 

Tashi sukayi suka futa da baya-baya.

 

Tun a daran Aljani Mak'asudu ya fara gudanar da kinsa, takan me Martaba ya fara, jininsa ya shanye tas,a ka wayi gari babu shi,a duniya.

 

*Innalillahi wainnailaiyi raji'un*

 

Gida ya kacame da ihu da tashin hankali na mutuwar me Martaba sarki Almustafa mutuwar ka tsaham, yayi sallama da kowa lafiya lou ya shiga turakarsa, Liman na jira ya futo sallah asubah, shiru abunda bai tab'a faruwa ba, Sarki! Ne ya shiga shashen Mamansa, domin nan me Martaba yake, suka had'u da ita a babban falo itama ta futo, cikin wasi wasi da damuwa suka nufi d'akin da yake.

 

Kwance suka ganshi kamar me bacci, idonsa a rufe, Sarki! Ya zauna gefansa yana tattab'a jikinsa, sanyi k'alau d'aga hannunsa yayi yaga ya koma ya kwanta yaraf!! Shi ba yaro bane yasan mecece mutuwa, Mama Fulani ta zube gurin a sume.

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿84*

 

 

 

 

Cikin damuwa da tashin hankali Sarki! Ya futa daga d'akin, Jakadiya Shafa'atu na tsaye a falon tana gyare-gyare taga futowarsa,a gigice, tace"Allah ya taimake ka lafiya"?

 

Sarki! Yace"Babu lafiya Jakadija, Allah yayi wa me Martaba rasuwa, Mama ta suma a d'aki,innalallahi wa'ina ilahi raji'un"

 

Futa yayi bai san Inda yake saka k'afar sa, lokacin gari ya soma haske, kai tsaye masalaci ya nufa domin ya shaidawa liman abunda yake faruwa.

 

Jakadiya Shafa'atu kuwa kasa shiga d'akin tayi, saboda tsoro da sauri ta nufi b'angaran Waziri domin ta kirawo Hajiya Kattime.

 

 

 

Lokacin da liman ya sanar da rasuwar me Martaba mutane da dama sai suka dunga k'aryatawa kafin kace kwabo kowa ya futo daga shashinsa,har Waziri,,, ya nufi shashen Mama Fulani domin ya tabbatar. Babu Wanda ya hanashi shiga,saboda me Martaba bashi da wani d'an uwa shak'ik'i kamarsa,duk da sun san cewar babu jituwa a tsakaninsu kwana biyu.

 

Tsallake Mama Fulani yayi ya nufi gawar me Martaba,yana dubawa, hamdala yayi a fili yace"Taka ta k'are Mustafah sai mun had'u, acan,

Lillab'e gawar yayi ya futo yana share hawaye kamar gaske,nan ya k'ara tabbatar wa da jama'a cewar me Martaba ya amsa kiran ubangijinsa.

 

Da k'yar Mama Fulani ta farfad'o ana tai mata fiffita, duk bata cikin hayyacin ta, Hajiya Kattime ta rungume ta a jikinta.

Balaraba a gefenta tana share mata hawaye Mama takasa cewa komai, tunda ta farfad'o bakinta sai motsi yake,babu abunda take fad'a sai Kalmar innalillahi wa'inna ilahi raji'un"

 

Balaraba hawaye  kawai yake sharewa tana addu'a Allah ya yaye musu wannan masifa da ta tun karo su,gani take kamar k'arya ne me Martaba bai mutu ba, sai data an futo dashi cikin suttura za'a kaishi makomarsa sannan ta gasgata,fad'uwa tayi a gurin ta suma,Mama Fulani kuwa rirrik'eta akayi domin itama saura kad'an ta fad'i da k'yar! ta samu tayi masa addu'a wasu hawaye masu zafi suna zubo mata, Waziri ya tasa gawar a gaba yana kuka kamar wani k'aramin yaro. Sarki! Kuwa wani mugun haushinsa yake ji,ganin yadda ya babba ke gaban gawar, ya hana mutane suyi masa addu'a, sai da aka sauke alk'urini me girma sannan aka sallaci gawar me Martaba ya samu jama'a sama da k'asa ko ina,haka aka d'auke shi aka kaishi makwancinsa na gaskiya.

 

***

B'angaran Hajiya Kulu da yaranta kuwa duniya sabuwa suka bud'e sun cika suna ciye-ciye da kalle-kalle tamkar ba mahaifinsu ne ya rasu ba, babu abunda ya dame su,Naja'atu ce me cewa,lokacin su yayi,za tayi facaka da kud'i, son ranta

 

 

Sarki! Kuwa wani irin zazzab'i ne yake damunsa tun bayan dawowarsu daga mak'abarta,daurewa kawai yakeyi ya zauna yana karb'ar gaisuwa gurin "yan uwa da mutan gari,suna kokawa da rashin da akayi, kowa sha'awa yakeyi Almansor ya maye gurbin mahaifinsa,hatta da su Galadima ma burinsu kenan,Governor da yazo gurin gaisuwar a bunda ya fad'a kenan,Waziri yayi tsagal yace" Ba haka al'adar sarautarmu yake ba,nine k'anin me mutuwa nine zan gaje shi,kafin "Yayanmu saboda haka tunda ina raye,ban mutuba ni zan zauna kan kujerar mulki" Governor yace"Wannan ba sarin mulkin k'asa bane, nine shugaba,dole nine zan zab'i sarkin gari na, saboda haka baza mubi tsarinka ba,Dan kar kace ba'ayi maka adalci ba,za muyi k'uri'a bayan sadakar uku wanda ya fi jama'a shine zai zauna kujerar mulki"

 

Waziri ya baza babbar rigarsa cikin bak'in ciki da b'acin rai yace"Lallai kam kun jawo masifa,domin rashin zaman lafiya zai tabbatar a masarautar nan, tunda iyayenmu da kakanimu suke mulki basu tab'a wata k'uri'a ba sai yanzu, mu baza'a rusa mana tsarinmu ba"

Yana gama fad'in maganganunsa ya mik'e ya futa daga fadar,ranshi a b'ace, yana ganin wannan Governor zai kawo masa matsala fa, yayin da buk'atarsa ta kusa cika

 

 

 

Sunyi mamakin abunda Waziri yayi,zahiri ya nuna mulki yake so,Sam mutuwar d'an uwansa ba itace a gabansa, wannan ya k'ara bawa Sarki! K'warin gwiwa da son sha'awar mulki abunda bai dame shi ba,a da yana so yanzu su fafata da Waziri, Allah yaba mai rabo sa'a.

 

Sai bayan sallahr isha'i Sarki! Ya shiga gida kai tsaye shashen Mamansa ya nufa,yana tafiya cikin sanyi jiki, ji yake duk duniyar tayi masa zafi, Lallai d'an adamu ba abakin komai yake ba,dubi irin hukuncin ubangiji,wata guda yayi rashin mutane biyu da bazai tab'a mantawa dasu ba a tarin rayuwarsa.

 

Balaraba da Mama Fulani da tare da Madabo,da Halisa,da Azima da wasu mata biyu, sai jakadiya Shafa'atu wacce take kusa da Mama Fulani tana b'are mata lemon zak'i,domin ta kasa cin komai, wani irin d'aci take ji a bakinta, da k'yar ta dunga shan lemon har tasha guda uku.

 

Da sallama ya shigo, falon Suka fara rige-rigen gaishe shi,da yi masa gaisuwa,amsawa yayi sama-sama ya shige turakar mahaifinsa.

 

Ko da ya shiga kwanciya yayi kan gadon me Martaba,ya d'auki rigarsa da ya rasu da ita a jikinsa,ya rungume ta,k'am wasu zafafan hawaye suka fara zubo masa.

 

Shikkenan Moddibo ya tafi me Martaba ya tafi,sun barshi shi kad'ai hakika duniya abar tsoro ce,hakama abun jikinta

 

Kuka Sarki! Yake sosai,kukan da bai tab'a yin irinsa ba, hak'ika yanzu yana buk'atar me rarrashinsa domin ji yake zuciyarsa zata iyayin bunduga, shi musulmi ne, dole ya yarda da mutawa da rayuwa yasan mutuwar wannan mutane biyu, babu wani mahaluki da ya isa ya tare ta sai,Allah domin shine ya hallice su, amma ya karb'i abunsa, shima kuma na hakane, yanzu kawai addu'arshi itace Allah ya sanya masa dauriya da jarumunta a zuciyarsa.

 

 

Kamar a mafarki yaji muryarta a kansa,tana kiran sunan sa.

 

Bud'e idonsa yayi dukansu ya sauke a kanta

 

Wani irin yarrrr taji lokacin da suka had'a ido ganin yadda k'war idonsa ta koma wata kala,tayi jazur kamar Jan gauta.

 

 

Wani irin tausayinsa ne ya tsirga mata,itama sai taji hawaye yana k'okarin zubo mata,daurewa tayi kawai,a zuciyarta tace"Maraici babu k'arya a cikinsa,komai girma komai dukiyarka, ka rasa iyaye kayi babban rashi,yanzu zai fara jin irin ciwon da take ji a zuciyarta na rashin iyaye.

 

Lumshe idonsa yayi yana jin tamkar ya kamo ta ya rungume a jikinsa ko ya samu sassaucin abunda yake ji a zuciyarsa,hak'ik'anin gaskiya yanzu Wanda zai rarrashe shi yake nema.

 

 Cikin taushin Murya tace"Ka tashi inji Mama kaci abunci,tace inyi k'okari in baka kaci kafin ka kwanta"

 

 

Yana jinta yayi shiru abunsa, wani sanyi irin na zazzab'i yana k'ara ziyartarsa.

Ta kure jikinsa yake yana neman bargo domin ya lullub'e jikinsa.

 

Duk tana kallon abunda yake yi, muryar ta na rawa tace"Don Allah ka tashi kaci abunci kaji ko, bana son abunda zai damu  Mama,ina tausaya mata da halin da take ciki,kar ka k'ara sanya mata wata damuwar tunda kasan rashin cin abuncin ka zai d'aga mata hankali, ba kai kad'ai kayi rashi ba,har damu,ni ina ganin kamar ni akayiwa mutawar ma"

Ta k'arshe maganar tana goge hawaye da suka zubo mata.

 

Yana lullub'e cikin bargo yace"A k'oshe nake,ko na tashi babu abunda zan iya ci, kiyi tafiyar ki kawai nagode"

 

 

Girgiza kai tayi kamar zatayi kuka ta zauna gefan gadon ba tare da wani tunani ba ta kama bargon tana k'okarin cirewa daga jikinsa, bargon ya rik'e ya had'a da hannunta, yana girgiza kai,alamar ta sakar masa

 

 

Girgiza  kanta tayi itama kamar yadda yayi mata, komawa yayi ya kwanta kawai ya rufe idonsa,

 

Kallonsa tayi taga yadda kwarmin idonsa suka zurma ciki sai girman k'war idon,sai kace Wanda yayi wata yana lalura, ba tasan sanda hawaye ya fara zuba daga idonta ba,wannan tausayi ta rasa daga ina yake zuwa, babu komai a zuciyarta face tsagwaron tausayin Sarki!Almansor.

 

Sheshshek'ar kukanta yaji yasa ya bud'e idonsa da Sauri, yana kallonta,tayi saurin kauda kanta,tana k'okarin  mik'ewa daga kusa dashi, ya ruk'ota da Sauri ya rungumeta tsam-tsam yana wata zafaffafiyar ajiyar zuciya!

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

_________________________

 

đŸ•șđŸŒđŸ•șđŸŒđŸ•șđŸŒ

          *NAMIJIN DUNIYA*

                    🙆🏿🙆🏿🙆🏿

 

 

*Story & writing*

       

            *By*

*Aunty Mamie*

 

_________________________

 

_Ina masoya wannan novel d'in, Aunty Mamie na gaida ku, kuma tana muku fatan alkairi, gaba d'ayan Ku, wannan novel d'in mai suna Namijin duniya ya koma na kud'i dan haka duk me buk'atar ci gaba da karanta shi sai ya tuntub'i wannan numbar_

08166526167

_________________________

 

 

 

 

 

 

*🅿85*

 

 

K'okarin k'wace kanta take daga jikinsa, ya rik'e ta tsam a k'irjinsa,sai sauke ajiyar zuciya yake,zuwa can taji d'igar wani abu me d'umi a bayanta, hannuta tasa ta shafo,taji ruwa, Wannan ya tabbatar mata da cewar hawaye ne, tunda take dashi bata tab'a ganin kukunsa ba sai yau, itama zuciyarta sai ta karye,babban mutum kamar Sarki! yana kuka lallai tashin hankalin ya kai inda ya kai.

 

Sunfi minti biyar rungume da juna, sai da taji jikinsa yayi sanyi sannan ta zare jikinta daga nasa,tana kallon fuskarsa, lumshe idonsa yake amma ba bacci yake ba, tana kallon yadda yake cije bakinsa,kamar wanda yaji ciwo me zafi. Jikinta a sanyaye ta futa daga d'akin.

 

Tana zama Mama Fulani tace"Ina fatan kin bashi abunci yaci ya k'oshi"?

 

 

Balaraba bata iya k'arya ba,dan haka kawai sai ta girgiza kai alamar A'a.

 

 

Tace"Mama nayi-nayi ya tashi yaci yace a k'oshe yake Wallahi"

 

 

Mama Fulani tace"Nasan dama abunda zai ce kenan, sam baya son cin abunci, tun safe a ce mutum babu abunci a cikinka, sai damuwa Allah ya kyauta"

 

 

Balaraba dai Shiru tayi tana tunanin abunda ya faru tsakaninta dashi.

 

 

Halisa ce ta mik'e da sauri tana kallon Mama Fulani tace"Bari inje in gwada bashi ko zai ci"

 

 

Mama tace"Aikuwa da kin kyauta"

 

Madabo tayi murmushi, tace"Ai dama ko wace mace da irin hikimar ta,da kin sani tun farko ita kika tura ba waccan ba, ita har yaushe ma suka shak'u da shi"

 

 

Mama ta gane magana Madabo ta fad'a mata, tabbas Madabo baza ta canza halinta ba, na fad'ar maganganu da habaici.

 

 

Halisa ta shige d'akin da Sarki yake cikin gadara.

 

Azima kuwa tana zaune tamkar ta d'ora hannu aka, ta lura babu Wanda yake sonta, Balaraba tana da fada,gurin Mama Fulani, Halisa kuma "yar uwarsa CE, ga uwarta a tsaye a kanta, itama dole ne ta zage damtse gurin ganin ta kafa gwamnatin ta.

 

Mik'ewa tayi itama tana shan. k'amshi  ta kalli Mama Fulani tace" Bari in shiga in duba jikin nasa"

 

 

 

Mama Fulani tace"A fito lafiya, kuyi k'okarin bashi abunci dai"

 

 

Azima tace"Insha Allah Mama" Wucewa tayi ko kallon inda Madobo take batayi ba.

 

 

 

Balaraba kuwa a manakinsu take in taga suna wani rawar jiki a kansa,abunda baza ta tab'a iya wa ba kenan, shi kuma dasuke domin shi, baya wani damunsa gwara ma Halisa yana sauraranta.

 

 

 

 

 

Halisa na zaune kusa da k'afafunsa, tana masa magana k'asa-k'asa,yana jinta yayi mata shiru, hannunsa ta  rik'o tana fad'in "Yallabai ka tashi kaci abunci don Allah kar ka kwanta da yunwa"

 

 

Ranshi a b'ace ya bud'e idonsa ya mik'e zaune yana hararata, saurin sakar masa hannu tayi, yace"Wai ni yaro k'arami ne da zaku dame ni da in tashi in ci abunci, ita tazo ke kinzo to me kuke nufi ne"?

 

 

 

Halisa tana jin tsoran masifarsa tace"Umarnin Mama ne"

 

 

Hararata yayi yace" Ko dai umarnin ki, nasan dai "yar aike ta farko da izinin Mama ta shigo, ke nasan neman maganar ki, dan haka ki tashi ki bani guri in inajin yunwa ai baku san sanda zan nemi abuncin ba"

 

Halisa ta bud'e baki zatayi magana kenan Azima ta shigo d'akin.

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

 

____________________

*Attention*⚠⚠

______________________

_Akwai masu kirana a waya suyi min zancan banza, kusani baku kuka aje ni ba,,,, ban san wulak'anci ba,saboda ba halina bane,cikin Ku masoya babu wanda na ware nace dashi nake,mutukar kika turo min sak'o kikaga ban baki amsa ba,to ki min uzuri, kar ki bini ta pravite ki gayamun magana littafin gimbiya balaraba dai nawa ne, mallakina ne,nake rubuta muku da basirar da Allah ya hore min,ina fatan Allah yasa sak'ona ya isa, Hak'ika abunda wata baiwar Allah taimin ya bani haushi wallahi, ta sanadin haka ma na janye typing kwana biyu, saboda haka duk wacce tasan ba maganar arzik'i zatai min ba,to kar ta kirani a waya, idan Gimbiya balaraba take so ta nema a groups,wannan shine magana_

_________________________

_Nagode muku masu bina domin jin abunda ya dakatar dani kwana biyu Hak'ika kun cika masoya na na hak'ika, ina mugun sonku iya wuya ana tare_đŸ„°

 

 

_Ku k'ara yawan comments ku ga redemore goma idan kunk'iyi na tafi hutu, wannan shine magana_________________________

 

 

 

______________________

*Husaini Atk 80k*

______________________

_Allah shine abun godiya ina taya d'an uwanmu Husaini Atk 80k murna da samun nasara daga abokan adawa,ina fatan Allah ya k'ara muku nasara a rayuwarku_

 

 

 

 

 

*🅿86*

 

 

 

Azima na shigowa Halisa ta sha kunu,  kallon banza tayi mata tana hararata k'asa-k'asa tsaki taja tayi saurin zama kusa dashi har jikinsu na had'uwa.

 

 

Azima ta k'araso kusa dashi cikin nata salon tace"Allah ya taimake ka, tuntuni nake so in samu mu zauna dakai Allah bai nufa ba, yau sati na biyu a gidan nan, ban keb'e dakai ba, tun mutuwar  Moddibo komai ya hautsi ne,Allah me yadda yaso a sanda yaso,gashi ya d'auke mana ubanmu maganin kukanmu, ina mik'a ta'aziyata a gurin ka bisa rashin da mukayi gaba d'ayanmu"

Azima ta k'arashe maganar tata tana sharar hawaye.

 

 

Wannan kalamai da Azima tayi sun k'ara mata martaba a idonsa, tabbas tanan Azima tafi Halisa hankali da sanin ya kamata shi a ganinsa, don haka sai ya maida hankalinsa kanta yana amsa mata maganar ta, cikin sakin jiki, yace ta zauna a d'aya gefan nasa.

 

 

 

Azima ta samu guri ta zauna tana k'ara lauya muryarta duk dan tayi dad'i ganin wacce tayi amfani da ita d'azu tayi tasiri a gurinsa.

 

 

Tace" Wallahi mutuwar me Martaba bakai kad'ai akai wa ba,har damu domin munyi rashin suruki nagari,hakik'a har abada baza mu daina yi masa addu'a ba"

 

 

 

Sarki! Gyad'a kai kawai idanunsa a lumshe suke yana jin duk irin rarrashin da Azima take masa,dama abunda yake buk'ata kenan,zuciyarsa ce ta fara yin sanyi, ya bud'e idonsa duka ya sauke su kanta, muryarshi k'asa-k'asa yace"Je ki d'auko min abunci naci"

 

Azima ta mik'e jiki na kyarma, ta girgiza jiki da gayya ta gallawa Halisa harara ganin ta samu nasara, abincin ta d'auko cikin wani irin fulas mai uban kyau da k'yalk'ali.

 

 

 

A fusace Halisa ta mik'e saura kad'an ta fad'i tana kumbure-kumbure ta futa daga d'akin.

 

 

Kallo d'aya yayi mata ya kauda kansa.

 

Azima ta had'a masa abuncin ta zauna kusa dashi yana ci tanai masa hira mai dad'i sai gashi yaci da yawa babu laifi.

 

 

Da kanta ta zuba masa ruwa ya wanke hannusa cikin wani abu mai kyau, ta yago masa abun goge baki ya goge bakinsa,ya mik'e ya koma kan gadon ya zauna yana kallon ta,har ta gyara gurin tazo ta tsaya kusa dashi,cikin nata sallon tace"To zanje in kwanta Allah ya taimaka ka,Don Allah kayi bacci karkayi tunani kaji ko"

 

 

 

Kallonta yayi na minti biyu yace"Karki damu, kije ki kwanta Allah ya bamu alkairi"

 

 

Azima ta juya da niyar futa daga d'akin,  tana wata irin tafiya domin ta d'auke masa hankali

Allah Sarki! Azima ai bai san ma tanayi ba,domin tana juyawa ya kwanta kan gadon rigingine ya lumshe idonsa,,,D'an juyowa tayi a sace taga ko yana kallonta,ganinsa tayi a kwance da ido a rufe, bud'e k'ofar tayi ta futa jiki a sanyaye, ta wani gefan kuma murna take k'untatawa Halisa ita da Mahaifiyarta Madabo,, sauranta Balaraba, Azima na futowa falo ta ga su Halisa da mahaifiyarta a zaune suna magana k'asa-k'asa, d'auke kanta tayi ta shiga wani d'aki harda bugo k'ofa.

 

Mama Fulani da Balaraba dama tuntuni sun bar falon.

Madabo ce tak'i tafiya wai Lallai sai taga futuwar "yarta Halisa.

 

 

K'wafa! Madabo tayi tace" Zanyi maganin ki ne yarinyar banza kawai tana fama rama sai kace jemage babu k'irjin arzik'i, ai da ni wata me fad'a aji ce a wannan gida,dana hana auran nan wallahi"

 

 

Halisa tace" Don. Allah Mamana kiyi masa magana gobe ya hanye maganar auran,ko da ya kuntatawa Baba Waziri , kamar yadda ya k'untatawa mahaifinsa"

 

 

 

Madabo tace"Rabu dashi gobe idan Allah ya kaimu zan masa magana ai yana jin magana ta"

 

 

 

Halisa tace"Allah yasa ya d'auki maganar taki Mamana"

 

Madabo tace"Ameen ke dai"

A ranar Azima kwanan farin ciki tayi yayin da Halisa ta kwana bak'in cikin abunda Azima tayi mata.

 

 

 

Bacci mai cike da rud'ani da mafarkai shi Balaraba tayi a ranar,  Asubar fari,ta farka jikinta.yayi sharkar da gumi tamkar babu Ac a d'akin,wani irin nauyi kanta yayi mata, ta dad'e kan gadon tana sak'awa da kwance wa,wani irin mafarki tayi mai tsananin rud'u da tashin hankali,abun mamaki kuma so take ta tuno ko menene takasa tunowa gashi dai tasan tayi, k'arfin addu'a ne ya tada ita tsaye, toilet ta nufa domin yin wanka da alwala .

 

 

Bayan idar da sallahr Asubah ne. Suna k'okarin futowa daga masallacin wani bawa ya k'araso gurin da sauri, ya zube gaban Sarki! Muryarshi na sark'ewa yace"Ranka ya dad'e babu lafiya shashen Uwar gida Hajiya Kulu, yanzu-yanzu Naja'atu da Fiddausi suka fad'i kwata-kwata sun daina numfashi sai wani abu dake futa daga bakinsu"

 

 

Hankali a tashe Waziri da Galadima suka nufi shashen Kulu. Shi kuwa Sarki! Abun ne ya fara bashi mamaki, da kuzari a jikinsa shima ya nufi shashan,sauran mutanen dake gurin suka rufa masa baya,, Yanayin yadda yake tafiya cike da jamurta yasa har yazo ya Tatar dasu,bai saurare su ba,ya kutsa kai cikin falon..

 

 

Fiddausi da Naja'atu ne kwance a k'asan tayal sun mik'e samb'al basa nuffashi, Kulu ta tasasu agaba tanata kwarma ihu! Kamar gaske.

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿87*

 

 

 

Jakadiya Ladi ce ta k'araso gurin hannuta d'auke robar ruwa me sanyin gaske, bud'ewa tayi zata zuba musu, Galadima ya buga mata tsawa yana fad'in  "Kar ki zuba musu ruwa,  gawa ba a zuba mata  ruwa"

 

 

Ihu! Kulu ta kurma ta mik'e tsaye a zabure! tace"Au! Ashe da gaske sun mutu? Wayyo na shiga uku na lalace ni Hauwa Kulu"

 

 

Waziri ya tsuguna yana duba gawar su Fiddausi cikin zuciyarsa yana tunanin shi kuma a cikin "yayansa ko suwa Aljani Mak'asudu zai tsotsewa jini oho.

 

 

Ihu kawai kake ji a b'angaran Hajiya Kulu babu me salati a cikin mutanan ta, lokacin k'ank'ani mutuwar su Fiddausi ta watsu a gidan, Ihun da Hajiya Kulu take ne ya b'atawa Sarki! rai kawai sai ya fuce daga shashan cike da b'akin ciki da damuwa.

 

Wannan al'amari ya tayarwa da kowa hankali, Mussaman Sarki!, Cike da damuwa a kai wa su Fiddausi suttura aka kaisu makwancin su, bayan an dawo daga makabarta Waziri ya shige fada ya zauna kan kujera tare da jama'rshi,, kafin kace kwabo "yan zaman makoki suka fara gulma,har da masu zuwa inda Sarki! Yake zaune suna fad'a masa ga Waziri can a fada bayan kuma Governor yace" Kujerar ta shi ce.

 

 

Sarki! Yace"Suyi hakuri su kyaleshi tukkuna a kwana biyu komai zai dai-dai ta, dama shi Galadima baya goyan bayan Waziri shiyasa basa shiri sosai, yanzu ma yana kusa da Sarki! Suna karb'ar gaisuwa.

 

Bayan sadakar uku Hajiya Kulu Duniya sabuwa saboda a yanzu kud'i baya yanke mata motsi kad'an zata sa a kira mata Sarki! Tace zata ciri kud'i dole ya bata, ko yak'i ko ya so,  watarana in ta umarshi da yayi Abu baya sab'awa umarnin ta,, Mama Fulani kuwa duk dan a zauna lafiya take k'ara tursasahi idan ya bujirewa bukatar Kulu wataran.

 

 

 

*******

 

Sati biyu da rasuwar su Fiddausi, su Latifa da Iklas sauran "yan matan dake gaban Kulu kenan,suka fara rigimar dole a raba musu gado suna so su fara kasuwanci,nan Hajiya Kulu tasa ai mata kiran Sarki! kan buk'atar " yayanta.

 

 

 

Bayan Sarki! Ya gama sauraron maganganun Hajiya Kulu kan rabon gado,sai yace mata ta kwantar da hankalin ta insha Allah za'a raba a cikin satin nan, yayi mata sallama ya tafi, yarasa me yasa idan yana gabanta baya iyayin katab'us.

 

 

Limamai da shedu ya Tara kan rabon gadon akayi shi cikin adalci inda Sarki! Ya tashi da kusan rabin dukiyar me Martaba had'e da kadarorinsa, a matsayinsa na Namiji matan ma aka basu abunda Allah ya sharanta,, bak'in ciki kamar ya kashe Hajiya Kulu dan haka a daran ranar ta nufi gurin Tsito domin ta nemi shawarar yaya za'ayi.

 

 

Tana zuwa Tsito ya bushe da dariya yana fad'in dama nasan kina tafe ai"

 

 

Kulu ta zauna tana sauke nuffashi tace"Dole inzo gurinka domin ka had'ani da Mak'asudu yanzu anyi rabon gado komai yaron nan ya kwashe mu mun tashi a tutar babu"

 

 

 

Tsito ya kece da wata mahaukaciyar dariya yana fad'in gaskiya Hajiya kina dan son kud'i sosai, Mak'asudu na jin ki kuma yanzu zan had'aki dashi"

 

 

Ai kuwa Kulu ta gyara zamanta Mak'asudu ya hauro ya fara magana kamar haka" Kinzo kan wannan yaron Wanda ya tsaya miki a zuciya ko"?

 

Kulu ta d'aga kai, yace"Kije kawai zaki samu yanda kike so akansa ko yau kuka karar da dukiyarku, daga zarar kin tambaye shi kud'i zai baki jikinsa na rawa"

 

 

Kulu ta dunga godiya sosai Aljani Mak'asudu yace"Ki kawo min k'wai d'anye goma sha d'aya yanzu zan sha"

 

 

Kulu ta mik'e da niyar tafiya tana fad'in "Yawwa yanzu kuwa zan aiko Ladi dashi, godiya nake Ubana"

 

 

******

 

 

Ina labarin su Shamsiyya ne?

 

 

Satin Shamsiyya d'aya a gurin Arrama kullum ta Allah zai bata wannan rubutu yace ta shafa jikinta, sai yaga ta b'ingire yazo ya kwashi gara, ya wani murmure saboda yana samun biyan buk'ata yadda ya kamata yanzu tunaninsa yaya za'ayi ya kafe Shamsiyya s gidan,Ku kuma ta dunga kawo kanta gurinsa dole sai yayi aiki a kanta.

 

 

Shamsiyya duk ta rame ta figale sai uban nonowa da suka cika k'irji ta futo daga k'aramin d'akin cikin shirin tafiya tunda dama tun daran jiya yace aiki ya fara ci, saboda haka zai sallame ta amma ta dunga zuwa lokaci zuwa lokaci domin a dunga dubawa.

 

 

Godiya sosai take masa, yace"Kinanan zaune zai zo gurinki yace ke yake son aura ba waccan ba"

 

 

Cikin rashin dabara da wayo Shamsiyya taita zabga godiya tayi masa sallama ta tafi, tana cike da farin ciki ganin bukatat ta takusa biya

 

 

 

*******

 

Lantana ce ta tafi mak'abarta da kanta

Ta samo k'asar sabon kabari ta kawo aka had'a maganin kamar yadda Arrama ya bada umarni, suna sauraron dawowar Shamsiyya

 

 

Shamsiyya ta dawo gida cike da farin ciki da annushuwa domin ta gazgata maganar Arrama gani take kamar ta auri Sarki! ta gama, Uwa! Taga duk ta rame ba kamar ranar da suka tafi ba, amma labarin da Shamsiyya ta bata na samun nasara yasa bata wani damu ba, suka cigaba da kulla yadda al'amarin zai kasance.

 

 

Sun yanke shawarar cewar Lantana ce zataje can gidan me Martaba domin ta gabatar da aikin nata,, Shamsiyya tace" Ai naji dad'in mutuwar me Martab  wallahi ko babu komai zan sake kuma ina sa ran zan auri Sarki! Domin na san d'anshi ne zai gaje shi"

 

 

"Bari ke dai " yar nan, ai bake kad'ai ce kikayi farin ciki ba har damu mun kusa hutawa dai da talauci mutukar kika auri Sarki! Ai kakarmu ta yanke sak'a"

 

 

Shamsiyya ta washe baki cike da farin ciki tace"Lantana ke zan fara kaiwa aikin hajji,domin ina ganin in bata dalilina ba,har ki mutu baza kije maka ba"

 

 

Lantana tace"Aikuwa dai ni kaina nakan fad'i haka,wallahi wannan bak'in talaucin namu ya ishe ni"

 

Dariya Shamsiyya tasa,, tana fad'in wai ina Babanmu ne"?

 

 

Tab'e baki Uwa! Tayi tace"Gashi can a kwance yau da lafiya gobe babu, sai kace me cutar farfad'iya kullum fad'uwa miyau na zuba"

 

 

Shamsiyya ta lek'a d'akin da Sallau yake kwance ta ganshi kan tabarma ko fulo babu,miyau sai dulala yake. Yana ganin ta ya d'ago mata hannu wai tazo,Shamsiyya ta mak'e kafad'a tana fad'in "Wallahi bazan zo ba Tabb! Ji wani zarni da d'akin yake,aini yau bazan kwana a d'akin nan ba, d'akin Wacan shegiyar zan bud'e in shiga in kwanciya ta"

 

 

Uwa!tace"Yo ba dole kiji zarni ba idan iskancin sa ya tashi nan yake sakar min futsari ke har guntin kashi sai ki gani a jikin wandonsa sai kace wani k'aramin yaro,duk yabi ya sakwarkwace aikin banza kawai"

 

 

Dariya sosai Shamsiyya take harda hawaye tana fad'in Lallai ba, tsufan ka da kallo tabdijam harka fara kashi da futsari aiko zan hayo masu jinya, domin ni bazan yi aikin kashi ba"

 

 

Uwa! Taja tsaki tana watsawa Sallau harara yana cikin daki yana kallon ta yana kuma jin duk abunda suke cewa bakin ciki kamar ya kashe shi,Uwa! Ta cigaba da cewa"Ai na kunshi takaici wallahi. da kike ji daga ni ko a gado wancan uban naku  babu abunda yake iya tsinana min sai dai inyi kid'ana inyi rawa ta, solob'iyo kawai,, in banda shan taba babu abunda yasa a gaba"

 

 

Cikin dariya Shamsiyya tace"Tab!! Uwa! A lokacin ki kin tsula tsiyar ki. yarda kike so,ai daga ni babu sauk'i waiiii''

 

 

Uwa tayi shewa tana fad'in "Ke rabu dani dan ubanki, ko yanzu garau nake ji na,zan iya da d'an shekara goma sha bakwai ma"

 

 

Shamsiyya ta zare ido tace"Kice kawai Babanmu ya wulla kawai ki sha shagalin ki"

 

Duka Uwa! Ta kai mata suka sa dariya tamkar wasu k'awaye,Allah yasa lokacin da suke wannan zancan Lantana ta tafi siyo kalanzir d'in futalar ta.

 

 

Shamsiyya ta mik'e tana fad'in bari inje in kwanta wallahi duk jikina ciwo yake yi"

 

 

Ganin tayi hanyar d'akin Balaraba na da yasa gaban Uwa! Ya fad'i tace"Ashe zakuyi rigima da Walidi domin wannan d'akin da kike k'okarin shiga ya dawo nasa.

 

 

Shamsiyya tayi mata wani irin kallo tana fad'in aikuwa bai isa wallahi domin bazan iya shiga cikin zarni da warin kashi in kwana a ciki ba"

 

 

Uwa! Tace"Mu da muke kwana a ciki me ya cimu, kin san halin Walidi sarai ba saurara miki zai ba"

 

 

Shamsiyya ta juya tana bud'e Kofa tana fad'in "Sai kiyi kuma"

 

 

Uwa! Tsoran fushin Walidi take domin yanzu kusan shine yake d'aukar nauyin gidan,Saboda ita yanzu duk jarinta babu ta karar dashi gurin Arrama, da siyawa Sallau magani, Sai Mabaruka ta dawo daga yawon tallanta watarar suke cin abunci da d'an abunda ta samo.

 

 

Shamsiyya na bud'e d'akin Walidi ya shigo gidan cikin sallama......

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

________________________

_Gaisuwar Ku daban ce, mutanan kirki, a gaskiya inajin dad'in addu'oin da kuke min  Wallahi nagode sosai da sosai,Allah ya kara zumunci_

_______________________

*Takwara ta: Hajiya Binta Shitu*

 

*Hajiya Indo Amadu*

 

_Wannan pege d'in naku ne, kuyi yadda kuke so dashi, nice taku Binta Umar AbbaleđŸ€đŸ»_

_______________________

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿88*

 

 

 

Da sallama a bakinsa ya shigo gidan, ganin Shamsiyya yayi a k'ofar d'akinsa tana k'okarin bud'ewa. Da sauri ya k'arasa gurin yana fad'in "Ke mai zaki min a d'akina ne,? sai kace wacce kika bani ajiya zaki bud'e min d'aki,wai ni garin yaya akai ma na tafi na bar d'akin a bud'e?

Ya k'arasa maganar tasa yana kallon Uwa! Cikin tuhuma.

 

 

Diriricewa Uwa! tayi, baki na rawa tace" Yo in banda ka fad'a ma yanzu ni bansan a bud'e ka bar d'akin ba"

 

 

Tsaki yaja ya juya yana kallon Shamsiyya cikin sigar rashin mutumci yace"Kinje kin gama yawon barbad'ar ki kin dawo gida zaki cigaba dai mana sace-sacen da kika fara ko"

 

 

A hasale Shamsiyya ta juya kamar zata kai masa duka tace"Kayi k'arya in maka sata wallahi, Yo ina abun yake banza shashasha kawai Kai har wani kud'i ne da kai wanda za a sata d'aki duk kud'in cizo da kwarkwasa"

 

 

"Kya k'araci sharrin ki dai ki matsa ki bamu guri banzaye masu mugun b'akin jini, duk sai an aurar da " yan matan unguwar nan kuna zaune a gida,saboda mugun bak'in halin ku"

 

 

Tsabar bak'in ciki yasa Shamsiyya fashe da kuka tana kallon Uwa!tace"Kinajin irin cin mutuncin da yake min ko,kin ja bakin ki kinyi shiru"

 

 

 

Uwa! Tace" Me zan ce miki ai na fad'a miki tun kafin ki tunkari k'ofar d'akin, kin san halin Walidi farin sani"

 

 

Buge hannun ta yayi daga jikin k'ofar ya bud'e abunsa ya shiga yana fad'in, Balaraba dai ta huta da bala'in ku shegu sai ku k'araci bak'in cikin ku mutu"

 

 

 

Rashin abunyi yasa Shamsiyya ta dunga k'unduma masa ashar! sai kace "yar maguzawa,yana jin ta yayi mata banza,ita kuwa sai sake fad'i take Cewar wallahi duk ranar da tayi aure Walidi yazo yace ya santa sai tasa and'aure shi, yana daga cikin d'akin yana mata dariya,domin shi yanzu d'aukar mahaukata yake musu ita da Mabaruka,ganin har yanzu sun kasa gane gaskiya, dama shi Iro ba'a sashi cikin lissafin mutane masu nagarta.

 

 

Nan suka zauna har aka kira sallahar magariba mutan gidan suka fara dawo wa, Iya ta dawo daga gidan jikarta domin yanzu can take wuni saboda haihuwar da tayi,dake gidan babu nisa dasu.

 

 

Ita kuma Sadiya Matar Kawu Maman, tana zuwa nany ne wata makaranta pravite tana d'aukar albashinta me tsoka, shiyasa bata da damuwa ta wanke goma ta tsoma biyar babu abunda ya dame ta.

 

 

 

Uwa! Tayi tayi ta raba Sadiya da gurin aikinta Allah baiyi ba, ta k'ulla munafurcin da Sharrin duk Allah bai amsa ba,haka dai ta hakura amma tana bala'in jin haushin ace k'arshen wata yayi Sadiya ta shigo da kud'in ta, tayi cefane me kyau suci su sha ita da mijinta, ta zubo ko babu yawa ta kaiwa Lantana. Ita kuwa tai ya murna baki zai sauya abinci.

 

 

 

 

Sai wajan goma da rabi Mabaruka ta dawo gidan hannunta nik'i-nik'e da manya-manyan ledoji, cike da fara'a ta zauna kusa da mahaifiyar tasu, wacce take ta washe baki tana k'okarin bud'e ledojin kana ganinta kasan tana cike da farin ciki yau zasuci kayan dad'i da alama Shamsiyya tayi sabon saurayi"

 

 

 

Jin motsin Leda yayi yawa a tsakar gidan,yasa Lantana rarrafowa ta futo, domin taji sallamar Maburuka tabbas tasan ta kawo kayan dad'i, ilai kuwa tana futowa tayi arba da wata k'undumeniyar kaza gasashiya taji k'uli-kuli da tumatur da albasa,Uwa sai k'okarin kaiwa bakinta take.  Lantana ta dunga washe baki tana fad'in Allah yasa banyi bacci kam,tun d'azu bacci yake so ya kwashe ni,Allah bai nufa ba"

 

Zam tayi gefan Maburaka tana tai mata banbad'anci Mabaruka ta ciro cinya da hak'arkari ta bata, sannan ta bata robar yoghot guda d'aya, tace"Shikkenan na sallame. Ki tashi kije ki kwanta"

 

 

Lantana ta mike tana. Fad'in "Ai ko baki fad'a 'yan nan, Allah ya bamu alkari"

 

 

Babu wanda ya kulata a cikinsu duk suna can suna rubibin cin gasashiyar kaza me maik'o

 

 

Sai da suka kusa cinyewa sannan suka tuna da Sallau, Uwa! Tace"Wannan ragowar k'ashushuwan sai ku barwa babanku ki"?

 

 

Shamsiyya tace"Wallahi ni har na manta ma dashi"

 

Tab'e baki Uwa! Tayi ta mike tsaye tana niyar shiga d'akin take fad'in kin manta dashi ko na manta dashi, ummm".

 

D'akin ta shiga,Mabaruka ta mik'e da Sauri,jiri yasa ta dafe bango sai da tayi minti biyu sannan ta d'an dawo dai-dai, cikin yanayin maye ta k'arasa bakin rijiya ta ja ruwa ta zuba a buta ta shiga band'aki.

 

Lokacin da suka gama alfashansu da saurayin batayi wanka ba,ko da yake a cikin motarsa suka yi komai, babu gurin wanka dole sai ta dawo gida.

 

 

 

***************

Yau sati biyu da rasuwar su Fiddausi mutuwar me Martaba kuma ta kasance sati uku,, Waziri ya saki jiki sosai kullum yana zama a fada sai dare yake tashi sosai ya jinjinawa Mak'asudu domin da yarjewarsa ya samu nasara, tun bayan mutuwar su Fiddausi Mak'asudu bai k'ara tsotsewa wani jini ba,ya bari ne k'ura ta lafa, amma yana sane da iya adadin mutanan da akai masa alk'awari.

 

 

Komai yana tafiya dai-dai ta b'angaran Hajiya Kulu ita da yaranta, biyu daga cikinsu ma sun kaso auransu sun dawo gida, kullum sai su shirya su futa basa dawowa gida sai dare can,wani lokacin ma a can suke kwana. Hajiya Kulu kuwa kullum tana tare da k'awayenta "yan duniya sosai suke shek'e ayarsu Hajiya Kulu ta zama k'umgurmar " yar lesbian, sosai take jin dad'in harkar shiyasa take ganin babu wani dalili da zai sa ta tadaina more rayuwarta yanzu ta fara, k'awarta Hajiya ta Masu, itace take kawo mata "yan mata zuguda-zuguda. Sai ta biya ta kudi masu tsoka.

 

Kuma duk abunda ta tacewa Sarki! Ya aikata sai ya aikata shi,domin baya tsallakewa umarnin ta.

 

 

 

******

 

Yau saura kwana uku d'aurin auran  Sarki! shine dalilin da yasa gidan ya hautsine da shirye-shirye b'angaran Mama Fulani ma haka bayi sai shige da fuce sukeyi, Mama Fulani taso Sarki! Ya d'aga lokacin d'aurin auran sai bayan futarta daga takaba. Yace tayi hakuri kawai a d'aura yanzu burinsa kawai a d'aura auran ya wuce gurin domin sunyi magana da governor maganar zama a fada yace sai bayan auransa wannan zai fara zama domin shine cikar mutum, wannan magana da Sarki! Yayi itace ta kashe masa jiki, yasa ya hak'ura kawai,amma sam baya kaunar ganin Waziri kan kujerar mulki domin sam bata dace dashi ba.

 

 

 

Halisa na keb'e a wani guri, a cikin gidan dai, Madabo da sauran " yan uwansu suna kula da ita tare da gyara mata jikinta sosai domin Madabo tace "yar baza tayi boranci ba,dole sai tafi sauran matan da zai aura shiyasa tasa ake had'a ta sosai

 

 

To itama Azima tunda aka fara hidamar bukin ta tafi garinsu domin ta shirya tsaf, duk da yake ita kullum cikin shiri take Mamanta ma ba a zaune take ba.

 

 

 

Su Shahid da Shatima ne suke fad'i tashi tare da shige da fuce, ganin ko wacce a bata hakkinta a kwatuna iri d'aya suka siyo irin me sha biyu nan, duk a bubuwan dake cikin d'aya a kwai a cikin d'aya,Kai dai-dai da kayan bacci iri  d'aya suka zuba musu, takalma mayafai gasu nan birjik,gaskiya sun had'a musu kaya kamar hauka.

 

Mama taji dad'in k'okarin dasu Shahid sukeyi domin in ta Sarki! Ne sai dai a d'aura auran babu lefe sam taga bashi ne a gabansa ba.

 

 

 

" Yan uwa da abokan arzik'i Mama ta kira suka mik'awa ko wacce nata Balaraba dai nata suna gaban Mama,inda tayi-tayi da ita tazo ta duba kuma ta d'ibi wanda take so a d'inka mata Balaraba kunya duk ta hanata, haka Mama ta hak'ura ta kira Jakadiya Shafa'atu ta d'ibar mata atamfofi da lesuka masu kyau da tsada a ka kaiwa masu d'inki.

 

 

 

Yanzu Balaraba bata futowa falo sosai, kullum tana d'aki a kulle indai ba Mama CE take kiranta ba bata futowa saboda wata irin kunyar ta da take ji,Su Sadiya kuwa ai sun zama "yan gari sun saba da Mama sosai hakanan Jakadiya Shafa'atu in zata wani guri sai ta tafi dasu domin suga gari.

 

 

 

Shi kansa Sarki! Ya kwana biyu bai sanya ta a idonsa ba, daurewa kawai yake amma kwanakin nan yana yawan jin fad'uwar gaba idan ya tuna da ita,kasancewar shi mutum ne Wanda baka ganin damuwarsa sai ta kai ta kawo shiyasa lokaci guda baza ka fahimci halin da yake ciki ba.

 

 

 

*********

 

Misalin hud'u da rabi na yamma Balaraba na zaune gefan gado tana duba wani k'aramin littafi irin na addu'oi, tana sanye da wata doguwar riga mai uban kyau da tsada rigar taji stone masu shek'i wuyanta da hannuta tayi amfani da k'aramin hijab irin me hulan nan fari k'al dashi, dai-dai kafad'arta ya tsaya, fuskarta tayi fayau sai annuri ne yake sauka, dama can ita wannan kwaliye-kwaliyen bai dame ta ba,ko Wanka tayi k'ark'ari ta shafa mai sai hoda,da kwalli sun ishe ta, amma fa akwai son k'amshi jidin jikinta na k'amshin turare.

 

 

 

Sadiya ce ta shigo da saurinta tana fad'in "Yayarmu kizo inji Mama,wai zaki kaiwa Magajin Sarki! Abunci yana zazzab'i"

 

 

Balaraba gabanta ya fad'i jin abunda Sadiya tace, tace"Wai ke ba na hanaki rashin kamun kai ba, don Allah dube ki sai wani rawar jiki kike yi"

 

 

Sadiya ta sunkuyar da kanta tana jin tsoran fad'an yayar tata.

 

 

"Karki k'ara shigowa babu sallama kuma ki daina wannan gudun da kikeyi"

 

Sadiya tace "To"

 

Ajiye littafin tayi kan gadon ta mike tsaye tana gyara zaman hijab din nata,tace"Yana ina ne Magajin Sarkin"?

 

 

"Yana shashensa tare da abokansa,muma bamu dad'e da dawowa ba ni da Usuman tun d'azu muna can"

 

 

 

Ita fa bata son zuwa shashensa gudun abunda ka iya zuwa ya dawo ta lura wani irin mutum ne shi, me saurin tab'a jikin mace ko haka yakewa sauran matan oho shi dai ya sani, amma dole zata kiyaye ta daina sakar masa jikinta.

 

_Niko nace Balaraba kenan maganar sakin jiki ta k'are tunda an kusa d'aura aure_

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

______________________

*Tsokaci*

______________________

 

*_Tun farkon farawa na fad'a cewa ban rubuta littafin Gimbiya Balaraba domin in ci zarafin wani ko wata ba, ku wani jinsi mutum me k'iba ko siriri, wannan labarin k'agaggene daga ni, Binta banga dalilin da zaisa kawai in ci mutum cin wani jinsi ba,kamar yadda wata "yar uwa ta fad'a min, Asali ma, wannan jinsin mutane da take magana akan su ina cikinsu to kun gani idan naci musu fuska har dani a cikinsu, Allah da kan shi ya hallici d'an Adam kuma ya karrama shi, duk a cikin hallitunsa ni Wacece da zanyi ciwa hallitar Allah fuska,, labari ne kawai saboda haka don Allah mu San abunda zamu dunga fad'a akan " yan uwanmu_*

 

 

 

 

 

 

 

*🅿89*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Mama Fulani na zaune a falo ita da Jakadiya Shafa'atu suna hirarsu cikin mutun ta juna.Balaraba ta futo a nutse ta k'araso inda suke ta tsuguna tana gaishe da Fulani.

 

 

Cikin "yar fara'a Mama Fulani ta amsa, tace" Dama nace Sadiya ta kira ki kaima Mutumin ki abunci yana can shashensa tare da abokansa su Shahid,watak'ila ya fi maida hankali yaci abuncin, tunda bashi kad'ai bane"

 

 

 

Cikin jin nauyi gami da kunya Balaraba tace"Mama Sadiya tace bashi da lafiya yana zazzab'i"?

 

 

 

"Ba wai bane, da gaske ne, yau ya tashi da zazzab'i amma dai yanzu nasan jikin da sauk'i tunda d'azu ma ya shigo mungaisa"

 

 

 

Balaraba ta mik'e tana fad'in Allah ya sawak'e, Mama ina abuncin yake"?

 

 

 

Can wani katafaran gurin cin abunci ta nuna mata tace "Kije ki had'a masa,amma yace nacin mutum uku za'a had'o in yaso in kika gama sai ki kira d'aya daga cikin " yan matan dake aiki a waje ta d'aukar miki'

 

 

Balaraba tace"To ta mik'e ta nufi gurin cin abincin.

 

 

A nutse ta had'a masa komai yadda yace d'in, Mama tasa Sadiya ta kira wata baiwa me suna Lahira ita tazo ta d'auki kwandon abincin suka futa tare da Balaraba.

 

 

 

 

Tun washe garin rasuwar Maddibo rabonta da b'angaransa shiyasa yanzu da ta shigo taji gabanta yana fad'uwa tunowa da tayi da rayuwarsu da Moddibo wasu hawaye ne masu zafi suke k'okarin zubo mata, ta fara k'okarin mai dasu,,.

 

 

 

 

Wasu k'yatattun takalma ta gani a bakin k'ofar shiga falon, kuma tana d'an jin magana a ciki, sai ta gyara yanayin ta,ta koma Balaraban ta ta asali, cike da jarumta tayi sallama ta shiga falon, Rahila na biye da bayanta.

 

 

 

Yana kishin gid'e cikin wata shirgegiyar kujera,me kamar k'aramin gado da wasu k'ananun fililluka a kai,  daga shi sai boxar da k'aramar shart me k'aramin hannu,abunda yasa yayi wannan shigar saboda jin jikinsa ya d'auko zafi gumi sai zuba yake,dalili yasha maganin zazzab'i shikkenan gumi sai karyo masa yake ko ta ina,shine fa yayi Wanka ya sanya k'ananun kaya,yazo ya ware AC har suna rigima da Shatima saboda k'arfin AC d'in yayi yawa,shi kuma yace ya rabu dashi haka yake so.

 

 

 

Hira suke irin ta abokai Sarki! Yana daga kishin gid'e yake sa musu baki, zumbur! Ya mik'e da sauri ya nufi tv memory ya zura jikin DVD ya kuna sai gasu shida Maddibo sun bayyana jikin faskekiyar TV plasma dake manne jikin bango, suna zaune cikin makaranta a can america new york, can sukai karatunsu, wani abokinsu ne me yawan yi musu photo da vidio, ranar dai Sarki! Ya samu memori ya bashi yace duk sanda suke zaune shida Moddibo suna karatu ko suna wani abun Ku suna hurawa to kawai ya dunga d'aukar su a hota ko yayi musu video aiko Ashir baya gajiya mutuk'ar yana kusa idan yagansu sun keb'e kawai sai ya ciro memori a zura a wayarsa yayi tai musu hotuna had'e da video.

 

 

 

Shahid da Shatima duk sun rud'e ganin Moddibo jikin tv kamar kayi masa magana ya amsa,kai wannan duniyar abar tsoro ce.

 

 

Balaraba na shigowa idanunta suka sauka akan fuskar tv Moddibo tayi tozali dashi yanai wa Sarki! Magana yana dariya

 

 

Kwandon da yake hannuta ta saki ta k'wala k'ara jikinta ya fara k'arkarwa, "Inallahi wa'ina ilahi raji'un"

Jin gina tayi da bango tana sauke a jiyar zuciya bakinta sai motsi yake.

 

 

 

Dukaninsu kallon ta suke sosai saboda ba suji lokacin da ta shigo ba, sai ihunta da sukaji Shahid ya zubawa fuskarta ido yana tunanin a ina yasan fuskar tabbas yasan me wannan fuskar

 

 

 

 

Shatima kuwa gulma yake son yayiwa Sarki! Sai ya lura babu fuska yaja bakinsa yayi shiru,amma fa bakinsa da akwai magana, domin yana kokwanton anya ba wannan ce,Balaraba da yaji Mama tana yawan ambatar sunanta ba.

 

 

 

Tv take kallo babu k'iftawa wasu hawaye masu zafi suna biyo kumatunta. Maddibo ne yake magana tamkar ta kirashi ya amsa mata.

 

 

 

In banda sautin kukan Balaraba babu abunda yake tashi a falon, Tsura mata ido yayi babu k'iftawa, wato har yanzu yarinyar nan bata far kukan mutuwar Moddibo ba kenan,a ganinsa ta shigo musu babu sallama kuma tazo tanai musu kuka babu gaira babu dalili.

 

 

Shatima ne da ya fuskanci kukan me take ya tashi da sauri yaje ya kashe tv d'in ya dawo ya zauna yana mamakin ta.

 

 

 

Shahid ne ya mik'e ya k'arasa inda take tsaya ya fara rarrashinta da kalmomi masu sanyaya zuciya, ya jima yana tausar zuciyarta sannan tayi shiru tana share hawayen ta, k'okarin futa take ba tare da tace musu komai ba.

 

 

Shahid yace"Ranki ya dad'e ai baki bamu abuncin ba, zaki futa kuma bamu gaisa ba, ya kamata kizo ki duba mutumin naki kafun ki futa"

 

 

 

Shahid yana da k'ima da mutumci a idonta, ta lura yasan abunda yake, kallonsa tayi babu yabo babu fallasa ta gaishe ya amsa fuskarsa a sake, tare suka jera suna tafiya har cikin falon.

 

 

 

D'auke kansa yayi daga kansu, yarinyar yau tayi masa kyau sosai tamkar wata balarabiyar k'asar saudia shigar tayi mata kyau, yana so ya ga mace na suturce jikinta.

 

 

 

Hannuta rik'e da kwandon abuncin ta nufi gurin cin abunci,shi kuma Shahid ya zauna kusa da Sarki! Suna magana k'asa-k'asa.

 

 

 

Mik'ewa yayi yana mik'e duk jikinsa ciwo yake masa, Tashi sukayi suka bi bayan sa.

 

 

 

Tsaf! Ta had'a musu kowa da plate d'insa, ta kalli Shatima da yake satar kallonta sosai yarinyar tayi masa kwarjini da yawa.

 

 

A nutse tace"Ina wuni"?

Shatima ya amsa da sauri sai murmushi yake yace"Lafiya lau amaryar mu, yo ke haka ake daga shigowa sai ki fara kuka uhum"?

 

 

Shiru tayi tana satar kallon Sarki! Da yake juya abunci da alama yunwa yake ji, tunda yake Neman abunci da kansa, tarasa wani irin mutum ne shi da baka gane gabansa da bayansa fuskarsa a sake take amma ko da wasa yak'i kallon inda take, abuncin sa yake ci kawai, su Shatima sun rik'eta da suturutu ita kuma tana ta k'okarin yaya za'ayi ta gudu domin mutuminta da yayi mata wani mugun kwarjini gashi tana so ta gaidashi amma babu fuska. Da k'yar dai tace" Barka da yamma"?

 

 

Shiru gurin yayi su Shahid suna kallonsa sun san da shi ake"

 

 

Lumshe idonsa yayi ya cigaba da cin abuncin sa, bai amsa ba. Shatima yace"Ana magana fa"

 

 

Da gefen ido ya kalleta ya d'an tab'e bakinsa yace" Naji ai bazan amsa ba, tunda duk sai da ta gama wulak'ancin ta sannan"

 

 

 

Shatima yace"Amarya ce fa kasan amarya bata laifi komai tayi dai-dai ne"

 

 

Wani irin kallo yayi mata me d'auke da ma'anoni daban-daban yayi wani murmushi irin na gefan baki,yace"Ai ba ita kad'ai gare ni ba, Anjima kad'an nasan Halisa nan tafe,kaga kuwa ai bazan damu ba"

 

 

 

Balaraba sarkin d'aukar zafi! Fuska ta turb'une  duk idanta ya rufe,wani kallo ta watsa masa,suka had'a ido dashi, tsaya wa yayi yana mamakinta, wani irin Abu tayi da idonta ta kalli su Shatima muryar ta a cunkushe tace"Ni zan wuce ku tashi lafiya"

 

 

 

Sauka tayi daga kan step d'in ta fara tafiya a nutse zuciyarta duk babu dad'i ta lura Sarki! Zuma ne shi ga zak'i ga harbi,dubi yadda kwana ki ya dunga lallab'ata har tana yi masa d'aukar mutum me saukin hali a she ba haka bane,wannan halin nasa nan, halin wulaknci da raina mutum,yo ita ina ruwanta ko mata dubo zai aura a rana d'aya ba damuwar ta b'ace,shine bai sani ba ita tafi sha'awar zamanta a haka tunda tayi rashin babban masoyinta Modiibo.

 

 

 

Shatima yace"Allah ya huci zuciyar gimbiyar mata, ai dukaninsu kin sha gaban su, kar ki manta ke fa amanrmu muce,bayan haka kuma kina da babban matsayi a zuciyarmu ki kwantar da hankalin ki.

 

 

Ko waigo wa batayi ba, ta bud'e Kofa tai fucewarta Rahila na tsaye na jiran futuwar ta sai ta take mata baya.

 

 

 

 

Shahid yace"Lallai addu'a ta ta karb'u, wannan yarinyar ba itace wannan yarinyar da sukayi saukar alk'urni shekaru biyu da suka wuce ba"?

 

 

D'aga kansa yayi kawai.

 

Shahid yace"Allah sarki Moddibo Lallai na yarda zuciyoyinku d'aya duk abunda kuke so iri d'aya ne,Allah bai hukunta zai aure ta,ba sai ya kawo maka ita har gida"

 

 

 

Shatima yace"Ni wallahi abunda kayi mata ne ya bani haushi da alama yarinyar tana da hankali da nutsuwa,kawai sai ka ci mata fuska, kasan dole taji babu dad'i a zuciyarta.

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

             _*GIMBIYA BALARABA*_

          đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

                 

 

 

 

                 _*NA*_

 

 

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

_*MARUBUCIAR*_

 

```NANA KHADIJA```

```YARO DA KUDI```

```GIMBIYA BALARABA```

```LOODING......```

             _*TSANTSAR BUTULCI*_

 

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 ____________________

_*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_

_______________________

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_

 

 

 

 

 

*🅿91*

 

 

 

 Balaraba tayi k'asa da idanunta domin baza ta iya jurar had'a ido dashi saboda kwarjini da Allah yayi masa.

 

 

 

Niyar koma dakin take, yayi gyaran murya tsayuwa tayi. Ta d'an waiwayo suka had'a ido lumshe nasa yayi ya bud'e baki a hankali yace"Jimana"

 

 

 

Sak  tayi jin abunda yace wai jimana! Sai kace Wanda bai san sunanta ba.

 

 

 

Ahankali ta taka ta k'arasa inda yake zaune, mik'ewa yayi yana gyara zaman sa,idanunsa a kanta, ita kuma tana tsaye gefansa duk jin ta take a takure, sai gyara fuskarta take.

 

 

 

"Zauna zamuyi magana dake"

 

Cikin k'asaita gami da jan'aji ta zaune kujerar gefansa.

 

Cikin bada umarni yace"Ki dawo wannan domin maganar da zamuyi dake tanada muhimanci"

 

Kujerar da yake nuna mata ta kalla, ita fa bataso tana had'a ido dashi domin. Idanunsa suna mutukar kashe mata jiki. Dakewa tayi tace"Duk maganar da zamuyi muyi ta anan da can da nan duk d'aya ne"

 

 

Shiru yayi na minti biyu, yace"Na fi so ina kallon fuskarki maganar zata fi armashi"

 

Tab'e baki tayi tana d'an hararsa,   minti biyu da maganar tasa ta mike a nutse taje ta zauna kujerar da ya nuna mata, zama tayi irin Wanda ake Dora kafa d'aya kai d'aya.

 

 

 

Kallonta yayi yana mamakin zaman k'asaitar da tayi, babu Wanda ya isa yayi irin Wannan zaman a gabansa, ba tare da ya karb'i hukunci ba, amma da yake ya san halinta sai ya share kawai ya gyara fuskarsa sosai idanunsa ya zuba mata babu wasa yace"Inaso ki yi min bayanin Asalinki dana mahaifiyar ki, domin inajin a jikina akwai wani al'amari a game dake, bazan b'oye miki ba, nafi k'arfin shekara goma shabiyar ina mafarki dake tare da wata mata da alama mahaifiyar ki CE,tunda kullum tare nake ganinku kuna zuwan min cikin mafarkina, wannan mafarkin babu Wanda yasan dashi sai ni sai ke, yanzu Dana fad'a miki"

 

 

 

******

******

******

 

A kori kura guda biyu aka cika da kayan masarufi, su Shatima suka nufi gidan su Balaraba inda suka samu rakiyar daga Bubu direba tunda shi kadai ne yasan gidan.

 

 

Sosai Shahid yayi mamakin inda mahaifar Balaraba take,ashe dama 'yar talakawa ce tilis, Lallai so babu ruwanshi ko a mafarki bai tab'a tunanin zai iya zuwa irin wannan gurin ba, Soyayar da Moddibo yakewa Balaraba ta gaske CE. Tabbas yayi mamaki da ya kalli yanayin jikinta da fatar ta, idan zata kwana tana rantsuwar babu Wanda zai CE a cikin irin wannan guri take rayuwa.

 

 

 

Yara ne suka fara taruwa a gurin suna tsale suna d'ane mota sai su ruga da gudu, hankalin Samar in dake can tsallake ya dawo Kansu da sauri suka k'araso gurin, Buba Direba ya bud'e mota da sauri ya futo ya bud'e wa su Shahid suka futo, ganinsu cikin kayan sarauta yasa yara zurawa da gudu zuwa gidajansu suna ihu! Suna fad'in ga sarki! Sarki ga sarki! Mutane suka fara lekowa daga gidajansu. Da sauri Shahid ya umarci matasan nan dake tsaye a gurin yace su fara d'ibar kayan nan suna shiga dashi, lungun su Balaraba, Buba yayi gaba, sukuma suka koma cikin motar saboda hayaniyar jama'a, yuuuuuu!! Jama'ar dake gurin yara da manya suka rufa musu baya domin ganin ina za a shiga da wannan uban kayan masarufi.

 

 

Lantana ta sawo Kai kenan zata futo daga cikin gidan suka buga karo da Sauri ta koma da baya tana masifa!

 

 

 

Abokin Walidi yace"Lantana ina zakije ne"?

 

 

D'ago kai tayi a fusace za tayi masa masifa"Aik.. Idonta ya sauka kan k'aton buhun shinkafar dake kansa ta bud'e baki kenan za tayi magana, sai ta hango matasa hud'u kowanne kansa da buhun shinkafa irin na kan Abokin Walidi kuma da alama suma gidan zasu kaita,, Zanin jikinta ne ya sabule garin sauri ta buge da kyaure bata damu ba, da sauri ta tsugans ta dauki zaninta da ya fad'i k'asa tana tafiya tana d'aura wa gami da k'walawa Maburuka kira.

 

 

 

 

************

************

*************

 

 

 

A nutse take kallonsa tace"Bangane kullum kana mafarkina ba, a ina kasan ni ka san uwata da har zaka dunga mafarkin mu"?

 

Ta karashe  maganar cikin mamaki.

 

 

"Duk ba wannan na tambaye ki ba,duk wata maganar ki ki aje ta gefe guda ki fara bani amsa ta tunda nine na tambaye ki"

 

 

 

Tab'e baki tayi yana wani murmushi irin na gefan baki nan, girgiza kai tayi ta dago kai tana kallonsa tace"Ni ba wata aba b'ace kamar yadda kake tunani hakanan kuma ni ba "yar kowa bace, Tunda nake da Moddibo bai tab'a turke ni yana tuhumata da dole sai ya San asalina ba,saboda yasan inda yaje ya d'auko ni"

 

 

 

Hararata yayi k'asa-k'asa cikin muskilanci yace"Ni daban Moddibo daban, in zaki fad'a min ki fad'a min banason, bata lokaci"

 

 Ganin fuskarsa babu wasa yasa itama ta gyara tata fuskar ta fara magana kamar haka.

 

 

 

*Sunana Balaraba Ayuba Tanko*

 

Dago kansa yayi yana kallonta sai ya tuna da lokacin saukar al'kuranin ta.

 

Basarwa yayi yace"B'angaran uwa fa"?

 

 

Ranta ya soma b'aci, dakewa tayi tace"Sunan babata Hafasatu, kakata kuma Kaka Suwaiba gurin haihuwar babana ta mutu"

 

 

"Allah sarki, Ubangiji Allah ya jikinta da rahama"

 

Ya fad'a cikin jimami!

 

"Uhumm"! Ina sauraron ki"? Yafad'a yana tsatsare ta da ido.

 

 

Wasu hawaye ne suke k'okarin biyo kumatun ta, Ă  kufule tace" Wai kai dolene sai kasan Asalina in baka aure na a haka ka fasa ai babu dole. Ni ban san asalin mahaifiya ta ba. Shikkenan Malam" mik'ewa tayi zata bar gurin tazo ta giftashi, kamar kububuwa Dan haushi sai nishi. Take, tana tuno Moddibon ta, duk tsawon lokacin da suka dauka suna soyaya dashi bai tab'a turke ta ba, sai wannan Dan rainin hankalin ai babu dole idan bazai aure ta ba sai ya fasa.

 

 

 

Hannu ya rik'e sosai yana murzawa ta sha kunu! Tana fad'in 'sakar min hannuna"

 

 

K'i yayi yanai mata wani irin kallo, me tattare da abubuwa kala-kala a zuciyarsa yace"Ashe dama wannan zafin kan nata yana nan.

 

 

Ajiyar zuciya kawai take saukewa idan da tasan tambayar da zai mata kenan babu abunda zai sata ta tsaya ta saurare shi.

 

 

Mintuna kusan biyar suna a haka bai sake ta ba. Hannusa a cikin nasa , muryarshi bata futa sosai yace"Naji na janye wancan maganar ta baya, tunda ba kyaso amma wannan dole ne ki amsa min ita, lokacin da kina sai da abunci cikin kasuwar sha tambaya maza nawa kika kula"?

 

 

 

*************

**************

***************

 

Mabaruka ta futo daga cikin d'akinsu a sukwane jin irin kiran da Lantana take k'uga mata, fad'i take 'wannan tsohuwa da jaraba take wallahi.

 

 

Lantana ta shigo gidan tana fad'in "Mabaruka kece me mutanan arzki masu kudi da naira, yau wani Dan sutturar daga cikin mutanen ki ya rufa mana asiri ga kayan arzkiki na......Kafun Lantana ta rufe bakinta Zaratan samari suka dunga shigowa da kayan masa rufi buhu-buhu.

 

 

Uwa! Ta futo daga ita sai d'aurin kirji da wata daud'addiyar biriziya duk Tasha d'auri hannuta duk ya saki, kanta inda kasan kan jaka fuskar ta sai maiko takeyi,, wata irin gud'a ta rafka Ayurrrrrrrrrr!!!

 

 

 

*Muje zuwa*

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

 

*🅿92*

 

 

 

 

 

 Uwa! sai zabga gud'a takeyi babu ji babu gani, sai da tayi me isarta sannan, ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya tace"Yau "yan bak'in ciki zasu mutu, nima lokacina yayi, haihuwa tayi min rana, Mabaruka farar aniya farar haihuwa,nasan wannan alkairin kece silar shi"

Ta k'arashe maganar tata tana dafa kafad'ar Mabarukan.

 

Ita kuwa tunani takeyi waye ya kawo mata wannan shatara ta arzkin domin basuyi da wani daga cikin samarin ta ba, wata zuciyar tace mata ko dai Alhaji Saminu ne, mutum da yake so yayi luwad'i da ita.

Nan take ta yardar ma kanta cewa shi d'in ne.

 

Bak'in ciki kamar ya kashe Shamsiyya domin suma a junansu hassada suke ma junansu.

 

Shigo da kaya abunci ake nau'i -nau'i tsakar gidan ya cika, sai suka fara d'orawa akai.

 

Sallau ya rarrafo ya futo duk ya rame ya susuce, ganin uban himilin kayan dake jibge a tsakar gidan yasa ya kusa fad'uwa ya kalli Lantana yana wani irin murmushi yace" Hak'ika Haihuwar Maburuka tayi min rana, yanzu wannan mutsiyaciyar matar zata San ni bak'ashin yar wa bane, ni mutum ne Wanda ya cancan ci a had'a jini dashi"

 

 

Aikuwa Uwa! Tayi kansa da masifa sai kuza masa ashar take tana fad'in k'arya yake ya zage ta ko yace ita ba me kashin arziki bace,

 

Fad'a suke sosai suna fad'a ma junansu bak'aken maganganu, da tada tsohon Abu da ya faru a tare dasu.

 

 

Gidan ya cika da matasa  da yara "yan unguwa kai harda matan aure wasu sun futo daga gidajansu domin su bawa idanunsu hakkinsu.

 

 

Abokin Walidi ne yace" Don Allah kuyi shiru mana arzki yana Neman Ku kuna kokarsa, wannan da kuka gani a zube to ake ne daga gidan me Martaba Almutafah Allah ya gafarta masa.

 

 

Shamsiyya najin abunda abokin Walidi ke fad'a sai kawai ta zabga wani ihu!!! da gudu ta shige d'akinsu tana ihu tana tsalle fad'i yake "An yanka ta tashi, dama ni nasan tunda Arrama yace" In saurara komai zai zo da sauk'i nasan lokacina yayi, tabbas aikinka kamar yankan wuka ne a gurina, Mabarukan banza ina taga arzikin da zata kawo wannan kayan"

 

Gudar dubu d'aya ta futo da ita a hannuta,bakinta kamar gonar auduga ta mik'awa Abokin Walidi tana fad'in "Karb'i tukwuci ai dole ne In biya ka, irin wannan alkairi haka"

 

Karb'a yayi yasa a aljuhunsa yana godiya ya kalli Lantana yana fad'in wasu Samari biyu sunaso su shigo Ku gaisa don haka sai Ku gyara guri"

Yana gama fada r maganar sa ya juya ya futa sauran abokansa da yaran suka rufa masa baya, d'aya bayan d'aya mutane suka futa suna ta gulmar su.

[9/8, 5:19 PM] Akwai CittađŸ’”đŸ’”: Sallau da Uwa! Cigaba da fad'an sukai Lantana tace"Sakarkaru kawai a gaban "yayan Ku kun zauna kuna fad'a ai sai kuje kuyi tayi"

Ta k'arshe maganar tana marmatsar da tarkacen takalman dake bakin k'ofa.

 

 

Sam! Baka jin sallamarsu saboda Hayaniyar Sallau da Uwa! Sai da abokin Walidi ya buga musu tsawa sannan suka dawo nutsuwar su,, suka hau washe baki sunawa su Shatima barka da zuwa.

 

 

Amsa sukeyi cikin mutum ci da karrama d'an Adam, Lantana ce tayi musu iso har rumfar ta, ta shimfida musu tabarma, bakinta kamar ya tsage dan fara'a sai wani sunkuya musu take tamkar wacce za'ayi musu sujjada, shi kanshi Shahid din ya fuskanci abun take yayi yawa, yace"Baba ya isa,ki nutsu kinji zauna sosai magana me muhimanci muke tafe da ita"

 

 

Lantana ta gyara zamanta har da tankwashe kafafu tana fad'in "To Allah ya jisshemu alkairi, ko da yake ai alamar karfi tana ga me k'iba, ina sauraron Ku"

 

 

 

Shahid ya zuba mata ido yana nazarinta daga busani yace"Ina mahaifin Balaraba? Gurin shi muka zo"

 

 

Wata irin faduwar gaba ce ta rikitowa Lantana bata shirya ba, baki na rawa tace"Wac...wace Balaraba..kuke tambaya?

 

Ashe duk abunda yake faruwa a kunnen Sallau da Uwa! Jan jiki yake domin ya k'arasa rumfar domin yajiyewa kansa tabbas,a sukwane Uwa! Ta tsallake shi,har tana take masa cinye, ta bankad'a labule ta afka cikin rumfar babu, Sallama fad'i take"Wace Balaraba kuke tambaya"?

 

 

 

Shatima ransa ya b'aci sosai ganin rashin mutumcin da Uwa! Take tazo ta tsaya musu aka, tunda ta shigo dakin ya d'ume da tsamin hammata,, sauri yake su tashi.

 

 

Shahid ya daure zuciyarsa domin ya fara fuskantar akwai babbar Matsala a tartare a gidan.

 

Yace"Balaraba Ayuba Tanko"

 

 

Lantana tace"Ayuba ya mutu shekara da shekaru Balaraba bata da uba kamar wannan Wanda yake zaune"tafada tana nuna Sallau dake rawar jiki.

 

 

Shahid ya kalleshi yana fad'in "Kaine Waliyyin ta"

 

Kamar wani k'aramin yaro Sallau ya d'aga kansa, yana sauraron abunda zai biyo baya

 

 

 

Shahid yace"Ga kaya can daga gurin Mama Fulani tace akawo muku a matsayin Ku na iyayen Balaraba mata ga Sarki! Me jiran gado wato Sarki! Almansur insha Allahu gobe za'a d'aura mata aure dashi"

 

 

 

 

Ihu!! Shamsiyya ta kurma ta afko cikin dakin tana fad'in "K'arya kukeyi Wallahi baku isa, ni za'a yaudara da muna furci billahillazi bazan lamunta, wannan kayan nawa ne, kuma gobe dani za'a d'aura auran ba da wancan shegiyar ba"

 

Cikin ihu da tashin hankali Shamsiyya take maganganun sai dara take tana tsalle, Uwa! Ta dunga zabga zagi tana habaice habaice

 

Sallau da Lantana kuwa Shiru sukayi suna mamakin wannan al'amari

 

 

Ganin sun gama abunda ya kawo su yasa suka mike cike da mamakin dabi'ar mutanan gidan tsallake Sallau sukayi Wanda yayi rashe-rashe a bakin Kofa suka futa cikin tashin hankali domin Sam Shatima baya San hayaniya da yawa yanzu kansa zai fara ciwo.

 

Ganin sun futa yasa Lantana mik'ewa da sauri ta bi bayan su, sai kuma ta dawo da sauri ta koma cikin d'akinta ta d'auko wani Abu tana boyewa cikin hijab, rad'a tayiwa Uwa a kunneta ta futa a sukwane!

 

 

Lokacin Buba Direba har ya kunna mota ta karasu gurin tamkar sabuwar mahaukaciya tana fad'in Ku tsaya kutsaya"

 

 

Shahid yace da Buba ya tsaya Lantana ta iso gurin tana haki!! Tace"Inaso in biku gidan sarautar domin a gudanar da harkokin buki dani, a matsayina kamar Balaraba.

 

Shatima yace"Bud'e mata Kofa ta shigo, aikuwa Buba ya bud'e kofar mota  Lantana ta shiga ta zauna tana  k'ara damk'e abun da yake hannuta.

[9/8, 9:34 PM] Akwai CittađŸ’”đŸ’”: **********

**********

**********

 

 

Wata irin fad'uwar gaba taji lokacin da taji abunda yake cewa, kar dai wannan mutumin zarginta yake.

 

Take fad'ar haka cikin zuciyarta.

 

Tamkar wacce aka aikowa da mala'ikan d'aukar rai! Haka ta kicin-kicin da fuskarta, cikin yanayi irin na b'acin rai tace"Wannan ba hurumin ka ba, cewar maza nawa na kula ko nayi mu'amula dasu lokacin ina sana'ata, kai bari kaji wani abu da baka sani ba, yau kasan dashi, na Dade da sanin dama kanai min kallon "yar tasha me sai da abunci cikin kasuwa, babu irin maganganun da baka fad'uwa Moddibo ba,kan kar ya aure ni, kushe da hassada basa hana gamji toho nida Moddibo soyyaya ce ta tsakani da Allah, ina mutukar alfahari da sana'ata,kuma duk inda na shiga na futa naji ana zagin masu irin Sana'a ta sai inda karfina ya tsaya, saboda haka tun kafin magana tayi nisa mutukar kasan da wani k'uli a ranka a game da aure na, sai ka janye kawai babu Lallai babu dole a ciki"

Ta k'arashe maganar tana sauke ajiyar zuciya.

 

 

Fuzgo hannuta yayi tafad'a kansa, ya rungume ta tsam! K'irjinta ya dunga fat-fat! Shima nashi haka, muryar shi a tsark'e yace"Ni kike k'okarin zagi ko saboda kawai na tambaya ki, abunda nake da hakki akansa"

 

 

Da sauri ta fuzge jikinta tanai masa kallo na wani irin mutum mai baud'adan ra'ayi yasan yayi Abu ya nuna bai yi ba, babban abunda yake bata haushi dashi shine son ya tab'a mata jikinta.

 

"Sama-sama tace" Babu maganar zargi a magana ta,ai gaskiya ce tun yanzu naga take-taken ka, kayi hakuri idan na b'ata maka rai,da kalaimai na"

 

Tana gama maganar ta shige d'akin da suke kwana.

 

Kallonta yake babu k'iftawa har sai da ta shige dakin sannan ya d'auke kansa, yana sauke wata irin zazzafar ajiyar zuciya, kwata-kwata a "yan kwana kin nan, yana yawan jinta a cikin zuciyarsa, duk sanda ya tuna da cewar tayi mu'amula da maza ta shiga cikin kasuwa ta saida abunci,sai yaji wata irin kibiyar kishi ta soke, ranar sai ya yini yana kwance duk ransa a b'ace! Yana kishinta sosai da sosai.

Kasa daurewa yayi yasa yayi mata maganar.

 

 

 

 

***********

***********

***********

 

 

 

Lantana na bayan mota duk tayi tsuru-tsuru sai zare ido take, burinta kawai ta isa gidan ta ganta gata ga Balaraba sai ta fara gudanar da aikinta.

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿93*

 

 

 

 Kai tsaye shashen Mama Fulani suka nufa,, bayan Buba yayi parking d'in mota suka futo cikin nutsuwa, Buba ya bud'ewa Lantana k'ofa ta futo daga cikin motar sai zare ido takeyi ganin wasu irin mutane manya-manya a shashen Mama Suna kaiwa suna kawowa kuwanne jikinsa sanye da kaya jajaye da k'aton ta wani, gefanta ya kalla taga wani tsaye hannusa rik'e da k'atuwar bulala sai zare ido yake ga idanunsa sunji kwalli rabad'au, saurin d'auke kanta tayi tana k'ara damke abunda yake hannunta.

 

 

Ganin suna ta zubewa k'asa suna gaidasu Shatima ne yasa ta shiga taitayinta, ta dunga bunsu a baya simi-simi har suka shiga falon a tare.

 

 

 

Lantana ta tsorata da ganin irin had'uwar falon Mama Fulani ko ina ta kalla sai taga kalarshi daban, ga kayan alatu na jin dad'i da more ta yuwa, wani irin mugun kamshi me dad'i yana shiga hancin ta.

 

 

Tun daga bakin Kofa ta zube tana gaida Mama.

 

 

Cikin mamaki Mama Fulani tace"Bisimilah mana ki shigo daga ciki sai mu gaisa sosai"

 

 

Da k'yar Lantana ta mike ta isa kusa da Mama Fulani ta zauna a k'asa sai washe baki take.

Tana fad'in "Ranki shi Dade ashe ina da rabon ganin ki a duniyar nan, ashe jinina zai had'u da jininku,gaskiya nagode Allah nagode Muhammadu rasililahi"

 

 

Mama tayi murmushi kawai tana kallonsu Shahid nan yayi mata bayanin Lantana

 

 

Cike da farin ciki ta kalli Lantana tana fad'in "Gaskiya naji dad'in zuwanki sosai,dama nace aje a sanar daku  halin da ake ciki,Gobe insha Allahu bayan d'aurin aure zan tura a d'auko sauran mutanan gida suma suzo ayi hidimar buki dasu"

 

 

"Lantana tace" Ai naji dad'in wannan abu ranki ya Dade nace Ashe da rabonmu muma zamuci arziki mu bar shi inda yake, haihuwa tayi mana rana"

 

 

Murmushi Mama tayi batace komai ba.

 

 

Su Shahid suka mike. Inda Shatima yake tambayar Sarki! Mama tace"Ya koma Shashen sa. Sallama sukai mata suka wuce Shashen Sarki!

 

 

 

Lantana ta dunga b'arin jiki sai zuba take tanaiwa Mama labari,tace"Ina angon namu yake ne yazo ya zab'a ko ni ko ita"

 

 

 

Mama bata iya surutu ba saboda ba d'abi'arta b'ace,gashi bata San wulakanta mutum sai ta dunga biyewa Lantana kawai domin karrama ta.

 

 

 

Jakadiya Shafa'atu ta shigo suka gaisa da Lantana, nan Mama take sanar da ita cewar kakar Balaraba CE,Jakadiya ta kara gaida Lantana cikin girmamawa, Mama tace, taje ta kira Balaraba dasu Sadiya su gaisa da kakarsu sannan Balaraba ta bata abunci, Sadiya da Usuman ne a gaba kafun Balaraba, da sauri suka ja tunga suka tsaya ganin Lantana a gurfane gaban Mama sai surutu take sai kace wata tsuhuwar redio, Sadiya ta juya da sauri zata koma suka ci karo da Balaraba tayi saurib tare ta tana tambayar ta menene"?

 

 

Bakinta na rawa tace"Yayarmu Lantance"

 

Da sauri ta kalli inda Sadiyar take nuna  mata, Lantana ce, kuwa hankalinta na kan Mama basu ga futowar su ba, fad'uwar gaba taji, tana mamakin me ya kawo Lantana gidanan,, wata zuciyar tace mata kika sani ko Mama ce tasa aka d'auko ta.

     Da kuzari a jikinta ta nufi inda suke, Binta sukayi a baya suna cike da tsoran abunda zai faru Usuman addu'a kawai yake a cikin zuciyarsa Allah yasa Lantana kar ta gudu dasu shikam yaji dad'in zaman gidan nan.

 

 

Lantana na hango Balaraba ta mike da sauri zaninta ya fad'i ta d'auka da sauri ta d'aura taje ta rungume Balaraba ta fashe da kuka tana fad'in "Ashe kina nan Balaraba, munyi neman duniya bamu ganki ba,Shima Sallau da k'yar ya koma gida ranar ashe alkairi ne a tartare dake Balaraba"

Wasu irin sambatu Lanatana ta dunga yi Mamaki ya kama Balaraba sai ta rik'e ta ta zaunar da ita tana fad'in ki zauna mana, don Allah ki nutsu sosai sai muyi maganar.

 

Ita dai Mama tana kallonsu cike da mamaki

 

 

Jiki narawa ta zauna tana hawo hannun Usuman yana fuzgewa yana komawa bayan Balaraba,

 

 

Tace"Zo nan Sadiya mu gaisa" k'in zuwa tayi yarinyar.

 

 

Fashewa da kuka Lantana tayi cike da munafurci da kitifi tace"kinga abunda nake fad'a miki ko Balaraba, dubi wai jina ne yake guduna duniya kenan"

 

 

 

Balaraba na jinta tasan dai makircin Lantana,, tace"Ki nutsu nu gaisa mana"

 

 

Jikinta na rawa ta hau gaida Balaraba, amsawa tayi kawai tana kunshe dariyarta ita Abunda Lantana take ya soma bata mamaki wallahi.

 

 

Mama kanta ta fuskanci rashin gaskiya gurin Lantana.

 

 

Da k"yar ta hillace ta suka nufi gurin cin abunci Lantana taka tunga ta tsayawa wai baza ta hau kan daining ba, haka ta had'a mata ta kai ta aje mata can wani k'ebabtaccan gurin Cin abunci take kamar wata jaka babu kamun Kai babu komai, Mama Fulani na daga gurin zaman ta tana kallon ikon Allah, Balaraba kuwa wata irin kunya ce ta kamata, a hankali tace "Lantana kici a nutse mana"

 

 

Ko saurarenta batayi ba,sai da ts cika Uwar hanjinta da kyau sannan ta tsame hannuta tana goge bakinta,,, Mik'ewa tayi ta koma falo kusa da Mama Fulani,,Tsaki Balaraba taja tana d'auke kanta,tanajin Lantana tana cewa Mama wai tana so ko bayan biki ta zata zauna anan"

 

 

Mama Fulani tace"Ai babu komai sai ta zauna d'in.

 

Mama Fulani dai shiru tayi musu ita da Jakadiya suke hira itama da tagaji sai tao shiru ta k'yaleta,, sai banbadanci takewa Fulani.

 

 

Mintu ashiri Mama ta kara a gurin ta mike tsaye tana musu sallama domin zataje ta kwanta, nan sukai mata sai da safe, ta shige d'akinta, Jakadiya ma sallama tayiwa Lantana ta mike ta nufi dakin kwananta.

 

 

Balaraba ta kalli Lantana da rai a b'ace tace" Ai sai ki tashi haka muje ki kwanta, wai don Allah meyasa kike haka ne"?

 

 

Lantana ta hau yak'e tana fad'in "Me na aikata " yar nan, baki San su irin wannan mutane dole sai kana musu banbad'anci ba"

 

 

Tsaki taja tana fad'in "To banda wannan masarautar ta masu hankali ce,don Allah ki dunga nutsuwa kar ki bani kunya gurin abokan zamana da mutanan gida"

 

 

Lantana tace"To naji zan kiyaye ai kina da damar da zaki fad'a min duk irin maganar da kike so, saboda Kinga zaki auri Sarki!

 

 

"Shiru kawai tayi mata tana surutai a cikin zuciyarta take fad'in ko wannan auren ya dama,ni a gurina sunan shi auran biyayya.

 

***********

***********

***********

 

 

*Komai yayi farko yana da k'arshe*

 

 

Cikin shiri sosai suka futo daga shashinsa gida ya cika ya tumbatsa baka jin komai sai busa da sarewa irin ta gidan sarauta, marok'a da magogo sai aikinsu suke, k'amshi suke ko ta ina Sarki yana cikin wata d'anyar Shadda gezner me mugun tsada anyi masa wani irin dinki babbar Riga da " yar ciki ita kanta hular dake kansa da da yankin shaddar aka had'a ta kafarshi sanye da wani takalmi rufaffe mai mugun kyau kalar kayan jikinsa sky blue yayi masifar kyau fysakarsa sai futar da annuri take, sajensa ya kwanta lif-lif a fuskarsa hannusa wani irin agogo ne, na zallahr azurfa, kana ganinshi kasan yana cikin farin ciki da annushuwa, sai gaisawa yake da manyan mutane gwamnoni da "yan majslisa sanatoci da sauransu, " yan abokan arziki duk murna sukeyi da farin ciki.

 

 

Wata kujera ya nufa wacce a ka k'wata ta da shimfud'u na alfarma yana tafe su Shatima na take masa baya, zama yayi cike da k'asaita, wasu nayi dake tsaye suna jiran zuwansa suka hau yimasa firfita, Shahid da Shatima suka zauna gefe da gefan sa.

 

 

 

 

K'irari kawai kakeji da busa marok'a sun rud'e kowa da irin nashi rok'on  kowa naso ace nashi yafi na d'an uwanshi.

 

 

"Masha Sarki! Ya futo fasa taro Jimana na gaban Giwa, baka iya ba Allah ne zai yi maka, yaro me Halin dattako! Fari mai farar anya! Hak'ika matayen ka sun dace da samun nagartaccan miji jarumin jarumai,, Duk zaka iya dasu har da k'warl'wara ma, Sarki! Almasur kujerar mulki takace Allah ya yataka ruk'o jamuje Gami sha sassaka duk wani mak'iyinka sai da ya mutu!!!!!!

 

faaaa!! Gurin d'aurin aure ya kai ya kawo jama'a d'aurin auran mataye uku ba wasa ba ne, Waziri Zayyanu na gefe guda shi da tawagar shi duk ransa a b'ace yake shi ba abun ya koma gida, wata zuciyar tana ce masa ya zauna kawai a k'arasa dashi, dole shine Waliyyin Ango kuma yayi rantsuwar bazai masa waliyi ba, Yana kallon Shige da fucen da Galadima yake shida Wambai, sam sunk'i su zauna kusa dashi,sun karkata gurin Sarki,yasan duk kalar munafurci ne, kujerar mulki sukewa yaga kuma yadda za'ayi a karb'eta a hannusa.

Gaisawa kawai yake da jama'a ba dan ransa ya so ba, mutane sai zind'ansa suke suna nuna shi a matsayinsa na Sarki me rik'on k'warya.

 

 

 

Sai da aka fara d'aura auranshi da Halisa kan sadaki dubu d'ari sannan aka d'aura da Azima itama sadaki dubu d'ari, sai Balaraba itama haka, Liman ne ya karb'i wakilcin Balaraba,saboda babu wakili Sallau ne kuma bai zo ba saboda tsabar bak'in ciki,shi kuma Maman baya gari yana can tafiya tafiyensa dake babbar motar d'aukar kaya yake ja,,, Kowa ce aka damk'awa Wakilinta sadakin ta, Liman ya rik'e na Balaraba a hannusa yace shi zai bata da hannusa.

 

Bayan d'aurin. Aure guri ya hargitse da ciye-ciye na abunci nau'i nau'i ana futo dashi daga gida,, Masha Allah kowa yaci kuma yayi guziri guri bai watse ba sai dab da sallahr azahur sannan kowa ya nufi gida domin yin sallah.

 

 

Mahaifin Azima ne suke keb'e da Waziri suna maganganu k'asa-k'asa karku manta da cewar dama tuntuni abokai ne

 

 

Tun daga nesa Sarki! Ya Fahimci akwai maganganu da suke tattaunawa. Kuma da alama basu da gaskiya, suna ganin sun k'araso gurin Mahaifin Azima ya saki fuskarsa sosai yana fad'in "Dama ina cewa azo a nemo min kai muyi sallama yau zamu koma ni da tawaga ta, inai maka fatan alkairi da d'or ewar zaman lafiya kai da iyalinka, ga Azima nan nabaka amana,yanzu ma abunda nake kara jaddadawa abokina kenan gashi nan a tsaye"

 

Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya mik'a masa hannu yana fad'in "Insha Allah karkadamu mungode sosai A sauka lafiya"

 

Cire hannusa yayi ya mik'awa Waziri Zayyanu, kauda kai yayi ba tare da ya bashi hannusa ba, yace"Ka rik'e gaisuwarka ni bana buk'atarta, na fad'a maka tun wuri tsalle d'aya mutum yake ya fad'a rijiya, amma sai yayi dubu bai futo ba"

 

Yana gama maganarsa ya wuce ya barsu tsaye a gurin,

 

Sarki!

Shahid

Shatima

 

Duk suka bishi da kallon mamaki.

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿94*

 

 

 

 

Sanin Hali yafi sanin kama,Sarki fuska yayi kawai ya wuce ba tare da ya tsaya ya k'ara sauraron wata magana daga bakin Mahaifin Azima ba wato me Martaba sarkin Yalwa, ganin ya wuce ne yasa su Shahid suma suka rufa masa baya suna cike da mamakin abunda Waziri Zayyanu ya aikata.

 

 

 

Suna tafe suke maganar har suka isa shashen nasa Shatima ya zauna kan kujera yana fad'in "Sai yanzu gajiya ta fara damuna kuma"

 

Shahid yace"Duk ba wannan ba, abunda wannan mutumin ya fad'a fa abun dubawa ne, Tsalle d'aya mutum yake ya fad'a rijiya,Wannan Kalmar a hausance meye ma'anarta"?

 

 

Wani k'asaitaccan murmushi Sarki! Yayi yace"Ku rabu dashi don Allah inajin shine zai fad'a rijiyar ya kasa futowa"

 

 

Shatima yace"magana ce me harshen damo kuma da gani akwai wani k'ulli

 

Shahid yace"Nima na lura da haka wallahi tunda muka doso inda suke, suna magana k'asa-k'asa"

 

 

Tab'e baki Sarki yayi yana kici-kicin cire babbar rigar dake jikinsa yace"Mugun k'ullinsa zai koma k'ansa ni ina tare da Allah"

 

 

"Wannan magana haka take,duk mutumin da yake tare da Allah kuwa to babu abunda wani mutum zai masa ba tare da Allah ya tsare shi"

 

Su Shatima ne suka fad'i wannan maganar.

 

 

Zama yayi kusa da Shahid da gashi sai Singelt da dogwan wando na shaddar dake jikinsa, yana fad'in zafi nake ji wallahi ga yunwa kasan tun jiya da yamma rabona da cin abunci"

 

 

Shahid yasa dariya yana fad'in ai zama da yunwa ya k'are me mata hud'u rigis"

 

Gabansa ne ya fad'i kad'an shi kansa yana tunanin yarda za'ayi ya zauna dasu lokaci guda.

 

 

Shatima yace"Mutumina ai jarumi ne, zai iya rik'e su, ni dai INA ja maka kunne da kayi adalci a tsakaninsu"

Shatima ya k'arshe maganar yana dariya

 

 

Hararasa yayi yana fad'in "Ank'i ayi adalci me yasa su baza ka fad'a musu suyi min adalci ba sai ni zaku ta damu da maganar adalci, duk wacce tafi kyauta ta min itace Gimbiya ta"

 

Dariya suke masa,Shahid yace"Maganar haka take duk macan da take kaytata ma kafi jin ta aranka. Ammafa kowa ce mace da irin nata salon wata akwai iya salo da jawo hankalin me gida da iya kwanciya wata kuma iya girki da iya hira wata kuma iya kwalliya da tarairaya duk dai gasu man, idan Allah ya hore maka mace me ibadah fa duk wannan abubuwan Dana fad'a to kayi sa'a a rayuwarka"

 

Shatima yace"Wannan maganar haka take"

 

Shiru yayi musu suna ta zubah, mik'ewa yayi ya je ya k'aro k'arfin AC sosai yake jin zafi abunka da wanda be saba ba,ya shiga cikin jama'a ga rana da cukurkud'u kowa naso ya gaisa dashi, shiyasa ya daure ya dunga gaisawa da jama'a domin futa hakkinsu

 

 

Shahid ne ya kalle shi yaga yana lumshe ido, yace"Ko a sa a kawo abunci ne"

 

Bud'e ido yayi yana kallon daining, babu komai a kai, d'aga kai yayi  ya mayar da idonsa ya lumshe.

 

 

Shahid ya mike yana k'okarin futa, bud'e idonsa yayi a karo na biyu yace"Kasan me"?

 

 

Shahid ya tsaya yana kallonsa, shi kuma yace"tea nake so mai kayan kamshi da tafarnu  idan nasha shi duk zan daina jin wannan mutuwar jikin"

 

 

Shahid yace"Bari in shiga shashan Mama yanzu nasan za'aha da maka"

 

******

 

Wasa farin girgi Shahid na futa yaga jama'ar gidan sun dura sabon buki irin na al'ada sai cashewa suke ana ciye-ciye ga masu kad'an k'warya nan sai bugawa suke "yan mata sun shiga suna ta rawa, gefe kuma wasu maza ne suke wasan wuk'ak'e, kai guri ya hargitse da sawu dukuna kowa na tashi murna, ko da yazo giftawa ta shashen Hajiya Kulu nan kad'e-kad'e ne kawai yake tashi irin na turawa,ta tara k'awayenta suna ta tsula stiyarsu Tsito ma yana zaune cikin mata yana ta busa sigari, duk macan da tayi masa sai daki d'uwawunta yana dariya aikuwa sai su saki shewa suna k'ara rawa da murgud'a d'uwawu" a gurin wasu daga cikinsu suke aikata fasadi batare da damuwar kowa ba.

 

 

 

B'angaran Mama ma buki suke sosai irin na al'ada "yan uwa da abokan arziki sun cika mata falo kowa yazo taya ta murna, tana zaune cikin shiga ta alfarma ta fuskarta cike da walwala, Gimbiya Halisa tare da Mahaifiyarta Madabo suma nan suke hidimar bukin tare da Mama Halisa taci uban ado gwal ko ta ina  alkyabar dake jikinta ma abar dubawa ce sai sheki take, jama'a sai kallonta suke ita kuma kanta yana kara girma dama so take ace tayi kyau , Taso Balaraba ta futo amma fafur tak'i futowa tana kulle a cikin d'aki kunya take ji sosai ita baza ta rashin kunyar da Halisa take ba, Lantana kuwa ai ta saje cikin mutane ta zama " yar gari sai kutsawa take tana shigshigi ga jama'a,,

 

 

 

Tana sanye da wani irin material me kyau da tsada Multi color ne jikinsa duk stone anyi mata wani irin d'inki bubu wuyan rigar yaji stone work sosai tayi kyau kamar ka sace ka gudu d'aurin d'ankwalin da tayi ya k'yatar sosai Sam babu wani tarkacan kwaliyya a fuskarta, tana zaune gefan gado tana sak'awa da kwance wa su Sadiya kuwa Duk suna waje tun safiya.

 

 

 

Da k'yar Shahid ya   ganin Mama Fulani yayi mata bayanin abunda ya kawo shi, tace"Bari yanzu za'a had'o akawo muku in yaso d'aya daga cikin matan nasa sao tazo ta had'a muku abunci"

 

 

Godiya yayi ya futa ta k'ofar baya,

 

 

Ita kuwa Gimbiya Azima dama can shashen Waziri ta sauka da jama'arta nan suke shagalinsu, don haka ko da ta shirya ta futa tare da wasu bayinta da ta tawo dasu suna take mata baya, kai tsaye shashen Sarki! Ta nufa domin da zafi-zafi ake bugun k'arfe a ganinta wannan kwaliyyar da tayi baza ta tashi a tutar babu ba, dole Wanda akayi domin shi ya gani.

 

Jakadiya Shafa'atu ce ta had'a musu duk abun buk'ata ta sanya baiwa Mariya wacce take shige da fuce shashen Sarki! Ta d'auko kayan abunci ta dunga kai wa can. Mama ta bi falon da kallo tana neman Halisa babu ita da alama ta futa, wasu k'wayenta ne suka zo, Sadiya ta kira Yarinyar tazo ta duk'usa Mama tace"Je ki kira Yayarku kice tazo inji ni"

Domin tasan idan ba haka akace ba Balaraba tana iya k'in zuwa.

 

 

 

Tana zaune taji sallama Sadiya kallonta take har ta k'araso kusa da ita tace"Yayarmu ka zo inji Mama"

 

 

Balaraba tayi shiru tana tunani Sam bataso ta futa mutane suyi ta kallon ka"

 

"Jeki ce gani nan zuwa"

 

Sadiya ta futa cike da walwala.

 

 

Mik'ewa tayi ta d'auki wani mayafi me kyau ta ya yafa har fuskarta sai da ta kusa rufewa, kanta a k'asa ta futa, kallonta kawai jama'ar dake gurin suke.

 

Har ta k'arasa kusa da Mama ta tsuguna tana fad'in 'Mana gani"

 

Shafa kanta tayi tace"Allah yayi miki albarka Balaraba ya albarkaci auranku,, Allah ya baku "yaya nagari"

 

Duk jama'ar dake gurin suka amsa da "Ameen"

 

Mama tace"An kai kayan abunci shashen me mijinku kije ki had'a musu shida abokansa"

 

 

Gabanta ne ya fadi jin abunda Mama tace, a nutse tace 'To Mama" mik'ewa tayi a nutsu take tafiya k'afafunta duk suna hardewa tasan idanun mutane dake gurin suna kanta, tana futa, kowa ya fara fad'ar albarkacin bakinsa a kanta.

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

 

*🅿95*

 

 

 

 

 

Da sallama a bakinta ta shiga falon.

 

Kujerar da yake zaune tana kallon k'ofar shigowa karaf suka had'a ido, kasa d'auke idonsa yayi daga kanta, ta k'araso cikin falon a nutse su Shatima suna amsa mata sallamarta.

 

Daining area ta tuna cikin yanayin tafiyar ta me d'aukar hankali, kallonta yake a sace har Shahid ya lura dashi sai ya tab'o Shatima yana nuna masa,suka dariya.

 

 

Wayancewa yayi ya kalle su yana ya mutse fuskarsa yace"Dariyar meye wannan"?

 

 

Da ido Shatima ya nuna masa Balaraba, tsaki yayi kamar gaske, ya d'an Sosa sumar kanshi kamar yadda ya saba yace"To sai me"?

 

 

A hankali Shahid yace"Gaskiya kai d'an gata ne Wallahi mata uku rigis!"

 

 

Tab'e baki yayi ya mik'e ya na k'okarin hawa saman bene.

 

 

Shatima yace"Ya haka kuma kai da zamu ci abunci ka hau sama"

 

 

Dai-dai baranda ya tsaya yana bashi amsa da cewar "Wanka zanyi yanzu zan futo"

Ya bud'e dakin ya shiga.

 

 

Tsab ta shirya abuncin cikin k'yatattun kwanuka irin na gidan sarauta, tasa wasu irin plate ta rufe masu kyau da k'yalli.

 

 

A nutse tazo ta zauna ta saki fuskarta kad'an suka gaisa dasu Shahid, sai janta da hira suke sama-sama take amsa domin tun d'azu da suka had'a ido da Sarki! Tarasa kuzarin ta,,, Hak'ika ya cika cikkaken namiji yayi kyau cikin singlet d'in dake jikinsa, sosai ta dunga jin tsigar jikinta tana tashi,, tana jin wani irin yanayi a jikinta.

 

Dai-dai lokacin da ya bud'e d'akinsa yana daga sama jikinsa d'aure da wani towol, da wani a hannusa, Balaraba yakewa magana, yana daga sama, Azima ta shigo falo bakinta d'auke da sallama, had'a ido sukayi da Balaraba sai taji zuciyarta ta buga, ganin irin d'anbanzan kyawun da Balaraba tayi kamar ka sace ta ka gudu,ji tayi kamar ta Burma mata wuk'a ta huta da masifar kishin da take ji nata.

 

 

Saurin komawa yayi cikin d'akin domin baya so Azima ta ganshi, bashi da tabbacin cewar Balaraba taji abunda yake cewa. Wayar sa ya  dauka ya kira numbar Shahid yace"Turo min Gimbiya tazo ta had'amin ruwan Wanka"

Kitttt! Ya kashe wayar bai saurin abunda Shahid din zai ce ba. Shahid ya kalli Balaraba dake k'okarin mik'ewa domin tafiya ganin shigowar Azima tasan baza su kwashe ta dad'i ba ganin irin kallon da take mata, yace"Gimbiya  umarni daga mijinku wai ki hau sama kije ki had'a masa ruwan Wanka"

 

 

 

Cikin mamaki ta ke kallon Shahid d'in ita fa bata son iyayi, da itace take had'a masa ruwanka da zai zo yace taje ta hada masa.

 

 

Shahid kamar yasan abunda take tunani yace"Nasan zakiyi tunanin cewar ai da bake bace kike had'a masa ruwanka ba, to yanzu duk nauyi ya dawo kanku" ya fad'a yana kallonsu ita da Azima ya cigaba da cewa "duk yawan bayinsa da kuyanginsa yanzu basu da alhakin kula dashi wannan aikin naku ne".

 

 

Azima ta zauna cikin kujera tana tab'e baki itakam ba zata iya Wannan bautar ba, duk yawan bayin gidan nan ace dole sai sune zasu had'a ruwan Wanka, wacce taga zata iya taje tayi.

 

 

Balaraba kuwa gudun kar magana tayi tsayi yasa ta nufi hanyar sama cikin nutusawar ta, wata banzar harara Azima ta bita dashi.

 

 

 

Shatima yace" Haka ake so Gimbiya kuma Amarya ta gaban goshin mijinta"

 

 

 

Azima taji kamar ita yake fadawa magana, kawai sai ta fara shan kamshi tana amsa musu magana sama-sama.

 

 

 

Yana zaune a gefan gado ta shigo dakin bakinta d'auke da sallama, had'a ido sukayi a karo na biyu, sai tayi saurin d'auke nata idon. Ganin yanayi da ta ganshi, a ciki, shikam ai kallo yake mata na mutukar kurrula ya kafe ta da ido gaskiya tayi masa kyau sosai da sosai, gyaran murya yayi cikin yanayi maganar sa yace"Ki shiga toilet ki had'a min ruwan ka amma kar yayi zafi sosai"

 

 

Balaraba ta kama hanyar toilet cikin tsarguwa kafarta sai rawa take tasan idonsa ne a kanta, ta bud'e band'akin kenan zata shiga yace"Jimana"

 

Tsayawa tayi ba tare da ta waiwayo ba, tana bal'in jin haushin Wannan sunan wai Jimana"

 

Idonsa ya lumshe ya bud'e su sun fara sauyawa yace"Ki matsa min makilin a brush kinji ko"

Haushi duk ya ishe ta, ta lura dashi d'an iko ne.Toilet d'in ta shiga ya fara had'a mishi ruwan kamar yadda ya buk'ata, ta  matsa masa makilin d'in ta aje inda ake ajewa, tana k'okarin futowa ne shi kuma ya shigo ciki, sauri kaucewa tayi domin ta bashi hanya kanta a k'asa kwata-kwata batason had'a ido dashi, tsayawa yayi yana kallonta ,,, jikinta ya bata cewar kallonta yake cikin zuciyarta take cewa dama haka mutumin nan yake da kallo, d'ago kanta tayi tan gyara fuskarta gudun raini, suka had'a ido, sai tayi saurim d'auke nata idon ganin yadda nashi ya kad'a yayi jajazur, gashi sun wani k'ankance duk girman idonsa, jarumta da dauriya ta aro tace"Zo ka wuce ga hanya"

 

 

"Zo ka wuce ga hanya? Ya maimata maganar da tayi masa tamkar wata uwarsa ce take bashi umarni yanda tayi maganar. Aikuwa sai ya tawo tayi k'asa da kanta tana jira ya wuce,, ya k'araso daf da ita taji gabanta na dukan uku-uku babu zato! Taji ya rungumeta sam! A jikinsa yana sauke wata zazzafar ajiyar zuciya, abun yazo mata a bazata! Shine yasa ta kusa fad'uwa k'asa sai yayi saurin tallafo ta jikinsa suka zube dandagaryar k'asan tayel,  Balaraba ta shiga rudu ganinta kane-kane kan cinyarsa,  shi kuma jikinsa na kyarma! Yake lalubar jikinta har sai da yayi nasarar cafko k'irjinta abunda yake mutukar muradi kenan ya gigice mata ya fara murza mata su duk da suna cikin Riga bai hanashi jin yaya taushin su yake ba a hannusa.

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

 

 

*🅿97*

 

 

 

 Wani irin yanayi ta shiga lokacin da taji abunda yake mata da k'irji, tsigar jikinta ta mik'e sosai,taji jikinta ya mutu murus ta kasa yin katab'us a jikinsa, ganin yadda jikinta ya shika ne yasa ya fara k'okarin cire mata rigar ko ta halin k'aka ne,,, nan ta dawo hayyacinta da sauri ta mike daga jikinsa,lokacin shi kuma jikinsa ya mace, saboda halin sha'awar da yake ciki, bakinta na rawa tace"Wato dama abunda zakayi kenan shine yasa ka kirani"

 

 

Wani kallo ya watsa mata a kasalance yace"Laifi ne,Ku haram na aikata da har kike min wannan maganar"

 

Kallo me kama da harara tayi masa ji take kamar tayi masa tsaki sai ta tuno kuma matsayinsa a gurinta,kama hanya tayi zata wuce Ya rik'e hannuta guda yana k'okarin mik'ewa tsaye ina k'arfin ba d'aya ba,ai kawai sai ta rikoto kansa,, tana nishi! riketa yayi sosai suka mik'e tare kallonsa take cikin jin haushi, ta kama hanya zata wuce a karo na biyu, had'e ta yayi da bangon d'akin yana fad'in "Idan baki rage min sha'awata ba, zaki shiga hakkina ina cikin halin taimako"

 

 

Maganar ta girme ta,, yanzu ta fara jin tsoransa  ganin yadda ya ware k'arfinsa a kanta duk ya tareta da gangar jikinsa,, Bakinsa na dab da nata hucin numfashinsa na duk fuskarta.

 

 

Lumshe ido yayi gami da tallafo kanta ya had'e bakinsu guri guda kiss d'inta yake babu sauki, Sosai Balaraba ta shiga shauki tana mamakin yadda take jin wani mugun dad'i na ratsa mata kwakwalwa wato dama haka ake ji shiyasa turawa da indiyawa Larabawa suka nacewa kiss had'a baki saboda suna jin dadi.

 

 

Sosai Sarki! Ya hargitsa ta da zafafan kiss d'in shi mai wahalar mantawa Sai da ya tabbatar da tayi laushi sannan ya sake ta da ido jajazur! Saura kad'an ta fad'i ta tsaya da  k'afafunta, da sauri ta futa daga toilet din tayi niyar barin d'akin ba tare da tayi tunanin halin da take ciki ba.

 

Shima abunda ya tuna kenan, tana gaf da futa ya k'araso da sauri ya cire key din ba tare da ya kalleta ba ya wuce toilet din domin yin abunda ya kaishi, amma fa daurewa kawai yakeyi yayi hakane domin ya ragewa kansa damuwa Ashe bai sani ba  damuwar sai ta kara nunkuwa kan ta da.

 

 

A daddafe yayi Wanka ya dauro towol dinshi ya futo yana goge jikinsa had'a ido sukayi da ita ta cikin mudubi, dukaninsu suka d'auke kai a tare,,, Murmushi ya saki Mara sauti cikin zuciyarsa yake cewa yarinyar nan fa bata da juriya da gani  romance kawai ya labdatar da ita,, Lallai ya gano lagonta.

 

 

Tana kallon shi yana shirya wa cikin kaya irin nasu na sarauta sai k'ak'ale yake turare kamar yayi magana ya fesa yafi kala bakwai a jikinsa d'akin Duk ya gauraye da kamshi,,,

 

 

Cikin k'asaita ya nufo inda take tsaye yana k'araso wa ya rik'e hannuta ya bud'e k'ofar suka futa daga dakin, babu Wanda ya kula kowa a cikinsu har suka sauka k'asa.

 

 

Shatima yace"Ai da mu muna cewa kawai mu tafi amarya ta rik'e maka wuya,, Shiru yayi musu yana kallon Azima da tayi kicin kicin da fuska kamar ta kurma ihu ganinshi rik'e da hannun Balaraba sai annuri suke futarwa.

 

 

Shahid dariya kawai yake kunshewa ganin abokinsa yayi shar da shi yasan halin mutumin sa sai da ya d'ana abun,ganin Duk yanayin Balaraba da alama bata cikin nutsuwa domin Sam taki had'a ido dasu Zama yayi cikin kujera,, Har yanzu hankalinsa na kan Azima, ita kuma sai cunkushe fuska take.

 

 

 

Ganin haka yasa Balaraba ta yi hanyar futa daga falon tanai wa su Shahid sallama. Domin tasan halin dabbacin su Azima yanzu sai ta hau hauka da surutai Wanda ita kuma tana ji tana gani baza tabari su zageta ba,

 

 

Kallo ya bita dashi har ta futa,yw sauke ajiyar zuciya me zafi, duk suna kallonsa wata kibiyar kishi ce tazo ta tokarewa Azima makogwaro wai dame wannan yarinyar tafisu ne? Ta lura fa Sarki! yana sonta tunda gashi ya kasa b'oye son yana nunawa a zahiri.

 

 

Yanayin fuskarta ta gyara domin bata so tayi masa magana cikin b'acin rai! taga alama dole sai ta had'a da kissa da shiyasa, tace"Yallab'ai ina ta sauri inzo in nuna maka adona ashe ban sani ba "yar uwata ta rigani,fatan dai ta kula da kai yarda kake buk'ata idan kana bukatar wani Abu ta b'angare na ka fad'a yanzu in tashi in aiwatar maka dashi,domin duk mu du muna karkashin ka ne"

 

 

Lumshe idonsa yayi ya bud'e a hankali har yanzu yana tunano abunda ya faru shi da Balaraba na d'azu, a hankali ya bud'e baki yace"Itama bani na kirata ba, Balle kiyi min wata fassara,maganar bukatar abu ta b'angaran ki, sai ki Bari sai da daddare kizo ina neman ki"

 

 

Shahid dai da Shatima mik'ewa sukai suka nufi gurin cin abunci suka bar Shi da Azima.

 

 

Wani k'asaitaccan murmushi tayi tace"Godiya nake ranka ya dad'e ai dole in amsa kiranka,da kamar k'arfe nawa zanzo"? Ta k'arasa maganar tana karkad'a idanuwan ta.

 

 

Abunda takeyi ya bashi dariya sosai, dakewa yayi fuskarsa babu yabo babu fallasa yace" Kizo ko da wane lokaci"

 

Azima taji dadin wannan abu tana ganin idan Sarki! Ya d'and'ana zumarta a farko, dole ya susuce domin ba k'aramin gyara tayiwa kanta ba, Mik'ewa yayi ya nufi gurin cin abunci, itama ta mike ta bishi a baya,, k'are masa kallo take a zuciyarta tana cewa Allah yayi hallita anan gurin,,, gaskiya yanzu sonshi da kaunarshi tsakani da Allah take, Sam baza ta yadda da auran sharad'i ba, yanzu ta gane dalilin da yasa Mahaifinta da Waziri suke son auranta dashi,saboda wata manufa tasu.

 

 

 

 

***********

************

***********

 

 

Lokacin da sak'o Mama ya isa  gurin su Uwa! da Sallau cewar ga direba nan na jiransu su shirya "yan uwa da abokan arzki kai da duk me ra'ayin zuwa gidan sarauta ya shirya ga mota tazo daukarsu har gida, domin. Suje su kalli shagalin bukin Sarki! Tare da matayen sa uku.

 

Kafin kace kwabo unguwa ta hautsine kowa na shiri babu Wanda yake so a barshi a baya,wad'anda basu sani ba, sukaita mamaki jin cewar Balaraba d'iyar Ayuba ita tw auri Sarki! Almansur,, lallai kowa ne dan Adam da lokacinsa.

 

 

Uwa! Kuwa kuka wiwi! Ta dunga yi mutan unguwa sun cika gidan suna kallonta wasu na bata baki wasu kuwa mamaki sukeyi kukan me takeyi wasu daga cikinsu kuwa dariya suke mata sun San bakin ciki ne yake d'akinta,Sadiya matar Kawu farin ciki ya cika mata zuciya tabbas yau Allah ya nunawa Uwa! Ita ba komai bace a rayuwa , yarinyar da take rainawa ta hau wani matsayin da babu Wanda ya isa ya kaita kansa sai Ubangiji makagin  baiwa.

 

Cikin farin ciki ta kulle d'akinta ta tsallake Uwa! Dake durkushe a tsakar gida tana gunjin kuka mutane sunyi dafifi a kanta suna bata hakuri, a zuciyarta tace" Kune wahallalu munafukai kawai, d'akin Iya ta nufa.

 

 

 

Tare suka futo da Iya sukayi fucewarsu, suka bi a yari zuwa gidan Sarki!

 

 

 

Duk wannan wainar da ake toyawa Shamsiyya da Maburuka basa gida. Shamsiyya dai, gurin Arrama ta tafi, ita kuwa Mabaruka wani sabon saurayin ta ne yazo ya d'auke ta a mota suka futa.

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

 

 

*🅿97*

 

 

 

 

 

Buki aka gudanar irin na al'adar masarautar ,matasan samari suka shirya kilisa, duk suka shirya dokunan su da ado me k'ayatarwa suka futa, yayin da masu busa da k'ida irin na gidan sarauta suka rufa musu baya suna aikin su.

 

A gaskiya shagalin buki ya k'ayatar ya kuma ni shad'antar, jama'ar unguwar su Balaraba, kafun su tafi sai da suka sa a kai musu iso gurin ta, suka gaisa sosai sunai mata fatan alkairi, Iya ta bata shawarwari sosai, Sadiya matar Kawu ta kalli Lantana wacce tayi kicin-kicin da fuskar ta,  so take kawai su tafi gida, domin ita gani take kamar zasu ce zasu zauna kamar yanda tayi.

 

 

Tace"Lantana ai sai ki taso mu tafi haka tunda dai an gama shagalin buki ko"

 

 

Wata k'atuwar harara ta Dan k'ara mata tace"Ai sai kizo ki ja ni ki kai ni gida munafuka, ai ni naga gurin zama, kuje Ku k'arata da iskancin ku"

 

 

 

Cikin mamaki Sadiya tace"Lantana daga magana kuma sai ki fad'a min me zafi"?

 

 

"Ke kika jawo ehe! masu gidan ma basu gaji dani ba balle ke karan k'ada miya"

 

Girgiza kai tayi cike da mamaki tace"Ai gaskiya ce,Lantana ke da ya kamata kiyi wa wani fada kece kike aikatawa"

 

"To bana son gaskiyar, nace bana son gaskiyar, gaskiya ko munafurci dai"

 

Ta k'arashe maganar a fusace!

 

 

Iya ta kama hannun Sadiya suka wuce, tana fad'in "Ke ma dai kin tsaya Ki na daka ta Lantana kamar bakinsan halinta ba, yanzu sai tasa mu raba abun kunya ba damuwarta bane"

 Akwai In da Mama Fulani take suka nufa, sukayi mata sallama gami da godiyar abun alkairin da a kai musu,, har wajan mota Balaraba ta rako su tare dasu Sadiya suna ji kamar su bisu gida, Balaraba ma idanunta duk ya tara kwalla  haka dai sukayi sallama suka tafi, kamar yarda aka d'auko su a mota haka aka mai dasu gidajan su, kowan ne kana kallonsa kasan yana cike da farin ciki.

 

 

 

Bayan sallah isha ne, masu karatun al'kur'ani suka zauna farfajiyar gidan suka fara karatunsu,  saukar alkur'ani me girma zasu yi.

 

 

 

*********

*********

*********

 

 

Arrama yana ganin Shamsiyya afujajan, yasan da akwai matsala, tana zama ta fashe masa da kuka wiwi! Murmushi yayi yana mata wani irin kallo yace"Da kwai matsala kenan malama Shamsiyya"

 

D'aga kai tayi domin kuka yaci k'arfin ta kasa maganar.

 

"Shiga ciki ganinan zuwa"

Ya fad'a mata yayin da ya ke zane-zane cikin yashin dake gabansa.

 

 

 

Wuff Shamsiyya ta shige d'an a kurkin d'akin tana goge hawayen ta domin ita gani take tazo inda za'a share mata hawaye.

 

 

 

Arrama dama kwana biyu babu kasuwa mutane duk sun gudu domin ganin aikinsa baya ci, a cewar su mak'aryaci ne, kullum sai yace buk'ata zata biya tak'i biya shiyasa kowa ya gudu, sai d'ai-d'ai ku ne wanda basu gane ba.

 

 

 

Mik'ewa yayi yaje ya zura sakata, ya k'wab'e babbar rigarshi ya aje ta gefe guda, ya afka d'akin.

 

 

Shamsiyya tace"Arrama yanzu meye abun yi"

 

 

Zama yayi kan wani dutse yana lashe baki yace" Aikin ki ya dawo sabo yarinya kin yi kuskure shiyasa komai yak'i tafiya dai-dai"

 

Shamsiyya ta dafa k'irjinta cikin damuwa tace"Na shiga uku ni Shamsiyya yanzu babu yadda za'ayi a gyara"

 

 

Arrama yayi wani bazawarin murmushi yace"Akwai hanyoyin gyarawa in har zaki bi umarni"

 

 

Shamsiyya tace"Zan bi umarni in Allah ya yarda ni dai burina shine kayi min aikin da zan auri Sarki! Ita kuma waccan tsinanniyar ya koro ta gida tare da takardar saki"

 

 

 

Murmushi yayi, ya mike yana fad'in "Ina zuwa"

Futa yayi daga d'akin

 

 

Allo ya d'auka yayi zane-zane layi goma ya sanya ruwa cikin k'ok'o ya d'auraye Tass, ya zuba wasu ciyayi, ya shiga d'akin yana motsawa ruwan.

 

 

Zama yayi inda ya tashi, yace"Karb'i wannan"

 

Shamsiyya ta mik'o hannu ta karb'a jiki na kyarma! Tana jiran abunda zai ce, gyaran murya yayi ya cigaba da cewa"Ki tub'e kayan jikin ki tass! Ki shafe jikin ki da rubutun yanzu kiyi a gabana ko ina ake so rubutun ya tab'a a jikin ki"

 

 

Aikuwa jiki na kyarma! Shamsiyya ta hau tub'e kayan jikinta a gaban Arrama duk idanunta sun rufe k'okarin ta kawai taga tabi umarnin da aka bata, domin aiki yayi"

 

Zigid tayi gaban Arrama ta fara shafa ruwan tawadar a jikinta, Arrama ya gigice ya d'imauce ganin yadda nonowan Shamsiyya suka k'ara girma sosai ba kamar yarda ya sansu ba, idanunsa suka kada sukayi jajazur tuni kayan aikinsa suka cika wando sai haniniya suke.

 

 

 

Ita ko shashashar sam bata lura ba shafe jikinta kawai take tana jujjuwa, muryarsa a sark'e yace"Ki shafa a mazaunan ki da bayan ki"

 

 

Tana shafawa tace"Hannuna ba zai kai ba"

 

 

Cikin futar hayyaci ya mike ya Isa inda take ya karb'i k'okon yana fad'in "Kawo in shafa miki kiga yarda ake"

 

 

Mik'ama masa tayi ta juya masa baya, aikuwa Arrama ya karb'a yana fara shafa mata a mazaunai yana mulmula masu

[9/14, 8:27 AM] Akwai CittađŸ’”đŸ’”đŸ„ł: Jin yanda Arrama yake Mulmula mata mazaunai, yasa wata mahaukaciyar sha'awa ta bujuro mata dama Shamsiyya tana daga cikin jerin mata masu masiyaffafiyar sha'awa(Harija) ce sosai lumshe ido ta dunga yi jikinta ya soma zuba,, babu shiri ta juyo, shima jefar da k'okan yayi saboda baya cikin hankalinsa, rungume juna sukai suna nishi, sosai da kanta ta cire masa ragowar kayan jikinsa, a gigice kwanta kan wata tsohuwar katifa, Shamsiyya ta bud'ewa Arrama k'afa ya afka kanta idanunsa a rufe.

 

 

 

 

***********

***********

***********

 

 

 

Tsito na d'akinsa yana aiki da aljanu domin yinin yau aiki yake sosai kan buk'atar da Waziri Zayyanu ya kai masa kan Sarki! Almansur, kawai sai yaji gida ya karad'e da karatun alk'urani me girma, Ihuhhhhhhhu!!! Ya kurma wani uban ihu! Ji da yayi jikinsa ya d'auki wani mugun zafi! Mik'ewa yayi ya fara zarya cikin d'akin yana wasu sambatu, duk a k'okarin sa na Koran aljanun idan tunda  ya kirasu. Jikinsa na kyarma! Yasan duk al'janin da ya k'one ta dalilin haka sai ya d'auki fansa a kansa.

 

 

 

 

**************

**************

**************

 

Lantana tana zaune ita kad'ai a d'akin da aka ware mata Wanda take kwana a ciki take cin karanta babu babbaka, tunanini take da sak'e-sak'e na yanda zata zubawa Balaraba garin magani nan a Lemo da kuma wannan k'asar kabari, kwana biyu hidima tayi yawa ga idanun jama'a shiyasa ta Bari sai bayan buki kowa ya wa tsa sannan, to amma tana wani tunani har indai Balaraba ta shiga gidanta to ganinta ma zai mata  wahala yanzu tunanin yaya za'ayi take.

 

 

*******

*******

*******

 

 

Tun bayan sallahr Isha'i su Shahid suka tafi kowa na da iyali, sun bari sai gobe kuma zasu zo da iyalinsu domin akwai walima da suka had'a domin farin cikin Wannan rana.

 

Yana zaune shi kad'ai a falo, yana duba wannan k'aramin littafin nasa idanunsa sakaye da farin gilashi as'usuel, a tak'aica dai wayoyinsa duk kashe su yayi saboda yanda kira da sakkoni suka dame shi, "yan uwa abokai, kowa nasu yayi masa fatan alkairi, sosai ya amsawa wasu, ganin abun bazai k'are ba ne yasa ya kashe wayar domin yana bukatar Hutu a tare dashi.

 

 

Karatun yake amma hankalinsa da tunaninsa baya kan abunda yake karantawa ya tafi wani guri na daban, tunanin moment (Yanayi) da ya shiga d'azu dashi da Balaraba,, yayi ne domin ya rage ma kanshi radad'i, amma kamar karawa kansa damuwa yayi, yanzu haka daurewa kawai yake, agogon hannusa ya kalla goma shaura, yana sane da zuwan Gimbiya Halisa, shiyasa yake yawan kallon agogo,  akai-akai. Minti biyar a tsakani yaji alamun bud'e Kofa, nutsuwa yayi sosai ya ki kallon k'ofar shigowar,Gimbiya Azima ta shigo cikin sallama fuskarta d'auke da kayattacan murmushi.

 

Amsa mata yayi ba tare da ya dago kai ya kalle ta ba, kusa dashi taje ta zauna har sai jikinsu ya had'u da juna.

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿98*

 

 

 

 

Cikin wani irin salo take gaida shi. Ya amsa hankalinsa na kan littafin dake hannunsa, tunani take yaya za tayi ta jawo hankalinsa,, Cikin siririyar murya tace"Yallab'ai fatan ka yini lafiya, ina fatan kaci abunci"?

 

 

Murmushi yayi a k'asaice yace"Alhmdullahi yanzu dai bana tare da yunwa, sai dai anjima zan sha coffee"

 

 

 

Gyara zama tayi sosai tace"Haka nake so, bari in ka tashi sha sai in had'a maka"

 

 

 

"Babu damuwa" Ya fad'a hankalinsa na kan littafin.

Shiru na minti biyar, yaji shi duk a takure saboda yanda ta nani k'e shi bayan haka kuma k'amshin da take ya fara tafiya da imaninsa, abunda da Wanda ya tara sha'awa, dama a kusa yake,,

 

 

A jiye littafin yayi gefe ya d'an kishingid'a kan kujerar yana lumshe idonsa, shi kad'ai yasan abunda yake damunsa a zuciyarsa.

 

 

Sosai ta matsa kusa dashi ta d'ora hannuta kan sumar kansa Wanda take bala'in so, lumshe ido tayi, yana jinta yayi mata shiru, shima sai yaji tamkar ta nayi masa Susa ne.

 

 

 

A hankali ta d'ora hannuta a cinyar sa tana mammatsa masa jiki, ya bud'e ido da sauri yana kallon ta, ganin abun nata yana nema ya wuce gona da iri.

 

 

Wani irin abu tayi da idonta Wanda ya d'auke masa hankali sosai ta burgeshi da salon ta abunka da Wanda yake jiran k'iris, hannunsa ya sa ya rungumo ta tafad'a faffad'an k'irjinsa lumshe ido yayi lokacin da yaji tudun k'irjinta a jikinsa,, sai ya k'ara shiga rud'u sosai, Azima kan tafi shi tafiya ji take tamkar numfashin ta zai d'auke saboda tsabar shauki.

 

 

 

D'aukar jarirai yayi mata ya nufi sama da ita, Allah yasa k'ofar a bud'e take ya aje ta kan bed d'in shi a nutse yake komai,, gashi dai a cikin buk'ata yake amma bai nuna zalamarsa ba sosai, Azima kuwa ganin ta samu shiga sai ta dunga futo da salo-salo na janye hankalin maigida,,Sarki! Ya ji ba zai iya jurewa ba, babu shiri ya kashe wutar d'akin ya damk'i Azima a hannu domin ita ta kawo kanta kuma halilinsa ce.

 

 

 

Babu laifi ya samu gamsuwa da ita, yadda ya kamata kuma ya same ta cikkakiyar mace sai tana da nak'asu gurin ni'ima ya jima yanayi kafin yayi rilizing. Gashi yana d'an jin zafi a jikinsa ko Dan wannan shine na farko a gurinsa oho,,

*Ni kam mace baza ka banbamce ba sai ka kwanta da sauran biyun*

 

 

A jigace Azima ta tashi tana cije bakinta sosai Sarki! Ya gurge ta tunda ya hau kanta bai saurara ba wajan awa guda yake sai da ya samu gamsu, gashi ya d'aga mata k'afafu sama yanzu ji take duk cinyoyinta ciwo ita kama baza ta d'orar da komai ba.

 

 

 

Da k'yar ta samu ta gasa jikinta ta dauro alwala ta futo ta tada sallah, kwanciya tayi kan daddaumar ta kama baccin gajiya mamakin k'arfin Sarki! Take kamar wani doki gaskiya ta gurzu.

 

 

Bakwai shaura ya shigo gidan, ya jima a waje yana gaishe-gaishe da jama'a nan ya tarar da Azima tana sharar bacci, girgiza kai kawai yayi ya shiga toilet da kanshi ya had'a ruwa yayi Wanka ya fito daure da towol, tsayuwa yayi dressing mrioow ya fara shirya kanshi,, komai yake a nutse yake, tsaf ya shirya jikinsa cikin wata shadda wagambari ta Asali sky blue duk ya wancin kayan shi sky blue ne,, d'inkin da akai wa shaddar abun kallo ne, wani takalmi mai kyau ya zura a kafar shi ya wai waya yana kallon Azima ko motsi bata yi ba duk da wannnan kusurkusur da yake a d'akin,mamaki yake na irin nauyin bacci irin haka, hannusa yasa ya d'an daki k'afafunta shiru bata motsa ba,,

 

"Azima"

Sunanta ya kira cikin hosky voice nasa, ina Azima Sam bata San yanayi ba,, sauka k'asa yayi kawai ya k'yaleta yasan dai tayi sallah tunda gata kan dadduma.

 

 

Bayin sa ne suke ta kai kawo a falon kowa na aikinsa, yana sakkowa suka dunga barin ayyukan su, suna zuwa suna kwasar gaisuwa,, Mariya baiwar sa kenan Wanda take hidamar gyara mishi bedroom, ta nufi sama, gyaran murya yayi,Mariya ta tsaya kanta a k'asa yace"Ki bar gyara d'akin yanzu wannan ba hurumin ki bane"

 

 

Mariya tace "Tuba nake ranka ya dad'e a ya fe ni"

 

Shiru yayi

 

Tazo ta wuce kanta a k'asa.

 

 

**********

**********

 

K'arfe goma da rabi na safe Halisa ta futo cikin k'asaitacciyar kwalliya, Mama Fulani na falo a zaune tare da Madabo Jakadiya Lantana Balaraba suna zaune kusa da Mama ana gaiggasawa kamar yarda suka saba.

 

 

Madabo na ganin d'iyar ta ta futo cikin shiga ta alfarma ta masu mulki sai wani dad'i ya kamata ita kanta tasan "yar daban take da kowa. Halisa ta zauna kusa da mamanta, tana gaida Mama Fulani, Cikin sakin Fuska ta amsa, Lantana kuwa sai b'arin jiki take tana gaida Halisa, ko kallonta ba tayi ba.

 

 

Balaraba ranta ya b'aci ganin yanda take wa mutane kallon banza, Jakadiya tace" Ranki shi dad'e an tashi lafiya"?

 

 

Halisa bata duba girman Jakadiya Shafa'atu ba balle ta a gaida ita, sai da ta gama shan k'amshin ta sannan ta amsa mata.

 

 

Mama Fulani ta tsani halin Girman kai irin na Halisa ga ta ga "yar uwarta a bokiyar zamanta amma tak'i kallon shashan da take, A nutse tace" Ga "yar Uwar ki nan ko Ku gaisa ya kamata tun yanzu Ku fara had'a kanku domin mijin Ku ya samu nutsuwa da ku"

 

 

Balaraba tace"Hakane Mama cikin Siyasa da iya zaman duniya tace"Ranki ya dad'e fatan kin tashi lafiya"?

 

 

 

Halisa kanta ya k'ara girma jin Balaraba na gaishe ta, amsawa tayi fuskarta babu yabo babu fallasa. Ta mik'e tsaya Maddo tace"Yawwa maza je ki Ku gaisa da mijin ki''ki samu lada"

 

Murmushi Halisa tayi tace"Dama can na nufa Mama.

 

 

Mama Fulani ta kalli Madabo da rai a b'ace tana fad'in "Yanzu nayi gyara , kina Neman ki b'ata da Halisa da Balaraba duk d'aya suke a gurina saboda haka idan zaki zartar da hukunci duk su biyun kina da iko dasu a matsayin ki na Uwar su"

 

 

Madabo tace"Kim fad'i dai-dai Mama amma kin San ni bana shiga shirgin yara har indai ta mai dani uwarta shikkenan, amma in zata dunga d'aukata a matsayin Uwar kishiyarta , babu ruwana da ita"

 

 

Shiru Fulani tayi mata saboda tasan halin ta baud'addiyar macace.

 

"Ke Halisa tsaya Ku tafi tare da " yar uwarki, insha Allahu zan zauna daku anjima"

 

Halisa taji haushin hukuncin da Mama ta yanke, babu yadda ta iya dole tabi umarni.

 

 

Fulani tace"Balaraba tashi kuje Ku gaisa da mijin Ku"

[9/15, 9:31 AM] Akwai CittađŸ’”đŸ’”đŸ„ł: A nutse ta mik'e tana gyara zaman hijab din ta, yau ma tana cikin dugowar riga  ash color tayi amfani da irin hijab d'in nan na larabawa e had'e da hula tayi kyau sosai sai da rigar ta d'an matse ta sharp d'inta ya futo sosai,, Halisa tayi mata wani irin kallo ta watsa a kwandon shara.

 

 

 

Tafiya sukeyi babu Wanda ya kula kowa dake safiya CE, babu mutane sosai a farfajiyar gidan, dab da zasu shiga shashen Sarki! Ne motar Shukura ta danno kai cikin gidan.

 

 

Halisa ta tsaya tana murmushi domin Shukura mutuniyar ta ce, Shuruwa yarinyar Hajiya Kulu ce ta dawo daga yawace-yawacen ta na dare domin bata kwana ma a gida ba.

 

 

Ganin sun tsaya suna hira yasa Balaraba wuce wa, Shukura ta bita da wani mayen kallo babu abunda ya rikita ta sai tsarin zubin halittar ta,Balaraba a kwai jiki me kyau.

 

 

Tace"Wacece wacan ne"

 

Halisa ta tab'e baki tana fad'in Balaraba kenan wacce akayi madadi da ita tsohuwar matar Moddibo Yanzu kuma matar Sarki! Ta uku"

 

 

Shukura ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in 'Gaskiya ta had'u iya haduwa wallahi"

 

 

Wani kallo Halisa tayi mata tana Jan tsaki. Dariya Shukura tasa tana bin Halisa da kallo tana fad'in "A Gaskiya CE dole In fad'a"

 

 

Ko kula ta bata yi ba tabi bayan Balaraba wacce take dab da shiga cikin gidan.

 

 

 

*******

Har yanzu yana zaune a falo yana duba littafin  zadi zaujen, littafin dake kunshe da zamantakewa irin ta aure. Yaji motsi da alama shigowa za'ayi kafin ya an kara, Balaraba ta shigo cikin sallama"

 

 

Muryar ta da yaji ita tasa yayi saurin dago kanshi yana kallon bakin bak'in k'ofa.

 

Lumshe idonsa yayi lokacin da suka had'a ido da ita ya mai da kansa k'asa tare da amsa mata sallamar ciki-ciki, a hankali take takawa domin ta k'araso kusa dashi.

 

 

Halisa ta shigo ita da sallama, abun ya bashi mamaki sosai ya amsa mata ita, itakam fuskar ta ta saki sosai tazo ta wuce Balaraba kai tsaye kujerar da yake zaune ta nufa.

 

 

 

Hankalin su ne ya koma can idan da suka ji motsin bud'e k'ofa duk su ukun,Sarki! Shaf ya manta da cewar Azima na d'akin shi a kwance,, da sauri ya mik'e ya nufi in da take, ganin tana k'okarin saukowa daga sama tana shirin fad'uwa kana kallonta kasan tana cikin wani yanayi na wahala.

 

 

Duf-duf-duf! Gaban Halisa ya dunga bugawa, kar dai wannan a nan ta kwana"?

Tambayar kanta takeyi.

 

 

Balaraba ma taji wani abu cikin ranta amma da yake tana da wayo da dabara bata nuna ba, ammafa zuciyarta babu dad'i.

 

 

Halisa kuwa rashin hakuri lokaci guda yanayin fuskarta ya sauya da mugun b'acin rai Lallai yau dole ayi ta domin tana gani an shiga hakkinta baza yadda ba.

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿99*

 

 

 

 

 

sai ya rik'e Azima a jikinshi suka soma saukowa a hankali daga k'afar bene, sai yanzu ya tabbatar da cewar ba k'aramin jigata Azima tayi ba,domin har fuskarta ta fad'a idanunta duk sun shige loko. Ganin ya rirrik'e ta ne yasa ta k'ara lanjarewa a jikinsa tana k'ara kwanciya a faffad'an k'irjinsa,, sai wani lumshe ido take duk dan ta k'untatawa su Balaraba. Aikuwa zuciyoyin su tamkar su babbake dan rad'ad'in zafi kai kishi masifa ne, mussaman akan wanda kake so,

 

 

Baki na rawa Halisa tace"Wai Yallab'ai me nake gani ne haka? Me ya kawo wannan gurin ka da safiyar nan,ai idan za'a bi yadda tsarin al'ada yake nice zan fara kwana da kai kafin ta, ni dai gaskiya an shiga hakki na"

Ta k'arashe maganar da murya a kaurare domin kishi ya rufe mata ido yasa ta manta da wa take magana.

 

Zaunar da Azima yayi kan kujera bai ce komai ba, ya zauna gefan ta shima, ita kuwa sai wani mar-mar take da idonta ita gata wanda miji ya kwana da ita.

 

 

Sarki tsabar haushin Halisa bai sa ya kalle ta ba, ya kalli Balaraba da fuska a had'e yace"Tsayuwar me kuke min anan ko kema kina da abunda zakice a kan hakan"

 

 

Gabanta ya fad'i jin abunda yace, Yo ita me zatace don ya kwanta da matarshi ta sunna kiji d'an neman rigima ita wacce tayi masa bai sauke fushin nasa a kanta ba sai ita da bata ji ba bata gani ba" Babu yabo babu fallasa ta d'an risina ta rage tsawon ta tace"Ina kwana fatan ka tashi lafiya"?

 

 

Sai da ya gama ya mutse ya mutsen shi sannan ya amsa ciki-ciki.

 

A zuciyarta tace"Dube shi don Allah wai mu zai nad'ewa tabarmar kunya da hauka.

 

Juyawa tayi da niyar tafiya ya kalle ta a fakaice ya d'auke kansa ganin yadda mazaunan ta suke juyawa gwanin ban sha'awa"Jimana"  Zuciyarta ta tsinke tasan da ita yake inda yayi mata wannan kiran tasan wata tsirfar ce.

 

 

Juyowa tayi tana kallonsa yayi saurin d'auke kansa, yace"Ke je ki had'ama abun kari, ita wannan babu lafiya" yana nuna Azima da baki

 

 

Wannan hukuncin da ya yanke yayi mata tsauri da yawa ita kam bata ga inda aka tab'a haka ba,  wacce ta kwana da miji daban me kula dashi daban,, zuba abunci kawai za'ace baza ta iya ba, Ba tace komai ba ta nufi daining area cikin yanayin tafiyarta,dama abunda yake so kenan kallo ya bita dashi babu ko kunyar su Halisa da Azima da take fafar tana tare dashi hankalinsa da tunaninsa nacan gurin kallon rausayar Balaraba da tsarin jiki me kyau da Allah ya hore mata, duk namijin da ya d'ora idonsa a kanta sai ya kyasa balle kuma mace "yar uwarta.

 

 

 

Halisa ta k'ara cika tayi fam-fam tamkar ta fashe da kuka haka take jin zuciyarta ita a ganinta ita aka takewa hakkin ta.

 

Yana sane yak'i kallon gurin da take tsaye domin ba k'aramin haushi ta bashi ba da kan maganar da tafad'a.

 

 

Jiki a sanyaye ta je ta zauna kusa da shi suka sashi a tsakiya, Azima cikin barikan ci da iya duniyan ci, ta mak'e murya irin me jin jikin nan, tace" Barka da safiya Uwargidan mu"

 

 

Ko kallonta ba tayi ba,, hankalinta na kansa Wanda ya d'auke kansa tamkar bai san akwai ta a gurin ba,

 

 

Murya a sanyaye tace"Ina magana fa ka share ni"

 

Kallonta yayi yace"Ki je ki koyo yanda ake magana tunda ke kin ki kiyi hankali har yanzu"

 

 

K'walla ta taro a idonta Lallai yau bata futo a sa'a ba komai a kanta ya k'are gara ma wacan wahalalliyar ita ya kula ta, cikin rashin abun yi tace"Ina kwana

 

 

Kallonta yayi kamar yasa dariya domin ta bashi ita sosai, wai Ina kwana, fuskarshi ya kara had'ewa yana fad'in"Bazan amsa ba, sai kinje kin koyo yanda ake lafazi"

 

 

Azima burinta ya cika jin yadda ake dizga Halisa sai wani lumshe ido take na jin dad'i.

 

 

Halisa hakurin ta ya soma zuwa k'arshe da Jan ido ta kalle shi tana fad'in "Wai me yasa kake min haka hubby naga dai ni dakai auran soyayya mukayi ba auran had'i ba, kuma ba wani ne ya mutu akayi maka madadi da ni ba, kana sona ina sonka,to me yasa zaka dunga wulakanta ni a gaban Wanda basu isa ba"

 

 

Kowa yayi zagi yasan da wanda yake,, Ba Azima ba har Balaraba sun gane habaici Halisa take musu"

 

 

Shi ko Sarki! Kallonta yake gwanin ban haushi har da goge hawaye, shi kam bai ga abunda yayi mata ba da har take kuka idan laifi ne itace tayi,dole ne kuwa ya koya mata zamantakewa domin baya son rashin zaman lafiya a gidan shi.

 

 

Yace"Kin shigo kina kallonmu d'ai-d'ai ke ga Gimbiya matar Sarki, ko? Bayan nan kin zo kina min wata maganar banza da bata da tushe balle makama, Eh na kwanta da Azima jiya kwanciya ya aure laifi ne, ke me ya hana ki kawo kanki tunda kina tak'amar da cewa kece Uwar gida wacce a ka fara d'aura min aure da ita" shiru yayi na minti biyu ya cigaba da cewa"Bari ki abunda baki sani ba, Dan an d'aura maka aure da mata uku ko hudu a rana to bai addini bane kace Lallai sai da wacce aka fara d'aura maka aure sannan zakayi tara da ita ba, alhalin basu tare ba, ita ta kawo kanta gurina sai me ai itama matata CE,don haka ya rage naku yanzu Ku tsara yaya zaku raba kwana kamar yadda addini ya tanadar"

 

 

 

Sosai Halisa take kuka taji zalin fad'an da yayi mata ahalin yanzu babu wata kalma da zata kara futowa daga bakinta bayan ya gama wulakanta gaban kishiyoyin ta.

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿100*

 

 

 

 

 

 

 Tashi tayi jikinta a mugun sanyaye ta nufi k'ofar futa daga falon, ko kallo bata ishe shi ba balle ya hanata tafiya.

 

Balaraba ma cikin k'warin jiki tayi saurin had'a duk abun buk'ata kan daining d'in ta jera komai gwanin sha'awa, cikin nutsuwa ta baro gurin, kanta a k'asa ta tsaya nesa dasu tace"An kammala komai"

 

Yana jinta sarai ya share tamkar bai  ji ta ba,, d'ago kai tayi suka had'a ido, gaskiya ta tsani kallo wallahi ta lura kuma kamar d'abi'arshi ce,abunda Balaraba bata sani ba kuwa kallon kurulla ba hallin Sarki! Bane mutuk'ar ya damu Abu da kallo to tabbas abun yayi masa kuma ya k'yatar dashi,, Kishin Balaraba kamar ya kashe Azima domin ita ma ta lura da irin kallon da yake mata.

 

 

Gyaran murya yayi k'asa-k'asa yace"Sauran ki d'akina ki hau ki gyara min, ita wannan bata da lafiya "

Ya k'ara maimaita mata maganar da yayi mata akaro na farko.

 

Farko yace mata ta had'a musu abunci yanzu kuma yace mata ta gyara masa d'aki wato yana nufin ta gyara inda suka b'ata ko yana so ya nuna mata Lallai yayi rayuwar aure da Azima ita a ganinta ba sai ya nuna mata komai ta gane sarai, b'ata fuska tayi kamar tace baza tayi ba, kuma sai ta tuno karamcin Fulani a gareta, kai tsaya ta juya da niyar hawa saman bene inda d'akunan baccin sa yake.

 

Wannan kallon dai ya bita dashi, yana sauke wata sihirtacciyar ajiyar zuciya,, Azima ta d'ago kanta dake jikinsa tana kallonsa sai taga kwata-kwata ma hankalinsa baya kanta, bak'in ciki kamar tayi yaya, murya a sanyaye tace"Yallab'ai ya kamata muje kaci abunci zan wuce b'angaran da na sauka a kwai "yan uwanmu nacan na jira na da yawa daga cikinsu yau zasu tafi"

 

 

Babu abunda yace mata, ya mike a tsanake ya nufi daining  mik'ewa tayi da kuzari ba kamar d'azu ba ta bi bayansa

 

Balaraba na shiga d'akin ta tadda bed d'in duk a  hargitse duk nauyin bedshirt d'in dake shimfid'e a bed d'in ya hautsine da alama ba k'amin dirama aka sha jiya ba, wani mugun b'acin rai ne ya turnuk'o mata zuciyarta tamkar ta tarwarshe haka take jin wani matsananci kishinsa yana damunta, wai ya akayi ne ta yarda mutumin nan ya raina ta, Wannan fa ba sara bace, yasan dole zata gani kuma zataji ciwo shine zai ce ta gyara masa d'akin,me yasa bai sa Halisa ba saboda yasan baza tayi ba kenan, don dai ita yasan komai yace tayi tanayi shine zai sanya ta wannan aikin gaskiya ta canza shawara baza tayi ba,ita wacce aka kwanta da ita tazo ta gyara abunta, wallahi ya mugun raina mata hankali ma, tana ganin zata dawo masa da ainihin kalar ta, gudun irin wannan rainin, rai a b'ace ta juya domin barin d'akin shi kuma ya sako kai zai shigo sukayi gware goshi da goshi, ja da baya tayi tans dafe goshin ta, cike da takaicin sa, shigowa yayi dakin sosai ya mai da k'ofar ya rufe yana bin d'akin da kallo ganin babu abunda tayi a ciki.

 

Kallon juna sukayi ita dashi,wannan karon tayi jarumtar tsayar da idanta a kansa domin ta fara yak'in k'watar kanta a ganinta rainin hankalin yayi yawa.

 

 

Cikin yanayin maganar shi yace"Baki gyaramin bed ba ina so in kwanta, oh ko da yake ma naga babu wani gyara a d'akin sai shimfid'ar ki cire bedshirt d'in ki sanya min wani zan kwanta in huta"

 

 

Babu zato taji bakinta ya sub'uce mata da cewar"Ita wacce ta b'ata me hanata gyarawa nifa wannan ba hurumi na bane Allah shi gafarta maka"

 

 

 

Yadda tayi maganar yaso ya bashi dariya Lallai itama za'aje da ita.Yace"OK yanzu me kike nufi"?

 

"Cewa nayi ba hurumi na bane gyara bed d'in nan da dai nice na kwanta a kai sai in gyara da hujja"

 

Sai da tayi wannan maganar tazo tana da tasani ganin tana nemam ta zarme, sai ta sunkuyar da kanta k'asa kunya na yunk'uro mata.

 

 

Tsaf ya fahimci abunda take nufi kuma ya gano kishi ne yake damunta,, wani murmushi yayi yana me tsatstsata da idanunsa masu dafi, yace"Kema kinyi magana me kyau, jiya Azima tazo ta faran ta min rai, ta d'ebe min kewa ta shekara da shekaru, yau kema kin kawo kanki bari kawai mu barshi in kin b'ata sai ki gyara naki"

 

 

Ita ba yarinya bace tsaf ta fahimci abunda yake nufi, kallonsa take cike da d'umbun mamaki wato shi rashin  rashin hak'urinsa bazai bari a kawo masa matayen nasa ba

 

Kulle k'ofar yayi sosai ya zare key d'in ya wuce toilet abunsa.

 

Baki sake ta bishi da kallo tana mugun mamakin k'arfin halinsa da sauri ta nufi k'ofar tana jijjigata,, kamar dotse take ja tak'i motsawa, wani bala'in tsoro ne ya tsirga mata tayi da ta sanin wannan maganar tayi shiru da bakinta tayi abunda ya sata yanzu yaya zatayi da fitinar wannan mutumin,, shiru tayi jikin Kofa tana sak'a wacce zata fisshe ta. Futowa yayi yana goge hannunsa ya zauna gefen bed d'in yana k'okarin cire rigar dake jikinsa,, kallonta yake a fakaice yaga duk ta mu zanta, yau zai ga tana da wayo ko bata dashi.

 

 

Shawarwari take da zuciyoyin ta wata na bata shawara kan taje tayi aikin da ya sata wata na cewa ta bashi hakuri wata na cewa kawai ta kyale shi dole ai sai da amunce war ta kome ye zai faru,,,

 

Da kansa ya janye bedshirt d'in ya jefar k'asa kan katifar ya kwanta sosai yayi rigingi ne gami da d'ora hannuwan shi saman k'irjinsa lumshe ido yake da alama baccin zai yi.

 

 

Da k'yar ta bud'e bakin ta tace"Ka bud'e min k'ofa zan futa ana jirana a b'angaran Mama"

 

"Yau duk wanda yake jiran ki sai ya hak'ura domin shi da ya sake ganin ki sai da gobe idan Allah ya kai mu"

Ya fad'i haka ido a lumshe.

 

 

"Kasan dai wannan ba al'adar mu bace ko,ai ka bari a kawo maka ni tukkuna"

 

 

Bud'e idonsa yayi yana kallon ta Jin abunda take cewa wai ba Al'ada bace"

 

Mik'ewa zaune yayi sosai ya fuskance ta tana daga bakin Kofa kamar kace kett ta ruga a guje yace"Zo ki fad'a min al'ada tun da ita ki ka sani, i n ban da shirme irin naki an riga an d'aura aure kuma me ya rage miki, dole sai an lullubo ki an kawo min,, shiyasa ni Azima take burge ni sosai take da waye wa, amma ke da wancan duk baku iya komai ba sai kishi" Kallonsa tayi jin abunda yake cewa kar dai ya gane cewar tana kishin sa,,

 

 

"Addini na bai hanani in kusance ki ba a yanzu saboda kina a matsayin matata ke kin zo kenan ma ba zaki koma ba kalas!!" Balaraba ta tsorata da jin abunda yace karfa girman kanta ya kai ya ya baro Bari kawai ta bashi hakuri durk'usawa wada ba gajiyawa bane,, murya na rawa tace"Kar muyi haka da kai ni dai don Allah ka bud'e min in futa kaji ko, wallahi ina jin kunyar mama sosai"

 

 

Komawa yayi ya kwanta k'asa -k'asa yace"Sai kin biya min buk'ata ta zan bud'e miki"

 

 

Ba taji abunda yace ba tace"Me kace ban ji ba sosai ba"

 

Bud'e murya yayi yanda zata ji yace"Sai kin biya min buk'ata ta zan   miki Kofa ki tafi"

 

 

Kuka tasa tana fad'in Wannan wace irin magana kake min ne, nifa kawai ka bud'e min Kofa in tafi gurin Mama Fulani daga zuwa gaishe ka sai ka kulle min k'ofa"

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿101*

 

 

 

 

 

Kallon ta yake tana kuka sai kace wata k'aramar yarinya, sosai ta bashi sha'awa, kuka yana sa wasu muni ita ya sa ta kyau Lallai Allah d'aya gari bam-bam,Ashe akwai abunda zai kar ya mata zuciya da sauri har ya sanya ta kuka irin haka. Mik'ewa yayi da kuzari a jikinsa ya durfafi in da take tsaye,, da sauri ta matsa da gurin, inda ta koma ya bita bai yi wata-wata ba ya d'auke ta kamar wata yarinya ya dure ta kan bed d'in gami da yi mata rumfa da faffad'an kirjinshi mai sanya mace me Lafiya ta manta kanta...

 

 

 

*********

*********

*********

 

Sosai Arrama yake sasakar Shamsiyya sai da yayi sau biyar sannan ya sirara mata, to da yake itama Shamsiyar numbar one ce a wannan gurin sam bata gaji ba, inda zai cigaba tana so,, domin ba k'aramin gamsar da ita Arrama yayi ba,, sosai taji dadin harkar, mik'ewa tayi yana mik'a gami da gan tsaro k'irjinta nonuwan ta suka ban k'aro, gaba, Arrama yaji kamar ya sume wata sha'awar ta rikito masa, ido jajuzur ya k'ara afka mata,, ta rungume shi k'am suka cigaba da aikata masha'arsu, kusan minti talatin sunayi daga busani suka samu nutsuwa a tare, fuskarsu cike da walwala da farin ciki suka sanya kayan su Arrama ya koma ya zauna kan wannan dutse da ya tashi, yace" Dole zan dage da tsayuwar dare gurin ganin na kafa sonki a zuciyar Sarki! Tunda kika bani kanki zan dage in yi miki aiki yadda ya kamata, don haka zamu d'auki tsawan sati biyu kina zuwa nan INA kwanciya dake kamar irin nayau, ni kuma ina miki aiki, zakiyi mamaki sosai kafin sati biyun aikin ki zai yi kyau yanzu ki shirya ki je gida gobe kizo kamar wannan lokacin"

 

 

 

Shamsiyya ta mik'e tana sanya kayan ta sai godiya take, shi kuma sai bin jikinta da kallo yake tamkar wani tsohon maye.

 

 

 

*****

 

Cikin tsanani b'acin rai Halisa ta fad'a cinyar Mamanta ta fashe da kuka sosai,, hankalin Madabo ya tashi fad'i take "Wai Lafiya zaki shigo kina wa mutane kuka "?

 

Mama tace" Tambaye ta a hankali mana"

 

Halisa tak'i cewa komai in banda kuka babu abunda take, sosai taji ciwon abunda Sarki! Yayi mata gabansu Balaraba.

 

 

Kiran sunanta Mama tayi ta d'ago kai tana goge hawaye Mama tace"Me ya faru INA Balaraba take"?

 

Murya na rawa Halisa ta warware musu abunda ya faru, tana k'arasa maganar da cewa"Baza ta k'ara zuwa ba sai dai in shine ya neme ta

 

 

 

Murmushi Mama tayi tasan kishi ne yake damun Halisa ba komai kawai daga kinje kin ga Ka shiyar ki da miji sai kice baki yarda ba, ai ke ce Uwar gida,, dole miji ke zai fara kulawa wannan ba addini ban.

 

 

 

Madabo ko fad'a take sosai tana fad'in an shiga hakkin "yarta  Mama duk na jinsu da abunda suke cewa sai da suka gama sannan ta kalli Halisa tana fad'in"Kullum aka ce dake baki da wayo sai ki k'i yarda, hum kinga su da yake suna da wayo gashi sun San yarda zasu bi su zauna dashi,, ke Kin yo zuciya kin tawo , ko wa ya gaya miki anawa namiji haka oho,, abunda kike tuhumar mijin ki dashi ba laifi bane, saboda sunna ya aikata,, babu laifi idan haka ta faru a kanki tunda dake dasu duk d'aya ne, saboda haka ki kwantar da hankalin ki ki daina zargin mijin ki kan ya zalin ce ki,, yawwa, Bari in yi masa waya yazo nan in ja muku kunne duka in sha Allahu yau ko wacce za'a mik'ata d'akin ta, tunda haka yake so"

 

Sai yanzu Halisa ta gane kwab'ar da tayi ta manta Halinsa baya son hayani ko kuma yayi tai maka magana ka k'i ji tuntuni ya fad'a mata ta canza hali tak'i gane wa.

 

 

Jakadiya ce ta mik'e ma mama wayar ta nemo numbar shi ta kira, a kashe ta ke sauran layin kan nashi ma duk a kashe,, tace"Ya kashe wayar watak'ila ya kwanta ne, saboda gajiyar jiya, amma insha Allahu yau da yamma zamu zauna daku, ki kwantar da hankalin ki"

 

Halisa tace"Insha Allah Mama zan kwantar da hankalina in fahimci abunda yake so da Wanda baya so"

 

 

*******

********

*******

 

 

B'angaran su Sallau kuwa zuciyoyin su suna cikin mawuyacin hali damuwa da b'akin ciki yasa Uwa! A gaba sam bata ganin tarin alkairai dake gidan domin yanzu basa awo tunda nau'in kayan abunci akwai a gidan Wanda Mama ta aiko musu dashi,, Sadiya da Iya sun had'e Kansu Sam basa shiga shirgin Uwa! Duk da irin habaice-habaice da take musu, girikin su suke su koshi har su bawa mak'ota Sadiya na fad'in"Hafsatu kin iya haihuwa albarakacin kaza k'adan gare keshan romo, mutukar Uwa! Taji to ranar yini take tana zage-zage, duk tabi ta zauce kullum ga ganta da d'aurin k'irji da ta d'aga hammta tsami! Da hamami za gume gurin gashi ne, cunkus! Yayi jajazur dashi,,, Komai ya hautsine mata ga jikin Sallau ya k'ara rikice wa sosai yake jin jiki kafarsa d'aya ta daina aiki tare da hannushi guda ga wani irin tari da yake Wanda idan ya turnuk'e masa sai yayi a wa guda yanayi majina me had'e da jini na futowa, amma duk da wannan halin da yake ciki mumman zuciyarsa bata risina ba,, Iro ya bud'a uwa duniya,, Mabaruka kuwa dama sai tayi sattitika a waje in kaga ta kwana a gida to akwai dalili. Walidi ne me dama-dama shine yake zuwa kasuwa duk ya bar abunda yake Allah ya shirye shi kullum cikin shiwa Balaraba albarka yake, yana Dan kula da iyayen sa babu laifi kasancewar yana zuwa makaranar magariba ta maza ana fad'a musu hakkin iyaye kan "yayansu, Duk sanda yaji Uwa! Ta damu da Zan can Lantana kan yak'i dawo wa sai yayi dariya yana fad'in " Kema wasa kike wallahi ki cire tsammanin dawowar Lantana ai ta tafi kenan , Lantana ce zata daula irin haka ta dawo, kuma Ku nemi yafiyar Allah kuma Ku nemi Afuwar Balaraba don wallahi duk hakkinta ne yake bibibyar Ku, mussaman kai Babanmu" Sallau babu bakin magana sai da kawai ya daga kai sama.

 

 

 

Ita ko Uwa cewa take, "In har sai na bawa Balaraba hakuri sannan al'amurana zasu gyaru wallahi gwara in mutu in huta"

 

 

*********

*********

*********

 

Numfashin su ne suka dunga had'uwa guri guda,, Saboda tsananin kusancin da yake tsakanin su, tsinin hancin sa na tab'o nata  hancin leb'unansu na goguwa da juna,, lumshe ido tayi tana jin wani yarrrr!! A jikinta,, hannun yasa ya na wasa da siraran leb'unanta masu taushi da sanya masa kasala,, bud'e idonta tayi tana kallon sa, bata da bakin magana,, domin ko tace zata yi to asirin ta na iya tunowa shiyasa ta yi shiru da bakin ta, babu zato taji ya bud'e mata k'afafu ya shiga tsakiyar ta, gami da d'ora bakin shi kan nata,, abun mamaki sai ta tsinci kanta da bud'e masa bakinta ya zaro harshen ta ya fara tsotsa tamkar Wanda ya samu alawa,, numfashi take futar wa me wahala, shi kuwa ubangayar ya gigice inda yake zuba mata kiss na gani na fad'a Wanda ba ko wacce mace zata samu haka daga gurin sa, ba, tana can wata duniyar taji saukar hannusa a k'irjinta da sauri tayi yunk'urin ture shi ta kasa, domin ya sanya mata k'arfin sa, kuka ta farai masa ganin da gaske yake yak'i ya daina abunda yake, mata, zare bakinsa yayi daga cikin nata, ya mayar wuyanta yana lasa, da harshen sa, sai ga Balaraba tana kyarma duk jikinta cinyoyin ta sai karrrr-karrr suke yi jin wani irin salo da yake mata, duk bayan sa take tana kukan shagwaba hakan ya k'ara gigita shi, sosai ya ke mata wassani masu zafi har sai da yayi nasarar cire mata rigar jikinta dake duguwa ce ya rage daga ita sai brz da pant,, ya samu yanda yake so shima ya rage kayan jikinsa ya fara cakud'a mata jiki, kai ranar Balaraba taga yanda maza suke sosai ta furge ganin yadda duk kamanin sa suka sauya, Abu da Safiya babu duhu in banda abun d'a namiji komai ai yana san sirri,, tsabar tsoro bai bar ta ta saki jikinta ba balle itama ta kwashi roman damukurad'iya,, Shi ko ai bai saurara mata ba sai da ya tabbatar da ya samu gamsuwa yadda ya kamata, duk ya b'ata mata jiki da bedshirt da abunshi,, jikinsa a mace ya sauka daga bed din daga shi sai k'aramin Wanda ya nufi toilet, kunya ta hana shi kallon fuskar ta.

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿102*

 

 

 

Balaraba ta rasa ta inda zata fara,, tsabar takaicin abunda yayi mata, Duk jikin rigar ta ya b'aci da abunshi babu damar ta sanya ta gudu tunda taga inda ya aje mukullin,, yanzu daga ita sai briz da wando, hawayen bak'in ciki take sharewa, tana tunanin yaya za tayi yanzu. Lullube jikinta tayi da bargo har fuskarta,, tana jin motsin futowar sa daga toilet d'in tayi shiru abunta har yanzu ba ta daina hawaye ba

 

 

Shirya jikinsa yake yana satar kallonta ganin ta rufe fuskarta,, ko motsi ba tayi,, a tsakana ke ya shirya tsaf Cikin shigar sa ta ko da yaushe wato kayan su na sarauta, turaren shi ya fesa tas dashi kana kallon shi kasan yana cikin walwala da farin ciki,, har inda take ya k'ara ya tsaya a kanta kusan minti biyar yana nazarin ta.

 

Duk da take lullub'e tasan da mutum a tsaye a kanta,, jikinta ne ya fara d'aukar zafi, gyaran murya yayi gami da fad'in"jimana" Banza tayi dashi ba tan ka masa ba

 

Zama yayi kusa da ita yana Jan bargon, ta rik'e da kyau, "Wai meye haka kike ne ? Sai kace wata " yar k'auye uhumm? Ki tashi ki kimtsa jikin ki ni zan fita"

 

 

K'in kula shi tayi, sai shashekar kukan ta da yaji,, yasa jikinsa yin sanyi yace"Kuka kike"?

 

A sark'e tace"Ba dole nayi kuka ba haba wannan abun takaici duba fa yadda ka b'ata min jiki da kaya na, yanzu wane kayan zan sanya"?

 

Fuskarta a lullub'e take maganar.

 

Sai yanzu ya fahimci yayi kwab'a rigar ta ya d'auko yana dubawa,aikuwa duk ta b'aci,,, bai CE komai ba ya mike tsaye had'e da cire alkyabar dake jikinsa kai s.tsaye toilet ya nufa da ita, da kanshi ya bude injin wanki ya sanya rigar ya wanke mata tass ya busar da ita,, hannushi rik'e da rigar ya futo daga toilet din ya tsaya kanta yana fad'in "Tashi gashi na wanke miki"

 

 

Cikin mamaki ta bud'e fuskarta tana kallon shi,, aikuwa rigar ta gani a hannushi da alama kuma a wanke take, hannu ta ziro ta karb'i rigar tana dubawa,, kallon ta yake fuskarsa babu yabo babu fallasa, ita kam mamaki take wai da kanshi ya wanke mata Riga,tarasa gane wane irin hali ne dashi,,

 

K'asa-k'asa tace"Ka matsa daga kaina to zan sanya rigar"

 

 

"Baki Isa ba"

Yafad'a kai tsaye ya cigaba da cewa "Ki tashi kawai kije ki tsarkake jikin ki sannan.

 

 

" Babu fa kaya. a jikina fa"

Tafad'a jikin haushi.

 

"Eh na sani"

Yafad'a yana zama kusa da ita,, yana fad'in "Ko ki tashi ko nayi me gaba d'aya, babu abunda akai miki kin lanjare, ita Azima ai jaruma ce"

 

 

Haushin abunda yace yasa ta mike a fusace daga ita sai k'aramin wando da briz ta nufi toilet d'in da gudu... .. Domin tana ganin ta tsaya sanya zai kalle mata jiki

😃

Ni ko nace Balaraba kenan yanzu ma ai ta kalle miki duk wayon ki Sarki! Ta fiki"

 

 

Dariya yake sosai bayan shigar ta ya mike a nutse ya sauka k'asa.Lokacin da ta futo baya d'akin cikin sauri ta sanya kayan ta, ta sauka k'asa,, yana zaune kan kujera da waya a kunnen sa, da alama waya take, da sauri ta nufi k"ofar futa tun kafin ya gama wayar ya b'ullo mata da wata tsurfar,, ba zato taji yace"Jirani mana mu tafi tare zanje mu gaisa da Mama"

 

Da sauri ta futa ba tare da taji karshen maganar tasa ba,yaya ma za'ayi ta jera dashi ga mutane da dama ai da kunya,, yanzu ma bata San abunda zata cewa Mama ba in ta koma.

 

 

*******

Shamsiyya kuwa kullum tana tafe a hanyar gidan Arrama ba ta dawo wa sai dare, sai sun gama sha'aninsu kullum yana fad'a mata ta kwantar da hankalin ta, kamar ta auri Sarki ta gama ne,, Uwa yau da bakin ciki ta tashi a gidan kasancewar ko ina ta juya babu dad'i gashi bata da ko kwabo yanzu bata sai dai komai duk jarin NATA ya k'are gurin bin malamai da bokaye,, Tsarkar gida ta futo tana ta surfa bala'i ta zauna kan kujera sai durawa Lantana ashar take tana fad'in"Ban tab'a ganin tsohowar najadu ba irin wannan matar kiri-kiri ta gudu ta barni da wahalar jiyyar danta shegiya munafuka Ashe da ta karb'i asirin domin  taje ta aiwatar ba abunda ya kai ta bane, to Wallahi yau sai naje na tona mata asiri a gidan,wai ni zata munafurta shigiya tsohuwar najadu"

 

Sallau na daki yana jin Uwa na zagin mahaifiyar shi bakin ciki kamar ya kashe shi,,, cike da taikaci yace"Uwa!! Yanzu Lantana kike zagi? itama fa a matsayin mahaifiyar ki take""

 

Cikin masifa tace"Rufe min baki mutsiya ci kawai Uwata ko uwarka ni wannan munafukar matar bata haife ni me halin "yan wuta"

 

Wani mugun tari ne ya sark'e Sallau yana daga hannusa guda yana son yayi magana ya kasa da k'yar yace"Uwa!ke ba matar rufin asiri bace kije na sake ki saki uku tunda kika zagi mahaifiya ta"

 

 

"Ahayye nanaye"!!! Ayurrrrrr" Yau Allah ya raba ni da k'aya mutan gida Ku futo Ku taya ni murna"

 

Sadiya da Iya duk suna jin abunda ya faru sukayi shiru suna mamakin abunda dama ya kai Lantana gidan sarauta duk Dan ta cutar da Balaraba ne, Allah yasa Allah ya tona mata asiri.. Iya bata tsinke da al'amarin ba sai da taji Sallau na fad'in ya saki Uwa saki uku sannan ta futo daga daki tana salati gami da fad'in "Assha Sallau ka yanke hukuncin da bai dace ba, Sallau ba a saki cikin fushi"

 

 

 

Sallau ya fashe da kuka yana fad'in "Dole In  rabu da Wannan bak'ar dagar matar Atika kina ji fa tana zagin Lantana duk lalacewar ta mahaifiyar ta CE kuma itama ta haife ta tunda dai yar uwarta ce"

 

Iya tace"Duk da haka dai, hukuncin da ka yanke bai dace ba"

 

Uwa! Ta futo daga daki Cikin shiri tana fad'in "Duk naji abunda kake cewa munafuki me kashi a kwance akwai bak'ar daga irin uwarka me muguwar zuciya kawai wallahi yau   sai na tona mata asiri a gidan Sarki yanda ka ganni nan a shirye nake" Waje ta futa kamar sabuwar mahaukaciya  sai surutai take, Iya da Sadiya suka bita da kallo cikin mamaki.

 

 

Tana futa Sallau ya dunga wani irin tari Wanda I n yayi sai wata majina ne kauri bak'ak'irin ta futo daga bakin sa, ga wani uban wari da take,, DA k'yar ya bud'e bakin sa yace"Atika ki yafe mun abubuwan da nayi muku ke da "yan uwanki Wanda na sani da Wanda ban sani ba ki yafe min Wannan ciwon nawa bana tashi bane, hak'ika na aikata abubwa Mara kyau don Allah ki nema min gafara gurin Balaraba da duk Wanda na batawa jikina na bani mutuwa zanyi"

 

Iya ta fara share hawaye tana cewa"cuta ba mutawa ba Sallau Insha Allahu zaka tashi kayi hakuri ka daina wannan maganar" Sallau yace"Kayya  Atika ni nasan abunda nake ji hak'ika na zalinci Ayuba da matar shi da yarsu Balaraba don Allah ko na mutu Ku Bini da addu'a"

 

Kuka iya take tana bashi hakuri gami da yi masa addu'a ta kalli Sadiya dake tsaye hawaye na zuba tace"Ki kira Maman a waya yazo su gana"

 

Cikin dauriya tace"Kin manta "yau kwanan shi biyu da tafiya sun tafi Jalingo,zasu sauke kaya"

 

Iya tace"Hakane kuma kira Walidi yazo ya kai shi asibiti jikin nasa yayi tsanani yau"

 

******

******

******

 

Fakad'an-fakad'an Uwa! Ta shiga gidan sarautar Sai ta hau zare ido ganin wasu mutane sun yi kanta da zabgegiyar bulala sun ganta kamar mahaukaciya, Dogari yace"Keee!! Wa kike nema ne"?

 

Cikin rawar baki tace"Nazo gurin... Ummm gurin Balar....Balaraba Nazo"

 

 

"Wacece Balaraba"?

Yafad'a yana daga bulala zai shauda mata gani yake kamar da mahaukaciya yake magana.

 

 

Jiki na kyarma tace" Matar me Martaba Sarki! Almansur wacce a ka  d'aura musu aure she karan jiya"

 

Nan take Dogari ya fahimci wadda take nufi cikin matan Sarki! ita ce matar Moddibo ta da, da kansa yayi mata jagora har shashen Mama Fulani, ya juya ya bar gurin ba tare da yace mata komai ba,, Harara ta bishi da ita tana tsaki kofar shiga ta nufa gadan gadan, masu tsaron gurin suka yo kanta suna zare ido suma a d'aukar su mahaukaciya CE, baya taja da sauri tana zare ido ta fara yi musu bayani nan suka gane suka bata hanya suna mamakin me ya kawo ta gurin Balaraba ko da yake sun San dama ba "yar gidan kowa bace.

 

 

Mama Fulani Jakadiya da Lantana had'e da Madabo suna zaune suna hira Lantana ta tsagalgale Sai labari take basu, kawai suka ga mace ta afko d'akin ba sallama.

 

 

A furgice suke salati domin sun d'auka mahaukaciya CE,,

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿103*

 

 

 

Uwa! bata tsaya ko ina ba sai gaban Lantana tayi mata k'ik'am a ka tace"Yau asirin ki zai tuno yau ranar Wanka ba a b'oyan ci bi, munafukar  Allah ta'ala,, kinzo da niyar ki cuci Balaraba kin samu gidin zama a gidan saboda an ga daula, da jin dad'i gami da cima me kyau da makwanci me kyau,, shine kika mak'ale kika manta da alk'awarin mu dake, to saboda haka sai ki tashi kije ki d'auko min kayan aikin da kika karb'a a hannuna"

Ta k'arasa maganar kamar zata kai mata duka.

 

Lantana ta mike da k'yar tana kallon ta tace"Uwa! Yaushe kika haukace ne, kawai zaki fado mana daki babu ko sallama to in kina cin k'asa ki kiyayi ta shuri nan ba gurin wasa bane, wallahi in kin saba yin rashin mutumin ki a can nan kikayi suka zaki ci"

 

 

Wani wawan mari Tayi tsalle ta tsinkawa Lantana tana hakki sai kace zakanya tace"Ni ai wa garin nan? Ni za'a yaudara wato kina so ki lauya maganar kenan munafukar tsohuwa kawai"

 

Cikin mamaki da al'ajabi Mama take kallon Uwa! da sauran mutanan gurin Balaraba ranta in yayi dubu ya b'aci wato sun zo suna hali ne sun zo su mata tone -tone a gida ne.

 Lantana kuwa tana gefe guda hannuta rik'e da kuncin ta tana mamakin marin da tasha daga Uwa! Lallai yau ta tabbatar da cewar Uwa! Ba tada mutumci kuma bata da kunya ko kad'an wai ita ta tsinkawa mari a gaban mutane,,,

 

 

Jakadiya Shafa'atu ta buga Uwa! Tsawa tana fad'in"Hattara dai baiwar Allah nan ba gurin wasa bane idan baki da hankali nan ake koyar dashi, kar ki manta kina gaban Fulani me dakin gabas matar Sarki Almustafah, in daga turo kika futo to yanzu za'a mai dake"

 

 

Uwa! Ta fashe da kuka ta zube gaban Mama tana k'okarin rik'e mata kafafu Mama ta janye k'afar ta cikin tsoro tace"Baiwar Allah me ya kawo ki nan"

 

 

Cikin kuka Uwa! Tace"Ki gafarce ni Uwar dakina ban so na shigo nan da wannan sigar ba, raina ne a bace" ta sauke ajiyar zuciya ta cigaba da cewa"Ni dai sunansa Uwa! Matar Sallau a da kenan Wanda yake a matsayin uban Balaraba, wannan kuma" tafad'a tana nuna Lantana da tayi tsilli-tsilli a tsaye har yanzu hannuta na dafe da kuncin ta, ta cigaba da cewa" Wannan ita ce Lantana Kenan Uwar mijina Sallau ta kasance muguwa CE azzalima me son kanta duk wata masifa Dana ke ciki dani da "yayana itace sila, hakanan duk wani bala'i da Balaraba ta shiga itace Sila, itace tayi sanadiyar kashe kishiyar ta Suwaiba mahaifiyar uban Balaraba Ayuba kenan, bayan haka kuma itace tayi sanadiyar kashe iyayen Balaraba, itace tayi sanadiyar da " yayana suka zama karuwai itace ta nuna min hanyar bin gidajan malamai da bokaye gami da "yan bori,, tun lokaci da mukaji labarin auran Balaraba da Sarki! Muka bazama gurin malama domin mu rusa abun Allah bai yi ba, sai da mukayi nasara karbo asiri gurin malamin mu Wanda aka je aka debo kasar kabari aka had'a dashi domin a zubawa balaraba. Kan hanyar ta ta wucewa idan ta tsallaka ta hau kace,sai Shamsiyya ta maye gurbin ta"

 

Mama ta rafka Salati da sallami tace"Da kanku kuka aikata wannan aiki"?

 

 

Uwa! Ta daga Kai tana share hawaye, ta cigaba da cewa"Duk nau'in kayan asirin yana gurin ta wannan zaman da kuke tare da ita bashi da amfani ne tazo ne domin ta aiwatar da kudirin ta,, Yau a kanta Sallau ya sake ni saki uku duk ya manta hallacin da nayi masa na ciyar dashi na shayar dashi duk ya manta shiyasa kawai naga gwara inzo in tona mata asiri"

 

 

Lantana ta dunga rantse-rantse cewar k'arya take mata duk sharri NE ta nayiwa Balaraba bakin ciki NE ganin ta a gidan sarauta, Balaraba kuwa in banda kukan bakin ciki babu abunda take,, lokacin su Sadiya da Usuman suna makaranta,, wani irin tausayin ta ne ya dura a zuciyar Madabo mahaifiyar Halisa kenan Lallai yarinyar tana ganin rayuwa.

 

 

Mama tace"Duk Ku rufe min bakin ku anan, sukayi shiru,, suna zare ido kallon Lantana cikin bada Umarni tace"Je ki d'auko min kayan asirin"

 

Lantana babu musu ta mike simi-simi ta shiga dakin da take, shiru falon yayi kowa na sake -sake, Lantana ta dawo hannuta rike da bak'ar Leda ta aje gaban Mama,, Cikin kunya da tsarguwa.

 

 

Mama tace"Bud'e muga abunda yake ciki"

 

Hannu na rawa Lantana ta fara bude ledar,,  Sosai Mama take mamakin ganin kayan asiri Wanda duk tarin kasa ne da wasu saiwowi tace"Wannan itace k'asar kabari"?

 

Daga kai Lantana tayi cike da kunya

 

"Wannan fa"?

Tafad'a tana nuna d'aya ledar.

 

Baki na rawa tace" Wannan yace"A sama ta a abunci sunan shi shashatau zata mance kowa bayan ta hauka CE"

 

 

Mama tayi murmushi me ciwo tace"Kin ce da k'arya ake miki"

 

Lantana ta hau inda inda

 

Daga mata hannu Mama tayi tace"Ya Isa"

 

Shiru tayi gami da sunkuyar da kanta kasa

 

Mama tace"Ina son duk Ku biyun kuji tsoran Allah Ku tuna yana ji yana kallon Ku da dukkanin abunda kuka aikata, Hak'ika shi ubangiji na kowa da kowa ne kuma mai amsa bukatun bayin sa, hakanan me yafiya ga Wanda ya sab'a masa,, Hak'ika kun aikata babban kuskure na had'a Allah da waninsa,, babu me yi sai Allah shine ya hallice mu ya hallice duk wani Abu me rai da Mara rai tsirai zafi sanyi ruwa wuta da sauransu shi ya halli rai da mutuwa,,, ina rokan Ku Ku tuba tun kafin lokacin mutuwar Ku yayi domin babu Wanda zai dawwama duniya, ga Balaraba nan a zaune a gaban Ku ku nemi gafara ta zata yafe muku abunda kukai mata kunga bata da hakki a kanku gashi da kanku kunzo kun tonawa kanku asiri,,, bayan kun nemi gafarar ta kuje kuyi ta istigafari domin Neman yardar Allah"

 

 

Uwa! Tana kuka wurjajan ta matsa kusa da Balaraba tace"Ki yafe min abunda nai miki Wanda na sani da Wanda ban sani ba,, nasan na cutar da rayuwar ki nayi miki sharri da kazafi gashi duk abunda nake jifan ki dashi bai same ki ba sai alkairi abun sai ya koma kan "yayana nasan hakkin kine wallahi"

 

 

Share hawaye tayi tace"Uwa! Ki daina kuka kinji ko har yanzu kinanan a matsayin uwata kuma na yafe miki duk abunda kikayi min Allah ya yafe mana baki d'aya"

 

 

"Nagode-nagode nagode sosai Balaraba Allah ya baki zaman Lafiya da mujin ki"

 

Mama tace"Amin haka ake son mumunin ya zama me ya fiya"

 

 

Lantana ma ta matsa kusa da ita tana kuka sosai Sam ta kasa magana.

 

Balaraba ta rike hannunta tana fad'in nasan abunda kike so kice"Na ya fe miki, dama tun tuni na ya fe miki kuma har yanzu kinanan a matsayin kakata naji mutukar dad'i da kuka gane gaskiya.

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿104*

 

 

 

 Mama ta kalli Shafa'atu tace"Ki d'auki wannan kayan tsubbu kije ki k'ona su can bayan gida, ubangiji Allah ka rabamu da sharrin zuciya"

 

Jakadiya tayi bisimillah ta d'auki ledar dake aje gaban Mama ta futa daga d'akin domin taje ta aiwatar da aikin da aka sata.

 

 

Madabo tayi musu wani kallon banza tace"Ya kamata Ku zo a mai daku gida domin zama daku annoba ne,wallahi Fulani ki barni da halina kawai amma na tsani mutum me asiri wallahi"

 

 

Murmushi Fulani tayi tace"Na san halin ki ciki da bai don me yasa bakya shiri da Kulu ai saboda halin ta ne"

 

 

Madobo tace"Wallahi kuwa ai Kulu tayi nisa sai addu'a"

 

Mama tace"Ita kad'ai ce magani"

 

Shiru falon yayi, kunyar duniya ta ishi su Lantana sun kasa d'ago kai su kalli mutane,,Balaraba ma kanta na k'asa tana sak'e-sak'e, k'amshin turaran sa ne ya gauraye falon,, da sallama ya shigo cikin yanayin tafiyar sa ya zauna kusa da mamansa.

 

 

Kwarjinsa da haibar sa ya cika falon, Lantana duk dadewar ta a gidan bata tab'a ganin shi ba sai yanzu, bakinta na rawa tace"Ranka ya Dade ya barka da yamma"

 

A nutse ya galli gefan da take ya amsa Cikin yanayin muryar shi.

 

Mama tace"Kakar Balaraba ce nasan baka gane ko wacece ba"

 

Mai da ganinsa yayi kan Lantana wacce tayi muzu-muzu a zaune tana tsoran kar Mama ta fada masa halin da ake ciki,, minti biyu yana kallonta yaji sam matar bata kwanta masa,, a hankali ya Dora idonsa kan Uwa! Ta zaune sai gumi take cikin zuciyarta take cewa dama wannan ne Sarki! Almansur din? Lallai Allah yayi hallita a gurin,, ina Shamsiyya ina shi,, a ya zama dole ta sanar da Shamsiyya cewar ta daina wahalar da kanta ko mutuwa zatayi ta san Sarki ya fi k'arfin ta,, Ya mutse fuska yayi ganin wata koriyar kwanta a idon Uwa! Abun k'yamk'yami yace"Ita kuma wannan fa"?

 

A hankali Mama tace"Matar Kawun ta ce, sunanta Uwa!" Tunda yaji haka ya d'auke kansa zuciyarsa tana tashi tunda ya kalli fuskar Uwa! Babu kyawun gani,, gai sawa sukayi da Madabo cikin mutum ci da girmama juna,, ya gaida mahaifiyar shi a mutumce, falon yayi shiru kowa da abunda yake sak'awa a zuciyarsa

 

 

Tunda ya zauna a gurin yake so su had'a ido da ita,, Allah bai bashi iko ba, itama gane hakan ne yasa taki d'ago kanta sai kara sunkuyar da kanta take.

 

 

Mama ta kalle shi tana fad'in "Dama yanzu nake cewa a kira min kai zamu zauna da kai da iyalin ka"

 

Shiru yayi yana d'an Sosa kai as'usuel.

 

Gimbiya Halisa ta futo daga wani daki dake cikin falon tw cire alkyabar jikinta yanzu tana cikin wata muguwar shadda wacce akai mata mugun aiki mai bala'in kyau (sirfani) abunka da siririya sai dinki yak'i zama a jikinta sosai, duk cikin kayan lefansu take Balaraba na da irinta Azima ma haka.

 

Mama ta kalli su Lantana da suka muzanta tace"Yanzu sai Ku shirya a mai daku gida ko"

 

Lantana kamar ta kurma ihu shikkenan, taga samu taga dashi,inama ace Balaraba ta ce ta zauna mata

 

 

Jakadiya Shafa'atu CE ta dawo ta zauna Cikin nutsuwa,, Mama tace"Jakadiya kar ki gaji  a had'a musu tsaraba zasu wuce gida"

 

 

Jakadiya ta mike tana fadin"An gama Uwar dakina"

 

 

Balaraba ta mike a nutse ta nufi dakin da take, duk wani Abu da tasan nata ne naci da na sawa ta had'a su guri guda ta futi dasu da k'yar,, zama tayi kujerar da ta tashi tace"Gashinan Ku raba Wannan nawa ne babu yawa,, Ku gaishe min da Iya matar Kawu"

 

Lantana godiya kawai take yau ta k'ara tabbatar da cewa Ubangiji mak'agin baiwa ne me yin yadda yake so da kowa wai tana raye a duniya Balaraba tayi aure kuma ta dauri Sarki! Lallai idan kace tukunyar wani baza ta tafasa ba to taka ma ko dumi baza tayi ba, tabbas taga ishara ta gane duniya ba komai bace, yanzu dole ta kwantar da kai suci su sha ta dalilin Balaraba..

 

 

 

*******

*******

*******

 

Shamsiyya tsugene a bakin kofar zauren Arrama ta buga-buga an ki budewa, wata zuciyar tace watak'ila yana ciki yana aiki shine ta tsuguna tana jiran ya gama,, wasa take da wani kara a hannunta taji zuciyarta tana wani irin tashi, da sauri ta mike taje bakin kwata ta dunga yunk'urin amai,, aikuwa kafin kice me sai ga wani amai Kore fatau tana kyalashi,, mutane suka fara taruwa a kanta suna tausayin ta,,wata mata tazo ta kamata ta mikar da ita suka samu dakali suka zauna, da k'yar ta dawo hayyacin ta sai haki take, matar tace"Yarinya daga ina kike haka ai gwara ki koma gida ki je ki huta"

 

 

Shamsiyya ta ya mutse fuskarta har yanzu tana jin tashin zuciya tace"Nazo gurin Arrama ne, tun d'azu nake bugu bai bude ba nace ko aiki yake ne"

 

 

Matar ta girgiza kai cikin takaici wato ire-ire "yan Matan da suke zuwa gurin Arrama ne, wannan wai duniya INA zaki damu bin malamai babu yara babu manya babu zawawara babu Matan aure da " yan mata, tace"Ai sai da kiyi hakuri jiya-jiyanan aka kama shi yanzu yana hannun hukuma saboda jiya wata buduwar yarinya tazo Ita da uwarta gurin nan cika yayi da d'an Adam tazo tana kuka yayi mata ciki wata uku shine sukaje suka d'auko "yan sanda a ka kamashi, to d'azu da safe labari ya same mu cewar ya kufce daga hannun " yan sandar ya gudu"

 

Shamsiyya ta d'ora hannu aka tana fad'in"Na shiga uku na lalace, Arrama me yasa zakayi min haka,, kace Saura kad'an aikina ya kammala shine zaka gudu baka k'arasa mun ba"

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿105*

 

 

 

 

Yara suka fara taruwa a kanta sai kurma ihu! Take, da sauri wannan matar ta d'ora ta a hanyar gida tana tafe tana kuka kamar shashasha sai surutai take.

 

**********************

Mota a ka kawo su har k'ofar gida cike da kayan arziki, yaran unguwa suka yi dafifi suna shafa motar suna tsalle har yanzu sun kasa sabawa.

 

 

Yara matasa suka kwashe kayan da suka zo dashi suna shiga gadan dasu,, suka bi bayan su duk jikinsu a sanyaye,, Buba direba yaja motar sa ya tafiyar sa,, suna k'okarin shiga gidan ana k'okarin futo da Sallau a rirrike jikinsa yayi tsanani, Lantana ta rafka salati gami da fashewa da kuka tana fad'in "Ina zaku kai shi"?

 

Walidi Yace" Asibiti za a kaishi domin jikinsa yayi tsanani, nan ta bisu a baya tana kuka, Uwa! Kuwa gida ta shige tana matsar hawaye, Sadiya da Iya na tsaye tsakar gida cike da tausayin Sallau Uwa ta shigo gidan, kallo suka bita dashi ganin tana matsar hawaye domin sun d'auka ko ganin jikin Sallau ya rikice yasa ta kuka, zauna tayi a tsakar gidan tana kukan nadama.

 

Ko minti goma ba'ayi ba sai ga Shamsiyya ta shigo gidan tana kurma ihu, ta zube gaban mahaifiyar ta tana fad'in"Shikkenan Uwa! Aiki ya lalace "yan sanda sun kama Arrama jiya da yamma"

 

 

"Don Allah ni yi min shiru da zancan wani Arrama in zaki hak'ura ki hak'ura ki zauna inda Allah ya aje ki, ni  kam. na dawo daga rakiyar wannan duniyar me cike da rud'u"

Uwa! Ta fada tana sharb'e hawaye

 

Shamsiyya ta d'ago kai tana kallonta cikin mamaki tace"Ban gane abunda kike nifi ba kina nufin in rabu da maganar aure na da Sarki! Ko me"?

 

"E abunda nake nufi kenan, Domin babu yadda za'ayi ya aure ki yana da Balaraba"

 

Shamsiyya ta fashe da kuka tana fad'in "Uwa kar muyi haka dake kinji, kece fa kika yi mana alk'wari cewa ko da zakiyi yawo tsirara sai in da k'arfin ki ya k'are zaki tsaya min gurin ganin buk'ata ta ta biya"

 

"Ke ni ki k'yaleni don Allah inji da masifar da nake ciki, ubanki ya sake ni saki uku, ga masifar Ku ta same ni, Nazo a banza zan koma a wofi ni yanzu waye zai aure ni" ta k'arashe maganar tana rusa ihu!

 

Shamsiyya ta dafa kirji tana fad'in "Baban bamu ne ya sake ni yau she haka ta faru"?

 

Nan Uwa ta kwashe duk abunda ya faru ta fada mata har da zuwan su gidan Sarki! Shamsiyya ta kwanta tana rusa ihu! Babu kamar wacce uwarta ta mutu

 

 

***********************

 

Suna zaune gaban Mama Fulani duk su ukun sai shi da ya zama  cikon na hud'un,, yana hakimce kan kujera.

Mama tace "Salati goma da Annabi" Duk suka amsa da "Sallalahu alaihi wasalam"Minti goma tsakani tayi addu'a ta shafa suka shafa suma,, ta kalli Sarki a nutse tace" Babban abunda yasa na tara ku anan shine, in ja muku kunne gami da nasiha, mussaman kai" tafad'a tana nuna shi da hannu, kansa ya sunkuyar kasa, ta cigaba da cewa"Allah ya d'ora maka wani babban nauyi a kanka na mataye har uku, dukaninsu suna da hakki a kanka babu wacce tafi kowa a gurin ka sai wacce tafi kyautata maka a cikinsu, don haka ina mai gargadin ka da ka rike amanar su ka bawa ko wacce hakkin su,da ya rataya a kan ka"

Yace"Insha Allah Mamana kar ki damu"

 

"Ku kuma na dawo kanku"

Tafad'a tana kallonsu duk su ukun, ta cigaba da cewa"Ku yi kokari Ku kula da mijin Ku Ku fahimci me yake so da Wanda ba ya so, yi nayi bari na bari Ku yi k'okarin zama lafiya da juna domin Ku kwantar masa da hankali gurin ganin ya rik'e amanar Ku, da jagorancin mutanan gari da ya hau kansa, ni Wannan kawai zakuyi min Ku faranta min, insha Allahu , kuma idan wani sab'ani ya shiga tsakanin ku dashi,  ba fata nake ba,, zama ya gaji haka zo mu zauna zo mu sab'a haka duniyar take, to sai Ku same ni Ku sanar dani insha Allahu komai zai zo da sauk'i"

 

"Mama Insha Allahu zaki same mu masu zaman lafiya da juna" Balaraba tafad'a kanta a kasa,, Azima da Halisa ma Abunda suka ce kenan, Mama tace"Masha Allahu Allah yayi muku albarka" Ameen suka ce gaba d'ayan su.

 

 

************************

K'arfe shida na yamma, gurin Walima ya d'auki harami ya tsaru ya k'yayatu sosai Shahid da Shatima ne suke ta kai kawo a gurin suna saukar abokan su, da suka fara zuwa.

Suna sanye da wata arniyar gezna wacce ta amsa sunanta anyi musu dinki iri daya hula da takalmi duk kalar shaddar ne,, ruwan toka kenan sai shek'i take aikin ya. zauna a jikinta.

 

 

Suna zaune a falonsa ko wacce kujerar ta daban da "yar uwarta babu wacce tayiwa " yar uwarta magana, suna sanye da kaya iri d'aya Shadda ce, sky blue anyi musu d'in ki Aliya taji sirfani duk gaban rigar ko wacce ta d'ora d'auri dai-dai da kwalliyar ta, gwal kuwa kamar yayi magana hannayen su da wuyan su, takalman su iri daya ne, Azima da Halisa sun sha kwaliyyar fuska, babu Mayafi a jikinsu, Balaraba kuwa babu laifi fuskarta babu komai sai farar hoda da kwalli da ta zizara a idonta, bayan haka ko man leb'e bata sa, amma haka bai hana bayyanuwar kyanta ba, ta yafa k'aramin mayafi Wanda ya sauko ya rufe mata k'irji.

 

 

 

A hankali yake sakko wa yayin da k'amshin tura ransa ya cika gurin , dukanin su suka mai da  su kansa,,

 

Kallo guda tayi masa ta d'auke kanta gabanta na fad'uwa. Yana sanye da shadda irin jikin su Sak,, anyi masa dinki irin na zamani,, me falmaran wacce yaji sirfani me tambarin sarautar su,gaba da baya hular shi ma da yanki shaddar aka had'a ta,, kafar shi sanye da wani ruffan takalmi mai gashi-gashi sky blue hannunsa daure da agogo na zallahar azurfa, ya tsunsa ma zobuna ne manya-manya masu d'auke da tambarin sarautar su.

Cikin nutsuwa ya k'araso gurin su,, Fuska babu yabo babu fallasa yace"Ku tashi muje" a nutse ta mike jin abunda yace, gaba yayi suna bin shi a baya,, sai ga Shahid da sauri ya tare shi tare da wasu fadawa su uku suna take masa baya, Shatima yace"Kuyi tafiyar ku kawai,, suka ce "An gama ranka ya Dade, magana yake masa k'asa-k'asa, tsayawa yayi yana d'an hararsa, shi kuma ya sa dariya, yace" Hakane mana sai kayi gaba ka bar amaran naka a baya kai fa d'an gata ne" banza tayi masa yana d'auke kai da alama yau "yan muskilancin nasa na kusa,, Shatima ya k'araso tare da su Balaraba dole suka tilas tashi ya shiga tsakiyar su,, suna tafiya su uma suna take musu baya.

 

Tunda futowar su har zaman su a masu hotona da vidio suke aikin su, marok'a duk sun cika gurin da roko, sosai gurin ya cika ya tumbatsa da mutane kowa sai farin ciki yake, ciki kuwa babu " yayan Waziri Zayyanu ko guda. D'aya suna can bakin ciki kamar ya kashe su, jin cewar har governor sai da ya hallarci gurin.

 

 

Walima tayi kyau sosai an raba kaya naci Dana sawa jakkunkuna atamfofi masu d'auke da hotanshi da amaran sa , duk Wanda yazo gurin ya samu kuma yayi guziri.  Bakwai shaura aka tashi saboda lokacin sallahr magariba ne. Kuma bayan sallah Isha'i Mama tace Ko wacce za'a kaita dakin ta.

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

 

*🅿106*

 

 

 

 

 

 

Hannuwan ta ya zubawa ido kurr!! Sun sha uban Jan lalle wanda yayi jajazur har ya fara yin b'aki, sosai abun ya burge shi kuma ya bashi sha'awa,, nata duk ya fi tafiya da imaninsa, nasu Halisa bak'i ne, irin wanda ake zanawa shima yayi kyau babu laifi, kowa da kalar nashi,Cikin nutsuwa ta had'a plate uku kowa da nashi,, ta mik'a masa nashi tana fad'in "Bisimillah" Ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe ido yace"Ke ina naki plate d'in, kin had'awa kowa nashi" babu yabo babu fallasa tace"Na ci abunci kafin na futo,, kai tsaye yace"Ko kinci dole kici na nan, ka'ida tace, wannan" Cikin mamaki ta kalle shi, ganin yanda ya b'ata fuska yasa ta fara zuba abuncin domin bata son ayi ta Jan magana,,Shiru gurin yayi, sai motsin cokola, satar kallonsa take yanda yake cin abunci kamar baya so,, ita kanta taunar sa ma abun kallo ne, Halisa kanta ya k'ara girma ganin yanda yake kula da ita domin shine ma ya tsiyaya mata ruwa,, ya mik'a mata lokacin da ta k'ware ganin, yana sanya Balaraba aiki yasa suka kara mike kafa suna ganin sun fita daraja a gurin shi kuma yasan su dama basu saba da aikin wahala ba,, shine ya fara mik'ewa daga gurin,, ganin ya tashi yasa ta mike da sauri ta gudu part d'inta... To Azima ma da ta kammala mik'ewa tayi ta wuce part din ta, aka bar Halisa tunda itace take da miji a hannu jiya da yau.

 

 

********************

********************

 

Tsito da Waziri ne zaune cikin duhu,, Aljani Mak'asudu ya hauro kan Tsito nan suka fara magana da Waziri,, yana fad'a masa buk'atun sa, Mak'asudu yace"Akwai alkwarina a kanka na k'afa biyu kar kace na manta da wannan alk'awarin ina sane dashi, kuma sai na bi jinina,, wannan buk'ata kuma da kawo mana, zata biya amma da sharad'i idan ka kuskura ka kauce sharad'in da muka gindaya maka to sharrin zai koma kanka kaji!!!!!!! Ko"!!!!!!!? Waziri yace"Arne ya dafa maka ai duk sharad'in da kuka gindaya min ina me tabbatar maka da cewar zan bishi bazan kauce ba" Mak'asudu yasa dariya yana fad'in"Shikkenan ni zan jirge!! Yanzu amma zan Sanar da Tsito duk sharad'inmu sai ya fad'a maka" Waziri yace"A sauka lafiya Mak'asudu me mukulin mulki mak'asudu d'an gidan K'azaza gaba salamun baya salamun Ubana"" Tsito ya dunga wata irin katantanwa a tsakiyar d'akin yana wani irin ihu!!!!!! D'if dakin yayi shiru kamar anyi ruwa an d'auke.

 

Wajan minti goma Tsito ya dawo dai-dai cikin duhu ya kalli Waziri yace"Da alama d'azu muna magana da kai Mak'asudu ya hauro ko"?

Waziri ya gyad'a kai yace"Akwai sak'on da yace zai fada maka ka fada min" Shiru Tsito yayi yana sauraron Mak'usudu sai gyad'a kai yake alamun yana sauroro,, bayan ya gama sauraron Mak'asud'u ya kalli Waziri yana fad'in"Yace"Mu nemo bak'ar kulb'a da bak'ar kunama sai bak'in b'era dunka sai tsohon kadan gare Wanda ya soma sab'a  saboda tsufa, duk a yanka su a cire musu fatar jikinsu,,  a shanya ta bushe, sai ka kafa kusa a d'akin ka, duk ka kafe fatocin bango d'aya ka samu Jan yanki kasa a tsakiya, bayan nan kuma hanjin su,, a had'a shi guri guda a sanya su su bushe a dake lukwi sai a zuba masa a abunci, da iziinsa sai ya mutu idan bai mutu ba to zai rasa wani b'angare na jikinsa, sannan in ka kuskura mutum ko guda ne, ya shiga dakin Da ka kafe fatocin nan to abun zai dawo kanka,,sai magana ta k'arshe yace"Ka tafi bakin kogi da k'aton rago me tozali ka yanka masa zai shanye jinin" Waziri yace"Duk za'ayi da izininsa mutukar bukatar zata biya, yanzu yanda za'ayi na samu wad'annan dabbobin shine abun dubawa" Tsito yace"Wannan babu matsala gobe sai ka futa dani a mota ni zan samo maka,, sai dai ka ware min lada na" Waziri yace"Duk kar ka damu zan maka kyauta ta ban mamaki in zaka tafi" Nan sukayi sallama Waziri ya futa yana godiya ga Mak'asudu.

 

 

*************************

*************************

Kwanan Sallau Uku a asibiti yace ga garin ku nan, Lantana ta dunga kuka kamar ranta zai futa,, Uwa! Ma duk da ya sake ta ta koko da mutuwar Sallau,, Shamsiyya kuwa tun sanda ta dawo daga gidan Arrama ta kwanta ciwo kariris,, Amai da zazzab'i duk ta rame ta jeme sai uban zubar da miyau da takeyi,, jama'a 'yan zaman makoki dayawa duk San fahimci ciki ne da ita Uwa! Ta gane da sauran mutan gidan rudanin mutuwa ya hanasu nuna b'acin ransu domin hausawa nacewa wani tashin hankalin yafi wani,,, Lokacin da Balaraba taji mutuwar Sallau kuka ta dungayi sosai, Mama tai ta rarrashin ta, tare suka tafi

 

 Da ita da du Halisa Madabo ma taje,, Sarki kuwa dashi akayi jana'izar Sallau, unguwar ta d'auka wanda ma bai yi niyyar zama gurin mutuwar ba dalilin zaman Sarki! A gurin ya zauna,, ya sa aka kafa rumfuna  sosai mutane suka zo suna kwasar girgi harda wadanda suka futa kasuwa, sai su dawo domin su kwashi abuncin gidan mutuwa, kullum sai sun zo har a kayi sadakar uku,, Balaraba suka dawo gida cikin jamami,, tayi mamaki da har aka share zaman makoki bata ga Iro da Mabaruka ba, har dai ta gaza hakuri ta tambayi Iya ina suke, sai tace"Mabaruka dai tafi sati hudu rabon ta da gida, shi ko Iro tun kafin ki bar gidanan aka neme shi aka rasa, tace"Shamsiyya fa"? Iya ta girgiza kai tana goge kwalla tace"Tana cikin daki ta d'auko abun kunya shiyasa take buyarwa jama'a" Balaraba ta dunga share hawaye tana tausayawa rayuwar su,, Shamsiyya kuwa tana jin ance ga Balaraba tazo zata dunga lekowa tana taga tana kallonta tana fad'in ina ma itace.

 

 *************************

*************************

 

Duk abubuwan da Mak'asudu ya ce a nemo sun nemo kuma sun aiwatar da aikin kamar yarda yace d'in abunda ya rage wa Waziri shine zuwa bakin ruwa ya yanka rago shima ya sa d'amba gobe da Asuba zai futo domin an samo ragon irin wanda Mak'asudu ya buk'ata...

 

 

 

Yau ne girki Balaraba ya kama,, duk dama wancan kwanakin ya na Cikon na Halisa ne, sai Azima da yayiwa kwana uku, wannan mutuwar da akayi yasa Balaraba taga kamar kwanakin sunyi sauri, ita fa bata lissafin komai yanzu duk bata cikin hayyacin ta domin mutuwar Sallau sai ta dawo mata da ta iyayen ta sabuwa,,  jiki a sanyaye take yin komai, k'arfe shida ta kammala girki mai rai da lafiya tayi Wankanta gami da fesa turare ko ina a jikinta, tana sanye da wani material sky blue yayi mata masifar kyau, inda tayi amfani da k'aramin mayafi tayi rolling dashi,, anyi mata kitso ta tattare shi a tsaki ta sanya manya-manya ribom sai ya zama kamar a cuci tayi kyau sosai d'inkin Riga da sket ne,, tayi fuskarta fayau,, ko kwalli babu sai mai leb'e da ta goga,, a nutse ta dunga d'ibar kayan abuncin tana kaiwa part d'insa,, su Amina da Hadiza bayinta sukayi-sukayi ta barsu su d'aukar mata tak'i tace"su barshi itama ladan take so, sai suka hak'ura suka k'yaleta ,, lokacin yana sama ta gama shige da fucen ta, ta koma part d'inta sai bayan tayi Sallahr magariba ne, sannan ta kimtsa, da niyar komawa part din nasa.

 

 

 

Da shirin zuwa masalaci ya sauko hankalin sa bai  kai kan daining ba, sai Mai dafa masa abunci fa ya gani a tsaye tsakiyar falo ya sunkuyar dakai kasa, gyaran murya yayi  da sauri ya dago yana masa barka da sakkowa, Yace"Kana tsaye gashi ana shirya-shiryen tayar da sallah" Yace"Allah ya taimaka ke Nazo zan jera abunci na ga an jera wani nace Allah yasa ba laifi nayi ba"

Kallon daining teble din yayi yaga wasu had'addan kuloli ba Wanda aka saba zuba masa abunci ba,, girgiza kai yayi kawai, yasan aikin Gimbiya ne, yana k'okarin tafiya yace"Yau an hutar sheka, gobe ma kar kayi gudun asara ka futar muku da Wanda ka girka" Yana gama maganar ya futa,, Shi kuma ya koma kicin, cikin zuciyarsa take cewa amma wannan matar tasa ta tarbiyantu ba kamar sauran ba, Allah ya kyauta.

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿107*

 

 

 

 

Sai bayan sallahr Isha'i ya shigo, zama yayi a falo da carbi a hannunsa yana ja,, a hankali ya dunga jin wani sanyayyen k'amshi na ziyartar hancin sa, d'aga kansa yayi yana kallon inda yake jin motsi, Balaraba ce take saukowa daga matattakala cikin nutsuwa, a sirance ya sauke ajiyar zuciya ya su kunyar da kansa wani Abu na tsunkullin sa,, ta k'arasa daining cikin nutsuwa ta gyara komai ta tako a hankali ta zauna kujerar dake kallon sa, kansa na k'asa bai dago ba, a hankali tace"Barka da dare" d'ago kansa yayi yana kallon ta, minti biyu yace"Barka kin wuni lafiya"? "Lafiya Lou ta fada'a tana wasa da hannunta,, yace" Ya k'arin hakuri kuma" ? "Alhamdullahi" Shiri falon yayi  sak'e-sak'e take a zuciyarta, shi kuma yana k'okarin ya cika carbin sa,, sai da ya kammala sannan ya aje ya d'auki wayar sa, numbar Halisa ya kira tans d'auka yace"Ki futo muci abunci " kashewa yayi ba tare da ya saurari abunda zata CE,ba, numbar Azima yake nema, sai gata ta shigo cikin uban kwalliya ta k'ananun kaya wanda suka d'ame ta,, b'ata fuska yayi lokacin da yayi arba da ita, kusa dashi ta zauna tana gaishe shi cikin wani irin salo,, a dakile ya amsa, yace"Wannan wane irin iskanci ne zaki futo da wannan kayan na jikin ki"? Azima ta sunkuyar da kai tana fad'in 'Yallab'ai me ye laifin su" A fusace! Yace"Ba duguwar magana na nema ba,, magana ta farko ta k'arshe kar ki sake futowa da irin wannan kayan in zaki saka kayan ki ki saka Ke ka dai a daki ba  sai kin nunawa jama'a ba, gida cike da mutane ki futo min da wannan shashancin" Ganin ransa ya b'aci yasa ta fara bashi hakuri , ko sauraron ta baiyi ba ya mike ya nufi gurin cin abunci ransa in yayi dubu ya baci"! Balaraba kuwa taji dadin abunda yayi wa Azima ta lura tayi shigar ne Dan Taja hankalin sa, a randa ba girkin ta ba,  dariya kawai take mata Cikin zuciyarta tace"Wallahi wani lokacin mutumin nan na burge ni da halinsa baudadden mutum ne! 

 

 

Gyaran murya yayi Balaraba ta mike da sauri kar ta samu rabon ta,, Azima ma ta mike jiki a sanyaye,zama tayi, daya daga cikin kujera ita kuma ta fara zubawa kowa nashi cikin nutsuwa, Halisa tayi sallama ta shigo,,, itama ansha kwalliya kamar masu zuwa gasar fidda kyau!! Gwara ita material ne, a jikinta dinkin riga da sket kusan irin na Balaraba kala ce kawai ta banbanta,, gaishe shi tayi ya amsa ba tare da ya kalle ta ba,,  sama-sama suka gaisa da junansu ko wacce na danne Kishi a zuciyarta. Balaraba ta zubawa kowa nashi ta zauna ta fara cin nata cikin nutsuwa.

 

 Sarki! Yaji dad'in girkin Balaraba sosai ya bude ciki ya ci ya k'oshi ya yagi tissue ya goge bakin sa,, da kuzari a jikinsa ya mike daga gurin, falo ya koma ya zauna,, to suma dai su Halisa sunji dadin girkin shiyasa babu wacce tayi k'orafi suka cinye plate din tass ko wacce ta tashi tana goge bakinta,, Balaraba ta gyara gurin tsaff!! Ta isa in da suke,, k'asa-k'asa yake kallon ta ganin tana k'okarin futa,, yace"Ina zakiji kuma? Duk gashi muna zaune da juna" A takure take jin jikinta kasan cewar tana cikin halin rashin tsarki,, wannan motsa jikinta da tayi Duk pad din ta ta jik'e haka take a rana sai ta sanya sau biyar,, tace"Yanzu zan dawo zan Dan watsa ruwa ne"" Nan ma akwai toilet kin shigo kenan ki dawo ki zauna" wannan halin nasa yana bata haushi wallahi, to in ta dawo ta zauna yana da pad din da zai bata oho masa,,, zama tayi kujerar dake daf da bakin kofa ranta a bace, duk ya lura da yanayin da take ciki,, Azima sai watsa mata d'an iskan kallo take,, Ita ko Halisa sai hira take masa yana biye mata,, goma shaura, sukayi masa sallama ko wacce ta wuce part d'inta, falon yayi shiru da shi sai ita  mik'ewa  yayi ya nufo inda take zaune,, Balaraba ta sunkuyar da kanta tana jiran taga me zaiyi,, kulle k'ofar yayi ya cire key din,,, ta kalle shi bakin ta na rawa tace"imm... Ina da Uziri a gurina fa,, yanzu zan futane in je in dawo naga kuma ka kulle kofar" Tsayuwa yayi a kanta yayi mata rumfa! Cikin wani irin voice yace"Me zaki je kiyi? Uhumm kin ce wanka nan babu toilet ne"? Girgiza kai tayi yace"To kin gani, tashi muje ki gyara min shimfid'a ta"" ta d'ago dararan daran idonta tana kallonsa,, lallai akwai rigima kenan mutuk'ar ya san halin da take ciki, yaya za'ayi ta fada masa,,, hannunta ya kama ya mikar da ita tsaye,, zura hannusa yayi ya rungumo k'ugunta suka fara tafiya, a haka suka dunga hawa mattatakala duk rabin jikinsa na jikinta,, lokaci guda ya soma neman nutsuwar sa,,, zama tayi gefen gado ya shiga toilet ya futo daure da alwala yace"Ki shiga kiyi wankan sai ki dauro alwala kizo muyi nafila" babu musu ta mike ta shiga toilet din,, Wanka tayi sosai,, ta sanya towol ta goge jikinta ta maida kayan jikin ta,, tana futowa taga ya shimfid'a dadduma yana tsaye yana jiran ta,, hijab ya mik'a mata, ta karb'a amma bata sanya ba,, ik'ama yake so ya tayar ya kalle ta yana fad'in"Ki sanya mana" A nutse tace"Bani da tsark" Yaji wani irin fad'uwar gaba, amma dake Namijin duniya ne,, sai ya maze Dan kar ta gane,, yayi minti biyu yana nazarin ta daga bisani ya tada sallahar shi,, zama tayi gefan gado jikinta a sanyaye , Ya dade kan dadduma yana addu'a har ta fara gyangyad'i,, ya mike a nutse ya kashe wutan dakin,, bed din ya nufa Balaraba tayi tsuro tana kallon inuwar sa,, sai da yw zauna sannan ya cire jallabiyar da take jikinsa,, babu zato taji ya jawo ta jikinsa, gabanta ya dunga fad'uwa duf!!duf!! Zif din yake k'okarin zugewa tayi saurin dafe hannusa,, kansa ya zura tsakanin wuyanta yana sakin ajiyar zuciya daki-daki,, k'okarin hanashi take, amma sai da yayi nasarar zuge mata zuf din ya cire rigar ya jefar kwantar da ita yayi k'asan shi yayi mata rumfa, Balaraba sai motsi take da bakinta taka cewa komai duk inda ya kai hannunsa sai ta kai nata duk a k'okarin ta na hana shi abunda yakeyi ya ta kasa,, sai ma jikinta da yayi la'asar sakamakon uban soyayyan da yake zuba mata,, Balaraba taji kamar ba a duniya take ba,, ta shagala Wanda ba san ma yayi nasarar cire mata brziyya ba,, aikuwa ta gigice amma yanai mata wani salo tuni ta bada kai bori ya hau suka hau soyayyar su irin ta ma'aurata,, Sarki! Ya sha mutukar wahala lafin ya samu nutsuwa,, Balaraba kam jin ta take a sama, ta manta a wace duniyar take, ita dashi sai sauke nuffashi suke,,,,, wani irin kullewa mararsa take,, shi kansa yasan ba duka ya zubar da abun ba, yanzu shine damuwar sa, zai iya shiga mugun hali, mutukar bai samu yayi sex ba, domin shine katt! Shine za samu sukuni,, a galabaice ya kira sunanta, ta amsa murya na rawa yace"Ki yarje min na je gurin "yar Uwar ki na biya buk'ata ta, ina Cikin wani hali" Sosai ta tausaya masa,, cikin raunin murya tace"Babu damuwa, ai dama amfaninmu kenan, na yarje maka kaje kawai" mik'ewa yayi yana zura jallabiyar sa,, Albarka kawai yake sa mata,,, sauka yayi daga bed din ya d'auki key zai futa, ta kira sunansa juyo wa yayi yace"Menene uhumm? Kiyi hakuri Yanzu zan dawo"' shiru tayi haka kawai taji kwallah na k'okarin zubo mata,, ya fuce da sauri,, Azima tafi Halisa dauriya, saboda haka shashen ta ya nufa Cikin duhun dare, dam ma akwai hasken futulu a wasu guraran,, Azima na zaune a gefen gado ta zabga uban tagumi sai tunani take kana kallonta kasan akwai abunda yake damunta,, taji ana bugu tana k'okarin tashi taji karar wayarta,, tana dubawa taga Sarki! Ne hannu na rawa ta d'auka, yace"Bude min kofa" jiki na rawa ta je ta bud'e masa ya shigo ta mayar da kofar ta rufe,, kai tsaye bed din ta ya nufa,, ta bishi a baya,, tana shiga ta ganshi yana k'okarin cire Riga, tace"Lafiya Yallab'ai "?  Kwanciya yayi bed din ta yace" Zo" Azima ta gane me ke da akwai,, zuciyar tace mata Allah ya kawo miki shi har dakin ki,, da sauri ta nufi friji ta d'auko Lemo mai sanyi ta k'araso kusa dashi,, tace"Yallab'ai tashi ka fara shan Lemo nasan ranka a b'ace yake"" sama-sama yake jinta ya mike ya karb'i lemon dake hannuta ta bud'e masa ya shanye Tass! Ta karb'i robar ta aje,, kashe futular tayi ta rungume shi,,, cikin mawuyacin hali ya biya ma kanshi buk'ata,, yana gamawa yaji wata irin muguwar kasala ta rufe shi,, da k'yar ya koma part d'insa, Balaraba na zaune ta rafka tagumi jiran dawowar sa kawai take, ya shigo ta bishi da kallo ya shigowa ya kwanta babu abunda yace mata,, kusa dashi taje ta kwanta gabanta na fad'uwa,,, da k'yar bacci ya dauketa mai cike da mafarkai! Asubah ya farka tare!dashi, ya d'aga kafa zai sauka k'afar tak'i d'aguwa yayi-yayi taki motsi sai wani yammmmmmmmm!!! Take masa.

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿108*

 

 

 

 

 

 

Kalmar Innalillahi wa'ina ilahi raji'un itace ta futo daga bakin sa, yunk'urin d'aga k'afar ya kuma yi a karo na uku, tak'i motsawa,, hannu yasa ya d'agota yaji wani Yammmmmmmm! Mara dad'i Dole tasa yayi saurin aje ta saboda ji yayi abun har tsakiyar kansa,,, zufa duk ta jik'a masa jiki kamar babu sanyi asubah,, salatin da yake ne,, ya farkar da Balaraba ta mike a zabure itama bakin ta na fad'ar kalmar Innalillahi wa'ina ilahi raji'un, saboda wani irin mumman mafarki da tayi,, hannuta ya Kamo ya rik'e tamm!! Suka  tsurawa juna ido,,, gumi taga goshin sa nayi,, yana ta cije baki!! Bakinta na rawa tace"Yallab'ai baka da lafiya ne"?  Da k'yar ya gyda mata kansa, yace"K'afata ta rike min" gabanta ya fad'in,, cikin zuciyarta tace"Kar dai mafarkina ya zama gaskiya,, hannu takai kafar tana shafawa idanunta har sun soma zubar da ruwan hawaye,,  a hankali yace" cire hannun ki babu dad'i" da sauri ta cire hannun nata tana kallonsa,, cikin dauriya yace"Yaya za'ayi nayi sallah"  tace" Ko in kama ka mik'e"? Gyad'a kai yayi yana murmushi me ciwo yace"Baza ki iya ba,, mik'omin waya ta""" sauka tayi da sauri ta d'auko wayar ta mik'a masa,,, numbar Shatima ya kira,,,, ya fada masa halin da yake ciki,, cikin tashin hankali Shatima ya futo daga gida,, kai tsaye gidan sarautar ya nufa lokacin har an idar da sallahr asubah,, Balabara na durkushe a gabansa jikinta sanye da hijab,, ba ta cire ba,, Shatima yayi sallama ya shigo,, zama yayi yana duba k'afar,, cike da alhini yace"Kurum wayar gari kayi kaji k'afar taki ta kuwa"? Sarki! Ta girgiza kai shi kadai yasan ciwon da yake ji yace"Da sauk'i ai idan kin takuwa tayi,, taki motsi fa" Shatima ya Dora hannunsa k'afar yana salati,, wayarsa ya Ciro yana kiran dector dake duba Sarki!! Yace"yazo yanzu yanzu,,, "Kamani in mik'e in kama ruwa sai in d'aura alwala inyi sallah". Shatima ya mike yana kici-kici ya samu ya mik'e inda Allah ya rufa asiri ma k'afa d'aya ta taku itama da k'yar da dafa bango suka je toilet yayi uzirin sa, kana ya dauro alwala suka futo,, dadduma ta shimfuda masa,,, cikin zuciyarta sai tasbihi take Allah ya gajar ta musu wahala

[9/26, 8:42 PM] BintubatulBintUmarAbbale👄: Da Jan k'afa suka k'araso gurin yayi nufin ya tsaya abun ya gagara,, sai ya zauna a nutse yayi sallahr sa,, duk suna tsaye suna kallonsa Balaraba sai goge hawaye take,, Shatima ko ya kira numbar Shahid yafi Sau a kirga bai d'auka mybe baya kusa,, dector ya shigo da kayan aiki,, cikin girmamawa ya gaida shi ya amsa a nutse ya fara yi masa tambayoyi,, Sarki! Ya fada masa duk abunda ya faru,,, A hankali ya kama k'afar yana dubawa,, lafiya Lou da ita a ido,, matsata yayi sarki! Ya cije baki!! Yace"Kar ka k'ara matsawa,, dector ya cire hannunsa da sauri yana neman afuwa,, yace"Yallab'ai ina ganin dole zamuje hospital dakai domin mu auna k'afar dole kuma a d'auke hoton ta, domin sanin maganin da ya dace da ita" Gyad'a kai kurum yayi,, Shatima yace" Bari insanar da Mama Halin da ake ciki,, babu Wanda yace masa komai,, yana sauka k'asa suka ci karo da Halisa ta shigo,, da fara'a ta tsaya suna gaisawa da alama batasan abunda yake faruwa ba,, Shatima ya wuce bai fada mata ba,, kai tsaye sama ta nufa cikin k'asaita! Tana shiga taga Balaraba durk'ushe gaban shi tana kuka, ga dector a tsaye a gefe yayi shiru  fuskar sa ta kalla taga alamun alhini ta k'arasa da sauri kusa dashi,, cikin kid'ima tace"Hubby menene wai naga duk kuna cikin damuwa!" Kallon ta yayi zuciyarsa a dake!! Yace"Babu komai ke me kika gani" ? Baki na rawa tace"Tashin hankali na gani"" d'auke kansa yayi baice mata komai,, Balaraba ta kalla tace"Menene "? Kafar sa ta nuna mata, tana kuka! Halisa ta kalli k'afar da sauri,, taga ta Dan kumbura" jiki a sanyaye tace"Ciwo take masa"? Balaraba ta girgiza kai tana fad'in "Idan ciwo ne da sauk'i yau tunda ya tashi ya kasa tafiya da ita tak'i motsi d'azu da k'yar aka kai shi toilet yayi alwala " Halisa tace"Innalillahi wa ina ilahi raji'un kuka ta fashe dashi tana k'unshe baki tace"Wannan wace irin masifa CE"???? Tsawa!! Ya daka mata yana fad'in"Bana son shashanci da koke -koke addu'a zakuyi min""""" a gigice ! Ta mike tana fad'in"Au! Da gaske ne Ashe? Sai ta kalli Balaraba Cikin daga murya tace"Ke nake zargi! Munafuka meye ribar ki anan, me yasa ranar da ya kwanta damu haka bata faru ba,, me kike nufi, bak'ar algumguma wato kina so ki kashe ki samu tumunin takaba"? Taji kamar ta watsa mata ruwan zafi,, a jiki ta dago jajayen idonta da suka rine!! Bakin ta na rawa tace"Mey...... Ka tsaye ta yayi ta hanyar daga mata hannu sai tayi shiru gami da toshe bakinta da gefen hijab dinta tana k'okarin b'oye kukan da yake k'okarin kufce mata a karo Mara adadi,,,, Halisa yake kallo cikin tsantsar b'acin rai da takaici.

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

_ALHERIN ALLAH YA ZO INDA KIKE_

 

*NANA AISHATU KADUNA*

 

_Hak'ika inajin dadin comment dinki ubangiji Allah ya kara kauna da aminci nagode sosai ina miki fatan alkairi a rayuwar kiđŸ„°_

 

 

 

_*Kuyi hakuri yau pege din babu yawa zazzab'i ne ke damuna wallahi Ku sanya ni cikin addu'ar Ku*_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿109*

 

 

 

 

Suna had'a ido dashi ta kara rikicewa tana fad'in"Wallahi Hubby kar ka yarda da ita,, itace Silar faruwan wannan al'amari ko mara kunne ne yaji wannan abun yasan da akwai lauje cikin nadi,, shiyasa hausawa suke cewa idan  takalan mutum mugun ice ne, idan ya samu guri yafi mai kudi iko,wallahi yanzu na daina ganin laifin masu kud'in da suke gudun talaka domin halin su ne ya ja mus............."Halisaaaa!!! Rufe min bakin ki anan gurin"" ya katse ta  cikin wata muguwar tsawa"" gum! Tayi da bakin ta tana shashshekar kuka,, Balaraba na durkushe a gurin kai a kasa tana zurarar da hawayen bakin ciki,, murya a cunkushe! Yace"Duk futa bana son ganin Ku" da sauri dector ya futa Halisa ta futa simi-simi,, mik'ewa tayi kwata-kwata jikinta babu lak'a, suka had'a ido saurin d'auke kansa yayi ransa a bace kalaman Halisa ba k'aramin kona masa rai sukayi ba,, wuce tayi tana waigen sa, duk yana kallonta,,, tana futa ya sauke ajiyar zuciya me zafi.

 

 

Tana sauka taga Halisa da Azima suna maganganu k'asa-k'asa suna ganinta suka hau rafka mata harara, d'auke kanta kawai tayi,, Mama ce ta shigo bayanta Jakadiya da Shatima Shahid da Madabo cikin tashin hankali ta nufi sama suka rufa mata baya,, kansa a kasa yaji shigowar su,murya Maman shi yaji a kansa, ya d'ago idonsa,, da sauri ta tsuguna kusa dashi tana masa magana,, cikin nutsuwa ya warware mata duk abunda ya faru,, cikin tawakkali tace"Allah yana ji yana kallo ko wane hali da kake ciki abunda za za'ayi yanzu muje hospital din ayi hoton kamar yadda dector ya fada insha Allahu komai mai sauk'i ne" A nutse ta ce da dector "Je ka d'auko while chair,, a d'auke shi,, da sauri ya futa, shiru dakin babu Wanda yayi magana har dector ya dawo su Shahid ne suka kama shi suka Dora shi kai, a hankali suka dunga sauka dashi, daga kafar bene, Mama na bayansu tans goge hawaye a fakaice.

 

Balaraba ta mike da sauri ta tsaya har suka k'araso gurin,, kallonta yayi yaga duk ta tayar da hankalin ta, ta bashi tausayi wannan alama ce da ta nuna tana cikin damuwa kuma ta damu dashi sosai,, babu yabo babu fallasa yace da ita"Wannan kukan da kike ya isa haka, cuta fa ba mutuwa bace, shikkenan ni Allah bazai jarrabe ni, ba Wannan ba yana nufin shikkenan bazan kara taka k'afafu na ba, insha Allahu inaji ajikina wannan abun na lokaci kankani ne saboda haka Wannan koke-koken da kukeyi ya Isa haka" Balaraba tayi shiru tana gyad'a kai, Azima kuwa ai batayi shiru ba sai cewa tayi "Duk ba anan take ba Yallab'ai dole muyi kuka Hak'ika an zalince ka kuma bazamu bari ba,, wallahi ka gurgunce sai mun d'auki mummanan mataki akanta " duk jama'ar gurin suka bita da kallo cikin mamaki,,,!! Mama tace "Ku muje mu wannan tsayuwar bata da amfani,, Azima da Halisa suka rufa musu baya, Balaraba aka bari a baya tana tafiya salau-salau babu kuzari ko na kwabo a jikinta.

 

 

Buba direba ya bud'e bayan mota suka d'auke shi suka saka ciki da gyara masa zama sosai sannan kowa ya shiga ya zauna,, ganin Matan nasa na k'okarin shiga ne ya dakatar da Buba,, kallonsu yayi cikin bada umarni yace " Ko wacce ta koma gurin ta""" umarni ya bawa Buba ya tada mota suka futa,, dake safiya CE, babu jama'a sosai a harabar gurin sai dai-dai Ku, motar na fucewa suka yo kan Balaraba da bala'i kowa na fad'in albarkacin bakinta,, Balaraba lalurar mijinta itace a gabanta shiyasa bata tanka musu ba,, wucewa tayi ta barsu a gurin suna zagin ta ta uwa ta uba.. Sun jima a gurin suna maida magana daga bisani kowa ya koma part d'insa,,, Azima labewa tayi sai da taga Halisa ta shige ta kulle kofa sannan ta futo kai tsaye b'angaran Waziri Zayyanu ta nufa...

 

 

Da futowar su da shigar su mota da futar su daga gidan sarautar duk akan idon Waziri da Tsito ,,  Tsito ya kwashe da dariya yana fad'in kaga aikin Mak'asudu ko, ai inda alkawairi to da cikawa,, kai kuma sai ka kula da haradin da ya gindaya maka"

 

 

Waziri ya kece!! Da wata mahaukaciyar dariya"  hahahahahaha"" Mak'asudu ka cika alk'awarina na yarda dakai akan aikin ka, daga yau zan fara mulkina cikin kwanciyar hankali da nutsuwa nasan wancan yaron ya zama musaki,, ka lalata masa k'afafu ya gama aiki, Hahahahaha"""

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

_*DEDIGATED*_

         _*TO*_

_RAHAMA ALIYU_

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿110*

 

 

 

 

Zuwan Azima gurin yasa Waziri ya bar dariyar da yake yi,ya d'ora hannunsa akanta fuskarsa cike da walwala da farin ciki yace"Kin gama min komai yarinya ta, hak'ika kin cika "yar halak d'iyar abokina aminina ya iya haihuwa ki fad'i duk abunda kike buk'ata zan yi miki". Jiki a sanyaye Azima tace." Nifa na soma nadamar abunda nayi gaskiya yanzu ina dana sani" Waziri da Tsito suka kalli juna, Tsito yayi wani murmushi, Yace." Ki daina nadamar abunda kika aikata idan kuma kina jin tsoro kar sunan ki ya futo ranar da asiri ya tuno to duk ki daina, aiki inda Mak'asudu a ciki baya karyewa sai dai Idan wanda yayi aikin ne ya kar ya doka saboda kije ki kwantar da hankalin ki,babu abunda zai faru,daga yau ma zan fara aiki domin zan daure wa duk mutan gidan baki" Azima ta sauke ajiyar zuciya gaskiya halin da taga mijinta a jiki ya bata tsoro amma aikin gama ya Riga ya gama, Waziri yace"Shiga ciki ganin zuwa" simi-simi ta shige cikin gidan nasa.

 

 

To duk wani alk'awari da Waziri yayi wa Tsito sai da yq cika masa mota guda akaiwa Tsito da tashi da ta kayan arzki ya tafi garin su, Hajiya Kulu ma tayi masa kyautar bajinta dake ba sosai take zama a gida ba shiyasa duk bata San abunda yake faruwa ba sai da Waziri ya shiga har gurin ta da sassafe ya sanar mata, murna ta dunga yi mak'iyinta ya gurgunce dama ita babban bakin cikinta shine kar yayi mulki tunda ita Allah bai bata 'ya'ya mata ba.

 

 

Babu irin aune-aunen da ba'ayi ba, abu d'aya yake nunawa k'afafun shi lafiya suke, cike da dumbun mamaki da al'ajabi suka dawo gida suna tunanin meye abun yi,

 

 

 

Waziri kuwa bayan sun rabu da Tsito gida ya koma ya shiga keb'antaccen d'akinsa da ya rataye fatocin su k'adan gare, Kunama da kulb'a gami da b'eran dunka bango guda ya kafe su, tsakiyar su wani Jan yanki ne a n daure wani Abu a tsakiyar sa, shiri yayi sosai ya nufi fada yana wani irin taku na k'asaita shiga Sarki aikuwa fada na cike da mutanan sa munafukai ya zauna suka fara aikin zugashi da wasashi shi kuma yana jin dad'i.

 

 

 

******

Yanda aka futa dashi haka aka shigo dashi dama tun safe Labari yaje kunnensu Limam da Galadima da Wambai don haka suna tsaye aka futo dashi daga motar, suna kallon ikon Allah kowanne yana mamaki da tu'ajibi k'afafun Sarki! Sun kumbura sosai, ba kamar d'azu da safe ba.

A daran ranar mai girma governor yazo suka zauna da Sarki! Duk aka basu guri, dake akwai sha kuwa a tsakanin su, Governor yace."Ina ganin wannan ciwon naka tafarar d'aya anya ba jifa bane? Nifa ka sanni da lek'e-lek'e saboda yadda yanayin al'amarin namu yake, gaskiya ina zargin jifa ne kuma duk wanda yayi maka makusancin ka ne"

 

 

 

Sarki! Yace."Kaga ni kuma bana wannan tunanin kawai nafi gazgata cewar jarraba ce daga Allah" Governor ya gyad'a kai yana tunani minti biyu yace."Shikkenan yanzu dai na sanya ayi mana vizar dani da kai dasu Shatima zamuje Saudi'a akwai k'wararun likitoci islamic a can insha Allahu kome ye zamu gane zamu samu sassauci" Gyad'a kai kurum yayi, . shiga don duk sun damu ne, amma sam baya jin wani ciwo a k'afar shi, illa kawai motsa ta da ya kasa yi duk da haka yanaji zai iya yin duk abunda mai lafiya zaiyi. Sallama sukayi governor ya mike ya futa mutanan sa suka rufa masa baya.

 

 

To a can babban falon Fulani ma Ashe tattauwar da ake kenan Liman ne ya bada sha'warar suje saudi'a wannan Asibitin dai da governor yake magana akai.

 

 

Ko da Halisa ta shiga part d'insa tun kafin ta zauna ya fattatake ta, jiki babu k'wari ta futa, tana da tasanin shirman da tayi masa d'azu.

 

Balaraba kuwa abunda tasan zata d'auka taje ta d'auko a part d'inta ta kullo ta dawo gurinsa, kula take dashi sosai tana jin wani irin tausayin sa, kallonta kawai yake yana mamaki ashe tana sonsa.

 

 

Yana zaune gefan gado da k'aramin littafi a hannunshi yana dubawa idonsa sanye da glass d'insa na fama ta futo daga toilet d'inshi jikinta daure da towol din sa,da wani akanta ta nannad'e kanta, had'a ido sukayi da sauri ya kauda kansa, ita yanzu kunyar sa ta ragu lafiyar sa kawai take so shiyasa bata jin kunyar saka kaya a gabansa ba, so take tagama abunda take taje gurinsa taji ko da akwai abunda zatayi masa,  yau tayi Wanka tsarki dadduma ta shimfid'a ta tayar da sallahr isha'i ,, dago kansa yayi yana kallonta sosai, zuciyarsa yace"Tayi Tsarki kenan hummmm! Lallai yau akwai budiri😍

 

 

 

*Bari muga yaya za'a buga kwallon😂*

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

            _*GIMBIYA BALARABA*_

                    đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

                  _*NA*_

_BINTA UMAR ABBALE_

*®BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

```MARUBUCIYAR```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUD'I*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

 

 

 

_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATIONđŸ€đŸ»*_

 

_________________________

```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades```

_________________________

 

 

 

 *DEDICATED*

         *TO*

*RAHAMA ALIYU*

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿111*

 

 

 

 

Saurin kauda kansa yayi daga kanta ganin tana zuwa gurin sa, kallon littafin dake hannunsa yake,sai ka rantse da Allah bai san da zuwan ta gurin ba, zama tayi kusa dashi ta d'an tsurawa littafin dake hannusa ido, ta lura yana da son karanta littafan addini,nan ta tuna da program d'insa da yake duk ranar juma'a, ake sanyawa tashoshin redio, a nutse tace."Ya jikin" ? Hankalinsa na kan littafin yace." Alhamdullahi " shiru dakin yayi minti biyu tsakani tace."Ko kana buk'atar wani Abu"? girgiza kai kurum yayi,kallonsa tayi zuciyar ta tace."Ubangiji Allah ya baka lafiya" k'asa-k'asa yace." Kashe mana hasken futular nan, na duba dana wayata" Mik'ewa tayi a nutse ya bita da kallo cike da so da sha'awa, futular ta kashe dakin yayi duhu sai hasken wayar sa, kad'an, zama tayi inda ta tashi tayi shiru tana zancan zuciya. Yace." Ki kwanta mana" a hankali tace." Idan na kwanta kuma kai zaka kwanta ban sani ba ko da wani taimako da zanyi maka kar bacci ya d'auke ni". Murmushi yayi iya kacinsa leb'ansa yace."Hakane, kawai kiyi kwanciyar ki, idan ina buk'atar wani abu zan ta she ki"  Hawa bed din tayi sosai taja bargo ta rufe iya kacin k'irjinta fuskarta a bude.

 

 

 

Sai misali k'arfe goma sha biyu da rabi ya rufe littafin ya aje shi, hannusa ya sa ya jawo while chair d'insa da ke gefe ya sai ta sosai cikin k'arfin hali ya hau ya nufi toilet, a nutse yayi uzirinsa ya futo, kai tsaye mirrow ya nufa, turaririka ya fesa sosai a jikinshi,  motsin sa taji yasa ta bude ido sai taga yana k'okarin sauka daga while chair d'in, da sauri ta sauko ta ruk'e hannunsa ya zauna bed din sosai, ta sanya hannunwan ta ta d'auko k'afarshi ta Dora a hankali haka tayiwa d'ayar ma, a raunane tace."Shiyasa fa nace ko kana da uziri me yasa baka tashe ni ba".? Cikin duhun d'akin yake, ganin yadda fuskarta ta nuna alamun jimami da tausayi, gyaran murya yayi yace." Kar ki damu toilet na shiga kuma na futo Cikin hukuncin Allah". Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta koma ta kwanta tana kallon shi yana k'okarin gyara kwanciya, lumshe ido kawai tayi tana shak'ar k'amshin tura ransa masu sanyi duk jikinta ya mutu jin saukar nuffashin sa a kusa da ita, babu zato taji hannusa a jikinta yana k'okarin jawo ta ya rungume, kallon fuskarsa tayi sai taga idonsa a lumshe, tanaji ya jawo ta jikinsa ya rungume k'am, gami da cusa fuskarsa tsakanin wuyanta, shiru tayi tsigar jikinta tana tashi, nuffashi ya dunga saukewa akai-akai taji yana k'okarin cire mata rigar bacci, hannusa ta dafe takasa dago kai ta kalle shi.....har sai da yayi nasarar cire mata rigar jikinta, ya d'auke ta ya d'ora ruwan cikinsu, fuskokinsu suka had'u guri guda, rintse ido  tayi tana mugun jin kunyar sa da mamakin abunda yake lallai bashi da dama, abu yake tamkar mai cikkakiyar lafiya, wuyanta ya rik'o da hannushi guda, muryarshi bata futa sosai yace"Kiss me plaesa". Balaraba ta dinga jin kanta yana wani irin juyawa saboda lokacin da yayi maganar wani mugun kamshi mai dad'i ne ya futo daga bakin sa, cikin sigar jan hankali mace ya k'ank'antar da muryar shi yace." Ki kula dani kin ce in ina da buk'ata nayi miki magana, toum ke nake buk'ata a yanzu, yanayin yadda yake mata wasa da gadon bayanta ne ya furgitata, sai ta hau kufce-kufce zata sauka daga kansa, ya rike ta sosai yana k'okarin b'alle mata briziyya, murya a sark'e tace."Kayi hakuri kai da baka da lafiy..... Ka tsata yayi ta hanyar fad'in" Lafiya k'alau mutukar a wannan fannin ne babu abunda bazan iya ba" Shiru tayi masa tana jinsa yayi dubara ya zare mata brziyya jikinta ya wani kara damk'e ta sosai yana sakin wata irin azabbabiyar ajiyar zuciya jin taushin brast d'inta a tsakiyar k'irjinsa, a gigice ya lalubo bakinta ya had'a da nasa ya farai mata lafiyyan kisses masu wahalar mantawa, Balaraba taji kamar ba'a cikin duniya take ba jin wani mugun dad'i da shauki yana dibanta, ga gashin k'irjinsa yana tsikarar ta a jiki, nan take ta sakar masa jiki, suka fara shan soyyayarsu irin ta ma'aurata. Nan na futo na barsu domin ganin sirrin wasu bashi da amfani.......Cikin dabara da hikima irin tashi ya dinga lallab'ata har ya samu ya mayar da ita cikkakiyar mace, Balaraba tayi kuka sosai kuma ta razana da jarumtar sa, cikin zuciyarta take fad'in"Babu Lafiya ma yayi mata wannan aiki ina ga idan ya samu sauk'i .. Ni ko nace Balarana kenan Sarki! fa lafiyansa lau kawai matsalar shi rashin k'afa babu  wani Abu da mai cikkakiyar lafiya zai nuna masa.

 

 

 

Cikin jin kunya da nauyi ta tashi da safe jikinta duk yayi tsami da nauyi da k'yar ta shiga toilet ta gasa jikinta ta futo lokacin shi yana zaune kan dadduma har ya idar da sallah tayi ta mamakin yaya akayi ya tashi yayi wanka haka har ya shirya jikinsa, dadduma ta hau tayi sallah bayan ta idar tayi addu'a yanda ya sauwak'a, jiki babu kuzari ta mike tana cire bedshirt din domin duk ya b'aci da jini, gyaran murya yayi, ta Dan kalle shi kad'an, ta d'auke kanta da sauri, can taji muryarsa yana fad'in"Ki bari kar ki bawa kanki wahala zasu zo su gyara" batasan sanda ta kwad'a masa harara ba, Murmushi ya saki yana girgiza kai toilet ta wuce da bedshirt din a hannu ta cikin zuciyar ta na fad'in "Abun kunya ne in bari wani ko wata ya ga sirrina da mijina komai sai na gyara da kaina. Tsaf ta wanke shi ta rataye ta kara wanke toilet din, a nutse ta futo, taka had'a ido dashi, shi kuma sai kallonta yake yana sakin k'ayattacan murmushi yarinyar ta gama masa komai yanzu baya jin wata damuwa a tare dashi mararsa sakayau kamar anyi masa wankin Mara,sab'anin jiya da shekaran jiya da take damunsa ko jiya da ya taki Azima ya rage wani abun ne, amma yau Balaraba ta gamsar dashi sosai don haka bakinsa bazai tab'a gajiya da shi mata albarka ba,

 

 

Gurin da ta aje kayan ta ta nufa ta d'auko wata duguwar riga mai hula rigar ta gaji da haduwa sosai kalar sky blue ce, dogon wando ta zura sannan ta Dora rigar ,duk idonsa akanta, cikin zuciyarsa yake fad'in" Yarinyar nan nason abu sky kamar tasan ina son shi.

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

       _*GIMBIYA BALARABA*_

              đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

~*NA*~

_BINTA UMAR ABBALE_

*BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

*MARUBUCIYAR*

 

 

```NANA KHADIJA```

```YARO DA KUDI```

```GIMBIYA BALARABA```

```TSANTSAR BUTULCI```

```LADIDI K'WADAGA```

 

 

 

 

_*ZAMANI WRITES ASSOCIATONđŸ€đŸ»*_

 

_____________________

```We are here to educate motivate and entertain aur reades```

_______________________

     

  

 

 

*ALHAMDULILAH*

 

*HAUWA S ZARI'A*

 _Maman Usuwan_

 

*Ina taya ki murna na kallama littafin ki HAKA ALLAHA YA NUFA* _KADDARA TACE_ *UBANGIJI ALLAH YA K'ARA BASIRA YA SA SAK'ON KI YA ISA INDA KIKE SO*

_________________________

 

 

 

 

*JAN KUNNE*

 

_*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_

 

 

 

 

 

*DEDICATED*

     ~*TO*~

*RAHAMA ALIYU*

   ~*ABUJA*~

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_

 

 

 

 

 

*🅿112*

 

 

 

 

 K'ok'arin futa take daga d'akin, ba tare da ta k'ara kallon inda yake zaune ba, cikin nutsuwa yace." Ina zakije kuma"? D'an juyo wa tayi tace."Zan je in kawo maka abun kari" k'asa yayi da kansa cikin so da k'aunarta yace."Na huttashe ki dawo ki zauna, domin yau bana jin yinwa saboda kin cika min ciki da so da k'aunar ki, hak'ik'a ina alfahari dake cikin matana Balaraba kece Gimbiya ta." Lumshe idonta tayi tana jin wani yarrr! a jikinta gaskiya taji dadin yabon da yayi mata, itama yanzu ta fara jinsa cikin zuciyarta, yace." Dawo ki zauna muyi hira" Simi-simi ta dawo ta zauna nesa dashi,sai kauda kai take cike da kunya, shi kuma ya k'ura mata ido yana sakin k'yatattacan murmushin sa,  cikin shagwaba'a tace." Ka daina kallona haka inajin babu dad'i a jikina."Lumshe ido yayi ya bud'e tare sa zuba mata su yace." Haka nake so ai da alama kin fara sona, ko da yake ma, jiya naga alamu daddare an karb'eni hannun biyu" rufe fuskarta tayi ta mik'e da sauri ta bude dakin ta futa cike da kunyar sa. Karo! Suka buga da Halisa ta d'ebe ta ta watsar! tab'e baki tayi tamkar taga kashi tace." Ke kuma wannan shashan cin fa? dube ki don Allah abun tausayi dake wai har kece zaki shigo cikinmi ki nakasa min miji,to bari kiji wallahi Duk irin k'ulunboton ki baki isa ki kashe min mijina ba, domin kici dukiya sai dai Idan mu, mu kashe ki, kar ki manta da cewar mun San kece silar mutuwa d'an uwanmu Moddibo, to wallahi Sarki! Almansur yafi k'arfin ki, jaka kawai, 'yar talakawa"

 

Wani mugun b'acin rai! Ya turnek'e zuciyar Balaraba, tabbas Halisa taci albarkacin mijinsu da bashi da lafiya, amma da badan wannan ba, da sai ta k'ara nuna mata ita wacece, da alama ta manta karon su da ita na farko, amma taci al'washin duk randa ta k'ara yi mata magana irin wannan tabbas sai ta nuna mata kuskuran ta. Azima ce ta k'araso inda suke tsaye ta buge k'afad'ar Balaraba tana zabga tsaki! Hannun juna suka rike suka wuce ta cikin wata irin tafiya ta k'asaita. Kallo ta bisu dashi zuciyarta tana zafi,! Lallai ruwa ya daki babban zakara, ita kad'ai take fad'in haka a zuciyar ta, idan da ba haka ba wallahi da sai sun gane kuransu.

 

Yana zaune inda yake tun futar Balaraba, fuskarsa cike da annuri suka same shi, amsa musu sallama yayi ya nuna musu gurin zama, jiki a sanyaye ko waccen su ta zauna, babban abunda ya sa jikinsu yayi sanyi shine ganin da sukayi yana cikin farin ciki da annushuwa kamar yadda suka ga fuskar Balaraba haka, wani irin kishin Balaraba ya damu zuciyarsu, sanin halinsa na rashin d'aukar raini yasa ko wacce tayi shiru da bakin ta, gai dashi sukayi sunayi masa ya jiki, ya amsa da walwala, Azima tace."Yau zaku tafi ne"? " Eh insha Allahu sha biyu na rana" Shiru sukayi. Halisa tace." Tunda ita wannan ta futa daga girkin ta, zan shiga nawa ina ganin ya kamata a tafi dani ko da wani taimakon da zanyi maka." Harararta yayi, ta sunkuyar da kanta da sauri, a hankali yace." Ke ko za'a tafi da wani waye zai tafi dake guri kije kiyiwa mutane shirme" Azima taji dad'in maganar sa, ji wani son kai na Halisa take fada a zuciyar ta, muryar shi sukaji yana fad'in"Duk Ku kwantar da hankalin ku babu da wanda zani, sai kace wani Yaro,ku munje ma ba wani zama za muyi ba."

 

 

Azima tace." Nima dai abunda nagani kenan." Halisa kuwa sai yak'e take ta lura mutumin nata haushinta yake ji, domin yak'i sakin jiki da ita hirarasu suke da Azima tamkar babu ita a gurin. Wayar shi tafara k'ara ta mike da sauri ta d'auko masa, karb'a yayi ba tare da yace mata komai ba, Governor na ne, suka gaisa yace." Fatan jikin da sauk'i, duk wasu shirya-shirye angama insha Allahu da kaina zan zo in d'auke ka cikin mota har filin jirgi" Sarki! Yace." Jiki alhamdullahi ni kam bani da matsala sai ta rashin k'afafu shima na wani lokaci ne insha Allahu, zamu zauna cikin shiri insha Allahu" Governor yace." Naji muryar ka rad'au da alama kana cikin nishadi kasan fa duk namiji da yake da mace sama da daya to mutukar suna kula dashi da kwantar masa da hankali babu Wanda ya kaishi dacewa". Murmushi yayi yace." maganar ka haka take, Aboki" dariya Governor yasa yace." Dole dai na koya maka surutu ko"? Yace." To ya na iya fa halin ka." Haka dai sukai barkwamci kafin suyi sallama suka kashe wayar, Azima da Halisa kuwa ganin babu fuska ko wacce taje zata je tayi Wanka, suka sauka babu wacce ta kara kula 'yar uwar ta.

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

       _*GIMBIYA BALARABA*_

              đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

~*NA*~

_BINTA UMAR ABBALE_

*BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

*MARUBUCIYAR*

 

 

```NANA KHADIJA```

```YARO DA KUDI```

```GIMBIYA BALARABA```

```TSANTSAR BUTULCI```

```LADIDI K'WADAGA```

 

 

 

 

_*ZAMANI WRITES ASSOCIATONđŸ€đŸ»*_

 

_____________________

```We are here to educate motivate and entertain aur reades```

_______________________

     

  

 

 

 

 

*JAN KUNNE*

 

_*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_

 

 

 

 

 

*DEDICATED*

     ~*TO*~

*RAHAMA ALIYU*

   ~*ABUJA*~

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_

 

 

 

 

 

*🅿113*

 

 

 

 

To Balaraba ma lokacin da suka rabu dasu Halisa gurin ta, ta nufa wanka ta shiga a gurguje ta futo ta kimtsa jikinta, ta kasance mace me son atampa duk ya wanci kayan ta itace doguwar riga,  da Riga da siket da zani basu da yawa, yanzu ma wata 'yar Ghana ta saka doguwar riga ce, sosai kasa ya bud'e daga iya kwankwanson ta ya matse da kirjin rigar komai ya futa har madauri ne da ita daga baya, d'ankwali ta d'aura dai-dai misali ta shiga kicin dinta dole tana ganin sai tayi masa abu motsa baki, cake ta fara had'a ma, zuciyar ta tace ki had'a masa Dambu nama ko yana so, nan take ta futo da zallar tsokar Neman sa cikin firji ta Dora kan wuta bayan ta sanya albasa da kayan k'amshi, ta cigaba da had'a cake din ciki k'warewa.

 

 

Balaraba ta k'aware sosai gurin had'a dambun nama shiyasa sam bai bata wahala ba, nan ta had'a komai cikin abunda bai fi awa guda ba, k'amshi ne kawai yake tashi kicin d'in, zuba shi tayi cikin warmers ko wanne ta aje ta samu wani had'ad'an akushi irin na gidan sarauta ta cika shi da cake d'in da Dambu nama,wannan ta aje shi ne sai zasu tafi zata bashi, ruwa ta d'ora a wuta ta zuba kayan tea masu sa kamsh gahwa na'ana'a citta kanifari kimba da dai sauran su sai da ya gaja da tafasa sannan ta kashe gas d'in ta tace sosai ruwan tea d'in yayi kyau sai kamshi yake ta juye cikin fulas mai kyau. D'auka tayi ta kai falonta ta aje ta dawo ta gyara kicin din tas! Sannan ta dawo ta d'auki, d'auki abunda ta aje, kai tsaye part din shi ta nufa. Lokacin har su Shahid sun zo sun d'auko dashi k'asa yayi wanka shar dashi kana ganinsa kaga ango sosai yake walwala Shatima na tsokanar sa wai farin cikin me yake, shi kuma yana basarwa.

A nutse tayi sallama ta shigo, da sauri ya dago kanshi yana kallonta, saurin sunkuyar da kanta tayi, cikin mamaki ya bi hannuta da kallo, yana kallon yanayin tafiyar ta, Shatima ya amsa yana fad'in"Gimbiya sannu ki da zuw..... Katse shi yayi ta hanyar fad'in"Ka tsaya kana surutu ka karb'i abun hannuta mana,bata da lafiya" Balaraba tayi saurin kallonsa, cikin mamaki, da sauri ta wuce Shatima ya bi bayanta yana fad'in"Ayya! Gimbiya sannu da kokari kawo in aje miki daining d'in." Murmushi k'arfin hali tayi tace." Ka rabu dashi don ni lafiya talau fa." 'Yar dariya yayi yace." Ai naga alama gashi kin sha aiki domin ki faranta ran maigidan ki mybe yana so ki huta ne shiyasa Yace in karb'e ki" Shiru kawai tayi masa tana sunkuyar da kanta cike da kunya,wato Dole dai sai ya tona mata asiri gurin abokan shi,kome amfanin fad'a musu haka oho masa. Gyara gurin tayi sosai, Shahid ya kawo shi har gurin, idonsa a kanta yace." Wato nace kije ki huta shine kika wahalar da kanki ko."  K'asa tayi da kanta kurum domin bata so tayi wata magar ya lafto wacce zai sa har su Shatima su gane. "Jimana" yafad'a yana tsare ta da ido, a nutse ta watsa masa wani kallo, Wanda ya shiga jikinsa,amma da yake ya saba karb'arsa sa'i da lokaci a gurin ta,sai ya dake! Yace." Bayan wahalar da kika sha jiya shine zaki na wahalar da jikin ki yanzu,wai ke bakya son hutu ne." ? Taikacinsa ya hanata cewa komai, sai aukin futo da warmers take, Shatima ya doki kafad'arsa yana fad'in." Kai kanai mata bak'in cikin ladan da zata samu ne, ina ruwan ka."? Shahid ya b'oye dariya yana fad'in"Lallai hausawa da sunyi gaskiya cikin karin maganar su, inda suke fad'in"Gurgu yafi...........Sarki! Ya galla masa harara! Dariya suka saka Shatima ya bashi hannu suka taga!Balaraba kamar ta nutse don kunya, simi-simi tabar gurin tana da ta sanin dawo da tasan tonan silili zai mata da bata dawo ba, dab da zata futa sai ga Mama ta shigo da jama'ar ta, sai ta tsaya tana murmushi , itama Mama murmushi ne a fuskarta, suka zauna cikin kujera Balaraba ta durkusa har kasa ta gaishe ta, cikin sakin fuska mama ta amsa tana tambayar me jiki, tace "Jiki alhamdullahi wallahi gashi yana k'okarin Mama muna sa ran samun nasara wannan tafiyar insha Allahu, Mama tace." Hakane dama babu abunda yafi k'arfin addu'a ai, jiya munyi waya da aminiya ta, Matar Sarkin  Yalwa sosai mahaifinta dake Malami ne yasa yara 'yan makaranta na addu'a jiya an sauke al'kurani babu adadi"

 

Mama ta cigaba da cewa." Insha Allahu tanan zuwa itama,kin san bata samu damar zuwa gurin bukin ku ba tun dai da tazo lokacin mutuwar me Martaba." Balaraba tace." Kai angode sosai wallahi ai Mama alk'urani mai girma yana tattare da waraka ko wace iri ce ,mutukar mutum zai rike shi, to ya rike babban kundi."  Mama tace." Haka maganar ki take Balaraba." Su Shahid ne suka k'araso gurin cikin nutsuwa suka tsuguna suna gaishe da ita, ta amsa musu da walwala a fuskarta tace." Ya mai jiki? Domin Ku zan tambaya." Shahid yace." Jiki alhamdullahi Mama kin ganshi zaune k'alau dashi,wannan kuma aikin Gimbiya ne ga tanan kusa dake." Cikin farin ciki Mama tace." Nasan zata aikata fiye da haka, k'okarin tura while chair d'in yake, da sauri Shatima yace." Kabari mana inzo." Ko saurarensa baiyi ba ya cigaba da turawa ya k'araso kusa dashi gami da kama while chair din yana fad'in"Da ka bari an turaka."  "Akan me zan bari hannuna aikin me yake." Yafad'a ciki-ciki murmushi kawai Shatima yayi yana fad'in" Dama kai ai babu me iyawa da kai sai Balaraba."

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

 

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

       _*GIMBIYA BALARABA*_

              đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

~*NA*~

_BINTA UMAR ABBALE_

*BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

*MARUBUCIYAR*

 

 

```NANA KHADIJA```

```YARO DA KUDI```

```GIMBIYA BALARABA```

```TSANTSAR BUTULCI```

```LADIDI K'WADAGA```

 

 

 

 

_*ZAMANI WRITES ASSOCIATONđŸ€đŸ»*_

 

_____________________

```We are here to educate motivate and entertain aur reades```

_______________________

     

  

 

 

 

 

*JAN KUNNE*

 

_*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_

 

 

 

 

 

*DEDICATED*

     ~*TO*~

*RAHAMA ALIYU*

   ~*ABUJA*~

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿114*

 

 

 

Shiru yayi masa har suka k'arasa kusa da Mama,ya fara k'okarin saukowa Mama tace." A'a kayi zaman ka kawai mu gaisa a haka lallai jiki yayi kyau,naji dadin ganin ka cikin walwala ubangiji Allah ya k'ara lafiya." Suka amsa da "Ameen" Cikin kauna irin ta d'a da uwarsa yace." Mama kin tashi lafiya."?  Tace."Lafiya lau na tashi amma na kwanta da tunanin ka, shiyasa da na shigo na ganka cikin koshin lafiya naji dad'i kuma na godewa Balaraba." Sunkyar da kai kurrum yayi yana murmushi,tace." Ina fatan ka karya ko."? Balaraba tace." Ga kayan karin can kan daining."  " To maza je ki d'auko masa in ga yaci a gabana." Kallon ta yayi yace." Mama sai kace wani k'aramin yaro." Murmushi tayi tace." K'aramin Yaro kake a gurina." Shahid yace." Wallahi hakane Mama mu yara ne a gaban iyayemu, Sarki! Shiru yayi yana kallon ikon Allah Mama tasa Balaraba ta had'a tea me kauri tace."fara bashi ya d'umama cikinsa." Balaraba ta mik'a masa kofin tae sai yak'i karb'a Mama tace." Ki cika ladanki mana." Sunkuyar da kanta tayi cike da kunya ta nufi bakinsa da cup d'in, a hankali ya bud'e bakinsa ya fara kurb'ar tea d'in, ji yayi sugar yayi yawa ga madara tayi yawa baya son k'arni, a hankali yace." Ki aje Wannan ki had'a min bak'i." Ajewa tayi kamar yadda yace ta fara had'a masa wani,hannu ya mik'a ya d'auki cake guda d'aya ya fara ci, sosai yayi masa dad'i a baki sai da ya cinye guda uku kafin taga ma motsa tea d'in yadda zai fi masa dad'i a baki ta fara bashi cike da kunya a idon Mama da su  Shatima, Mama sam hankalin ta baya Kansu tana can tana magana da Jakadiyar ta, Su Shahid sai tsokanar sa suke yak'i tanka musu, a hankali ta dinga bashi yana kurba yana gutsirar cake d'in, sai da ya ci guda shida sannan ya d'aga mata hannu alamun ya ishe shi, tissue yake k'okarin yagowa, ta ya ciro masa mik'ewa tayi tana goge masa gefan bakinsa,ya tsura mata ido yana kallo, ita ko taki yadda su had'a ido dashi, Halisa da Azima ne suka shigo cikin wannan hali, turus sukayi ganin abunda yake faruwa kowacce jikinta yayi sanyi ga Mama a zaune ga uban tafiyar zaune cikin shiri Balaraba ta had'u sosai domin shigar ta ta yau tayi mata kyau, tana tsaye kusa dashi tana goge masa gefan bakinsa . Suka zazzauna jiki babu k'wari  suna gaishe da Mama ta amsa musu a sake tana tambayar su me jiki, Azima da yake tafi Halisa wayo ta b'oye damuwar ta ta saki jiki suna hira dasu Shatima,har tana sa Balaraba a ciki kamar ba itace ta bangaje ta d'azu ba, ita ko Halisa sai shan kunu take tana hira da Mama kawai, cikin wannan hali me girma governor ya iso, suka gaisa da Mama cikin girmamawa, Halisa ta kalli Mama k'asa-k'asa tace." Mama ina gani tafiyar nan ayi ta dani domin yau girki na ne, kinga sai in kula dashi" Mama tace."aikuwa kin kawo shawara me kyau dama ya kamata a d'auki daya daga cikinku a tafi da ita, to amma kinga Balaraba bata futa daga lokacin ta ba, ina ganin da ita za'a tafi, in yaso in ya dawo sai ya sauka a dakin ki, kin gane ko"?

 

Halisa ta b'ata fuska bata ce komai. Me girma governor yaji dadin ganin jikin shi yayi kyau, sosai ba tare da wani b'ata lokaci ba, suka mik'e domin tafiya Shahid shine yake tura shi har suka futa harabar gidan jama'a a tsatstsaye Suna sauraron futuwarsu kowa na addu'a da fatan alkairi, tare da samun lafiya. Waziri  na fada zaune shi da mutanan sa labari ya riske shi cewa gashi can an futo da Sarki! Zasu tafi Saudi'a sai ya kece da dariya yana fadin "Duk inda zasuje suje su dawo shida ya taka doran kasa da k'afafunshi to sai dai idan lahira yaje" mutanan sa suka ce "Wannan haka yake,takawar ka lafiya gyara kintsi dai!!!!!! Wani mugun dad'i ya rufe shi, jin yadda suke faman zuba masa kirari,abunda yake mutuwar so kenan a rayuwarsa.

 

 

Azima da Halisa, na tsaye sai gani sukayi kawai Mama ta rik'o hannun Balaraba ta zaunar da ita bayan mota kusa da Sarki! Ta maida kofa ta rufe, fad'i take." Ubangiji Allah ya bada nasara a rayuwa Yarona ka dawo da k'afafun ka.' Sarki! Yayi mamakin abunda Mama tayi,sam ba son daya daga cikinsu ta bishi saboda ya San rigima ce, yana kallon b'acin rai da zallahr kishi a idon Halisa, amma bai san manufar Mamanshi ba, Wambai da Galadima da Liman suka shiga motar su,suna dagawa Mama hannu, Shahid da Shatima motar me girma governor suka shiga, shi kuma tashi daga shi sai Balaraba sai direba, d'ayan bayan d'aya suka futa daga gidan da niyyar zuwa eirport. Addu'a sosai Mama takeyi, har suka futa, ta dawo da hankalinta Kansu Halisa kamar su d'aura hannu aka don bakin ciki, nan ta basu umarnin ko wacce ta koma shashen ta.

 

 

**********

 

Bayan awa biyu da tafiyar su.

 

B'angaran Waziri Zayyanu, Khalifa ne da Ansar, Suna zaune a falo suna ciye-ciye sai dariya sukeyi da alama suna jin dad'i saboda yanda Babansu ya sakar musu kudi Sosai saboda duk cikin 'yayansa yafi son su, sune zai ce suyi Abu kai tsaye suyi babu gar dama, Khalida ya kalli d'an uwansa yana fadin"Kai wai ya kabarin wancan gurgun ne,? Wallahi naso ma mutuwa yayi shege Dan asara,wato shi da yana zaune yana jiran mulki, kakansa yayi ubansa yayi Dan rashin imani,shine yake so yayi shima, ko an fada masa muma ba 'yan sarautar bane oho,ai yanzu kuma mulki ya dawo hannunmu Dan uwarsa sai dai yaga anayi sai mun kashe shi da bakin cikin mu." Ansar yace." Kaii manta da wannan, sai muga da wace k'afar zai hau kujerar mulki ballantana ya zauna." Hahahahahaha!!suka kwashe da dariya, kamar da wasa sai Khalifa ya k'ware ya fara tari!! Ansar ya mik'a masa ruwa ya kurb'a tarin yak'i tsayawa idonsa yayi jajazur har yana k'okarin fad'uwa daga kujerar ya damk'e k'irjinsa sosai yana ta tari idanunsa duk sun futo waje, Hajiya Kattime ta futo daga dakin taga abunda yake faruwa da sauri ta k'arasa gurin tana salati, har ya fado daga kan kujerar ya kifa sosai ya galabaita, Ansar duk ya gigice' yan uwansa dasu kenan sunyi tsaye a kanshi, ji sukayi kamar anyi ruwa an d'auke, da saurin Al'amin ya d'ago shi, sai yaga wuyansa ya karye ya tafi luuuuuu ya fad'i kasa, salati suka saka, Hajiya Kattine tace." Innalillahi, waina'ilahi raji'un.! Khalifana babana ka mutu ka barni babana kabi Dan uwan ka Moddibo, ya Allah ya jikanka Khalifa na." Tana share hawaye take fadin Wannan maganar, aikuwa gida ya rude da kuka sosai, mutuwar ta girgiza su mussaman dai Ansar da suke, hira dashi, da sauri Al'amin ya nufi fada domin ya sanar da mahaifin su halin da ake ciki.

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

       _*GIMBIYA BALARABA*_

              đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

~*NA*~

_BINTA UMAR ABBALE_

*BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

*MARUBUCIYAR*

 

 

```NANA KHADIJA```

```YARO DA KUDI```

```GIMBIYA BALARABA```

```TSANTSAR BUTULCI```

```LADIDI K'WADAGA```

 

 

 

 

_*ZAMANI WRITES ASSOCIATONđŸ€đŸ»*_

 

_____________________

```We are here to educate motivate and entertain aur reades```

_______________________

     

  

 

 

 

 

*JAN KUNNE*

 

_*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_

 

 

 

 

 

*DEDICATED*

     ~*TO*~

*RAHAMA ALIYU*

   ~*ABUJA*~

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_

 

 

 

 

 

*🅿116*

 

 

 

Waziri na zaune a fada sai bada umarni yake cike da izza! magana ma da k'yar yake yin ta,wai shi dole ga Sarki, Al'amin ya shigo cikin tashin hankali ya zube gaban mahaifinsa ya fara Sanar dashi halin da ake ciki. Hankali a tashe ya mik'e fadawansa suka rufa masa baya,kwata-kwata ya manta da alkwarinsu da Mak'asudu, yana isa ya Tarar dasu hankali a tashe mussaman Hajiya Kattime da ta kusa zautuwa domin. Bayan tafiyar Al'amin shima Ansar d'in fad'uwa kawai suka ga yayi yana rike cikin sa kafin su ankara sukaga jini na b'ulb'ulowa ta bakinsa da hancin sa,gaba ki daya sun rasa wanda taimako zasuyi masa, Khalifa kuwa tuni Allah yayi masa rasuwa kafin Waziri ya k'araso mutuwar Ansar din ta afuku a gabansa, zaman dirshan yayi a gaban gawawwakin 'yayansa ya sunkuyar da kansa kasa yana kukan zuci,kamar daga sama yaji wata murya kamar ta Mak'asudu yana fad'in." Kar ka manta da alk'awari mu dakai,yau na cika shi shiyasa ma na shanye jinin 'yayan ka saka fi so da kauna."!!! Zumbur!!! Ya mik'e tsaye idonsa yayi jazur ya kalli sauran 'yayan nasa yace." A shirya yi musu suttura." Yana gama fad'in haka ya shige asirtaccan d'akinsa, Hajiya Kattime ta bishi da kallo cikin mamaki ganin bai damu ba, yanzu tafara zargin sa, Sosai take zargin wannan dakin da ya kulle ya hana kowa shiga,dole tafara bunkice a kansa.

 

 

Kafin kace kwabo mutuwar su Khalifa ta watsu a gida da waje, su Sarki! Ma labari ya same su,sunyi mamaki sosai daga bisani Sarki yace." Ba'a mamaki da ikon Allah, Galadima da me girma governor ne suka dunga tur da halayyan Waziri domin su sun San abunda yake faruwa saboda mulki babu abunda Waziri bazai yi ba.

 

Mama ce ta dinga d'ebe wa Kattime kewa har akayi sadakar uku kowa ya watse Hajiya Kattime ta kudiri aniyar bibbiyar mijinta da abunda yake aikatawa tana fatan asirinsa ya tuno a duniya shine sanadin mutuwar 'yayan ta uku, tayi da tasani data aure shi. Saboda mugun bakin halinsa.

 

Waziri kuwa yana shiga d'akin sirrinsa ya kulle da mukulli ya zube bakin kofar yana warware nadin dake kansa, gumi na tashin hankali kawai takeyi wasu zafaffan hawaye ne suka fara zubo masa, lokaci guda yayi rashin 'ya'yan shi biyu lallai Mak'asudu ya shammace shi, kuka yayi sosai daga bisani ya miki ya maida rawaninsa ya futa daga dakin, yanzu yasan kuma Mak'asudu baya binsa wani bashi tunda ya biya shi. *Niko nace haka kake gani Waziri aljan ba'a iya masa sai Allah*

 

 

*********

 

Uwa! na zaune tsakar gida ta zabga uban tagumi tunanin rayuwa kawai take, duk ta rame ta ko jale,Shamsiyya ce ta futo daga ban daki hannunta rike da buta cikin ta ya tsofa sosai duk ta kumbura, Sadiya matar Kawu na hangota tace." Ki dinga tafiya a a hankali da gurin nan kar ki fad'i saboda santsi." Shamsiyya ta d'aga kanta cikin tausayin kanta taje kusa da uwarta ta zauna da k'yar.Uwa! Ta sauke ajiyar zuciya tace." Shikkenan yanzu kamar yanda na fidda rai da Iro haka zan hak'ura da Mabaruka, anyi neman duniya ba'aganta ba." Shamsiyya tace." Jiya fa Walidi yake ce miki ya samu labari gurin wani abokin kasuwanci sa wai ya ganta cab portarcouht ita da saurayin ta." Uwa! ta share hawaye tana fadin ." Allah ya dawo da ita gida ubangiji Allah ka shirye ta kasa ta gane duniya ba mattabata bace." Cikin sanyi murya Shamsiyya tace." Ameen" Lantana ta futo daga d'akinta ta zauna suna Tisa maganar,Lantana Duk tayi sanyi,kusan kullum tana daki tana Jan carbi sallar walha bata wuce ta, ta koma ga Allah sosai domin mutuwar Sallau ta gigirgaza ta, yanzu basa cikin k'angin rashi Walidi na tsaye a Kansu basu da yunwa,kuma daga gidan Sarauta Mama nayi musu aike duk wata.

 

 

 

**********

Alhmdullahi yau satin su guda A k'asa me tsarki, sauk'i ya soma zuwa da izinin ubangiji duk Wannan kumburi da k'afafun sukayi ya sab'e kwanan su biyu da zuwa aka fara yi masa amfani da magunguna na islaminc masu d'auke da ayoyin Allah a ciki, yasha a shafa k'afafun nasa, dasu yanzu yana iya motsa su, amma bai iya taka su,yayi wata kib'a sosai saboda samun kulawa daga my life d'in shi Balaraba soyayyar sa yake sha sosai idan yaga babu idonsu su Shatima, dake su in Safiya tayi suna tafiya harami su yini sai yamma suke dawo wa, wannan damar da ya samu ya dinga more amarcin sa, Balaraba ta saki jiki dashi sosai tana bashi kulawa, shi kuma sai yayi tayi mata shagwaba yana lanjarewa, da dare yayi zata ga ya watsake yana Mata kallon love, tun bata gane wayon sa ba har ta gane shi, sai dai kawai tayi masa dariya, suna samun waya sosai daga gurin Mama, taji dad'i da taji jiki yayi kyau, Balaraba ta sha addu'a a gurina.

 

 

 

Daga Wanka ta futo daure da towol cinyoyinta duk a waje ga kanta sai d'igar ruwa yake, yana zaune gefen gado daga shi sai k'aramin wando,  da alama angama love ne, bude mata hannuwan sa yayi wai ta zo. A hankali ta k'arasa amma me makon ta shiga jikinsa kamar yadda ya buk'ata sai ta zauna gefan gadon tana ya mutse fuska, Ka fad'ar ta ya kamo ya Dan matsa kad'an k'asa-k'asa yace." Menene hummm."?  Lumshe ido tayi tace." Bana jin dadin. Jikina yanzu na fara zargin kaina saboda banga period d'in ba, wannan lokacin nake yi shiru bai zo ba."

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

       _*GIMBIYA BALARABA*_

              đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

~*NA*~

_BINTA UMAR ABBALE_

*BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

*MARUBUCIYAR*

 

 

```NANA KHADIJA```

```YARO DA KUDI```

```GIMBIYA BALARABA```

```TSANTSAR BUTULCI```

```LADIDI K'WADAGA```

 

 

 

 

_*ZAMANI WRITES ASSOCIATONđŸ€đŸ»*_

 

_____________________

```We are here to educate motivate and entertain aur reades```

_______________________

     

  

 

 

 

 

*JAN KUNNE*

 

_*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_

 

 

 

 

 

*DEDICATED*

     ~*TO*~

*RAHAMA ALIYU*

   ~*ABUJA*~

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿113*

 

 

 

 Hannunsa ya sanya ya rungumo k'ugunta fuskarsa d'auke da wani kyakykyawan murmushi yace." Lallai Allah ya amsa min addu'a ta da wuri Ubangiji Allah yasa ciki ne dake, idan hakane zan yi farin ciki sosai da sosai." Sunkuyar da kanta tayi tana jin kunyar sa a hankali tace." Gaskiya ina zargin haka domin ban tab'a batan wata ba,ko lokaci nayi nake amma wannan kwana hud'u akai gaskiya da akwai alamun tambaya." Cikin farin ciki yace." Yanzu nan zan auna ki domin in tabbatar da hakan." Towol din yake k'okarin cirewa ta rike hannunsa cike da tsoro! Kallon ta yayi yana lumshe ido,tace." Wai kai baka gajiya ne."? Kanne mata idonsa yayi yace." Kece ai kamar zuma kike sam bakya gimsa ta." Nauyin maganar sa taji yasa ya juya baya tana girgiza kai. Ya rungume ta k'am! Yana sakin ajiyar zuciya yace." Ki barni in gaisa da babyna." Shiru tayi, sai ya zura hannunsa yana shafo cikin tamkar Wanda yake mata tafiyar tsutsa ya dinga shafa mata mara lumshe idonta tayi tana sauke ajiyar zuciya, ni dai nan na futo na barsu.

 

 

*******

Hajiya Kattime ce zaune a falo tana jiran futowar mijinta, sai gashi ya futo cikin shirin zaman fada, tace."Allah ya taimake ka ina da magana da kai." A k'asaince yace." Ina sauraron ki,zan shiga fada ne." Zama ta gyara tana fuskantar sa sosai tace." Dama tambaya nake so in maka." Yace." Ina sauraron ki."  "Me yasa da yaran ka suka a mutu baka nuna damuwar ka ba? Kuma me yasa baka so a shiga  wancan dakin na kulle."? A hasale! Yace." Ke saurara min da maganar banza haka." Shiru Kattime tayi ya cigaba da cewa." Idan mala'ikan d'aukar rai yazo kan 'yayana sai in hanashi kan wane dalili zan tashi hankalina zaki mutu zan mutu zamuje inda sukaje,saboda haka babu dalili da zai sa in tada hankalina, bayan wannan kuma kina maganar wancan dakin dake kulle dakin sirri na ne,ko da wasa kar ki kuskura ki kai kanki gurin zan iya sakin ki a kan hakan." Kattime ta saki baki tana kallonsa cike da mamaki.

Futa yayi ya bar ta da tunani.

 

 

*********

Mabaruka ne da saurin ta cikin mota zasu dawo gida, duk suna cikin maye, Alhaji Ashiru sai fafara gudu yake, ba tare da bin ka'idar tuki ba, wata k'atuwar mota ta buge su,suka gangara cikin daji,ihu!! Mabaruka take kurmawa tana k'okarin futowa ta fado kasa motar ta bi ta kan kafafunta, ta cillata can gefe, motar ta cigaba da katantanwa a gurin, tayi raga-raga Alhaji Saminu kansa ya fashe take ya amsa kiran ubangiji ita kuma Mabaruka ta suma.

 

 

 ********

Hajiya Kattime na  zaune a inda take tun bayan futar mijin nata take tunani kan yadda zata yaudare shi har ta samu nasarar shiga dakin sirrin shi, murmushi tayi lokacin da ta tuno abunda zatayi masa, gyad'a kai tayi a fili tace." Insha Allah sai asirin ka ya tuno mutukar ba abun kirki kake shukawa ba."

 

 

'Yan a gaji ne suka kawo dauki gurin, ba tare da b'ata lokaci ba,a ka dauki Mabaruka a kaita asibiti ,shi kuma Alhaji Saminu cikin motar suka duba suka ga katin sa da shaidar garin da yake, nan suka saka gawar sa a mota domin su kaishi dangin sa.

 

 

*******

Ranar Sarki! Da Balaraba sun sha soyayya sosai ji suke tamkar su kadai suke rayuwa a duniyar Balaraba har fargaba take su koma gida, in ta tuno da masifaffan kishiyoyinta wanda ko anan ma sun dunga damunsa da kiran waya babu dare babu rana.

 

Sai k'arfe shida shu Shahid suka shigo gidan,dama me girma governor ya koma lokacin da yayi kwana uku, nan sukayi sallahr magariba, suka zauna suna cin abunci suna hira, Shatima ya futo da magunguna ya mik'a masa, b'ata fuska yayi yak'i karb'a.Balaraba na kallonsa, ta kalli Shatima a hankali tace." Ka bari zan bashi in anjima har na shafarwar ma." Shahid yace." Hakan yayi ke in kika bashi sai yafi karb'a mu kam kullum sai ya bamu wahala." Murmushi tayi kawai. Gyaran murya yayi yace. " Na fa gaji da zaman gidan nan, Dole gobe nima na futa in kusanta kaina ga Allah don haka sai Ku shirya futa dani." Shahid yace." Allah ya kaimu goben muna fatan a sanya mu cikin addu'a."  Yace." Jikina na bani insha Allahu da k'afafu na zan koma gida." Shatima yace." Idan Allah ya yarda kuwa haka muke so." Nan suka cigaba da hira suna kallo, sai k'arfe goma da rabi sannan sukayi sallama kowa ya shige makwancin sa. Balaraba ce ta tura shi bedrom ta d'auko masa kayan bacci, ta taimaka masa ya sa, ta sanya nata sukayi kwanciyar su, cikin so da kaunar junan su.

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

       _*GIMBIYA BALARABA*_

              đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

~*NA*~

_BINTA UMAR ABBALE_

*BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

*MARUBUCIYAR*

 

 

```NANA KHADIJA```

```YARO DA KUDI```

```GIMBIYA BALARABA```

```TSANTSAR BUTULCI```

```LADIDI K'WADAGA```

 

 

 

 

_*ZAMANI WRITES ASSOCIATONđŸ€đŸ»*_

 

_____________________

```We are here to educate motivate and entertain aur reades```

_______________________

     

  

 

 

 

 

*JAN KUNNE*

 

_*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_

 

 

 

 

 

*DEDICATED*

     ~*TO*~

*RAHAMA ALIYU*

   ~*ABUJA*~

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_

 

 

 

 

*🅿114*

 

 

 

 To bayan likitoci sun gama binkicen su a kan Mabaruka nan suka yanke shawarar yanke mata k'afafu domin babu wani sauran dubara da ta rage k'afafun Mabaruka duk sun karye karaya mafi muni! Wanda ko dori akayi baza su k'ara amfani ba, Mabaruka tana ji tana gani aka yanke mata k'afafu, ta futa daga cikin hayyacin ta saboda azaba fatan mutuwar ta kawai take.

 

***********

 

Ranar Juma'a da misalin k'arfe d'aya shaura na rana, Waziri ya shigo cikin gidan, cikin sauri ya bude dakin sirrin shi ya shiga tare da kullewa, Hajiya Kattime na zaune a falo tana kallonsa, ya shiga ya fi minti goma a ciki sai gashi ya futo da sauri, yaja kofar tare da murza mata mukulli ya cire ya futa ba tare da ya kalli inda take ba. Kamar wacce aka bawa umarni ta mike Zumbur! Kofar dakin taje tana murza wa, abun mamaki kofar ta bude, bata tsaya tunanin komai ba ta afka cikin dakin, abunda ta gani yayi mutukar gigita mata tunani,nan take sai kanta ya fara juyawa ta zube a gurin a sume.!

 

 

 

*******

Tsaf! Ta shirya shi cikin wani parkinstan irin na maza sunyi masa kyau sosai kanshi sanye da hula irin ta Larabawa tsaf idan ya shiga cikinsu zai saje, turare ta d'auko tana fesa masa, ya rike hannunta yana murzawa, murmushi tayi tace." Ka bari in fesa maka fa kar Ku makara gasu Shatima na jiran ka."

 

A kasalance yace." Kece duk kin gajiyar dani jikina duk ciwo yake." Hararsa tayi kad'an tace." Kana da Neman magana ko." Murmushi yayi tare da lakuce mata hanci yace." Gaskiya ne ai." While chair d'in ta kama tana k'okarin tura shi domin ta futa dashi farlo, yace." Bari ki gani da izinin Allah yanzu zan taka k'afafuna." Balaraba ta matsa gefe tana kallon ikon Allah, ya yunkura bakinsa d'auke da Addu'a sai gashi tsaye da kafafunsa, cikin mutukar farin ciki ta furta "Alhamdullahi ala kullu halin." Shima cikin farin ciki yace." Allah ne abun godiya." K'okarin futa take yi ya rike hannunta da sauri yana fad'in " INA zakije kece 'yar jagora ta fa." Cike da farin ciki tace." Wallahi duk na rasa ya zanyi saboda farin ciki,hak'ika ubangiji naji rokan bawansa ne." Yace." Hakane mutukar bawa zai mik'a lamarin shi ga ubangijinsa to babu shakka dukanin Matsalar sa ta kare." Rungume shi tayi sosai tana sauke ajiyar zuciya, cire ta yayi daga jikinsa yana Dan murmushi yace." In kika karya min alwala fa , zamuje massalaci yanzu in mun dawo kiyi min tanadi me kyau." Ta sinne kanta kafadar shi suka futa a haka

 

Su Shahid na zaune suna jiran futowar sa,kawai suka ganshi ya futo da k'afafun sa,tare suka mike tsaye cikin mamaki ! Shatima yace." Alhmdullahi Alhmdullahi ala kulli halin, yaushe ka mike ka fara tafiya." Suka fada a tare. Balaraba tace." Yanzu ne kamar da wasa wallahi ya mike." Shahid ya zube gurin yana sujjadar godiya ga Allah,shiko Shatima waya ya futo da ita zai kira mutan gida, Yace." Ka bari tukkuna muje mu dawo ko meye sai ya biyo baya in ka kira mutane yanzu zasu hana mu ibada." Shahid yace." Hakane bari muje mu dawo kawai, tare suka futa har da Balaraba tana sanye da dogun hijabinta fari tass dashi mijinta ya rike mata hannu suka fara tayi,dake gidan da suke bashi da nisa da harami da kafa suka tafi,

Bayan an idar da sallahr jama'a suka zauna massalaci suna add'a tare da karatun alkur'ani me girma.

 

 

**********

Waziri Zayyanu kuwa yana futa fadawansa suka rufa masa baya tare da kareshi da lema saboda rana sai baza babbar riga sukeyi, kamar daga sama yaji wani irin ihu!! A kunnensa ,zabura! Yayi yana kalle-kalle, wani ihun yaji Wanda yafi na d'azu, can yaji gurnanin Mak'asudu sama-sama yaji muryar shi yana fad'in "Aiki ya lalaceee!!!!! Ka janyo min ka janyowa kanka, ihuuuuuuuu!! Shikadai yake jin wannan ihu,ya tsaya yana dira-dira Wani bafade  yace." Gyara kimtsi daiiii!!! Allah yaja zamaninka ko kayi mantuwa ne." Waziri ya girgiza masa kai a mutukar tsorace!! Yake, tuni jikinsa ya fara tsiyayar da gumi! Ya juya zai goma gida, k'afafun sa suka sark'e suka lauye suka kwalmad'e ba tare da bata lokaci ba ya zube a gurin, yanda k'afafun sa sukayi haka hannuwan sa sukayi, bakinsa ya kar kace idonsa ya wurkile, hallitunsa suka sauya gaba ki daya. Fadawansa suka saka salati tare da d'aukar sa domin kai shi cikin gida.

 

 

Ko da suka shiga dashi cikin gidan suka tarar da tashin hankali domin sauran 'yayan ne tsaye kan Mahaifiyar su suna k'okarin ceto rayuwar ta.

 

 

 

*********

 

Shamsiyya ce cikin kuryan d'akinsa tunda ta tashi da safe take jin ciwon ciki tayi shiru bata fada ba,sai da taga wani abu me kama da jini yana zubawa daga gabanta shine fa ta kira mahaifiyar ta ta fada mata, Uwa ta kira Lantana hankali a tashe! Tasan haihuwa CE,nan suka fara bata taimako ganin yadda take yunk'urin da alama haihuwar a kusa take.

 

********

 

Tashin hankalin da iyalin Waziri suka shiga ba a fad'ar sa, ganin yadda hallitun ubansu ya sauya ya munana ya jirkita sai kace ba mutum ba, tuni wasu suka fara kuka mussaman mata, da k'yar aka samu Kattime ta dawo hayyacin ta, ta kallin mijinata da ya koma kamar tsumma! Lokaci guda ubangiji ya tagayarashi  tace." Alhamdullahi Allah na gode maka da ya mayar da kai haka hak'ika mutuwar  ita tafi amfani da RAYUWAR ka, ka cucu ni ka cuci 'yayanka saboda son zuciya irin taka, ka kashe rai Wanda bamu San adadi ba, hak'ika nayi nadamar auranka bana fatan ko a lahira ubangiji ya had'a fuskoinmu"

Tana gama maganar ta fashe da kuka me cin rai!

Nan fa fadawan da suka kawo shi suka dinga silalewa suna futa cike da kunya.

 

********

Cikin hukuncin ubangiji Shamsiyya ta haihu lafiya inda ta haifi d'anta namiji yaro lafiyyaye dashi me kama da ubansa sak!!! Kuka sosai take uwa na tayata wai yau itace zata Goya Dan shege rayuwa kenan, haka Lantana ta dafa ruwan zafi tayiwa jinjiri Wanka tas ta shirya shi cikin kaya,ta goyashi tana daure zuciyarta itama amma kukan zuciya kam kullum sai tayi shi.

 

 

 

******

To ranar bayan sun dawo daga massalaci Shatima ya kira wayar mama ya Sanar mata halin da ake ciki, murna sosai Mama tayi ta dinga godewa Allah da ya kawo wa yaron ta sauk'i cikin lokaci kankani lallai duk Wanda ya dogara ga Allah yayi dace duniya da lahira

 

Me girma governor kuwa yana ganin kamar yafi kowa farin ciki, don haka nan take yasa mutanan sa afara shirye-shiryen nad'i domin a cewarsa me Martaba Sarki!Almansur na biyu na dawowa za'a fara shagalin nadin sarauta, aikuwa gari ya d'auka da murna,dama labarin halin da Waziri yake ciki ya karad'e ko ina cike da waje harda wajan gari ma kowa yaji wasu na turr dashi wasu kuma na tausaya masa halin da yake ciki.

 

 

 

Yau Litinin Wanda yayi dai-dai da sati uku kenan da tafiyar su saudi'a a yau din ne kuma suke d'aura niyyar dawowa gida cikin farin ciki da samun nasara, Balaraba tayi wani fresh da ita kyallin ciki duk ya bayyana a tattare da ita, ta kara cika da kwarjini sosai duk Wanda yasan mace me ciki ya kalleta a lokacin sai ya gane, shiko uban tafiyar tamkar ba Wanda yaje jinya ba ya had'a wata kiba fatarshi tayi sumul-sumul sai shek'i take,shida Balaraba har nasara Wanda yafi wani kyau da gogewa

 

 

******

 

Can gida kuwa ya hautsine da shagali gami da kid'e-kid'e da busa ko INA ka kalla jama'a ne suke kai kawo  kowa yana cike da farin cikin dawowar me Martaba cikin aminci da koshin lafiya.

 

 

Halisa da Azima sai kintse-kintse sukeyi kowacce tana k'okarin tayi abunda zata fi 'yar uwarta dashi, Azima kokari kawai take tana ji ajikinta kamar asirinta zai tuno tunda dai gashi Waziri yana cikin wani hali shine dama ya yaudare ta, gashi yanzu tana mutukar son auranta addu'a kawai take Allah ya rufa mata asiri.

 

 

 

 

Fili jirgi a cike da a yarin gidan sarauta tare da ayarin me girma governor suna jiran saukar jirgin su, Sha biyu dai-dai jirgi ya sauka Shahid da Shatima ne a gaba, sai Sarki! Da BALARABA a bayansu ya rungomo ta jikinsa, tuni gadawan gurin suka fara zubewa suna kwasar gaisuwa, cike da kunya take k'okarin kwace jikinta ya ki s'akinta,cikin walwala suke gaisa da jama'arshi su Governor da Galadima da sauransu mota ta mussaman aka bude masa ya shiga ya zauna Balaraba ta shiga direba ya shiga domin su Kansu su Shahid wata motar daban suka shiga, direba yaja su suka nufi gida

 

*****

Tsabar hayaniya jama'a tasa kansa ya fara ciwo nan take yace. da Babu direba su huce can shashen Maman shi, amma duk da haka jama'a bin motar suke suna banbadan ci tare da roko da kid'a kowa na fadin albarka cin bakinsa, Sarki ya futo cikin walwala ya dinga daga musu hannu ya rike hannun matar shi tamm!!fadawa suka dunga sanya duka da bulala da k'yar dai ya samu ya tattatka suka shige gurin Maman shi, wacce take tsaye gurin wani k'aton window tana ganin abunda yake faruwa, ganin yaron ta yayi kiba da lafiya gashi kamar ba Wanda ya tafi jinya ba,yasa ta godewa Allah sosai yana shigowa ya rungume ta, Balaraba ta koma gefe tana murmushi, Mama ta rik'o hannunta tana fadin"Zonan yarinyar ta hak'ika ke alkairi ce a tare damu kin zama Wani jigo na rayuwar mu, Balaraba ina jinki a cikin jinana tamkar nice na haifeki ubangiji Allah ya sauke ki lafiya." Balaraba tayi saurin sunkuyar da kanta cike da kunya, lallaima ashe sai da ya fadawa Mama halin da take ciki" Mama ta cigaba da cewa." Duk irin dawainiyar da kikayi da mijinki ina da labari, babu abunda zan iya saka miki dashi sai dai addu'a ladan ki na gurin Allah domin kinyi ibada kin bautatawa mijinki ubangiji Allah ya jikan iyayaenki yayi miki albarka a rayuwar ki." Balaraba ta sunkuyar da kai kasa tana amsawa da amin kwalla duk ta cika mata ido.

Sadiya da Usuman ne tsaye can gefe suna kallonsu Mama ta kirasu tace." Kuzo ga aunty ta dawo,. " BALARABA ta daga Kai tana kallon yaran sunyi kyau sosai sun murje sun kara girma Sosai Mama take kula dasu, makaranta suke zuwa me tsada su saka suttura masu tsada babu. Shakka babu abunda zatace da Mama Fulani bisa alkairin ta a garesu.

 

Nan b'angaran Mama suka biyo shi Halisa da Azima kowacce tana wace wannan gurin ado gwal sai walwali yake a jikinsu, Balaraba ta basu gurin ganin yadda sukeyi I junansu tamkar su bangaji juna,duk wannan k'awancan babu shi, kowacce ta kwaci kanta, Halisa duk ta kanainaye shi, a cewar ta ai girkin ta ne yau don haka duk su matsa gefe, shidai kawai kallonsu yake, yana tunanin halin da zai shiga zai kwana ba tare da gimbiyar sa ba, ya Riga ya saba da dumin jikinta da shagwaba shi da take sosai da soayyarsu duk dare, to itama b'angaran ta hakan take duk tayi sanyi tana tunanin ta yaya zatayi bacci bataji kanta a kirjinsa ba yana mata wassanin kamar yanda suka saba a saud'ia.

 

 

 

 

 

*Daga wannan pege din sai na k'arshe Ku zauna cikin shiri*❤❤❤❤

đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

       _*GIMBIYA BALARABA*_

              đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»

 

 

 

 

 

~*NA*~

_BINTA UMAR ABBALE_

*BINTUBATULA👄*

 

 

 

 

 

*MARUBUCIYAR*

 

 

```NANA KHADIJA```

```YARO DA KUDI```

```GIMBIYA BALARABA```

```TSANTSAR BUTULCI```

```LADIDI K'WADAGA```

 

 

 

 

_*ZAMANI WRITES ASSOCIATONđŸ€đŸ»*_

 

_____________________

```We are here to educate motivate and entertain aur reades```

_______________________

     

  

 

 

 

 

*JAN KUNNE*

 

_*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_

 

 

 

 

 

*DEDICATED*

     ~*TO*~

*RAHAMA ALIYU*

   ~*ABUJA*~

 

 

 

 

 

 

_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_

 

 

 

 

 

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

 

 

*🅿115*

 

 

 

 

Da k'yar ya samu ya kufce daga hannun Halisa ya gudu part d'insa inda su Shahid suke zaman jiransa,nan kama kafin ya tafi sai ya gargade su kar wacce ta bishi, saboda hutawa zaiyi Balaraba cikin zuciyarta tace." Dama ni ko ka neme ni ba zuwa zanyi ba, zama zanyi inyi jinyar zuciyata da zatayi kwana hudu ba tare da Kai ba.

 

Nan gurin Mama suka zauna dukaninsu, kallon Balaraba sukeyi a fakaice ganin yanda tayi Wani mugun kyau, tayar ta kamar ka tab'a jini ya futo ta kara cika da kwarjini, wani kyashi da bakin ciki ya damu zuciyarsu babu abunda ya kara daga musu hankali sai yanda Mama take kula da ita, tana kaf-kaf da ita da tayi motsi zatace "Ya akayi in dai akwai abunda kike sha'awar ci kiyi magana akawo miki." Girgikai kai kurum take cike da kunyar Maman, Halisa ta kalli Mama da jiki a sanyaye tace." Bata da lafiya ne."? Murmushi tayi tace." Cutar ta arziki ce ai insha Allahu kun kusa samun baby." Ita da Azima ban San wanda yafi wani shiga rud'u da tashin hankali ba, neman miyau tayi ta rasa abakin ta, idonta ya ciko da ruwan hawaye, Balaraba na da ciki,cikin kuma na masoyinta Wanda taci burin ita zata fara Haifa masa 'yaya, to wai abun tambaya anan, shine mutumin da ya tafi Neman lafiya ta yaya har ya iya kwanciyar aure babban abun tambaya yaya akai shi da bashi da kafa ya sarrafa kansa.

 

*Dariya nayi nace lallai Halisa kin cika hamaguwa😄*

 

 

To tunani da take shi Azima take duk sun shiga tashin hankali Lallai BALARABA tayi musu fintinkau tayi musu zarra,yanzu meye abunyi? Halisa take tambayar zuciyar ta, wani b'angare na zuciyar tata Yace mata,kawai yau kema ki matsa masa yayi miki ciki ki haihu, aikuwa ta yarda da wannan shawarar ta zuciyar tata.

 

*******

Walidi ne ya siyowa Shamsiyya atamfa guda biyu dinkakkau ya siyo rago ranar suna yaro yaci sunan mahaifin su,wato Sallau, Salihu kenan, a ranar ne kuma labarin Mabaruka ya same su, ta hanyar k'afafun yada labarai, an nuno ta kwance gadon asibiti babu k'afafu, ana cigiyar danginta harda Lamar waya aka kawo wa Walidi aikuwa atake ya kira wayar yayi musu kwantan inda suke, ba tare da bata lokaci ba aka sako Mabaruka a mota tare da keken guragunta tana kuka tana da tasani abunda tayi,  Ranar kwana sukai kuka Iya da Sadiya matar Maman suna ta tausar zuciyar su.

 

 

******

 

Ana kiran idar da sallahr Isha'i Halisa ta dura a part din Sarki! Cikin shirin ko ta kwana, tayi kwalliya iya kwalliya, sama ta hau domin baya farlo,shima tunda su Shahid suka tafi ya hau sama domin ya huta, bude kofar tayi ta shiga bakinta d'auke da sallama ya amsa babu yabo babu fallasa, zama tayi kusa dashi, tana sak'e-sak'en maganar da zata yi masa, yace." Halisa mun same Ku lafiya ko."? Cikin dauriya tace." Lafiya lau Yallab'ai." Shiru yana sauraron ta yasan da akwai magana a bakinta, yace." Wane tanadi kikayi min."? Yake tayi kawai tace." Ni wane tanadi zanyi maka,nice ma Nazo kayi min tanada kamar yanda kayiwa Balaraba." Bai gane hausarta ba yace." Wane tanadi nayi Mata." Inda-inda ta fara yace." Ke nake saurare."  Tace.'Nima ciki nake so kamun.' Cikin mamaki yake kallonta. Yace." Ciki Allah ne ke ba dashi ba mutum ba, sai kice ni in zama silar shi." Kuka ya fara yi sosai harda sharb'ar majina." Yace." Meye abun kuka, kuma." Tace." Ina jin takaicin yadda wata zata fara haihuwa dakai bani ba." Tsaki yaja yana girgiza kai yace." Matsalata dake rashin wayo da dubara ni dake da balaraba babu Wanda ya Isa ya hana Allah ikonsa akanmu Balaraba zata fara haihuwa dani haka Allah ya tsara.'' Kuka sosai takeyi takasa cewa komai ta kwanta kan bed din tana Jan ajiyar zuciya, tausayinta ne ya kamashi,ya kashe futal dakin tare da aje k'aramin littafin hannunsa ya rungume ta yana fada mata daddadan kalamai, nan labari ya sha BABBAN, na futo na barsu ina fatan samun nasara da 'yaya masu albarka.

 

To sarki! Ya biya Halisa domin dai jiya ya kashe ta da soyayyar sa mai wahalar mantawa lokaci kad'an ta manta da damuwar ta,ta cigaba da kyautatata masa.

 

 

******

Tsito ne ya dura a gidan kamar tsohon mahaukaci ya nufi b'angaran Hajiya Kulu me dakin kudu, yazo domin ya karb'i sauran kud'in aikin sa. Nan ya samu babu. Kowa a shashen nata sai hadiman ta, suka ce masa satin ta biyu bata gida,hakanan yaranta suma ba kullum suke kwana a gida ba, haka ya futo yana tunanin ina zashi,domin yanzu duk aljanun da suke kanshi sun dare sun gudu baya iya yin aikin komai watarana ma da yunwa yake kwana, ya tabbatar da cewa abunda suka aikata da Waziri ne ta shafe shi, zuciyarsa ta bashi shawarar kawai yaje ya nemi afuwar iyalin Waziri ko Allah zai sa ya gama da duniya lafiya, sannan suyi masa iso gurin Sarki! Almansur domin ya nemi gafarar sa Halin da yaga Waziri a ciki ya bashi tsoro bakinsa ya dinga rawa ya rasa abun cewa,Hajiya Kattime tace." Bawan Allah daga ina haka domin banga ne ka ba."?

 

Tsito ya fashe da kuka yana fad'in." Yanzu haka Waziri ya koma oo ni Tsito." Kattime tace." Kayi min bayani mana, yace." Nine Tsito wanda nayi ma mijin ki aiki duk Dan yayi mulki nan ya warware mata duk abunda ya faru, yaran ta suka taso domin suyi masa duka ta hanasu, tace." Ku kyale shi shima zai ga karshen sa, nan Tsito yayi dasu su masa iso gurin me Martaba Kattime ta hana, haka suka tarkatashi suka futa dashi fadawa suka tasa keyarsa har waje, yana futa ya kasa gane hanya kawai sai ya dauki wata haya ta daban yana tafiya yana tsayawa bola-bola yana tsince-tsince duk ledar da ya gani sai ya d'auka ya sa a bakinsa yana taunawa.

 

*Ubangiji Allah kasa muyi kyakyawan  k'arshe*

 

 

*******

Kwana biyu da Halisa tayi ta samu kulawa sosai a gurinsa ganin yanda ta kwantar masa da kai tana kula dashi komai sai tace idan BALARABA ta haihu za'ayi kaza da kaza, hakan ne yasa ya Sakar mata jiki suka sha soyayya.

 

 

Azima ya ta karb'i girki sai girin gidishi take tasha magunguna mata kamar banza mararta sai kullewa take jira kawai take dare yayi ta shiga part din Yallab'ai a kashe boss.

 

 

*****

Hajiya Kattime ce tayi sallama ta shiga a nutsue Mama ta amsa Jakadiya ta gyara mata gurin zama,sannan ta futa ta basu guri,  Kattime ta gyara zama tana fadin ." Fulani magana nake tafe da ita." Mama tace." Ai tunda naga fuskar ki nasan akwai magana."

 

 

Kattime tace." Wallahi kuwa, jiya na samu wani labari da bakin da ya fada min bazai k'arya kai asalima shine ya asassa al'amarin." Mama ta zuba mata ido, Kattime ta cigaba da cewa." Kin san Azima da ita aka had'a baki gurin cutar da Almansur." Mama ta mike zaune sosai tana kallon ta cikin mamaki! Kattime ta cigaba da cewa.' Jiya Tsito mashirikin da yayi aikin yazo ya warware min komai, saboda haka Nazo na fada miki auran Azima da Almansur dama da wata manufa aka had'a shi don haka  ki umarce shi da ya rabu da ita tun wuri."

 

 

Mama jikinta yayi sanyi sosai da sosai tace." Dama ni kaina banyi na'am da wannan hadin ba wallahi oh! Mugu  bashi da kama yanzu Azima itace ta bawa yarona guba yaci domin  ya nakasa."? Kattime tace." Kina mamakin wannan duniyar wallahi."

 

 

Mama tace." Yanzu zan sanya ayi min kiran su ki zauna a gaban ki za'ayi komai, Jakadiya ta kira ta umarce ta ta kira mata Azima da Halisa BALARABA

 

 

Wayar ta ta d'auka ta kira uban gayyar, suna tare da me girma governor suna shirye-shuiyen  yanda za'a gudanar da nadin sarauta,domin an tsai da rana jama'azuwa ,Yaga kiran Mama a nutse ya d'auka tace." Kazo yanzu shashena." "Insha Allahu ganin zuwa." Ya fada yana kashe wayar.

 

Sallama sukayi da governor suka futo tare me girma ya shiga mota tare da mutanansa shi kuma ya. Nufi shashen Maman shi tare da jama'ar sa, duk suna zaune suna jiran isowarsa yayi sallama ya shiga duk suka amsa, matansa na rige-rigen gaishe ya amsa mu a nutse ya zauna, yana gaida Maman shi tare da Hajiya Kattime, Fulani tace." Kattime yi musu bayani da bakin ki." Nan Kattime ta fara fada masa duk abunda ya faru tun daga farko har k'arshe da manufar Waziri akan auransa da Azima. Nan take Sarki! Ya tuno da ranar da ya shiga gurin Azima da daddare har yayi Tara da ita tunda lokacin nan ya tashi da wannan ciwo, Azima tayi tsuru-tsuru tuni hawaye ya soma ambaliya a fuskarta tayi da tasani yagi cikin kwando shikkenan yanzu tasan karshen zamanta dashi ya kare ganin yadda ransa yayi mugun b'aci, shiru farlo na minti biyar yayi gyaran murya yana goge gumn da ke tsatsafo masa, yace." Mama ki gafarce ni, da abunda zan aikata yanzu hak'ika zama da Azima babbar musiba ce saboda  haka na sawwake mata igiya guda taje in ta samu miji tayi aure." Yana gama fadin haka ya mike ya futa zuciyarsa babu dad'i.

 

 

Babu Wanda yace komai cikinsu,Azima ta dunga kuka tana rokan Mama ta sanya shi ya janye sakin Mama tayi shiru da rarrafe taje ta rike k'afafun Halisa tana rokonta Halisa ta fuzge kafarta tana maka mata harara tace." Wallahi na tsane ki Azima muguwar azzalima kawai." Cikin kuka Takarasa kusa da Balaraba tana rokonta wai tabawa Sarki hakuri Balaraba tayi shiru kawai tana Mamakin halin Dan Adam.

Fadawan dake waje mama ta umarta tace su futa da Azima kuma su tsaya kanta ta had'a duk wani ko matsanta ta kama gabanta. Aikuwa haka akayi aka tasa Azima a gaba har garin su.

 

 

********

đŸ”•đŸ“ŁđŸ“ŁđŸ“ŁđŸ”ŠđŸ”ŠđŸ”ŠđŸ”ŠđŸ“ąđŸ”±đŸ”±đŸ”±đŸ”±đŸ”±đŸŽ¶đŸŽ¶đŸŽ¶đŸŽ¶đŸŽ¶đŸŽ¶đŸŽ¶đŸŽ¶đŸŽ¶đŸŒ™đŸŒ™đŸŒ™đŸŒ™đŸŒ™đŸŒ™đŸŒ™đŸŒ™đŸŒ™đŸ’„đŸ’„đŸ’„đŸ’„đŸ’„đŸ’„đŸ’„đŸ’„đŸ§đŸŒđŸ€ŽđŸ»đŸ€ŽđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ‘žđŸ»đŸ€ŽđŸ»đŸ€ŽđŸ»đŸ€ŽđŸ»đŸ€ŽđŸ»đŸ€ŽđŸ»đŸ€ŽđŸ»đŸ€ŽđŸ»đŸ€ŽđŸ»đŸ€ŽđŸ»đŸ€ŽđŸ»đŸ§đŸŒ

 

 

 

*Rana bata karya*

 

Yau juma'a uku ga watan uku, yau aka gudanar da shagalin nadin sarauta.

 

Wannan nad'i ya samu halartar dubban mutane kama daga shugabanin kasa she,governor ni shahararun malamai da limamai da shahararun 'yan kasuwa duk sun samu damar halarta nad'in sarautar Sarki! Almansur YARO me dattako me halin manya me nagarta da sanin abunda takeyi kowa na masa fatan alkari tare da jagoranci me cikin adalci,  lokacin da ake gudanar da wannan nad'i Waziri na kwance yana zurarar da hawaye duk an d'ad'e an barshi shi kadai kuka yake tukuro gami da nadamar abunda ya aikata,, labari ya riske cewar ga Almansur can an mik'a masa sandar mulki, ihu!!! Ya kurma yana buga kansa a bango nan take ya futa daga hayyacinsa .

 

 

Balaraba takasa nutsuwa sai shige da fuce take da hidima da mutane duk 'yan gidansu sunzo tare da wasu 'yan unguwar su, Wanda suke mata wani irin ladabi da biyayya tamkar zasuyi mata sujjada, ita kam sam bata son abunda suke mata. Lantana ce me sallamar baki da taga Balaraba ta motsa zata hanata wai saboda cikin jikinta, su Uwa da Iyalinta na gefe guda gwanin tausayi, Mabaruka kadai aka bari a gida saboda babu k'afafu, Shamsiyya kuwa danta ya girma har yana rarrafe, Walidi dashi ake komai yana can waje cikin jama'a yana shige da fuce.

 

 

Har magariba gidan sarautar babu masaka tsinke, shi kanshi me Martabar bai samu damat shigowa gida ba tun safe da ya futa sai bayan sallahr Isha'i lokacin jama'a sunyi sanyi, ya nufi part d'insa tare da dakarunsa.

 

 

Balaraba da Halisa sun shirya masa guri sosai suna tsaye bakin kofar shigowa sun ci uwar kwalliya ba'a magana, yana shigowa suka fara watsa masa wani abu me kyalkyali yana takawa wani. A jikinsa, murmushi yayi ya rungumo su gefan kafad'unsa yana manna musu kisses cike da so da kauna yace." Allah yayi muku albarka."suka amsa da amin. Sama suka nufa suna rungume a jikinsa.

 

*****

Kulu me dakin kudu kuwa tun da taji labarin abunda ya faru da Waziri ta tattara inata-inata ta gudu domin tana jin tsoron tunowar asirinta, ba karamar sata ta labta ba, Sarki! Da ya samu labari yaji ciwon abun sosai saboda 'yan uwansa su Shukura dole duk inda suka shiga ya sanya a nemo su.

 

*****

 

Kwana biyu kura ta lafa me Martaba ya fara zama a fada cikin aminci yana gudanar da mulki cikin adalci da yanda Allah yace aikuwa jama'ar gari suka fara kiransa da "D'an karaminsu babansu, Babansu kuma a cikin sarakai mulki azo a koya a gurin shi, Sarki! Ya zama mutum na matasa na tsofaffi na dattijai na yara kanana.

 

 

 

*****

Balaraba ciki ya tsufa sosai ya shiga wata tara yayin da Halisa ma NATA yake da wata shida,me Martaba kullum cikin sarauraren haihuwar ta yake tayi kib'a sosai ga wani girma da cikin yayi shiyasa sai ya shiga gida sau uku a rana har India lya futa sallah baya komawa fada sai ya koma ya ga jikin nata.

 

 

*****

Ranar litinin misalin k'arfe goma da rabi na safe Allah y sauke ta lafiya inda ta haifi 'yaya uku rigis duk maza, cikin hukuncin Ubangiji haihuwa tazo mata cikin sauk'i ba tare da tasha wahala me tsanani ba, Ubangiji kenan me bayarwa da hanawa Allah ya azurta me Martaba da 'yaya uku lokaci guda, gida ya d'auka gari ya d'auka tunda ga ranar aka fara shagali babu kama hannun YARO,Mama kullum a tafe take gurin 'yayanku kullum cikin yi musu hidima take, shi kam me Martaba ai da k'yar yanzu yake zaman fada, kullum yana nanike da baby's din sa tare da Queen d'inshi da yake jin yanzu ta zame masa wani b'angare na RAYUWAR sa, ranar suna yara suka ci sunan Abdullahi Abdulraham Abudr jabbar, shagali da aka gudanar har sai da na wajan gari ya San dashi domin gidanan tv ne suka dinga d'auka suna watsa shi duniya me jego da 'yayanta tare da me girma Me martaba sunga kauna da soyayyar mutan gari,. Iya ce ta zauna mata har sai da akayi arba'in, sannan aka had'a mata shatara ta arziki aka kaita har gida, tare dasu Sadiya da Usuman zasuje Hutu kafin a koma makaranta. Tofaaa! Yallab'ai fa na ganin ta fara sallah ya bud'e huta domin can gurin Halisa babu bayani cikinta ya tsufa gashi daman can raguwa ce bata d'aukar laluransa, Balaraba ta karbe shi hannu biyu ta fara shayar dashi madara da Zuma irin na aure, sai ga Yallab'ai yana kin zuwa fada, kullum yana kan aiki  😄Balaraba tace batasan wannan ba, sai da yaga ranta ya b'aci sannan ya cigaba da zaman fada, hakan ma tana raya masa zai gudu ya biya buktarsa sannan yayi Wanka ya koma, aikuwa ciki ya samu babu shiri.

 

 

 

Watansu Abdulrrahan uku Halisa ta haihu 'yan ta gwaye duk mata, Wai-wai murna gurin Yallab'ai ya samu 'yan mata masu kama dashi, ranar suna an dagargaji buki babs suka ci sunansu Hasana da husaina.

 

Balaraba kuwa ta fahimci wani cikin ne da ita sai ta fara Neman yaya zatayi gudun karsu Abudul su sha ciki.nan family dector dinsu yace babu matsala zata cigaba da shayar dasu da nonon ta, amma cikin na kaiwa wata shida dole ta cire su daga nono sai a dorasu kan madara me kyau. Aikuwa haka akayi yara suka cigaba da shan nono Mamansu cikin koshin lafiya, inda Yallab'ai ya durfafe ta, ganin yadda yake kwasar gara, kunsan dai mace me yaron ciki abun marmari ce ga mijinta.

 

 

 

 

*Alhamdullahi* *Alhmdullahi*

*Alhmdullahi*

 

 

Nan na kawo karshen wannan littafin Ubangiji Allah ka yafe min kurakurana abunda na rubuta dai dai Allah kasa a amfana ka sanyamu cikin ladan baki d'aya

đŸ‘đŸ»đŸ‘đŸ»

 

 

 

 

 

 

*đŸŠčđŸŒBABBAN YAROđŸŠčđŸŒ*

       Cigaban littafin.

  _*Yaro da kud'iđŸ’”đŸ’”*_

*WASA FARIN GIRKIđŸ“Č*

 

 

*INA KUKE MASOYA LITTAFIN YARO DA KUD'I, TO MAZA KU GARZAYO KU CASKALO KU ANTAYO KU SAMU CIGABAN YARO DA KUD'I WATO BABBAN YARO WASA FARIN GIRKI, YANZU AKA FARA KAFCEN, WANNAN DABAN YAKE DA SAURAN DOMIN YAZO MUKU DA SABON SALO ME SANYA KU NISHAD'I, BABBAN YARO LITTAFI NE ME K'UNSHE DA RIKITA-RIKITA, BABBAN YARO!!!!! BABU SHAKKA YA AMSA SUNAN SAđŸŠčđŸŒ♂đŸ’· BABBAN YARO YA ZO DA SABON SALO MAI SAKA NISHAD'I MAZA KU GARZAYO KU SAMU NAKU KAN KUD'I NAIRA D'ARI UKU KACAL   KU BIYA KU SAMU BABBAN YARO  DOMIN KU GA YA KAFCAN YAKEđŸŠčđŸŒ. Hummmm!!! KAR KU BARI A BAKU LABARI...... DUK ME BUK'ATA ZAI NEMI TA WANNAN NUMBAR KAMAR HAKA*

08089965176

07084653262

 

 

*NI CE DAI HAR ILA YAU*

 

_BINTA UMAR ABBALE_

 

 

```MARUBUCIYAR WANNAN LITTATAFAN```

 

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

*TSANTSAR BUTULCI*

*LADIDI K'WADAGA*

 

 

*MUJE ZUWA MASOYA NA*

 

 

 

A KAFTA!!!!!!!!!!!!!!

 

 

 

*BABBAN YARO CIGABAN LITTAFIN YARO DA KUDIđŸŠčđŸŒ♂đŸ’”đŸ’”đŸ’”đŸ’”*

 

 

Kar Ku bari a baku  labari

 

Post a Comment for "GIMBIYA BALARABA COMPLETE"