TARAYYA 43-44
Haske writers association +
Not edited.
Murmushin qarfin hali tasaki
tareda sake damqe hannunsa dake cikin nata tana kallon fuskarsa dashima ita
yake kallo yana yiwa Allah hamdala cikin ransa.
Tashi zaune takeson yi ganin
kamar batada qarfin jiki yasashi tayarda ita zaune tareda cire mata cannula
dake hannunta ya gyara mata zama sosai.
Cikin sanyin murya da kulawa
yace,
Ya kikeji yanxu?
Girgiza masa kai tayi tana
kallon fuskarsa.
Jakadiya ce tayi knocking qofar
dakin ahankali ta sanarda zuwan sultana.
Zare hannunta tayi cikin nasa
tareda lumshe ido sbd yanayin datakeji ajikinta har lokacin.
Cikin nutsuwa ammyn tashigo
idonta kan rumanah din
Hankalinta ya'dan kwanta ganin
ta farka harta tashi zaune.
Qarasowa tayi tareda miqawa
maheer hannu ya kama hannun da hannunsa daya cikin nutsuwa yace,
Ina kwana ya ammy?
Murmushi tayi tace,
Lfy klau..tana kamo hannun
rumanah tace,
Ya jikin?
Naji sauqi
ammy"""ta fada cikin qarfin hali da danne ciwon datakeji.
Miqewa yayi ya fita yana amsa
kiran khaleefa dake kiransa kan maganar test result 'dinta dasuka fito.
Ammy dakanta ta kamata takaita
toilet tayo wanka da brush tana fitowa taga doguwar riga mara nauyi akan
dressing chair ta dauka tasaka ta shirya tana qoqarin busar da kanta sbd wankan
tsarkin datayi na haihuwa ammy tashigo tareda nuratu dake daukeda babban tray
Jere da breakfast ta ajiye zata juya rumanah takira sunanta ahankali.
Tsayawa tayi tareda juyowa
cikin ladabi
Rumanah ta miqa mata hand dryer
cikin sanyin murya tace,
Taimakamin.
Ammy na ganin hakan tasan
magana zasuyi ta kalli nuratu tace,
Tayi breakfast.
Jinjina kai tayi alamar tou.
Ahankali take busar mata da
gashin babu Wanda yayi magana acikinsu.
Tana gamawa ta daure mata
gashin tareda ajiyewa a natse.
Miqewa tayi itama ta nufi inda
take sallah tana idarwa ta dawo kan couch din dakin ta zauna har lokacin nuratu
na tsaye kanta a sunkuye cikin tarin damuwa da kadaici.
Ahankali takamo hannunta ta
zaunar da ita kusada ita ta kalli fuskarta kafin ta sauke kanta itama ta qurawa
gabanta ido cikin sanyin murya tace,
Kiyi hakuri nabarki alokacinda
kike tsananin buqatata,
Kin kuladani kin tayani kuka
kin rarrasheni alokacinda na rasa nawa iyayen saidai ni nakasa miki hakan
alokacinda kike buqatar wani ataredake..
Kallonta nuratu tayi hawayen
datake riqewa suka gangaro mata tace,
Wlh idan nace miki bana
buqatarki ataredani na miki qarya rumanah saidai yanayin rayuwa daya kawo
bambamci arayuwarmu ayanxu rayuwarki daban take data baiwar datafi kowace baiwa
baqin jini sbd mahaifiyarta data.....
Rintse ido tayi tareda budewa
idanuwanta na cikowa da hawaye ta juyo ta kalleta cikin sanyin murya tace,
Ada damuke bayi rayuwarmu tafi
kwanciyar hankali da nutsuwa tareda dadin gudanar da rayuwarmu,
Rayuwar bayi wata rayuwace mara
yanci amma wlh wani lokacin tafi rayuwa irin wadda nasamu kaina aciki,
Nuratu idan zaka roqi Allah abu
ka roqi alkhairinsa sbd wlh rayuwata ina baiwa tafimin kwanciyar hankali akan
yanxu.
Gangaro mata hawaye sukayi sbd
jin tausayin kanta da abinda zata fada tace,
STORY CONTINUES BELOW
Nuratu na 'yantaki daga yanxu
ke ba baiwa bace kinsamu 'yancinki,
Babu wata rayuwar jin dadi da
kwanciyar anan dan haka za'a maidaki gida acan zaki samu rayuwar kwanciyar
hankali damukai burin samu idan ni bansamuba zan qoqarta gurin ganin ke
kinsamu...
Kallonta nuratu takeyi
hawayenta na tsananta gudu tace,
Tare mukayi alqawarin komawa
gida.....
Zanzo wata rana nima idan
nauyin alummar dake kaina ya sauka
Zanzo idan inada rayuwa da
lafiya sbd burinane nima nahadu da dangin iyayena dan haka karkiyi wasa da
damarki kice zaki jirani kije Allah zai sake sadamu da yardarsa.
Kuka nuratu ta fashe dashi tana
girgiza kai tace,
Bansan ta yaya zan fuskanci
mutanen da basusanniba nikadai nace musu dukkanin iyayenmu da sauran danginsu
da akaje dasu sun mutu ba...
Itama kukan takeyi sosai saidai
bazata iya cewa komaiba sbd wannan shine gatan datasan zata yiwa nuratu takoma
gida ta fuskanci sabuwar rayuwa cikin amincin Allah.
Kuka sukeyi sosai na rabuwa da
juna daqyar rumanah ta miqe ta bude wardrobe ta dauko wata jaka dake daukeda
qatuwar sarqar zinari ta miqawa nuratu tareda juya mata baya sbd kukan datake
riqewa tace,
Allah ya hada fuskokinmu da
alkhairi.
Ta baya nuratu ta rungumeta
tana sakin sabon kuka tana cewa,
Kisani zan jira zuwanki har
qarshen numfashina.
Daqyar suka saki juna suka fito
palonta na biyu inda suka tararda ammy da maheer da khaleefa tareda Jakadiya
suna jiran fitowarsu.
Fuskokinsu suka bayyanarda
halinda suke ciki.
Ya qurawa fuskarta datai jajir
ido kafin ya dauke kai yanajin damuwar ganinta hakan cikin zuciyarsa.
Gefen ammy ta qarasa ta tsaya
ahankali ta bude baki tafada musu tafiyar Nuratu din zuwa qasarsu.
Ammy sosai ta yiwa nuratu addua
da fatan alkhairi tareda cewa jakadiya nuratun ta sameta kafin washe gari ta
wuce.
Bayan fitarta khaleefa yabi
bayanta da kallo kafin maheer yayi masa magana da ido suka fita.
Bayan fitarsu ammy ta zaunar da
ita tasa aka kawo wani abincin breakfast din.
A palon yarima maheer suka
zauna cikin nutsuwa yace,
Khaleefa zaka karbi duk wani
bayanin tarihin my queen da mahaifiyar nuratu ta bayar ka kaita har gida kafin
ka karbi takardun iyayenta kayi amfani dasu ka nemomin asalinta.
Shiru khaleefa yayi yana sake
tauna zancen sbd tafiyar ta jirgin ruwa ce sbd ta ruwa kawai zasubi su bulla
garinsu nuratun kai tsaye a yanda akace gashi bai cika son tafiyar ruwa ba
saidai kuma dole haka zai daure saidai suyi amfani jirgin dazasu isa cikin
kwana biyu.
Acikin daren rumanah tayi kukan
tafiyar Nuratu,
Iyayensu sunzo qasar dasu
acikinsu gashi su zasu koma batareda ko dayansuba.
Washe gari bayan sallar asuba
suka wuce bayan khaleefa yakarbi duk wani tarihi na asalinsu daga hannun anees
mai haqqin tattara tarihin sarakunan masarauta Wanda aka ya karbi bayanan daga
mamani ya rubuce a littafin tarihi kafin rasuwarta.
Bayan tafiyarsu takira Jakadiya
ta miqa mata wani zungureren saqo a rubuce tace takaiwa harooun sarkin fada.
Lokacinda Jakadiya takaiwa
harooun saqon yana gama karantawa jikinsa yayi matuqar sanyi da abinda ke
rubucen saidai kuma yasan hakan datake shirin yi shine qarshen abinda yake
bibiyar mineelik dan haka babu bata lokaci ya fita dakansa yaje gurin Negus
sarkin qirar mineelik yayi masa bayani ya karbo littafin zanen karagar mulkin
qarnikan baya yadawo yabawa jekadiya takai mata.
STORY CONTINUES BELOW
Lokacinda Jakadiya takawo mata
shirgegen littafin mai nauyi ko budesa batayiba tace,
Kije na zabi lamba ta biyar.
Babu musu Jakadiya takoma ta
mayar tana jinjina alamarin rumanah sbd idan Allah ya taimaka abinda take
shirin yi shine daidai.
Acikin daren ranar Negus da
yaransa suka fara aiwatarda aikin qera sabuwar karagar mulkin mineelik wadda
basu ta6a qera abu mai kyau da darajartaba sbd abubuwan dasuka narka ana hadawa
dasu gurin qirar.
Lokacinda Jakadiya ta sanarda
ammy abinda yake shirin faruwa numfashi ammy tasauke cikin danne fargabarta dan
batason tunanin faruwar wani abin saidai zataje tayi magana da sultan sbd shine
yasan komai ciki da waje gameda komai na karagar fiyedasu.
Da daddare bayan ko ina yayi
tsit sultana ta fito ta nufi sashen sultan kai tsaye aka barta tashiga sanin
matsayinta gurin assultana.
Zaune yake hankali kwance yana
karatun wani shirgegen littafin tarihi yana shan madara mai zafi da aka kawo
masa kullum kafin ya kwanta sbd tana qara lafiyar qwaqwalwa.
Kallo daya yayi mata yasaki
murmushi yana cigaba da abinda yakeyi.
Qarasowa tayi kusadashi ta
zauna cikin girmamawa ta gaidasa tana kallon littafin dayake karatu tace,
Meyasa haryanxu bazaka sauke
dukkanin wani tunani na sharrin shaidanba ka fuskanci gaskia ka bita,
Ka tubarwa ubangijinka ka ajiye
duk wata niyya da qudirinda bana alkhairi ba wlh Allah zai karbi tubanka sbd
shi mai yafiyane ga bayin dasuka tubarmasa.
Wani irin murmushi yasaki
tareda rufe littafin ya ajiye gefe ya kalleta yace,
Baiwarki kuma matar 'danki tayi
babban kuskure na aikata abinda ta aikata sbd kaf tarihin mineelik babu wani
sultan da aka taba muzantawa saini sultan abdulshams jinin ajani....
Numfashi tasauke cikin takaici
da baqin cikin halinda mijinta yasamu kansa idanuwanta na cikowa da hawaye
tace,
Son zuciyar kakannin kakanninka
shine yasamu ahalinda muka tsintsi kanmu aciki karka bari zuciya takaika aikata
irin kuskurensu.....
Katseta yayi da cewa,
Meya kawoki ki fada kai tsaye
sbd nasan akwai abinda yakawoki a wannan lokacin.
Kallonsa tayi ganin Sam
idanuwansa da zuciyarsa sun rufe..
Cikin sanyin murya tace,
Assultana na shirin canza
mineelik gabaki 'daya da wata......
Da sauri ya kalleta yana ajiye
cup din hannunsa sbd girgiza da zuciyarsa tayi.
Cikin bayyanarda tsananin
tashin hankalinsa yace,
Zata aikata wani babban
kuskuren sbd rusa karagar gabaki 'daya na nufin rusa rayuwarta sbd zata rushene
tareda jininsu jamal na qarshe daya hau karagar yayi mulki akanta......
Shiru yayi zufa na karyo masa
sbd yasan dagashi sai itane suka rage aduniya wainda suka taba zauna karagar
har sukai mulki akanta,
A bangaren jini kuwa shikadaine
jininsu na qarshe dayayi mulki akan mineelik ita 'din ba jininsu bace akwai
yiyuwar abin bazai shafetaba koya shafeta saidai ta nakasta amma shi babu
tantama rayuwarsace ke rawa jinin qarshe nasu jamal.
Wannan rumanah gabaki 'daya
rayuwarta ta zame masa masifa mai barazana bai taba tunanin ko namiji zai iya
fuskantarsaba ya girgizasa bare 'yaya mata daya dauka marasa amfani saigashi ko
acikin 'yaya matan ma baiwace take barazaga rayuwarsa,
Bazai Bari su aikata hakanba
dole ya juya musu zancen..
Gyara nutsuwarsa yayi cikin
vasarwa yace,
Karku bari ta aikata hakan sbd
rayuwartace acikin hadari dan kuwa haqqine na qarshe zai fita akanta.....
STORY CONTINUES BELOW
Murmushin baqin ciki ammy
tasaki tareda girgiza kai hawayenta suka sauko tace,
Yanayinka da kulawar daka nuna
yasamin kokwanto akan amsarka dan haka mun dangana munbarwa Allah komai zamu
barta takawo qarshen mineelik duk abinda Allah ya qaddaro zamu runguma mu dauki
dangana.
Miqewa tsaye tayi zata fice ya
riqo hannunta akaro na farko dayaji tsoro da fargaba sun ziyarci zuciyarsa ya
bude baki daqyar yace,
Karki bari ta aikata sbd
rayuwatace a hadari kuma tatama na cikin hadari.
Hawayenta suka qara gudu ta
sunkuyar dakai tanajin zuciyarta na karyewa sbd qaunar mijinta uban yayanta
saidai kuma kodan sbd 'yayanta da jikokinta zataso akawo qarshen masifar
mineelik.
Zame hannunta tayi ahankali
tace,
Allah yazaba mana abinda yafi
zama alkhairi.
Ficewa tayi jiki asanyaye
zuciyarta na sake karyewa saidai bazata bari ta karayaba hakan da rumanah
zatayi shine daidai insha Allah.
Zaune yake bakin gadonsa yayi
shiru tareda zurfi cikin tunani Sam bayajin nutsuwa a zuciyarsa wani irin
rashin sukuni yakeji..
Baca Juga
Ahankali tashigo dakin rungume
da abeel jikinta amatuqar sanyaye sbd jikinta datake yana tsananta dan ko yanxu
kafin tafito saidata yanke jiki ta fadi jini na fita hancinta saidai bata fita
hayyacinta ba kuma ta hani Jakadiya fadawa kowa abin yafara tsanani.
Qarasowa tayi ahankali ta
kwantarda abeel kan sofa tadawo gefensa ta zauna ahankali tareda dafa hannunsa
takalli fuskarsa.
Shima ita ya kalla ta sakar
masa murmushi ahankali tareda riqe hannunsa ta lumshe ido sbd abinda taji yana
taso mata ta danne yanayin daqyar tasake qaqalo murmushi tana kallon hannunsa
dake cikin nata ahankali tabude baki tace,
Karka saki hannuna har
lokacinda zan shaqi numfashin qarshena a duniya,
Ka zamo jiqo kuma majingini
arayuwata
Ka hanani 'daukar hanyarda zata
batardani zuwa duniyar daba tawaba,
Qarfin soyyarka yaci qarfin
abinda nakeji ajikina saidai bansaniba ko hakan zai jima shiyasa a yanxu nake
roqonka da har abada karka rabu da suhailat sbd itace macen da soyayyarta
bazata taba barin cuta ta kutso kai rayuwarkaba..ni tamkar baquwace a rayuwarku
ba lallaine na qarasa rayuwa acikinkuba.......
Matse hannunta dake cikin nasa
yayi yana rintse idanuwansa dasukai jajir..
Hawayen datake riqewane suka
6alle mata ta kalli fuskarsa datai jajir ya rintse idanuwansa ta shafi fuskarsa
hawayenta na tsananta tace,
Maheer abdulshams nagode da
soyayyarka gareni..
Bude jajayen idanuwansa yayi
yana kallon hawayenta dake gudu sosai yakasa magana sbd radadi da nauyin da
zuciyarsa tai masa sai kawai ya rungumota jikinsa.
Ahaka suka kwana cikin wani
irin sanyin jiki dana zuciya.
Kwanansu khaleefa biyu a ruwa
aranar na uku da yamma sosai suka isa saidai kuma sunsha wahala sosai sbd tuni
bakin ruwan yazama border saida sukasha wata irin wuya kafin suka samu wucewa
da taimakon wani 'dan asalin qauyensu mamani din.
Bayan wucewarsu duk yanda
sukayiwa saurayin bayani bai ganeba sbd basajin hausa ko kadan har gwara nuratu
tanaji kadan kadan sbd su mamani da umman rumanah sunayi musu tun suna qanana
saidai ya jasu kan mashin dinsa sukayi wani irin mugun overload yajasu dan
kaisu cikin qauyen daya samu canji ba laifi.
Tafiya mai tsawo sukayi kafin
suka isa qauyen mai tsananin girma da cikar mutane.
Gidan shugaban qauyen yakaisu
cikin sa'a lokacinda suka isa yana gida.
Kallonsu aka taru anayi sbd
ganin baqaqen labarawa musamman khaleefa dayake cikakken dan Ethiopian asali.
Bayan anbasu guri sun zauna ya
fidda tambarin masarautar dasuka fito ya miqawa shugaban ya kalli nuratu yayi
mata magana yace,
Kiyi musu bayaninmu yanda
zasu gane ko yayane.
Gyara zama tayi muryarta na
rawa tace,
Munfito daga qasar Ethiopia ne
qarqashin masarautarsu,
Sun siya bayin dasuka fito daga
wannan nahiyar tsawon shekara ashirin da biyar yanxu.,
Acikinsu akwai mamani da asma'u
dasuka tafi da juna biyu acan suka haifi 'yaya mata dukkaninsu Wanda 'daya daga
cikin 'yayan itace ni 'dayar kuma a yanxu itace sarauniyar qasar.
Da wani irin mugun mamaki suke
kallonta musamman shugaban garin daya zamto kutti mijin mamani yasake kallon
nuratu da gabaki 'daya take kamar yar asalin Ethiopia itama.
Cikin nutsuwa yace,
Ke 'yar wacece acikinsu?
Ni 'yar mamani ce.
Wata irin kabbara tsoffin gurin
suka dauka cikeda murna da mamakin wannan alamari kutti yace,
Ina iyayenku?
Dukkaninsu Allah yayi musu
rasuwa mamani ko sati batayiba yanxu haka.
Sake daukar kabbara sukayi
cikin jimami da tsananin girmama wannan alamari.
Ahankali ta zayyane musu komai
gameda rayuwarsu kafin ta gabatarda khaleefa amatsayin Wanda zai karbi takardun
dukiyar asma'u da bulama dan neman asalin sarauniya ummu-rumanah.
Bayan dogon koke koken saduwa
da baqin cikin rashinsu mamani dasu bulama nan kutti yagabatarwa da su nuratu
kansa amatsayin mahaifinta.
Duk wani zuriar gidan antaru an
karbi nuratu da hannu Bibbiyu da zuciya daya da wainda suka San faruwar abin da
wainda ma ko haihuwarsu baayiba nan dai kowa yataru ana farin ciki.
Ganin yanayin garin yasa
khaleefa yanke shawarar wucewa dan sake kutsawa cikin Nigeria dan gabatarda
abinda yakawosa.
Kutti ya basa takardun dasuka
tsufa sosai ga sanyin ruwa daya soma lalatasu tun wancan lokacin saidai ba
laifi yana iya ganin rubutun dake jikinsu atake ya karancesu daganan ya roqi
alfarmar tafiya da wani yaron kuttin dayake jin yarensu kadan kadan sbd aiki
dayakeyi a border dinsu.
Da mashin din salee suka isa
inda zasu samu mota bayan sunyi tafiyar awowi akan mashin din.
Motar dazata kaisu Maiduguri
kai tsaye suka hau inda duk hankalin khaleefa yatashi sbd ganin inda yasamu
kansa dakuma wata irin azabar wuyar tafiya data fara gigitasa.
Gaf da asuba suka isa Maiduguri
kai tsaye wani lafiyayyan babban hotel suka sauka anan yayi baccin wahala ga
zazzabin dakeson kamasa na baqar wuyar dabai taba shaba.
#mamuhgee
Haske writers association. +
Not edited.
Duk yanda yaso yayi komai cikin
lokaci yakoma hakan bai samuba sbd zazzabi mai qarfi daya kwantar dashi tsawon
kwana biyu
Qarshe dai dole ya daure suka
tafi kai tsaye companyn dake rubuce a jikin takardun da taimakon wani
ma'aikacin hotel din suka isa.
Da farko sunsha wahala kafin
suka samu ganin shugaban companyn alhaji babaye salmanu bulama.
Kai tsaye khaleefa yafitarda
takardun dayazo dasu ya ajiye gaban alhaji babaye.
Kallo daya yayi musu harzai
dauke kai yayi magana yaga sunan dake jikinsu yayi musu wata irin damqa yana
dubawa sbd basuyi masa kama dana yanxuba wannan rubutu da sunan company dinne
tunna iyayensu na shekarun dasuka wuce.
Budesu yaringayi daya bayan
daya haryakai qarshe ya miqe tsaye sbd tabbarda sune asalin takardun da
'yayansa da matarsa suka tafi dasu.
Kallon khaleefa yayi da sauri
tareda zagayowa daga table dinsa jikinsa na wata irin rawa tun kafin yayi
magana khaleefa yaciro alamar masarautar daya fito ya miqa masa cikin turanci
yace,
Nazone dan neman asalin
sarauniyar qasata ummu-rumanah bulama..
Rawa jikin alhaji babaye yaqara
yace,
Ina kasamo wainnan takardun?
Ina masu su suke?
Masu wainnan takardun sun rasu
saidai 'yarsu wadda itace sarauniyar qasarmu ayanxu....
Wani irin kuka alhaji babaye
yasaki tareda rungume khaleefa duk da dai yasan dole yayi bincike akan hakan
kafin yagama yarda.
Waya yaciro yakira
qanwarsu hajiya yakurah yafada mata nan hankali ya tashi sbd farin ciki
da murna tareda wasi wasin zamtowar zancen gskia.
Da kansa yakaisu gidansa akai
musu masauki kafin yatabbarda zancen duk da yasan baza'a yimusu qarya dan a
cucesu tun daga qasar Ethiopia ba kuma daga masarautarsu.
Washe gari cikin manyan motoci
suka dunguma zuwa garinsu kutti dan sake tabbatarwa.
Sai tsakiyar dare suka isa kuma
acikin daren aka tara duk dattijan garin dasukasan su bulama da asma'u tun
zuwansu garin da duk abinda yafaru.
Kuka sosai alhaji babaye yayi
dayaji irin rayuwar da 'dan uwansa da matarsa sukayi saidai kuma yanzu babu
abinda yakeson gani kamar 'yar dan uwansa.
Daga alhaji babaye sai khaleefa
suka koma sbd khaleefa jirgi zaibi yakoma bazai iya tafiyar ruwaba kuma sauran
binciken da tabbatarwar idan sun haduda rumanah zasu qarasa tabbatarwa.
Koda suka koma gida sosai
hajiya yakurah taso bin khaleefa suje tare saidai maigidanta yace tabari yadawo
daga China saisuje gabaki dayansu da haka khaleefa yatafi sbd ciwo dake neman
kwantar dashi sbd bai qaramar wahalaba yasha a tafiyar.
A yau saqon haroun ya iso
gareta an kammala aikinta.
Shiru tayi bayan fitar Jakadiya
sbd tunanin yaya maheer zai karbi zancen sbd dole tana buqatar aiwatarda abinda
tayi niya dan tanaji jikinta yasaki sosai jininta qarewa yakeyi sbd tsananta da
abin yafarayi ajikinta sbd jinin dataqi zubarwa har lokacin tasan daf take da
rasa hankalinta dan wata irin zabura dake kamata yanzu duk da tana qoqarin
boyewa ammy da maheer tanaji abin yafara cin qarfinta.
Kallon abeel dake kwance
jikinta tayi zatai magana jini ya digo ta hancinta ya sauka kan fuskarsa tayi
saurin goge masa tareda ajiyesa ta dauki tissue tana dafe kanta da jiri ke
juyawa dashi.
Durqusa gurin tayi tana fidda
wani irin nishi cikin azaba tsawon mintuna kafin tasamu taci qarfin abin tana
kiran sunayen Allah harya lafa kafin tayi wani yunqurin miqewa ya turo qofar
dakin yashigo cikin nutsuwa idanuwansa kanta yana kallon tissues din gabanta
dasuke lalace da jini hakama hancinta zuwa bakinta duk jini.
STORY CONTINUES BELOW
Saurin goge hancinta tahau yi
saidai kuma atake jinin yasake 6allewa ta rintse ido cikin wani irin hali
tafara nishi mai wuyar fita.
Da wani irin gudu ya qaraso
gareta tun kafi yakai hannunsa gareta idanuwanta suka fara qoqarin rufewa yayi
saurin tarota jikinsa yana kiran sunanta da qarfi. 2
Ganin tana neman fita
hayyacinta yasa ya bude bedside drawer dinta yadauko maganin da negasi yabayar
ariqa bata idan jinin yazo mata ya bude gabaki daya ya zuba mata abaki cikin
tashin hankalin saidai jinin bai tsayaba amma idanuwanta sun bude tafara qoqarin
tashi tana karbar tissue din dayake qoqarin kaiwa hancinta tace,
Banda lokaci inason sanardakai
abinda nake ashirin aikatawa ayau sbd banason na mutu abanza batareda na
tsayarda abinda ke faruwaba.....
Wani irin tari tayi jini mai
tarin yawa ya fito bakinta kamar amai
Atake ya rungumota abinda bai
taba ba arayuwarsa hawaye suka gangaro masa yafara girgiza kai yana hanata
magana..
Girgiza masa kai tayi awahalce
tace,
Taimakeni na shirya muje mukawa
qarshen matsalar sbd 'yan baya su samu nutsuwa da kwanciyar hankalin gudanarda
mulkin adalci.
Kasa motsi yayi saidata saki
kuka ahankali tana kallonsa cikin rawar murya tace,
Karka manta ka min alqawarin
tsayawa dani dan kawarda matsalar data lalata farin cikinmu dana wainda
basujiba basu ganiba.
Cikin wani irin hali yace,
Na miki alqawari amma banda
sadaukar da lafiyarki ko rayuwarki meyasa z......
Rufe masa baki tayi cikin wani
irin yanayi tace,
Mu barwa Allah zabi zai mana
mafita.
Amatuqar wahalce ya taimaka
mata ta shirya sbd tuni alummar mineelik da kewayenta suka hallara sbd mahimmin
saqon daza'a bayyanar garesu.
Duk yanda yakeson daurewa
kasawa yayi lokacinda zasu shiga inda dukkanin jama'arta zasu ganta jawota yayi
ya rungume da qarfi cikin rawar murya yace,
Kisani har abada bazan saki
hannunkiba zamu fuskanci duk abinda zai tunkaromu atare, ummu-rumanah bulama
kece zuciyar maheer abdulshams so please fight this battle for my love...
Ajiyar zuciya tasauke ahankali
tareda zamewa daga jikinsa tana riqe hannun ammy dake hawaye gefenta Jakadiya
dake gefensu tayi saurin miqawa ammy tissues ganin jinin yanason sake tsananta.
Ammy dakanta ta goge mata tana
danne kukanta.
Murmushi tasaki tareda riqe
hannun ammyn ta karbi tissue din tana goge hancinta zuwa bakinta da hannunta
dake rawa sbd ko tsayuwa daidai bata iyayi abinda yafi daga hankalinsu kenan.
Sultan ma aranar da safe ta
bayarda takardar sakinsa dan haka shima tuni ya fito ya halarci taron tareda
sauran dattijawon masarautar duk da ayau jikinsa a sanyaye yake da abinda yake
faruwar saidai a safiyar yau 'din ya gana da dukkanin 'yayansa dasuka zo dan
halartar wannan taro kuma ganinsu ayau din da maganganunsu sun sanyaya jikinsa
sunbar zuciyarsa da dana sani musamman maganganun maheer dayayi masa gameda mutuwar
iyayen rumanah...
Hakan yasa ya ajiye dukkanin
makaman yaqinsa akawo qarshen masifar duk da su sunriga sunbi sahu.
Tana fita ko ina yayi tsit
dukkanin alummar gurin suka nutsu ahankali haroun yabada umarni nan take aka
bayyanarda wata irin sabuwar karaga mai tsananin kyawu da kyalli mai daukar ido
atake dukkanin jamar gurin mamaki da tsoro yakamasu musamman maheer dabaisan da
hakanba yakalleta da sauri saiyaga tana qoqarin danne abinda takejine dan
daidaita nutsuwarta yafasa maganar dayayi niyya ya damqe hannunta dake cikin
nasa sbd har lokacin a tsaye suke taredasu ammy da jakadiya da masu tsaron
lafiyarta.
Cikin wata irin budaddiyar
murya sarkin fada haroun ya bude wata irin zungureriyar takarda mai daukeda
tambarin masarautar mineelik dake daukeda saqon assultana yafara karantowa kai
tsaye da qarfin muryarsa yanda kowa zaiji.
"""" NI
SARAUNIYAR MINEELIK UMMU-RUMANAH BULAMA AYAU SHA BIYU GA WATA NA BIYAR A
SHEKARA TA DUBU BIYU DA UKU NA SOKE KARAGAR MINEELIK DAN KAWO QARSHEN MULKIN
ZALINCI INA GABATAR MUKU DA SABUWAR KARAGA GA WANNAN MASARAUTA...HAKA KUMA AYAU
SHA BIYU GA WATAN BIYAR SHEKARA TA DUBU BIYU DA UKU NI UWAR MAGAJI SARAUNIYA
UMMU-RUMANAH NA SAUKA KAN MULKIN MASARAUTAR MINEELIK TAREDA 'DORA SABON SARKI
ABDALLAH ABDALLAH AMMED""
Atake dukkanin gurin yadauki
wata irin kabbara da koke koken farin ciki da sbd wannan wani irin babban
alamarine yazo musu na sauyi daga mulkin azaba musamman Abdallah Abdallah ammed
mahaifin khaleefa mutum ne dazai kawowa rayuwarsu sauyi na adalci gashi shikansa
baisanda zancenba.
Tsit aka sakeyi lokacin wasu
irin majiya qarfin bayi kusan goma sha biyar suka ciccibo karagar mineelik
Wanda keda wani irin girma tareda hularta.
Wani irin baro mai tsananin
girma da fadi daukeda wani irin mahaukaciyar tukunta mai tsananin tiriri yaran
negasi kusan su ashirin da biyu suka turo aka ajiye tsakiyar filin harabar.
Ta lumshe idanuwanta dasuka
fara rufewa suna gani dishi dishi ta budesu daqyar ta iya 'daga hannu ta bada
umarni atake haroun yabada umarni aka 'daga karagar aka saka ciki atake tafara
nitsewa tana narkewa cikin ruwan dalmar tun tana gani dishi dishi sbd jinin
daya balle hancinta atake idanuwanta suka rufe ruf ta yanke jiki ta zube gurin
jini na qarasa balle mata ta hanci da bakinta.
#mamuhgee
Post a Comment for " TARAYYA 43-44"