TARAYYA 17-18
Page 17
Jikinta har rawa yakeyi gurin
zuwa tasanarda mamani,
Da ace bawa nada ikon gudu
Dan karan kansa ba sakasa akayi
to yau da bazata tafiyaba gudu zatayi domin ta
isa gurin mamani da wuri tafada mata kyakkyawar rayuwarda tayiwa rumanah
qwanqwasa. +
Tana isa babban kicin din ta
sake nutsuwa Cikin girmamawa take gaida masu kula da bayin sakewa masarauta
girki harta isa gaban mamani dake kwashe farfesun wani qatoton kifi ahankali
sbd karya wargaje ahaka ake dorasa cikin inda za'a kaisa,
Murya qasa qasa cikin
tsananin farin ciki tace, 1
Mamani a yau sultana ta
'yanta ummu-rumanah sbd aurawa yarima maheer ita ataqaicema an 'daura
au........ 1
Cak mamani ta kafe idonta
akan fuskar nuratu 'din babu alamar motsi atareda ita
Cikeda tsoro ta ta6ata tace,
Maman........bata qaraba taga
ta yanke jiki ta fadi cikin tsananin tsoro da fargaba takira sunanta da qarfi
Wanda yasa masu kula dasu qarasowa da sauri suna tambayar abinda yasameta. 5
Girgiza kai nuratu tayi
idanuwanta na cikowa da hawaye sai dai batasan mezataceba Dan tasan tsabar
hassadace ta sumar da mamani. 12
Ruwa akace nuratu ta 'debo
sbd rikicewa ta ciko silver da ruwan masu tsananin zafi tana qarasowa ta zuba
matasu amatuqar gigice mamani ta saki wahalalliyar ajiyar zuciya tareda bude
ido ta tashi zaune jikinta na wani irin sililin zafi ta 'dago ahankali tana
kallon nuratu ta tuno da abinda tafada mata wani irin kuka ne ya kufce mata hadda
shesheka ita shikenan rumanah ta mayar mata da burinta mafarki,
Ita sai yaushene bulama da
iyalinsa zasu bari taringa samun abinda take burin samu,
Rumanah tasan duk burinta
akan nuratu ne tasamu wannan matsayin amma ta shiga tsakaninta da burinta. 4
Wani sabon kuka tafashe dashi
tareda miqewa tana qoqarin cigaba da aikinta sililin jikinma tuni baqin ciki
yasa batajinsa ko kadan.
Saidai ita mamani kutti ayau
tana rantsuwa dasai ta raba rumanah da duk wani farin ciki dazai shigo
rayuwarta kamar yanda iyayenta su asma'u suka rabota da farin cikinta,
Hakama tayi alqawarin shiga
tsananin ummu-rumanah da duk wani burinta kamar yanda ta rabata danata. 7
Jiki amatuqar sanyaye nuratu
ta juya tabar sashen kicin din tana tunanin tabbas mamani bazata bari azauna lafiyaba
saidai dukda tana mahaifiyarta bazata ta6a bari ta cutatarda ummu-rumanah ba
koda hakan na nufin zasu raba hanya ne. 1
Cikin wani irin yanayi
yashigo part din na sultana tareda Jakadiya dake biye dashi daukeda sadakin
rumanah 'din fuskar yalwace da farin ciki.
Suna shigowa dukkanin wainda
ke palon suka miqe banda sultana da rumanah dake zaune cikin lullubi.
Tsayawa yayi batareda yakalli
inda takeba
Ganin haka yasa sultana
miqewa tsaye tareda riqo rumanah ta tayarda ita ahankali takawota gabansa suna
fuskantar juna
Tanajin yanda dukkanin jikin
rumanah yake rawa haka ta saketa tareda saka hannu ta yaye mata lullubin. 1
Kamar bazai kalli fuskarta ba
ya bude fararen oily eyes dinsa akanta,
Karo na farko daya kalli wata
mace a duniya yaji gabansa yayi mummunan bugawa ya 'dauke idanuwansa ahankali
cikin rashin kulawa yayi Jakadiya wani kallo a hanxarce ta matso tareda miqawa
ummu-rumanah tray dinda yake daukeda sadakinta cikin tsananin girmamawa tace, 1
Allah yataimaki amarya
ummu-rumanah ga sadakinki Allah yayiwa aure albarka. 1
Hannuwanta dake cikeda
awarwaro da zobunan zinari ta 'dago yana rawa sosai ta karbi tray din har
lokacin kanta na qasa bata dago takalli kowaba.
Sultana ta miqawa tray din
batareda tace komaiba sbd bazata iya maganaba itadai duk yanda sukazo haka zata
bisu sbd tasan wannan shine fate dinta.
Karba sultana tayi tareda
sakin murmushin qarfin hali tace,
STORY CONTINUES BELOW
Allah yayiwa aure da rayuwaki
albarka ummu-rumanah bulama.
Mayar mata da lullubinta
akayi suka dunguma zuwa gurin sultan .
Acikin dubban taro aka
gabatarda ummu-rumanah bulama amatsayin sabuwar matar yarima.
Jama'ar gari da wasu
masarautun sun jinjina kyawu irin na ummu-rumanah sbd ayanda tarihin
sarakunansu yake zuwar musu shigowar mace mai tsananin kyawu a cikin zuriar
sarauta baya zamtowa alkhairi.
Ana gama gabatarwa aka
mayarda rumanah gefenta tareda sabbin bayi da kuyangi goma.
Bayan angama shagalin sultana
ta shirya dukkanin kayanta tareda sa jakadiya tasa ayi mata booking ticket na
flight dinda zai tashi da dare zuwa Libya.
Wanka yayi yashirya cikin
fararen qananan kaya transparent marasa nauyi shiyasa mur'dadden jikinsa yake
kusan a bayyane sbd shi Sam bayajin damuwar komai sbd auren bai sakasa akansaba
sbd yasan bazai ta6a takura kansa ya canza sbd waniba, baya buqatar wata mace
arayuwarsa bayan suhailat so bayajin yanada wani lokacin 6atawa gurin zama yana yiwa mata ciki
saikace wani injin. 5
Damuwarsa 'dayace barin
sultana masarautar zai ta6a martabarta da qimarta a idanuwan mutanan da mineelik
ke mulki dakuma mutanen masarautar mahaifinta.
Kwanciya yayi tareda lumshe
ido.
Suhailat kwananta biyu bata
fito part dintaba sbd nauyin ciki dakuma rashin son kusanta kanta da duk inda
zataga ummu-rumanah kokuma zancenta sbd batason kishinta yafi qarfinta qarshe
tayi abinda zata zubarwa kanta mutumci tabarwa kanta da 'yayanta abin fa'da
gashi maheer ma anyi mata iyaka da ganinsa sai baiwarsa tasamu ciki shiyasa ta
kama kanta a part dinta tasamu ta haihu ta tattara takoma Georgia ko zata samu
hankalinta yadan kwanta. 2
Zaune take a palo tana waya
da mum 'dinta cikin sanyin murya tace,
Mum inason nazo gida na haihu
agurinku sbd nasan anan ne nida abinda zan Haifa zamu samu soyayya da qaunar
yanda muke buqata....
Cikin rarrashi mum dinta
tace,
Suhailat my dear kiyi hkr
tunda kinsan a inda kike aure,
Idan kin haihu I promise to
come by Allah's grace my dear,
Kicire damuwa da tunanin
komai sbd condition you're in.,
Wen is your edd???
Saura sati hudu.
Ok akwai sauran time ma ashe?
Yes mum,
Mum can you just give me a
minute I will call you back someone is here.
Aje wayar tayi tareda kallon
Jakadiya data shigo daukeda kaya batai maganaba tagyara zamanta tana jiran jin
mai zata fada.
Kai tsaye jakadiya tace,
Saqon tausar zuciya ne daga
sultana na aure da yarima maheer yaqara ayau Allah ya sanyaya zuciyarki.
Kasa motsi tayi sai ido data
kafe Jakadiya dashi,
Wani irin radadi da ciwo ya
ziyarci zuciyarta da mararta alokaci 'daya
Rintse idanuwanta tayi da
sauri hawayen dasuka cikasu suka gangaro tayi saurin dafe mararta tareda fara
qoqarin tashi sbd jin danshi nabin qafafunta.
Jakadiya ganin halinda
tashiga da jinin dake gangarowa daga qafafunta yasa tayi saurin qarasawa gareta
daidai lokacinda azaba da ciwon suka taso gadan gadan tasaki wani irin kukan
azaba tana dafe cikinta sbd jin axabarda bata taba jiba gurin haihuwa.
Ganin abin yayi muni sosai
yasa Jakadiya bada umarnin aje atahoda masu karbar haihuwa sbd tanasa ran qila
haihuwarce.
A gaggauce aka kirawosu suka
kamata aka shiga daki da ita nan Jakadiya taje ta sanarda sultana
Cikin qanqanin lokaci
masarauta ta 'dauka labarin haihuwar da za'ayi saidai kuma masu karbar haihuwar
sunkasa sbd jini take fiddawa har lokacin ruwan haihuwarta basu fasheba gashi
tafara fita hayyacinta. 5
Cikin gaggawa jakadiya taje
tasanarda sultan abinda masu karbar haihuwa sukace na za'a iya rasa ran
suhailat da abinda yake cikinta.
Jin haka sultan dayace kar
asanarda yarima sbd karyaqi tarewa da rumanah yau amma jin za'a iya rasa abinda
za'a haifa yasa yace asanarda yarima yayi gaggawar bata taimako sbd bayason
arasa abinda ke cikin sbd basusan ko meneneba.
Lokacinda ya isa yaga halinda
take ciki ransa yayi mummunan 6aci sbd ganin irin jinin data zubar sbd baqin
ciki kai tsaye ya fitarda wayarsa yakira khaleefa kai tsaye yace,
Khaleefa ina buqatar tickets
na jirgin dazai tashi acikin daren yau.
Yana kashewa ya matso gefenta
ya zauna tareda riqo hannunta ya share mata zufa da handkerchief dinsa cikeda
kulawa sbd ganin nata yana qara muni.
Fita yayi ya nufi part dinsa
ya shirya luggages dinsa ya canza kaya.
Cikin qanqanin lokaci aka
shiryasu amah.
Koda khaleefa yasanarda
sultan buqatar maheer
Kallonsa sultan yayi yace,
Ka karbo musu ticket shida
Shida mahaifiyarsa da matansa
tareda 'yayansa.
Jin haka khaleefa yaje yayi yanda
zaiyi ya karbo guda shida 'din koda ya dawo harsun gama shiri tuni jakadiya
taje bisaga umarnin sultan ta hadawa ummu-rumanah kaya cikin wasu kyawawan
akwatina marasa girma sosai guda uku tasakata ta canza kaya zuwa doguwar Riga
baqa suka fito.
Sam baisan abinda yake faruwa
aka dauki suhailat dake kwance kamar gawa aka saka mota suka nufi airport.
Sultana da rumanah taredasu
amah kuma suka shiga mota 'daya suka Mara musu baya.
Suna isa Sam bai lurada
rumanah ba aka dauki suhailat akai cikin jirgi da ita yabi bayansu sultana da
yara tareda rumanah da jikinta ke sanyaye suka rufa masa baya.
Amatuqar sanyaye take sbd
wannan shine karo na farko data taba fitowa daga cikin masarautar tun duk
tsawon rayuwarta.
Ganin yanayin suhailat dakuma
ummu-rumanah yasa sultana yanke shawarar qin zuwa Libya binsu zatayi sbd
batasan wani irin riqo su maheer din zasuyiwa rumanah idan basa ganin idon kowa
duk da tasan ba ruwan maheer da ganin idon kowa akan alamarinsa.
Suna shiga jirgi a darare ta
zauna kusada sultana tana kama jikinta kanta a sunkuye har jikin ya daga sama
ta rintse idanuwa tareda qanqame
jikinta.
#mamuhgee
Page 18
Tun acikin jirgi aka fara
bata taimakon gaggawa jinin ya tsaya amma Sam bata farfadoba koba'a fada masaba
mmatsayinsa na likiti yasan ba lallaine abinda ke cikinta ya rayuba musamman
dasuka duba cikin ya daina motsi,
Adduarsa da damuwarsa itace
suhailat ta tsira koda za'a rasa babyn ne. +
Su amah dake taredasu sultana
tuni sukai bacci
Sultana takalli rumanah da
har lokacin bata iya gano yanayinda ta kar6i aurenta da maheer, farin cik
kokuwa sabanin hakan saidai Sam yanayin sanyi na rumanar yakasa saka tagane
yanayinta.
Cikin kulawa da sanyin murya
takira sunanta.
'Dagowa tayi takalleta tareda
amsawa cikin sanyin murya kafin ta sunkuyar dakai.
Rumanah karki sakawa ranki
sbd maraicinki da zamtowarki baiwa duk wannan abin yake faruwa dake
Jarabawar ubangiji ce dakuma
qaddararsa Wanda tuni ya qaddaro miki hakan,
Na tabbarda Allah zai haskaka
rayuwarki sbd kinrugumi qaddararsa da dangana.,
Ina taredake rumanah,ke
amanace agurina bazan taba bari ki cutatuba matuqar inada zarafi da ikon
hanawa,
Naso kubutar dake daga wannan
rayuwar ta hanyar 'yantaki sbd ki haramta ga yarima saidai bansan hakan zai
qarasa hargitsa komaiba sai kuma Allah yayi yanda yakeso bamuda wani ikon
hanawa saidai rumanah qaunar danake miki bazata sa nayi sonkai a wannan
al'amariba
Yanxu ke ba baiwace kinada
iko da ra'ayin kanki matuqar bakya son wannan auren nayi miki alqawarin zansaka
maheer yasakeke zan mayardake masarautar iyayena ki rayu cikin aminci da
kwanciyar hankali.
'Dagowa tayi takalli sultana
Duk wannan alamarin hawaye ko
'daya bai taho mataba sbd tariga ta rumgumi kome yazo da Wanda zaizo amma yanxu
wasu irin hawayene suka ciko fararen idanuwanta takalli sultana ta sunkuyar
dakai tareda rintse idanuwanta cikin sanyin murya tace,
Ta yaya zan bude bakina
agabanki ammy nace banason zama acikin zuriarki,
Har abada ammy kece mai
zartarda hukunci akaina nabisa koda 'yanci koba 'yanci bazan cewa aa ga duk
hukuncinda zai fito daga bakinkiba,
Ni baiwace sai yanda akayi
dani haryanxu ni baiwace agurinki banida zabi sai Wanda kuka zabarmin. 1
Lumshe ido sultana tayi
cikeda tausayin rumanah batason takurata amma zasu bawa wannan auren dama
basusan abinda Allah ya tanada acikinsaba.
Shiru suka sakeyi kowa da
tunanin dayakeyi aransa.
Qarfe hudu na asuba suka isa,
Gida aka wuce da sultana da
rumanah tareda yara shikuma maheer tuni motar asibinsa tazo sukai asibiti cikin
gaggawa sbd yasan ma dole cs zasuyi mata.
Suna isa gidan sultana ta
fito motar da kanta tasaka password na securityn gate 'din gidan sbd tasani.
Shiga sukai driver yayi
parking suka fita yashigar musu da luggage dinsu har first palon dake qasa
kafin ya aje keys din motar ya wuce dama drivern dake kaisu amah school ne.
Da gudu su amah suka nufi
bedroom dinsu bayan Mac driver yakira Carolina a waya yace sundawo tadawo itama
tace gatanan zuwa shiyasa suke murna sbd sunason Carolina tana kula dasu sosai.
Lafiyayyan babban bedroom din
dake gefen nasu amah sultana tace rumanah ta shiga kafin itama ta wuce Wanda
yazamto kamar nata idan tazo.
Jan kayan sultana tayi tabita
dasu tashigar mata har dakin ta ta ajesu kafin tafara qoqarin gyaran dakin
sultana ta dakatarda ita da cewa,
Rumanah kibarshi kiyi sallah
tukuna.
Ba musu tace to tareda ficewa
taje dakinta
Kasancewar batada kwadayin
babbar rayuwa yasa duk tsaruwa da haduwar dakin bata tsaya wani kalle kalleba
ta shiga bathroom tayo alwala tana fitowa ta bude akwatinda takesaka ran zata
samu abin sallah tasamo doguwar Riga da gyalanta ta nada ta fito taje dakin
sultana taga inda take kallo tana sallah takoma ta tayarda sallah.
STORY CONTINUES BELOW
Bayan tagama ta cire rigar
sallar ta zauna shiru tana qara bawa sultana lokaci kafin ta miqe takoma
'dakinta tayi knocking ahankali kafin tabude tashiga cikin ladabi da girmamawa
tace,
Ammy barka da safiya.
Kai kawai ta daga mata sbd
gajiyar da rashin bacci dake tareda ita amma bata iya kwantawa matuqar ba gyara
mata dakin akayiba aka canza bedsheets sbd ankwana biyu ba'a cikinsa duk da
komai nanan lafiya klau ba'a cewama babu mutane acikinsa sbd babu ta inda iska
zaishigo bare yayi qura.
Zanin gadon tafara yayewa
daidai shigawar Carolina dakin nan ammy takalleta cikin turanci tace takawowa
rumanah new bedsheets.
Da sauri ta karbi na hannunta
data cire taje takawo wani fari qal sbd kusan gidan basu cika amfani da kowane
kalar bedsheets ba kamar fari.
Karba tayi ta shimfida tafara
gyaran dakin sbd Carolina taso karba tace tabarsa ita kanta sultana tafison
aikin rumanah sbd itace kawai ke mata aiki yayi mata yanda takeso.
Tsaf tagyara dakin ta wanke
toilet ta kunna AC da burner nan take dakin ya canza ta fice.
Tana fitowa taga Carolina
nata aikin gyara koina an kunna duka ac ac da fridge fridge ta bude store ta debo
ruwa da drinks ta jera ako wane frudge harna sama inda dakunansu maheer da
suhailat suke
tuni gidan ya dauki sanyi da
qamshi masu dadi
Itadai dakinta tashiga tayi
wanka tasaka doguwar Riga baqa ta dawo ta zauna bakin gado tana jiran sultana
takirata asata aiki sbd ita tafi sabawa da aikin wahalar Sam zama guri daya ko
Hutu bata saba dashiba.
Sultana bayan takira maheer
bata shiga itadasu amah bacci suka kwantayi cikin nutsuwa sbd agajiye suke
sunsaba da Hutu su Sam jikinsu bayason gajiya.
A asibiti duk yanda sukaso
ganin ta haihu da kanta abin ya gagara sbd taqi farfadowa duk wata allura sun
mata har naquda suka qwaqwalo mata ta hanyar fasa mata ruwan haihuwa amma shiru
shiyasa suka shiga emergency theater da ita kai tsaye sbd suna gap da rasata
Dan tuni suka gano babyn ya dade da mutuwa.
Bashine yayi mata cs din ba
doctor Edward yayi mata shiyasa haryasamu damar zuwa office dinsa yayi amfani
da wayar office dinsa yakira sultana yasanarda ita halinda ake cikin.
Zama yayi tareda jingina
bayansa jikin kujerar ya lumshe idanuwansa
Kwanakin nan he is in so much
stress daga wannan sai wannan kansa har Sarawa yakeyi sbd baisaba da irin
wainnan damuwarba.
Cikin ikon Allah anyi komai
lafiya aka kaita dakin hutawa Dan har lokacin bata farfadoba,
Lokacinda duba gawar babyn
saida yaji mumman faduwar gaba tareda dafe goshi kafin yasaki boyayyar ajiyar
zuciya sbd ganin namiji ne,
Yana son duk abinda matarsa
zata Haifa masa sbd jininsa ne saidai bazaiso ta haifi namiji ba yanxu sbd
bazai iya bari uwar 'yayansa ta fada cikin harkar sarautar mineelik ba shiyasa
ya godewa Allah Dan shikadai ne yasan meyasa yayi hakan.
Saidayaga komai yadaidaita
jiran farfadowar suhailat kawai akeyi ya nufo gida.
Driver yakira yazo yadaukesa.
Yana isowa babu kowa a palon
qasa sai Carolina dake aikin girka abinci a kitchen yawuce sama kai tsaye.
Komai Carolina tagyara a
saman tundaga bedroom dinsa harna suhailat da palonsu.
Tubewa yayi ya shige bathroom
ya shiga bathtub dinda tuni Carolina ta hada masa ruwan wanka cikinsa masu zafi
kasancewar ya dade baidawoba yasa suka zama masu 'dumi.
Lumshe ido yayi sbd jin
nutsuwa tafara jikarsa.
Ya jima kafin yayo wanka
yafito ya shirya cikin kayan bacci masu laushi ya kwanta cikin gadonsa dake
daukeda pillows masu laushi kusan guda takwas tareda shigewa duvet ya lumshe
lazy eyes dinsa.
Sai qarfe goma sha 'daya su
ammy suka tashi nan kowa yayi wanka yafito palo breakfast.
Batareda sultana ta kalli
Carolina tace taje takira rumanah.
Knocking qofar tayi kafin
tashiga.
Kwance take amma ba bacci
takeyiba tana ganin Carolina ta tashi zaune tana jiran jin mezata fada.
Sanarda ita tayi ana kiranta
ta juya ta fita.
Saukowa tayi gadon ta gyara
hular doguwar rigarta data zame sbd gashinta da baya daure ga tsancinsa ta nufi
qofar ta fita.
A palon ta tararda sultana
zaune cikin doguwar rigarta mai tsada kamar koyaushe saidai duka sarqoqin kai
dana wuya na sarauta datake sawa ko yaushe acan nan babu ko daya ajikinta
saidai sarqoqin qafarta da bata rabuwa dasu.
Sosai tayi kyau cikin simple
shigar shiyasa rumanah tasaki fuskarta da wani qayataccen murmushi ganin kamar
hankalin sultana din ya kwanta ta qaraso gabanta tareda durqusawa cikin
girmamawa tace,
Barka da tashi ammy.
Itama murmushi tayi cikin
sakewa tace,
Rumanah abinci zamuci nace
kifito kuma kisaki jiki nan gidan mijinki ne su amah yanxu tamkar 'yaya suke
agareki saiki ringa kula dasu kema.
Girgixa kai kawai tayi kafin
ta miqe ta nufi Carolina dake jera abinci a dining room tana zuwa ta sakar mata
murmushi tareda karbar mata tray din samosas dake hannunta itakuma ta dauko
sauran kayan suka nufi dining suka aje kafin taje tasanarda ammy angama komai.
Saidatayi serving ammy da duk
abinda tasan tana breakfast dashi sbd ko acan itace tasan komai na abincin
ammy.
Su amah kuwa Carolina ce
tasan me sukeso ita tayi serving dinsu fammah ma abaki Carolina din ta tsaya
tana bata sbd tasaba mum dinta ke feeding dinta idan tanan.
Harzata juya ammy tasata
dawowa ta zauna a takure sbd rashin sabo acan tasaba layi sukebi abasu abinci
suje susamu guri su zauna suci.
Cikin tsananin sanyi take cin
abincin ammy na lureda ita takyaleta sbd tasan zata saba ahankali.
Itace tafara miqewa ta nufi
hanyar kicin Dan taya Carolina gyaran kicin din dakuma girkin lunch.
Bayan su sultana sungama ita
takwashe komai tagyara gurin sbd itadai
idanma batayi aikiba batajin dadin jikinta.
Sultana palo tazauna kallon
wani Arabic progm yayinda su amah sukai dakinsu Dan kallon cartoon.
Bata gane maganar Carolina
itama bata gane tata amma suna kwatanta ganewa ahaka suka fara aiki suna
qoqarin sabawa da juna.
Sai qarfe 'daya da rabi
yatashi daga barci
Ya bude idanuwansa dake
cikeda bacci ya kalli agogon gefen gadonsa yaga time ya lumshe ido ya tashi zaune ya sauko gadon ya nufi toilet
yayi brush yayo alwala yafito yayi sallah azahar yana gamawa ya tube harzai
shiga wanka yadawo yayi amfani da wayar bedroom din yakira wayar palon qasa
Carolina dake kicin ta nunawa
rumanah dake yanka fruits pancake dindata zuba ta fita da sauri.
Tana zuwa ta dauki wayar
cikin girmamawa tace,
OK sir"""bayan
tagama sauraran abinda yafada.
Aje wayar tayi harta juya
sultana ta tambayeta abinda yace ta fada mata cewa yayi akai masa breakfast
dinsa sama maida kallonta ga TV tayi tace takirawo mata rumanah.
Tana zuwa tace,
Ammy gani.
Rumanah ki hada breakfast a
tray kikaiwa maheer sama.
Yawu ta hadiye ahankali
tareda gyada kai ta wuce Dan hadawa.
Sanyi jikinta yayi amma ammy
tafi qarfin komai agurinta,
Shirya komai tayi a tray mai
kyau ta fito palon ammy ta nuna mata hanyar zuwa sama ta juya jikinta nafara
rawa tana qoqarin saita kanta.
Harta fara hawa sultana tace,
Rumanahh.
Cak ta tsaya numfashinta na
fita da sauri ta juyo.
Idan kinje karki tsaya palo
kikai masa har cikin bedroom dinsa. 5
'Daga kai tayi ahankali ta
juya tacigaba da hawa.
#Mamuhgee.
Post a Comment for "TARAYYA 17-18"