TARAYYA 19-20
Page 19
Cikin nutuwarta ta tura qofar
palon tashiga da siririyar sallama taga baya palon ta sake hadiye wani yawun
tana qoqarin daidaita numfashinta da
nutsuwarta ta nufi qofar bedroom din data
gani tayi knocking ahankali sbd sanin bayason hayaniya. +
Jin shiru yasa tasake
knocking din amma shiru ganin kar abincin ya huce tayi laifi kuma ga tunanin
bayason yin mgn ne yasa ta murda cikin tsoro tsoro ta shiga tareda rufe qofar
ta juyo ta tsaya jiran umarni
kanta asunkuye yake jin shiru
yasata dagowa taga baya dakin saitayi tunanin qila yana dayan dakin harzata
juya sai qofar bathroom ta bude ya fito daure da towel a qugunsa light brown
sabo qal murdadden jikinsa da muscles sai glowing yakeyi ruwan wanka na gangara
alamar tsantsin fatarsa,
a tsorace ta kalli qofar
idanuwanta yashiga cikin nasa da sauri ta juya masa baya duk ilahirin jikinta
da muryarta na rawa tace,
Yi,,,ha...kuri ammy tace na..
Tray din hannunta ne ya kufce
sbd rawar da jikinta keyi tayi saurin riqewa tana qoqarin saita nutsuwarta sbd
jin baice komaiba har lokacin.
Bayanta ya qurawa ido duk da
tajuya baya yana iya ganin yanda numfashinta ke fita da qarfi sbd kafadunta
dake sama suna sauka baisan da ita akazoba saidai kuma baiyi mamakin ganintaba
sbd sanin waye ammynsa idan tanason mutum.
Closet dinsa ya nufa yaciro
kaya marasa nauyi,
Wata black transparent Louis vuitton longsleev yasaka da farin wando
na Louis Vuitton sai turarensa na Clive Christian imperial Majesty.
Duk abinda yakeyi ko ajikinsa
baburuwansa da tsayuwarta
Zama palo ya nufo batareda
yace mata qalaba ganin harya fice baice mata komaiba ta biyo bayansa,
A palon ta tarardashi yazauna
yana kunna wayoyinsa daya kashe
Sanin yanda jinin sarauta
yake yasa ta matso gabansa a natse ta ajiye tray din kan table din gabansa ta
bude masa komai cikin tsoro tsoro sbd gudun laifi.
Fridge ta bude ta dauko ruwa
marasa sanyi sosai tazo ta ajiye masa.
Kallonta yayi wannan karon ba
'Dan mamaki sbd wannan shine karo na farko dazaici abinci agidansa da ruwa ajiye
gabansa tun baici abincinba batareda yace akawo masaba,
Koyaushe idan zaici abinci
suhailat da mai aikinta Carolina basa kawo masa ruwa kullum saiyace akawo masa
bayan yayi nisa dacin abincin. 1
Ficewa tayi tasauko ta nufi
kicin suka cigaba da aikinsu.
Bayan mintuna Carolina takoma
takwaso kayan.
Saukowa yayi su amah dake
fitowa daga dakinsu suna ganinsa suka zo gurinsa da gudu suna kiran sunansa.
Daukar fammah yayi yariqo
hannun amah yana cewa,
Heyy daddy's girls.
Zama yayi kusada sultana yana
ajiye fammah kusadashi yace,
Gud morning ammy?
Morning or afternoon maheer
look at the time.
Bai kalli agogonba yace,
Nace ina kwana ne ammy sbd
bamu haduba tun safiyar yau sai yanxu so.....
Murmushi tasaki tareda dafa
hannunsa dake kan nata ta juyo da kyau takallesa cikin kulawa tace,
Yaya suhailat I hope kunsamu
shawo kan matsalar?
Shafa kan amah yayi yace,
Amah take your sister and go
to your room idan nagama mgn da ammy zanzo okkk?.
Tashi sukayi riqeda hannun
juna suka nufi room dinsu da gudu cikin wasa.
Lumshe oily eyes dinsa yayi
batareda yajuyo yakalli ammyn ba yace,
Anmata cs babyn bezo da raiba
Sbd wahalar datasha sosai
bamason ta farko yanxu saitayi 48 hours.
Kallonsa sultana tasakeyi
cikin tausayawa tace,
STORY CONTINUES BELOW
Allah yabata lafiya yakuma
tsare gaba amma babyn mace ce ko....
Kasa qarasawa tayi sbd
faduwar da gabanta yayi na rashin wace amsa zai bata.
Its a boy.
Kallonsa tayi amatuqar
firgice da tsananin mamaki saidai tayi saurin yin istighfar sbd agurin Allah
komai mai yiyuwane.
Shiru tayi zuciyarta na wasi
wasin abinda takeda niyar yi akan zaman rumanah dashi saidai tsoro yafara
shigarta,
Idan dama 'yaya mata Allah
yaqaddaro maheer zai fara haifa kafin yaya maza idan ta tura rumanah gurinsa
tasamu ciki yanxu yaya kenan..
Rufe ido tayi Cikin Cikin
zuciyarta tace,
Ya Allah kasa 'Dan nan daya
shi maheer zai Haifa harsai sunsamu makarin dazai karye abinda ke bibiyar
sarakunan mineelik.
Fitowar rumanah daga kicin
zatazo tambayar ko ammyn nason wani tana ganinsa ta juya tun bata qarasoba
sultana tabita da kallo tana cewa,Allah yakaremin ke 'yar amanata.
Tashi yayi yanufi dakin
yaransa ya tararda suna drawings ya zauna bakin pink gadon amah yayi crossing
legs ya qura musu ido sun saba da dadynsu bamaison magana bane yasa basu damuba
presence dinsa kawai nasasu farin ciki.
Saida maraice yaje asibiti ya
dudduba reports din suhailat sai bayan magrib yadawo lokacin ammy na bedroom
dinta.
Kai tsaye ya wuce sama wanka
yafarayi yasako jallabiya fara qal tareda tareda sakin gashinsa dakeda 'Dan
tsawo ya sauko ya nufi gurin ammy.
Yana bude dakin tana budewa
ta fito harsaida qirjinsu ya hadu da juna tayi saurin ja da baya tana sauke kai
Shikuwa yi yayi kamar baisan
meya faruba ya shigo tayi saurin ficewa.
Dakinta taje tana shiga ta tube
tafada wanka.
Tana fitowa tayi sallar ishai
ta fesa spray ta saka kayan bacci Riga da wando farare masu santsi tana cikin daure gashinta Carolina tashigo tace sultana nakiranta.
Aje daurin gashin tayi ta
dauki diguwar riga bai budadden gaba tasa tareda rufe kanta da hular rigar ta
fita.
Zaune ta tararda ammyn bakin
gado cikin shirin bacci cikeda girmamawa tace,
Ammy gani.
Yauwa rumanah idan kingama
shirin bacci kije sama dakin maheer ki kwana can idan zaki kitafi masa da
tuffa.
To tace kanta asunkuye tareda
juyawa ta fice..
Wannan halin na biyayyar
rumanah akan kome akasata yasa take qara qaunarta.
Bata koma dakiba kicin taje
ta bude fridge ta dauko apples din guda biyar ta jera a glass bowl da 'yar
qaramar wuqa ta fito ta nufi saman.
Sanin qila baya palo yasa ta
bude qofar palon ta shiga ta nufi bedroom dinsa tayi knocking ahankali.
Saidatayi so uku taji shiru
tasan bazai amsaba yasa ta bude dakin tashiga.
Zaune yake yana waya da
doctor Edward daya kirasa yana fada masa wasu results din suhailat dasuka fito.
Gabansa ta isa ta aje kan
table din daya Dora qafafunsa ta juya
Palo taje ta dauko masa ruwa
da cup tadawo ta ajiye daidai lokacin ya gama waya ya miqa mata hannu tabasa
ruwan yakarba yasha
Kamar bazaiyi magana ba yace
bana buqatar apples din yanxu take them back.
Dauka tayi tamayar fridge din
palonsa tadawo ta dauke cup da ruwan dayasha tamayar saita kasa dawowa cikin
dakin ta tsaya qofar dakin tana zullumin komawa kuma bazataso taqi bin umarnin
sultana ba koda kuwa a mafarkintane.
Tun tana tsaye qofar bedroom
din hardai ta zauna bakin qofar dakin ta jingina da qofar ta lufe idanuwanta
tana tunanin rayuwarta yanda ta jujjuyawa yau wannan gobe wancen,
Tafaro amatsayin 'yar bayi,
Tadawo baiwa daga baiwa
takoma tamkar sa 'daka yanxu kuma gata a 'yantatta kuma matar 'Dan sarki
batasan kuma gobenta meta tanadar mataba.
Da asuba ya tashi yayi alwala
yasaka jallabiya da farar qaramar hula yasa ya nufi qofa Dan zuwa masallacin da
dake kusa dasu na wani balaraben qasar.
Yana bude qofa yayi tuntube
da ita kafin yayi qoqarin hana kansa kaiwa qasa tuni ya fada samanta da sauri
suka kalli juna cikeda mamaki yake kallon idanuwanta dake cike taf da tsoro.
Kallonta yakeyi batareda
yadagataba kokuma yayi mgn.
Idanuwansa yamaida kan
qirjinsu dake hade numfashinta dake fita da qarfi yana qara hade jirjinsu.
Hawayen azabarda hannunta
keyine suka gangaro mata kuma bazata iya cewa yadagaba.
Hawayen yabi da kallo kafin
yakalli cikin idonta cikin wata irin murya yace,
Inada nauyine? 20
Rufe ido tayi ahankali tareda
girgiza kai.
Sake kallon idonta yayi
yagano wani Abu yatashi ahankali ya miqe tsaye.
Tashi tayi ta dafa zata miqe
takasa sbd azaba Dan taji lokacinda kashin hannunta ya targade.
Hannun yakalla nantake yagane
taji ciwone yagane dalilin kukanta kenan.
Hannu ya miqa mata cikeda bin
umarni ta kama ya miqar da ita ta juya da sauri zata fice ya riqo hannun tareda
dawo da ita harsaida ta fado jikinsa hular kanta ta Zame.
Juyo da ita yayi suna
fuskantar juna ya zuba mata idanuwansa tareda kamo hannun ya matsa still
idanuwansa na kanta
Rintse ido tayi da qarfi sbd
zafi
cikin lazy voice yace,
Akwai zafi? 4
Saki jikinta yayi daqyar ta
iya girgiza kai.
Mamaki tabasa wani malalacin
murmushi ya fito gefen bakinsa ya sake matse hannun sosai sai kawai ganin yayi
ta zube jikinsa idanuwanta na rufewa. 1
Shiru yayi yaji tabbas suman
azaba tayi ya dago fuskarta yakalleta cikin maqoshinsa yace,
Unbelievable.
'Daukarta yayi ya kwantar a
kujerar palon ya tayarda sallarsa hankali kwance saida yagama tukuna yadauko
ruwa a fridge yazuba mata kadan
Ajiyar zuciya tasaki tareda
bude idanuwanta ahankali
Kan fuskarsa idanuwanta suka
sauka ta lumshe ido tasake budewa sai kawai hawaye suka fara gangaro mata.
Qura mata ido yayi yana
mamakin hawayenta sbd dukkanin alama na ciwon datajine abinda baitaba ganiba ga
suhailat duk kuwa wuya da azaba yanada wuya suhailat tayi hawaye
Ita kuma wannan hawayen nata
na shagwabane tunda daga Dan wannan ciwon sai hawaye.
#mamuhgee
Page 20
Haske writers association💡
+
Not edited.
Dagowa tayi takallesa tana
qoqarin tsayarda hawayenta
Suna hada ido ya miqe tsaye
ya nufi bedroom dinsa batareda yace qalaba ko waiwayenta.
Kallon hannunta tayi dake
radadi sosai tasaka 'dayan hannun ta share hawayenta ta miqe ahankali taja hular
rigarta ta rufe kanta ta nufi qofa ta fice.
Tana saukowa ta tararda
Carolina a palo tana qoqarin fara aikin gyaran gidan sbd su amah zasu school.
Kallonta Carolina tayi cikeda
mamakin ganinta tana saukowa daga saman a wannan time din saidai kuma ba abinda
yashafi aikinta bane sai kawai taci gaba da aikinta
Itama rumanah nauyin Carolina
din taji yasa takasa yimata magana ta nufi dakinta tashige.
Toilet tashige tayo alwala
daqyar sbd ciwon hannunta tafito tayi sallah tana gamawa ta fito ta nufi kicin
saidai duk yanda taso tayi aiki kasawa saidai takoma daki ta zauna ta qurawa
hannun ido tana tuno yanda ciwon yasamu.
Lumshe ido tayi tuno
kalamansa"""inada nauyi ne?"""
Sai a lokacin mamakin
maganarsa yake shigarta
Tasake tuno qaqqarfan jikinsa
saikuma tayi saurin lumshe idanuwa sbd kunyar ganinsa dataji saikuma taji
sanyin qamshin turarensa yashiga hancinta tayi saurin bude ido taga babu kowa
zuciyarta ta buga da qarfi.
Mikewa tayi ta nufi jikin
window ta tsaya
Wani sabon qamshinsa taji
yashiga hancinta har zuciyarta ta rufe fararen idanuwanta ahankali tareda
budesu takoma bakin gado tasake zaunawa har lokacin hancinta da idanuwanta
sunkasa daina jiyo qamshinsa
Zuciyarta takasa sukuni
Rashin sukunin hakan yasata
miqe tafito jiki asanyaye ta nufi kicin.
Duk yanda taso yin aiki a
kicin kasawa tayi sbd rashin nutsuwar datake ciki gashi hannun yafara kumbura
saidai batajin zafin kamar yanda takejinta cikin rudu da rashin sanin abinda
yake damunta.
Kallo Carolina tabitadashi
ganin kamar tana cikin damuwa gakuma hannunta daya kumbura cikin tausayawa tace
taje daki ta huta tana kwatanta mata da hannu.
Murmushi qarfin hali tayi
zatayi magana doorbell yayi qara atare suka kalli agogo da Carolina sukaga
qarfe bakwai da minti goma,
Wanke hannu Carolina tayi ta
fito cikin din ta nufi qofa ta bude.
Dawowa tayi riqeda leda fara
ta kalli rumanah tace taduba mata chips data zuba ta nufi sama.
Knocking tayi ahankali saidai
ba amsa hartagaji bail budeba harta aje saidai tadawo qasa dashi takalli
rumanah tace magani ne batasaniba ko urgent yake buqatarsa gashi bata shiga
bedroom dinsa ta miqawa rumanah tace ta taimaka mata taje gurin sultana tafada
mata kozata kirasa awaya tasanar masa.
Qura mata ido rumanah tayi
sbd sanin bata tada sultana idan tana bacci ataqaicema lokacinda take tashi
bacci baiyiba saidai zuciyarta na fargaba da idan yana buqatar maganin ne a
gaggauce.
Karbar maganin tayi ta fito
palo ta nufi dakin sultana saidai kuma tasamu kanta da tsayawa cak sbd qila
yana cikin wani haline yake jiran maganin.
Juyawa tayi ta nufi saman
tana qoqarin danne faduwar gabanta harta isa ta shiga palon ta nufi qofar
bedroom din tayi knocking.
Shiru ba amsa tasake yin
knocking din still ba amsa
Kasa juyawa tayi ta rabe
qofar dakin gabanta na tsananta faduwa hakama takasa tafiya sbd fargaba.
Jin shiru sosai yasata qara
kwankwasawa cikin nutsuwa tana qoqarin sake kwankwasawa aka bude dakin hakan
yasa saura kadan ta fada masa tayi saurin daidaita tsayuwarta tareda sauke
kanta qasa daqyar ta furta,
Ga saqo aka kawo.
Batareda yakalletaba ya karbi
maganin cikin maqoshinsa yace,
Wait.
STORY CONTINUES BELOW
Cak ta tsaya ya bude ledar
yaciro maganin yaduba ya miqa mata.
Dagowa tayi suka hada ido
danasa dake kafe da ita tasaka hannu takarba hannunta yakalla batareda yaqara
cemata komaiba ya rufo qofar.
Hannunta daya kalla yasa ta
fahimci mai hakan ke nufi takalli ledar maganin tasaki fuska akaro na farko
datayi murmushin daya fito daga zuciyarta tun bayan rasuwar iyayenta.
Baca Juga
Saukowa tayi ta nufi dakinta
ta ajiye maganin ta zauna duk bayan minti qalilan tana waiwayowa takalli ledar.
Qarfe takwas su amah suka
tafi school bayan fitarsu da awa 'daya ya sauko cikin wasu blue black
Balenciaga's suit dogon gashinsa a daure qamshin turarensa na annick goutal mai
sanyi ya ratsa palon sosai wayarsa ce kawai ahannunsa sbd meeting zaije ba ba
asibiti ba saiyadawo zaije hospital din.
Itakadaice a palon itama
fitowarta kenan cikin doguwar riga ash zata dakin sultana sbd lokacinda ake
gyaran dakinta yayi.
Sunkuyar dakai tayi sum sum
tashige dakin sultana.
Tana shiga ta tararda ita
zaune kan couch tana waya cikin girmamawa ta durqusa tagaida da kai ta daga
mata sbd wayar datakeyi. 1
Tashi tayi tafara qoqarin
gyaran dakin cikin dauriya sbd tsananin azabar da hannunta ke mata saidai
bazata iya barima sultanar tasaniba.
Shigowa dakin yayi da
sallamarda shikadai yaji abarsa ya nufi gurin ammyn ya sumbaci hannunta data
miqa masa yana cewa,
Saba'ul khair ya ammy.
Murmushi tasakar masa tareda
katse kiran ta ajiye wayar tana cewa,
Barka da fitowa yarima
maheer.
Kallonta kawai yayi batareda
ya amsaba yace,
Zan fita sainada dawo.
Allah yatsare but did you
take your breakfast?
Kai kawai ya daga mata ya
juya haryakai bakin qofar dakin ya tsaya batareda yajuyo ba cikin husky voice
dinsa yace,
Bani fruits din gaban ammy. 1
Yawu ta hadiye cikin faduwar
gaba sanin da ita yake saidai bazata iya dauka da hannu dayaba dole sai biyu
gashi batason ammy tasanda ciwonta.
Kallonsa ammy tayi cikin
mamaki ganin baya tabacin abinda bashi aka kawowaba.
Cikin sanyin jiki ta aje
pillon dake hannunta ta je gaban ammy ta dauki dan glass bowl din amma tuni
hannunta ya gaza bowl din yafadi qasa ya fashe.
Da sauri ammy takalli fuskar
rumanah din
Da sauri ta durqusa zata bada
hakuri sultana takalli hannunta cikeda mamaki da kulawa tace,
Rumanah hannunki akumbure,
Ciwo kikaji shine kike aiki?
Numfashi ya sauke a
maqoshinsa kafin ya ficewarsa sbd dama abinda yakeson ammyn ta fahimta kenan. 2
Ita kanta tagano dan ammy
tasan taji ciwo yasata daukar Abu mai nauyin da bazata iya dauka da hannu
dayaba saidai batasan dalilinsa nayin hakanba.
Qura mata ido ammy tayi cikin
sigar fada tace,
Meya samu hannunki ya kumbura
haka kamar ma karywa ko targade.
Kallon qofar daya fita tayi
asace kafin ta sunkuyar dakai cikin sanyi tace,
'Yar buguwace nayi.
Yanayinta sultana takalla
taga alamun ba gskia tafada mataba sbd tasan rumanah tun tana jaririya saidai
tasan bata taba yimata qaryaba.
Qofar itama takalla sbd taga
lokacinda rumanah tasaci kallon qofar lokacinda maheer yafita kenan yana sane
da ciwon,
Kodai dama da gangan yasata
daukar Abun?
Maida kallonta kan rumanar
tayi cikin kulawa tace,
Menene kika bugu dashi?
Qofa.
Sake kallonta ammy tayi tasan
tabbas ba abinda tafada din bane taji tausayinta yakamata tace,
Tashi kije zansa maheer
yaduba miki hannun idan yadawo.
Miqawa tayi ba musu ta fice
sbd zata iya cewa tunda take arayuwarta batasanma ya ake musuba a alamari duk
abinda aka sata shitakeyi sbd suma basu taba sata abinda yakaucewa addininta ko
lafiyartaba.
Abinci taci kadan tasha
magani dakuma shafa ta kwanta nan take bacci yayi gaba da ita.
Ranar Carolina ce tayi aikin
komai ita kadai.
Suhailat ta farfado saidai ko
motsin kirki da magana bata iyayi komai sai anyi mata koda su amah suka dawo
school da yamma tareda sultana suka nufi hospital dubo mum dinsu.
Kodata tashi bacci hannun ya
sauka gabaki daya babu wani zafi sosai ta sauko gado ta tube tashiga toilet
tayo wanka da ruwan zafi sosai hannun da jikinta dayaso kamuwa da zazzabi suka
saki tayi sallah ta fito taci abinci nan takama aikin dinner babu bata dogon
lokaci suka gama home made pizza sai boiled vegetables da kuma fruits salad din
yarima.
Itace ke jera abinci a dining
din suka shigo
Shine agaba hannunsa riqeda
riqar suit dinsa ta sama farar long sleeve dinsa kamar yanxune yasata
Kallo daya tayiwa hanyar
shigowar ta sauke kai tana aje cups din hannun ta.
Shi ko kallon inda take
baiyiba duk da acikin idon juna suka fara cikin karo ya wucewarsa sama.
Dagowa tayi tabi bayansa
dakallo yana kaiwa qofa zai shiga ya tsaya cak
Tayi saurin dauke kanta shima
baijuyoba sai yashige.
Ajiyar zuciya tasaki cikin
ranta tana qoqarin daidaita numfashi.
Ammy dake kallonsu tun
shigowarta tasaki numfashi tareda nufar hanyar bedroom dinta tashiga.
Wanka yayi yayi sallar magrib
yana zaune kan sallayar akayi ishai yafito yaje masallaci dagacan yana dawowa
ko shigowa baiyiba hospital yakoma.
Kwance take idanuwanta a rufe
amma hawayen daya gani yasashi sanin idonta biyu yakalli nurses din dake tareda
shi da sauri suka fice.
Shafa fuskarta yayi ta bude
idanuwanta dasuke jajir ta qura masa ido zatai magana ya girgiza mata batareda
yabude bakiba.
Share hawayenta tayi daqyar
sbd nauyin jikinta cikin tsanani sanyin murya tace,
I love you...i love you and
pls always remember it even in the future.
Lumshe ido yayi batareda yace
komaiba ya sunkuya yayi kissing forehead dinta murya daqyar yace,
Time to sleep,Gud night.
Lumshe ido tayi tareda gyara
lullubinta ya sake kissing dinta yafice bayan yaduba file dinta.
Koda ya isa gida babu kowa a
palo sai sultana itama dan tanason ganinsa ne.
Yana ganinta yasan dawowarsa
take jira yayi kissing hannunta yace,
Gud night ammy jeki kwanta
nadawo.
Murmushi tayi tareda miqewa
ta fuskanci qofar bedroom dinta harzata wuce tace,
Gobe inason kayi mana booking
flight zamu wuce Libya nida rumanah zuwa jibi,
Kuma inason kafin natafi da
ita tasan matsayin aurenta sbd idan munje ba dawowa zamuyiba acan inason tasamu
sabuwar rayuwa dan haka kanada zabin iya sauwaqe mata kafin jibi muwuce.
Tana gama fada bata juyoba ta
shige dakinta.
Cak ya tsaya bakin stairs din
tun lokacinda tafara magana harta gama yana waiwayowa tana shigewa.
STORY CONTINUES BELOW
Qofar dakinta yakalla kafin
ya haye yana isa daki ya kashe wayarsa data damesa da ringing batareda yaduba
mai kiranba.
Tubewa yayi yafada toilet
yayo wanka yana fitowa yagama shirin kwanciya ya kwanta.
Gari na wayewa ya qarfe tara
saura ya sauko cikin shirinsa sbd yanada tiyata har biyu yau.
Motsi yaji dakinsu amah yasa
ya tsaya tareda waiwayo qofar tareda tunanin meyasa basu tafi school ba har
time din.
Tura qofar dakin yayi daidai
zata fito saura kadan suyi karo tayi sauri matsawa gefe cikeda jin nauyin rigar
dake jikinta ta bacci sbd ganin Carolina taje kaisu amah school tareda driver
yasa take gyaran koina kafin caro din tadawo ta rage aiki.
Qura mata ido yayi tsawon
mintuna kafin yakalli hannunta ya dauke kai yafice ko gaisuwarta bai tsaya
amsawaba. 1
Saidata tabbatarda ya fice ta
dago kai tareda kallon qofar ta daga hannu daqyar taci gaba da aikinta.
Bayan tagama gyaran dakin
sultana harzata fita cikin kulawa takira sunanta.
Dawowa tayi ta zauna gabanta
cikin ladabi ta amsa.
ki shirya gobe insha Allah
zamu wuce Libya,
Rumanah duk Wanda qaddara da
jarabawar ubangiji tasama ya rungumeta da imani Allah baya taba bari ya
wulaqanta shiyasa nake miki kyakkywan zato sbd ke mai hkr da yarda da qaddarace
dan haka ki yarda da qaddarar dazatazo miki dangane da aurenki insha Allah zaki
samu kwanciyar hankali da kwakykyawar rayuwa Libya.
Gyada kai tai jiki asanyaye
sbd dama tasan aurenta bamai dorewa bane.
Miqewa tayi ta fice.
Tausayinta sultana taji
saidai tasan raba auren shine yafi a rayuwar rumanah din sbd maheer bazai taba
daukarta amatsayin mataba dan haka gwara ya sauwaqe mata su tafi can ko karatu
tasamu tayi har Allah yakawo Wanda zaisota sbd tasan sunyiwa rayuwar rumanah
illar da har abada basa fatan tasan sune sukayi mata wannan illar dan kuwa
qiyayyarsuce zata ture girmansu a idonta shiyasa takeson ta nesantata ma kwata
kwata da mineelik idan tana tareda maheer batai nesa da mineelik ba kuma
shikansa idan yagano wannan sirrin saiya tsani sultan da ita kanta
mahaifiyarsa.
Rumanah na fitowa tacigaba da
ayyukanta jiki asanyaye harsuka gama ta nufi daki tayi sallah azahar tananan
zaune Shiru akai la'asar tayi ta fito suka hau aikin abincin dare.
Suna gamawa Carolina ta nufi
dakin suhailat tafara aikin gyara sbd washe gari da safe akace za'a sallamota
tadawo gida.
Itadai rumanah Suna gama
girki ta nufi dakinta tayi alwala tayi sallar magrib tana idarwa tafara hada
dukkanin kayanta ta shiryasu a akwatinanta biyu tana gamawa ana kiran sallar
ishai tasako wata alwala tazo tayi sallah.
Bayan tagama abinci tafito
taci daqyar sbd ko yunwa ba bataji ta dauki apple daya takoma daki.
Tana shigowa ta tube tashige
toilet tayo wanka ta zauna sanyaye gaban mirror spray na Prada tadaure dogon
gashinta ta zauna zugum.
Qarfe takwas su amah sukai
dinner Carolina tashige dasu tayi musu wanka sukai shirin bacci kafin suka fara
karatu da tab dinsu daganan kowannensu bacci yayi gaba dashi.
Sultana sai qarfe tara da
rabi tayi dinner sbd ganin maheer baidawo da wuriba.
Tana zaune palon tana kallon
news qarfe goma da rabi yashigo yana waya.
Ganinta zaune yasashi
dakatarda wayar ya kashe gaba daya ya zauna gefenta yana gaidata.
Ciro komai na tafiyarsu yayi
ya miqa mata sosai gabanta ya fadi da ganin itada rumanah nedai zasu tafi,
Duk da wani sashe tanason
raba auren amma batayi zaton zai barsu su tafi tareba tayi zaton itakadai zai
siyowa ticket din.
Karba tayi tareda ajewa
gefenta tace,
Wane time ne flight din?
9:00am""""yafada
yana miqewa.
Abiyoka da dinner dinka?
Girgiza kai yayi batareda
yajuyo ba yace,
Abani fruits kawai.
Ajiyar zuciya tasauke sbd
zancen dazata fada amma ta daure tace,
Idan takawo ka rubuto mata
sallamarta sbd nunawa sultan sheda nan gaba.
Juyowa yayi yakalleta kafin
ya juya ya wuce.
Yana shiga dakinsa tubewa
yayi yafada wanka.
Dakanta ta isa kofar dakin
rumanah din ta tura ahankali tashiga da sallama.
Miqewa tayi da sauri ganin
sultana dakanta tazo kiranta cikeda kunya dajin nauyi ta durqusa sbd rigar
bacci kawai ajikinta.
Ganin tanajin nauyi yasata
dauke kai tace,
Kije ki kaiwa maheer fruit.
To
ammy'""""tace ahankali cikin nutsuwa.
Idan kin kai kindawo
inajiranki adakina.
Sake gyada kai tayi.
Saida ammyn ta fice ta miqe
ahankali tareda daukar doguwar riga mai ma6alli biyu agaba da hula tasaka
tafito ta nufi kicin.
A qaramin tray ta zuba ta
dauki qaramar wuqa ta nufi saman.
Sanin baya palo yasa ta murda
tashiga ta isa qofar bedroom dinsa ta daga hannunta dake rawa tayi knocking
ahankali.
Jin shiru harso uku yasata
murda tashiga
Duhune sosai adakin shiyasa
ta tsaya cak tsakiyar dakin.
Ba zato taji anriqo hannunta
tayi saurin rintse ido numfashinta na fita da sauri.
Bedside lamp ya kunna tagansa
tsaye gabanta cikin sanyeda dogon wandon bacci fari qal amma baisaka rigaba
murdadden jikinsa a bayyane ya kafeta da lazy eyes dinsa tuni jikinta yasake
daukar rawa ta aje tray din kan table din tsakiyar dakin ganin zai kufce mata.
Yana ajewa ta Juya taji
hannunsa yariqo nata ta tsaya cak.
Dawo da ita yayi ta baya
ahankali bayanta yahadu da qirjinsa.
Rintse ido tayi numfashinta
na tsananta fita ya zura hannunsa daya ya balle botins din rigarta lokaci daya
ta zame qasa ta fadi
Sake rintse idonta tayi da
qarfi amma ko hannu daya bata daga.
Juyo da ita yayi suka
fuskanci juna yana kallon fuskarta yasa hannu ya zame rigar baccinta
Rigar na barin jikinta tasaki
kuka ahankali ya jawota yasaka cikin jikinsa lokacin kukanta ya tsananta
Sai kawai ya dauketa ya nufi
gadonsa da ita akaro na farko ya hada bakinsa da nata.
#mamuhgee
Post a Comment for "TARAYYA 19-20"