TARAYYA 29-30
29
Not edited
Daqyar
tasamu tayi bacci sbd ciwon kai koda gari ya waye bata fitoba saida dukkaninsu
suka fice aiki tafito daqyar tasha tea takoma daki tayi zamanta ko kallonma a
dakinta tayisa duk da
rabin hankalinta baya ga kallon.
Daga office
ma yau tare suka dawo da wuri sbd driver yaje yadauko suhailat suka biyo suka
daukesa suka dawo gida tana kicin ta hango shigowarsu palo ta lafe taqi fitowa
Suhailat na
maqale da hannunsa suka wuce sama tana fada masa wani zance sai murmushi yakeyi
harda shafo fuskarta.
Harsuka
shige bata daina kallonsu ba ta aje freshmilk dinda tazo sha takoma daki a
sanyaye.
Qarfe takwas
da minti ashirin suke dinner Carolina tazo kiranta inji suhailat tazo suci
abinci.
Batai musuba
ta miqe ta nufi qofa tafito.
Tundaga nesa
take hango wani irin kallo dayakewa suhailat dataci wani irin ado cikin wata
doguwar riga mara hannu black sai qyalli takeyi tana masa magana tana dariya
shikuma saidai ido.
Riqo hannun
suhailat yayi cikin miskilanci yace,
Hmm my wife
is this Talkactive and I don't know wow..
Murmushi
tayi tareda yiwa hannunsa dake riqe da nata kiss tace,
I love you
maheer.
Shafa
fuskarta yayi yace,
Ok time to
eat.
Juyawa
rumanah tayi jiki sanyaye sbd zuwanta gurin zai rage musu jin dadine kawai
musamman suhailat dataga tana cikin farin ciki sosai.
Bayanta yabi
da kallo a sace harta shige dakinta sbd tun fitowarta yaganta sbd dama
hankalinsa na nutsuwarsa nakan qofar.
Abinci
Carolina tazo ta dibarwa rumanah babu Wanda yace tasake kiranta sukaci
abincinsu suka yakoma sama suhailat taje ta taya Carolina shirin baccinsu amah.
Yana kwance
idanuwansa a rufe suhailat tashigo ganin kamar yayi bacci yasata komawa dakinta
tayi kwanciyarta.
Tundaga
ranar rumanah taqara nesanta kanta dasu sbd ganin sunfara mantawa da wanzuwarta
a gidan
Dama aikinta
yaqare tunda tasamu cikin da akeso.
Sati 'daya
kenan basu saka juna a ido ba sbd qauracewa musu datayi har gwara suhailat tana
zuwa dubata duk tadawo aiki sbd sanin lafiyarta musamman yanxu da Cikin yaqara
fitowa.
Yau da wani
irin ciwon kai da zazzabi ta wuni ko ruwa daqyar take iya sha sbd komai taci
sai amai.
Qarfe tara
suhailat tashigo dakinta dubata taganta kwance lamo tayi shiru jikinta yayi
matuqar zafi.
Cikin kulawa
da tausayawa tace,
Subhanallah
bakida lafiya haka shine baki fadaba.
Cikin
dasashiyar murya tace,
Kaina ne
yake ciwo sosai.
Fita dakin
suhailat tayi da sauri ta nufi dakinsa
Koda tashiga
yafito wanka yana zaune sanyeda wandon bacci mai tsantsi black bai sanya
rigarba yacika dakin da qamshinsa da sanyin AC yaqarawa da'di yana zaune kan
kujera ya dora qafafunsa kan table yana waya da ammy.
Cikin 'yar
damuwa tace,
Baby rumanah
batajin dadi sosaifa tace kantane yake ciwo sosai and the condition she's in
kasan ba'ason tana fama da damuwar ciwo ko yayane.
Aje wayar
yayi batareda yakalletaba a miskilance yace,
Mezan mata?
Zaunawa tayi
kusa dashi tareda dafasa tace,
Baby pls
kadubata kasan maganin dazaka bata baza'a barta cikin halinda take cikiba wlh
daga gani kuka ta yini tanayi....
Wani kallo
yayi mata jin abinda tace kafin ya dauke kai yace,
Idan tabaki
tausayi har haka ki kawota naga abinda zan iya yi.
Miqewa tayi
tafice cikin jin dadi.
Daqyar
rumanah ta tashi tabiyota tana tafiya ahankali sbd Sam har cikinta jitake yayi
mata kamar ya kumbura ya danne saman cikinta.
Koda suka
isa dakin rumanah sauke kanta tayi har kusa dashi suhailat takaita ta zauna
Shi ko kallon
inda suke baiyiba yana duba Abu cikin laptop din dake gabansa.
Cikin kulawa
suhailat tace,
Bari naje
nasa carolina ta hado miki abinda zakici kafin kisha magani,ta fice.
Shiru tayi
numfashinta na fita da sauri jinta kusadashi sosai
Shikuwa
aikin gabansa yakeyi sai dai ganin yana neman fara shirme yasashi rufe laptop
din yajuyo ya qura mata idanuwansa.
Jin kallonsa
na yawo ajikinta yasata 'dagowa ahankali takallesa nan take idanuwanta suka
ciko da hawayen masifaffiyar kewarsa dake cinta.
Yana kallo
hawaye suka gangaro daga Cikin idanuwanta ya lumshe ido yasake budesu akanta
Hannu ya
miqa mata babu musu takama tareda fadawa jikinsa tana sakin kukan datake riqewa
duk kwanakin.
Rungumeta
yayi tareda rufe ido yana jin nutsuwarda yarasa duk kwanakin tana dawo masa.
Qanqamesa
tayi tana sake shigewa jikinsa sbd sabuwar kewarsa dake shigarta dukda tana
jikinsa din.
Sun jima
ahaka kafin ta dago fuska ta kallesa shima ita yake kallo tasaki murmushin
cikar buri
Ya shafo
fuskarta zuwa lips dinta yace,
Kukan da aka
yini tanayi na ciwon gske ne kona kewar ammy ne?
Soke kanta
tayi sbd sarai tagano 'dan ammy yake nufi ba ammy ba.
Murmushi
yasaki sbd qin dago kanta datayi sbd kunyar zancen sbd ta tabbarda yariga
yagane shine kukanta shine murmushinta.
Dago
fuskarta yayi tayi saurin rufe idonta ya zura hannu cikin rigarta ahankali
yashafo cikinta
Ta bude ido
tana kallon fuskarsa.
Da ido
yanuna mata cikin yayi kicking tanajin motsin itama musamman yanzu da hannunsa
ke kan cikin saitaji qaunar cikin da maishi sun sake shigarta ta dora hannunta
kan nasa dake kan cikin suka kalli juna sbd sake motsi da Cikin yayi.
Suhailat
data shigo basusan tashigonba ta tsaya cak tareda kallonsu jikinta na 'dan rawa
tayi saurin aje tray din tsakiyar dakin ta fice ko dakinta bata komaba dakinsu
amah taje takwanta kusada fammah tareda Rungumeta ajikinta tana kiran sunayen
Allah.
Basuyi
tunanin suhailat zata dawoba hakama basu lurada abincinda takawoba yabata
fruits din dake gabansa wainada suhailat takawo masa tuni tasha kadan yabata
magani tasha tana kwance jikinsa daganan ko mintuna nawa batayiba bacci ya
dauketa dama akwai na bacci sosai aciki sbd yanayinta daya nuna bata samun
isashen bacci.
A jikinsa
tayi bacci yazare mata doguwar rigar jikinta yazare mata bra yabarta da pant
yasaka mata rigarsa ta bacci duk da ta mata mugun yawa ya kwantarda ita kan
gado tareda rufeta bayan yayi kissing idanuwanta dake rufe.
Kan kujera
yakoma yabude laptop dinsa yanason cigaba da aiki amma yakasa yayi crossing
legs yadauki fruits 'din data rage yana sha idanuwansa nakanta ya zuba mata
yana kallonta nutsuwa nasake shigarsa.
Washe gari
kusan tare suka tashi hannunsa cikin nata suka shiga toilet sukayo alwala sukazo
sukai sallah daganan bacci suka koma Wanda ita rabon datai irinsa ta manta
shikuwa banda kallon fuskarta da cikinta babu abinda yakeyi daga baya yasake
shigar da ita jikinsa ya lumshe ido bacci yadaukesa.
Qarfe bakwai
suhailat tayi shirin zuwa aikinta ta fice ko breakfst bata tsayaba apple kawai
taci bayansu amah sun wuce school.
Sai qarfe
goma suka sauko tana gefensa sanyeda jallabiyarsa datai mata mugun yawa ta nufi
dakinta da sauri sbd batason haduwa da suhailat da rigarsa ajikinta.
Shikuwa black
Gucci trouser ne ajikinsa da black shirt fuskarsa sosai take bayyanarda
annashuwar da zuciyarsa ya nufi dining yana waya da sultan dake sanardashi
abinda ya 'daga hankalinsa na cewar sufara shiri kowane lokaci zasu iya dawowa
gida sbd rumanah a mineelik zata haihu.
To kawai
yace sbd kai karshen zancen dan zai iya samun matsala da sultan din idan yace
aa.
Wata doguwar
Turkish gown tasaka Maroon wadda tayi mata kyau matuqa musamman da cikinta
yafito tayi rolling kanta ta sanyo loafers black tafito tana fidda siririn
qamshin daya zama tamkar na jikinta.
Kai tsaye
dining ta nufa itama tunkan taqaraso ya zuba mata ido yana kallonta musamman
murmushin dake fita fuskarta dayafi 'daga masa zuciya.
Tana zuwa
kusada shi ta zauna tareda duba abincin ta zuba masa Wanda tasan yanaci ta dibi
chips kadan taci da mango mango juice mara sanyi ko kadan sbd tuni yasawa
Carolina dokar karta kuskura kaiwa rumanah Abu mai sanyi.
Suna gamawa
ta sanarda Carolina zata fita ta fice Kodataje yana cikin Mercedes-maybach
exelero 'dinsa da alama shine zaiyi driving din
Taqaraso
tashiga sukabar gidan.
Asibiti suka
nufa,suna isa kai tsaye office dinsa suka nufa
Suna shiga
ya nuna mata quryar resting room din dake cikin office din yace tashiga yana
zuwa.
Shiga tayi
taga harda 'dan madaidaicin gadon hutawa mai kyau a dakin sai couches da table
harda TV da fridge ga split ac dake aiki
Ta zauna kan
couch tareda lumshe ido tana kallon hotonsa dake cikin qaramin frame kan table.
Murmushi
tasaki tareda 'daukar frame din qasan maqoshinta ta furta,
Iwe dihalhu.
Cikin
kunnenta taji ance,
I heard
that.
Saurin
juyowa tayi tana ganinsa ta rufe idanuwanta cikeda jin kunyar kanta.
Ya riqo
hannunta yana murmushi ya nufi gadon dakin da ita yana cewa,
Karki damu
suhailat is kind hearted bazata hanaki mijintaba.
Murmushi
tayi tana zaunawa bakin gadon sbd har lokacin bata daina jin kunyar zancentaba.
Janye
rigarta yayi yafara scanning din cikinta cikin qwarewa harya gama yayi rubutun
dazaiyi fuskarsa batadaina bayyanarda annurin da zuciyarsa take cikiba.
Tayarda ita
zaune yayi suna fuskantar juna ahankali yace,
Babynki
saura wata hudu yazo duniya yaga stubborn mom 'dinsa mai kishi da antyntah
dabatasan tafita son mijintaba ba.
Kallonsa
tayi da sauri jin abinda yace bayan baisan meye sirrin tata zuciyarba saidai
baisan tayi masa kyakkyawan saniba dahar tagano maganarsa is like yana
challenging dinta akan sonda take masa.
Murmushi
tasakar masa tareda kai bakinta daidai kunnensa cikin wani irin salo ahankali
ta furta,
Kanason
tabbatarwane?
Wani irin
murmushin jin dadin daya ratsa zuciyarsa yace,
Tabbatarwar
nake buqata.
Murmushi
tasaki mai qaramin sauti tareda qara 'dora bakinda kunnensa saidataja wani irin
numfashin datasan zai 'daga masa hankali kafin cikin ra'da tace,
Umarni ne ko
buqata?
Kasa haquri
yayi saidaya ha'data da jikinsa ya shafi wuyanta yana sake sakin wani sabon
qayataccen murmushin Shima qasa qasa yace,
Duka.
Tashi tayi
tana 'yar qaramar dariyar data sake burgesa yariqota tadawo jikinsa cikin wani
irin salo tana fadowa ta dora bakinta anasa bayan tayi qoqarin yakice kunyarta
da qarfi.
Cikeda
mamaki da farin ciki mai tsanani yake kallon idonta tayi saurin rufe masa ido
da hannunta 'daya
Nan suka
samu damar kissing juna cikeda kewar juna.
Sai rana
tsaka suka koma gida har lokacin suhailat bata dawoba babu kowa sai Carolina
shiyasake basu damar sakewa a dakinsa sukayi abinda sukaga dama sukayo sabon
wanka suka sauko cin abinci
Ko a dining
sosai yau Carolina take satar kallonsu tana mamakin irin abinda taga yana
faruwa atsakaninsu.
Koda
suhailat tadawo suna sama batai shishigin zuwaba tayi wanka dakinta tashiryo
cikin qananan kaya marasa nauyi bata fitoba sai lokacin dinner kuma suma
lokacin suka sauko
Rumanah na
ganinta taji nauyinta sosai
Shiyasa ko
kallon inda yakeyi bata sakeyiba ta maida hankali gurin cin abincin ta hankali
kwance.
Suhailat ma
bata nuna damuwar komaiba saima qoqarin ganin tasake data ringa mata.
Suna gamawa
suhailat ta matso kusa dashi ta ranqwafo tai kissing hannunsa tace,
Gud night
baby.
Ta juya
gurin rumanah dake qoqarin barin gurin tace,
Gud night
rumanah.
Cikeda kunya
tace,
Allah
yatashemu lafiya.
Dakinta ta
nufa tabarsu suna binta da kallon girmamawa.
Da kansa
yadauketa har zuwa dakinsa ya kwantar da ita ahankali kan gado batareda yace
komaiba ya juya yashige toilet.
Kwananta
biyu agurinsa ranar na ukun tana sane da abinda suhailat ke nufi shiyasa tun
wuri tayi kwanciyarta dan ko agurin dinner tariga kowa tashi tayi musu saida
safe
Shima yagane
mai suke nufi shiyasa bai damuba ahaka suhailat tagama kwananta biyu saidai
kuma kwanan biyu bata yisu cikin lafiya ba sbd wani irin zazzabi da ciwon kai
datake fama dashi.
Tashin farko
dayayi mata test cikin wata uku ya bayyana ajikinta Wanda ya basa mamaki ta
yanda bai taba luraba ita kuma dama tasan da abinta kawai taga tunda bana farko
bane kuma akwai wadda tafita buqatar kulawa tunda ita natane na farko shiyasa
kawai tabarwa kanta.
Rungumeta
yayi cikin nutsuwa yace,
Thank you
suhailat.
Shafo
fuskarsa tayi cikin qaunarsa tace,
Why are you
thanking me?
Sbd you're
always given me happiness.
Murmushi
tayi tareda taba hancinsa tace,
Ka godewa
Allah not me.
Ina godewa
Allah koyaushe daya bani best wife datake qaunata,
Ina fatan
komai na zama anan gaba zaki cigaba da sona bazaki barniba.
Hakanan taji
faduwar gaba tareda tausayin kansu tace,
I promise to
be with you and support you komai rintsi komai wuya koda akan abinda kakesone.
Rungumeta
yayi jikinsa da zuciyarsa na shiga wasi wasin komai zaizo gaban.
Ranarda
cikin rumanah yacika wata bakwai na suhailat yacika wata biyar mumman saqo ya iso
daga mineelik na 'daukar rumanah da suhailat dan zuwa haihuwa.
Lokacinda
yakira ammy yasanarda ita atake tafara shirin komawa mineelik 'din tsoro da
fargabar data danne na dawo mata sabo.
#mamuhgee
[12:36 AM,
7/30/2019] +218 94-4138736: TARAYYA
wattpad@mamuhgee
Haske writers association💡
30
ita soyayya
da fahimtar juna Allah ne yake sakata acikin zukatan wainda yaso kuma babu wani
shedani daya isa ya raba abinda Allah ya hada sbd shi daya hada yasan abinda
yasa yahada dan haka soyayya da qaunar dake tsakanina da daughter na BILLYN
ABDUL babu wani shedani ko munafukin daya isa yashiga tsakani bare yaraba
Wasu sunso
hada fitinar cewa labarinmu yazo 'daya to ai dama dole labarinmu zaiyi
kamanceceniya sbd ra'ayinmu 'daya shawararmu 'daya abinda yake gudana aranmu
'daya to mezai hana labaranmu kamanceceniya?
Naso
dakatawa sbd wasu dalilai saidai hakan na nufin mundakata gaba 'daya daga TARAYYA har RAINA KAMA sai munafukan
dake cewa 'dayane su qarasa labarin tunda dayane ai bazai musu wuyaba saidai
kuma masoyi duk inda yake yafi maqiyi shiyasa muka bar komai ya wuce kuma kuji
da babbar murya duk munsanku masu halayen kafiran farko
MAMUH DA
BILLYN ABDUL BAZAKU TA6A GANINSU YANDA KUKESOBA
Tarayya daga
yanzu har gamawarsa sadaukarwane ga daughter na BILLYN ABDUL💋
Z B I i love
you guys as much💋
sorry wainda
ban daga wayarsuba da kuma basu reply na massage dinsu
naga masoya
nakuma gode🤝
Not edited.
Ammy na gama
waya da maheer din jikinta yayi sanyi matuqa sbd Dama tasan hakan na zuwa sbd
tun barowarsu mineelik tasan sultan yazuba tsaro sosai akansu ta yanda duk wani
motsinsu arayuwarsu yana sane dashi saidai batai tunanin zai nemesu da wuri
hakaba.
Shikuwa
lokacinda saqon ya Isar masa yana hospital kallo 'daya yayiwa abaas dameer
aqeel da sultan ya Aiko takanas daga mineelik din ya dauke kai tareda 'daga
masa kai alamar yaji yabasa guri,
Rufe ido
yayi tareda jan 6oyayyan numfashi.
Da wuri
yadawo gidan koda yashigo rumanah ce kawai a gidan tana dakinta kwance tana
bacci sbd kwanakin Sam bata cika lafiya ba sbd girma da nauyin cikinta.
harya taka
steps biyu na zuwa dakinsa ya tsaya cak tareda juyowa yakalli qofar bedroom
dinta,
Yau gaba
'daya baiganta ba sbd suhailat ce keda kwanan kuma tunda safe yafito shiyasa
gabaki daya yau ya rasa gane kansa ga qarin saqon sultan daya riskesa.
Juyowa yayi
yadawo ya nufi dakinta batareda yayi knocking ba yashiga tareda turo qofar.
Kallonta
yayi yanda ta tayi kwanciyar tana dafe da cikinta da alama hannunta nakan cikin
tayi baccin.
Sanyin ac
dayayiwa dakin yawa yakalla tareda qarasawa yadauki remote yarage ac din.
Baca Juga
Bakin gadon
yazauna tareda zuba mata ido tsawon lokaci ya lumshe ido yabude ahankali
yanajin wani irin yanayi mai zafi game da ita.
Riqo
hannunta yayi ya matse cikin nasa ya rufe ido yana qoqarin yakice fargabar
datake shigarsa akanta,.
Ahankali ta
bude idanuwanta ta zuba a fuskarsa tana masa kallon mamaki sbd baitaba shigowa
dakinba a iya sanintama baya shiga dakunansu.
Qoqarin tashi
tafarayi ya mayar da ita tareda girgiza mata kai ahankali still yana kallonta.
Mamakine
yasake kamata ganin yanda yake kallonta cikin wani yanayi.,
Ahankali ta
furta,
Dehina
neh?(are you ok?)
Lumshe ido
yayi tareda 'daga mata kai.
Cikeda wani
sabon mamakin takallesa sbd ganin ya amsa mata ba kamar yanda yasaba zuba maka
ido ko shareka idan ka tambayesaba.
Kasa 6oye
mamakinta tayi hakan yasashi sakin Murmushi yana sake damqe hannunta dake cikin
nasa murya a shaqe yace,
Kinshirya
ganin ammynki?
Saidata
kalli cikin idonsa tasaki murmushin kwanciyar hankali ta daga kai.
kinason
komawa mineelik?
Ba zato taji
tambayar takallesa gabanta na faduwa takasa cewa komai.
Kwantawa
yayi jikinta zuciyarsa na qara shiga wasi wasin kaita haihuwa mineelik.
Kallon fuskarsa
tayi taga idanuwansa a rufe tasan baya buqatar hayaniya alokacin
Sai kawai
tayi shiru tareda lumshe nata idanunwan tareda sake riqe hannunsa dake cikin
nata itama.
Sun jima
ahaka har bacci yadaukesa itadai kasa baccin tayi ta zuba masa ido hankalinta
yaqi kwanciya Sam da yanayin data lura yanaciki.
Maida
tunaninta ga maganarsa ta zuwa mineelik dayace tayi taji gabanta yayi mugun
faduwa,
Tabbas tasan
zata koma mineelik haihuwa saidai duk lokacinda ta tuno hakan hankalinta na
matuqar tashi sbd jikinta na bata idan takoma shikenan ta rasa maheer,
Maheer
yazamo wani babban 6angare na rayuwarta,
Yazamo
zuciyarta datakejin bazata iya rayuwa babusaba,
Shine uban
abinda zata Haifa saidai tanajin kamar tafison kasancewa da maheer din akan
abinda zata Haifa dan idan ta tuno abinda ke cikinta mineelik da zagayenta suke
jira ta haifo aga ko menene ke qara bata tsoro da daga mata hankali.
Baccin
baiwani dadeba ya farka kansa na 'dan ciwo ya kalleta da sauran bacci a
idanuwansa yace,
Ki daukomin
kaya zanyi wanka anan.
Saukowa
gadon tayi ta nufi qofa yabita da kallon tausayinta da qaunarta mai qarfi sbd
ganin girman cikinta cikin laushin murya qasa qasa yace,
Hey.
Tsayawa tayi
tareda juyowa ya tashi zaune tareda lumshe ido ya miqa mata hannu ahankali.
Jitayi
zuciyrta tasake sanyi ta dawo ahankali ta kama hannunsa ta zauna gefensa sukayi
shiru dukkansu sai can yasaki ajiyar zuciya ahankali yana dago da fuskarta suka
kalli juna ya shago cikinta cikin wani irin yanayi yace,
Allah ya
albarkaci zuriata.
Dora
hannunta tayi kan nasa cikin sanyin murya ta furta amin.
Tashi yayi
yakama hannunta cikin kulawa suka nufi toilet yayi wanka yayo mata,
Sosai yake
cikin wani irin tunanin yanda zaiyi nisa da ita idan suka koma mineelik sbd har
cikin zuciyarsa yakejin duk wani laulayin cikin datake ciki.
Suna fitowa
da kansa ya bude wardrobe ya dauko mata doguwar rigar chiffon mara nauyi yasaka
mata,tasaki murmushi tana kallonsa ta madubi yanda yake gyara kansa.
Tsayawa yayi
yana kallon Murmushinta qasa qasa yace,
I'm all
yours zaki iyayin abinda yafi kallonma.
Zaro ido
tayi cikin wata muguwar kunya ta miqe da sauri zata bar gurin yadawo da ita
tareda Rungumeta ta baya jikinsa da babu kaya ya hadu da bayanta da kusan rabi
yake abude sbd yanayin rigar.
Shinshina
gashinta yayi tareda lumshe ido yana sake matseta jikinsa sbd tuni tasakar masa
da sabuwar kasala bakinsa yakai kunnenta cikin kasala yace,
Meyasa
zakiji kunya bayan kinsan yes you have all the rights kiyi abinda yafi kallon.
Qanqamesa
tayi cikin wata sabuwar kunyar tace,
Please
kabari.
Ba musu yayi
shiru yana murmushi tareda mayarda hannunsa kan cikinta ya lumshe ido ya bude,
Allah ne
kawai yasan irin son dayakewa cikin jikinta sbd ganinta daukeda cikinsa ke
sakar masa nutsuwa da wani irin farin ciki sbd ganin ita 'din dai tasace
mallakarsa,gonarsa,hurumsa da babu Wanda ya isa tunkarowa duk fadin duniya,
Gonarsa da
babu Wanda ya isa yayiwa kallo biyu batareda yasa anraba kansa da gangar
jikinsaba,
Allah ya
'dora masa son amah fiyeda dukkanin sauran 'yayansa da abinda ya mallaka kuma
bayajin zai samu wani 'da ko 'yar dazaiso kamar amah 'dinsa sbd tsananin
soyayyar yarinyar ajinansa take tun ranarda aka haifi har zuwa yanzu,
Abinda ke
cikin rumanah kuwa tun 'yanxu yanajinsa cikin azuciyarsa sbd shine abinda yake
nunawa duniya gabaki 'daya rumanah tasace shikadai shiyasa yake tsananin qaunar
cikin tunkafin yazo duniya.
Fuskarsa ta
shafo tana Murmushi tace,
Kana tunanin
mezan Haifa ne?
Kallonta
yayi yakalli cikin ya riqo hannunta cikin nasa cikin yanayi na sanyin murya
yace,
Bana tunanin
mezaki Haifa ta 6angaren jinsi sbd agurina ko me zaki haifa shine babban abinda
zai cigaba da sakani farin ciki har abada sbd shine fitilarda take haskomin abu
mafi soyuwa azuciyata.
Sanyi
jikinta yayi takallesa da idanuwanta dasuka ciko da hawaye tasake riqe hannunsa
cikin sanyin murya tace,
Ko agurin
haihuwarsa na mutu ayanzu nasan bazaiyi maraici kamar niba,
Abinda yake
cikina shine hasken rayuwata sbd shine cikakkiyar shaidar soyayyata da batada
mahadi,
Shine abu
mafi soyuwa a zuciya da rayuwata sbd shi tsotsonkane saidai bansaniba ko zan
cigaba da zama uwa agaresa kamar yanda nake mafarki.....
Rufe mata
baki yayi yana kallon idonta yace,
Har abada
kece zaki zauna amatsayinki na mahaifiyarsa babu Wanda zai rabaki da abinda
zaki Haifa....
Mutuwa ko
qaddara "" tafada muryarta na rawa sbd tsoro da fargabar dake
shigarta.
Girgiza mata
kai yayi da sauri tareda Rungumeta cikin wani irin yanayi daya bata mamaki
yace,
Ina roqon
Allah daya cigaba da azurtani da 'yaya mata daga dukkanin matana.
Ajiyar
zuciya ta sauke ahankali ta furta amin saidai hankalinta yariga yatashi sbd
ganin shima bayason ta haifi namijin sbd guje mata arabata da 'danta da
mijinta.
Shiru sukayi
tsawon mintuna saida suka samu nutsuwa kafin yatashi suka fito ya nufi dakinsa
ya shiryo yana saukowa suhailat tashigo agajiye sbd cikinta dayayi girma itama.
Cikeda
tausayinta ya ware mata hannu ta rungumesa yayi kissing goshinta batareda yace
komaiba.
Cikin kulawa
tace masa,
Thank you
baby"" sbd tasan sannu yake mata da gajiyar dayaga ta debo koda baiyi
maganar ba.
'Dauke kai
rumanah tayi tareda juyowa ta nufi cikin ahankali zuciyarta na bugawa da sauri
sauri.
Bayanta yabi
da kallo jikinsa na sanyi
Ganin yanda
yayi yasa suhailat juyawa taga rumanah ce harta kusa shigewa kicin
Ta juyo
takalli idanuwansa taga yanda yanxu soyayyar rumanah bata 6oyuwa acikinsu duk
kuwa da iya qoqarinda yakeyi dan boyewar amma soyayyarta tafaracin qarfinsa sai
kawai taji yabata tausayi tasaki murmushi qarfin hali ta dafasa cikin sanyi
tace,
I will go
and freshen up.
Tana fada ta
wuce idanuwanta na cikowa da hawayen tausayin kanta da rayuwarta nan gaba sbd.
Ya lurada
halinda itama tashiga yabi bayanta da kallo tausayinta nasake kama zuciyarsa ya
zauna sofa yana sake kallon qofar kicin cikin damuwa.
Da daddare
gurin dinner kowa nacin abinci cikin nutsuwa da rashin sukunin zuciya ya 'dago
ya kalli rumanah dake cin fruits kawai yaji damuwar hakan sbd batason cin
abinci saiya sakata dole idan suna sukadai kenan sbd lurada hakan yasa wani
lokacin suhailat ke qin cin abinci a dining taredasu sbd su sake saitace akai
mata daki.
Bayan
sungama harzai bar dining din yacewa Carolina data qaro drink taje ta dafo masa
noodles kadan a plate.
Suhailat
najin haka tasaki murmushi tace,
Ok baby
nizanje na kwanta bacci nakeji sosai so gud night.
Riqo
hannunta yayi yana kallonta yace,
Zamu koma
mineelik this weekend so idan kinje office kiyi magana dasu.
Ok tace
gabanta na faduwa akaro na farko taji ankirama sunan mineelik hankalinta
yatashi bare dataji zasu, asanyaye ta nufi dakinta tashige dama yau take fita
girki.
Kallon qofar
dakin rumanah yayi yanufa yashige lokacin harta gama shirin bacci.
Da mamaki
takallesa ya qaraso bakin gadon ya hau ya kwanta yana lumshe ido.
Ranar asabar
suka wuce Libya dukkaninsu sbd lahadi zasu isa mineelik gashi lokacin cikin
rumanah yashiga wata na takwas suhailat kuma wata shida kuma sosai yake bata
matsala sbd cs dinta shiru kawai tayi sbd batason dagawa maheer hankali saidai
Sam batajin wannan karon cikin nada lafiya kamar sauran cikin datai tayi nasu
amah.
Lokacinda
ammy tayi ido biyu da rumanah da cikinta jin tayi hawayen farin ciki sun ciko
idanuwanta sbd Allah ne kawai yasan iya adadin qaunar datakewa rumanah gashi
tana 'daukeda cikin maheer 'dinta datafi kaf cikin 'yayanta.
Rungumeta
tayi cikeda farin cikinta daya kasa 6oyuwa
Rumanah ma
batasan haka tayi kewar ammynba saidata ganta hawaye suka ciko idanuwanta ta
rungume ammyn tana cewa,
Ammy nayi
kewarki sosai.
Cikin farin
ciki sosai ammy ta zaunar da ita tana cewa,
Rumanah babu
ranarda ammynki bata kewar kulawar dakike bata.
Murmushi
tayi tace,
To ammy
aigashi nadawo.
Kallon
maheer daya shigo lokacin tayi tace,
Ko kindawo
babu ruwan ammy dasaka matar mutane aiki bayan ga yanayinda ma take ciki.
Yagane ammy
dashi take yayi kamarma baijiba ya qaraso gurinta suka rungume juna yace,
Nafekushy ya
Ammy.
I miss you
too maheer""tafada tana sakinsa takamo hannun suhailat dake tsaye
bayansa tana Murmushi ahankali
Tace,
Suhailat
yakuke?da yaran duka.
Lafiya klau
ammy munsameku lfy?
Alhmdllh
zoki zauna suhailat kinji sannunki.
Zama sukayi
rumanah kuwa sashen s salma ta nufa acan s salma ba qaramin farin cikin ganin
rumanah tayiba harda tsokanarta tayi da cewa,
Yanzu bada
dadewaba zansa akira aarib yazo dalibarsa tadawo.
'Yar qaramar
dariya tayi tace,
Idan yazoma
babu ruwanah da abinda zai samesa.
Dariya s
salma tayi tace,
Eh mana
tunda miskilin mijinki nanan dole zakice haka.
Tsayawa yayi
bakin qofar yana kallon yanda tasake take magana sosai da s salma baitaba ganin
tayi surutu sosai hakaba musammanma dariyar datake tayi hankali kwance cikin
farin ciki kamar ta dauwama cikin farin ciki haka harwarshen rayuwarta.
Qamshinsa
yashiga hancinta ta juyo ahankali takalli qofar suka hada ido murmushin dake
fuskarta bai daukeba taci gaba da kallonsa soyayyarsa mai qarfi nasake shigarta
musamman irin kallon dataga yana jefota dashi,
Ahankali
yaqaraso cikin babban palon yazo gabanta ya zauna kusada ita yana sake kallon
Murmushi da farin cikin dake kwance fuskarta.
Cikin
tsananin farin ciki s salma ke kallonsu tace,
Allah
yadauwamarda farin ciki mai darewa a rayuwarku da abinda zaku haifa.
Kallonta
sukayi atare suna amsawa da amin acikin xuciyarsu.
Sake
kallonta yayi sosai zuciyarsa ke tsumayin son sake ganin dariyarta data dauki
hankalinsa fiyeda komai.
Ganin irin
kallon da yake mata ta fara qoqarin miqewa ya riqe hannunta ta zame ta miqe ta
nufi dakin s salma tashigewarta tana Murmushi.
Da kallo
yabita itakuma s salma nabinsa da kallo tana tausaya masa da irin soyayyar data
hango yana yiwa rumanah sbd tasan atarihin mineelik soyayya itace mugun makamin
dazai kashe mai ita ko tabarbare rayuwarsa sbd tana cikin asalin asalin masifar
datake bibiyar masarautar musamman data hada da haqqin mutenan 6oye dabasa
yafiya musamman ita rumanah dasukewa gujewar haihuwar namiji sbd nesantata da
kujerar mulkin mineelik.
Wani
6oyayyan murmushi yasaki Wanda zaiyi wuya ga gani ya miqe bayan sun 'dan taba magana
da s salma Wanda gabaki dayan Rabin hankalinsa na cikin dakin s salma Wanda duk
tana lure saikuma taji jikinta yayi sanyi sbd tausayinsa.
Dakinsa yaje
yayi wanka yayi sallah ya nufi gurin sultan jalaluddeen.
Suhailat
agurin ammy tayi zamanta tayi wanka itada yara da Carolina sukaci abinci tana
gama sallolinta baccin gajiya yayi gaba da ita.
Ammy Palon s
salma ta nufa sbd ganin rumanah ta qaurace masu takoma can wanda tasan qila sbd
suhailat su samu sakewa tabar nan din.
Acan abinci
sosai s salma tasa taci sbd maheer daya bar mata saqon ta tabbarda rumanah din
taci abinci.
Ammy data
shigo kuyanga daya a bayanta daukeda qaton tray cikeda abinci masu qara lafiya
kala kala tace a ajiye gaban rumanah dake zaune tana cin boiled vegetables.
Cikin kulawa
ammy tace,
Rumanah
saurake suhailat taci abinci hanacan tana hutawa.
Kallon ammy
tayi kamar zatayi kuka tace,
Ammy gashi
naci abinci naqoshi amma anjima zanci insha Allah.
Sam ammy
bazataso takurataba tace to ki tabbatarda anjima kinci.
To ammy
insha Allah.
Har dare
tana gurin s salma bata komaba ammy so biyu tana dawowa kawo mata abinci da
samuwar dafaffiyar madara mai zafi Wanda suke famar dirka mata da wasu maganin
haihuwa lokacinda ammy tagama bata saida hawaye suka gangaro mata ta riqe
hannun ammyn cikin wani irin yanayi na tsananin qaunar ammyn tace,
Nagode ammy
sbd kinzamo uwar data kasa bawa maraicinah damar juya rayuwata,
Kin maye duk
wani gurbi da uwa take dashi arayuwata sbd kin qaunaceni tun ina a tsumman 'yar
baiwa harna girma amatsayin baiwa nazamo mutum mai 'yanci ayanxu,
Bazan taba
sakamiki da soyayyar dakikeminba amma nayi miki alqawari bazan ta6a zama butulu
mai manta akhairinki agareniba zan cigaba da zama tamkar baiwa agareki har
qarshen rayuwata sbd kece kikabani abu biyu danafi so arayuwata 'yanci da......
Kasa fada
tayi sbd nauyin ammyn saidai ko bata fadaba ammyn tasan maheer take nufi
Tausayinta
da sabuwar qaunarta tareda zancenta yasa jikin ammy mutuwa matuqa cikin sanyin
murya tace,
Rumanah ina
qaunarki ne aranarda kika fado duniya tamkar 'yar dana Haifa nakejinki shiyasa
nakeso kiyimin alqawarin komai zai faru har abada bazaki daina kallona kina
tuno matsayina na uwa agarekiba wadda bazata taba yin wani abu dan cutatarwa
agarekiba.
Da hawaye a
idanuwanta tace,
Ammy nayi
miki alqawarin har abada zan kare martabarki ta uwa dakike da ita agareni.
Rungumeta
ammy tayi tashin hankalinta da fargabarta tareda tausayin rumanah nasake ninkar
mata.
Har dakin
dake palon s salma ammy taraka rumanah ta kwanta sukai saida safe ta fito ko
tsayawa gurin s salma data shiru cikin jimamin zancensu ta fice.
A palon ammy
yaci abincin dare yana gamawa ya wuce dakinsa ya kwanta duk da zuciyarsa na
kwadayin ganin 'daya daga cikin matansa.
Washe gari
qarfe goma na safe masarautar tacika da baqin mineelik Ethiopia sbd daukar
matan yarima maheer uwayen magajin mineelik tareda sultana zaarah da aka mayar
mata da matsayinta lokacinda labarin cikin rumanah ya isa ga sultan.
Harda
jakadiya da itace zata karbi ragamar kulada cikin rumanah tun daganan Libya
harzuwa haihuwarta.
Lokacinda
aka fito da rumanah cikin wani irin shiri na adon doguwar royal gown cikinta
yafito sosai tana tafe kusan bayi da guards goma zuwa sama Suna bayanta.
Kallonta
ammy tayi jikinta na sanyi
Jakadiya ma
cikin ta qarawa ido numfashinta na fita da sauri tasaki ajiyar zuciya.
Gogan kuwa
tunda yaga abubuwa sunfara canxa masa daga yanxu ya rintse ido tareda budesu
yayiwa Jakadiya kallo 'daya tagano manufarsa ta qarasa ta tarbi rumanah din ta
suka nufi motar da zaishiga aka bude mata tashige nan kowa yashiga motocin suka
nufi airport.
Tunda suka
shigo motar hannunsu suke sarqe dana juna saidai babu mai iya magana acikinsu
dan kowanne da halinda zuciyarsa take ciki.
Ko acikin
jirgi tafiyar babu Wanda yake iya magana acikinsu sbd kowa da abinda yake kai
kawo acikin zuciyarsa.
Suhailat dama
tuntuni tasan ita farin ciki yaqare arayuwarta daga ranar da mijinta yafara son
rumanah musamman yanxu datakejin duniyar dakomai ya fice mata arai gashi ciwon
dakecinta yafara fin qarfinta musamman yanxu datake yawan ciwon mara mai
tsanani.
Qarfe hudun
asuba jirginsu ya sauka a Ethiopia.
Matse
hannunta dake cikin nasa yayi ta juyo takallesa da idonta dasukai ja sbd
tsananin damuwar dake ziciyarta.
Ahankali ta
zare hannunta ta miqe ta wuce gaba su Jakadiya da sauran suka mara mata baya
tana qoqarin maida hawayen dake qoqarin zubo mata.
Bayanta yabi
da kallo idanuwansa na canxawa
Hannunsa
suhailat ta riqo idanuwanta cikeda hawaye cikin rawar murya da kulawa tace,
Zan zamo
bangon jinginarka aduk lokacinda kake buqatar hakan.
Rintse ido
yayi idanuwansa naqara canxawa suka fito jirgin.
Motar
rumanah daban ita kadai da masu tsaronta kuma itace agaba sai sauran nasu
lokacin gari baigama haskeba.
Ruwa yaji
ankelaya masa yayi saurin bude ido yatashi a matuqar zafafe saiyaga jini kaca
kaca a jikinsa da sauri yatashi tsaye aka mayar dashi zaune da qarfi tareda
dora masa wata doguwar takobi mai tsananin kyallin sbd kaifinta tsoro bai
kamasa sbd dama yasan hakan zata iya faruwa ko yau ko gobe....
Cikin wata
irin murya data amsa amo har cikin qwaqwalwarsa yaji ance"""asauke
kansa Daga gangar jikinsa a qawata qofar shigowa masarautata dashi kowa ya
'dan'dana kalar mulkin assultana the redblood Queen.
Daga takobin
akayi da qarfi za'a sare kansa yayi wani irin yunquri yana hada mugun zufan
daya jiqa dukkanin jikinsa yakalli adama dake gefensa itama ta farko tana hada
nata zufan da alama itama wani mugun mafarki tayi kamar shi sbd harma tafisa
rudewa sbd rawar da jikinta keyi.
Saukowa yayi
kan lafiyayyan qaton gadonsa yanajin wani irin tashin hankali na shigarsa busar
data cika masarautar tashigo kunnensa kenan su maheer sun iso.
#mamuhgee
Post a Comment for "TARAYYA 29-30"