TARAYYA 33-34
33
A gaggauce
Cikin
tsananin tashin hankali Jakadiya tasa akayiwa Dr ammenen kiran gaggawa koda ta
iso itama hankalinta tashe yake da jin abinda yafaru atake suka
fara qoqarin
tsayar da jinin daqyar yarage zubowar sosai saidai bata farkaba sbd allurar
dasukai mata sbd jininta yayi matuqar hawa mai muni idan ta farka awannan halin
zata iya samun paralyz.
Sai bayan
sunbaro gurinta aka sanarda maheer abinda yasameta lokacin yana qoqarin ganin
rumanah ta farfado sbd duk iya abinda zaiyi ta farfado yayi bata farfadoba
tashin hankalinda yake ciki yanxu yafi kowane tashin hankali na rayuwarsa,
Rasuwar
yaransa gakuma halinda rumanah take ciki yanxu kuma ana fada masa suhailat
ma...dafe goshinsa yayi tareda fitarda numfashi mai qarfi da zafi idanuwansa na
sake canzawa.
Ammy sbd tashin
hankalinda take ciki ko tsayuwa sosai bata iyayi tsaye take gaban gawarwakin
yaran a palonta kallo daya tayi musu ta dauke kai hawaye na ciko idanuwanta sbd
ganin yanda kalar jikinsu takoma mai duhu sbd dafin daya shiga jini da
jijiyoyinsu sosai.
Zaman
dirshan Jakadiya tayi tareda dora hannu 'daya akai tana jinjina wannan baqar
rana data zo musu koda suke tsananin buqatar haihuwar maza gashi ansamu mazan
amma tun ranarda aka fara naqudarsu masifa tafara saukar musu saidai wannan
masifar dasuke ciki yanxu mai hadari ce sbd koda misali sunanka yafito cikin
wannan zancen mutuwace hukuncinka..
Jikinta na
rawa ta miqe ta dauki gawar su biyun ta nufi fada qafafunta na wani irin rawa
daqyar ta iya kai kanta gaban sultan ta zube tareda shimfidesu ahankali tana
furta,
Tuba nake da
kawo mugun gani gaban sultan da muqarabansa.
Kallo daya
yayiwa likitan gargajiyansu ya taso yazo gaban yaran ya durqusa yadauki abeel
Hussain yadubasa tareda zura hannu cikin bakinsa ya Ciro yakalla ya kalli
sultan ahankali ya sunkuyar dakai ya girgiza kai alamar yariga ya rasu.
'Daukar
jemaal yayi yaduba shima ya tabbar musu da yarasu.
Atake sultan
yakalli kaleeb cikin zallar 6acin rai da nuna ikonsa yace,
Akai mai
laifin kurkuku mafi tsanani ahadata maciji mafi hadari har zuwa gobe kafin
tafadi Wanda yasata sbd bayin kantabe batada isar dazata iya yiwa ko bawan
mineelik kallon banxa bare iya kashe jinin sultan.
Cikin zaquwa
kaleeb yace,
Angama
sultan...ya fice yana kwatanto irin azabar dazasu ganawa mamani.
Cikin wani
irin mummunan yanayi na firgici da tashin hankali ta farka tareda miqewa zaune
jikinta na bata irin rawa tafara qoqarin tashi yayi saurin riqeta yana son
kallon cikin idonta amma taqi tsayawa gabaki daya bata cikin hayyacinta fixgewa
takeyi da qarfi yasake riqeta tareda girgizata da qarfi yakira sunanta.
Tasaki wani
irin kuka mai qarfi tareda fixgewa daga jikinsa ta zube qasa tafara kuka sosai
tana qanqame jikinta sbd wani irin ciwo da ra'dadi mai zafi takeji cikin ranta
kamar zuciyarta bazata iya daukaba.
Sake riqota
yayi ya rungume jikinsa da qarfi duk yanda taso qwacewa kasawa tayi tacigaba da
fidda kuka mai radadi.
Wani irin
ciwo da baqin ciki takeji na cin zuciyarta numfashinta har sarqewa yakeyi
gurin kukan.
Kasa magana
yayi sbd radadin da zuciyarsa ke ciki na rashin 'ya'ya biyu lokaci 'daya dakuma
ganinta cikin wannan halin.
Ammy kallon
Jakadiya tayi idanuwanta na qoqarin boye qwallarta tace,
Ya akayi
mamani tashigo nan harta bari aka kamata domin na tabbarda tana sane tabari aka
kamata akwai abinda take nufi da hakan Wanda shine tashin hankalina.,
Meyasa bata
kashesu a dakunan uwayensuba sai agurina?
Innalillahi,
allahumma ajirni fi musibati
Wannan wace
irin masifa ce mai wuyar cinyewa.
Cikin sanyin
jiki a raunane Jakadiya tace,
Alqawarin
Allah ne zai tabbata sbd sbd ayanxu alamu sun fara bayyanar mulkin mace a
mineelik Wanda hakan na nufin ba'a zubarda jiniba yanxune za'a zubar dashi.
Girgiza kai
ammy tayi da sauri cikin tsananin fargaba da rudu tace,
Rumanah
bazata taba zama mai zubarda jinin bayin Allah ba,
Nayi gudun
haka kowa yakasa fahimtata,
Na roqi
Allah a zuci da fili akan kar rumanah ta haifi namiji idanma ansamesa yazo babu
rai amma hakan bata faruba yanxu bansan ta ina kuma wannan masifar ta 6ullo ba.
Duk yanda
yaso ganin rumanah tadawo nutsuwarta abin ya gagara saima zuru datayi da ido
kukan yadaina fita saidai hawaye kawai ko motsin kirki bata iyayi ta rakube
gefe guda ta takure kanta.
Lokacinda
aka shigo aka sanarda ita zuwan ammy dubata bata motsaba saima rufe idanuwanta
datayi hawayen ciki suka gangaro tunani abubuwa da dama na dawo mata,
""
mafita 'dayace karta haifi namiji idanma ta haifesa mutuwarsa itace
mafita""
""
yaya kike tunanin zan fuskanci rumanah ranarda ta San cewar mune sanadin
mutuwar iyayenta""
Rintse
idanuwanta tayi da qarfi nauyi da zafin zuciyarta na qaruwa saidai batason
barin zancen yashigeta a irin yanayin datake ciki yanxu sbd tanason tayiwa ammy
fahimta mai kyau bazataso abinda kunnuwanta sukaji mata ba yazama gaskia.
Ammy kasa
haquri tayi ta nufi dakin lokacin maheer yaje dubo suhailat.
Har ammy
taqaraso gabanta bata motsaba daga inda take takure idanuwanta jajir.
Cikeda
tsananin kunya da tausayinta murya na rawa tace,
Rumanah har
abada bazan iya cire qaunarki arainaba sbd qaunace Allah yasakamin cikin raina
Wanda kisani har abada bazan iya yin abinda nasan zan cutatardake ina fatar
zaki riqe hakan aranki...Allah yaji qan abeel Hussain.
Juyawa tayi
ta fice jikinta asanyaye sbd tana iya hasaso wasi wasi azuciyar rumanah.
Tana fita
rumanar sulale ta kwanta agurin tasaki sabon kuka tana dafe qirjinta dake mata
zafi da wata irin tafasa.
Cikin wata
irin kaca mai tsananin nauyi da zafi aka na'do mamani da nauyin kacar yasata
tafiya ahankali a duqe sbd ko qafarta daqyar take dagawa sbd nauyin kacar
datake 'daureda ita.
Aka bude
wani tsohon kurkukun dayafi shekara goma ba'a shigesaba aja jefata ciki da
qarfi kanta ya bugu da bango take goshinta ya fashe da jini ta fitarda numfashi
daqyar sbd azaba gashi batada hannun shafawa taji sbd irin 'daurin da'akayi
mata ko numfashi daqyar take fitarwa.
Ta lumshe
ido cikin azaba ta bude idon takalli qofar dishi dishi take gani sbd ba qaramar
buguwa tayiba gashi anyi mata wani irin duka na rashin imani dan kariya biyu
akayi mata a hannu 'daya.
Wani irin
kwando aka bude tareda jeho abinda ke ciki aka rufe qofa
Wani irin
baqin maciji tagani ya bude kansa yana fitarda huci.
Mummunar
faduwa gabanta yayi wasu irin hawayen azaba da tsoro tareda baqin ciki suka
gangaro mata jikinta ko qarfin dazaiyi rawa bashidashi sbd ti6is akayi mata.
Tana kallo
macijin ya kwantarda kai yayi cikin wani qaton rami dake gurin Wanda shikansa
ramin baza'a rasa wani macijin acikiba ko abinda yafisama.
Maganarta da
adama ta tuno tana fargabar kar komai yaqi tafiya yanda suka tsara.
"""
idan kikai nasarar basu wannan dafin suka sha zasu mutu atake kuma ki
tabbatarda ankamaki duk wuya da azaba karki ce nice kice sultana ce Wanda kowa
yasan hukuncinta na kisa ne kafin akasheta za'a bani matsayinta na sultana
nikuma zanyi amfani da wannan matsayin na hana akasheki kuma daga lokacin
namiki alqawarin matsayin Jakadiya kintashi daga baiwa har abada saidai kuma
idan kika fadi sunana kisani babu 6ata lokaci dukkaninmu za'a kashemu amma idan
kikace itace nizan kubutar dake kinga burinki na shekara da shekaru yacika ga
'yanci da dukiyar kanki dazaki tara""""
Numfashi
tasaki a wahalce tana sake qarfafawa zuciyarta dan cika sauran aikin dan kuwa
koda ta mutu tasan burinta akan zuriar bulama da asma'u yacika.
Suhailat
data farfado ahankali hawaye kebin fuskarta suna sauka kan qirjinta idanuwanta
arufe sbd ko hannunta daqyar take iya motsasa.
Qunci ne
arayuwarta da zuciyarta,
Rayuwarta ta
lalace batada wani sauran farin ciki,
Ta rasa
mijinta badan ya rasuba,
Ta rasa
rayuwar aure mai farin ciki,
Ta rasa
lafiyarta,
Ta rasa
mahaifarta gurin haihuwa ga abinda ta haifa ta rasashi mai zaunawama ya
rungumeta ya rarrasheta ta rasa
Wace irin
rayuwace mai tattareda garari take ciki?
Wani irin
kuka mai qaramin sauti tasaki zuciyarta na mata ciwo mai tsanani
Kewar
iyayenta da 'yayanta takeji sbd sune kadai sukasan zafinta da damuwarta.
Qarasawa
yayi bakin gadon tareda Rungumeta da sauri yana jin tausayinta fiyeda kansa sbd
yasan tafi kowa cutatuwa sbd tafi rasawa tunda ba wata haihuwar zata sakeba.
Akaro na
farko arayuwarta taji batason kusancinsa agareta sbd nauyi hakan ke qarawa
zuciyarta saidai ko motsi sosai bata iyayi bare ta zame jikinta hakan yasa wani
sabon kukan qunci zuwar mata ahankali.
Sosai ya
lurada batai farin ciki ko jin sanyi da ganinsaba akaro na farko arayuwar
aurensu daya hango wani yanayi daban akansa wanda ba sonsa bane atareda ita ya
rufe ido cikin wata sabuwar damuwar yanajin tausayin kansama sbd wata jarabawace
Allah yake jarabtarsa da ita akan rumanah wadda idan baiyi taka tsantsanba zai
tashi da Rabin jiki ranar lahira saidai kuma baisan yaya zaiyiba sbd sonta
yazama halitta ajininsa.
Ahankali ya
furta,
Allah yaji
qan jemaal.
Sakinta yayi
ya miqe tareda ficewa batareda ya qara kalma 'daya ba.
A wannan
daren mineelik ba kowa yasamu damar kwantawaba bare ya rintsa sbd dukkanin dole
da masautar na cikin tasa kalar damuwar.
Rumanah dai
duk yanda akayi da ita taci abinci ko motsi taqiyi daga inda take idanuwanta
sun bushe sunyi jajir ko gani sosai batayi sbd kumburin idanuwanta.,
Suhailat
kuwa har lokacin bata iya kwakwaran motsi sai hawaye da ciwon qirji dayake
cinta ita kanta anyi anyi taci abincin amma ko bude ido taqiyi sai hawaye take
zubarwa.
A rayuwarsa
wannan ne karo na farko dayaji yayiwa sarauta da gidan sarauta wata irin
muguwar tsana sbd yasan son mulkine yasa akai hakan,
Ya
tabbatarda kisace ta tabbata akan baiwar datayi da wainda suka sakata saidai
bayajin zai tsaya ganin hakan gobe zaayi hidimar radin sunansu a goben zasubi
jirgin dare su koma dan idan yananan zuciyarsa zata bugane da halinda matansa
suke ciki musamman suhailat datake buqatar kulawa sosai.
Ammy da
jakadiya kusan a zaune suka kwana ko ruwan arziki babu Wanda ya iya sakawa
maqoshinsa sbd tashin hankalin dazai iya faruwa gobe sbd duk Wanda sunansa
yashiga koda misali ne cire kansa ya wajabta gashi a sashen ta abin yafaru
shine babban tashin hankali da damuwar dasuke ciki musamman dasukasan wacece
mamani.
Ayau
mineelik acike takeda duk wata masarautar dake zagaye da maqwaftaka da ita
tareda wasu sarautun wasu qasashen da dama sbd gabatarda sunan magajinnta
dakuma miqawa uwar magajin mineelik kambun saukewa da 'dora sabon sultan.
Wannan
matsayin daza'a bata ayau shine abu mafi ha'dari da tashin hankalinda yake ciki
ayau
Ammy duk
yanda taso daurewa kasawa tayi saida hawayen baqin cikin datake ciki suka
gangaro mata tun a daren jiya ta hana su ganta bare ta sanarda ita hadari da
kuma illar abinda zata fada.
Saidai
alqawarine shi ya daukarwa kansa zai tabbarda ta miqa mulkin nan ga sultan ya
dauketa sunkoma adaren yau din.
Lokacinda
aka hallara dan qaddamarwa saqo ya isowa sultan uwar magaji batada lafiya
bazata iya fitowa.
Kai tsaye
aka fara qaddamar da komai aka radawa abeel Hassan sunansa tareda qaddamar da
sunan ummu-rumanah acikin littafin tarihin mineelik amatsayin uwar magaji.
Nan take
masu rubuta tarihi aka bude paging fara rubuta nata.
Daga ammy
har yarima maheer babu Wanda ya halarci taron kuma sarai sultan yagano
manufarsu tayin hakan zasu fuskanci hukuncinsa daga baya ayanxu baiwa mamani ce
agabansa zai bata wata irin mutuwa mai firgitarwa itada wainda suka sakata ga
'yan baya.
Koina yayi
tsit jiran hukuncin sultan akeyi lokacinda mamani ta tabbatarda Jakadiya ce
tasakata amatsayin itama sultana ce ta aikota.
Tsita
akayi kowa wuta ta dauke masa musamman sultan da mamakin baiwa mamani
yakamasa sbd yafi kowa sanin sultanarsa bazata aikata hakanba,
Tabbas
wannan baiwa mai taurin raice saidai ji da ganin hukuncin sultan kawai tajeyi
batasan waye sultan ba.
Kallo daya
yayiwa kaleeb cikin babbar murya yace,
Aje ajefawa
zakuna ita su cinyeta da ranta akawo qashinta asa 'dakin kayan tarihin
mineelik...
Da ido adama
dake dake gefensa tayiwa sultan aqeel magana ya gyara zamansa tareda kallon
sauran sarakunan dake Royal hall din yace,
Idan aka
kashe wannan baiwa batareda ta fadi wainda suka sakataba baka kai qarshen
matsalar a mineelik ba sbd gobe ko jibi magajin ne da kansa za'a kashe kuma
hakan zaisakawa mutane wasi wasin hukuncinka tunda ta fadi wainda suka sakata
anshare anyi kamar bata fadaba.
Ido cikin
ido yakalli sultan aqeel yace,
Babu Wanda
ya isa yayi wasi wasin hukuncina a qarqashin mulkina da ikona ko wanene
batareda na ciyar da namansa ga dabbobinaba.
Murmushin
mulki sultan aqeel yasaki yace,
Hakane kuma
idan kanason hakan yacigaba da faruwa saika nunawa mineelik Kaine sultan kuma
Kaine kake yanke hukunci kowane irine akan ko wanene.
Nan take
sauran sarakunan suka marawa gaskia baya suka qalubalanci sultan akan adalci
idan har sultana ce tasakata to ayi adalci ayanke hukunci daidai yanda
yakamata.
Atake mutane
suka fara kallon kallo da hayaniyar abinda aka fada nan mamaki ya kama sultan
kenan har akwai wainda zasu iya tambayar hukuncinsa su qalubalanci yanayin
mulkinsa
Atake yace
aje a kama Jakadiya arufe ya 'daga hukuncin zuwa gobe duk me hannu aciki kafin
faduwar rana baya duniya.
Lokacinda
akaje aka kama Jakadiya aka rufe
Sultana kuwa
rufe sashenta akayi tareda aje masu tsaron qofar da doka mai qarfi daga sultan
babu Wanda zai shiga gurinta ajira hukuncinsa zuwa gobe.
Lokacinda
zancen ya isa kunnen maheer kai tsaye gurin sultan yanufa akai masa iso lokacin
anwatse sai gobe a shaida hukuncinda zai iya yankewa.
Kallonsa
yarima yayi cikeda takaici da baqin cikin yanda yasan sultana bazata aikata
hakan ga yayansa ba amma ya yarda haryana iya tunanin yanke mata hukunci
Kai tsaye
yace,
Amatsayina
na uban magaji zan kar6i mulkin mineelik har lokacinda zai girma ya karbi da
hannunsa.
Wani irin
murmushin takaici sultan yasaki batareda yakallesaba yace,
Mulkin
mineelik da za6ar mai mulkin na mutum 'dayane yanxu dan haka ka rasa damarka,
Mahaifiyarka
kuma koni bazan iya kubutarda itaba idan har bincike ya nuna da hannunta aciki.
Yana fadar
haka ya shige tabarsa zaune idanuwansa na kadawa jajir.
Duk inda
tashin hankali yake masarautar na ciki dan shi kansa sultan jinjina alamarin
yake aransa yana jaddadawa yana kuma fatar bincike yasa kar asamu hannun
sultana aciki.
Acikin daren
babu kalar azabar daba'a bawa mamaniba tace Jakadiya tasaka ta.
Jakadiya aka
hau bawa baqar azaba amma daqyar take iya furta babu saka hannunsu aciki.
Acikin daren
saqon neman sulhu da sassaucin hukunci yazo daga masarautar Libya dakuma wasu
masarautun duk sai alamarin yasake girmama ya sake cabewa sultan gashi komene
adaren ne sbd gobe dolene zai yanke hukunci.
Nuratu datun
jiya take kuka da tashin hankalin halinda mamani ta fada koda bincike yazo
kanta ba qaramin rikicewa tayiba saidai tafada musu komai na dangane da zancen
dasukaji su Jakadiya nayi da sultana itada rumanah akan basuso ta haifi namiji.
Atake aka
kaiwa sultan wannan zancen hankalinsa ya matuqar tashi saidai har lokacin
yanada wasi wasin zancen ga asirinsu na 6oye daya fara shigowa cikin zancen
Wanda tonuwar dolema yayi gaggawar yanke hukunci sbd kar maganar ta bankado
atake ya yanke hukuncin kisa ga dukkaninsu ukun gobe.
Acikin daren
hankula suka masifar tashi jin anyekewasu sultana hukuncin kisa washe gari.
Duk wata
zuriar masarautar tun acikin daren suka fara isowa musamman 'yayan sultana da
kuka sunyisa na zuci dana fili hankalinsu amatuqar tashe yake.
Yarima
maheer Kansa ya rufe adaki duk yanda yake tunanin masifar ta wuce nan abu 'daya
yasani bazai mahaifiyarsa ta fuskanci hukuncin kisar wulaqanciba.
Kwance take
lamo idanuwanta jajir ko kukan bata iyayi duk abinda yake faruwa bata saniba
sbd ta hana abar kowa shigowa gurinta.
Ahankali
taji antsaya akanta batareda tadagoba ta lumshe ido tareda budewa taji muryar
suhailat cikin wani irin yanayi tace,
Nazo neman
alfarma agurin sbd kece kawai zaki iya tsayarda abinda ke shirin faruwa.
Tashi zaune
tayi ahankali batareda takalli suhailat dinba
Itama
suhailat sauke kanta tayi sbd batason kallon rumanah dan ganinta ke tuno mata
da ba itace zuciyar mijintaba.
Hawayene
suka gangaro mata tasaka hannu ahankali tashare taci gaba da cewa,
Baca Juga
Nice uwar
datai rashin abu biyu lokaci daya kuma zuciyata cike takeda neman adalci,
Ina roqonki
amatsayina na uwar data rasa 'da da mahaifarta akan adalci zanso ganin anmin
adalci saidai bazanso akashe Wanda bashine mai laifinba sbd mai laifin zai
cigaba da aikata 6anna aboye har wadda tafi wannan.
Cikin
dasashiyar murya da sanyi tace,
Adalcin nima
nake nema amatsiyana na marainiyar da aka raba da iyayenta dakuma uwar da aka
rabata da 'danta tun bata gama warkewa daga zafin naqudarsaba.
Asubar fari
yashigo dakinta idanuwansa da yanayinsa suka karya mata zuciya ta dauke kai
daga kallonsa tareda mayarda kanta kan gwiwoyinta.
Tsayawa yayi
agabanta zuciyarsa cikeda baqin cikin kasancewarsa shine zai roqi wani yabasa
sarautarda shine ya gada saidai yasan kubutarda ammynsa na nufin ya karbi
sarautar ayau yazamo shine zai yanke hukunci sbd yagano sultan sbd 6oye wani
sirrinsa yakeson yanke hukuncin da gaggawa ayau.
Kallonta
yayi da idanuwansa dasukai jajir yace,
Inason
kibani sarautar mineelik ayau.
Kallonsa
tayi da sauri da jajayen idanuwanta dake budewa daqyar sbd kumburi.
Juya mata
baya yayi yace,
Ki shirya
ina jiranki kafin lokacin yanke hukuncin su ammy yayi.
Ficewa yayi
tabisa da kallo zuciyarta na harbawa.
Cikin wani
irin yanayi na sabon tashin hankali ta 'dauki abeel hassan ta fito palo takalli
nuratu dake rakube tun acikin daren tana jiran fitowarta tayi kuka har batada
qarfin yin wani.
Kai tsaye
tace,
Meke faruwa?
Da sauri
nuratu ta tashi ta zube gabanta tana hawaye tace,
Ina neman
afuwa akan shaidar dana bayar akan sultana da jakadiya gashi zasu rasa ransa
sanadin shaidata saidai wlh ina rantsuwa da rayuwata mamani bayin kantabane
sakata akayi saidai wlh bansan wayake sakataba dana fada nan fitardasu sultana
dan haka ashirye nake da daukar hukuncinki.
Da wani irin
sabon baqin ciki da takaici takalli nuratu saidai takasa cewa komai ta nufi
qofa ta fice kai tsaye sashen suhailat ta nufa.
Zaune take a
dakinta taqurawa akwatinanta data saka Carolina hadawa ido idanuwanta jajir.
Tsayawa
gabanta rumanah tayi tareda miqa mata abeel hassan idanuwanta na cikowa da
hawaye tace,
Duk duniya
ayanxu kece kawai na yarda dake akan 'dana sai Ammy dan haka ina riqonki daki
riqesa har sai lokacinda kikaji zuciyarki ta gamsu da adalcin dazan baki,
Na miki
alqawarin duk Wanda yakeda hannu aciki ayau zai fuskanci hukuncinsa.
Ficewa tayi
kai tsaye ta nufi sashenta tashiga wanka zuciyarta na wani irin zafi tana
fitowa tagansa tsaye cikin 'dakin idanuwansa jajir ya kalleta ta 'dauke kanta
tareda isa gaban madubi ta zauna.
Cikin zafi
ya jawota gabansa cikin 'daga murya yace,
Me kike nufi
da abinda kika fadawa suhailat?
Bata
kallesaba tace,
Kubutarda
uwata.
Sakinta yayi
da sauri tareda kallon cikin idonta yace,
Kinsan
abinda kike fada?
Kinsan
abinda hakan ke nufi?
Bana buqatar
ki shiga komai abu 'daya nace kiyi shine ki bani matsayin danace inaso....
Kallonsa
tayi da jajayen idanuwanta cikin rawar murya tace,
Nima bana
buqatar ka saka kanka cikin ha'dari dan haka bazan taba baka mulkin mineelik ba
koda hakan na nufin rasa rayuwatane....
Riqota yayi
da qarfi tareda girgizata yace,
Idan kina
sona bazaki taba bari ataba mahaifiyata ba sbd itace rayuwata dan haka dole
zaki bani mulki.
Hawayen
dasuka cika mata idone suka gangaro mata ahankali tace,
Namaka
alqawarin babu abinda zai samu uwar data haifi halitta mafi soyuwa arayuwata
kozan rasa raina.
Shiga
jikinsa tayi ahankali tareda rungumesa hawaye na tsinke mata.
Rintse ido
yayi tareda rungumeta ahankali ya furta,
KECE
RAYUWATA UMMU-RUMANAH BULAMA.
Dagowa tayi
takallesa hawaye far in ciki na tsiyayo mata saidai bazata iya cewa komaiba.
Ruwan kan
table din dake tsakiyar dakin ta dauka tareda kaiwa bakinsa tana tsiyayar
hawayen tausayinsa dana kanta.
Ahankali
yasha yana kallon cikin idonta.
Ahankali ta
furta,
Karka gujeni
kome zanzama arayuwa dan allah,
Ko bayan
raina kayi kayi alqawarin tunawa dani.
Lumshe ido
yayi jikinsa na mutuwa idanuwansa na fara gani dishi dishi a firgice yake
kallonta sbd gano wani abune tabashi saidai kafin yayi wani yunquri ya zube kan
gadon ta durqusa ta gyara masa kwanciyarsa tareda shafa fuskarsa ta miqe.
Dukkanin
wani maison sheda hukuncin sultan na cikin qasar da wajenta sun hallara sultan
na fitowa guri yayi tsit ya zauna kan kujerar mulkinsa atake aka fito da mamani
da jakadiya dukkaninsu babu mai iya tsayuwa sbd azaba da 'daurin dake jikinsu.
Kukan baqin
ciki Jakadiya takeyi sbd irin mutuwar tozarcin dazasuyi tareda sultana.
Mamani na
ganin masu jiran umarni sun tsaya akansu da takobuna suna kashe ido sbd laifi
da qyallinsu hankalinta yatashi tabude ido daqyar tanason magana kaleeb ya take
mata kai.
Ana jiran
ana fitoda sultana cikin wani irin ama aka sanarda fitowar uwar magaji.
Atake kowa
yayi tsit sultan yayi saurin kallon qofar
Tafito cikin
wata irin doguwar ethiopiany royal gown red colour mai tsananin tsawo da adon
black stones wuyanta da kanta na kyallin farin zinari kallo 'daya zakayi mata
kasan tana cikin baqin ciki.
Cikin wainda
ke tareda ita Dan tsaron lafiyarta ta kalli gefen daya jiki na rawa ya fidda
bayananta dake rubuce jikin fatar rubutu ya miqawa sarkin na'din sarautar
mineelik.
Budewa yayi
tareda fara karanto da qarfin muryarsa yanda duka alummar dasuka halarci gurin
zasuji.
""
NI UMMU-RUMANAH BULAMA MATAR YARIMA MAHEER UWAR MAGAJIN MINEELIK AYAU KWANA
'DAYA DA NADIN SUNAN MAGAJIN MINEELIK NA SAUKE SULTAN ABDULSHAMS ABDALLAH DAGA
MULKIN MINEELIK NA KARBA HAR ZUWA RANARDA 'DANA MAGAJI ABEEL HASSAN ZAI KARBI MULKI
DA HANNUNSA.."""
Tsit koina
yayi sbd firgici da mamaki
Sultan da
adama kusan atare suka miqe tsaye tsabar firgici.
Ammy da ake
fitowa da ita kadan ya rage ta yanke jiki ta fadi sbd jiyo sanarwar.
Jiki na rawa
sarkin nadi tareda duk sauran sarakuna da wazirai suka miqe ta nufi kujerar
mulkin mineelik gabanta da numfashinta na fita da sauri
Sultan
dayayi mutuwar tsaye ya zare hular mulkin ya miqawa sarkin gida atake aka dauko
kayan rantsarwa aka rantsar da ita atake ta zauna kujerar mineelik aka saka
mata hular.
Lumshe
jajayen idanuwanta tayi wani irin baqon yanayi mai qarfi na shigarta
Wani irin
qarfin zuciya da taurin zuciya taji yana shigarta tsawon lokaci ahaka duk anyi
tsit anajiranta.
Ahankali ta
bude idanuwanta dasuka bushe nan take tagyara zama takalli inda sultan yake
zaune yana kallonta cikin isa shima yanajiran jin nata hukuncin ta juyo takalli
indasu mamani suke cikin daga murya tace,
Akawo abinda
mamani tafiso aduniya.
Cikin
gaggawa aka jawo nuratu aka durqusar tsakiyar gurin kai tsaye tace,
Ku yankata
agabanta uwarta idan bata fadi Wanda yasakataba cikin seconds uku.
#mamuhgee.
[12:36 AM,
7/30/2019] +218 94-4138736: TARAYYA
wattpad@mamuhgee
Haske writers association💡
34
Not edited.
Arazane
sultan,adama,ammy,da baqin sarakunan dasukazo suka kalleta
Babu Wanda
ta kalla acikinsu tayiwa kaleeb kallo 'daya idanuwanta na sake bushewa cikin
gaggawar cika umarninta kaleeb ya daga shar6ebiyar takobinsa mai cire kai
lokaci 'daya ya 'dora a wuyan nuratu dake hawaye ta qurawa rumanah ido.
Numfashin
wahala mamani ta fitar cikin tashin hankali ta bude baki zatai magana adama
datai mutuwar zaune tayi sairi tashi tsaye jikinta na wata irin tsuma zatai
magana rumanah ta 'daga hannu batareda takalleta tace,
Duk Wanda
yayi magana batareda hukunci ya gama tabbatuwaba abakin rayuwarsu ko wanene.
A gigice
adama tasake kallonta cikin wani sabon tashin hankalin takoma ta zauna zufa na
karyo mata jikinta na wata irin tsuma.
Tayar da ita
akayi tana numfashin azaba takalli takobin datake qyalli a wuyan nuratu takuma
tabbarda yankata din za'ayi.
Ahankali
rumanah ta 'dagawa kaleeb kai alamar yacika aiki.
Atake ya
'daga takobin cikin wahalalliyar murya mamani tace,
Gimbiya
adama ce.
Cak kaleeb
ya tsaya sbd harya 'dora takobin a wuyan nuratu harma saida ya'dan yanketa.
Arazace
sultan yakalli adama data jiqe jagaf da zufa jikinta na tsuma tanason kare
kanta gashi ance duk Wanda yayi magana bbakin ransa kuma tasan tsaf rumanah
zata iya sbd tasan abinda ka cikin karagar zaifi shigarta kasancewarta mace dan
haka zatafi rashin tausayi da imani.
Sarakunan
dake gurin duk ita suke kallo cikin mamaki yayanta kuwa kuka suka fashe dashi
gashi babu ikon ko qwaqwaran motsi.
Rufe ido
rumanah tayi wani irin yanayi na tsuma zuciyarta gawar 'danta da iyayenta tana
mata yawo ido da irin tozarcinda ammy ta fuskanta akan hakan
Fuskar
maheer ce ta fado mata da irin tashin hankalinda tagani ataredashi tsakanin
jiya zuwa yau ta bude idanuwanta dasukai jajir tace,
Ni sarauniya
ummu-rumanah bulama na halastawa takobin kaleeb adana jinin adama kisheer ayau
agaban mijinta da 'yayanta tareda sauran alumma duk Wanda ko a fuska ya nuna
hukuncina baimasaba a shayar dashi dafi daidai irin Wanda adama tashayarda
qannen magajin mineelik.,
Baiwa mamani
arufeta mai rubuta tarihi yaje tabasa tarihin sarauniya rumanah arubuta
atarihin mineelik tana gamawa bazata qara minti biyar aduniyaba a shayar da ita
Kofi 'daya na daafin macijin dayafi kowanne kaifin dafi,
Sultana
zaarah da jakadiya sunfita da zargin da ake musu.
Sultan
abdulshams arufesa a turakarsa babu shiga babu fita aabisaga zarginsa na
qoqarin yanke hukunci batareda bincikeba harsai angama bincike akan niyarsa
sultana zaarah ce kawai keda damar shiga da fita agurinsa sai yarima maheer.
Arikice
sultan yakalleta ransa na mummunan 6aci da baqin ciki ace rana 'daya cikin
mintunan dabasu wuce biyarba baiwa wadda bama asalin 'yar qasaba ta saukesa
akan mulkin daya gada iyaye da kakanni,
Ta yankewa
matarsa kisan wulaqanci agaban dubban jama'ar dasuke shakkar ko kallon inda
yake sannan yanxu tace arufesa a turakarsa wannan shine tozarci mafi muni
arayuwa...
Yanxu ta
karbi mulki idan tagano shine asalin dalilin mutuwar iyayenta akwai masifa
sosai sbd yanda sihirin karagar nan ke shigarta nan cikin qanqanin lokaci zata
zamewa kowa masifa mai matuqar hadari musamman shi saidai duk masifa duk balai
bazai bari yayi mutuwar wulaqanci a hannuntaba koda hakan na nufin hada hannu
da balain da aka binne shekaru tun kafinsu.
Kama adama
akayi aka fara janta tayi saurin kwacewa ta isa gaban rumanah ta zube tana
kukan tashin hankali jikinta na mugun karkarwa saidai takasa magana sbd
umarninda rumanar tabayar ko kallonta rumanah batayiba ta kalli su kaleeb atake
suka fara yiwa adama jan wulaqanci.
Jikin ammy
ne yadauki rawa cikin sabon tashin hankali take kallon rumanah tana girgiza kai
sbd matuqar tafara mulkinta ayau da zubarda jinin wani to tabbas zaiyi wuya
bata zamewa mutane abin tsorobas.
Qoqarin isa
gurin rumanah din tayi aka dakatar da ita ta hanyar tareta tayi saurin kallon
rumanah data rufe idonta tanajin wani irin baqon yanayi shigarta.
Cikeda
rashin imani da tausayi kaleeb ya daga takobinsa yacire kan adama data mutu
tana ihu da fizge fizge.
Tsit gurin
yayi sbd tsoro da firgici sbd duk mulkin sultan ba'a taba kashe mutum agaban
alumma ba sai yanzu nantake kowa yaji tsoro da fargaba tareda tashin hankali na
shigarsa atake kaleeb ya 'daga takobinsa dake 'digar jinin adama sama ta bude
idanuwanta ahankali takalli jinin dake diga qasa ahankali tasauke ajiyar zuciya
ta miqe tsaye.
Cikin wani
sauti da babban sauti sarkin na'di yace,
Dogon zamani
MINEELIK ASSULTANA UMMU-RUMANAH UWAR MAGAJI.
Juyawa tayi
wasu irin samudawan masu bata tsaro da kuyankinta mata suka mara mata baya
tashige.
Tafiya kadan
tayi ta tsaya cak sbd abinda takeji ajikinta
Wani irin
abu takeji kamar yana tafiya da motsi ajikinta ta dafe qirjinta da takejin yana
quna.
Ammy tayi
saurin nufota aka sake tareda
Rumanar ta
'daga musu hannu daqyar alamar subarta ammyn tayi saurin qarasowa kafin tayi
yunqurin ta6ata sukaga ta yanke jiki ta fadi jini na fita ta hancinta atake
hankalinsu yayi masifar tashi ammy na qoqarin 'dagota suka gansa kansu
idanuwansa jajir jijiyoyin sun firfito ya durqusa ya dauketa ya nufi sashenta
da ita cikin qanqanin lokaci aka zuba wasu irin tsaro tundaga qofar sashenta
har zuwa qofar masarautar atake labarin halinda take ciki ya yadu nan mutane
suka sake shan jinin jikinsu atake aka rufe duk wata qofar shige da fice dake
mineelik aka dauko duk masu bada maganin sarauta na asalin gargajiyarsu nanda
nan aka hau dubata suna qoqarin tabbatarda abinda suke tunani.
Cikin wani
irin tashin hankali da damuwa yake,
Zafi sosai
yakeji acikin xuciyarsu akaro na farko dayaji zuciyarsa na karaya akan abu
saidai yasan mutuwace kawai zata rabasa da rumanah dan haka duk abinda zata
zama ayanxu ashirye yake daya sadaukar da rayuwarsa akan cetota daga masifar
dake tattare da wannan karagar.
Jini ne
sosai yake fita ta hancinta ahankali tafara wata irin jijjiga jijiyoyin jikinta
suka ringa firfitowa Kore sosai nan take hankalin su negasi(masu maganin
gargajiyar qarnin baya na sarauta) ya tashi
Maheer da
idanuwansa sukai mugun rikidewa yayi saurin nufarta zai rungumota cikin wani
irin sauti negasi yace,
Karka
kusanci inda take ko kusa a wannan yanayin hadarine mai matuqar gaske dankuwa
dafine yake yawo ajikinta yanxu idan jininta yafi qarfin dafin zataci qarfinsa
ta tashi idan kuma dafin karagar yafi qarfin jininta shikenan sai hakuri sbd
har abada bazata koma daidaiba zata zama rabi hankali rabi nakashe.
Cikin wani
mumman tashin hankali ya dafe goshinsa akaro na farko yaji idanuwansa suna
qoqarin tara hawaye ya fito dakin baya gani sosai sbd tashin hankali
Ahankali
yaji andafasa yana juyowa yaga suhailat rungume da abeel baisan sanda ya fada
jikintaba ta rungumesu gaba daya shida abeel din hawaye na gangaro mata cikeda
tausayinsa dana rumanah taso tafiyarta ayau saidai ganinsa Cikin halinda bata
taba ganinsaba yasata jin bazata iya tafiya tabarsa a lokacinda yafi
buqatarta,tabbas idan tanada wata qaddara arayuwa to soyayyar maheer ce dan
haka kamar yanda zai sadaukar da rayuwarsa gurin kulada rumanah duk halinda
zata shiga mai kyau ko mara kyau to itama zata zauna ta sadaukar da rayuwarta
gurin kula dashi da zame masa garkuwa duk lokacinda zai nemi hakan.
Ammy dake
zaune tareda sauran 'yayanta yayun yarima sun biyu da Jakadiya da sauran masu
tsaro da jiran tsammanin halinda ake ciki ta rafka tagumi zuciyarta na harbawa
da qarfi sbd tasan me hakan ke nufi dan kuwa rumanarsu tariga ta tafi sbd idan
har komai yagama shiga jikinta duk abinda yafaru shekara da shekaru tun kafa
mineelik zata gani Wanda shine idan kaga masifun dake ciki yakeda wuya baka
haukaceba idan ka farka.
ASALIN
MINEELIK.......
#mamuhgee
Post a Comment for " TARAYYA 33-34"