TARAYYA 35-36
35
Not edited
Asalin Labarin
mineelik
Soyayya da cin Amana haɗi da Yaudara suka,
kafa daular, asalin masifar ya fara ne, daga ranar laraba ga watan maris 1836.
Mafarin rigimar daga mutane huɗune, jigogin masarautar,
Musaman Sultan Jamal
wanda shi ya haifar da kome....
Tafiya suke a gajiye ga dare ya fara rabawa,
yunwa da kishirwa ya addabesu, dan haka suka yanke hukuncin da zaran sun sami,
wani guri a can gaba zasu yada zango kasancewa sun fito daga yanki sham,
fatauci duk cikinsu babu wanda yake iya magana sai Jamal, sabida Allah yayoshi
mutune magananne, da kuma son raha,
"Kayyasa! Ajani karda ka gaji da tafiyar dan naga kaman
rakuminka ke janka ba kai kejanshi ba."
"Wai shin Jamal baka gajiya da
magane, haba tun da muka fito kaiɗai ke surutu gaskiya kacika surutu kayi mana
hakuri haka dan yunwa muke ji." inji Kojo.
"Shi kenan kojo nayi shiru
kuma bazan sake magana ba, amma kusan matuƙar muka ce zamu shiga Ehtophiea a
wannan daren akwai damuwa mu yada zango anan gaba."
Shirun da sukayi ya tabbatar da amincewar
sauran.
Tafiya sukayi sosai har suka isa dajin
kurfa, wanda yake cike da ababen tsoratarwa, ɗan tafiya kaɗan sukayi ɗayansu
amari yaga wani irin Haske mai tsananin kyalli cikin duhu ya ware ido sosai
yasake kallawa domin kuwa ya tabbatarda mage yake gani mai shegen hasken nan
kamarna zinari cikin zaquwa da fargaba yace.
"Ku
dakata naga wani abu, kamar Zinari."
"Amari nima nagani tsoron siffar abin
yasani shiru gashi can kamar mage ko?" Inji Jamal,
Linzamin rakumarsu suka ja, suka tsaya Jamal da Amari suka sauka, daga
bisa rakumansu, Ajani da Koja suna tsaye suna kallonsu, tafiya sukayi me ɗan
nisa suna niman Zinarin basu ganshi ba,
Tsaki Ajani yayi wanda ya kasance shine
babbansu, cikin fushi yace.
"Dalla
kuzo mutafi kusan inda muke ciki wannan dajin kurfa cike yake da al'ajabi da
ban tsoro matumar kuka ce zaku bi na gane gane mutuwa zamuyi ku fito
muje."
Murmushi Amari yayi cikin nutsuwa yace.
"Na
rantse da abin bautana bazan bar dajin ba, Jamal idan zaka bisu ba damuwa amma
ni sai naga abinda ya turewa buzu naɗi"
Shiru sukayi sunsan Amari da kafiya da
kuma taurin rai, matukar yace zai yi abu ba makawa sai ya aikata,
Cikin laluma kojo yace.
"Shikenan
zamu tayaku nima! Ai duk cigabanmu ne, Ajani kayi hakuri mu tayasu niman
zinariyar."
Tsaki Ajani yayi sannan ya koma inda
suka ajiye rakumansu, suka kafa tanti karan dake wajen dajin suka tsinta, suka
kunna wuta suna shan ɗumi,( bawai dan lokacin sanyi ba'a mutanen da suka kuna
wuta su zauna suna hira, musaman fatake matafiy idan suka yada zango.)
Zama sukayi a gurin, sannan suka
ciro guzirinsu suka fara ci, bushashiyar gasashiyar fulawa sai bushashen inabi,
sai ruwa suna ci suna hira, har dare ya raba sannan kowa ya koma tantinsa.
Kasancewa dajin mugun gurine koda suka shiga
sai da suka kafe ilahirin gurin dan kar wani mugun dawa ya iya shigowa ya cutar
dasu.
Asalinsu wadanan, Fataken yan
garin Ethiopia ne, sun kasance marayu basu da uba basu da Uwa, sai wani
marikinsu wanda shima bai jima da mutuwa ba.
Ajani shine babba a cikinsu sai mai binshi
Kojo, sai kuma Amari da karamunsu jamal.
Dukda kasancewarsu marayu haka bai
hanasu kaunar junansu ba, dan ko ciwo ɗaya keyi duk sai sun kwanta kamar marasa
lafiya, dukda haka suna da mabanbanta halaya, Ajani baida yawan magana, amna
kwai saurin fusata sai amma haka bai sashi ya gaza zama mai hakuri ba,
Sai Kojo, mutune mai matukar fahimta ga daɗin
zama da kowa kuma duk inda zai zauna zai matukar wuya kaji ance ana rigima
dashi, sabida ya iya zama da kowa, sai Amari, masifaffe mara hakuri amma kome
zaiyi akan gaskiyarshi yake, yana da matukar taurin kai, dan shi duk abinda
yasaka agaba toh sai yaga bayanshi, amma mutune mai me tsage gaskiya.
Sai Autansu
Jamal wanda ya kasance mutum ne hakuri da juriya ga barkwace da iya zama
da mutane, kuma yana da shiga rai dan duk inda ya zauna sai kasamu ana alfahari
dashi, sai dai yana da abun dariya dan idan yazauna kusada kai sai ya cika maka
cikinka da barkwace da raha.
Wannan kenan....
Washi gari da safe duk suka tashi, nan suka
karya a gurguje suka shiga dajin, niman zinarin nan, har rana takusan faɗi basu
gani ba, tsurawa dajin ido amari yayi yace.
"Jamal
jiya ba'a nan muka ga kyalin zinarin mai sufar mage."
Gyaɗa mishi kai Jamal yayi cike da
bashi kwarin gwiwa, murmushi Ajani yayi sannan yace
"Amari
zan tura kojo gari ya sayo mana kayan aiki sai mun tono wannan zinarin na yarda
da kai."
Cikin farin ciki Amari ya rungume Ajani
yana cewa,
Yene dan
uwa.
Gurin tantinsu suka dawo suka
ciro kuɗi silalar akabawa Kojo, yaje ya sayo kayan aiki.
Tafiya ce ta wuni guda dan haka ya haye
rakuminshi ya kutsa cikin gari, bai isa ba sai da duhu ya fara rabawa, sannan
ya isa gidansu anan ya kwana washi gari ya shiga kasuwa ya sayi abinda suke
bukata wanda, na kayan tono,
Yana gamawa ya aza kayan akan
rakuminshi,sannan yabar garin,
Tafiyar kaman dai yanda yazone sai da
dare ya fara ya isa gurinsu dan ba iyakar kayan aikin yasaya ba, har da kayan
abinci yasaya musu,
Zama sukayi a gurin suka ci
abinda ya kawo, sannan suka shiga hira yanda zasu tono rijiyar zinarin.
Suna gurin har dare ya farayi
sannan suka shige tantinsu.
**
Washi gari suka je inda suka hango zinarin
suka shiga tonoda kwashe kasa, a hankali
suka ta aikin tono har dai sukayi nisan zango ga dare yayi dole suka hakura
zuwa gobe.
Washi gari ma haka suka cigaba da tonon ba
dare ba rana har sai da suka shafe kwanaki goma sha takwas da yini daya babu
zinarin babu labarinshi karshe hakura sukayi da tono, duk suka zauna jigum,
cike da bakin ciki Amari ya fashe da kuka, wanda ya kashe jikin yan uwanshi,
rarrashinsa suka shiga yi, kafin yayi shiru mikewa yayi yace.
"Dole
sai na isa ga, Ebo sarkin bokaye dan shine zai iya duba min abinda idanuna ya
gani."
Cikin son mara mishi baya suka
mike take suka nufi cikin gari, dukda dare ne haka bai hanasu tafiya ba, har
suka shiga garin gidansu suka nufa, suka kwana washi gari suka tashi dukkansu
suka nufi gidan Ebo.
Sarkin bokayen garin, tun daga bakin kofar
gidanshi suka hangoshi kwarjale, irin
wanda mahajata ke raɓawa akafaɗarshi hannunshi rike da sandar tsafi, goshinsa
yashafa bakin gari, inda yaja jan gari a goshinsa,
"Lalle lallae da zuwan sarakunan
karnin farko, barka da zuwanku, a koda yaushe k'addara kamar zare ce mai kaifi,
amma shahara da ɗaukaka tana biye a bayanta ku shigo ciki."
Jikinsune yayi sanyi, zama sukayi akan
fatar zakin dake shimfiɗe, a tsakar ɗakin, shi kuma ya koma kan kujeranshi.
"Ina jinku."
Yace musu, tunda suka ɗauko niyyar zuwa
gurinshi, yaji haka ajikinshi sai dai lokacin da ya hangosu yaga tagomashin ɗaukaka
wanda yake ɗauke da duhun na ban mamaki.
Cikin zakuwa Amari ya buɗe
bakinshi zaice wani abu m, take bokan ya dakatar dashi ya kalli Ajani, ya masa
alamun yayi magana.
Cikin nutsuwa ya faɗa mishi abinda suka
gani.
D'auko wata yar jaka yayi, ya buɗe
bakinta, ita wannan jakar da fatar jimina akayita, sabida ajiyar abubuwa
kananu.
Wasu duwatsune a ciki wanda suke
cakuɗe da wuri, wasu kalamai bokan yayi sannan ya jijjiga duwatsun ya watsa, a
tsorace yakalle su baki ɗaya sake ɗiba yayi ya watsa, a firgice ya mike yace.
"Shin
kungatane?"
Suma atsorace suka kalli juna, sannan suka
kalleshi, kaman haɗin baki suka ce.
"Wa
kake nufi?"
Komawa gurin zamanshi yayi a nutse,
yace.
"Sarauniya
Mineerlik?"
"Mineerlik kuma? Sarauniya kuma ai mu
bamu ganta ba, kawai mage muka gani ita kuma ta zinarice."
Suka faɗa mishi haka a tsorace.
"Tabbas ita kuka gani, itace
tafito dan sau ɗaya take fitowa ashekara, kuma ta tafi bazaku sake ganinta ba
sai wata shekara idan da rabon haka kuma ko wace shekara da kalar siffar datake
fitowa amma tabbas k'addaranku ce takaiku gurin har kuka ganta."
Shiru sukayi cike da damuwa, suka
shiga kallon juna Kojo shi yayi karfin halin tambayar bokan yace
"Wacece
ita haka.?"
"A'a ɗan saurayi wannan duniyace ta
taskar arziki, daula ce ta musaman Sarauniya Mineerlik sunanta sunan
kujeranta."
"Toh Ebo taya zamu sake
ganinta? Tunda ake kaddaranmu ce ta haɗamu da ita domin kuwa wannan zinarin
saimun mun mallakesa" Inji Ajani,
Gyara zama yayi cikin yarda da abinda
zaice.
"Wato
wannan dajin da kuke gani ba daji bane, kamar sauran da dazuzzuka, shi ɗin
alkarya ce ta aljanu ko nace muku duniyar aljanu ce, shi yasa yake cike da
abubuwan al'ajabi, masana tarihi sun tabbatar da cewa, babbar masarautane a
gurin me ɗauke da babbar fada na sarkin aljanu Penya, shine mamallakin fadar da
kuma alummarsu ta aljanu, lokacin da cutan ajali yazowa penya sai ya bar
wasiya, koda ya mutum Kalsh shine shine magajinshi, alakacin matar Kalsh
Sultana Neelah tana ɗauke da tsohon cikin, haihuwa ko yau ko gobe....
Bayan kwana biyu jikin mai martaba penya
yayi tsamari, haka duk wasu likitotin gargaji suna fama dashi, tashin hankali
yayiwa Kalsh yawa domin a lokacin aka sanar mishi, Sultana Neelah tana, kan
gwiwa,
Hankalinshi yayi matukar
tashi, ana cikin haka Sarki Penya ya mutu, hankalin Kalsh yayi matukar tashi ga
rashin Uba ga matar a wani hali gabi ɗaya sai ya shiga kiɗima, ana hidima kai
mahaifinshi amna shi ya koma kofar ɗakin karɓan haihuwa, ya zauna.
Sai da Neelah tashafe kwana biyar
sannan ta sami nasaran haihuwar Y'arta mace, mai tsananin kyau wacce tunda ake
haihuwa azuri'ar ba'a taɓa samun y'a kamar yarinyar ba, sai dai abin takaici
kwanar Sultana Neelah ta mutu sakamakon ciwon cikin haihuwa, gashi a ranar aka
bawa Kalsh mulkin garin, ga murna ga bakinciki, fito mishi da Yarinyar jakadiya
tayi ta zube a kasa cikin kuka tace.
"Sultan
ga yarinyar nan, ta rasa uwarta a daren jiya."
Idanunshi cike da zubda kwalla ya
karɓi Yarinyar ya ɗagata ga Alummarshi yace.
"Sultan
Kalshe Penya, Nasamu Y'a mace naka mata Suna Mineerlik, haka kuma kujeran
mulkina shima sunansa kenan Mineerlik, da fatan ku sanya mata albarka."
Cikin maɗaukakkiyar murya alummar
aljanu sukace mun ji mun amince da abinda kace munawa Sultana Mineerlik, Barka
da zuwa da kuma albarka ya cika rayuwarta."
Juyawa Sultan kalsh yayi rike da jaririyar,
zuwa cikin gida ya isa har ɗakin da gawar Sultana Neelah, yana shiga ya zuɓa
gwiwarshi cike da zubda kwallah yace.
"Neelah
kin ɗaukar min alkawari baki cika ba, Ina soyayyar da kika fada min zamu shimfiɗa
ina kaunar da kika min alkawarin zamu nunawa abin ciknki Neelah ya zaki tafi
kibarni da ɗawainiyarta, Ina soyayyar da kika min alkawari min, abar kaunata
kin tafi kin barni da kewarki da soyayyarki wanda yake tankar gubace a
gareni."
Kuka yake cike da damuwa da ɗimauta,
ruwan kwallar dake zuba daga idanunshi yana sauka akan fuskar mineerlik, a
hankali ta buɗe idanunta tana kallon mahaifinta, sai ta rufe, sabida ɗigar
kwalla, jakadiya ce tazo amshi Sultana Mineerlik a hannunshi wacce take motsi
da kuka kasa kasa, na alamun yunwa, dan har tasaka hannunta abakinta....
#mamuhgee
TARAYYA
wattpad@mmamuhgee
Haske writers association💡
36
Not edited
A gaggauce
Mineelik
nada kwarjini da wani irin haske na tsananin kyawu Wanda yasaka Sam babu mai
ganinta daga haifinta sai mai kulada ita shiyasa bakowane yasantaba musamman
daya zamto itace kujerar mulkin mineelik ayanda abin yake mahaifinta yariga
yayi amfani da wani irin sihiri akan karagar da sunan mineelik yanda ko bayan
mutuwarsa babu Wanda zai iya raba mineelik da karagarta kuma barinta a nahiyar
na nufin mutuwar duk Wanda ke nahiyar kuma babu Wanda yasan da hakan sai ita
mineelik din da mahaifinta sbd ganin bai haifi namiji ba yasa aka fara farautar
karagar mulkin.
Mineelik na
zama cikakkiyar budurwa qannan mahaifinta su hudu suka hada kai suka kashe
mahaifinta mutuwar wulaqanci sbd wani irin zalamar son hayewa karagar saidai
bayan kashesa suka kashe junansu agurin sbd kowa nason shine zai hau.
Lokacinda
mahaifin mineelik zai mutu saida ya shafawa karagar jininsa dake zuba na suka
hudu dasukai masa cikin tsananin azaba da taurin zuciya tareda fushi mai
tsanani ya daf karagar yace,
Ni penya
maqagin wannan karagar ayau jinina ya zuba sbd wannan dazata zamewa duk wani
makusanci agareta masifa ayau ina mata baki mai hadeda tsinuwa duk Wanda
zai hauta tazamo ajali mai masifa agaresa matuqar ba MINEELIK-ASSULTANAH bace
take kanta har ranar dazata na'da wani akai da kanta sbd jinina da aka zubar
akanta daga wannan qarni nawa ta haramta ga dukkanin qarni masu zuwa.
Lokacinda
mineelik ta fito bayan mutuwar mahaifinta aranar duk Wanda ke bousk yaganta
sukaga zallar kyawun halittar dabasu taba ganiba saidai cikin rashin sa'a
fitowarta tasaka rayuka da dama mutuwa dan kuwa wani irin haskene da maganadisu
atareda ita dake jan mutane zuwa gareta Wanda wannan abin shine atareda karagar
mai janyo mutane da rufewar zuci da ido akan hawanta.
Ranarda
mineelik tahau karagarta amatsayin assultana aranar akayi wani irin tashin daya
faru aranar shine koda gari ya waye duk Wanda ke nahiyar babusa.
Tashin
hankali data shiga shine tabarwa datayi alamun mulkintane bazaiyi kyawuba sbd
karagar tayiwa jininta qarfi kasancewarta mace.
Ita kadai
tayi rayuwa mai tsayi,shekaru masu tsayi batareda kowaba,
Kadaici,qunci,baqin
ciki da kewa sune abokanan rayuwarta sai karagar wadda ahankali take zuqe mata
tausayinta sbd babu wani Wanda za'a yankewa hukunci a zubarda jininsa shiyasa
abin yake cinta itakadai makari 'dayane mahaifinta yasanarda ita na wannan
karaga shine soyayya mafi qarfi amma idan idan sadaukarwar abu mafi soyuwa
tashigo.
Sanin kaf
acikin duniyarta babu Wanda zai iya ko 'dago kai yakalleta sbd kwarjininta bare
ya iya samun soyayyarta saidai ta tabbatarda wannan azarbabin da gaggawar
tareda rashin tsoro da kwadayin sai bil adama.
Wannan shine
burin
Hakan yasa
ta rufe daularta babu wanda yake ganinta sai ita tafara fitowa duniyar
bil adama domin kuwa babu abinda take buqata da tsananin buri kamar soyayyar da
babu irinta a qarnin.
Aduk shekara
da kalar suffan datake fitowa saidai bata taba dacewaba amma alqawarine bazata
daina neman soyayyaba harsai ta mutu.
Shiru sukayi dukkansu kowanne najin zuciyarsa a bushe babu wani
tsoro ko fargaba sbd dama nema suka fita duniya dan haka su sunga zinari kuma
bazasu danganaba harsaisun mallaki wannan karaga Ajani ne ya gyara zama yayi
gyaran murya yace,
"Toh
shi zinarin yana tare da ita kenan?
Gyara zama aqoob yayi cikin muryan da ta manyanta da
tabbarda abinda zai fada yace,
"Ita da
kanta itace zinarin sbd itace kujerar mulkinta,sunanta sunan karagarta daularta
itace arziki da kowa ke fatar samu saidai hadarin dayayi Katanga wa arzikin
shine soyayyarta wadda itakaice mukulli ga wannan taskar arzikin.
Kallon kallo suka shiga yiwa junansu
saidai babu Wanda alamar tsoro ko fargaba yake ataredashi Jamal ya kalli cikin
idon aqoob yace,
Shirye muke da mallakar wannan dukiyar kota halin
yaya koda soyayyar tatace mun shirya nema.
Murmushi bokan yayi yana jinjina qarfin zuciya da buried tareda
rudu irin nasu sannan yace,
"D'ayanku
zai faɗa soyayya da ita amma kafin nan sai kunyi jiran shekara ɗaya,
wanda haka zai kasance kamar ganganci da wasa da rayuwarkune sbd hadarin dajin
dakuma tsawon lokacin dakuma mataki uku masu matuqar hadari,
idan kuka
tsallake mataki uku da zai faru kafin bayyanarta toh tabbas soyayyar ɗayanku
zai kulu da ita, sai dai ba soyayyar bace mai muhimmanci dukiyarce mai
mahimmanci domin sonda zai gwada mata shi zai sanyanta buɗe mishi alkaryanta da
taskar mineelik.
Kallon juna suka sakeyi kowannensu idanuwansa acikeda
rashin tsoro ajani yace,
"Toh
boka matakai uku da zamu bi dan samun kusanci da ita menene fa'idar
haka."?
Mikewa bokan yayi tsaye, ya shiga zagayesu har ya tsaya a tsakiyarsu murmushi
yayi yace,
Zakusansu da
sharadin taskar arzikin tamuce muduka.
Kallonsa sukayi cike da mamaki da jinjina kwadayinsa saidai
zasu iya yin komai da mallakar taskar kojo ya kallesa yace,
Baca Juga
"Mun
amince, zamu raba da kai.
Dariyar
jin dadi yayi yace,
Tareda
yarana biyu za'ayi wannan tafiyar tareda rubuta sheda a faifan fatar raqumi da
jinin dukkaninmu za'ai rubutun kowa zaibada nashi arubuta a ajiye tarihi ya
shaida wannan taskar arzikin mineelik tamuce mu duka.
Babu musu
kowanne yafitarda 'yar qaramar wuqarsa dake some a qafafunsu suka 'diga jininsu
a 'yar qwarya akai rubutun atake ya ratayesa a bangon dakin.
Yaransa biyu
suka shigo yonas da haji yakallesu yace,
Gasunan kuma
tabbas akwai haske mai disashe duhu akwai duhu mai disashe haske.
Dayake zuciyoyinsu a shirye suke sun kafe
kwaɗayi da son zuciya ya rufe musu ido ba tare da wani bata lokaciba suka
amince Jamal dake gyara zaman wuqaqensa dake shanye da dafi kala dabam dabam na
macijai da kunamu harma da dafin kada yace,
"Tunda
nine zan fara aikin kwada soyayyata dole kasona yazamo mafi nauyi a raqumi.
"Jamal kasonka shine mafi nauyi a raqumi sbd kaine
zaka bamu gudunmawa mafi girma a cikin tafiyar,
abinda zai
faru idan kuka isa dajin domin jiranta akwai tsoratarwa daga muyagun aljanu da
dabbobi masu firgitarwa da suke yawo cikin dajin,
matakin farko zai farane
daga kwanaki uku kafin bayyanarta zaku kasance kamar makiyan juna a ranar
farko,
Zakiji tsana
da qarfin son kashe juna mai qarfi na shigarku saidai karku bari hakan yaci
qarfinku sbd dayafi qarfinku zaku kashe junanku cikin rashin imani.
rana na biyu
kuwa bazaku ga giftawar tsuntsaye ko wata dabba ko dayaba ko wni iri har kukan
namun dajin bazaku ji ba.
a rana na
uku da zata bayyana wani mugun zafi da kishirwa zai buwayeku kamar zaku mutu,
domin zaku ji har cikin jikinku zai koma kamar babu ruwa da jini a ciki, zuwa
yamma ko dare zata bayyana, kai Jamal aikinkane kutsa kai cikin dajin domin haɗuwa
da ita duk rintsi duk tsanani babu waiwaya.
Shiru sukayi
cike da al'ajabi suke kallon kallo sabida jin abinda zai faru dasu wanda suke
gani kamar faɗar bokane,
Kallon bokan jamal yayi cikin nutsuwa yace.
"Wannan
indai shine sharuɗan mun amince.
Murmushi boka yayi sannan yace,
Tafiyace mai
zuwa babu tabbacin dawowa abin bautarku ya kubutar daku.
"Toh ni dai har yanzun abinda nakeson ji
shine me zamu mata musamu dauko dukiyar mu mallaketa" Inji Amari.
Kallon Jamal bokan yayi cikin murmushi ba shi yayi
tambayar ba amma ya maida idanunshi kan jamal,
ɗaukar
duwatsunshi yayi ya watsa har lokacin idanunshi nakan jamal, juyawa yayi
yace,
"Lokacine
zai nuna mana abinda zai faru ynz zan baku wasu madaurin dantse ku ɗaura gudun
karku cutar da kanku.
"Wannan
zai kareku daga cutar da juna, sannan babu wani abinda zai cutarku nagama daku
sai ranar da yasamu nasaran isa birnin Sarauniya mineelik, zamu karasa aikinmu
nakarshe."
Mikewa sukayi baki ɗaya suka fita koda suka isa bakin kofa, kallon
jamal yayi cike da tausayi, sannan yace.
"Duk
bayan lokaci mai dan tsayi ina son Babbanku yazo ya faɗa min cigaban da kuke
samu."
Kallon
'yayansa yayi ya jinjina kai cikin muryar jarumta da bankwana yace,
Abin bauta
yasa musake haduwa.
Haka sukayi bankwana dashi suka tafi.
**
Tunda
suka tafi, kaman yanda bokan ya faɗa musu haka ya faru, sabida sun ɗaura ɗanbar
wani kudiri a ransu, ranar farko, suna kwance sai suka fara jin shashekar kuka,
kamar na yaro kaman na babba haka aka cigaba da razanasu da wani irin
mahaukacin kuka, kafin aka samusu dariya irin na bantsoron nan, can da dare
yayi tsakiya, sai kana kwance a cikn tantinka za'a zo ana kiranka daga kan
ajani aka fara,
yana kwance ya dunkukune a marufinshi yaji an
tsaya abakin tantinsa ana cewa.
"Ajaniiiiiiiiiii"
D'auke numfashinsa yayi cak, tsabar tsoron, haka aka
kewayasu ana razanasu.
Wasa wasa sai da suka kwashi fiyye da wata
biyar ana tsoratasu da abubuwa a gurin tuni suka saba da rayuwa adajin sbd dama
dukkaninsu sunsaba da rayuwa a daji dan haka yanzu gida suka dauki dajin sbd
burinsu abune dazasu iya komai akansa.
lokacin da suka cika wata shida Ajani yaje ya
faɗawa boka abinda ya faru, nan ya zauna ya faɗa mishi abinda zasuwa Mineelik
dazaran ta faɗa soyayya da Jamal. Bokan ya cigaba da cewa,
"
Matuƙar mukace muna son dukiyar baxata bamu cikin lumana ba. Karshe rabaku
xatayi da ɗan uwanku amma idan mukayi haka toh babu wata damuwa sannan zan nema
muku abubuwan da zakuyi amfani dashi, karka bari ɗan uwanka yaji labarin dan
matukar yaji bazai yarda yayi aikin ba."
Gyaɗa kai ajani yayi sannan yabar garin ya koma dajin, nan suka
cigaba da zama ga tsoratasu da ake ga kwanakin kamar baya tafiya, duk sun kaqu
da faruwan haka,
Da zaran sun zauna hiransu kenan, akan yanda zasu juya dukiyarsu da suka
samu, daga gareta, a hankali lokacin yana tafiya wasa wasa sai gashi har saura
kwanaki bakwai zata bayyana,
......
Bayan kwana huɗu wata rana da safe suka tashi da mugun faɗa
kaman zasu kashe junarsu, kaman dai yanda bokan ya faɗa musu, karshe rabuwa
dasu Jamal yayi ya koma gefe dan ya hassaso wannan rigimar yana cikin alamomin
bayyanarta nan yatunatar dasu nan kowa yayi nesa da 'dan uwansa suna fidda wani
irin gumi najin wani irin qarfi mai razanarwa na son kashe dan uwansa.
rana tabiyu
kuwa sun tashi da babu giftawar tsuntsaye ko ɗaya tareda wani irin tsoro mai
firgitarwa dayake shigarsu wanda suka tabbarda natane amma haka suka dinga
daurewa cikin wata irin jarumta.
Rana mafi tashin hankali shine ranar bayyanarta tsananin
zafin da ake yaja sukaita fad'uwa, gashi sun shanye ruwansu, dakyar Jamal ya
mike yace.
"Yaku
Y'an uwana wannan itace rana mafi hadari ageremu saidai ina fatar mana samun
nasara."
Daqyar su
kojo suka rarrafo gurinsa suka rungume juna cikeda tsoron rabuwa da juna saidai
burinsu ya zarce komai.
Daqyar suka
rabu da juna yana rangaji yana faduwa yana tashi sbd yunwa,zafi da qishirwa
dake neman lahantasu ya nausa dajin inda ranar suka fara ganinta baisan inama
yake jefa qafafunsa ba sbd azabar dayake ji cikin hanjinsa da cikinsa.
Duhun
dare nayi yana isa gurin saidai ba'a cikin hayyacinsa ba sbd tuni yafara ficewa
hayyacinsa atake ya yanke jiki gurin yafadi yana fitarda numfashi daqyar.
Ahankali kunnuwansa suka fara jiyo amo da sautin sarqar zinarin
qafarta sanye take cikin kaya ruwan
makuba fuskarta na fitarda wani irin annuri duk da cikin duhune atake yaji wani
sanyi na yaye masa yunwa da wahalarsa suna barinsa ahankali.
Cikin wani irin takun nutsuwa da wata irin haiba ta nufo hanyar taku kadan tayi
ta tsaya cak tareda lumshe fararen kyawawan idanuwanta.
A hankali ta
juyar da kanta tahangosa kwance ba alamar yana numfashi.
A hankali
takalli jikinta ahankali ta rikide ta sauya zuwa wata kyakkyawar bafulatar
baqar Ethiopia sarqoqin jikinta na
zinari suka koma duwatsun dandaye masu qaramin kyau ta nufosa numfashinta na
wani irin sarqewa sbd wannan shine karo na farko data taba ganin wani biladama
wadda take tabbarda shine Wanda ta dibi shekaru da qarnika tana jira.
A hankali ta durqusa gabansa tareda daga daga
dogon hannunta ta ta6a goshinsa atake ya bude idanuwansa yana kallon fuskarta
bai san lokacin da ya sume ba,
ruwan dake
cikin goranta ta fulanin daji ta ɗauka ta watsa mishi, a hankali ya buɗe
idanunshi sai akan fuskarta.
Cikin idanunta ya kalla kamar wanda aka ɗiga mishi ruwan
gold, lumshe idanunshi yayi.
"Sannun ko" tace mishi...
Wani irin
sauti yaji daga muryarta wanda yakusan sake sumar dashi yayi wani irin jarumtar
daidaita numfashinsa da nutsuwarsa yayi kalar wanda ke cikin tsananin wuya ya
daga mata kai daqyar alamar amsawa yana jan numfashin qarya daqyar.
Kasa wata
maganar tayi tasauke kai tana kallon qafafunsa dake cikin takarmin fatar
damisa.
Sunkuyar da kanshi yayi ahankali kwalla na
zuba daga idanunshi cikin muryar tsananin damuwa da baqin ciki rayuwa yace.
"Me
yasa kika taimakeni?
me yasa baki barni na mutu ba? na gaji
da rayuwar duniya gwara na mutu nabar duniyar nan."
Kallonsa tayi cikin sauri da nutsuwa da laushin murya
tace,
"Koma Ya-yane dai rayuwarka tana da
amfani,
ka daina cire tsamani da rayuwa, dan ko badaɗe
ko bajima zaka amfani rayuwarka tana da amfani."
Kuka ya fashe da shi yans kwaɗa
kanshi da bishiya yana cewa,
"Kaicon
rayuwa dan ina maraya shine bazanyi rayuwa kamar kowa, gwara mutuwata."
Duk ya jiwa
kanshi ciwo,
tausayinshine da mamakin bil adamane ya kamata
musamman ace yaganta mace cikin wannan dajin da tsakar dare amma bai nuna
shakku ko tsoro da fargaba ba kodai yasan da fitowartane?
Satar
kallonta yayi yaga alamar tunani da nazarinsa takeyi yasan dole yayi dubarar
hanata zarginsa hadiye wani mugun yawu tareda zabura gefe jikinsa na wani irin
mazari ya nunata da hannunsa dake mugun rawa a tsorace da rawar murya yace,
Ke...keee...ke
wacece?
Me...mee
kikeyi anan ke daya?
Kallonsa
tayi ahankali cikin nutsuwa ganin yanda yarude yake neman zaucewa atake tasaki
numfashi mai Sanyi tasaki murmushin daya sakasa zubewa kan gwiwoyinsa.
cikin sanyi
murya tace.
"Nima
marainiyace kiwo yakawoni kusadanan 6atan hanya yasakani shigowa nan hanyata
nake nema amma nakasa ganewa.
Cikin dubara
yayi baya alamar tsoro ya buga kansa da bishiya sosai nan take yafadi Jini na
fita goshinsa.
Hannu ta
daga ahankali zata shafa ciwon danya warke ta dakata sbd karya sake tsorata
idan ya farko.
Tashi tayi ta fara niman ganyayyaki tashiga haɗa
mishi magani, tasaka mishi a ciwon,
Sun ɗauki kwanaki biyu a gurin tana kula dashi,
tun ranar da duka haɗu sukayi magana bata ce mishi kome ba, tsakaninta dashi
ido duk abinda majinyaci ke bukata take mishi. Zaman kuramen da suke ba
karamin, haifar musu da wani shakuwa yayi ba, dan zata zauna a fakaice tana
kallonshi, ko shi yayita kallonta, da zaran sun kama juna take kowanensu zai
shiga kame kame, ba yanayin da suke yana tafiya da wani irin tsari na musaman,
Jakarsa ta
kaya ya bude ya buga tantin rumfarsa itace take kwana aciki shikuma yana
kwanciya da wajen.
. . A hankali suke iya faɗawa junansu magana ko kuma hira
sama sama, a wata safiya ya tashi ya zauna dake ciwon jikinshi ya warke yace
mata.
"Zan
koma cikin gari, amma baki faɗa min sunanki ba, ni dai sunana Jamal ni maraya
ne, zanje sake komawa gurin dangin iyayena dana gujewa.
Kura mishi ido tayi cikin nutsuwa tace,
"Nima
marainiya ce bani da kowa,sai kai da na haɗu da kai gashi zaka tafi kabarni
Sunana Mineelik."
Wani irin
bugawa qirjinsa yayi sbd ambatar sunan kawai musamman duka kwanakin yayisu ne
babu ko kyaftawar ido bare bacci sbd yasan rayuwarsa na tsakanin mutuwa da
rayuwane idan yabari yayi kuskure dan qanqani taganosa.
Cikin tausayawa yace.
Bakyason
nabarki cikin dajin nan ne na zauna?
"Zanyi fatar haka idan ta kasance amma bazan maka dole
ba." tace mishi.
Shiru sukayi, suka cigaba da satar kallon
juna, a hankali shakuwar da sukewa juna ta sake samun matsaya na musaman ma
inda ta rikiɗe ta koma soyayya mai matukar ɗaukar hankali, tare suke
farautar abinda zasu ci, idan zatayi wani abu zama yake ya kareta, gabaki ɗaya
jamal ya sadaukar da lokacinsa sabida ita,, musaman suke zama suyita hira da
zaran yaga ta fara alamun jin barci zai barta ta shiga ta kwanta yana gadinta.
Tausayinsa
ne mai tsanani yashiga rayuwarta sbd kaf baida abinda yake sai kulada ita
tamkar sarauniya duk da baisan wacece itaba tabbas zata taimaki rayuwarsa kodan
soyayyarsa data ginu a zuciyarta.
#mamuhgee
Post a Comment for " TARAYYA 35-36"