TARAYYA 45 LAST PAGE
Saki jikinsa yayi sbd wutar data daukewa jikinsa da wani irin
qarfi ammy ta jijjigasa tareda kiran sunanda da qarfi ya durqusa tareda jawota
jikinsa ya dauketa gabaki 'daya yabar gurin da ita. +
Anso tsayarda nadin sarautar
amma haroun ya fitarda saqonta na gaba dake cewa duk abinda zai faru kar a
tsayarda nadin dakuma takardarta tagaba dake cewa a raba mara masarautar biyu a
rushe Rabin a gina masallacinda yafi kowane girma a qasar Ethiopia.
Hakan yasa aka cigaba da nadin
yayinda sultan dake zaune har aka gama bai motsa daga inda yakeba saida aka
watse aka gano ya rasu zaune agurin gakuma jinin da aka ganin ya digo daga
hancinsa.
Lokacinda su negasi suka rufu
akanta dan ceto rayuwarta alokacin ne aka zo da saqon rasuwar sultan Wanda ya
girgizasu ya qarasa wargaza dukkanin sauran nutsuwarsu musamman ammy data kasa
riqe kukanta maheer yayi saurin rungumeta yana riqe nasa hawayen sbd Allah
yasani yana qaunar mahaifinsa duk mugun halinsa sbd koyaya ya zama
mahaifinsane.
Cikin qanqanin lokaci rasuwar
sultan da halinda assultana take ciki tareda canza karagar mineelik suka yadu
'yan jaridu da kafafen yanda labarai sukaiwa masarautar wani irin dandazo ana
yada abinda ke faruwa.
Dukkanin iyalan marigayi
abdulshams sun halarto cikin tsananin baqin cikin wannan rana data riskesu
musamman 'yayan marigayiya adama dasuke ganin sun rasa uwa da uba.
Da maraice akai jana'izarsa
inda dubban alumma na nesa dana kusa suka hallara inda yawan jama'arsa yasa
maheer jin sanyi sanyi aransa tareda yiwa mahaifinsa adduar samun rahamar
Ubangiji.
Duk damuwar dayake ciki ta
halinda rumanah take ciki bai koma gurinta ba sai dare bayan an watse.
Kai tsaye sashen ammynsa ya
nufa inda ya tararda ita tareda sauran 'yan uwansa ya qarasa kusada ammyn ya
zauna yana kallonta cikin nutsuwa da tausayawa ya riqo hannunta ahankali ya iya
furta,
Allah yaji qansa ammynah.
Kwantarda kanta tayi kafadarsa
tareda cewa "amin" da muryarta data shaqe kafin ta 'dora da fadin,
Kaje gurin rumanah dan sanin
halinda take ciki duk da meenah da jakadiya na gurinta.
Jinjina kai yayi jikinsa na
qara sanyi da tuno wani tashin hankalin dayake ciki.
Lokacinda ya isa sashenta har
lokacin bata farfado ba sai jinin daya tsaya Wanda suke sakaran jinintane yayi
matuqar qasa sosai.
Zaune ya kwana gabanta yana
mata addua cikin wani irin hali dabai ta6a tsintar kansa aciki ba.
Washe gari koda akaga bata
farkaba hankula sukai matuqar tashi musamman da jikinta yayi wani irin fari
fari Kore Kore ga 'yan jarida dasuka kasa suka tsare a masarautar sunason
ganawa da sarauniyar data kafa sabon tarihi a qasar daba tataba.
Duk wani kalar likiti na turai
da gargajiya an nuna qwarewa amma abu yaci tura gashi alamunta na sake 6aci
ranar da akai uku aranar gabaki dayansu suka tattara suka nufi Georgia..shi,ammy
da jakadiya data samu 'yancin rayuwarta itama sai sauran 'ya'yan da kowace
takoma inda take aka bar sabon sultan dan gabatarda mulkinsa cikin aminci.
Suna sauka kai tsaye motar
asibiti tazo daukarsu aka wuce asibiti dasu cikin tashin hankalinda yafi na
farko sbd saki jikinta daya farayi.
Matsayinsa a babbar asibitin
garin yasa ana isa da ita dukkanin likitocin dake nan suka taru aka fara
qoqarin gano matsalar cikin gaggawa cikin tashin hankali da mamakin yanayin
matsalarta sbd basu taba cin karo da irin hakanba.
Ammy daqyar ta iya zama gida
saidai gabaki 'daya hankalinta da damuwarta na asibitin gabaki daya cikin kwana
ukun ta rame tayi wani irin sanyi ko doguwar magana bata iyawa.
STORY CONTINUES BELOW
Har gari ya waye likitoci na
kanta duk wata dabararsu da qwarewarsu sun nuna dan ganin ta farfado saidai Sam
bata farfado ba saidai fatarta data fara komawa daidai sbd jinin da aka saka
mata kusan leda biyu hakan yasa suke sakaran idan fatar ta gama komawa daidai
ta farka.
Daqyar yake iya hadiye yawun
bakinsa sbd tsananin bushewar bakinsa da maqoshinsa,
Duk wata nutsuwarsa da
tunaninsa sungama barin jikinsa idanuwansa tuni suka qanqance ko gani bayayi
sosai da idonsa dukkanin abokanan aikinsa sun tausayawa halinda yake ciki
shiyasa suma gabaki daya hankalinsu tashe yake da ganin ta farfado 'din.
Khaleefa aranarda suka wuce
aranar yasauka Ethiopia ya tararda abinda ke faruwa kasa kwana yayi duk da
rashin lafiyarsa washe gari yabi jirgin asuba sbd yasan aminin nasa na tsananin
buqatarsa.
Har yamma bata farkaba khaleefa
ma saukarsa garin alhaji babaye yakirasa sbd news din dasuka gani gameda abinda
yake faruwa a qasar nan yaqara yasanardasu abinda yake faruwa nan hankalinsu
yayi matuqar tashi suka fara shirye shiryen tahowa cikin gaggawa.
Qarfe goma na dare ta bude
idanuwanta dasukai wani irin shigewa sukai nauyi da ja.
Atake dukkanin likitoci suka
sake hawa kanta cikin gaggawa da nuna qwarewa tareda fatar samun nasarar sanin
matsalarta.
Kasa miqewa yayi sbd saki ga
gabobin jikinsa sukayi sbd fargabar abinda za'a fada masa saidai khaleefa ne ya
dafasa yana jinjina masa kai alamar qwarin gwiwa ganin halinda yake ciki.
Wasu sabbin dogayen hours suka
'diba suna qoqarin gano matsalar wadda suka gano daga qarshe wadda tayi
mummunan 'daga hankalinsu haka suka ringa fitowa jiki amatuqar mace zuciyoyinsu
ba dadi sbd dukkanin hotunansu da test test dinsu sun tabbatar musu da abu
'daya.
Dr Edward ne yafito qarshe yana
zare glasses dinsa yakalli maheer da khaleefa yace,
Can we talk in my office pls..
Tashi tsaye maheer yayi tareda
kallon qofar dakin da take yakalli Dr Edward din yana rintse idanuwansa da
abinda za'a fada masa yace,
Just tell me dr Edward I
c........
Dafasa Dr Edward yayi cikin
tsananin tausayi ganin daqyar yake iya bude bakinsa yayi magana cikin sanyin
murya yace,
I'm really sorry Dr m.a shams
matarka ta rasa gangar jikinta bazata taba gara aikiba ma'ana tanada rai tana
gani tana numfashi tanaji saidai bazata iya motsa jikintaba ko kadan bare
magana har abada.
Wani mugun jirine ya dibesa
khaleefa da Dr Edward sukai saurin nufarsa zasu taresa ta rigasu taresa cikin
kulawa da tausayawa.
Khaleefa ne yakalleta cikin
mamaki Dr Edward kuwa jinjina mata kai yayi alamar ta kula da maheer din yana
buqatarta fiyeda koyaushe.
Shikuwa idanuwansa na ganinta
baisan sanda ya sake fadawa jikinta yana qoqarin tsaida hawayensa saidai Sam
basu tsaiduba saida suka zubo ya sake qanqameta yana cewa,
Suhailat please pray for me wlh
zuciyata zafi takeyi I just can't live without her sbd wannan ma baida banbanci
da mutuwa agareta. 4
Murmushin tausayinsa tasaki
cikin sanyin murya tace,
Insha Allah zata warke
Nayi maka alqawarin zamowa
majingini agareka duk lokacinda kake buqatata wannan alqawarin yananan haryanxu
kuma nayi alqawarin cika makashi har qarshen rayuwata kuma zan tayaka jinyarta
harta ji sauki sbd sonka shine qaddarata maheer abdulshams..
'Dagowa yayi kalleta da
idanuwansa itama hawayen takeyi tana murmushi ahankali yaji wata irin
soyayyarta mai tsafta tashiga zuciyarsa akaro na farko cikin wata irin rawar
murya yace, 2
STORY CONTINUES BELOW
I love you suhailat sbd kece
hasken rayuwata dakike tallafoni koyaushe. 2
Wasu hawayene suka gangaro mata
ta rintse ido tana kwabar zuciyarta dake neman shegala da kamansa datasan ta
samesune sbd nuna qaunarta ga rumanah saidai matuqar qaunarta ga rumanah zata
jawo masa soyayyar mijinta to tabbas ta shirya samun soyayyar mijinta ta hakan.
Duk yanda ya 'daga hankalin
likitocin asibitin akan abinda sukace dole ya dangana yadauki qaddara sbd
result din dayane.
Ko ammy saidata kwana ta yini
tana kukan halinda rumanar ke ciki da Wanda yashiga sbd gabaki daya ya birkice
musu ko abinci sai ammyn tayi kuka yake iya shan abu mai ruwa ga suhailat data
zamo batada wata hidima saita kula da dukkaninsu sbd sundawo gida. 1
Idan yazo ya zauna kusada ita
haka zai riqe hannunta cikin nasa ya qura mata ido
Itadai hawayene kawai ke iya
gangarowa ta gefen idonta musamman idan ammy tasata gaba tana kuka kokuma shi
idan yazo ya zauna yasaka gaba ya qura mata ido tana iya hango mawuyacin
halinda yake ciki.
Ranarda su hajiya yakurah suka
iso aranar kuka yadawo sabo ganin halinda 'yarsu dasuke 'dokin gani take
ciki...
Ko alhaji babaye dake dattijo
saida ya zubarda hawayen baqin ciki da farin ciki.
Akwance take itama amma
hawayene keta bin gefen fuskarta suna zuba Wanda hakan yaqara bawa kowa
tausayi.
Duk da akwai Carolina sosai
suhailat ke wahala sbd lalurar rumanah din.
Kusan satinsu alhaji babaye
biyu kafin shi ya koma yabar haj yakurah dataqi dawowa tana jiran isowar
mijinta dazasu tafi tareda rumanah sbd gwada nasu na addinin.
Satin alhaji babaye daya da
tafiya alhaji mukhtar mijin haj yakurah ya iso kallo 'daya yayi mata yagano
lalurarta Allah takeson akomawa sbd lalurace ta iska nan take suka yanke
shawarar tafiya da ita maheer kai tsaye ya nuna rashin amincewarsa
Saidai ammy dataga yana mutuwar
tsaye kullum sbd lalacewa da rayuwarsa ke nemanyi dan ko aiki bai taba fitaba
koyaushe yana gida ga suhailat data zamto abar tausayi gurin qoqarin kulawa
dashi da rumanah duk ta rame tausayinta da qaunarta yasa kai tsaye ta zaunar
dashi cikin nutsuwa ta fahimtar dashi kuskuren dayake jefa rayuwarsa da
iyalinsa ciki dan haka yabar rumanah aje da ita ya tsaya ya gyara mu'amalarsa
da rayuwar aurensa da suhailat.
Sosai jikinsa yayi sanyi kuma
yasan matuqar yanason gyara rayuwar iyalansa ta inganta saiya boye soyayyar
rumanah kwata kwata dan haka zai danne Zuciyarsa yafara daga yanzu.
Da haka ya amince aka tafida
rumanah din amma hardashi suka tafi saidaya kwana biyu yadawo dan qoqarta gyara
mu'amalarsa da suhailat.
Koda yadawo su ammy da jakadiya
tareda abeel sun komawarsu Libya dan haka gidan dagashi sai suhailat sbd su
amah ma suna Mali tabarosu dama itakadai tazo.
Aranar daya dawo lafiyayyan
tarba tayi masa cikeda Dari darin yanda zai dawo yayi rayuwa a inda babu
rumanah.
Ganin yanda take kama kanta
dashi duk sai yaji ya muzanta ya tattaro jarumtarsa ya danne abinda ke ransa ya
riqo hannunta ahankali tareda jawota jikinsa yana kallon fuskarta dake kallonsa
yasaki qayataccen murmushi yajata suka zauna bakin gadon dakinta daya shigo yasameta
hartayi shirin bacci zata kwanta.
Kallonsa takeyi tanason gano
damuwarsa saidai takasa ganin komai sai murmushin dayake sakar mata
Wani irin sanyi da farin ciki
taji na shigarta ahankali kenan kalamansa daga zuciyarsa suka fito lokacinda
yafada matasu.
Rungumesa tayi da sauri tana
sakin hawayen farin ciki ta murmushin jin dadi.
Dagota yayi tareda zare mata
riga yana murmushi yace,
Banyi wankaba so yau kece
zakiyi wannan aiki.
Noqewa taso yi tana murmushi
yayi saurin riqeta yana kallon cikin idonta ya girgiza mata kai ahankali yace,
STORY CONTINUES BELOW
Don't make that mistake again
suhailat.
Kallonsa tayi tareda jinjina
kai takama hannunsa ta nufi hanyar toilet dinta dashi suka shige.
Aranar wata irin rayuwa suka
gudanar data mantarda suhailat dukkanin damuwarta ta dah inda sukai alqawarin
dora sabuwar rayuwar aure ta fahimta,soyayya qauna da aminci atsakanin su uku
da 'yayansu daga yanxu.
**
Ahankali ake gudanar da adduoi
da sauran abubuwan addini tareda sauke al-qur'ani da sadaka ana fatar samun
sauqi.
Kulawa sosai da wata irin qauna
da soyayya suke mata kaf zuriar banda zuriar gidansu aqeel data gama tarwatsewa
babu wani nakamawa acikin zuriar gidansu shiyasa koda sukaji 'yarsu bulama
tadawo kuma a nakashe kota kan zancen basubiba.
Su kuwa haj yakurah tamkar 'yar
data haifa da cikin ta takejin rumanah duk wata kulawarta da dukkanin hidimarta
takoma ta rumanah shima alhaji babaye kullum saiyazo gidan sbd yayi yayi tabari
rumanah takoma gidansa taqi yarda tabari.
Watanta hudu a Nigeria yazo
dubata babu adadi duk tareda suhailat suke zuwa Wanda itama tanajin farin cikin
ganinsa da suhailat sbd ganin hankalinsa ya 'dan kwanta sosai duk sukazo idan
zasu tafi daurewa kawai yakeyi yakoma sbd alqawarin adalci daya daukarwa kansa.
Baca Juga
Ammy kuwa kusan tamafi maheer
din zuwa kuma takan dade idan tazo.
Ahankali tafara samun sauqi sbd
wasu gurare dasuka fara motsawa ajikinta Wanda hakan ba qaramin farin ciki da
qwarin gwiwa yasakasuba nan aka sake maida himma ga sauke al-qur'anai da sadaka
da adduoi.
Ba'a rufa wata biyu da fara
motsinta ba tafara magana ahankali har tana iya tashi zaune da kanta ta tashi.
Lokacinda wannan saqon ya iso
masa aranar suhailat harda hawayen farin cikin ganinsa cikin tsananin farin
ciki mara misaltuwa tayi sbd Sam kasa boye farin cikinsa yayi.
Kafin sati biyu dukkanin
kuzarinta sun dawo lafiya kalau saidai bata iya komai da sauri ko qarfi Wanda
hakan shima ahankali zai dawo. 1
Washe garin ranarda umma
yakurah da ammy suka fada masa samun lafiyarta yatafi wannan karon suhailat qin
biyosa tayi sbd ganinta kusa zai hanasu nuna kewar junansu.
Sai dare sosai ya isa Wanda
tareda khaleefa dazaije gurin nuratu sukayo tafiyar dole suka sauka masaukinsu
kai tsaye sai washe gari suka nufi gidan guraren qarfe goma shima sbd khaleefa
daya hanasu tafiya tunda safe.
A babban palo suka tararda su
umma da ammy harmada Jakadiya da sabuwar mai rainon abeel suna ganinsa umma
tayi murmushi sbd tanajin dadi da farin cikin yanda yake tsananin qaunar
rumanah dinsu.
Ammy ma dariyar tayi masa inda
aka gabatar musu da abincin breakfast saidai sunyi breakfast already.
Duk yanda yaso ganinta qin
barin su kebe umma tayi qarshema anan palo tasa Nana aishat 'yar autarta taje
kairawo rumanah din tajima kafin yafito sanyeda dogon hijabi har qasa daya
matuqar yimata kyau sbd wannan ne karo na farko daya ganta sanye dashi itama
anan din takoya sakashi sai tanajin dadinsa.
Kasa 'dauke mayun idanuwansa
akanta yayi musamman yanda ta canza sosai takoma kamar ba rumanarsaba datasha
wahalar rayuwa dan lokacin.
Wani irin murmushi yasaki Wanda
shikadai yasan yayi abinsa sai ita data gani ta dauke kai tana gaidasu cikin
yarensu sbd har gwara khaleefa yafara son koyar yaran Hausa sbd nuratu dayake
yawan ziyarta shikuwa haryanxu yakasa koyan komai.
Koyaushe da turanci yake magana
dasu umma da alhaji babaye hakama ammy.
Kwanakinsa uku amma Sam umma
taqi barinsu kebewa hakan ya matuqar dama lissafinsa shiyasashi tattarawa
yakoma gashi ko waya basayi bare yarage zafi.
STORY CONTINUES BELOW
Koda yadawo suhailat ta lurada
bai cikin dadin rai da walwala saidai batai shishigin tambayaba tunda bai shiga
haqqintaba.
Bayan sati biyu kai tsaye
yakira alhaji babaye yasanardashi yanason rumanah tadawo tunda taji sauqi koda
alhaji babayen yayiwa umma magana kai tsaye tace sai wani wata sbd zasuyi walima
dakuma 'yan shirye shirye.
Baisoba amma sbd ammy data basa
hakuri saiya bari din badan yasoba.
Hidima sosai da gyara irin nasu
na asalin 'yan Maiduguri.
Taron biki sosai akayi tamkar
yanxune zaa daura mata aure akai walima da yinin biki na alfarma inda ko nanma
'yan jarida basuyi qasa da gwiwaba sunxo ganawa da tsohuwar sarauniyar qasar
Ethiopia saidai maheer daya bada gargadi mai qarfi akan karta kuskura barin
kowa yadauki hotonta ko fira da ita.
Lokacinda nuratu ta iso gurin
bikin sosai sukayi farin cikin ganin juna dakuma auren nuratun da khaleefa
keson yi.
Irin gyaran da akai mata da
shirin da akai mata ita kanta burge kanta takeyi ga wani irin qamshi daya kama
jikinta. 1
Dukiyarta kai tsaye tace suci
gaba da kulawa da ita tabar musu halak malak bata buqatar komai.
Ranarda zasu tafi ammy ce da
jakadiya sai umman da matar alhaji babaye da yaransu 'yan mata da nuratu suka
rakasu har Libya tareda dukiyar aure mai tarin yawa inda sukai kwana biyu suka
juyo suka barota.
Sabuwar rayuwa ta bude a Libya
inda nanma ammy wani gyaran ta dora ranarda tacika kwana shida cif aranar aka
sai mata ticket ta wuce batareda abeel ba.
Qarfe uku na yamma jirginta ya
sauka suhailat ce tazo daukarta sbd ogan na hospital gurin aiki baimasan aranar
zata dawoba ammy suhailat kawai tafadawa shiyasa tazo daukarta.
Cikeda farin cikin ganin juna
suka rungume juna suhailat na mata sannu da zuwa da cewa,
Where is my abeel?
cikin farin ciki ta amsa tana
cewa,
Ammy ce ba ruwana.
Wani gida na daban taga sun
nufa Wanda yafi nada girma sosai tun a harabar gidan ta fahimci kowaccensu nada
wadataccen gurinta yanxu.
Da gudu su amah suka fito suna
mata oyoyo ta riqe hannun fammah data fara mantata tayi kissing goshinta tana
cewa,
Famman mum 'dinta.
Babban lafiyayyan qaton palonsu
suka shiga nan suhailat ta rakata da luggage dinta har cikin dakinta dake
daukeda parlour da two bedrooms aciki ga komai nata is white.
Bayan fitarsu wanka tashiga
tana fitowa tayi sallolin dake kanta dasu magrib da akayi tana gamawa ta shirya
cikin pencil skinny jean blue daya kama cinyoyinta da White shapeless top sai
White club scarf data rufe kanta dashi ta fito fiddo wayarta daga handbag dinta
taga misscalls dinsu umma da ammy harma dana nuratu tafara kiransu daya bayan
daya tana cikin wayane da ammy suhailat tashigo tana murmushi itama cikin
adonta na wani black straight skirt daya fiddota da red chiffon top gashinta
daure saidai bata saka hula ba tace,
kiyi sallar ishai kifito muyi
dinner already your ango is home.
Murmushi tayi tana cewa,
Ok ganinan zuwa.
Sallar ishai tayi tana gamawa
ta gyara scarf dinta tareda fesa turare da humra mai sanyin qamshi ta fesa
mouth freshner abakinta ta dauki wayarta ta fito.
Zaune yake kan dining din
shidasu amah sai suhailat dake qoqarin zama ta gama zuba nata abincin
Ta bayansa yajiyo wani irin
qamshi ya lumshe ido ya bude dan tabbas kodata canza turare kusancinta
sanannene a zuciyarsa tana qarasowa gabansa abincin daya saka bakinsa ya
sarqesa ya rufe baki yana tari da sauri suhailat tabashi ruwa tana dariya tace,
STORY CONTINUES BELOW
Easy karka illatamin kanka
she's really here ba gixo bane.
Karba yayi yasha yana watsa
mata wani kallo yace,
Dake aka hada baki right...
Murmushi tayi tace,
Ba ruwana ammy ce.
Juyowa yayi ya kalli inda take
cikin wani irin shauqi da tsananin soyayyarta dake fizgar zuciyarsa duk yunwar
dayakeji ta bace.
Ita kuwa abincinta takeci
hankali kwance duk da zuciyarta rawa takeyi sbd irin kallonsa datakeji yana
yawo ajikinta.
Barin dining din yayi sbd zai
iya bada kansa yakoma kan kujerun palon ya zauna yana canxa channel zuwa news
duk da dai Sam baimasan meyakeyiba sbd halinda zuciyarsa take ciki.
Bayan sungama Carolina ta
tattara gurin suhailat takaisu amah daki sukai duk abinda zasuyi suka kwanta
saidata tabbatarda sunyi bacci tafito lokacin ba kowa palon kowa na dakinsa.
Dakin rumanah ta nufa kai tsaye
tayi mata saida safe tareda sanarda ita kwana biyu biyu zasu riqa yi tace mata
tou.
Tana sane ta sharesa taqi zuwa
gurinsa ta tube ta dauko rigar baccinta zata saka saidata daga hannuwanta zata
saka taji an zare towel 'dinta da sauri ta juyo Ashe amatse yake da ita tana
juyowa sai a jikinsa atare suka sauke ajiyar zuciya yana zare rigar hannunta
yayi jifa yana kallon cikin idanuwanta dashi itama take kallo.
Jikin wardrobe ya matseta yana
cigaba da kallonta zuciyarsa cikeda wani irin farin ciki ahankali yace,
Wani irin sone zuciyata ke miki
ummu-rumanah bulama.
Kunnensa takai bakinta cikin
wani irin salo tace,
Irin sonda ummu-rumanah kewa
maheer abdulshams..
Wani irin murmushi yasaki
tareda hade fuskarsu sbd tsikar jikinsa data tayar masa ya dora bakinsa kan
nata yace,
I love you ummu-rumanah bulama.
I love you more maheer
abdulshams.
Hade bakinsu yayi suka saki
numfashi atare cikin tsananin kewar junansu ya cirata suka isa gadonta ya zura
hannu ya kashe wuta.
Washe gari da wuri ya tashi
yayi shirin office bayan sun gama lalacewarsu har gurin wanka.
Atare dukkaninsu sukayi
breakfast kafin shiya fara fita tukuna yaran sai suhailat data futa qarshe.
Yaso dawowa gida da wuri amma
sbd dorarta zaman lafiya da qauna tsakanin iyalinsa yafasa harsaida lokaci yayi
yadawo.
A ranarma a dakinta suka
bajewarsu saidai duk yanda yaso qin latti saidayayi sosai.
Watanta shida da dawowa tafara
laulayin ciki Wanda take samun kulawa sosai daga garesu har Allah yasauketa
lafiya tasamu 'yan biyu mace da namiji.
Zaman lafiya kwanciyar hankali
tareda aminci da qaunar juna mai cikeda fahimta suke gudanarwa tareda girmama
juna. 1
ALHMDLLH nan nakawo qarshen
tarayya da yardar Allah masoya ina miqa godia sosai sbd wlh yawanku bazai bari
na iya batokuba.
Kusani dai mamuh takuce kuma
natane. 2
Idan nayi kuskure ko mantuwa to
kuyimin uxuri Allah yabamu ikon daukar darasin ciki.
FAHIMTARWA...
Idan marubuci yayi rubutu
za'ace bai San abu ba baiyi bincike akan abu ba amma yaje yarubuta sbd shirme
da rashin sanin meye rubutu..
Tou kuma idan mutum yayi
binciken yarubuta yanda abin yazo ace baida ilimi..
Labarin tarayya yaxone akan tun
asalinsu ba musulmai bane akwai kafurci jahilci ataredasu Wanda hakan duk
shine silar komai dan haka dole sai an bayyanarda jahilcinsu da
kafircinsu ta hanyar sunayensu da ayyukansu yanda labari zai tafi
daidai.....ga masu cewa sunayen ciki basu halastaba kenan...
Masu cewa babu addini,babu riqo
da addua da basu komawa Allah ba kuma ta yaya zasuyi hakan bayan anbayyanar
dasu marasa sani acikin labarin idan lokacin yi da amfani da hakan yakai ai
za'a sakane... dan Allah muriqa duba asalin tsarinda aka 'doro labari mu riqa
binsa daki daki dan sanin abinda zamu riqa cewa. 1
Nagode Allah yaqara sadamu
gaba.
Post a Comment for " TARAYYA 45 LAST PAGE"