TARAYYA 15-16
Page 15
Shiru sultan yayi yana
sauraren bayanin Jakadiya ya lumshe idanuwansa ya bude, +
Allah yataimaki sultan sarkin
dayafi sarakunan qarninsa
Haryanxu baiwa rumanah bata
zama cikakkiyar baiwa ga yarima ba""""""
Sune abinda Jakadiya tafada
yasaka kallonta kafin cikin 6ayyanarda ikonsa yace,
Asanarwa yarima na sauke
zaraah daga yau nabawa adama sultana kuma na dakatarda ita daga matsayinta na
matar sultan harsai ranarda ya hada shimfida da baiwar.
Wani irin yawu Jakadiya ta
hadiye cikeda rawar murya da girmamawa tace,
Angama da yardar Allah.
Tana fita aka isarda saqon ga
yarima.
Aje cup 'din hannunsa yayi
tareda rintse idanuwansa dasuka canza lokaci 'daya yabudesu yakalli ammynsa
dake zaune taredashi a dining din palonta sunacin abinci.
Lumshe idanuwa sultana tayi
ahankali tareda daukesu daga maheer daya qura mata sbd karya gano halinda
tashiga ta miqe ahankali ta nufi hanyar bedroom dinta ya riqo hannunta tareda
dawo da ita ya rungume ahankali.
Zamewa tayi takallesa tareda
sakin murmushin dole cikin kulawa tace,
Karka takura kanka kayi
abinda bakada ra'ayin so zan iya qarasa rayuwata akan wannan hukuncin nasa matuqar
baka cikin takura maheer.....
Ahankali yabude baki cikeda
kulawa yace,
It's okay ammy zanyi abinda
yace ba buqatar ki damu da idan inaso ko banaso.
Bazaka kallesa ka gano 6acin
ransa sbd kyakkyawar fuskarsa koyaushe bata nuna 6acin ransa amma Tsananin
6acin ran dayake ciki ayau yafi na kullum sbd sultan nason ganin iyakarsa
koyaushe da mahaifiyarsa yake amfani Dan cimma buqatarsa garesa Dan yasan
aduniyarsa babu kamar mahaifiyarsa agurinsa.
Yau wani irin sabon turare
Jakadiya tasa aka kawo daga gidan turaren dake qasar Wanda yafi kowane turare
dadin qamshi da hanawa duk namijin daya shiga hancinsa nutsuwa.
Farar rigar bacci yau aka
zabo mata daga closet tasaka akaro na farko da aka hanata saka bra jakadiya
dakanta ta bita koina da turaren ta feshe kafin suka fito.
Kamar koyaushe tana shiga
Jakadiya ta juya ta fice daga part din.
Ahankali ta nufi gurin
kwananta.
Hasken blue and red bulb ya
gauraye dakin.
Cak ta tsaya tsakiyar dakin
bugun zuciyarta na canxawa har kirjinta yana dagowa amma takasa juyowa.
Akaro na farko daya qurawa
wata mace daba matarsaba lazy eyes dinsa,
Dogon wandon kayan baccine
kawai ajikinsa fari qal mai matuqar santsi da laushi,
Wani irin murdadden namijine
maji qarfi da kyawun gabbai sbd yawan yin geam ya bude duk wani qarfi na
jikinsa.
Abayanta taji tsayuwarsa
numfashinta ya tsananta fita hannuwanta da qafafunta suka fara rawa ta rintse
ido.
Bayanta dayake fari qal
yaqurawa ido da gashinta daya rufe wuyanta yanaji qamshinta na shigarsa yanason
ta6o wani bangaren na sha'awarsa akaro
na farko dataji muryarsa cikin wani irin taushi da aji yace,
Juyo.
Juyowa tayi ahankali tareda sunkuyar dakai tanajin wata irin
muzanta na shigarta sbd tanajin kallon dayake bin jikinta dashi na qyama.
Kusan atare suka rintse ido
suka bude sai acikin idanuwan junansu ta mayarda nata ta rufe da sauri tareda
sunkuyar dakai.
'Dauke idonsa yayi tareda
juya mata baya.
STORY CONTINUES BELOW
'Daga qafa tayi duk ilahirin
jikinta rawa yakeyi zata wuce yariqo hannunta.
Barin jikinta numfashinta ke
qoqarin yi tayi saurin Jan boyayyan numfashi yadawo jikinta saidai tuni
qafafunta suka kasa riqeta ta zube qasa kan gwiwoyinta tana dafe qirjinta dake
bugawa da qarfi haryana mata zafi.
Tattara numfashi tayi ta dafa
table din dake tsakar dakin ta miqe har lokacin numfashinta bai daina fita da
sauriba jikinta bai daina rawaba ta fuskacesa kanta na sunkuye.
Sake kafeta yayi akaro na
biyu.
Hannu ya daga yamatso da ita
sosai har kirjinsu na haduwa musamman idan numfashinta ya taso sosai qirjinsu
ke haduwa.
Ahankali yadauke fararen
idanuwansa daga fuskarta zuwa qirjinta dake gugar nasa.
Hannu yadaga ya dora
akafadunta yana kallon idanuwanta dake rintse hawaye na qoqarin fitowa cikinsu.
Ahankali ya zame siririn
hannun fingilalliyar rigar dake jikinta data gama bayyana komai na surar
jikinta.
Zamewa rigar tayi tafadi qasa
Rintse idanuwansa yayi tareda
ja baya ya juya tareda kallon jikinsa ganin tsikar jikar jikinsa ta tashi
abinda baitaba yiba kenan tun tashinsa.
Bakin gadonsa ya isa ya zauna
tareda zamewa ya kwanta rigingine ya rufe idanuwansa batareda yasake kallon
sashen datake ba.
Daukar rigarta tayi tamayar
jiki amatuqar sanayaye ta matsa inda take rabewa ta lafe hawaye suka gangaro
mata ta goge ahankali tareda rufe ido.
Har asuba tayi babu Wanda yayi
bacci acikinsu tanajin anyi kiran farko ta miqe ta nufi qofa tana fita Jakadiya
na isowa taqare mata kallo bataga alamar komaiba tasaki ajiyar zuciya afili
kafin tamiqa mata doguwar rigar tasa suka wuce.
Yau ko palon farko bai iya
fitaba sbd bayason magana ko 'daya yau sultana ma saidai yayi mata massage
Fruits 'dinda ke cikin small
fridge
Din bedroom din kawai ya
iyasha Sam yau ko apatite bayada.
Yau rashin sukuninta yafi na
kullum sbd har dare yasakeyi jikinta bai koma daidaiba ko cup tariqe hannunta
rawa yakeyi data duba taga dare yakusa yi sai gabanta yafadi saidai tana bawa
kanta hkr da qwarin gwiwa
Babu abinda takeson gani
yanxu kamar nuratu,
Tana tsananin buqatar Wanda
zatai magana dashi koda so dayane ayini.
Da daddare tun gurin kaita
Jakadiya ta lurada yanda take cikin tsananin damuwa tashareta suna isa tashige
itakuma tadawo.
Zaune yake akan cauch 'din
datake lafewa gefen yana aiki da apple laptop,
Fararen kayan baccine
ajikinsa as usual ya miqe qafarsa akan glass center table dake gaban couch din.
Ba haske adakin sosai saidai
tana iya ganinsa yana iya ganinta.
Tsayawa tayi takasa qarasawa
kujerar sbd ganinsa agurin.
Aikinsa yakeyi hankali kwance
batareda yanuna yasan da alamar wani mutum adakinba bayan kansa.,
Saida yagama ya ajiye laptop
din tareda miqewa ya nufi lafiyayyan royal bed dinsa ya kwanta Kansa na sarawa.
Saida yakashe wuta yana kalli
ta qarasa ta kwanta qasa ahankali.
Gurin datake yaqurawa ido
itama ahankali tabude idanuwanta ta qurawa gadonsa ido akaro na farko
Duk da akwai duhu adakin.
So kusan hudu yana gwada
ta6ata kozai iya kwanciya da ita amma Sam zuciyarsa na qyanqyami da hakan Wanda
hakan yayi matuqar tunxura sultan yayi wani irin fushi mai muni tareda yanke
wani irin mummunan hukunci aransa yace adaren yau idan yarima bai keta budurcin
baiwa rumanah ba washe gari su saurari
hukuncinsa.
Koda saqon yaje masa
baidamuba matuqar hukuncin kona menene bazai shafi ammynsaba.
Jin sanarwar abinda sultan
yafada ya tsananta damuwarta da quncinta saidai batada Wanda ko fira dashi bare
Wanda zata tattauna damuwarta dashi shiyasa taqara rungumar qaddararta tana
jiran hukuncin yanda za'a cigaba da yanda akaso da ita.
**
Sama sama Cikin bacci take
jin kukan yara da manya,
Mazaje da mata tareda wata
irin iska mai daukeda hayaniya na amsa kuwwa ako ina na cikin masarauta da
wajenta koina na amsawa a fadin garin.
Bude ido tayi ahankali tareda
kallon inda take tayi ido biyu da maheer duqe agabanta yana idanuwansa sunyi
wani irin mummunan ja wata irin damuwa da tashin hankali tareda neman mafita
take hangowa acikin idanuwansa.,
Da sauri ta sauko daga gadon
taji qafafuwanta sun nitsa cikin ruwa ta sauke idanuwanta ta duba a firgice
tayi baya jikinta na wata irin rawa ganin jini kwance yana gudana.
Kallon maheer tayi da sauri
ya girgiza mata kai cikin wata irin murya mai ciwo da sanyi yace,
mineelik assultana the
redblood Queen.
Zaro idanuwa tayi cikin
tsananin tashin hankali jin abinda yace,
Rawa jikinta yadauka
Ihun datake ji tun farko
yafara yawa cikin kunnenta yana neman gigitata ta fita da sauri tafara gudu
cikin jinin daketa gudu kamar ruwa ako Ina na bangon masarautar stains ne na
jini,
Tana fitowa babban filin
harabar palace din taga gawarwaki harbabu gurin saka qafa su zaka taka dole ka
wuce ga ruwan sama dake sauka sosai Wanda suke qarawa jinin dake zube koina
gudu.
Wata irin busa taji anyi
wadda ta amsa kuwwa koina
Nan take taga mutane nata
taruwa kamar tururuwa sbd mugun yawansu,
Haka suka cigaba da taruwa
suna kallon wata babbar qofa dake been sama inda sultan ke fitowa idan zai fito
yayi magana inda kowa ke iya ganinsa.
Kutsawa tafarayi Cikin
mutanen tana bin mutanen da kallo
Nan tafara girgixa kai ganin
ba jama'ar daularsu bace kawai hardana wasu daulolin,
Wanda alamu suka nuna da
qarfin mulki aka mallakesu ana mulkarsu harsu har sarakunansu.
Saida aka taru harbaka iya
qwaqwaran motsi sbd taro da yawan jama'a aka sakeyin busa nan guri yayi tsit ko
kukan tsunstu babu kowa yamaida kallonsa ga qofarda sultan zai fito itama tayi
saurin kallon qofar daidai lokacinda aka wangale qofar wadda tafi kama data
zinari sbd kyalli.
Cikin wata irin doguwar Riga
maroon colour tana ja da qasa tafito daga cikin qofar ta bayyana
Gashinta azube yake har
bayanta yaji adon sarkokin zinari nakai har zuwa kafadunta hakama wuyanta
sarkace har saman cikinta ta zinari,
Wani irin kyau da kyalli take
fitarwa daidai hannuwanta a lalace suke kaca kaca da jini har jikin rigartama
haka
kujerar karagar mulkin
mineelik Wanda keta tsiyayar jini wasu irin samudawan guards suka ajiye mata
tasaki wani irin qayataccen murmushi zata zauna......
Cikin wani matsanancin ihu
takira sunanta da qarfi tana cewa,
Rumanahhhhhh karki zauna a
wannan kujerar......rumanahhhhh
Zama tayi cikin wani irin iko
da mulki nan gari yadauki ihun sunanta.
Amatuqar gigice sultana ta zabura daga baccinta tana
tareda lalubar bedside lamp takunna da sauri jikinta na muguwar karkarwa tafara
karanta innalillahi tana hada wani mugun gumi.,
Wannan mafarkin nata babu
alkhairi acikinsa,
Meya hadata da wannan
mummunan mafarkin?
Tsoro da fargaba taji yana
shigarta tayi saurin saukowa tafada toilet tayo alwala tazo tafara jera
nafiloli kafin asuba tayi.
Har gari ya waye bata sake ko
kwanciyaba bare rintsawa,
Abinda tagani amafarki tamkar
wani gargadine ga abinda suke shirin
yiwa rumanah bata fatar ko acikin bacci tasake irin wannan mafarkin bare
ya tabbata.
Dan haka ta yanke shawara
komai zai faru shirye takeda daukar
hukuncin sultan.
Qarfe goma sha 'daya na rana
saqon kiran sultan yazo gareta babu bata lokaci ta miqe cikin shirinta da
adonta ta nufi part dinsa kuyanginta na biyeda ita,
Duk inda ta gifta kafin ta
qaraso anrabe anxube qasa ana gaidata cikin matuqar girmamawa harta isa tun a
qofar palon farko suka dakata itada Jakadiya data fito tarbonta suka qarasa.
Tana isa jikinta yayi mugun
sanyi sbd ganin yanda kowa ya dauke wuta sai mizurai akeyi sbd ran sultan ya
baci kuma kowa yasan hukuncinsa ba sauqi ba kyau haka itama ta isa kujerar dake
matsayin tata tazauna bayan ta kwashi gaisuwa.
Maheer ransa amatuqar bace
yake sbd baisan hukuncinda sultan zai yankeba akan ammynsa.
Cikin kakkaisar murya yakalli
Jakadiya yace,
Inason jin dalili qwaya 'daya
daya daga yarima Wanda ya hanasa cika umarnin sultan dinsa.
Cikin rawar murya Jakadiya
takalli yarima zata maimaita masa abinda sultan ya tambaya batareda yakalli ko
dayansuba kai tsaye yace,
Banada sha'awar kowace mace
bayan wadda igiyoyin aurena suke kanta.
Wani numfashin bacin rai
sultan yafitar yana kallon yarima sbd yasan daga yau hukuncinda zai yanke
akansa yagama da rayuwarsa gaba daya cikin isa da mulki yabude baki yace,
Jakadiya atambayesa yana
buqatar qarin lokaci kokuwa shikenan......
Cikin tsananin dauriya da
danne fargabarta da fargabar abinda zai biyo bayan abinda zatayi tabude baki
tace,
Ina neman afuwar sultan amma
baiwa rumanah ta haramta garesa daga yau sbd na 'yantata daga wannan lokacin
harzuwa qarshen rayuwarta,
Daga yanxu ita ba baiwa bace
sbd haka ta haramta ga kowane namiji idan ba mijin aurentaba.
Cikin wani irin mugun mamaki
da 6acin rai dabai taba yiba yake kallonta jin abinda tafada,
Ta 'yanta baiwarda yabada
umarnin yarima ya kwana da ita kenan 'danta takare daga aikata abinda baiso
Tabbas zasu 'dandani hukuncin
sultan daga ita har 'danta.
'Dagowa yayi yakalli
wazirinsa cikin wani irin yanayi na nuna rashin damuwa yace,
Ta 'yanta baiwarta sbd ta
rahamtata ga 'danta sbd bayaso nikuma zan halasta masa ita ayau sbd umarnin
sultan baya bin iska,
KUJE ABADA SANARWAR 'DAURIN
AUREN YARIMA MAHEER IBN ABDULSHAMS ABDALLAH DA 'YANTACCIYAR BAIWA UMMU-RUMANAH
BULAMA nanda awa biyar duk Wanda baizo ya shaida 'daurin aurenba nakoresa daga
qasata sai bayan shekara biyar yadawo.,, 3
SULTANA ZAARAH BAYAN 'DAURIN
AURE ZATA KOMA GURIN IYAYENTA BAZATA DAWOBA SAI MATAR YARIMA MAHEER RUMANAH TA
HAIHU.
#mamuhgee
Page 16
Not edited.⚠ +
Wani irin kallo sultana ta
'dago tayi masa cikeda mamaki da takaicin abinda yake shirin yi kafin ta bude
baki tayi magana cikeda nuna isarsa da matsayinsa yace,
Lij(sadaukin kuma amintaccen
mayaqin meneelik) duk wanda ya nuna rashin gamsuwa da hukuncin sultan ko a
fuskane ko wanene shi arabasa da abinda yafiso ajikinsa,
Idan nace ko wanene ina nufin
kowanene,
Jakadiya kije ashirya sabuwar
surukar sultan nanbada jimawaba zata zama uwar magajin meneelik. 2
Yana gama fada ya miqe
yashige palonsa na hutawa tareda manyan masarauta dazasu tattauna wani abin,
Wasu majiya qarfin samudawa
suka tsaya qofar Dan bata tsaro.
Kai tsaye ya miqe yabar palon
batareda fuskarsa ta nuna meke cikin zuciyarsaba.
Sultana ma miqewa tayi
jikinta amatuqar sanyaye zuciyarta cikeda takaici da tunanin rashin ganin
amfanin 'yantawarda tayiwa rumanah tunda hakan baisa ta tsirar da ita daga
masifar datake gudar mataba ta haihuwar namiji a wannan masarauta ta mineelik.
1
Jakadiya kuwa wani irin zufa
take yarfewa Tana qoqarin ganin ancika umarnin sultan saidai itama damuwarta da
tsoronta yahana farincikinta wanxuwa musamman idan taduba yanayin tsoro da
fargabar dake yawan samunsu idan sukayi tunanin rabon dazai shiga tsananin
yarima da rumanah., 1
Wannan masarauta batada
tarihi mai kyau,
Jinin mutanen da ake kashewa
yananan yana bibiyar duk wani hakkinsa,
Masiface acikeda masarautar
wadda babu Wanda yasanta saisu dasuka ginu acikinta
Har abada bazata ta6a yiwa
rumanah fatar shiga cikin jerin wainda masifar zata cigaba da shigarsuba
aqarshe tabasu qarshe mai matuqar tausayi da kokawa saidai tasan bawa baya wuce
qaddararsa,
Duk dubararsu da qoqarin
kubutarda ita idan Allah yace tana cikin masu wannan mummunan qaddarar saita
shiga. 1
Zubewa sultana tayi kan daya
daga cikin kujerun palonta na farko sbd bazata iya qarasawa na biyunba tareda
'dagawa kuyanginta hannu nan suka watse cikin girmamawa.
Dafe goshinta dake daukeda
adon sarqar zinari tayi tareda rufe ido tarasa wane irin hali zuciyarta take
ciki sbd takasa riqe tunani ''daya dazatayi cikin biyu auren maheer da rumanah
kokuwa korarda sultan yamata gefe 'daya kuma tsoro ne fal yafi cika mata
zuciya.
Ya Allah kadubi maraicin
rumanah kazaba mata kyakkyawar rayuwa agaba.
Tana cikin wannan halin
Jakadiya tashigo 'yan mata biyar na bayanta 'daukeda manyan trays suna qyalli
kamar zinari suka jeru sanku sunkuye.
Kallo daya Jakadiya tayiwa
sultana 'din tasan tana cikin tension murya asanyaye tace,
Allah taimaki sultana
anshirya zuwa gurin shirya sabuwar amaryar yarima maheer sa albarki akazo
karba.
'Dago fuskarta datai ja tayi
takalli jakadiya batareda tace komaiba ta miqe tashiga bedroom dinta tafito da
wani madaidaicin akwati yana kyalli.
Zama tayi tareda aje akwatin
batareda takalli jakadiya ba murya ba kuzari tace,
Allah yasawa aure albarka.
Amin jakadiya tace tareda kai
hannu tabude akwatin.
Sarqoqin zinari ne masu nauyi
da marasa nauyi nakai dana qafafu taredana wuya da awarwaro har kusan basa
qirguwa.
Hannu Jakadiya tasa tana
zarosu tana zubawa acikin tray dinda suka shigo dasu harsaida tray din yacika
suka fice,
Sashen adama suka isa tana
zaune cikin royal kushins din dasuka qayata palonta cikeda girmamawa aka iso
mata da saqon zuwansu Jakadiya tace sushigo. 1
'Yan matanda ke bayan
Jakadiya 'daukeda manyan trays din takalla cikeda mamaki sbd alamu na sakawa
aure albarka zaka bayar.,
Wane zaiyi aure kuma ayau
batareda tasaniba?
Lallai ana wasa da ita amma
karsu damu da zarar ta 'Dora mazaunanta akan kujerar mulkin mineelik tayi
alqawarin bawa dabbobin dake zagaye da qasar naman wainda suke wasa da
alamarinta.
STORY CONTINUES BELOW
Cikin girmamawa Jakadiya ta
katseta da cewa,
Sultana zaarah ta 'yanta
baiwarta ummu-rumanah ayau kuma ayau sultan zai aurawa yarima maheer ita akan
sadaki tiren zinari,
Sultana ta bada nata tiren
saka albarkar aure saurake gimbiya adama ina fatar ba'a shiga cikin lokacin
hutawarkiba.
Cikin wani irin yanayi na
mamaki ta kalli Jakadiya tace,
Aure tsakanin yarima da
baiwa?
Kozansan dalilin wannan auren
na gaggawa?
Allah yataimakeki maganar dai
'dayace.
Rintse ido tayi tareda Jan
numfashi cikin takaici
Sam sultan bazai bari tashaqi
numfashi mai dadi ba sbd wannan masifar tasa tason haihuwar magajin mineelik,
Meyasa koyaushe yake son 6ata
mata aiki idan yayi nisa,
Tana qyalewane ta lafe sbd
bokanta yace mata sa'arta ba yanxu takeba saizuwa gaba takwantarda hankali
tajira sbd ba'a taba haihuwar namiji ba a masarautar yayi duba yaga tabbas mace
ce zatayi mulkin mineelik bayan sultan takuma tabbatarda itace macenda zatayi
mulki amma badan hakaba da tuni tasaka anbinne sultan da ransa takaiga cikar
burinta. 1
Murmushi tasaki tana 'dauke
gira 'daya tace,
Allah yayiwa aure albarka.
Sarkar jikinta data kanta
taredata qafafunta tasa baiwarta nuratu ta cire ta daura akan tray din suka
miqe suka fice.
Nuratu duk ilahirin jikinta
rawa yakeyi gurin cire mata sbd tsananin farin cikin data shiga jin zancen,
Ta matsu tagama yiwa
sarauniya adama yankan fruits taje tafadawa mamani sbd yau tun safe adama
tasakata aikin abinci kusan kala biyar sbd 'yarta meenah zata zo hutun
makaranta daga Sydney.
Part dinsa ya isa cikin wani
irin yanayi da babu mai iya gano maike zuciyarsa ya zauna kan sofa tareda
rintse idanuwansa yana shafo sumar kansa.,
Miqewa yasakeyi ya nufi
bathroom yashiga cikin bathtub bai tsaya bata lokaciba yayi wanka yafito ya
zauna gaban mirror yana goge jikinsa,
Shiri yayi cikin Ethiopian
royal kaftans black and golden wainda yasaka ranar daurin aurensa da suhailat.,
Turare yafesa tareda saka
takalmi ya fesa turare tareda gyara gashinsa mai 'Dan tsawo ya 'daure tsakiyar
kai yasaka hula batareda yakalli kansa a madubi ba ya nufi qofa ya fita inda
guards kusan guda goma da fadawan sultan suke jiransa Dan masa rakiya har gurin
daurin auren.
Zaune take kan kujerar mirror
ita kadai kamar koyaushe shiru tayi nisa cikin tunani tareda qurawa kanta ido.
Qura mata ido Jakadiya tayi
kafin tayi gyaran murya tareda yiwa 'yan matan alama da ido cikin nutsuwa suka
zo gaban rumanah data miqe cikeda ladabi tana gaida Jakadiya suka Jere matansu.
Sam bata shiga ko saka kanta
ga duk abinda tasan bai shafetaba shiyasa ko inda aka ajiye kayan bata kallaba
ta sunkuyar dakanta tana jiran umarni daga jakadiya sbd tasan dole akwai abinda
yakawota.
Fuskarta Jakadiya take kallo
tace,
Ayau sultana zaarah matar sultan
abdulshams sarkin masarautar mineelik ta 'yantaki ummu-rumanah bulama sbd ki
auri 'danta 'yarima maheer Wanda za'a daura miki aure dashi yanxu nanda mintuna
qalilan.
Kallon Jakadiya tayi da kyau
taga fuskarta babu wasa ko raini yasa tayi qasa da kanta sbd tasan babu abinda
zaisa Jakadiya tafadi abinda bahakaba sbd dokace a masarautar duk Wanda yayi
kuskuren qarya aka ganosa allurar dabazai qara maganaba ake masa shikenan
yazama kurma shiyasa duk tsanani duk wuya ba'a qarya a mineelik. 1
Shiru kawai tayi sbd haryanxu
batajin kanta amatsayi na an 'yantata tunda za'ayi auren manufa da ita,
Aurenda tasan dalilinsa Dan
haka babu abin murna a 'yancinta.
Riqota sukayi zuwa toilet
batai musuba jiki asake tabisu.
Wani irin gyara na musamman
aka hau yimata idanuwanta arufe har aka gama suka fito nan aka zaunar da ita
gaban madubi nan wasu mata suka shigo su hudu cikin wani irin ado irin na
al'adarsu suka fara gyara mata fuska cikin qanqanin lokaci suka tsara wata irin
kyakkyawar kwalliya a fuskarta,
Ana gamawa kallo 'daya
Jakadiya tayi mata taji numfashinta ya sarqe tayi saurin sakin tari tana dafe
qirjinta.
Wata irin doguwar Riga fara
qal mai adon wasu irin golden stones masu matuqar kyau da qyalli aka saka mata
tareda daure dogon gashinta tsakiyar kanta kafin aka saka mata wata irin
kyakkyawar doguwar sarqar zinari tareda awarwaronta sai wata irin kyakkyawar
sarqar kai data qafafu kafin aka lullubeta da dogon mayafin daya fito daga
hannun sultana.
24
Suna gamawa Jakadiya tayi
gyaran murya nan dukkaninsu suka miqe tareda miqarda rumanah data zauna sai
yanda akayi da ita itadai tasan da dah da yanxu duk 'dayane babu wani banbanci
arayuwarta.
Kai tsaye part din sultana
aka nufa da ita inda ana gama 'daurin aure itace zata kaita ga sultan yasawa
aure albarka.
Kamar yanda sultan yabada
umarni bayan awanni biyar cif dubban jama'ar qasar da maqwaftanta sun shaida
'daurin auren yarima maheer abdulshams da ummu-rumanah bulama akan sadaki
silallan zinari guda hamsin.
Ana gama daurawa yarima
sultan yafara kallo cikin wani irin yanayi na murmushi.
Yarima har lokacin baiyi
magana ko daya da kowaba har aka watse.
#mamuhgee
Post a Comment for "TARAYYA 15-16"