TARAYYA 3-4
Page 3
Haske writers association💡
Asma'u bilalu bulama shine
asalin sunan mahaifiyarta asalinta 'yar qasar Nigeria ce ubanta bilalu dan
Maiduguri sai mamarta ummu-rumana shuwah ce.
Bilalu bulama Nada tarin
dukiya mai yawa hakama matarsa ummu-rumana kasancewarta tanada gadon iyayenta
dasuka barmata.,
'Yarsu qwaya 'daya tak
aduniya Nana asma'u wadda duk wata soyayyarsu da burinsu sun 'dorasa akanta.
Bilalu bulama Nada qanne biyu
jabir bulama da salmanu bulama
Kowannensu matarsa 'daya da
'yaya uku uku banda bilalun dakeda 'ya daya,
Jabir babban dansa shine
ishaq sai qannensa mata biyu hassana da husasaina,
Salmanu kuwa sunan babban
dansa bulama sbd sunan mahaifinsu yaci sai qaninsa babaye da yakurah.
Kowannensu nada arziki daidai
gwargwado amma ba kamarna bilalu ba sbd shi ba qaramin arziki Allah ya hore
masa Wanda hakan yasa shedan yashiga kwadaitawa qannensa dukiyarsa nan
kowannensu yafara qoqarin ganin ya cusa dansa gurin Neman 'yarsa Nana asma'u,
Tun kowanne natura babban
'dansa a 6oye gurin neman soyayyar asmaun hardai kowa yafito fili yanuna buqatarsa
tason nemawa 'dansa auren,
Alhaji bilalu baiyi tunanin
komaiba saima farin ciki dayayi saidai abun daga baya lalace sbd fada da tashin
hankali daya shigo ciki sbd tuni kawuna suka rarrabe sbd alamarin ganin haka
sai alhaji bilalu yace abari asma'u tazaba Wanda takeso acikin yaran dakanta
sbd ya fahimci bulama shine Wanda tafiso kuma maganar gaskia yafi ishaq nutsuwa
da tarbiya ga hankali amma shi bazai fadaba saidai ita asma'u tafada Wanda
takeso dakanta.
Tashin farko da'a tambayeta
gaban kowa ba 6oyo ta za6i bulama
Hakan datayi shiya qulla wata
irin qiyayya da sabani tsakanin jabir da yayyunsa bilalu da salmanu.
Bayan auren da wata biyar aka
wayi gari gidan alhaji bilalu ya qone qurmus dagashi har matarsa ummu rumana
babu Wanda yafita kuma a iya binciken da akayi aka gano wutar dai kunnata akayi
da man petrol.
Haka akayi zaman makoki aka
watse dakyar aka samu asma'u ta dangana Wanda saida aka hada da adduoi da sauke
al-qur'ani kafin tadawo daidai.
Duk inda hankalin alhaji
jabir da ishaq yake yasake hargitsewa sbd sai yanxu kukaga wautarsu ta kashe su
alhaji bilalu sbd yanxu duk tarin maqudan dukiyarsa yarsa zata gada tokuma ai
mijinta da uban mijinta suzasu juya dukiyar kenandai alhaji salmanu yayi
arzikinda ba ranar qarewarsa shikenan shi yatashi abanza.
Cikin watanni hudu shida
ishaq sunkasa sukuni suna qulla yanda zasu qwato dukiyar su raba su salmanu da
ita.
Ranarda suka gama qulla suka
aika 6arayi gidan alhaji salmanu tsakiyar dare,
Gurin karbar takardun bulama
da mahaifinsa sukai gardamar bayarwa Wanda yaja nan take aka harbe alhaji
salmanu da matarsa bulama naganin haka ya buge babbansu da flower verse ya
fizgo matarsa asma'u suka gudo tareda takardun dukiyar
Yakurah da babaye dama suna
schools hostels suke zama.
Gudu suke sosai atsakiyar ko
gani sosai basayi sbd duhun dare amma haka suke gudu hannunsa damqe Dana asma'u
suna keta duk hanyarda suka samu sbd sunajinsu abayansu biye dasu.
Basu ankaraba suka gansu har
sun fara barin anguwanni suna qoqarin ketawa daji amma haka suka cigaba da gudu
agalabaice cikin tsananin wahala da gajiya
Can wajen gari sukaga wani
kangon gida daya qone suka shige tareda boyewa.
Wani irin kuka asma'u tasaki
jikinta na karkarwa
Bulama yayi saurin saka
hannuwansa ya toshe mata baki sbd takun su ishaq da barayin daya jiyo yana
kusantonsu.
Dudduba koina sukayi suna
haskawa Allah yasa basu gansuba
Iska ishaq ya daka cikin zafi
da tsananin 6acin rai yana huci yakira abbansa yafada masa 5
Cikin takaici da baqin ciki
abban yace,
Kutafi tashoshin motar duk
garinnan kudubasu banason kowannensu da rai takardun kawai nakeso Ku karbo
saiku harbesu
Hakama atura su tiger duk
wata station su zauna daga nesa da anhangosu sunzo station kafin sushiga
aharbesu.
Aje wayar yay yakallesu yace
kumuje tashoshin mota amma wasu su tsaya anan sbd nasan idanma sunanan kusa
idan gari ya waye zasu fito idan sun fito Ku harbesu kawai.
Barin gurin sukayi sukuma su
bulama najin haka koda gari ya waye sake lafewa sukayi sukaqi fitowa saida duhu
yasakeyi suka fito cikin sanda suka fice tareda qarasa kutsawa cikin dajin suka
fara gudu
Jini sosai qafafuwansu ke
fitarwa sbd ko takalmi babu maishi acikinsu ga yunwa ga wahala da kishirwa amma
hakanan suka cigaba da tafiya sbd komawarsu nada matuqar ha'dari yanxu.
Basu hadu da qauye ko dayaba
har asuba tayi musu atsakiyar daji gashi tuni asma'u tafara riqe ciki tana
murqususu cikin tsananin azaba ta durqushe agurin awahalce tace,
Bulama marata zan mutu.
Da sauri ya aje takardun ya
durqusa ya tallafota jikinsa shima daqyar yake hade yawu sbd bakinsa daya bushe
qyam ko yawu daqyar yake samun na hadiyewa a maqoshinsa ga wata irin rana mai
tsananin azaba,
Ko tsuntsaye babu adajin sbd
a bushe yake babu damshin ruwa ko kadan itatuwan dajinma duk abushe suke babu
mai inuwa.
Jinin dayaga yanabiyo qafafuwantane
yasa yayi saurin kallonta murya na rawar wahala yace,
Asma'u cikine dake dama
bansaniba?
Innalillahi-wainnalaihirrajiun.
Ganin tana Neman fita
hayyacinta yasa ya goyata tareda daukar takardun yacigava da tafiya daqyar
shima sbd shima yafara daina gani daidai.
Ahaka rana takuma faduwa wani
Daren yayi musu a tsakiyar jeji wannan karon kam ya tabbatarda wata duniyar
suka fado sbd kalar yanayin dajin ya
sauya sosai
Tun yana gani har duhu yasake
yi dare Yakuma tsalawa sosai cak ya tsaya tareda yanke jiki ya fadi asma'u dake
bayansa ta fado da qarfi kafin ya bude idanu daqyar Dan taimakonta sai ganin
yayi kamar tana gangarawa
Bude idanuwansa yayi awahalce
da sauri saiyaga Ashe bakin cliff suke mai tsananin zurfi da ruwa masu tsananin
yawa yana miqewa daqyar kafin yakamota idanuwansa suka rufe yasake yanke jiki
yafadi tareda fadawa shima.
********
Ahankali ya bude idanuwansa
dake gani dishi dishi harsuka bude daqyar suna kallon sama,
Lumshe idanuwan yasakeyi
yabudesu yaga tabbas rufin sama bukkar karace yake ciki,
Qoqarin motsawa yakeyi Dan ya
yunqura yatashi aka shigo bukkar yayi saurin dagowa.
Tashin namijine kamarsa dago
fari tas sanyeda kayan saqi na fulani.
Qarasowa yayi da sauri tareda
dafasa yana cewa,
Yi ahankali kana kariya
aqafa.
Kallon qafar bulama yayi sai
alokacin yaji azaba ya lura da 'dauri amma bai damuba cikin dasashiyar murya da
fargabar amsarda za'abasa yace,
Ina matata?
Inane nan?
Ina takardun dake daure
ajikina?
Kwana na nawa anan?
Cikeda mamaki da rashin
isashiyar hausar fahimtar me bulaman ke fada yake kallonsa kafin ya gyara masa
zaman qafar mai 'dori yace,
Kayi hkr sbd bansan mezan
fada makaba amsa daya zan iya baka shine kwananka takwas anan sauran tambayar
anjima idan mahaifina yadawo ya amsa maka.
Yana fadar haka ya fice
Saigashi yadawo da qwaryar
magani da akushin wani irin abinci kamar tuwa kamar kunu ya zauna tareda miqawa
bulama yace,
Gashi kaci saikasha magani.
Kallon abincin bulama yayi
yaga shi kama ma abincin yayi masa da aman tuwon semo amma sbd yunwa da matsuwar
jin inda matarsa take ya karba ya dauke numfashi ya shanye. 2
Ruwan magani ya miqa masa
suma ya karba ba musu ya shanye.
#Mamuhgee
Page 4
Haske writers association💡
+
Jingina jikinsa yayi jikin
darnin ginin qasar dakin da kusan rabin ginin karane ya dafe goshinsa ahankali
tareda rufe ido yana zuciyarsa na tsananta fargabar kar asanardashi ba'aga
matarsaba kokuma ta rasu.
Qurawa qofar shigowa ido yayi
yana sake tabbatarwa da kansa tabbas wata qasar suka fado sbd yanayin shigar
Wanda yafita dazu da yanayin abincinsu da maganarsa tareda yanayin muhallin.
Ya jima yana tanane tunanen
fargaba da rashin sukuni kafin wani dattijo sosai daya manyanta ya shigo dakin
da gwararriyar sallamarsa.
Saurin 'dogowa daga jinginar
yayi yatashi zaune daidai duk da rashin qarfin jikin dake tattareda dashi
tareda zubawa mutumin ido Dan amatse yake dason jin ina matarsa take.
Kallon bulama dattijon yayi
kafin yajuyo yakalli 'dansa dake bayansa cikin wani yare yayi masa magana kafin
cikin hausarsu da bata fita yace,
Dama yatashi baka fadaminba
kutti ?
Bai dadeba da tashi baabah
magani natsaya bashi kafin naje kiranka saigashi kadawo.
Kallon bulama baaban yayi
yace,
Sannu da kaji,yanzudai babu
inda yakema ciwo ko?
Cikin qarfin hali yace,
Banajin komai yanxu qafardaice
idan na motsata da 'Dan zafi,
Nagode sosai baabah amma Dan
Allah ina asma'u mata.....
Baca Juga
Kwnatarda hankalinka matarka
nanan tareda kai saidai itama tayi jinya ta rasa cikin jikinta amma ta warke
sosai.
Ajiyar zuciya yasake a6oye
sbd ba qaramin dauke numfashi yayiba Dan gudun jin muguwar amsa.
Kutti ne yasake shigowa dakin
wannan karon Asma'u na bayansa bakinta daukeda siririyar sallama.
Qura mata ido yayi sanye
takeda kayan saqi irin nasu da wani juyayyen 'dankwali dako kanta bai rufe
dukaba tayi wani irin mummunan baqi ta rame gabaki 'daya kamanninta sun fara
sauyawa
Wani irin tausayinta Dana
kansa ya rufeshi amma dai tunda sun tsira kuma suna cikin qoshin lafiya daidai
gwargwado to alhmdllh.
Cikin sanyin jiki ta durqusa
qasa tace,
Ina wuni baabah.
Lafiya lafiya mai sunan
innejo mijinki ya farka daga yanxu kar asake kuka Dan ba'a kuka agidan baabah
namiki uzirine kema.
Duqar dakai tayi cikin sanyi
ta 'daga kai sbd akwanakin datayi agidan taga dokoki da sabbin alamuran rayuwa
a gidan da mutanen garin wanda cikin qanqanin lokaci ta fahimci tsantsar
jahilci da rashin wadataccen ilimin addini suke ciki Dan acikin duhu suke
sosai.
Fita baabah yayi kutti yabi
bayansa ta 'dago kai ahankali takallesa sai kawai tasaki qaramin kuka ahankali
tareda toshe bakinta.
Hannu yamiqa yajawota
kusadashi ya rungumeta shima daurewa kawai yayi amma yasan gararin rayuwa
yasamesu.
Rarrashinta yayi daqyar yana
cewa,
Asma'u kiyi hkr insha Allah
komai zai daidaita Dana sake warwarewa zamu koma gida mu fuskanci su......
Kallonsa tayi amatuqar razane
tana girgiza kai tace,
Yaya Dan Allah mubar maganar
komawa yanxu kwata kwata nan inda muke wani yankine dabashida suna acikin wani
lungun daji mai nisa daya ruwa masu yawa ya raba tsakaninsu da Nigeria dakuma
wasu qasashen,
Sunada kwanciyar hankali duk
da suna cikin tsananin duhun ilimi da rayuwa,
Jin dadi ba komai bane idan
ga kwanciyar hankali da Wanda kakeso,
Bamuda uwaye ko 'daya duk
ankashesu su yakurah komawarmu yanxu zamu saka rayuwarsu acikin hadarine suma,
Mu gwada bawa rayuwa wani
chance anan sbd kwanciyar hankali da nutsuwa,
Mubari gaba idan komai ya
Dade da shidewa saimuje da zuriar da Allah zaibamu anan cikin kwanciyar
hankali.
STORY CONTINUES BELOW
Shiru yayi yana kallonta sbd
tagama kashe masa jiki tunowa da mutuwar iyayensu kuma tabbas komawarsu saka
rayuwarsu yakurah ne ahadari.
Ganin yana tambabar yarda da
zancenta yasa hawayenta tsananta cikin kuka tace,
Yaya kadaina tuno dukiya da
rayuwarmu tabaya sbd rayuwa dakai anan yafimin komawa cikin daular dazata saka
mu rasa juna.
Tsananin tsoro da figicin
datake cikine yasa yayi saurin rungumeta yace,
Asma'u zamanki cikin
kwanciyar hankali yafimin wata dukiya da daular rayuwa.
Satinsa biyu da farfadowa
yafara miqewa kutti ne keta faman dawainiyar kula dashi
Ahankali yake koyan tafiya da
sanda har waje suke fita suna zago qauyen Wanda tsaf yagama gano tabbas cikin
duhun rayuwa suke sbd dajine zallah saidai akwai niima kasancewar zagaye sukeda
ruwa.
Asma'u tuni tasaki jiki da
matan gidan zuriar baabah Dan tuni aka ware musu fili acikin gidan da nufin
bulama na warkewa yaje ya sassaqo icce ya Gina musu dakinsu acikin gidan.
Cikin ikon Allah ya warke
sosai bai tsaya wata wataba yafara binsu kutti daji baji ba gani ya zage yazama
nimiji sbd dolene yasaba da baqar wahala sbd itace rayuwar garin gashi garin
koina hakine mai shegen tsawo Wanda wani gurinma idan kana tahowa baka ganin
mai tahowa.
Cikin sati uku ya kammala
musu dakinsu ita kuma asma'u matansu suka koya mata kara taringa binsu suna
yowa tare harta hada musu gadansu na kara da tabarmar saqi.
Ahankali suka saje suka zama
'yangari suma baabah yabasu sunan zuriarsa kasancewarsa shine shugaba agarin
nan kowa agari suka sakasu cikin zuriar gidan baabah.
Duk wata wahala ta rayuwa sun
iya sunsaba yanxu sbd sun tasarwa shekara biyu agarin
Kwata kwata kamanninsu sun
tashi daga nada sunkoma wasu kamannin daban duk wani kyau da tsari suncireshi
sunkoma munana kamar sauran 'yan garin
Iliminsu na addini dasukazo
dashi ya haskaka qauyen sbd sosai suka qararda 'yan qauyen yanxu ba laifi
ilimin addini yadan yadu Dan yanxu wasunsu na wankan janaba idan sun sadu da
iyalansu.
Suna cikin kwanciyar hankali
sosai sbd ana qaunarsu har mantawa akeda su 'din ba asalin nan bane tuni aka
zama daya,
Asma'u ma tuni tashiga jerin
surukan gidan baabah babu bambamci
Matar kutti MAMANI ce kawai
ma suke samun matsala wasu lokutan sbd kishin matan sauri.
Shekaru sunja sosai manyanci
yafara kamasu amma har lokacin babu haihuwa sai 6ari takeyi data samu ciki
kusan 6arinta biyar gashi girma yazo musu.
Lokacinda baabah yabuqaci
bulama ya qara aure bai musaba sbd bin umarnin baabah din
Haka aka hadasa da wata 'yar
maqocinsu sbd shi baabah 'yayansa mata takwas duk sunyi aure.
Tuni bulama ya duqufa aikin
sassaqo itace ba dare ba rana sbd yiwa kantali 'dakinda zaisata idan anyi auren
danma wata uku aka dibarwa bikin sbd yasamu yin dakin cikin nutsuwa.
Cikin ikon Allah asma'u Ashe
tanada shigar ciki har wata biyu amma tayi shiru sbd kar ayi tunanin fasa auren
Dan ko yanxu tana tunanin bazai tsayaba.
Sauran sati biyu bikin cikin
na wata biyar tuni yafito kowa yafahimci cikine da ita nan murna ta kaure
sbd cikinta baita6a wuce wata biyu zuwa
ukuba.
Duk da haka tace kar bulama
yafasa auren ayi kawai ta yanda zai samu 'yaya da yawa tunda yafara manyanta ba
haihuwa,
Hakan datayi yaqara kawo
fahimta da shaquwa tareda qaunarta ga matanen qauyen tuni aka fara shagulgulan
biki irin nasu na al'adarsu.
Ana saura kwana biyu 'daurin
aure da tsakar dare asma'u ta fito
fitsari ta nufi bayinsu na kara dake baya na kowa da kowa na gidansu
Tayi tagama harta juya
saitaga kamar tana hango hutattaki na tahowa cikin qauyen ta bude idanu da kyau
saitaga tabbas kamar mutane ne da yawa ke shigowa qauyen.
Sakin butar qasar hannunta
tayi ta nufi bukkarsu da sauri tashige jikinta na rawa ta tayarda bulama,
Cikin sauri da magagi yatashi
Dan yadauka cikinne yasamu matsala yana kallon cikinta da sauri yace,
Innaje lafiyanki kuwa?sbd
shine sunan datun zuwansu ake kiranta dashi sbd sunan mahaifiyar baabah ce tuni
aka manta sunan asma'u.
Murya na matuqar rawa tana
kallon qofa qasa qasa tace,
Mutane ne da hutattaki suka
shigo qauyen nan na hangosu kuma......
Ihu da hayaniyarda qauyen ya
'dauka ne ya katse maganarta suka kalli qofa afirgice tayi saurin cakumosa tana
cewa,
Kajiko wlh mutane suke
kashewa...
Zabura yayi ya miqe tareda
damqo hannunta suka fito tsakar gidanda kowa yafito cikin tashin hankali da
firgici.
Baabah cikin tsananin firgici
da tashin hankali yace,
Dukkaninku kubi ta bayan gari
ku gudu karku tsaya saikun kai iyakar ruwa Ku shiga Ku lafe qasan ruwa masu
kamen mutane ne su sayar wata qasar amatsayin bayi.
Gaban bulama da innaje ya
buga da mugun qarfi ya qara damqe hannunta tareda kallon fuskarta yace,
Duk tsanani asma'u kadaki
rabu da hannuna.
'Daga masa kai tayi hawaye na
gangarowa idonta.
Dukkanin zuriar gidan sukabi
ta qofar baya suka fara gudu suna waiwaye cikin tsoro da tashin hankali suna
tsallake gawarwakin wainda aka kashe kwance cikin jini sai gudana yake
Ihun yara da mata tareda na
maza saitashi yake ga huta da aka cinnawa wasu bukkokin.
Sun kusan isa bakin ruwa
innaje tayi tuntu6e da wata gawa ta fadi tareda sakin wani razanannen ihu tana
rawar jiki
Mamani dake bayansu da
cikinta itama tayi saurin ra6esu da gudu zata wuce qafar innaje dake qoqarin
tashi ta kifarda ita
Bulama cikin tsananin hanzari
ya riqosu duka su biyun ya tayar suka wuce da gudu amma sai wani tashin
hankalin sukayi arba dashi domin kuwa su kutti da sauran yan gidan sun 6ace
musu.
Kallon mamani yayi cikin
tsananin tashin hankali yace,
Inane hanyarda baabah yace
wadda mu bamu saniba?
Tsabar musiba da tashin
hankali ya rudata takasa ganewa sai rarraba idanu take tana tsima cikin kuka.
Fizgarsu yayi suka nufi wata
hanya da gudu Dan tsira
Qaddara ta Riga fata sai gashi
tsaye turus agaban shugaban qungiyar.
Saurin kallon qasa yayi gaban
shirgegen mutumin idanuwansa suka sauka kan gawar baabah kwance cikin jini ga
rigarsa harta faraci da wuta.
Bai ankaraba yaji saukar
dukan gora atsakiyar kansa ya dafe kai idanuwansa suka rufe ya yanke jiki
yafadi agurin.
Suna ganin yanada sauran rai
suka jasa aka jefa cikin qaton jirginsu na ruwa hakama innaje da mamani.
Sun samu nasarar kamo mutane
sama da sittin maza da mata banda yara suka gargada jirginsu na ruwa suka lula.
#mamuhgee.
Post a Comment for "TARAYYA 3-4"