YAU DA GOBE 47&48
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🌹YAU DA GOBE 🌹
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & writing by mmn fareesa
🅿️47&48
"""Murya na rawa zarah tace wlh Yaya itace sanadin komai"naji da kunnena tana cewa dama tace saitaga bayan shegen cikin"tafad'a tana nuna rukky... rukky zaro ido tayi had'e da cewa sharri zakimun?"
zarah bata kulataba
ta nufi Gurin sumayya dake kwance cikin jini!Afusace Dr safana ya fisgota sbd ganin zata gudu"
Wani wawan mari yad'auke ta dashi"yakoma k'ara Mata"wata gigitacciyar k'ara tasaki sbd jinta na wucin gadi daya d'auke ,had'e da wasu stars datagani suna Mata shawagi"atake shatin hannunsa suka fito rad'o rad'o afuskarta"
Yana huci yace inhar narasa gudan jinina nine ajalinki wlh! Yanafadin hakan yaturata d k'arfi yanufi gurunsu sumayya wacce ta sume...da sauri yacewa zarah maza kije kicewa driver yafito da mota...d gudu ta fice"
Safana cike da tausayi yasuri sumayya" yafara sakkowa down stairs"gaba d'aya jinin yab'atamishi jiki! amma be damuba"
Sadda suka iso parking space" har anfito da motar" da sauri yashige back sit , sumayya n jikinsa"driver yaja suka nufi asibiti....
Zarah kuwa komawa tayi part d'in.sbd tagyara Gurin daya b'aci"tanacikin gogewa ta lura da Ashe *karkashine*.
Rukky ta zubawa sumayya ta taka!tsaki taja tacigaba da goge wurin"
bayan ta idar ta fito ,sukayi clash da rukky"ta yafo gyale da key d'in motar ta ahannunta!da alama fita zatayi..fusakrta ta kumbura tana hawaye...wani tsakin zarah Takoma ja"ta fice..part d'in su Takoma"tasami ummi a kitchen..nan tasanar Mata abinda ke faruwa... Innalillahi wa inna ilaihir raju'un!
Ummi tafad'a hankali tashe"kafin ta ce maza kije dak'in ta kifito Mata da abun buk'ata mutafi asibitin"
Shikuma nidashine wlh"inhar yanuna mahimmanci cikin aibazatayi ganganci irin wannan ba"amma koyazube Kobe zubeba tagama Zama dashi tunda abin yazama haka...fita zarah tayi aranta tanajin dadin kalaman ummi"sbd gara a karb'e sumayya k'ila yafi nuna soyayyar ta"amma tasan baza'a raba aurenba"da wannan tunanin ta debowa sumayya duk abinda zata buk'ata. ta fito ta Sami ummi suka wuce asibitin...
A b'angaren safana kuwa"suna Isa asibitin"emargency yanufa da sumayya d'auke a hannunsa...bebar wani Dr yabiyo Shiba! saidai wata doctor mace d'aya"itadashi suka tsaya kan sumayya..har jinin yatsaya"akuma bincikensu suka gano cikin d'aya yafita saura d'aya"Kuma shima saiyyi 4 morth tukum za'a San dashi..wato saiyasake maimaita kwanakin dayyi...drip yadaura Mata bayan yamata allurar bacci..
Kafin yaturota"zuwa wani room.. adedenan Kuma su ummi d Dr Nasir suka k'araso.
Saidai safana yadda yaga fuskar ummi yasha jinin jikinsa!gaida ita Dr Nasir yyi had'e da mata ya mai jiki!safana yace muje ga d'akin can dazan kaita..
binsa sukayi d'akin da zai kaita..ummi ta zauna tanata kallon sumayya cikeda tausayi"kafin ta dubeshi fuska a'daure tace cikin yazube Kobe zubeba?"
Duk'ar da kansa k'asa yyi"Dr Nasir yace subahanallahi"nifa bansan meke faruwaba"garin Yaya hakan ta faru ummi??"
Ummi tace gashinan saiya gayamaka"Amma maganar Zama dashi tagama"dole yasallameta ,sai yazauna dawacce yakeso...inta tashi ta haifa mishi yara dubuma"Amma Sumayya tagama Zama dashi"tunda yau anfara kan cikinta anason azubar dashi"gobema akan ranta za'a koma ko?"atake Dr Nasir yafahimci meyafaru?"kiyi hakuri ummi insha Allah hakan bazai sake faruwa ba"cewar safana Kai aduk'e!hmmm Allah ko?"to da gske cikin ya zube kenan?"to bari kaji dg nan sai part d'ina zanwuce da ita"dg baya kabata takardarta"sannan bance kayiwa yarinyar nan komaiba"kabarta da duniya indai rayuwace"YAU DA GOBE !batabar komaiba "insha Allah sai ubangiji yamata sakayya",badan tafi k'arfin adauki mataki kantaba nace ka k'yaletaba...kutashi kubani guri"tashi safana yyi suka fice shida Dr Nasir...
Office d'in Dr Nasir suka nufa"Rai bace Dr Nasir yace wlh ummi tamun daidai akan hukuncin data yanke maka"gara ta auri Wanda kesonta...look mlm!dame kakeso najine?"bazaka bani mafitaba sai k'aran takaici!eh bazan bakaba" sbd lokacin danaso baka mafitar k'iyawa kayi ko?" Indai rukky take komenene gaka gata nan wlh" bantab'a ganin irin k'in dakake nunawa sumayya ba" ana nunawa wanishi! Itakuwa tanamaka biyayya! Tunda ita y'ar gwal d'in taka zata iya saita d'auki wani cikin...shiru kawai Dr safana yyi sbd yatono mishi inda kemishi k'aikayi" yanaso yasanar mishi rukky na warin JAB'A!
ammq Yana gudun yagaya mishi mgn, damishi surutai..saikawai yashare"yad'auki wayarsa dake ringing" bak'uwar number yagani" d'agawa yyi had'e da sallama" mahaifin rukky yace nine Aliyu kazo inason ganinka inbbu damuwa...to daddy "yafad'a Yana kashe wayar...wani haushi da tsanar rukky yaji ya nunku aransa"da ace suka cikin nan yab'are data gane kuranta.. tab'e baki Dr Nasir yyi sbd yaji komai..
##########
Zaune suke atsakkiyar carpet suna fira" ummi ta Kira abba tasanar mishi suna asibiti sumayya tayi b'ari...salati yyi had'e da cewa to suna nan tafe.
Kashe wayar yyi"yasanarwa mama tace Allah y kyauta"Abba yace kitashi kishirya muje...ah ah alh!kajedai Kai"ninaje namata me?"
Hmmmm andena kunyar d'an fari"gara kidena"cewar Abba Yana tashi tsaye! yace bara naje nasanar ma da jamilah ta shirya sai muwuce"jitayi tamkar tace yabari"amma Kuma saitayi zaton yanada dalilin yin hakan"bed room d'in ta, ta wuce sbd twins nagun Mai rainansu...
Abba na zuwa parlourn hjy jamilah yamata bayani!wani miskilin Murmushi tasaki had'e da cewa"ikon Allah!kodai ita Tasha wani abu cikin yazube koshi Aliyun yazubar da cikin??"
Subahanallahi!waike wacce irin mutum ce?"kikasance baki fad'in alkhairi sai sharri"to shikenan kiyi zamanki"nafasa zuwa dake.
Yo saime?" Aitafi nono fari wlh,akan wane dalili zanje dubata"sbd nafadi gsky zakace banjeba"k'arya nayine?"ai kwad'ayi yasakata auren"ana hura Mana hanci tayi ciki"aigashi yab'are"saitaga kishiya na haihuwar...tsaki Abba yaja had'e da cewa Allah yashiryeki...yaficeabinsa"hjy jamilah ta saki murmushin jin dad'i tace Allah nagode maka da shegen cikin yazube wlh...
🍁🍁🍁🍁🍁🍁🍁
Ahankali yake zare Mata drip d'in sbd yak'are"yyinda ummi da zarah ke d'akin sai musty dayazo yanzun... bud'e ido sumayya tayi had'e da kallon d'akin"atake tafahimci asibiti ne take...anan abinda yafaru d'azun yadawo Mata ak'wanya..
wasu hawayen b'akin ciki suka zubo Mata afuska"tanajin dg yau tagama Zama da safana"sbd ta dalilinsa cikin data k'wallafa ranta akansa "matarshi ta zubar Mata"ta tabbatar inbe zubeba ,bazata ganta a asibiti ba"sannan Kuma tasan bazai d'auki mataki akan rukky ba....kallonsa tayi sbd jin hannunsa akan naza zai zare Mata kanula!azabure tajanye hannunta. ta banko mishi harara..
Hakan yasa su ummi maida attention d'in su akanta"safana kuwa cikeda tausayi yake kallonta yaga tanata harararsa dakuma hawayen dake tsiyaya afuskata...karka koma tab'ani"natsaneka !kaida matarka banyafemuku ba"wlh bazan cigaba da Zama dakaiba... tafad'a tana akwancen...yo ai sumayya dg nan sai part d'ina zanwuce dake "kobaki fad'a ba"zamanku yak'are kedashi"gaba d'aya sumayya kunya ta kamata sbd kwata kwata Bata lura dasu ummiba!
Ummi nifa bansan meke faruwaba"kitambayi baby atare nasamesu"Amma duk kun azamun laifi...zarah tace hakane gsky ummi...tashiga sake kora musu bayani... rufe idonta sumayya tayi.ita kad'ai tasan b'acin ran datakeji...ummi tace bbu ruwana dabai San komaiba"inda yanuna mahimmanci cikin da ita Sumayyar aihakan bazai faruba"tunda kacire Mata drip d'in saika tashi..kallonsu musty yyi"fuska a'daure yace dallah kukuma magulmata !Kuna sauraron anamun fad'a" zaku fita ko kuwa?"musty yaduk'ar dakai Yana dariya"k'asa k'asa"rad'a yyiwa zarah dake zaune kusa dashi"kafin safana yace wani abu"Abba da mama da twin's sun shigo room d'in!
Wata fad'uwar gaba safana yaji da kunya"fatansa Allah yasa Kar sumayya ta fad'a musu gaskiyar abinda yafaru...ji yyi dama yasanarwa ummi baduka cikin yafita ba!kansa aduk'e ya gaidasu"yad'auki twins daketa k'iriniyarsu".akunyace mama suka gaisa da ummi ta tambayeta yamai jiki...musty da zarah suka gaida abba!bayan ya amsa yace to mamana!kingama karatu nabaki wata2 kifito da mijin aure!kina jina?"yafad'a fuska bbu wasa"da to zarah ta amsa!
Sumayya kuwa rufe idonta tayi,tamkar me bacci"sbd tasan dataga su Abba kuka zai k'wace Mata"sukuma tambayeta dalili"batasan me zatace musu ba!
Safana kuwa twins na jikinsa Yana wasa dasu"gaba d'aya son yaran yakeyi"suna burgeshi"musammun sbd duk sadda zai gansu cikin tsabta da k'amshi suke.. sab'arsu yyi yafito dasu dg room d'in yanufi office d'in shi dasu...
Harsu Abba suka Gama zamansu"safana bedawoba"sumayya Kuma Bata tashiba"suna k'ok'arin fita saigashi yadawo da twin's da uwar shopping na kayan ciye ciye daya musu"godiya sosai Abba da mama suka mishi"saiga twins harda kukansu sun lik'ema safana"ummi tace gashi ba'a yayesuba"dasai nace abarsu su kwana... murmushi mama tayi had'e da cewa ai ankusa yayensun... sumayya kuwa har ranta taji dad'i sosai akan yadda safana yanuna kulawa akan twins duk shima k'annensane....bayan tafiyarsu Abba" ummi tace tunda taji sauk'i inta tashi gd zamu wuce"gaban safana ya Fadi"ahankali yace kibari tayi ko kwana 2 ne ummi"sbd abata kulawa sosai!to ai shikenan"zarah kuwa gabanta ket fad'uwa akan abinda Abba yafad'a"musty kuwa murna fal aransa"zai saka Mata ido yaga shizata zab'a ko wani?"inhar wani ta zab'a to wlh saidai amutu kowama yarasa....
Da misalin karfe 8:25 pm"safana ne zaune aparlourn daddyn sumayya"bayan yamasa bayani akan aika aikar da rukky tayi!salati kawai daddy yyi! had'e da cewa wlh niba haka tafad'a munba!ke dan uwarki yakikacemun?"yafad'a Yana kallon rukky daketa cika tana batsewa"mommy d'inta tace ah ah alh akanme zakayi saurin yarda?"ita yarinyar kasan metake matane ?"koma mitayi yakamata yadaketa"dubifa yadda hannunsa ya kwanta afuskarta"sbd wata banzar talaka matsiyaci!wani kallo daddy yyiwa mommy"cikin b'acin rai yace Asiya!kikiyayeni wlh"duk abinda yarinyar nan keyi kece kike bata goyon baya ko?"sbd haka bbu ruwanki"yanzun in ita aka zubarwa xiki nasan bazaki hakuraba har k'ararta saikinyi!dole kace haka Mana"ai wlh dataji ta tawa dabata aureshi"ta zauna da kishiya ta had'i bak'in ciki!karki koma mgn anan!cewar daddy murya akausashe"
Safana kuwa haushi gaba d'aya mommyn ruky tabashi"sai yanzun yagano"itace bata bawa rukky tarniyya ba"kanajina Aliyu?"muryar daddy ta katse mishi tunani"ahankali yace eh daddy!yace to Dan Allah kayi hakuri insha Allah hakan bazai sake faruba"zanje har gida nabawa yarinyar hakuri da mamanka"sbd anzalinceta"ko k'ara aka kaita dole za'a Mata hukunci indai akan gsky za'ayi shari"ar "sbd haka katashi kuje"dg yanzun inta maka Abu kasanarmun komai"kekuma wlh Dani kike mgn "Allah yasa yace kinyi wani abun kiga yadda zanyi dake"shashasha kawai...turo baki tayi sbd duk iskancinta tana shakkar mahaifinta!tashi safana yyi Yana mishi sallama"yafice rukky ta tashi"had'e da cewa daddy nifa banida ko sisi a account d'ina"baya bani ko ficika" daddy yace inkudi kikeso sai kinema ta hanyar yin sana'a "bakisan kinemaba"sai kashewa kika sani"to bazan bayarba!ah ah alh ai abin sai yyi yawa"kabata kud'i koka Mata transfer"su 2 ka mallaka aduniya"inbasu ji dad'i da dukiyarka ba saisuyi me?"
Girgiza Kai kawai yyi yace taje zanmata transfer d'in 500K..fita tayi"tasameshi Yana amota"uffan bece mataba,itama haka ta bud'e front sit ta shige..
Har suka iso gd bbu Wanda yacewa d'an uwa kanzil...
Wanka fasana yyi ,yawuce asibitin bayan yatsaya yasiya musu kayan k'walama"
Zaune sumayya take ta jingina da pillow"plate d'in abinci akan cinyarta tana ci ahankali"
Sallama yyi yashigo"ummi ta tafi gd"tabar zarah ta kwana anan"da safe saitazo ita"
Gaidashi zarah tayi"yace ummifa?"
Aitana gd Yaya!ok yafad'a Yana ajiye ledojin hannunsa"
Fita zarah tayi"hakan yasa yataso yazo yazauna kusada ita"jikinsu na gugar juna"wani haushi sumayya taji"gashi bbu wani space balle ta matsa...Mrs safana ya jikin?"yafad'a Yana kallon ta!banza tamishi"shikuwa mgn yake nema ko masifane ta mishi"amma tak'i kulashi"nasan akan abinda yafaru kiketa fushi haka ko?"inkikayi hakuri saiki sake samun wani tunda mijinki lafiyayyene...Afusace tace ni ayanzun banida miji"saidai nan gaba zanyishi insha Allah"maisona da k'aunata"Mai tsoron Allah....ai Mrs safana inma Zaki Dena wasik'ar jakin nan gara kidena"nidake aurenmu mutu ka karaba"sannan karki koma zancen wani Zaki aura da aurena akanki!"
Allah ko?"bansaniba!karka sani!ni sumayya nace ba matarkace bace ni"wawiyar matarka nacan gd kabaro"kugodewa Allah dayasa bazan koma gdnka ba"wlh da dg ita harkai sainabaku mamaki!
Murmushi yyi had'e da cewa"sai muga ta yadda zakiyi kik'i komawar!shiru kawai tayi"ledar magun guna ya d'akko"da robar ruwa"yadubi abinci yaga bawani sosai taciba"Kisha magani ,saiki k'ara da wani abu!bazanshaba in ruwanka da lafiyata?"
Had'e Rai yyi"yace wlh kokisha ta arzik'i kokisha tatsiya"danneki zanyi namiki d'ura dukda Baki lafiyar"batace komaiba ta karb'a Tasha tana yamutsa fuska"
Ledojin daya shigo dasu"yabude yafito da kaza gasassa"yazuba aplate"yafito da maltina"ya ajemata kan cinyarta"bayan yad'auke plate d'in abincin...malam ka d'auki abinka"banason duk wani abu daya fito ahannunka...sbd Kinga na k'yale ki ko?"yafad'a Yana hawa bed d'in"k'ok'arin fincikota yyi"da sauri tace Dan Allah zanci"kadena...tabe baki yyi had'e da tashi yaduba agogo yaga har10 ta wuce... adedenan Kuma zarah ta shigo"Zama tayi"yace ki kula da ita baby nizan wuce Saida safe insha Allah zanzo!zarah tace to Yaya"
Kallon sumy yyi yaga tanacin naman"Kuma da alama yamata dad'i"murmushi yyi"yamatso gab da gadon"yaja hancinta"ta buge mishi hannu"magulmaciya kawai kinaso kina kaiwa kasuwa..bejira cewartaba yafice"zarah dai nata murmushi sbd ta lura safana yafara shiga hannu...
*Bayan kwana2*
Zaune suke a parlourn ummi"kasancewar Basu jimaba da dawowo dg asibiti..zarah tadubi sumayya,wacce Kevin ayaba! tace dan Allah kicanza waya"wannan waya dukta tsufa...murmushi sumayya tayi had'e da cewa to kisani ajikka Mana"kafin Zara tace wani abu sameera ta shigo parlourn...gaisawa sukayi da zarah kafin zarah ta fice tabasu guri"
Sameera tace k'awata yajikin?"sumy tace da sauk'i nayi fushi dake!dariya sameera tayi had'e da cewa wlh kinsan abun sai ahankali ga shi gobe ankoma skul"yaushe Zaki Fara zuwane?"
Ware idanu sumy tayi tace sai next week"suna cikin mgn safana ya shigo...kauda Kai sumy tayi"sameera ta gaidashi"zama yyi kan kujera"yadubi sumayya wacce hankalinta baya gareshi"har cikin ransa yaji Babu dad'in ko inkulan data ke nuna mishi"dama ransa ab'ace yake"yadawo da yunwa "yasami rukky bata aza komaiba"yamata mgn kaitsaye tace Bata iyaba...
Tashi yyi ya wuce dining area"yaja kujera, yabud'e warmer's yazuba abainci"sameera murya k'asa k'asa tace bakida kirki wlh"mijinki yadawo bbu ko sannu da zuwa kinshareshi..banza sumy ta Mata ta galla Mata harara... adedenan Kuma ummi ta shigo parlourn"kallo d'aya tayiwa safana ta d'auke kanta"Zama tayi suka gaisa da sameera"kafin tamusu sallama ta fice!ummi ta dubi safana tace meye dalilinka nazuwa nan kaci abincine?"bacin kanada iyali"shiru yyi Yana sosa Kai"sumy aranta tace aisai inta iya gorkinko"
To wlh Bari kaji karkoma zuwa nan kaci abinci in ita bazata iya maka girkiba to kafasa cin abincin"sannan inajiran ka kamun takardar sumayya...bece komaiba" yataso yabar dining area d'in kasancewar yagama cin abincin...
Yana k'ok'arin fita hjy kaka da anty zainab suka shigo parlourn Rai b'ace...
Hjy Kaka tace wace irin macece ka aura Aliyu?"
dg b'angaren ku muke munzo duba sumayya"azatonmu sumayyar nacan...Ashe tana nan?"anty zainab tace lallai bakayi daceba wlh"Yar iskar yarinya marar mutunci..
Ummi tace wani abu ta muku ko???
Mu had'e alhamis gobe inada uzuri..
Share
By mmn fareesa 🖊️
Assalam.
ReplyDeleteGaskiya labarin na Yau Da Gobe ya matukar tsaruwa, dole masu karatu su jinjinawa Maman Fareesa.
Dauki cikakkun littafin hausa a shafin Top Hausa Novels.
Godiya.