AZIZA DA AZIMA 61-70
*PAID.*
🅿️=6️⃣1️⃣↪️6️⃣2️⃣
Sakin wuyarta Azima tayi tana huci,tana sakinta Sumy ta zube kasa a sume, cikin tashin hankali suka ɗagota,Beenah wacce saukowarta kenan daga sama dan dama bata nan akayi wannan show din, Mamanta tace
"Beenah! Hanzarta dauko ruwa a fridge" ganin Sumy a baje yasa beenah kwasa da gudu taje kitchen ta dauko ruwa aka yayyafawa Sumy, da karfi ta fizgi numfashi, ganin ta saki ajiyar zuciya yasa Al'mazeen ya fizgi Azima ya wanka mata mari, wani gurnani Azima tayi tasa hannu zata shaƙi wuyar Al'mazeen da hannu biyu amma tamkar an daskarar mata da hannu ne ta kasa, cike da mugun zuciya da mugun jin haushin kanta ta yi hanyar waje, ganin haka yasa Al'mazeen dafe kai yana ambatar sunanta amma kamar ba da ita yake yi ba.
Gate ta nufa da niyyar barin gidan, dan ta ga Alkadarinta yana gaff da karyewa, kamata ya yi ace ta kashe sumy dan ita duk wanda ya tabata hukuncinsa kisa ne! haka ma Hamma Mazeen da ya mareta, amma ta kasa aiwatar da komai,to me hakan ke nufi? ai gwara ta bar gidan kafin abunda take rayuwa da shi shekara shabiyar zuwa sha shidda a rabata da shi.
Al'mazeen ne ya biyota yana kiranta amma kamar ba da ita yakeyi ba dan ta zuciya, karamin kofar gate tasa kafa tayi kwallo da shi,ga mamakin mai gadi sai ganin kofa ya yi a kasa da sauri ya tashi ya matsa ya bata waje, tana sa kafarta a waje da niyyar fita kamar wanda wutar lantarki ta kama haka taji a jikinta, ji tayi kamar an ja kafarta akayi sama da ita sannan aka wurgota cikin gidan, sai da ta yi sama tukunna ta faɗa kan wani dutse kanta ya bugu, zare ido Al'mazeen ya yi yana fadin
"Azimaaaa!" da sauri ya yi kanta yasa hannu ya dagota, harta baƙin tabarau dinta sai da ya fadi, a lokacin da Al'mazeen ya matso gareta ta rufe ido jin yadda wani mashahurin jiri dake kwasarta dan kanta ya buge sosai, cikin tashin hankali Al'mazeen ke fadin
"Subhanallahi! Azima! Azima! Azima! Dan Allah kiyi hakuri ba da nufi bane,meya sameki?" jinta shuru ba motsi yasa ya dauketa cak ya koma da ita ciki, yana shiga har yanzu ana tsaye a kan sumy wacce bata gama farfaɗowa ta dawo hayyacinta ba.
Ganinsa sukayi ya shigo da Azima a hannun sai kace baby yana shirin sa kai ya haura sama,cikin masifa Maman Hanan ta ce
"Kai Al'mazeen! Wannan wani irin rashin hankali ne! Ya zaka dauko yar aiki haka a hannunka sai kace matarka!? A gabanka fa ta shaƙe Sumayya tana shirin kasheta amma baka dakatar da ita ba, zata bar gidan ka je ka dawo da ita, ga Sumayya nan dake bukatar taimako amma baka kalleta ba ka wani dauko wannan ƙidahumar jejin matarka ce ko aurenta zakayi! bayan kasan kuma su Sumayya da Sadiyya sune matan da zaka aura ko? ko dai akwai wani abu a tsakaninka da wannan daukar kaddaran ne?" (wai Azima ce daukar kaddara) rai a haɗe Al'mazeen ya juyo ya ce
"To auranta zanyi! Ta fiye min su Sumayya da Sadiyya sau dubu! Ina sumayyan ce ta jagaleta? Ita ma Azima ta suma,ku kai sumayyar sama bari na duba Azima tukunna,zan zo na duba Sumayyan daga baya" yana gama fadi ya hau sama ya bar su shanye da baki.
A gadonsa ya kwantar da ita yana dubata, gefen kanta ya gani ya ɗan fashe, hannu yasa da niyyar yi mata treatment ji ya yi ta riƙe hannunsa, kallonta ya yi ya ga har yanzu idonta a rintse yake, a hankali ta miƙe ba tare da ta kallesa ba tasa kai zata fita yayi saurin shan gabanta,
"Azima yi hakuri! Ki fahimceni ba da nufi na mareki ba, laifinki ne inata miki magana ki saketa amma kin ƙi ki
saurareni, taya zaki shaƙeta haka idan ta mutu me kike tunani zai faru? Ba ke kaɗai ba harta ni sai an kulleni dan anyi kisan kai a gidana! da kin kasheta sunanki fa zai koma criminal ne, kuma ba zan so hakan ta faru ba amma kiyi hakuri kinji? karki yi fushi" ya faɗa yana haɗe hannuwansa alamun roƙo,Azima kuwa juya kanta tayi gefe har yanzu taki yarda ta buɗe, yana gama magiyarsa ta rab'a ta gefensa ta fice, riƙe kai Al'mazeen ya yi yana jan ajiyar zuciya,box dinsa ya dauka ya fito yayi side din su Hanan, ya nufi dakin baki wanda su Sumayya suke zama idan suka zo, da sallama ya shiga har zuwa yanzu suna tsaye a kan Sumy, rai a haɗe fuskarsa ba annuri ya shiga, allurai ya yiwa Sumy sannan ya ɗora mata ruwa, nan da nan bacci ya kwasheta, kwashe box dinsa ya yi zai fita Maman Beenah ta ce
"Al'mazeen? Amma ina fatan batun auren yarinyar nan kawai ka faɗa ne ba da gaske kakeyi ba?"
Cak Al'mazeen ya tsaya ya juyo ya ce
"Da gaske nakeyi! Zan aureta! taya zan auri Sumayya? daga zuwanta yau ta bi Azima da sharri! Laifi biyu wanda na tsana a rayuwata! tayiwa Azima ƙarya da ƙazafin abunda bata yi ba,ƙazafin ma kuma na sata!" yana gama fadi ya fice, aka barsu da zare idanu.
Part dinsa ya koma, yana tajin babu dadi na ganin Azima tayi fushi, shirin bacci ya yi ya kwanta dan yana tashi sallar dare.
@@@@@
Da washe gari kamar yadda Azima ta saba haka ta shigo ta kawo masa abinci amma bayan sallama ko gaishesa taƙiyi, shi kuwa kallonta yakeyi yadda ta duƙar da kai fuska babu rahma ranta a haɗe, ganin har zai fita bata yi masa magana ba ya saka shi fadin
"Ba ki huce bane? na fa baki hakuri, ba zaki min magana ba? to ga wayarki, kalli ki ga yadda zakiyi amfani da shi" turo baki tayi tana fadin
"Bana so" sannan ta fice, Al'mazeen ya sosa kai ya ce
"Tab lallai abun babba ne, duk yadda jiya ta nuna murna da farincikinta akan wayar yanzu kuma tace bata so?" haka yasa kai ya fice, a office sai tunaninta yakeyi, Azima kuwa wuni tayi fuskarta a murtuke dan abunda ya dameta ya dameta, tunda tazo fita akayi sama-sama da ita sannan aka maidota gidan ta rasa inda zata saka kanta.
Wasa-wasa Azima ta dauki zafi dan har aka kwashe sati daya bata magana da Al'mazeen tsakaninta da shi sai dai ta kai masa abinci ta gyara masa daki,duk kulawar da take ba shi bata daina ba magana ce dai bata masa, a sati dayan nan kuwa Al'mazeen ya yarda ya kamu da soyayyar Azima, kullum sai ya bata hakuri amma taƙi ta sauraresa dan ita kadai tasan bakincikin da take ciki.
Ta bangaren su Aziza sun fara shirin bikin Sultana wanda zai gudana nan da sati biyu ciff, Aziza daurewa kawai takeyi tana abubuwa, amma bata da wani kuzari da karfin dafi.
Ana saura sati daya biki duk hankalin sultana a tashe yake.
Al'mazeen ya shaidawa Nawaz a kan cewa idan ana saura kwana uku ɗaurin aure zai zo.
Ko da Sultana ta kara yiwa Khalil magana a kan tafiyarsu kano yace ta hakura kawai sun yi magana da Al'mazeen yace zai gaya musu ita ba sai taje ba,sultana ji tayi kamar ta kurma ihu dan bakinciki.
@@@@@@@
Fitowa daga daki Aziza tayi zata hau sama da wani jiri ya ɗibeta zata fadi dai-dai lokacin da Nawaz ya sawo kai parlorn amma kafin ya iso ya tarota tuni ta fadi kasa,sunanta ya ambata ya dagota yana jijjigata a hankali yana kiran sunan Mom da sultana, da sauri suka sauko kasa suka samu Aziza kamar ta suma ne yaya ne oho
"Nawaz me ya sameta!?" mom ta tambaya hankalinta tashe, Nawaz yace
"Wlh mom ban sani ba,ina shigowa ne na ganta tana faɗuwa!" Mom ta ce
"A gaskiya Nawaz shawaran Malam Yunusa zamu bi, kawai ranar daurin auren sultana a haɗa a daura da naka da Aziza! mu tausayawa yarinyar nan halin da take ciki! Sai daurewa takeyi tana hadiyar zafin ciwo, a kananun shekarunta tayi ƙanƙanta da jurewa!" mom ta fada tana sakin kuka mai ban tausayi, Nawaz wanda shima idonsa ya canza kala ya ce
"Duk yadda kikayi dai-dai ne mom"
"Ka dauketa ka kaita daki! Sultana ke kuma ki zauna da ita, bari naje na sanar da cewa auren biyu ne" mom ta fada tana hawa sama, shi kuwa Nawaz ya dauki Aziza ya kwantar da ita a daki sannan ya fice yana neman layin Al'mazeen dan ya shaida masa har da shima za a daurawa aure.
A cikin ƙanƙanin lokaci mom tayi sanarwan auren Nawaz da Aziza wanda mutane sun sha mamaki, amma da shike ance ba a mamaki da ikon Allah sai kowa ya bi lamarin da fatan alkairi.
Sadda Nawaz ke gayawa Al'mazeen akan cewa zai auri Aziza ba karamin mamaki Al'mazeen ya yi ba, har yaushe Nawaz ya fara soyayya da Aziza da har ta kaisu ga maganar aure nan da sati daya? Sannan Nawaz baya son auren yarinya kamar yadda baya son auren babba sosai ,ya tabbata idan Nawaz ne zai iya cewa Aziza tayi masa yarinta, haka dai ya share maganar yana fadin shima ga shi ya kamu da son Azima,yana so ya ba wa Nawaz labarin Azima amma sai yaji kamar an riƙi bakinsa, dan haka ya share maganar gabadaya yana tambayar Nawaz dame-dame zasu shirya da bikin tunda aure yazo a bazata, nan Nawaz ke gaya masa babu wani abunda za ayi wanda ya wuce daurin aure daga shi shikenan, dan harta sultana tace babu abinda zatayi da an daura aure kawai a kaita,babu yadda khalil baiyi da ita ba ko da walima ayi nan ma tace ta yafe, ya fahimci rigima ce kawai take ji da shi amma da ta shigo hannunsa zai sauke mata shi.
@@@@@
Da misalin karfe tara hamma mazeen ya kira Hadiza a waya yace ta kirawo masa Azima, Hadiza ta amsa da to sannan taje kiran Azima wacce yanzu dakinta daban ita daya, a lokacin tana kwance a gado ta zama macijiya, Hadiza kuwa tana zuwa ta sako kai ta tura kofa, wani burki tayi turuss! Ganin abunda ko a mafarki bata taba gani ba, shirgiɗeɗen maciji blue sai sheƙi yakeyi, wani mahaukacin ihu Hadiza ta sake tana zubewa a kasa sumammiya, da sauri Azima ta waigo nan tayi saurin komawa mutum ta yo kan Hadiza.
Da gudu su Maman Hanan suka fito har da Al'mazeen wanda ya sauko daga part dinsa, dakin Azima suka nufa inda suka ji ihu ya fito, suna shiga suka samu Hadiza a baje Azima na tsaye a kanta, suna shigowa ta duƙar da kai kasa.
"Me kika mata!" cewar Maman Beenah hankali tashe, Sumy wacce ta jima da dawowa dai-dai ta ce
"Ba mamaki itama an shaƙeta ne! Duk yadda akayi wannan yarinya ta taba zaman prison" Al'mazeen cikin fushi ya kalli Sumy yace
"Ban ce duk wanda yake son kansa da zaman lafiya a gidan nan ba ya daina shiga hidimarta!!?" shuru sukayi ya kalli Azima ya ce
"Me kika mata?"
"Ban mata komai ba,nima daga kewaye nake naji ihu na fito da sauri sai na ganta a sume,idan kuma baku yarda ba idan ta farfaɗo ku tambayeta" Al'mazeen ya kalli Sady yace
"Kawo ruwa a yayyafa mata"
"Me?"
"Nace kawo ruwa a yayyafa mata!" ya faɗa a tsawance Sady ta fice tana yatsine fuska, ruwan ta kawo aka yayyafawa Hadiza a firgice ta farka da karatun ayatul'kursiyyu a bakinta! Nan aka hau tambayarta menene, cikin fitar hayyaci Hadiza ke fadin maciji! maciji!
"Maciji!!" Sumy Sady da Hanan da Beenah suka rungumi juna suna ihu,harta su Maman Hanan da Maman Beenah bayan Al'mazeen suka koma jikinsu na kyarma suna tambayar Hadiza ina macijin, yayinda Azima take kallonsu ɗaya bayan ɗaya ta cikin gashin kanta da ta sauko dashi ya rufe mata fuska, Al'mazeen yace maciji dai a dakin nan?"
"E wlh nagani! Katon maciji! Ruwan ganye! Babba ya cike wannan gadon! Na ganshi a kan gadon nan! Wlh na gani! Maciji! Babba maciji!" duk a ruɗe Hadiza ke magana,jin abunda take fadi yasa suka maida maganar ta ta shirme ba mamaki tayi gamo ne,su sumy suka hau tsaki
"Hanan je ki kirawo Talatu ta zo ta kai Hadiza daki,kafin nan bari nayi mata alluran bacci" ya fada yana ficewa, su ma su Maman Hanan duk ficewar sukayi.
Ba jimawa Al'mazeen ya sauko da allura a hannunsa ya zo ya yiwa Hadiza sannan ya ce Talatu ta kaita daki ta kwantar da ita,bayan sun fita Al'mazeen ya kalli Azima wacce kanta ke duƙe yace
"Zan sha shayi, za a iya haɗawa a kawo min?" ya tambayeta yana mai ƙura mata ido, gya ɗa masa kai kawai tayi sannan ya fice ita kuma ta nufi kitchen dan haɗa masa.
Bayan su Sumy da Sady sun koma daki Sumy ke fadin
"Duk lokacin da na kalli wancan jakar yarinya 'yar fulanin can ji nake kamar na kashe shegiya! har yanzu ban manta da kaini kofar lahira da tayi ba" Sady tace
"Mu jawo shegiya yau mu ci ubanta a dakin nan kawai" Sumy ta ce
"Haka za ayi" fitowa sukayi nan suka hangi Azima da tray a hannunta tana hawa part din Al'mazeen, Sady tace
"Kalli Matsiyaciya, mu jira ta dawo mu ja banza muci uwarta!" nan suka tsaya suna jiran saukowar Azima.
Da sallama ta tura kofar parlorn a lokacin Al'mazeen suna waya da Nawaz, tana ajiyewa ta tashi ta juya zata fita da sauri Al'mazeen ya ce
"Azima tsaya!"
Nawaz ya ce
"Azima? Azima kuma? Al'mazeen wace Azima?"
🍃🍃🍃🍃🍃
MOMYN AHLAN✍🏻
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
*PAID.*
🅿️=6️⃣3️⃣↪️6️⃣4️⃣
"Amm Nawaz ina zuwa zan kiraka" Al'mazeen na faɗi ya ajiye wayar, da kallo Nawaz ya bi wayarsa da shi yana fadin
"Azima irin sunan yar uwar Aziza ce fa? anywhere mutane nawa ne masu suna iri daya" daga wannan tunanin ya ajiye wan can a gefe.
"Azima pls ki tsaya ki saurareni! Fushin ya isa haka kiyi hakuri dan Allah! Har tsawon wani lokaci zaki dauka kina fushi dani?"
ƙin magana tayi yace
"To shikenan idan ba zaki min magana ba, ga wayar ki karba,babban aminina Nawaz zaiyi aure shi da kanwarsa yau saura kwana shidda bikin,ni kuma zan tafi nan da kwana uku kafin nan gobe zanyi kwana biyu a asibiti dan akwai mutum bakwai da zan yiwa aiki, ki karbi wayar dan na dinga jin lafiyarki, sannan idan na dawo jibi ba lallai bane mu samu magana da juna ba, dan ba da wuri zan dawo gida ba, da washe garin kuma da wuri zan kama hanyar kaduna" saurin karban wayar tayi tana fadin
"Nima zan bi ka bikin" tashi yayi yana fadin
"Ba zaki bini ɗin ba, ba fushi kikeyi dani ba ana neman sati uku baki min magana"
"To kayi hakuri na daina fushin amma zan bi ka"
"To naji, saiki shirya, mutanen gidan nan ma zasuje, idan kika je ma zaki ga wata mai kama dake"
"Mai kama dani kuma!? Ni babu wani mai kama dani a duniya! ni ni daya ce"
"To naji amma ki dai shirya da wuri,dan inaso ace karfe shidda da rabi mun bar gidan nan" murna ta hauyi tana tsalle zataje yawo, watakila ma daga can ta samu kafar guduwa ta gudu ta huta da ala'ƙaƙai, sai da safe ta masa zata fice ya dakatar da ita, yace
"Kina son makaranta?" tabe baki tayi ta girgiza kai, ƙura mata ido yayi yana hango gaskiyarta yace
"Kwanaki na tambayeki kin sauke al'kur'ni kika ce min a'a shima nace zaki ci gaba kince bakiso,ke baki san ilmi shine mutum ba?"
Azima a ranta ta ce
"Humm! Wani karatu ni da ko sallah bane yi" amma a fili da shike tana murnan barin gidan ya sakata fadin
"Idan muka dawo daga kaduna na yarda zanyi makarantar" ta faɗa tana murmushi"
"Kinyi alkawari?"
"E nayi" ta faɗa tana ficewa.
da murnanta ta hau saukowa tana zuwa dai-dai step din tsakiya taji an fisgota an shige daki da ita aka wurgata ta fadi kasa, tana daga kai ta ga su Sumy da Sady ,hade rai Azima tayi tana shirin magana sady tace
"Inyeee yar banza miye a hannunki? Kinje ya gama kwalularki sai ya baki me?" ta faɗa tana sa hannu ta fizgi wayar daga hannun Azima, tashi tsaye Azima tayi, sumy tasa hannu ta yaye mata mayafi ta jefar,Azima ta duƙar da kai,maganar Al'mazeen ne ya faɗo mata da yake cewa shi a rayuwarsa baya son rigima, sannan yadda yasa doka su daina shiga tsabgar Azima haka itama Aziman yace ta daina shiga tsabgarsu idan kuma maganar aiki ne to yanzu ma shi zata dinga yimawa tinda dama shike biyan duk ma'aikatan gidan, tunowa da haka ya sakata fadin
"Kunga bani shiga hidimarku tunda Hamma Mazeen bai son rigima,ku bani wayata!?" Azima ta faɗa tana cije baki gami da miƙa hannu, Sady ce take ƙurewa dalleliyar wayar kallo tace
"Inyeee! waya mai tsada wa yar aiki! yar aikin ma ƙidahuma!? To wlh ba zan bayar ba fasawa zanyi sai dai duk abunda zai faru ya faru" da sauri Azima tace
"Karki fara wannan kuskuren dan na....." maganarta ne ya tsaya cak sakamakon rutsa wayar da Sady tayi da bango, saurin zuwa daukar wayar Azima tayi jikinta na b'ari alaman b'acin rai, tana daukar wayar ta ga ya ragargaje, bata gama saita b'acin ranta ba taji an jawo wuyar rigarta, waigowa tayi ta ware blue eye dinta a kan Sady, Sady na ganin ido a rine tayi saurin sakin wuyar Azima taja da baya,ihu Azima ta sa ta haɗa hannuwanta biyu ta ɗagasu sama ta tayar da guguwa ya dauki Sady ta dinga bugata da bango, ihu Sady keyi yayinda Azima ta wurga wani bakin abu a kofar shiga daki wanda duk ihu da kacaniyar da za ayi a dakin babu mai ji, nan ta haɗa da sumy ta dinga cin uwarsu,kuka suke suna bata hakuri tare da gaya mata basu san cewa ita ba mutum bace tayi hakuri, Azima da ta kara yin sama da Sady ta buga mata kai a silin fuskar Sady duk jini ta ce
"Shin zaki iya maida min wayata ta koma yadda take? Na sha gaya muku karku tunzurani ku ga asalin wacece ni amma kun kasa fahimta! An gaya muku ko wane yake mutum! Balle kuce zaku takasa son ranku!" cikin kuka Sumy tace
"Dan Allah Anty Azima kiyi mana rai! Ni wlh yau din nan bana kwanan gidan nan,gobe da sassafe kuma katsina nayi,wlh har ta auren Hamma Mazeen din ma nikam na yafe" Sady ma mai kwasar baƙar wuya tace itama ta yafe, sakinsu Azima tayi suka zubo a kasa sharab kamar an watso kaya, suna faduwa suka hau tattaren kayansu, a daren suka fice ba tare da kowa ya sani ba sai mai gadi da kuma driver da suka ce masa ya kaisu gidan wata kawarsu, Azima sai da ta gargaɗesu da cewa wlh idan suka sake suka gaya ma wani abunda ya faru sai ta maida Sady kunkuru ta maida Sumy gwaɗo, jin haka yasa sukace bakinsu ƙanin kafarsu.
Bayan sun tafi Azima ta dau wayarta ta sa hannu ta shafe kayanta ta koma yadda take kamar ba abunda ya same shi tayi hanyar dakinta ta kwanta tana murmushi tana kallon wayar wajan kusan sha biyu da yan mintoci,bayan ta gama daddannawa ta ajiye ta lumshe ido alaman bacci yazo sai taji wayar na ƙara,dubawa tayi tana hararan wayar, to waye kuma a wannan lokacin? Ta tambayi kanta, dagawa tayi kamar yadda Al'mazeen ya nuna mata tasa a kunne, da masifa ta fara tarban wanda yake kan layi
"Dalla waye! A wannan lokacin! Baka iya hakura ka kira gobe ne! Ko baka san yau na karbi wayar bane? Idan Hamma Mazeen ya sani ai sai ya kwace! Idan kuma ya kwace ko ma waye kai Allah ko a ina kake sai na maidaka burgu!" dariyan Al'mazeen taji ta zare ido tace
"Hamma Mazeen? Dama kai ne? Bakayi bacci ba? Ina dai ba wani abu kakeso ba?" ajiyar zuciya ya sauke mai karfi ya ce
"Na kasa baccin ne shine nace bari na kiraki muyi hira"
"Oh to inajinka" hira suka hau yi ko wannensu ya saki baki,Al'mazeen yana son gayawa Azima yana sonta amma sanin ba ko da wani lokaci take saiti ba zata iya tsince masa notinan kai ta damka masa a tafin hannunsa, shiyasa ya yi shuru suka ci gaba da hira har wajan biyun dare, harbi suka ji ya fara tashi a gidan, Al'mazeen yace
"Ƙaran miye haka? Subhanallahi! ba dai b'arayi ba! Azima karki fito!"
"A'a Hamma mazeen kai karka sauƙo"
"Azima nace miki karki......"
"Na ce maka ka tsaya ko!" ta faɗa a tsawance tana ajiye wayar ta fito, fitowarta ya yi dai-dai da balla kofar parlor da sukayi suka shigo dik da kofar security door ne, suna shigowa da Azima suka fara karo duk sun rufe fuska suna riƙe da bindigogi, Azima suka cafka suna tambayarta ina mai gidan tace baya nan, ogansu ne ya bada umarni a shiga lungu da saƙo na gidan a fito da duk mutanen gidan har da ma'aikata, nan kuwa aka hau fito da ma'aikata sannan aka sauko dasu Maman Hanan da Beenah da Maman Beenah,Hanan da Hanif duk aka fiddo dasu,bindiga aka ɗorawa Maman Hanan a goshi ana tambayarta ina Al'mazeen kafin Maman Hanan tayi magana Azima ta kuma faɗin baya nan da karfi babu alamun tsoro a tattare da ita, Al'mazeen kuwa yana aikin dambe da kofar dakinsa wanda ya kasa buɗewa, Maman Hanan jin bindiga yasata fadin
Ai part din Al'mazeen na saman nasu dan haka yana can sama, nan ogan b'arayin yace su hau su duba,dama wa inda suka hau daga farko basu lura da dayar step din ba, wani ke fadin yau zasu cika aljihunsu da kudi a wannan gidan, Azima tace
"Idan baka cika aljihunka da kudi ba,ni na maka alkawari zan cika maka cikinka da gubar dafin maciji!"
"Kai wannan yarinya bata da kunya! Waike bakinki baya shuru ne zan fasa kanki da bindiga fa!" cewar wani daga cikin b'arayin, ogansu yace ku kyaleta mun san irinsu ai, bari mu karbi abunda ya kawo mu daga nan mu rabata da baki har abada muyi mata fyaɗe muyi gaba, wani kallo Azima ta musu tana shirin magana taga an fito da Al'mazeen ana jansa, ranta ne ya b'aci ganin yadda suke fizgar shi kamar kaza.
Gaban ogan aka kawosa ya dago ido yaga ahalin gidansa a zube a kasa an kewayesu da bindiga Azima kuma ana riƙe da ita.
"Dan Allah karku yiwa kowa komai plss" Al'mazeen ya faɗa hankalinsa a tashe
Wani dariyar mugunta ogansu ya sake ya ce
"Abunda ya kawo mu ba mai tsanani bane Kuɗaɗe kawai zaka bamu sannan mu yiwa wannan yarinyar fyaɗe mu kama gabanmu" zare ido Al'mazeen ya yi jin sunce zasu yiwa Azima fyaɗe hakuri ya hau basu amma da shike zuciyarsu ta riga da ta bushe da rashin imani sukace babu abunda ya damesu, Al'mazeen yace
Su fadi kudin da zai fanshi Azima,nan suka masa wani zunzurutun kudi wanda idan ya basu ya kwashe kudin acct dinsa kaff kai har ma da gidan da suke ciki a yanzu, zufa ce ta hau wankewa Al'mazeen jiki yace musu baya da wa innan kuɗaɗen a gida, sannan kudinsa na acct bai kai wannan ba sukace karya yake yi,idan babu kudin a gida to ya musu transfer (kai b'arawo da karfin hali yake wlh).
"Ko da yana da shi ba zai bayar ba!" Azima ta faɗa jikinta na rawa sabida bakinciki izuwa yanzu yaci ace kaff ta sare b'ayin nan amma fitowar Al'mazeen ya dakatar mata da komai.
"Ai kuwa idan bai bayar ba lahira zatayi baƙo, ke kuma zamu yaga-yaga dake! idan kuma kinci musu ya kuma fadin cewa ba shi da kudin da muka tambaya ya gani, dan ko biyar ba zamu rage ba" shuru Al'mazeen ya yi zuwa can suka ce yana bata musu lokaci akwai gidan da zasuje
Almazeen yace
"Wlh kudina na acct bai kai haka ba,kuyi hakuri na baku kuɗin duka amma bai kai yadda kuke bukata ba"
"Amma lallai ka raina mana hankali, a wannan babban gidan naka zakace baka da kudin da muka tambaya ashe kuwa baka son rayiwarka da ta wannan yarinyar!"
"Ku kashesa!" ogan b'arayin ya faɗa, daga Al'mazeen akayi aka saita masa bindiga ganin haka yasa da sauri Azima ta rintse ido hannunta ya kama da wuta ta ciki, saurin saketa wanda suka riketa sukayi sakamakon wani bala'in zafi a tafin hannunsu, rintse ido Al'mazeen yayi yana kalman shahada, ji yayi karan an saki kunnamar bindiga, kafin bullet din ya shigo jikinsa Azima ce ta fara shigewa jikinsa bullet din ya shigeta a baya, saurin buɗe ido Mazeen ya yi ga Azima a jikinsa da Alama bullet din jikinta ya shiga!
"Azimaaaaa!!" Mazeen ya faɗi hankalinsa tashe da sauri tasa hannu ta shafi fuskarsa nan ya kafe, sannan ta juya ta watsawa su Maman Hanan wani baƙin hayaki nan suma suka kafe sannan ta juyo tana kwashe gashin fuskarta ta nannaɗe ta waro blue eye dinta, dan idan bata ci ubansu ba hankalinta ba zai kwanta ba,bakinciki zai iya sawa ma ta sari kanta ta mutu.
Su kuwa b'arayi tsayuwa kallon bala'i da ikon Allah suka yi, wani gurnani Azima tayi ta juya nan ta zama macijiya.
Karyan iskanci nan suka saka ihu, ta ce
"Kamar yadda baku da imani haka nima ban da shi, nawa kam har ya fi naku! RUWA BIYU! AZIMA! AZIMA BANJU MACIJIYA! NI MACIJIYA CE!" tana faɗi ta hau binsu da sara, sai da ta saresu kaff sannan ta naɗesu kaff dinsu da jelarta ta sulale ta jasu suka bar gidan, b'acewa tayi ta kaisu jeji ta watsar dasu sannan ta koma gidan, nan ta samu mai gadi a sume an harbesa a kafa shima,bata yi ta kansa ba ta koma ciki ta samu har yanzu suna nan a daskare hannu tasa ta shafe jinin dake wajan tass sannan ta watsawa su Maman Hanan wani bakin hayakin nan ta sakesu, Al'mazeen kuwa kara shigewa jikinsa tayi ta shafo fuskarsa nan shima abun ya sakesa a firgici ya riƙo Azima wacce ke sulalewa a jikinsa yayi saurin haɗeta da kirjinsa yana ambatar sunanta, dago kai yayi bai ga kowa ba yaga wayam
To meya samesa sai kace wanda komai na jikinsa ya tsaya na wucin gadi.
Su Maman Hanan kuwa masu fitsari a jiki da masu kashi duk sunyi, Hadiza kuwa cewa tayi wlh yau gidansu zata tafi dan daren nan babu abunda ta gani sai bala'i ido da ido, Al'mazeen na daukar Azima suka fito gabadaya nan ya iske mai gadi a kwance shima da harbi a kafa, kwashesu yayi duk ya kaisu asibiti a lokacin da ya fito ana kiran sallan assalatu.
Bayan sun isa asibitinsa duk yan gidan aka hau basu taimakon gaggawa shi kuwa ya wuce cikin emergency da Azima, shi da kansa ya hau mata aikin cire mata bullet din da ya shiga bayanta,duk abunda yakeyi tanajinsa sarai har ya gama yi mata komai, allura ya dauko zai mata tayi saurin riƙe hannunsa tana girgiza masa kai, da sauri ya hau kiran sunanta,murya can kasa tace
"Hamma karka a yi mini allura zai cutar dani, jikina bana allura bane karka mini dan Allah" hawaye Al'mazeen ya goge yana gya ɗa kai alaman ba zai mata ba, duba agogo ya yi ya ga bakwai dan haka ya wuce masallaci dake cikin asibitin ya yi sallah sannan ya koma ya duba lafiyar kowa ya ga kowa lafiya harta mai gadi an cire masa bullet yana zaune, sai a lokacin yaji ya samu natsuwa ya kira jami'an tsaro ya shaida musu duk abunda ya faru, bayan ya gama musu bayani ya tuno da ashe ya bar wayarsa a gida dan da wayar asibiti ya kira jami'an tsaron kasancewar akwai wa inda ya sani a ciki, wayar wata nurse ya karba ya saka lambar Nawaz ya hau kira, sai da ya masa kira uku kafin nawaz ya daga Al'mazeen ya ce
"Dude ni ne"
"Kai Dude jiya muna magana kace zaka kirani baka kirani ba ni kuwa nata kiranka baka daga ba,ina fata dai komai lafiya?"
"E to da sauki dai" nan Al'mazeen ya ba wa Nawaz labarin abunda ya faru, hankali tashe Nawaz yace gashi nan tahowa Kano, Al'mazeen ya ce
"Noo! Wlh karka zo don't worry we are safe now alhamdulillah! and Karka gayawa Mom am sure hankalinta zai tashi but still zan taho jibin In sha Allah dan na saka jami'an tsaro a lamarin,pls karka damu ina lafiya"
"Pls take care of urself" daga haka sukayi sallama.
Sai wajan karfe hudu kafin suka gama watsatstsakewa sannan suka ɗunguma sukayi gida har lokacin yan sanda suna zagaye da gidan,nan maƙota aka hau yiwa su Al'mazeen jaje ana yin Allah ya kiyaye gaba, nan police suka ba wa Al'mazeen rahoton sun san b'arayin sun jima suna aikata b'arna amma yanzu sun nemesu sun rasa amma zasu ci gaba zurfafa bincike, godiya Mazeen ya musu sannan yace yana da bukatar matakan tsaro a gidansa, nan D.P.O. ya shaida masa babu komai, sannan ya kamo Azima wacce ke zaune a mota ya fito da ita suka shiga ciki, dakinta ya kaita ya kwantar da ita ya kalleta yace
"Meyasa kika tare min harbi?"
"Nima ban san meyasa nayi hakan ba, amma naji a jikina ba zan iya bari a harbeka ka mutu ba" shuru Mazeen ya yi sannan ya tashi ya fita.
Sai dare tukunna su Maman Hanan da Maman beenah suka hau neman su Sumy da Sady, ko da aka kira wayarsu cewa sukayi sun jima a katsina, nan aka basu labarin abunda ya faru Sady tace
Ashe da rabon ba zamu ga masifa biyu ba,munga daya kun ga daya,maganar auren Almazeen kuwa sun yafe Allah zai bamu wani kar muzo mu bamuci kudi ba mu mutu a banza sai anjima anty suka kashe wayarsu.
Bayan kwana biyu Azima ta warware sai shirin tafiya kaduna akeyi gobe, har yanzu kuma ba a samu wani rahoto ba dangane da b'arayin, su Almazeen zasu tafi gobe shida Azima, su Hajiya Lawiza kuma sai ana gobe daurin aure zasu je.
Da washe gari kamar yadda Mazeen ya cewa Azima ta shirya akan lokaci hakan ce kuwa ta kasance karfe takwas suka kama hanyar kaduna, gaban Azima sai bugawa yakeyi.
Itama Aziza yau da bugun zuciya ta farka dan bata san da maganar aurenta da Nawaz ba duk wannan hidima sai a daren jiya, tun tara suka tafi gidan gyaran jiki da lalle dan idan basuyi yau ba gobe Sultana tace ba fita zatayi ba,kuma mom tace dole ayi walima a goben tunda jibi ne daurin aure jumma'a kenan.
Goma da rabi Al'mazeen suka iso, a lokacin gidan ya fara cika da mutane yan biki, yana shiga ciki ya yi parking din motarsa bugun zuciyar Azima ya tsananta,kallonta ya yi ya ce
"Menene?" girgiza masa kai tayi alaman babu komai
"To fito" suna fitowa Nawaz shima na fitowa daga part dinsa zai shiga wajan mom ta kirasa ya hangi amininsa, da sauri yazo suka rungumi juna ya kara yi masa jaje, bai ma lura da Azima dake maqale kanta na mugun juyawa ba ga jiri ga zufa, har sun fara tafiya Al'mazeen ya waigo ya ce
"Azima?" da sauri Nawaz ya juyo ya kalleta tana sanye da black shadow a idonta, fuskar a bude amma tayi rolling din veil mai rufe rabin fuska,ƙura mata ido Nawaz yayi, ya kalli Al'mazeen yace
"Who is she?"
"I will tell u later, now let's go inside, Azima muje ko?" jinjina kai tayi tana gaishe da Nawaz ya amsa ba yabo ba fallasa suka shiga, suna shiga aka hau yiwa Nawaz tsiya ango ango aure ba shiri a lokaci guda mun zata sai mun buga mata gangan gauro ashe yanzu kuwa wa Almazeenu zamu buga mawa, cewar tsofaffi, su dai dariya sukayi suna hawa sama Azima na kan binsu a baya, dakin mom suka shiga da sallama mom ta amsa tana yiwa Almazeen oyoyo gaisheta yayi ta amsa cikin kulawa tana fadin
"Ka ga ikon Allah ko? Abokinka zaiyi aure ,da ina shirin takura muku ashe Allah ya riga da yayi ikonsa, yanzu ma kai zan takura ma wa, naso ace a tare zakuyi aure wlh!"
"Mom ba komai ai,komai lokaci ne nima ranata tana zuwa in sha Allah"
"Amma dai ba da wannan Alishan ba ko?" Nawaz ya fada yana hararan Mazeen
"To wai ina ruwanka?mom ki masa magana"
"E kuma gaskiya ne ina ruwanka kai zaka zauna masa da ita ne" mom ta fada tana daga kai ta kalli Azima dake tsaye a bakin kofa kanta a duke jikinta na rawa
"Wacece kuma?"
"Amm umm e mom tare muka zo da ita, inasu Sultana?"
"Ayya sannu da zuwa ɗiyata" Mom ta fada tana kurawa Azima ido ganin wani sirhitaccen kamanni da takeyi da Aziza, duƙawa har kasa Azima tayi ta ce
"Ina kwana mom? Mun sameku lafiya?" hakan da tayi ba karamin dadi Almazeen yaji ba, Mom ji tayi muryan ma irin na Aziza amma sai dai Aziza ta fita sanyin murya sosai,
"Alhamdulillah! Ga shi kin zo su Sultana sun tafi gidan lalle da gyaran jiki, amma zo na nuna miki dakin sultana sai ki zauna ki jira su, ko kina so a kaiki gidan lallen kema a miki?"
"A'a ban taba yi ba ma a rayuwata, zan jira su ɗin kawai" mom tayi murmushi ta kama hannun Azima caraf idonta ya sauka akan zoben hannun Azima iri daya sak da na Aziza,kuma Aziza tace sadda aka haifesu kakansu Arɗo shi ya ba wa Hajjarsu ta saka mu shi a hannu, daurewa Mom tayi ta ce ya sunanki?
"AZIMA!"
"Ma sha Allah Azima suna mai dadi, Azima wa?"
"AZIMA BANJU!!" ba iyakar Mom ba harta Nawaz wanda yake kokonta sai da ya waigo a firgice, da kyar Mom ta iya riƙe kanta tana murmushin yaƙe ta rungumo Azima ta kaita dakin sultana sannan ta koma daki ta samu Almazeen na tambayar Nawaz meke damunsa, Mom Na shigowa Nawaz ya mike yana fadin
"Wlh ita ce mom, yar uwar Aziza ce, Allah Alhamdulillahi³!" Mom da Nawaz suke faɗi, Al'mazeen da kansa ya shiga duhu yace
"Dan Allah Mom ku min bayani ku fiddani a duhu, dama Aziza tana da yar uwa ne?" mom tace
"Dole zamu maka bayani amma kafin nan a ina kasan Azima ina ka sameta?" bai boye musu ba aiki takeyi agidansa a cam ma ya sameta dan tun bayanan su Maman Hanan suka gaya masa an dauke sabuwar mai aiki, har izuwa sadda ya dawo da shakuwar da ta shiga tsakaninsu.
"ALLAH KENAN MAI YIN YADDA YA SO, HAKURINKA BAYA FADI KASA BANZA! ALLAH YA TAKAITA MANA WAHALA" cewar Mom tana jinjina kai, zama sukayi nan Mom ta hau warwarewa Al'mazeen komai bata kara ba bata rage ba, Al'mazeen ya zare ido yace
"Kenan mom *AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE? SANNAN YAN BIYU NE?* mom ta gya ɗa kai,
"Kenan Azima ba Azima bace Banju ne?" mom ta ƙara jinjina kai
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" mom ta kara da cewa
"Wannan shine dalilin da yasa auren Nawaz da Aziza ya tashi babu shiri dan yin jahadi ya taimaki Aziza" jinjina kai Al'mazeen yayi ya ce
"Idan har Aminina zaiyi wannan aikin ladan ba tare da ya faɗa soyayya ba ina ga ni da na fara son Azima? Sannan ta taimakeni da badin sanadinta ba da yanzu b'arayi sun kasheni!" nan ya bai wa mom labari mom ta hau salati tana sanar da ubangiji, sannan ya kara da cewa
"Ta taimakeni! Ta ceci rayuwata yayinda ta saka nata a hatsari! mom ina son Azima! Ina so kuma jibi nima a ɗaura min aure da ita amma karta sani, kamar yadda Banju shaiɗanin aljani ne zai iya kashemu idan har yasan da hakan, sannan ya kamata a gayawa Aziza kar ta dawo gidan nan dan karsu haɗu da Azima har sai bayan an daura aure" Mom tace
"Hakan ma wata shawara ce mai kyau,idan yaso aka daura auren da washe gari ranar sai mu shirya tafiya yola,ko kuma da an daura kawai mu wuce tinda Aziza tace cikin daci suke, sai ku shirya mota mai ƙarƙo da zai iya kaimu zamu tafi da Malam Yunusa da ƙanin mahaifinku da kuma Hajiya Lawiza ko kuma Hajiya luba"
"E hakan ma yayi mom" cewar nawaz, na suka gama tsara abunda zasuyi.
An gama yiwa Aziza lalle tana zaune,ita kuwa Sultana ana wanke mata nata, gajiya da zaman Aziza tayi ta ɗan jinginu tana lumshe ido, tana lumshe ido wa zata gani? Azima ta hanga wani ajiyar zuciya ta sauke da jan numfashi ta buɗe ido tace
" *AZIMAA!?"* sultana tace
"Azima kuma? Ina kika ganta?"
"Wlh na ganta Anty Sulty ina rintse ido na ganta,ina zuwa bari na sake dubawa" rintse ido tayi ta shafo tafin hannunta nan ta hangi Azima kwance a gadon sultana, a hankali ta buɗe ido tace
"Azima a gida kuma a dakinki a gadonki?" sultana zatayi magana wayarta ya yi kara, tana dubawa ta ga mom saurin dauka tayi tasa a kunne tayi sallama mom tace saurareni da kyau Sultana" nan mom tayiwa sultana bayanin komai sannan tace
Idan sun gama su biya gidan kawarta Hajiya Biba su ajiye Aziza sannan su su dawo, yanzu sultana ki yiwa Aziza bayanin komai yadda na miki, mom na gama fadi ta ajiye waya,sultana ido bude ta kai bakinta saitin kunnen Aziza tayi mata bayani dalla-dalla,itama Azizan ido a waje ta kalli Sultana, sultana ta jinjina mata kai.
Basu gama ba sai gaf magriba dan haka ko da suka tashi suka biya suka ajiye Aziza a gidan Hajiya Biba su kuma suka wuce gida.
Ko da suka isa Sultana bata nunawa Azima komai ba tayi maraba da ita ta hau janta a jiki.
Nan sanarwan aure ya koma na mutum uku.
Da washe gari walima Mom ta ba wa Azima haɗaddiyar dogon riga wanda yasha stone, a jiya ne ma da dare tasa aka nemo mata kasancewar ba ayi shiri da ita ba, bata tayi ta saka Azima ta karba ta mata godiya, kasancewar a gidan za ayi walimar a tare kusa da juna Mom ta zaunar da sultana da Azima,itama Aziza ana can anayin nata a gidan kawar mom, sadda aka fara wa'azi dodon kunnenta kamar zai tarwatse ji take har fatarta ƙuna yakeyi dan da karfi Malama Rasheedat Hassan Usman ke fadin Allah yace Annabi Yace.
Duk wanda yazo ya tambaya wannan itace amaryan Nawaz din sai mom tace a'a ta Al'mazeen ce, lokacin dasu Maman Hanan suka iso kamar su mutu da bakin ciki dan tun a jiya labari ya iskesu nan suka dinga tsinewa Almazeen da Azima, har suna cewa dama ya sane ya ƙi fada musu zaiyi aure.
Anyi walima lafiya aka watse lafiya.
Da washe gari karfe sha ɗaya za a daura aure kasancewar su Nawaz zasu kama hanyar yola ne da an daura aure.
Tun wayewar gari Azima ta kasa zama ta kasa tsayuwa ta rasa dalili, a gidan Hajiya Biba kuwa itama Aziza ta matsu suyi ido huɗu da Azima.
Ma sha Allah sha ɗaya nayi dai-dai aka shaida daurin auren Khalil Alhaji Yaro da Amaryarsa Sultana Alhaji Sardauna, sai kuma na NAWAZ ALHAJI SARDAUNA DA AMARYARSA AZIZA MAGAJI BAWA, SANNAN AKA DAURA NA AL'MAZEEN ALHAJI SAHABI DA AMARYARSA AZIMA MAGAJI BAWA! ana daura aure Azima na zaune a daki da su Sultana da kawayen sultana nan ta riƙe kirjinta ta hau tari, ana gama daura aure Nawaz da Al'mazeen da wasu abokai sukayi gidan Hajiya Biba dan dauko Aziza, da lullubi aka fito da ita kanta na juyawa kasancewar mahaɗi daya suke da Azima wacce take mayuwacin hali a gida su Sultana sun rufo a kanta.
Da kyar Aziza ke fizgar numfashi ta gaida su Al'mazeen suka amsa ,hankalin Nawaz na kanta yana lura da halin da take ciki.
Suna isowa gida guɗa ya hau tashi ana ga angwaye ga angwaye, Mom tace su hauro sama, Aziza ta taka step jiri ya kwasheta zata fadi da sauri Nawaz ya tallabota nan jama'a aka sa ihu ana musu tafi, shi dai matarsa kawai ya kama suka hau sama, hannun kofar Aziza ta murɗa fuskarta a murtuke, tana tura kofar a lokacin Azima na duƙe sultana na bubbuga bayanta.
"AZIMA!" Aziza ta kira sunanta murya a daskare, wani wawan dagowa Azima tayi caraf idonta ya sauka cikin na Aziza wacce Nawaz ke rike da kafaɗunta.
🍃🍃🍃🍃
MOMYN AHLAN✍🏻
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
*WA INDA BASU BIYA BA SUN BIBIYI PAGES BA, CMLPT DCMNT #300 NE, NOR #100.*
*PAID.*
🅿️=6️⃣7️⃣↪️6️⃣8️⃣
Murtuƙe fuska Banju ya yi ya ce
"Magaji! ba dawowa nayi ba"
"Na sani Banju! ba dawowa kayi ba,jarumar 'yata ce ta dawo da kai"
"Kaii Magaji! Kunceni! Idan ba haka ba yankin kwana ta koma toka! Dan kasan wanene Banju! Bana da imani! Kasan karonmu da kai!" murmushi Baffa yayi yace
"Amma ni Magaji Bawa! ban gudu ba hakane Banju?" haɗe rai Banju yayi baffa ya ci gaba da fadin
"A yanzu ko Magajiyata Aziza tsaf zan iya sakata kasheka! amma halin da ka sakani yasa nake son kasheka da hannuna! ka fara ƙirga numfashinka daga yanzu zuwa gobe" dariya Banju ya yi yace
"Ashe kuwa idan zaka kasheni zaka haɗa da 'yarka, karka manta gangar jiki daya muke da ita" Baffa shima murmushi ya yi ya ce
"Duk makahon da kaji yace ayi wasan jifa yasan ya taka dutse bare mai ido kuma kai ma kasan bakin rijiya ba wajan wasan makaho bane, a wannan tafiyar kaine makahon inaji ka manta da cewa yanzu haka Azima na da aure ko? mijinta shine zai fiddaka daga jikinta ni kuma na kawo karshenka ta yadda ba zaka kuma dawowa ba, kisan farko da na kasheka ban so ba, amma a yanzu ne zan kau da ka" wani ihu Banju ya yi yana son tsincewa, Baffa yace
"Aziza!" juyowa tayi ta kalli Baffa, Baffa ya mata alama da ido, ta gya ɗa masa kai sannan tayi gaban Banju tana shirin sake kafar da shi, da karfi ya furta mata "BAHULAAAAA!!" a kunne yana son tada Bahula dake jikin Aziza, wani ja da baya Aziza tayi ta dafe saitin zuciyarta da kanta, ganin haka yasa Baffa jan Aziza da sauri ya watsa mata wani farin hoda nan Aziza ta sulale zata faɗi Nawaz bai yi kasa a guiwa ba ya tare matarsa, da yatsa daya Baffa ya do ki goshin Banju, kamar anyi ruwa an dauke haka Banju ya tsaya cak, Mom cikin tashin hankali ta kama hannun Aziza wacce take kwance a jikin Nawaz ta ce
"Dan Allah Baban Aziza kayi wani abu, Aziza ta sha wuya wlh! Duk wani masifa kanta yake afkawa dan Allah tunda ga Azima a cire mata Banju ko Aziza ta huta, me yasa baka kashesa yanzu ba?" cikin kunya Baffa yace sabida har yanzu yana jikin Azima, idan na kashe Banju a yanzu Azima ma ta tafi!" nan Mom ta gane abunda Baffa ke nufi, ta kalli Hajja wacce ke tsaye a gefe tayi lullubi tana duƙe da kai, Mom ta ce
"Nawaz shiga da Aziza cikin gida, Maman Aziza? Dan Allah ki daina ɗaurewa kina wannan kunyar taki, ki saki jiki ki rungumi yarki, an wuce wannan zamanin kunyar, yarki ce fa? Karki cutar da kanki kina son jin dumin yarki amma ki ta rabewa, dan Allah bana son haka, ai gwara ki ja ta a jiki kafin na dauketa" rasssss!! gaban Hajja ya faɗi jin mom tace zata dauke Aziza, amma bata iya furta ko da uhum bane tabi bayan Nawaz da ya shige da Aziza, mom ta ce
"Baban Aziza zamu yi magana" Baffa ya ce
"To madalla bismillah" gefe suka koma suka kebe, mom ta ce
"A ba wa Almazeen matarsa yau suyi mu'amala ta aure dan a kawo karshen wannan masifan, karka ce zaka biyewa kunya, wajan ceton rai babu zan can kunya, a nema masa inda za a kai masa matarsa, a gobe ka kashe Banju,idan kuma hakan ba zai yu ba to a bamu su mu koma birni idan yaso komai ya daidaita a can Banjun ya fita sai a kashesa a can birni sai mu tafi tare da ku, amma ya ka ce?"girgiza kai Baffa ya yi cikin sauri ya ce
"Maganar a bar yankin nan a shiga gari akwai matsala, ba zan boye miki ba, Almazeenu zai fuskanci kalubale wajan kusantar Azima, Banju ya wuce duk tunaninki , kuma bayan ya kusanceta zaiyi ciwo, ba lallai bane ku a cikin gari kuna da maganguna irin tamu ta gargajiya, ga misali a kan Aziza haka tayi ta faman ciwo sai da ku ka zo kafin ta samu furen huriri ta warke, a nan aka fara yaƙin a nan kuma nake so a ƙarasata,bana so a kai muku masifa kuna zaman lafiya, burin Banju kenan ya sake barin yankin nan,ni kuwa ba zan bar haka ta faru ba ta yardan Allah, dazu bayan munyi sallar asuba maganar da Baffa Mandi da Arɗo suka min kenan a ba wa Almazeenu Azima yau, akwai wani gida da Arɗo yasa aka zagaye a can kusa da wajan gari, amma akwai tsirarakun fulani a wajan kawai dai gidan ne shi daya, yanzu haka zamu tafi da shi Almazeenu din, kafin nan zan ba shi wasu magunguna da rubutu su sha shi da Nawazu din, dan shi ma yana da bukatar haka tunda miji ne ga Aziza" Mom ta ce
"To ba damuwa hakan ma yayi Allah ya iya mana" Baffa ya amsa da amin, mom ta kira Nawaz da Almazeen tace musu su bi Baffa, Malam Yunusa kuma da kanin mahaifinsu Nawaz Alhaji Karami suna tare dasu sarki chubado da mai unguwa ori sai hira sukeyi ana shan damemmen fura da nono, gwanin sha'awa.
@@@@@
Gidan suka je, duk da gidan kara ne amma yadda aka shirya gidan ya burge Almazeen, tarko Baffa ya saka a ciki da waje ta yadda ko Banju ya fice a jikin Azima ba iya guduwa zaiyi ba.
Sannan Baffa ya ba wa su Almazeen da Nawaz wasu maganguna da rubutu yace su sha, ya basu na kariya da na sha da na wanka da na gogawa dana murzawa dana ɗorawa duka babu wanda bai basu ba, daga nan sukayi wani gida gaba kaɗan da na inda aka ba wa Almazeen, Baffa yace
"Nawazu, kai ma a nan zaka zauna ka riƙe Aziza, dan a lokacin da abun da ke jikinta zai fita zata iya shiga wani hali, zata iya fita hayyacinta, idan kuma ta subuce zamu iya rasata na har abada dan babu abunda Banju ba zai yi ba" Nawaz yace
"In sha Allah hakan ma ba zata faru ba Baffa, hakuri da gaskiya sune a sama, zamuyi nasara a kan Banju bi'izinillahi ta'ala!" Baffa ya yi murmushi na jin dadin samun sirkai kamarsu Nawaz da Almazeen, haka shi ma wannan gidan ma ya saka matakan tsaro.
Wunin ranar kuwa Baffa bai zauna ba shiri yayi sosai ya koma asalin Garkuwa Magaji Bawansa kyakkyawa fari dogon bafulatani mai dogon hanci da halin girma da cikar zati da haiba.
Da daddare mom ita ce tayiwa Azima da Aziza komai,ita da Maman Beenah suka raka Azima da Aziza, Almazeen wani irin kunya yakeji, hajja kuwa ta kasa fitowa a bukka tana zaune tana tasbihi ga Allah, tana roƙon mai duka da ya fidda mata yaranta lafiya, hakika ita kam ta ga jarabta.
Bayan an mikawa Almazeen Azima wacce take da ita da babu za a iya cewa duk daya, sannan aka wuce aka kai wa Nawaz Aziza duk da shi ba wani abu bane zai wakana a tsakaninsu.
Ko da su Mom suka koma itama ba kwanciya tayi ba, alwala tayi ta zauna ta fuskanci gabas, Maman Beenah kuwa gadon kara ta haye tayi kwanciyarta dan tace bacci takeji.
Baffa ma uban gayya bai ga ta zama ba balle ya rintsa dan kuwa a tsaye yake kyam.
💕💞💕💞💕
*AL-MAZEEEN DA BANJU AZIMA.*
A bukka kuwa Almazeen zama ya yi ya kurawa Azima ido yana kallonta, shi bai ma san ta ina zai fara ba, ya kwashi kusan mintuna talatin yana kallonta daga bisani ya tashi ya ɗauro alwala ya yi sallah raka'a biyu, ya ciro wayarsa ya yi karatun alkur'ani mai girma ya daga hannunsa sama yana adduoi sannan ya shafa ya miƙe a hankali ya fara rage kayan jikinsa, wani magani da Baffa ya basa yace ya shafa a jikinsa idan zai taba Azima, maganin ya shafa a hannunsa da dukkkan jikinsa, yana tabata sai da ta girgiza,kwantar da ita yayi, Banju dake jikinta yana kallon abunda ke faruwa ɗauresa kawai Baffa yayi, wani gurnani ya fara nan ya hau buge-buge, Almazeen da iyakacin karfinsa ya fizgi kayan dake jikin Azima, nan dambe ya kacame duk da banju yana daure amma ba shi ya hanasa kokarin yunkurin kashe Almazeen ba shima Almazeen yaci albarkacin daure Banju da Baffa yayi amma duk da haka yanaji a jikinsa, duk kalman da yazo bakin almazeen indai na salati ne yin shi yake yi
,Banju bai gama sarewa ba sai da ya ga Almazeen ya yiwa Azima kaff da kayan jikinta, yunkurin komawa maciji Banju yayi amma kafin ya fara hakan tuni Almazeen ya karanto adduar saduwa ya fara kokarin shiga jikin Azima, wani sarawa kansa yayi tare da wani wawan jiri dake shirin watsa shi waje daurewa yayi ya riƙe kokaran gadon karan gam jikinsa na kyarma, nan Azima ta fara canzawa tana zama wata halitta daban mai matukar ban tsoro da firgitarwa, kokarin zare jikinsa yayi dan dama bai shigeta sosai ba, tunowa da maganar Baffa na cewa kar ya kuskura ya kyale Azima har sai ta yi attisha sau uku dan duk hanyar da Banju zai bi dan ya ga ya hana Almazeen kusantar Azima zaiyi, daga karshe kuma zai kashesa ya kuma guduwa, tunowa da haka yasa Almazeen ya dage da iyakacin karfinsa sakamakon b'ari da jikinsa ke yi ya shige Azima gabadaya, wani ihuu Azima ta saka da karfi wanda sai da ya karaɗe gefe da kewayen inda suke, ta shaƙo wuyan Almazeen wanda shi kadai yasan abunda yakeji kamar ana zare ransa haka yakeji tsananin azaba dan harta fatarsa ji yakeyi kamar ana soya masa shi, sake damƙar kafaɗun Almazeen Azima tayi ta dage ta saki wani attishawa mai karfin gaske dan kuwa an karya makarin Banju tunda Almazeen ya afka cikinta, tana yin attishawa na ɗaya tayi na biyu, na ukun ne nan wani guɗa ya hau tashi, tana attishawar Banju wanda ya yi tsalle ya fice ta baki da hancin Azima, ƙauuuuu! Azima taji yayinda ta wani firgita tana jan wani numfashi da iskar duniya,da nauyin kai ta hau ware ido da kyar jin idon kamar an liƙe mata su, tana ji tamkar yau ne uwarta ta haifeta, tana gama buɗe ido mutum ta hanga a saman kanta, Almazeen wanda yake gaff da sumewa yana ganin ta bude ido a hankali ya sauke bakinsa saitin kunnenta cikin mayuwacin hali da kyar ya furta
"Alhamdulillah! Wlcm back my dear wife, am so happy, u are back! i promise that i wouldn't let any harm attack u, i will sacrifice my life to u, cox I luv u, am really luv u, i fell in luv with u Azima! pls don't leave me alone" Almazeen na faɗi ya hau kokarin zare jikinsa daga na Azima, a lokacin Azima taji wani mugun raɗaɗi ta kasanta hakan ne yasa taja wani numfashin mai cike da azaba, a tare suka suma.
Banju dake tsaye yana
kallon Almazeen wanda yake son kashesa dan ya lashi takwabin sai ya kashe Almazeen, amma inaaa ya kasa kusantar almazeen balle ya kashesa kasancewar Almzeen mutum ne mai riƙo da ibada baya sanya.
💕💞💕💞
*NAWAZ DA AZIZA.*
Sadda aka raka Aziza tsayuwa tayi a bakin bukkar taki karasowa, Nawaz na zaune yana danna wayarsa da tun shigowarsu garin babu network ko ɗigo, ɗaga ido ya yi ya kalleta ya ga jikinta sai rawa yakeyi, da alama tsorata tayi, a hankali ya tashi yaje gabanta bata ma sani ba tayi zurfi a tunani, ji tayi an kama hannunta, a firgice ta dago idonta ya haɗe da na Nawaz, ganin duk ta taburce yasa Nawaz rausaya kai yace
"Ya haka? Jaruma a waje, matsoraciya a gabana?" ya faɗa yana matsota sosai, ja da baya tayi tana shirin ficewa yasa hannu ya jata ta shige jikinsa,
"Haba jaruma, karki bani kunya mana" mutsu-mutsu ta hau yi tana son kwace jikinta, yasa hannunsa duka biyu ya kewayeta ta kasa kwacewa ya ce
"Ko za a watsar dani ne?" nan ma bata masa magana ba, ya ce
"Idan baki min magana ba, zan cinye bakinki" mamaki ne ya kama Aziza, oh dama haka Nawaz yake? take tambayar kanta, bata gama yankewa ba sai da taji ya dauketa ya ajiyeta a saman gadon kara yana shirin kwanciya a kanta tayi saurin miƙewa zunbur tana fadin
"Sorry Hamma" murmushi ya yi a boye, ya ce
"To matso kusa dani, kin san Baffa yace na rikeki da kyau dan haka matso" ya faɗa yana ware mata hannu alaman ta shigo cikin jikinsa, ganin yadda ya sauya fuska ba alaman wasa yasa ta matso a hankali ta shige jikinsa ta kifa kanta a ƙirjinsa, yasa hannu ya rungumeta da kyau yana son fassara me zuciyarsa takeji game da Aziza.
A lokacin da Almazeen suka fara dambatuwa da Banju, a lokacin Aziza na kwance a jikin Nawaz, lokaci daya kamar an zabureta haka ta miƙe, cikin hanzari Nawaz ya fizgota ya maidata jikinsa ya matseta dan ya tuno da maganar Baffa da yake cewa idan Aziza ta subuce za a iya rasata shiyasa ya kara matseta sosai a jikinsa, ihu Aziza ta saka jin fatar jikinta na sabulewa, saurin ture Nawaz tayi ta koma gefe tana ƙanƙame jikinta, fuskarta ne ta ji yana b'anb'arewa, hannu biyu tasa tana tare fuskarta tare da ihu, ganin halin da take ciki yasa Nawaz saurin tashi zai zo gareta, nan yabga masifa, daga ƙugunta abunda ya yi sama ta zama macijiya fara sol sai kyalli take yi, sak irin wanda yake gani a mafarkinsa, hannu ta miƙa masa cikin azaba tana fadin
"Help me plss! ka taimakeni Hamma Nawaz!" ta faɗa siffar jikinta na ƙasa na haurawa zata zama macijiyar gabadaya, da saurin Nawaz ya rintse ido yaje ya rungumeta ƙaƙam! Yana rungumarta ta tsaya a haka, a lokacin da Banju zai fita a jikin Azima itama Aziza taci azaba dan nan suka hau gwada karfi da Nawaz, hakika shima ya jikata, dan kuwa sadda abun zai fita gani ya yi wani farin abu shi ba dutse ba shi ba tsuntsu ba ya fice ta goshin Aziza, yana fita numfashinta ya tsaya cak yayinda ta koma mutum, haka Nawaz ya zauna riƙe da ita a jikinsa, gab'ob'insa na masa ciwo sosai, har asuba.
💞💞💞💞💞
Sanyin asuba ne ya fara farkar da Almazeen wanda da kyar yake iya buɗe ido sabida nauyin da suka masa, ya jima a haka kafin da layi ya tashi ya janyo kayansa ya saka, ya rufawa Azima jikinta, ya koma ya kwanta a gefenta yana sauke huci mai zafi.
Baffa suna idar da sallar asuba Arɗo yace su je a duba yaran nan.
Mom aka kira dan da ita za aje Hajja ta ƙi fitowa ƙememe.
Suna zuwa gidan Hajja zata shiga da saurin Baffa ya dakatar da ita ya hanata shiga, yace tana shiga Banju zai iya kasheta dan shi yanzu duk wanda ya samu zai kashe ne" Baffa ne ya fara shiga cike da yarda da kansa sabida ya yi imani da Allah ya yi riƙo da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam,duk wanda ya yi riƙo dasu baya da fargaba a kan kowa, yana shiga kuwa Banju dake neman hanyar guduwa a gidan tun daren jiya ya kasa sabida Baffa ya ɗaure ko ina da ina, suna ido huɗu Baffa ya daga takwabi, Banju yace
"Magaji a gwabza idan ba tsoro! karka kasheni sai mun gwabza!" Baffa ya yi murmushi yace idan ka so haka"
"Zan so! amma ka ajiye takwabi" Baffa ya ce
"Ba daga yanzu zamu fara ba, kafin nan ga wannan" Baffa na faɗi ya wurgawa Banju wani igiya nan ya daure Banju ya fito da shi, yana fitowa da shi ita kam mom bata iya daga ido ta kalli Banju ba, dan tace mugun ji da mugun gani Allah ya rabamu dasu, Baffa na cewa zata iya shiga da sauri ta wuce shi kuma ya wuce da Banju, mom na shiga ta samesu a yashe, Azima ta jijjiga sannan ta taba Almazeen wanda jikinsa ke rawa alaman ciwo jikinsa zafi raɗauu kamar wuta, na Azima ma akwai zafi amma na Almazeen ya fi nata, babu wani taimako da zata iya masa, amma zata iya taimakawa Azima, dan haka ta fito ta haɗa ƙirare ta tafasa ruwan zafi, kafin ruwan ya gama sai ga jikan Ardo Sanda ya kawo wasu magunguna yace Baffa yace idan su Hamma Almazeen da Azima zasuyi wanka a zuba musu shi a ruwan wankan suyi wanka da shi, wannan kuma su sha, sannan a ba wa Hamma Mazeen wannan,wannan kuma a ba wa Azima" mom ta karba tana masa sannunsa da aika.
Mom da kanta ta taimakawa Azima tanuna mata yadda zatayi wankan tsarki, sannan tayiwa mata wanka haka,ita dai Azima wani iri take jin kanta, riƙota mom tayi suka shiga bukkar har yanzu Almazeen ya kasa motsi koda da yatsarsa daya ne, taimakawa Almazeen mom tayo shima ya yi wanka ya yi sallah a zaune ya sha magungunan da Baffa ya bada a ba shi daga nan ya hau bacci,itama Azima maganin ta sha ta hau bacci, haka ma Aziza wanda aka aika aka ba wa Nawaz yasha ita ma ya bata ta sha duk suka buge suka hau bacci.
Can wajan dandalin yanki Baffa yaje ya daure Banju, ko kaɗan Banju baida kyawun halitta gani, ga girma katam da shi tamkar basamude ga baƙi fiye da misali, kai babu ta yadda za a sunfanta zubin halittan Banju.
Bayan Baffa ya daure Banju yasa maga isar da sakon yankin kwana a kan ya rubuta wasika yayi aike sauran yankuna ana gayyatar su izuwa kallon fafatawa a tsakanin aljani Banju da Baffa bisa umarnin gayyatar sarkin yankin kwana wato sarki chubaɗo, kamar irinsu yankin ja'i da yankin tudu da yankin ja'o da yankin gangare, da yankin shani, da dai sauran yankuna.
Sadda wasika ta iskesu sun sha mamaki, kai wannan ai babban fafatawa ne a tsakanin Magaji bawa da Maciji Banju, wanda ya yi b'arna da ta'adi a yankin kwana, wanda ya kashe shahararrun masu kama macizai irinsu jarman macizai dasu Innu maciji, da iro mai maganin macizai da dai sauransu, hakika duk yankuna sun amince zasu zo ganin wannan fafatawar tsakanin mutum da aljan,duk da wannan ba sabon abu bane a wajan Garkuwan Kwana Magaji Bawa Arɗo.
Mom ce ta cewa Baffa dan Allah ya taimaka ya raba Aziza da Bahula ta koma asalin cikakkiyar mutun ɗinta ta huta gaba daya, Baffa ya yi murmushi ya ce wannan ba wata matsala ba ce, suka je gidan har zuwa yanzu suna bacci, goshin Aziza Baffa ya riƙe ya rintse ido, attishawa Aziza tayi sannan ta fara hamma, wani farin abu ne ya fito ta bakinta, a hankali farin abun ya koma kamar farin hayaki haka, daga nan abun ya zama mutum wanda ake mata kallon dishi-dishi, Baffa ne kawai yake iya ganinta dan kuwa mom ba ganinta take yi ba, kallon Baffa Bahula tayi tana girgiza kai hawaye na zuba a idonta dan tasan Baffa kashe mata Yayanta Banju zaiyi dan tasan ko a wasa Yayanta Banju ba zai haɗa karfinsa da kwatan karfin da Magaji ke da shi ba,kawai dai a mugunta ne baya da lamba ta biyu, dukar da kai Baffa yayi, daga haka Bahula ta b'ace, muryan mom Baffa yaji tana magana
"Baban Aziza? Yanzu shikenan sun warke babu wata matsala ko?"
"In sha Allahu, sun warke, amma wanda ba yanzu zaiji sauki ba wanda shi ba mu san a ya zai farka ba shine Almazeenu, amma harta Azima zata farka lafiya lau,kuma idan ta farka za a gaya mata gaskiyar abunda ya faru kar a boye mata duk da abun da suka faru zata iya gani duk da ta kasance a sume amma zata iya gani kamar mutum mai bacci yana mafarki sabida sun rayu a jiki daya da Banju,jikin ma kuma nata ne, zata tuna komai kuma zata gane komai shiyasa za a gaya mata sabida rashim gaya mata zai iya haifar mata da wani matsala, mom ta gya ɗa kai tana mai tausayawa Almazeen.
🍃🍃🍃🍃
Basu suka farka ba sai lokacin sallar azahar, wani ɗauuuu!! Aziza taji a kunnenta da ta farka, zata fadi da saurin Nawaz ya riƙeta, wanda shima yanzu baya jin komai ciwon jikin nasa ya tafi
"Kina lafiya?" Aziza ta gya ɗa kai tana gyara tsayuwarta, zuwa can ta ce
"Azima? yar uwata?" ta faɗa zata fice da sauri Nawaz ya rikota yace suyi sallah kafin su tafi, sallan kuwa suka gabatar shi ya jasu sannan suka fita sukayi gidan da Almzeen da Azima suke, mom ma tana gidan tana kula da Almazeen wanda a zaune ma ya ƙara gabatar da sallah, Azima kuwa tunda ta farka har tayi sallah karo na farko a rayuwarta, bata furta ko da uffan bane kallo kawai take bin mutane da shi abubuwa suna dawo mata kamar a mafarki haka take tariyowa, tana zaune a kan sallayar kaba su Nawaz da Aziza suka shigo da sallama, Aziza tana ganin Azima a kan sallaya tasa kukan farinciki tana fadin
"Azima?" daidai lokacin su Inna wuro da su Yawuro har ma da Hajja dasu Baffa suka shigo, juyowa Azima tayi tana binsu da kallo, ganin Aziza yasa ta ce
"Aziza?" wani kuka Aziza tasa ta ƙaraso da sauri suka rungume juna ƙaƙam
"Me ya faru Aziza?" Azima ta tambaya cikin sheshsheƙar kuka
" zan gaya miki" cewar Arɗo, nan ya hau yiwa Azima bayani dalla-dalla tun fara kisa da yaƙi da komai da barin yankin kwana har izuwa yanzu, wani kwalalo idanu waje Azima tayi ta hau girgiza kai tana fadin
"Ni....ni....ni....ban.....ban....ban...kashe....kowa....ba.....Baffa.......bana....da niyyar kasheka...Hajja ban miki rashin kunya ba.....Aziza...banyi faɗa dake ba.....dan Allah kuyi hakuri..... Ban kashe kowa....ba..." duk Azima ta bi ta ruɗe mom ta jata a jiki ta ringume tace
"Mun sani Azima,mun san cewa jinin Magaji da Jamila ba zata aikata hakan ba, kwantar da hankalinki, ba ki kashe kowa ba,mugun nan azzalumin aljani Banju shine ya kashe" ɗago daga jikin mom tayi tana kan ci gaba da kuka, duk da zafi da ciwo da ƙasanta ke mata ba shi ya hanata tashi da gudu ta shige jikin hajja da kuka ba, itama Hajja kukan takeyi, dagowa tayi ta kalli Baffa ta hau girgiza kai da hannu tana fadin.
🍃🍃🍃🍃
GARKUWAN MACIZAI🐍
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
*PAID.*
🅿️=6️⃣5️⃣↪️6️⃣6️⃣
"Aziza?" Azima ta kira sunanta itama murya a sarƙaƙe, Nawaz ne yace kawayen Sultana su fita, da sauri kuwa suka fice,suna fita Al'mazeen ya sawa kofar key, wani kallo Azima ke bin Aziza da shi har ma dasu Mom, Mom ce ta tunkari Azima tana shirin yi mata magana da sauri Aziza ta ce
"A'a Mom!" tsayawa cak mom tayi, Aziza ta mata ido a kan taja baya, Al'mazeen ne ya matso kusa da ita ya ce
"Azima zan iya ce miki wani abu?" shuru Azima tayi kirjinta na bugawa,
"Azima Ina sonki! Kuma na au...." maganar da Al'mazeen bai karasa ba kenan Azima ta saki ihu tana toshe kunne, matsowa kusa da ita Aziza tayi ta duƙa a gabanta tace
"Azima? Ohh ina nufin Banju! Ka sa kunne da kyau, yanzu haka yola zamu tafi, yau sai yankin kwana In sha Allahu! zaku haɗe da Baffana! dama kasan karonku dashi ba dadi" wani dariya Azima ta hauyi marar dadin sauti tace
"Ke a tunaninki zan yarda na koma ne?"
"To taya zaka iya guduwa? Albishirinka! Yanzu haka da aure a kan Azima!" wani zaro ido Banju ya yi yana fadin
Sun ci amanarsa sai ya kashe miji waye mijin, Al'mazeen ya amsa da cewa
"Ni ne mijin!" wani kururuwa Azima ta saka ta miƙe da karfinta da niyyar zama macijiya dan ta saresu da sauri Aziza tasa hannu da wani farin haske ta tokari goshin Azima nan tayi ɗiff!.
"Na kafar da ita zamu iya tafiya" Aziza ta faɗa jiri take ji amma ta rasa yadda zata yi, Mom tace
"Nawaz Al'mazeen ku kama matayenku ku saka su a mota, bari na yiwa Umma magana (Umma yaya ce ga Mom wanda itace zata tsaya a karasa biki a kai sultana dakinta) har zasu fita sultana ta fashe da kuka tace
"Aziza! Za ki dawo? Kiyi min alkawari zaki dawo?" itama Azizan kuka tasa suka rungumi juna, Nawaz zai ja Aziza mom ta daga masa hannu alamun ya barsu, dagowa Aziza tayi tace
"Ban san me zance miki ba Antyna...."
"Shiiiii! Yanzu kece Antyna tunda da auren Yayana a kanki" murmushi Aziza tayi hawaye na zuba a idonta tace
"Ba a canzawa tuwo suna, ke ɗin antyna ce wacce nake ji da ita sosai, da fari zan fara neman gafararki! aurenki guda amma ta sanadina da yar uwata ba a miki shi yadda ya kamata ba, kiyi hakuri ki yafe mana, ga shi zamu kara tafiya da mom,mu kuwa me zamu ce muku? Sai dai mu muku fatan Allah ya muku sutura ranar lahira, dan kuwa kunyi mana a duniya"
Sake rungumeta Sultana tayi ta ce
"Ni kam alhamdulillah! Naji dadin aurena,dan kuwa an daura tare da Yayuna, sannan karki damu da batun tafiya da Mom, Umma tamkar mom take har ma taso tafi mom, lafiya za a kaini gidana,ni dai fatana dan Allah kiyi hakuri ki dawo a kan lokaci,kinji?" share hawaye Aziza tayi ba tare da tayi magana ba dan bata sa a ranta zata dawo ba, Nawaz ne ya kama hannun Aziza ya jata ya rabasu da sultana suna kuka suna komai, mom ce ta rufe musu fuska kowa ya kama matarsa a haka suka sauko jama'a sai guɗa ke tashi, da manyan motoci biyu zasu tafi wanda zai juri wahala da afkawa jeji mai gudu, mom da Hajiya Luba Maman Beenah kenan ba dan taso ba haka aka sa ta shiga mota,Maman Hanan kuwa cewa tayi wlh ba zata je ba, da kanin mahaifinsu Nawaz Alhaji Karami da Malam Yunusa abokin Mahaifin su Nawaz.
Al'mazeen da Azima suna zaune a bayan mota Nawaz da Aziza suna zaune a gaba,mota daya suke su hudu Nawaz ke driving, Azima tamkar gunki haka ta koma, lokaci zuwa lokaci Al'mazeen zai waiga ya kalleta, sunyi nisa Al'mazeen yace
"Aziza? Hope dai Azima lafiya take?"
Gya ɗa kai Aziza tayi a sanyaye tace
"Lafiya take Hamma Mazeen, kawai na kafar mata da dafi ne idan ba haka ba sunanku gawa dan Banju zai kasheku! Ni ba zata iya kasheni ba, kuma kafin ace nayi kokarin yin wani abu dan dakatar da ita zata iya kashe ko da mutum daya ne ba zan so hakan ba, zamanta a haka shine mafi alkairi har mu isa" jinjina kai Almazeen yayi yana kara maida idonsa kan Azima.
Basu isa yola ba sai yamma lilis, dan haka Aziza tace ba zai yu su afka jeji ba su bari su sake yin asubanci gobe, dan haka suka kama hotel inda zasu kwana.
A gida kuwa karfe biyu Umma tayi oya-oya aka dauki amarya sultana aka kaita danƙareren gidanta da Khalil dinta ya gina aka ajiyeta, Umma ce tayi mata komai tamkar Mom tana nan, Umma ce ta wakilci mom a komai aka sallami baki da wasu daga cikin yan uwa.
Sadda aka ajiye sultana a gidanta za a watse a barta tasha kuka, duk hankalinta da adduarta Allah yasa Aziza ta dawo.
Kamar yadda suka ce da washe gari asubanci sukayi, sallar asuba kawai suka yi suka yanki cikin jeji inda zai sadasu da ƙauyen yankin kwana, Aziza ke nuna musu hanya, Nawaz ya kalleta yace
"Zamu iya isa a yau?" tace
"Hamma Nawaz yadda wannan mota ke gudu kamar a iska inaji nan da yamma zamu isa"
"Kai har yamma?" Nawaz ya tambaya a gajiye dan tsakani da Allah ya gaji, yadda ya zare ido ya ba wa Aziza dariya dan haka tayi murmushi, suna tafiya Nawaz ya cewa Mazeen ya musu video recording ɗin hanyar, Mazeen ya ciro waya ya hau musu video ɗin.
🍃🍃🍃🍃
Yau tinda Hajja ta farka gabanta ke faduwa, ga shi jiya tayi mafarkin Azima da Aziza sun dawo, duk da mafarkin ba sabon abu bane a wajanta.
Da yamma ligis wajan irinsu shidda haka Aziza ta shigo yankinta wani murna da annashuwa takeji, yayinda hawaye ya b'alle mata, hakika yanayin al'karyan ya tafi da zuciyar su Nawaz, gari kore shar dashi abun sha'awa ma sha Allah, ga korayen shuke-shuke da 'ya'yan itatuwa, yankin kwana sun ga abunda basu taba gani ba, dan tun farkon shigowar su Nawaz a idon Salti ɗan gidan jauro nan yaje ya baza a gari ya ga wasu sabbin masifa ya shigo musu gari, wasu bayyanannun aljanu,nan yara da manya aka hau bin motar har gaban kofar gidan Baffa, nan aka hau cewa a kofar gidan Magaji masifan ta tsaya, mota na tsayuwa da gudu Aziza ta fito, su ma su mom fitowa sukayi,yayinda Mazeen ya fito da Azima Banju, dasu mom suka rufawa Aziza baya, mutane an cika ana kallon su mom, ko sallama Aziza bata iya yi ba tana shiga ta tsaya turuss tana kallon mahaifiyarta wacce ta rame sosai ta karayin wani fari fal da ita, Hajja na duƙe ta dibi ruwa a kwarya zata zagaya kewaye, su Mom ne suka shigo suma, cikin wani irin kuka da shauki irinta 'ya wanda takeji a kan mahaifiyarta murya na rawa mai fizgar kuka Aziza ta ce
"Hajja!" kwass!! Hajja ta saki kwarya ta juyo da sauri, haba duk daren daɗewa muryar Azizanta ba zai goge a kunnuwanta ba, kallon Aziza Hajja ke yi jikinta na rawa tama kasa magana, da kyar Hajja ta ce
"Dan Allah Aziza yau karki b'ace ki barni, na yarda zan dinga zama da gizon naki dun Allah karki tafi" da gudu Aziza ta shige cikin hajja ta riƙeta gam-gam suna wani irin kuka mai ban tausayi, harta su Mom suma hawaye sukeyi, Malam Yunusa ya kalli Mom ya ce
"Hajiya Kamila(mom)Allah ya saka miki da mafificin alkairi, Nawaz da Al'mazeen Allah ya muku albarka" suka amsa da Amin.
Ɗago Aziza daga jikinta Hajja tayi tana shafa fuskarta, Aziza cikin dashashshiyar muryarta tace
"Hajja nine na dawo, mun dawo" Hajja na shirin magana sai ga Baffa wujigan a muraran, yana can garkin shanakunsa Salti yaje ya samesa yace ai ya ga bataliyan aljanu sun nufi gidansa yanzu haka aljanun suna gidansa, shiyasa Baffa yazo a hargitse, Baffa na shigowa da sauri Aziza ta zo ta ce
"Baffa ni ce Azizanka! Baffa na dawo, kace kar na dawo sai da Azima, Baffa gata nan ga Azima nan" duk irin kunya irinta fulani nan Baffa ya rungume Aziza yasa kuka, an jima ana koke-koke, Sarki Chubaɗo dasu mai unguwa ori dasu Garkuwan yankin kwana, kai duk jama'ar yankin kwana an taro agidan Baffa, sai bayan an gama kuka tukunna aka basu abun zama, Sarki Chubaɗo yace
"Kafin a zauna ya kamata mu fara sallar magriba, hakan kuwa akayi, Aziza ta basu ruwa sukayi Alwala suka nufi masallaci.
A cikin gida ma Hajja ce ta ba wa Mom da Maman Beenah ruwan alwala, taki yarda ta daga kai ta kallesu sabida kunya irinta fulani, Maman Beenah kuwa ba bakinciki kauyen ya mata kyau ya burgeta.
Bayan sun idar da sallar, Hajja na zaune kusa da yaranta nan suka hau gaisawa dasu mom,mom ta kalli Hajja tayi murmushi ta ce
"Kyawu! Kyawun hali! Kunya! Natsuwa! Ashe duk ba a banza Aziza ta dauko ba, ta biyo Mahaifiyarta ne, dadtako halin girma! Jarumta a fuska da kuma jiki ta biyo halin mahaifinta ne! Ina tayaku murna da samun 'ya kamar Aziza" Al'mazeen da suke shigowa cikin gidan yace
"Kai mom,Aziman fa?"
"Har da itama mana"
"To kishi kakeyi dan an yabi Aziza?" cewar Nawaz yana hararan Mazeen, murmushi su Arɗo sukayi sannan aka zauna aka hau gabatarwa da juna kai, mom ce tayi musu bayanin komai har izuwa auren da su Azima da Aziza suke da shi a yanzu, sannan ta gabatar da Nawaz a matsayin mijin Aziza ta gabatar da Al-mazeen a matsayin mijin Azima, ta ɗan bada tahirin kansu a gajarce, dago ido baffa yayi ya kalli Al'mazeen ya Kalli Nawaz kawai sai ya fashe da kuka, Baffa Mandi ya hau bubbuga kafadun Baffa yana fadin
"Alhamdulillah! Hakika Allah baya bacci,kuma yana tare da masu hakuri da masu jahadi da sadaukarwa, hakika kayi jahadi wa yankuna da dama, kayi sadaukarwa wa yankinka da komai naka, sannan kazo ka kara bi da hakuri da juriya, taya Allah zai barka a haka Magaji? yanzu dubi ka ga mijin da Allah ya bai wa Azima da Aziza, da munata tunani da kokonta wa zai auri Azima da Aziza dan ya kawo mana karshen Banju, sai ga shi Allah ya turo mana mutane daga wasu duniya daban"
Sarki Chubaɗo ya ce
"Tabbas kuwa Magaji,kai ba mutum bane kamar kowa bane, hakika muna yiwa Allah godiya daku sirakananmu, mun gode da wannan jahadi Allah ya baku lada" aka amsa da amin, nan Sarki Chubado da mai unguwa ori suka bada umarni a shiryawa manyan baƙi kuma sirakanan Magaji Bawa Shugaban garkuwan kwana abinci mai rai da lafiya, nan aka kawo wa su Mom hadaddiyar kindirmo yasha damu, Inna wuro ta ce
"Wata kila ba zaku iya cin abincin mu ba" Mom tace
"Ai idan muka sha wannan furan wlh alhamdulillah sai kuma gobe" Al'mazeen ya ce
"Ana ta magana amma banji anyi maganar matata ba?" Baffa ne ya sunkuyar da kai Hajja kuwa rufe fuska tayi, Arɗo ne yayi murmushi ya ce
"Ohh Allah Kaɗo babu kunya, yanzu kai a gabanmu kake maganar matarka?"
Almazeen ya sosa keya ya ce
"To ai kaka gani nayi to bari dai nayi shuru" aka sa dariya, Baffa yace
"Kayi hakuri ɗan nan, sakin matarka ba tare da kayan aiki ba babban hatsari ne ga mutanen yankin nan gabadaya, ka jira har zuwa gobe idan na daure shi tukunna, ai yanzu ba matarka bace katon aljani ne mugu" shuru Almazeen yayi yana kallon Azima wacce ta koma gunki, a hankali Aziza ta miƙe zata shiga bukkarsu, jiri ne ya kwasheta nan ta fadi, kafin kowa yayi kanta Nawaz ya fara dagota, Hajja kuwa ganin su Mom sun rufu a kan Aziza yasa ita taji kunya ta koma gefe tana leken fuskar Aziza, Baffa ne ya kama hannunta ya ce
"Ya salam! Aziza an huda jikinki ko?" gya ɗa kai Aziza tayi tana jan numfashi, Baffa yace
"Dole sai an nemo furen huriri"
"Me hakan yake nufi Baffa?" cewar Almazeen
"Ai kasan ita ba asalin mutum bace,maciji kuma baya son tab'o"
"Amma an harbi Azima bai bata illa har haka ba?"
"E sabida ita Aziza Banju ya rigada da ya maidata macijiya shine dalili, ga shi yanzu dare yayi ina zan samu furen huriri?" tashi Baffa ya yi ya fita zaije jejin kwana ko Allah zai sa ya samu, yana fitowa da Inno Fandi ya hadu ta mika masa furen huriri tace
"Ina matukar farin ciki da Allah ya dawo da Azima da Aziza lafiya, sai kuma shirin kashe Banju a gobe ko?" Baffa ya sosa kai yace
"Humm Fandi, abun kunya nake jin kunya" Inno Fandi ta gano abunda yake nufi dan haka ta hau masa dariya, dan kunyar kuwa na kusantar Azima da Al'mazeen zaiyi ne,tunda dole sai Almazeen ya kusanci Azima kafin Banju ya fita a jikinta a kashesa.
Da sauri Baffa ya koma ciki, Ardo yace
"Magaji ina da kaje?"
"Da wai zanje jejin kwana ne nemo furen huriri to sai Fandi ta kawo mini" jin sunan Inno Fandi yasa Aziza fara murmushi.
Jiƙa mata furen huririn akayi,tana sha ta ware.
Su mom sun saki jiki da mutanen yankin kwana sai hira sukeyi kamar an jima da sanin juna.
Sai da dare ya tsaga Ardo yace su mom suje su kwanta su huta, su mom gidan Arɗo aka kaisu aka gyara musu wajan kwanciya, su Nawaz kuwa gidan Sarki Chubaɗo aka kaisu.
A ranar Aziza da Hajja basuyi bacci ba kwana zaune sukayi suna kuka suna hira, Azima na kafe a gefe, sai da akayi asuba tukunna Aziza ta fara jin bacci Baffa kuma ya ce mata ta fito zai daure Banju sai ta sakesa, Aziza ta miƙe tana hamma dan bacci takeji.
Kayan yaki Baffa ya tanada, sai wajan takwas jama'ar yankin kwana suka hallara, Baffa ya kalli Aziza ya mata ido alaman ta saki Azima, gya ɗa kai Aziza tayi tasa hannun ta dafe goshin Azima wani haske na shiga goshin Azima, wani ajiyar zuciya Azima ta sauke, nan ta dawo hayyacinta, idanunsu ne ya sarƙe da na Baffa
"MAGAJI BAWA!!?"
"na'am BANJU! maraba da dawowa Yankin kwana!"
🍃🍃🍃🍃🍃
MOMYN AHLAN✍🏻
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
*PAID.*
🅿️=6️⃣9️⃣↪️7️⃣0️⃣
"Wlh Baffana bani bace! Wlh ban yi yunkurin kasheka ba!" gya ɗa kai Baffa ya yi yana shafa kan Azima ya ce
"Na sani Azima" riƙe Baffa tayi gam tana kan ci gaba kuka, nan al'umman yankin kwana suka hau hamdala ana taya juna murna, wa inda sukayi wauta da farko ta hanyar dukan Aziza suka hau ba wa Baffa hakuri yace shi kam ya wuce a wajansa, nan aka zauna ana ci gaba da jajinta lamarin, lokaci zuwa lokaci Azima tana ɗaga ido ta kalli Almazeen wanda yake lullubi idonsa a lumshe bai san hayaniyar da ake yi ba.
Maga isar da sako ne ya shigo da sallama yace Sarakunan Yankuna da Muƙarrabansu sun fara isowa da wani lokaci za a fara fafatawa?" Baffa ya ce
"A shirye nake, amma a bar fafatawar sai anyi sallar la'asar da yamma kenan, a ƙara shiryawa mutanen yankuna wajan zama mai kyau da abun motsa baki dan kar su gajiya, sannan a dama musu nono mai kyau a tabbatar an basu isasshe ba ƙasasshe ba" Maga Isar da saƙo ya amsa da to, sannan Baffa yace
"Mu tafin ku dan a kara shiri" dukkansu suka fice aka bar Nawaz da Azima da Aziza, Azima idonta na kan Almazeen wanda lokaci daya taji zuciyarta ta harba da shi, a yanzu yana cikin wannan halin ne sabida ita, wani kuka Azima ta kara sakawa tana rufe fuskarta da sauri Aziza tasa hannu ta riƙo hannunta tana fadin
"Haba Azima miye haka? Godiya zakiyi wa Allah dasu Mom da Hamma Mazeen" cikin kuka har tana sheshsheƙa ta dago idonta wanda yanzu ya koma daidai amma dik da haka basu da baƙin ido ta kalli Aziza tana girgiza kai ta daga hannuwanta hawaye na zuba ta ce
"Aziza! Ni! Wai ni da kaina na ke son kashe mahaifin da ya haifeni! Wai ni da kaina na rayuwa bana bautar wanda ya halicceni! Wai ni da kaina mutane suka shiga masifa da tashin hankali! wai ni da kaina na maida yar uwata ta biyuna macijiya! Wai ni da kaina....!" kuka yaci karfinta da sauri Aziza ta rungumeta tana bubbuga bayanta itama tana kuka
"Taya zan manta da wannan abun a rayuwata! Kenan mu haka kaddararmu take!" ɗago fuskarta Aziza tayi tace
"Karki yi sab'o, ki godewa Allah, sannan duk abunda kika lissafa ai bake kikayi ba Banju ne ya yi, dan haka ki bar fadin haka Sis" cikin kukan tausayi da Azima ta kasa tsayarwa tace
"Amma da jikin wa!? Da fuskar wa?"
"Koma da miye ne komai zan zama tahiri, ki ta nanata kalman Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Yafi wannan sambatun da kikeyi dan bana so,kina ji na ko?" Azima ta gya ɗa kai hawaye na kan sauka tana kallon Almazeen wanda Nawaz ke riƙe da hannunsa yana ji kamar yasa kuka dan tausayinsa, zuwa can da suka gama kukan Nawaz ya kalli Aziza ya ce
"Tashi mu tafi watakila yanzu kam ana can filin yaki, zo muje karo na farko a rayiwata naga yadda ake faɗa tsakanin mutum da aljan" tashi Aziza tayi ta kalli Azima tace
"Ki kula da kanki da kuma Hamma Mazeen uhum?" Azima ta gya ɗa kai, Nawaz da Aziza suka fita, suna fita Azima ta miƙe a hankali ta karasa jikin gadon ta kwanta a kusa da Almazeen har yanzu jikinsa da zafi sosai, tana kwantawa ta kama hannunsa tana kallon kyakkyawar fuskarsa ta ɗora hannunsa a fuskarta ta lumshe ido.
⚔️⚔️⚔️⚔️⚔️
Hakika su Mom sun sha mamakin ganin mutane him a wannan alkarya, mutanen yankuna sun zo daga yankuna daban-daban, jama'a an cika ana kallo, Aziza na zaune kusa da mom, Nawaz yana gefen hannun hagunta, ya ce
"Mom wlh naso ace sultana tana nan da ta ga abunda take kalla a zahiri a tv" mom tayi murmushi.
A hankali Baffa ya fito yana riƙe da zureren takwabinsa wanda ya kashe Banju da shi a karon farko amma wannan karon bai yi amfani da zaren sakar dana ba, dan ko ya koma jejin lore ba ba shi za ayi ba,amma duk da haka yau sai ya kashe Banju da yardan Allah.
Kunce Banju Baffa ya yi, Banju yana ganin takwabin hannun Baffa ya ce
"Magaji! ka ajiye takwabin nan ba da shi zamu gwabza ba" murmushi Baffa ya yi ya kalli Nawaz ya miƙa masa takwabin, zuwa Nawaz ya yi ya karba yana riƙewa sai da yaji damtsen hannunsa ya girgiza, kara sarawa Baffa Nawaz ya yi sannan ya koma ya zauna.
Banju ya kalli Baffa ya ce
"Ba kai ka yarda da kanka ba?to inaso ne mu gwabza da karfin-karfi,ni aljani ne faɗa da aljani kuma ba dadi" jan kafa baya Baffa ya yi ya ware hannunsa ya ce
"Bar ganin ka ƙereni a tsayi da girman jiki! a haka na daureka na kasheka a farko, ni mutum ne amma ba irin wanda kake tunani ba na san kasan da haka" Baffa na fadi ya hau tada guguwa, ganin haka yasa Banju wani juyi ya koma wani shirgegen Maciji🐉 blue mai matukar kauri da girma, wayyo karka so ka ga yadda wasu daga cikin masu kallo aka watse daga ciki kuwa har da mom, dan tace wlh wannan kallo ba da ita ba.
Kokarin sara Banju ya hau kai wa Baffa Baffa na b'acewa a cikin iska, yayinda masu kallo aka kara ja baya ana darewa ana basu fili dan yau abun babba ne, an gwabza sosai tsakanin Baffa da Banju, da ya ga tabbas ba fa zai samu galaba a kan Baffa ba nan ya yanki wajan jama'a yana shirin ya kai musu sara dan kuwa ya tabbatar da Magaji zai kashesa! to dan haka a cikin wa innan dibbannin alumman gwara ya shafe ko da rabi ne, nan ya yi kansu gadan-gadan ganin haka yasa Nawaz fizgar hannun Aziza suka sa gudu tare da mutane, ganin yadda Banju ya yi kan alumma yasa Baffa haɗa hayaki ya kwashe mutanen ya zubar dasu gefe, jelarsa Banju yasa zai kwashi wasu kafin ya kwashe Baffa ya kuma kwashesu, ganin haka yasa ya buɗe bakinsa zaiyi musu b'arin ambaliyar wuta cikin hanzari Baffa yayi wani tsalle ya tashi sama, dan kuwa idan Banju yayi b'arin wutar nan za a mutu dayawa, kafin Banju yayi tuni Baffa ya haye saman kansa tare da zaro wani wuƙa ya dab'awa Banju a tsakiyar kai, cak Banju ya tsaya, a hankali ya fara sulalewa yana zama mutum har ya zama mutum gabadaya, yana gama zama mutum Baffa na zaune a saman wuyarsa da karamin wukar da ya dab'a masa, tsalle Baffa ya yi ya sauka daga wuyar Banju ya dirƙo akan kafafunsa ya juya baya ya maida hannunwansa ya rungume a bayansa.
Da kyar Banju ya ce
"Wuƙar Dafi!" Banju na faɗi wukar ta narke a cikin kan Banju ta b'ace bat, dan kuwa ba wuƙa bace kamar sauran wuƙaƙe, Baffa ne ya haɗa da hannunsa dan zuwan wannan rana, sharabbbb!! Banju ya zube a kasa, nan take ya kama da wuta har sai da yaci ya ƙone ƙurmuss!! Hamdala da Wani ihu da guɗa da al'umma suka saka suna fadin
"Magaji! Magaji! Magaji!" suna daga hannu, wani hawaye ne ya tsiraro daga idon Baffa, da gudu Aziza ta tashi ta zo ta rungume mahaifinta tasa kuka, shima Baffa tamkar an cire masa wuƙa a maƙoro haka yakeji, Nawaz ne ya taso ya zo shima Baffa ha rungumesa, sannan ya karbi wuƙar ya damƙawa Aziza a hannunta yace a mallamaka mata dan tare sukayi yaƙin, nan aka kara sa ihu ana kabbara kafin kace me an daga baffa sama ana ambatar sunansa, sarki chubaɗo mai unguwan yankin kwana ori da kowa na yanki kwana murna sukeyi harda hawayen farinciki, sauran yankuna kuwa ji sukeyi ina ma ace Magaji a yankinsu yake, ko ba komai zasu samu karramawa da girmamawa da daukaka daga sauran manyan yankuna, haka aka dinga miƙawa Baffa hannu ana jinjinawa jarumtarsa.
Da kyar suka saffe sukayi sallar magriba, wasu yankuna wa inda basu da nisa sai sun koma yankinsu wasu gobe zasu koma.
Ranar yankin kwana wasai, duk majalisa kuwa hiran Magaji Bawa ake yi da yaransa Azima da Aziza, Jauro kuwa dan kunya da tsangwaman da ake masa yasa ya kasa fitowa.
Washe gari bayan manyan yankuna sun karrama Baffa nan suka gaya masa ai a yankuna yanzu babban yanki shine yankin kwana, bayan an gama komai suka yi masu sallama, godiya sosai jama'ar kwana sukayi ma wa inda suka samu damar halartan wannan gayyata ta fafatawa.
Bayan kwana uku da faruwar hakan komai ya zama daidai alhamdulillah Ma sha Allah.
Yanzu Baffa ya maida hankalinsa a wajan yiwa Almazeen magani, sai da Almazeen ya shafe sati curr kafin ya farfaɗo ya dawo hayyacinsa, a wannan lokacin su mom sunyi sabo da mutanen kauyen kwana fiye da tunanin mai tunani.
Washe garin ranar da al'mazeen ya farka nan sarki chubaɗo ya tara su yace yana da magana, bayan kowa ya haɗu nan yake shaida bukatarsa na son sauƙa a kan kujerar mulkin yankin kwana, sannan ya bayyana Baffa a matsayin wanda zai mulke yankin kwana, girgiza kai Baffa ya hau yi kafin yace a'a tuni alumma sukace sunji sun gani, babu yadda Baffa ya iya dan kuwa bai so ba amma kowa ya nuna yana son Baffa ya mulke yankin kwana, haka sarki chubaɗo yasa aka rubuta sakon gayyata inda yankuna suka ce zasu zo, dan za ayi bikin da ba a taba yi ba na al'adun fulani.
🍃🍃🍃🍃🍃
Kamar yadda aka tanada haka kuwa ta kasance wajan karfe goma na safe aka fara bikin naɗa Baffa sarautar kwana, inda manyan yankuna da ƙananun yankuna duk sun zo, anyi walima Baffa ya samu alkairi ba ma iyakar shi daya ba harda jama'ar yankinsa, yankin kwana Allah ya ɗagata sama.
Wajan irinsu biyu haka aka kammala taro lafiya, an yanka su shanaye dasu kaji da zabbi an sha kindirmo, kai taro dai tayi saidai muce Allah ya taya Baffa Magaji Bawa Arɗo riƙo.
Da yamma Azima da Aziza suna zaune a bukkarsu, hajja kuma suna bukkarta dasu mom, bayan Aziza ta gama koyawa Azima karatu ta kalleta ta ce
"Aziza dama ina son na tambayeki" gyara zama Aziza tayi tace
"To inajin yar uwata" maganganun da Al'mazeen ya gaya mata a kunne ne take son Aziza ta fassara mata, dan ta kwashe maganganun tsaf a cikin kanta, dan haka ta gayawa Aziza tace ta fassara mata, dariya Aziza ta hau yi har tana riƙe ciki ta ce
"Inyee! Kin faɗa soyayya ne?" haɗa rai Azima tayi tace ban son wulakanci idan ba zaki gaya min ba sai naje na tambayi mijinki Hamma Nawaz ko naje na tambayi mom"
"Allah ya baki hakuri maida wuƙar" nan ta fassara mata abunda kalmomin ke nufi, wani murmushi Azima tayi tana rufe fuskarta da tafin hannunta, Aziza zatayi magana sukaji sallamarsu Nawaz sai da gabanta ya faɗi, su dai basu fito ba sunajin maganarsu dai a tsakar gida, Almazeen ne ya ce
"Mom ya kamata mu koma gida, dan muje mu dubasu mu ga lafiyarsu, barin ma mu da muke da asibiti" mom ta ce
"Nima na fara wannan tunani zuwa anjima zamuyi magana da Baban su Azizan" wani zaro ido Azima da Aziza sukayi bama su kadai ba harda Hajja, dan tasan za a kwashesu a tafi dasu ne tunda yara da mazajensu, kuka ta fara haɗiyewa, Almazeen ya kuma cewa
"Mom ina yaran naki suke? Ya kamata dai yau su zo su kai mu yawo mu ga gari" mom ta ce
"Hakane, Azima! Aziza!" a sanyaye suka amsa da na'am, barin ma Aziza damuwarta yafi bayyana ƙarara a fuskarta, a tare suka fito suka duƙa, mom tace
"Ku dauko mayafi kuzo ku kai mazajenku yawon ganin gari" amsawa suka yi da to suka dau mayafin dama dogon abaya ce iri daya a jikinsu, mayafinsa suka dauka suka rufa kansu da shi, a kofar gida suka samu Almazeen da Nawaz sannan suka hau tafiya babu mai cewa qala, duk inda suka wuce sai an bisu da kallon burgewa ganin yadda suke tafiya tamkar wasu taurari masu haska sararin samaniya.
Bayan sun kewaya dasu, Azima ta kalli Aziza tace
"Ukhty muje rafin jimulo" a sanyaye Aziza ta amsa da to, dan tun lokacin da taji anyi maganar tafiya jikinta yayi sanyi dan idan tace tana son komawa tayi babban karya, suna isa rafin wani iska mai dadi da yake kaɗawa ga ruwa farin sol abun burgewa ga ganyaye kore shar kwance a wajan,
"Wowww!" Nawaz da Almazeen suka furta, Azima tana satar kallon Almazeen, hannunta ya kama suka zagaya ta gefen rafin dan yana da bukatar suyi luv, dik da mugun kunyarsa takeji, suna barin wajan Nawaz ya maida idonsa kan Aziza wacce duk ta taburce kamar ma kuka take son yi, dan ita har yanzu bata taba ji Nawaz yace yana sonta ba, dan haka itama ba zata buɗe zuciyarta ba balle ta cutu, hannunta ya kama tayi saurin daga ido ta kallesa, janta yayi ya haɗata da bishiya murya a can kasa ya ce
"What's the matter?" girgiza kai tayi sai kuma hawaye suka biyo baya, hannu yasa ya goge mata yace
"Ba ki so ki koma ne ko?" shuru tayi, wani murmushi yaƙen takaici ya yi yana sakinta ya juya baya ya ce
"Na faɗi daidai shiyasa kika ƙi cewa komai?, karki damu duk yadda kike so kiyi, bcox u are free now" ya faɗa kamar a ɗan zafafe, rungumesa ta baya Aziza tayi tasa kukanta mai sauti, rintse ido ya yi ya ce
"Kamar dai na taba gaya miki bana son kuka ko? To sakeni!" sake riƙesa tayi, hannunta yaja suka isa bakin ruwan ya zauna ya zira kafafunsa a ciki, itama zaman tayi kusa da shi ta kamo hannunsa ta kifa kanta a kafadarsa, bata san lokacin da ta furta masa cewa
"Hamma Nawaz, ka taba ji kana sona? Ko kawai tausayina kakeji?" ajiyar zuciya ya sauke ya juyo ya fuskanceta yace
"Idan har zaki iya karanta abunda yake cikin idona, sannan ki auna bugun zuciyata" ya fada yana ɗora hannunta a saiti zuciyarsa dake bugawa da sauri
"Zaki iya ba wa kanki amsa, idan hakan bai samu ba, ki bari idan muka koma kd zaki tabbatar" daga haka bai sake cewa da ita komai ba banda rungumeta da yayi.
💞💞💞💞
Almazeen suna zagayawa baya da Azima ya rungumeta sosai a jikinsa, rufe fuskarta tayi da kirjinsa tana murmushi tanajin wani bakon yanayi a tare da ita, sakinta Mazeen ya yi ya rungumeta ta baya ya ce
"Na gama haukacewa na susuce a kan son...." shuru yayi ganin tana ta wani aikin rufe fuska, bakinsa yasa a saitin kunnenta yace
"Wai ni wannan kunyar na miye ne? tinda na farka ake guduna, ko dan sabida daren...." bai karasa ba ta jiyo ta sauri ta rike bakinsa tana shigewa jikinsa, murmushi yayi yace to faɗamin
"Ana sona?" ɗago kai tayi tasa idonta a na shi ta ce
"Idan ban furta hakan ba na zama butulu! wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin tawa, miye ribata idan ban so shi ba, ance tukaicin so kauna, sabida haka ina kaunarka Hamma Mazeen" wani runguma Mazeen yayiwa Azima cike da so, kafin ya haɗe bakinsa da nata ya hau bata hot kiss, Azima tayi alkawari ba zata taba juyawa Mazeen baya ba kamar yadda shi ma bai juya mata ba a lokacin da take abun gudu a wajan mutane, shiyasa ko da yake romantic dinta bata yi yunkurin dakatar da shi ba, tsayuwa ce ta gagaresu suka zube kasa, murzanta yake yi cikin salo da shaukin kauna, Azima ganin hankalinsa ya fara gushewa ne ya sakata zare jikinta daga na shi,yayi saurin riƙota ta ce
"Don Allah Hamma, ka duba inda muke,kuma ma ai" sai kuma tayi shuru, saurin saita natsuwarsa Almazeen ya yi, amma gaskiya ba zasu kara sati a garin nan ba zasu koma dan ya samu yaji dadin bai ji ba a daren farko dan wuya kawai yaci.
Tashi yayi ya kama hannunta ya ɗagata tsaye, yace
"Muje gida" riƙesa tayi tace
"Kayi fushi ne?" ɗan murmushi yayi ya girgiza mata kai alaman a'a, wajan su Nawaz suka dawo har yanzu suna zaune a bakin ruwa yana rungume da Aziza, Almazeen ya ce
"To romio and Juliet muje gida lokacin sallar magriba yayi" Nawaz yace
"Okay Laila da Majnun" dariya Almazeen yayi dan zuciyarsa fari sol.
Gida Suka tafi, bayan sallar isha'i mom ke gayawa su Nawaz yadda sukayi da Babansu Aziza kuma itama tayi na'am da maganarsa na cewa a dan barsu Azima da Aziza tukunna, su zasu tafi gobe, Almazeen da Nawaz kamar su kurma ihu, Nawaz da gajen hakuri yace
"Har na kwana nawa?" mom tace ungo nan naka🖐🏻
"Har na tsawon wata daya,ni kuma nace a barsu suyi wata biyu tunda alfarma suka nema,kuma ai gaskiya ne tinda sun jima basu ne, yanzu kuma zama na dindindin zasuyi daku"
"Haba dan Allah mom, yanzu dake za a yanke wannan shawaran?" cewar mazeen,mom tace bana son rashin kunya, maza ku tashi ku fara shiryawa, a zuciye Nawaz ya fice Almazeen ya bisa a baya.
Washe gari asubanci sukayi, kaff jama'ar kwana aka fito yi musu sallama, Almazeen ne kawai yayi sallama da Azima inda ya jima yana tsotsar bakinta, Nawaz kuwa ya ƙi kallon Aziza dan yace itama harda haɗin bakinta dama ba son komawa take yi ba.
Baffa ya haɗawa su Mom kaya sha tara ta arziki yayinda suke zubawa juna godiya cikin mutunci da mutuntawa, haka Baffa ya rungumi su Almazeen da Nawaz, sukayi musabaha da Malam Yunusa da Alhaji Karami, su Inna wuro ma sunyi wa mom da Maman beenah abun arziki, mom tace
"Dan Allah wata rana ku kawo mana ziyara, da sunyi wata daya kuma mazajensu zasu zo su daukesu"
"In sha Allah" mota suka shiga aka dinga ɗaga musu hannu, da gudu Nawaz ya figi motar Aziza ta fito itama da gudu tana daga masa hannu ya hangeta ta glass din mota amma sai ya kara gudun motar, cikin rashin jin dadi tin daga Azima har Azizan suka juya jiki a sanyaye, a ranar haka suka wuni zuciyarsu babu dadi amma suna zuba hira da wasa da dariya da Hajjarsu,yayinda Yawuro ta fara musu gyara tana tsumasu dan tana so ace kafin nan da wata dayan nan sun sama zam-zam dasu, idan mazajensu suka kusancesu basu ba kara tunanin wata mace.
@@@@
Sabida gudun da suke yi yasa biyar na yamma suka fice daga jeji suka b'illa titi, yau ma sai da suka kara kwana cikin garin yola kafin da washe gari suka kama hanyar kd, suna isa mom ta kira sultana tace mata sun dawo, wani ihu da murna Sultana tayi a waya mom ta bata labarin abunda ya faru, bata gama ji ba zumudi yasa ta katse wayar ta kalli Khalil dake danna waya tace
"Dear su mom sun dawo" da murna a fuskarsa yace
"Alhamdulillah"
"Dear tashi mu tafi ina son ganin Aziza"
"Oh Allah sultana ki bari su huta sai muje da daddare"
"O'o ni kawai ka tashi mu tafi yanzu sai ka dawo ka daukeni da daddaren" ta fada tana buga kafafunta a kasa" hararanta yayi yace "ai saiki dauko mayafinki" kiss ta sauke masa akumatu tana godiya da gudu ta hau sama dan dauka mayafinta ta sauko a mota ta samesa ya tada suka nufi gidansu.
🍃🍃🍃🍃
MOMYN AHLAN✍🏻
GARKUWAR MACIZAI🐍😂
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
Post a Comment for "AZIZA DA AZIMA 61-70"