Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

AZIZA DA AZIMA 51-60


*PAID.*

🅿️=5️⃣3️⃣↪️5️⃣4️⃣

Cikin girmamawa Hadiza ta amsa da to, sannan ta yi waje can wajan kofar baya na kitchen, ta samu Azima zaune tana tsinke fulani tana wurgarwa, Hadiza ta ce

"Azima meke damunki?" ɗagowa tayi ta girgiza kai alaman ba komai

"To ki zo mu haura sama na nuna miki part din Oga Al'Mazeen zai dawo nan da sati biyu, Hajiya Lawiza tace

Ki fara karkaɗe kura" zunbur Azima ta miƙe  tana fadin "muje"


     saman suka haura step na hawan uku can ne part din Al'mazeen, kasancewar baya son hayaniyar gidan, shiyasa idan yana gari ya dawo office yake hawa ya zauna a can shuru abunsa, harta ƙaramin kitchen akwai a saman, shiyasa baya damuwa da a kawo masa abinci, dan baya so ma yana cin abincin gidan dan bai yarda dasu ba, suna iya zuba masa abinda ba haka ba a cikin abinci.



       Tunda suka fara taka step din bugun kirjin Azima ya tsananta, Hadiza ke gaba Azima na binta a baya, har suka je bakin kofar parlourn Hadiza tasa key ta buɗe suka shiga, duk da mai dakin ya shekara baya nan amma har yanzu da kamshin turarensa na tashi, sai kuma uban kura kasancewar idan baya nan babu mai cewa a dinga bude dakin ana karkaɗewa, Hadiza ce ta kalli Azima ta ce

"Azima bari na tayaki dan kuran yayi yawa"

"A'a ki bar shi kawai Hadiza, ai aikina ne je ki kawai" 

"Yanzu zaki iya wannan aikin ke daya?" shuru Azima ta yi bata ba wa Hadiza amsa ba,ganin haka yasa Hadiza ajiyewa Azima su tsintsiya da mopa dasu omo da dai kayan aiki, har Hadiza zata fita Azima tace

"Dama kin tafi da wa innan kayayyakin naki dan ba amfani zanyi dasu ba" da mamaki Hadiza ta juyo ta ce

"To idan ba kiyi shara da tsintsiya ba dame zakiyi?"

"Ban taba shara da tsintsiya ba" Azima ta faɗa tana zuwa wajan jikin hoton da ta hango, hannu tasa ta goge hoton, nan take fuskar AL'MAZEEN ya bayyana, rasssrasssrasss!! ƙirjinta ya buga ta ja da baya tana girgiza kai, Hadiza ta ce

"Karki tsorata, shine Al'mazeen ɗin, karki ga fuskarsa a haɗe mutum ne mai saukin kai, nan gidansa ne, amma idan kika ga yadda yake rayuwa a cikinta sai kin tausaya masa" Hadiza ta fada tana matsowa kusa da hoton tasa tsummar dake hannunta ta goge wani wanda suke su biyu ta ce

"Kinga wannan? Sunansa NAWAZ babban aminine ga AL'MAZEEN,idan har kika ga Al'Mazeen na fara'a to yana tare da Nawaz, shi Nawaz a kaduna yake,kuma dukkansu likitoci ne, sabida tsananin shaƙuwa da son da suke yiwa juna,bayan sun bude asibitinsu suka saka masa suna mai harufan sunayensu *ALWAZ HOSPITAL* na Nawaz na shi na kaduna, shi kuma Al'Mazeen na shi na nan kano, yana da kyauta,baya da kyashi, yana da taimakon duk wani na kasa da shi,duk yadda zan baki labarin Al'Mazeen yafi haka, amma idaa ya dawo zaki tabbatarwa kanki" Hadiza na gama fadi ta juya ta fice.


Girgiza kai Azima ta hau yi, Banju dake jikin Azima yaji a jikinsa tabbas idan bai bar gidan nan ba, AL'MAZEEN shine makarinsa na farko a karo na biyu, to amma taya zai bar gidan? dan ya sha yunkurin haka amma zaiji kafafunsa tamkar an dauresa ne.



  Baya-Baya Azima ta yi ta koma jikin kofa ta bude blue eye dinta ta zaro dogon harshenta tana busar da wani tururi shi ba fari ba, shi ba baƙi ba, shi ba blue ba, tana hura wanna iskan hayakin nan take parlour da dakin da toilet din da kitchen din suka zama sabbi dal, harshenta ta maida sannan ta saka key a kofar ta shige bedroom ta zama macijiya ta hau gado ta kwanta dan bacci take ji, a macijiyar tayi kwanciyarta ta hau bacci.




       🍃🍃🍃🍃



"To yanzu Aziza a ganinki taya zamu je kano? Khalil ya hana, Mom kuma ta biye masa,kuma kinga yanzu ne nake da freedom bayan aure kuma sai abunda Allah ya yi, ga shi yanzu bikin saura wata daya da sati biyu, bai ma cika da sati biyun ba, wlh na rasa yanda zanyi" ajiyar zuciya Aziza ta sauke ta ce

"Anty Sulty, abubuwa suna shirin cakuɗe mana,ni a ganina ya kamata mu maida hankali a guda daya"

"To wanne kenan Aziza?"

"Bikinki! Kinga kamata yayi ace mu maida hankali a kan shirye-shirye,idan yaso bayan anyi auren a lokaci hankalu zai kwanta,idan ya so sai mu dubi gaba"

"Tabb lallai Aziza na tabbatar har yanzu da ƙuruciya na yawo a kanki, taya Khalil zai bar ni da aurena muje yawon gari ya gari neman Azima? A yanzu ma da ba ayi auren ba ya na ƙare? Gaskiya wannan shawara taki bata yi ba, ni wlh wannan biki da an bar sa idan na cika shekara ashirin sai ayi! tinda yanzu ina sha tara" ta faɗa da fuskar haushi, waro ido Aziza ta yi ta ce

"Cab Anty Sulty shekara ashirin fa kika ce? to wlh da a rugarmu na yankin kwana ne ace kamarki bata yi aure ba wollah ko zanar kofar gidanku bakki iya fita sabida gori da habaici da bakar magana, kin ganmu nida Azima, shekararmu sha biyar amma yadda kika san kamar mun shekara dari ne bamuyi aure ba, dan a al'adan rugar yankin kwana yarinya tana da shekara goma za a fara yi mata wankan kindirmo, tana shiga sha daya za a aurar da ita"

" a shekara sha dayan!?" Sultana ta faɗa tana zaro ido

Aziza ta ce

"Wlh da gaske Anty Sulty"

"Tabdijam, lallai kam, ai mu kam nan ke baki isa aure ba, amma da shike zamani ya canza ana iya miki, amma karatu ne yafi dacewa dake, ina son zuwa kauyenku"


"Tab to mu dai a can kinga bamu san wani abu karatun boko ba amma akwai manyan malaman Muhammadiyya,kasancewar muna can cikin jeji ne amma bamu da wannan duhun kan na jeji muna da ilmin addini sosai, amma In sha Allah idan na koma zan wayarwa da mutane mahaifata kai ta hanyar karantar dasu ilmi daga cikin wanda na samu daidai gwargwado, tabbas na yarda ilmi ginshiƙi ne na rayuwa,ilminka baya cika kuma sai ka haɗa duka biyu a kanka, farko sai ka ajiye ilmin da zai ceceka ranar lahira, sannan ka kara da na bokon wanda shima ta sanadinsa zaka iya shiga aljanna, Allah ya bamu ilmi mai albarka, rugarmu kuma In sha Allah idan Hamma Khalil ya bar ki zakije, amma fa karkije ki ƙi dawowa"🤪


"Amin ya Allah Aziza, hahaha taya zan ƙi dawowa?"


"Idan kikaji dadin rugarmu mana"

"Humm ke dai, ai kya bari naje na ganewa idanuna ko?" Aziza ta yi murmushi ta ce

"Ai shiyasa ban baki labarin ni'imar dake yankin sassaninmu ba" Sultana ta yi dariya ta ce

"To naji, kar dai ki shashantar da 

maganata"



"To abunyi shine kawai ki ƙara tuntubarsa" Sultana ta jinjina kai tana fadin

"Ok zanyi hakan In sha Allah,ina zuwa" ta faɗa tana ficewa a dakin.




      @@@@@@@


Kamar yadda Aziza ta cewa Sultana ta kara tuntubar Khalil da maganar ya bar su suje kano hakan kuwa akayi, ganin ta takura yasa yace ta bari to idan su Nawaz suka dawo aka karasa saita komai sai taje tayi kwana biyu idan ana biki saura sati daya, tasan halinsa baya canza magana dan haka ta amsa da to, amma a zuciyarta ta yi lissafin garin da zasuje ya kai shidda, tace ai ba ayi auren ba, balle idan ta tafi tana tafiya akan wutar jahannama (Allah ya kiyashemu amin).




        🍃🍃🍃🍃


Tunda aka shiga saura sati su Nawaz su dawo, Mom dasu Sultana da Aziza wacce faduwar gabanta ya tsananta a kwana biyun nan wanda ta rasa dalili hakan, suke shirye-shiryen dawowarsu Nawaz da Al'mazeen, da aka shiga satin karshe murna a wajan Mom da sultana abun sai wanda ya gani, Aziza ta kasa gane ita wani hali take ciki, shin murna take yi ne ko akasin haka, ta bangaren Azima ma kullum tana sama part din Al'mazeen zata shiga ta gyara ta zama macijiya ta kwanta tayi baccinta.



       @@@@@


*MA SHA ALLAH.*



A jiya ne su Nawaz shi da Amininsa Al'mazeen suka samu damar sauka a kasarsu nigeria, sun sauka ne a airport din abuja, Al'mazeen ya kalli amininsa ya ce

"Dude mu wuce kd kawai"

"No wlh sai na huta, mu wuce hotel kawai mu watsa ruwa mu huta idan yaso gobe da safe tunda driver ya zo 10 ma muna kd in sha Allah, ka ga kaima idan ka so zaka huta kafin ka wuce kano,ko ya kace?" 

"As u wish" Al'mazeen ya faɗa yana shiga mota.



     A waya Nawaz yake gayawa Mom cewa sun sauka lafiya sai gobe da safe zasu shigo Kd, sannu da gajiyar hanya mom ta musu,sannan ta ce Allah ya kaimu goben lafiya,bayan ta katse take gayawa Sultana sun iso amma Nawaz yace sai gobe zasu shigo, itama dai Allah ya kaimun ta yi,     ko da Sultana ta gayawa Aziza sai gobe su Ya Nawaz zasu shigo kd amma sun dawo nigeria suna abuja,itama Allah ya kaimun tace jikinta duk a sanyaye,     ta bangaren hajjaju Azima,itama da taji kishin-kishin watakila sai gobe ko jibi Al'mazeen zai shigo kano amma ya dawo nigeria ko kaɗan bata ji dadin hakan ba, amma tace tayi hakurin jiransa na watanni masu tsayi dan dai kwana biyu babu damuwa.




      Washe gari tunda sukayi sallar asuba basu koma bacci ba, suka share cikin gidan tass suka goge, Aziza ta ce

"Anty Sulty kije ki k'ara gyara part din Hamma Nawaz, ni zan tsaya a kitchen" Sultana ta amsa da to sannan ta fice ta bar Aziza ta hau aikin haɗa su abinci,ko da Mom ta shigo kitchen Aziza ta ce

"Haba Mom kina damu a raye me zaki zo yi a kitchen, dan Allah kije ki kwanta ki huta" murmushi Mom ta yi ta kalli Aziza ta ce

"Hakika mahaifiyarki tayi farin haihuwa da ta haifeki, na yaba da hankali da natsuwarki, Allah ya miki albarka ƴata" Aziza ta dukar ta kai tana juya white eye dinta ta ce

"Amin Mom ɗinmu" fita Mom tayi tana wasu tunani a ranta, hakika da ace Aziza mutum ce babu abunda zai hana bata yiwa Nawaz kwadayin aurenta ba, duk da Nawaz Allah ya yisa da rainakon mace, yanzu zai iya cewa Aziza tayi masa yarinya,ita kuwa zata so Allah ya bata sirka kamar Aziza wacce zata maye mata gurbin Sultana idan tayi aure, ga shi dai Aziza ta shiga ranta sosai, duk da ita bata taba ganinta a macijiya ba, bata ma fatan ganinta a macijiyan, amma taya zata fahimtar da Nawaz har ya aureta? Dan Nawaz murɗaɗɗan mutum ne, zama tayi a bakin gado tana sauke ajiyar zuciya mai karfi,ta jima tana tunane-tunane sannan ta hau adduar neman zabin Allah wa ɗanta da kuma Aziza wacce bata so ta rabu da ita.




         Karfe tara da rabi suka kammala komai suka jera a dinning, sannan suka sakawa gidan turaren wuta ya dauki kamshi, Sultana tace

"Aziza je ki dau wanka nima bari na tafi"

"To Antyna a huta gajiya" Sultana ta hau sama, aziza kuma ta shiga dakinta, toilet ta wuce dan tana da bukatar wankan nan sai kamshin abinci take yi,bayan ta fito ta dan murza mai kaɗan a fatarta wanda yake sheƙi, wani doguwar abaya ta saka, ta shafawa kanta mai,ta daure gashin, bata sa hula ba,illa lullubi da ta yi ta rufe fuskarta wanda ta jima bata rufe ba Mom ta hanata rufewa tace tayi rayuwarta ta daina takurawa kanta tunda sun san gaskiya, amma da shike yau Nawaz zai dawo harda bako yasa tayi lullubin.


     Tana nan zaune a dakinta har wajan goma da minti asharin, ihun Sultana ta jiyo tana fadin

"Oyoyooo my 2 Brother's!!" wani wawan faduwar gaba ne ya dira a zuciyar Aziza jikinta ya dauki rawa, tana ji ana oyoyo tare da fadin ya hanya, muryan Sultana ta jiyo tana kwala mata kira, a hankali ta miƙe ta gyara mayafinta ta fito jikinta na rawa, a lokacin Nawaz da Al'mazeen suna rungume da Mom, Sultana na tsaye a gefensu tana dariya bakinta yaki rufuwa dan murna, bayan sun saki mom take kara musu ya hanya suna amsa da lafiya alhamdulillah, nan Mom ta rufesu da addua na nasarar da suka samo,zama sukayi a kujeran cikin parlourn, Sultana ma ta zauna kusa da Yayanta, tana kara gaishesa ya amsa yana tsokanarta amarya-amarya, rufe fuska tayi da tafin hannunta jin Al'mazeen shima ya hau tsokanarta, ganin yadda suke murna da nishaɗi yasa hawaye zubowa a idon Aziza tana kallonsu tana murmushi dan sun burgeta, a hankali ta juya zata koma daki idon Sultana ya sauka a kanta, ta ce

"Aziza kina jina tun dazu nake kiranki Yaya sun dawo amma kika min shuru?" tun sadda Sultana ta kira sunan Aziza hankalin Nawaz ya koma kanta yana kare mata kallo kirjinsa na bugawa, tunda ya bar nigeria mafarkin yarinyar nan ya hanasa kiba, Al'mazeen ya kalleta shima yaji gabansa ya fadi, Mom tace

"Karaso mana ɗiyata" a hankali Aziza ta fara taka kafarta wanda take jinsa tamkar baya jikinta dan kafafun sun mata nauyi, ta karaso ta duka tana gaishesu kanta a duƙe fuskarta kuma a lullube, amsawa Al'mazeen ya yi sabanin Nawaz da yake ji kamar zuciyarsa zata tsaga kirjinsa ta fito waje, bayan ta gaishesu ta mike ta kawo musu abun sha, suka ce ba zasu ci abincin yanzu ba, zasuje su kwanta su ɗan yi bacci zuwa azahar,  sai sun farka kafin su ci abinci, a tashi lafiya Mom ta musu suka miƙe a tare, har sun kai kofa Mom ta ce

"Al'mazeen amma ba yau zaka tafi kano ba ko?"

"E Mom sai Allah ya kaimu gobe"

"To Allah ya kaimu lafiya"

"Amin" ya amsa a sanyaye yana bin bayan Nawaz wanda shi bai tsaya ba.



        Kwanciya sukayi ba jimawa kuwa bacci ya suresu, karfe daya da rabi suka farka suka yi sallah, Nawaz ne ya fara tashi yana fadin

"Yunwa nakeji yanzu kam, ka zo muje muci abinci"

"Okay muje" Al'mazeen ya faɗi shima yana tashi, wayar Al'mazeen ne ya dauki ruri Nawaz na ganin mai kiran ya yi tsaki yana fita.



        A hankali take tafiya Mom ta bata sako ta kai wa driver zai kai wa Hajiya Hauwa, kanta a sunkuye ga shi ta yi lullubi ga tunani,tana tafiya tana tunani, shi kuwa Nawaz hankalinsa na cikin waya yana dannawa, dai-dai wajan kofar shigowa babban parlour sukayi karo nan kafarta daya ya zame yana shirin wucewa ƙananan step guda uku na shigan parlourn ɗin, ganin haka yasa cikin saurin Nawaz yasa hannu ya fizgota, mayafinta ya faɗi kasa, gashinta da bata yi masa daurin kirki ba ya koma baya yana lilo, tsoro yasa ta waro idonta gabadaya waje, caraf sukayi 4 eye da Nawaz, wani mahaukacin bugawa kirjin Nawaz ya yi ganin white eye ɗin Aziza, saurin saketa ya yi ta faɗi ta bugu da duwawu, taji zafi dan haka tace

"Washhh Allah na!" Al'mazeen dake waya ya ga Nawaz ya saki yarinyar mutane a kasa ta bugu dan ya ga sadda sukayi karon zata faɗi ya riƙeta amadadin ya tsaidata da kafarta sai kuma ya saketa?.



      "What's wrong with u dude?" Al'mazeen ya faɗa yana shirin sa hannu ya dago Aziza,kafin Al'mazeen ya ɗagata,tuni Nawaz yasa hannu ya sake fizgota ya tsaidata da kafafunta, ya duka ya dauki mayafita ya sa mata a kai, murya a daqile yace mata bar nan, da sauri kuwa Aziza ta bar wajan, Al'mazeen ya kallesa ya girgiza kai ya wuce ya bar sa tsaye, jikin Nawaz ne ya dau rawa yana kara tariyo yadda ya ga idon Aziza, me hakan ke nufi? Ya tsaya yana tambayar kansa.



          🍃🍃🍃🍃



MOMYN AHLAN✍🏻[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃


    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨

    (🐍 _Macizai ne_🐍)


    MALLAKAR.


*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*


SAHIBAR KAINUWA.


Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.


Sanarwa.

Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association


*____________________________________*


*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_


_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_


   🍃🍃🍃🍃🍃



TNK U 4 CMMNTS MY PPL'S.



*PAID.*

🅿️=5️⃣1️⃣↪️5️⃣2️⃣




"To meyasa kika ce ba zaki je ba? Ni wlh na zata Hamma Khalil shine Abokin Hamma Nawaz" cewar Aziza,Sultana ta ce

"A'a kinga hoton Khalil" Sultana ta faɗa tana nunawa Aziza hoton Khalil a wayarta, Aziza ta yi murmushi ta ce

"Ma sha Allah,kun dace sosai, Allah ya kaimu musha shagali"

"Amin-Amin" 

"To ke yanzu Anty Sulty miye abun damuwa dan za a saka bikinki?"

"Ke Aziza baki da hankali ko? Ke kin san takura irin na Khalil kuwa? Wlh idan ya dawo ba zai bari na dinga motsawa ko nan da can ba,kuma duk abunda ya faɗi Mom zata hau kai ta zauna, taya zamu fara tafiye-tafiye wajan neman Azima? Sannan ma duk ba wannan ba, wannan babban lamari bai kamata ace zamu iya mu biyu ba, Mom tana da fahimta ni a ganina tun a ba kowa mu gaya mata gaskiya, dan kar a zo wata rana ta sani kuma abun ya kwab'e mana" jikin Aziza ne ya dauki rawa ta kalli Sultana ta ce

"Anty Sulty Mom zata koreni!" ture abincin gabansu gefe Sultana ta yi ta kamo hannun Aziza ta ce

"Taya Mom zata koreki Aziza? Babu amfanin boye mata abunda zata sani duk daren daɗewa kamar yadda nima na sani a yanzu, dan haka gwara mu gaya mata a san abun yi tun a yanzu, ga shi ana maganar tsaida bikina kwanan nan, tsammaninki yanzu Khalil zai dawo a cikin sati, su Yaya Nawaz zasu dawo nan da wata daya,ina mai tabbatar miki za a iya aurar dani nan da wata biyu, dan haka gwara muyi da gaske, yanzu ki tashi muje mu samu Mom mu gaya mata gaskiya, dan hausawa na cewa da zafi-zafi ake dukan karfe"

"Wani gaskiya zaku gaya min?" suka ji magana daga bayansu, ba iyakar Aziza ba, har ta Sultana sai da ta kwalalo ido waje, Mom ta ce 

"tambayarku nake yi, sai zazzare idanu kukeyi ku min magana mana, dan wannan idon naku baku da gaskiya" Sultana ta kalli Aziza wacce take girgiza mata kai alaman kar ta faɗa, Sultana ta hau in-ina tama kasa magana,idan ta kalli Mom, Mom zata ce ta gaya mata me suke boyewa,idan ta kalli Aziza zata girgiza mata kai kar ta faɗi, dan haka Sultana ta kasa magana banda in-inar da takeyi dan an sakata a tsakiya, ganin ta ruɗe har zufa take yi, ga Aziza da ka kalleta kaga tashin hankali a fuskarta ganin haka yasa Mom kamo hannun Sultana ta ce

"A iya sanina ban yi miki tarbiyyar k'arya ba,ba halinki bane, sannan baki boye min abu, duk da ban san Aziza sosai ba amma zan iya tsayawa na bugi kirji na faɗi halin Aziza, dan haka karku fara min karya daga yau, karku boyemin komai, tun dawowarku nake ganin damuwa a fuskarku, ku gaya min meke faruwa" kuka Aziza ta fashe da shi tana duƙawa ta rufe fuskarta da tafin hannunta, Sultana tace

"Aziza ki kwantar da hankalinki, Mom zan gaya miki" Sultana ta zaunar da Mom tace

"Ban san taya zaki fara daukar maganar ba, watakila da ace ni daya ce zakice nayi gamo da aljanu" Sultana bata fara cewa Mom Aziza macijiya bace,tun daga tushen labarin ta dauko mata tana bata tiryan-tiryan har ta kawo mata shi karshe ta dasa aya, wani ware ido Mom tayi tana bin Aziza da  kallo wacce ta haɗa kai da guiwa tana kuka, hakika hankalin Mom ya tashi, Sultana kuwa ta gaya mata ta ga Aziza a macijiya kuma ita ce ma ta taimaketa daga hannun su dan gidan Alhaji wanda da badin Aziza ba da sunyi mata fyaɗe, jikin Mom banda kyarma babu abunda yakeyi, ta jima tana karanto kalman

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" kafin ta fara jin tana samun natsuwa, sai da ta ware tukunna ta yi kan Aziza ta duka duk da zuciyarta na dukan tara-tara ta kama Aziza ta rungumeta tana rarrashinta, cikin kuka Aziza tace

"Mom dan Allah karki tsaneni! Dan Allah karki koreni! Dan Allah karki ji tsorona!" girgiza mata kai Mom ta yi ta ce

"Ko daya ba zanji ba, kamar yadda kike a da haka kike a yanzu, ai ba laifinku bane, a gaskiya Banju ba karamin mugu azzalumi bane marar imani, Allah sai ya saka muku, Allah ya bayyana mana Azima lafiya, Allah kuma ya kare bayinsa wanda Banju yake shirin tarwatsawa" suka amsa da amin,bayan sun gama yan koke-kokensu da jajinta lamarin Mom ta miƙe ta fice zuciyarta cike da zullumi, abu sai kace a film, bata fata ta ga Aziza a macijiya a labarin ma ya isa, Mom na fita Sultana da Aziza suka sauke ajiyar zuciya, Sultana ta ce

"Alhamdulillahi! Mom ta rage mana aiki"

"Kamar ya?"

"Da taji mana, da yanzu muna nan muna wallahi tallahi dake" murmushi Aziza ta yi tace

"Duk da haka ku zuciyarku daban yake, mutane irinku kaɗan ne"

"Humm! Yanzu ke kuma kenan dole  kafin ki koma mutum sai kunyi aure?"

"Ai babban damuwar yana jikin Azima, idan har ta warke nima na warke In sha Allah, amma da kamar wuya a samu wanda zai auremu har ya taimaka mana mu dawo mutane kamar kowa"

"In sha Allahu, Allah zai kawosa,kuma zaki gani,muddun kunyi tawakkali Allah zai dubi hakurin da kukayi na cinye wannan babban jarabawan, sannan ya saka muku ta yadda baku tunani"

"Haka ne kam" Aziza ta faɗa tana gyara zama, sun jima suna hira.



🍃🍃🍃🍃🍃🍃


       Bayan kwana biyu komai ya dawo dai-dai, kamar yadda Khalil ya faɗa zai dawo cikin sati to hakan ne ta kasance,dan kuwa shirye-shiryen dawowarsa akeyi,dan da ya dawo biki kawai za a sha, yace ayi biki a ba shi matarsa.




       Ranar lahadi da da daddare ya iso gari, bayan da ya huta maganar biki Hajiyarsa ta hau masa, yace tunda yau ya dawo a bari nan da kwana hudu ko biyar sai aje dan a saka rana, duk da shima Nawaz ɗin yace zasu dawo su ma kwanan nan, da haka suka ajiye maganar.



      Washe gari da misali karfe goma na safe yasha wankansa yasa manyan kaya na mutunci ya shiga ya gaida hajiyarsa, ta ce

"Khalil ina zuwa ne haka? Ko dai za a je ganin ɗiyata Sultana ne?" 

"E wlh Mom, zanje dai gaishe da Mom ne"

"Ah ba wani nan kar ma ka wani fara fakewa da Mom Ah to ,a gaishe min da su Sultanan" tashi ya yi yana dariya yace zasuji sannan ya fice.


@@@@@


      Bai gayawa Sultana a kan cewa zai zo da safe ba, ya dai gaya mata ya shigo kaduna da daddare da misalin takwas da rabi, ko da ya isa gidan kasancewar mai gadi ya san shi ya hau masa sannu da dawowa, Khalil ya amsa yana dariya, da shike gidan ba baƙonsa bane, nan ya shige kansa tsaye yana buga sallama, Aziza ce kawai ta farka a lokacin ta gana mopping kenan, ta ga mutum,tana ganinsa ta ganesa ta ce

"Lahh Hamma Khalil marabalale" ta fada tana hawa sama da gudu ya yi murmushi ya ce.

"Kanwarmu kenan" ya nemi waje ya zauna, da gudu Aziza ta shiga dakin Sultana ta haye gadon ta janyeta, Sultana ta bude ido cikin haushi ta ce

"Dan Allah miye haka Aziza!?"

"Kai Anty Sultana kin san da cewa Hamma Khalil zai zo shine kike bacci har yanzu baki masa girki ba, ba kiyi wanka ba haba dan Allah" ai Sultana tana jin an ambaci sunan Khalil yazo ta miƙe zunbur, ta ce

"Ke Aziza da gaske Khalil yazo?"

"Wlh yazo yana parlourn kasa" da sauri Sultana ta miƙe da kayan bacci ta ɗiro a gadon ta fita ta shiga dakin Mom ta ce

"Mom wai Khalil yazo" 

"E na sani"

"Shine Mom ni ban sani ba, bai fa gaya min zaizo ba, ga shi ban shirya masa komai ba, ban yi wanka ba" Mom ta dauki mayafinta tana fadin

"Too idan kin gama mitan saiki haɗa masa komai ɗin sannan kiyi wanka" ta fice, fita itama Sultana ta yi, ta samu Aziza na kwashe kaya a parlourn sama,ta ce

"Aziza yanzu ya zanyi?"

"Karki damu Antyna,yanzu kedai kawai kije ki cakare wanka, zan kula da saura"

"Thats my lil'sis" Sultana ta fada tana shiga daki da sauri, kasa Aziza ta sauko ta shiga kitchen, a cikin mintuna qalilan ta jera tray ta haɗa abubuwa a kai na burgewa da ban sha'awa tazo ta ajiye a gaban Khalil wanda yake duƙe a gaban Mom suna magana, sun jima suna magana da Mom kafin Mom ta tashi ta koma sama, ba jimawa gimbiyar tasa ta sauko, nan aka hau hiran soyayya na yaushe gamo, sannan ta kara gabatar masa da Aziza.




         Kamar yadda Khalil ya fada bayan sati daya da dawowarsa aka zo aka tsaida ranar aurensa da Sultana wanda za ayi nan da wata daya da sati uku,wanda Nawaz shi da Khalil ɗinne suka yanke wannan shawara.



      Tunda aka saka wannan rana Khalil ya hana Sultana sakat, tayi-tayi ya bari suje kano amma ya ƙi, yace ta bari ba yanzu ba,ita da basu shiri da yan kano din ma, bayan sunyi haka da shi ta gayawa Aziza, Aziza ke tambayarta meyasa bata son kano, Sultana ta ce

"Ni da Hanan yadda kika san kamar wuta da auduga, sannan rashin kirki da mugunta irin na Maman Hanan da Maman Beenah abun ba a magana karki so ki yadda suke yiwa Yaya Almazeen, kuma shine mai kudin fa, gwara ma dai Beenah muna ɗan shiri amma banda Hanan, bana son halinsu ne sabida muzgunawa Yaya Al'mazeen da sukeyi"

"Mutane kam ai sai addua, Allah ya kyauta kawai" Sultana ta amsa da amin.




       🐍🐍🐍🐍



Hadiza! Hadiza! Hadiza!.


Da gudu Hadiza ta fito ta zube a gaban Hajiya Lawiza Maman Hanan kenan, cikin yauki ta kalli Hadiza ta ce

"Hadiza, maza ki kirawo Azima ki haura da ita can sama part din Al'mazeen ta fara gani da tattare ƙura, suna nan dawowa nan da sati biyu"




      🍃🍃🍃🍃



*BACCI NAKEJI WLH🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🥱😴🏃🏻♀️*

[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃


    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨

    (🐍 _Macizai ne_🐍)


    MALLAKAR.


*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*


SAHIBAR KAINUWA.


Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.


Sanarwa.

Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association


*____________________________________*


*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_


_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_


   🍃🍃🍃🍃🍃



*PAID.*

🅿️=5️⃣7️⃣↪️5️⃣8️⃣




Damm! Gaban Azima ya buga tayi saurin ware blue eye dinta,  ta maimaita

"Azizaa! Aziza dai!?" Maman Beenah ne ta kallesa ta ce

"Al'mazeen kasanta ne dama? Sannan sunanta ba Aziza bane, wannan sunanta Azima ne" girgiza kai Al'mazeen ya hau yi yana ƙarewa Azima kallo,yatsar hannunta ya kalla yaga irin zoben da ya gani a hannun Aziza dazu, sannan ace kuma ba Aziza bane? Ko dai ya yi gamo ne? da sauri ya haura sama, yana shiga part dinsa ya ga sai kyalli yakeyi an gyara sosai bai tsaya karewa ɗakin kallo ba, wayarsa ya ɗaga zai kira Nawaz sai kuma ya fasa ya kira layin mom,ringing uku mom ta daga suka gaisa yace mata ya isa lafiya,mom tayi hamdala ta masa sannu da hanya ta kara da cewa

"Ya ka samu mutanen gidan,su Hajiya Lawiza da Hajiya Luba?da kuma yaran?"

"Lafiyar su lau"

"Ya naji muryarka haka Al'mazeen? Kamar kana cikin tashin hankali ko damuwa, ba dai daga dawowarka suka fara cusa maka baƙin ciki ba?"

"A'a mom basu bane, amm nace ba mom? Aziza fa? Ya jikin nata?"

"Alhamdulillah da sauki, ko ba sauki musulmi ai ba zai ce babu ba sai dai yace alhamdulillah, Sultana tana tare da ita dik da naji tace tana da paper 12 zataje skull ga abokin naka ma shima baida lafiya, bayan tafiyarka da ya shigo idonsa a kumbure wai kansa ke ciwo"

"Subhanallahi! Allah ya basu lafiya, dama tunda na ga yanayinsa na san bai da lafiya dan ina kyautata zaton jiya bai yi bacci ba dan a parlor na samesa zaune da asuba, amma da na tambayesa yace min ba komai,zuwa 12 in sha Allah zan kirasa naji ya jikin nasa maybe yanzu yana bacci, bari na kira sultana naji ya na Aziza yake" nan ya yiwa Mom sallama yana katse wayar, sultana ya kira a lokacin tana magana da wata classmate ɗinta a waya,tana gaya mata ba zata samu zuwa skull ba, Brothern'ta da sistern'ta basu da lafiya, suna cikin magana ta ga wayar Al'mazeen ya shigo dan haka sukayi sallama da kawarta ta daga na  Al'mazeen, sai da ta masa an isa lafiya kafin yace mata 

"Ya jikin Aziza?" kuka ta sa tana kara masa wayar a saitin fuskar Aziza dake fidda huci tana gurnanin zazzabi,bayan ta kara masa wayar  yaji kafin ta maida wayar kunnenta tana ci gaba da kuka tana fadin

"Bro ka ji ta ko? Yadda ka barta haka take sai ma abunda ya ƙaru"

"Subhanallahi! Allah ya bata lafiya kin bata wa innan maganin kuwa?"

"E bai jima ba da na bata,amma kamar bai yi aiki ba"

"Karki damu kinji zai mata a hankali kiyi ta yi mata addua, Allah ya bata lafiya!"  daga haka ya katse wayar,ya hau jeka ka dawo a daki yana saƙa da warware, "AZIMAA!?" ya faɗa yana rike kai

"To ko dai yar uwar Aziza ce? Tunda sunansu mai haɗi iri ɗaya ne? Amma kuma Nawaz yace an kashewa Aziza kowa bata da kowa! To ba mamaki kamanni ne" daga haka ya miƙe ya shige toilet abunsa ya watsar da tunanin jin yana shirin saka masa ciwon kai.



        A kasa kuwa ba ƙaramin daru aka sha da Azima ba a kan abincin da za a kai wa Al'mazeen, ta dage ta kafe tace wlh ba zai ci wannan abincin ba, Maman Hanan ta ce

"E lallai kam Azima, wato kin samu waje kinyi freesh shiyasa zaki fara murza iskanci son ranki ko! To wlh ki bi a hankali" ba tare da Azima tayi magana ba ta karbi abinci a hannunsu Hadiza tayi wajan kitchen da shi ta ajiye ta hau yiwa Al'mazeen sabo, girki takeyi duk da ba wai ta wani iya sosai bane, amma da taji ance Al'mazeen zai dawo yasa kullum tana kitchen dasu Hadiza tana ganin yadda ake girkin barin ma wanda aka ce mata Al'mazeen ɗin ya fi so.



      Tana girki tana tunanin sunan da Al'mazeen ya kirata da shi,hakika hankalinta ya ɗan tashi

"Aziza! Aziza! Ina Al'mazeen ya san Aziza? Shi da baya ma kasar, to ba mamaki wajan kiran sunanta aka samu kuskure zai ce Azima yace Aziza" share zancan tayi ta ci gaba da aikinta dan ta san wan can sakaryan tana can jeji, sai bayan da ta kammala ta jera a tray ta dauka ta haura sama.



       A hankali ta tura kofar ba tare da tayi sallama ba, Al'mazeen na zaune a parlour da system a gabansa da alama aiki yake yi, yaji mutum ya shigo ba sallama, haɗe rai ya yi, ita kuwa Azima sallama baya daya daga cikin dabiunta, abunda Al'mazeen ya tsana kenan, dan shi mutum ne mai girmama addininsa fiye da komai a rayuwarsa, Al'mazeen da na riƙo da addini fiye da tunanin mai tunani, murya can kasa yace

"Fita ki min sallama, karki sake ki min magana ba tare da kin min sallama ba" juyawan kuwa tayi ta fita ta sake shigowa tare da fadin

"Salamu alaikum" tana tura bakin, bakintan kawai yake iya hangowa yadda take tura shi tana murguɗa shi tunda fuskarta a rufe yake, abun dariya ya ba sa dan haka ya ɗan murmusa ba tare da ta gani ba, abincin ta ajiye tare da fadin

"Kayi hakuri" bata ma san sadda tace masa ya yi hakurin ba, jinjina kai Al'mazeen ya yi,ya ce

"Kece Azima?" ta gya ɗa kai, 

"Daga ina kike?" damm! gabanta ya buga, amma da shike zuciyarta a tsaye yake ƙyam tace

"Daga can cikin kauyen kano a wata rugar fulani"

Al'mazeen a ransa ya ce

"E tabbas to basu da alaƙa da Aziza"

"Ina abincin da aka dafa min?" murguɗa baki Azima tayi tace

"Na ajiye musu a bayan kitchen idan sun ga dama su dauka su ci ko su san yadda zasuyi da shi" tana gama fadi ta mike fuuuu ta fice, girgiza kai Al'mazeen ya yi ya ci gaba da aikinsa, sai wajan sha daya da rabi ya ja tray din da ta ajiye masa ya buɗe yana kan buɗewa sai ga ta ta shigo ta duƙa tunowa da dazu ya koreta akan bata yi sallama ba sai ta kara ficewa da sauri ta shigo tana fadin

"Salamu alaikum! ai saika kirani nazo na zuba maka"

"Kina da waya ne?" girgiza kai Azima ta yi ta ce

"A'a bani da shi,amma idan kace AZIIIMAAAA!!🗣️Ai zanji na taho da sauri!" girgiza kai Al'mazeen ya yi ya tashi zai shiga daki, da sauri ta ce

" *HAMMA MAZEEN* abincin fa?" 

Cak Al'mazeen ya tsaya yana nanata sunan "Hamma Mazeen!" kirjinsa ne ke bugawa da sauri-sauri,

"Ina zuwa ki zuba kawai ki tafi" ya faɗa yana shigewa bedroom, Azima haushin kanta ne ya kamata, wai meyasa take masa abu kamar wanda ake sakata ko ana bata umarni ne? Meyasa take jin faduwar gaba a kansa, meyasa take jin makarin gubarta yana tattare da shi? Amma kuma tana ji kamar ita da shi an jona musu kuran karfe, saurin tashi tayi ta fice.




         🍃🍃🍃🍃🍃


Sai 1 Nawaz ya farka ya ɗan ji kan nasa da sauki amma kan ya yi masa nauyi, wanka ya yi a nan daki ya yi sallah, sannan ya lallaba a hankali ya shiga cikin gida, ba kowa a parlor dan haka ya fara haurawa sama, sai kuma ya juyo yana kallon kofar dakin Aziza, saukowa ya yi ya nufi dakinta, a hankali ya tura da sallama, mom da sultana ma ashe suna dakin, Aziza na jingine tana sallah a zaune a kan gado, saurin karasowa kusa da mom ya yi ya ce

"Mom jikin nata ya yi tsanani ne haka shine baku tasheni munje asibiti ba?"

"Humm! Nawaz kai ma fa ba lafiyar gareka ba, ka ganta nan jiya bata rintsa ba"

"Bari ta idar da sallar sai a kaita asibiti"

"A'a Nawaz ba sai anje asibiti ba, babu amfani, zaku ƙara huda mata jiki ne kawai, yanzu sai kuce zaku sossoka mata allura a ɗaura mata ruwa aja jini, wanda hakan kuma...!" sai Mom tayi shuru, a lokacin Aziza ta sallame sallarta, Nawaz ya miƙe yana fadin

"Mom dan ta gaya miki bata son allura sai a biye mata dan lafiyar wa akeyi? Ina dan lafiyarta ne!" ya faɗa cikin haɗa fuska, ya nufeta yana faɗi wa Sultana ta tashi taje ta cewa driver ya juya mota.


    Aziza kuwa ganin ya nufota yasa ta kwalalo ido waje, dan kuwa jikinta yana fidda farin sab'ar maciji idan ya gani fa? Saurin girgiza masa kai ta hau yi muryarta a shaƙe da baya fitowa sosai ta hau fadin ya kyaleta kar yazo inda take, ko kaɗan bai tsaya ya saurareta ba yasa hannu ya yaye bargon jikinta ya kamo hannunta,ji yayi kamar wani fata ya maqale masa a hannunsa, sake hannun nata ya yi yana kallon tafin hannunsa, wani zare ido Nawaz ya yi sai kace idon zasu faɗo ƙasa,ganin sab'ar fatar maciji fari sol a hannunsa, Aziza kuwa banda kakkarwa babu abinda jikinta ke yi,tana sake boye hannunta a cikin hijabin dake jikinta tana jan bargo tana son rufe kafafunta, saurin fizgar bargon Nawaz yayi jikinsa na kyarma, yasa hannu ya figi hijabinta ganin haka yasa mom cewa da sauri

"Nawaz ka haukace ne!? baka da hankali ne!? mai kake shirin yi!?" ba tare da ya saurari mom ba ya ɗago Aziza tsaye wacce jiri ke kwasarta, hannunta ya riko ya ware nan kuwa ya ga jikinta duk b'awu, a lokacin kuma Aziza ta suma, dagota ya yi yana jijjigata cikin tashin hankali yana tambayarta wacece ita.


Cikin kuka Sultana tasa hannu ta kwace Aziza daga hannun Yayanta ta rungumeta ta ce

"Yaya ta suma fa? Dan Allah Mom kiyi wani abu a kai"


 Nawaz yasa hannu zai kara jan Aziza daga jikin sultana, sultana tayi saurin juyawa da ita ta kwantar da ita tana murza tafin hannunta tana kuka

"Zan fa karyaki Sultana ina wasa dake ne!!?"

"Wlh Yaya ko kasheni zakayi ba zan bari ka kasheta ba, dan Allah mom kiyi magana ki gaya masa gaskiya,babu amfanin wannan boye-boyen"



       "Nawaz ya isa haka! Aziza Macijiya ce!" Mom ta faɗa a tsawace,

Nawaz ne ya yi baya-baya yayi zaman yan bori sharab, mom ta karaso ta kama hannunsa.


   kenan mafarkinsa akan yarinyar macijiya ce gaskiya ne? Kallon Mom ya yi da jan ido ya ce

"Mom da macijiya muke rayuwa kuma ke ma kin sani? Taya hankali zai dauka ace mutum maciji? Da ace sultana ce ta faɗa ba abunda zai hanani ban kaita asibiti an duba min kwakwalwarta ba"

Ajiyar zuciya mom tayi tace

"Zaka iya tsayawa ka saurareni uhum? Nawaz magana nake maka" kifa kansa ya yi a kafadar Mom hawaye suka hau gangaro masa wanda bai san dalili ba.


       "Nawaz labarin Azima da Aziza da baffansu da kauyensu abun tausayi ne mai cike da zallar al'ajabi" cikin taushin murya Mom ta hau zayyanawa Nawaz labarin Aziza bata boye masa komai ba kamar yadda Aziza ta ba su haka ta bai wa Nawaz, mom tana gama ba shi labarin ya dago yana fadin

"Wlh mom yawancin  abun da kika faɗa min ina ganinsa a mafarkina, tun ranar da na bugeta a mota na kawota kaduna tun daga ranar na daina bacci kirki,mom ina yawan ganinta a siffar macijiya tana kuka tana neman taimakona!" jinjina kai Mom tayi ta ce

"Ba mu san me Ubangiji ya boye tsakaninka da Aziza ba Nawaz, amma inaso muyi wani jahadi wana Allah ya zama silar shigarmu aljanna, Nawaz har zuciyata ina jin Aziza,yarinya ce mai hankali da natsuwa da sanin ya kamata duk da tana da kananun shekaru amma tana da hankalin manya da imani da kaddara ga tawakkali da miƙa wuya,kuma dama abunda akeso kenan ga musulmi mumini ko mumina, Nawaz sultana zata bar gidan nan kwanan nan, dan Allah ina so kayi jahadi ka *AURI AZIZA!!*" dummm!! gaban Nawaz ya bada ya kalli Mom da sauri, Mom ta gya ɗa kai tana fadin

"Tun kana yaro ban taba cewa ina neman alfarma ka kasa min ba, ina so ka taimaka ka auri Aziza, ka zamo silar warkewarta, duk wanda ya zama silar farin cikin mutum daya Allah zai zama silar farincikinsa a ranar da babu wani mai gata sai fiyayyen halitta, Nawaz kana da ilmi duk abunda zan gaya maka ka sani sai dai na kara yi maka tuni, idan ka auri Aziza ka zamo silar warkewarta hakika zaka saka mutane dayawa ne farinciki, zaka fidda UWA da UBA daga ƙunci, da sauran yan uwansu, wlh har zuciyata na aminta" kallo fuskar Aziza Nawaz ya yi, hakika daga fuskarta zaka san cewa tana jin jiki

"NA AMINCE MOM! ZAN AURETA!" da sauri Sultana tazo ta duƙa ta rungumesa cikin murna, "da gaske yaya zaka aureta!? Wayyo dadi wlh nayi farinciki"

"Allah ya maka albarka Nawaz" cewar  mom tana shafa kansa.



      Nan suka zauna a dakin har sai da aka yi sallar la'asar kafin suka fita da niyyar sallah, nawaz msallaci yaje, bayan sun idar ya jima yana kwararo adduoi a kan wannan lamari da yake gani tamkar a mafarkin da ya saba ne.



     Bayan ya dawo part dinsa ya wuce, ya dauki wayarsa ya ga miss calls din amininsa,kiransa ya yi ya daga yana tambayarsa ya jikinsa,Nawaz ya amsa da sauki shima yana masa ya gajiyar hanya, Al'mazeen ya amsa da alhamdulillah ya kara da fadin ya jikin Aziza, alhamdulillah Nawaz ya fada, sun ɗan jima suna magana inda Nawaz yake ji ko ya gayawa Al'mazeen? Daga baya kuma ya fasa har suka gama wayar sukayi sallama.




      Sai wajan shidda Aziza ta farka sultana ta taimaka mata tayi alwala tayi sallah a zaune kamar dazu, bayan ta idar tayi addua sultana ke gaya mata sadda ta suma mom ta gayawa Yaya Nawaz komai, a lokacin da sultana ke gayawa Aziza Nawaz sun shigo shi da mom, kuka Aziza ta saka tana fadin

"Shikenan zai koreni! Dan Allah Anty Sultana ki ba shi hakuri kar ya koreni, wlh da na samu Azima zan tafi da kaina,tafiya na har abada ba zai sake ganina ba in sha Allah" rasss! gaban Nawaz ya buga jin tace zata tafi na har abada, a hankali Nawaz ya juya ya fita ganin  yadda take kukan duk sai yaji babu dadi yana danasanin abunda ya mata, tayi mugun karya masa zuciya.



Mom tace

"Injiwa yace zai koreki a gidan nan? Bana so na ƙara ji kince zaki bar gidan nan na har abada, dan kuwa kina nan a gidan nan har abada In sha Allah,kinji ko?" Aziza ta gya ɗa kai tana kuka.



@@@@@@@@


          Da washe gari tana kwance tana fama da kanta,bata san ta yadda zata samu furen huriri ba, da ace ta samu da tuni an wuce wajan, turo kofar akayi da sallama, jin muryan mai sallaman yasa gaban Aziza bugawa, murya na rawa ta amsa, karasowa yayi a hankali ta dago idonta ta kallesa a tsorace, ta gansa da plate a hannu, mamaki ne ya kamata, zama yayi a gefen bedside'drower fuskar yau da sassauci, murya a can kasa ya ce

"Ya jikin naki?" 

"Alhamdulillah, ina kwana?"

"Tashi kici abinci ki sha wannan rubutun, wani babban aminin Daddyna ne malami ne wajansa naje jiya da daddare na masa bayani a kan matsalarki, yace na baki wannan zakiji dama-dama duk da ba lallai bane ya dauke miki abunda kike ji gabadaya ba, amma zaki  samu karfin jiki" mamaki ne ya ƙara kamata, amma bata da lokacin tsayawa mamakin, a hankali ya dagata ya jinginata da pillow, ya dau spoon ya ɗibi abincin ya kai mata shi saitin bakinta, tsananin mamaki ya hana Aziza buɗe baki taci dan ji take kamar mafarki takeyi, ganin yadda jikinta ke rawa yasa Nawaz furta kalman

"I'm sorry Aziza" a sanyaye, sake yin ƙasa da kanta Aziza tayi gabanta na ci gaba da bugawa, muryarsa taji yana kara fadin

"Na sani, na cusa miki tsorona a zuciyarki, am sorry once again" kuka ta fashewa da shi, ya ɗan rintse ido ya ce

"Kamar na gaya miki bana son kuka ko?" ta gya ɗa kai

"To meyasa kikeyi?"

"Na...ba...ri" ta fada murya na rawa, 

"To kici abincin" ya fada yana bata a baki cike da tausayinta, bata wani ci sosai ba ta ce masa ta koshi, cup ya dauka ya tsiyaya mata rubutun ya bata tasha tana sha taji kanta na wani mugun juyawa, ba jimawa ta zube ta hau bacci, ganin tayi bacci yasaka shi tashi ya fita,a parlour ya samu Mom da sultana, zama ya yi kusa da mom, ta ce

"Allah ya maka albarka Nawaz, Allah ya faranta maka duniya da lahira" a tare suka amsa da amin shi da sultana.




      Ko da ta farka taji jikin nata da dama-dama,dan kuwa ta miƙe da kafafunta har tana iya tafiya, jirin ne dai bai daina dibarta ba.



🍃🍃🍃🍃🍃🍃


         Bayan kwana biyu taji sauki alhamdulillah amma lokaci zuwa lokaci jiri na zubar da ita, tsakaninta da Nawaz kuma yanzu babu tsangwama, sai tausayawa, har mamakinsa take yi,ita dai ba zata gushe ba tana yiwa su mom addua.



🍃🍃🍃🍃🍃


Bayan sati daya da dawowar Al'mazeen kano komai ya canza a gidan, Azima ke zuba mulki son ranta, ga shi yanzu tana kwatowa Al'mazeen yancinsa a cikin gidan, duk wani guba da maganin mallaka idan aka zuba masa a cikin abinci sai dai azo a samu Azima ta juyewa karnuka abincin, su Hajiya Lawiza da Hajiya Luba sun rasa yadda zasuyi da Azima, ta bangaren Al'mazeen kuwa a sati ɗayan nan kacal ya shaƙu matuƙa da Azima dan har zuciyarsa yake jinta, shi mutum ne mai son kulawa da soyayya amma bai samu ba, sai ga shi rana tsaka ya samu a wajan mai aiki dan ba karamin kulawa da shi Azima ke yi ba.



Kamar yadda Azima bata son dogon magana haka ma al'mazeen, amma su kan zauna suyi hira, inda take gaya masa ai itama bata da kowa duk an kashesu, idan Azima na magana ya kan ji muryan Aziza, duk da ba wai ya taba ganin fuskokinsu sosai bane, dan itama Azima duk shaƙuwan nan bata buɗe fuskarta, bayan dawowarsa da kwana uku taso guduwa ta bar gidan amma haka ta kasa har ya kai sati daya,inda takeji kafafunta sunki amincewa da barin gidan.



    Yau ma kamar kullum ya shirya zai tafi asibiti, yana kan saukowa kasa har ya zo step din karshe sai ga Hanan, tana ganinsa sarai ta bangajesa briefcase dinsa ta faɗi, amadadin ta tsaya ta ba shi hakuri sai tana shirin rab'awa ta gefensa ta wuce, Al'mazeen cikin haushi ya ce

"Kee Hanan! Baki ga abunda kika min bane! Zo ki dau jakata ki bani"

"Wlh Al'mazeen sauri nake yi inaso naje na gwada wannan memoryn ne" ta faɗa tana shirin hawa sama taji an wani fizgota ta baya, ta ma zata Al'mazeen ɗin ne amma tana juyowa ta ga Hajja Azima wacce yau tayi shigan riga da wando idonta sanye da wani black shadow, Al'mazeen ne ya siyo mata jiya kasancewar itama ta masa karya da cewa ai idonta na ciwo.


    fuskarta a haɗe da ka ganta sai tayi maka kama da irin bosawan film din indian nan, ashar Hanan tayi  ta kalli Azima sama da kasa tace

"Wato na kauye ya shigo gari ko?"


       "Ki duƙa ki ɗau jakarsa ki basa sannan ki ba shi hakuri" Azima ta faɗa cikin murya mai nuna umarni take badawa ba shawara ba.


"Lalala! Wlh ni ba irinsu Hajjaju bane, da zaki dinga yab'a musu magana kina juyasu kina basu umarni kina gasasu! Wlh ni karyaki zanyi! dan ni bana son raini!" 


Hannunta Azima ta kama ta murɗe Hanan tasa ihu, Azima ta cije baki tace

"Kinga ni nayi miki kama da wacce take son raini? Tun kafin ki san wacece asalin Azima dau jakarsa ki ba shi sannan ki ba shi hakuri!" 


Maman Hanan da Maman Beenah da beenah da Hanif ne suka sauko jin ihun Hanan.


     Nan suka ga Azima murɗe da hannun Hanan Al'mazeen na cewa da Azima a kan ta saki hannun Hanan, ita kuwa tace ba zata sake ba, sai Hanan tayi abinda ta sakata,jin wuya yasa hanan cewa zata yi yadda Azima tace, sakinta Azima ta yi ta duka ta dau jakar ta ba shi ta ce

"Kayi hakuri"


     "Kayi hakuri wa?" Azima ta faɗa a tsawa ce.


"Kayi hakuri Al'ma...." dauketa da mari Azima tayi har saida Hanan ta kai kasa,Azima tace

"Hamma! Daga yau idan na cire su Hajiya duk gabadaya Hamma Mazeen zaku na ce masa tunda ya girmeku, maza gaya masa!"


"Kayi hakuri Hamma Mazeen" Hanan na faɗi ta hau sama da gudu, Maman Hanan da Maman Beenah da Beenah suka bi bayanta, Al'mazeen ya haɗa rai yace

"Ina bakijin maganata? Ina cewa ki saketa amma kinki ko?" turo baki tayi tace

"Ba komai nake yi daukawa ba,kuma ma ai sabida kai nayi" tana gama fadi ta fice tana tura baki ta bar shi tsaye, murmushi Almazeen yayi ya fice ya tafi office.



       Ko a office din ya kasa aikin kirki tunanin Azima kawai yakeyi, wayarsa ce tayi kara yana dubawa ya ga Alisha,guntun tsaki yaja,yau kusan sati tin dawowarsa kano take kira baya dagawa.



       @@@@


"Yanzu me zamuyi wa wannan yarinyar dan tana son fin karfinmu?" cewar Maman Hanan, Maman Beena ta ce

"Shegiyar taga kudi duk yadda akayi sonsa takeyi"

"Abunda za ayi muyi mata sharrin sata na san shi da kansa zai koreta, dama yau su Summy da Sady zasu zo ko?"


"E sunce ma sun kusa isowa".



    (Summy da Sady, kannan Hajiya Lawiza da Hajiya luba, wanda suke so su aurawa Al'mazeen).



      🍃🍃🍃🍃


MOMYN AHLAN✍🏻

[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃


    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨

    (🐍 _Macizai ne_🐍)


    MALLAKAR.


*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*


SAHIBAR KAINUWA.


Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.


Sanarwa.

Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association


*____________________________________*


*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_


_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_


   🍃🍃🍃🍃🍃



*PAID.*

🅿️=5️⃣5️⃣↪️5️⃣6️⃣




Da kyar ya tattaro jarumta jin yadda kafafunsa suka yi sanyi ya shiga parlourn, ya samu Al'mazeen zaune yana cin abinci, zama shi ma ya yi Sultana ta zuba masa ta tura masa gabansa, amma tunani yasa ma yaji abincin ya fita kansa, Aziza kuwa tin sadda ta ba wa driver sako ta maqale ta kasa shiga gidan ganin yayi babakere a bakin kofa, sai da ya shiga ta siɗaɗo a hankali ta shige dakinta da gudu,tana shiga ta zube a gado ta saki kuka, ba jimawa Sultana ta shigo ta sameta tana kuka ta ce

"Subhanallahi! Aziza lafiya me ya faru?"

Cikin kuka ta dago ta ce

"Anty Sulty Hamma Nawaz ya ga idona"

"Mtswww! To sai me dan ya ga idonki?"

"Wlh tsoro nakeji kar ya koreni, dan naga yana mini kallon tuhuma kamar yasan wani abu a kaina"

"Kinga Aziza dan Allah ki kwantar da hankalinki ki samu natsuwa kinji? Babu abinda zai faru,na san me zanyi, kuma ma ai idan ya san wani abu a kanki ai ya rage mana aiki, balle ina ma zai sani? daga wajena sai wajan Mom,kuma Mom da kanta ta kwabeni tace kar na gaya masa ta san ta yadda zata gaya masa,na tabbata mom bata gaya masa ba,dan da ta gaya masa zata gaya min, dan haka ki dai na damun kanki" rarrashinta Sultana ta yi har ta samu tayi shuru, kafin suka koma hiran karatu.



        Da kyar Nawaz ya yi cokali uku a abincin ya tashi, Al'mazeen ya ce

"Dude ka ce yunwa kakeji amma ka kasa cin abinci i hope dai komai lafiya?" 

"E lafiya,ina zuwa" ya fada yana ficewa, part dinsa ya koma ya kwanta a dogon kujera, hakika idonta babu bambanci da wanda yake gani a mafarkinsa, wai wacece wannan yarinyar nan ne kam? Ya zama dole ya tambayeta ita wacece sannan miye haɗinsa da ita,idan ma mayya ce to wlh shi namansa da ɗaci,kuma sai ya danna mata kashedi ta fita rayuwarsa ya huta, ya kara jan tsaki.




      Bayan Al'mazeen ya gama cin abinci ya koma part din Nawaz ya samesa yana kwance a dogon kujera,zama ya yi a 1siter yana fuskantar Nawaz ya ce

"Dr lafiya kuwa?"

"Nml, kawai kaina ke ɗan min ciwo"

"Ayya sorry, to ka sha magani mana"

"No ba yanzu ba, bari na gani zuwa dare idan banji dai-dai ba zan yiwa kaina allura ko kuma ka min"

"Ok, Allah yakara sauki"

"Amin" Nawaz ya fada yana lumshe ido, wayar Al'mazeen ne ya sake ƙara, Nawaz ya bude ido yana jan dogon tsaki

"Mtswwwwww!!! Wannan mayyar ce ko!?"

"Meyasa kake ce mata mayya bayan kasan ita zan aura?"

"Wlh Allah ya sawwake maka da aurar wannan kakar taka, duk da nasan bana son yarinya karama amma ina zaka kai Alisha? ni fa wlh na rasa meke damunka, duk matan duniya ka rasa wacce zaka zab'a ka aura sai Alisha? Ga uban saka gashin doki a kai, ga ƙarin farce, ga saka gashin ido, ga rashin kunyar taunar cingam, gabakidayanta ma wlh zube take da karuwai! Dan Allah ka bar batun auren Alisha!"


     "Haba dan Allah Nawaz ya isheka haka mana! Kai kullum baka da aiki sai kushe Alisha? A tsammaninka dadi nakeji idan kana kusheta? Shuru fa kawai nake yi" Al'mazeen ya faɗa ransa a haɗe, Nawaz ya yi tsaki ya ce

"Aikin banza! Abunda kai ma ba sonta kake yi ba, dan an kusheta miye naka na jin haushi,wlh da ace kana son Alisha yadda nake kusheta da mun jima da rabuwa da kai"  girgiza kai Al'mazeen ya yi ya ce

"Mace ba zata rabamu da kai ba Nawaz, idan na rabu da kai waye zai dinga supporting dina? Plss karka kara fadin haka, abunda yasa nake son auren Alisha ita tana sona sosai,kuma ina sa ran zata bani kulawar da na rasa da soyayyar da ban samu ba" ya karasa fadin idonsa na canza kala,ganin haka yasa Nawaz matsowa kusa da shi ya zauna a hannu kujera ya riƙo kafadarsa yace

"Karka fadi haka, In sha Allah Aminina ya kusa fara dariya, ka tsaya kuma ka gani,mahakurci mawadaci, na fadi dai-dai?" Nawaz ya fada yana murmushi tare da miƙawa Al'mazeen hannu, shima Almazeen murmushin ya yi yana haɗa hannunsa da na Nawaz sannan suka rungume juna.



      Yau wuni zunbur Aziza ta yi a daki ta ki fitowa, bayan sallar isha'i gabadaya suna zaune a parlour suna hira, Aziza kuma na daki tana rike da book amma a zahiri ba karatun take yi ba,tunani takeyi na yadda idan mom ta gayawa Nawaz cewa ita macijiya ce ya zai dauki lamarin, tayi nisa sosai a tunani taji an turo kofar da sallama, amsawa tayi tana ɗaga idonta ta sauke a kan Mom, Mom ta ce

"Lafiya kuwa yau kika wuni a daki Aziza? Ko wani abu na damunki shine kika kasa gaya min?" murmushin yaƙe Aziza ta yi ta ce

"A'a Mom, yau din ne dai nake ɗan jin zazzabi amma ba sosai bane"

"Subhanallahi! Ai saiki faɗi ba wai ki zauna shuru a daki ba, gamu da likitoci har biyu a gida, bari nayi wa Nawaz magana ya zo ya dubaki, ko allura ya miki" zare ido Aziza ta yi sai kuma ta koma ta hau narai-narai da fuska, Mom ta ce

"Ai ba zaki zauna da ciwo ba" Mom ta fita tana ambatar sunan Nawaz, wanda suke lissafin bikin sultana shi da Almazeen

"Na'am Mom" Nawaz ya amsa yana maida hankalinsa ga mom

"Nawaz dan Allah zo ka duba Aziza kayi mata allura, ashe bata jin dadi ne shiyasa ta wuni yau a daki" Sultana ta ce

"Ya Salam! Aziza akwai zurfin ciki wlh,nan fa dazu babu kalar tambayarta da banyi ba amma tace min babu komai, dan Allah Bro Nawaz muje ka dubata"

"To ba ga Al'Mazeen ba" Nawaz ya fada yana shagwabe fuska yana kallon Mom, mom ta ce

"E ai naga Al'mazeen din nace kai kaje ka dubata, idan kuma ba zaka dubata ba sai ka gaya min na cewa Son yaje ya duba min ita" Nawaz ya miƙe yana fadin

"Yaushe na isa, yi hakuri Mom luv ɗina, yanzu kuwa zan dubata, Sultana je ki dauko min box ɗina" Sultana ta amsa da to ta fice da gudu, shi kuma ya yi hanyar dakin,yana zuwa ya tura kofar ya sameta kwance ta zubar da gashinta a kan pillow, a ransa ya ce

"Wai idan wannan gashinta ne ma sha Allah" sai da ya yi gyaran murya kafin ya yi sallama, da sauri Aziza ta mike tana jan hularta dan ta rufe kanta, tana saka hular wanda bai rufe mata gashi ba sauran ya kwanta a kafaɗunta, ta dukar da kai jikinta na rawa, kallonta Nawaz ke yi yana yaba kyawunta a zuciyarsa sai furta ma sha Allah yake yi, har Sultana ta shigo dakin tana masa magana amma bai ji ba, sai da ta tabosa kafin ya juyo, dariya Sultana ta hau maqalewa tana miƙa masa box din, ganin haka ya dalla mata harara ba shiri ta hadiye dariyarta, murya can ciki yace

"Me kike ji a jikinki?"

Murya na rawa Aziza ta ce

"Amm.....uhum......zazzabi ne sama-sama" 

"Kinci abinci?"

"E naci"

"Tun yaushe?"

"Tun karfe biyu" 

"Na rana?"

"E"

"Baki da hankali ne! Taya zaki zauna da yunwa bayan baki da lafiya! Ko baki san shima wani babban ciwon bane! Sultana je ki kawo mata abinci yanzun nan taci a gabana, na duba na gani allura zan mata ko magani zan bata" jin ya kira sunan allura yasa Aziza ta ɗago, nan hawaye suka b'alle kamar an buɗe pampo, cikin fuskar tausayi ta ce

"Dan Allah Hamma Nawaz zan sha magani amma banda allura,bana son allura" ta hau masa magiya tana kallonsa amma shi idonsa a kwayar idonta yake yana kalla bugun zuciyarsa yana kara tsananta, da kyar ya dauke idonsa a kanta ya juya baya,   sultana ce ta shigo da plate da abinci da ruwa ta mikawa Aziza dake kuka wiwi, Nawaz ya ce

"Na fa tsani kuka, kici abincin nan idan baki son allura,bana son shirme, idan kuma baki ci ba alluran zan miki" jin haka yasa Aziza fara ɗurawa cikinta abinci, sai da taci rabi ta kalli Sultana da tayi shuru kamar bata wajen, ta ce

"Anty sulty na koshi, Hamma Nawaz bani maganin" kallon Sultana yayi babu alamun wasa ya ce

"Karba plate ɗin ki fita da shi" karba sultana ta yi ta fita,sultana na fita ya hau jan ruwan allura ganin haka yasa Aziza fashewa da kuka tana ba shi hakuri kar ya mata allura, bata so ko kaɗan karfe ya huɗa jikinta kasancewar tana da jikin maciji hakan zai iya mata illa dan karfe ne zai huɗa jikinta,maciji kuma baya son tab'o, ko kaɗan Nawaz bai damu da kukanta ba duk da yanaji har can kasar zuciyarsa, ya rasa meyasa yake jin tausayin yarinyar, bai so ko kaɗan yana mafarkinta a mugun yanayi, bayan ya saita alluran ya nufeta, da sauri Aziza ta miƙe ta diro a gadon ta hau ja da baya, ihu ta saka zata gudu yasa hannu ya jata, Mom da Sultana da Almazeen da suke parlour suka jiyo ihun Aziza da sauri suka tashi suka yo dakin da gudu, suna shigowa suka samu Aziza da Nawaz sai zagaye daki suke yi, Mom tace

"Miye haka me zan gani?" ganin Mom yasa Aziza rugawa da gudu ta buya bayan mom, tsaki Nawaz yayi yasa hannu ya jata a bayan Mom yana fadin

"Mom ai kinga irinta, bana son hidiman yarinta wlh,allura fa zan mata amma kalli yadda ta sakani zagaye daki sai kace wacce zan zare ranta!" 


 

"Haba Nawaz! Miye haka sai kace ba likita ba, ka lallabata mana ka bita a hankali, Aziza ki tsaya kinji? idan ya miki zakiji sauki, kinga yau kin wuni a daki ga jikinki da zafi, bana son ina ganinki a haka kinji?" girgiza kai Aziza ke yi tana fadin

"Mom zai min illa!" 

"To dan Allah fa kiji mom, wai zai mata illa, taya allura zai miki illa ana shirin nema miki lafiya" yana faɗi ya haɗata da jikinsa ya matseta,a karfinta na nml mutane ta kasa kwace kanta, sadakarwa tayi, jin ya matseta ya danna mata allura yasa ta ƙanƙameshi tana kara sa kuka, allura biyu ya mata kafin ya saketa ya fita a dakin, Al'mazeen wanda ya ƙura mata ido yana kallonta ya fita ya bar su Mom da sultana suna rarrashinta, cikin kuka ta ce

"Mom allura karfe ne,kuma jikina na maciji ne, zai min illa" a tare mom da sultana suka zaro ido,mom tace "Aziza meyasa baki gaya mana da wuri ba? Subhanallah! Yanzu me zai faru?" girgiza kai Aziza tayi jiri na dibarta ta zube a jikin mom abun tausayi, hawaye Mom ta goge tace

"Ya Allah, kasa abunda yake zuciyata wanda nake shirin haɗawa ya zama alkairi, Allah kasa ya zama jahadi dani da iyalaina, ya zama silar shiganmu aljanna!"

"Me kike shirin yi Mom?"

"Inaso na saka Yayanki Ya Auri Aziza!" jinjina kai Sultana tayi ta ce

"Mom nima na jima da fara wannan tunanin, dan babu wanda zai auresu yayi wannan jahadin idan ba wani ikon Allah ba,mom ya kamata ki gayawa Yaya tun daga yanzu, sannan dan Allah mom a daga bikina zuwa shekara mai zuwa" wani harara mom ta gallawa Sultana sannan tace

"To je ki gayawa Nawaz" shuru Sultana tayi dan ko giyar wake take sha ba zata gayawa Yayanta Nawaz a daga bikin ba, yanzu sai ya daki banza.




        Aziza zazzabi da kaɗan-kaɗan ya fara rufeta, ga shi abunda take so babu shi a cikin gari, furen huriri shine zata jiƙa ko ta tauna ganyensa shi kadai ne zai dawo da ita hayyacinta,amma ina zata samu?" haka ta dinga b'ari.



@@@@@@@


         A daren yadda Aziza bata rintsa ba,haka ma Nawaz, wanda da ya rufe ido ita yake gani sadda take kuka tana cewa kar ya mata allura, tausayinta ne ya rufe masa zuciya, tashi ya yi ya kalli Almazeen dake bacci, parlor ya fito ya zauna ya riƙe kansa, ji yake kamar yasa kuka, ko yaje ya ganta ko zaiji sauki a ransa, abunda ya shafe wata uku yanaji a ransa bayaso ya tabbata, baya so zuciyarsa ace ta kamu da son wannan jaririyar yarinyar, sannan meyasa yake mafarkinta tun daga ranar da ta shigo rayuwarsa, meyasa yake ganinta a siffar macijiya? Saurin tashi tsaye ya yi, tare da naushin iska, a fili yace

"Kamata ya yi ace na tsaneki, dan kin takurawa rayuwata da yawa! Tsawon dare bana bacci duk sabida dake! Why! Why! Why Azizaaa!!" ya faɗa yana rike kansa da yakeji kamar zai rabe gida biyu, anan ya zauna har asuba,   bayan Almazeen ya farka ya shiga bathroom yayi alwala ya fito parlor nan ya ga Nawaz yashe a parlor, kallonsa ya yi ba tare da ya yi magana ba yace

"Nawaz kayi alwala kazo muje sallah" Almazeen na fadi ya fice, shima Nawaz din alwala ya yi ya bi bayan almazeen bayan sun dawo daga masallaci, Al'mazeen ya hau shiri, yana shiri yana tambayar meke damun Nawaz, Nawaz yace masa ba komai, bai takura ba ya kammala shirinsa, takwas ya shiga ya yiwa mom sallama, mom tace dan Allah kafin ya wuce ya shiga ya duba Aziza ya bata magani dan jiya bata rintsa ba jikin ya yi tsanani,da to Al'mazeen ya amsa.


    Aziza kwance sai b'ari takeyi jikinta mugun zafi, hannunta Almazeen ya kama ya ga wani zobe a hannunta a ƙaramin yatsarta na karshe, bai damu ba, ya gama dubata ya ajiye mata magunguna sannan yamusu sallama ya tafi.



      Har wajen mota Nawaz ya raka amininsa tare fadin sai sunyi waya Allah ya tsare, sai da Al'mazeen suka fice kafin Nawaz ya shiga ya gaida mom idonsa a kumbure shima dan baiyi bacci ba ga kansa dake ciwo,cikin kulawa mom ta ce

"Nawaz lafiya kuwa?"

"Mom kaina ke ciwo jiya banyi bacci ba" 

"Subhanallah! Sannu Allah ya baka lafiya, ka sha magani ka kwanta"

"To Mom" ya faɗa yana tashi, yana so ya tambayeta Aziza amma yakasa,dan haka ya koma part dinsa ya sha magani ya kwanta.


    bayan ya fice wayar Mom ya dauki ruri, tana dubawa ta ga malamin da tasa ya mata istihara a kan Nawaz da Aziza, da sauri ta daga suka gaisa cikin girmamawa,nan ya shaida mata akwai alkairi mai girma da yardan Allah tsakanin Nawaz da Aziza, shi gwargwadon abunda ya gani kenan, godiya sosai mom ta masa nan ta kara jin karfin guiwa.



      Dakin Aziza taje ta samu jikin nata ya kara tsanani, sultana idonta ya zazzago tsananin tashin hankali, Sultana tace

"Mom a gayawa Yaya ko akwai maganin da zai bata, kar ta mutu"

"Sultana shima baya da lafiya idonsa a kumbure da kyar yake budewa shiyasa ban gaya masa na Azizan ba,mu bari nasa ya sauka tukunna" Sultana ta ce

"Mom,anya kaddaran Yaya ba a haɗe yake da na Aziza ba kuwa?" shuru Mom tayi, sai zuwa can tace

"Allah ka bayyana mana Azima cikin sauki Ya Allah, Allah ka jinkirtawa wannan baiwa taka Aziza,duk da tana karama da kananun shekaru amma tana da hakuri da tawakkali da juriya" hawaye Sultana ta goge ta fice a dakin, khalil ta kira a waya tana kuka tana roƙonsa a kan a daga bikin nan kar ayi nan da wata daya, dalili ya fara tambayarta amma ta kasa gaya masa,inda a karshe ya katse wayarsa dan ya kasa gane me Sultana take nufi ko dai ta daina sonsa ne?.



       🐍🐍🐍🐍



Yau fa Azima murna tun daga baka har kunne, Al'mazeen na hanya, bayan su Hadiza sun gama shirya masa abinci ita kuma ta gyara masa part dinsa tas, ta zo shiga cikin kitchen ta hangi Maman Hanan akan abincin Al'mazeen tana barbaɗa masa magani, girgiza kai Azima tayi, ta bar wajan ba tare da maman hanan ta ganta ba,amma tayi alkawari ba zata bari al'mazeen yaci abincin nan ba.


 


        Goma da rabi motar Al'mazeen ta yi parking a harabar parker motoci, ya jima a motar yana sauke ajiyar zuciya kafin ya fito, nan ma aikatan gidan suka hau masa sannu da dawowa tare da gaya masa sunyi kewarsa, cikin parlour ya wuce nan Maman Hanan da Maman Beenah suka hau murna suna masa oyoyo, a hankali ya russuna ya basu girmansu ya gaishesu sannan ya fara haurawa samansa, Maman Hanan ta ce

"Fuskar mutum kamar fura a dame kullum, Hadiza! Zo ku kai masa abincinsa sama"


       "Ba zai ci wannan abincin ba, wani zan dafa masa!" saurin juyowa Maman Hanan da Maman Beenah sukayi suna kallon Azima da kanta ke duƙe da lullubi, cak Al'mazeen da zai hau sama yaja ya tsaya jin kamar ya san mai irin muryar, Maman Hanan ta ce

"Sabida me ba zai ci ba?"

"Sabida bana da bukatar yaci, a bai wa wasu su ci,ko a ajiyewa su Hanif su ci idan sun dawo!" a daqile Azima ke magana, da sauri Al'mazeen ya dawo da baya,nan kuwa ya ganta sanye da bakin abaya itama fuska a lullube, yatsar hannunta ya kalla ya ce

"AZIZAAAA!?" a mamakin ce.



         🍃🍃🍃🍃


*PAID.*

🅿️=5️⃣9️⃣↪️6️⃣0️⃣




"To yanzu miye mafita? Wani sharrin satan zamuyi mata?" cewar Maman Hanan, Maman Beenah ta ce

"Yanzu ke Maman Hanan idan kikace ta sace miki abu za ace dan ta murɗewa Hanan hannu ne, Al'mazeen ba zai yarda ba, tunda su Sady suna hanya mu jira isowarsa kafin mu yanke shawara" Hanan dake kuka ta ɗago tana kallon hannunta da shati ya fito raɗa-raɗa ta share hawaye tana fadin

"Wlh sai na koya mata hankali, zata gane shayi ruwa ne,ita har ta isa! Wacece ita! Waye ubanta! Tana 'yar aiki!"



"Bar ta ubanta zamu ci dan naga abun nata ya fara wuce gona da iri" Beenah ta ce

"Hummm! Ku ga sadda tazo gidan nan ba ruwanta, amma daga dawowar Al'mazeen sai wani falli take ji da shi, ga shi kullum tana part ɗinsa da yana nan da baya nan, anya kuwa babu wani abunda yake gudana a tsakaninsu?"


       "Ai dama ba banza ba! kinga dai yadda Al'mazeen ke shakkarmu..."


"A'a fa Maman Hanan ba dai shakkarmu ba,yana dai kyalemu kasancewarsa mai biyayya yana shanye duk baƙinciki da takaicin da muke ƙunsa masa" Maman Beenah ta katsewa Maman Hanan hanzari ta hanyar faɗin haka.



       "To ai ga shi yanzu wannan 'yar banzar mai aikin tana shirin hanamu rawar gaban hantsi 'yan kuɗaɗen da muke karba a wajansa wannan shegiya 'yar banzan tayi ƙyam-ƙyam" Maman beenah zata kuma yin magana suka jiyo sallamarsu Sumy da Sady da karfi sai kace zasu tada gidan, kafin su Maman Hanan su sauko Azima ce ta fara sauƙowa ta fito part din Al'mazeen hannunta dauke da kaskon turaren wuta da alama saka masa tayi, wani kallo Sumy da Sady suka bi Azima da shi har ta gama saukowa tayi hanyar waje ta kofar baya ba tare da tasan Allah ya yi wasu halittu a wajan ba, Sumy ta ce

"Tooo! Ina aka samu balarabiya ko ba india?" yatsine fuska Sady tayi ta ce

"Oho" saukowarsu Maman Hanan ne ya katsewa su Sumy maganar da sukeyi, nan aka hau musu sannu da zuwa, sai amsawa sukeyi a gadarance,Sumy ce mai gajan hakuri ta ce

"Anty (maman Hanan kenan) wacece wata 'yar dogowar yarinya fara ,tasa riga da wando da wani baƙin glass sai kace ba india?" Maman Hanan tayi tsaki tana bin Sumy da Sady da kallo ta ce

"Yoo ai ita ce wacce muke gaya muku Azima" 


"Kan Uba! To ma uwarwa ta yiwa wannan shigan a gida tana mai aiki uban wa ya bata wannan damar!?" cewar Sumy, Hanan ta share hawayen da suka gaza tsayuwa dan ji take kamar hannunta zai fita ta ce

"Ba dai yanzu ku ka iso ba? To tunda Al'mazeen ya dawo take ji da iskanci iri da kala"


"son Al'mazeen din take yi ne?" cewar Sady tana tabe baki, Beenah tace

"Kar dai har kin fara kishinsa?"

"Wa? Ni? Allah ya kyauta! Al'mazeen baya raina sam, dan haduwa ya hadu amma ni zan auresa ne dan kudinsa kamar yadda ku ka ce Anty,zamu auresa ne sabida kuɗinsa da mun kwasheshi sai ya sakemu"


"Kai kuyi magana a hankali a ƙasa fa muke, kuma wannan shegiyar tana nan, to ma yanzu kin san me ya faru?" cewar Maman Hanan, nan ta basu labarin tsiyar da Azima ke yi a gidan, ta kara da murɗewa Hanan Hannu da Aziman tayi da safe sadda Al'mazeen zaije aiki, har Hanan na nuna musu hannunta da ya kumbura, haɗa baki Sumy da Sady sukayi suna fadin zasu ci Uban Azima, suna kan meeting din yadda zasu korata a satin nan sai gata ta shigo tana shirin sake wucewa kamar dazu Sumy da ta hangeta tun farkon buɗe kofa ta ce

"Keee ƙidahumar jeji jikar shanuka! Zo nan" wani birki Azima taci ta tsaya cak ba tare da ta dawo ba, Sady ta ce

"Dake ake ballagaza!" cije baki Azima tayi idonta na sake rinewa, rintse ido tayi ta hadiye takaicinta sannan ta dawo da baya ta tako tazo gabansu ta tsaya, Sumy ta ce

"Keee! Cire wannan bakin glass din idon naki!"


     "Ke a wa fa!? idan naki cirewa wata uwar zakiyi!?" Azima ta faɗa tana tinkaro Sumy, ja da baya sumy tayi, ganin haka yasa Maman Beenah faɗin

"Kee Azima! ba kya ganin baki ne? Ki dau kayansu ki haura musu da shi sama a wannan dakin da Hadiza ta gyara dazun nan"


"Su ɗin kutare ne? ko basu da hannun dauka ne? idan sun ga dama su da kayan nasu su kwana a nan" Azima na gama faɗi ta juya tana taku jikinta na langwasa harta taka step daya ta juyo ta kalli Sumy ta ce

"Kee kuma! karki kuma kuskuren fadin cewa na cire wannan madubin, dan kuwa kallo daya ake yiwa idanuna! idan kika kallesa baki kara kallon komai a rayuwarki!" Azima na fadi ta hau sama fuuuu! Aka bar su Maman Hanan a daskare.



        "Ahaf kun gani da idonku ko?" cewar Maman Beenah, Sumy ta ce

"Na san yadda zanyi da shegiya bari Al'mazeen din ya dawo" ta fadi tana hawa sama, Beenah ta kira su Hadiza suka dauki kayan su Sumy suka haura musu da shi tunda Hajiya Azima Banju tace bata hawa da shi.



        @@@@@


Yau kasancewar ya wuni a office yana tunanin Azima yasa bai yi wani aikin komai ba, ga shi yana son magana da ita kuma ba hali tunda ba waya ne a hannunta ba,kuma tin daga ranar da ya dawo ya fahimci babu jituwa a tsakaninta da mutanen gidan balle yace zai kira alfarma su ba shi Azima yayi magana da ita, shawaran da ya yanke shine idan ya tashi a office ya biya ya siya mata waya sai ya koya mata yadda zata dinga amfani da shi.



     Bai fara aiki da wuri ba sai wajan hudu ya fara duba marasa lafiya shiyasa yau bai tashi da wuri ba sai wajan takwas da rabi, bayan ya tashi sai da ya biya ya siyawa Azima waya tukunna ya nufi gida.



      A lokacin Azima na parlour hankalinta tashe tana ta aikin safa da marwa sabida ganin yau Al'mazeen bai dawo da wuri ba, tana cikin wannan zullumi ya yi sallama ya shigo, wani ajiyar zuciya ta sauke wanda bata san lokacin da ya fita ba, da sauri ta karasa gabansa tana tura baki ya ce

"Yi hakuri 'yar fullo" 

"To yau ina ka tsaya kasa duk na damu! Nifa tinda nake a rayuwata ban taba damuwa da damuwar kowa ba sai a kanka na rasa dalili! Ban taba sanin miye tunani ko damuwa ba sai a kanka, abunda na sani a rayiwa shine daukar fansa!"


      "Fansa kuma!? To kiyi hakuri yau aiki ne ya min yawa a office,nima wuni nayi ina tunaninki kuma babu ta yadda zanyi magana dake shiyasa na siya miki waya da zan dawo, zancan kuma nuna damuwa a kaina ba mamaki ni ɗin na musamman ne!" gaban Azima ne ya faɗi amma da shike tana zumudin waya yasa bata bada hankalinta a kan fadin da ya yi cewa shi ɗin na musamman bane.



     Wayar ya nuna mata amma yace ba zai bata ba har sai ya mata chajinsa, jakar hannunsa ta karba, ya yi gaba tana binsa a baya idonta kyam a kansa,gani take kamar akwai wani mugun haske dake fita ta ƙeyarsa tare da wani farin mutum na mata kwala

"MAGAJI BAWA!" ta faɗa tana shirin kaiwa keyar Al'mazeen duka, juyowar da yayi ne yasa tayi saurin maida hannunta, ya ce

"Mene? Waye kuma Magaji Bawa?" haɗe rai Azima tayi ta ce.

"Tsohon abokin gabana ne"

"Abokin gaba kuma?" Al'mazeen ya faɗa cike da mamaki.

"Karka fiye tambaya" ta fada tana wucewa gabansa ta rigasa hawa, duk abunda sukeyi a kan idonsu Sumy:Sady:Maman Hanan:Maman Beenah:Hanan:  Sumy tace 

"Muje kasa ku ga yadda zan tsara wasan nayi cilli da shegiya wajen gate a daren nan" suka sauko a tare, suna saukowa, Sumy ta ware murya tana kwalawa Azima kira sai kace gidan ke ci da wuta, a lokacin Azima na tsaye a kan Al'mazeen dake jona mata wayarta a chaji, jin kira kuma Al'mazeen ya gane murya ya ce

"Sumayya? Sun zo ne? To meyasa take kiran Azima haka?" Azima wacce zuciyarta ya tunbatsa jin yadda ake kiran sunanta abun ya bata haushi, a tare suka sauko da Al'mazeen,ya kalli Sumy ya ce

"Sumy, Sady, yaushe ku ka zo? Sannan meya faru kike kiran Azima haka?" 


        "E mana,mun zo dazu, da muka zo na ba wa Azima kayana ta haura min da shi sama, na zo da sarƙata ta gwal amma yanzu na duba ban gani ba, da na shiga dakin kuma na ga Azima a jikin kayana ta bude min akwati har nake tambayarta me take yi sai ce min tayi babu komai nayi hakuri, ka dai ni ba saninta nayi ba banda yau" Maman Beenah ta ce

"Anjima ana yi mana dauki ɗaɗdai, amma dai bamu taba zarginta ba, kasancewar mun yarda da ita"


"Haka ne kam, nima na nemi sarkata wanda ka siya min ɗin nan ban gani ba" cewar Hanan.



     Al'mazeen a rayiwarsa ya tsani mai halin b'era dan haka ya ɗago ido yana kallon Azima wacce jikinta ke rawa idonta sun ƙanƙace sun kara rinewa, harta hannunta ya fara sab'ulewa yana zama blue, cikin wani irin murya Al'mazeen ya ce

"Azima da gaske ne? Kin dauka mata sarƙa?"  


      Wani ihu da gurnani Azima tayi tasa hannu ɗaya ta damƙi wuyar Sumy, nan Sumy ta hau jijjiga kai jin an shaƙe mata magudanar numfashi, cikin daga murya Azima ta ce

"Faɗi gaskiya ko yanzu ki jiki a kabari! Kikace na sace miki sarƙa! Nayi miki kama da b'arauniya! Da ku ka sakani daukar kayanku na dauka!?" duk maganar da Azima take yi tana rike da makogoron Sumy wacce ke mutsil-mutsil idonta har ya fara zazzagowa, su Maman Hanan sai dambe sukeyi da hannun Azima a kan ta saki wuyar Sumy amma sun kasa koda motsi ne da hannun Azima, harta Al'mazeen ya kasa b'anb'are Azima daga cikin Sumy, cikin in-ina da shaƙewa gami da fitar hayyaci Sumy murya irinta wa inda suka sha azaba ko suke sha ta ce

"Wallahiii.....karya......na.....ke...yi...."



        🍃🍃🍃🍃


Post a Comment for "AZIZA DA AZIMA 51-60"