HALIN GIRMA 6-10
*HALIN GIRMA*
 6
*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi
08184017082 or 09134848107*Â
_ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL PEOPLE!! ZAFAFA BIYAR
FAMILY💯💯🙌ðŸ½â¤ï¸_
_MUNGODE DA ZABIN LITTAFAN ZAFAFA BIYAR. ALLAH YA KARA BUDI YA KUMA BAR ZUMUNCI_
_KAMAR KO DA YAUSHE, WANNAN KARON MA MUNZO DA KOKON BARAR
YOUTUBE CHANNEL DIN YARON MU, SUDEIS MASOYI KUMA MAKARANCI, MAHADDACIN
ALKUR’ANI MA GIRMA_
_WANNAN KARON MA DAN ALLAH A TEMAKA ADANNA WA CHANNEL DINSA
KARARRWA DOMIN KASANCEWA DA MU A DUK SANDA MUKA DORA FEFAN BIDIYON SA, A
TALLAFA A KALLA A KUMA DANNA MASA SUBSCRIPTION. HAKAN NA KARAWA SUDEIS KWARIN
GWIWAR SAKE DAGEWA YA KUMA KARA KAIMI WAJEN YIN KARATUN SOSAI. MUNGODE
KWARAI💯🙌ðŸ½â¤ï¸_
_GA CHANNEL DIN DAKE YOUTUBE NAN👇ðŸ¾_
https://youtube.com/c/sudaiskura
_Sudais is a young boy who has passion in recitation of the Holy
Qur'an at a very young age._
_Please help him grow his YouTube channel by subscribing and
liking his videos to encourage the little boy. Jazakumullahu khairanðŸ™ðŸ»_
***
Girgiza kai ya hau yi da sauri da sauri.
"Habib aiki na, innalillah wa inna ilaihi rajiun."
"Me ya samu aikin naka?" Mama ta matso da sauri tana
rik'e shi
"Wai sun dakatar dani, babu wani kwakkwaran bayani kawai
wai daga sama ne."
"Innalillah wa inna ilaihi rajiun, zo ka zauna, rik'e shi
Habib ya zauna."
Zaunar dashi Habib yayi, yayi saurin dauko masa ruwa ya mik'a
masa
"Sha ko zaka ji sauki a zuciyar ka, ba wani abu bane babba
in sha Allah, wata yar matsala ce zasu gyara da yardar Allah."
Jujjuya kansa yake ya kasa magana, shi kadai yasan hakan me yake
nufi, shi kadai yasan yadda yake ji a halin yanzu, tabbas idan suka hana mishi
aikin nan sun yi masifar cutar sa, akan me? Me yayi haka da ya chanchanci
wannan hukuncin? Bayan irin kokarin da yake ganin ya rik'e aikin sa, tsawon
lokacin da ya dauka kafin ya samu aikin, da irin wahalar da yasha kafin ya kawo
matsayin da yake, sai yanzu? Daga sama ta ka kawai ace an dakatar dashi?
Innalillah wa inna ilaihi rajiun. Ya sake maimaitawa.
"Kalle ni nan Khalil, karka ce zaka daga hankalin ka akan
abinda kasan baka da iko dashi, kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka, in sha
Allah ba wata matsala bace, kaji?"
Gid'a mata kai yayi kamar karamin yaro, ya kwantar da kansa yana
jin kamar ya zubar da hawaye saboda bacin rai. Shiru sukayi kowa yana jimamin
abinda ya faru, ya ma manta da abinda yake shirin aikatawa. Shigowa Zeenat tayi
dauke da wasu manyan ledoji,uwar ta bita da kallo bata ce komai ba.
"Daga ina kike?" Habib yace yana bin hannun ta da
kallo
"Bashir ne yazo."
Kallon Mama yayi, yaga ta dauke kanta
"Mama fa Bashir din nan naji wasu maganganu akan sa marasa
dadi, ya kamata a duba sosai kafin a barta tana fita wajen sa."
"Bana son maganar nan yanzu, dame zamu ji? Da abinda ya
faru da Khalil din ko da naka zancen?"
Tsuke bakin sa yayi be sake cewa komai ba, ya tashi ya bar falon
ma,
"Me ya samu Uncle Khaly din Mama?"
"Babu komai, ki wuce ki bani waje uwar yan magana."
Da sauri tayi gaba da ledojin ta, ta shige dakin uwar ta rakata
da kallo kafin ta sauke ajiyar zuciya tana tuna abinda ya faru daren jiya ita
da Abban su.
***
"Ya ake ciki da yaran nan?"
"Name fa?"
"Akan maganar yaran da suke zuwa wajen su, Yaya yayi min
magana akai yace ya kamata asan abinda ake ciki, kindai san tsarin gidan nan
ba'a wani daukar dogon lokaci ana zance."
"Eh toh, ita Iman akwai wani wanda yazo."
"Zuwan sa biyu kamar ko?"
"Ashe ka sani?"
"Eh ina sane da komai ai, kinga alamun zasu dai-dai ta ne?
Naga zuwan nasa biyu dududu."
"Toh idan bashi ba waye? Babu kowa ai."
"Khalil din fa?" Yace yana mata kallon mamaki
"Wai Dr bar maganar Khalil din nan, ba da gaske yake ba
wallahi."
"Ana wasa a maganar aure ne Hajara?"
"Shi dai yayi, gwara a tsayar da magana akan wanda yazo din
dan da alama ba da wasa yazo ba."
"Toh shikenan, Zeenatu fa?"
"Eh ita ai Bashir ne dama."
Tashi yayi tsaye yana girgiza kansa
"Ban yarda ba sam, ban amince da yaron ba, binciken da nayi
akansa be min dadi ba, kamar ance min ma kuma yana da mata duk da hakan ba zai
hana a bashi aure ba, sai dai na samu labarin bashi da hali me kyau gaskiya, a
wani labarin ma ance min har zaman prison yayi, sai ki fad'a mata nace banda
Bashir ta kawo wani."
Hankalin ta a tashe tace
" Amma baka ganin sharri akayi masa? Don a hana a
bashi?"
" Akan me za'a masa sharri? Akan wanne dalili kenan?"
Ya tsare ta da idanun sa, sunkuyar da kanta tayi bata ce komai
ba, tsoron yadda za'a kwashe da Zeenat din take domin ta san yadda ta saka
Bashir din a ranta, gashi babu laifi yana mata hidima sosai, hakan ya saka
Maman sake yarda dashi da yar ta ta.
"Bari na shiga ciki Anty." Khalil yace yana mikewa, ta
daga masa kai kawai ya wuce ya barta tana cigaba da tunanin yadda zata bullowa
al'amuran.
***Tana zaune a falon Gajin tana tunanin abinda ya faru tsakanin
shi da Uncle Khalil, wayarta dake saman cinyarta tayi kara, ta kalli wayar
ganin bakuwar number ya saka ta tashi, ta wuce zuwa bedroom din Gajin ta daga
tana zama a gefen gadon ta
"Assalamu alaikum." Tayi sallama cikin muryarta da
tafi komai tafiya dashi, lumshe idon sa yayi ya bud'e a hankali ya amsa
sallamar ta ta
"Wa alaikisalam..."
"Ina wuni?" Ta gaishe shi jin muryar sa
"Lafiya lou Mi Love, na barki lafiya?"
"Alhamdulillah." Tace a kunyace ganin shi kai tsaye
yake maganar sa.
" Kina jina Zahraaah na? "
" Na'am?" Tace tana mike kafafunta
" A zahirin gaskiya ba da wasa nazo ba, da gaske nazo neman
auren ki ba kuma naso a dauki wani dogon lokaci in sha Allah, ni din dai ba
wani bane kin dai ganni, bawan Allah ne me neman amincewar Fatima Zahra, ina
fatan zaki bani dama dan Allah!"
" Hmm..." Ta sauke ajiyar zuciya maganganun sa na taba
ta, me zata ce toh? Da gaske take jin ya kwanta mata duk da taga alamun ba wani
shi nne dashi ba, amma sai taji yadda yake abu kai tsaye ya birgeta sosai, babu
karya straight kawai yake maganar sa, bayan haka da gaske take son matsawa daga
wajen Mama, ko ba komai ta samu yanci itama.
"Baki ce komai ba?"
"Allah ya shige mana gaba, Allah ya zaba mana abinda zai
zamar mana alkhairi gaba daya."
Wani irin dadi yaji ya shige shi, ya rufe idon sa, ya dau yan
sakanni yana jin sonta na sake ruruwa a zuciyar ta, yana tuna tsawon lokacin da
ya dauka yana dakon soyayyar ta, a lokacin da shi kansa be san me ake nufi da
so din ba.
 Mahaifiyar sa 'ya ce ga sarkin Kano kuma shi jika ne a
gidan, hakan ya saka yake da alaka me karfi da garin na Kano duk da mahaifin sa
da mahaifar sa Adamawa-Yola ne, rayuwar sa bayan ya tasa yayi ta ne tsakanin
Kano da Adamawa, shiyasa babu in da be sanin a Kanon ba, yake kuma jin kamar
yafi zama comfortably a Kanon, musamman da bashi da son hayaniya sosai sai nan
din yafi zamar masa peaceful wajen hutawar sa.
  Akwai ranar da ya fito shi da abokin sa Musaddik,
suna tafe a mota hanya ta biyo dasu ta area din su Fatima, a lokacin ya ganta
duk da lokacin ba ta kai yanzu ba, be kuma taba jin abinda yaji akanta, shiyasa
ya nace a lokacin suka yi ta bin ta har suka ga gidansu, suka kuma yi tambaya
akan ta da komai. A lokacin yaso ya shigo da karfin sa, sai dai wani labari da
ya samu ya sauya masa tunani da shawara, ya kuma yanke ma kansa shawarar da
yake ganin itace zata daga masa darajar ta, a ranar da gaskiya ta bayyana.
 Musaddik be aminta da shawarar ba duba da gidajen da
Muhammad din ya fito, amma haka ya kafe akan bakansa, shiyasa ma kawai Musaddik
din ya kyale shi amma fa kullum cikin masa korafi yake.
  Bangaren aikin sa zai iya cewa yana cikin yan
gata da sai abinda suka zaba da inda suka zaba zasu zauna, kasancewar gaba daya
k'asar babu in da kakan shi mahaifin Ammi zai nemi alfarma ba'a masa ba, sannan
gefe guda mahaifin sa yayi sunan da zaka yi mamaki sosai.
 Duk da hakan be daina aikin sa ba, sai dai babu wani
matsi ko takura tun ma be kai matakin captain ba, balle yanzu da yake da rank
me girma.
"Kinsan me?"
Yace yana gyara kwanciyar sa sosai, sanda Musaddik ya murda
handle din dakin ya shigo bayan yayi knocking ya bashi izinin shigowa.
"Ya Iman Abba na kira." Marwan ya fad'a mata yana
tsaye a gefen ta, hannun sa ta riko shi kuma yace
"Yaya Iman ki gaida min da Abba, idan kin dawo ki kira ni
please, zan fad'a miki wani abu." Murmushi tayi me sauti yana jiyo ta
"Ok bye." Ta ajiye wayar ta rik'e hannun Marwan din
suka fito a tare..
"Yaushe Abban ya dawo?"
"Be dade ba, yana falo yana cin abinci."
"Owk." Tace suna karasawa.
" Abba barka da gida."
" Barka da Uwata, na dawo ban ganki ba, da zan fita ma ban
ganki ba, shiyasa nace ya kira min ke."
" Ina wajen Gaji Abba."
" Eh haka maman ku tace, amma ai na ganki dai ko?"
K'asa tayi da kanta Mama ta karbe
" Tafi son zaman chan yanzu ai."
" Kuna shan hira da Gaji kenan ko?" Yace yana murmushi
" Ko kuma tafi jin dadin tayi wayarta a chan ba, ko
'yata?"
Maman tace cikin son a sako zancen Moh, shiru kawai Iman tayi
Abba ma ya girgiza kansa kawai
"Allah ya kyauta, kinci abinci dai ko? Nasan ki da wasa da
cikin ki."
" Naci Abba."
" Toh karbi nawa ki kara, nasan ba da wani yawa kika ci
ba." Ya tura mata plate din gabanta
"Maza kirawo min zeenatu Marwan."
Gaban Mama ne ya fadi, ta zamo daga kujerar tana sakin salati a
ranta. Tana gyara daurin dankwalin kanta ta shigo falon, ta zauna a kusa da
Iman ta gaida Abban.
"Abinda yasa na kiraku ke da yar uwarki, akan maganar yaran
da suke zuwa wajen ku ne, duk da shi wanda yake zuwa wajen Uwata bansan shi ba,
inaso ki sanar dashi yazo yaga Yaya kafin ya cigaba da zuwa."
Abincin da ta diba ta hadiye da k'yar gabanta na dukan uku uku.
"Ke kuma..." Ya nuna Zeenat
"Ki kawo wani daban ba yaron nan Bashir ba, ki sake dubawa
a cikin sauran ki nemo wanda ya dace da nasabar gidan nan, me Halin Girma
mutumin kirki, kinji na fad'a miki."
Waro ido tayi cikin tashin hankali ta kalli Abban
" Hakan shine abunda ya kamata muyi a matsayin mu na iyaye,
dan haka kiyi hakuri."
Tashi yayi, ya kalli Iman da tayi tsam a wajen, ya juya ya kalli
Mama yayi mata alama da ido sannan yace
" Na fita!"
Da k'yar Mama ta bud'e baki tace
" Adawo lafiya."
" Allah ya kiyaye Abba." Iman tace yana kokarin fita
" Amin." Ya amsa kafin ya fice gaba daya.
Wani kallo Mama tayi mata, tayi kwafa ta mike sannan ta kalli
Zeenat da ta soma kuka wiwi tace
" Ki same ni a daki."
Kamar wadda zata fadi saboda kuka haka ta tashi, ta kusan fadowa
Iman din aka, a ranta tana jin babu abinda zai hana ta auren Bashir, duk tashin
hankalin da za'a yi sai dai ayi shi, amma babu wanda zai hanata abinda zuciyar
ta take so.
***Cikin wani yanayi bayan ya gama jin komai ya gaida Abban da
ya fito, yayi masa adawo lafiya sannan ya juya zuwa wata hanyar ya fasa shiga
dakin. Idan har abinda yaji gaskiya ne, wannan me zubin yan boko haram din aka
bawa damar turowa kenan, ba zai taba yarda yayi biyu babu ba, ba aiki ba Iman,
shi zai fara isa wajen Yayan idan yaso ayi wacce za'a yi, yasan ba zasu taba
hanashi ba, domin shi ya chanchanta ba wani bare ba, da ba'a san daga ina yazo
ba.
***
Tashi zaune yayi zaune bayan ya ajiye wayar, ya kalli Musaddik
da ya zauna a gefen sa
"Ya akayi ne?"
"Na shigo kana ta waya"
"Eh wallahi, ni da Wifey ne."
"Wifey kuma? Yaushe kayi aure ba labari?"
"Bana son iskanci, kasan wa nake nufi ai."
"Toh ai sai kace aljanar ka da ka nacewa, amma kace wifey
bayan bamu shafa fatiha ba."
Jefa masa dan pillow din da yake kusa dashi yayi
"Dan iska, ka jira ka gani ai."
"Wai karo maka yaran ka akayi ne? Naga gate din naka ya
sake cika ga wani uban iyayi kamar basu san mutum ba?"
"Sai hakuri kawai, ya ake ciki ne?"
"Normal, shiru ne ko ina, ya ka baro su Ammi?"
"Lafiya lou wallahi, Bubu yayi min maganar aure ai, nace
zan zo musu da magana in less than a month, kafin nan mun gama daidaitawa da
Wifey."
" Ya zakayi toh idan aka ce ka turo?"
" Shine matsalar wallahi, amma zan san yadda zan dai."
" Toh Allah ya sa muji alkhairi angon Fatima."
" In Sha Allah." Yace yana dafe saitin heart dinsa,
dai-dai lokacin kiran ta ya shigo wayar, yayi saurin dora hannun sa akan baki
alamun Musaddik yayi masa shiru, wurga masa pillow da ya jefe shi dashi yayi ya
fice yana cewa
" Ka same ni a kasa idan ka gama zan kalli laliga."
Da kai ya amsa masa yana kara kiran a kunnen sa
" Nagode sosai da kika kirani, na zata ba zaki kira
ba."
" Haba! Zan kira ai."
" Nagode sosai, bari na kira ki toh."
" A ah ba komai, muyi magana akwai kati kar a cinye maka
naka kai kadai."
Murmushi yayi me sauti
" Kinga kuma 200 nasa dazu har ta kusa karewa, bari na fita
sai na sake siyo ko na 100 ne sai na kiraki."
" Allah ba sai ka fita ba, ga sanyin nan da ake yi
ma."
" Shikenan Nagode."
" Me kikayi a wajen Abba."
" Abinci naci."
" Iyeeeee, yar gata! Har abinci abba ke baki? Allah sarki
ni."
" Kaima ai dan gata ne."
" Ni din? Tab ni ba dan gata bane, gashi ke har abinci Abba
yake baki, niko kin ganni a dan shago na sanyin nan duk a kaina zai kare, babu
me tausayi na ya bani abinci."
" Allah sarki."
Tace cikin tausayawa, da ace sun saba sosai da tace yazo ya
karbi abinci, ta hada masa har da abin rufar ta idan yaso ita sai ta samu wani
wajen Gaji, amma ba zata iya ba, sai kawai tayi shiru tana tunanin ta yadda
zata fad'a masa Abba yace yazo ya samu yayansa.
"Dama... Dama...Abba ne yace."
"Me?" Yace cikin zakuwa
"Wai ka fara zuwa ka samu Abba (Baban yayansu) ka nemi
izinin zuwa kafin ka cigaba da zuwa."
"In Sha Allah zanzo, yaushe ake samun sa a gida?"
"Kamar da yamma haka zuwa bayan Magriba."
" Ok in sha Allah zanzo, nagode sosai da wannan karamcin na
Abba, duk da ni din ba kowa bane, amma har aka bani wannan damar, nagode
Sosai."
" Ni dai dan Allah ka daina cewa kai ba kowa bane, a
islamiyya an fad'a mana, babu wanda yafi wani sai wanda yafi tsoron
Allah."
" Haka ne, wai kinga ina nufin ni din ba kudi ne dani ba,
amma..."
" Kudi ba sune farin ciki ba ai, wadatar zuciya itace
mutum, dan Allah ka daina wannan maganar kana sani jin wani iri."
"An daina ta daga yau, ba zaki sake ji ba, kiyi hakuri idan
na bata miki rai."
" Babu komai."
" Yawwa, kiyi min murmushi naji toh."
Shiru tayi
" Kinji mana, pleaseee."
Yace sai kuma yayi saurin daidaita kansa ganin zai zarme da yi
mata shagwaba har ta ranfo wani abu
"Nayi fa, ai baka gani na."
"Tam shikenan, idan naje na nemi izini wajen Abban mu,
zanzo na gani a zahiri."
"Uhum." Tace tana jin zuciyar ta na sake nutsuwa
dashi, ko ba komai ta samu wani da yake dauke mata damuwar ta da kadaici
"Bari na barki haka kar na cinye miki kudi..."
"Goodnight, sweet dreams of meeeee."
"Allah ya tashe mu lafiya." Tace tana yin dariya k'asa
k'asa
"Amin ya Allah, bye inji turawa."
"Bye." Tace mishi ta ajiye wayar.
"Yess!" Yayi tsalle ya dire kafin ya fice yana saka
hannun sa cikin aljihun dogon wandon sa. A falon ya tarar da Musaddik da tea
yana sha, ya zauna ya diba shima yana murmushi.
_"You don make me fall in love, you don make me fall in
lov, Baby I love you."_💕
Dariya sosai Musaddik ya saka
" JJC kawai, zaka cika mana kunne da wata wakar ka."
"Idan fitsari abin banza ne, kaza ma tayi mana?"
"Okh haka ne, shikenan ai.Wait and see. Ni yanzu ba wannan
ya kawo ni ba, me yasa ka saka aka dakatar da gayen nan ne?"
Tashi yayi rik'e da cup din yana bata fuska
"Kaga dacewar ya nemi irin abinda nake nema?"
"Kamar ya?"
"Ba'a takara da Sarki, be chanchanci karawa dani ba, bashi
da qualities din da zai iya neman auren ta, cika bakin sa ya saka na nuna masa
iyakar sa, anyways warning ne kawai, zan sake gwada hankalin sa , idan yayi
hankali fine, idan be ba kuma sai muje a haka, sai a karbi application din
wasu."
Gid'a Kai Musaddik yayi be sake cewa komai ba, yasan waye Moh,
yasan bashi da matsala ta kowanne bangare, amma bashi da dadi idan har kayi
crossing din sa, zai nuna maka shi din babba ne a cikin manya!
"Ka fahimta dai ko?"
"Yes Captain!" Ya mike sannan ya sara masa.
"Aje waya!" Yace masa suka kwashe da dariya a tare.
HALIN GIRMA
Hafsat Rano
WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da
wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na
MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu
dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma
kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN
NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL👉ðŸ¾
Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉ðŸ¾hafsat
rano_*
*_TAKUN SAƘA👉ðŸ¾billyn
abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉ðŸ¾miss
xoxo_*
*_ÆŠABI'AR ZUCIYA👉ðŸ¾huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ÆŠAI ÆŠAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU
AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2👉ðŸ¾400
3👉ðŸ¾500
4👉ðŸ¾700
5👉ðŸ¾1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE
DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½
#team zafafa biyar .
___________
1/6/22, 17:52 - Buhainat: *HALIN GIRMA*
      7
*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi
08184017082 or 09134848107*Â
I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my
photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
***
Kukan ta ne yake karuwa Mama na tsaye a kanta, ta ja tsaki tace
"Bana son shirman banza kina ji na? Akan namiji zaki zauna
kina rafka wannan kukan kamar uwarki ce ta mutu ko ubanki?"
"Mafita nake so mu samawa kanmu, saboda anga zaki huta
shine aka shiga aka fita ake so ayi mana bakin ciki, idan ba haka ba, me ya
kawo wadannan zantukan?"
Cikin kuka tace
"Wallahi Mama nasan Iman ce taje ta samu Gaji da maganar
tunda dama ita yace yana so ai, shine dan taga wanda yazo wajen nata talaka ne
shine zata min bakin ciki, toh wallahi babu wanda ya isa ya hanani auren
Bashir, naji na gani kowanne hali ne dashi."
Shiru Maman tayi tana kallon yar ta ta, idan har ta bari maganar
ta sha ruwa akwai matsala, sanin cewa Zeenat din ba wani farin jini bane da
ita, dama dai jamaar Iman din ne tun farko take sanin yadda zatayi, dole ta san
abinda ya kamata amma duk da haka ba zata nunawa Zeenat din komai ba
" Kina jina? Ki tashi ki tafi dakin ku, ki daina wannan
kukan tunda ba ubanki bane ya mutu, zan san yadda zanyi komai ya
daidaita."
Da bayan hannun ta ta goge kukan, ta fice tana rangaji, tana
sake kudurewa a ranta babu gudu babu ja da baya a auren ta da Bashir din.
 Tana isa daki ta tarar da missed calls din sa, ta bi
kiran da sauri tana sake daidai ta kanta.
" Gani a waje." Yace tana dagawa.
" Mu hadu a bayan layi akwai matsala karka zo gida."
" Me ya faru?" Yace a kidime.
" Babu komai gani nan zuwa."
Kashe wayar ta, tasan zai ta tambayar ta menene gwara kawai taje
suyi magana su sama wa kansu mafita dan ba zata iya hakura dashi ba.
Â
Ficewa tayi ta kofar kitchen bayan ta gyara fuskar ta, ta bar
gidan cikin sauri tana tsoron haduwa da Ya Habib ko wani.
 A chan bayan layin ta hange shi jikin motar sa, a tsaye
yake yana ta jijjiga jikin sa daga gani baya cikin nutsuwar sa, tana isa ya
juyo da sauri.
" Lafiya baby?" Yace yana riko hannun ta. Kuka ta saka
da sauri yace
" Na shiga uku, me ya faru?"
" Abba ne yace wai na rabu da kai, wai yayi bin..."
" Shisshsh..." Yace da sauri yana dora hannun sa a
saman bakin ta
" Kinsan dai hakan ba gaskiya bane ko? Sharri akayi min ko
menene akace domin a hana mu aure, duk wanda ya yi min wannan sharrin na bar
shi da Allah kawai." Yace yana girgiza kansa
" Shikenan yanzu rabuwa zaki dani? Nasan rayuwata shikenan
ta kare, idan har zaki iya yarda mahassada su shiga tsakanin mu, bakya so na
baby, rayuwata shikenan ni."
" Ni ban yarda da duk abinda akace ba ai, kawai sharri ne
na sani, amma ya zanyi da Abba? Bayan shi din kaifi daya ne akan maganar
sa."
" Dan Allah Zeenat karki yarda a raba mu, wallahi Ina sonki
, bansan ya zanyi da rayuwa ta ba idan har baki aure ni ba."
Hawaye ya fara yi tayi saurin sa hannu ta goge masa
"Zanyi duk yadda zanyi, ba zan bari a raba mu ba..."
" Da gaske? Kinyi alkawari?"
" Nayi maka alkawari."
" Dan Allah karki saba alkawari dan Allah, ki taimaka wa
rayuwa ta, kinji?"
" Karka damu." Tace tana jin wani karfin zuciya,
" Ba zan taba yarda su yi min abinda bana so ba, Kai nake
so kuma duk yadda kake ina son ka a haka.*
"Nagode nagode baby, in sha Allah ba zakiyi dana sanin
amincewa dani ba."
Zatayi magana wayar sa tayi kara
" Sorry." Yace mata kafin ya daga yana rage volume din
wayar sosai
" Malam tun dazu nake jiran ka, ka dawo min da mota zan
fita, wai ina ka tsaya ne?"
" Gani nan yanzu in sha Allah."
Ya kashe kiran ya ce
" Baby bari naje, urgent call daga Baba, zamuyi waya
kinji?"
" Tam shikenan." Tace a sanyaye
" Yawwa ga sakon ki..." Ya bud'e murfin motar ya fiddo
da ledoji, hannu tasa ta karba tayi godiya, ta juya ta soma tafiya shi kuma ya
shiga motar ya tada ita da sauri ya bar wajen, yasan ba zasu kare kalou ba da
ita, amma kuma hakan shine kadai zai kankaro masa mutuncin sa.
***Daki ta koma ta ajiye ledar bayan ta bud'e taga ice cream ne
da Pizza, sai charger waya da yake ta lalace ta ta, sai wasu tarkachen alawoyi.
Bata taba komai ba sai charger din ta jona wayarta a jiki sannan ta fice zuwa
bangaren Gaji dan ta samu Iman a yi wacce za'a yi.
  Iman din ce kuwa kadai a falon tana karanta
hisnul muslim. Sai ganin mutum tayi a kanta, bata tanka mata ba ta sauke kanta
ta cigaba da karatun ta kawai.
"Saboda kina bakin ciki kin samu fakiri talaka shine zaki
kai munafurci kice Bashir bashi da hali ko?"
"Wacce irin magana ce wannan Zeenat?"
" Malama karki pretending kaman baki sani ba, idan bake
kika fad'a ma Gaji wata magana akan Bashir ba waye ya samu Abba ya fad'a masa
Bashir bashi da hali me kyau?"
Tashi tayi zaune tana kallon ta, ta girgiza kanta kawai kafin
tace
" Kinsan bani da lokacin batawa akan irin wadannan
maganganun, dan haka please bana son maganar."
" Zaki ce bakya so mana kina min bakin ciki, toh wallahi
sai dai ki mutu da bakin ciki amma aure na dashi babu fashi, kije chan kiji da
wanda zaki aura, mutum kamar shi ya kawo talauci duniya."
Tashi kawai tayi ta bar falon zuwa bedroom din Gaji dan ba zata
iya irin wannan shirmen na Zeenat ba, sai dai da gaske maganar ta taba ta, har
taji ta rasa gaba daya walwala da farin cikin ta, kwanciya kawai tayi ta rufe
idon ta tana hasaso rayuwar ta nan gaba!
***Cikin shigar Khaki pants da wata jibgegiyar rigar sanyi da ya
saka a saman armless rigar sa ya fito, kansa da yake a kwance yasha gyara ya
tsaya yana sake dubawa a katon mudubin da yake ajiye a falon, yasan Takawa zai
saurare shi ya kuma bi abinda yake so sai dai baya son ko kad'an karya ko wasa
ya shigo a cikin maganar auren sa. Kallon kafar sa yayi, sai ya koma ya sauya
takalmin zuwa wani daban sannan ya fice yana tura hannun sa cikin aljihun dogon
wandon nasa.
  Suna tsaye k'yam suna jiran fitowar sa, kowanne
su cikin shigar da take nuna shi din waye, bud'e masa motar akayi da sauri ya
fad'a yana makala bakin glass din sa yasan yau zai same shi a wajen hutawar sa,
in da ya dace da maganar da zasu tattauna, shiyasa ma yayi shigar sa da yasan
Takawan bazai masa surutu ba, dan ya riga ya san shi, ko yace kowa ya san shi
da tsanar manyan kaya musamman a lokacin zafi sai yace wai takura masa suke.
  Da yake sun san in da zasu, kai tsaye suka wuce
dashi Family house din, in da Takawan ke hutawa a duk ranaku irin wannan ba
tare da shigowar wani shaani na mulki ba. Iyakar abinda ya shafi kansa da
iyalin sa kawai yake tattaunawa a rana cikin saukakakkiyat shiga da ba zaka
taba cewa sarki bane duba da ko yaushe yana nannade cikin rawani da manyan
kaya.
  A kofar wajen motocin nasa suka tsaya, ya balle
murfin tare da me bud'e masa ya fito yana kallon ko ina na harabar gidan. Kansa
sanye da hular sanyi ya cire glass din idon sa ya shiga takawa zuwa ciki.
Gaisuwar da ya tsana ya dinga kokarin kaucewa har ya dangana da inda takawan
yake ya hange shi a zaune a cikin wajen yayi matashi da pillow yana kallon
yadda yan yaran da suka kasance jikokin sa ke wasa a wajen.
  Sarkin dogarai ne ya fara ganin shi,ya washe
cikin farin cikin ganin shi yace
"Maraba da Yarima!"
"Sarkin dogarai..."
Muryar sa ta saka takawa d'agowa, ya gyara daga gishingid'ar da
yayi, ya fad'ad'a fara'ar fuskar sa da tayi ma Moh iso har gaban kakan nasa.
Russunawa yayi cikin girmamawa ya kai gaisuwa, hannu ya mik'a masa ya matso
kusa dashi sosai, ya shafi saman kansa
" Sai yau kaga damar leko ni ko Muhammadu?"
" Tuba nake Takawa, ayyukan ne suka yi min yawa."
" Toh madallah, naji kace kana son gani na, toh gani ya
akayi?"
" Dama magana ce akan abinda Bubu yayi maka magana."
" Auren ka? Jairi toh sai akayi yaya?"
Dariya ya saka sosai
" Toh kunce sai nayi aure yanzu kuma nazo da maganar kuma,
sai na fasa auren ma gaba daya."
" Fasa mana, waya yayi asara? Kaji dan nema."
Dariya suka saka a tare, kafin Takawa yace
" Toh sai ka fadi a inda yarinyar take ko? Idan yaso sai a
nemi iyayenta."
" A ah ni dai Takawa, ayi min aikin gafara a bari a samu
wasu suje su nema min auren ta."
" Wasu?" Yace yana kallon sa
" Eh a dangi haka ba, ba manya sosai ba, Ina nufin ba cikin
manyan masarauta ba, yan chan kasa kasan dai."
" A wanne dalili?"
" Kawai ni bana so suji tsoro su ga kamar mun fi karfin
su."
Girgiza kai Takawa yayi
" A neman aure babu boye boye Muhammadu, a sak dinka zaka
je, kai ne fa jika na farko a gidan nan, sannan a wajen mahaifin ka, wanne irin
tunani ne haka ya shiga kanka?"
Sosa kai Moh yayi yana marairaice fuska
"Ni dai dan Allah takawa, a bar wasu suje."
"Sam sam kaima kasan hakan ba mai yiwuwa bane, dole ne su
san kai din daga gidan da ka fito."
Shiru yayi yana jin kamar ya daure kansa da ya budewa Takawa
zuciyar sa, yasan shi sarai da tsayawa akan ra'ayin farko, amma yayi tunani zai
fuskance shi duba da irin son da yake masa, dama Musaddik ya gaya masa, babu me
yarda da shirmen sa kamar yadda yake jaddada masa a kullum, babu me biye masa
ko bashi goyon baya. Tun daga lokacin yasan sarai babu me tsayawa ya saurare
shi, balle ya yarda da tsarin sa. Ammin sa ce kadai itama bata ja da maganar
Takawa, ballantana Bubu da baya iya aiwatar da komai sai abinda Takawa din
yace.
 Â
"Kana jina Muhammadu, maganar da kazo da ita bata kamawa
bace. A tsari na gidan nan ma zamu iya aika musu suzo nan din domin muna da
damar bada diyar tasu, sai dai ba zamuyi haka ba, zamu basu girman su da
darajar su in Sha Allah, za kuma musu duk abinda Muhammad yake so amma banda
shiririta."
Ya karashe yana murmushi, murnushin shima yayi kawai ba tare da
yace komai ba. Suka cigaba da hira irin wadda suka saba har be san iya adadin
awoyin da ya bata ba, sai da suka ci abinci da Takawar sannan ya lallaba ya
shiga gidan ya gaida matan gidan ya kare a dakin kakarsa ya tarar da yan matan
family din sunzo suna da wani get-together da suka shirya sannan suyi maganar
tsari bikin Abidah guda daga cikin jikokin gidan.
  A kaidar sa baya sakar musu fuska ko kad'an domin
suna da rainin hankali sosai, duk da shi basa yi masa neman ma ya kula su suke
amma shi sam baya tsayawa shirmen su, da gaske suka shakkar shiga shirgin sa
hakan yasa yana shigowa shashen suka dinga yayewa da d'aya d'aya.
 Dan tsiririn tsaki yaja sanda suka gama ficewa ya zauna
yana muzurai a dole baya son raini shi. Mutane da yawa na fad'a masa yadda yake
abubuwan sa kadai ya tabbatar da shi din jini ne na sarauta amma shi sam be san
ma yana yi ba ma.
  Ya dan jima a wajen nata kafin ya tafi yana jin
zai dan dade kafin ya sake waiwayo su duba da tafiyar dake gaban sa akan aikin
sa.
***Yana zaune a gate din gidan yana dakon shigowar Abba Babban,
a kan idon sa ya dawo ya tashi da sauri ya tare shi ya bud'e masa kofar mota.
"Sannu da zuwa Abba."
"Yawwa Ibrahim, kaine yau a gate din kenan."
" Wallahi kuwa Abba, sannu da dawowa, ya aiki?"
" Alhamdulillah mun gode Allah, ya naka aikin?"
" Alhamdulillah." Yace yana tuna abinda ya faru dashi.
" Allah ya taimaka ya bada sa'a."
" Amin Abba." Yace yana bin sa rik'e da jakar sa a
baya.
" Mika jakar ciki bari na fara gano Gaji."
Yace yana bin hanyar da zata kaishi bangaren Gajin, da sauri
Khalil din ya kai masa jakar ya dawo ya zauna yana jiran ya fito. Ya dan jima a
wajen Gajin kafin ya fito sai dai ganin Khalil ya saka shi mamaki, abunka da
Babba nan da nan ya gane akwai wani abu.
" Ya akayi Khalil? Kana son gani na ne?"
" Eh Abba." Yace yana sosa kansa
" Haba ko da naji, toh zan turo a kiraka kaji?"
" Toh Abba Nagode." Girgiza kai Abban yayi ya wuce
bangaren sa. Maimakon ya koma gida sai yayi zaman sa anan yana jiran kiran
Abban. Yana zaune kuwa yaga fitowar Sadik ya tashi da sauri ya tare shi
"Yawwa wai kazo in ji Abba."
Rik'e hannun sa yayi suka koma yana jin wani iri a ransa, bakin
sa dauke da addu'a ya shiga falon ya tarar Abban ya chanja kaya yana zaune da
alama abinci ya gama ci. A chan gefe ya zauna yana jin kunya.
"Yawwa ina jin ka Ibrahim, ya akayi?"
Shiru yayi yana tsara yadda ya kamata ya ce, sai da ya dau
sakanni yana hado maganar kafin yace
"Dama Abba akan maganar Fatima ne."
"Uhum ina jinka. Ya akayi?"
"Dama... Dama so nake dama a bani dama kamar yadda tsarin
gidan nan yake."
Murmushi Abba yayi cikin jin dadi yace
"Masha ALLAH naji dadin wannan abu matuka, Allah ya
tabbatar mana da alkhairi kaji? Allah yayi muku albarka."
" Amin Abba." Yace a ciki-ciki farin ciki na kamashi,
" Kaje ku daidaita idan Allah yayi mu haka muke so, an riga
an zama daya ai in sha Allah babu wata matsala."
" Nagode Sosai Abba, Allah ya kara girma."
" Amin." Yace yana chanja tasha a tv, shiru Khalil din
yayi kafin ya mike
" A huta lafiya Abba."
" Yawwa Ibrahim."
Yana fita ya daka tsalle a wajen yace
"Yes!!"
Da sauri ya bar wajen yana jin kamar ya same ta ya gama ne, zai
nuna wa fakirin saurayin ta cewa dan gida yafi bare.
***Sabon yadi ne me saukin kudi sosai, dinkin ma irin dan 1500
din nan ne, a rayuwar sa be taba hasashen saka ire-iren kayan da yake sakawa a
yanzu ba, wani kallo Musaddik yake masa yana jin kamar ya kamashi yayi ta bugu.
"Yanzu Moh irin kayan da zaka saka kenan zaka ganin sirikin
ka?"
"Wait and see." Yace yana kawo wata leda a kusa dashi,
ya wurga masa yana cigaba da kallon kansa a mudubi
"Ka chanja mu tafi idan yaso muyi sallar magriba a hanya
sai mu karasa."
"Na saka me?" Musaddik yace da sauri yana bud'e ledar.
"Wait what! Kana nufin ni zan saka wannan kayan."
"Mu nawa ne a dakin nan?"
"You must be kidding me, haba haba an fad'a ma kowa ma irin
ka ne."
"Allah su zaka saka mu tafi, kayi sauri karka batan lokaci
I'm dying to see my love."
"Aiko sai dai ka tafi kai kadai wannan karyar ba dani
ba."
"Da wa toh? Wa nake dashi bayan kai? Kasan da ace ban samu
kanta ba dole kaima ka tattaro ka dawo sabon shagon nan dana zauna mu zauna tare.
Allah dai ya taimake ka wallahi."
" Ai wallahi babu yarinyar da ta isa nayi mata irin wannan
son, the whole you, Captain Muhammad Ahmad Santuraki, dan ga sarki jikin sarki
sannan kuma babban soja, ko da yake fa dama ance ku sojoji baku iya soyayya ba,
musamman idan allurar ku ta motsa."
Daina abinda yake yayi ya matso kusa dashi
" Idan bansa an saka min kai frog jump ba, kace ba suna na
Muhammad ba."
Dariya maganar ta bawa Musaddik,
" Ni zaka saka frog jump?"
" Sosai, ka cigaba da batan lokaci kaga."
Tashi Musaddik yayi ya sake daga kayan, kafin ya fara sawa yana
cigaba da mita.
" Kanka akeji wallahi." Moh yace yana cire agogon
hannun sa.
" Ka cire watch dinka please, anything da zai sa ta zama
suspicious, I don't care idan kowa na gidan su yasan ni waye, amma ita? Da
marikiyarta will be the last da zasu sani, surprise ne me kyau nake son basu
dukka, sai dai kowanne da yadda surprise din zai zo masa."
" Wicked soul." Musaddik yace yana jefar ta watch
dinsa akan mirrow
" What ever!" Yace yana yin gaba yabi bayan sa yana
jin dadin kayan jikin sa, babu nauyi shawai shawai amma kuma ba zai yarda Moh
din yasan ya ji dadin kayan ba.
A daidai shagon aka daajiye su, yace su je chan in da suka saba
jiran sa su jirashi zai kirasu. Duk da basu so ba amma haka suka tafi suka
barsu, Musaddik ya dinga jan tsaki suna tafiya a k'asa har suka isa kofar
gidan. Wayar sa ya ciro ya kira ta, tayi ta ringing bata daga ba,
" Bata daga ba."
" Da ka kirata tun kafin muzo ai."
" Wannan ba matsala bace, bari kaga."
Ya kwankwasa gate din kafin ya dan tura shi suka shiga, dai-dai
lokacin Khalil ya taho zai fita sukayi kichibis, wani kallo ya bisu dashi irin
na sama da k'asan nan, kafin ya tuntsure da dariya sosai, hakan yayi bala'in
bata ran Musaddik da dama chan baya daukar nonsense.
" Malam lafiya zaka kalle mu kayi dariya?"
" Lafiyar kenan, sai dai kun makara, dan gida ya shiga ya
fita ya gama tabbatar da komai akansa, sai abi wani sarkin dan an riga an gama
magana kuma su din ba kananan mutane bane da zasu sauya maganar su."
" Kana nufin?" Musaddik yace a zafafe
" Ina nufin kamar yadda na fada mishi ne a baya, Iman
matata ce an riga an gama magana rana kawai ake jira a saka mana."
Wani kallo Moh yayi masa da ya saka Khalil shan jinin jikin sa,
amma sai ya dake ya cigaba da gaggayawa musu magana. Muhammad be ce komai ba
har ya gama, ya juya ya fice ya barsu a tsaye kamar mutum mutumi.
" I have no option than to show him my real identify, idan
yaso duk abinda ya biyo baya yayi kuka da kansa ba da kowa ba, karfe nawa ne
appointment dinsa?"
" Da safe ne, goma kamar."
" Owk Allah ya kaimu."
" Amin." Musaddik ya amsa ransa na sake baci akan
abinda Khalil din yayi musu
HALIN GIRMA
Hafsat Rano
WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da
wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na
MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu
dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma
kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN
NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL👉ðŸ¾
Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉ðŸ¾hafsat
rano_*
*_TAKUN SAƘA👉ðŸ¾billyn
abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉ðŸ¾miss
xoxo_*
*_ÆŠABI'AR ZUCIYA👉ðŸ¾huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ÆŠAI ÆŠAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU
AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2👉ðŸ¾400
3👉ðŸ¾500
4👉ðŸ¾700
5👉ðŸ¾1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE
DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½
#team zafafa biyar .
___________
1/6/22, 17:52 - Buhainat: 08
*zafafa biyar na kudine,tuntubi wadan nan numbers din don samun
naki copy din ki karanta cikin aminci*
08184017082
Ko
09134848107
*_follow us @ instagram_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1h9y2qgfg67x5&utm_content=nj79azb
Or facebook
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
___________________________
Dan kwantar da kujarar
yayi kana ya miqe sosai Samanta yana jin yadda gajiya take bin jikinsa,don gaba
daya wunin yau bai shirya fita ba,ya shirya zama ya huta sosai a gida,saboda
satin gaba daya cikin aiki ya yisu,babu dare babu raba,har inda ma a tsarinsa
babu schedule na zuwansa sai daya ratso masa a sannan din.
hannayensa saman
kansa yayin da idanuwansa suke a rufe,yayi nisa a tunaninsa sosai,busy busy ne
dashi irin wanda mutane da yawa ke mamakinsa,sam bai bawa kansa hutu ba.
a qalla ya kusa
minti ashirin a zaune a haka,wanda hakanan yaji zaman yayi masa dadi,ko ba
komai ya dan samu break na wasu mintuna.
Dan waiwayawa yayi
gefansa,a sannan ya hango tahowar professor shi da wasu mutane hudu,saiya miqe
ya gyara zamansa,ya kuma kunna motar yana jiran qarasowarsa.
yana jin sanda ya
shiga yana sallama da mutanen,suka maida murfin motar suka rufe masa,don haka
saiya tashi motar,dai dai sanda professor ya furta
"alhamdulillah"yana sauke ajiyar numfashi.
A nutse yake tuqin
har suka fita daga airport din,a hankali professor rashid yace
"lawan....ko ka sake koyon sabon salon tuqi ne?"raba
idanu samir yayi hagunsa da damansa,saiya lanqwashe murya yace
"eh alhaji"dan jim professor yayi sannan yace
"to yayi kyau"daga haka bai sake cewa komai ba,zaman
shuru yaci gaba da ratsawa a tsakaninsu.
"Daka sani
ai baka wahalar da kanka ba samir....."yaji abban nashi ya fada bayan
tsahon wani lokaci,ya ganeshi kenan,qyaleshi yayi kamar bai gane ba,qaramin
murmushi ya subuce a kuncinsa,jerarrun fararen haqoransa suka bayyan,har yayi
kamar bazaice komai ba sai kuma ya tanka
"yau daya dai abba....ai nima na samu ladan yau
din"wayar hannunsa professor ya ajjiye,ya tsurawa gaban motar idanu,kamar
anan fuskar samir din take,baisan me yasa a kullum shi da tilon dan nasa komai
nasu yasha banban ba,komai nasu ba iri daya bane,abinda yake sam ba cikin tsari
da burinsa ba,ya jima da sanin cewa ba haka yakeso ya kasance ba,ba haka
tsarinsa yaso ya zama ba,to amma duk ta inda yake tunanin zai gyarota babu wani
sauran dama data rage masa,don haka a maimakon yayi magana,saiya buge da hade
yatsunsa waje daya,yana maida tunaninsa wani waje daban.
Duk sanda yayi
tafiya irin wannan ya dawo iyalansa dama ma'aikatan gidan kan cika da
murna,kamar yanzun,da samir ke biye dashi dauke da wata qawatacciyar qaramar
jaka mai zubin akwati,yana biye da professor har zuwa cikin qawataccen falon
gidan,mai yalwa da kuma burgewa,wanda ya wadata da dukkan wani nau'in kayan
alatun rayuwa.
mutum uku ne ke
dakonsa zaune cikin falon,biyu daga cikinsun matasan yammata ne,daya tafi daya
tsaho da haske,kamar yadda daya tafi daya shekaru da basu wani taka kara sun
karya ba,don dukkansu ba zasu gaza shekara sha tara da ashirin ba.
Daga wata kujera
kuma mai mazaunin mutum biyu,macace xaune itama wadda ta mallaki shekaru É—ai
É—ai har shekara hamsin,saidai idan har
kai mai kallo xa'a qyaleka kayi mata ƙiyasin shekaru,to ba shakka zaka ce
dauka cewa bata wuce shekara talatin da biyar ba.
Tun a kallon
farko xaka bata sunan HAMSHAQIYA saboda ta cancanci sunan,fara ce
sol,shekarunta sam basu boye hasken fatarta ba,tana da matsakaicin kyau wanda
ya cakuda da tarin ado da qawar da take qawata kanta dashi kullum kwanan
duniya,kallon farko zai gaya maka ta saba da ado ya zame mata jiki,salon irin
abun nan da hausawa suke cewa WANKA YABI JIKI,tun daba hannayenta zuwa wuyanta
kayan ado ne na mata,fuskarta wadace take da murmushi kamar bakinta zai
yage,idanunta qur bisa saman fuskar wadan nan halittu guda biyu,wato samir da professor,tana
dubansu da wani irin kallo me nauyi da zurfi.
Dukkaninsu suka
miqe kowanne fuskarsa na nuna tsantsar farinciki,daya daga cikin matasan
yammatan nan wadda da alama batakai shekarun daya ba ita ta tako da sauri zuwa
inda professor yake
"Abba.....sannu da dawowa"ta fada da 'yar siga ta
shagwaba,da alama kuma hakan habit dinta ne,tana dora kanta saman
kafadarsa,kamar marayan daya samu tallafi,murmushi ya saka yadan dora kansa
saman kanta
"barka kadai auta....na sameku lafiya?"
"lafiya qalau abba,saidai munyi missing
dinka"murmushin yakuma saki
"gani na dawo ai jauhar,duk wata kewa ta qare ko?"kai
ta gyada,sai dayar itama ta matso,tasa hannu kadan tana gyara eye glasses
dinta,fuskarta itama murmushinne kwance
"barka da zuwa abba"
"barka kadai lelen abba.....na sameku lafiya?"
"lafiya lau abba ya hanya?"
"alhmdlh,ya karatu?"saida ta saki wani ni'imtacce
murmushi,tana jin wani dadi na ratsata,ta daga idanun a hankali ta maida
gashi,samir.......wanda har yanzu yake tsaye a bayan abban nasu tamkar wani
dogari,hannayensa zube cikin aljihun wandonsa yana kallon dukkan abinda ke
faruwa, inside him yana jin tsaiwarsa a wajen cikin abubuwan da suke gundurarsa
nan da nan,ya qagu duka a gama wadan nan gaishe gaishen.
dauke idanunta
tayi ta maida kan abban,a duniya tana jin dadi tana alfahari abban nasu ya
tambayeta karatunta,tana jin wani qwarin gwiwa yana shigarta aduk sanda ya
tambayeta wani abu daya danganci karatunta,takanji burinta kwadayinta da qwarim
gwiwarta yana daduwa
"alhmdlh abba....komai lafiya"
"ma sha Allah"ya fada yana maida dubansa xuwa
gareta,har yanzu bata matsa daga inda take tsaye ba,amma hankalinta idanuwanta
da hankalinta dukka yana kansu
"sarautar mata.......yada tsaiwa a nan?"murmushi ta
saki
"to ai naga hankalinka duka yana kan yaranka,kaga gwara na
barku ku gama tukunna.....barka da dawowa"
"barka kadai.....na sameku lafiya?"
"alhmdlh"ta fada taba jifansa da wani murmushin,saita
tako a hankali ta raba ta gefansa,idanunta saman fuskar samir,suna hada idanu
ya kauda kansa ya miqa mata jakar professor dake riqe a hannunsa,hannu ta miqa
zata amsa tana cewa
"ka kyauta samir"ya fahimci abinda take nufi,saiya
saki qaramin murmushi yana juyawa kadan zai fita
"ya da haka son...ka bari daddy ya kintsa muci abincin rana
tare mana"ta furta cikin nuna zallar kulawa,kansa ya girgiza yana sosa kan
mashi da tsinin key din mota,shida yakeson tsallakewa fadan professor,yayi
imanin idan ya zauna suci abin tare zai tono laifin da shi yaketa qoqarin
bunnewa ne
"akwai abubuwa da yawa dana bari,zanje na rage wasu,bazan
jima yau a waje ba zan dawo gida" sanda yake maganar shima professor ya
nufi hanyar da zata sadashi da sassansa da suka qunshi bedrooms manya guda
biyu,da.katafaren falo guda daya
"da zaki daina wahalar da kanki wajen tsaidashi,ki barshi
ya tafi kawai, saboda haka yakeso,hakan ya tsarawa kansa kamar ko yaushe"
sarai samir yasan magana ce mai harshen damo yayi masa,sai data waiwayo ya
kalli samir
"ohk....saika dawo,Allah ya tsare" kansa ya gyada
sannan ya juya zai fice,itama ta rufawa professor baya.
"ya
saraki"kiran da aka masa shine abu na biyu daya shiga kunnensa daga hirar
professor da matarshi,sai yaja tunga ya tsaya sannan ya waiwayo a hankali sanda
take tasowa a shagwabe ta riskeshi.
Idanuwan najwa tar
bisa fuskar jawahir sanda take nufar yayan nasu,saita sanya hannunta ta cire
airpiece guda daya cikin biyun dake maqale a kunneta,tana jin wani abu na
tokare zuciyarta,ta tsani taga tana magana dashi sam,tana son taji yanzun me
zatace da shi ne.
"ya
saraki.....please,alqawarinmu fa" ajiyar zuciya yayi hade da lumshe
idanu,lokaci guda kuma ya furzar da iska daga bakinsa,baice komai ba saiya cusa
hannunsa cikin aljihunsa ya fiddo sabbin 'yan dari biyar biyar masu dama ya
miqa mata,wani dan tsalle ta saki bayan ta amshu kudin
"thank you so much,am proud of you my yaya"murmushi
kawai ya bita dashi sannan ya taka ya fice.
kudin na hannunta
tana juyasu,fuskarta a wadace da murmushi ta koma kujerar data tashi akai ta
zauna,duk abun nan da ake idanun najwa a kanta,tana binta da wani kallo da zai
nuna maka zallar tkaici da haushinta daya cika mata zuciya,sam jawahir batasa
me take ba tana irga kudinta hankali kwance,ganin cewa da gaske jawahir batasan
tana yi ba,lissafin kudinta kawai take,saita miqa hannu ta fusge kudin a tare
tana furta
"banza"da qarfi,hakan yaja mata hankalin jawahir din
yadda takeso,dubanta take baki bude
"me na miki ya najwa"
"banza"ta sake maimaitawa tana hararta,idanuwanta
kamar zasu fado akan jawahir din
"wai me na miki?"
"ke wai.me yasa baki da zuciya,kuma baki da kishin
kanki?,na meye zaki tambayesa kudi,momi ba zata baki bane da ba zaki tambayeta
ba?"sosai jawahir ta bata fuska tana kallon najwan,ranta a dan bace
"amma shi da momyn ai duk daya ne ko?,kuma ko ita ai taga
ina tambayarsa,kuma bata ce komai ba"baki najwa ta tabe
'bakya ganewa,kuma ba zaki taba ganewa ba....."
"nidai koma meye bani kudina"ta furta tana miqa mata
hannu
"naqi na bayar din"najwa ta fada tana cusa kudin a gefan
cinyarta,sai jawahir din ta sake gimtse fuska sosai
"kinga ki bani kudina ya najwa,ko momy tace ki daina shiga
harkata ko?"
"idan kina da qarfi ki danne ni ki qwata,sarai dai kinsan
babu abinda zanyi da kudin nan.....".
A hankali ta buda
qofa ta dawo ta cikin falon,idauwanta ya sauka a kansu sanda jawahir ke sake
maimaita wa najwan ta bata kudinta
"lafiyanku?"momyn ta jefa musu tambayarsu,wanda banda
tayi magana babu wanda yaga fitowarta cikinsu
"momy....ya saraki na tambaya kudin ankon yasmin tun
rannan,to ya bani shine ya najwa ta karba ta hanani,tana masifar wai don me zan
tambaya ya saraki"jawahir tayi caraf ta gaya mata,sai data tabbatar ta
aikawa jawahir saqon harara sannan ta maida dubanta ga mony da nufun yin nata
bayanin
"momy wai ba....."wani kallo momyn ta aika mata,sannan
ta daga hannunta kawai ba tare da tabi takan qorafin da takeso. sako.mata ba
tace
"bata kudinta"fuska ta bata
"momy...."
"nace ki bata kudinta ha'an...?"ta fada da dan zafi
zafi yanzun a muryarta,fuskar najwa a cunkuse,ta zaro kudin ta jefawa
jawahir,ya fada saman cinyarta,bata damu ba ta dauki kudinta taci gaba da
irgawa,momyn ta kalleta
"ajjiye kudin nan kizo kitchen ki hadama daddynku
drink"
"to momy"ta amsa mata tana miqewa da kudinta a hannu
tabi bayanta,yayin da najwa ta bita da harara,tana jin kamar ta shaqeta,saita
gyara glass din fuskarta,ta kuma gyara zaman qaton littafin dake ken cinyarta
taci gaba da dubawa,can qasan ranta abubuwa da yawa na mata yawo,inda tana da
qarfin iko da sai ta canza abubuwa da dama cikin gidan nasu,abubuwa masu tarin
yawa da basuyi rayuwarta yadda takeso ba,basu zauna kuma a gurbi da muhallin da
takeson ganinsu ba.
*_9:30 am_*
*_DARMANAWA HOUSING ESTATE_*
*_PROFESSOR RASHID USMAN AZARE RESIDENT_*
Daya ne daga cikin
jerin qawatattun gidaje dake gine cikin unguwar,,wanda suka qawatu aka kuma
ginasu bisa basira da kuma kyakkyawan tsari.
Gini ne na alfarma
mai cike da qayatarwa da ban sha'awa,kamar yadda akasan ire iren gidajen masu
sukuni suke da kuma unguwaninsu.
A hankali momy ta
daga kanta,fuskarta na fidda wani irin murmushi mai haske tunda ta jiyo sautin
muryarsa,tun gabanin ma ya iso inda suke din,yayin da ta tsaida dukkan abinda
takeyi,ciki harda cin abincinta,da kuma hira da take da 'yammatan dake gefanta
su uku,najwa jawahir da kuma ramla da take 'yar ruqo a wajenta.
Dukkaninsu sunsan
meye ta baiwa hankalinta haka gaba daya,ba wacce bata saba da ganin tarin
kulawa da qauna daga gareta ba zuwa ga samir,wadda ta banbamta da ta kowanne da
dake cikin gidan.
Kallo daya
professor yayi mata yaci gaba da cin abincinsa a nutse,don shi din ma hakan ba
baqon al'amari bane a wajensa,illa dai ya kada kansa sannan ya maida hankalinsa
ga farantin gabansa.
Cikin sakanni da
basu kai goma ba ya bayyana cikin falon dab dasu,matashin saurayi muhammad
samir me laqabin saraki,ma'abocin tsaho,wanda murjewar jikinsa ta hana
bayyanuwar tsayin da Allah yayi masa yadda za'a fahimta,ya mallaki kalar fatar
da hausawa suke kira da wankan tarwada amma irin wankan tarwadan nan dake da
haske,taqi kadan zai dada ka kirayeshi da farar fata,matsakaicin kyau
gareshi,saidai abubuwa guda biyu sun taru sun qarawa siffarsa kyau da cikar
haiba KWARJINI da yake dashi,da kuma wasu lumsassun idanuwa masu kama da na me
jin bacci.
Yana da sanyin
murya,irin sanyin da bai hana bayyanar cikar mazantakarsa gami da jarumtarsa
ba,sam ba miskili bane,kamar yadda wasu mutane da yawa suke masa kallon
haka,abubuwa ne guda biyu suka sanya suke masa wannan kallon,baya shiga sabgar
da bata shafeshi ba,bashi da shishshigi sam,hakanan bai fiya magana kan abinda
yasan yana da qarancin muhimmanci,koma kwata kwata bashi da muhimmancin,yana da
kamewa da wata irin nutsuwa mai jan hankali,yana da zurfin ciki a yawancin
lokuta,komai nasa bisa tsari da dacewa yake tafiya,shi yasa wasu ke ganin abune
mai wuyar gaske iya zama dashi,abunda basu sani ba shine,zama dashi din wani
abune mai dadi ga duk wanda ya soma mu'amala dashi.
Akwai boyayyun halayyensa da ba kowanne ya
sanshi dasu ba,ciki kuwa harda makusantansa,yana da tausayi yana da taimako,a
wasu abubuwan ba zaka taba tsammanin cewa ya fito daga gidan girma da arziqi
irin wannan ba,rayuwa sassauqa da yakan gudanar....saidai,matuqar kazo lokacin
da yake kan tsininsa,zaka dauka baida kirki ko kadan.
Muhammad samir,da
namiji guda daya tilo da Allah ya mallakawa professor rashid usman azare,wanda
tarin banbamce babancen halaye da zabi na rayuwa yaso ya zama babban shinge
tsakaninsa da mahaifinsa da samun dukkan wata yarda da qauna tashi.
"welcome
son.....na tsammaci yau ba zaka fita ba?,naji shurun yayi yawa,duk da na kira
wayarka taqi shiga....saina zabi na barka ba tare dana aika ba,wala'alla kana bacci
ne kada a katse maka shi" hajiya jidda wadda auke kira da mommy ta
fada,dukkan kulawarta tana tare da samir din,fuskarta na fidda wani kalar
murmushi dake nuna farincikin dake tattare da ita na ganin fitowar samir
din,kamar yaune lokaci na farko data fara ganinsa,ko kuma wani gari yayi tafiya
mai nisan zango ya dawo a yau din.
Washewa fuskarsa
tayi da wani murmushi mai aji,ya soma qoqarin jan kujera daya don yiwa kansa
mazauni sannan ya amsa mata
"A'ah anna....bani da wani abu da zan aiwatar ne da
safen....shi yasa na zabi na huta kafin na fita yau,don jiya ban samu zama
yadda naso ba" ya qarashe maganar yana duqawa zuwa qasa gefan
mahaifinsa,muryarsa cike da tsantsar ladabi ya furta
"Barka da asuba daddy" kallo daya yayi masa ya maida
kansa ga abincinsa yana amsa masa da
"Ka tashi lafiya?"
"Lafiya alhmdlh" sai ya maida dubansa ga mommy wato
hajiya jidda
"Barka da asuba mommy"
"Barka kadai yarona....da fatan ka tashi lafiya"
"lafiya qalau alhdmdlh"
"To ma sha Allah" ta amsa masa fuskarta na nuna jin
dadin samunsa lafiya da tayi kamar kullum,saita miqe da kanta ta fara bude
dukkan wani kwano dake saman teburin sanda qannensa ke gaisheshi daya bayan
daya yana amsa musu,kamar yadda ta saba tanayi kullum kwanan duniya matuqar ya
halarci wajen cin abinci,zata bude masa dukka ya zaba abinda yakeson ci,don
wani lokaci ma abinda ya zaba yana so shi za'a dafa kowa da kowa,koda ba
zabinka kenan ba,tun suna yiwa mommy mita da qorafi har ya zame musu jiki.
"Me zakaci a ciki samir?,Allah yasa akwai wanda ya dace da
ra'ayinka" mommy ta fada tana murmushi kamar kullum,wanda baka rabata
dashi saman fuskarta,sai a sannan alhj mukhtar yayi magana tun fitowar samir
din,idanuwansa saman fuskar mommy,wani abu na yawo saman zuciyarsa,wani abu mai
nauyin daya wuce a aunashi a mizani
"Ki kalleshi mana da kyau,ba yau ko jiya ko shekaran jiya
aka haifeshi ba,amma kullum kina kallonshi ne kamar ranar nan da aka miqo miki
shi cikin tsumman goyo,a qa'ida ya isa aure,a kuma qa'idance kamata yayi ace a
gaban matarsa yake" kanta ta langabe tana duban professor
"Haba daddy.....kai kake ma samir kallon yayi girma har
haka,ni kam a wajena har yanzu kamar yaron goye nake kallonsa.....bugu da qari
ma daddy idan ba'a kula da samir ba...wa zamu kula dashi?,karka manta shi kadai
Allah ya bamu...."
"Abbaaaa"sautin muryar jawahir tayi kutse cikin
maganar mummy,sautin daya fito a narke,kamar me shirin sakin kuka,waiwayawa
suka dukka suna kallonta,sai daddyn ya daga hannayensa duka biyun kafin yace
"You see.....su kuma daughters dina ki kaisu ina?"
Murmushi ya saki,wani abu na lilo can qasan ranta da zuciyarta
"Dole dukkaninsu subi bayan samir a wajena" a nutse
tsaf daddyn ya waiwaya ya dubi samir din sosai kuma kai tsaye,duk da idanun
samir din na kai kawo ne tsakanin yan uwansa,fuskarsa tana fitar da wani
murmushi me sanyi mai kuma cike da nutsuwa
"Gwara da kika ce a wajenki,ta ina yaronkin zai kama qafar
yarana?,yaron naki da ba jin magana yake ba,wanda ya sarayar da alqiblarsa,babu
wanda ya gane har yau inda yasa gaba" samir ya gama fahimtar qorafinsa na
jiya da yaketa gujewa shi yakeson sokowa a yau din,saiya dan sunkui da
kansa,kana ya daga kan nasa,yana muradun rushe wannan maganar,don baida
sha'awar ci gaba da yinta,don haka cikin girmamawa yace da ita
"Kome akayi yau din zanci mommy,ki zauna ki huta....zan
zuba da kaina,ina sauri ne ma,jiya akwai taron da zanyi da ma'aikata,ban samu
zama ba nasa aka maidashi yau"ya fada yana miqa hannu zai hada tea.
jawahir ce ta miqe
da hanzari ya dauka cup din ta soma hada masa,mummy tadan kalleta saita dauke
kanta
"yi a hankali sarkin rawar kai,kada ki zuba masa a
jiki"mummyn ta fadi sanda jawahir ke aje masa tea din,murmushi yayi ya
dauka yana.kaiwa bakinsa,shi yasa yakeson autar tasu,sosai take nuna kumawa kan
dukkan wani abu daya shefeshi,ba kamar 'yar uwarta ba,wadda har yanzu bai
fuskanci inda ta sanya gaba ba,shegen sin jiki gayunbanza,izgili da yiwa.mutane
kallon banza hadi da rashi iya magana dukka najwa ta hadasu,abu daya da yasa
bata iya wani kyakkyawan abu a gabansa ko a kansa shine,baya daukar raini,kamar
yadda baya raina kowa,tafi kowa sanin ainihin wayeshi,wannan shine ya ke mata
waigi a kansa.
miqewa prof yayi
yana yagar tissue
"idan ka dawo yau din bayan sallar isha'i,ka sameni zamuyi
magana dakai"
"ok daddy"ya fada da muryarsa mai dadi,sannan yaci
gaba da kurbar tea din a nutse.
cup din ya ajjiye
bayan ya gama amsa wata waya,mummy ta dubeshi
"bakaci komai bafa samir?"
"mommy,am late"
"a maka packaging ka tafi dashi mana,ya zaka fita aiki babu
cikakken abinci a cikinka"
"ba komai mommy,zan nemi wani abun naci idan na samu
break"
"a'ah..,.najwa......maza,shiga kitchen ki cewa baraka ta
baki warmers qanana"fuska tadan bata
"Mommy.....yace a barshi fa"idanu ta fitar mata gaba daya
"ni kuma nace ki dauko....."tuni ta miqe ma kafin
mummyn ta qarasa bayani,saboda wani kallo da samir din ya jefeta dashi,harta
soma takawa tajishi yana fadin
"dawo ki zauna,jawahir.....jeki dauko,guda daya ma is
ok"taf tsoro ya cika cikinta,saboda ba kasafai yake bi takanta ba,tana
tsoron irin wannan kallon nasa,saita ci gaba da tafiya ta miqe zuwa kitchen
din,wata tsawa ya watsa.mata wadda ta sanyata tsaiwa,ta kuma kasa juyowa,har
jawahir tazo ta wuceta da saurinta kuwa kamar yadda ya umarceta
bata motsa ba har sai dataji fitarsa
yana cewa idan an zuba jawahir din ta miqa masa yana cikin mota.
koda ta koma harara
Mommy ta bita da ita,sannan ta rufeta da fada,tana kallon fuskar jawahir,da
alama taji dadin yadda mummyn ta balbaleta da fadan,sai tayi sakato,mamaki fal
ranta,me yasa mummy ke mata fada da zafi har haka?,bata tanka ba har jawahir ta
fice daga parlour din,saita dauki jakarta dake gefe wanda dama shirin makaranta
tayi,kawai ta fice a falon.
yana daga zaune a
driver seat ta buda gidan baya ta sanya warmer din sannan ta rufe,saita zagayo
inda yake zaune din,fuskarta da murmushi
"a dawo lafya yaya"
"Allah yasa"ya amsa yana shirin rufe murfin
motar,saidai jawahir din bata matsa ba tana tsaye still a wajen,kansa ya daga
bayan ya sauke glass din motar yana dubanta
"ya akayi auta?"murmushi ta sakeyi
"kayi haquri yaya da abinda ya najwa keyi....ni kaina
bansan meya canza ba"qawataccen murmushin gefan baki ya saki
"karki damu, she's still my sister.....ina tunanin tana da
damuwa,but we will talk later"kaita gyada kawai kana taja baya,ya tada
motar a nutse,ya qarasa bakin gate ya danna horn,idanunsa saman fuskar mai
gadinsu da yaketa marmashe gyada yana zubawa cikin jiqaqqen garin kwaki,ya taso
da hanzari ya durfafi qofar zai budeta,sai samir ya yafitoshi da hannu,don haka
yabar bude qofar ya iskoshi da sauri ya iso bakin window inda samir ke zaune
"Allah ya taimaki saraki"
"an tashi lpy baba"
"lafiya qalau dana"
"abinda aka dafa ne yau baba bai maka ba,na ganka da
garinka harda gyada?"samir ya tambayeshi yana dan murmushi,murmushin shima
yayi,a ladabce yace
"ko daya mai gida,yau dai bamu samu abun karin
bane"fuskarsa cike taf da mamaki bayan yadan yamutsata yace
"kamar yaya?,kune baku da sha'awar ci?"da sauri ya
girgiza kai
"ko daya,Allah ya taimakeka wazaiqi abinci irin na gidan
professor?,inajin dai yau da gobe ne irin ta bahaushe,wani lokaci ku samu,wani
lokacin kuma saidai kowa ya siya abinda yake dashi"baice komai ba saiya
duba agogon hannunsa,bashi da lokaci da cikin gidan zai koma,bai zaci wasu
cikin gida dake rayuwa tare dasu ba'a basu abinci ba,saiya bude aljihun gaban
motarsa ya aciro yan dubu dubu guda biyu ya miqa masa
"gashi,ka ajjiye wancan ka siya wani abun me dumi
kaci"hannu bibbiyu yasa ya amsa kudin yana zabga masa godiya,sannan ya
tafi qofar ya dage masa gate din,yaja motar da dan hanzari ya fice.
1/7/22, 08:18 - Buhainat: Halin Girma
  9
*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi
08184017082 or 09134848107*Â
I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my
photos and videos.
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb
***
Yana jin sanda motar ta tsaya, ya juyo da sauri ya kalle shi,
hankalin sa na kan wayar sa yana dannawa, fuskar sa a hade tsaf babu alamun
wasa ko kadan, tsoro ne ya sake shigar Khalil din sosai, yaji kamar yayi ta
kurma ihu yana neman taimako, amma kuma ya san babu wanda zai taimaka masa
musamman idan aka zo aka ga wanda yake tare dasu.
 Ji yayi an murda handle din bangaren sa, yayi saurin
matsowa sai gashi a tsakiyar motar, daf da Moh, wani banzan kallo ya watsa masa
da ya sakashi saurin komawa inda yake zaune.
"Come ou!" Wani murdadden soja yace matsa bayan kofar
ta gama budewa, idanu ya soma rabawa tsakanin Moh da sojan fuskar sa ta nuna
matukar tashin hankalin da ya shiga
"I said come out!" Ya daka masa tsawa da ta saka shi
saurin fitowa
"Dan Allah Oga kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan ne da
rashin hankali, duk abinda na farfada ba wai har zuciya ta bane wallahi."
Ya hau magiya yana kallon Moh da yayi kamar baya wajen, damtsen
hannun sa sojan ya kama ya shiga jan sa har zuwa wata kofa in da ya hangi
sojoji sun fi su ashirin suna tsalle tsalle a wajen.
"Oga dan Allah ka bawa oganku hakuri Dan Allah!"
"Kasan waye oga kuwa?"
Da sauri ya girgiza kansa
"Ban sani ba wallahi, rashin sani ya jawo nayi masa abinda
nayi amsa amma dan Allah na tuba yayi hakuri."
Dariya sojan ya saka sosai
" Baka da hankali amma, ka zo har nan wajen kayi tunanin
zamu kyale ka, ka tafi free? Nah sai mun dan sassamaka yadda gobe ba zaka kara
ba. "
" Dan Allah nace fa? Ka tayani bawa ogan hakuri. "
" Naka wasa ne. "
Yayi gaba yana rik'e dashi, yanayin rikon da yayi masa da yanayin
jikin Khalil din zai baka dariya sosai, dama bashi da wani jiki sosai gashi
kuma a hannun manyan maza, wani daki ya kaishi sannan ya sake shi yana masa
dariyar mugunta
"Zaka kwashi kashin ka hannu yau, wallahi Oga zai iya sawa
a batar da kai a k'asar nan, kasan waye kuwa? Tab."
Jawo masa kofar yayi ya rufe ta har da key yana kwasar dariya.
 Chan karshen dakin yaje ya tsugunna yana jin dana sanin
barin zancen da yayi, dama a maida baya da ya goge duk abun da yace ma Muhammad
din cikin rashin sani. Ji yayi cikin sa na kara alamar ya lalace, ya tabbatar
bala'in tsoro da firgicin da ya shiga ne ya saka cikin nasa lalacewa. Mikewa
yayi da sauri ya hau zagaye a dakin yana maimaita
"Innalillah wa inna ilaihi rajiun."
Ji yayi ana murda key din dakin, ya tsaya yana kallon kofar
cikin tsoro. Captain Moh ne ya shigo sojoji biyu na biye dashi a bayan sa, daya
rik'e da kujera yazo ya ajiye masa ya zauna yana wa Khalil murmush
"Alhaji Khalil barka da warhaka."
"Dan Allah dan Allah kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan
ne da yarinta wallahi amma ba zan sake ba."
"Haba Khalil, so soon haka? Ka sani ko sojan gona ne ni,
kasan fa talaka da samun wuri."
"Wallahi ni dai ba zan sake ba, kayi min rai, mahaifiyta da
ni ta dogara, dan Allah."
"Calm down magana zamuyi, ka nutsu ka saurare ni, warning
ne me hade da dokoki, ina fatan zaka bud'e kunnuwan ka kaji ni sosai."
"Ina ji wallahi."
"Babu kai babu abinda ya zama mallaki na, Ina nufin Fatima,
ko a hanya ka hadu karka taba nuna ka santa balle har magana ta hada ku, a da
nayi niyyar barka ka gwada sa'ar ka akanta, amma kuma a yanzu na gama yanke wa,
baka kai na nemi abu tare da kai ba, dan haka ko son ta zai kashe ka sai dai ka
hakura... "
" Na biyu, a yau ba sai gobe ba zaka wuce in da ka fito, ba
tare da ka bud'e bakin ka kace wa kowa komai ba, ina nufin, bakin ka ya zama
kanin kafar ka, kar naji zancen a wajen kowa ciki har da ita yayarta ka da bata
tsoron Allah. "
" Last but not the list ka koma bakin aikin ka, ka rik'e
mutuncin ka sannan bakai ba wulakanta kowa. "
" Duk abinda ka fad'a wallahi zanyi, nayi alkawari, ni dai
kar ka raba ni da mahaifiyata wallahi bata da kowa sai ni. "
" I'm done with you, gashi nan take him back, ku tabbatar
ya bar Kano kafin karfe shida na yamma. "
Juyawa yayi cikin wani irin taku ya fice daga wajen, yana fita
sukayi kansa
" Ai wallahi ba zaka shigo nan a banza ka fita bamu ci
ladan ka ba. "
Wani soja yace yana kai masa rankwashi.
" Tashi kayi frog jump. " Dayan ya daka masa tsawa yana
zaro belt dinsa. Da sauri ya hau yi yana hada zufa su kuma suna tuntsura
dariya, sai da suka gajiyar dashi sosai sannan suka fito dashi suka sashi a
mota suka maidashi har kofar gidan suka ajiye sannan suka tafi.
***Abba na zaune yaji text message ya shigo wayar sa, tunanin sa
ma ko alert ne ya bud'e sai yaga sako daga bakuwar number da be sani ba, bud'e
message din yayi ya soma karantawa
_" Dr. barka da warhaka, ya aiki? Allah ya taimaka. Dama
wata magana nake son yi akan fatima, ina rokon alfarmar daka saka ido sosai
akan abinda yake faruwa a cikin gidan, in sha Allah zaka gano wani abu da ya
dade yana faruwa ba tare da sanin ka ba. Sai anjima a huta lafiya. "_
  maimaita karanta sakon ya dinga yi yana kokarin
daidaita tunanin sa waje guda, waye ko wace wannan? Me sakon yake nufi? Me ya
faru da Fatima din? Duk wadannan tambayoyin ne suka shiga yi masa yawo aka, be
san me yasa ba, kawai sai yaji hankalin sa ya kasa kwanciya da abinda ya
karanta. Tashi yayi ya fito zuwa falon gidan, ya k'wala kiran Iman din. Zeenat
ce ta fito
" Ina Ummi? "
" Ina ga tana wajen Gaji. "
" Je ki kira min ita. "
Fita tayi shi kuma ya cigaba da tsaiwa awajen har suka shigo a
tare.
" Ki same ni a daki na. " Yace yana juyawa tabi
bayanshi, dariyar mugunta Zeenat tayi a tunanin ta wani laifin Iman din tayi
dan sosai yanayin Abban ya nuna bacin rai.
A gefen gadon sa ya zauna, ta samu chan gefe daga kasa ta rakube
tana tunanin dalilin kiran.
" Kina jina Uwata? Kina da wata matsala wacce ban sani ba?
"
Girgiza kanta tayi
" A ah Abba babu. "
" Kalle ni nan, ni ne mahaifin ki, baki da wanda yafi ni
bayan mahaifiyar ki, ki fad'a min gaskiya idan akwai wani abu da yake
damunki."
Zuciyar ta ce tayi rauni, taji kuka na taho mata, ta k'asa rike
shi kawai ta fashe da kuka. Dafe kansa Abban yayi, ya shiga tunanin me yake
faruwa? Wanne irin abu ne haka da har shi ya kasa ganewa?
"Fatima..." Ya kira ainihin sunan ta a karo na farko a
rayuwar ta
"Na'am." Ta amsa cikin muryar kuka
"Kowanne bawa da irin yadda rayuwa take zuwar masa, kiyi
hakuri zanyi bincike, sannan akwai shiri da nake yi na kaiki wajen mahaifiyar
ki da zarar maganar bikin ku ta tabbata, nayi mata alkawarin kai mata ke da
zarar lokacin auren ki yayi, mahaifiyar ki na son ki fiye da yadda take son
kanta, ki rik'e wannan."
" Tashi kije kinji, ki daina kukan haka."
Tashi tayi bayan tace
" Nagode Abba." Ta fice ya bita da kallo yana jin
kamar be kyauta mata ba.
Dakin su ta wuce ta tarar da Zeenat na waya har da shewa, juyawa
tayi zuwa store ta zauna a gefen katifar ta, tayi kuka sosai har sai da taji
babu abinda yayi saura a zuciyar ta. Tsawon lokaci ta sauka a ciki har sai da
taji maganar Mama tana fad'a a waya anan ta gane ta dawo dan dazu bata gidan.
Tashi tayi ta fice ta kofar baya bayan ta gyara fuskar ta a sink din kitchen.
***Zama Mama tayi tana sababi akan tafiyar Khalil din babu
sanarwa, sai dai a k'asan zuciyar ta taji dadin hakan domin a kalla hankalin sa
zai dauke daga kan Iman din har a gama magana da shi dayan da yazo. Abba ne ya
shigo ya sameta tana zaune , ya zauna a gefenta sai tasha jinin jikin ta
musamman da ta gama sanin halin sa tsaf.
"Me yasa kika ce min Ibrahim ba da gaske yake akan maganar
Ummi ba, sannan shi kuma yaje ya samu Yaya da maganar."
Yadda ta zabura yaso bawa Abban mamaki.
"Khalil din ne yaje wajen Yaya? Yaushe akayi haka? Me yayan
yace masa?"
"Duk ba wannan na tambaye ki ba, baki bani amsa ta
ba."
"Toh toh ai gani nayi shi Khalil ba yanzu zai yi aure ba,
su kuma yaran nan yanzu ne muke so mu aurar dasu, bana so Zeenat ta tafi da bar
Iman tunda kaga tare suke komai, shiyasa nace gwara wanda ya shirya."
"Haka ne kuma." Yace yana mata wani irin kallo da ya
sakata tunani sosai
"Toh hakan yayi ai, Ina fatan dai zeenatu ta sallami yaron
nan Bashir ko? Dan ina nan akan bakana ba zan bashi ba."
"Dan Allah Dr ka bar wannan maganar, tunda tana son shi
kayi hakuri kawai ayi tunda an wuce zamanin da za'a yi wa yara auren
dole."
Girgiza mata kai yayi yana dakatar da ita
"Wannan maganar taki shirme ce, musulunci mu ya bawa damar
zaba wa yayanmu mazaje na gari, dan haka ban yarda da Bashir ba, idan akwai
wani ta kawo shi."
Ya tashi ya fice ransa na baci da yadda maganar Bashir din taki
karewa, sam Hajara bata shirya gane abunda yake hango musu ba, eh hango musu
tunda duk in da aka je aka jawo ita uwa sai tafi cutuwa da abinda zai samu
yarta.
***Text message biyu ya tura a lokaci daya, address din sa da
Abba yace ya tura masa ta message sai kuma message din da yayi wa Abban Iman
din, wanda yake ganin shine kadai hanyar da zai bi wajen hana Maman sanin duk
wani abu akan Iman din, ya tabbata daga lokacin Abban zai saka ido sosai, ba
kuma za'a dau lokaci ba zai gano komai, shi kuma sai yayi amfani da wannan
damar ya nemi alfarmar barin komai ya zama sirri a tsakanin su iyaye maza,
domin dama su iyaye maza baa sansu da ratatin zance ba, ba kasafai ma suke zama
suyi ta magana anyhow ba, ya tabbata idan har hakan ta yiwu toh zai samu abinda
yake so, zai kuma tabbatar da Fatiman sa ta samu gatan da bata taba tunani ko
hasashen samun sa ba.
***Tunani Abba ya fad'a ganin address din da Muhammad ya turo
masa a matsayin in da yake,Emir Palace Kano, Emir Palace Adamawa-Yola, me hakan
ke nufi? Kiran Abban su Fatiman yayi yazo ya same shi a part din sa, ya nuna
masa message din sannan ya kira sauran yan uwan su Abba Musa suka hau
tattaunawa akan abinda ya kamata su yi. Dama chan Abba Musan yana siyasa sosai,
sai sukayi shawara akan shi ne zai wuce gaba wajen binciken waye Muhammad din a
cikin kwana uku kachal. Haka kuwa akayi, washegari ya same su da maganar da ta
yi matukar basu mamaki. A yadda suka sani idan wani daga cikin irin wannan yaga
yarinya yana so, kawai aikawa ake iyayenta suzo ayi magana a fadar sarkin, a
matsayin shi sarki dama uban kowa ne, sai suga ga banbanci inda Muhammad din
yazo kai tsaye ba tare da ya nuna shi din waye ba, ba kuma tare da ya nuna
karfin iko na mulki ba, hanyar da ta dace da kowa yake bi wajen neman aure
shima ita yabi.
 A cikin su babu wanda be yi amanna da maganar ba,
musamman binciken da Abba Musan yayi da irin yabon da Muhammad din ya samu daga
wajen mutane da dama musamman mazauna masarautar.
  Shiru Abba yayi bayan kowa ya gama tofa
albarkacin bakin sa, aka bashi dama a matsayin sa na mahaifin Iman din,
"Bakwa ganin idan iyayen yaron nan suka san in da yazo
neman aure zasu kyale shi, duba da mu din ba wasu bane akan irin girma da
nasabar gidan da ya fito."
"Idan har a yadda bincike na ya nuna min ne, iyayen sa basu
da matsala masu son talakawan su ne, dan haka muyi addua kawai in sha Allah
alkhairi ne."
"Shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi,."
"Yanzu kayi magana, Amin ya Allah."
" Ina neman alfarma daya, da mu bar maganar nan a tsakanin
mu zuwa muga abinda Allah yayi."
" Hakan yayi, Allah ya shige mana gaba."
Suka hada baki a tare, sai kuma suka shiga wata hirar tunda
daman su dan dade basu yi irin wannan zaman ba, anan duk suka ci abinci a tare
sannan kowa ya tafi zuwa sabgar sa. Aka bar Yaya a zuwan zai kira Muhammad din
da daddare ya sanar dashi ya bashi izinin yazo yaga Fatiman su daidaita, da
daddaren bayan ya gama komai ya turawa Muhammad din text message akan ya cigaba
da zuwa. Muhammad na zaune shi da Musaddik suna kallon video da ya saka akayi
wa Khalil suna kwasar dariya text din ya shigo, tashi yayi ya daka tsalle kafin
yace
"Yess!!!
" Ya akayi?"
" Karfe nawa yanzu?"
Yace yana kallon agogon falon
" Opss Ashe dare ya fara, ba dan ba dan ba da yanzu zanje
na ganta, amma ba komai kafin na wuce Abuja zan tsaya na fara ganin ta."
" Me faru wai."
" Karanta!" Ya mik'a masa wayar
" Ah congratulations angon fatiti, Allah ya tabbatar mana
da alkhairi."
Rik'e k'ugu yayi yana hararar sa
" Allah ka sake bata mana suna sai na saka frog jump, kaji
ma na ratse."
" Kut! Allah fa ka raina ni Moh, komai sai kace zaka sani
frog jump an fad'a ma nima kamar wadanchan dogs din naka ne na bakin
gate."
" Ka dai kula, kana magana ne da Captain Muhammad Ahmad
Santuraki, Captain Moh!"
" Whatever, ni dai muhammadu na sani, ba wani bragging da
zaka min."
" Zaka gane ne idan na dauke ka na je na jefa wa mayunwatan
zakunan nan na barack, ba zaka sake kiran sunana gatsal ba."
" An gaya ma kowa irin khalil ne? Lusari!"
Dariya suka saka Muhammad ya shiga gwada yadda Khalil din yake,
suka sake tuntsurewa da dariya suka tafa
" Ashe farar kura ce a wajen, sai uban cika baki dan iskan
yaro, gobe ma ya sake, naso ka dan saka su sun sassama masa jiki
wallahi,."
" A hakan ma nasan sai sunci zalinsa ai."
" Wicked soul!" Yace yana dariya
" Naji, bari naje na kira Baby na, naji voice dinta me dadi
kafin gobe naje na ganta, dan yanzu ina da license, na matsu na ganmu tare,
muna yawo a garin nan cikin mota my hands in to her's, ga cool music na tashi
Malam, wow love in the air."
" Toh Mr Romeo, Allah ya kaimu dai zamuyi kallo, yadda kake
son ta Allah yasa tana maka ko rabin sa ne."
" I don't care, as long as munyi aure, zan koya mata yadda
zata so ni."
" We shall see."
***Ruwan zafi ne a katon bawo, Khalil na zaune a gaban ruwan
hajiyar su na danna masa bayansa, gaba daya jikin sa ciwo yake kafarsa kamar
zata cire yake ji, babu irin tambayar da batayi masa akan me ya same shi ba
amma yaki fad'a mata, haka Mama ta bugu tana fad'an tafiyar Khalil din hajiyar
ta fad'a mata a yadda ya dawo, kuma yaki cewa komai. Yana jin su har suka gama
ya tashi ya koma dakin sa ya kwanta yana tariyo abinda ya faru cikin tausayin
kansa. Shi ya jawo yana takama da shegen bakin sa ya je ya kaishi ya baro, dama
an fad'a mutum ya kiyayi harshen sa, akwai hadisi guda da akayi magana akan
harshe da kiyayar sa, yaga izina a kansa, gashi bashi da damar fadawa wani
abinda ya faru domin yasan shi za'a yi wa dariya, ko da muhammadu a iya soja ya
tsaya matsayin da yake kai ya isa ya taka shi son ransa ba kuma wanda ya isa
yace dan me? Balle ganowar da yayi waye Muhammad din, anan ya gane bakin rijiya
ba wajen wasan yaro bane, shi din ma ganganci ne da kuruciya. Eh toh kuruciya
mana tunda dai yasan a girme Muhammad din zai girma shi dole ya fishi hankali
da komai. Abu daya ne zai hana shi walwala, yadda zai yi da tarin soyayyar ta,
gashi yayi masa kashedin ko a hanya babu shi babu ita, ya kuma tabbatar idan
har ya kuskura yayi wani abu, za'a iya neman shi ma baki daya a rasa, dan masu
kudin nan yasan ba wani abu bane a wajen su su batar da mutum bat, har abada a
daina jin labarin sa.
  Tagumi ya rafka yana jin kamar yayi ta kurma ihu
ko yaji sassaucin radadin da zuciyar sa ke masa. Allah sarki Khalil 😂
1/9/22, 10:17 - Buhainat: Halin Girma
  10
*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi
08184017082 or 09134848107*Â
I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my
photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb
***Be ji sallamar ta ba, sai ganin ta yayi kawai a dakin bayan a
zahiri tayi sallamar amma saboda baki daya hankalin sa na ga tunani shiyasa be
ji ba sam.
"Ya Khalil wai a kawo maka abinci..."
Ai kafin ta karasa ya daka mata uwar tsawa
"Uban abincin, dallah Malama karki dame ni."
"Toh... Me yayi zafi? Hajiya ce ta aiko ni ai."
"Fitar min daga daki!" Yace yana tasowa, da gudu ta
juya tana dariya, sai da ta ga ta fice sannan ta daga murya tace
"Bani na kar zomon ba..."
Ransa ne ya sake baci, ya bigi kofa yana komawa ya fad'a saman
katifar sa yana jin kamar yayi ta cizon kansa.
A falo ta samu Hajiya ta zauna tana haki
"Allah ya taimake ni na kusa cin duka, daga tambaya kawai
ya hayayyako min Hajiya."
"Toh wai ko dai Khalil tsokana yayo ne aka tattaka shi,
kinsan fa Khalil ba dai tsokana da cika baki ba."
"Alamu dai sun nuna Hajiya, fad'a ya takalo da yafi karfin
sa wallahi, gashi nan yaki fad'an abinda ya faru."
"Toh Allah ya kyauta " Hajiyan tace tana tashi ta fita
zuwa dakin nasa.
***Tana tsaye a bayan kitchen dinsu, wanki ta gama tana ta sauri
saboda kwana biyu bata maida hankali zuwa islamiyya saboda abubuwan da suka
sako kai, tana wankin tana tunanin maganar da sukayi da Abba da ta zama tamkar
bitar karatu haka take yin sa, takun tafiya taji, ta juyo sai taga Abban a
tsaye yana duban ta, da sauri ta dan russuna,
"Abba sannu da zuwa."
"Wanki ake ne?"
"Na'am.?" Tace tana zaro ido sanin cewa ba da sanin sa
take wankin ba, musamman ya samu almajiri yake wanke musu kaya ita da Zeenat da
Marwan yake biyan shi ta hannun Mama, duk da yasan dole zasuyi wanki irin kayan
ciki da abubuwan da ba za'a iya bawa me wanki ba, amma kuma tarin kayan da ya
gani a wajen da ya gane na Marwan ne sai wasu na Maman ya saka ransa mummunan
baci, har a jiya sai da Maman ta karbi kudin wanki a wajen sa da zumar yau me
wankin zaizo karbar kudin sa ya kuma bata babu musu. Yanayin sanyin garin zai
yi wuya wajen wanki musamman da tun da dadewa yasan fatar Iman din bata son
wahala idan tayi wanki hannun ta kanyi ja sosai, shi kuma Allah ya hore masa
son yaya Kuma gasu ba wai yawa ne dasu ba shiyasa duk wani aikin wahala baya
son siyi duk da ba wai kwata kwata ba zasuyi komai ba, amma kamar wanki yana
ganin be kamata shima a saka shi a cikin aikin mata ba, mata na wahala da aikin
gida kula da yara da girki wankin aka dauke musu zasu samu sassauci. Matsowa
yayi ya sake leka kayan kafin ya girgiza kansa ya juya bayan yace
"Ki bar wankin nan kizo ki wuce ciki."
Sakalo tayi a tsaye tsoro na kamata
"Bakya ji ne?" Ya daka mata tsawa, da sauri ta bi
bayansa har cikin gidan, dakin su taga ya wuce ya kwankwasa sannan ya tsaya
"Waye?" Zeenat tace tana daga kwance cikin rufa, a
yadda tayi maganar zaka gane knocking din ya takura ta, sake kwankwasa wa yayi
sannan ya tura kofar da sallama, be shiga ba, ya tsaya a kofar yana karewa
dakin kallo, gadon zuwa katifar dake shinfid'e a kasa da ta tabbatar masa da ta
Iman din ce. Tuna lokacin da ya bada kudin gadajen nasu yace a siyawa kowa nasa
amma sai Mama tace daya ya ishesu me dan girma saboda hakan zai sake shakuwa
tsakanin su,da wannan yayi amfani a ganin sa hakan ne ya kuma dauki hakan a
matsayin soyayyar da Maman ke wa yar tasa. A yadda yake jin zuciyar sa a lokacin
zai iya yin komai, sai kawai ya fice daga gidan gaba daya ba tare da ya koma
daki ba.
Tsoro ne ya kama Iman
musamman da bata san me zata ce wa Maman ba akan wankin, shiryawa tayi cike da
fargaba ta tafi makarantar tana fatan koma menene ya taso ya zama daidia kafin
ta dawo dan a rayuwar ta, ta tsani tashin hankali ko kad'an.
Rabi da kwata bata gane
kan karatun ba, haka dai ta taho gidan tana ta zulumi, tana shigowa ta ganshi a
tsaye ya harde hannayen sa a gadon bayan sa yana kallon kofar shigowar. Shigar
jikin sa ta bi da kallo zuwa gyaran da yayiwa fuskar sa, murmushin da ta gani
kwance a fuskar tasa, ya saka ta samun nutsuwa har ta karaso wajen da yake a
tsaye.
"Ashe kina kusa da shigowa, naji a jikina."
Murmushi tayi kafin tace
"Sannu da zuwa."
"Yawwa, ya hanya?"
"Alhamdulillah wallahi.*
" Akwai wanda ya kalleki da kina tahowa? Idan akwai fad'a
min naje na same shi."
Sosai ya bata dariya,
" Kai... Babu kowa fa, ya gida yasu Mama?"
" Mama? Ammi muke ce mata, tana nan lafiya tace ma na
gaishe ki, na gaida wacce ta kwace mata yaronta kafin tazo haka tace."
Rufe fuskar ta tayi tayi yar dariya
" Allah sarki, ina amsawa nagode."
" Itama ta gode, tace ta matsu ta ganki."
"Watarana zata ganni in Sha Allah."
"In Sha Allah, very soon."
"Abba Babba yace idan kazo ka shiga ciki."
" Da gaske? Kice na zama dan gatan Abba."
Dariya tayi
" Naga alama kam, Abba ya yarda da kai sosai."
" Allah sarki, ai yana da kirki sosai."
" Sosai." Tace
" Bari na bud'e maka, chan ne seat room din sa."
" Owk." Yace ya harde a jikin ginin yana kallonta, har
ta bud'e ta dawo sannan ya bita a baya yana admiring steps dinta zuwa ciki.
A kofar dake farkon
kofar ya zauna ita kuma ta shiga ciki, yana zama Aliyu ya shigo da ruwa a tray,
ya ajiye ya gaishe shi sannan ya fita, ruwan ya dauka ya sha sosai sannan ya
kalle ta, gefe take kallo tana wasa da jikin kujerar da take kai.
" Zahraah, tafiya ce ta kamani, ba zan iya wucewa ban sanar
miki ba, ba wani dadewa zan ba in sha Allah, inaso kafin lokacin da zan dawo mu
sake fahimtar juna sosai, idan na dawo sai a shigo da magana me karfi, bana so
a ja lokacin."
" Allah ya kiyaye ya tsare, ya dawo da kai lafiya."
" Amin ya Allah, Amin Amin Zahraah Nagode"
Shiru ne ya dan shiga tsakani, shi yana kallon ta yana sake
ganin ainihin kyawun ta, ita kuma ta tafi tunanin Allah yasa ya dawo din kar
taji shiru idan ya tafi, har zuciyar ta bata son tafiyar tasa, amma kuma ya
zatayi? Ba zata hanashi ba ai.
"Ina wannan yayan naki da muka hadu ranar nan? Har ya korar
min ke?"
" Uncle Khalil?" Tayi dariya
" Auw sunan shi kenan."
" Eh kanin Mama ne, a nan gidan ya taso kafin ya koma
gida."
Gid'a kansa yayi kamar be sani ba
" Shiyasa ya nuna min iko kenan."
" Uhum." Tace kawai bata ce komai ba.
"Yana ina kuwa?"
"Kamar dai ya koma, naji dai mama na fad'an ya tafi be
sanar ba."
"Ai be isa ya sanar."
"Na'am?" Tace tana kallon sa
"Sorry ba komai." Ya maze kamar be ce komai ba, be san
maganar zata fito ba shima.
" Bari na gudu, kar nayi rana."
Mikewa tayi
" Daga nan zaka wuce?"
" Eh gaskiya, idan na koma gida na koma baya."
" Ok ina zuwa."
Ta fita ya tashi ya dan zagaye falon yana observing komai na
ciki, yana tsaye jikin wani frame ta shigo dauke da leda ta mika masa tana dan
russunawa
" Gashi ka kaiwa Ammi, ina gaishe ta."
Rik'e ledar yayi yana kallon ta, tayi saurin dauke kanta k'asa
ta sakar masa ledar gabanta na faduwa.
" I love you."
Ya samu kansa da whispering cikin muryar da tayi masifar shigewa
ciki, wani irin feeling taji, sarai ta jishi sai tayi kamar bata ji ba, ta ja
baya sosai tana diriricewa, shi kansa wani iri yake ji, be taba tunanin haka
daga gareta ba, da tasan yadda Ammi take a wajen sa, da kuma yadda sakon nan
yayi nasarar kara masa son ta ninkin ba ninkin, da tun ranar da ya fara zuwa
tayi, kasa matsawa daga in da yake yayi, sai murmushi yake shi kadai.
"Nagode sosai, Ammi ta gode."
"Ba komai." Tace tana jin nauyi da kunyar yadda yayi
"Zan tafi, ki kula da kanki kinji? Karki yarda wani ya bata
miki rai, kin fi karfin haka, ke din ta daban ce, ta musamman ce."
"In Sha Allah." Tace tana jin dadi , a kalla idan tana
tare dashi tana jin cewa itama tana da yanci, sannan takai matsayin a so ta.
Ta cikin idon sa yake ta
kokarin aika mata da sakon sa, sakon da yake so ya tafi ya bar mata, irin me
zafin nan da zatayi wuyar dauke shi daga tunanin ta, sau daya ya samu nasarar
aika mata da sakon, ya kuma je a yadda yake so, sai ya marairaice mata fuska
yana jijjiga kansa.
"Allah ya kiyaye Allah ya kaimu lafiya." Tace da sauri
ta bud'e kofar kuusa da ita ta fice ta bar shi a ciki, dariya sosai ya saka, ya
sake rik'e ledar hannun sa gam gam, ya fice yana jin sa tamkar yana yawo a
cikin gajimare.
A kafa yake tafiya rik'e da ledar, iska na kada shi, sam baya
jin komai baya ganin kowa sai tsadadden murmushin sa, shi kadai yasan yadda
yake ji a lokacin, shi ya saka shi tafiya kawai ba tare da ya neme su ba. A
chan bayan layin da suka saba haduwa suna tsaye tana masa mitar kwana biyu be
zo ba, hakuri yake bata akan wata tafiya ce ta taso masa Muhammad din yazo
wucewa
"Kaga saurayin Iman."
Tace da sauri tana nuna masa shi. Wani kallo Bashir yayi masa
daga nesan kafin yayi saurin juya bayan sa, yayi saurin bud'e motar ya shiga
ciki, yayi kamar yana neman wani abu a ciki
"Baby me kake nema? Fito ku gaisa da Malam mana."
Kin fitowa yayi ya cigaba da bud'e dashboard yana rufewa,
"Assalamu alaikum." Moh yayi musu sallama yana karewa
motar kallo.
A wani yanayi Bashir ya fito bayan nacin da Zeenat din tayi
masa, ya diririce ganin Moh din
"Sannu ko?" Moh yace masa yana mika masa hannu
"Sunana Muhammad, kaifa?"
Yace masa, a sakale Bashir ya miko nasan hannun kamar me tsoro
cikin rada rada yace
"Bashir."
"Yayi Bashir, sai anjima." Ya wuce ba tare da yace
komai ba. Dariya Zeenat ta saka
"Shi wannan din kika ce shine zai auri Iman?" Yace da
sauri
" In Sha Allah, baka ga sun dace ba? Ko baka ga yanayin su
daya bane?"
" A haka yake tun zuwan sa gidan kuma?
"Babe me ta faru?"
"Noo noo babu komai."
"Naga duk ka damu ne, me ya faru?"
" Ah babu komai, kawai na ganshi haka haka ne."
"Dan ma baka ganshi sanda ya fara zuwa bane, tab!" Ta
sake kwanshewa da dariya
"Abun mamaki." Ya furta ba tare da ya sani ba.
"Abun mamakin gaske , mutum kamar wani mahau."
"Keee." Yace mata yana zaro ido, sai kuma ya waske da
sauri
"Bari naje, ya kamata mama tayi tayi ya shawo kan Abba ina
so na turo manya."
"Ka turo kawai, ka bar komai a hannu na, bbu me min auren
dole, wanda nake so zan aura babu me hanawa."
"Toh shikenan."
Sallama sukayi ya tafi itama kuma ta koma gida, tana shiga ta
tarar da Abba a compound, ya tasa ta a gaba ransa a bace.
***Wani kallo da Maman tayi wa Iman lokacin da ta shigo ya saka
ta shan jinin jikin ta, ta wuce bayan ta gaishe ta bata amsa ba, ta ajiye jakar
ta sannan ta fito ta shiga kitchen ta sha ruwa ta dora ruwan abinci sannan ta
fito falon, tana tsaye ya hade ran ta sosai, ta tsaida ita
"Uban waye ya baki izinin ajiye min wankin da na sakaki? Ka
tafi?"
"Ubanta ne!" Abba da suka shigo tare da Zeenat yace,
da sauri Mama ta juyo sukayi ido biyu dashi
***Ba karamin matse kaina nayi ba saboda na cika alkawari, kuyi
hakuri babu yawa
Post a Comment for "HALIN GIRMA 6-10"