Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

HALIN GIRMA 41-45

   


   _Halin Girma_

            *41*


***Ruwa ta fara ambata sanda ta farka, da sauri Mamma tayi wajenta itace take tsaye dama, Mummy na kan sallaya tana lazimi ta mike da sauri cikin tsananin farin ciki.


"Alhamdulillah." Ta furta tana karasa kusa da Mamma da take jera mata sannu, da ido kawai take bin su tana son tuna abinda ya faru karshe. Murmushi tayi cikin dauriya tace 


"Mamma."


"Na'am Iman, sannu kinji?."


" Alhamdulillah mun auna arziki. " Ta juya tana fadawa Mummy da ta kasa boye farin cikin ta


"Fatima. "


"Mummy. "


" Sannu kinji, akwai abinda yake Miki ciwo? "


Da hannu ta nuna cikin ta, taba cikin Mummy tayi kila saboda wankin cikin da akayi mata ne, 


" Bari nayi musu magana tunda ta farka. "


" Bari naje. " 


Mummy tace tana yin gaba, ta bar su da mamma tana tambayar ta. Tare suka shigo da nurses su biyu, mamma ta matsa suka duba ta, sukayi mata tambayoyi sannan suka ce a bata ruwa tasha da abinci sannan suka fita daya ta sauki file din ta daya kuma ta tafi kawo mata magunguna daga pharmacy. 

   Taimaka mata mamma tayi tunda an cire drip din ta kai ta toilet, ta gasa mata jikin ta, ta taimaka mata tayi wanka da brush kafin ta fito Mummy ta hada mata tea me kauri da kidney pepper soup da aka kawo daga fada.

  Daure da alwala ta fito bayan ta sauya kayan jikin ta zuwa doguwar riga mara nauyi ta saka Hijab ta zauna a gadon ta biya bashin sallolin da suke kanta, sai da ta idar sannan ta dan ci abincin kad'an ta koma ta kwanta lamo tana jin jikinta babu kwari ko kad'an.

   Abba ne ya shigo tare da wasu  mutane masu rawani, suka dubata sukayi mata ya jiki sannan suka tafi, Abba ya rakasu ya dawo ya zauna yana sake dubata. Tsam Mummy ta bar dakin ta koma waje ta bar Mamma a ciki suna magana da Abban, ya dan jima a ciki sai da yaga alamar ba zata dawo dakin ba bayan kuma ita ta kirashi da Iman din ta farka sai ya tashi kawai yayi sallama ya tafi akan zai dawo anjima.

   A waje suka hadu da Mummy din, ya sameta har wajen da take zaunen yayi mata magana, ta amsa masa sama sama kamar tana jin haushin sa ko wani abu, be gane dalilin ta ba, ganin a waje ne ga kuma Moh da ya nufo su ya saka shi kyale ta ya tafi, suka gaisa fuskar sa fayau alamun ya samu labarin farkawar Iman din. Komawa yayi ya raka Abban har mota sannan ya dawo, ya tarar da mummy da Mamma din duk a waje, kila Mummy din ce ta sanar mata da zuwan sa shiyasa suka fito ba sai ya shiga su hau fita ba, gaishe su yayi da tambayar ya mai jiki sannan ya danyi jim a wajen sai da Mamma tace ya shiga sannan ya tashi ya nufi dakin da daukin ganin ta. 

   Ko sallama ya maita yayi sai da ya tura kofar ya shiga sannan ya tuna yayi sallama ta dago daga kwanciyar da tayi ta kalle shi. Da sassarfa ya karasa kuwa, ya haye saman gadon ya tattaro ta zuwa jikin sa, ya rungume ta tsam damuwar da yake ciki na raguwa. Luf tayi a jikin nasa tana jin nutsuwar da ta rasa tsawon kwanaki, bata san haka tayi kewar sa ba, sai yanzu da suke tare, kuka ta saka masa ya sake rungume ta yana jin shima kamar ya rushe da kukan. Sai da yaga kukan nata na neman zarcewa sannan ya dakatar da ita ta hanya shafa bayan ta ya shiga magana a kunnen ta


"Shssh... Karki karawa kanki wani ciwon please, you are safe now. Babu wani abu da zai sake faruwa, I will protect you with my life."


Shiru tayi tana jan numfashi, ya cigaba da shafa bayanta har sai da yaji tayi shiru gaba daya, sannan ya dago ta daga jikin sa yana kallon fuskar ta, murmushin ya sakar mata ta maida masa itama.


" Me yake miki ciwo yanzu? "


" Kai na.. " Tace a hankali


" Sannu zai daina a hankali, komai zai wuce, ba zan sake tafiya ba barki ba nayi miki alkawari nan."


Maida kanta tayi jikin sa ta kwantar ya gyara mata kwanciyar yadda zata ji dadi, ya saka hannu yana mata tausa a hankali.


  Sun dade a haka har sai da akayi knocking a kofar, ya zameta ta kwanta sosai akan gadon ya sauka sannan yace


" Bismillah a shigo."


Bataliyar yan gidan su ce, tun daga kan su Ya Maryam da matan gidan hadda Dadah da wasu ma da be san su ba, a gurguje ya gaisa dasu ya bar musu dakin dan dakin ma yayi musu kad'an.

   Dakin da Musaddik yake ya wuce, ya sameshi a zaune ya gama cin abinci, yayi fes dashi jikinsa kuma yayi kyau, kanin sa ne yake kula dashi suka gaisa da Moh din sannan ya basu waje dama yana so yaje ya siyo abu a shop sai yayi amfani da damar ya tafi.


"Jikin ka yayi kyau sosai friend."


"Wallahi Alhamdulillah, mun gode Allah, ya jikin Madam din?"


"Itama Alhamdulillah wallahi, ta samu sauki."


"Masha ALLAH. Allah ya kara mana lafiya baki daya. "


"Amin, ka tabbata kana cikin abokai na gari, Allah ya hada mu tare a inuwar al'arshi, bansan da wanne baki zan gode maka ba, ban kuma san da wanne ido zan kalle ka na gode maka ba, ta ya akayi na kasa ganewa? Na kasa banbance ka da wani daban? How long ka zauna a wajen sa.? "


" Mu daina tunawa dan Allah, tunda ya shigo hannu shikenan nasan dole zai girbi abinda ya shuka. "


" Still dai inaso nasan komai... "


" Ka bari mu koma gida, zan baka labarin komai, for now kayi fucusing akan case din cikin gida, yau saura kwana uku su juya komai, kana bukatar gabatar da evidence din nan."


" Haka ne, kuma abinda ya faru yanzu ya saka na kara jin kowanne abu akwai good side da bad side dinsa, abinda na tsana nake ganin shine kawai matsalar ta, har naki bin umarnin Bubu akai,shi zan yi facing yanzu, zan karbi abinda ya zama mallaki na, zan farantawa mahaifi na kamar yadda ya dade yana burin ganin ranar. "


" Da gaske kake? " 


" Da gaske nake. "


" Kai masha ALLAH, Bubu zai fi kowa murna shi da Aji. Dama a komai alkhairi ake nema ba son zuciya ba,nayi murna sosai aboki na, Allah ya baka sa'a. "


" Amin. " Yace yana daukar ledojin maganin sa


" Kana shan magungunan nan kuwa?"


" Ina sha. "


" Good, da baka sha da sai na saka ka... "


" Frog jump. " Ya karasa masa suka kwashe da dariya suka tafa


" Wallahi ka raina ni, Capt guda, Capt Muhammad Ahmad Santuraki, babu wani respect ko? "


" Ayi hakuri tsohon Capt! "


Duka ya kai masa a kafadarsa, ya goce suka sake kyalkyalewa da dariya.


***Baki daya ta rasa abinda yake mata dadi, ta rasa in da zata tsoma ranta taji sanyi, cikin jikinta yayi masifar takura mata, babu abinda take so take kulafuci sai mijinta Bashir, takanas ta aika aka samo mata irin turaren da yake amfani dashi amma duk a banza, watarana sai ta shiga daki tayi kuka gashi Abba yayi shiru da maganar, ko dan abinda ya faru a kwanakin ne? Babu irin kiran da batayi wa Bashir amma sai yace mata ta kara jira zaizo,. Takanas ta samu Mama a daki da ita ma kanta ta gaji da zaman Zeenat din ta kuma damu da shirun da Abban yayi dama Bashir din. Da kallo ta bita har ta zauna a kusa da ita, tun ma kafin tayi magana ta riga tasan me ya kawo ta


"Yau zan samu Abban ku da maganar, ni kaina hankali na ba akwance yake ba, kema kuma duk alamu sun nuna dakin mijinki kike so, ki tattara ki koma Allah ya baku zaman lafiya, me afkuwa ta riga ta afku shiyasa yayi biris damu shima Bashir din yasan ya gama damu, sai ki koma kawai ya zamuyi?"


"Nima dama maganar da nazo muyi kenan."


"Ai na sani, oh Zeenatu ana son miji. "


Da sauri ta rufe idon ta, ta tashi ta bar dakin a kunyace, ita kanta bata san menene ya hau kanta ba, yadda take ji idan bata koma ba, komai zai iya furuwa da ita. Ga wani masifaffen son cikin jikin ta da take ba zata so ya taso ba tare da mahaifin sa ba, ta taba karanta wani littafi da yarinyar ciki tayi gangancin kashe aurenta ashe akwai ciki, karshe haka ta haife dan a gida kuma ta cigaba da rainon sa a cikin bakar wahala, gashi duk wanda yazo auren ta sai yace ba zai rik'e mata da ba.

   Text message ta sake tura masa na ban hakuri, kamar yadda take masa kullum amma baya reply, ko ranar da yazo gaisuwa gidan taso suyi magana amma kemaimai ya ki bata dama karshe ma ya daga wayar Hajiyar sa yayi tafiyar sa ya barta a wajen.


*Adamawa-Yola*



Ayi maneji😢😢🙌


_ZAFAFA2022🔥_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO_*

_SO DA ZUCIYA_


*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI'AR ZUCIYA_


*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_


*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_


*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_


*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D'aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k


*_Zaku tura kudin a_*


6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*


*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇


08184017082


*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇


09134848107

2/24/22, 08:09 - Buhainat: ®*Hafsat Rano*

      _Halin Girma_

            *42*


***

*Adamawa-Yola*


Dukkan su sunyi shiru da abinda yake sak'awa a rai, idan har ta tabbata Muhammad yana da evidence akan su, toh gaba daya lissafin su ya sauya. Amma kuma akwai abin mamaki ace yasan komai tsawon wannan lokacin amma be taba fadawa kowa ba, hatta mahaifiyar sa da yafi kusanci da ita akkowaan kowa. 

   Sanarwar shigowar sa masarautar ya sake saka su cikin tashin hankali, rige rigen lekawa suke kowa yana so yaga da wacce yazo, ba karamin kaduwa sukayi ba ganin shi cikin shigar saurata yayi masifar kyau, ya dauki wani siririn glass fari ya dora akan fuskar sa, murmushi ne kwance a fuskar tasa yana tafiya irin ta kasaita. Fada ya wuce kansa tsaye, bayan ya tabbatar da an gama tattara duk wasu masu fad'a aji na masarautar tasu, shi kanshi Bubu a cike da Mamaki yake musamman da irin hakan bata taba faruwa, ba ruwan Muhammad din da harkar cikin gidan balle har ya nemi ganawa da manyan fadar.

    yadda ya shigo fadar kai tsaye ya saka wasu da yawa daga ciki yin mutuwar zaune, sakon shi ya iso musu tun kafin ya karaso. Wajen da ya saba zama ya samu ya zauna bayan ya kwashi gaisuwa. Su hudu suka shigo a tare hadda Kamal, suka samu waje suka zauna, daga nan bubu ya soma magana cikin nutsuwa da makasudin taruwar su a wajen. 


"Mun taru ne domin danmu Muhammad yana da bukatar ganawa da manyan masarautar saboda muhimmiyar maganar da ta kawo shi, wadda muke kyautata zaton zata kawo cigaba a masarautar tamu baki daya."


Mikewa tsaye yayi ya sake gaisuwa sannan ya soma magana idon sa fes akan wambai da jama'ar sa.


"Tsawon lokaci na dauka ina bin diddigin mutuwar marigayi tsohon sarki. Duk da karancin shekarun da nake dashi a wanchan lokacin amma ban manta ba, ban manta fuskokin mutanen da sukayi sanadiyar mutuwar sa ba."


Hayaniya ce ta cika fadar kowa na kokarin tofa albarkacin bakin sa cikin tsananin mamakin maganganun Mohammad din wanda shi kansa Bubun be san da wannan maganar ba. Murmushi ne a kwance a fuskar sa yana karanta tashin hankali dake kwance a fuskokin su, tuni suka fara jikewa da gumi cikin yanayi na wahalarwa


" Wacce irin magana ce wannan yarima?" 


Gyara tsaiwar sa yayi, ya sake kafe su da ido yace


"Ayi min afuwa, na dauko maganar daga sama, sai dai ba kai tsaye nazo da maganar ba sai dana tabbatar da ina da gamsashiyar shaida wanda zasu zama madafa a gareni."


Babu be tanka ba, ya dai zuba masa ido yana kallon sa yadda ya dake ya sake burgeshi, ya kuma ji a ransa lallai Muhammad ya shiryawa koma menene ,yadda ya dade yana nuna halin ko in kula da harkar gidan sai ya dauka be san komai ba, ashe yana sane har yana kokarin samun hujjar da zai tsayawa wan nasa da ya tabbatar da akwai wani bayanin a cikin labarin mutuwar tasa.


"Mecece hujjar taka Yarima? Ko zamu iya sanin ta?"


"Kwarai." Yace yana matsawa gaban Bubu, ya fito da envelope ya ajiye a gaban sa. Wannan ita ce hujjar da na rik'e nake kuma fatan abi duddugin abinda ya faru tun daga farko sannan ayi hukunci ga duk me hannu a ciki.


 Wani irin zillo wambai yayi, ya kalli Kamal ya kafe shi da ido yana masa alama da ya kasa ganewa, gaba daya ma shi baya cikin nutsuwar sa sakamakon maganar mahaifin sa da Mohammad ya taso da ita haka ta sama ta ka.

  

   Matsawa jikin wambai hakimi yayi, yayi masa magana cikin rada yace


"Nayi zaton mun riga mun samu shaidar da yake magana a kanta a wajen Kamal ko? Ko wata shaidar ce daban da bamu sani ba?"


"Yanzu ba lokacin maganar nan bace hakimi, kasan Kamal din be san flash din menene ba ya kawo mana, muyi fatan babu wata shaidar kuma."


Moh na ankare dasu, yana kuma lura da yanayin su, wato a tunanin su sun zata flash din da ya basu a matsayin Musaddik shi kadai ne shaidar sa, lallai suna wasa dashi.

  Budewa Bubu envelope din akayi, flash guda biyu ne a ciki sai hoto da aka dauka amma yayi dishi-dishi alamun ya kwana biyu. Kallon hoton Bubu yayi sosai amma be gane komai ba. Projector aka kawo, aka jona Moh ya harde a wajen zaman sa yana fatan duk wanda yake cikin video din ya yanke jiki ya fadi a wajen saboda tashin hankali.

   Jikin wambai ne ya soma kakkarwa lokacin da aka kunna video, shine yake magana da Kilishi,maganar sa radau a lokacin da yake ce mata in dai suna so su rufe sirrinsu sai dai su kawar da maimartaba, da fari batayi na'am da maganar tasa ba, amma yayi yadda zaiyi ya saka ta amince, daga nan sai hoton ya dauke sai kara shuuu da ta cika wajen, zare shi akayi aka saka dayan, wanda yafi tayar da hankalin mutane, tsohon sarki ne a kwance sanda suke kokarin kashe shi, babu irin magiyar da be musu ba, amma suka ki, suka kashe shi ta hanyar danna masa pillow har sai da ya daina numfashi gaba daya, akan dalili daya tal, dalilin ya gano zaluncin da suka dade suna masa shi da Kilishi, dalilin da su da kansu zasuyi wa fad'a bayani kafin yasa a tusa keyar su.


Salati ne ya cika a fadar, Bubu ya kawar da kansa yana jin dadi da Aji baya wajen, dalilin kenan da Muhammad din ya hanashi zuwa yace ya zauna a gida, dole idan yaga tashin hankalin nan ya rikice ga yanayi na girma.

  

Mikewa wambai yayi ya hau fad'a yana nuna Moh


"Karya yake yi wallahi karya yake, wannan shiryawa akayi amma karya ne, ni zaka wulakanta ko?"


Wasu fadawa ne majiya karfi suka taso, suka dankwafar dashi sannan suka ce


"Karya kake yi dan talakawa, Yarima yafi karfin ka jefe shi da wannan kalmar."


"Ku kyale shi." Yace kamar be damu ba, ya kalli Bubu da shima yake kallo ya yi masa murnushin kafin yace


"Za'a ji sauran bayanan da dalilin su na aikata wannan mummunan aikin daga wajen su."


"Me zuku ce game da wannan video da Yarima ya gabatar?" 


Bubu yayi maganar yana dubansu dukkasu, kamar wanda aka soma a ruwan zafi haka sukayi tsamo tsamo, babu me magana a cikin su dan basu da bakin da zasu karyata shi, hawaye sosai Kamal yake bayan ya gama amincewa dasu ashe mayaudara ne. Juyar da fuskar sa Bubu yayi, yan sandan da Moh ya kira suka shigo, suka tattara su gaba daya suka fita dasu, jikin kowa yayi masifar sanyi da abinda ya faru, sannan sun yabawa kwazon Moh, sun kuma yarda da chanchantar sa na zama shugabansu, a take wasu suka fara maganar, Bubu na jinsu ya dinga murmushi yana kallon tilon dan nasa, cikin so da kauna, a yanzu ya kara tabbatar masa da shine zabi na kwarai da zai wa al'ummar sa, ya kuma gane dalilin sa na kin amsa tayin sa tsawon lokaci, ya kuma gane dalilin sa na zuwa a sauya dukkan tsarin sarautar gidan tasu.

   Yana kallon yadda mutane suka dinga zuwa suna kwasar gaisuwa, fuskar sa a sake yake amsa musu, da haka ya samu ya zame ya fice daga fadar ya nufi bangaren Kilishi wanda yasan sakon sa ya riga ya iske ta, ko tana wanne hali yanzu? Zai je ya gani da idon sa kafin ya karasa wajen Ammin sa, yana son ganin Laila suyi maganar Samha bayan nan. 

   A duk abinda ya faru abu daya ne yayi masa ciwo, shine bayyananr asalin Kamal wanda ya kasance da ne ga wambai da Kilishi, ba dan tsohon sarkin bane, dalilin da ya saka su kashe shi kenan, saboda su binne gaskiya, su binne cin amanar da sukayi masa, duk don soyayyar su da mulki. Amma dole ba yadda ya iya, dole ne gaskiya tayi halin ta, ko da be fad'a a gaban kowa ba, yasan wadanda suke da hakkin su sani zasu sani din.

   Da kwarin guiwar sa ya isa shashen nata, ya shiga kai tsaye ba tare da wani ta tsaida shi ba, ya kuma sameta a zaune tana ta kuka wiwi, kamar wadda aka ce wani nata ya mutu, Kamal na tsaye a kanta ransa na suya, be taba tunanin abinda suka aikata ba kenan. 

   Wani abu ne ya daki Moha, a karo na farko yaji tausayin su dukka, yasan rudin duniya da shaidan ne ya dibi Kilishi ta aikata abinda ta aikata din, shiyasa a kullum take shakkar sa, ta kasa aikata masa komai saboda yasan wani bangare na sirrinta, a tunaniin ta maganin ta ne ya ci shi da ya nuna halin ko in kula da harkar gidan, bata san yayi hakan bane domin ya samu gamsassun hujjoji, wanda zai karya duk wani mara gaskiya da tsoron Allah, ya kuma karbi kujerar da ta jima tana dakon jiran shi. Ya kuma amsa sunan Sarki Muhammad Ahmad Santuraki! 



*****

Satin ta daya aka sallameta, suka tattaro suka dawo gida,kwana daya su Mamma ta kara itama ta tafi dama Mummy ta wuce tun a kwana uku da tayi a asibitin. Gidan ne duk taji yayi mata ba dadi, ta mike daga kwanciyar da tayi tunanin mutuwar Mahfuz na bijiro mata, tayi kuka sosai da ta samu labarin dalilin ta ne ya gamu da iftila'in, shiyasa aka ce ajali ko aina yake komai nisan wajen sai kaje ka tarar dashi. 

   Ranar da Yaya mahaifiyar sa tazo sai da kowa ya tausaya mata, dan yadda take magana kadai zaka gane yadda mutuwar ta dake ta, mutuwar danka saurayi matashi ya tasa, bata tafi ba har yanxu kuma kusan kullum sai tazo asibitin taga Iman din wadda take sake sakata jin nauyin ta har ma da shi kansa Muhammad din, kwata kwata sai ya rage zuwa asibitin dan baya son suna haduwa zuciyar sa karye wa take, daga baya ma sai ya shirya tafiya adamawa yana kuma chan har aka sallame ta be dawo ba sai waya da suke yi. 

  Sallama taji anayi daga falo, ta mike a hankali saboda rashin kwarin jikin da take fama dashi, ta bud'e kofar ta fito. Da dan saurin ta ta karasa ganin yan matan nan ne da suka taba zuwar mata. Su biyu ne yanzu suka gaishe ta ta amsa a sake tana zama kusa da daya da take kan three seater tace


"Ashe zaku zo?"


"Eh Fulani ce tace muzo mu tayaki zama kafin Ya Moha ya dawo."


"Kai amma naji dadi, sannun ku da zuwa ya mutanen gidan?"


"Lafiya lou, ya jikin? Allah ya kara sauki."


"Amin ya Allah, Nagode."


Sai suka shiga hira suna bata labarin gidan su da wasu yan uwansu da duk sai a dubiyar ta sassansu. Ummimi ce ta shigo ta gaida su ta gyara wajen dining sannan ta fita, ta dawo dauke da manyan warmers ta jera a wajen tsaf sannan ta sake fita.

   Su kadai suka ci abincin dan bata da appetite har lokacin, tea kawai ta sake sha tace zata dan kwanta, ta haye sama ta barsu suna kallo da danne dannen waya.

    Tayi nisa sosai a cikin baccin ta wayar ta dake jikin socket ta shiga kara, kamar ba zata tashi ba, saboda yadda baccin ya soma dadi, kiran ne ya kara shigowa bayan wanchan ya katse, ta tashi da k'yar ta dauko wayar ta daga


"Hajiya kinyi bakuwa."


"Wacece?" 


Mike mata wayar yayi 


"Nice Iman..."


"Zeenat, sannu da zuwa bashi wayar."


"Sister dina ce, ku kyale ta."


Ta katse kiran ta mike gaba daya ta shiga toilet ta gyara jikinta ta sauya pad sannan ta sakko. Da fara'a take kallon Zeenat din dake zaune tana karewa falon kallo cikin yanayi me ban tausayi, bata san Iman din ta fito ba har sai da ta dan dafa ta, ta kira sunan ta


"Sannu da zuwa."


Tace tana murmushi


"Yawwa, bacci kike kamar na tashe ki."


"Wallahi kinsan har yanzu ban gama samun sauki gaba daya ba, ya gida yasu Mama?"


"Lafiya lou wallahi."


" Ya jikin?"


" Da sauki Alhamdulillah."


" Allah ya kara sauki, ya bada na aike me albarka."


" Amin."


"Sai kika ganni kawai."


"Umm..." 


Tace tana mikewa tayi hanyar kitchen, taje ta fad'a musu abinda zasu kawo sannan ta dawo tace ta taso, suka shiga wani daki a k'asan, suna shiga ta cire mayafin jikin ta da dankwalin ta ajiye a gefe.

   Sallama Ummimi dake dauke da tray da abinci da ruwa tayi ta ajiye ta gaishe ta sannan ta ja musu kofar.


"Bismillah ga abinci."


"Toh..." Ta jawo kayan ta bud'e, yawun ta ya cinke ta zauna dirshan ta shiga dibar abincin nan babu kakkautawa, Iman na kallon ta bata ce mata komai ba, sai data ci ta koshi tasha juice da ruwa sannan ta mike kafarta sanyin AC na ratsa ta sosai.


"Magana ce ta kawo ni, dan Allah taimako na zakiyi Iman."


"Me ya faru?"


"Dan Allah yallaban zaki ma magana ya kira Bashir dan Allah ya zo ya maida ni, wallahi na gaji so nake na koma dakin mijina."


"Kina nufin dama kina gida?"


"Tun yaushe? Tun sunan Anty Bilki fa."


"Kai wallahi ban sani ba, matsala kuka samu?"


"Uhmm.."


"Ina jinki."


"Shi da Mama ne, bayan yazo mu tafi mama tace ba in da zani taje ta same shi a waje bansan me ta gaggayawa masa ba, shikenan ya kyale ni."


"Abba kuma ya sani?"


"Ya sani, har magana yayi min wallahi, amma Bashir din yaki zuwa kemaimai, har gidansu Mama tasa Ya Habib ya kaini amma sam yaki, a dah ban damu ba, amma wallahi yanzu nayi karatun ta natsu, ko dan dan tahalikin nan da yake cikina."


"Kema kinyi wauta, ita rayuwar nan baki daya da kika gani kowa hakuri yake da yadda tazo masa, shi kuma arziki lokaci ne."


" Haka ne, na ga aya ai, son zuciya bacin ta, daga kin gaskiya aka ce sai bata, kema sam ban kyauta miki ba abubuwan da nayi miki a baya, ko yanzu kinga sakayya, Allah ya baki miji me sonki na nuna sa'a, gashi ya hada duk wasu qualities."


" Ni ban rik'e ki ba ko da din ma."


" Um um Iman, ni dai kiyi hakuri dan Allah."


" Na hakura toh."


" Nagode Allah ya saka da alkhairi, dan Allah ki taimaka ki masa maganar nasan shi idan shi ya kirashi ba zai taba ki ba."


" Bari kiga." Tace tana tashi, taje ta dauko wayar ta dawo, ta zauna sannan ta kirashi


" Bari naji idan yana free sai muyi maganar kawai."


"Yawwa dan Allah."


"Assalamu alaikum."


"Wa alaikisalam Baby, na zata bacci kike ai, shiyasa ban kiraki ba ina jira ki tashi."


"Na tashi ai, ban jima ina baccin ba. "


" Kar dai yaran chan ne suka hanaki baccin da shegen surutun su. "


" A ah, Zeenat ce tazo. "


" Zeenat? " Yace cikin son tuno sunan, 


" Zeenat fa. "


" Oh wai matar Bashir? "


" Kai ko? "


" Allah na manta ta, lallai ta kyauta, duba ki tazo. "


" Eh. "


" Ok yayi, ya gidan ya missing dina? "


" Ina nan inayi, amma kad'an. "


" Kiji tsoron Allah, ni nasan kinyi missing dina kamar yadda nayi "


" Umm.. haka dai kace. "


" Haka ne ma, idan na dawo zan gasgata kai na ai."


" Can't wait." Ta saka dariya


" Toh me yake faruwa? Babu wata matsala dai ko?"


" Eh toh, dama Zeenat ce tazo, shine tayi min magana akan tana so dan Allah ka kira Bashir kace yazo ya dauke ta, Ashe tun ranar da mukaje suna gida bata koma ba, shi kuma be zo ba."


" Toh... Ina Zeenat din?"


" Gata."


" Bata wayar." 


" Gashi." Ta mika mata,


" Ina wuni?"


" Lafiya lou, ya gida?"


" Lafiya lou."


" Menene ya faru?"


" Dama..." Ta bashi labarin da ta bawa Iman bata rage komai ba, murnushin yayi yana daga zaune, a kalla yasan zuwa yanzu ta dawo hayyacin ta, ta kuma yi nadama tun daga yadda ta kwantar da kai tana masa magana, ya kuma tabbatar da uwar ta ma tayi laushi tubus, dama abinda yake so kenan, su russuna wa Iman dinsa har su nemi alfarma a wajen ta.


"Shikenan ki koma gidan zaizo anjima."


"Nagode Nagode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara girma..."


"Amin."


" Hello..."


" Baby zan kiraki anjima, ki kula da kanki kinji? Bye."


" Bye." Ta kashe wayar


" Yace naje gida zai zo." Ta fad'a cike da murna


" Masha ALLAH hakan yayi."


" Bari kiga na tafi, Mama bata san nan nayo ba asibiti nace mata zani, Nagode Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci."


" Amin."


Kofa ta rakota tare da bata kaya masu yawa a cikin leda tace ta gaida gida, ta kuma sa aka fitar da ita har in da zata samu abun hawa. 



*Ayi min afuwa jiya nayi kuskure wajen cewa Iman tayi sallah bayan tayi bari, ban ma lura da aika-aikar da nayi ba sai daga baya, ban yi editing page din ba sam ina ta sauri na tura. Ayi hakuri kuskure ne






_ZAFAFA2022🔥_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO_*

_SO DA ZUCIYA_


*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI'AR ZUCIYA_


*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_


*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_


*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_


*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D'aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k


*_Zaku tura kudin a_*


6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*


*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇


08184017082


*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇


09134848107

2/25/22, 18:10 - Buhainat: *Hafsat Rano*

      _Halin Girma_

            *43*


***kiran Bashir din yayi bayan sun gama wayar, be same shi ba, kila baya kusa. Ajiye wayar yayi ya maida hankali sa wajen Aji da suke magana kafin shigowar wayar tata.


"Me ma kake cewa?"


"Ungo nace." Yayi masa dakuwa


Dariya ya saka har da buga kafa


"Dan tsohon nan akwai riciki, toh ba zan waya da matata ba, naga kaima idan yar tsohuwar chan ta kiraka cikin rawar jiki kake zuwa."


"Gwara ni ai, kai daga gani mijin tace ne ai, sai uban rawar kafa sai kace kanka farau a aure."


Sake fashewa yayi da dariya cikin son kular da Ajin yace


" Naga alama dai kana taya yar tsohuwar chan kishi ne."


" Oho dai, matanmu na dah sun fi naku na yanzu komai da komai."


" Habawa, banda tawa matar dai, tawa daya tamkar da dubu ce."


" Toh Baban masoyan duk duniya, kaine ma ramiyo yake ko wa?"


" Romeo ake cewa, ai nama fishi."


" Kaji dashi, Allah yasa dai kar ayi lusarin sarki wanda mace zata dinga jujjuya shi, ya kasa aiwatar da komai."


" Ai tunda kuka dage sai kun bani mulkin nan haka zaku hakura, ana cikin zaman fada zaku ga nayi fit na fice toh Itace tayi kira."


Mikewa Aji yayi cikin kuluwa yace


" Ka bada maza wallahi, kaga tafiya ta ba zan iya kin wannan shirmen naka ba mara kan gado."


" A gaida min tsohuwar sarauniyar taka, zan shiga anjima naci tuwon wajen yar tsohuwa."


Murmushi kawai yayi, ya fice fadawan sa suka bi bayan sa, yana da kwarin sa har yanxu ba zaka taba cewa ya kai shekarun sa ba, Allah ya bashi lafiya me inganci sai dai fatan gamawa lafiya.


  Yana fita Bashir ya kira, sai da ta kusan katsewa sannan ya daga yana mikewa tsaye daga kishingid'ar da yayi dan yana so yaje yaga Ammi dan da wuri sai wuce gobe, sai kuma ya gama tsaf da chan sannan zai tattaro ya dawo nan din.


" Yallabai barka da warhaka, ayi min afuwa ashe ka kira."


" Barka dai Bashir, eh na kira ai ban dauka ma ta shigo ba."


" Wallahi network din ne, Allah ya baka yawan rai ya aiki?"


" Mun gode Allah."


" Masha ALLAH, Allah ya taimaka ya bada sa'a."


" Amin, alfarma nake nema wajen ka."


" Habawa, wane mutum, ka fadi ko menene kake so, an gama kawai."


" Bashir kenan, toh Nagode. Dama so nake idan Allah ya kaimu bayan Magriba kaje ka dauki matar ka ku tafi gida, shi aure daka gani ya wuce duk in da kake tunani ko hasashe, hakuri shine ribar zaman dan haka ka ajiye duk abinda ya faru a baya, ka fuskanci rayuwar ka."


"In Sha Allah an gama, dama so nake ita da mahaifiyar ta su fuskanci rayuwar yadda take."


"Zuwa yanzu sun gane ai na sani, kaje ka dauki iyalin ka."


"Zanje in sha Allah, nagode Allah ya kara girma."


"Amin nagode."


Sallama sukayi ya ajiye wayar, dama yana son yaje ya tafi da ita dan ya gane yadda ta damu ta dawo ko da text message din da take masa, shima kuma abinda yake so kenan, abu daya ya saka shi delay shine kayan dakin da ya saka akayi mata masu kyau daidai kudin sa, sai sabon gidan da Moh din ya bashi a lokacin bikin me kyau madaidaci two bedroom da falo da kitchen sai parking space, wanchan gidan da aka kaita hayar sa suka karba amma ba shine ainahn gidan da ya bashin ba.

  Kayan duk sun zama ready an saka komai an kwaso kayan kitchen dinta an zuba mata gidan yayi kyau daidai gidan amarya. Shi kansa yanzu yake jin sa a angon na gaske, bayan doguwar dambarwar da suka sha da hajjajun sa karshe dai sun rabu bayan ya dawo ya tarar da ita suna aika-aikar su da kawayen ta, da yayi magana ta taso masa kamar zata dake shi, karshe ma tace ya saketa ta gaji da auren sa, ta samu wani sabon saurayin me jini a jika, da farko yayi ta mata magiya akan tayi hakuri amma fafur taki, sai kawai ya danne zuciyar sa ya saketa, aikuwa yana sakin nata yaji wani sakayau kamar an zare masa wani mugun nauyi, sai ya hau tunanin ta yadda akayi ma ya aure mace irin ta bayan ya san abinda take aikatawa, abu daya ya sani shine kwadayin abun duniya ne ya kwashe shi har ya yarda ya amince ya aureta, bayan ta jika shi da kudi masu yawan gaske.

   Text message Moh ya turawa Iman yace ta fadawa Zeenat ta shirya zaizo bayan sallah, aikuwa tayi mata forwarding text din tana gani kuwa ta kirata ta dinga mata godiya. Dakin Mama ta wuce ta sameta a zaune ta rafka tagumi yadda abubuwan suka sauya mata a lokaci daya shine yake bata mamaki, ba tun ranar ta gano Abba so yake ya maida auren su da Maman Iman ba, sai yau ta gasgata hakan da yace mata ya tafi Abuja. Karamin hauka tayi masa amma yayi biris yayi tafiyar sa.

   Ko da Zeenat ta zo mata da labarin zuwan Bashir din sai taji dadi, a kalla zata huta da maganar yan gidan da ma makwafta akan zaman Zeenat din a gidan.


"Sai ki hau shiri ai, kafin yazo, kinje kin shantake a asibitin da tun dazu kika dawo ai da kin yi shirin da ya kamata."


"Anya ma asibitin kawai kika je?"


"Eh mama, chan naje likitan ne be zo da wuri ba."


"Toh sai ki shirya." Tace mata


"Toh." 


Daki ta koma ta dan harhada abinda zata hada, ta zauna tana lissafin awowin da suka rage, sai ga Mama ta shigo da Madara a kofi me dumi ta bata tace ta shanye, ta karba ba musu ta shanye tas ta bata kofin ta fita.

  Har akayi sallar magriba aka idar da wajen minti talatin be zo ba, ta gama matsuwa Mama na lura da ita, ita mamaki ma take yadda ta juye lokaci daya. 

  Ana idar da sallar isha'i ya aiko yaro wai Zeenat tazo inji Bashir, da sauri ta mike Mama ta harare, ta koma jiki a sanyaye ta zauna


"Je kace ya shigo wai."


"Hankalin ki ya dawo jikinki kinji? Wannan rawar kan ta mecece? Anya ma yaron nan haka ya barki kuwa?"


"Mamaaaa."


"Ba wasa nake ba, ki nutsu ki dawo nutsuwar ki wannan rawar kan babu abinda zata jawo miki sai raini wajen namiji, kayi biris da harkar namiji ma amma be fasa gasa ka ba, ina ga kana rawar kafa akansa? Daga cewa gashi sai ki mike kina barin jiki ke me miji ko? Toh ki shiga taitayin ki."


"Mama ai ba laifi bane, tunda shi din miji na ne."


"Inyeee Zeenatu?" 


Ta fad'a cike da mamakin Zeenat din, sallama yayi a kofar, kafin ya shigo sanye cikin shadda sabuwa kar, sai kyalli take da kamshi, cikin ido suka kalli juna da Mama, ta kauda kanta haushin shi na tike ta, sai ta ga ma kamar da gayya yake wani irin murmushi.


" Mama ana gaishe ki." Zeenat tace jin Maman bata amsa gaiswar Bashir din ba


" Lafiya lou, ya gida." Harara ta watsa wa Zeenat din ta dauke kai kamar bata gani ba, sai ta tashi tsam ta tayi hanyar barin wajen tace


" Ku gaida gida."


" Mun gode Mama


Yace yana hayewa kujerar, tashi Zeenat tayi tabi bayanta dan yi mata sallama, ya bita da kallo yana kara bararrajewa a saman kujerar.

   Suna shiga Mama ta turnuke ta da fad'a, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, tayi mata tatas saboda bakin ciki, karshe tace ta bata waje. Sallama tayi mata bata amsa ba, sai ta tsaya taki tafiya tana kallon Maman


" Uban me kika tsaya kina yi anan? Ko jiranki zai yi? "


" Naga kina fushi ne, kiyi hakuri dan Allah ko na hakura da tafiyar kawai tunda naga kamar bakya so. "


" Inji uban wa nace bana so? Yadda ma kike rawar kafar nan ko bana so zaki hakura ne? "


" Eh. " Ta daga mata kai


" Ke ni karki rainan hankali, wuce kibi mijinki Allah ya bada zaman lafiya. "


" Amin. " Ta amsa hakan ya sake tike Maman. Ta juyar da kanta sai da Zeenat din ta fita sannan ta zauna cikin rashin sanin abinda kuma ya kamata tayi. Gashi dai a karshe abinda tayi ta yi akan Zeenat din duk ya tashi a banza, gashi ta rasa damar ta a wajen Abba wanda ba zata taba dawowa ba, karshe kuma yar ta zabi mijinta akan zaman gidan nasu.

   

***Da dan gudun Amaani da Amaan suka tare shi, kamar sun sanshi tun da dadewa, kamar sun saba dashi. Yana da son yara ko dan saboda be haifa da yawa bane, Amaani sak Fatiman sa sai dai ita bata da hayaniya da kwarafniya irin ta Amaani din, kamar yadda mahaifiyar su take haka take itama a nutse tun tana karama har kuma girman ta.

  Su suka jagorance shi zuwa ciki, ya zauna yana tuna shekarun baya da ya kasance a same wajen, a lokacin da yazo su kayi magana da Alhaji, kamar a lokacin komai yake faruwa. 

   Turo kofar da akayi ne ya sakashi waigawa, itace dai a shekarun baya sai dai girma da ya soma kamata, duk da haka ba zaka taba bata shekarun ta ba, balle har ka kawo ta ajiye budurwa kamar Iman din, kullum cikin gyara take tsaf. Ko a baya yasan yayi missing mace kamar ta, sai dai a yanzu sam be zo da wasa ba, da gaske yake wannan karon sai dai duk abinda zai faru ya faru. Babu gudu ba ja da baya!


"Sannu da zuwa." Tace tana zama a chan nesa da kujerar da yake kai. Sannan ta gaishe shi ya amsa yana satar kallon ta, shiru suka dan yi kafin ya sake bijiro mata da maganar da ta sakashi tasowa gari i gari zuwa Abujan, a tsammanin sa sai sun kai ruwa rana zata amince, amma sai ta bashi mamaki matuka, yadda kai tsaye tace Allah ya zaba musu mafi alkhairi. Da farin ciki ya baro garin na Abuja, ya dawo ya tarar da Mama bata da lafiya, ya tausaya mata tunda shi mutum ne me tausayi, har ma ya saka Habib suka kaita asibiti in da aka ce dole ta rage tunani saboda jinin ta da ya hau sosai, aka rubuto mata magunguna suka tattaro suka dawo gida.


***Bayan sun gama waya da daddare zasuyi sallama yace ta shirye shi gobe yana nan dawowa, reaction dinta kadai ya gamsar dashi yadda tayi kewar shi. Yana jin yadda take farin ciki ta cikin wayar sai dai kara irin tata ta hana ta nuna masa, a hakan ma ya gode dan yasan ya chanja ta sosai daga auren su zuwa yanzu. Sauran chanjin kuma sai a hankali zata saba da kalolin soyayyar sa masu tsayawa a zuciya.

   Neman baccin da take yi tayi ta rasa, ta tashi ta sauka daga gadon ta bud'e wardrobe dinta, ta hau duba kayan da take ganin ya dace ta saka, sai data dau lokaci tana zaba kafin ta tsaya akan wani hadadden lace wanda dinkin sa ya fita sosai. Murmushi tayi ta fito dashi ta ajiye a gefe ta hada da set of jewelries da zasu dace da lace din sannan ta kwanta tana lissafa kalolin girke-girken da ya kamata ta tarbi mijin nata dashi, da haka bacci ya dauke ta bayan ta gama hada komai a cikin kanta saura kawai girkawa gobe idan Allah ya kaimu.

   Kasancewar tana cikin zumudin dawowar sa yasa ta tashi da wurwuri, ta duba kitchen na abubuwan da zata bukata wajen girkin wanda babu ta bawa Ummimi sautu suka je da driver suka sissiyo, sannan suka shiga aikin tare da sauran ma'aikatan dake kula da kitchen din amma kuma Itace akan girkin sai dai su taimaka mata da dauko wa da mikowa.

2/26/22, 19:09 - Buhainat: *Hafsat Rano*

      _Halin Girma_

            *44*


***Da wurwuri yaso tahowa amma sai case din Kamal da Kilishi ya tsaida shi, sosai Kamal ya tada hankali a gidan tun bayan da ya tantance ainihin shi din waye, ya kuma gano wambai ne Mahaifin sa. Baki daya Kilishi ta nemi kwanciyar hankalin ta ta rasa, gashi har lokacin bubu be ce ga hukuncin ta ba, sannan ita kanta Laila ta birkice mata, babu Moh kamar yadda ta kwallafa rai, ga bakin cikin cin amanar da Samha tayi mata ga kuma abinda mahaifiyar ta wa mahaifin ta.

   Takanas taje ta samu Bubu ta roke shi akan ya barta ta koma karatun ta dan zaman ta anan din komai zai iya faruwa,da farko be amince ba sam, yace mata be yarda ba tayi hakuri ta kawo miji aure zai mata. Sanin bata da wani tsayayye da zata nuna yau yasa ta samu Moh ta roke shi cikin kwantar da kai tace ya rokar mata Bubun ya barta. Ko da ya samu Bubun da magana shima fafur yaki, sai da yayi ta masa magiya sannan yayi masa alkwarin duk wani abu da ya faru shine zai dauki responsibility din, a haka yayi convincing Bubun ya amince yace ta koma din,amma da sharadin idan yaji wani abu mara dadi ko mara kyau toh fa shi zai kama da laifi kuma dole ya karbi aurenta. 

    Godiya tayi ta zuba masa kamar ta rungume shi haka take ji, har gobe tana son sa, ba kuma ztaa daina son nashi ba, zatai ta hakura for now tayi concentrating akan karatun ta, ta samo ta kammala shi kafin tasan kuma me ya kamata tayi kuma anan gaba. Akalla idan tayi nisa da gida zata manta abinda Kilishin tayi da dan lokaci ta kuma samu damar mantawa da Moh din shima na wani lokaci hankalin ta ya kwanta ta nutsu waje daya.

   

***A daki ya tarar da Ammin tasa, wanka tayi ta gama shiryawa kenan zata fito ta yi breakfast ya shigo, ta bishi da kallo har ya zauna a k'asa wajen tumtum din da take hutawa idan tana dakin, ya tankwashe kafafuwan sa sannan ya gaishe ta cike da ladafi. Kusa dashi ta zo ta zauna tana amsawa, tasan sallama yazo yayi mata tun jiya dama ya sanar da ita komawar tasa yau ba kuma zai dawo ba sai ya gama da chan din, sannan yazo a shiga bikin nad'in nasa, wanda tun yanzu Bubun ya soma aikewa da goron gayyata dan taro yake shiryawa na ban mamaki.

   

"Tafiyar ce Babana?"


"Eh wallahi, na zata ma fa baki tashi ba."


"Wa? Ka manta da wuri nake tashi, kwana biyu ne da kafa ta matsa min bana samun bacci sosai da daddare sai na rama da safe."


Kafar tata ya matsa mata


" Har yanzu tana ciwon?"


" Ta warke yanzu ai."


" Allah ya kara sauki."


" Amin."


" Idan naje sai mun tashi dawowa gaba daya, ina fatan abun da nayi ya dace."


" Kayi abinda ya dace, kuma ka farantawa mahaifi ka da zaka cika masa burin sa, Allah yayi maka albarka ya baku zuria dayyiba, inaso na goya yan jikokina a bayan nan nawa."


" Dukka ma zamu baki Ammi ta, halak malak. "


" Um um dai Babana, kar kayi alkawarin da ba zaka cika ba. "


" Da gaske nake Ammi. "


"Toh shikenan Allah ya kawo mana masu Albarka. "


" Amin ya Allah. " Ya amsa yana mikewa


" Ammi zan wuce, ayi mana addu'a. "


" Allah ya taimaka ya bada sa'a, a gaida min da yata kafin tazo, zan kira na sake dubata idan ka sauka. "


" In sha Allah Ammi ta. "


Bin sa tayi da kallo har ya bace wa ganin ta, ta sauke ajiyar zuciya tana jin soyayyar tilon dan nata, tana alfahari dashi, daya ne tamkar da dubu yana mata biyayya daida gwargwado.


  Be samu ganin Bubu ba, dama sun riga sunyi sallama tun jiya, dan haka kai tsaye mota ya shiga, karo na farko zaiyi tafiya cikin rakiyar tarin fadawa ba sojoji ba, wani daban yaji, gargajiya sosai da al'adah irin ta gidan sarauta. Shi kansa shigar da yayi kenan, shiga irin ta Yarima me jiran gado, a dan kwana biyun da yayi har ya saba da saka kayan , yana kuma jin dadin su dan suna sake fito da kamalar sa.

   Tun daga airport ya fara cin karo da abinda ya tsana da sarauta, yadda ake kokarin kaiwa kasa wajen gaishe shi, har ga Allah baya so kuma dole zai san yadda zai ya hana irin wannan gaisuwar. Basu jima da zuwa ba jirgin su ya tashi zuwa birnin na Kano, in da ya tanadi kalolin soyayyar da zai bajewa sahibar tashi, kafin ya dawo ya karbi sha'anin mulkin da baya jin zai rage masa wani abu daga cikin irin rayuwar da ya tsara musu, sai dai yasan dole sai ya dinga raba lokacin da mutane, amma haka zai yakice ya dinga yin abinda ya dace.

   

***Tun da taga komai ya gama haduwa sai abinda ba za'a rasa ba, sai ta bar musu sauran aikin su karasa ita kuma ta haye sama don yin wanka ta shirya tarban mijinta. So take ta burge shi sosai, duk da ita din ba gwanar kwalliya bace amma zata kokarta, sannan zata cire kunya ta rungume mijinta taji dumin jikin sa sosai.

   Wanka tayi ta sake wanke bakin ta tas, sannan tayi amfani da mouth freshner me kamshi ta kuskure bakin sannan ta fito tayi zaman shiryawa a gaban mirror. Ta dan dau lokaci tana shiryawar duk da ba wani make up tayi ba, amma tayi kyau ainun. Kayanta da ta turara akan kabbasa ta dauko ta saka, sannan ta sake bin jikinta da turarurruka masu sanyi da dadin kamshi. Samun kanta tayi da yin murmushin yadda ta fito tayi fes, sai taga har wani fari kamar ta kara tayi fresh da ita.

    Zama ta cigaba da yi a saman nata tana dakon zuwan sa. Waya ta dauko da nufin kiran Mummy sai taji karar zuge gate din gidan, ta fasa ta tashi da sauri tayi wajen window ta daga tana kallon motocin da ke shigowa suna samun matsuguni a cikin gidan. Motar da yake ciki ta zubawa ido, a hankali ya zuro kafarsa cikin takalmin sa da akayi da zallar fatar damisa, daga yanayin takalmin nasa ta gane irin shigar dake jikin sa, tun kafin ma ya gama fitowa ta gama wassafa yadda kayan suka karbe shi. 

   Kamar wanda aka ce ya daga kai zuwa saman, sukayi ido biyu tana leken sa, da sauri ta saki labulen sanda ya kashe mata ido daya gami da murmushin sa me tarin bayanai a cikin sa.

    Gaban mirror ta koma ta sake fesa turare sannan ta shafa khumra me kamshi a tafin hannun ta, ta dauki flat shoe me kyau ta saka ta sauko k'asa. Tana saukowa yana shigowa falon. Tsayawa yayi a kofar ya toge ya bud'e mata hannayen sa, cikin sanyin ta, ta tafi zuwa gareshi, ta fad'a jikinsa ya rungume ta yana jujjuyasu a wajen, kamshin turaren ta na ratsa kofofin hancin sa.


"Ya Allah, ashe haka nayi kewar ki?"


"Um... Barka da zuwa yallabai."


Tace tana dago kanta daga jikin sa 


" Barka dai gimbiyar Muhammad."


" Muje ciki?"


" Bismillah... Ladies first " 


ya matsa yana nuna mata hanya, yana so ya more kallon tafiyar ta. Bata kawo komai ba tayi gaba ya bita yana murmushi, a tsakiyar falon suka yada zango.


"Wash." Yace yana taro ta jikin sa, ta zame tana masa dariya


"Wanka ko lunch?"


"You." Ya kashe mata ido, dariya kawai tayi, ta je ta kawo masa lemon kwakwa da tayi masa yayi sanyi sosai ta zuba masa a glass cup ta dan russuna ta mika masa, ya hada da hannun ta ya rik'e tayi yar kara


"Auw, sorry baby."


Ya saki hannun ta zame shi tana marairaice fuska kamar zatayi masa kuka.


"Sai na rama." 


Ta koma ta kawo kayan abincin ta jera masa a wajen, ya mik'a mata hannu ta daga shi, ta noke tana durkusawa da nufin zuba masa, rigar ta da akayi wa dinkin V-shape daga wuyan ya kalla yana cije lips dinsa.


"Bismillah." 


Tace tana dagowa, ga mamakin ta sai gani tayi ya zuba wa kirjin ta ido, kunya ce ta kamata ta daga da sauri, ya waske yana zamowa


"Kayan nan yayi miki kyau"


Kin kallon sa tayi, ya dauki spoon din ya fara cin abincin yana kunshe dariyar sa.


"Ya jikin naki?"


"Alhamdulillah, da sauki. Yasu su Ammi?"


"Lafiya lou, suna gaida ki, tace zata kira ma ta sake duba ki kafin muje."


" Ayya, na samu sauki ma ai."


" Naga alama ai, har wata kiba kika kara da kyau, musamman ta nan..."


Ya nuna chest dinta da idon sa, kau da kai tayi tana hararar sa


" Kai ko?"


" Me nayi? Daga fadar gaskia? Allah baki gani ba."


" Uhummm."


" Da gaske fa nake, komai masha Allah."


Murmushi kawai tayi, dan ta lura jan magana yake so yayi, aikuwa ya cigaba da yi zuzutawa kyaun da tayi. Ita ma kanta tasan tayi kara wani irin kyau na ban mamaki. Sai da ya gama tas ya shanye lemon kwakwar nan sannan ya kama hannun ta suka haye saman, su Ummimi suka zo suka tattare wajen suka gyara aka saka turaren wuta.





Manage muna biki ne

  

2/27/22, 23:33 - Buhainat: *Hafsat Rano*

      _Halin Girma_

            *45*


***Washegari suka tashi cikin farin ciki da annushuwa. Yana shiryawa a gaban mirror ya kalle ta ta cikin mirror din tana ajiye masa kayan da zai saka yace


"Maganar school dinki, transfer zamu nema zuwa adamawa."


Tsayawa tayi da abinda take ta kalle shi


"Komawa zamuyi chan?"


"Yes, zamu koma gida, zan ajiye aiki na, na karbi Bubu."


Wani gingirim taji maganar, ta tsaya a wajen sakato tana son ta fuskanci zancen. Gabanta yazo ya tsaya yana murmushi


"Kina mamaki?"


"A'ah, ban gane bane I'm confused."


Dariya ya saka


"Don't be, ki shirya you are soon to be the wife of his royal highness!"


Wani shock tayi cike da mamakin


"Zaka karbi mulki?"


"In sha Allah, shine burin Bubu, zan cika masa burin sa kamar yadda yake so."


Da baya ta koma ta zauna a gadon kanta na mata wani iri. Matar sarki fa? Ta Yaya zata iya? Taya zata fara? Bayan bata san komai cikin sha'anin irin wannan ba, dafa ta yayi ya mik'ar da ita tsaya yana mata dariya


"Look at you, bafa yaki bane, normal ne kawai."


"Bansan komai ba ai, ta yaya zan fara? I'm nervous." 


" Karki damu kinji? Muna tare ai."


" Allah ya taimaka ya bamu sa'a, Allah ya bamu ikon yin adalci da aikata daidai."


" That's my queen, abinda zaki ce kenan kawai, nasan zaki iya, I trust you."


" Banda fasa kai."


" Da gaske nake, nasan zaki iya handling kowanne irin situation."


Murmushi tayi, sai kuma wani tunani ya fado mata, 


" Shikenan sai ka kara aure?" Ta samu kanta da tambayar shi cikin sanyin murya


" Aure kuma?"


" Eh ba sarakuna basa auren mata daya ba, wasu ma har da kwarkwara suke yi."


" Eh toh..." Ya mike yana saka links a jikin rigar, 


" Me?"


" Ban dai san nawa zan ba ni ma, amma nasan zan kara uku na cike kinga hudu kenan."


Gabanta ne yayi mummunar faduwa, ta dinga kokarin karanta gaskiyar sa ta hanyar kallon fuskar sa. He looks serious, sai taji wani kuka na taso mata, tayi kokarin dannewa tana kokarin barin dakin gaba daya, riko ta yayi da sauri ya dawo da ita yana dariya


"Kishi?"


"Zanje k'asa na dauko abu ne." Tace tana avoiding kallon fuskar sa dan ji take kamar ta fashe da kuka


"I love this new side of you Baby, yayi miki kyau."


Haushi ne ya sake turnuke ta, wato shi wasa ma ya mayar da abun, fusge jikinta tayi, tayi gaba da sauri ta bar masa dakin, tana fita hawayen da take da rikewa suka zubo, shikenan ace a karaamin shekarun ta zata fara zama da kishiyoyi ba ma kishiya ba, har ga Allah bata da hayaniya da fitinar da zata iya zama dasu, ga hayaniyar gidan sarauta da shegen makirci wanda take tsoro tun farkon fari da ta gano waye ta aura. Tsaye take jikin staircase bata sauka ba, ya fito ya tadda ta a wajen, sai ta waske tana kokarin sauka ya chapko ta.


"Babu in da zaki sai mun karasa maganar mu."


"Ni fa babu komai, abu zan dauko a k'asa."


"Ba in da zaki." Ya juya da ita zuwa ciki, ya zauna ya dora ta a saman cinyarsa.


"Ashe dai ana kishi na haka."


"Nifa ba kishi nake ba, tambaya kawai nayi kuma ka bani ansa ai."


"Bari kiji, kinga bamu ne muke da ikon tsarama kanmu rayuwa ba, idan ma ka tsara tsarin Allah daban ne. Bani da sha'awar kara aure amma bansan me gobe zata haifar ba, karki damu let's pray for the best kinji? Muhammad dinki yana sonki sosai, wannan kawai ya isheki ki mikar da kafarki kamar kin hau jirgin sama mai ya kare."


Duka ta kai masa suka yi dariya a tare, a kalla dai ya fad'a mata iyakar gaskiyarsa, kuma hakan da yayi ba karamin burge ta yayi ba, taji ta kara son shi fiye da baya. Tare suka karasa shiryawa ya taimaka ya saka mata Alkyabba akan kayan ta, ya gyara mata sosai tayi kyau, ya ciro waya ya yi musu hoto me kyau, sannan suka fito, suka tarar da su Ummimi da sauran yan matan uku sun shirya tsaf suna jiran su, waje kuma fadawa ne suma a shirye an gyara motar. Hannun su sarke da juna suka sakko, duk suka zube suna kwasar gaisuwa, kafin su karasa an bud'e musu motar sai da ya bari ta fara shiga ta zauna sannan shima ya shiga. Sauran motocin su Ummimi suka shiga sai fada.

   Sanda suka isa Takawa be riga ya fito zaman fada ba, sai suka wuce kai tsaye wajen sa, suka sameshi a wajen karatun sa tare da Fulani,a kunyace Iman ta gaishe su amma sai taga kamar basu damu ba, sun sake sosai kamar ba sarki ba, suka dan tsokani juna da muhammad kafin su barsu ita da Fulani zuwa bangaren ta, ba chan waje suka koma ba, wani corridor suka bi har chan din, tasha kallon haduwar wajen a hanyar su ta zuwa har suka dangana da chan sashen.

    Har yamma likis suna gidan, bata sake ganin muhammad ba sai da yazo zasu tafi, ya shigo kamar bashi ba, hatta da takun sa sai data ga ya chanja ya zama irin na saraki masu ji da jini a jika, za'a ga hadadden young Sarki, ga kyau ga aji. 

   Sai da ya zauna fadawan suka fita sannan ya dube ta ya kashe mata ido ba tare da Fulani ta gani ba, murmushi tayi kawai ta saukar da kanta dan Fulani ta fad'a mata yadda tsarin sarautar yake, dole tayi takatsantsan da abubuwa masu yawan gaske, ta kuma ce nan zata dinga zuwa kullum tana ganin yadda abubuwan suke kafin tafiyar su.

   Haka kuwa akayi, kullum sai sun fito da safe sai dare suke komawa kuma bata sake ganin shi wani lokacin ma sai dai su hadu a mota idan zasu tafi.

    

***Maganar Abba da Maman Iman ta 






Rayuwa ta cigaba da garaw


Post a Comment for "HALIN GIRMA 41-45"