Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

HALIN GIRMA 36-40

2/17/22, 09:45 - Buhainat: Halin Girma

36

*******�

Cikin wani yanayi taji kamar bacci yana fuzgarta, ta sake gyarawa sosai Ummimi ta matsa mata sosai ta

kwanta a bayan, nan take kuwa bacci ya dauke ta. A tunanin Ummimi tsabar gajiya da wahala ce ta saka ta baccin, dan tun safe suka fito kuma tana lura bata saka komai a cikin ta ba sai ruwa, ita dai ta bata kudi taje cafeteria ta siya abinci taci, amma ita kuwa bata ci komai ba, dole ne ko ba karatu kake ba, ka jigata balle. Tausayin ta taji, musamman da ta gama fuskantar halin kirkin da, bama ita kadai ba duk

ma'aikatan gidan na murna da samun ta a matsayin uwargijiyar su, babu hantara balle tsangwama, gaba dayan su son ta suke da gaske.

   Tafiya suke tayi babu alamun zasu tsaya, har duhu ya fara mamaye sararin samaniya, kallon ta Ummimi tayi taga har lokacin bacci take da gaske, shiru kake ji a motar babu wanda yake magana a cikin su, a tunanin da za'a samu ko yar karamar hira ce tsakanin driver da na gaban amma babu wani wanda yayi magana a ciki, jakar dake kusa da Iman din ce ta fadi kasa, Ummimi ta sunkuya da nufin dauka, abinda ta hango a hannun shi ya saka hantar cikin ta kadawa, a firgice ta dago tana dunkule jakar a hannun ta, juyowa yayi ya dube ta, ya sake dago mata hannun nasa da kyau dan ta gani sosai, bindigar ce kuwa, tsoro ne ya kamata,

"Idan kika sake kika bud'e bakin ki a wajen nan, sai na fasa kanki da alburushi."

Da sauri ta rufe bakin ta da hannun ta, juyawa yayi kan driver yace

" Idan ka kai karshen titin zaka gangara haggu."

Da ka ya amsa, daga gani a tsoroce yake, rashin sani ya hanasu ganewa tun shigowar su motar. Kallon Iman take ganin da gaske bacci take, bacci me nauyi da ya hanata jin duk abinda ya faru, mamaki ne ya kama Ummimi, dama ta saba irin bacci haka ko kuma dai akwai matsala, da sauri ta dan taba ta, sai taga ta motsa kad'an tamma kuma bata tashi ba, ajiyar zuciya ta sauke, hawayen da take ta makale shi ya gangaro zuwa fuskarta, me yasa mutane suka lalace haka? Labarin da suke ji a gidan radio yau shine ya faru dasu? Idan har masu sarauta da masu hannu da shuni basu da tsaro toh waye kai kuwa talaka? Anya rayuwar zata tafi a haka?

   Cikin tsananin fargaba take har suka karaso wani gida, karami a cikin gungurmin jeji, babu gida gaba babu baya, ba zaka taba tunanin halitta irin ta mutum zata rayu a wajen ba, tana jin yadda suka dinga shiga kan tudu da kwari alamun sam hanyar bata mota bace, ko tace mota bata taba bi ba. Murfin motar ya bud'e yana nunawa driver bindiga, suka fito a tare ya zagayo wajen sa ya rik'e kugunsa. Fito yayi da bakin sa, sai ga wasu kartin maza su biyu sun fito, tare da wata mace a bayan su, tafawa sukayi da daya daga ciki sannan yace

"Kayi babban aiki, aikin da zai firgita ilahirin k'asar har ma da ketare, tana ina?"

Bayan motar ya nuna masa, ya tafi zuwa wajen ya bud'e yana leka ciki

"Baccin ne be sake ta ba har yanzu?"

"Eh!"

"Tasha ruwan kenan!" Yayi murmushi yana rufe kofar

"Tasha sanda ta shigo motar."

"Kayi kokari sosai... Kudos!"

"Thank you sir."

"This is a shame to the Nigerian Armies, The royalties, government, gaba daya ma, duk sunyi failing, ta yaya kake tunanin mutane zasu sake yarda dasu? Bayan sun damka hakkin kulawa rayuwar su garesu, sai ya zama sun k'asa tsare kan su?"

Sai ya kwashe da dariya

" Yaron nan a bayan mu yazo, yaron nan ta dalilin sa na rasa komai, ciki harda aikin da na kwallafa rai, saboda shine shafaffai da mai? Saboda shi din dan gata ne, shiyasa aka fifita shi akan kowannen mu, me yafi mu? Mulki?"

"Oga!"

" Haka ne mana!" Ya fad'a da karfi

"Haka ne. Kullum cikin favoring dinsa ake, kullum cikin yabon sa ake, na kai mataki Babba amma yaron nan, ta dalilin sa komai ya baci, ya kake tunanin zan iya hakura?"

"Kunsan shekarun da na dauka ina gina rayuwata har na kawo wannan lokacin?"

"A ah." Suka girgiza kai dukka

" Shekara goma sha daya, amma cikin sakan da be wuce goma ba, ya kwace komai, khaki na, rank dina, mutunci na a idon duniya, na muzanta, na zama abin gudu da k'yama."

Duk sun yi shiru kowa na sauraren sa, shirun shima yayi dan bashi da abin fad'a kuma

" Ku shigar dasu ciki, idan princess ta tashi a fad'a min."

Sai ya juya ciki ransa fari tas, ya tabbatar saura kiris bomb ya tashi, bomb din da zai tarwatsa duk wani farin cikin Muhammad Ahmad Santuraki da duk wani makusancin sa, shekara biyar kenan yana bibiyar sa, ya kuma samu nasarar samun duk abinda ya samu a yanzu, wanda yake tabbatar da su kadai sun isa su tarwatsa duk wani farin cikin sa. Matsala daya da ya samu, bashi kadai ne yake son ganin bayan sa ba, nasa kawai yafi zafi ne, sai ya hada guiwa dasu, yayi amfani dasu wajen samun abinda ya samu akan sa, ya kuma tabbatar da babu wata alaka da zata sake hada su a nan gaba, ya datse duk wata hanya da zasu neme shi.

   Ta jima tana bacci sosai, Ummimi dake durkushe a gabanta tana kuka sosai taga ta motsa, ta cigaba da motsawa tana yamutsa fuska kafin ta bud'e idon ta da kad'an kad'an da sukayi mata matukar nauyi, saman dakin ta fara kalla, sai kuma ta shiga jujjuya idanunta tana son gano a in da take, da sauri ta yunkura zata mike, Ummimi ta taimaka mata tana rik'e ta

"Karki tashi da sauri jiri zai iya daukar ki, ina tunanin sun zuba miki magani ne.". Ta fad'a cikin muryar kuka

"Ina ne nan? Me muke anan Ummi?"

"Ni ma ban sani ba, wanda kukayi magana dashi, shi ya kawo mu nan, sun sato mu!"

"Musaddik?"

"Eh."

"Innalillah wa inna ilaihi rajiun." Ta furta a hankali, kanta da yake jujjuyawa ta saka hannu ta dafe, amai ne taji yana taso mata, ta yunkura da nufin tashi amma kafin ta kai kofar har ta soma aman, wanda babu komai a cikin sa sai zallar ruwa, tun tana yi har ta koma kakari kasancewar babu abinda yake cikin ta tun safe, rik'e ta Ummimi tayi tana kuka, tana jera mata sannu, sai da taga ya lafa sannan ta taimaka mata ta maida ita gefen tabarmar da ta tashi,

"Bari na samo miki ruwa, sannu."

Ta tashi ta fito, su biyu ne a zaune suna karta, suna ganin ta suka tashi

" Ruwa take so dan Allah. "

Da Ido sukayi wa juna signal, kafin daya daga ciki ya shiga wani daki, ya dawo da ruwa ya mik'a mata, ta karba ta juya ciki, ta tarar da ita tana ta juyejuye akan tabarmar, ta rik'e cikin ta da yake murda mata kamar zata amayar da kayan cikin ta. Dagota tayi, ta bata ruwan ta kuskure bakin ta, sannan ta sha, ta koma ta kwanta tana sake rik'e cikin ta.

   ***Kwanan Zeenat biy babu Bashir babu alamar sa, Abba kuma ya zuba musu Ido be sake cewa komai ba, ko Mama be sake mata maganar ba, shirun nasa yayi masifar bata tsoro, dan bata san me yake shiryawa ba, ranar suna zaune Zeenat din na cin wainar fulawa, ba wani dadin ta take ji ba amma itace kadai take mata dadin ci, sai nama da tuwo idan ta same su kamar wata tsohuwar mayya, jigum jigum suke kowa da abinda yake damun sa. Kofar falon ce ta bud'e duk suka kalli kofar a tare, Abba ne ya shigo, ya wuce dakin sa, k'asa k'asa Zeenat din tayi masa sannu da zuwa be ma ji ba, ya shige jimawa kadan ya fito, ya dubi Mama da tayi tsam tana kallon sa yace

"Tunda har ban isa na saka ko na hana Zeenatu abu a gidan nan ba, kin nuna min ban isa ba tun fil'azal, na bar miki ita, idan har tana so mu shirya da ita lallai ta koma dakin ta, ke kuma, hakuri na ya gaza, kije gida kya dawo duk sanda kika shirya gyara auren yarki, idan har Zeenatu bata koma dakin mijinta ba, toh zaman mu ba zai cigaba ba. "

Daga haka ya saka kai ya fice, ba don darajar yaran dake tsakanin su ba, ba kuma don darajar zaman da tayi dashi na dadi a baya ba, da zai sauwake mata ne kawai, amma hakan ba zai yiwu ba, har yanzu yana sonta yana kuma son ta gyara halayenta.

   Tashin hankali ba'a saka maka rana, da girman ta da komai gotai gotai zai ce taje gida, zagaye ta dinga yi a falon kaamar tayi hauka, duk tsawon shekarun da sukayi da Ibrahim be taba nuna mata ko yatsa ba, sai gashi a yanzu da girma ya soma hawa kansu, tayi abinda gaba daya mutuncin ta ya zube a idon sa, har yana cewa zaman su ba zai yiwu ba.

" Mama dan Allah kiyi hakuri, zan koma wallahi ba zanzo ku samu matsala da Abba akai na ba, zan jure koma menene dama ni na jawo ma kaina. "

" Ba laifin ki bane, babu abinda zai faru , sake gwada kiran Bashir din idan be daga ba sai kawai na saka Habib ya kaiki chan gidan su, daga nan sa neme shi ai dole yazo ya dauke ki."

Da sauri ta dauko wayar, ta kira amma sai taji alamar anyi blocking number, ajiyewa tayi jiki a sanyaye tana fadawa Maman, kira mata Habib tayi, tace yazo maza gida yanzu duk abinda yake yi, be dau wani lokaci ba sai gashi, ta fad'a masa abinda take so yayi,yace mata babu mota Abba ya fita, sakashi tayi yaje ya kira musu napep yazo suka tafi, suka fita ta ja ajiyar zuciya, ba zata iya jure tafiyar ko ina ba, ta riga tayi girman da zaman gidan su zai mata wahala sosai, idan kuma ta tafi bata san ta yadda zata dinga ji daga wajen Zeenat din ba.

***Yana zaune bayan sun gama wani taro da sukayi, ba zaka iya tantance yanayin da yake ciki na bakin ciki bane ko na farin ciki, kiran layin Musaddik yake amma still amsar daya ce, switch off, sunyi dashi kafin su taso zai kirashi, gashi babu wani isashen lokaci da zasu sake batawa, su biyu ne suka shigo, suka sara masa sannan suka koma gefe suka tsaya

"It's time sir."

Mikewa yayi be ce komai ba, ya shige cikin dakin, ya dauki jacket dinsa da dayar wayarshi, sauran kayan nasa sun riga sun fitar dasu tun dazu,gaba yayi suka bishi a baya, yana cigaba da kiran Musaddik din, ganin da gaske ba zai same shi ba, shiyasa ya sauya akalar kiran zuwa kiran ta. Jiya basuyi magana ba gaba daya, yasan tana kaiwa yamma a school haka kuma yasan ta dawo a gajiya, ko da ya kirata no answer sai kawai ya kyale ta, a zuwan suyi magana a yau kafin ya taho. Ringing wayar tayi tayi ba'a daga ba, bayan ta katse ya sake kira amma still no answer, sai ya kashe wayar tasa baki daya ya tura ta cikin aljihun wandon sa, sanda suka karaso wajen motocin da zasu dauke su, tuni duk sun shiga shi kadai ake jira, dama kuma shine Captain din tafiyar. Yana shigowa duk suka mike tsaya, irin doguwar babbar motar nan ce, sai da ya zauna sannan duk suka zauna, driver ya jasu suka bar harabar wajen.

   Tun daren jiya labari ya kai fadar Maimartaba na rashin dawowar Iman din daga makaranta wanda ma'aikatan gidan ne suka kai labarin, kamar wasa da kowa ya dauka, a tunanin su ko wani wajen ta biya, amma ganin har dare ya soma yi ya saka hankali ya fara tashi, zama ma neman gagarar Fulani tayi bayan an tabbatar da bata je gidan su ba, ba kuma wani da zata je wajen sa, number driver da tata duk suna shiga amma kuma babu answer. Waya Maimartaba yayi a dare ya sanar da yan sanda abinda yake faruwa, a take ya tashi jami'an tsaron ko ta kwana, suka bazama neman, in da aka samu wayar Iman din da ta driver a cikin makarantar in da aka ajiye a waje daya cikin wata farar leda.

   Tsawon daren babu wanda ya runtsa a tsakanin su, in da suka gama tabbatar da sace su akayi, kuka sosai Fulani take tana hango kalar tashin hankalin da muhammad zai shiga idan ya dawo. Zuwa safiya labari ya fara fita, bayan Maimartaba sunyi waya da gwamna, da wasu manyan jami'an tsaro, cikin kankanin lokaci labari ya baza lungu da sako na k'asar har ma da kasashen dake da makfwataka da k'asar.

  Ana zargin an sace matar dan sarkin Adamawa, jikan sarkin Kano babban jami'in sojoji Captain Muhammad Ahmad Santuraki haka gidajen jaridu suka dinga wallafawa a shafukansu, nan da nan mutane suka dauka kowa na kokarin tofa albarkacin bakin sa.

_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*

_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D'aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

2/17/22, 09:45 - Buhainat: Halin Girma

37

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

*******�

Cikin matukar tashin hankali Abba ya shigo gidan, bayan abinda ya gani a shafin BBC HAUSA, ya saka shi matukat kaduwa, idan har suna nufin surukin sa kenan, toh kenan Iman aka sace? Innalillah wa inna ilaihi rajiun,tashin hankalin da ba'a saka maka rana. Sauri sauri yake yana kokarin isa bangaren Abba babba, kiran Mummy ya shigo wayar sa,

"Shikenan." Ya furta

"Sun samu labari kenan, ta tabbata da gaske ne."

Ya sake fad'a sai kuma ya daga wayar yana kokarin daidaita tashin hankalin da yake ciki.

"Hello Abban Iman, abinda nake gani a news gaskiya ne?"

"Labarin da nake samu yanzu kenan, yanzu muke shirin tafiya dan samun sahihancin labarin, ki kwantar da hankalin ki, in sha Allah babu wani abu da zai faru."

"Innalillah wa inna ilaihi rajiun." Ta furta tana sakin kuka

"Zan tawo yanxu.."

"Sai kin zo." Ya katse kiran da sauri yana shiga ciki, a tsaye ya tarar da Abban yana kaiwa da komowa, yana shiga Abba Musa da Abba Kabiru suka shigo, babu wata magana da suka tsaya yi suka fice da sauri, suka dauki hanyar gidan sarki, dan anan ne kawai zasu samu gaskiyar abinda suke so suji, da Abba Musa yace su kira Muhammad din amma kuma sai suka fasa suka ga gwara su je din kawai ba lallai shima ya iya daukar waya ba.

  Haka sukayi, cikin tsananin tashin hankali suka isa gidan, bayan sun gabatar da kansu aka shigar dasu har in da maimartaba yake, babu wasu mutane sai makusantan sa, suna jimamin abinda ya same su haka bakatatan, sannan lokaci zuwa lokaci suna communicating da chan police station din, duk da babu wani labari akai, dan duk wanda yayi aikin yayi masifar kwarewa wajen gudanar da plan din nasa dan be bar duk wata hanya da za'a neme shi ba, amma duk da haka ba zasu karaya ba, zasu yi iyakar kokarin su dan ganin an samu so cikin kankanin lokaci.

   Labarin da su Abba suka samu yayi masifar sake daga musu hankali dan har kwalla sai da Abba yayi ba tare da kowa ya lura, yadda ake bada labarin rashin imanin masu kidnapping din nan kawai yake tunawa, ga iman sam bata da hayaniya, zata cutu ainun a wajen su sai dai fatan Allah ya bayyana ta cikin aminci da koshin lafiya.

  Suna zaune jugum kowa yana tunanin yadda Moh zai idan ya dawo, ya ci karo da wannan mugun labarin duk uban tsaron da yake ganin ya zuba a gidan sa, lallai addu'a ce kawai mafita a wannan zamanin, dan a duk in da mutum yake ba wai ya tsira daga sharrin su bane.

   Haka kawai yaji kamar bashi da lafiya, duk daukin da yake na zuwa gida ya ganta bayan tsawon lokacin sai yaji kamar duk guzarin sa na barin sa. Tun a airport din yaga kamar ma'aikatan na kallon sa, kallon da ya kasa gane na menene, sai kawai ya kyale hakan a wani dalili nasu da suka sani. Daga nesa ya hango motocin sa, suna jiran isowar sa, dora jacket dinsa yayi a saman kafadar sa ya shiga takawa zuwa wajen su dan basu ganshi ba. Sai da ya kusa daf dasu sannan suka ankara, duk suka taho da sauri kowa na kokarin riga dan uwansa isa, kayan hannun sa suka karba, aka bud'e masa motar ya shiga ya zauna.

"Muje mana." Yace ganin yaki tada motar

"I'm sorry sir." Yace sannan ya tada motar suka bi bayan su sauran. Sake neman layin Musaddik yake a lokaci daya yana neman nata amma duk magana daya ce, switch off, kansa ne ya daure sosai ta yadda za'a ce basu da charge a wayar su kuma tun jiya, be san me yasa ba, sai kawai yaji kamar babu lafiya.

"Me ya faru?"

"Na'am?"

"Kaji ni ai, what's going on!"

"I'm very sorry sir, bamu san yadda akayi hakan ta faru ba, amma we are trying our best kuma gaba daya k'asar ma."

"Ban gane ba, me kake nufi?"

"Kayi hakuri sir, in sha Allah za'a gansu."

" Nace maka me ya faru? Me kake nufi?" Ya fad'a a tsawace yana tasowa kamar zai dake shi

"Kayi hakuri sir, ana neman Madam da driver ta da House help din, tun jiya basu daw...**

" What!!!" Ya fad'a da karfi

"We are very sorry sir!"

" Wannan zancen banza ne, zancen wofi, menene amfanin ku? Nace menene amfanin ku?"

Ya harzuko sai kawai ya taka birki suka tsaya

" Ta yaya akayi tun jiya basu dawo ba, kuma babu wanda zai kirani ya fad'a min? Tun jiya fa!"

" Ohhh... Innalillah wa inna ilaihi rajiun, what's going on, me yake faruwa?"

A cikin tsananin tashin hankali yayi maganar, zuwa lokacin idanun sa sun yi masifar kadawa, wani abu me karfi yazo ya tsaya masa a makoshi, ya dinga jin kamar ya kamasu yayi ta bugu har sai sun fada masa yadda akayi suka yi wannan sakacin.

   Basu wuce gida kai tsaye ba, station suka wuce yana ta kiraye kirayen waya cikin karfin hali, ashe tuni labarin ya kai wa shugaban su har ma da abokan tafiyar sa amma kowa yayi masa kus, ransa yayi masifar baci, ga wani irin tashin hankali da yake ciki, yana tsoron wani abu ya faru da ita, ba zai taba yafewa kansa ba, ba kuma zai yafewa duk wanda yake da hannu a wannan al'amarin ba.

     Duk bayanan da ya kamata ya samu ya samu a station, abu daya ne basu da tabbaci shine in da suke, dan duk babu waya a tare dasu,sannan an cire tracker din dake hade da motar ta daina aiki tun daga cikin school din anan ne last location din motar.

   Jiri ne yaji yana kokarin kayar dashi k'asa, da sauri aka bashi kujera ya zauna yana dafe kansa, wayar sa da take ta faman kara alamun kira ya zaro yana duba number din, Ammi ce tun dazu take son su yi magana be samu dama ba, yace zai kirata amma kuma yasan ta kasa hakuri ne, kowa ya shiga tashin hankali da dimuwa kasancewar kuma har an kwana amma babu wani labari.

    Daga wayar yayi muryar sa a chan ciki, ya gaida Ammin ta amsa cike da tausayawa tilon dan nata, tasan yana da karfin zuciya da kokarin maida komai ba komai ba a tsawon rayuwar sa bata ga wani abu da ya gigitashi ya firgita shi ba, amma tasan dole ne wannan tashin hankalin ba zai iya rik'e shi ba, ba zai iya shanye shi ba ace matar ka na hannun bata gari, ba kuma kasan abinda zai je ya dawo ba. Lallashi da ban baki ta dinga yi masa, tana so ko yaya ne ya kwantar da hankalin sa duk da tasan ba lallai ba, yaji ta ne kawai amma bashi da sukunin nan, yana cikin wasiwasi da tunanin wanda zai aikata masa wannan danyen aikin, idan kidnapping dinta akayi saboda ransom yasan tabbas zasu neme su a tsakanin kwana uku, amma kuma idan ba dan hakan bane fa? Tsoro ne ya kara kamashi, ya mike da k'yar cikin wasiwasin abinda zai je ya dawo, baya fatan wani abu daban ya bullo wanda be taba tunani ko hasashe ba, a tunanin sa duk wani me matsala dashi ba zai wuce gidan su ba, Kamal da mahaifiyar su, wambai da sauran masu goyon bayan Kamal din, bayan su, baya tunanin akwai wani da wata matsala ta hada su da har zai iya yi masa haka.

   Tunanin sa ne ya katse, yana tuna abinda yake cikin flash din nan da ya bawa Musaddik, yana bukatar sake dubawa ko zai samu wata amsa a cikin video din, amma kuma ya kalla yafi sau nawa, sai dai kamar akwai wani abu da yake missing, be san menene ba, amma kuma zai koma baya ya sake dubawa sosai.

    Tunanin sa ne ya tsaya akan Kamal, dalilin da ya kaishi bangaren sa har ya ajiye masa wannan macijin robar, babu wani abu da ya dauka bayan wannan ajiyar da yayi,tashi yayi da sauri

"Tracker ce!"

 Ya furta ba tare da yasan a fili yayi maganar ba.

"Me kake tunani?" Shugaban yan sandan yace shima yana tashi tsaye

"Kwanakin baya an ajiye min abu me kama da micijin robar irin na wasan yara a adamawa,ina kyautata zaton tracker ce a jiki, ya akayi nayi missing step din?"

"Wa kake tunani?"

" Bana tunanin kowa, amma koma waye ne, yana da alaka da wannan case din."

" Ina macijin robar."

" Yana gida!"

" Nan ko adamawa?"

" Yana nan..."

"Ok muna bukatar shi ko zai taimaka mana wajen binciken mu."

" Shikenan."

Hannu ya mik'a masa

" Sai naji daga gareku."

" In sha Allah zamuyi kokarin mu."

" Nagode." Ya juya ya fice yana ayyana yadda zai fara bibiyar su tamkar yadda suka dade suna bibiyar sa suma.

" Kamal...! I'm coming for you."

A waje ya tarar dasu Abba da wasu yan tsirarin makusantan fada, sai Musaddik da yake zaune daga gefe, wani kallo Moh yayi masa suna gaisawa dasu Abba suna jajantawa juna, sai ya taso ya iso wajen su, ya tsaya daga gefe suka gama gaisawa, tafiya Moh yace su Abba suyi saboda daren da ya fara yi sosai, sallama sukayi masa akan zasu dawo gobe jikin kowa a mace suka tafi gida.

" Ina ka shiga?" Ya jeho masa tambayar bayan ya raka su Abba da ido sanda suke barin station din

"Ina gida, bansan me yake faruwa ba saboda an dauke min waya a masallaci bayan mun idar da sallah jiya, sai Mom ce take fad'a min wai meenal ta gani a media shine...."

"Is ok." Yace yana yin gaba

" Menene kake shirin yi next?" Ya bishi yana tambayar shi

" Me zanyi? Bayan case din yana hannun da ya dace, sai mu zuba ido mu gani."

 Yayi maganar kamar be damu da abinda ya farun ba, gid'a kai Musaddik yayi ya cigaba da bin bayan sa ganin yadda yake sauri kamar zai tashi sama. Har wajen mota ya rakashi, ya tsaya daga baya maimakon ya shiga kamar yadda suka saba, alamar ya akayi Moh yayi masa ganin ya toge daga baya be shigo ba

" A mota nazo, zamuyi waya Allah ya bayyana ta Allah ya rufa asiri."

" Ok."

 Kawai yace ya zuke glass din motar sama, suka bar wajen.

"His acting strange, amma tun yaushe?"

Ya tambayi kansa yana mamakin yanayin Musaddik din, share zancen yayi kawai ya lumshe idon sa, kirjin sa na masa wani irin suya.

   A harabar masarautar suka tsaida motocin, aka bud'e masa ya fito ya nufi ginin bangaren Takawa, yanayin tafiyar sa kadai zaka kalla ka gane tsantsar damuwar da tayi masa dabaibayi, har be san kalar tunanin da ya kamata yayi ba, a wanne hali take? Me taci me suke mata? Duk shin yake masa yawo akai, a daren yau ba sai gobe ba, zai fara aikin da yake ta jinkirtawa tsawon lokaci yana jiran right time kamar yadda yasha cewa, sai dai yanzu yana ji aransa shine right time din.

   Tun da ya shigo Takawa yake kallon sa cike da tausayawa, akwai sauran dauriya da jarumta a tattare dashi duk kuwa da babu kaso mafi rinjaye na karsashin sa, amma karya kake daga kallon fuskar sa ka iya tantance abinda yake wakana a zuciyar sa. Hakan ya dade yana bashi nasara akan duk mutanen da basa son shi, dan be basu kofar da zasu gano lagon sa ba, kuskuren sa daya, da yake kyautata zaton shi ya basu damar cutar dashi, shine yadda ya kasa boye son da yake mata, har ya zama musu wani tsani na ganin sun kaishi k'asa.

  Ya jima da sanin Kilishi bata son ko ganin wulgawar shi, haka Kamal yana cikin jerin mutanen da zasu iya yin komai don ganin bayan sa, sai kuma wambai da wasu mukarrabn fadar, sai dai asalin kiyayar ba tashi bace, ta mahaifiyar shi ce da suke ganin an auro ta daga gari irin na kano, suna ganin kamar hakan zai saka kanawa su zama sune zasu mulke su. Sai dai idan ka tattara duk wadannan mutanen toh zaka samu basu da wata alaka da iman din, balle idan sun cutar da ita su amfana da wani abu, hakan ya saka kansa ya sake chunkushewa, ya rasa kalar tunanin da zai.

   Zubewa yayi agaban Takawar, sai a lokacin yaji kamar an zare duk wani karfin zuciyar sa, yaji bashi da sauran katabus, yaji komai masa ya saki, sai ya dinga jin sa tamkar wani karamin yaron da aka dake shi aka kuma hanashi kuka.

"Karka yi kokarin shanye bacin ran da kake ciki muhammadu, ka fitar da komai zaka ji sauki." 

Jan jikin sa yayi zuwa gaban Takawan, ya kwantar da kansa a saman cinyar sa.

    Ya jima sosai a haka, kafin ya fara jin nutsuwa na saukar masa, sai a lokacin ya dago, ya zauna daidai.

"Sannu, babu abinda zai faru in sha Allah, zasu dawo lafiya lou."

"In Sha Allah."

***Babu wanda batan Iman be girgiza ba, hatta Mama da take ikirarin bata son ta sai da taji babu dadi, gidan ya cika duk kowa ya zo suna zaman jajantawa juna, zeenat dama ko da Habib ya kaita gidan su Bashir din achan suka same shi, yace su dawo zai zo da daddare sai su tafi, haka suka sake kwaso kafa suka dawo gashi shiru be zo ba har washegari sai kuma wannan bakin labarin.

   Mummy da Mamma sun zo a ranar suma, suka sauka a gidan Iman din, kana kallon su kasan suna cikin tashin hankali, kowa baya cikin nutsuwar sa musamman Abba, da mahaifiyar ta wanda suka fi kowa kusanci da ita idan ka cire mijinta. Shi ba zaka taba gane ainahin yanayin da yake ciki ba. Tunda ya shigo gidan ya shige daki ya kulle kansa, ya dauko system din sa ya jona ta, yayi playing video din nan yana son ganin wani abu. Ya dade sosai a dakin, har ma suka manta da ya shigo gidan, ba laifi gidan da mutane wanda suka zo daga chan gidan sarki, sai su Ya Maryam da yan uwa dai na kusa. Duk suna jiran tsammani.

***Sosai take galabaita saboda aman da take ta faman yi, babu wani abu da yake zama a cikin ta komai taci sai ta dawo dashi, zuwa lokacin ta gama galabaita dan ko tashi bata iyayi komai sai dai Ummimi tayi mata. Sau biyu yana fad'a musu cewa gimbiya ta bata da lafiya amma suka yi biris da ita, suka kyaleta a cikin wahalar suna sane da labarin yadda ake neman su babu dare babu rana, duk wani moves din da jami'an tsaron suke suna sane dashi.

   Sigari ya zuka ya fezar, sannan ya karbi sabbin layukan da ya saka aka kawo masa wajen guda hamsin, daya ya dauka, ya mik'a hannu ya dauki yar karamar waya a gefen sa ya saka, ya hau kai yayi murmushi ya shiga text message ya saka number Moh, ya rubuta

_"Ba kudi muke bukata ba, rayuwar ka muke bukata a matsayin fansa ga rayuka biyu masu muhimmanci a wajen ka, matar ka da cikin da take dauke dashi." _

Yana tura wa ya balla sim din, ya kyalkyale da mahaukaciyar dariya.

_" Let the game begins Captain MAS!" _

_ZAFAFA2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO_*

_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D'aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

8

2/19/22, 19:58 - Buhainat: Halin Girma

38

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

****

Zaune yake a office din commissioner of police lokacin da message din ya shigo wayar, karantawa yayi yana kai karshe ya mike tsaye da sauri.

"Ya akayi?" CP ya tambaya shi yana kallon yana yin sa

"Akwai matsala..." Sai ya mik'a masa wayar ya soma zagaye a cikin office din cikin tsananin tashin hankali, idan har akwai ciki a jikin Iman toh lallai tana cikin halin tashin hankali, yasan yadda ciki musamman a watannin farko yadda yake wahalar wa yawa yawan mata suna shan wahala kafin ciki yayi kwari wasu kamar zasu rasa ransu saboda tsabar wahala. Ya take ciki yanzu? Me take ci?

"Akwai wani da kake da matsala dashi banda matsala ta cikin gida?"

CP ya tambaye shi bayan ya maimaita karanta sakon fiye da sau goma, har ya gano abu daya a cikin sakon, akwai kiyayye me zafin gaske tsakanin duk wanda ya turo sakon, duk wanda yake son ranka ba karamin kiyayye yake maka.

  Girgiza kai yayi ba tare da yayi magana ba,

"Idan ka gamsu da maganganun da mukayi, lallai muna da bukatar Kamal a binciken mu, domin idan har ka tattara bayanan baya da na yanzu zaka gane akwai wani abu da yake a boye a bayan dukkan cases din, case din ka da Laila, evidence din da ya wanke ka, sannan matar ka, zai iya yiwuwa wani ne da yake son ta tun ba yanzu ba, ko kuma wanda yake da matsala da kai ne amma shi da kansa yake son daukar fansa shiyasa har yayi kokarin wanke ka a baya, duk wannan tunani na ne, ban ce ya zama gaskiya ba, amma ina ji a raina, cases din suna da alaka da juna."

Zama ya kuma yayi a kujerar da ya tashi yana tattare bayanan dukka a kwakwalwar kansa, jiya baki daya ranar a cikin bincike yayi ta, babu mutum daya da binciken sa ya nuna masa sai Kamal. Evidence din farko shine sanda ya shiga bangaren sa, sai na biyu da suke zaune suna magana da wani mutum ya sunkuyar da kansa, wata mace a gefen sa itama babu fuskar ta, fuskar Kamal din ce kadai ta nuna wanda ya tabbata shi be sani ba, yana kyautata zaton gadar zare suka danawa Kamal din sukayi amfani da son mulkin sa suka samu abinda suke so sannan suka yi dumping din sa.

"Duk abinda ya kamata ayi, ayi Sir."

"Zamu fara da Kamal, ina fatan hakan ba zai zama matsala ga Maimartaba ba."

"In Sha Allah." Yace yana mikewa, jiri ne ya debe shi, yayi kamar zai fadi da sauri CP ya tashi yana riko shi

"Subhanallah, Capt akwai matsala ba, sai ka daure saboda tana matukar bukatar taimakon ka a wannan gabar."

Gid'a masa kai yayi yana rik'e kansa da yake mugun sarawa, be runtsa ba tunda ya diro garin Kano, ba kuma yajin idan ka cire ruwa ya sakawa cikin sa wani abu, sai da ya dawo daidai sannan ya mike yayi masa sallama, ya rakashi da ido yana yaba wa kwazon sa.

***Gidan su Iman din ya wuce kai tsaye, dan sunyi waya da Abba da safe yake ce masa bashi da lafiya, kamar ma bp din sa ne yayi sama, yasan batan Iman din ne ya saka shi shiga matsalar.

   A kofar gida ya tarar da Habib da saurayin nan na ranar nan, dauke kai yayi kamar be gansu ba, sai da Habib din ya taso yazo wajen sa yana kokarin kiran waya.

"Sannu da zuwa."

"Ah... Babban Yaya."

Ya mik'a masa hannu suka gaisa, sannan yayi masa jajen abinda ya faru, suna maganar Mahfuz ya karaso wajen, ya mik'a masa hannu kansa tsaye, kamar ba zai bashi hannun ba, sai kuma ya mik'a masa a dakile suka gaisa.

"Zanga Abba."

"Owk Bismillah."

Yayi gaba, shi kuma suka biyo bayan shi tare da Mahfuz har part din su, Abba na kwance a falo kan doguwar kujera, Mama ta shiga ciki dauko Hijab suka shigo, ya durkusa har k'asa ya gaida Abban, wanda yake kallon sa ciki da tausayawa, ya ga dauriyar sa sosai dan kana kallon sa zaka gane yadda ya tabu, ya rame sosai amma be karaya ba, be kuma zauna ba tun da ya dawo.

"Akwai labari ne muhammadu?"

"In sha Allah Abba, ana iyakar kokari."

"Toh basu kira ba har yanzu ko?"

"Basu kira ba Abba."

"Shikenan Allah ya dawo mana dasu cikin koshin lafiya."

"Amin Abba"

"Sannu da kokari, kai ma Allah ya biyaka, Allah ya tona asirin azzalumai, tun jiya ban runtsa ba, na rasa in da zan saka raina naji dadi, shikenan mutun bashi da daraja a k'asar nan tamu? Ace satar mutum tafi satar kaza sauki? Wannan wacce irin musiba ce... Allahumma ajirni fi musibati..."

"Allah ya bayyana su."

" Amin ya Allah. "

Suka hada baki gaba daya, shigowar Mama da Zeenat a bayan ta ne ya katse maganar da Moh yaso yayi, ya dan kalle su sai ya dauke kai ya maida wajen Abba da alamun sa ya nuna yana jin jiki. Gaisawa sukayi da Mama sama sama tayi masa jaje, sannan Zeenat da gaishe shi itama ya amsa yana mikewa.

"Bari na koma Abba, duk yadda ake ciki zan kira dan Allah ka kwantar da hankalin ka."

"Shikenan, Allah yasa muji alkhairi."

" Sai anjima." Ya dan kalli gefen da Mama take ya fad'a sannan ya fice Habib da Mahfuz suka bi bayan sa, sun kusan kai gate din gidan Mahfuz yace

" Zan iya taimakawa."

Tsayawa chak Moh yayi da tafiyar da yake ya juyo.

"Idan har zaka yarda zan iya taimakawa."

"How? Ta yaya?"

"Security ne from an intelligent agency a UK."

"Sounds good."

Moh yace yana dan rage hadewaar fuskar sa. Sai ya bud'e hannun sa alamun babu matsala yace

"Idan har zaka iya taimakawa, shikenan sai muje ko?"

"Let me freshen up, zan zo daga baya. Ina zan same ka?"

" Habib ka rakoshi gida na, don't take long please."

" In Sha Allah."

Juyawa yayi ya fice su kuma suka koma ciki don Mahfouz ya shirya, anan suka tarar da Gaji a part din ta saka Abba a gaba tana ta rusa kuka, bata samu labarin ba sai da Moh yazo yanzu sannan tasan abinda yake faruwa, taji zancen a radio har ta tausaya amma bata kawo Iman bace ,bata ma fuskanci zancen ba kwata kwata ma gaba daya. Baki Abba yake bata akan tayi hakuri amma taki, sai kuka take ita lallai sai an kaita gidan Iman din, a dole haka Abba ya saka tabi su Habib din ko ta barshi ya ji da kansa shima kawai dauriya ce irin ta namiji.

   Yana shiga gidan ya tarar da motocin masarauta, ciki ya shiga kansa tsaye, da mamaki yake kallon Fulani a zaune a falon nasu, tare da mummy da Mamma sai wasu matan, suna zaune jingum jingum cikin alhini da jimami, daga gefe hadiman Fulanin ne suma a falon, kallo daya yayi ma duk matan falon, ya karasa gaban Fulanin ya durkusa ya gaishe ta, ta amsa muryar ta na rawa alamun  bata dade da gama kuka ba, juyawa yayi ya gaida su mummy wanda sai a lokacin ya samu ganin su, ta fad'a tayi fayau amma kuma a nutse take sosai, sai yace ma Mamma ta fita fita hayyacin ta, wuce su yayi zuwa ciki, suka rakashi da kallon tausayawa.

   Dafe kansa yayi bayan ya zauna a gefen gadon, komai nata yana nan a dakin hatta da handouts din da ta fito dasu ranar da zata tafin gasu nan a saman gado, be san me yasa abubuwan suka juye masa a yadda be yi zato ko tsammani ba. Wayar sa ce tayi kara, ya dauka yana kallon sunan, Bubu ne

"Menene alakar Kamal da batan matar ka?"

"Barka da rana Bubu..."

"Barka dai, ya mukaji da alhinin? Allah ya bayyana su cikin koshin lafiya."

"Amin ya Allah."

"Ina jin ka, menene alakar Kamal da batan matar ka?"

Saman goshin sa ya shafa kad'an, kafin yace

"Bincike ne ya kawo hakan Bubu."

"Shikenan, Allah ya sa muji alkhairi."

"Amin ya Allah." Yace sannan sukayi sallama.

   A tsammanin sa Musaddik zai neme shi da zarar gari ya waye, ya kuma rakashi duk wani waje da zai je, amma kuma ga mamakin sa sai gashi har rana ta daga babu ko waya daga gareshi, bayan yafi kowa sanin muhimmancin da Iman take dashi a wajen sa, shine mutum na farko kuma na karshe da ya yarda dashi kaf duniyar nan idan ka cire mutane hudu mafiya kusanci dashi, Ammin sa, Takawa, Aji da Bubun sa, bayan su be yarda da kowa ba sai Musaddik wanda ya yarda da tsantsar kaunar da shi ma yake masa, fiye da wadda shi yake masa, say da yawa Musaddik ya sha shiga rigima saboda shi, ya kuma sha shiga tashin hankali saboda shi, amma kuma ya kasa gane dalili daya, da zai saka Musaddik din kasa jajanta masa kamar yadda ya saba a baya, duk wani abu masa tare sukeyi.

   Tashi yayi yana dan zazzagaya dakin, yana so ya dauke tunanin daga zuciyar sa,yana so yayi wa Musaddik din uzuri a karo na farko kasancewar dan Adam ajizi ne, watakila wani uzurin ne ya danne wannan din. Wayar sa ce tayi kara, ya matsa yana dubawa, sakon text message ne from an unknown number, da sauri ya dauki wayar yana dubawa.

_"Ka shirya?"_

Da sauri ya maida masa reply

"Waye kai, me kake so?"

Sai da aka dau lokaci sannan akayi reply da wata number daban

"Ashe har kana da lokacin tsayawa tambayar waye bayan rayuwar matar ka da ke cikin hatsari."

"Ina zamu hadu? Ka dawo da ita nayi maka alkawarin zan kawo maka kai na da kai na."

Nan ma sai da aka sake daukar lokaci kafin yayi masa reply da wata number daban kuma

_"Idan na shirya zan neme ka, karka bata lokaci wajen tracking din number, ba zaka taba samu ba." _

Kiran number yayi da sauri, amma sai yaji ta a kashe, ya bi sauran layukan da sukayi magana suma duk a kashe, text message ya turawa CP na numbers din dukka.

    Kira ne ya shigo wayar sa daga gate din gidan, kamar be zai daga ba sai kuma ya tuno da zuwan su Habib, dagawa yayi suka tambaye shi ko yasan su, yace a farsu su shigo brothers din Iman ne, da haka ya kashe ya sauya rigar sa zuwa mara nauyi saboda zafin da yake ji.

***Dagata Ummimi tayi ta taimaka mata bayan ta gama amai, ta gyara wajen ta dawo ta tsugunna a gabanta tana mata sannu, da kai ta amsa mata, ta rufe idon ta hawaye ya gangaro mata. Shigowa sukayi su hudu, shine a gaba suna bin bayan sa, ya zo gabanta ya durkusa ya saka hannu ya dago kanta.

"Fine Lady." Ya shafi gefen fuskar ta, ta saka ragowar karfin da take dashi ta ture shi, ya tuntsure da dariya yana kallon ta

"Ga Dr nan zai duba min ke, dan ina tunanin nine zan maye gurbin Capt bayan na aikashi barzahu, kina da kyau."

"Dr matso, a duba min da kyau idan har ciki ne, a cire shi ko ta yaya ne, ba zan iya jure ganin sa ba, kaga auren mu ba zai dau lokaci ba idan aka cire shi."

Matsawo likitan yayi, ya bud'e idon ta, sannan ya taba goshin ta, ya dauko wata roba a cikin kayan sa ya mikawa Ummimi.

" Gashi fitsari zatayi."

Kin karba tayi, na bayan ya daka mata tsawa, ta karba da sauri tana daga Iman din, dukkan su hawaye suke amma babu me bud'e baki yayi musu saboda tsoro. Tare sukaje tayi fitsarin suka fito ta dawo ta kawo masa, ya karba a wajen ya duba, ya kuma tabbatar da ciki ne, yan tambayoyi yayi mata akan period dinta ta amsa tana kuka.

"Ciki ne oga, na sati shida."

"Ya za'a yi dashi?"

"Ba zai wahalar fita ba, tunda karami ne. Yanzu dai zan dawo sai nazo da maganin da zata sha."

"Yayi kyau, rakashi yaro." Rik'e masa jaka wanda aka kira da yaro yayi suka fita, sannan shi ma suka fita.

"Hello... Samha baby." Ya fad'a da yaji ta daga wayar

"Eh tana hannu har yanzu."

"Eh ya tabbatar da ciki ne, amma za'a cire shi tunda baki da bukatar shi."

"A ah... Babu fa abinda zan yi wa masoyinki, kawai wata yar harkalla ce zamu karasa ta. "

" Yawwa toh" tace tana jin dadi.

" Sai mun sake magana ko? "

" Amma ai bana samun ka kwata-kwata a waya, me yasa?"

" Babu komai, idan akwai bukatar muyi magana ni zan kiraki da kai na."

" Shikenan."

Dariya yayi sosai bayan sun gama maganar, be san bata da tunani ba kwata-kwata sai yanzu, amfani yayi da ita ya samu abinda yake so, ba kuma zai kyale wanda ta kwallafa rai akai ba, ba zata taba samun cikar burin ta ba in dai yana numfashi.

***A waje ya tarar da su Habib din bayan ya gama parker motar, ganin tare suke da Gaji ya sakashi saurin karasawa ya taimaka mata ta fito, sannan suka gaisa ya saka aka rakata ciki su kuma yace su biyo shi garden dake baya. Kujeru ne a wajen, ya zauna sannan suka zauna suma, yana karantar yanayin Mahfuz din, sai a lokacin yayi masa kallon tsaf, ya kuma fahimci hakan yanayin sa ne, ku kuma yanayin environment din da ya taso kamar yadda Habib yayi masa bayani dazu.

"Ta yaya zaka iya taimakawa?" Yace bayan ya gama nakaltar yanayin sa, gyara zama yayi sosai, yayi murmushi sannan yace zai masa yan tambayoyi,da ka ya amsa masa ya bashi go ahead.

"Babu wani message ko kira da ka samu daga wajen kidnappers din?"

"Akwai."

"Zan iya gani?"

"Why not?" Ya mik'a masa wayar, ya karba ya duba messages din dukka, ya jima yana sake dubawa kafin ya mik'a masa wayar sa

"Kayi tunani sosai, wanene kake da matsala dashi, irin wadda kasan lallai da zai samu dama akan ka zai iya aikata maka komai?"

"Babu shi, bansan waye ba gaskiya."

" Babu ko old friend? Ko abokin aiki?"

Shiru yayi cikin tunani

" Think... "

_" Zan dawo komai daren dadewa, sai na dauki fansa akan ka, ko da zan karar da komai da na mallaka ma duniya sai na maida rayuwar ka abun kwatance! "_

"JABIR! " Yace yana mikewa tsaye da sauri, tashi Mahfuz yayi shima yana kallon sa

" Waye shi. "

" Aboki na ne, abokin aiki na ne. "

" Recently na samu labarin ya zama babban terrorist kuma yana da connection da manyan k'asar, bayan shi bana tunanin akwai wanda zai bukaci rayuwa ta, babu. "

"Ya akayi na manta? Ya akayi? "

" Kasan in da za'a same shi? "

Girgiza kai yayi,

" Ban sani ba. "

Komawa sukayi suka zauna, Mahfuz ya ciro biro da paper ya rubuta wani abu, daidai lokacin da Moh ya daga wayar Musaddik yace ya same shi a garden, yana ajiye wayar sai gashi ya zagayo dama chan yana cikin gidan, da kallo Mahfuz ya bishi kafin ya karaso wajen yace

"Waye shi?"

"Best friend dina ne."

"Ok." Yace a gajarce ganin ya karaso, ya mik'a musu hannu suka gaisa amma da ya bawa Mahfuz hanun sai ya rik'e  hannun nasa har sai da suka kalle shi dukka, sai ya saki yana murmushi ya jingina da kujerar da yake kai, wani kallo Musaddik yayi masa ya zauna yana maida hankalin sa kan Moh.

"I'm very sorry Capt..."

"Babu komai, nasan wani uzuri ne dakai." Ya katse shi kafin ya karasa.

"Babu wani progress ko?" Yace

"Babu."

"Allah ya bayyana su."

"Amin."

"Ya aiki?" Mahfuz ya tambayi Musaddik unexpectedly

"Aiki Alhamdulillah."

"Wanne aiki kake?"

"Harkar kwangila, kaifa?"

"Detective!"

Wani kallo Musaddik yayi masa, yayi shiru,.sai kuma ya kalli Moh

"Naga kamar kana da baki, dama inaso muyi maganar flash din nan ne tunda naga ka dawo."

"Flash?" Mahfuz yayi karaf ya tambaya

"Let's talk about that later." Moh yace sai ya mik'a wa Musaddik hannu

"Suna ina?"

Sosa kansa yayi

"Dalilin da yasa kaga kamar ina janye kaina a case din nan kenan, wallahi bansan ya akayi ba, na rasa su gaba daya."

"What!"

"Kayi hakuri,ranar da aka sace wayata aka hada dasu gaba daya, bansan ya zan maka bayani ba, nasan kuma muhimmancin flash din a wajen ka, shiyasa na kasa nutsuwa."

Murmushi kawai Mahfuz yayi, ya dire pen din hannun sa akan dan deborin da yake gaban sa, ya dora hannun sa akai ya jingina yana masa kallon tsaf.

" Idan nace wani abu zaka yarda dani?"

Girgiza masa kai Moh yayi dan maganar batan flash din ba karamin bashi mam I'llaki tayi ba.

"Ina bukatar yara hudu cikin yaranka na gate."

" Me zasuyi maka?" Musaddik yace ransa a bace.

" Wait and see." Yayi murmushi, shi Moh ba gane kan maganar ba kwata kwata, yayi dai abinda Mahfuz yace ya kirawo su suka zo, suka tsaya daga gefe, tashi Mahfuz yayi ya zagayo ta bayan Musaddik,

"Take off your mask!"

"Kamar ya?"

"Me kake nufi Mahfuz?" Moh da shima ya mike ya fad'a cike da mamaki

" This man is deceiving you, ka kalli hannun sa, ka kalli fuskar sa, akwai banbancin skin color, he's definitely using a mask, idan har ya musa, zan tabbatar maka."

"Noo...you are mistaken, wannan Musaddik ne, trusted friend dina ba zai taba deceiving dina ba,you cannot accused somebody without a proof."

" Shine zan maka proving yanzu ai, wait and see, guys... Ku rik'e shi."

" Dakata!"

Moh yace ransa na baci, ba zai dauki wulakanta Musaddik yana kallo ba.

"Waye wannan Capt, waye zai zo ya shiga tsakani na da kai?"

"Calm down aboki na, misunderstanding aka samu amma zan masa magana..." Sai ya juya wajen Mahfuz din

"Let's call it a day, zamuyi magana gobe, Habib ku jirani a wajen mota."

"Muje Mahfuz."  Wani kallo yabi Musaddik din dashi, sannan ya juya suka bar wajen da Habib.

Juyawa kan Musaddik yayi da ransa yayi masifar baci, ya shiga bashi hakuri akan abinda Mahfuz din yayi, yace ya jirashi yana zuwa bari ya sallame su. Yana barin wajen ya ciro waya, ya kira shi yana matsawa chan gaba.

"Akwai matsala." Yana dagawa yace

"Ya fara suspecting dinka ne?"

"Be fara ba, wani banzan yaro ne bansan daga ina yazo ba, yaso dole sai ya nuna masa gaskiyar mask da na saka..."

"Ya yadda?"

"Be yarda ba, kasan ya yarda dani sosai, so ba zai taba kawowa ba. "

" You have to be very careful, shi kuma yaron zan san yadda zan yi dashi. "

" Ok sir. " Ya kashe wayar yana juyowa, sukayi ido biyu da Moh da yake tsaye a bayan sa kamar mayunwacin zakin da ya shekara be ce ba.

***Assalamu alaikum sisters, masu korafi naga wasu daga cikin korafin ku, ina mai baku hakuri akan matsalolin da aka samu, dan gane da rashin posting halin girma shekaran jiya da jiya, hakan ya faru ne sakamakon ciwon hakorin da ya matsa min hade da zazzabi, wanda har ta kai ban iya samun duba sakonni ba balle har na iya zaman rubutu

  Duk cikin zafafa biyar babu wadda a cikin mu take jin dadi a duk sanda batayi posting ba, Allah ne shaida ana iyakar kokari wajen ganin Anyi abinda ya dace. Sai dai idan abu ya sha kan mutum a ba yadda ya iya. Allah ya huci zuciyar duk wanda ransa ya baci ta dalilin jira ko wani abu, ba da gangan bane wani lokacin kuma ajizanci ne na dan Adam.

Allah ya rufa asiri ya sa mu gama lafiya

2/21/22, 08:16 - Buhainat: Halin Girma

39

"Capt... Yaron nan ya bata min rai, ya za'a yi ya zarge ni haka?"

Sassauta fuskar sa yayi, ya dafa shi

"Karka damu yarinta ce."

"Naga alama, waye shi? Aina yake?"

"Bansan shi ba, abokin Habib ne I guess!"

"Amma ka barshi ya zage haka, naji ma kamar hausar shi bata fita."

"Eh, born and raised a UK ne, dole zaka ji banbanci, anyways ya wuce na masa fad'a kuma."

"Shikenan, yanzu menene next? Da ya kamata muyi?"

Daga kafada Moh yayi cikin halin ko in kula yace

"Babu komai for now, muna cigaba da addu'a."

"Bari na wuce, I'm sorry akan maganar missing files din nan."

"Karka damu."

Da kallo ya bishi har ya fice daga wajen, ya daga waya ya kira waya, sukayi magana sannan ya kashe. A kalla Mahfuz ya zama wani haske a binciken sa, kowa da yanayi da tsarin aiikin sa, ya san aikin sa sosai ya kuma masifar burgeshi, he's smart and intelligent daga ganin shi,kuma da yake akwai banbancin yadda k'asar mu take da tasu sun fi mu skills da kayan aiki.

  Shugaban su ya kira, ya fad'a masa abinda ake ciki, ya kuma tabbatar masa da zasu yi duk yadda zasuyi, a yanzu za'a binciki layin mudassir din a nan za'a gane da wadanda yake waya, yana ajiye wayar ya kira Ammi sukayi magana sannan ya kira Aji da yake ta avoiding kiran sa tun ranar, yana dagawa kuwa ya haushi da fad'a akan kin daga wayar sa da yayi, hakuri ya bashi kawai sukayi magana ya kashe.

  Bayan kamar awa daya aka kirashi, ya shirya a gurguje ya fita cikin tawagar yaran matasan sojoji, kowanne a cikin su a kalla zaka gane babu sauki a tattare dashi, bakin glass ne a fuskar Moh, baka ko ganin kwayar idon sa. A wani waje suka hadu, ya tarar da taron jami'an tsaro birjik kowannen su cikin shiri, babu kalar da babu na jami'an tsaro tun daga kan police, DSS, civil defense, uwa uba sojoji. Gaisuwa ya dinga amsawa daga kananan ma'aikata har ya karasa wajen manyan da suke kasan wata rumfa suna magana. Details din bayanan da aka samu ta wayar Musaddik din suke dubawa, in da ya nuna babu wata waya da yake yi illa da mutum uku, Moh din sai wata number da take kiran sa kullum a private number sai kuma Samha Bello Turaki, da Kamal Abubakar Santuraki

   Kansa ne yayi masifar daurewa, menene alakar Samha a cikin case din? Karba yayi ya sake dubawa sosai ya tabbatar da abinda yake a rubuce. Yasan Laila ce take son shi ba Samha da take kawarta ba,menene akalar Samha da Iman dinsa da har za'a hada kai da ita a sace ta?be san dalili ba,  abu daya ya yarda dashi, dukkan su anyi amfani dasu ne, domin a samu galaba akan sa, su kuma idon su ya rufe, suna son ganin bayan  din suka fadawa gadar zaran JABIR!

"Mun gabatar da duk binciken da zamuyi akan shi, mun kuma tabbatar da ba Musaddik bane, yayi amfani da fuska ne, sannan yayi amfani da wata na'ura da take kwafar murya, wadda take da masifar tsada Kuma alamu sun nuna ya jima tare da kai, ba zaka taba ganewa ba idan har ba sani kayi ba, Musaddik yana da kusanci da kai shiyasa har sukayi amfani dashi wajen samun kanka, da weakness dinka, sai kuma dan uwanka  Kamal da suka taimaka musu don cimma tasu bukatar da hadin guiwar Samha da bamu san wata alaka dake tsakanin ku ba."

"Layin  da yake private mun saka an bud'e mana shi, kuma mun tabbatar da ana kira da layin ne daga wani bangare ma dajin falgore! "

"Yana ina yanzu? "

" Yana ciki, idan an gama shiryawa shine zai shige gaba, kaine team captain din da zai jagoranci tafiyar daga bangaren mu. "

" Ok sir! "

Yace yana sara masa, wucewa yayi zuwa in da aka ajiye fake Musaddik din, yana so ya tantance banbance banbancen dake tsakanin sa da Musaddik dinsa da ya kasa ganewa, yana durkushe a k'asa bayan dukan da ya sha, ya tabbata dai da JABIR ya tantance shi sosai kafin ya kawo shi, dan hatta tsawo da yanayin sa irin ma Musaddik din ne, fuskar sa ya dago, ya kare masa kallo zuciyar sa na tafarfasa, kamar zai daure amma sai ya k'asa, ya dunkule hannu ya naushe shi a baki, nan da nan kuwa sai jini, ya saka kafa ya hambare shi. fitowa yayi ya tsaya a filin yayi bayanin yadda zasu yi idan sun isa, duk suka amsa suka shiga motocin su a gurguje suka dauki hanyar dajin falgore.

    Gudu suke kamar zasu tashi sama, haka suke a duk sanda suka fita operation amma kuma na yau yasha banban da sauran operation da suka taba zuwa, yau abun nasu ne, su aka taba kai tsaye shiyasa kowa yake ji kaamar abin ya shafe shi sosai, cikin kankanin lokaci suka isa saboda masifar gudun da suke, barbazuwa sukayi a dajin kamar yadda yake according to plan. A daidai lokacin Dr da zai kawo maganin ya iso, tana kwance kamar kullum ta gama galabaita sosai ya shigo rataye da jakar sa, tana ganin sa ta mike da sauri, bata ma san tana da ragowar karfin nan ba sai data ganshi, ya ajiye jakar ya ciro magungunan a ajiye su, sannan ya koma gefe ya tsaya yana jiran shigowar ogan, jim kadan sai gashi ya shigo, ya duba magungunan yayi masa bayanin yadda za'a sha.

"Tashi!" Ya daka mata tsawa yana tamke fuska

"Dan Allah kayi hakuri, dan Allah."

"Wallahi sai kin sha."

"Dan Allah kayi hakuri." Ummimi tace tana kuka

"Shut up munafuka, idan na sake jin bakin ki sai na sheke ki har sai kin daina numfashi. "

Gefe ta koma jikin ta yana ta rawa, bindiga ya ciro ya nuna Iman dashi

"Karbi kisha kafin na harbe ki. "

Hannu ta miko ya zuba mata, ya kafe ta da jajayen idon sa, yana nuna ta da bindigar, ta sha sannan ya juya yana murmushin mugunta ya fice likitan yabi bayan sa. Dakin da ya ajiye Musaddik da driver ya shiga, ya tarar da Musaddik din a kwance amma kuma sallah yake daga haka, kwafa yayi ya fito bayan ya rufe kofar, yazo wajen yaran nasa da suka cika harabar wajen dauke da manyan bindigu cikin shirin ko ta kwana.

"Zan shiga na kwanta, ku kula sosai bana so a samu matsala."

"An gama Oga."

  Suka hada baki wajen fad'a, ciki ya shiga su kuma suka cigaba da tsaiwa a wajen.

  Zagaye gaba daya dajin sukayi, kowa ya kama stand dinsa, Moh da sauran zaratan sojojin suka kutsa kai ciki, sai da suka dan shiga sosai sannan suka hango bukkokin dake wajen, wanda suka tabbatar da nan suke. Sake rarrabuwa sukayi waje waje, suka sake zagaye bukkukin.

  Sai da suka gama shiryawa tsaf, sannan Moh ya basu signal na su yi attacking dinsu, nan fad'a musu ta sama ta ka, nan suka rikice suka shiga kokarin maida martani, sai dai yawan Jami'an tsaron ya ninninka yawan su,. Cikin baccin da ya soma dauke shi yaji alamun yamutsewar wajen, kafin ya kai ga mikewa aka bugo kofar dakin aka shigo, Moh ne a gaba yaran sa na take masa baya, dukkansu a shirye suke su bada rayuwar sa dan ceto Madam din Oga. Kasancewar be shiryawa zuwan su ba, sai ya zama kamar sun ci galaaba akansa ne, babu bindiga ba babu komai a hannun Moh, ya matse shi a jikin bango ya shiga bugun sa, bugu ba na wasa ba, sai da yayi masa laga-laga ya sake shi cikin jini ya fadi kasa, ya bi ya take kansa da kafarsa cikin tsananin bacin rai ya soma magana.

"Kafin kaga karshe na, ni zan ga karshen ka da duk wanda ya goya maka baya..."

" Oga an samu Madam, she's bleeding so badly." Da sauri ya juya yabi bayan dan sanda da ya shigo, ya bar yaran nasa da JABIR.

  Jini ne sosai yake zuba, da sauri ya karasa gabanta, idon ta da yake kokarin rufewa da kalle shi. Rawa jikin sa yake ya tallafota jikin sa

" Bude idon ki, dan Allah ki bud'e idon ke, me sukayi miki? Me sukayi miki?"

Karasa rufewa idon sukayi ruf, ya dagata ya fita da ita jikin sa na rawa, idan har wani abu ya same ta, sai ya karar da dangin JABIR kaf.

_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*

_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D'aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

2/24/22, 08:05 - Buhainat: Halin Girma

40

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

****Wasu daga cikin sojin ne suka bi bayan sa, in da sauran jami'an tsaron suka cigaba da dudduba bukokin har suka samu nasarar ganin Musaddik da driver a wani daki, sai makamai masu yawan gaske suma daki gida, dukkan su suna bukatar taimakon gaggawa musamman Musaddik da yake cikin mawuyacin hali.

   Karar harbi suka ji, daga baya wanda basu san dalilin harbin ba, a zaton su sun kama duk yaran JABIR din, da shi kansa JABIR din bayan dukan da Moh yayi masa. Zagayawa baya sukayi, suka ga mutum a kwance cikin jini, bashi da alamun yana tare da sauran yan iskan amma kuma basu san me ya kawo shi wajen ba.

"Mu taimaka masa."

"Waye ya harbe shi?"

"Akwai sauran yan iskan a baya, let's check, ku dauke shi ku tafi dashi zamu biyo bayanki. "

" Ok. "

Suka ce suka taimaka masa, da k'yar yake numfashi saboda tsabar wahala, a motar da aka saka Musaddik suka saka shi, suka bi bayan motar da Moh suke ciki dan basu taimakon gaggawa. Rik'e yake da hannun ta yana kuka wiwi kukan da ya kasa dauriyar rik'e shi,  gani yake kamar motar bata sauri duk kuwa da irin gudun da suke tsulawa, idan har wani abu ya same ta, ba zai bar kowa ba wannan alkawarin sa ne.

  Sanda suke karaso asibitin tuni iyayen gulma yan jarida sun iso domin samun na watsawa, kofar baya suka koma suka bi, suka shiga asibitin dan a yanayin da take ciki ba zai yarda wasu yan iska su dauke ta a hoto su yada wa duniya ba, duk ma wata gidan jarida ko talabijin da tayi gangancin haka sai ya yi shari'a dasu.

   Da sauri nurses din suka karbeta, daidai lokacin da Babban likita ya karaso cikin tawagar sauran manyan likitoci mata da maza, aka shiga da ita ciki domin bata taimakon gaggawa.

   Zagaye ya soma yi a wajen cikin yanayi na fitar hayyaci, wayar sa da take ta faman nemam agaji ya gaza fitowa da ita balle ya iya amsa kiran da ake ta faman doka masa da ba zai wuce daga makusantan sa ba, bashi da sukunin ciro wayar balle ma ya amsa ta, balle ya iya wata magana ba tare da yasan halin da Iman din sa take ciki ba.

     Cikin kankanin lokaci asibitin ya cika da manyan mutane daga masarauta da kuma gidan gwamnati, Takawa ne ya karaso a karshe ya samu shiga wajen da Moh din yake shi kadai sai wasu sojoji daga gefe, sauran mutane suna ta dayan bangaren in da aka kai Musaddik da saurayin da aka harba wanda yake cikin yanayi mara dadi.

   Yana ganin Takawa yayi saurin isa gareshi, sai kuma ya ja ya tsaya a gabansa ba, hannun sa ya kama, ya ji yadda hannun yake rawa sosai kamar wanda yake jin masifaffen sanyi.

"Kayi addu'a muhammad, babu abinda zai faru kaji?"

Da ka ya iya amsa masa, sai a sannan ya ga su Abba, ya matsa ya gaishe su, dukkanin su suna cikin tashin hankali, Abba kamar bashi ba saboda tashin hankali, sun riga Takawa zuwa wajen amma ba'a barsu sun shigo ba saboda tsoron da yake wajen sai da Takawa yazo sannan suka samu shigowa. Sunyi waya da Maman Iman din tun dazu ya kuma san zuwa yanzu sun karaso amma ba lallai su shigo kai tsaye ba, sai ya dubi Muhammad yace

"Mahaifiyar ta suna waje, nasan ba za'a barsu su shigo ba."

"Bari naje." Ya fad'a yana yin gaba, daya daga cikin sojan ya bishi suka tafi tare, daga chan baya ya hango su a tsaye suna magana da wani Soja da yaki fafur barin su, su shiga wajen, ganin Moha da kansa ya nufo wajen ya saka sojan sake kallon matan.

"Alhamdulillah." Mamma tace tana share hawayen ta

Bud'e musu sojan nan yayi tun ma kafin ya karaso, dan yayi masa alamar ya barsu, suka shigo suka sameshi, ya gaishe su, sannan suka tambaye shi Iman din, Alhamdulillah kawai yace suka bishi zuwa ciki duk jikin su ya kara sanyi sosai da lamarin.

    Be barsu sun karasa wajen da su Takawa suke ba kasancewar duk maza ne, sai yasa aka kawo musu kujera suka zauna shi kuma ya karasa ciki.

   An dauki tsawon lokaci kafin likita guda daya ta fito, har zata wuce sai ta ga Takawa, da sauri ta je ta durkusa ta gaishe shi, sannan tace suna kokarin su in sha Allah babu matsala, sannan ta je ta dauko abu ta dawo ta koma ciki.

     Sun iya iyakar kokarin da zasuyi wajen ganin sun tsaida cikin amma kuma hakan be yiwu ba,saboda karfin maganin da aka bata ba zai bar cikin ba, Allah yaso babu wani illa da yayi mata bayan fitar da cikin. Wankin ciki suka hada sukayi mata sannan aka saka mata drip saboda ta rasa ruwa sosai a jikinta tsawon kwanaki tana amai sannan babu abincin da take ci. Numfashin da take fitar wa ne kadai zai baka tabbacin tana da rai bayan haka babu wani abu na jikinta da yake motsi, tayi fayau kamar ba ita ba, sai uban fari da tayi kamar babu wadataccen jini a jikinta.

   Tura ta akayi zuwa dakin da aka kwantar da ita, sannan Drs din suka fito wajen da su Takawa suke, suka kwashi gaisuwa sannan sukayi bayanin yadda al'amarin ya kasancewa pills din da aka bata ne yayi karbi sosai, jiri ne ya kwashi Muhammad yayi kamar zai fadi wani bafade yayi saurin taro shi, ya rik'e shi jikin sa. Hakuri kowa na wajen ya dinga bashi, kafin a bada damar a shiga a ganta, Takawa ne ya fara shiga sannan su Abba suka shiga tare dasu Mummy, sannan suka fito aka bar Muhammad din ya shiga. Tunda ya shigo ya hangi yadda take fitar da numfashi a wahalce, jikin sa ya kara sanyi sosai, shine duk ya jawo mata wannan matsalar tana zaman zaman ta. A da ya dauka matsalar sa kawai gidansu ne, shiyasa gaba daya ya taso da tsanar mulki tun bayan da yaga abinda ya faru da Baban su Laila lokacin bashi da wani girma sosai amma hakan be bar kwakwalwar sa ba, ya taso da tsanar mulkin da ganin cewa duk wata masifa tana cikin gidan sarauta.

   Sunyi aiki tare da JABIR zai iya kiransa da abokin sa mafi kusanci dashi a wanchan lokacin, bashi da hannu a matsalar da JABIR din ya samu daga sama har aka sallame shi aka kuma karawa Moh din matsayi irjn wanda ya Jabir din ne ya chanchanta, bayan nan duk wata alaka tasu ta yanke, har ya manta dashi sai lokaci zuwa lokaci yake tunashi,be taba saka wani abu a ransa game dashi ba, rayuwar sa yake kansa tsaye ba tare da sanin akwai babban makiyinsa da yake burin ganin bayan sa ba.

   Maganar Takawa ce ta fado masa wadda yayi masa ita dazu kafin ya bar asibitin

_"Ka sani bawa baya taba wuce ko ketare kaddarar sa, dan haka ka dauka wannan din kaddarar ka ce kayi addu'a Allah ya baka ikon cinyeta. Sanin kanka ne mutum be isa ya hana ko dakatar da kaddarar ka ba, kafi kowa sanin yaran da suke tare da kai suna tsaron ka gida da mota ba wai na matsayin da kake dashi bane a aikin ka, alfarma tace ya saka aka baka su har haka, wanda duk munyi hakan ne saboda mu baka kariya a gida da waje, sai dai yanzu na kara tabbatar wa babu dan adam din da ya isa ya tsare ka face Allah, kuma duk abinda Allah ya kaddara zai faru toh fa sai ya faru ko da a gaban idon mutum ne."_

   Gaban gadon ya ja ya tsaya cikin tsananin tausayin ta, be taba kawo tunanin wani abu zai faru da su haka ba a dan kankanin lokaci nan, ya zata shikenan ta rabu da duk wata matsala tun da suka riga sukayi auren su, ashe ba haka bane. Hannun wanda babu drip a jiki ya rik'e, ya zauna a gaban gadon yana karewa fuskar ta kallo, daga gani kasan ba jin dadin baccin take ba, bacci ne me cike da wahala iri iri.

    Ya jima sosai a dakin, babu motsin komai, kamar babu kowa aciki, knocking akayi, ya cire kansa da k'yar ya kalli kofar ba tare da yayi magana ba, sai da aka sake kwankwasawa sannan yace

" Bismillah. " Turo kofar akayi, Zeenat da Habib ne a gaba sai Mam, sai sauran jama'ar gidan da sai yanzu suka samu damar shigowa wajen, tashi yayi daga zaunen, ya mikawa Habib hannu suka gaisa, fuskar sa ta dan daga alamun yayi kuka, ya mai jiki yayi masa sannan suka gaisa da sauran matan, suka fita tare da Habib din waje,

"Ina Mahfuz?"

Yayi karfin halin tambayar sa dan yayi tunanin tare zasu zo. Dan duban sa Habib din yayi kamar me tunani, sai kuma yace

"Ai tare aka fito dasu daga wajen da Iman din take."

Kallon rashin fahimta Moha yayi masa yace

"Ban gane ba?"

Kwalla ce ta zubowa Habib din yayi saurin sharewa yana daurewa yace

"Dazu da safe ya fito daga gida akan zaizo ya same ka, nace zan raka shi amma ya bari anjima yace zai gane ma ai, shikenan ya tafi, bansan ya akayi ba, sai gashi shima an same shi a chan in da Iman din take."

Kafin ma ya karasa tuni Moh ya firgice, yasan an ce akwai mutum uku bayan iman da Ummimi, daya an harbe shi ma aamma sam be kawo tunanin komai ba, be ma kara tunawa ba saboda damuwar da ta danne shi, yana so dai yaje ya tabbatar da Musaddik na cikin wadanda aka samo din amma sai yake ganin kamar idan ya matsa daga wajen ta komai zai iya faruwa.

"Yana ina?"

"Yana chan emergency unit har yanzu bamu ji komai daga garesu ba, su Abba dai suna chan?"

"Innalillah wa inna ilaihi rajiun, muje."

Sauri sauri ya dinga yi kamar zai tashi sama, idan wani abu ya samu yaron fa? Ya zai da ransa wai? Ba'a barin kowa ya shiga wajen nasa saboda yadda case din nasa ya zama very complicated case, bayan sun yi nasarar cire bullets din amma sam jinin ya ki tsayawa, ana kara wani, wani yana fita, su kansu abin ya basu tsoro ganin yadda yake zubar da jini, shiyasa suka hana kowa shiga, su Abba da suka dawo wajen tun da suka samu labari jikin kowa ya gama sarewa da al'amarin Mahfuz din.

   Moh na isa wajen dr na fitowa daga ciki, jikin sa babu kuzari ya nufo wajen da su Abban suke, ya kalle su daya bayan daya kafin yace

" Sai dai muyi hakuri... "

Wani irin zubewa Moh yayi a wajen, kirjin sa na masa wani irin suya, ashe Ajali ne ya kawo shi k'asar? Ashe dama shine sanadin mutuwar sa, me yasa yayi masa wannna tsawar, me yasa ya ci masa mutunci bayan be san wani abu dangane dashi ba,

"Nooo Dr... No be mutu ba, Dan Allah karka ce min ya mutu dagaske, ban kyauta masa ba, be kamata ya mutu ba, he's innocent be kamata yayi facing irin wannan mutuwar ba, me yayi? Menene nasa a ciki?"

"Get hold of yourself Capt, kullu nafsin za'ikatul ma'ut, hakikaa kowacce rai sai ta dandani zafin mutuwa, shi da ya tafi be yi sauri ba, mu kuma bamuyi jinkiri ba, addu'a kawai yake bukata."

Dr yace ya juya ya barsu a wajen, babu wanda ya iya motsi a wajen saboda tsabar kaduwa, yaro me zumunci me shiga rai, me son yan uwan sa, ya Yaya zataji? Labarin mutuwa irin wannan mara dadi, kullum korafin ta akan Nigeria shine rashin tsaro, ko waya sukayi ta kan ce musu Nigeria ta zama abinda ta zama, rai ba abakin komai yake ba. Kullum maganar ta kenan, tsoron ta kenan, ashe bata tsira ba, Ashe zaman ta a chan bashi ne zai sauya kaddara ba? Innalillah wa inna ilaihi rajiun kowa yake maimaitawa babu hargitsi ko hargowa, saboda dauriya irin ta maza, sai dai kana kallon su zaka san mutuwar ta dake su, musamman Habib da Moh, kafin kace kwabo labarin ya zagaye ko ina, kowa sai da ya tausaya wa Mahfuz irin kaddarar da ta fad'a masa.

   Zuwan Aji da Bubu ne ya dawo da Moh cikin hayyacin sa, babu hawaye ko digo a fuskar sa amma ya daku, ya kadu da zaka iya rantsewa ya dade a kwance yana jinya me tsanani.

   Baya magana bayan amsa gaisuwa sai dai kawai ya amsa maka da ka, har zuwa lokaci itama bata farka ba, yaje yaga Musaddik wanda yake da sauki sai ciwuka a jikin sa yawanci na duka ne. Sai kuma yunwa da ta ramar dashi sosai, driver da Ummimi babu abinda ya same su dama su ba sune targets din ba.

   Wajen azahar ya dawo dakin da take, har lokacin bata tashi ba, mummy ce kawai a dakin tana zaune gaban gadon da Iman din take, idon ta yayi ja sosai, addu'a take tofa mata ya shigo ta tashi a kunyace tana kokarin barin dakin

"Dan Allah mummy ki yi zaman ki, dama nazo na duba ko ta farka ne, zanje station din na dawo."

Komawa tayi ta zauna shi kuma ya fita, ya shiga mota ya nufi station din. Direct office din CP ya wuce ya samu DSP yana press conference akan case din, kokarin fita yayi amma babu dama sun riga sun ganshi, sukayi masa cha kuwa kowa na son masa tambayoyi, be basu dama ba dan yanzu ba wannan ne a gaban sa ba, da kansa zai shirya ya basu lokaci amma ba yanxu da be ma san me yake masa dadi ba sam. Hakuri aka basu, aka kuma sallame su sannan ya samu ganin CP din sukayi magana, ya kuma shiga wajen da aka ajiye Jabir din. Yayi matukar laushi sosai saboda ba karamin duka sojajin nan sukayi masa ba, dama yasan ba zasu kyale shi ba, hakan ba dan dai basaso a samu matsala ne amma tsaf zasu iya kashe shi a wajen.

    Baya jin a yanzu akwai wata halitta da ya tsana sama da Jabir din, shiyasa ya tsaya daga kofar be shiga ba, dan idan ya shiga zai iya shake shi har sai ya daina numfashi. Wani dan sanda ne a gaban sa rik'e da wani katon katako, yana masa tambayoyi, sai kuma wasu yan sandan suma daban daga gefe cikin fushi suke interrogating dinsa yana rokon suyi hakuri. Juyawa yayi ya bar wajen ya koma suka karasa magana da CP sannan ya bar station din ya dawo asinine, in da ya wuce kai tsaye wajen Musaddik, ya samu dakin da yan sanda suna daukar bayanai daga wajen sa, wucewa yayi ya koma bangaren Mahfuz da har yanzu ba'a saki gawar sa ba, sai an gama bincike tsaf sannan za'a basu suyi masa sutura. A chan ya zauna tare da su Habib dasu Abba har bayan Magriba sannan aka basu gawar tasa, suka dauke ta suka nufi gida da ita don yi masa sutura a mika shi gidan sa na gaskiya.

   Zuwan su ya saka gidan rikicewa, dama kowa ya iso ana zaman jira cike da alhini, ba karamin taba kowa mutuwar tayi ba, nauyi da kunya ya Moh shiga ciki, sai yake ganin kamar shi ya jawo, da be saka shi a cikin maganar ba, da duk hakan bata faru ba, a daren aka hada shi, aka kuma rakashi gidan sa na gaskiya. Allah sarki.

Mutuwa darasi ce babba, Rayuwa bata da tabbas, Allah ya bamu ikon amfani da lokacin mu kafin ya kure mana,Allah kasa mu cika da imani. Amin 😭

***Wani irin juyawa cikin Samha yayi lokacin ta samu labarin an kama Jabir, tsoron ta daya kar sunan ta ya shigo ciki, itace ta bawa Jay din shawarar kidnapping Iman din, kuma ita kadai ce tasan plan dinsa duk da itama bata san amfani yayi da ita ba. Wayar ta ce tayi kara da take gefen ta,dan tsorata tayi, sai kuma ta kai hannu ta dauka tana kallon number, Kamal ne yake kiranta, dagawa tayi ta saka wayar a handsfree

"Ashe dama abinda zaku aikata kenan ke da dan iskan chan shine kuka shigo dani ciki kuka samu duk wani bayani akan shi, daga karshe kuka watsar dani."

"Ai kai ba karamin kidahumi bane, idan banda gara irin ka, waye yake da amana a wannan zamanin, kowa kansa ya sani bari kaji, dan haka karka dameni ka kyale ni naji da abinda yake damuna."

"Ai wallahi kadan kika gani, asirin ki ya gama tonuwa dan na gama zayyane komai a gaban yan sanda, abubuwan da kuka sakani nayi duk na fad'a sai ki jira hukunci, wallahi ko shi MOH ya kyale ki wallahi ni ba zan kyaleli ba kinji na rantse!"

Kit ta kashe wayar ta jefar da ita,

"Wannan wacce irin masifa ce?"

Da sauri ta ja jakarta ta fito, bata tarar da maman ta a falo ba dan haka tayi saurin ficewa ta dauki mota ta bar gidan, tana tafe tana gwada kiran Laila amma bata dagawa, ta rasa abinda yake mata dadi, sai kawai ta wuce gidan ta sameta suyi magana ko zata taimaka mata, amma tana zuwa gate sai aka hanata shiga, tayi mamaki sosai hadda fitowa tayi musu bayanin kanta, amma kemaimai suka hanata bayan sun tabbatar mata da sun gane ta, umarni ne aka basu kar su sake barin ta, ta shiga masarautar.

Post a Comment for "HALIN GIRMA 36-40"