HALIN GIRMA 31-35
31
Ledar ya dora mata akan cinya. Tare da sake rufe murfin motar .
"Budemun. "Ta fada a hankali.
Hade da kaudar da fuskar ta zuwa kan murfin motar. Don sam
batason kallon fuskar Maheer. Domin tamkar sudeis yayi kaki ya tofar. Saboda
tsananin kamar da suke.
"Tsiwar ki ta bude miki" Ya fada cikin muryar umarni .
Ya kuma bata rai don karta dauka da wasa yake.
‘Kunkuni ta fara yi ahankali . Maheer ya saki siririn tsaki,
“Dauka ledan ki fita. Kuma this should be the very last time
da zaki tsallake dokata kinji na gaya miki.�
Ya karasa ransa a matukar bace . Cikin zuciyar sa na masa zugi.
“Toh ina ruwanka da rayuwata.�
“Ni kike gayawa haka?� Yana kokarin jefa mata wani kallo mai
dauke da kalamai.
“Ni dai ka budemun na fita…�
Ta karasa fada tamkar zatayi kuka.
. Hade da sake kiciniyar bude murfin motar. Hannun sa d’aya ya
dora akan nata da zummar hanata kokarin fitar da take.
Wani Irin electric shock ne ya ziyarce ilahirin jikin su da
kwakwalen su. Da sauri ya janye itama ta dauke nata hannun.
“Dauki kayan ki fita . Kuma su zaki dinga amfani dasu wajen
fita unguwa da sauran su. Kar ki kuskura ki kawo wani abun a zuciar ki. Amanar
da dan uwana ya bani nake zartarwa.� Ya karasa hade da jan kasan leben sa
ahankali .
Lock din ya cire, Ta fice da sauri har tana tuntube. Ya sauke
zuciya kawai hade da girgiza kai. Ya ja motar zuwa bangaren sa.
Ya sha mamaki kwarai matuka wajen ganin masu aikin gidah nata
rushe rushen bangaren nasa ana sake kawata shi.
Zai yi magana kenan sai ga fitowar Addayo daga ciki. Fuskar ta
kumshe da murmushi. Gayar da ita Maheer yayi ya na mata kallon karin bayani
game da gyaren bangaren nasa.
“Addayo�
“Na’am na ikko dan albarka. Kaga bangaren ka ya fara sauyawa
ko?�
Ya daga kai alamar eh hade da susar keyar sa.
“Toh me zaa jira, Aure an rigada an daura, Sai tariya kadai ta
rage. Ina ita kishiyar tawa ne.�
“Ta shiga sashen su.�
“Yauwa inason ganin ku an jima da yardar Allah.�
“Tohm Addayo! Saukar yaushe?�
“Tun dazu fa nazo. Dan na tsaya gidan Harisu ne.�
“Okay Masha Allahu.�
“Allah ya maka albarka, Allah ya jikan mahaifan ku da dan
uwanka.�
Ta karasa fada tana mai goge hawayen dake tsiyaya a idanunta
“Aaamen Addayo� Ya bata amsa yana runtse idanun sa.
“Muje bangare na nan aka mayar maka da kayan ka kafin a
kammala nan din.�
“Toh Addayo.�
Tana gaba da yar sandar da take dogarawa, Shi kuma Maheer yana
biye da ita a baya yana tunanin yadda zasu kwashe da Zaraah idan suka tare.
Dubada ganin su duka biyun ba kaunar junan su suke ba. Gwara gwara ma shi yakan
‘daga mata kafa awasu abubuwan saboda amanar ta da Sudeis ya bashi.
••�.
••�.
Tana shigewa parlorn
nasu bakinta dauke da sallama ta ajiye ledar hannunta akan kujera. Hadi da
kwaye hijabin dake jikin ta, Ta ajiye a kusa da ita.
Dadaa dake daki tafito tana jijjiga baby sudeis daya tashi a
bacci.
“Dadaa barka da yammaci.�
“Barkan mu..�
“Love of my life� Zo nan.� Ta karbu baby sudeis a hannun
ta tana kallon sa. Har cikin bargon jikinta take kaunar baby Sudeis. Idan ta
dauke shi ji take nutsuwa da kwanciyar hankali ta dabaibayeta.
Dadaa na hankalce da ita, Ta zauna akan kujera hade da janyo
ledar da Zaraah ta ajiye.
“Wannan kayan fa?�
“Yaya Maheer ne ya sayo�
“Na waye?� Dadaa ta tanbayeta tana dudduba hijaban da su
safa hadi da sabuwar wayar.
“Wai nawa ne� ta karasa cikin kasa da murya.
“Yauwa zo ki zauna anan Zaraah. Ki bani hankalin ki da
nutsuwar ki. Abunda zan gaya miki abune mai muhimmanci a rayuwar ki. Kinga
saura kwanaki kalilan ku fara jarabawar kare makaranta ko? Dan haka inaso kafin
lokacin ki samu nutsuwa ki kuma sa aranki hukuncin da aka zartar akan ki shine
mafificin alkhairi agare ki.�
“Tohm Dadaa. � Ta fada, Hadi da zama a gefen kujera . Tuni
hawaye suka shiga reto a idanun ta.
“Allah yasa ba laifi nayi ba Dadaa da aka yankemun hukunci�
“Aa wallahi ko d’aya! Hasalima nina bada hadin kai wajen
yanke hukuncin. Illa dai kiyi hak’uri na rashin neman yarjewar ki da bamu yi
ba. Kina sauraro ko?�
“Toh Dadaa. Ina ji�
“Ba wani abu bane fyace daurin auren ku da akayi da Maheer.
Maheer dai yayan Sudeis marigayi…�
Dadaa na karasa fada, Maheer ya doka sallama ya shiga parlorn.
Don sanarwa Zaraahn nema su da Addayo take�
Zaraah ta daga idanunta da suke zama tamkar garwashi saboda
tsananin yadda suka rine sukayi ja. Ta sauke akan Maheer. Hawaye d’aya na bin
d’aya suka shiga kwarara a fuskar ta.
Unedited
Sorry for the late post
Thank you â¤ï¸â¤ï¸
*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da
wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na
MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu
dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma
kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN
NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL👉ðŸ¾
Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉ðŸ¾hafsat
rano_*
*_TAKUN SAƘA👉ðŸ¾billyn
abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉ðŸ¾miss
xoxo_*
*_ÆŠABI'AR ZUCIYA👉ðŸ¾huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ÆŠAI ÆŠAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU
AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2👉ðŸ¾400
3👉ðŸ¾500
4👉ðŸ¾700
5👉ðŸ¾1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE
DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½
#team zafafa biyar
XOXOWRITES🤩
2/9/22, 20:30 - Buhainat: Halin Girma
   31
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇ðŸ¾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
******* �
Lokacin da suka isa Abuja dare yayi dan basu suka bar Yola ba
sai wajen karfe takwas na dare, sun dan samu delay ne shiyasa, direct Hotel
suka nufa ta dinga masa magiya akan ya kaita gida amma fafur yaki, yayi mata
kunnen uwar shegu har suka huta bata bar mitar ba, yi yayi kamar be ji ta ba,
shima akwai gidan Bubu da suke sauka duk sanda suka zo ko shi yazo kawai akwai
dalilin sa na zuwa nan din. Waya taga yana ta faman yi, da mutane daban daban
duk akan maganar zuwan nasu, sai da ya gama tas wajen takwas da rabi sannan ya
tashi ya nufi kofa ya bud'e, ya karbi sakon ya rufe ya dawo yana ajiye ledar a
saman makeken gadon hotel din.
"Tashi ki shirya akwai dinner da Chief of Army Staff, da
sauran manyan soldiers na k'asa, a madadin wanchan event din kawai aka hada
wannan dinner din kowa da family nasa."
" Owk." Tace tana mikawa, ya nuna maya ledar da hannu
yana shigewa toilet. Daukar ledar tayi me dauke da tambarin wani babban Mall,
ta bud'e doguwar riga Abaya ta gani me kyau, ciro ta tayi tana ware ta, sosai
tayi mata kyau ta ajiye a gefe ta ciro sauran tarkacen kayan hadda wata kar
karamar jaka da tafi kama da purse sai takalmi hills amma ba chan ba. Shiryawa
ta hau yi tana yi tana kallon toilet din har ta gama be fito, ta matsa wajen
yar trolley dinsu da ciro perfumes ta faffesa sannan ta zauna tana dauko
wayarta da take haske alamun kira ne ya shigo, Mamma ce, tasan cewa zatayi taji
su shiru,ita kanta batayi tunanin nan din zasu zarto ba dan tasan an gama
shiryar su kada ma Mamma taji labari tasan ba zata huta ba har sai sun iso.
Dagawa tayi daidai lokacin da ya fito daga shi sai gajeren wando, faffadan
kafadarsa ta kalla da take a mummurde, ta sauke kanta tana jin wani yanayi da
bata san na menene ba, a gabanta ya tsaya yana rik'e k'ugu, yana, hannun sa
daya rik'e da karamin towel, ganin ta dauke kai kamar bata ganshi ba, ya saka
shi yarfa mata ruwan da yake hannun sa a fuska, yi tayi kamar zata tashi amma
da daure ta cigaba da wayar, ta bawa Mamman hakuri yana ji ta gama ta ajiye
wayar tana tashi da sauri.
"Kinyi kyau Matar Muhammad."
"Nagode." Tace a kunyace bubbude hannayen sa yayi, ya
ja baya yana tattare fuskar sa.
"Shirya ni..."
"Na'am?"
"Eh ki shirya ni, ki shafa min mai ki saka min
kaya..."
"Kamar dan baby?"
"Toh da mene? Ai babyn naki ne ni."
Dariya ta saka tana sake gyara zaman ta
"I'm serious fa, kinga we are running late, kar suyi ta
jiranmu."
Ganin da gaske yake, ya sakata tashi ta dauko man, ta shiga
shafa masa yana lullumshe ido, da gangan ya dinga sata komawa baya yana cewa be
yi ba, nan fa. Da dai daga alamun so yake ayi tayi sai ta tattara man ta mayar,
ta dauko masa suits din da ta gani tare da abayar ta, ta mika masa ya noke yana
sake bararrajewa. Girgiza kai tayi, ta shiga saka masa, yana sake narke mata
kamar wani karamin yaro a gaban mahaifiyar sa, sai data gama tas ya rage saura
necktie sannan ya karba ya karasa sawa a gaban mirror, ya kalli kansa yana
hango ta ta cikin mirror din,da hannu yayi mata alamar tazo, ta tako ta tsaya
daga kuibin sa, ya matso da ita jikinsa yana kara kansa a jikin fuskar ta.
"Perfect!" Yace yana dariya, wayar sa dake kusa da
wajen ya dauka, yayi musu hoto me kyau a gaban mirror din, sannan ya daga kiran
da George yake masa.
"We are on our way."
Kawai yace ya katse kiran, ya rik'e hannun sa cikin nata suka
fito, duk da suka hauro reception din suke shan kallo, tana jin shi yana jan
tsaki k'asa-k'asa har suka shiga wajen da yake a cikin hotel din ne dalilln da
ya saka ma suka sauka anan din kenan saboda already an riga anyi booking dakin
tun kafin ranar ma. Duk in da suka wuce sojoji ne a tsaitsaye sun yi shirin ko
ta kwana, cikin girmamawa suke gaida su, har suka kai babbar kofar shiga wajen.
 Â
  Wata iriyar kunya ce ta dabaibaye ta lokacin da
suka shiga wajen, mutane ne masu yawa kai kace wani gagarumin biki ake, kowacce
kofar shiga wajen dankare take da jami'an tsaro, ji tayi ido yayi mata yawa,
gashi duk sun tashi da shigowar su. Mafiya yawancin su ba hausawa bane, sai yan
daidaiku da tayi hangowa daga in da take. Wajen zaman su waitress dake tsaye a
wajen ta nuna musu, basu wuce chan ba kai tsaye sai da suka je wajen manyan
kusoshin, suka kwashi gaisuwa in da taga yayi wata irin gaisuwa tasu ta daban,
sannan suka samu wajen zama suka zauna sai a lokacin ya sakar mata hannu.
"Sannu Amarya!"
Wata bahaushiya a kusa da ita tayi mata magana, amsawa tayi tana
maida mata murnushin da tayi mata, sai kuma suka gaisa da sauran matan wasu
hausawa wasu ba hausawa ba, kafin kuma a fara gabatar da abinda ya hada su.
 Captain Is'mail ne a gaba gaba akan komai shi da George,
su ne ma organizers din event din shiyasa ko zama sun kasa yi, har sai da
lokacin cin abinci yayi sannan suka zauna shima na wucin gado,ana gama ci aka
cigaba da gudanar da event din. Sun sha kyaututtuka sosai har sai da Iman ta
gaji da karba, idon ta yayi nauyi kwanciya take so kawai yayi, yana lura da
ita, yasan ba karamin aikin su bane su kai fiye da biyu a wajen babu kuma wanda
zai damu, ita kuwa akwai rashin sabo, tashi yayi yana zura hannunsa cikin
aljihun wandon sa, ya nufi wajen da Is'mail yake ya jashi gefe, yayi masa
magana kana ya dawo wajen zaman sa ya zauna. Sai da aka kara kamar mintuna
ashirin sannan isma'il din ya bada sanarwar amarya bata jin dadi zata je ta
huta, da haka suka samu suka sulale daga wajen suka nufi masaukin su. Dukkan su
a gajiye suke dan haka babu abinda suka kara bayan sauya kayan jikin su sai
bacci, cikin kankanin lokaci bacci yayi awon gaba dasu.
  Da wuri ta tashi, ta shirya ta zauna tana duba
lokaci, baccin sa yake tsakanin sa da Allah tun bayan dawowar sa sallar asubah
gashi ta matsu ta ganta a gidan, gashi babu alamun zai tashi har past 10, an
kawo musu breakfast daga reception din taci kad'an ta ajiye masa sauran ta
cigaba da zaman jiran sa. Wasa wasa lokaci ya dinga ja, babu abinda yake sai
chanja kwanciya da juyi daga nan ya koma nan cikin jin dadin baccin. Ganin da
gaske ba zai tashi ba, ya sakata zuwa daidai saitin kansa, ta dan rankwafa da
niyyar tashin sa, hannu takai kan sajen fuskar sa, ta taba kadan, juyi taga
yayi ya sake maida kansa dayan barin, sake durkusowa tayi ta bayan nasa ta kai
hannun ta jikin sa, kam taji ya riko hannun ya makale shi tsakanin hannun sa da
jikin sa, ja tayi taji ya makale shi kam, gashi sauran kad'an ta fado kansa
gaba daya, dayan hannun ta saka ta taba shi,
"Please ka tashi zamu makara."
"Uhum..." Yace cikin muryar dake cike da nauyin bacci,
ya sake kankame hannun nata a jikinsa wanda ta jawo mata fadawa kansa ta gefe
daidai saitin bayan sa.
  Sun jima a haka tana jin shi yana fitar da
numfashin bacci, kafin yayi motsi ya bud'e idon sa da suke cike da bacci sosai,
ya juyo bangarenta yana sakin hannun nata.
"Ka tashi dan Allah."
"Um um..."
"Ka manta zamu fita?"
Da kai ya amsa mata da eh, kokarin tashi tayi zaune ya daddanne
ta, ta hanyar dora kafarsa a jikin ta
"Kinsan fa jiya bamuyi wani bacci ba, please muyi bacci
idan muka tashi sai mu fita."
"Past eleven fa, please please please."
"Ohhhh! Ni dai gaskiya, gaskiya bacci nake so nayi, anjima
sai muje idan mun tashi, bari kiga."
Ya sake kadannade ta da kafafun nashi da sukayi mata nauyi ta
kasa janye su,gani tayi yana maida idon sa zai rufe tayi saurin rik'e fuskar sa
"Dan Allah!"
"Shikenan." Yace yana sauke kafarsa, ta samu ta mike
tana murmushi
"Amma da sharadi, ke zaki min wanka ki shirya ni, ki kuma
bani abinci a baki."
"Ahhhh." Ta bud'e baki cike da mamaki
"Fine, bari na koma bacci na sanda na gama mun fita."
Da sauri ta rik'e blanket din da zai sake rufa
"Zanyi."
"Good girl."
 Yace yana mata murmushin mugunta. Janye blanket din
tayi, ya zuro kafafun sa k'asa yana mika mata hannu, kama hannun tayi ya tashi,
yayi kamar zai fadi ya fado jikin ta, nauyi sosai taji, amma ta daure dan taga
take taken sa zai iya cewa ya fasa, a haka suka isa toilet din, ya zauna a
gefen bathtub din ta hada ruwan, ta dauko masa brush da toothpaste ta matsa
masa ta bashi, kin karba yayi ya bud'e mata bakin wai tayi masa, sake mika masa
tayi ya noke yana tashi alamun zai bar toilet din, da sauri ta riko shi, ya
koma ya zauna ta fara yi masa, dariya ce take kamashi amma ya kanne, yadda ta
daddage kawai zai baka dariya, hannun sa ya dora a saman nata ya karbi brush
din, ya karasa, ya bata ta cilla shi a dustbin din toilet din daga nan tayi
hanyar fita
"Kina fita zan fito nima."
Tsayawa tayi ta dawo tana tura baki, ya hau cire kayan sa a
gaban ta, tayi saurin juyar da kanta, murmushi yayi ya shiga ruwan da yayi masa
daidai da yadda yake so, sai data tabbatar ya shiga ciki sannan ta juyo tana
cigaba da dauke kanta ta dauko sponge da sabulu ta bud'e ta ajiye a dan wajen
da aka tanada, zama tayi a gefen bathtub din, taki kallon gefen sa ta
juyar da kanta gaba daya hanya, bata yi aune ba taji ya jawo ta cikin ruwan, ta
saki kara, ya hade bakin su waje daya ya hana karar tata tasiri.
  Sai da suka bata lokaci mai tsawo a ciki sannan
suka fito, ta dinga turo baki tana jin kamar tayi masa kuka, ta riga ta gama
shiryawa tsaf har kayan da ta saka dama su tayi niyyar sawa amma ya jawo sai ta
sake sabon shiri, a wajen shiryawar ma haka tayi ta fama dashi da ya janye mata
towel ta nan sai ya janye mata ta nan haka dai yayi tayi har sai data gama cika
fam, zata fashe kafin ya kyaleta su shirya a nutse.
  Kasancewar ciki da falo ne dakin, sai tayi
ficewar ta, ta barshi a ciki yana karasa shiryawa ta hada masa breakfast din ta
ajiye da yazo ci kawai zai yi su tafi. Da waya a makale a kunnen sa ya fito,
yayi zaman amsa wayar da ta fuskanci da Musaddik suke magana, sai da ya gama
wayar tsaf sannan ya jawo abinci ya soma ci a yangace kamar ba jiran sa take
ba, bata dai ce komai ba, ya gama duk bata lokacin da zai yi, sannan ya tashi
yana goge bakin sa da tissue. Tashi tayi itama dama tayi ready har da jakarta a
kusa da ita, gaba yayi ta bishi a baya, ya murda kofar sojan da yake jiran sa a
wajen ya karbi Notepad da wayoyin sa, shi kuma ya zuba hannuwan sa a aljihu
suka shiga takawa zuwa wajen da aka tanadar domin parking motoci.
  Bud'e mata kofa yayi, ta shiga ya rufe sannan
shima aka bud'e masa nasa bangaren ya shiga suka fita daga harabar hotel din!
Bashin Jiya....so sorry banajin dadi ne
_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/12/22, 11:07 - Buhainat: Halin Girma
   32
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇ðŸ¾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
*******�
Address din drivern ya dinga bi har suka isa gidan, tun kafin
motar ta gama daidatuwa a harabar gidan take kokarin fita, chapko ta yayi yana
bata fuska
"I'm jealous!"
Da mamaki dake kallon sa
"Yes I'm jealous, I want my share of love too, inaso naga
same action na murna anytime mukayi nisa da juna, inason soyayya, inaso a
gatata ni, aji dani sannan a damu dani please."
Dariya ma ya bata, ya saki hannun ta yana sake bata fuska shi a
lallai yayi fushi, girgiza kanta tayi cikin muryar lallashi tace
"I'm so sorry toh, kawai I'm eager ne, ban wani zauna dasu
sosai ba, shiyasa kawai."
"Shikenan reason din?"
"Shikenan, ko baka so naga Mama ta? Kullum fa kai kana tare
da Ammi fa, nifa?"
"Ba haka bane, banda Mummy ai nake nufi, Mamma, Amaani,
Amaan and rest, su nake kishi dasu."
Dariya ta sake yi, ta rik'e kofar ta bud'e, ya zuba mata ido kamar
bashi da niyyar fitowa, sai da tayi masa alamar da hannu sannan ya bud'e ya
fito ta dayan side din, yana karewa gidan kallon.
  Kofar shiga part din suka nufa, yana biye da ita
a baya hannun sa sakaye a cikin aljihun sa, daf da zasu kai kofar ta bud'e,
Amaani ce a gaba da shegen gudu, tayi kanta tana ihun wallahi itace, kamar zata
kada ita, sai da k'yar ya nutsu tana numfarfashi, hango shi da tayi a baya sai
kawai tayi wajen sa , ta rik'e masa hannu ta fara zuba masa surutu kamar tayi
shekara da sanin sa. Cike da sha'awa yake duban ta, ta rik'e shi gagam har ciki
tana bashi labarin da be gane kan sa ba.
 Mamma ce ta fito daga wani corridor, tana sanye da
lullubi akanta, fuskarta cike da farin cikin ganin su,
"Sannun ku da zuwa."
Tace sanda ta karaso falon, idon ta akan Iman dake zaune da
Amaan a kusa da ita. Russunawa yayi cikin ladabi ya gaida Mamma din, a daidai
lokacin Mummy ta fito itama, ya gaishe ta a kunyace dan kallo daya yayi mata
yaga tsantsar kama da Fatin sa, amsawa tayi ita din ma a yanayin kunya irin
tamu wadda aka gada tun iyaye da kakanni. Iman ce ta gaishe ta, ta amsa
daga tsaitsaye ta juya ciki, murmushi kawai Mamma tayi dan tasan yadda ta matsu
da zuwan nasu, amma ba zata taba nunawa ba, yadda tayi zaka dauka ma bata damu
ba sam,nan kuwa tsantsar kara ce irin tata da har take nema tayi yawa.
  Abinci aka shiga jere musu, yayi mata alama da
ido akan tafiya zai, ya dauki bottle water guda daya ya mike yayi musu sallama
akan zai dawo, mamma ce ta hau korafin me zai sa ba zai tsaya yaci abinci ba,
hakuri ya bata akan zai dawo akwai wanda yake jiran sa ne. Shikenan tace ya
fice ta harari Iman
"Haka ake wa miji? Tashi mana kije kiji."
Tashi tayi tana dariya, ta bi bayan sa ta same shi har ya kai
wajen mota, tsayawa yayi ganin ta fito ya choge jikin motar sai data karaso
sannan ya shiga, ya sauke glass din motar yana kallon ta
"Kwana zanyi ko?"
"Inji waye? Da yamma zan dawo zuwa magriba."
"Dan Allah..." Girgza mata kai yayi tun kafin ta
karasa.
"Zaki dawo next time, sai na dawo bye."
Ya daga glass din ta dan ja baya tana kallon motar har ta fice
daga gidan, kamar zatayi kuka haka taji, taja kafarta a hankali ta koma ciki ta
samu Mamma ta zuba mata abincin mummy kuma ta dawo falon ta zauna tana wa
Amaani fad'a akan rawar kanta.
  Taji dadin zuwan ta gidan sosai, kamar tayi ta
zama haka taji, amma tasan tun da yace zai dawo toh zai dawo din, amma taso ya
barta ko zuwa da safe ne sai yazo su tafi ko ya turo a dauke ta.
 Ta idar da sallar magriba kenan a dakin Mummy, Amaani ta
shigo tace ya dawo, har ga Allah taji babu dadi, ta tashi ta nannade sallayar
ta ajiye a gefe ta zauna a saman sofa tana ciro wayarta. Tana zaune har wajen
minti talatin babu wanda yazo kiranta, har ta kishingida sai ga Mamma ta shigo,
tace ta tashi su tafi yama fita,
"Na zata zai barni na kwana."
"Kul... Dududu yaushe akayi auren? Kar ma ki soma yi masa
maganar kina ji na? Watarana da kanki zaki zo ma"
" Wuce muje kar suyi ta jira." Tace tana sakata a gaba
suka fito falon, uban kaya ne jibge a gefen falon dangin su shinkafa kayan
abinci dai masu yawa, Mummy na zaune tana juya kudi a hannun ta
" Kinga wahalar da yayi ko? Kiyi masa godiya nace ba za'a
karba ba amma ya dage dole." Tayi maganar tana ajiye kudin a saman center
table, bin kudin Iman tayi da ido wanda a kalla zasuyi hundred thousand, sai
kayan abincin da yake a dankare awajen, jinjina kanta tayi cike da mamakin sa,
ko alama be nuna mata ba balle ta gane shirin sa, dadi ne ya kamata ta fito
bayan sun yi sallama da Mummy tana zuba masa ido ta cikin hasken compound din
gidan, duk da motar tint ce, amma tana iya hango inuwar sa, cike da karsashi ta
karasa wajen motar, dai-dai lokacin da kofar ta bud'e, ta shiga da sallama tana
dagawa su Iman hannu.
  Suna fita daga gidan ya matso kusa da ita cikin
lallashi yace
"I'm sorry na hanaki kwana, kinga gobe da wuri zamu tafi
amma next time da kaina zan kawo ki har sai kin gaji."
"Laa ba komai fa, dama wasa nake yi, su Mamma ma ba zasu
barni ba ai, wai dududu yaushe akayi auren?"
"Haka suka ce ko?"
"Eh..."
"Yawwa kin gani."
"Babu komai fa, ni nama manta ma ma na tambaya, I'm
sorry."
Ta kama kunnenta, zare hannun nata yayi yana jawo ta jikinsa.
" Thanks dear."
****
Washegari suka dauki hanyar Kano, tun kafin su isa an gama gyara
musu gidan su, dama dai ba wani baci yayi ba saboda akwai masu aiki da kula da
gidan banda sojojin da suke waje suna gadi, suna isa ya fice tare da Musaddik,
anan ta tarar da uban kayan lefen ta, tayi zaman kallon su cike da mamaki, idan
kaya na yawa toh ita dai sun mata mugun yawa, ya zatayi dasu? Shine kuma har da
siyan mata wasu kayan saboda dai ba'a san wahalar kudin ba. Gajiya tayi da
kalla ta saka masu aikin suka kwashe su, suka maida su wani daki guda kafin ta
kira Mamma taji abinda ya kamata tayi dasu da mutanen da ya kamata a bawa.
  Slippers ta zura ta zazzagaya gidan nata, wanda
yasha kaya na alfarma, har da wani babban garden a baya da pool daga chan gefe
shima, gidan yayi kyau amma yayi girma ace mutum daya kwal dan ma ma'aikata
masu yawa wanda yawanci daga masarauta suke sai wanda aka turo su daga adamawa.
Daki ta koma ta haye gado tayi kwanciyar ta dan bata jin yunwa tasha cornflakes
suna zuwa sai kawai ta kwanta da niyyar ta tashi wajen azahar ta dafa masa simple
dish dan wata gajiya take ji na nukurkusar ta.
  Ta jima batayi irin baccin da tayi ba, ga sanyin
AC da kamshin fresheners masu dadin kamshi da ya cika dakin, hakan ya kara
taimaka mata jin dadin baccin sosai har sai da taji ana mata knocking sannan ta
tashi bakin ta dauke da addu'a ta yane kanta ta fito ta bud'e kofar, daya daga
cikin masu aikin ce Atine, ta russuna ta gaishe ta sannan tace tayi baki ne a
falo. Ok tace ta rufe kofar ta koma ta gyara fuskar ta, ta fesa turare ta dauko
wayarta ta fito. Yan mata ne su biyu kyawawa dasu masha ALLAH, suna zaune suna
kallon TV ta fito,
"Sannun ku da zuwa."
"Yawwa." Suka amsa a sake, suka gaishe ta sannan suka
gabatar mata da kansu
"Fulani ce ta aiko mu, kayan gara ne dangin su alkaki dasu
bakilawa da dublan, sai gireba da sauran su, tace gashi nan zaku iya tayin baki
tunda kun dawo."
"Kai mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi."
Ta tashi ta bubbude, ta dawo ta zauna tana murmushi ta sake
godiya, aikin gidan mace ne kayan gara amma basu bari anyi mata ko daya ba,
dama tasan dai ko za'a yi sai dai a gayawa su Mamma suyi mata sai gashi sunce
ba sai anyi ba,itama yar su ce kamar Muhammad din.
  Hira sukayi sosai tun tana nokewa har ta saki
jiki dasu dan suna da hira ga faram faran kamar sun saba. Tare suka ci abincin
da suka zo dashi alkubus da miyar taushe, suka bita kitchen da zata yi ma Moh
dan abincin sa, suka tayata sai yamma suka tafi, bayan sun mata alkawarin zasu
dawo basa so ya dawo ya same su dan tsaf zai kore su, jin su kawai tayi dan
batayi tunanin zai aikata ba, bata san yadda yake tsare musu gida da daure
fuska bane shiyasa har yake mamaki dan sun ce ba zasu zauna ya same su ba.
  Suna fita kuwa sai gashi ya shigo, yaga fitar
motar su amma basu tsaya ba suka kara mai. Bud'e hannun sa yayi ya tsaya daga
jikin kofa, ta tafi a sanyaye ta fad'a jikin sa, ya rungume ta yana shafa
kanta.
"Sannu da zuwa yallabai."
Ta karbi rigar hannun sa suka rankaya cikin falon, sai da ya
zauna sannan ya amsa mata sannun ya dora da
"Baki kikayi?"
"Su umaima ne, daga chan gida aiko su."
"Yan rawar kai, tun yaushe suka zo?"
" Wajen twelve din rana."
" Ah kice kin samu yan hira ko nace yan surutu dan bakin su
sam baya shiru."
" Naji dadin zuwan su kuwa, sun tayani hira ai."
" Sun kyauta da suka tafi kafin na dawo, dan tsaf zan saka
yarinya frog jump ba abinda ya damen."
Ya fad'a yana kai cup din ruwan da ta zuba masa bakin sa,
" Da gaske wai?"
" Da gaske mana, suma sun sani ai, kila ma sun fada miki
ko?."
" A ah." Tace tana dariya
" Ya yau din? Ya gidan naki?"
" Alhamdulillah, komai yayi Masha ALLAH, Allah ya kara
arziki, thanks for everything,
" Amin Amin, I'm glad you like it."
Yace cikin jin dadin addu'ar ta
" I love it!"
" Masha ALLAH."
***Tun ranar farko da Bashir ya samu damar shigowa dakin har
yayi abinda yayi, tun daga lokacin duk dare sai ya lallabo, ranar farkon tana
jin su suka haura sama da uwargidan tasa suka fado, sai da k'yar suka daidaita
dan shima jan wuya yayi mata ganin idan ta biye masa zai iya cewa su rabu yasa
ta kyale shi, taga kansa rawa yake ya samu yarinya karama shiyasa ta kwantar da
kanta ta cigaba da bin sa tana so taga iyakar limit din iskancin nasa, tasan
sarai yana zuwa dakin da dare amma ta share bata taba nuna masa ba, wani zubin
ma akan kunnenta komai yake faruwa amma ta daure dan plan dinta akansa ba na
yanzu bane, shigo shigo babu zurfi tayi masa sai ya gama sakankancewa zatayi
maganin sa.
  Ranar ma kamar yadda ya saba kawo mata waya suyi
magana da Mama haka ya kawo mata, ta karba tana daga kwance da babu wani aiki
da takeyi yanzu matar gidan ta rage takura mata, dattijuwar me aikinta da ta
tafi gida ta dawo shiyasa aikin ya rage mata sai dai taci ta kwanta ga uban
kasalar da take fama dashi ga shegen nacin Bashir da yake hanata sakat, tana
shan wuya sosai a hannun sa dan baya daga mata kafa ko kad'an, tun tana masa
rashin kunya har tazo ta kyale shi yayi uwar da zai yi, ranar da zata samu
hanya kawai take nema wallahi ta tafi ba zata dawo ba ko me za'a yi mata kuwa.
 Wayar ya mika mata bayan ya gama amsawa da toh, suka
gaisa da Mama ta take fad'a mata haihuwar Aunty Bilki, tayi murna sosai ana
take jin gobe suna kuma a gidan su za'a yi sunan saboda akwai fili sosai
"Ki lallaba shi ya kawo ki na dai gaya masa."
"Toh shikenan, zan kira." Ta katse wayar ta mika masa
"Dan Allah ka barni naje suna gidan mu gobe."
"Ki shirya da safe zan mika ki sai na wuce garari na, idan
na gama sai nazo mu dawo."
Yace ya sa kai ya fice da bishi da kallon mamaki, bata taba
tunanin zai yarda haka kai tsaye ba, murna ta hau yi ta dinga zagaye dakin tana
jin kamar wahalar ta, ta kare kenan dan ko giyar wake take sha idan taje gida
ba zata dawo ba sai dai Abba ya kashe ta.
 Murmushin mugunta yayi yana barin dakin, shi kadai yasan
tsiyar da ya shirya ya kuma tabbatar da ko taje gidan toh sai ta dawo da kanta
ko Maman ta sakota gaba ta dawo da ita.
***Waya suka gama yi da Ya Maryam ta cigaba da shiryawa a
tsanake saboda safiya ce, sannan yace ta jira shi ya fita toh dole sai ya dawo
zata tafi, tana so taga Abban ta da Marwan da Gaji da sauran yan gidan, shiyasa
ta tashi tun wuri ta hau shiryawa yadda zata samu zuwa da wuri ta dade kuma.
  Tana zaune taji shigowar motocin sa, ta yaye
curtains din dakin ta ga wasu motoci guda biyu da bata san su a gidan ba, sakin
labulen tayi, ta sake fesa turare ta fito suka hadu a falo.
  Tafi ya shiga yi mata dan ba karamin kyau tayi
ba, lace ta saka me orange da black yayi mata kyau ya dace da kalar ta, zaunar
da ita yayi ya dauke ta hotuna masu kyau sannan yace idan ta gama ta ga driver
nan idan yaso zai zo da daddare su dawo tare. Jakar ta, ta dauko ya rakota har
wajen motar ya bud'e mata ta shiga, sannan suka fita daga gidan yana tsaye yana
kallon su. Tasa motar ya fad'a shima ya bar gidan dan yana da important abun da
zai yi. A daidai lokacin Zeenat suka fito da Bashir, ya kunna machine din da ya
aro a wajen abokin sa dan Hajiya ta fita da motar ta, kamar tace ba zata hau
ba, sai kuma ta hau dan bata da ko biyar din da zata dauki adaidata sahu,
tunanin idan taje gida ta karbo masa sam be zo kanta ba.
Â
_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/12/22, 11:31 - Buhainat: Halin Girma
   33
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇ðŸ¾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
*******�
A kusan jere suke tafiya da motar Abba da Habib ke ciki shida
mama, kasancewar tint ce ya saka basu gane Iman din bace a ciki, suna shigowa
layin su Habib ya sake kallon motar yace
"Ina tunanin fa Iman ce a motar nan."
"Wacce motar? " Mama tace tana waigawa, gabanta ne ya
fadi ganin dalleliyar mota a bayan su,
" Ta ya akayi ka sani?"
" Number na duba. "
Ya amsa mata yana tsayawa a daidai kofar gidan, daidai lokacin
motar Iman din itama ta tsaya, yayi daidai da isowar Zeenat a saman machine din
Bashir. Mutuwar zaune Mama tayi ta kasa bud'e murfin motar balle ta fito, idon
ta yana kan motar da ta gama gane wacece a ciki, ta saitin ta Bashir ya zagayo
bayan ya faka machine din, ya leko yana cewa
" Sannu da zuwa Mama. "
Wani abu taji, ta kalle shi a kaikace kamar ta falla masa mari,
tayi dauriya ta danne zuciyar ta ta amsa tana jan kofar ganin yana kokarin
bud'e mata, matsa wa yayi ta fito idon ta akan Zeenat da tayi wani irin haske,
hasken da tana kallon ta, ta gane na menene, kamar wadda aka sage wa guiwa haka
ya shiga jan kafarta zuwa cikin gidan, suka rufa mata baya a jere Iman din na
magana da Zeenat da take ta kokarin maida hawayen da take jin zasu zubo mata
wanda bata san dalilin su ba
"Ashe zaki zo?" Tace a sanyaye
"Wallahi, ya gida? Ko waya bamuyi ba."
"Wayata ta lalace ne. "
" Ayya." Kawai tace suka karasa ciki, nan da nan
mutanen dake harabar gidan sukayi kan Iman, kowa so yake ya ganta, duk sun rude
babu wanda yabi ta kan Zeenat, ganin haka yasa ta sulale ta gudu bangaren su,
ta samu Mama a zaune tana kuka wiwi, kukan bakin ciki, kukan dana sani da aka
ce keya ce wadda bata da amfani, ta tuna watarana da aka zo akayi sallama da
Iman, ranar ce ta farko da aka fara zuwa kuma wajen Iman din, tun basu kai
yanzu ba, da kanta ta saka Hijab ta koreshi irin korar wulakanci, ba tare da
kowa ya sani ba sai Habib, wanda bayan ta kore shi ne Habib yake gaya mata waye
shi, da kuma gidan da ya fito,. Tun daga lokacin ta dauki alwashin dakushe Iman
din, ta kara maida ita mara yanci cikin rashin sanin cewa gata tayi mata, babu
in da zata shiga rayuwa ta bata wahala musaman irin abubuwan da suka shafi kula
da gida.
  Taba ta Zeenat tayi ganin sai sallama take amma
bata amsa ba, firgigit tayi tana dawowa tunanin ta, suka rungume juna Zeenat
din ta fashe da kuka, bata hanata ba, sai da tayi me isar ta dan tasan kukan
zai rage mata abinda take ji, gwara ace kishiyar uwa ke gallaza maka akan ace
kishiyar ka ce zata hanaka sakat da sukuni, abinda tayi ne ya juyo kanta amma
ta siga ta daban, sigar da bata taba tunani ko tsammani ba.
 Yan uwan Abba ne suka biyo Zeenat din har cikin gidan
nasu, da mitar me ya faru zata shigo ta wuce su babu ko gaisuwa, Mama na jinsu
bata ce komai ba, dan tasan da biyu suka zo maganar, tana jin Zeenat din tace
suyi hakuri, wanda ya saka su jin nauyi da kunya kuma, suka tafi cike da borin
kunya.
 Suna fita Iman ta shigo, ta russuna har k'asa ta gaida
Mama kamar yadda ta saba, ko ba komai ita a uwa take kallon ta, dan itace tayi
mata komai na mahaifiya idan aka cire shekarun haihiwa zuwa yaye, ita ta sani,
ko ma menene dai tayi mata wani abu.
 A chunkushe ta amsa, har yanzu akwai haushin Iman din a
zuciyar ta, wanda bata jin zata daina sai ko ranar da ta bar duniya, har gobe
tana kallon Iman din ta tuna cin amanar da akayi mata, wanda take ganin da
gaske Itace baa kyautawa ba.
  Ta dan zauna a bangaren nasu, babu me magana a
cikin su, sai jefi jefi da suke magana tsakanin ta da Zeenat wadda take cike da
mamakin sauyawarta, tayi sanyi sosai kamar ba ita ba, ta kuma hangi wani abu a
idon ta, da take da yakinin damuwa ce. Tashi Mama tayi ta barsu a falon tayi
shigewarta daki, domin ta samu damar yin tunanin abinda ya kamata tayi akan
auran Zeenat din.
  Bin ta Zeenat tayi, ganin haka ya saka Iman
ficewa ta koma bangaren Gaji in da anan me jegon take, ta shiga yan uwa aka
cigaba da kuranta ta da yaba ta, kowa yana so ya samu ya kafa kansa ganin cewa
yanzu ta wuce duk wani matsayi ta kai in da basu taba tunani ba, shiyasa kowa
yake kokarin chusa kansa dan idan wata dama ta taso ko da ta aikin Hajji ne,
toh Iman din zata tuna da mutum.
  Wajen azahar sai ga Yaya Maryam tazo, sai da ta
biya ta asibitin da take ANC sannan ta tawo shine dalilin rashin zuwan nata da
wuri. Jan Iman tayi suka koma gidan su, suka zauna su isu matasa aka hau hirar
aure da yadda rayuwar auren take ma baki daya, sosai Iman take daukar haske,
tana karuwa da wasu abubuwan tunda sun fita jimawa, bata saka musu baki ba, a
tunanin Yaya Maryam ma bata jin su, nan kuwa ta haddace komai akanta.
 Â
***Tare suka shigo da Musaddik, wanda kallo daya zaka yi musu
kasan a gajiye suke sosai, babu wanda yayi magana sai da suka huta sannan ne
Musaddik ya mika masa wayar sa da ake ta faman kira tun suna hanya, karba yayi
ya daga yana kishingid'a a saman kujerar
"Ya akayi? Kun duba yadda abun ya samu kansa a cikin part
din?"
"Mun duba dukka CCTV footage na gaba daya area din, bamu ga
kowa ba a kusa da wajen ma, har zuwa kofar shiga shashen, falon kuma babu CCTV
kasan, time da za'a saka kace baka so. "
" Na sani, shikenan ba damuwa. "
Yace yana zare wayar daga kunnen sa, ya ajiye yana murmushi
wanda ya saka Musaddik kallon shi
" Akwai wanda yake so yayi wasa da hankali na, ko ma waye
yasan babu cameras a ciki, target din su iya na wajen ne kawai. "
" Me kake tunani? "
" I can't say exactly, amma dai akwai wani abun daban ba
sarauta ba, ko ma waye yana da matsala da aure na, ba sarauta ba. "
" Laila fa? "
" Ba ita bace. "
" Toh me zasuyi benefiting anan, ban gane komai ba. "
" Guy, baka san wanne irin mutane ne suke zagaye da gidan
nan ba, da kuma kudurin kowa, zaka sha mamaki amma. "
"Ka sansu? "
" Almost.. "
" Then why are you allowing them to walk over you? Bayan
kana da duk damar da zaka yi musu abinda zakayi to get rid of them. "
" Ba zai yiwu ba, this is not a military war, wannan fad'an
ba ma makami bane, ko na gwajin kwanji ba, sai ka zama very very careful da duk
moves dinka, akwai bakin ciki a gidan sarauta, akwai kyashi, da hassada. Masu
son kujerar ba mutane bane yan kad'an, suna da yawa kuma kowa zai iya komai
domin ganin ya samu abinda yake so"
Gid'a kai Musaddik yayi yace
" It's harder than i thought. "
Murmushi Moh yayi, ya hade hannuwan sa waje daya, suka fitar da
sauti me dan kara, ya mike yana zuba hannayen sa cikin aljihun sa
"Muje naga Takawa."
"Owk." Yace ya mike suka fita
***Be samu ganin Takawar ba kamar yadda ya saka rai, ya zauna
zaman jiran sa dan yana so ya nema masa alfarma akan tafiyar da za'a yi akan
wani aiki gashi har da sunan sa, baya son yayi nisa da gida dan a kalla zasuyi
wata guda cif, yasan idan ya samu Takawar ya kira waya za'a iya cire sunan sa,
duk da tun daga last yace ya daina nema masa alfarma, tun da shi yaji ya gani
dole ne yabi dokar aiki, sai gashi ya dawo yanzu be kuma san yadda zata kaya
musu ba, shi kansa kunyar neman alfarmar yake amma kuma baya son tafiya ya bar
Iman ita kadai bata gama sanin komai ba.
  Har sukayi la'asar suka dawo Takawan be dawo ba,
cigaba da zaman jiran sa sukayi Muhammad har da dan baccin sa,ya bar Musaddik
yana kallo dan dama shi mayen kallo ne. Sai goshin Magriba sannan suka ji
dawowar sa, alwala suka daura suka fita zuwa masallaci aka yi sallah,.
  Yadda ya dawo da irin wannan lokacin dama babu
wani zama da zai kara direct ya wuce gida dan yana bukatar ya huta sosai.
  Shawara sukayi akan kawai su dawo gobe da wuri
kafin ya fito zaman fada. Da wannan shawarar sukayi amfani suka tafi, suka wuce
kai tsaye gidan su Iman daukota. A ransa ya kuduri zai kaita ya nuna mata dakin
da ya zauna har ya kwana aciki saboda ita!
***Akwai Yayar su Abba da take turai tare da iyalin ta, sukan
dade basu zo ba yawanci sai dai waya suke yi, akwai dan ta Mahfuz zai yi sa'an
su Habib ko ya dan d'ara su da kadan, duk ciki shine me zumunci me son dangin
sa, tun da ya girma idan ya samu lokaci ya kan zo yayi wata biyu ko daya ya
koma, karshen zuwan da yayi ya jima sosai be dawo ba, sai wannan lokacin da
yazo. Yaso ya samu bikin da aka ce masa za'a yi, duk da ba wani sanin su yayi
ba saboda yawansu sai kuma aka samu yar matsala da ta dakatar da zuwan sai
yanzu. Yana da wasa sosai da sakin fuska , abu daya yake hada shi da kowa shine
yadda dabi'un sa da al'adun sa suka sha banban da na Malam bahaushe, gashi dama
bahaushe ko yaya ka kuskure wajen al'ada wadda ba irin tasa ba be kuma karbe ta
ba,toh fa zaka samu matsala dashi. Hakan ce ta kasance ga Mahfuz, yadda yake
mu'amular sa tasha banban da tamu, dole ne za'a ga banbanci wanda shi tsakann
sa har ga Allah ba da wani abu yake ba
 Tun da ya shigo falon ya dora idon sa akan Iman ya kasa
daukewa, be kawo matar aure bace sam, gefen ta yaje ya zauna daf har sai data
dan matsa, suka gaishe shi dukka ya amsa idon sa na kanta.
"You are beautiful." Yace mata kan sa tsaye, gabanta
ne ya fadi, ta kalli Yaya Maryam ta kalli sauran yan dakin, sai kawai ta mike
tana tattare jakar ta.
"Bari naje wajen Gaji kafin ya zo."
Bata jira amsar su ba tayi gaba, ya tashi da sauri ya bi bayanta
ya jera da ita yana yi mata surutu, da hausar sa da ba wani ganewa take ba,
tana shiga part din Gajin text din Moh ya shigo wayarta,
"Muna waje." Yace a text din kawai, sallama tayi wa
Gaji kawai dan kuma babu zama, ta juya zuwa nasu gidan ta tarar da Zeenat a
zaune tana cin tuwo, nan ma tayi wa Maman sallama tace ta gaida gida. Fitowa
tayi rik'e da hannun Marwan, ta koma wajen su Yaya Maryam tayi musu sallama,
suka firfita zasu rakata, anan suke ganin ana sauke kayan abinci a irin motar
da Iman din ta gani dazu a gida, ranta ne ya bata lallai aikin sa ne, tana jin
su Maryam suna maganar sai dai idan shine ya aiko dan cikin surukan gidan babu
wanda zai aiko da kayan abinci haka masu yawa. Har gate suka rakata sannan suka
juyo, Mahfuz na ganin zata bita ya tashi ya sake bin ta suka rankaya
zuwa waje, kamar tace masa ya koma amma sai ta kasa tana jin nauyin sa. Tun da
suka fito idon Moh akan su, ya gama tabbatar da ba Habib bane, ba kuma Khalil
bane dan ba zai kara gangancin da yayi a baya ba. Ransa ne ya baci,
ganin yadda suke jerawa yana mata magana da yanayin yadda yake maganar. K'asa
hakuri yayi, ya balle murfin motar ya fito daidai lokacin da Mahfuz yake
kokarin kai hannu ya bud'e mata kofa, gashi yayi kusa da ita sosai.
"Dalla malam baka da hankali ne?" Ya daka masa tsawar
da ta saka Iman sakin yar jakar hannun ta, tsayawa Mahfuz yayi yana kallon sa
yace
"Pardon?"
Wani banzan kallo yayi masa, ya zagayo ya kama hannun ta, ya
jata zuwa dayan side din motar ya turata ciki, be lura ba sai data bigi ya rufe
kofar da karfin sannan ya dawo wajen Mahfuz din dake tsaye rik'e da jakar Iman
din da ta fadi cikin mamakin abinda ya harzuka gayen.
"Wannan shine last warning dinka akan matata, ko waye kai
komai alakar ka da ita, kar na sake ganin ka haka kusa da ita, idan ba haka ba
wallahi sai na balla kafarka, nonsense."
Be jira abinda zai ce ba, ya bud'e motar a fusace ya shiga ya
rufo, Musaddik dake gaba ya juyo zai magana yaga yanayin sa, sai kawai yayi
shiru, yace ma driver ya ja, jan motar yayi suka bar wajen.
_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/14/22, 19:05 - Buhainat: Halin Girma
34
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇ðŸ¾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
*******�
Tun da suka dauki hanya babu wani wanda yayi magana a cikin su,
ransa a bace yake matuka. Manne da jikin kofar take, cike da mamakin dalilin
fushin sa haka, a kalla ya tsaya ya fuskanci abinda yake faruwa kafin ya yanke
hukunci haka, abun ma dariya ya so bata, yadda ya jata zuwa cikin motar, lallai
da gaske sojoji akwai su da temper, idan ba haka ba, menene abun tashin hankali
anan? Tana jin sanda suka sauke Musaddik yana masa sai da safe ya amsa da
k'yar, suka ja motar sai gida.
  Motar na gama tsayawa ya balle murfin motar ya
fice ko bi ta kanta be ba, jiki a sanyaye ta fito itama, ta bi bayan sa cike da
mamakin sa. Bata same shi a falo ba, kai tsaye ta wuce bedroom dan rage kayan
jikin ta da suka dame ta, baya dakin kamar yadda tayi tunani, kuma be shigo ba
har ta gama sauya kayan ta fito falon ta zauna tana bud'e wayarta. Ta jima a
zaune a wajen, sannan ya fito sanye da kajaren wando babu riga a jikin sa,
wuceta yayi ya dauki abu a cikin wata drawer a falon ya koma dayan dakin da ya
fito. Ya sake dadewa sosai dan har tayi tunanin ta bishi ta gani sai gashi ya
fito ya doro gajeriyar jallabiya a jikin sa, yana kamshin turaren sa na hugo
boss.
"Abincin nan za'a kawo maka ko achan zaka ci?" Ta
tambaye shi bayan ya zauna
"No ba zan ci ba."
Sak'alo tayi tana duban sa, yaki ko kallon sashen da take sai ma
fito da waya da yayi yana daddanawa. Tashi tayi ta bar falon ta koma daki cikin
rashin jin dadin abinda yayi mata, wannan ai wulakanci ne, me tayi haka? Ji
tayi hawaye na kokarin zubo mata, kokarin maida shi tayi tana daga
fuskar ta sama.
  Tana tashi kiran Takawa na shigowa wayar sa, ya
daga yana mikewa tsaye
"Barka da wannan lokacin Takawa."
"Barkan ka dai, kuna lafiya ya iyali?"
"Alhamdulillah wallahi."
"Toh madallah, alfarma akayi min akan tafiyar da zakuyi,
dalilin da ya saka sunanka ya fito saboda ana bukatar jajirtattun mutane kamar
kai, kuma kai zaka jagoranci tafiyar, sannan akwai alkwarin karin girma
akan ka bayan an dawo, dan haka nake so ka ajiye komai ka tafi, Allah ya baku
sa'a ku dawo lafiya."
" Amma..." Yace a firgice
"A'ah fa! Bana so naji komai Mohd, na jima ina neman
alfarma irin wannan akan ka, komai idan har baka so toh fa an barshi, waya
kawai zan, wannan kuwa takanas ya kira ni mukayi magana na kuma bashi tabbacin
zaka je, toh kayi hakuri kaje."
" Shikenan Nagode Allah ya kara girma, zanyi duk yadda
akace."
" Yawwa, Allah ya taimaka ya baku sa'a, Allah yayi
albarka."
" Amin."
Ya amsa a dunkule zuciyar sa na wani irin suya, wato sai DG ya
riga shi samun Takawa akan maganar ya kuma nemi alfarma yasan Takawa dole ya
amsa masa, me ma ya saka shi wai kin tsayawa yaga Takawan a dazu ya tafi? Ai da
duk haka bata faru ba. Wani abu me ya tokare masa makoshi, ya jefar da wayar a
saman kujerar yana barin falon da sauri zuwa daki.
 Tana zaune a gefen gadon tana tunani ya shigo, ya wuce
wajen da jakar sa take ajiye ya ciro flash din, ya dauki system ya sake barin
dakin. Hada su yayi da dayan na wajen Iman, ya kunna kowanne yayi copying dinsa
akan system din, sannan ya saka su a envelope ya mayar jakar. Tafiyar da zai yi
Itace zata basu kafa wanda har za'a iya samun matsala be samu dukka bayanan da
yake son samu ba, yanzu dai zai damka wa Musaddik flash din guda biyu, ya ajiye
a wajen sa dan sune manyan evidence dinsa idan ya tashi yin abinda ya jima yana
shiryawa.
 Wayar sa da ya jefar dazu ya dauko ya kira Musaddik din,
sukayi magana sannan ya ajiye yana dafe kansa. Zai iya jure komai amma banda
abu biyu, iyayen sa da matarsa, idan har aka samu matsala zai dauki matakin da
ba zai ma kowa dadi ba.
  Tun tana jiran shigowar sa har ta gaji ta hakura,
ta kwanta tana matsar kwalla, bata ga abin fushi ba sam, bata kuma san ta yadda
zata fara bashi hakuri ba, ba wai dan tana ganin ai bata yi laifi ba me yasa
zata bashi hakuri, sai dai ta rasa fuskar da zata iya bashi hakurin.
  Chan cikin dare ta farka bayan bacci ya dauke ta
da k'yar, ta ganshi a gefen gadon yana bacci hankalin sa kwance, ya riga ya
saba mata tun farko tare suke kwanciya, cikin bargo daya amma sai gashi yau,
akan abinda bata da laifi akai,yana fushi da ita. Baccin ne ya kaurace mata
gaba daya, ta dinga tunanin wai dama haka auren yake kenan? Sai wajen asuba
sannan ta samu baccin ya kwanshe ta bayan ta sha kuka ta gode Allah.
  A kanta ya tsaya yana kare mata kallo, yadda ta
kwanta sai ta bashi tausayi sosai, be san me ya hau kansa jiya ba, amma ba wai
haushin ta yake ji ba, bayan ma wayar da yayi da Takawa zai iya cewa ya manta
abinda ya faru, tunanin abinda zai faru idan baya nan shi yafi daga masa hankali
har ya hanashi zuwa ya kwanta sai dare sosai.
 Hannu ya kai ya shafi gefen fuskar ta, ta bud'e idon
tana salati a hankali, ganin shi da tayi a tsaye akanta yana mata murmushi ya
sakata tashi da dan sauri tana gyara jikin ta
"Good morning Baby,."
Yace kamar babu wani abu da ya faru, bata amsa ba, sai zuro
kafarta da tayi ta sakko, ta wuce shi zuwa toilet dan ta makara daga ganin
yadda haske ya cika dakin. Hijab ya ciro mata ya shinfid'a mata abun sallah, ya
zauna yana jiran fitowar ta. Ko da ta fito bata kalle shi ba, ta tada sallar
ta, da ta idar ma sai kawai ta kwanta a wajen tana janyo hijab din ta rufe
fuskar ta dashi. Tasowa yayi tsam yayi zaman dirshan a gaban ta, ya janye hijab
din yana dagota, hawayen da ya gani a saman fuskar ta yayi mugun bashi mamaki
"Innalillah, kuka? Don't tell me kuka kikayi tayi the whole
night..."
"Ya Salam...Look at your eyes, I'm very sorry, ki yafe min
dan Allah."
Bayan hannun ta tasa tana share hawayen da suka ki tsayawa, ita
kanta bata san na menene ba, kawai tasan she's weak, tana jin wani irin
weakness a tattare da ita, she can't take fushin sa a gareta, he's so nice to
her ko yaya yayi fushi zai bata wahala sosai. Rarrashin ta ya dinga yi da
kalamai masu taushi, har sai da ya tabbatar da kukan ya tsaya, sannan ya
taimaka mata suka bar kasan suka koma saman gado.
"Dole zanyi fushi, shi zaman aure dama zo mu zauna ne zo mu
saba, I can equally make mistake, ina da kishi sosai Fatima, ba kuma wai dan
naji a raina wai kin kula shi bane, son da nake miki ya saka, please ki kula
sosai. "
" I'm so too. " Tace bayan ta amsa masa da toh.
" Baki komai ba ai, nasan wacece matata, kawai dai...
"
" Me?"
" Ashe dai ana so na... "
Duka ta kai masa ya goce
" Allah da gaske, naji dadi sosai, zan biya bashin duk
tears din da akayi min asarar su, amma kafin nan, zanyi tafiya, karshen week
din nan. "
Da sauri ta kalle shi, sai ya kama hannun ta ya fara yi mata
bayani yadda zata fahimta
" Kinsan yanayin aikin mu dama yadda yake, ni dinma dai
kawai dai kawai dai, amma wannan karon ba zan iya kin zuwa ba, dole ne dan
akwai Takawa a cikin maganar. "
" Dadewa zakayi? "
" Uhmm... Ban dai sani ba, amma in sha Allah ba zamu dade
yadda kike tunani ba. "
" Allah ya kaimu, ya bada abinda aka je nema. "
" Amin ya Allah, an koma strike, akwai driver da zai dinga
kaiki ya jiraki ya dawo dake, hakan nasan zai debe miki kewa, da ina tunanin ko
a chanja school, amma kuma tunda har kun kai 300lv gwara ki karasa ko? ".
" Eh hakan yayi. "
" Yawwa my wife, yi min murmushi na gani toh."
Murmushi tayi, sukayi dariya a tare suka bar komai a bayan su,
suka fita domin karya kumallo.
***Zaune yake a irin kujerar nan me jujjuyawa, kansa sanye da
cowboy hat, sai bakin glasses da ya rufe kusan rabin fuskar, jujjuya yake akai
yana busa sigari, daga bayan sa yara ne biyu majiya karfi, kowannen su ka kalla
zaka tabbatar da zai iya aikata koma wanne irin aiki ne. Knocking akayi, ya
daga kansa yana duban su, kafin ya gid'a kan nasa alamar eh, wanda yake ta bangaren
kofar ne yaje ya bud'e yana matsawa baya, suka shigo su biyu mace da namiji,
kujerun gaban sa suka zauna, ya cigaba da busa sigarin sa ba tare da yayi musu
magana ba, sai da suka dau wani yan dakiku a wajen sannan ya jefar da sigarin
ya saka kafa ya murje ta.
"Kun samo abinda ya kamata ku samo din?"
"Za'a samo dai, komai yana tafiya according to plan, gashi
zai yi tafiya."
" Tafiya? " Yace yana kallon su
" Eh zaiyi tafiya karshen satin nan. "
" Wonderful, opportunity me kyau, lallai lokaci yayi da
kowa zai samu abinda yake so. "
" Menene next? "
" Tafiyar sa, let me know when he's gone."
" Me zakayi?"
" Matsala ta ce wannan, bani da matsala da cikin gidan ku,
abu biyu ne suka hada mu zuwa uku, a wannan gabar kowa has to play his on part
dakansa. "
"Shikenan. "
Zaro wata sigarin yayi ya kunna mata wuta, suka mike suka fita,
ya bi su da kallo kafin yayi murmushi. Moh zai yi tasting abinda yaji a lokacin
da ya raba shi da abinda yafi so, shi abu daya ya raba shi dashi, amma shi zai
raba shi da kusan abubuwa uku zuwa hudu masu matukar muhimmanci a rayuwar sa,
ko zai mutu sai ya dauki fansa akansa, sai ya dandana masa bakin cikin da be
taba dandana irin sa ba.
 Mikewa yayi bayan ya gama zukar sigarin, ya tura kofar
wani daki, ya shiga bayan ya kunne flashlight din wayar sa, saboda tsananin
duhun da dakin yake dashi. A gaban mutumin da yake kwance magashiyan ya
durkusa, yana tallafo kansa, sannan ya haske shi da wayar sa da ta kusan kashe
masa ido
"Ka kusa samu yancin ka, bayan na tabbatar da na samu duk
abinda nake so a wajen shi wanda yafi ma hatta iyayen ka, kayi hakuri aiki ne
ya biyo ta kanka, kai kadai ne kafi kowa kusanci dashi, dan haka dole ne kaima
ya sha wahala!"
"Gwara kayi ta ajiye ni a bakin dakin nan, akan kayi wani
abu akan sa, wallahi wallahi kaji na rantse ma ko? Kuda idan ka bari ya taba
wani abu na jikin sa, sai ya karar da duk dangin ku!"
Dariya ya kece da ita mahaukaciyar dariya, ya saki kansa da ya
tallafo ya bige da simintin wajen
" Idan yana takama da mulki ne, ko kuma khakin da yake
jikin sa, toh bari kaji, babu abinda ya isa yayi min dan nayi nisan da bazaka
taba tunani ba, k'asar nan tayi lalacewar da su kansu masu tsaron lafiyar taku
ba tsira sukayi a wajen mu ba, shi karamin kwaro ne."
Soma takawa yayi har ya kai kofa, sannan ya juyo yace
" Daga yau zuwa gobe amfanin ka zai kare, zabi na ne, na
barka ka tafi, ko kuma na kare rayuwar ka gaba daya Musaddik Izzeeddin!
_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/14/22, 19:05 - Buhainat: Halin Girma
35
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇ðŸ¾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
*******�
Da wuri Musaddik ya iso gidan, dan basu samu haduwa ba tun ranar
da sukayi waya sai yau din da zai tafi, ya riga ya shirya shi kadai yake jira,
yana zuwa ya dauko envelope din ya damka masa a hannun sa
"Ka kula sosai dan Allah, idan har lokacin da ya kamata
yayi, ban dawo ba zan fada maka sai ka damka su a hannun Aji! Dan Allah kar
kayi kuskure, ka kula sosai, kai kadai na yarda dakai da wannan amanar."
"In Sha Allah." Yace yana rik'e envelope din sosai.
  Ciki ya koma, ya barshi a wajen ya tarar ta gama
hada masa jakar sa waje daya, tana gaban jakar ta zabga tagumi har ga Allah
bata son tafiyar tasa, amma kuma dole zata hakura saukin ta daya fitar da
zatayi school, ga ma'aikata birjik an kara karo wasu ma, gate din ma kuma cike
yake da jami'an tsaro da ba dan haka ba, ba zata iya zama a wannan tafkeken
gidan ba.
  Tashi tayi ganin ya shigo,ya kalle ta ya kalli
jakar sai kawai ya rungume ta
"Zanyi missing dinki sosai, take care of yourself for me
dan Allah, idan kina bukatar wani abu, reach out to me, idan baki sameni ba,
Musaddik yana nan, nayi miki saving number dinshi kema zan bashi naki."
" Ai babu ma abinda zan nema, akwai komai."
"In case dai."
" Owk tam, nagode. "
" Yawwa, muje ki rakani. " Ya rik'e hannun ta suka
fito har wajen mota, ta tsaya daga gefe bayan ya shiga ya zauna, yayi mata
murmushin karfafa guiwa itama ta maida masa zuciyar ta na rauni, daga mata
hannu yayi har suka fice daga gidan gaba daya.
***Abinda ya faru lokacin da Bashir yazo daukar Zeenat bayan
tafiyar Iman, suna barin kofar gidan yana zuwa, adaidaita sahu yazo dan ya
maida machine din wa maishi, aikawa yayi a kirata, dan babu waya a hannun ta,
Mama na jin sakon kiran ta zira mayafi taje wa Zeenat din tana zuwa, ta je ta
same shi a tsaye yana jira ta fito suna magana da me napep din. Be yi mamakin
ganin Maman ba, dan dama yasan ba za'a yi komai ta sauki ba, gaishe ta yayi
taki amsawa, sai ma cewa da tayi tana bud'e hannun ta
"Bani takardar yata."
"Ban gane ba Mama?"
"Eh ina nufin ka sauwake mata kaddareren auren ka dan ba
zata koma ba ku karasa kashe ta kai da tsohuwar matar ka."
" Amma Mama Zeenat tana so na, nima Ina son ta, kiyi hakuri
dai ta fito mu tafi."
"Wanne so? Bayan yaudarar da kayi har kana tunanin tana son
ka?"
"Toh ni dai nasan auren soyayya mukayi da ita, kiyi hakuri
ki bimu da addu'a kawai."
"Ba zan hakurin ba, Malam takardar 'yata kawai nake so ba
dogon surutu ba."
"Ba zan iya sakin ta ba gaskiya, kiyi hakuri kawai."
Sai ya juya ya haye napep din,da sauri ta bishi tana kiran sa,
me napep yaja suka bar kofar gidan. Tana juyowa da nufin komawa gida sai ga
Abba a tsaye a bayanta, ya harde hannayen sa yana kallon ta ransa a matukar
bace, bacin rai da be taba yin irin sa ba tun da aka fara hayaniyar auren
Zeenatun, tsoro ne ya shige ta, dan yadda taga bacin rai a fuskar sa zai iya
aikata komai.
"Dan Girman Allah..."
Daga mata hannu yayi
"Babu abinda zaki ce min, bana son naji komai!
Jikin ta ne ya hau rawa, yayi ciki ta bishi tana son yi masa
bayani, ba zai tsaya jin komai ba, ba kuma zai dauki maganar da sauki ba wannan
karon, tayi abinda ba zai mata uzuri ba. A zafafe ya shiga falon yana k'wala
kiran zeenatu, ta tashi jikin ta na rawa har tana yar da dan kwalin kanta da
yake hannun ta,
"Me kike yi har yanzu baki tafi ba."
"Uhm.. uhm.. dama..."
"Karya kike yi, munafuka!"
"Minti biyar kachal na baki, ki fice ki koma gidan mijin
ki, na fad'a miki!"
Be jira ya sake jin ta bakin ta ba, ba kuma zai saurari magiyar
da Mama take masa akan dalilin da ya saka tayi abinda tayi ba, yayi gaba kawai
ya shige dakin sa ya rufo.
  Kuka Zeenat ta fashe dashi, da gaske bata son
komawa gidan Bashir, ya zatayi yanzu? Gashi taga wani irin fushi a fuskar Abban
da bata taba gani ba,dama mama so tayi bayan ta kori Bashir din idan Abban yazo
tace shi Bashir din ne yace Zeenat din ta zauna a gida zai yi tafiya ya dawo, daga
nan sai suyi ta matsa mata har ya sake ta, shikenan Abban ba zai zargi komai
ba, amma sai gashi komai ya lalace tun ba'a kai ko ina ba.
"Kina da number Bashir ko?"
Girgiza kai tayi
"Dan ubanki baki haddace number sa ba? Yanzu ya kike so
muyi? Dole ya dawo ya dauki ki ku tafi kafin nasan abinda zanyi akai."
"Mama ni ba zan koma ba."
"Aikuwa sai kin koma, baki ga fuskar babanku ba? So kike
yace na tafi gida shikenan ki rasa wanda zai tsaya miki? Tashi maza ki kira
bashir ga wyata kice ya dawo, idan yaso sai mu san abinda zamuyi."
Kuka ta cigaba da rerawa a hankali, ta karbi wayar ta saka
number tasa ta kira, tayi ta ringing amma be daga ba, ta cigaba da jera masa
kira amma babu alamun zai dauka. Rasa yadda zasuyi sukayi, har goma saura gashi
bata san gidan ba balle idan tafiya zatayi da kanta ta gane. Suna nan a falon
ya fito, ya kalle su sannan ya fice gaba daya.
***Bayan tafiyar sa sai taji gidan yayi mata girma da fadi, ta
kwanta a saman kujerar falon tayi lamo tana jin cikin ta na juyawa sama-sama.
Bacci ne ya dauke ta a wajen bata tashi farkawa ba sai da rana tayi. Sallah ta
fara yi taci abinci sannan ta zauna ta dauko littafan ta na islamiya ta shiga
duba su, tana muraji'ar na baya, tana so ta cigaba da karatun ta ko ita da
kanta ne ta dinga karawa kanta, zatayi amfani da damar duk da sun koma boko
amma ba zata kyale na islamiyya ba, akwai wasu littattafi da take son koya
wanda dole sai dai ta samu manyan malamai su koya mata, amma bata san yadda
zatayi ba. Tana nan zaune yayi mata text message, tayi masa reply sannan ta
cigaba da abinda take har zuwa la'asar, gaba daya sai taji ta rasa ma me
zatayi, sai kawai ta zagaya baya wajen ma'aikatan gidan ta same su suna hira,
suka tashi da sauri suna tambayar ta abinda take so, murmushi kawai cike da
mamakin yadda suke girmama ta take ta zauna a wata kujerar roba, tace zuwa tayi
zaman cikin ya ishe ta, nan fa suka hau murna suka cigaba da hirar tana
sauraren su, a kalla sun debe mata kewa dan bata dawo ciki ba sai bayan da aka
kira sallar magriba.
  Washegari ta tashi da murnar zuwa school bayan
tsawon lokacin da sukayi a gida, jin ta take tamkar sabuwar shiga dan wasu
abubuwan ma ta mance su, tasan da yawa duk yau zasu koma saboda dai kowa ya
gaji da zaman gidan. A tsanake ta shirya tsaf, sannan tasaka madaidaicin mayafi
akan doguwar rigar atamfar da ta saka brown da touches din blue, ta dauki jaka
da takalmi da suka shiga sosai ta saka, tayi shigarta ta mutunci ta fito ta
nufi kitchen in da ta hanyar ne ake bi zuwa bq, a kitchen ta tarar da Ummimi,
tana karasa hada breakfast dinta, ta russuna har k'asa ta gaishe ta, ta amsa a
sake tana dudduba aikin.
"Zan je school ba jimawa zan ba, idan an gama komai sai a
jera a dining, zanyi bakuwa anjima da rana."
"Allah ya dawo dake lafiya gimbiya, idan kina bukatar abu
ba sai kin zo ba, kira kawai zakiyi ranki ya dade."
"Babu komai karki damu."
"A dawo lafiya, Allah ya bada sa'a."
"Amin."
Tace ta juya ta fita, ta samu driver ya gyara motar, sai kawai
ta fad'a baya tana tuna rayuwa yadda take a shekarun baya, shekarun da basu
gaza biyu ba. Tun da suka isa makarantar duk in da suka wuce sai an kalle su, a
department dinsu kuwa kamar an ga nama ko wata sabuwar halitta, dama labari ya
riga ya karad'e ko ina amma dama ance gani ya kori ji, wasu takanas suke zuwa
su tabbatar da gaskiyar abinda suka ji. Tayi ta zuba ido ko zata ga Zeenat amma
ko me kama da ita bata gani ba, har suka gama abinda zasuyi suka koma gida.
  Tun daga ranar kullum sai taje school din ta
dawo, sai zaman gidan ya zama mata kad'an, duk dare kuma suke shafewa suna
magana da shi a waya, ba wani sosai take jin kadai ta ba, sannan kuma duk sanda
take free da rana ko ta dawo da wuri tana zama ta koya wa masu aikin karantun
al'qurani da ta lura kusan rabin su basu iya ba, kawai rayuwar su sun taso ne
akan hidimtawa gidan sarautar, tun iyaye da kakanni suke a haka har zuwa yanzu
babu wani sauyi da ya samu rayuwar su. Hakan ba karamin dadi yake mata ba, a
kalla ita ma zata samu lada me dinbin yawa.
  Wasa wasa sai gashi yayi sati uku cif da tafiya,
duk sanda ta tambaye shi yaushe zai dawo sai yace mata surprise zai mata kawai,
haka take hakura ta kyale shi, kullum cikin shiri take dan tasan zai iya zuwa
mata bakatatan, wasu magunguna da momma ta bata wanda yawancin su na fruits ne
da madara su take ta faman sha, dan sosai suke mata dadi har ta kanyi mamakin
kanta a lokacin da Mamman ta bata , bata wani ji dadin su kamar yanzu ba.
  Wata rana a cikin ranakun da take zuwa school ta
kai yamma, ta tashi duk jikin ta babu dadi, ciwo take amma bata san takamainai
me yake mata ciwo ba, kamar kar taje school din amma sai ta daure dai, ta
shirya ta kira Ummimi ta rakata, tunda dama sai da yace lallai ta dinga tafiya
da masu rakata amma bata tafiya dasu. Tare suka tafi yau haka nan taji bata son
tafiya ita kadai, suka jirata tayi lecture ta fito wajen biyar na yamma, a
gajiye likis gashi ko ruwa bata saka ma cikin ta ba, kaidar tace bata cin abu a
school tun da ma, sai dai idan zata dade irin haka taci ko snacks ne shima ba ko
yaushe ba, dan mafiya yawancin lokuta rage kudin da Abba yake bata Mama take ta
bata kadan, shiyasa ta koyi yadda zata yi karatun haka,sai kawai ya zame mata
jiki ko yanzu da take da komai bata damu taci din ba
  Da sauri Ummimi ta karbi Jakarta da kayan hannun
ta, ta tayata bud'e mata motar ta zauna sannan ta zagaya ta shiga bangaren ta,
bata lura da su biyu ne a gaba ba, har da wani sai da ya gaishe ta
"Amarya barka da rana."
"Barka dai, ai ban ma lura ba, ina wuni?"
"Lafiya lou wallahi, dama wannan gajiya da kuka kwaso, dama
munyi waya dashi ne yace na biyo ta makarantar taku sai mu wuce, zasu sauka da
karfi shida da rabi, sai mu dauko shi a airport, amma fa yace kar na fad'a miki
dan wai so yake yayi surprising dinki."
Dariya ta saka
"Lallai, ina ta tambayar sa yaushe zai dawo yaki fad'a min,
so yayi kawai yanzu ma sai dai na ganshi kenan."
" Ai irin wai surprise din masoya."
Dariya kawai tayi, bata kawo komai a ranta ba, ganin Musaddik
ne, haka kuma sai taji wani yanayi na dokin ganin mijinta, wanda yau ya cika
sati uku da kwana biyar cif da tafiya. Hanyar airport din suka dauka, ta
kwantar da kanta a bayan da yake saramata sosai.
**A word of encouragement to All TTC mother's (Trying to
conceive) do not lose hope, Allah yana tare daku, ku cigaba da addu'a, Allah ya
baku 'yaya masu albarka da mu baki daya. Baa debe tsammani daga rahmar Allah.
Post a Comment for "HALIN GIRMA 31-35"