Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

HALIN GIRMA 26-30


2/2/22, 18:35 - Buhainat: Halin Girma

      26

 ******* â˜?

 Sai da ya gama komai sannan ya biyo ta dakin ya yaye abinda ta rufan yana shigewa jikinta

"Kinyi bacci?" Yace yana leka ta kin motsi tayi a dole tayi bacci, fuskar sa ya matsar jikin ta ta, ya taba saman idon ta, motsi yaji idon nayi yayi dariya yana cewa

 

"Stop pretending ki tashi, nasan ba bacci kike ba."

 

"Uhum..."

 

"Yawwa, hira zamuyi, zaki iya tambaya ta koma menene akai na, zan sanar dake."

 

_"Farko  dai sunana Muhammad Ahmad Santuraki, kamar yadda kika gani, mahaifi na shine sarkin Adamawa, sannan Mahaifin Ammi shine sarkin Kano, na taso tsakanin Kano da adamawa in da zama na yafi yawa a Kano saboda yadda Maimartaba ya kwallafa rai a akai na. Nayi karatu na both na addini dana boko har na kai matakin captain a yanzu a bangaren aikin soja. Ni kadai Ammi da Bubu suka haifa,bani ne dansu na farko ba, kuma bani ne na karshe ba amma ni kadai ne Allah ya raya musu. Aji shine Mahaifin Bubu da sauran yan uwansa su hudu, shine na biyu akwai babban wansa wanda Allah yayi masa rasuwa, shine Mahaifin Laila da Kamal, bayan rasuwar sa ne Bubu ya auri matar wan nasa wadda ake kira da Kilishi,a lokacin kuma rikon su ya dawo hannun Bubu tunda dama chan gida daya muke baki daya. Daga nan ne kuma Aji ya sauka ya nada Bubu domin ya huta shima. Tun farkon dawowar Kilishi gidan mu, daidai da sakan daya bata taba kauna ta ba, infact idan za'a bata wuka ace wa zata kashe toh tabbas ni zata kashe, bata kaunata ko kad'an duk akan sarautar da take ganin Kamal dinta ne yafi dacewa ya karbi kujerar tunda Mahaifin su shine gaba da Bubu. Tun da na taso bani da ra'ayin sarauta ko kad'an, mutane da yawa na min kallon wanda be san abinda yake ba,. abubuwa da yawa sun faru wanda ni kadai na san su, wanda suka kara taimakawa sosai wajen ganin ban karbi tayin bubu ba, tsawon lokaci ya dauka yana bibiyata da maganar amma sam ban taba nuna masa zan iya ba, illa iyaka sai ma na nisanta kaina da duk wani abu da ya shafi gidan da sarautar baki daya. Wannan dalilin shine ya saka ni zama lafiya har wannan lokacin. Akwai abubuwa da yawa na ban mamaki a gida irin na sarauta, wanda sai wanda yake cikin ta ne kawai zai iya ganewa, babban kalubale shine tsantsar makirci da nake kyautata zaton dashi ake haifar da yawa yawan yayan sarauta. Amma duk da haka akwai mutane na gari a ciki wanda basu da matsala ko kad'an sai abinda ba za'a rasa ba."

 

Shiru yayi kamar me nazari, kafin daga bisani yace

 

" Laila ta jima tana so na, tun bayan da ta taso ta san menene soyayya ta kwallafa rai akaina, sai dai nayi ma kaina alkawarin ba zan auri jinin saurata ba, sannan ba zan iya auren mace me irin halin Laila na rashin sanin darajar hatta mahaifiyar da ta kawo ta duniya, a sangarce ta tashi ganin duk wani abu na duniya ta same shi, kyau kudi mulki sannan uwa uba gata, sai ya zama na bata san komai ba sai kanta, bata son talaka da duk wani da zai rabe ta, she's very selfish, mutum ce ita da zata iya komai dan ganin ta samu muradin ranta. Mafiya yawan lokuta takan aika min da sakonni, na kyaututtuka ko wani abu, amma ban taba nuna na gane me take nufi ba, har tazo ta tarkata ta bar k'asar don karatun ta na Masters, hakan ya saka ni samun sauki, sai gashi ta dawo a lokacin da maganar auren na ta kai mata, bansan da wanne shiri ta dawo ba, amma nasan ba zata hakura ba."

 

" Humm..."

 

Taja numfashi tana jin shi, kanta a saman chest dinshi yana wasa da gashin kanta, dagota yayi, suka kalli juna,

 

"Nayi alkawari zan kula dake da dukkan karfina, gatan da kika rasa zaki same shi yanzu har sai kin ce na gaji Muhammad dina."

 

Ya karashe cikin kwaikwayon muryarta, dariya tayi tana dora fuskar ta a saman tasa.

 

"Baka fad'a min dalilin da ya saka ka boye identity dinka ba."

 

"Saboda step mom dinki ne, na samu labarin komai ta wajen Sadeeq abokin yayanki Habib, shiyasa na zo a haka dan na tabbata ba zata taba hutawa ba har sai ta tabbatar da auren mu, wanda na tabbata da nazo a ainihin identity dina da ba lallai ta bari ba."

 

" Haka ne." Tace a sanyaye cikin son kauda tunanin Maman da zaman da sukayi.

 

" Na tambaye ki..."

 

" Ummm." Ta daga mishi Kai

 

" Did you love me?"

 

Da sauri ta kalle shi

 

" I'm serious, inaso na sani, ko tausayi na baki kika taimaka min kika aure ni!"

 

" Inji wa?"

 

" In jini, haka nake gani, tunda ni banga wata alama ba, baki taba furta min ba, ni kadai nake kida na nake rawata."

 

Sauka tayi daga jikin shi, ta kwanta tana juya bayanta.

 

" Ni dai goodnight bacci yazo."

 

Da sauri ya jiyota

 

" Ai baki isa ba, sai kin fad'a min."

 

Sake juyawa tayi tana jan duvet ta rufe kanta, ya shiga ja tana ja, ganin zata bashi wahala ya saka shi dagata gaba daya, ya mike da ita a jikin shi zuwa doguwar sofa din dake chan gefe a dakin, zaunar da ita yayi akan cinyar sa ya warware duvet din daga jikin ta, yunkurawa tayi zata gudu ya riko waist dinta ya dawo da ita.

 

"Sai kin fad'a min, ko kuma na miki irin abun jiya."

 

"Na shiga uku."

 

Danne dariyar sa yayi ganin yadda ta firgice

 

"Allah kuwa da gaske, tell me you love me or else..." Ya rad'a mata a kunne

 

"Me zance toh?"

 

"Abinda nayi ta ce miki, I love you Zahraah, Iman, Fatima, Baby, sweetheart duk dai."

 

"Ni dai... Ni bansan me.zance na."

 

"Kice I love you baby, ki hada da hot kiss a nan." Ya turo bakin sa gaba, hannun ta tasa akan bakin ya dan cije ta, tayi saurin janye hannun ya maida shi baya.

 

"Oya ina jinki, say it, inaso naji muryar ki tana fad'a "

 

Shiru tayi kunya na kamata, kunyar sa take ji sosai ta yaya zata fara furta masa wani I love you right in front of him, ai da kunya tunda ba sabawa tayi ba, gashi har da wani hot kiss shi ko kunyar nan ma babu. Rufe idonsa yayi ya sake turo mata fuskar tasa

 

" I'm all ears."

 

Minti kad'an yaji shiru ya bud'e idon, lokacin har sun sauya zuwa wani abu daban, saurin dauke kanta tayi tana turo baki. Kamar daga sama taji hannun sa a cikin rigarta, ta juyo da sauri tana rik'e hannun

 

" Dan Allah tsaya zan fada, wallahi zan fad'a."

 

" Oya ina ji, don't waste my time."

 

" I lo...ve... You." Tace a rarrabe

 

" Ban yarda ba, ki fad'a kai tsaye daga chan k'asan zuciyar ki, in a romantic way., Kice I love you Muhammad. "

 

" I love you Muhammad. "

 

Tace da sauri kamar wadda tayi gudu ko tsere.  Murmushi yayi mata ganin yadda ta fitar da maganar, yana son komai nata, har kunyar ma, ya san in dai suna tare toh har wanka ma sai ta yi masa wataran, zai koya mata komai, yadda yasan yana so rayuwar auren su ta kasance.

  Zaka rantse wani babban laifin ta aikata ganin yadda take jujjuyar da fuskar ta gefe, zaunar da ita yayi ya fita, tashi tayi da sauri ta haye gadon ta kwanta, shigowa yayi dauke da cups akan tray da vacuum flasks dake dauke da black tea, dorawa yayi akan table ya zuba ya mika mata, sannan ya zauna a gaban table din ya shiga kurbar nasa da zafin sa. First time na shan black tea dinta kenan amma sai taji yayi mata dadi sosai, sai dai bata shanye ba ta ajiye a gefen nasa ta dawo ta sake zama, sai kuma ta tashi ta nufi toilet din ta daurayo bakin ta, ta fito ta haye gadon ta kwanta. Kallon ta yake har ta gama ta rufe idon ta, sai da ya gama shan tea din tas, ya wanko bakin sa sannan ya kashe hasken dakin ya barshi k'asa k'asa, ya kwanta rigingine yana kallon sama, yana tunanin yadda zai bulowa al'amarin Lailah don baya son a samu matsala, gashi har lokacin bashi da wata hujja da zai kare kansa. Ganin zai cigaba da bata lokaci wajen tunanin abinda bashi da iko akai yaga gwanda kawai yayi abinda zai karu ya kuma samu dumbin lada, duk da yasan duk gudun sa take amma ba zai iya hakura ba.

  Ji tayi an matso ta sosai, tsoron ta ya karu zuwa sanda taji yana jujjuyata, kuka ta saka masa bil hakki da gaskiya dan tayi masifar tsorata da abinda ya faru,

 

"Dan Allah kayi hakuri."

 

Ta hau bashi hakuri ganin ya dauki hanyar da yar kwakwalwarta ta gaza dauka balle ta gane karatun. Tsayawa yayi chak da abinda yake, ya soma lallashin ta cikin kalamai masu dadi da kwantar daa hankali, a hankali ta dinga samun nutsuwa har ta dawo da nutsuwar ta, ta saduda ta saddakar ta mika wuya, domin dama ance shi aure yakin mata ne, toh tabbas wannan yana daya daga cikin manya manyan yakin matan. Ba zata iya cewa ga kalar wahalar da tasha ba, duk da yayi matukar kokari wajen ganin bata sha wahala sosai ba, amma kuma dole ne, sai dai a hankali a hankali komai zai daidaita haka rayuwar take haka kuma kowa yayi har ya saba. Ita dai bata san sanda wani baccin wahala ya kwashe ta ba, a hakan ba tare da ta gyara ba, sai chan cikin dare ta farka ta zame jikin ta, ta wuce toilet ta gyara kanta sosai sannan ta dawo dakin ta kwanta tana shigewa jikin sa, sake rungume ta yayi tsam a jikinsa bacci ya sake awun gaba da ita.

 

   Da yake tafiyar wuri zai saboda ogan sa da yake son gani, ya saka yana sallar asubah yayi mata sallama ya tafi, kamar ta hanashi tafiyar haka taji amma bata nuna ba, dan ta lura da muhimmancin tafiyar tasa shiyasa ma bata nuna damuwar ta ba, bayan gari yayi haske sosai Ammi ta aiko aka tafi da ita chan shashen ta, daga nan kuma aka kaita ta gaida Bubu, ya saka musu albarka sannan ya hada da nasiha akan rayuwar zaman aure wadda ba zaka taba iya gane ta ba sai ka shiga cikin ta.

  Sai dare ta dawo bangaren ta, tayi wanka ta dauki waya da nufin kiranshi sai ga kiran nashi ya shigo, sunyi exchanging text message amma basuyi magana ba tun da ya tafi, whatspp yace ta hau ya kirata video call suka dade suna waya, kamar kar su rabu da k'yar suka hakura suka kwanta.

  Kwana biyu da tafiyar sa, babu wani abu da suka samu daga ita har Muhammad din, duk da yace yana kokarin sa daga chan din ma amma sam hankalin ta ya gaza kwanciya, gaba daya bata cikin hayyacin ta kwata kwata dan ko sunyi waya korafin ta kenan.

   Duk shirin da ya kamata Laila tayi taa gama, ta saddakar dole ne ya aure ta, dan bashi da wata hujja duk wata hujja ma bata bar mishi ba, shiyasa take shirin ta hankali kwance kuma shiri gagarumi dan biki zatayi na kece raini, ita kanta Kilishi sai ta zama yar kallo, amma kuma ita kanta tana son auren ya yi wu, dan rashin samun mafitar Muhammad din shi zai taimaka sosai wajen cikar burin ta, dan ta riga ta gama aikawa duk wasu manyan masarautar sakon abinda muhammad din yayi, ta kuma san ba zasu taba bari a zaba musu muhammad din a matsayin shugaba ba.

  Ana gobe wa'adin da Bubu ya gindaya masa ya dawo, shi kansa ba a nutse yake ba amma yayi kokari sosai wajen kwantar mata da hankali. Takanas yaje ya samu Aji sukayi magana be baro wajen Ajin ba sai dare sosai, yayi tunanin ma zai tarar tayi bacci amma sai ya ganta a zaune tana jiranshi.

   Tsokanar ta ya hau yi har sai da ya tabbatar ta manta, suka kwana cikin farin ciki sai dai asubah nayi duk jikinta yayi sanyi, duk abinda take yana kallon ta, ya kuma kara tabbatr da da gaske tana son shi tana kuma kishin shi sosai, sai dai bata son ta nuna kishin nata a fili, ta barshi a zuwan kawai tana tayashi ne. Da wuri ya shirya ya fice ta biyo shi har kofa kafin ya fita, ta rik'e shi sai hawaye, janta yayi zuwa falon ya rarrasheta ya samu da k'yar tayi shiru ya fice yana waya da Musaddik.

   Kasancewar ranar ne ranar da Bubu ya shirya ranar da zai sauka ya bawa muhammad mulkin duk da shi Muhamamd din bashi da masaniya, sai ya zama na gaba daya masarautar ta cika sosai da manyan mutane, tun a daren jiya wasu suka iso. Hakan ya jawo bubu ya shiga busy sosai, sai da suka hadu da muhammad din a masallaci yace ya same shi karfe takwas na safe a bangarensa. Shiyasa ya shirya ya fita da wuri, ya kuma same shi yana shiryawa,. Kai tsaye Bubun ya tambaye shi idan yana da wata magana akan abinda ake tuhumar sa? Kai tsaye yace bashi da wata hujja da zai kare kansa, amma yasan be aikata abinda ake zargin sa ba, shiru Bubu yayi dan yadda maganar ta karade ko ina har kunyar fita yake a yau, sallamar sa yayi kawai ba tare da yace komai ba.

   Fitowar Bubu ya saka kowa nutsuwa, fadar tayi tsit bayan ya zauna, wanda suka sanshi suna kallon shi zasu gane ransa a bace yake,limamin babban masallacin Masarautar ya saka aka kira masa shi gaba, ya matso gaba, Bubun ya bada umarnin za'a daura auren Muhammad da Laila. Nan da nan fad'ar ta dauki hayaniya, kowa na kokarin tofa albarkacin bakin sa!

 

 

 

2/2/22, 18:24 - Buhainat: Halin Girma

      27

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

******* �

 

Matsowa Limamin yayi ya zauna, sai wambai da zai karbi auren shima ya matso zuciyar sa fes shirin su ya tafi yadda ya kamata. Dakatar da su Aji yayi, ya bada umarnin a fara gabatar da nadin sarautar kafin daurin auren ya biyo baya, babu wanda yayi magana dan babu me ja dashi, sai dai kuma sam manyan fadar sun ki amincewa da nad'in Muhammad saboda abinda ya faru, Bubu na zaune be tanka ba, suka shiga tattaunawar gaggwawa in da kaso saba'in cikin dari suka amince da nad'in Kamal, sai kaso talatin suka nun Muhamamad din, idan aka samu irin haka toh dole ne a dauki ra'ayin bangare mafi rinjaye, a take aka gabatar da Kamal a gaban fadar, aka kuma shiga yi masa nad'in cikin yanayin da ya saka Bubu a matukar tashin hankali, be gamsu da karbar mulkin Kamal din ba dan akwai gyara sosai a rayuwar sa, ganin da gaske idan yayi wasa komai na masarautar sai ya rushe, sai kawai ya dakatar dasu. Duk kowa yayi zuru yana jiran bayanin sa, be san me zaice ba, duk kuwa dashi ne shugaba amma kuma idan har aka zauna tsakanin manyan fadar aka zartar da hukunci toh shi ma dole ne yabi. Shiru ne ya biyo bayan dakatarwar da Bubun yayi, kowa na jira yaji abinda zai sanar.

   Magatakarda ne ya shigo, ya fadi yayi gaisuwa sannan ya mik'a sakon rubucacciyar wasika daga fadar kwamnatin adamawa akan sabuwar dokar da aka zartar a daren jiya, aka kuma kayyade shekarun da ake so duk wani sarki ya cika su kafin zamtowar sa sarki, ajiyar Zuciya Bubu ya sauke ganin ko kusa da shekarun Kamal be kai ba. A karshe kuma gwamnati ta jaddada lallai Sarki Ahmad Santuraki ya cigaba da zama akan kujerar sa kafin a samu wanda zai gaje shi da irin shekarun da yake a rubuce, da kuma cika duk sharadin da aka gindaya.

  Hayaniya ce ta dauka a cikin fadar, masu kushe abun nayi masu nuna farin cikin su nayi, shi dai Bubu sai yayi shiru yana duban kowa, sai a lokacin ya kara tabbatar da masu son sa tsakani da Allah a cikin manyan masarautar da kuma wadanda da gaske suke son ganin bayan sa.

   Sai da kurar ta lafa, kowa yayi shiru bisa umarnin Sarki Ahmad din, dan gani yayi abun nasu na neman ya zarme shi kuma bashi da katabus akan dokar da taxo a rubuce daga gwamnati wadda take da dama da ikon sakawa ko sauke duk wani Sarki. Jawabi ya soma yi cikin son ganin ya kwantar da hankalin kowa, da kuma kokarin nuna bashi da masaniyar komai akan sakon gwamna, duk da dole ne sanar da gwamnati kafin dora sabon sarki kuma sunyi hakan amma be san ainhin dalilin gwamnati na fito da wannan dokar ba.

  Shigowa Muhammad yayi, ya samu gefe ya zauna suka hada ido da Bubu yayi masa murmushi yana tuna haduwar sa da gwamna a daren shekaranjia, ya kuma je masa da bukatar sa ta son sauya baki daya dokar, ya bashi kwararan hujjoji masu gamsarwa wanda dama chan mutumin sa ne tun kafin zamowar sa gwamna, babu abinda Muhammad din zai nema be masa ba in dai be saba ka'ida da doka ba.

   Babu wanda yasan da wannan shirin nashi, babu kuma wanda yayi tunanin hakan zata kasance, makasudin tafiyar tasa kenan da be shirya karbar mulkin ba, ba zai kuma bari Kamal ya samu ba, yana da bukatar morewa rayuwar sa da Fatiman sa, idan har ya sake ya karbi mulki toh dole akwai abubuwa da yawa da be isa yayi wa kansa ba, ko ita.

   Bayan gama bayanin Bubu ne, kowa yai shiru masu tattaunawa da zuciyar su nayi, masu tunanin mafita nayi amma kuma babu me sake furta komai dan an gama maganar sai kuma wani lokaci idan me dukka ya kaimu.

  Liman ne ya sake dawowa gaba, domin gabatar da daurin auren tunda an gama da wanchan babin, wambai da fuskar sa ta kasa boye damuwa da bacin ransa ya matso bayan yayi wa Muhammad din wani kallo da shi kadai ya san dalilin sa.

   Kamar yadda addini ya koyar, ana aure ne bisa doran abubuwa guda uku, sadaki, siga da kuma shaidu, wanda duk sun hallara a wajen, liman ni ya soma magana da gabatar da abinda ya tara su, kafin ya kai karshe Muhammad ya katse shi, ya taso daga wajen da yake zaune ya iso gaban su ya durkusa, ya mikawa wambai wayar sa yana komawa ya zauna daga gefen wamban bayan ya tankwashe kafar sa, idon sa fes akan wamban yana karanta yanayin fuskar sa. Da farko tsayawa wamban yayi chak da kallon video din, sai kuma ya saki wayar ta fad'a saman cinyar sa jikin sa a mace ransa y kai kololuwar baci.

  Hannu Muhammad ya saka ya dauke wayar sa,ya mikawa Malam Liman ya kunna video ya kuma karo volume din sosai yadda duk wanda yake kusa da wajen zaiji. Muryar Laila ce take magana ita da baiwar nan tata, a daren da za'a kawo Iman, a lokaci da suke maganar turaren, tun daga farkon hirar su har karshen ta. A fuskar Bubu zaka hangi tsantsar farin ciki, amma kuma rawanin kansa ya boye, sai ta kwayar idon sa kadai zaka gane, be ce komai ba dan dama ba zai ce ba.

   Karbar wayar Muhammad yayi, ya mikawa sauran dake wajen suma suka kalla, sannan ya kunna na karshe wanda yake nuna Laila sanda take shiga part dinsa, bayan ta bawa masu tsaron kofar wani abu a cikin envelope, wannan kadai ya isa hujja, hujja me karfi.

   Girgiza kai kawai Aji yake, dama yasan gaskiya zatayi halin ta. Laila da Muhammad duk su din nasa ne kuma yana kaunar su amma kuma ba zai taba goyon bayan karya ba.

   Wata hayaniyar ce ta sake kaurewa, aka hau Allah wadai da hali irin na Laila, kuma ko babu hujjar nan Laila Itace mara gaskiya, babu yadda za'a yi idan har cutar da ita Muhammad din yayi a sameta a bangaren shi, idan har hakan ce ta kasance toh lallai shi za'a samu a nata bangaren amma sai aka samu akasin haka.

  Aikawa Bubu yayi aka taho da baiwar nan, hade da masu tsaron shashen muhammad din, tun kafin aiken ya je sun samu labari, sun shiga matukar tashin hankali dan basu yi tunanin za'a gane gaskiya adan kankanin lokaci haka ba, basu san cewa duk wanda yace Allah, toh ya gama komai.

 

Jifa tayi da dankwalin kanta da shahararriyar me kwalliya da ta taho kafa da kafa tun daga Abuja tazo ta tsara mata shi, ihu ta saki ta hau jifa da kayan dake saman dressing mirror dinta, ta riga ta gama duk wani shirin ta, ya akayi haka ta kasance? Wacce irin sa'a ce da yarinyar da har komai zai kasa tasiri akanta? Me take takama dashi? Me take ji dashi? Kanta ta hau bubbugawa a jikin bangon kafin ta fashe ta kuka, ba zata dauka ba, bata san ya zata iya rayuwa babu shi ba, bata sani ba.

   Aikowa Bubu yayi a tafi da ita, lokacin Kilishi na wajenta, tana bata baki, bata san me zata ji ba, da fasa nad'in Kamal din ko da abin kunyar da Iman din ta jawo musu? Kamar mahaukaciya haka ta nufi bangaren Bubun. Shi kadai ne a turakar sa, bayan an tashi daga zaman ne ya dawo gida dan yana so ya huta, tension din da ya shiga a kwana biyun nan ba kad'an bane shiyasa yace babu zaman fad'a har sai bayan kwana biyu idan ya huta sosai, be ga muhammad ba tun bayan an tashi daga zaman, bayan ya saka an aika da bayin nan gidan gyaran hali sai kawai ya zarto nan ya kuma bada umarnin a kawo masa Lailan, sai gashi sun shigo ita da mahaifiyar ta, kan Lailan tsaya ta shigo sai dai kamar wadda aka bubbugewa guiwa haka ta koma, kwarjinin Bubun ya sakata shiga hankalin ta, fuskar sa a daure take tamau babu ko digon fara'a hakan ya sakata shan jinin jikinta, dan bata taba ganin sa a haka ba, sosai yake sakewa da ita har suyi hira, yana son ta sosai tamkar shine ya haife ta,sai gashi yau ta kasa kwakkwaran tsaiwa a gaban sa, ta makale daga gefen wata kujera tana leken fuskar sa.

  Be bi ta kan Kilishi ba, dan ba ta ita yake ba, ya kira sunan Lailan da kausashshiyar murya, bata iya amsawa ba, sai matsowa da tayi da jan kafa ta gurfana agaban sa.

   Sanarwar shigowar Muhammad ta dakatar da maganar da Bubun yayi niyyar yi, ya shigo kansa tsaye zuciyar sa fes ko babu komai yasan ya wanku tas a wajen Bubu, dama kuma babban tashin hankalin sa ace Bubun na fushi dashi.

  Ganin su ya saka shi juyawa, amma sai Bubun ya dakatar dashi, ya dawo ya zauna a gefe yana jin kamar dakin yayi musu kad'an, kamar idan ya cigaba da zama yana shakar iska daya da Laila zai iya nakasta ta. Ammi ce ta shigo tare da Iman tana bin ta a baya, fuskar Ammi fes ba zaka taba gane halin da take ciki ba, daidai saitin kafarta Iman ta zauna kanta a k'asa sosai kwarjinin Bubun ya cika ko ina na dakin, ganin su ya saka muhammad din sakin ransa, ya dinga satar kallon Iman din cikin so da kauna.

  Gyaran murya Bubu yayi, ya shiga bayani da harshen da yake tunanin duk zasu fuskanta, muryar sa na fitar da amo me tsoratarwa, babu wasa ko digo a cikin maganar sa, ta in da yake shiga bata nan yake fita ba, yayi wa Lailan tas, ya kuma tabbatar mata da sai ta karbi hukunci daidai da abinda ta aikata, gaba babu wanda zai yi sha'awar aikata irin abinda ta aikata, karshe kuma yace y haramta mata karatun nata baki daya, ta dawo gida kenan ba zata koma ba, tunda babu abinda ta sake daukowa sai mugun hali.

  Ko gezau batayi ba, dama kuma babu wanda ya saka ran zata girgiza ko ta tsorata, kanta dai yana k'asa dan bata isa ta hada ido da Bubun ba, amma tana zaune kekam har ya gama ya kuma juya kan Muhammad da Iman ya sake basu hakuri musamman Iman da ta shigo gidan ta kuma fara da karo da irin wannan abun, kachokam ya dora laifin Lailan a akansa, ya sallame su ya zama daga shi sai Kilishi.

  Gaba Ammi tayi zuwa bangaren ta, tare da Iman dan bata bukatar sake jin komai hakan ma ya isa, Allah ya kawo komai cikin sauki, ba zata kuma bata lokaci a abinda ya riga ya wuce ba, shi dama sharri dan aike ne, duk in da yaje sai ya dawo.

   Sauri-sauri yake ya isa gida a tunanin sa Iman chan tayi, ya matso yaji yadda akayi ta samu evidence din, a lokacin da ya riga ya cire rai, tsaida shi Laila tayi, ya tsaya yana juyowa,

 

"Ni ka wulakanta ko cap..."

 

Ai bata kai karshen maganar ta ba, ya dauke ta da wani gigitaccen mari, marin da ya dauke mata ji da gani na wani lokaci

 

"Ni ka mara?"

 

"Shine kawai abinda nake ganin zan miki na huce, duk da addinin musulunci ya hane mu da dukan mace, musamman ma a fuska, amma bani da zabi, nayi duk kokarin da zanyi nayi avoiding dinki, amma saboda ke jaka ce sai da kika saka ni aikata abinda nake gudu, idan kika cigaba da shiga rayuwata ko? Wallahi sai na miki abinda baki taba tunani ba."

 

Hannun ta dafe da fuskar ta, ta kasa cewa komai har ya juya da nufin barin wajen, cikin daga murya yadda zai ji tace

 

"Sai dai idan kashe ni zakayi, amma nayi maka alkawarin sai ka aure ni, ko kana so ko baka so!"

 

Be tsaya ba, dan bashi da lokacin batawa, yana kyautata zaton Laila ta haukace, ko kuma tana shaye-shayen kayan maye, idan ya biye ta zai iya mata illa, dan yadda yake ji kamar ya saka hannu ya shake mata wuya har sai ta bar numfashi.

 

  Sababbin masu kula da kofar ya tarar, suka gaishe shi ya amsa musu da kai, har ya wuce ya dawo ya nuna su da yatsa

 

"Idan har na samu wani abu daga gareku, wallahi tallahi sai kun yabawa aya zakinta."

 

Ya wuce su yana juyo su suna bashi hakuri da alkawarin ba zasuyi komai ba, kofar ya buga da karfi, ba zai cigaba da zama a cikin gidan nan ba, idan ma ya zauna toh fa ba zai iya da tsarin su ba, tafiyar sa zai wata k'asar ya huta sosai, ko da zai dawo amma sai ya tabbatar da ya samu enough time da matar shi, ba zai yiwu wasu banzaye su nemi hana shi morewa ba,daga yin auren sa.

  Abincin dake saman dinning ya kalla, ya wuce ya hau bubuda dakunan yana neman ta, bata cikin ko daya, ya dudduba toilets nan ma bata nan, ya zata nan zata wuto be yi tunanin Ammi zata bi ba.

  Dawowa yayi falon ya kwanta rigingine ya rage volume din tv ya rufe idon sa. Bacci ne ya soma daukar sa, yaji kamar ana taba shi, bud'e idon yayi ya ganta a tsaye a wajen kafar sa, kallon kayan jikinta yayi daga sama har kasa, doguwar rigar material ce me budadden hannu, sai kanta dake rufe da inner cap, murmushi tayi masa ya mayar mata yana mika mata hannu ta daga shi, make kafada tayi alamun a ah, ya sake mika mata ta noke, marairaice mata yayi yana sake mika mata hannun, karba tayi da nufin dagashi amma sai ya saka karfi ya jawo ta, ta fado kansa ya saka hannu ya zagayeta a jikinsa.

 

"Dama na san haka zakayi, shiyasa naki."

 

"Toh laifi nayi? Mutum da iyalin sa halaliyar sa."

 

"Zuhr ake kira toh ai."

 

"Don't tell me azahar tayi."

 

"Tayi, har ma nayi sallah ta."

 

"Ohh... Ya Salam rayuwar nan tana gudu."

 

"Wallahi, tashi toh kayi sallah." Tace tana kokarin daga shi, maida ita yayi yace

 

"Zan tashi, amma sai kin min tausa, I'm weak kwana biyu ban fita exercise ba."

 

Gefen kadarsa ta danna masa, zuwa saman chest dinshi

 

"Gashi nan na gama."

 

"Ojoro, wannan ai ba tausa bane, danna ne."

 

Dariya ta saka

 

"Menene banbancin?"

 

"Tausa daban danna daban, ji fa yadda kika danna min kafada kamar wani katako."

 

Dariya ta kwashe da ita sosai, irin wacce be taba ganin tayi ba, tsayawa yayi yana kallon ta yana admiring dinta, komai idan tayi burgeshi yake sosai, sai da ta lafa sannan ta ga irin kallon da yake mata sai kuma taji kunya, ta dora fuskar ta a saman kirjinshi tana dannawa.

 

"Sarkin kunya." Ya mike yana dagata, zama sukayi akan kujerar ya rik'e hannun ta cikin nashi

 

"Thank you so much, kin taimaki mijinki a lokacin da yake cikin tsananin bukatar taimako, dama mace ta gari itace me taimakon mijinta idan ya shiga matsala, I'm very proud of you, bari nayi sallah nazo ki bani labarin yadda akayi, I hope baki saka kanki a matsala ba ko?"

 

Girgiza masa kai tayi

 

" Ko daya, kayi sallah ga abinci na shirya mana da kaina"

 

"Really? Kece kika girka?"

 

" Nice." Tayi folding hannunwanta a kirjinta tana murmushi

 

"well-done, hakan yayi min dadi, bari na zo naci girkin amarya ta."

 

Dariya tayi ya shige ciki ita kuma ta zauna tana jin dadi sosai.

 

***Cikin dare ya tashi, ya kalli Hajiya Layuza dake shirge kamar kayan wanki, bayan ta hanashi sakat da zalamar sa ya samu ya bata maganin bacci shine tayi bacci, sadaf-sadaf ya sulale ya fice yana kallon hanya sai dakin da Zeenat take. Tura kofar yayi yaji ta a rufe, ya shiga kwankwasawa a hankali kamar barawo, cikin baccin wahala Zeenat din ta farka taji kamar ana taba kofar, tsoro ne ya kamata ta, ta makale a wajen daya tana zaro ido,

 

" Zeenat kina ji? Bashir ne dan Allah bud'e min. "

 

" Ba.. bazan bude ba." Tace tana sake makalewa a jikin ginin dakin

 

" Dan Allah ki cece ni, ki bud'e muyi magana akan tafiyar ki gida, na samo hanyar da zaki koma gida cikin ruwan sanyi, dama naji an ce an janye yajin aikin da jami'oi suke, bud'e kiji."

 

" Da gaske kake? "

 

" Da gaske nake, bud'e dan Allah kafin ta gane bana nan ta biyo ni tazo ta tafi dani. "

 

Tashi tayi ta bud'e kofar, tana gama budewa ya fado daga shi sai gajeren wando, wani iri taji tayi saurin dauke kanta, kamar wanda yasha wani abu kawai taga mutum yayo kanta, ya dakume ta yana kokarin rabata da kayan jikin ta, dukan sa ta shiga yi amma kamar ingiza shi take, toshe mata baki yayi sosai ta hanyar saka abu ya daure bakin yadda ihun da zatayi ba zai fito ba. Duk yadda tayi kokarin ganin ta hana shi amma sam be hanu ba, sai da ya karbi sadakin sa, ya kyaleta yana maida numfashi, kamar wanda yayi tsere da zaki. Bayan kamar minti goma ya tashi da sauri ya fice daga dakin ba tare da ya kalli in da take ba.

   Tun tana kuka har ta daina ta galabaita sosai, ko hannun ta bata iya dagawa balle tayi wani kwakkwaran motsi ko ina na jikinta ciwo yake balle uwa uba chan kasanta da take jin kamar zata mutu dan tsabar azabar da take ji

 

 

 

2/3/22, 21:11 - Buhainat: Halin Girma

      28

 

******* �

Jan kafa ta dinga yi har zuwa wajen da jakar ta ke ajiye, ta hau zazzage ta ko Allah zai sa taga wayar ta, tun da tazo gidan bata sake ganin wayar ta ba, gashi tana matukar bukatar tayi magana da Mama, ji taka kamar mutuwa zatayi saboda azabar wahalar da take ciki. Bata ga wayar ba, sai yan kayan ta da Bashir din ya dauko mata daga wanchan gidan da yafi mata nan sau dubu duk kuwa da rashin haduwar gidan amma chan a kalla zata samu yancin ta, ba kamar nan da take xaune karkashin matar Bashir din ba.

  Kwanciya tayi a tsakiyar dakin, tana cigaba da rera kukan ta, har zuwa lokacin da taji ana taba kofar, kafin ta bud'e ta zuro kanta

 

"Uban me kike wai har yanxu baki fito kin yi ayyukan ki ba?"

 

Ta tsinkayi muryar ta har cikin kwakwalwarta, matsawa tayi amma bata tashi ba, shigowa tayi a fusace ta mik'ar da ita, ta k'wala ihu cikin azaba tace.

 

"Dan girman Allah kiyi hakuri bani da lafiya."

 

Da sauri ta saketa, ta ja baya tana kare mata kallo

 

"Kutmar U! Ni Bash zai munafunta? Kan bala'i amma wallahi sai na yi masa rashin mutunci, dan wulakanci duk yadda nake kaff-kaffa amma sai da ya zagayo ya taba yarinyar na? Ni xai zawo wa raini!"

 

Kamar wadda ake hankadawa ta fice da sauri, Zeenat na jinta tun daga kofar ta fara k'wala masa kira, baya kasan da ta barshi haka kuma baya sama ya riga yasan abinda ya aikata shiyasa ya bar gidan. Sake dawowa tayi dakin ta tashi Zeenat din tsaye da karfi

 

" Tunda har kin iya kwana da miji sai ki fito kiyi aiki, babu wani langabewa da zakiyi wallahi sai kin min aiki."

 

"Dan Allah kiyi hakuri wallahi zazzabi nake ji, jikina duk ciwo yake."

 

"Hehehe..." Ta saki shewa tana mata kallon banza gami da tafa hannu

 

"Idan kinga na kyale ki sai dai idan mashasharar mutuwa naga kina yi, amma wallahi tunda kika kwana da miji sai kinyi min aiki."

 

Kuka Zeenat din take da gaske ba da wasa ba, kuma da gaske take zazzabin take ga wani irin ciwo da ta kasa gane wanne iri ne, a lokacin ne ta tuna wtaa rana ana ruwan sama, haka Mama ta tursasawa Iman wanke mata wasu kaya masu yawan gaske,sannan tana wankin tana girki duk kuma a bayan, har aka kare ruwan nan tana kaiwa da komowa ba tare da Maman ta tausaya mata ta duba halin da zata shiga ba, a lokacin ita tana kwance a daki tana karatun wani littafin hausa, sai bayan an gama ruwan ne ta fito ta sakawa cikinta abinci ta sake komawa.

   Tulin kayan wanke-wanken da yake gabanta ta kalla, ta sake fashewa da wani sabon kukan, a hankali ta zauna a gefen dandamalin ta shiga wanke su tana yi tana kuka shabe-shabe.

   Sai da ta gama komai ta gyara gidan tas sannan ta samu ta sakawa cikinta ruwan tea da take jin shi kadai zata iya sawa a cikin, ta koma daki ta kudundune tana jin sanda Hajiyar ta bar gidan cikin rakiyar kawayenta. Bayan kamar minti goma sha biyar da tafiyar ta, ta tashi ta dauki jakar hannun ta, da mayafi ta fito ta nufi hanyar gate din gidan, fatan ta kawai ta bar gidan idan har ta fita toh babu ita babu auren Bashir ko me za'a iya sai dai ayi amma ta gama auren. Har taje gate din bata ga kowa ba, haka babu me gadi a wajen tayi saurin isa kofar ta kama ta bud'e ta, sai taji ta a rufe, ta ja da dan ragowar karfin ta amma still ko motsi kofar batayi ba, tana haka ne sai taji alamun ana saka key ta waje, kafin ta iya barin wajen har Bashir ya shigo sanye da sabuwar shadda kunnen sa makale da waya yana magana yana dariya sai dayan hannun nasa rik'e da wayar ta da leda me tambarin sahad stores.

 

"Zan kiraka oga, nagode sosai." Ya katse kiran yana dubanta

 

"Ba dai guduwa zakiyi ba?"

 

"Ban sani ba." Tace tana matsawa gaba tana cigaba da kokarin bud'e kofar dan da ya shigo rufe tayi yayi

 

"Muje ciki kiji."

 

"Babu in da zani, na gama zama a bakin gidan nan, da muguntar matarka, wallahi gidan mu zani ba zan iya ba."

 

"Naji toh, amma kizo muje kinga na siyo miki chocolates masu kyau da gasasshiyar kaza, da yogurt."

 

"Da yake ka samu mayya ko? Toh ba zan koma ba wallahi."

 

Sai ta fashe da kuka da karfi, da sauri ya toshe mata baki, ya sungumeta tana ihu be ajiye ta ba sai da ya kaita dakin, sannan ya dire ta, gani yayi idan ya biye mata zata tara masa mutane. Yana ajiyeta ya zauna a gefe yana bud'e ledojin

 

" Nasan kinsha wahala jiyan nan, taso kisha fresh yogurt din nan zaki ji dadi."

 

Banza tayi masa ta cigaab da gursheken kukan ta. Ci ya hau yi yana kallon ta, yana jin da zata yarda da ya sake zuwa karaye, amma yasan yadda ta sha wahalar nan zai yi wuya ta amince masa, yaga kiran Hajiya wajen sau goma amma be daga ko daya ba, dan yasan kwanan zancen yanzu ma sai da ya tabbatar ta bar gidan sannan ya shigo, da ace Zeenat din zata amince masa da lafiya lou, shiyasa ma ya tsaya yayi mata siyayyar yasanta da shegen kwadayi, amma sai yaga ko kallo be isheta ba daga shi har kayan hannun nasa. Sai da ya kusan cinyewa sannan ya tuna ya rage mata, ya mike zai fita ta tsare shi

 

" Bani wayata."

 

"Hauka nake? Kije ki kira min ruwa kenan, ai kinga na baki wayar nan ko? Toh nasan me na taka in da ko kinje sai kin dawo da kafarki."

 

Matsar da ita yayi ya fice yaje ya dora ruwa, yayi zafi ya juyo mata a wani babban bawo ya kai mata toilet ya dawo ya sake sungumarta tana dukansa da komai ya kaita, ya danna ta ciki ta dinga ihu tana tashi amma sai da ya daddanne ta har ta hakura ta zauna, sannan ya fito ya barta a ciki, ya nufi gate ya samu me gadi ya dawo ya ja masa kashedi akan kar ya kuskura ya barta ta fita sannan ya fice daga gidan da baya saka ran dawowar shi sai dare yayi sosai saboda Hajjajun sa da yasan ta tama zata kare masa tanadi tsaf dan ba abinda ta tsana kamar tarayya ita da wani akan abu guda!

 

***Tana zaune ya dawo daga sallar, ya chanja kayan jikin sa zuw doguwar jallabiya maroon colour me kyau, bata kai masa har k'asa ba, tashi tayi suka hadu a hanya sannan suka karasa tsakiyar falon, ta wuce zuwa dining area din ta dauko warmers din ta dawo ta jere su a k'asan bayan ta ciro table mat ta shinfid'a akan carpet din

 

"Me yasa zaki bawa kanki wahala bayan duk wannan aikin kina da wadanda zasuyi."

 

"Ban iya zama haka nan babu aiki ba wallahi, ni nama sallame su tun dazu nace su je zan neme su."

 

Jinjina kai yayi yana yaba mata, tashi yayi ya tayata suka karasa sakko da sauran kayan, sannan yayi serving nasu a plate daya, da spoon daya, debowa yayi ya nufo bakin ta yace

 

"Oya, it's my duty bud'e bakin ki."

 

Dariya ta saka ta bud'e bakin a kunyace ya saka mata, sannan shima ya diba ya ci dadin girkin ya ratsa shi, lumshe idon sa yayi ya bud'e yana ware su akanta

 

"Da gaske kice kika yi abincin nan?"

 

"Da gaske!"

 

"Wow... Alhamdulillah Ya Allah, I'm blessed ta ko ina, Allah nagode maka, abincin nan yayi dadi sosai,Allah yayi miki albarka."

 

"Amin."

 

Ta amsa tana jin dadi sosai, babu abinda mace take so irin idan tayi abu a yaba, tana fatan ya dore har gaba, hakan yana karawa mace karfin guiwa wajen kyautata ma mijinta. Cikin nishadi suka gama cin abincin, ya sake tayata suka tattare kayan zuwa kan dining din, in da masu aikin zasu kwashe daga nan zuwa kitchen. Falon suka dawo suka zauna, ya matso kusa da ita ya ajiye kansa a saman kafarta, yace

 

"Ina jinki, bani labarin yadda akayi."

 

Dan muskutawa tayi ya gyara shima, tayi murmushi me sauti ya maida mata yana jan kunnensa

 

"Na matsu naji!"

 

"Abinda ya faru bayan ka fita, na dawo daki na zauna ina tunanin mafita, duk tunanin da zanyi nayi babu wani abu da nake ganin zamu iya rik'e shi a matsayin hujja, duk da haka ban karaya ba, inaji da yakinin Allah ba zai bata nasara ba, hakan ya saka ni tashi na dauro alwala, nazo nayi nafila, na sake rokon Allah akan ya taimaka ya bayyana gaskiya, bayan na idar ne kawai nayi deciding bari na shiga kitchen na ga abinda yake wakana, domin a rayuwa ta kitchen na daya daga cikin wuraren da ya zama tamkar daki na, domin nayi masa sabon gaske. Na tarar da ma'aikata da yawa suna ta hada-hadar hada girki, shine na karbi aikin namu, nace su ji da nasu. Muna aikin ne sako ya iso, a cikin envelope din nan..."

 

Ta nuna masa tana mika masa

 

" Flash ne a ciki, wai inji wata mata sanye da nikaf tace a bani, a haka sakon yazo."

 

Jujjuya envelope din yake a hannun sa, tambarin gidan ne a jikin envelope din, wanda ba kowa ne yake samun ta ba sai jinin gidan... Cigaba tayi

 

"Shine nazo na saka a jikin Tv, abinda na gani ya saka ni rawar jiki, nayi sauri na nufi daki na dauko system dinka da kayi amfani jiya, naci sa'a na sameta a bud'e, na saka flash din a jiki nayi copying komai a wayata sannan na tura maka, na kuma kiraka da nufin nace ka duba amma kuma har ta gama ringing baka daga ba, a lokacin babu irin tashin hankalin da ban shiga ba, na dinga kaiwa da komowa a tsakani ina fatan ka daga wayar ko kuma ka duba sakon kafin lokaci ya kure. Ganin shiru shiru babu alamar zaka daga, sai na yanke shawarar zuwa da kaina, har fadar dan ba zan iya jurewa ba, har na dauki abinda zan dauka na fito na kuma kira wadda zata rakani, sai ga kiran ka."

 

Zaune ya tashi ya jere da ita akan kujerar, yana cigaba da jujjuya envelope din, yana son gano wanda zai aiko da sakon, duk iya tunanin sa be samu amsa ba, sai ya ajiye a gefe ya rungumota jikin sa yana murmushi

 

"Thank you so much Baby, nagode sosai da kokarin ki."

 

"U welcome."

 

"Ashe dai Ashe ana so na tunda har ake kishi na."

 

"Kishi kuma?"

 

"Ehen menene? Kishi ne mana, hadda kuka fa daxu da zan tafi, kamar wanda zai tafi filing daga!"

 

Sai ya tuntsure da dariya yana gwada yadda ta riko shi, turo baki tayi tana tashi daga kusa dashi

 

"Tayaka jimamin abun nake fa, aiko ba zan kara tayaka ba."

 

" Fadi gaskiya dai, kinga za'a kwace miki handsome mijinki, hankali ya tashi."

 

" Na shiga uku."

 

" Ba haka bane? Kinga hanci zur har baka, yarinya taga handsome guy tace idan bani ba sai rijiyar kusugu."

 

" Allah kaiko?"

 

" Ai gaskiya ne, ki rantse ba kishi bane."

 

Shiru tayi ta kyale shi, ta lura yana da so wasa da tsokanar ta, is like kamar ma yafi jin dadin sakata a gaba yayi ta tsokana, amma ka ganshi da sauran mutane kamar bashi ba.

 

   Bayan yayi sallar la'asar ne ya sake chanja kaya ya fita, lokacin yaran sojojin sa sun iso, dama sunyi waya akan suna hanya, yazo ya baza su a kofar shashen sa in da babu shegen da zai sake gigin shigar masa, balle har wani abu ya faru, duk da ma ba wani zama zai ba, sati daya zasu kara ya tattara yayi tafiyar sa Kano daga nan kuma yana tunanin ma k'asar zai bari, ya rasa yadda zai da abokan aikin sa da suka ce sun shirya masa kayataccen bikin sword crossing gashi har date din ya wuce sun sake rescheduling wata ranar, dole ya yarda dan sun kashe kudi sun kuma gayyaci manyan mutane, shiyasa kawai ya hakura yace zasu zo, daga nan sai suje su ga mahaifiyar Iman din daga nan suyi tafiyar su Kano Adamawa sai an Baba ta gani. Akwai tafiyar da zasuyi akan wani babban assignment daga wajen aiki duk da ba'a saka rana ba, amma baya so tafiyar ta zo nan kusa, yafi so sai sun je sun dawo ma, amma zai sake tuntuba yaji, yaji kuma iya dadewar da za'a yi idan yaga za'a shiga rayuwar sa zai iya fadawa dan baya son abinda zai saka shi yin nisa da Iman din, musamamn ya barta a gidan su ita kadai, be yarda da kowa ba, haka nan be yarda da duk wanda ya aiko da flash din nan ba, akwai wani hidden bayani a k'asa, ya riga yasan gidan su, ya san abinda za'a iya da wanda ba za'a iya ba,be kuma san iya adadin mutanen da suke son ganin bayan sa ba, duk da ya nuna bashi da ra'ayin saurata ko kad'an, amma ya tabbatar da akwai wadanda suke tsoron sauyawar ra'ayin sa, wanda suke gudun wani abu ya faru ba abinda suke fata ko suka tsara ba.

   A wajen Bubu ya shantake dan tare sukayi har sallar magriba yayi masa tas akan abinda ya aikata dazun akan sakon gwamna, duk da yaji dadi a kasan ranshi amma be nuna masa ba, sai ma fad'a da yayi masa akan kar ya sake, ya amsa da toh ba zai sake ba, sannan suka cigaba da hirar su irin wadda suka dade basu yi irin ta ba.

  Ana magriba Ammi ta aiko kiran Iman din, ta tashi cikin rakiyar hadiman ta suka nufi wajen Ammin in da ta tarar da wasu baki wanda daga gani masu muhimmanci ne ga Ammin, gaishe su tayi a ladabce bayan ta gaida Ammin, sannan Ammi ta gabatar da ita a matsayin matar Muhammad suma ta gabatar dasu ga Iman din, matar gwamnan Adamawa ce da yarta wadda Iman din ta lura da girman kanta, dan tun shigowar Iman din ko daga kai batayi ta kalle ta ba, tana ta danna waya tana cin chewing gum. Share ta ita ma Iman din tayi, suka cigaba da zaman shiru bayan tashin Ammi da matar suka shiga ciki suka barsu. Wayarta ta kara a kunne, tana yatsine kafin tace

 

"Moha gani a part din Ammi fa."

 

"Wallahi tun dazu ma, zaka shigo?"

 

"Owk ina jiran ka."

 

Satar kallon ta Iman tayi suka hada ido, sai ta dauke kanta kamar bata gane me take magana akai ba. Suna zaune a haka har wajen minti talatin kafin kofar part din ta bud'e, ya shigo yana kokarin daidaita kallon sa akan Iman da take zaune ta dayan bangaren.

 

"Ina chan ina jiranki ashe kina nan kin ma manta dani ko?"

 

Yayi maganar yana zama a hannun kujerar da take kai

 

"Nazo gaida Ammi ne, sorry na maka text baka gani ba?"

 

"Sai yanzu na gani fa, shine nayo nan da sauri na."

 

Dariya tayi, ta dan taba shi alamun kai ko? Gyaran murya suka je, ya kalli wajen

 

"Samha! I'm so sorry na manta munyi magana kince kina nan, gaba daya hankali na yayi gaba wallahi,."

 

"Uhm ba komai, ai kana tare da Madam."

 

"Yes yes wallahi kin ganta, Baby ga Samha my classmate."

 

"Allah sarki sannu."

 

" Sannu." Tace a gajarce tana dauke kai

 

"Samha this is my wife, baki zo biki ba zamu ciki tara."

 

Yak'e tayi

 

"Bana k'asar time din, naga Amarya Allah ya sanya alkhairi, Laila ta fad'a min ai."

 

" Kin gama mu wuce?"

 

Yace yana bagarar da zancen jin ta sako maganar Laila

 

" Ai bance ma Ammi zan tafi ba."

 

" Owk bari na fad'a mata." Ya tashi shiga ciki, ya barsu su biyu, murmushi ne a fuskar Iman, a kalla taji dadi da yadda muhammad din yayi dan ta gane sarai so tayi ta kunsa mata haushi shine har da kiran sa a gabanta. Be dade da shiga ba ya dawo yace ta tashi su tafi, suka fice suka barta da bakin ciki. Suna fita ta dauki waya ta kira Laila

 

" Wai baki dawo ba?"

 

" Na kusa shigowa ki jirani."

 

" Ina nan ina jiran ki, ashe rabon zanga kayan bakin ciki, haka Muhammad yake rawar kafa akan yarinyar nan?"

 

" Me yayi?".

 

"Kinga yadda ya narke mata kamar bashi ba, kinsan dai tsaurin sa ko? Toh wallahi a gabanta kamar ruwan sanyi haka ya koma, ni kaina baki ga yadda ya amsa min a sake ba wallahi, kamar fa bashi ba."

 

" Toh an fad'a miki haka ta barshi? Bari kawai na karaso muyi magana."

 

" Shikenan kiyi sauri please."

 

Suka ajiye wayar, jefar da tata Laila tayi a gefen ta, ta shiga jan tsaki a jere cikin bacin rai.

 

 

_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

 

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)  s_*

_SO DA ZUCIYA_

 

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI'AR ZUCIYA_

 

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

 

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

 

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

 

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D’aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

 

*_Zaku tura kudin a_*

 

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

 

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

 

08184017082

 

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

 

09134848107

2/7/22, 09:08 - Buhainat: Halin Girma

      29

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

******* �

 

Tana daf da shigowa ta kira Samha tace ta wuce part dinta dan ba zata iya zuwa wajen Ammi ba, tashi tayi ta fita bayan ta saka wayarta a cikin purse dinta, taja kofar ta nufi wajen Laila din da ya kasance nata ita kadai kusa da na Kilishi. A waje suka hadu ita tana fitowa daga mota ita kuma tazo daidai bangaren, sallamar driver tayi yaran suka dauko mata kaya suka biyo ta, suka hadu suka rankaya ciki tare da Samha. Bayan sun zaune ne Lailan ta tuge mayafin kanta da yake dan yalolo da ta yane kan, ji taka kamar iska bata ratsa kan nata sosai shiyasa duk take jin ranta a jagule babu dadi, ga haushin abinda ya faru ga na karatun ta da take jin kamar ta rasa komai a yanxu.

 

"Kin ganki kuwa Queen, ya akayi haka?"

 

"Menene ma ba zaki gani ba, hmm wallahi bansan waye yayi min zagon k'asa ba, amma ko waye toh tabbas baya kaunata ko kad'an!"

 

" Kin binciki Hadimar nan? Ba kince ita kadai tasan da plan din ba."

 

Girgiza kai tayi

 

" Ba ita bace ba, someone very close to me ne, dan yadda ba kowa ke shiga part din nan ba, toh lallai wanda yake da direct access da part din ne."

 

" Lallai, gaskiya ko waye be kyauta mana ba, yanzu ya ake ciki?"

 

" Wai hakuri? Wallahi ban ba,kinsan yadda nake son Capt tun muna school haka shima kinsan kaunar da yake min ba kad'an bace, ba zan iya rayuwa da kowa ba sai shi, bayan haka kinsan matsala ta da Dr. Bryan Ford."

 

" Haka ne, toh shikenan yanzu menene next move dinki?"

 

" Har yanxu ban dawo daidai ba, I need time to recover nasan me zanyi."

 

" Shikenan, duk abinda zakiyi dai kiyi informing dina, zan baki shawara yadda ya kamata."

 

" I know I can count on you, Nagode Bestie!"

 

"DM!"

 

 Tayi murmushi yana relaxing sosai akan kujerar, tana tunanin yadda zatayi amfani da Laila ta samu cikar burin ta!

   Sai wajen tara sannan suka tafi, bayan Maman sun gama zantawa da Ammi, babbar aminiyar ta ce sama da kowa a kaf adamawa dan da ita ta fara sabawa lokacin da aure ya kawota, sannan yaransu ma tare suka taso ita tana da yara biyar compared to Ammi da take da guda daya tal...

   Zuciyar ta fari kal sanda suka isa gida, ta san ko babu komai zata dinga samun duk information din da take so ta bakin Laila, tunda tayi masifar yarda da ita fiye da yadda ma ta yarda da uwarta mahaifiya. Bata da kirki ko kad'an idan har ka shiga gonar ta, amma kuma tana masifar ganin mutuncin Samha din, dan itace tafi mata kowa a yanzu, gani take ma babu me kaunar ta sai Samha din kawai. Ko Kilishi ta san ta Kamal kawai take yi ba tata ba, shiyasa itama bata wani sanar da ita idan zatayi abu sai dai daga baya, daga Samha sai amintacciyar hadimar ta guda daya wadda zata iya bada ranta fansa ga Laila din saboda tsabar biyayyar da take mata.

  Wurgi tayi da tarkacen da ta debo daga mota tayi a saman gadon ta, ta kwanta tana kallon sama ba tare da ta cire dogon takalmin kafarta ba, murmushi take ita kadai duk kuwa da abinda Muhammad din yayi ya bakanta mata rai, amma kuma ta raina yarinyar da ya kira ta da matarsa, a shekaru ba wata babba bace haka ma wayewar rayuwar duniya sam bata cikin sahun amma kuma tana da nutsuwa a yanayin ta, da kuma iya handling abu dan yadda tayi da taji da wanda take waya ya matukar bata mamaki, kamar bata fahimci komai ba bayan sarai ta gane, kuma bata ko bi takanta ba ,ko ta tuhume shi ko ta chanja masa fuska sanda ya shigo, sai ma ta tarbi mijinta da fara'ar da ta mantar dashi komai da kowa.

  Tashi tayi tsaye ta soma zagaye a tsakanin dakin tana jin kamar taje ta jawo ta da karfin gaske ta fidda ta daga gidan, duk yadda suka kai da wayewa amma ya tsallake su ya dauko wadda bata kai ko rabin ajin sa ba, adah Laila kawai take jin haushi amma yanzu na Laila ya daina damunta, dan tasan babu wani abu da zatayi sai da sanin ta, yarinya karama ce yanzu take neman zame mata ciwon ido.

  

 

***Suna shiga part dinsu tun daga kofa ya daga ta sama, ta saki siririn ihu tana kankame shi, da gaske taji tsoro dan bata yi tunani ba, sai ji tayi anyi sama da ita, kin ajiyeta yayi sai da ya kai karshen falon sannan ya zaunar da ita ya bita ya zauna a gefenta yana dariya

 

"Kin fiyaa tsoro Allah!"

 

"Ai it was unexpected shiyasa."

 

"Ba wani, tsoro dai kawai, ki yarda, you have to be strong, kinsan dai ance a wife of a soldier is a soldier!"

 

" Wasa suke suma wallahi." Ta saka dariya

 

" Haka dai aka ce." Yayi dariyar shima

 

 

"Yawwa... Dazu na gani a WhatsApp wai anyi calling off strike?"

 

" I can't say, bari na kira naji, amma zaki koma ne? Ko a samu wata school din daban?"

 

" Duk yadda akayi yayi."

 

" Owk toh bari naji." Yace yana ciro wayar sa daga aljihu, yayi dialing number wani lecturer abokin sa, suka gaisa sannan ya tambaye shi, baa gama daidaitawa ba amma dai akwai yiwuwar komawar nan kusa. Ajiye wayar yayi ya fad'a mata yadda sukayi

 

"Matsalar k'asar nan kenan, yanzu fisabilillahi fiye da 9month ana strike amma gwamnati tayi shiru? Shikenan karatun yara ya lalace akan wani dalili mara tushe, it's so unfortunate gaskiya."

 

"Wallahi har sai mutum ma ya gaji da zaman, babu dadi sam."

 

"Dole ai, Allah ya kyauta."

 

"Amin." Tace sai sukaayi shiru, chan kuma yace

 

"Bari muga idan basu daidaita ba, kawai sai mu chanja ko Base ne, ko kuma wata private uni din na Kano."

 

"Owk Allah ya zaba mana mafi alkhairi."

 

" Amin Matata!"

 

*** Tare suka shiga ciki bayan sun kammala duk abinda ya kamata su kammala a falon, zama yayi ya kunna system ya shiga aiki ita kuma ta wuce toilet dan ta watsa ruwa tazo ta kwanta. Sharp sharp tayi wankan ta fito sanye da rigar da ta cire , be kalle ta ba, har ta isa gaban wardrobe ta dauki wata mara nauyi iyakar ta kasan guiwa, dan duk sauran kayan da take dasu anan ba zata iya kwanciya dasu ba, idan ma ta saka tasan shi, zai iya yin karfa karfa ya hanata yayi amfani da damar yayi mata wayo. A gajiye take jin ta yau din ba wai don tayi wani aiki ba, bata san dalili ba gaba daya jikin ta ciwo yake mata, wankan da tayi take saka ran zai dan saka taji dama-dama.

  Kallon ta yayi bayan ta sako rigar, yayi mata alamar tazo, ta taho ta zauna agefen sa, ya cigaba da aikin da yake na hada kan wasu takardu masu muhimmanci sosai, yana lura da ita yadda jikinta yayi sanyi sosai, jawo ta yayi bayan ya dan matsar da system din, ya kwantar da kanta a jikin shi

 

"Goodnight sweet dreams." Ya rankwafo yayi mata peck a kunci, lumshe idon ta tayi bacci na cin karfin ta sosai. Be san iya adadin awoyin da ya dauka a wajen ba, ya dade sosai har sai da ya fara jin bishi-bishi, sannan ya rufe system din, ya gyarata a hankali sannan ya tashi yana mika, alwala yayi yazo yayi sallah raka'ah biyu, ya lura da ko shafa'i da wutri da ta saba yau bata yi ba, be san wanne irin bacci take ji haka ba, dan har ya gama aikin sa ya tashi ko motsawa batayi ba. Taimaka mata yayi zuwa gadon ya kwantar da ita ya lullube mata iya kafarta, sannan ya kwanta bayan ya rage kayan jikin sa ya rage daga shi sai boxer kawai.

  Cikin dare sosai taji ishirwa, irin wadda bata taba jin irin ta ba, tashi tayi ta lallaba ta fito bayan ta duba fridge din dakin ta tuna babu ruwa a ciki, ta manta kuma bata kawo ba dan bata bar kowa cikin masu aikin sun taba shigar mata dakin ba, iyakar su falo shima dan babu yadda zatayi ne amma ko yaushe suna BQ sai wani abu me muhimmanci sannan take kiran su.

   A kitchen ta samu ruwan, tasha sannan ta dauko karamin katan na ruwan ta taho dashi. Falon yayi dim amma kuma akwai dan haske kadan da ya hasko ta corridor din kitchen da yake a kunne, kafarta take sawa a hankali tana tafiyar har ta kai tsakiyar falon, da yake falo ne katon gaske da sai kayi tafiya tsakanin kitchen da corridor din bedrooms din, motsi taji kad'an kad'an, tana matsowa yana karuwa har ta kusa kai wa corridor din abinda ta gani a wajen ya sakata daskarewa a wajen. Chak ta tsaya ta kwalla wata irin kara da ta tashi Moh daga bacci, ya mike a firgice yana kiran sunan ta, sai kuma yayi hanyar fita daga dakin da sassarfa kirjin sa na bugawa da karfi!

 

 

 

 

BIYAN BASHI ⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️😂😂😂😂😂

2/7/22, 19:06 - Buhainat: Halin Girma

      29

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

******* �

 

Tana daf da shigowa ta kira Samha tace ta wuce part dinta dan ba zata iya zuwa wajen Ammi ba, tashi tayi ta fita bayan ta saka wayarta a cikin purse dinta, taja kofar ta nufi wajen Laila din da ya kasance nata ita kadai kusa da na Kilishi. A waje suka hadu ita tana fitowa daga mota ita kuma tazo daidai bangaren, sallamar driver tayi yaran suka dauko mata kaya suka biyo ta, suka hadu suka rankaya ciki tare da Samha. Bayan sun zaune ne Lailan ta tuge mayafin kanta da yake dan yalolo da ta yane kan, ji taka kamar iska bata ratsa kan nata sosai shiyasa duk take jin ranta a jagule babu dadi, ga haushin abinda ya faru ga na karatun ta da take jin kamar ta rasa komai a yanxu.

 

"Kin ganki kuwa Queen, ya akayi haka?"

 

"Menene ma ba zaki gani ba, hmm wallahi bansan waye yayi min zagon k'asa ba, amma ko waye toh tabbas baya kaunata ko kad'an!"

 

" Kin binciki Hadimar nan? Ba kince ita kadai tasan da plan din ba."

 

Girgiza kai tayi

 

" Ba ita bace ba, someone very close to me ne, dan yadda ba kowa ke shiga part din nan ba, toh lallai wanda yake da direct access da part din ne."

 

" Lallai, gaskiya ko waye be kyauta mana ba, yanzu ya ake ciki?"

 

" Wai hakuri? Wallahi ban ba,kinsan yadda nake son Capt tun muna school haka shima kinsan kaunar da yake min ba kad'an bace, ba zan iya rayuwa da kowa ba sai shi, bayan haka kinsan matsala ta da Dr. Bryan Ford."

 

" Haka ne, toh shikenan yanzu menene next move dinki?"

 

" Har yanxu ban dawo daidai ba, I need time to recover nasan me zanyi."

 

" Shikenan, duk abinda zakiyi dai kiyi informing dina, zan baki shawara yadda ya kamata."

 

" I know I can count on you, Nagode Bestie!"

 

"DM!"

 

 Tayi murmushi yana relaxing sosai akan kujerar, tana tunanin yadda zatayi amfani da Laila ta samu cikar burin ta!

   Sai wajen tara sannan suka tafi, bayan Maman sun gama zantawa da Ammi, babbar aminiyar ta ce sama da kowa a kaf adamawa dan da ita ta fara sabawa lokacin da aure ya kawota, sannan yaransu ma tare suka taso ita tana da yara biyar compared to Ammi da take da guda daya tal...

   Zuciyar ta fari kal sanda suka isa gida, ta san ko babu komai zata dinga samun duk information din da take so ta bakin Laila, tunda tayi masifar yarda da ita fiye da yadda ma ta yarda da uwarta mahaifiya. Bata da kirki ko kad'an idan har ka shiga gonar ta, amma kuma tana masifar ganin mutuncin Samha din, dan itace tafi mata kowa a yanzu, gani take ma babu me kaunar ta sai Samha din kawai. Ko Kilishi ta san ta Kamal kawai take yi ba tata ba, shiyasa itama bata wani sanar da ita idan zatayi abu sai dai daga baya, daga Samha sai amintacciyar hadimar ta guda daya wadda zata iya bada ranta fansa ga Laila din saboda tsabar biyayyar da take mata.

  Wurgi tayi da tarkacen da ta debo daga mota tayi a saman gadon ta, ta kwanta tana kallon sama ba tare da ta cire dogon takalmin kafarta ba, murmushi take ita kadai duk kuwa da abinda Muhammad din yayi ya bakanta mata rai, amma kuma ta raina yarinyar da ya kira ta da matarsa, a shekaru ba wata babba bace haka ma wayewar rayuwar duniya sam bata cikin sahun amma kuma tana da nutsuwa a yanayin ta, da kuma iya handling abu dan yadda tayi da taji da wanda take waya ya matukar bata mamaki, kamar bata fahimci komai ba bayan sarai ta gane, kuma bata ko bi takanta ba ,ko ta tuhume shi ko ta chanja masa fuska sanda ya shigo, sai ma ta tarbi mijinta da fara'ar da ta mantar dashi komai da kowa.

  Tashi tayi tsaye ta soma zagaye a tsakanin dakin tana jin kamar taje ta jawo ta da karfin gaske ta fidda ta daga gidan, duk yadda suka kai da wayewa amma ya tsallake su ya dauko wadda bata kai ko rabin ajin sa ba, adah Laila kawai take jin haushi amma yanzu na Laila ya daina damunta, dan tasan babu wani abu da zatayi sai da sanin ta, yarinya karama ce yanzu take neman zame mata ciwon ido.

  

 

***Suna shiga part dinsu tun daga kofa ya daga ta sama, ta saki siririn ihu tana kankame shi, da gaske taji tsoro dan bata yi tunani ba, sai ji tayi anyi sama da ita, kin ajiyeta yayi sai da ya kai karshen falon sannan ya zaunar da ita ya bita ya zauna a gefenta yana dariya

 

"Kin fiyaa tsoro Allah!"

 

"Ai it was unexpected shiyasa."

 

"Ba wani, tsoro dai kawai, ki yarda, you have to be strong, kinsan dai ance a wife of a soldier is a soldier!"

 

" Wasa suke suma wallahi." Ta saka dariya

 

" Haka dai aka ce." Yayi dariyar shima

 

 

"Yawwa... Dazu na gani a WhatsApp wai anyi calling off strike?"

 

" I can't say, bari na kira naji, amma zaki koma ne? Ko a samu wata school din daban?"

 

" Duk yadda akayi yayi."

 

" Owk toh bari naji." Yace yana ciro wayar sa daga aljihu, yayi dialing number wani lecturer abokin sa, suka gaisa sannan ya tambaye shi, baa gama daidaitawa ba amma dai akwai yiwuwar komawar nan kusa. Ajiye wayar yayi ya fad'a mata yadda sukayi

 

"Matsalar k'asar nan kenan, yanzu fisabilillahi fiye da 9month ana strike amma gwamnati tayi shiru? Shikenan karatun yara ya lalace akan wani dalili mara tushe, it's so unfortunate gaskiya."

 

"Wallahi har sai mutum ma ya gaji da zaman, babu dadi sam."

 

"Dole ai, Allah ya kyauta."

 

"Amin." Tace sai sukaayi shiru, chan kuma yace

 

"Bari muga idan basu daidaita ba, kawai sai mu chanja ko Base ne, ko kuma wata private uni din na Kano."

 

"Owk Allah ya zaba mana mafi alkhairi."

 

" Amin Matata!"

 

*** Tare suka shiga ciki bayan sun kammala duk abinda ya kamata su kammala a falon, zama yayi ya kunna system ya shiga aiki ita kuma ta wuce toilet dan ta watsa ruwa tazo ta kwanta. Sharp sharp tayi wankan ta fito sanye da rigar da ta cire , be kalle ta ba, har ta isa gaban wardrobe ta dauki wata mara nauyi iyakar ta kasan guiwa, dan duk sauran kayan da take dasu anan ba zata iya kwanciya dasu ba, idan ma ta saka tasan shi, zai iya yin karfa karfa ya hanata yayi amfani da damar yayi mata wayo. A gajiye take jin ta yau din ba wai don tayi wani aiki ba, bata san dalili ba gaba daya jikin ta ciwo yake mata, wankan da tayi take saka ran zai dan saka taji dama-dama.

  Kallon ta yayi bayan ta sako rigar, yayi mata alamar tazo, ta taho ta zauna agefen sa, ya cigaba da aikin da yake na hada kan wasu takardu masu muhimmanci sosai, yana lura da ita yadda jikinta yayi sanyi sosai, jawo ta yayi bayan ya dan matsar da system din, ya kwantar da kanta a jikin shi

 

"Goodnight sweet dreams." Ya rankwafo yayi mata peck a kunci, lumshe idon ta tayi bacci na cin karfin ta sosai. Be san iya adadin awoyin da ya dauka a wajen ba, ya dade sosai har sai da ya fara jin bishi-bishi, sannan ya rufe system din, ya gyarata a hankali sannan ya tashi yana mika, alwala yayi yazo yayi sallah raka'ah biyu, ya lura da ko shafa'i da wutri da ta saba yau bata yi ba, be san wanne irin bacci take ji haka ba, dan har ya gama aikin sa ya tashi ko motsawa batayi ba. Taimaka mata yayi zuwa gadon ya kwantar da ita ya lullube mata iya kafarta, sannan ya kwanta bayan ya rage kayan jikin sa ya rage daga shi sai boxer kawai.

  Cikin dare sosai taji ishirwa, irin wadda bata taba jin irin ta ba, tashi tayi ta lallaba ta fito bayan ta duba fridge din dakin ta tuna babu ruwa a ciki, ta manta kuma bata kawo ba dan bata bar kowa cikin masu aikin sun taba shigar mata dakin ba, iyakar su falo shima dan babu yadda zatayi ne amma ko yaushe suna BQ sai wani abu me muhimmanci sannan take kiran su.

   A kitchen ta samu ruwan, tasha sannan ta dauko karamin katan na ruwan ta taho dashi. Falon yayi dim amma kuma akwai dan haske kadan da ya hasko ta corridor din kitchen da yake a kunne, kafarta take sawa a hankali tana tafiyar har ta kai tsakiyar falon, da yake falo ne katon gaske da sai kayi tafiya tsakanin kitchen da corridor din bedrooms din, motsi taji kad'an kad'an, tana matsowa yana karuwa har ta kusa kai wa corridor din abinda ta gani a wajen ya sakata daskarewa a wajen. Chak ta tsaya ta kwalla wata irin kara da ta tashi Moh daga bacci, ya mike a firgice yana kiran sunan ta, sai kuma yayi hanyar fita daga dakin da sassarfa kirjin sa na bugawa da karfi!

 

 

 

 

BIYAN BASHI ⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️⛹️😂😂😂😂😂

2/7/22, 19:06 - Buhainat: Halin Girma

      30

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

******* �

 

A durkushe ya ganta tana kuka ta rik'e kanta, saurin durkusawa yayi a gabanta yana janye hannun nata

 

"Menene?"

 

"Miciji!"

 

Tayi maganar tana nuna masa wajen, saurin kalla yayi amma be ga komai ba, ya yunkura zai tashi ta kankame shi sosai tana fashewa da kuka. Hannun ta ya kama zuwa wajen switch din falon, ya kunna haske ya bayyana a ilahirin falon, wurwurga idonsa ya dinga yi a gaba dayan falon amma be ga komai ba,

 

"Aina kika ganshi?"

 

"Adaidai nan zai shiga dakin chan!"

 

"Tsaya ." Ya tsaida ita yana sake dubawa amma babu komai. Riketa yayi ya kaita daki, tayi saurin rikeshi ganin zai fita

 

" Dan Allah karka fita ka barni."

 

" Kinaji? Calm down babu abinda zai faru, yanzu zan dawo.".

 

Sakin sa tayi, ya fita ya taso securities din a gaba, suka zo suka hau bincika falon da ko ina na part din,ciki ya koma ya sameta ta kudundune a saman gadon still jikinta be bar rawar da yake ba, tana addu'a kasa kasa, daga gani kasan ta tsorata sosai dan bata taba ganin shi haka a zahiri ba. Jawota yayi jikin sa, ya mannata da kirjinsa yana shafa mata baya kad'an kad'an.

 

" Babu abinda zai faru kinji? Ki kwantar da hankalin ki."

 

Da kai ta amsa masa, zuwa lokacin ta fara dawowa nutsuwar ta, sai wani uban juyi da taji cikin ta nayi,ta dora hannun ta a saman cikin yana yatsine fuska, kallon hannun nata yayi, ya dauki nasa ya dora a saman nata yana tayata shafa cikin,

 

"Ciwo?"

 

"Eh."

 

"Sannu zai daina, bari na dubo ko sun gama dubawar."

 

Ya kwantar da ita ya fita, a tsaye ya same su rik'e da abu me kama da maciji, matsawa yayi yana dubawa cikin son karin bayani

 

"Macijin roba ne ranka ya dade!"

 

"Roba?" Yace cikin yanayin mamaki

 

"Me ya kawo shi nan? Me yasa bamu ganshi ba tun da rana sai yanzu..."

 

"Waye da waye suka shigo part din nan?" Ya fad'a yana daure fuskarsa tamau. Rantse rantse suka hau yi, kowa na son kare kansa, wata uwar tsawa ya daka musu, duk suka nutsu suka kame suna masu saukar da kansu k'asa

 

"Kwana daya tal na baku, ku gano wanda ya shigo part din nan har ya ajiye wannan shirmen, koma waye sai ya fuskanci hukunci me tsanani!"

 

" Yes sir!"

 

Har ya juya sai kuma ya tsaya.

 

" Get ready, we are leaving tomorrow in the afternoon!"

 

" Yes sir!"

 

Suka kara hada baki wajen fad'a sannan ya juya ya bar su a wajen da sassarfa. Dayan dakin ya shiga, ya hau bincike wasu kaya da sauri da sauri, ba zai yarda a taba masa ita ba, idan har ba zasu iya tsayawa iya kansa kawai ba, toh zai yi abinda zai girgiza su matuka. Ya dan dau lokaci a dakin, sai da ya tuna ya barta ita kadai ya kuma san tsoro take ji, sannan ya koma da sauri, ya tarar bacci ya dauke ta, ta takure waje daya tana fitar da numfashi kad'an kad'an. AC din dakin ya rage, zuwa low ya dawo ya gyara mata kwanciyar, ya kura mata ido yana jin son ta na kara ruruwa a zuciyar sa, ba zai bari banzar al'adar gidan su ta taba ta ba, zai yi duk abinda zai yaga ya kareta da dukkan karfin da yake dashi.

   Da asubah ya tashe ta, sukayi sallah a dakin, sannan ya fita ya shigo mata da micijin robar yana mata dariya

 

"Matsoraciya, nina fa na shigo dashi jiya by mistake, abun wasan yaran chan ne suka bani, ashe sai na yar dashi ban ma lura ba."

 

Shiru tayi tana kokarin daidaita maganganun nasa da abinda ta gani, idan har ba gizo idon ta yayi mata ba, toh tabbas tafiya ta ganshi yana yi, har ya kai kofar dakin kafin ta daina ganin sa.

 

"Common!" Yace yana son dauke tunanin ta

 

"Babu komai fa I promise you."

 

"Amma na ganshi fa yana motsi!"

 

"Imagination ne kawai nothing else, karki damu ki kwantar da hankalin ki."

 

Shiru tayi tana kallon sa, yanayin sa yayi mata kama da na wanda yake so ya dauke hankalin ta, amma idan ba haka ba babu yadda za'a yi taga abu yana tafiya da idonta ya zama imagination kuma, hore mata idon yayi yana jawo ta jikinsa

 

"Karki yi ta tunani kinji? Anjima zamu wuce ma, Abuja zamu fara zuwa na gaida Mummy, daga nan muyi tafiyar mu gidan mu mu sha soyayyar mu."

 

"Da gaske?"

 

"Da gaske mana, are you happy?"

 

"Naji dadi sosai, bari na fara hada kaya na, da wuri zamu tafi ko? Ko sai da yamma."

 

"Yamma!"

 

Komawa tayi ta zauna tana jin kamar yamman ya mata tsayi

 

"Zanga Aji ne, sannan bana son kowa yasan mun tafi sai Ammi kawai, shiyasa ba zamu dauki yaran chan ba, i mean ma'aikatan gidan, akwai screening da za'a yi musu kafin su biyo mu."

 

" Owk Allah ya kaimu."

 

" Amin my beautiful wife."

 

Murmushi tayi, ya dauko musu al'qurani me girma suka shiga karantawa, ya dinga admiring muryarta da yadda take bawa kowanne harafi hakkin sa, cikin nutsuwa da fitar da tajweed a duk in da ya dace. Sai da rana ta fito, sannan sukayi wanka, suka shirya a tare suka fita don karyawa, bud'e warmers din yayi, ya kakkala sannan ya saka aka kwashe masa su daga wajen, ya aika part din Ammi aka karbo musu breakfast din, taso ya barta tayi amma ya hanata, ya kuma ki gaya mata dalilin da ya saka shi sawa a kwashe abincin da aka girka a part din, bata ce komai ba, ta barshi a zuwan kawai zata ji koma menene daga baya, dan ta lura yadda ya boye masa kanta kafin aure akwai abubuwa da yawa da yake boyewa a yanzu ma, duk da haka ba zata zarge shi ba, zata bashi lokaci sosai ta kara fahimtar shi, jikinta na bata akwai wani abu da shi kadai ya sani, sai ko Aji da take ganin kusancin su yafi na kowa hatta mahaifiyar sa da mahaifin sa.

  Bayan sun gama breakfast din ne ya fita, cikin shigar kayan sojoji da suke masifar yi masa kyau, cikin rakiyar yaransa ya nufi part din Kilishi, wanda tun kafin ya karasa sakon zuwa nasa ya ishe mata, tana zaune ta gama karyawa, tashi tayi da sauri ranta na baci, tasan zuwan sa babu abinda yake jawo mata sai bacin rai. Daki ta shiga ta chanja kaya, ta zauna tana jiran sanarwar isowar sa. Tana jin sanda ya shigo, dan har falon ta na ciki ya shigo, ya zauna fuskar sa fes dauke da farin ciki, idonsa na kan kofar da zata fito, ya dan dauki lokaci a zaune har ya fara tunanin ko ba zata fito ba, agogon hannun sa ya kalla, ya daga kai ya kalli na jikin bangon dakin, a tare suke tafiya dakiya daya, sauke idon sa yayi yana murza agogon nasa, takun tafiya yaji, yaki d'agowa amma yasan itace,sai da ta zauna sannan ya dago yana dubanta, yayi murmushi cikin salon girmamawa yace

 

"Barka da gida ranki ya dade."

 

"Barka dai, ya iyali?"

 

"Lafiya kalou kalou, kamar yadda kike fata a kowanne lokaci."

 

Yak'e tayi, tasan magana ya fad'a mata, dan ya saba gasa mata ita dama, murmushi ya sake yi yana lankwasa hannayen sa baya

 

" Haka ake so ai, sai a sake kula sosai."

 

" In Sha Allah, za'a kula kulawa me kyau, duk wani me sharri Allah zai maida masa kansa ma, saboda addu'a itace makamin mumini, kuma matakin duk wata nasara."

 

" Haka ne!" Tace tana gid'a kanta. Mikewa yayi cikin salo na burgewa, ya dan rankwafa yace

 

" Na barki lafiya!"

 

" Nagode!" Tace tana danne zuciyar ta, bayan sa tabi da kallo har ya fice gaba daya,

 

"Ahhhh!" Tayi kara tana jifa da trow pillow din dake kusa da ita,kamar ta shako shi haka taji, gashi kamar masifa yasan duk wani shirin ta, ta rasa yadda zatayi dashi ya zame mata tamkar kadangaren bakin tulu! Ya kuma zame mata ciwon ido, da za'a bata makami ace ta kashe mutum daya toh tabbas shi zata kashe, bata son ko ganin wulgawar sa.

   Laila ce ta shigo, ta tarar da ita cikin halin da take ciki na bacin rai, bin ta tayi da kallo har ta dauki jakar ta, ta bud'e ta dauki ATM cards din Kilishin, ta juya zata bar dakin.

 

"Laila!" Tsayawa tayi ta juyo

 

"Ina zaki? Me kuma zakiyi da Atm dina?"

 

"Haba Mah, tunda har na dauka ai amfani zan dashi."

 

" Shine ba zaki iya fada min ba?"

 

" Da ma fa na saba dauka kuma bana fad'a miki, why now?" Sai ta juya ta cigaba da tafiyar ta

 

" Zan dawo dashi wani payment kawai zan." Sai data kai karshen kofar sannan ta fad'a, ta saka kai tayi ficewar ta, kwafa Kilishin tayi ba tare da ta sake cewa komai ba.

 

****Bayan fitar sa ne tana zaune da waya a hannun ta suna chatting sama-sama da Ya Maryam,rabin hankalin ta na kan Tv sai tana duba sakon lokaci zuwa lokaci, ta kira Abba bata same shi ba, kila ko ya fita ko kuma baya kusa da wayar. Kara wayarta tayi a tunanin ta Abban ne, sai taga number Ya Maryam ce, dauka tayi tana tashi zaune

 

"Ina ta magana a whatspp kin sauka, yanzu aka kira ni a gida Aunty Bilki ta haihu!"

 

" Dan Allah!"

 

" Wallahi yanzun nan kuwa ta haihu."

 

" Masha ALLAH, me aka samu?"

 

" Ina ma na tsaya tambaya? Murna ta saka ni kiranki, kinga al'amarin Allah, bayan ta cire rai, dama ba'a cire rai da  rahmar Allah."

 

" Wallahi, kai Masha ALLAH, nayi murna sosai Allah ya bata lafiyar shayarwa."

 

" Amin ya Allah, zuwa kano ya kamaki."

 

" Gaskiya, dama yau zamu bar nan din, amma Abuja zamu wuce daga nan zamu dawo Kanon."

 

" Ah shikenan ma, ki kirata toh kafin nan, bari na kira Amira itama na fesa mata."

 

" Owk ki tura min number ta, Inaga kamar bani da ita yanzu."

 

" Ok tam, zan ajiye miki a WhatsApp."

 

" Yawwa."

 

Ajiye wayar tayi farin ciki na kamata, after all a karshe dai itama ta samu nata babyn, shekara ashirin da aure amma bata taba ko batan wata ba, sai yanzu Allah yayi, dama dai sunji kishin kishin din ciki ne da ita musamamn da bata zo bikin da akayi ba, sai mutane suka kara tabbatar da zargin su, boye labarin sukayi sun fi so kawai aji haihuwa daga sama. Duk da bata da yawan magana amma tana masifar son kananan yara, musamman jarirai zuwa 4years haka, ko magana sukayi sai taji dadi, shiyasa take son kaninta Marwan ba kuma tajin komai idan Mama ta sakata aikin sa.

   Daukar number aunty bilkin tayi, ta kirata tayi mata murna sosai, suna wayar kiran Abba ya shigo, ta katse na Aunty Bilkin ta daga nasa suka gaisa, anan yake fad'a mata labarin haihuwar ta nuna kamar bata sani ba tayi farin ciki sosai, bayan sun gama wayar ne ta kira Mamma take fad'a mata zuwan su, amma bata san ko a yau din zasu iso ba ko sai gobe dai, murna tana jiyo su Amaan ta wayar kamar zasu shigo ciki saboda karadin su.

  

 

***Tana idar da sallar la'asar sai gashi ya shigo, ba kayan da ya fita dasu bane a jikin sa, wasu ne daban da sukayi mata kama da sababbin da ba'a taba sakasu ba, gaishe shi tayi a ladabce tana daga kan sallayar, ya amsa yana zama, yanayin sa ya nuna a gajiye yake, sai ta tashi ta ninke sallayar ta ajiye ta nufi kitchen ta dauko masa ruwa da soft drink, akan tray ta doro ta dawo falon ta ajiye masa tana rissinawa, saurin tayata yayi yana hadawa da hannun ta da tray din, sukayi dariya a tare ta zauna a gefen sa tana zuba masa ruwan. Karba yayi yasha, sosai saboda tunda ya fita be saka komai a cikin sa ba, gashi sam baya jin yunwa so yake kawai su tafi.

 

"Ga abinci akan dinning ko na kawo maka nan?"

 

"Waye yayi?"

 

"Nice."

 

"Owk zanci, amma ki zubo min a plate ba da yawa ba, sai ki taimaka min da fruit please,."

 

"Ok." Ta mike bayan ta karbi cup din ruwan ta ajiye, taje ta zubo masa abincin ta kawo ta koma ta yanko fruits din ta kawo, yana kwance ya mike kafafunsa, har sai data zauna a gaban abincin sannan ya sakko yana saka spoon din a gaban sa ya soma cin abincin hankalin sa a kwance, sosai yaci dan beyi tunanin zai ci kamar haka ba, sannan ya sha fruits din kadan, bayan ya gama yace

 

"Thank you...Abincin yayi dadi."

 

Blushing tayi cikin jin dadin yabon da yayi mata, ta hau tattare kayan zata kwashe ya rik'e mata hannu

 

"Ki barshi yaran chan zasu gyara idan mun tafi."

 

"Ai ba wahala, bari na kwashe kawai."

 

Sakin hannun nata yayi, ta dauki tray daya, cikin takun da bata san tana dashi ba, ta shiga takawa zuwa kitchen din, kallon ta yake har ta kule kafin ya dawo hayyacin sa, yana kallo ya sake dawowa ta kwashe sauran ya sake bin steps din nata da kalllo, ba zai iya hakura ba, musamamn idan ciki ya dauka, ga kuma abunka da sabon angon da be san ya isa ba, tashi yayi har da dan saurin sa, ya sameta a kitchen din tana tattare dattin plates din, sam bata ji shigowar sa ba, sai ji tayi an rungume ta, ta baya. Ta juyo a dan tsorace kafin kamshin turaren sa ya mamaye ilahirin kitchen din.

   Manne bayan su yayi waje daya, ya dora kansa saman gadon bayanta, ya shiga goga mata bayanta da kan nasa.

 

"Ba... Bari... Na karasa gyara kayan."

 

"Barshi, ai dama ba aikinnki bane, ga aikin lada me yawa."

 

Ya sake chusa kansa sosai, tsam ta dauke hannun ta, sanda taji hannun sa na yawo a daidai tsakiyar cikin ta, yana shafawa har zuwa kasan rigar ta, rik'e jikin kitchen cabinet din tayi dan ji tayi kamar zata fadi, Allah yaso ta dafe wajen. Daga ta yayi sama chak, ya wuce falon zuwa bedroom dinsu, ya dire ta yana mata murmushin mugunta,  a matukar tsorace take dashi amma kuma ba zata hanashi ba, dan ba zai taba bata damar da zata hanashin, yabi ya kanainayeta da salon kaunar shi me tsayawa a makoshi!

   Sai da suka bata lokaci sosai, dan har wani dan guntun bacci yayi bayan nan, da k'yar ta tashe shi yayi wanka ya shirya, suka fita a mota zuwa wajen Ammi, daga nan suka fice daga masarautar da magribar fari!

 

***

Tun bayan fitar sa bata tashi daga wajen da take ba, sai da taji yunwa na neman kai ta k'asa, ta tashi ta jawo ledar da ya bari ta cinye ragowar,tasha ruwa ta kwanta a wajen.

   Har wajen takwas na dare Hajiyan bata dawo ba, turo dakin akayi, ta dago tana kallon sa, tashi tayi zaune da sauri tana kare jikin ta, murmushi yayi ya zauna a kusa da ita, ya ciro wayar sa a aljihu ya rik'e a hannun sa yace

 

"Zan kira miki Mama,dan ta kira tana son magana dake nace mata wayarki ce ta lalace, idan kika kuskura kika fad'a mata wani abu sai ranki ya baci."

 

Banzan kallo tayi masa, ta warci wayar lokacin da taji tana ringing, bata jira Maman tayi magana ba ai tana jin ta daga ta rushe da kuka,

 

"Lafiya Zeenat, wannan kukan fa?" Tace a kidime tana saka handsfree dan Habib yaji shima

 

"Mama dan Allah kice wa Abba yayi hakuri na tuba, dan Allah!"

 

" Ki nutsu ki fad'a min abinda yake faruwa, menene?"

 

" Bana son auren nan Mama, dan Allah kizo ki tafi dani wallahi zan mutu!"

 

" Mutuwa? Me yayi miki Bashir din?"

 

Shiru tayi ta rasa me zata ce, dan bata isa ta fadi abinda ya faru tsakanin ta da Bashir din ba, a sanyaye tace

 

" Mama yana da Mata, kullum sai ta sakani aikin wahala babu dare babu rana, ga tsangwama, karshe ma Mama a BQ nake wallahi." Sai ta sake fashewa da wani kukan,salati Mama ta saka, ta kama zagaye a dakin tana jin bayanin Zeenat din

 

" Yana ina, bashi wayar."

 

Tun kafin ta bashi ya karba yana mata murmushi,

 

" Hello Mama."

 

" Kana ji? Wallahi tun muna shaida juna da kai ka dawo min da 'yata, wannan ai wulakanci ne, wallahi ka dawo min da ita kafin kasha mamaki na."

 

" Kiyi hakuri Mama, amma Zeenat matata ce,a yanzu nine nake da iko da ita,dan haka kiyi hakuri dai."

 

" Kan bala'i, ni kake fadawa haka Bashir?"

 

" Ayi hakuri Mama, gaskiya ce, sai mun sake kira mu gaishe ki."

 

Kafin ta sake magana ya kashe kiran, ya kuma kashe wayar gaba daya ya jefa ta aljihun sa, yayi gaba zai bar dakin ta chakumo shi ta baya

 

" Na rantse da Allah sai ka rabu dani,sai ka sake ni wallahi ba zan zauna ba, na tsane ka bana son ganin ka."

 

Maganganun ta sun masa zafi kwarai, amma sai ya danne ya jawota ya hadata da bangon dakin, ya dalle mata baki sannan ya bi ta da kiss me zafi.

 

"Idan kika sake yi min ihu wallahi sai nayi fata-fata dake, aure na dake babu saki ko yaji, auren mutukaraba kenan, ko nace miki auren zobe, idan bakiyi wasa ba sai na tabbatar miki da haka a yau din nan, ta hanyar zuba miki ajiyar da baki isa ki guje min ba."

 

Tofar da yawu tayi ta durkushe a wajen tana sakin kuka gwanin tausayi. Tsallake ta yayi, yayi ficewar sa yana dariyar mugunta, yana son Zeenat din da gaske, amma kuma ba zai dauki rashin kunyar ta ba, ko kuma ya kyale iyayenta su taka shi ba, sai abinda yaga dama zai yi da ita tun da dai shine me iko da ita a yanzu.

Post a Comment for "HALIN GIRMA 26-30"