HALIN GIRMA 21-25
1/31/22, 19:12 - Buhainat: Halin Girma
   21
Ta kofar ya koma ya fice bayan ya tabbatar da ya isar mata da
sakon da yake son isarwa, yana kallon yadda tayi laushi sosai ta bishi da kallo
har ya fice gaba daya.
  Kai tsaye wayar sa ya dauka ya kira Bashir, ya
daga yana tafiya zuwa shashen Takawa dan yana son ganin shi
"Ya akayi Bashir?"
"Barka da warhaka Ranka ya dade"
" Barka dai, ya taro?"
" Mun gode Allah, an kawo amarya yallabai."
" Yayi kyau, Allah ya baku zaman lafiya, ka kula da ita
sosai kar naji wani abu mara dadi, karka kuma taba yarda mahaifiyar ta ko wani
yace zai taka ka akan matar ka."
" In Sha Allah ranka ya dade, hakan ba zata faru ba."
"Yayi kyau, sakon ka na wajen Musaddik."
Godiya ya hau yi dan dama abinda ya saka kiran kenan. Cilla
wayar yayi a aljihu sanda ya isa sashen Takawan da ya zata ya jima da isa a
adamawa.
***A tsorace take tun bayan da mutane suka yaye, yan matan biyu
da aka barta dasu suma basu wani jima ba suka cikawa wandon su iska dan ba zasu
iya zaman ba, babu kalar ma da bata yi musu ba akan su zauna amma suka ki, a
cewar su idan suka zauna basu san uban da zai maida su gida ba su ba samari
masu mota ba ga unguwar da shegen nisa kafin kaje titi. Haka tana ji tana gani
suka yi tafiyar su suka barta. Tasha kuka kuwa kamar ba zata mutu, ta dinga tsinewa
Bashir albarka taji kamar ta gudu ta bar garin ma baki daya.
  Tana nan a zaune cikin duhu taji ana saka mukulli
a kofar gidan, tashi tayi da sauri tana zaro ido,a duhu take dan dama da wayar
ta, ta haska kuma babu charge ta mutu tun dazu.
  Shigowa yayi yana haske gidan da wayar sa, ya
shigo ciki ya dalle ta, tayi saurin kare fuskar ta tana cewa
"Waye!" A tsorace
"Amarsu ta ango."
Wani abu ne ya tokare mata a makoshi jin muryar sa, tayi kansa
da sauri ta hau kai masa duka tana kuka
"Allah ya isa ban yafe maka ba, Allah ya isa."
Rik'e hannun nata yayi da karfi ya juyar da ita ta dawo tana
jingina da bayan sa
"Ni kike wa Allah ya isa? Lallai ma yarinyar nan."
"Allah ya isa na fad'a mugu, macuci maha'inci."
Juyo da ita yayi ransa na soyuwa amma ya danne kamar be ji komai
ba, ya dalle mata baki da bayan hannun sa, yayi murmushi yana sake haske ta
"Duk abinda ma zaki ce ki fad'a amaryata."
Kuka ta shiga rusa wa da karfi, ganin zata iya jawowa a jiyo su
a makota ya sakashi jawota ya shiga sumbatar ta, ta dinga dukansa tana harbin
sa a kafa amma ko a jikin sa, sai da ya gajiyar da ita sosai sannan ya saketa
yana murmushin, a kalla ya rage zafi dan yasan ba lallai Hajjaju ta yarda ta
barshi ba.
  A wajen ta duk'a tana kuka, ta dinga jin kamar ta
mutu ta huta da abinda take ji, tana jinshi yana waya har ya gama kafin ya
dagata tsaye ya rik'e hannun ta a cikin nasa su shiga barin gidan.
  Mota ce a kofar gidan irin wadda yake zuwa wajen
ta zance, bud'e mata gaba yayi ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga
mazaunin driver ya tada motar suka bar unguwar.
  Tafiya sukayi da dan nisa har suka iso unguwa,
gangarawa taga yayi zuwa wata doguwar hanya suka dinga tafiya kafin su isa
kofar wani babban gida, horn taga yayi da sauri me gadin ya bud'e gidan ya
shiga da motar ciki. Tunanin ta ne ya tafi wani waje daban, ko dai Bashir gwada
ta yake yana so yaga yadda zatayi idan ya kaita wanchan gidan shiyasa ya kai
ta? Ko kuma dai duk shiri ne. Murmushi ya sakar mata ta cikin hasken da ya
hasko cikin motar bayan ya tsaya a gaban ginin gidan.
  Sauri taga yayi ya bud'e motar sanda wata babbar
mata hamshakiya ta nufo su cikin wata irin kwalliya, ta sha ado sosai tana
walwali, katuwar gaske ce dan zatayi biyu ko ma ukun Bashir din idaan aka hade
shi da Zeenat din waje daya.
  Kafin ta kai ga garasowa Bashir din ya isa
wajenta. Yayi kamar zai zube a k'asa a gabanta, ta riko shi tana masa murmushi,
ware ido sosai Zeenat tayi tana tunani toh ko Maman shi ce? Karasowa tayi
daidai kofar da Zeenat din take ciki ta bud'e mata tana sakar mata murmushi
"Amarya."
Ta kira ta tana sakin hannun Bashir din ta kama na Zeenat din
tana jawo ta daga ciki.
"Sannu da zuwa kanwata, sannu sannu."
"Kanwata?"
Zeenat ta maimaita sunan tana bin Bashir da kallon neman karin
bayani amma sai taga ya fuske kamar be ganta ba. Takawa suka shiga yi har zuwa
cikin gidan wani babban falo da yasha kawa sosai. Wasu mata ne hamshakai suma
kamar matar farkon suka tarbi Zeenat din suna tafi, ita dai Zeenat gaba daya
kanta ya kulle jira take su samu kebewa da Bashir ta tambaye shi me yake
faruwa. Zaunar da ita matar tayi ta ja hannun Bashir din sauran mstan suka hau
shewa da dariya, bin su Zeenat tayi da ido har suka haura sama, zuwa anjima kad'an
sai gata ta sakko ita kadai babu Bashir din cikin shigar kayan bacci ta karaso
falon ta kalli sauran matan tace
"A rakata dakin ta ko?"
"An gama Lay, an gama."
Suka tashi gaba daya, daya ta kama Zeenat din suka nufi wata
hanya da take a bayan kafar benen dake falon, wani dogon corridor ne suka bishi
har zuwa bayan dakunan gidan, sai wani daki guda daya a wajen da kofar sa tana
kallon kofar da suka fito, nan taga an bud'e, sannan sun shiga gaba daya ciki.
  Katifa ce a k'asa karama kamar ta yan boarding
sai wata karamar kujerar roba fara, suna shiga kamar jira dama suke matar da ta
shigo da ita ta wurgar da ita a saman kujerar har sai da kanta ya bugu da
bango, tayi kara saboda zafin da taji kafin wadda suke kira da Hajiya Lay
(Layuza) ta rankwafo akanta tana mata kallon tsana tace
"Ke dan yar iska ce ke, har kin isa mu hada miji daya? Kin
isa nayi sharing dake? Karamar yarinya da bata fi sa'ar yata karama ba, kece
kishiyata ko? Toh ni ko a zamanin kuruciya ban zauna da kishiya ba balle yanzu
da nasan ciwon kaina nasan abinda nake so, dan haka nan dakin da nake ajiye
masu aiki nane kuma na sallame su dan yanzu basu da amfani, sai ki cigaba daga
in da suka tsaya, shara wanke wanke, wankin undies dina da girki, komai ma dai
da kika sani."
Gaba daya kwakwalwar Zeenat ta gaza gane me matar take cewa, ji
tayi kamar wani yare take mata na daban da bata sanshi ba, ta dinga jujjuya
kanta tana son gasgata abinda taji akan Bashir din, yana da mata dama? Mata
babba kamar wanna da ta yi sa'ar uwarsa? Abba ne ya fado mata, sanda ya kirata
yake mata magiya kamar ba Mahaifin ta ba, ya kaskantar da kansa yana rokon ta
akan ta rufa masa asiri ta hakura da Bashir amma ta shafawa idon ta toka, ta
kekeshe kasa tace taji ta gani, yanzu ta yaya hakkin Abban ta zai barta? Tun a
ranar farko ta fara fuskantar wannan tashin hankalin.
  Firgigit tayi sanda taji saukar abu kamar ruwa
asaman fuskar ta, ta saka hannu ta shafa da sauri tana daga kanta
"Kinji abinda na fad'a miki ko?"
A hankali ta daga kanta alamar eh, ta daka mata tsawa tace
"Baki zaki bud'e kiyi min magana bana son rainin
wayo."
"Naji." Tace tana barin kwallar da ta taru a idonta ta
shiga sakkowa saman fuskarta. Dariya suka kwashe da ita, suka juya suka fita
suna cigaba da zantuttukan su mara sa dadi ji.
***Bangaren amarya Iman kuwa komai na tafiya daidai, ta dade
batayi bacci ba tana tunanin Moh da kalar soyayyar sa me tsayawa a zuciya,
koman sa abin so da birgewa ne tun daga maganar sa har yadda yake tafiyar da
ita. Da k'yar ta samu bacci ya dauke ta bayan ta gama tunanin nasa. Tun asubah
da suka farka basu koma ba, kana jin yadda hayaniya take tashi a masarautar
kasan akwai gagarumin shirin da ake yi. Shiryawa suka hau yi ita ta fara wanka
sannan su Khadija suka yi. Suna fitowa falon suka tarar da abinci a jere na
alfarma yana jiran su, nan suka hau kai suka ci suka yi nak, sannan aka turo
tafiya da Iman din shashen Fulani. Alkyabba aka sake saka mata sannan suka fito
kanta na k'asa tana jin yadda take shan gaisuwa kamar ta tsaya ta amsa amma yan
matan nan sunce mata ksr ta tsaya amsawa haka sarautar take.
  Da murna Fulani ta tarbe ta yau din ma, ta saka
aka kaita har uwar dakin ta in da mutane suka dinga shigowa suna ganin ta wanda
suke da kusanci da gidan. Ta jima sosai anan har suka soma jin tashin kidan
kwarya in da adaidai lokacin su Mamma suka iso sai dai babu Mama, gaisuwa aka
sake kafin a rakasu in da ake kidan kwaryar aka nuna musu wajen zaman su, kafin
daga bisani a rako Iman din wajen itama.
  Da yamma kuma aka dawo ciki aka sake shiryawa in
da aka nufi hall din dan gabatar da bikin da kuma kyaututtukan da aka shiryawa
Iman din.
 Sakon Maimartaba ne ya samu Fulani akan yana son ganin
Matar Muhammad din dan a yau zasu wuce komai dare, mamaki ya kama Fulani dan a
yadda suka shirya kwanaki uku zasuyi a nan din kafin su tafi adamawar, bata
sani ba Muhammad din ne da kansa yaje ya samu Takawan ya roke shi akan a rage
bidiar dan shi kam ya gaji sosai, take kuwa ya amince har ma ya sanar da Bubu
tun a daren jiyan.
  Maimakon a wuce da ita hall din sai aka fara
kaita wajen Takawar. Kanta a k'asa sosai kwarjinin sa ya cika wajen ta yadda
kowa ya kasa sakewa, nasiha ya soma yi cikin maganar sa da ta saka jikin kowa
mutuwa, yayi musu fatan alkhairi sannan ya kare da sake jan hankulan mutane
akan yadda rayuwar ta zama, basu dade a wajen ba, suka fito kowa na yaba
karamci na Maimartaba da ya karbe su hannu bibiyu ba tare da nuna banbanci ko
wani abu ba.
  A gaggauce akayi taron, saboda tafiyar da zasuyi,
sosai iman ta samu kyaututtuka masu tarin yawa a yan awowin da basu gaza biyar
ba, kowa so yake ace shine yafi, kowa so yake ya burge Fulani da Maimartaba,
dan kowa ya san yadda muhammad din yake a zukatansu.
***Motoci ne guda uku suka dauke su zuwa airport din daga su Mamma
sai wasu yan uwan Abba su uku shikenan wanda zasu adamawar, shima saboda bikin
da zasuyi ne suma badan haka ba da babu me zuwa. a lokacin Moh sun dade da isa
suna zaune dasu Musaddik ana hira a wani kebantaccen wuri.
  Zuwan su da aka dan suka dauki hanya babu wani
bata lokaci. Ita kadai ce a wajenta, babu kowa a saman duk suna k'asa sai ita
kadai kwal har ta dinga tunanin dalilin da ya saka aka kawo ta nan din ba
abarta wajen su Mamma ba. Kamshin turaren sa ne ya amsa mata tunanin ta, ya
karaso ya zauna kusa da ita yana kashe mata ido. Kayan jikin sa ta kalla wanda
suka kasance na sarauta, sai takalmin kafarsa da akayi da fatar zaki yayi kyau
sosai shigar gidan sarauta, babu hula akan sa ya rik'e ta hannun sa, sumar sa
ta fulani ta sha gyara ya fito a bafulatanin sa sosai.
  Shi din ma shigar ta yake kallo, yana kuma yaba
yadda komai ta saka sai yaga ya karbe ta yayi dai-dai da ita.
"Ba magana?" Yace bayan ya gama kallon nata
Mirgina kanta tayi gefe tayi masa murmushi tace
"Sannu da zuwa toh."
"Yawwa."
Yace yana jingina da kujerar jirgin sosai, be sake magana ba sai
dai yanayin sa ya nuna mata kamar akwai damuwa, tasan yadda yake mata dan haka
yau din sai taga kamar bashi ba, bata sani ba ko sarautar ce ta motsa. Satar
kallon sa ta dinga yi sai taga ya kulle idon sa yayi kamar me bacci. Duk sai
taji ta takura ta kuma damu, taba shi tayi kad'an, ya motsa amma be bude idon
nasa ba, sai kamo hannun ta da yayi ya sakalo shi ta tsakanin nasa hannun ya
harde su waje daya, kusan rabin jikin ta ya sauka a nasa, bata sake attempting
komai ba har zuwa sanda suka iso jirgin ya sauka suka fito still hannun sa na
sarke da nasa.
 Â
***Kafarta a mike take tana sauraron bayanin da take mata, ko
motsi batayi ba, kamar bata jin me take cewa har ta kai karshen bayanin tayi
shiru tana kallon ta. Sai da ta dauki lokaci me tsawo kafin ta gyara zama, ta
bud'e hannun ta, ta mik'a mata shi, jikinta na rawa ta ciro kwalbar da take
nannade a gefen zanin ta, ta saka mata a cikin tafin hannun ta. Jujjuya shi
tayi tayi a hannun nata tamkar me son gano wani abu.
"Turare ne ranki ya dade, a jiki kawai ake shafa shi bayan
haka babu wani abu."
"Kin tabbatar da abinda kika ce?"
"Allah ya taimake ki, yadda nayi miki bayanin haka yake,
yace kar ayi wasa dashi, sannan kuma kar ayi sakacin da za'a samu
matsala."
"Rik'e." Ta mika mata, da sauri ta karba tana damke wa
a hannun ta sosai.
" Kin tabbata babu wani abu da ya faru tsakanin su?"
" Na tabbatar, sai da ya nuna min komai kafin ya bani, yau
zasu iso sai kiyi kokari kafin su tare a sabon bangaren su dan naji rad'e
rad'in bikin ba zai dau kwanakin da aka tsara ba, bisa umarnin Sarki."
Murmushi tayi me kyau, ta dawo ta zauna bayan ta ciro wata
karamar riga ta karata a jikin ta,sai kuma ta ajiye tana mikar da hannun ta
baya.
" Kinyi kokari, kina da kyauta me tsoka idan har na samu
biyan bukata."
" An riga ma an samu gimbiya, ki kwantar da hankalin
ki."
"Tukunna dai."
" Me yayi saura? Yan awoyi ya rage miki ki samu abinda kike
so gimbiya ta."
Jikin tagar dakin ta karasa, ta daga labulayen tana kallon
harabar gidan da yadda hadiman gidan ke kaiwa da komowa a tsakanin bangaren Moh
din da na Ammi, tasan duk shirin tarbar bakin ake, hankalin kowa ya riga ya
koma chan dan haka zatayi amfani da damar ta isa bangaren Moh ta yi zaman jiran
dawowar shi!
Rano💕
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)Â s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
Â
1/31/22, 19:14 - Buhainat: Halin Girma
   22
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇ðŸ¾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
**********
Tamkar rana haka harabar masarautar take, komai an shirya shi an
tsara saboda shirin tarbar su. Tafiya sukayi doguwa a ciki kafin su kai wajen
manyan gine-ginen cikin masarautar.
  Ba mota daya suka shigo daga airport din dashi
ba, shiyasa ma bata ganshi ha a sanda suke fitowa daga mota. Cikin rakiyar
hadiman shashen Ammi da na gidan ma baki daya suka isa babban falon nata, da
aka kawata shi matuka ana jiran isowar su. Kamar yadda suka samu tarba ta
musamman a Kano haka aka karbe su anan dinma. Hakan ya kara bawa su Mamma
nutsuwa da tunanin irin yadda Iman din zata samu kanta a gida irin wannan wanda
yake cike da abubuwan da ba lallai ta iya dauka ba.
  Bayan sun huta an gabatar musu da abinci ne Ammi
ta saka aka rakasu masaukin su, wanda aka ware musu tun kafin isowar su. A
gajiya kowa yake dan haka suna zuwa kowa ya mike aka shiga maida maganar yadda
aka karbe su da irin sa'ar da Iman din tayi.
  Tana jin su bata tanka ba, hankalin ta ya tafi
sosai wajensa tana son jin yadda yake dan ta tabbata da akwai wani abu da ya
rage masa walwala.
***Tun isowar su ta samu labari wanda dama abinda take jira
kenan, ta shirya tsaf babu Kuma abinda zai hanata aiwatar da abinda tayi niyya
shiyasa ma bata bari Kilishi ta sani ba balle har ta hanata.
  Shigar sa shashen nasa bayan ya bar wajen Bubu
hadimar ta, ta sanar mata wanda dama ta saka ta ne ta saka ido tana ganin ya
shiga ta fad'a mata.
  Tashi tayi tana gyara gashin kanta da ta saka
ribbon din tayi sako-sako dashi, ta daura babbar Alkyabba akan kayan da suke
jikin ta da ya kasance karamar riga ce mara hannu iyakar ta guiwa kawai, sai
dogon wando a k'asan da ta saka saboda yadda zai zama ko ina na jikinta ya
rufe.
  Turaren da yake cikin Jakarta ta ciro, ta dunkule
shi a hannun ta, ta fita ta kofar bayan cikin rakiyar amintacciyar hadimar ta.
Tafiyar dake tsakanin bangaren Moh din da nasu da akwai tazara dan haka yasa
suka bi ta baya har suka isa. Idon ta, ta daga ta dubi bangaren bedroom dinsa
amma sai taga dakin babu haske sai sauran dakunan. Zagayo wa sukayi zuwa gaban
ginin masu kula da kofar suka tashi ganin ta, da ido sukayi magana da daya, ya
girgiza mata kai alamar eh sannan yace
"Yarima na jiranki gimbiya Lailah."
Jin haka ya saka dayan saurin bud'e mata kofar, ta kutsa kanta
ciki kai tsaye tana jin kamar anyi an gama ta samu cikar burin ta.
  Tafiya ta ke a cikin falon tana kallon komai,
yadda aka sauya komai kamar ba part din da take shigowa a duk sanda ta ga dama
ba, babban hoton da ke manne a jikin bangon dakin ta kurawa ido tana matsawa
gaban sa. Iman ce a jiki, ita da Moh ranar da aka daura aure, sunyi masifar
kyau kamar kayi musu magana su amsa. Wani bakin ciki ne yazo ya tokare mata a
makoshi, taji kamar tayi wurgi da hoton ya tarwatse a wajen amma sai ta daure,
ta maida hannun ta baya tana nufar bedroom din nasa in da tasan zata same shi.
  Kafin ta karasa ta hango glass cup a k'asa a
farfashe, ta durkusa ta dauki ragowar tana kaiwa hancin ta, murmushi tayi tana
da yakinin komai ya zama daidai, everything is in order kamar yadda ta tsara.
Hakan ya saka ta wucewa Kai tsaye ta murda kofar dakin ta kutsa kanta ciki tana
zare alkyabbar da take jikin ta, ta zame a wajen ta fadi.
  Muryar sa da ta soma bacewa yayi kokarin cewa
"Waye!"
Yadda yayi maganar ya saka ta sake tabbatar da komai yayi
daidai, basu yi mata shirme ko shiririta ba. Karasawa tayi jikin gadon, ta kai
hannu ta taba shi ta hasken bedside lamp da ke kunne, take kallon sa, idon sa
yayi masifar komawa ciki yana lumshe su tamkar wanda yake shirin yin bacci irin
baccin da yafi karfin sa yake neman kai shi k'asa.
"Waye?" Ya sake maimaitawa da k'yar kansa da yake juya
masa ya shiga kai masa sakon mayen kamshin da yaji ya karad'e dakin,kamshin da
ya dauke shi zuwa wata duniya ta daban, a take yaji komai ya hargitse masa, ya
mike da k'yar yana duban ta cikin ido, gaba daya komai ya chanja masa,ta juye
masa Iman dinsa gaba daya. Hannu ya kai zai taba ta, ta saka karbi ta tura shi
baya ya fad'a saman gadon!
***Text message ne ya shigo wayar ta, ta bud'e da sauri tana
fatan ya kasance daga shi, kamar yadda tayi tsammani, shi din ne kuwa,
_"A rako ki shashe na."_
Haka kawai sakon ya kunsa, kifa wayar tayi tunanin yadda zata
fara fadawa Mamma yace a rakota bangaren sa. Da kunya sosai bata kuma jin zata
iya,shiru tayi tana wassafa abun a ranta, zuciyar ta na ce mata kawai ta kira
mamma ta fad'a mata ai ba wani abu bane, wata zuciyar kuma na ce mata a ah. Ta
na nan zaune har aka dau tsahon wani lokaci, sakon ya sake shigowa irin na dazu
a karo na biyu, sai dai banbancin lokaci. Amaani ta kira suna zaune suna cin
snacks da juice, ta bata wayar tace ta kaiwa Mamma. Sai ta kifa kanta tana jin
nauyin Mamma. Tana jin sanda Mamman tazo kanta, tana sababi
"Yanzu haka ake gaya miki anayi Iman? Mijinki yana kiranki
tun dazu kika yi shiru. Kunyar me? Zamani ya chanja kinji? Tashi maza ki gyara
jikin ki, ga masu kula dake nan da yawa daya sai ta rakaki, tashi maza kina
kara bata lokaci."
Tashi tayi kunya na nukurkusar ta,ta dinga sunne kai taki yarda
su hada ido da Mamman, tana kallon ta, ta fito mata da wasu kayan tace ta
sauya, sannan ta kawo mata wani abu a cup da madara ta bata ta shanye, ta
faffesa mata turarurruka masu kamshi sannan suka fito in da yan matan ke zaune,
da sauri suka tashi su biyu, suka sakata a tsakiya suka nufin bangaren Moh din
da yake da dan tazara da wanda aka sauke su.
  Babu kowa a kofar, kai tsaye ta shiga su kuma
suka samu waje daga wajen suna jiran ta dan tace musu ba jimawa zatayi ba, babu
kowa a falon babu motsin komai, dakin farko ta bud'e da sallamar ta, baya ciki,
sallama take amma ba da karfi sosai ba, a tunanin ta ko ya shiga toilet ta
zauna jiran shi, shiru shiru babu alamar sa, ta kasa kunne ko zata ji karar
ruwa a toilet sai taji kamar shesshekar kuka, sake kasa kunnen tayi sosai ta
tabbatar da abinda taji, sai ta fara tunanin aina take ji, dakin da yake
karshen falon ta kalla, babu alamun haske a ciki amma kuma tabbas da ga nan ne
sound din yake fitowa. Tashi tayi ta nufi dakin tana taraddadin abinda zata
tarar. A hankali ta tura kofar, ta leka da kanta kafin ta shiga da jikin ta
gaba daya, tana gama shiga wutar dakin ta kawo, kwakwalwarta ta dauke kamar
yadda ake dauke wutar nepa, idanun ta suka sauka akan Moh yayi ruf da ciki a
saman gado yana bacci cikin kwanciyar hankali, boxer ne kawai ajikin sa dgaa
shi babu komai. Da sauri ta maida kallon ta kan matar dake zaune a kasan tiles
din dakin, kanta babu dankwali gashin kan nata da ya hargitse ya barbazu har
zuwa saman fuskar ta, shigar jikin ta kawai ta kalla tayi saurin dauke kanta
tana kokarin barin dakin, sai dai bata kai ga barin wajen ba dan ko taku biyu
batayi ba, taji sanarwa shigowar Maimartaba, bayan sanarwa ne taji shigowar sa.
  Karuwar kukan Laila ya sake sakata cikin yanayin
da ta shiga, har Maimartaba ya karaso bakin dakin tana tsaye kamar an dasa ta,
bata san me zatayi ba. kallon ta yayi kafin ya maida kallon sa cikin dakin,
yayi musu kallo daya wani abu me dacin gaske yana tokare shi a goshi. Juyawa
yayi sai a lokacin kwakwalwarta ta kai mata sakon waye wanda ya shigo din, da
sauri ta zube a wajen ta gaishe shi cikin muryar ta da take rawa sosai.
  Be amsa mata ba, sai daga mata kai da yayi ya
juya ya fice yan rakiyar sa suka bi bayan sa cikin tunanin dalilin zuwan Bubun
shashen Moh.
  Kasa daga kafarta tayi daga wajen, ta jingina da
bangon dakin tana karanto duk addu'ar da tazo bakin ta, ji tayi kamar ana mata
magana, ta dago tana kallon cikin dakin
"Amarya! Kinyi farin gani ko?"
Me zata ce? Shiru tayi tana maida idonta ta rufe shi ruf tana
kokarin ajiye abinda ta gani din da kuma abinda zuciyar ta take haska mata waje
daya.
"Anya? Anya kuwa? Muhammad? Me ya faru? Me yake shirin
faruwa? Wacece wannan din?"
"Karki wahalar da kanki tunanin wacece ni, sunana Laila,
gimbiya Lailah."
Yawu me karfi ta hadiye, ta hau kokarin daidaita kanta waje
daya, shigowa taji an sake yi, ta daga idonta da sauri wannan karon wata babbar
mata ce ta shigo a hargitse, tayi saurin yin kan wadda ta kira sunan ta da
Laila tana rik'e ta, tana kallon yadda Lailan ta cigaba da rusa kuka kamar
Allah ya Aiko ta, matar na bata baki jikin ta na rawa sosai. Daga ta tayi da
sauri, ta yafa mata mayafi ta rik'e hannun ta, suka zo daidai in da Iman din
take tsaye, matar tayi mata wani mugun kallo, ita kuma Laila tayi mata
murmushin da ta tsaya mata a rai. Fita sukayi tayi saurin zuwa ta sakawa kofar
key, ta dawo ta durkusa a k'asan falon ta shiga kuka, kukan da take ta kokarin
rikewa dan bata son su ga weakness dinta, dama chan ita mutum ce me taurin
zuciya da wuya kaga weakness dinta, shiyasa yanzun ma ta daure har suka fita.
  Sai da tayi kuka sosai sannan ta tashi ta share
hawayenta, a kalla zata so taji ta bakin shi, kar ta yi judging dinsa da abinda
ko a musulunci babu hujja, dan bata gansu suna aikata wani abu mara kyau ba.
Duk da ta na kokarin karfafa jikinta da zuciyar ta akan ta bari taji komai,
amma kuma jiki da zuciyar ta ta sunyi sanyi, sanyin da take jin kamar komai ya
kare mata, kasan zuciyar ta tana jin zafin sa, tana jin haushin sa amma kuma
bata da damar yanke masa hukunci.
  A yan awannin da tayi a cikin gidan nasu ta
fuskanci akwai wani Babban al'amari da ya shafi Moh dinta. Tana jin kamar gadar
zare aka hada masa har ma da ita. A nutse take duk da abin ya kadata, dan babu
matar da zata ga wata mace a dakin mijinta cikin yanayin da taga Laila ba tare
da taji komai ba, sai dai ta yarda da addu'a dan haka ta dage sosai har ta soma
jin nutsuwa na saukar mata.
  Bata san dadewar da tayi a wajen ba, taji kamar
motsi a dakin, ta tashi ta dubo cikin rashin sa'a ta cire takalmin ta, ta taka
glass din da yake fashe a wajen, kara tayi hakan ya farkar da Moh gaba daya, ya
mike da sauri kansa yayi wani irin sarawa da be taba jin irin sa ba, jiri yaji yana
neman kayar dashi yayi saurin komawa ya zauna yana dafe kan, bayan kamar sakan
goma ya mike a hankali ya fito.
  A durkushe ya ganta tana rik'e kafarta da har ta
fara jini, da sauri ya karaso ya durkusa a gabanta yana kama kafar
"Me ya same ki? Me kika taka."
Kokarin janye kafarta tayi, ya sake kama kafar ya rik'e yana
kallon kafar cikin tausayawa.
"Cika min kafata."
Tace ba tare da tasan me yasa ba, kawai ganin sa ya sakata jin
haushin sa. Kin cika mata kafar yayi, sai ma daukar ta da yayi gaba daya duk da
yadda yake jin sa babu kwari, ya ajiye a gefen gadon ya dauko first aid box din
sa yazo ya durkusa a gabanta ya gyara mata kafar Allah ya taimaka kwalbar bata
shige ba.
"Yaushe kika zo nan? Ya akayi nayi bacci? Me ya faru aina
aka samu kwalba a wajen nan har kika taka? Ina masu kula da wajen?"
Ya jero mata tambayoyin cikin son tuna wani abu, da Ido kawai
yake bin sa kamar me son karantar sa, sai dai bata ga komai ba sai tsantar
gaskiyar sa a yadda yake maganar. Janye kafarta tayi ta mikar da ita a saman
gadon, ya dawo ssman gadon ya zauna yana jan kafar ya dora akan cinyar sa.
"Bacci ne ya dauke ni bayan na sha juice daga nan kuma
bansan me ya faru ba, kin dade kina jirana? Da baki tashe ni ba?"
"Bana so na katse maka barci ne." Tace ganin duk ya
damu, ajiyar zuciya ya sauke yana matsowa ya gyara mata kafar yadda zata ji
dadi, ya mannu a jikinta.
" Kiyi hakuri, kaina ne naji yana min ciwo sosai shine
kawai nazo na dan huta bansan zanyi bacci ba."
" Ba komai."
Tace tana rufe idon ta
" Bacci?"
" Umm."
Tace a gajarce dan bata son doguwar magana tana son tattara
bayanan da ta samu ta hade su waje daya kafin wayewar gari.
Tashi yayi ya fita bayan ya maida rigar sa, ya hau k'wala
kiran ma'aikatan wajen, da sauri ya shigo yana raba ido, masifa ya fara yi masa
akan dalilin barin kwalba a hanya, hakuri yayi ta bashi yayi saurin gyara wajen
sannan ya fita.
  Ji yayi duk jikin sa yana masa ciwo, chan k'asan
zuciyar sa kuma wani irin feeling ne da be san dalili ba, ji yake kamar idan
har be samu abinda yake so ba zai iya rasa ransa, yana wanka yana tunani har ya
kammala ya fito daure da towel iya ka guiwar sa, kallon in da take kwance yayi,
ta dunkule waje daya kamar me jin sanyi.
  Kaya ya saka sannan yayi sallah ya duba wayar sa
yaga misscalls da yawa, ganin dare yayi ya saka shi ajiye wayar ya hawo gadon
yana juyo da ita tana kallon shi. Hawaye ya gani a saman kuncin ta, ya saka
hannu cikin mamaki yace
"Kuka?"
Kamar wadda take jiran kiris ta shiga rera shi sai dai babu
sauti, rikicewa yayi ya hau tambayar ta menene, bata amsa masa ba, ta cigaba da
kukan ta wanda ita kanta bata san me yake sake tunzura ta take kukan ba, da
farko ta zata zata iya daurewa sai daga baya ta gane duk dauriyar ta wannan ya
wuce in da take tunani, kishin mijinta ne ya sakata kuka. Magiya ya cigaba da
yi mata akan ta fad'a masa dalilin kukan ta amma taki, rungume ta yayi a
jikinsa yana lallashin ta amma kamar kara ingizata yake, ya rasa yadda zai, ga
wani irin abu da yake jin yana taso masa. Kasa daurewa yayi ya hade bakin su
waje daya, da karfi tayi kokarin turashi ta amma ta kasa!
Rano💕
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)Â s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
Â
1/31/22, 19:15 - Buhainat: Halin Girma
   23
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇ðŸ¾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
*******
A hankali ya shiga bin ko ina na jikinta yana aika mata da
sakonnin shi, kukan da take na taba shi, yana jin har cikin kansa, sai dai ba
zai iya controlling kansa ba, abinda yake ji yafi karfin ikon sa, ba kuma zai
iya tsere masa ba.
  Da fari ta dauka babu wani abu da zai mata sai
son ganin ya rarrashe ta, amma daga baya sai taga abin yana chanja salo.
Jikinta ne ya hau rawa ta ko ina, ta sauya akalar kukan nata zuwa magiya da
rokon sa, baya jin ta, idan ma yaji ta baya tunanin zai iya yi mata abinda take
so din.
  Juyo ta yayi ta zama a saman sa, ya sake hautsina
ta zuwa kasansa , ya ajiye mata dukkan karfin sa, ji tayi kamar numfashin ta na
janye wa daga jikin ta, ta dinga jansa tana kuka tana kiran sunan sa, yadda
yake kissing dinta kamar mayaunwacin zaki ya sake tsorata ta,shi kansa jikin sa
rawa yake,ga wani karfi da yake ji ya zo masa wanda be taba jin irin shi ba.
Kayan jikin ta ya shiga janyewa yana wurgi dasu ta kowanne angle, har yayi
nasarar rabata da komai. Idanun sa da suka rine sosai ya zuba mata yana kallon
ta, wani abu yana kaiwa da komowa a tsakanin wuyansa.
"I'm so sorry."
Ya furta mata da k'yar kafin ya shiga aiwatar da abinda yayi niyya.
  Sama sama yake jin ta, cikin muryar da ta shige
ciki saboda kukan da ta sha, kamar mafarki haka yake jin abun, juyowa
yayi da k'yar ya dune ta, tana kwance agefen sa taci kuka har ta gode Allah.
"Subhanallah!"
Ya furta yana tashi, abinda ya faru ya shiga dawo masa akai, ya
akayi haka? Bayan yayi ma kansa alkawarin zama so gentle, yadda yasan ba zai
bata wahala sosai ba, what has gotten in to him? Me yayi mata?
 Rik'e ta yayi yana kokarin daidaita kansa ya samu damar
kwantar mata da hankali
"I'm so sorry dan Allah, dan Allah kiyi hakuri ki yafe min,
bansan me ya hau kai na ba, this is not me, bani bane ba."
Bata da karfin da zata kwaci kanta, sai kawai ta lafe a jikin sa
tana jan numfashi. Kanta ya dinga shafawa a hankali a hankali, yana jin wani
irin son ta, na saka shigar sa. Idan har abinda kwakwalwar sa ta dawo mata
dashi gaskiya ne, toh lallai sai yaci uban Lailah, dole ne yayi mata abinda ko
a hanya ta hadu dashi ba zata nuna ta sanshi ba.
 Idonsa a rufe yana tariyo abinda ya faru, tabbas ya
ganta a tsaye a kansa, lokacin da baccin da be san na menene ba dauke shi da
sauri. Tunanin sa ne ya koma baya, zuwa sanda ya shigo ya tarar da juice akan
table din da ake ajiye masa, a gajiya yace amma ya tsaya ya sha daga nan ne ya
fara jin wani abu me karfin gask yana taso masa, sai wani irin bacci me nauyi
da be taba jin irin sa ba.
"Desire pills?"
Ya furta yana kokarin tashi, k'ara tayi mara sauti ya tuna tana
jikin shi, yayi saurin komawa ya zauna yana sake gyara ta.
" I'm sorry."
Ya saka hannu ya goge mata hawayen da suke sauka a fuskar ta.
Tsawon minti talatin yana a haka yana tunanin abubuwan da suka faru a daren,
tabbas koma menene an shirya masa abu ne, be san ya akayi ya bada kafa ba, har
aka yi galaba akansa. Tashi yayi bayan ya gyara mata kwanciya, ya shiga toilet
ya gyara jikin sa, sannan ya fito, ya taimaka mata, ta tashi tana ciccijewa sai
dai taki yarda su hada ido, ta hade fuska sosai a dole haushin sa take ji,
haushi biyu ne suka hadu waje daya, ta kasa manta abinda ya faru farko da na
karshen.
 Toilet din ta shiga sai taga ya biyo ta, ta dube shi
tana tsaye gaban bathtub din, ta marairaice fuska, yi yayi kamar be ganta ba,
ya rufe kofar ya karaso ya durkusa yana taba ruwan.
"Ka fita."
Ta fad'a muryar ta babu karfi, banza yayi kamar be ji ta ba, ya
ciro towel a cikin jerin sabbin towels din dake jere a cikin wata drawer,
sannan ya dauko brush da toothpaste ya saka mata a jiki ya ajiye a gefe ya hau
nannade hannun rigar sa. Kamar ta rusa ihu haka taji, ta rasa yadda zatayi ta
hanashi, bata ga alamar ma zai hanun ba, sai kawai ta hakura ta zubawa sarautar
Allah ido, bata san rashin kunyar namiji ta kai haka ba. Sai da ya gama abinda
yayi niyya ya tabbatar yayi mata yadda zata ji dadin jikin ta sannan ya
kyale ta ya fito yana jawo mata kofar.
  Kwanciya ta sake yi a cikin tub din ruwan na
ratsa ta, gefe tana tuna abinda ya wakana tsakanin su. Murmushi tayi, duk
kalaman sa na dawo mata daki daki, abu daya ne ya tsaya mata har take kokarin
alakanta shi da abinda ya faru kafin nan, idan har shi din ba mutumin kirki
bane, idan har wani abu ya faru tsakanin sa da Lailah, ba zai sha wahala wajen
neman hanya ba.
  Saurin kawar da tunanin tayi kunyar kanta na
kamata kamar yana wajen, da wanne idon zata koma wajensu Mamma ma wai tukunna,
da wanne idon? Kwankwasa mata kofar yayi ganin ta dade, sai ta tashi tana
karfafa jikin ta, ta dauro towel din bayan ta goge jikinta ta fito kanta a
k'asa. Ajiyar zuciya taji ya sauke bayan ya kare mata kallo, hankalin sa yaki
kwanciya tunanin sa ko yayi mata illa ne, sai yaga akasin haka, be sani ba ko
duk cikin dauriyar da ya gane tana da ita bane. Lokacin sallah ake kira a cikin
masallacin cikin Masarautar, daga jikin kofar ya tsaya be fita ba, yana kallon
ta har ta gama ta saka doguwar jallabiyar sa daya ajiye mata a gefen gadon,
murmushi yayi ya fice kansa sanye da farar hula da ake kira da tashi ka fiya
naci ya dora doguwar riga irin wadda ya dauko mata.
  A sahun farko ya samu Kamal, daga liman sai shi,
hakan ya bashi mamaki amma ya share, bayan an idar suka gaisa a tsattsaye ya
fice yana son komawa ya ga halin da take ciki. Sun hadu da Bubu amma be masa
magana ba, ya dai ce masa ya sameshi idan garin ya gama wayewa, sai dai yanayin
fuskar Bubun ta saka shi tunanin akwai wani abu me girma.
  A saman sallayar ya tarar da ita, ta kwanta akan
hannun ta ta mik'ar dashi, karasawa yayi ya daga ta, ya maida ta saman gadon
yana zama a gefen ta. Rufe idon ta tayi da sauri jin ya matso da fuskar sa
daidai saitin tata. Iska ya fitar me zafi, ya tashi ya kashe wutar dakin ta
dawo ya hawo gadon ya kwanta.
"Me ya faru?"
Yayi mata tambayar kai tsaye, yadda yayi sounding zaka gane daga
muryar sa, maganar yake so suyi, shiru tayi bata ce komai ba, dan bata san me zata
ce ba, tace masa ta same shi da wata a daki ko me? Ta yaya ma zata fara?
"A lokacin da kika zo dakin part din nan, wani ya shigo? Ko
kinga wani a ciki?"
Nan din ma shiru ta sake yi masa, kasan zuciyar ta na ce mata
kar ta yarda,kawai zai yi amfani da innocent dinta ne ya nuna mata kamar be san
komai, daga gefe kuma wata zuciyar na ce mata ta fad'a masa watakila be sani
ba, watakila so ake a hada su, tunda har yanxu bata san komai akan sa ba, ba
zata iya dorar da wani abu ba balle har ta iya judging dinsa, kawai dai a
matsayin ta na mutum me tunani , tana kyautata masa zato.
  Birkitota yayi da karfi muryar sa na fita da dan
karfi akan dazu yace
"Tell me, me ya faru? Wani abu ya faru? Kin samu wata ko
wani da kika zo? Wani ya fad'a miki wani abu ne? Me ya faru!"
Kuka ta samu kanta da fashewa da, ya tashi da sauri yana kunna
wutar dakin, ya dawo ya tashe ta zaune suna fuskantar juna, zuwa lokacin ya ji
yana neman loosing temper dinshi.
"Kalle ni, look at me! Menene? Me ya faru da ban sanshi ba?
Tell me, waye yazo?
" Maimartaba ne yazo."
" Maimartaba!?" Ya furta da dan karfi cikin yanayin
dake nuna tsantsar mamakin sa
"Me yazo yi a part dina? Me yace? Me ya faru? Wani abu ne
ya faru while i'm sleeping?"
" Eh." Ta daga masa kai, tsugunawa yayi a wajen yana
tattaro dukkan nutsuwar sa, gabansa na faduwa da abinda zata ce dan yasan ba
karamin abu bane zai kawo Bubu part din sa.
" Believe me, bansan komai ba, kamar yadda babu alkalami
akan me bacci, na rantse miki bansan me ya faru ba."
Goge fuskar ta, tayi da hancin ta a jikin sa, ta dago tana
kallon kasa tace
" Naga wata Laila a nan."
Ta nuna wajen da Lailan ta zauna
" Lailah!? "
"Eh."
"Ehen, sai me?"
"Tana zaune a wajen tana kuka sosai, daga nan sai Maimartaba
ya shigo, sannan ya tafi sai kuma wata mata ta shigo ta daga ta suka fita
  Abu ya hadiye me karfi, ya yi kokarin ganin be yi
wani abu ba, a hankali yaji kamar ana masa rad'a
_Be calm Moh, be calm."_
Kamar wanda aka saka abu aka bubbuge ma guiwa haka ya zube a
wajen, zai tolerating komai amma banda fushin Bubu, shi za'a wa wannan kazafin?
Abinda be taba tunani ko shaawar aikatawa ba, Zina? Shi Muhammad shi aka yiwa
wannan sharrin? Saboda yayi kamar be san wani abu yana faruwa ba, shine har aka
samu damar yi masa wannan kullin?
 Tana ankare da yadda ya shiga kaduwa, tana kuma ganin
yadda Adam apple dinsa ke hawa da sauka tsakanin makogwaron sa, idon sa kadai
zaka kalla ka tabbatar da ransa yayi masifar baci.
  Sai da yayi kusan minti goma be ce komai ba, ba
dan bashi da abinda zai ce din ba, sai dan yadda mamakin Iman din ya hanashi
komai, be zaci haka daga gareta ba, idan wata ce, ba zata iya daukar abinda ta
gani ba, har ta tsaya jiran shi, ya ga kokarin ta sosai kuma ya jinjina mata, hakan
ya kara mata matsayi a zuciyar sa.
 Girgiza mata kai yayi yana kama hannun ta
"Kin yarda dani?"
" I don't know." Tace tsakanin ta da Allah
"Bansan yadda zan dauki abun na ajiye ba, all I know shine
I'm hurt, more than yadda nayi tunanin I ll be."
Folding hannun nata yayi a cikin nasa ya damke.
"I promise to make everything right, koma menene we will
over come it, in sha Allah, together we will build tomorrow, I promise you
that!"
Shiru sukayi babu wanda ya sake magana, ko be ce ba, ko be ba
ita zata gano komai, zata gane kafin ma ya gane, tana da kaifin tunani, sannan
tana karantar komai kafin tayi judging din mutum.
  Kwanciya tayi ganin suna zaune kowa da abinda
yake tunani, ganin ta kwanta sai ya mike ya fita, ya nufi part din Ammi duk da
lokacin garin ke karasa yin haske. Ya san tana zaune har lokacin tana azkar
kamar yadda ta saba a ko da yaushe.
  Yadda ta ganshi ya shigo jikin ta, ya bata babu
lafiya, katse abinda take tayi ta mike tana kallon sa har ya karaso
"Lafiya Babana?"
"Ina kwana Ammi?" Ya duk'a k'asa ya gaishe ta, kafin
ya amsa mata tambayar ta
"Ba lafiya ba Ammi, yarinyar nan Laila tayi abinda zan nuna
mata ko ni waye, ganin kamar ban san me take ba ya bata damar aikata abinda ta
aikata wanda zai zame mata dana sani, dama chan Ammi kece kike hanani, saboda
zumunci amma not anymore."
"Me ya faru?!"
"Bubu be sanar dake komai ba?"
"Be ba, me ya faru?"
Iyakar abinda ya sani ya sanar da ita, jikinta yayi sanyi, ta
kuma san Bubu zai iya daukar kowanne mataki akan muhammad din, tun da be taba
sanin wani abu daya danganci Laila din ba da shi, ita kawai da Muhamamd din ne
suka sani sai Kilishi.
"Babu abinda zai faru, kai dai ka rike gaskiya, zatayi
halin ta."
"Shikenan, zanje naga Bubu, zanji me zaice."
"Allah ya taimaka, zanyi magana dashi nima in sha
Allah."
Fita yayi ita kuma ta zauna a wajen tana hango abinda zai je ya
dawo.
Kasancewar safiya ce, shiyasa ya shige kai tsaye wajen Bubun, a
lokacin ya fito wajen shashen bayan sallah yana duba wasu littattafan sa. Sai
dai yau ya kasa yin komai, tunda aka fito masa da littafan ya kasa taba ko guda
daya, balle har ya karanta, abinda ya gani jiya yayi masifar girgiza shi, ya
kada shi sosai, har yayi furucin da yake jin idan har Muhammad be wanke kansa a
tsawon kwanaki biyar ba, ko da yana da gaskiya ya zama dole ya auri Lailah tun
kafin maganar ta fito waje, a jita a ko ina.
  Aji ya samu da maganar a lokacin dan ji yayi
yana neman faduwa k'asa, sai dai yadda yayi tunanin maganar zata taba Aji sai
yaga akasin haka, yana zaune kem fuskar sa bata chanja ba ko kad'an, har sai da
Bubun ya kasa daurewa ya tambayi Aji dalilin da be ji abun ba, murmushi yayi
yace.
"Ahmadu kenan, da Muhammad da Laila su dukkan su nawa ne,
ni na haifi iyayensu na kuma san kowa a cikin su, na san abinda kowa zai aikata
da wanda ba zai aikata ba, duk da yanzu ance baa shaidar mutum, amma ni zan
shaidi Muhamamd ko aina ne, lallai akwai wani al'amari bayan abinda kai din ka
gani."
"Amma kuma komai ya nuna, a yadda na ganshi naga Lailan,
bani da hujjar kare shi ko yarda dashi, idan har nayi haka sai naga kamar banyi
wa Yaya adalci ba, mutane zasu ce ko dan babu shi. "
" Duk abinda zakayi karka tuna mutane dan dama su baa raba
su da abin fad'a, kayi gaskiya kawai. "
" Toh ta yaya zan yarda da Muhamamd be aikata ba? Da wacce
hujja zan yarda dashi? "
" Ka bashi lokaci, ya kare kansa, idan har ya amsa laifin
sa shikenan, idan kuma ya kawo hujja gamsasshiya toh."
" Idan har muhammad ya kasa kawo hujjar bai aikata abinda
ni da mahaifiyar Laila muke tunanin ya aikata ba, nayi alkawarin aura masa ita
a tsakanin kwanaki hudu! "
 Dawowa yayi daga tunanin yadda suka kwashe da Aji yayi,
ya bata rai sosai sanda Moh ya dire a gabansa, cikin girmamawa ya gaishe shi,
amma sai yaki amsawa, ya kausasa murya yace
" Ban kiraka nan dan ka gaishe ni na amsa ba, ban kuma
kiraka nan dan muyi doguwar magana ba, me ya faru tsakanin ka da Lailah? "
" Babu komai Bubu. " Yace kai tsaye dan dama ya riga
ya shiryawa tambayar
" Babu komai? "
" Eh babu, duk abinda ka gani sharri ne, bansan komai akai
ba. "
" Waye shaidar ka? "
" ALLAH! "
Ya fad'a kai tsaye, shiru Bubu yayi, ya dauki wani lokaci kafin
yace
" Ka dauki alaka ta da kai ta d'a da mahaifi ka ajiye a
gefe, ka kalle ni a matsayin alkali da aka kawo min kara ka, na baka nan da
kwana hudu ka kawo min kwakkwarar hujja, idan har kwana hudu ya wuce babu
komai, nayi maka alkawarin aura maka Laila! "
" Aure?!!! "
" Aure, tashi ka bani waje."
Jikin sa a sanyaye ya tashi, ya fice cikin sauri sauri ya nufi
part din Lailan, yana tafiya yana huci, ji yake kamar ya dauko bindiga ya harbe
ta, mutanen da suka fara fitowa wanda suka kasance masu aikace aikace a
tsakanin parts din suka hau mamakin ganin Moh a irin lokacin shi kadai babu
wani tare dashi. Be same ta a bangaren nata ba, tana bangaren Kilishi,juyawa
yayi zuwa bangaren Kilishi yana ayyana kalar rashin mutuncin da zai yi musu.
   Sai da ya kusa zuwa sai kuma zuciyar sa
tace yaje yayi musu me? Yafi karfin haka, ba girman sa bane, dan haka sai kawai
ya koma nasa part din yana lissafin kwanaki hudun da Bubu yace, yasan zai iya
yin komai ba kuma sai karya alkawarin sa ba, idan kwanakin suka cika bashi da
wata hujja. Abu na karshe da zai iya shine auren Lailah, gwara ya hakura da
komai akan ya aure ta.
  Bacci ya sameta tanayi, baccin da yasan na
wahala ne, duk tausayin ta ya kamashi, shi da yaso ta huta sosai kafin ta fara
sanin komai amma sai gashi daga shigowar ta gidan ta fara da karo da abinda
yafi komai muni. Peacefully take baccin,fiye da wanda tayi jiya, a kalla yanzu
ta samu kwanciyar hankali bayan ta sanar masa da abinda yake damun ta, yasan
tayi dauriya sosai.
  Kissing goshin ta yayi, ya gyara mata kwanciyar
ya koma dayan side din ya kwanta da tunanin kwana hudu
Rano
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)Â s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/1/22, 10:25 - Buhainat: Halin Girma
   24
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇ðŸ¾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
Sai da rana ta daga sosai sannan ta farka, da sauri ta mike tana
mamakin dadewar da tayi tana bacci ita da ya kamata ta koma wajen su Mamma.
Sakkowa tayi tana jin jikin ta da dama-dama, ta shiga takawa a hankali zuwa
toilet din dakin,ta wanko fuskar ta, ta fito ta gyarata sannan ta cire
jallabiyar tasa ta maida kayan ta, ta ajiye masa a gefen gadon ta fito zuwa
falon. Tunanin yadda zata iya komawa wajen su Mamma take da kuma yadda zatayi
da kunyar da take ji daga zuwa ta dawo sai kwana bayan ba haka ya kamata ba a
ganinta. Abin takaicin ma bata dauko wayar ta ba balle ta kira, tana tsaye tana
tunanin yadda zata fita taji maganganu a kofar part din,wajen window ta isa, ta
daga curtains din tana son ganin komai. Gabanta ne ya fadi, tayi saurin cika
window din a daidai lokacin da taji suna karasa maganar su. Kyakkyawa ce ajin
farko, kana ganin ta kaga bafulatanar adamawa, yau ba kamar jiya da ta soma
ganin ta ba, tana cikin shiga me kyau harda Alkyabba, tayi kyau fuskar ta fes
alamun tana cikin farin ciki. Kokarin daidaita kanta tayi sanda taji an turo
kofar an shigo, idonsu ya hadu lokaci daya, wani banzan kallo Lailan ta watsa
mata tana karaso wa ciki a gadarance, ta samu saman daya daga cikin kujerun
falon ta hakimce baiwar ta,ta gyara mata k'asan rigar sannan tace ta fita ta
basu wuri. Tana fita ta kalli Iman irin kallon sama da k'asa kafin tace
"Barka da rana amaryarmu."
"Sannu." Kawai Iman din tace ta juya zata bar wajen
amma sai ta dakatar da ita
"Nace ba, ya kika ji da kwanan bakin ciki? A ranar farkon
ki a dakin mijinki?"
"Bakin ciki kuma? Na me kenan?" Ta tambaya Kai tsaye
kamar bata gane me Lailan take nufi ba
"Na abinda kika gani mana, bakin gani, kinga true color din
so called mijinki ko?."
" Ohh, wannan wasan kwaikwayon wai? Yayi kyau sosai ya kuma
tsaru yadda ya kamata, sai dai shi actor din be san kan wasan ba dan be ma san
me yake faruwa ba, shine kawai matsalar film din amma yayi kyau."
"Me kike nufi?" Tace a hasale tana mikewa tsaye
" Abinda kika sani shi nake nufi, kin dauka zan yarda da
banzan plan dinki? I'm not an illiterate, I can tell when someone is lying,
beside mijina ba zai taba aikata abinda kika ikirarin ya aikata, and i trust
him yadda bakya tunani."
"Wow! Wow!! Wow!!! Sannu da kokari, I love your confidence,
amma wanne irin sani kikayi masa haka? Da har zaki bashi irin wannan yardar?
Kinsan waye namiji kuwa?"
" It doesn't matter yaushe na sanshi, all that matters now
shine, miji na ne, kuma nayi trusting nashi, dari bisa dari."
" Shikenan, sai muga yadda zakiyi depending mijin naki at
this critical condition, let's see how far you can go...."
" Kwana hudu kachal kike da, idan har baki samu way out ba.
Ki shirya karba ta a matsayin kishiyar ki, sannan na fitar dake ta karfin
gaske, dan baki da waje a gidan nan, captain nawa ne right from the start kuma
he will always be mine."
Murmushi Iman tayi mata, tana jin wani irin tsana da haushin
Lailan, tana jin zata iya komai, idan tace komai tana nufin komai domin taga ta
fitar da shi daga koma menene, akwai babban kalubale a gabanta, amma ba zata
karaya ba, duk wanda ya rik'e Allah da addu'a ya gama, da ikon Allah sai tayi
galaba akan duk wani makiyin su. Ta daina shiru, duk wanda yace mata kule! Zata
ce masa chas! Ita kanta bata san tana da courage din da zata iya maida mata
martani ba, sai gashi.
Juyawa tayi ta koma bedroom din dan ba zata cigaba da bata
lokaci akan wadda bata tunanin tana da hankali ko kad'an. Wayarta ta gani ajiye
a saman chest of drawers ta dauka ta kira Mamma da k'yar, sukayi magana ta
ajiye ta zauna tana lissafin rayuwar da zatayi a irin wannan gida, tuna sanda
ake mata fad'a irin na bankwana tayi, wata Babar su Abba tana ta jaddada mata
hakuri da kuma shirya wa duk wani kalubale na gidan sarauta, karta bari a
takata kar kuma ta cuci kowa, akwai makirci sosai wanda zata gamu dashi amma
idan ta nutsu tayi hakuri da karfin addu'a Allah zai bud'e mata komai.
  Bata jima a zaune ba taji ana mata knocking, ta
tashi ta bud'e ta fito, russunawa tayi har k'asa da sauri ta gaishe ta, kunya ta
kama Iman din ganin Matar da zata yi kusan sa'ar Mama tana gaishe ta a haka.
Kaya ta mika mata cikin girmamawa tace ta chanja zata rakata bangaren Fulani
(Ammi) juyawa tayi ciki, dan dama kayan jikin ta sun dame ta sosai. Sai da ta
shirya tsaf sannan ta fito, ta lura Laila ta jima da barin falon sai dai
mayen kamshin da take yana nan a falon. Kai tsaye shashen Ammi suka wuce wanda
sai a sannan ne ta sake karewa fadar gani sosai. Anan suka tarar da su Mamma da
wasu mutanen wanda da yawan su kana kallo zaka gane alakar su da gidan saboda
yanayi na kama da suke da juna. Shigowar su ya saka kowa maida hankali kanta
kowa na son ganin amarya, tunda jiya babu wanda ya samu ganin ta saboda dare.
Kanta a k'asa taki yarda ta dago saboda yadda take jin kamar ta nutse, a
tunanin ta duk sun san daga in da ta taho, bata san Mamma bata fad'a ba sun dai
barshi a zuwan sun barota ne tana shiryawa. Sai da duk suka lafa ne aka
zazzauna sannan ta gaida Mamma da take kallon ta da murmushi, murmushin da ita
kadai ta san ma'anar sa, hakan ya sake saka Iman din cikin jin kunya.
 Sanda ta shigo Ammi bata falon, tana zaune suna magana
da Amaani ta dawo, da sauri Iman din ta zamo daga kujerar ta gaishe ta, ta
rik'e ta, ta mik'ar da ita tsaye tana amsawa a sake sosai, sannan ta saka a
raka Iman din part din Kilishi.
  Hannun ta cikin na Amaani suka shiga, babu kowa a
falon farko sai wata baiwa guda tana goge-goge,wadda ta rako su ce tace su
zauna sannan ta nufi kofar ciki don sanar da zuwan su. Jim kad'an ta dawo ta
tsaya a gefe, zuwa wani lokaci Kilishin ta fito, fuskar ta kadaran kadahan ba
zaka gane komai ba, Iman bata kalle ta ba, ta gaishe ta cikin girmamawa ta amsa
a yatsine bata ma zauna ba.
"Hari wannan din itace sirikar tamu?"
"Itace ranki ya dade."
"Lallai sannu yarinya, shi ko Muhammad ya rasa wa zai dauko
mana sai yar karamar yarinya haka? Ko da yake ra'ayin sa ne ai, ba kuma a san
ya akayi ba dai, ko da yake dama dai yaran talakawa sai a hankali, idon su idon
me arziki sai in da karfin su ya kare, sannu kinji? Allah ya bada zaman
lafiya."
Sai ta juya
" Hari naga amarya, ki gaida uwar dakin naki."
Wani abu ne ya tokare wa Iman a makogwaro, idan har ta fahimci
maganganun matar tana nufin asiri tayi ta aure shi kenan, a fakaice ta ci mata
mutunci babu gaira babu dalili, bayan bata san ta ba, idan banda jiya sai yau
ne karo na biyu da ta taba ganin ta. Ajiye ta tayi a daidai mazaunin da da
ajiye Laila, ta kuma kuduri aniyar zama dasu daidai da yadda suka zaba.
 Daga nan sai suka wuce bangaren Aji da Hajja, amma a
mota saboda tazarar dake tsakanin bangarorn biyu, sosai taga karamci da
girmamawa dan Adam, Hajja kamar ta goye ta saboda murna, ta dinga tsokanar ta
da ta kwace mata miji da rana tsaka, murmushi kawai Iman din take, hakan ya
janyo suka dade sosai a bangaren har zuwa sanda taji sallamar sa, ta dago suka
hada ido sanda yake shigowa ciki, jamfa da wando ne a jikin sa kalar sararin
samaniya, ya tsaya iya kar guiwar sa, kansa sanye da hula me kalar duhu, yayi
kyau sosai, da sauri ta janye idon ta kunyar abinda ya faru daren jiya na hasko
mata, murmushi yayi me kyau ya karaso ya zauna kujerar dake fuskantar ta. Hajja
dake nade a saman wani cushion me laushi ta tabe baki tana dubanss
"Saboda rashin kunya shine ka biyo bayanta ko?"
"Toh ya zanyi? Kin rik'e min ita kin hanata tafiya."
"Ah lallai, shine ka biyo baya kazo kaga ni, toh ba zan
cinye ta ba ai."
"Kai yar tsohuwar nan kin fiye rikici wallahi, kishi ne
nasan yake damunki ba wani abu ba."
Dariya tayi tace
" Ai na bar mata kai tuntuni, kuje ku karata nima Amadu na
ya ishen."
A tare duk suka yi dariya, ya kashe mata ido daya tayi saurin
dauke kai kamar bata ganshi ba.
" My wife!"
Yayi kiranta a hankali karaf sai a kunnen Hajja, ta banka masa
harara ya sosa kai
"Dan nema, kin hadu da aiki kinji Fatima, mijin nan naki
bashi da kunya sam, bari kiga na tashi, taso yan mata muje na baki wani abu ki
bar wadannan."
Tashi Amaani tayi tabi Hajjan, suna shigewa yayi saurin komawa
kusa da ita.
"Ka ganka ko?"
"Me nayi?" Ya tsare ta da ido yana marairaice fuska
"Gashi nan ka kori Hajja."
"Rigimar tace kawai fa, mun saba irin haka da ita."
"Toh ka koma chan ka zauna."
" Wai kunya ta kike ji? Ko kunyar Hajja?"
" Both!" Tace tana kauda kanta
Murmushi yayi kawai
" Kinsan me? Bubu ya bani kwana hudu na kawo masa
gamsasshiyar hujja, idan ban kawo masa ba, zai aura min Laila."
Sak tayi, duk da Laila ta riga ta fad'a mata amma ji daga bakin
sa ya sakata shiga yanayi,
" Karki damu, hakan ba zai faru ba, I promise you
that!"
" Allah ya bada sa'a." Tace a sanyaye
" Zan je Abuja anjima ko gobe da safe zanyi kwana biyu, na
dawo"
" Tafiyar ba zata bamu matsala ba?"
" In sha Allah."
" Shikenan, Allah ya kaimu ya dawo da kai lafiya."
Tayi shiru tana tunanin yadda zata taimaka masa ta taimaki kanta
dan ba zata taba iya zama da Laila ba a yanayin ta.
***Idan tace tayi bacci a ranar tayi karya, tun bayan fitar
matar gidan da kawayenta bata sake nutsuwa ba, kuka take tun tana yi da hawaye
har ya zama babu hawayen sai suya da zuciyar ta, take kamar zata fito. Da
asubar fari taji ana buga kofar dakin amma a hankali, tashi tayi da k'yar tana
jin jiri jiri saboda yunwar da ta kwaso ta zare sakatar dakin. Da sauri ya
shigo ciki ya maida kofar ya rufe yana kallon ta, matsawa tayi baya tana masa
kallon tsana
"Karka matso nan wallahi zan iya illataka, ka maida ni
gidan mu wallahi ba zan zauna anan ba."
"Rage muryar ki dan Allah, kar taji, kiyi hakuri zan yi
kokari naga na lallabata ta bar mu, mu koma gidan mu dan wallahi a matse nake,
kinsan dai mutum da sabuwar amarya."
"Wallahi bazan koma ko wanne gida ba, gidan mu zaka mayar
dani ka sake ni kuma, ba zan zauna da kai ba na tsane ka."
Saurin damkota yayi, ya toshe mata baki yana hade jikin su waje
daya
"Idan kina daga murya wallahi zamu dade a haka, idan ta
gano na sato hanya nazo ni dake duk ba zamu fita ba, yanzu ki kwantar da
hankalin ki, ki bita duk yadda tace zan dinga shigowa nan din da asubah tunda
bata tashi da asubah sai gari yayi haske sosai."
Fizge kanta tayi tana masa mugun kallo
"Na tsane ka, na tsane ka Bashir har bansan iya adadin
tsanar da nayi maka ba, Allah ya isa cutar dani da kayi, kasan dama kana da
mata amma shine ka auro ni, wallahi sai ka sake ni ko na jawo maka abinda zaka
dade kana dana sani."
"Baby!" Yaji muryar hajjajun tasa tana k'wala masa
kira, jikin sa ne ya hau rawa yayi hanyar fita hankalin sa a tashe,kafin ya
karasa ta turo kofar cikin shigar kayan bacci masu shegen kyau, tayi musu wani
kallo kafin ta kama hannun sa tana murmushi
"Kana nan ashe, toh wuce muje ko?"
"Toh;" yace yana yin gaba.
"Ke kuma, ki fito ki fara min aiki kafin gari ya gama
wayewa, akwai menu na kalolin abincin da nake son gani kullum a saman dining
bana kuma so ki wuce karfe goma baki gama komai ba."
Ta juya tana karkada mata mazaunanta ta buga kofar. Hawayen
bakin ciki ne suka sakko mata, ta share tana shiga dan kurkutaccen bandakin da
ke gefen dakin ta dauro alwala da k'yar sboda yadda yake wani shegen wari ta
shinfid'a dankwalin ta, tayi sallah akai sannan ta bi ta hanyar zuwa kitchen
din dan ta tabbata idan har ta sake muguwar matar ta dawo bata fito ba zata iya
nada mata shegen duka babu abinda ya dameta gashi babu me kwatar ta dan shi
kansa Bashir din ba abakin komai yake ba.
 Menu din ta dauka tana kallo, babu abu daya daga cikin
kalolin girke-girken guda biyar da ta iya a ciki, tasan dai tabbas Iman tana yi
musu dukka a gida amma ita bata taba ko da sha'awar gwadawa ba, daga indomie
sai tea sune kadai take yi, sai yar taliya ko macaroni shima ba kullum ba, duk
wani girki me wahala kamar su tuwo da sauran su.
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)Â s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/1/22, 10:25 - Buhainat: Halin Girma
   25
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇ðŸ¾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
***Ta dade a kitchen din tana jujjuya yadda zata yi, gashi
lokaci na tafiya dan har kusan bakwai ce zatayi, barin kitchen din tayi ta wuce
ta fara gyara falon, duk da ba wani datti da yayi amma sai da ta sake share shi
ta bubbuge kujerun ta tattare komai ta ajiye a gefe har da rigar baccin da ta
gani a jikinta dazu. Daga nan ta sake komawa kitchen din kawai ta yanke
shawarar tayi abinda zata iya, ta dauki indomie ta dafa da egg sannan ta dafa
ruwan tea ta jera musu akan dinning din ta wuce dakin da yake a mazaunin nata
da tunanin yadda zata samu waya ta kira gida, ko kuma ta samu hanyar da zata
bar gidan dan bata ga alamar Bashir zai kyaleta ta sauki ba.
 Tana zaune tana sak'awa da warwarewa aka turo wata
yarinya kiranta, kamar ba zata tashi ba, sai kuma ta mike tabi bayanta tana
taraddadin abinda zata tarar. Matan jiya ne jere akan dinning din, sai uwar
gayyar daga gefe ta hade rai sosai tana mata mugun kallo, tun kafin ta karaso
ciki ta hau surfa mata ashar
"Saboda tsabar ke yar iska ce, abinda nace ki dafa daban
abinda kika dafa daban ko? Zo nan."
Kin zuwa tayi, ta k'ame a wajen tana kallon su
"Ji yadda ta tsare mu da ido Hajiya Lay, amma dai yarinyar
nan bata da kunya."
"Ku barta, bata san wacece Layuza ba, zan koya mata
hankali."
Bud'e baki Zeenat din tayi, tace.
"Ke nake aure ne wai ko shi?"
"Kutmelec! Ni kike wa wannan tambayar?"
"Toh ai naga dai iyaye na Bashir suka aura min ko? Me yasa
kike nuna kamar ni din me aiki ce a gareki, ni bansan ki ba, bansan wacece ke
ba kawai zaki dinga nuna iko akaina "
"Lallai yarinya, kinyi babban kuskure da har zan fad'a ki
mayar, toh dake da Bashir din duk a karkashi na kuke, kuma baki isa ki hada
miji dani ba wallahi, kinyi kad'an ace kece kishiyata, dan haka yanzu baki da
maraba da me aiki a gidan na, kuma dan ubanki dole kiyi duk abinda nace, na
samu labarin komai da yadda auren ya kasance, shegen kwadayi da son zuciyar
uwarki dake ya jawo miki, dan haka ki wuce ki yi abinda na saki kafin na taso
na yi miki mugun dukan da zaki kasa tashi wallahi."
" Ai da kawai daidaita mata shegen bakin nan nata akayi
gobe ba zata sake fad'a ki fad'a ba."
" Barta, zata gane kurenta."
Zumburo baki tayi, ta ki barin wajen ita a lallai basu isa ba,
ganin haka ya saka Hajiya Layuza tasowa aikuwa tana ganin haka ta kwasa da gudu
bata tsaya ba sai data kai dakin tayi saurin saka sakata tana maida numfashi.
***Tagumi Mama ta rafka, duniyar gaba daya ta daina mata dadi
tun bayan da ta tabbatar da babu wani abu da zata iya dan Abba sai da ya sake
jaddada mata akan duk wani abu da ya samu auren Zeenat toh ta tabbatar da
mutuwar nata auren, ada taso suyi duk wacce zasuyi amma daga baya sai tayi wa
kanta fad'a ta hakura ta zuba wa sarautar Allah ido, gashi ta kikkira wayar
Zeenat din amma ko da yaushe bata shiga, takanas ta tura Habib ya je har kofar
gidan amma sai ya tarar a rufe, abinda ya kara daga mata hankali kenan, ta saka
Abba a gaba tana kuka dole ya dauki waya ya kira Bashir din, ya kuma yi mata
handsfree dan taji. Maganar an je an ga gidan a rufe Abban yayi masa nan ya
shaida masa ai suna family house dinsu sai sun danyi kwanaki zasu dawo gida
haka al'adar gidan su take, addua Abban yayi musu daga nan ya kashe yana kallon
Maman da tayi tsuru tana ji har suka gama.
"Kin dai ji ko? Ko kuma address din gidan nasu zan
baki?"
"A ah." Tace a sanyaye tana mikewa. Cigaba da aikin
gabansa yayi dan be ga dalilin da zai saka ta tada hankalin ta ba, bayan sun
riga sun aurawa Bashir din basu da ikon bibiyar in da duk zai kaita.
***Zuwa yamma masarautar ta cika sosai, duk wanda Ammi ta
gayyato sun hallara, yan mata ne kyawawa masu aji suka fi yawa sai manya
tsirari wanda Ammi ta barsu sai ranar nadin dan kar ya zama an takure mutum,
Ba'a dau lokaci aka shiga gabatar abinda ya tara su, saboda a ranar su Mamma
suke so su wuce. Tsarin daban ne da duk wani taro da akayi na bikin, Muhammad
da be niyyar attending ba, amma ganin abinda ya faru ya sakashi shiryawa cikin
shigar da yasan zai burge Iman dinshi, wanda be san iya adadin yan matan da
suka sake faller masa ba a ranar. Yana zaune kusa da ita daf ya dan karkace
yana fuskantar ta, yana mata magana k'asa-kasa, tana jin sa sarai amma ta fuske
dan ta gama gane shi so yake suyi abin da zata sha kunya dan taga kamar shi be
san kunya ba sam. Daga nesa ba zaka gane yanayin da suke ciki ba, zaka dauka
yanayin zaman nasa na mulki ne, sai ka matso sosai zaka gane kan abun. Shigar
da Laila tayi a wajen ta kusan fin ta Iman din, babu laifi Allah ya hore mata
kyau ba kad'an ba, dan sanda ta shigo wajen sai da gaban Iman ya fadi ganin
uwar kwalliyar da taci kamar wata dawisu, kai tsaye wajensu ta nufo tana tafiya
tana karkada kowanne lungu da sako na jikin ta, kamar bishiyar da iskar rani ke
kadawa haka ta dinga karkada jikin ta har ta karaso wajen fuskar ta a washe ta
matsa daidai saitin Capt Muhammad ta rankwafo tana nunawa camera man sign din
ya dauke su.
 Da ido Muhammad yayi masa alamar idan ya dauki hoton sai
dai wani bashi ba, sum-sum ya bar wajen hakan ya bata wa Laila rai tace
"Capt wanne irin wulakanci ne wannan?"
"Baby kinga waccar da ta shigo yanzu?" Yayi kamar be
ji ba, ya matsa jikin Iman din yana nuna mata wata,
"Kanwar Ammi ce, itace Aunty Fatima."
"Ok wadda ka bani labarin ta ko!?"
"Yea ita."
"Allah sarki, she's nice."
"Sosai." Sai ya sake kai fuskar sa jikin ta sosai
"Baby perf din nan akwai kamshi, i just love it, yayi
dadi."
"Thanks dear." Tace tana smiling
Bakin ciki ne ya tuke Laila, tayi saurin barin wajen kafin
zuciyar ta, ta buga. Tana barin wajen sukayi wa juna murmushi.
A gajiye suka koma cikin gidan bayan an gama taron, su Mamma sun
jima da tafiya dan haka part din Ammi aka maida ita, daga nan Ammi ta saka
mutane da yawa suka yi mata rakiya zuwa nata part din da ta riga ta tare tun a
jiya ba tare da Ammin ta sani ba, sai gobe za'a rakata wajen Bubu idan ta huta
shi ma baya nan yau sai goben zai dawo.
  Masu kula da bangaren da duk wani abu da ya shafe
ta Ammi ta nuna mata, suna isa kuwa suka shigar da kayan su dakunan su dake
bayan part din suka shigo suka fara aikin gyara shashen, suka gama suka saka
masa turaren wuta sannan aka jere musu abinciccika masu rai da lafiya. Sai da
suka tabbatar babu wani abu da zata bukata sannan sukayi mata sallama suka
tafi.
  A gajiye take sosai amma kuma dole tayi wanka dan
sosai Mamma ta jaddada mata muhimmanci wanka da gyara jiki, cire kayan jikin ta
tayi, ta zari towel daya ta daura ta nufi toilet din, wanka tayi ta hado da
alwala ta fito tana sharce kanta. Wayarta ce tayi kara ta dauka tana dubawa,
Mommy ce ke kiranta, tunda aka fara bikin basuyi magana ba, sai dai ta jisu da
Mamma suna yi, zama tayi tana daga wayar dadi na cikata
"Mummy barka da dare."
"Iman... Kuna lafiya?"
"Lafiya lou mummy, dama yanzu nake so nazo na kira."
"Ko? Toh gashi na kira ni ai, ya sabon waje?"
"Alhamdulillah."
"Mamma ta sanar dani duk yadda abubuwan suka kasance, nasan
kuma duk abinda ya kamata ki sani ta sanar dake, dan haka ita rayuwar aure yar
hakuri ce, sannan duba da irin gidan da kika samu kanki, sai kinyi hakuri kin
kuma zama me lura sosai."
"In Sha Allah mummy."
"Yawwa, ki kula sosai da mijinki da duk abinda kika san
yana so, karki ga tarin ma'aikata ki sakar musu kula da mijinki, duk wani abu
da ya danganci mijinki ki taske kiyi shine hanyar samun ladan ki, kuma hanyar
aljannar ki."
" In Sha Allah Mummy, nagode sosai."
"Ki ajiye kunya ki kula da mijinki sosai, banda sanyin jiki
da lalaci."
A kunyace tace
"Toh mummy."
Turo kofar akayi, yana sanye da 3quarter wando babu riga a jikin
sa, saurin dauke kanta tayi tana amsawa mummy bayanin da tayi mata akan wasu
magunguna da ta saka mata a bag dinta. Gabanta yazo ya tsaya k'yam yana karewa
cinyoyin ta dake bayyane saboda kankantar towel din. Tsugunawa yayi a gabanta
ya saka hannu ya shafa saman cinyar ta ta, tayi saurin janye su tana jan
numfashi,
"Kina ji na Iman?" Mummy tace jin kamar attention
dinta ya tafi wani wajen.
"Am.. am ina ji Mummy."
Ta amsa a firgice ganin ya kai hannu jikin towel din ya janye,
da sauri ta saki wayar bayan ta danne power button din, ta mike tana rik'e
towel din. Idonsa a shanye yake kallon ta
"Zanyi wanka."
Yace yana shigar da idonsa cikin nata, kasa matsawa tayi daga
wajen, sai jan towel din take a dole sai ya sauka ya rufe bayanta. Bata taba
jawowa zai shigo a lokacin ba, ta yi tunanin ma ya tafi, sai ganin shi tayi.
Dariya ta bashi,yadda ta hakikance a dole sai ta saukar da towel din.
"Zanyi wanka." Ya sake maimaitawa yana folding hannun
sa, kamar ta dora hannu a ka tayi ta kurma ihu ta shiga takawa zuwa toilet din
tana cigaba da jan towel din. Ji tayi an rungume ta, ta baya ya dora kansa a
saman kafadarta.
"Me kunya, kunyar me kike ji?"
"Ba komai."
"Shine kike ta jan towel din bayan halal dina ne, sai a
barni na more kallon kayana ko?"
"Uhum".
" Emana. " Ya sake tura kansa wuyan nata sosai,yana
jujjuya kan, hakan ya haifar mata da kasala, ta dinga kokarin zamewa amma ya
hanata, a dole ta kyaleshi yayi budurin sa. Sai da ya tabbatar da tayi laushi
sosai sannan ya jata zuwa toilet din. Mamakin rashin kunyar sa take, shi ko a
jikin sa babu abinda ya dame shi, ita kuwa kamar ta shide idan ta kalleshi a
hakan sa, da k'yar ta samu ya barta bayan ya kara tattabe ta, ta samu ta fito
ta barshi a ciki, a gurguje ta shirya ta saka kaya ta tada sallah ko da ya fito
tana sallah sai kawai ya shirya shima ya fita falo dan cikin sa ya fara kiran
yunwa. Zaman jiranta ya dinga yi jin shiru bata fito ba ya leko ya kirata, dan
baya so a kara kwana be bata labarin komai ba, a kalla hakan zai saka ta sake
yarda dashi ta kuma taimaka masa dan ita kadai ce ta fara ganin Laila sanda ta
shigo part din. Tsattsakurar abincin tayi tace ta goshi dan da gaske tsoro take
ji, tsoron kar yace zai sake yi mata irin abinda yayi mata jiya, ba zata iya
dauka ba, shiyasa tana gama ci ta sulale ta gudu ta kwanta ta kudundune a dole
tayi bacci. Sai da ya gama komai sannan ya biyo ta dakin ya yaye abinda ta
rufan yana shigewa jikinta.
Post a Comment for "HALIN GIRMA 21-25"