HALIN GIRMA 16-20
Halin Girma
16
*****************
Yana zaune a daki kiran Aunty Faty ya riske shi, dagawa yayi yana tashi dan yasan dalilin kiran
"Mun shirya tafiya kawai zamuyi kana ina ne?"
" Ina cikin gidan bari nazo."
Yace yana cire wayr, takalmin sa ya zura ya fito falon, fadawan dake wajn part din suka yunkuro jin motsin sa, da hannu yayi musu alamar kar su bi shi ya shiga takawa zuwa shashen Fulani da ya san a chan zai same su.
Babban falon ta ya nufa in da ya tarar da su da yawan su, daga gefe akwatuna ne masu yawan gaske, da ido ya bi kayan kafin ya zauna suka hau tsokanar sa da ango ango, yawancin su yan uwan Ammin sa ne,sai dangin Bubu da matan abokan sa da badu da yawa sosai, komai Takawa yace sai Bubu yace masa ba sai an zo ba, ayi komai a nan din kawai. Yanzu ma dan dai abun kamar al'ada ne, shiyasa kawai Takawa yace ya kyale su idan yaso sai ya zama ba kowa da kowa ba.
Anty Faty ce ta tashi ta hau nuna masa yadda kayan suke
"Wannan saitin na Takawa ne, gasu nan 12 ne cip, kaya ne na alfarma komai da kasan ya kamata a saka an saka ciki, sai wannan masu pink din su kuma saitin Ammi ne, suma Sha biyun ne kamar na Takawa, wadannan kuma masu purple din na Hajja ne da dan tsohon mijin ta Aji, guda shida ne gasu nan ko? Sai masu maroon din nan na karshe, namu ne dan muma ba za'a bar mu a baya ba, suma guda 6 ne idan ka hada set nawa kenan? "
" 36!" Yace yana sake bin kayan da ido.
" Wadannan kwandunan kuma, gasu nan guda 24 kowanne da ka gani, abokin Bubu Maimartaba sarkin Ghana ne ya aiko dasu."
" Allah sarki." Yace yana murmushi
" Kilishi fa?"
" Auw kaga na manta ko? Gasu chan fito dasu Harira."
Tayi wa daya daga cikin bayin dage tsaye daga gefen kayan magana,
" No a barsu bana bukatar su, a barsu anan zan duba su daga baya, akwai kayan da za'a kai na rabon da zasuyi a dangi, suna cikin Ford 2 nasa an saka su, zaku duba kafin ku wuce, komai yayi in sha Allah."
" Owk shikenan, kaga wadannan boxes din da kasa aka yi musu design a dubai da hoton ku?"
" Na gani aunty sunyi kyau sosai, su nake so a fara fitowa dasu, dan Allah aunty ayi duk yadda nace."
" An gama karka damu."
" Shikenan, Musaddik zai shige muku gaba, ya za'a yi tafiyar?"
" Eh da wai kamar motoci goma haka, sai wanda za'a zuba kayan Hilux din Takawa masu rufin bayan nan, idan yaso sai su biyo baya ko?"
Murmushi yayi me aji, ya girgiza kansa yana ayyana kalar tsiyar da ya shuka yana kuma jinjina abinda zai faru nan da wasu yan awoyi. Bed room din Fulani ya shige, ya sameta da yan uwata da suka zo, ya zaune tsakanin wasu tsofaffi biyu ya dinga tsokanar su ya hanasu sakat, kowa ya ganshi yasan yana cikin farin ciki mara misaltuwa, yanayin sa kadai zaka san ba karamin murna yake da auren ba, su kuwa basu san harda murnar hawan jinin da ya tabbatar zai kama Mama, dama ita hassada ga mai rabo taki ce, idan kuma zaka gina ramin mugunta toh ka gina shi gajere baka san ko kai ne zaka fad'a ciki ba.
****Mama babu zama tun da taga yamma tayi ta tabbata suna hanya ko sun kusa zuwa, tayi nan tayi nan duk farin ciki ya hana mata sakat, karar tsayawar manyan motoci a kofar gidan ya saka kowa nutsuwa aka hau sake gyara wajen, kowa ya zauna ana dakon shigowar su.
Gate din gidan me gadi ya bud'e da sauri, aka shigo da motocin da akwatunan suke ciki, sauran aka bar su a waje saboda babu wajen da zasu shiga dukka.
Sauke akwatunan aka fara yi a harabar wajen, kafin su gama sauke su dukka guda talatin da shida, sai baskets din suma. Boxes din da Anty Faty tayi masa magana akai suka riko kowacce mace ta rik'e daya a hannu dama yan kanana ne, matan da Mama ta wakilta da idan sun zo su tare su ne suka karaso kowanne fuskar sa dauke da fara'ar suka tare su sannan suka yi musu jagoranci zuwa ciki, Mama na zaune an sha lullubi da kayan alfarma suka shigo, ta bisu da kallo ta kasan Ido, mata ne hamshakai wanda suka amsa sunan su mata, hutu da jin dadi ya kama jikin kowacce kai ba sai an fad'a maka ba. Rawar jiki jamaar Mama suka fara su a lallai an zo wajen su, dangin su Abba na gefe sun zama yan kallo, akwatunan aka dinga shigowa dasu Mama ta hadiye wani yawu me karfi, cikin al'ajabin uban kayan da ake ta shigo dasu, gaba daya ma sai ta bata lissafi suka dinga yi mata gizo, kamar ta tashi ta hau bubbudasu taji, wani farin ciki na ziyartar ta. Duk gaishe gaishen da ake tsakani bata wani fahimta saboda yadda ta tafi tunanin kalar hutu da gatan da Zeenat zata shiga, gashi alamu sun nuna dangin mijin nata masu karamci ne, basu da nuna kyama ko wulakanci ko kadan.
"Baki ne daga gidan sarki, mun kawo lefen dan mu, jikan Maimartaba sarki, sannan d'a ga sarkin Adamawa Alhaji Ahmad Santuraki,Ina mahaifiyar amaryar tamu take?"
Mama tayi firgigit sanda taji wata cikin matan na tambaya, murmushi ta yi tana sake kama kanta ita a dole akwai surkutar nan. Aunty Faty ce ta tashi tsam, ta isa gaban Maman ta mika mata akwatin hannun ta, dake dauke da hoton Moh da Iman da ita kanta Iman din idan ta gani zatayi mamakin yadda ya same shi, hoton yayi masifar kyau zaka rantse tare suka dauka, yana sanye cikin shigar babbar riga da rawani, yayi wani murmushi da zaka kalla ka sake kalla. Wani irin shock Mama taji lokacin da ta karbi akwatin a hannun ta hoton da yake jiki ya shiga cikin idon ta ya aikawa da kwakwalwarta sako a take.
"Wannan itace kyauta ta farko ga yar mu Fatima, akwai sauran kyaututukan da bazasu kirgu ba, amma dai ita wannan din ita ce zamu iya cewa ja gaba ga sauran."
Kamar mutum mutumi haka Mama ta dinga kallon matar da take mata wani yare da sam kwakwalwarta ta gaza dauka balle ta fassara mata abinda matar take cewa.
"Wadannan kayan kad'an ne daga cikin abubuwan da muka tanadawar Fatima, in sha Allah ba zata taba dana sanin amincewa da dan mu Muhammad ba.
" Dan sarki jikan sarki kuma sarkin gobe idan me dukka ya kaimu."
Wata mata tace daga gefe, duk suka amsa da in sha Allah.
Guda aka saka a wajen, gudar da Mama taji kamar an saka allura ne ana chacchaka mata a tsakiyar kanta, kokarin sakin box din hannun nata take, wata kanwar su Abba da take lura da ita tuntuni ta taso da sauri ta karbe tana ma yan uwan Maman kallon banza.
"Masha ALLAH, lallai mun ga Halin Girma da karamci na wannan babban gida, mun kuma tabbatar da yar mu ta shiga hannu na gari"
Ta fad'a bayan ta koma wajen zaman ta, ta kuma mikawa wata babba a dangin box din. Murmushi matan sukayi dukka, sannan aunty Faty tace
" Sai a bude kayan ko?"
Da karfin guiwar su dangin Abba suka tashi, aka fara bud'e box din farkon nan, kowa ya shiga mamaki, mukullaye ne wajen guda uku na mota, sai mukullin gida da takardun su, sai kuma wani babban set of gold masu girman gaske. Wata irin guda da tafi ta dazu aka sake saki, jira ya soma dibar Mama, ta kasa gane komai sai hajijiya da take ji kamar zata kayar da ita daga zaunen da take, me yake faruwa? Me yake shirin faruwa.
Daya bayan daya aka dinga bud'e kayan, tun mutane na irgawa har kowa ma ya gaji aka zuba ido ana kallon tarin dukiya, dukiya me sunan dukiya, dangin Abba da Mama ta dinga dagawa kai sai suka zama kamar sune kawai a wajen, farin ciki suke dama kowa yaji haushin abinda Maman tayi a dan tsakanin gabatowar bikin, sai kuma yadda ta dinga yada habaici a ranar da za'a kawo kayan wanda suka tabbatar dasu take shiyasa suka ji haushin ta sosai, amma yanzu da haka ta faru sai suka hau murna suka dinga yin abu da gayya dan su kara haukata Maman.
Tashi sukayi bayan an gama ganin kayan, aka damka duk wasu abubuwan da suke da muhimmanci sosai kamar golds da takardun gida da keys a hannun kannen su Abba sannan suka yi musu sallama, abubuwn da aka shirya da sunan Zeenat suka je suka dauko aka saka musu a mota, basu ma so karba ba amma yadda suka dinga insisting yasaka suka karba dan kar suga kamar sun raina musu ne.
Suna gama fita daga gidan masu kawo kayan Zeenat ta shigowa, mata ne kwantsam masu mugun yawa, masu goyo ne, gasu nan harda wanda suka ciko bus suka zo. Ana kokarin daga Mama a maida ta cikin daki sanarwar zuwan su ya katse su, a sanyaye suka dawo suka zauna, suka shigo bayan an matsar da kayan Iman an tura wasu dakin Abba da dakin Maman.
Da kallon bakin ciki Mama take bin su, kamar ta tashi ta hau bugun su haka taji, yaran da suka zo dasu suka dinga ihu na goyen sai da aka sakko su, na hannu kuwa suka hau wasa a falon. Gaisawa akayi suka gabatar da kansu, kafin ma su dire sunan Zeenat din Mama ta ja numfashi da take jin kamar zai fice daga jikin ta.
"Kuyi hakuri asthma ce da ita nema take Kuma ta tashi tun dazu, tashi Yaya mu shiga ciki ki huta."
Aunty Maimuna kanwar Maman tayi saurin rufawa ta janye Maman dan ta hango matsala babba, kamar ma kokawa take da numfashiin ta. Suna shiga dakin ta kurma ihu, ihun da kowa ya ji shi, da tayi sauri ta saka hannu ta rufe mata baki
"Haba Yaya Hajara, ai sai aji kunya, dan Allah kiyi hakuri."
"Kutmar uban hakuri, kike ce min nayi hakuri? Bayan kinga abinda ya faru? Kinga yadda Ibrahim ya munafurce ni da yan uwansa? Bayan duk halaccin da nayi musu ? Amma kike cewa nayi hakuri, ke kinsan me nake ji? Innalillah, wayyo Allah na."
" Ni dai kiyi hakuri, ko ma menene ki bari a gama taron nan, kinga mutane zasu tafi dake a baki."
" Taro? Ke kina ganin za'a cigaba da taron nan?"
" Toh me za'a yi Yaya?"
" Ba zai yiwu ba, wallahi sai dai a fasa auren, amma ba zan bari bakin ciki ya kashe ni ba a banza." Sai ta sake fashewa da kuka, kuka irin wiwi din nan da kana gani zaka tabbatar da ba karamin kuka mutum yake ba. Duk yadda Aunty Maimuna taso ta bata baki tayi hakuri ta kasa, sai kawai ta fito ta rufo mata kofar ta dawo wajen bakin, lokacin har an soma bud'e kayan, akwatu na guda hudu sai kit daya, da kayan ta masu kyau daidai da tsarin akwatunan, amma ganin da mutane sukayi wa kayan Iman ya saka zasu ga na Zeenat din kamar bola, a daddage kowa ya kalla, suka dauko dubu ashirin suka ce gashi nan ta kai dinki ba'a samu an dinka ba saboda kurewa lokaci. Daga haka sukayi musu sallama aka je dakin Mama a dauko ragowar kayan da suka rage ta ce idan an basu ko ruwa ba'a za'a basu ba, da k'yar Aunty Maimuna ta bata hakuri aka saka musu ruwa da lemo a bayan mota suka tafi.
Daya bayan daya yan uwan Abba suka zo suka kwashe kayan iman suka maida su bangaren Gaji a cewar su kar bakin ciki da kishi ya saka Mama ta saka wuta ta kona su.
Hauka hauka Maman ta soma da suka shigo, kowa yayi mata banza suka dinga dariya suna yada mata da magana, suka kwashe komai suka yi tafiyar su. Jiki a sanyaye kawayen Mama suka dinga sulalewa suna guduwa kowa burin sa ya isa gida ya bada labarin abinda ya faru.
Zeenat na wajen saloon suna ta waya da Bashir kiran Maman yake ta shigowa tana kin dagawa, da dai taga kiran ya ishe ta sai tace ya bari ta daga wayar Maman, katse nasa kiran tayi ta daga na Maman.
"Kina gidan uban wa wai?"
"Mama kinsan fa ina saloon."
"Toh ki bar komai kike ki taho gida, kizo yanzu ki same ni."
"Mama ban gama ba, kuma kinga zamu je mu siyo head din da zan saka da dinner da Bashir daga nan..."
"Bashir din yaci abu ta kaza uban sa, na rantse da Allah kika bari man da awa guda baki dawo gida ba, sai kinga yadda zan miki" tana kaiwa nan ta katse kiran, saroro Zeenat din tayi rik'e da wayar cike da mamakin Maman.
"Me ya faru kuma?" Ta Tambayi kanta cike da mamaki.
Safa da Marwa Mama ta dinga yi a daki tana jiran Zeenat, ko sama da kasa zata hade ba zata yarda ayi auren nan ba, tasan idan ita kanta Zeenat din tazo taga abinda ya faru zata ce ta fasa ne, shege matsiyaci dama munafurtar su yayi kenan.
" Yaya Hajara da kin zauna kin nutsu, tashin hankali ba zai gyara komai ba."
" Ba zaki gane halin da nake ciki ba, ba zaki gane ba, ina cikin tashin hankali, bayan kunyar da nake ciki." Ta fad'a tana cigaba da zagayen, idanun ta ya kada yayi jajur taci kuka ta godewa Allah. Jugum sukayi kowa da abinda yake rayawa a ransa. A haka Zeenat ta shigo ta same su, Mama tayi kanta da sauri ta fizgo hannun ta da sauri.
" Kika ce min talaka ne, kayan jikin sa ma a yayyage, daga gani bashi da komai."
"Waye? Wai Mama menene ya faru?"
" Ubanki, bake ce kika ce min wanda yazo neman auren Iman talaka bane?"
" Eh Mama, dan baki ganshi ba."
Dundu Mama ta kai mata ta goce cikin bacin rai tace
" Toh dan ubanki dan sarki ne."
" Sarki!!!" Zeenat ta fad'a da karfi tana zaro ido
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_1aHALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
1/21/22, 12:57 - Buhainat: Halin Girma
  17
Hafsat Rano
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇ðŸ¾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
****************
"Sarki!" Ta zaro ido cikin tsananin kaduwa
"Laifin ki me, duk laifin ki ne, da baki yi min karya ba, da baki boye min abinda kika gani ba, da nasan abinda ya kamata nayi tun a lokacin."
"Haba Yaya Hajara, komai fa da kika gani ya faru toh dama chan haka yake a rubuce."
" A ah Maimuna, wannan kam sakaci na ne, ni ce duk na jawo komai, gashi yanzu bansan yadda zan ba, komai ya kwabe min."
" Hakuri kawai zamuyi mu tayasu da addu'a, kudi ba shine kwanciyar hankali ba,rufin asiri shine, idan har Bashir din zai kula da ita ai shikenan, a hankali sai suyi kudin su."
" A ah, ba zai yiwu ba, shegen yaron nan da har zai iya yaudarar mu, ya ha'ince mu ke kinsan ba mijin kwarai bane, dole Dr yazo a sake sabon zama, wallahi ba zan bawa yata mayaudari ba."
" Toh wai yama akayi? Kika ganshi a fakiri sannan kuma ya koma dan sarki? Ta yaya hakan ta faru? Bayan babu wani abu da ya nuna hakan tun farkon zuwan sa?"
" Salamu alaikum." Habib ya yi sallama kafin ya shigo dakin, su i su ne a ciki shiyasa ya shigo kai tsaye, ya gaida sisters din Mama sannan ya kalli Zeenat dake gefe tana matsar kwalla, yayi kwafa ya zauna akan kujerar gaban mudubi yace
"Kiyi hakuri Mama dan Allah, amma ni da kaina na fad'a miki Bashir ba mutumin kirki bane, yanzu dai hakuri kawai za'a yi tunda lokaci ya riga ya kure, dan Allah karki yiwa Abba wata magana kinsan dai ba zai saurara ba, dan Allah ki kwantar da hankalin ki, kiyi musu addu'a arziki ai na Allah ne. "
Wani kallon banza Mama tayi masa, kafin ta nuna masa kofa
" Fice ka bani waje bana bukatar maganar ka. "
Mikewa yayi, yana jin babu dadi abinda Maman take yi, tun daga irin rikon da tayi wa Iman din wanda sun sha haurawa sama a kai idan yayi mata magana, daga baya sai ya daina kawai ya watsar amma kuma ya kan yawan yiwa abokin sa sadeeq maganar ta akan zai bashi Iman din saboda yadda yaga zaman da take yana so yaga ta samu yanci, akwai ranar ma da hira ta saka ya kwashe komai ya sanar wa sadeeq din duk da yasan kamar tonawa mahaifiyar sa asiri yayi amma kuma ya zai? Baya jin dadi sam.
 Kofar ya ja musu ya bar gidan ma gaba daya dan ba zai zauna ya cigaba da kallon bacin rai ba. A waje suka hadu da Abba ya aike shi karbo wasu kaya sai kawai ya biya ya dauki sadeeq suka wuce tare.
 Â
***Har dare Abba be shigo ba, idon Mama kamas tana jiran sa, Zeenat ma idon ta biyu sun shirya samun Abban ita da Maman ayi magana dan da gaske take ba zata kuma auri Bashir ba yanzu, musamman bayan taga kayan da aka ce wai nata ne, toh wai mana, dan bata saka rai ko hasashen irin su ba ko kad'an.
  Kamar Abban yasan za'a yi haka yaki shigowa da wuri har sai da suka soma kosawa, gaba daya duniya bata musu dadi sam, Bashir sai kiranta yake amma sam taki dagawa dan bata da lokacin sa balle ta wayar sa.
  Wajen sha biyu Abba ya shigo bayan ya gama kallon kayan iman din a bangaren Gaji duk da be iya kallon komai ba sama-sama shima don sun matsa masa ne, Gaji ce ta kirashi daki tace ko me Maman zatayi kar ya yarda ya biye mata, ayi a gama komai lafiya shine kawai.
  Yana shigowa ya gansu a falon Zeenat na rakube a k'asan kujera tana cigaba da matsar kwalla, yi yayi kamar be gansu ba, yayi hanyar dakin sa Mama tayi saurin tare shi
"Dr."
"Kinga dai a yadda na shigo kinsan akwai gajiya, ki bar duk wata magana zuwa gobe da safe idan ALLAH ya kaimu."
"Ba zai yiwu ba, idan na bari aka kai gobe na samu matsala, yanzu zamuyi ta mu san abinda muke ciki."
Kada kansa yayi ya dawo ya zauna sannan yace
"Ina jinki."
"So nake a fasa auren Zeenatu, ba zata auri Bashir ba."
Wani banzan kallo Abban yayi mata, kafin ya hade rai sosai yace
"Ashe ma ke mahaukaciya ce ban sani ba Hajara, Ashe baki da tawakkali ma, ashe ma baki san komai game da rayuww ba, bari kiji."
Ya juyo yana kallon ta
"Dama shi sharri dan aike ne da kike ganin sa, duk in da yaje sai ya dawo, dan haka Wallahi, Wallahi kinji ma rantse ko?"
" Ba zan karya alkawari na ba, ba kuma zan zama mutumin banza ba, sai dana jaddada muku ke da ita gata nan, nace kunji kun gani? Sai yanzu da ya rage yan awowi shine zaku zo min da maganar banza? Saboda bansan me nake ba ko?"
" Idan kana kaunar Allah Dr ka rufa min asiri a fasa auren nan dan Allah!"
" Lallai Hajara kin haukace, wallahi babu abinda zai hana auren nan sai dai idan cikin mu biyu babu wani, ko ni na mutu ko ita Zeenat din ta mutu, amma in dai da ranmu da lafiyar mu wallahi sai an yi, kinji ma na gaya miki."
" Abba dan Allah kayi hakuri, wallahi zan iya mutuwa."
" Allah ya jikan ki."
Ya tashi yayi shigewar sa daki ya saka key kar ma ta samu damar biyo shi dan a yadda ya hangi tashin hankali a idon ta, zata iya jure su kwana a tsaye akan maganar da babu komawa baya.
Wani irin marayan Kuka Zeenat ta fashe dashi, bata san ba son Bashir take ba, kwadayin abun sa da kuma kishin Iman ya sakata ganin kamar son nashi take, sai yau ta gane kawai bakin cikin da take wa Iman ne ya sakata amince dashi.
 A zaune suka kwana, babu kalar tunanin da Mama batayi ba akan washegarin, har da tunani ko ta dauki Zeenat ta gudu da ita? Kafin gari ya gama haske tuni hayaniyar gidan ta cika ko'ina wanda ta tabbatar da gangan suke yi don a kular da ita.
  Da k'yar taayi sallah ta saka Zeenat ma tayi lokacin yan uwa har sun tashi sun fara gyara shashen Maman.
  Dakin Abba Mama ta shiga, ta same shi ya fiddo sabbin kayan sa da zai saka ya ajiye a saman gado, yana waya da Maman Iman, duk da ta shigo amma be daina wayar tasa ba, ya cigaba da yi mata bayani
"Masu zuwa daurin auren su taho da ita, kinga anan dinma za'a so a ganta, in yaso daga nan sai a wuce kawia da ita."
"Owk shikenan."
Ta amsa sannan ta kashe wayar. Haushi ya sake turnuke mama amma ta share dan ba abinda ya dameta bane a yanzu, matsalar da take ciki yanzu tafi wannan.
"Ina kwana?" Ta durkusa a k'asa ta gaishe shi,
"Lafiya lou." Ya amsa a gajarce yana cigaba da duba sakwannin wayar sa.
"Dan Allah Dr kayi hakuri, hannun ka baya taba rubewa ka yanke ka yar, kar ka hukunta yar ka akan laifin da ni na aikata, naji duk hukuncin da zaka yi min kayi min amma dan Allah a fasa auren nan."
" Kinsan Allah?" Yace yana ajiyewar wayar hannun sa
" Ba zan fasa auren nan ba, iyayen yaron nan sun zo na karbi maganar su nayi komai har sun kawo lefe sai yau ranar kawai kice a fasa? Nace musu me kenan? Tun farko ban fad'a muku ba? Ban nuna muku illaar abinda kuka nace akai ba, kuka nuna min ku ba zaku fasa ba, har kika saka zeenatu ta watsa min k'asa a ido ina mahaifin ta, ko da ace Bashir yaron kwarai ne idan nace ta hakura dashi ba zaki taimaka wajen ganin ta yi min biyayya ba? Amma me kikayi? Sannan sai yanzu, sannan zaki zo min da maganar banza, ya kike so nayi?"
" Dan Allah nidai kayi hakuri ka yafe mana,dan Allah ka taimaka."
" Wallahi Hajara babu abinda zan iya akai, kinji ma na rantse, ki barni dan Allah."
Zama tayi dabas a k'asa, sai kuma ta tashi da sauri ta fice ta nufi shashen Gaji, ta same su a falon yan uwa ana ta shewa, ta wuce su zuwa ciki kamar wadda ta zare. A k'asa ta tsuguna ta gaida Gaji wanda rabon da tayi haka an dade.
" Dan Allah ki taimaka ki saka baki Dr ya fasa auren nan, wallahi idan akayi auren komai zai iya faruwa, nasan ke kadai yake jin magana dan Allah."
" Yana ina?"
" Yana gida, dan Allah ki taimaka min."
" Kije kice idan ya gama ina neman sa, Allah ya kyauta ya rufa asiri, sai a hakura kawai."
Tashi tayi da sauri, ta manta ko godiya bata yi ba, ta fice kowa ya bita da kallon mamaki cike da jin haushi. Ko da ta fadawa Abban be ce mata komai ba, da ya fito ya shiga wajen Gajin bata yi masa maganar ba, ya gaisa da kowa sannan yayi breakfast da masa ya wuce wajen yan uwan sa.
 Â
***Daren ranar Moh be runtsa ba, duk wasu bakin da zasu iso sun gama isowa a lokacin kowa an sama masa masauki na alfarma. Abokan sa da sukayi karatu tare suke kuma aiki tare sai dai kowa wajen da take daban ne suka sauka a cikin gidan a bangaren Moh din, kafin a daura auren su wuce adamawa sannan su sake dawowa Kanon saboda events din da za'a yi a Kanon.
  Raba dare sukayi ana hira, anan suke fad'a masa suma fa sun shirya masa kayataccen bikin sword crossing amma a abuja saboda suna so manyan su na wajen aiki su ma su zama sun samu halarta. Abubuwan sun so suyi ma Moh yawa saboda shi dai tsakanin sa da Allah zai fi so ace da an daura auren kawai su yi tafiyar su shi da ita,amma kowa kokari yake ya shirya wani abu da zai sake rik'e su, shi dai kawai dan kar ya fito fili yace baya so ne, amma har ga Allah da kowa ya hakura.
  Da suka tashi da safe ma wasu suka dora da hirar in da Musaddik da wasu ciki suka tafi karasa abubuwan da basu samu gamawa ba, duk da sai bayan sallar juma'a za'a daura auren kuma komai da ya kamata su yi an ma riga an gama amma suma zasuyi nasu kokarin ko yaya ne.
  Tun wajen sha biyu Takawa ya saka aka kira masa Muhammad, ya same shi da manyan mutane har da Mr President sai Bubu da tasa jama'ar. Aji dan tsoho ma ba'a barshi a baya, yaji dadin ganin su musamman Aji da be saka ran zuwan nasa ba. Bin su yayi daya bayan daya ya gaishe su dukka, kowa ya kawo kyautar bangirma ya damka masa, harda masu blank cheque duk dan a birge Takawa.
  Godiya yayi musu dukka ya koma wajen jama'ar sa, suka dauki duk abinda zasu dauka suka wuce gidan Moh din dake Lamido Crescent yadda zasu fi yin komai a tsare.
 Â
***Wanka na wajen uku kenan idan tayi ta gama da wannan hadin ruwan sai Mamma ta sake bata wani, gaba daya wani irin sulbi fatar jikin ta take yi, tayi wani irin haske me kyau fatar ta sai glowing take kamar fuskar ta taji labari.
  Tun da aka soma mata gyaran jiki ta tabbatar da komai nata ya sauya, hatta lallen da aka yi mata da gyaran gashi na daban ne, bata kara tabbatar da gatan da take dashi ba sai a event din da aka yi jiya taga tarin mutanen da suka zo domin ita, kowa don ya ganta kawai. Tasha kyaututtuka daga kawayen Mummy da yan uwa kowa burin sa ya yi mata abinda zai burge mummy din.
 Sosai kuwa Mummy taji dadi ba kad'an ba, duk kuwa da miskilancin ta amma sai da yanayin ta ya sauya sosai.
  Bayan an yi taron an gama ne da daddare take bawa Iman din labarin yadda akayi suka rabu da mahaifin ta.
"Kinsan aure rai ne dashi, idan lokaci yayi sai an rabu, amma har gobe ina son mahaifin ki, kaddara ce kawai ta raba mu, a lokacin alhajin mu yayi fushi sosai akan auren da mukayi ba da sanin kowa ba. Alhajinmu me kudi ne sosai kuma dan siyasa ne, yana matakin senate president a lokacin, hakan ya saka dole Ibrahim ya sake ni akan kar abinda mukayi ya shafi mutuncin sa, dan wasu ba zasu taba yarda da cewa munyi aure ba, ko bayan an haife ki nan ma yace a dole dole sai ya karbi yarsa, ya rik'e ta dan baya son ko kad'an mutuncin sa ya tabu. Hakan ya saka Ibrahim yin fushi, ya karbe ki ya kuma yi alkawarin ba zai bani ke ba, nasha kuka nayi ta rokon sa ina masa magiya karshe yayi min alkawarin idan da rai da lafiya zai kawo ki idan kin isa aure."
" Amma fa ko bayan nan Alhaji yazo daga baya yayi regretting abinda yayi har ya nemi Ibrahim din da kansa ya kuma roke shi ya bashi ke, dan a lokacin girma yazo gashi yana son gyara, Mamma ce babbar mu gashi har lokacin Allah be bata haihuwa ba ,amma sai Abban naki yaki yace yayi hakuri ba zai iya ba."
" Ni banga laifin shi ba dan nasan shi da Zuciya idan har aka taba shi,karshe dai nima nayi aure bayan na kammala wani course da nake na auri wani dan siyasa Babba, na dade sosai a gidan kafin karshe Allah ya bamu haihuwa daya, na haifi yan biyu Amaan da Amaani, daga nan kuma sai muka rabu."
Shiru Iman tayi tana harhada maganganun.
"So kinga kowanne bawa baya wuce kaddarar sa, ni dake haka kaddarar mu take, dole ne kuma mu karbe ta hannu bibiyu mu gode wa Allah."
"Haka ne mummy, wallahi na zata so Amaan yaran Mamma ne."
Murmushi tayi
"Yaranta ne kam, tunda dai ni ban wani san komai akan su ba, Itace komai dinsu, Allah be bata haihuwa ba shiyasa ta dauki son duniya ta dora akan su."
"Hajiya fa?"
"Step Mom dimu ce,itace ta haifi Zayd."
"Allah sarki tana da kirki."
" Sosai, kirkin ta yayi yawan da karyar mutum ya shigo gidan nan yace ba ita ce ta haife mu ba, ita ta kula da koman mu, Itace kuma a matsayin mahaifiyar mu har gobe."
" Ashe akwai step moms masu kirki?"
" Akwai su da yawa Iman, ba dukka aka taru aka zama daya ba, wasu kuma zaki ga yaran ne basu da kirki sam, sun takura mata sun hana ta sakat, komai dai da kika gani akwai good side dinsa akwai bad side haka rayuwar take."
" Haka ne." Tace tana tuna Mama da Zeenat
Shirya ta aka yi cikin wasu yan ubansu kaya, kayan da ta tabbatar ba kananun kudi aka kashe wajen samar dasu ba, komai na jikin ta unique ne, me kyau da ya dace da ita. Sarkar gold din da Mummy ta siya mata Mamma ta saka mata, sannan ta zaunar da ita a gefen gado ta dauko mata abinci, ta zauna da kanta ta taimaka mata ta ci dan ta tabbata idan suka tafi babu batun cin wani abinci a wajen amarya. Ci tayi sosai sannan ta dauko wayar ta tana duba misscalls ko ya kirata, be kira ba, ajiye wayar tayi akan cinyar ta har lokacin tafiyar su yayi, text message ta tura masa ta saka wayar a jaka suka fito gaba daya, wajen Hajiya aka kaita tayi mata nasiha sosai kafin su nufi airport da su Ya Mubarak da sauran jama'ar da zasu halarci daurin auren, sai kuma su Amaani, Mamma da yan uwan su da zasu je a karasa bikin da su a matsayin dangin Mamanta.
  Mintuna kad'an suka isa dasu Kanon, dan ma basu taho da wuri ba, Abba ne ya saka aka je aka taho dasu daga airport din, aka sauke su a bangaren Abba babba, ita kuma Iman aka wuce da ita ta gaida Gaji sannan suka shiga wajen Mama.
  Gabanta ya fadi tun shigowar su, ko wanka bata yi ba, duk da ta dan samu nutswa bayan ta samu Gaji, tana da yakinin zata hana Abban kuma ya hanu, amma kuma jikin ta duk yayi sanyi tana dai zaune ne tana kallon kowa, masu kaya-kaya ma a cikin yan uwan ta haushin su take ji, gani take ai kamata yayi su tayata alhini. Kawayen ta kuwa da sun kirata take dagawa tace an daga bikin zata neme su, abinda bata sani ba zance ya gama zagaya ko ina wasu ma da gayya suke kiran dan su tabbatar.
Gaishe ta Iman take amma ta tsura mata ido ta kasa amsawa, tsabar bakin ciki ta kasa boye shi, mamakin yadda yarinyar ta sauya take, Ashe haka take da kyau bata sani ba? Ko Kuma dai yanzu ne kyawun ya fito. Kayan jikin ta kawai ta kalla tasan an kashe kudi, idon ta ya sauka akan sarkar wuyan ta, tana ta sheki da kyalli kana gani zaka gane zallar gold ne. Tari ne taji kamr zai sarke ta, duk suna lura da ita da suka ga kamar bata hayyacin ta sai kawai suka tashi suka koma in da aka sauke su.
Lokaci lokaci Iman na kallon wayar ta, ta matsu suyi magana ta san halin da ake ciki, ba zata kirashi ba dan tasan yana cikin hayaniya amma taso ko yaya ne ya kirata.
  Daidai lokacin da aka saka na daurin auren yayi, ta kwanta kawai lamo tana jin faduwar gaba, wani iri kamar tace ta fasa, ba'a gidan ake daura auren ba, a babban masallacin Kano ne da yake kusa da gidan sarki shiyasa basu san abinda yake faruwa ba.
  Ji tayi gidan yayi tsit, kamar babu mutane, ta dinga jin wani tsoro tsoro yana shigar ta, Mamma ce ta taba ta, tayi mata murmushi tace
"Kowacce mace ta kan ji irin haka idan za'a daura mata aure, kiyi addu'a kinji yata?"
Da kai ta amsawa Mamman, ta soma karanta hasbunallahu wa ni'imal wakil, a hankali taji nutsuwa na saukar mata. A daidai lokacin suka ji karar tsayawar motoci, kafin gidan ya kaure da wata irin guda me karfin gaske.
 Wani maroki ne me muryar tsiya, ya shiga kirari cikin muryar sa da ta shiga har kwakwalwarta, ta tsaya chak da tunanin abinda kunnen ta yaji
"Alhamdulillah, Allah mun gode maka, an daura auren Yarima Muhammad da amaryar sa Gmbiya Fatima, dan sarki jikan sarki, kuma sarkin gobe idan Allah ya kaimu."
Farin ciki ne ya kama su Mamma suka hau murna, bata fuskantar komai, a daidai lokacin sakon sa ya shigo wayar ta,
"Duba whatsapp dinki amarya tah."
Da sauri ta shiga whatsapp din har ta mantawa bata kunna data ba ,kunnawa tayi messages din suka shigo tayi saurin bud'e nasa. Hotuna ne masu yawa, ta hau bud'e su tana kura idon ta, hoton farko ya saka numfashin ta tsayawa na dan sakanni
"Capt Muhammad Ahmad Santuraki."
Yayi captioning hoton, yana sanye da nadi irin na sarauta, da kunnuwan sa guda biyu a sama da yake nuna yadda tsarin sarautar take, gaba daya gani tayi an sauya mata shi,shine sai wasu abubuwan da yawa da suka dauke ta zuwa wani tunani na baya tana kokarin alakanta abubuwan da tayi ta shakku akan sa. Kwanciyar fatar sa, da yadda yake magana yana bata mamaki matuka.
Sauran hotunan ta shiga bubbudewa, duk akwai shi aciki tare da manyan k'asar da ma ketare, hoton sa da Takawa da yadda Takawan ya rik'e shi says alot. Ji tayi gaba daya ya goge mata hadda, ya bar kanta blank bata ma san wanne irin tunani zatayi ba.
Wasu mata ne suka dinga shigowa, wanda kana ganin su zaka san su din hadimai ne daga gidan sarauta, duk suka taru waje daya cikin girmamawa suka hau gabatar da kansu.
Kayan hannun su Mamma ta saka suka ajiye a gefe sannan ta aika wata bangaren Gaji akan wasu suzo a cikin dangin Abban, hakan ya bawa Iman damar sulalewa ta shige dakin Umma, sannan ta kira Ya Maryam ya waya tace dan Allah tazo dakin Umma. Sai gata tazo har da saurin ta, murna fal fuskar ta dan suma ba karamin mamaki suka shiga ba.
Hotunan ta soma nuna mata, sannan ta hau mita kamar zatayi kuka, katse ta Ya Maryam tayi,
"Yarinya kad'an ma kika gani, sai kin ga uban lefen da aka kawo miki, wallahi Iman Allah ya baki miji, miji na kere sa'a me sonki tsakani da Allah, kinyi sa'a, halin ki ne ya jawo miki amma."
"Amma me yasa zai rufe ni?"
"Haka tasa salon soyayyar yake, kin ganshi kuwa? Salo,aji kyau ga kudi."
Turo baki Iman tayi, ta rasa me ma zatayi, Itace zata shiga gidan sarauta? Sarauta ma babba irin ta Kano? Katse mata tunani yayi da wani sakon nasa
"Meet me a seat room din Abba, na matsu na ganki, I want to feel you right close to me."
Da sauri ta kife wayar,. Maryam da taga komai ta kyalkyale da dariya
"Su Iman an shiga sahun manya, jeki dan Allah yaji duminki, halal dinsa ce ke yanzu ehe."
Duka ta kai wa Maryam din ta manta ma basa yar haka da ita, ta sake kwanshewa da dariya tana tsokanar ta
"Saura kije ki dinga wannan nuku nukun naki, tashi ki sake gyara jikin ki, bari naje na karasa jin drammer da ake a gidanku, Zeenat na chan ta tada aljanu wai ba ta yarda ba, kinsan an riga an daura itama."
"Kamar ya?" Tace cikin mamaki
"Jeki ke dai wajen aikin Allah, bari zan baki labari in details."
Ta juya da sauri ta fice bayan ta sanarwa da Mamma cewa Iman zata je yarima na seat room suyi hotunan tarihi.
Rano💕💕
#Note edited
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)Â s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_1aHALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
1/21/22, 12:58 - Buhainat: Halin Girma
  18
Hafsat Rano
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇ðŸ¾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
**************
Shigowa Mamma tayi, ta same ta a tsaye ta ma rasa abinda zatayi. Hannun ta, ta kama ta zaunar da ita, ta bud'e jakar da suka zo da ita ta ciro turare me dadin kamshi na daban ta fesa mata, ta duba fuskar ta sannan tace
"Ki kwantar da hankalin ki dan Allah,bari na duba kayan da yan matan nan suka kawo, ba za'a rasa alkyabba ba. "
Fita tayi sai gata ta dawo tare da daya daga cikin yan matan, ta russuna har k'asa ta gaida Iman din da gabatar da kanta da sunan ta Ummimi sannan ta matsa daga gefe,
" Tashi ta taimaka miki ta saka miki. "
Mamma tace tana murmushi, wani banbarakwai Iman taji, ta tashi cikin sanyin jiki yarinyar ta hau saka mata alkyabbar cikin k'warewa. Ji take tamkar mafarki, kamar zata farka taga komai yana yadda take. Har ta gama gyara mata, ta kawo sauran kayan ta sassaka mata ta fito sosai a gimbiyar ta mamaki be bar ta ba.
 Â
  Khadija da Zahra ne suka shigo, kusan sa'annin Iman din ne a family, doki ya saka su zuwa suka Iman din suma su bawa idon su abinci, suna shigowa dakin suka ganta cikin shigar da tayi masifar mata kyau, shigar alfarma.
  Hoto Zahra ta ciro waya ta hau daukar ta, kala kala har da videos dan dole ne yau followersa dinta na Instagram su kara kiyayarta.
  Kiran ta ya sake yi dan da gaske ya matsu ya ganta, irin matsuwar ba don idon sirikai ba, da dumbin jama'a da sai dai kawai ta ganshi a duk ma in da take.
  Mamma ce ta dakatar da hotunan haka, tace suyi mata rakiya zuwa in da Muhammad din yake, ko tace Yarima Muhammad dan sunan kam be chanchanci a dinga fadar sa haka nan kai tsaye ba.
  Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, haka ta tashi tana turo baki. Tare suka fito da biyu daga cikin hadiman yan matan nan, suna daga bayan ta suna take mata baya, domin da gaske Ammi tayi musu gargadi akan surukarta ta, su kula da ita da komai nata
  Suna zuwa daf da seat room din suka soma jin hayaniyar maza,amma ba irin hayaniyar da zaka ji ba irin ta wasu mazan marasa aji da tsari. Hayaniya ce ta nuna farin cikin su da taya murna cikin ilimi da wayewa. Ji tayi kamar ta koma da baya, dan yadda ta tsani taro na maza har ya zama tana ciki, bata san kalar kunyar da zata sha ba, dan da alama dukkan su masu surutu ne. Bata dai ji muryar uban gayyar ba, ta kamo addu'a ta soma yi har ta samu nutswar ta
"Iman." Ya kirata yana karasowa wajen, tare suke da Habib da abokin sa Sadeeq. Murmushi tayi masa
"Uncle Khalil, ashe kazo."
Murmushin yak'e ya maida mata, ya tuna da warning din da Moh ya kada masa, duk da yayi kokari matuka be saba ka'ida ba, yanzu ma dole ce ta sakashi zuwa tun da dai ba zai ki zuwa daurin auren Zeenat ba.
"Nazo Iman, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya."
"Amin."
Ta amsa a ciki tana jin babu dadi, lokaci daya yanayin sa ya sauya, yayi saurin barin wajen yana yin gaba, suka gaisa da Sadeeq da Ya Habib sannan suka wuce zuwa in da zasu.
  Sallama Ummimi tayi daga kofar, ta sanar da zuwan Iman din kamar yadda yake a tsarin masarauta, murmushi Moh yayi me aji, ya mike da kansa yana hararar su Ja'afar
"Amaryata tazo dan Allah muna bukatar privacy."
Dariya suka kwashe gaba daya, ya hade rai da gaske ba da wasa ba,su ka hau tsokanar sa amma yayi fumfurus yace wallahi sai sun fita. Musaddik ne yace
"Ai ka bari ta shigo mu gaisa ko? Sai mu fita daga baya."
Da kai ya amsa ya koma ya zauna yana jin rawanin da ke kansa ya soma gundurar sa. Shigowa sukayi bayan sun saka Iman din a tsakiya, idanun ta da tayi kokarin saukar dasu k'asa sosai suka shiga cikin nasa, da sauri ta dauke idon ta, ta zauna su Zahra suka sakata a tsakiya. Gaishe su sukayi suma suka amsa sannan suka gaisa da Iman din da take amsa musu ciki ciki dan ji take kamar ace fit ta fice saboda tsoro.
"Capt. Lets snap please."
Wani abokin sa Gbenga yace yana kallon sa
"Ok sir." Yace yana tashi, taimaka mata Zahra tayi, ta isa wajen da yake a tsaye, daga gefen sa ta tsaya, sai taji kamar ana saka abu ana bubbuge mata kafafunta. Hannun ta taji yana laluba ta cikin babbar rigarsa, ta daga kai da nufin kallon sa, shima a lokacin kallon ta yake, Ja'afar yayi sauri ya dauki scene din, hoton yayi masifar kyau, duk suka hau yabawa.
  Masifaffiyar kunyar da take ji ta hanata sakewa sam, duk da haka an dauki hotunan sosai sun fita, banda camera man suma wayoyin su duk babu na banza.
  Wani irin laushi hannun sa da yake cikin nata taji,ta tuna kullum cikin safar hannu yake zuwa mata, duk sanda zata ganshi hannun sa da kafar sa, na sakaye, sai yanzu ta gani dalilin nasa na yin hakan.
 Mammatsa mata hannun ya dinga yi, ya hanata sakat ya sakata a wani irin yanayi me wuyar fassarawa, gashi ya saka shi cikin rigar yadda ba wani wanda zai lura, sai da aka gama hotunan tas sannan suka fita suka barsu da nufin idan sun gama gaisawa sai su fito a shiga cikin gidajen ayi sauran hotunan a cewar Musaddik.
  Kamar me jiran kiris kuwa, suna gama ficewa ya saka dukkan karfin sa, yayi hugging dinta kamkam yana sauke tagwayen ajiyar zuciya.
 Â
"Alhamdulillah." Ya furta yana murmushi
"Mrs Muhammad Ahmad Santuraki."
Ya rada mata a kunnenta, ture shi tayi tana turo bakin ta gaba, ya tsaya yana kallon ta dan be taba sanin ta iya shagwaba ba sai yanzu
"Me yasa kayi haka?"
Tace cikin dan daga murya ita a dole ya bata mata rai, riko ta yayi da sauri ya dora hannun sa akan lips dinsa yace
"Shssh... Ba'a dagawa miji murya babu kyau."
Kokarin ture shin ta cigaba da yi amma sam ya hanata damar hakan, sai ma sake manne ta da yayi sosai da jikin sa suna shakar kamshin juna. Luf tayi ta daina motsawa kowa na sauraron bugun zuciyar dan uwan sa. Wajen minti daya suna a haka kafin ya saketa yana jan ta suka zauna a saman kujerar, ya rik'e hannayen ta yana kallon cikin idanunta
"I promise you ba abinda kike tunani bane, zan miki bayanin komai amma ba yanzu ba, yau ranar farin ciki ce, let's not discuss duk wani abu da be shafi ranar ba kinji matata? "
Turo bakin ta sake yi, ya saka hannu ya shafa yana murmushi
" I love that. " Saurin rufe fuskar ta tayi kunya na kamata
" Itama kunyar duk ina so, komai ma ni so nake kinji? Amma dai ki ajiye mana zuwa sanda zamu tare a gidan mu, ko nawa ne zan biya na siya. Bana so a samu matsala dan zai iya yin abinda ban shirya ba. "
Da sauri ta gyara bakin ta, ta kuma gyara zama tana matsawa kadan, matsowa yayi ta sake matsawa ya sake matsowa kafin ta samu damar sake matsawa ya saka hannu ya tokare ta, ya matso da fuskar sa daf da tata, tayi saurin runtse idon ta tana jin kamar zata saki fitsari. Light kiss taji yayi mata a saman idonta dake a rufe.
  A hankali ta bud'e idon ta, tayi saurin rufewa ganin yadda nasa ya sauya sosai.
" Amm.. amm muje kaga su Mamma da yan uwan mummy, sai Gaji da sauran yan uwan Abba ko? "
" Hmm. " Yace yana jan ajiyar zuciya
" Tohm bari na kira Musaddik yazo. "
Tashi yayi tsaye, ita kuma ta dukar da kanta k'asa, murmushi ta samu kanta da yi, tayi saurin katse shi ta sake saukar da kanta dan kar ya gani.
Dawowa su Musaddik sukayi, su Zahra da aka samu sabbin samari suka shiga ciki don sanar da shigowar su Mubamamd din.
  Ta bangaren Gaji aka fara, akayi hotuna sosai da kowa da kowa, sannan aka dawo in da su Mamma suke nan ma akayi musu, sai sauran mstan gidan da jikoki da sauran yan uwa da abokan arziki har ma da makwafta da suka shigo ganin kwaf.
 Â
***Yadda Zeenat ta koma zaka rantse tayi shekara tana jinya, gyaran gashin ma da aka yi duk ya hargitse kamar ba'a yi ba, ta tada aljanu yafi kala biyar duk da muryoyi kala kala akan suns gargadin in dai aka sake aka kai ta gidan sai sun kashe ta.
  Ko da Mama ta kira Abba ta fad'a masa cewa yayi karya ne, ya kashe kiran dan yana cikin mutane ne, amma kuma sai ya dinga jin babu dadi yana kuma tausayawa Zeenat din sosai, amma ya zai yi? Su suka jawa kansu duk da ba irin muna musu da be yi ba.
  Kayan kitchen su Aunty Maimuna suka dauka, suka kira Bashir din dan ba ma a samu damar zuwa an yi jeren kitchen din ba. Cewa yayi zai aiko a tafi dasu, ba'a dade ba kuwa sai ga wani saurayi yazo a golf irin ta hayar nan, dole suka saka Habib bin bayan su da wasu kayan bayan ya dauko yar kurkura dan yawan kayan kadai sun isa a yiwa wasu amaren biyu amfani dasu bayan Zeenatun.
  Sanda suka shigo unguwar gaban kowa ya hau faduwa, basu gama shiga masifa ba sai da suka ga kofar gidan da aka tsaida, katuwar kwatar dake kwance a kofar gidan ce ta fara tsorata su. Haka suka daure suka fito ya bud'e musu gidan suka shiga.
  Babban tashin hankali sanda suka shiga gidan suka tarar da kayan da suke gidan da Bashir din yace ya saka mata kaya kar ayi komai, su kansu kujerun bayan yadda aka daina yayin su, ba set bane dan babu three seater ko kankantar falon ya hanata shiga ko kuma ba'a yi da ita ba oho.
  Sanda suka shiga kitchen din sai da suka kusa kurma ihu, kwatan kwatan abinda Maman ta siya ba zai shiga kitchen din ba. Babu wanda yake wa wani magana a cikin su, suka saka abinda zai iya shiga kitchen din da ko kitchen cabinets babu, sauran na amfanin suka saka mata a cikin sip dan wannan ba za'a kirashi da wardrobe ba sai da sip😢😂 ragowar kayan suka juya dasu cike da tunanin yadda za'a kare da Mama. Babu maganar uban kayan turaren wutar da ta siya wajen hadaddiyar me turaren wutar nan*yerwa incense and more.*
   Shigowar su kenan suka tarar ana ta hotuna da Iman, jiki a sanyaye suka wuce bangaren Maman suna taraddadin yadda za'a kwashe. Mama ma jin ance sun dawo ta yi zumbur ta tashi, sai dai tun kan su gama zama ta san da matsala.
  Aunty Maimuna ce ta jata daki tayi mata bayanin komai sai ragowar kayan da tace an loda su a motar Aunty Muhibba dan kar a shigo dasu saboda yan saka ido.
  A k'asa dirshan ta zauna, ta cire dan kwalin ta da take jin yayi mata nauyin gaske saboda yadda kanta ke masifar sarawa
"Amma Bashir ya cuce mu, ya cuci rayuwata, yanxu dan Allah wannan abun kunya da me yayi kama? Na shiga uku."
Ta jefar da hannun ta gefe,
"Be kyauta ba gaskiya, ha'inci ne wannan kuma, sam be kyauta ba."
Aunty Maimuna dake kokarin bata baki ta fad'a duk babu dadi
" Allah ya isa ban yafe ba wallahi,shege macuci. "
"Kiyi hakuri Yaya Hajara, cuta dai Bashir ya riga yayi mana ita sai dai muyi hakuri, mu lallaba a kai ta idan yaso daga baya idan hankalin kowa ya dauke sai musan abinda ya kamata. "
Wani kallo tayi mata, kamar ma ta rufe ta da duka take ji
" Sai bayan an kai ta ya gark'ama mata ciki sannan ne kike tunanin zai rabu da ita? "
" A ah Yaya, kinga wai ai dai yanzu daga daure aure yau ai ba za'a ce ya saketa ba, kinga hakan ai kema zai iya baki matsala da Dr. "
" Matsala ta nawa kuma? Ni yanzu ya riga ya fita daga kaina, ta yata kawai nake, dole na bata farin ciki ko ta halin Kaka. "
Shiru kawai Aunty Maimuna tayi dan ba kuma tasan yadda zatayi ta bawa Maman hakuri ba. Aunty Muhibba ce ta shigo, tace maman ta tashi ta gyara jikinta Iman da mijinta zasu shigo. Kamar ta danna ma Aunty Muhibban ashar taji dan dai akwai kunya tsakanin su kasancewar ta matar babban wansu, dole ta tashi ta wanko fuskar ta a bathroom ta shafa mai da yar hoda ta saka kwalli sannan ta fito.
***A zaune take ta tankwashe kafar ta akan dan carpet din da yake jikin gadon dakin, ranta a bace yake tun bayan da ta samu labarin auren da Yarima Muhammad zai, taso ta tada hankalin ta amma Kilishi ta hanata, yanzu gashi tana ji tana gani an daura.
Â
"Laila!"
Ta kira sunanta tana daga zaune a gefen makeken gadon ta, da ido ta kalle ta ba tare da ta amsa ba, ta mike tsaye. Sanye take da doguwar gown ja, sai gashin ta da yake a tattare a waje daya da yasha gyara na musamman.
"Yaushe zaki koma?" Ta ta da tambayar bayan tasan amsar da zata bata. Da ido ta sake dubanta, ranta na sake baci tace
"Na dawo kenan."
Da sauri ta mike daga gishingid'ar da tayi, ta dauka zata ce mata soon zata koma kamar yadda take bata amsa a ko da yaushe idan tayi mata maganar komawar.
"Kinsan me kike cewa? Ba zaki koma ba? Me yasa?"
"Ba zan koma ba har sai na samu cikar burina. Ni ce na chanchanta da zama a wajen da aka bawa yar talakawa, wadda bata da komai da kowa. Yarima nawa ne ni kadai babu kuma wanda ya isa ya dakatar dani."
"Har ni?" Tace tana zaro ido cikin mamaki
"Duk wanda yayi kokarin shiga hanya ta, ko waye kuwa, ko da Bubu ne!"
Tsam kilishi tayi a in da take tsaye ta kasa cewa komai. Tana son Laila tamkar yadda take son Kamal,sai da tafi son Kamal ya gaji ubansa akan yadda ita Lailan take so. Sai dai idan taga da gaske Kamal ba zai samu sarautar ba, toh zatayi duk yadda zatayi ta samu Laila ta shiga rayuwar Muhammad din.
  Juyawa Lailan tayi cikin takun ta na isa, ta bar dakin. Da kallo Kilishi ta bita ta girgiza kai
"Ba zan taba barin ki da tsarin ki ba har sai na ga da gaske plan dina ba zai yiwu ba, wanda bani da shakku, Kamal shine zai gaji ubansa a ranar da suka shirya bawa dan gatan dan nasu. Maimartaba da kansa zai yi fushi dashi, fushi irin wanda be taba yi ba!"
Dariya ta saki ta koma ta zauna tana harda kafarta, indai tana numfashi Muhammad ba zai taba sarauta ba wannan alkawari ne da tayi wa kanta.
****
  A gajiya Bubu ya dawo, shiyasa be samu ganin kowa ba ya shige turakarsa. Tun da wuri Ammi ta shirya tana jiran sa dama,aiko yana dawowa ta tafi dan tana so su karasa maganar da ya fara yi mata ranar basu samu damar gamawa ba
  Har ta karaso ta zauna be bar kallon ta ba, babu wani babban chanji akan sanin da yayi mata a dah da nayi yanzu, jikin ta me kyau ne zaka rantse bata ajiye garkamemen saurayi kamar Muhammad din ba.
"Barka da zuwa gimbiya a fad'ar Ahmadu."
Yayi mata kirarin da ya saba mata tun zamanin kuruciyar su. Dariya tayi ta zauna tana dora tray din da ta shigo dashi a saman table.
"Sannu da zuwa, kun sha gajiya. An rabu da taro lafiya da kowa?"
"Lafiya Alhamdulillah, Takawa yayi matukar kokari sai dai muci Allah ya saka masa da alkhairi."
"Ai dama yace shine uba, kuma shine kuma kaka, mu yan kallo ne kawai."
Murmushi Bubu yayi yace
"Gaskiya kam ga zahiri nan mun gani ai."
"Allah ya basu zaman lafiya, har na matsu su tawo nan wallahi."
Hannu ya kai saman hancin ta ya lakace mata fuska yace
"Ko kunya, dan farin."
"Kuma dan auta ba."
Sai suka saka dariya a tare.
"Allah dai ya basu zaman lafiya da zuria dayyiba, kwanan nan zaki ga yan duguiw duguiw suna yawo a tsakiyar masarautar nan, lokacin na dawo gida nima na huta kamar Aji, kinga sai kawai na dinga kallon su ina jin dadi."Â
" Allahu ya sa, Allah ya nuna mana. "
" Amin. " Yace yana hasaso lokacin idan da rai da lafiya
" Ka gama yanke shawarar nad'in ranar juma'a din? "
" Haka muka tsara da Aji kuma na sanar da Takawa shima yayi na'am da hakan. "
" Kana ganin babu matsala? "
Rik'e ta yayi a jikin sa, yasan me take tsoro take gudu kuma
" Babu komai in sha Allah, babu abinda zai faru. "
" Aikin sa fa? "
" Ajiye shi zai kinga ba zai yiwu a hada ba ai. "
" Amma... "
" Ki tayashi da addu'a har ma dani din ma, idan ban ajiye mulkin nan ba hankali na ba zai taba kwanciya ba. "
" Allah ya nuna mana, Allah yasa ayi lafiya a gama lafiya. "
" Yawwa ko kefa, addu'ar kenan. "
#Rano💕
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)Â s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
1/25/22, 10:41 - Buhainat: Halin Girma
   19
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇ðŸ¾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
**************
Ta cikin ido Moh ya kalli Mama da ya lura kamar tsaiwar na neman gagarar ta tunda aka fara daukar hotunan, gashi sai dauka ake an ki dainawa itama a cikin yanayi take da saura kad'an ta zube a wajen idan aka cigaba da daukar hotunan. Sai da ya tabbatar da tayi masifar kaiwa karshe har tana neman fito da abinda yake zuciyar ta ne sannan yace ya isa haka, tayi saurin fadawa daki babu ko magana, hannun Iman din ya kama a gaban kowa, suka juya suka bar part din yana jin a kalla Mama zata yi hankali, a kalla zata san rayuwa da yadda take juya wa bawa.
  Tafiya sukayi bayan sun yi sallama akan zuwa magriba za'a zo a dauki Iman din. Sake chanja kaya tayi zuwa wasu kayan na daban, suka zauna cikin yan mata da sauran yayan da aka ma aure a family aka dinga hira cikin farin ciki. Bata saka musu baki sai dai tayi murmushi musamamn da ya zama kusan rabin maganar akan zaman aure ne wanda take jin kamar wasu maganganun sun girmi kanta.
  Gabatowar la'asar ya sake saka Iman din a cikin yanayi fargaba, irin wanda ake ji idan za'a rabu da gida. Tashi tayi ta ja Khadija suka fita zuwa shashen su, tana son ganin Zeenat sannan tana son daukar wasu abubuwan a dakin su.
  Shigowar su ya saka kowa na falon bin su da kallo, kai tsaye dakin Mama ta wuce Khadija na binta a babu yadda zatayi. Kusan zabura mama tayi ganin ta, ta tamke fuska tamau tana jin haushin shigo mata da tayi a halin da take ciki. Har kasa ta duk'a, ta gaida Maman sannan ta gaida su Aunty Maimuna. Duk sun amsa banda Maman da tayi kamar bata ji ba, tashi tayi bayan nan ba tare da wata magana ba ta wuce zuwa dakin su. Tayi mugun mamakin ganin Zeenat din, sai taji tausayin ta ya kama ta, ta durkusa a gabanta tana tuna lokacin da ta taimaka mata da bata jin dadi.
"Zeenat?"
Ta kira sunan ta, sai a lokacin ta san sun shigo dakin ma. Da ido tabi Iman din kamar taga sabuwar halitta,
"Iman?"
"Na'am, baki da lafiya ne? Kin ganki kuwa Zeenat?"
"Bani da lafiya Iman, bana jin dadin komai, wallahi bana son auren nan gashi an riga an daura, tsoro ma nake ji kar naje na aikata wani abu mara kyau."
" Me ya faru? Me yasa bakya so?"
" Bashir karya yayi min, babu gaskiya a maganar sa, bashi da komai fakiri ne wallahi."
Shiru Iman din tayi dan bata san me zata ce ba, tunanin yadda akayi hakan ta faru take, sai dai bata san yadda zata dauki maganar ta kuma ajiye ta ba. Kuka Zeenat din ta sake fashewa dah, kuka dacin da take jin sa a chunkushe a makoshin ta. Baki Iman din ta dinga bata, ta samu da k'yar tana maida numfashi. Tashi Iman din tayi ta duba wajen da ta ajiye jakar islamiyyar ta, ta dauka sannan ta sauki abubuwan da tasan zata bukata ba kaya ba. Khadija ta bawa ta tafi kai mata wajen Mamma sannan ta dawo ta cigaba da kwantar wa da Zeenat din hankali.
  Kamar ba Zeenat ba da take taka Iman din tayi mata duk wulakancin da ta ga dama, tayi laushi sosai,har tana dora kanta a kafar Iman din.
  Wayar hannun ta ce tayi k'ara, Moh ne yake kira, dagawa tayi tana tashi daga gaban Zeenat din
"Amaryata."
"Umm." Ta turo baki, dariya yayi sosai kafin yace
"Ki cigaba da turo bakin nan, babu ruwana aka samu matsala wallahi"
Murmushi ta samu kanta da yi, ta jujjuya kanta tace
"Kaiko?"
"Me nayi?"
"Ba komai."
"Sharri kawai zaki min dan kin ganni bawan Allah."
"Nima ai baiwar Allah ce."
" Na yarda kuwa, are you ready?"
" Mefa?"
" Shigowa fadar Moh."
" Ummm."
" Get ready kinji? Yanzu zasu zo, kwana biyu zuwa uku zamuyi anan sai mu wuce adamawa."
" Adamawa?" Tace tana zaro ido
" Calm down, zan miki bayanin komai."
" Shikenan." Tace a sanyaye
" That's my wife, Allah yayi miki albarka."
" Amin." Ta amsa tana sakin murmushi a hankali.
Kashe kiran yayi, Zeenat ta bita da kallon sha'awa, tana hango tsantsar dacewar da Iman din tayi, gashi ita ta tashi a tutar babu.
"Zeenat bari na tafi, zamuyi waya in sha Allah, kiyi hakuri dan Allah ki kwantar da hankalin ki."
Jumbur ta mike, ta rik'e jikin rigar ta tana goge kwallar da ta zubo mata
" Dan Allah Iman karki tafi ki barni, wallahi ba zan iya zama da Bashir ba."
" Me yasa? Bakya son sa ne wai dama?"
" Wallahi bana son shi, ko kad'an wallahi laifin Mama ne."
" Iman!" Taji muryar Mamma a kofar dakin tana kiran ta, juyawa tayi ta fita tana kallon Zeenat din cikin tausayawa
" Ke kuma daga zuwa daukar abu sai ki zauna? Kinga ai lokaci yayi ko?".
Bata ce komai ba sai kawai tabi Mamman suka bar bangaren, ranta babu dadi ko kad'an.
  Wanka mamma ta sake sata tayi, kayan da zata chanja ta tarar a dakin, an turara mata su da turarurruka masu dadin kamshi. Tana shiryawa tana tunanin halin da Zeenat din take ciki, yadda ta firgice ta shiga tashin hankali zaka gane akwai wani abun a k'asa, ba wai kawai dan Bashir din bashi da hali bane kamar yadda ya Maryam ta bata labari.
  Duk shirin da tayi da taimakon su Harira, aka kuma kawo wata sabuwar alkyabbar aka dora mata, tayi kyau ainun, babu make-up babu komai amma yadda fuskar ta take sheki kadai zaka gane ba karamin gyara tasha ba.
Â
  La'asar likis sai ga jama'ar gidan su Bashir, motoci goma ne gaba daya har data amarya , yadda za'a samu kowa ya je har mutanen unguwa, a lokacin babu irin kiran da be yiwa Zeenat din ba akan gasu nan amma bata dagawa, shiyasa kawai ya kyale ta domin shi a yanzu ba ta ita yake ba, yadda zasu kwashe da hajiyar ce kadai matsalar sa, labari ya riga ya kai mata ya kuma san gamon su bazai taba yin kyau ba, gashi akwai wasu kudade da ya ta bashi da nufin zai mata wani aiki ya bi ta kansu.
  Hankalin Mama ne ya kara tashi sanda suka iso, ta tabbatar da gaske Zeenat dai sai ta tare gidan Bashir, kiran Abba tayi, kafin ma ta fadi komai yace
"Ina falon Yaya idan kun gama ki turo min Zeenatun."
Daga haka ya kashe kiran, cikin sanyin jiki Mama ta nufi dakin su Zeenat din, ta tarar da Aunty Maimuna na ta fama da ita akan ta tashi ta shirya, ganin shigowar Mama ta saka ta saurin tashi ta nufi wajen Maman.
"Jeki shirya Zeenat, kiyi sauri Mahaifin ku yana kiranki."
"Mama?"
"Ya zanyi? Ya zanyi? Aure an riga an daura ba kuma zan je na chakumi wuyan Bashir nace lallai sai ya sake ki ba, tunda kuma an daura ai dole ki tafi, dole ki bishi shine mijinki, ya zanyi."
Fashewa tayi da kuka, tayi saurin fadawa toilet din ta rufo kofar, danne zuciyar ta sosai Mama tayi, ta juya ta bar Aunty Maimuna a dakin ta kuma jaddada mata kar su bata lokaci. Mamaki sosai Aunty Maimuna tayi da yadda Maman ta dake, amma kuma ta hango tsantsar tashin hankali a tattare da ita.
  Da k'yar ta taimaka mata ta fito ta shirya har lokacin kuka take, kaya kawai ta saka sai turare babu batun powder ko makeup. Lullube mata fuska Aunty Maimuna tayi suka fito, kai tsaye aka wuce da ita wajen Abba. Su uku ne a dakin daga shi sai Abba kabiru sai Abba (Babba) nasiha suka soma mata, me shiga ciki akan rayuwar da zata shiga sabuwa, yawanci magana daya ce hakuri wanda Zeenat din ta kasa fahimtar su, bata gane me suke cewa balle ta san a wanne mazauni zata ajiye maganganun nasu ba, har suka gama bata fuskanci komai ba, hankalin ta ma baki daya baya wajen su ta tafi tunanin kalar rayuwar da zata fara a gidan Bashir din. Sadakin ta Abba ya dauko a aljihun ta ya mik'a mata
"Gashi zeenatu,Allah ubangiji yayi miki albarka ya baku zaman lafiya."
K'asa karba tayi, ta fashe da kukan da take ta rikewa, mikewa Abba yayi ya fice daga dakin zuciyar sa na tabuwa, yana jin kamar ya dawo da hannun agogo baya a lokaci da ya dinga nunawa Zeenat din illar abinda take shirin aikatawa.Â
  Abba Kabiru ne ya karbi kudin a hannu Abba yace
"Barshi Yaya, bari wani cikin yaran nan sai yaje ya saka mata shi a account, idan yaso bayan komai ya lafa sai ta ciro tayi amfani da abinta."
"Hakan ma yayi, shikenan zeenatu kudin ki za'a saka miki shi a account kinji? Ki daina kuka."
Tashi tayi da k'yar tana gid'a kai kamar gadangaruwa ta fita, daga nan ne kuma kowa ya firfita dan zuwa kai ta gidan Ango Bashir. Sai dai duk mutane suka gama shiga mota sannan aka fito da ita aka sakata a mota, tana kuka Mama na yi haka aka tura ta a motar. Dangin Bashir din sukayi ta mamakin abinda yake faruwa dan kowa ya ga kukan yasan ba kawai na rabuwa bane akwai wani abu daban.
  Shiru kake ji a motar babu motsin kowa kamar ba ma mutane a ciki. Wata Yayar su Abba ce da Aunty Maimuna suka sakata a tsakiya, hannun ta na damke ana Aunty Maimuna tana cigaba da kukan ta a ciki ciki. Har suka karaso bata daina kukan ba. Sauran jama'ar motar ne suka fiffito, kowa tayi cirko cirko suna jiran a nuna musu gidan Zeenat.
 Â
***Text message ne ya shigo wayar Bashir din, ya duba yana sauri sauri dan yana so yaga Moh kafin tafiyar da zai yi,
_"Ina jiran ka kaida kanwar tawa a gida, na saka an gyara muku daya daga cikin dakunan nan. Sai kunzo." _
Gaban sa ne yayi mummunar faduwa, yayi sakale rik'e da wayar yana tunanin mafita, be shi da niyyar hada Zeenat da Hajiya Layuza gida daya, amma kuma be isa ya ki kai ta ba dan komai zai iya faruwa. Kiran ganin sa Ghali yayi ya tabbatar da sun karasa, yace idan kafa ta dauke ya kirashi ya sanar masa. Yana kashewa yayi mata reply da an gama hajjaju sannan ya saka wayar a aljihu ya fita yana sauri
  Yadda dakunan suke kananu ya saka gidan ya chunkushe, kowa so yake yaga abinda zai samu na dorarwa a gaba, masu bud'e kitchen masu bud'e toilet har da masu bud'e rijiya dan tabbatar wa.
  Aunty Maimuna ce tace kowa ya fita za'a koma gida saboda zuwa kai Iman, mutane suka hau saurin fita dan kowa ta kama motar da taxo amma suna fita suka ga wayam babu ko mota daya duk sun gudu,. Nan fa waje ya rude kowa ya hau tofa albarkacin bakin sa, yan uwan Mama suka shiga tashin hankali dan babu abinda yafi ciwo a debo mata a kawo su gidan amarya a watsar dasu, komawa cikin sukayi aka tilastawa Zeenat kiran Bashir din, be daga ba har aka gaji da kiran sa suka hakura suka fita, aka fara tunanin yadda za'a yi kowa ya koma gida.. saukin ta ma dama duk cikn garin ne dan tuni wasu ma sun dade da tafiya sun tari napep. Wanda suka rage ne dole su Aunty Maimuna suka san yadda sukayi kowa ta samu abin hawa. Sai yada habaici da bakar magana suke musamman yan uwan Abba da Mama ta bata wa rai tun a farkon fara bikin.
  Sanda suka gama dawowa gida magriba ta kawo kai, a lokacin ne kuma motocin masarauta suke jere kansu a cikin layin wanda ya kasance tun daga farkon layin har karshen sa. Motar da za'a dau amarya daban take ta gaji da haduwa, anyi decorating dinta tayi kyau.
 Â
Gashi nan na biya bashin na ranar Friday.
 Â
#Rano💕
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)Â s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
1/25/22, 10:41 - Buhainat: Halin Girma
   20
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇ðŸ¾_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇ðŸ¾_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇ðŸ¾_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
**************
Gaban Iman din ne ya dinga faduwa sanda taji tashin algaita da bud'a a lokaci daya, rik'e hannun Mamma tayi tamau bayan sun dawo daga wajen su Abba da wajen Gaji. Zaunar da ita Mamman tayi tace tana zuwa Amaani tayi saurin dawowa ta manne kusa da ita hakan ya saka ta dan ji dama dama. Mukullin motar da Abba ya damka mata a hannun ta da wasu abubuwan ya sakata shiga yanayin da ta shiga, har yanzu bata bar mamakin yadda abubuwan suka sauya salo ba, wanda bata taba tunani ko hasashen hakan zai faru da ita ba.
  Bayan kamar minti biyar sai ga Mamma nan ta dawo ta kalli sauran tace
"Matar nan bata da kirki sam, bansan me yake damunta ba, amma ni dai na fad'a mata lallai ta shirya tazo ta kai Iman dakin ta, idan ma wani abun ne yake damun ta ko hassadace ita ta sani, na dai bata girmanta."
"Toh ai Mamma kina gani kinsan bakin ciki take, dama kin kyale ta kawai mu kadai mun isa."
"Ai ba haka ake ba, mu muka zo muka same ta kuma duk tsiya dai itace marikiyar Iman din."
" Toh yanzu zata je din ko yaya?"
" Ban san mata ba wallahi, na dai fita ai ni dai,ruwanta taje ruwanta taki zuwa, babu abinda za'a fasa."
" Wallahi kuwa, Allah ya kyauta."
" Amin." Tace tana zama.
   Kayan Iman din aka gama fitarwa, aka saka a booth din motocin, sannan suka shigo da kansu su uku, suka ce sun zo daukar amaryar su, akayi barkwanci dai tsakanin su da su Mamma sannan suka fita su kuma su Mamma suka fito da Iman din.
  A harabar gidan suka hadu da Mama, ta yafa mayafi ita da Aunty Muhibba, kallo daya Mamma tayi mata ta dauke kai suka fice, bayan su suka bi, suka tarar an gama tsara mutanen kowa ta samu mota ta shiga, kowacce mota da kayyadadden mutanen da za'a saka kuma kowa ya samu an shirya komai yadda ya kamata.
  Motar amarya ce kawai ta rage sai guda daya da tazo a karshe, wasu ne suka shiga dayar tare da Aunty Muhibban sai Mamma da Mama suka shiga ta amarya suka sakata a tsakiya kamar yadda ake yi. Chan jikin kofar motar Mama ta makale taki yarda ta rabi Iman din, jawo ta sosai Mamma tayi jikin ta ta dora kan Iman din a saman kafadarta ta kwanta sosai.
  Lamido Crescent suka nufa in da nan ne ainihin gidan Iman din, sojojin da ke zube birjik a gaban gidan ya saka mutane sake jinjina lallai Babba ne Muhammad din, gida ne hadadden gaske wanda dama chan a nan Muhammad din yake amma an masa gyara sosai da ba zaka taba cewa ba a lokacin aka gina shi ba. Tsaruwar gidan da yadda aka kawata faluka da dakunan gidan da kaya na alfarma ya kusan saka Mama shan k'asa, ta rik'e hannun Aunty Muhibba dan da gaske ta tsorata da yadda taga gidan. Falo biyu ne daya sama daya k'asa sai dakuna biyu a sama, uku a k'asa kuma kowanne Masha Allah kaya ne aka zuba na alfarma, kar Azo batun kitchen wanda duk yadda Mama ta kai ga kure siyayyar ta sai taga ta raina kanta, komai na ciki unique ne ga wasu shegun electronics wasu ma bata san menene amfanin su ba. A daddafe ta daure ta shiga ko ina dan yadda kowa ya zura ido a kanta kowa so yake ya ga yadda zata shiga dimuwa ko ma ta kasa rik'e bakin cikin ta har ta nuna a samu abin fad'a.
  Basu wani jima a gidan ba suka fito, dama saboda dai su san gidan Iman din tunda yanzu ba anan za'a fara kaita ba, masarauta zash dan suna da shagalin bikin da zasuyi su ma.
  Kin yarda Mama tayi ta koma motar amarya ta fad'a wajen Aunty Muhibba dan komai zai iya faruwa idan ta zauna gata ga Iman din. Bata taba tunanin kalar wannan daukakar ga Iman din ba. Sai gashi in da Iman din taje ko zata je nan gaba bata isa ta taba kai wa wajen ba har abadah. Tayi mata nisan da za'a iya cewa ya kai tsakanin nisan sama da kasa.
  Bata kara raina kanta ba sai da ta gansu a cikin masarautar, babbar masarauta irin ta Kano, da bata kawo kanta a ciki ko da wucewa tazo yi kuwa bata taba hasashen kasancewar ta ba.
  Wani tsari akayi na tarbar su, wanda ya sake bawa mutane mamaki, kana kallon fuskokin kowa zaka tabbatar da yadda suke ciki. Sanda suka isa bangaren Fulani kakar Moh din da kanta ta taso ta rungume Iman a jikinta, ta kuma zaunar da ita a kusa da ita, jikokin ta sauran suka hau dariya suna tsokanar ta, ta biye musu suka dinga yi kamar ba matar sarki ba, duk da ba kowa ne aka bari ya shiga wajen ba, iya makusantan Iman din ne daga Mamma sai Mama sai dangin Abba su biyu sai Amaani da take makale da Iman din, sauran mutanen a wani babban falo aka ajiye su aka shiga gabatar musu da nau'ikan abinci kala-kala na gida dana kasashen ketare.
  Sun dan jima a shashen Fulanin mutane daban daban manya wanda suka zo bikin suka dinga zuwa suna ganin Iman din, kunya kamar ta nutse ta dinga boye kanta wanda hakan ya saka suka kara son ta kowa ya dinga yabon ta yana yaba sa'ar da Moh din yayi.
  Rakasu bangaren Moh din Fulani ta saka akayi, wanda dama chan aka ware wa Iman din da wanda zasu tayata zama kafin gobe yan uwan ta su dawo shagalin da za'a yi a babban Hall din gidan da tun a ranar an gama tsara shi an kawata shi.
  Two bed room ne sai falo da kitchen, tuni masu kula da shashen sun gyara komai, daya daga cikin dakunan aka kaita, sannan su Mamma sukayi mata sallama aka bar mata Amaani, khadija, Zahra sai su Amira, duk dai yan matan aka bari a zuwan su Mamma sai su dawo gobe. Kamar zatayi kuka haka taji da zasu tafi amma kasancewar ta me dakiya ta daure kawai tayi shiru tana cigaba da kallon komai tamkar almara.
  A falon su Amira suka zauna bayan sun raka su Maman sun dawo suka dasa kallo da hirar gidan Iman din da irin yadda aka karbe su a masarautar. Tana jin su sama sama bata fito ba sai ma tayi kwanciyar ta saman gadon dakin tana shakar kamshin da ta tabbatar da kamshin sa ne dan shine kamshin da ko da yaushe take jin sa yana yi.
  Tana kwance taji kamar motsi, ta daga kai ta duba, sai taga kofa a jikin karshen bangon dakin wanda sai ka lura sosai zaga gane don ta saje da kalar curtains din dakin. Budewa taga kofar tayi, ta mike daga kwanciyar da tayi da sauri kafin ta gama daidatuwa har ya shigo, cikin shigar bakin dogon wando da riga armless, cikin mamaki take kallon sa har ya shigo cikin dakin gaba daya. Mikewa tayi tsaye lokacin da ya karaso daidai in da take. Ya saka hannu ya shafi gefen fuskar ta.
"Wai tsoro kika ji?"
Da ka ta amsa, ya rik'e ta ya zauna a gefen gadon sannan ya zaunar da ita a daidai kusa dashi, k'asa kallon sa tayi, ya zuba mata ido yana kallon ta kamar a ranar ya soma ganin ta. Farin cikin da yake ciki a yau din mara misaltuwa ne, ba zai iya tafiya adamawa be sake ganin ta ba shiyasa kawai ya hakura da zuwan sai da safe.
  D'agowa tayi da nufin ta ga abinda yake, tayi saurin sake maida kanta k'asa ganin yadda idanun sa sukayi k'asa sosai. Hannun ta ya kamo ya rik'e a cikin nasa yana murzawa, yana kokarin danne abinda zuciya da gangar jikin sa ke wassafa masa. Yadda yake murza hannun nata da yadda suka samu kusanci sosai ya saka ta a yanayin da bata taba samun kanta ba, shi din ma hakan ce, dan yadda yake ji yayi imani idan aka dauki lokaci me tsawo baa bashi matar sa ba toh komai zai iya faruwa. Lissafin ta yaji sunayi ya saka shi jin gaskiya ba zai iya bari har tsawon kwanakin da su Ammi da nan Kano kowa ya diba na shagalin da zasuyi ba. Kwana daya ya isa anan ko biyu chan kuma daya idan yaga zasu ki yarda zuwa zai ya samu Aunty Fatima ya karanta mata komai a taimaki dan maraya a bashi matar sa ko kuma yayi musu aika-aika.
  Turo kofar akayi, su dukka suka kalli kofar, da sauri Khadija ta juya tana fadin
"Dan Allah kuyi hakuri."
Tashi yayi tsam bayan ta fitan, ya sakawa kofar key ya dawo ya mikar da ita, ya cire mata alkyabbar da take jikin ta har lokacin, saurin runtse idon ta tayi saboda yadda dinkin fitted gown din jikin ta ya kamata sosai dan sai da suka kusan haurawa sama da Mamma kafin ta yarda ta sakaa. A abuja aka mata duk dinkunan nata kuma kaf babu wani dinkin arziki a duk kayan da Maman ta bayar akayi mata tace idan tazo kayan lefen ta sai ayi mata wasu na fita amma ita nata duk na zaman gida ne ayi wa Moh kwalliya. Dogon numfashi yaja, a karo na farko ya ganta haka babu hijabi balle mayafi. Kayan su zauna das a jikinta,ta wajen hips din sun zauna kamar a jikinta aka dinka su. Idon sa ya shiga rarraawa daga tsakanin kirjinta zuwa kasan hips din ta, yabi flat tommy dinta da kallo wanda zaka rantse ba'a saka masa abinci saboda shafewar sa.
"Masha ALLAH!"
Ya samu kansa da furtawa, kunyar da take ji kamar ta haka rami ta shige gashi ya hanata sakat ya rik'e ta babu damar ta zauna. Sai da ya more kallon ta tsaf sannan ya dawo samar fuskar ta ya matso daf da ita har tana jin hucin numfashin sa a saman fuskar ta, tayi saurin runtse idon ta ya kura wa lips dinta ido, ya kai bakin sa daidai kan nata ya shiga kissing dinta passionately ba tare da ya shirya ba.
  Jikinta ne ya hau rawa tayi kokarin hanashi amma sai ya sake matso da fuskar ta sosai, ya tallafo ta ta baya ya sakata a jikin sa ssosai ya cigaba da aikin sa. Ta saman bayanta taji yana neman abu, har ya kai wajen da zip din ta yake, ya shiga jan shi zuwa k'asa, da sauri ta rik'e hannayen nasa tana girgiza masa kai hawaye har ya fara sauka a idon ta.
"Pleaseeeeee." Ya furta cikin muryar da taji kamar ba tasa ba, ta shige ciki sosai.
"Dan Allah kayi hakuri." Tace tana sake rik'e hannun nasa, dan taga kamar ma baya gane me take cewa.
  Wayar sa dake cikin aljihun wandon sa ce tayi kara, ya janye ta yana murmushi ya ciro wayar yana daidaita kansa.
"Zan kira ka Bashir."
Kawai yace yana kashe kiran. Lokacin ta koma ta zauna tana kokarin daidaita kanta dan ba karamin yanayi ta shiga ba.
  A gabanta yayi kamar kneel down, ya tallafo fuskar sa yana mata kallon tsantsar kauna, turo baki tayi ta harare shi ya tuntsure da dariya
"Pretender kawai."
Ya saka hannu ya lakaci gefen hancin ta, murnushin ita ma tayi ta juyar da kanta daga kallon sa abinda ya faru yana cigaba da haskawa a idon ta.
"Kaje anan kiran ka."
Tace ganin yaki tashi ya kuma hanata sakat da kallon sa da idon sa da suke sake bata tsoro a game dashi.
"Kora ta kike? Wallahi sai naki tafiya na kwana anan din dama ai daki na ne."
" Ya hakuri ni dai dan Allah."
" Matsoraciya, kin fiye tsoro wallahi."
" Tsoro ai halak ne." Tace tana dariya
"Inyee kinyi baki haka? Yarinya zaki maimaita maganar nan ne, for now zan barki amma gaskiya zan dawo, kice ma su Amaani su kwana dayan dakin ke kadai zaki kwana anan, kinga dama akwai secret door dita kawai sai na shigo mu sha soyayyar mu."
" Tab!"
" I'm serious
 Â
 Â
#Rano💕
#Rano💕
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)Â s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
Post a Comment for "HALIN GIRMA 16-20"