Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

HALIN GIRMA 11-15

 


1/11/22, 15:42 - Buhainat: Halin Girma

    11

 *Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

 _(Palace of exotic scent and more)💯❤️_

 _MD: is ur plug! Muna siyarda kaya kala2 kamar jaka da takalmi kamfanin lamis,Dior,vellabela da dkny da sneakers 'yan yyi dominku da yaranku,Muna order kaya dga kasashe daban-daban,Muna siyarda da kayan decors,plated gold,da turaruka kala-

kala Hadi dna tasa (oil perfume) dga kamfanin naseem hr suratti,Muna da room fresh da turarukan wuta Dan gangaria. Muna adashe na yargata(kaya) Dana kudi ku tuntube mu awannan nmbr kamar haka wa.me/07039773001 Muna turawa ko Ina afadin Nigeria da wasu kasashen ketare ngd_

 

***

A wani yanayi Maman ta dago, gabanta ya fadi ganin Abba a tsaye a kofar Zeenat na rakube a gefe kamar munafuka

 

"Dr, Sannu da zuwa."

 

"Kinsan daga ina yarinyar nan take?"

 

Ya nuna Zeenat yana jin kamar ya rufe ta da duka.

 

"Aiken ta ne nan baya gidan Amarya me koko." Tace bayan tasan ba hakan bane. Kwafa yayi cikin kada Kai yace

 

"Yaron da nace babu ita babu shi take zuwa suna haduwa a bayan layi, na fad'a miki na kuma bana son yaron domin ba yaron kirki bane, amma a bayan kunnenku."

 

"Idan har ta dage ba zata ji magana ta ba, zata dinga fita suna haduwa a wani wajen ba da izini na ba ko na yan uwana, zan sallama masa sai tace ya turo,amma..."

 

Ya nuna ta da yatsa

 

"Idan har wani abu ya je ya dawo, kar ku  kuka da kowa, ta kuka da kanku!"

 

Shiru Maman tayi taki cewa komai, haka Zeenat din da ya zaci zata bashi hakuri sai yaji tayi shiru

 

" Kin amince da Bashir din, kin yarda zaki aure shi?"

 

Daga kanta tayi da sauri babu kunya ba tsoron Allah, wani irin faduwa gaban Abban yayi, yaji tamkar zai fadi saboda wani jiri da ya nemi zubar dashi, be zaci haka daga gareta ba, sam ba tarbiyyar da yayi wa yaransa bace, sake maimaitawa yayi cikin danne abinda yake ji yace

 

" Kinji kin gani, kin Amince?"

 

" Dr ka bar maganar nan idan muka shiga ciki sai mu..." Dakatar da ita yayi da hannu, ya dakawa Zeenat din tsawa

 

" Ki bani amsa!"

 

" Eh Abba." Tace tana nokewa idon ta fes tamkar an soye gyada

 

" Shikenan, shikenan." Ya maimaita

 

" Kice dashi ya turo magabatansa, suzo wajen Yaya."

 

Sai ya juya wajen Iman da tayi kamar ta bud'e kasa ta shige saboda kunyar abinda Zeenat din tayi yace

 

" Kema ki ce masa ya turo dan ba zan bata lokaci ba."

 

Daga kanta tayi da sauri, ya wuce su yana jin wani irin tashin hankalin abinda Zeenat din tayi, tabbas laifin Hajara ne, ita ce bata tankwarata ba, bata nuna mata daidai da akasin haka ba, abinda ma ya lura Itace take son abin, ba zai yarda wani abu ya faru ba a dalilin hana ta auren Bashir din, dan yaran yanzu zasu iya komai akan soyayya, shiyasa kawai ya yanke shawarar aura mata shi din idan har ta kafe, da azo ana wallahi tallahi.

   Abban na barin wajen itama Iman tayi saurin ficewa dan tasan sarai Mama zata huce akanta, tana juyo fad'an da take wa Zeenat din sama-sama, ta kara sauri ta zagaya ta baya ta shiga ta kitchen ta wuce dakin su kawai.

   Tsawon kwanakin Abba bashi da walwala sam, ita kanta Mama ta kasa gane kansa, da ya shigo zai wuce dakin sa kawai sai kuma gobe, a da tayi tunanin fushin ba zai nisa ba, sai taga abin yana neman zarcewa, takanas ta same shi da maganar da ban hakuri amma sai ya share ta yama yi ficewar sa ya barta, haushin hakan ya sakata share shi itama ta san dole zai gama fushin sa ya dawo ko da Anyi auren yaji su kalou zai ajiye komai ya dawo, tasan ta fishi gaskiya shiyasa taki goyon bayan sa, dan tasan zugashi akayi dan an ga Zeenat din zata huta.

  

***Bayan tafiyar Muhammad basu yi magana da ita ba, sau biyu tana kiran number sa bata samun sa, hakan ya saka ta damu sosai, gashi tasan Abba zai sake mata magana akan abinda yace ta fad'a masan, gashi bata sameshi ba, tsoron ta daya Allah yasa ba guduwa yayi ba, dan har ga Allah zuciyar ta, ta yarda dashi. Har tana jin son sa na shigar ta, koman sa daban ne hatta maganar sa, ta kasa gane komai akansa musamman a fagen da zata ajiye shi, yanayin sa da koman sa yasha banban da shigar sa, tana bukatar sanin sa sosai kila ko bayan sunzo da iyayen sa an daidaita, a lokacin zata bijiro masa da tambaya akan sa, ko da ba komai ba, a kalla ya bata labarin wani abu da ya shafe shi.

   Fitowa tayi falo ta zauna bayan ta gyarawa Gaji daki, maman su Maryam ce ta shigo, ta gaishe ta tana tashi ta kira mata Gaji, tare suka dawo da Gajin ta gaishe ta sannan suka soma hira akan abubuwa da dama. Ita dai Iman na zaune tana jin su tana duba wayar ta. Maganar Maryam suka shiga ya sakata d'agowa tace

 

"Umma Ya Maryam din ce bata da lafiya?"

 

"Wallahi Iman, wai har kwananta uku a asibiti amma basu fadawa kowa ba, bari tayi an sallameta dazu amma, shine nake tunanin wanda zai je mata ya dan taimaka mata ko na sati daya ne."

 

"Allah sarki, Allah ya kara sauki."

 

" Ko ke zaki je ne takwara?"

 

"Toh..." Tace har cikin ranta bata so ba

 

" Iman bata son mutane ai, zata iya zuwa kuwa? Maman su Maryam din tace tana murmushi

 

"Idan ta kamata ya zatayi?" Gaji tace

 

"Wai kar a takura ta dama."

 

"Haba kinji wani zance, yar uwarta ce fa? Idan batayi mata ba wa zatayi wa?"

 

"Haka ne."

 

"Zance Umma, ba komai ai."

 

"Toh shikenan, anjima sai wani cikin samarin ya mik'a ki."

 

"Ai ba sai anjima ba, yanzu zata shirya sai su wuce, ki shiga sai ki sanar da Maman tasu, idan yaso sai ta fadawa Ibrahim din duk da nasan babu abinda zaice."

 

"Toh shikenan bari na shiga wajen nasu." Ta tashi ta fita,ita kuma Iman ta wuce ciki ta dauko charger ta tazo ta fita.

 

   A zaune ta tarar da Umman suna maganar da Mama, tana shiga tace

 

"Ki shirya zaki je gidan Maryam kiyi kwana biyu, Allah ya kara sauki."

 

"Toh." Tace ta wuce ciki, ta dauki wata karamar Jakarta, ta saka kayanta kala biyu sai undies da hisnul muslim, da dan abinda tasan zata bukata ta fito, bata ga su Maman a falo ba, sai ta nufi dakin ta rataye da jakar a kafadarta, ta kwankwasa kafin ta shiga

 

"Mama na fito." Tace daga kofa, jakar ta dake kan gado ta dauko ta ciro dubu daya ta mik'a mata

 

"Sai kin dawo."

 

Hannu biyu tasa ta karba mamaki na kamata, tayi godiya ta fito still tana jin kamar mafarki, magana me dadi daga Mama har da bata kudi? Akan me? Sam sai taji hankalin ta be kwanta ba, taji kamar ta koma ta tambaye ta dalilin action dinta amma babu hali.

  Ita kadai ta dinga juya dubun har suka isa gidan Maryam din, ta fito rik'e da jakar ta shiga gidan. A falo ta tarar da ita da mijinta sai sister dinshi wata babba haka. Wani farin ciki ne ta gani a fuskar maryam din, ta tashi zaune tana mata sannu da zuwa.

  Gaishe su ta fara yi suka amsa dukka sannan ta nufi wajen Maryam din tana mata ya jiki,

 

"D-D bari naje na kai Yaya gida tunda ga Maryam tazo."

 

"Ok tam." Tace

 

"Nagode sosai Anty Saliha, ku gaida gida."

 

"Gida zaiji Maryam, Allah ya kara sauki ki kula da kanki sosai kinji? Ki dinga cin abinci sosai saboda kiyi saurin dawowa dai, Allah ya kawo wani rabo me albarka."

 

" In Sha Allah zanci, nagode." Tace a kunyace, sukayi sallama suka fita

 

" Sa mana key din a kofar."

 

 Tace wa Maryam din tana gyara zaman ta. Key din Maryam ta saka musu ta dawo ta zauna kusa da ita

 

"Ashe ke zaki zo, naji dadi da ba'a turo wata cikin yaran chan ba wallahi."

 

"Wallahi, ya jikin naki? Naga kinyi fari sosai."

 

" Toh ba dole ba, kin ga uban wahalar da nasha kuwa? Kai Iman aure- aure akwai wahala wallahi."

 

" Sannu, Allah ya kara sauki."

 

" Amin ya Allah."

 

" Ya gida yasu Mama, Gaji da kowa da kowa?"

 

" Kowa lafiya lou, duk suna gaishe shi."

 

" Ina amsawa, amma zasu zo su dubani ai ko?"

 

" Eh toh nasan zasu zo, dan baki ga ma fad'an da Umman tayi ba, kwana uku a asibiti baku fad'a ba."

 

" Ina na sane, hankali na baya jikina, laifin D-D ne, shi ne be fad'a ba wallah. Anty Saliha ma baki ga fad'an da tayi ba."

 

" Ai dole, wani abun kana bukatar Babba kusa da kai."

 

"Aikuwa."

 

" Allah ya kara sauki ya kiyaye gaba."

 

" Amin addu'ar kenan."

 

" Sai naji labari kuma, Ashe su Abba sun fara maganar ku, Umma tace min ma ke kamar su abba sun gama bincike akan shi har ma sun tabbatar da shi din zasu bawa, Umma tace bata taba ganin Abba ya damu da wani a cikin masu zuwa neman yayan gidan ba kamar yadda ya damu da wannan din, ko dai wani Babban kika samo mana ko wani basarake?"

 

Tace cikin zolaya

 

" Kai Ya Maryam, bafa kowa bane hasalima dai ba wani me kudi bane kawai dai inaga ko Abba ya gamsu da halayen sa ne."

 

" Eh toh haka ma Umma tace, nima tsokanar ki nake, ke yanzu ka samu miji na gari me son ka me son farin cikin ka shine, ba yalwar arziki ba, da wani arzikin gwara rufin asiri."

 

" Haka ne."

 

" Allah ya kaimu lokavin, musha biki."

 

Dariya tayi kawai dan ita jikinta a sanyaye yake da rashin jin sa har tsawon kwanaki hudu, ta damu sosai sosai har ta kan zauna tayi ta tuna moments din da sukayi tare, wani lokacin tayi murmushi ita kadai wani lokacin kuma ta ji kunya ta kamata.

 

_"I love you."_ Kalmar da yadda ya fade ta take ta tunawa, har yadda lips dinsa suka hade waje daya yayin da yake furtawa, cikin muryar da take yawan yi mata amsa kuwwa a cikin kunnenta

 

"Dan Allah dafa min danwake, shi kawai nake sha'awa baki na babu dadi wallahi."

 

Maryam ta katse mata tunanin da take, ajiye wayar ta tayi a gefen Maryam din, ta tashi zuwa kitchen din, minti kad'an ta leko

 

"Toh ai bansan Ina kayan naki suke ba."

 

Tasowa Maryam din tayi, tazo ta dauko nata komai ta nuna mata sauran sannan ta dawo falon ta jona wa Iman din wayar ta a charge kusa da ita ta kunna tv ta koma ta zauna tana kalla, jefi jefi tana yiwa Iman din hira daga nan.

  Wayar Iman din ce tai kara, alamar shigowar kira, tana daga kitchen din amma sai da ta ji gabanta ya fadi, saboda tsabar jiran kiransa har ringing tone ta chanja masa nashi shi kadai saboda da ya kira yadda zata fi saurin ganewa,

 

"Ana kiran ki Iman." Maryam tace tana jawo wayar ta kalli screen din

 

"M ne yake kira, M M M waye Ma? Sirikin nawa?"

 

Tace tana murmushi, maimakon Iman din ta fito ta karba sai kawai ta cigaba da aikinta tana jin Maryam din na mata sababin zata katse, kamar ba kiran da take jira bane, amma kuma a kalla yanzu hankalin ta ya kwanta, tasan cewa da gaske be manta da ita ba. Sake kira akayi karo na biyu,

 

"Bana son wulakanci Iman, bari na daga kizo ki karba."

 

Dagawa tayi ta saka a kunne

 

"Sweetheart."

 

Ya furta cikin rada yana sauke ajiyar zuciya, da sauri Maryam tayi gyara murya tana cire wayar kafin ta mayar tace

 

"Yayarta ce maryam, tana kitchen ne."

 

"Anty Maryam, Ina wuni?"

 

"Lafiya lou wallahi, ya aiki?"

 

"Alhamdulillah."

 

"Dama tana kitchen ne, amma yanzu zata zo zata kira."

 

"Owk nagode sosai."

 

"Nima Nagode." Ta katse kiran tana tashi, zuwa tayi kitchen din da daddage da d'aka mata duka a baya

 

"Dan wulakanci kina ji yana kira ko? Wannan irin hot guy din ba'a musu jan aji wallahi, kinji kuwa? Haka yake kashe ki da soyayya? Hmmm lallai yau ga wanda yafi D-D na."

 

Banza Maryam din tayi mata tana murmushi, ta karbi wayar ta ajiye a gefe ta karasa kwashe danwaken ta zuba a flask ta zuba ruwan zafi akai ta rufe, ta soya man ta hada komai a babban tray ta dora Maryam din na tsaya a akanta tana mata hirar Moh din ita a dole sai taji wani abu daga iman din amma tayi mata fumfurus

 

"Mara lafiya ba'a cika son shi da yawan magana ba, muje na kai miki abincin falo."

 

Dukan ta kara kai mata ta goce tana dariya, suka jero Maryam din na rik'e da bottle water ta ajiye mata komai a falon ta zuba mata sannan ta dauki jakarta tace

 

"Ina ne dakin?"

 

Da baki Maryam din ta nuna mata lokacin ta cika bakin ta da dan wake. Dakin ta nufa ta shige ta rufo kofa sannan ta cire hijab dinta ta ajiye a agefen gadon ta zauna tana kallon wayar, kunya da nauyin kiran sa take amma kuma tana bukatar kiran nasa, tayi missing dinsa da muryar sa gaba daya. Kiran nasa tayi tana tashi tsaye lokacin da ta soma ringing, be daga ba, amma kuma tana katsewa ya biyo kiran a take.

 

"Assalamu alaikum."  Tayi sallama wayar a hannun ta bata saka a kunne ba

 

"Wa alaykisalam."

 

Ya amsa sai yayi shiru, itama shirun tayi tana saka abinda zata ce

 

"Shine baka kirani ba?" Ta samu kanta da fad'a ba tare da tayi tunani ba. Abinda dama yake son ji kenan, tayi missing dinsa in dai har tayi korafi akan rashin kiran, murmushi yayi wanda taji sautin sa ta cikin wayar

 

"Kinyi kewa ta kenan ko?"

 

"Um um." Tace da sauri

 

"Kawai dai na kikkiraka bata shiga, kuma Abba ya bani sako shine kawai dama."

 

"Ohh, sakon Abba ne yasa kika kira ni ba don kinyi kewa ta ba?"

 

Shiru tayi dan a zahirin gaskiya ba hakan bane, tana bukatar ji daga gareshi, tana bukatar comforting words dinsa, tana bukatar shi kawai ma in short.

 

"Ni kuma kinga nayi kewar ki, sosai sosai komai ma da nake anan din yinsa kawai nake ba don naso ba, kiyi hakuri kin kirani, ina wajen da dole na kashe waya, shiyasa har kika jini shiru haka."

 

"Ok." Tace a ba tare da tasan me zata ce ba

 

"Ya gida ya kowa da kowa?"

 

"Alhamdulillah, yasu Ammi? Ka samesu lafiya?"

 

"Lafiya lou, banje gida ba, yau nake shirin zuwa in sha Allah."

 

"Ok tam, karka manta ka gaishe ta."

 

"Ba zan manta ba, zance mata sirikarta na gaishe ta, zan kira sai na bata kuyi magana."

 

" Um um ba zan iya ba."

 

" Kunyar ta kike ji? Irin kunyar surkutan nan ko?" Ya kyalkyale da dariya

 

" Ni dai bance ba."

 

" Ni kuma nace."

 

" Uhum."

 

" Wacece Maryam?"

 

" Yayata ce da akayi bikin su, nazo gidan ta bata da lafiya zan kwana biyu na dan taimaka mata."

 

" Owk ayya, ki duba ta, Allah ya bata lafiya."

 

" Amin zataji."

 

" Baki fad'a min ba, me Abbanmu yace?"

 

" Na zata ba zaka tambaya ba ai?"

 

" Na isa? Ina sane kawai dai."

 

" Dama cewa yayi, a turo."

 

" Me!!! Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulillah! Kina nufin Abba yace na turo magabatana ayi magana? Kenan Abba ya yarda ya bani ke? Kai mAsha Allah, Alhamdulillah."

 

" Wannan murnar haka." Tace cikin mamaki

 

" Ba zaki gane ba, ba zaki gane ba Zahraah, Nagode sosai, Allah ya sakawa da Abba da alkhairi. Nagode nagode, wannan ranar ta shiga cikin ranaku masu matukar muhimmanci a tare dani, Alhamdulillah."

 

" Allah ya tabbatar mana da alkhairi."

 

" Amin Zahra nah, Amin Amin. Bari kiga na tashi, banga ta zama ba a yau zanje na same su da maganar, in sha Allah a kwana daya zuwa biyu magabatana zasu zo, ayi komai a gama, Allah yasa Abba ya saka mana lokacin kankani, bansan irin farin cikin da zan ba, Alhamdulillah."

 

" Uhum." Tace dadi na kamata, a kalla ta samu wani da yake son ta sosai, irin soyayyar da ta rasa tun tana yar kankanuwar ta.

 

" Zan kiraki anjima, ki kula da kanki."

 

" In Sha Allah. Ba-bye."

 

Fadawa tayi saman gadon tana jin farin ciki matsananci

 

" Ya Allah ka sa ya zama alkhairi a rayuwa ta, Allah ka tabbatar mana da alkhairi."

 

Ta furta tana jin kamar bata da saurin bakin ciki.

 

***Da karfin sa da kwarin guiwar sa ya isa masarautar su, wannan karon shigar da yasan Bubu yafi so yayi, shigar Manyan kaya da rawani, yayi masifar kyau ya fito a basaraken sa na ainihi, duk wanda yaci karo dasu sai sun kalle shi sun sake kallon sa, kai tsaye bangaren Aji ya nufa, domin wanchan karon be samu ganin Hajjan sa ba, shiyasa ya fara tachan dan tasan sai tayi korafi. Tana ganin shi kuwa ta hau murna, ta rasa in da zata sakashi, mace ce me jin mulki sosai domin mulkin a jinin ta yake dan har tafi Aji, amma kuma a duk abinda ya hada da muhammad bata hada shi da komai da kowa, da kanta take masa komai duk abinda yake so kuma shi take so ko da kuwa kowa ba zai goyi bayan sa ba.

  Sai da ya gama mata shagwabar sa son ransa sannan ya gabatar mata maganar auren da yake so aje a nemar masa, murna a wajen ta kamar ta dauke shi ta goye haka taji, karshe ta dinga tsokanar sa da sauran idan amaryar tazo ya manta da ita, da tsohuwar zuma dai ake magani. Da haka ya wuce fada in da yasan zai samu Bubu wanda tuni labari ya riga ya kai masa, ya shirya yana dakon karasowar Muhammad din. Ganin sa ya saka Bubun farin ciki, musamman da ya ganshi cikin shiga irin ta gidan sarauta!

 

***Abba na zaune ya gama karatun alkur'ani me girma Maman ta shigo, ta zauna a gefen sa yayi kamar be ganta ba

 

"Dr wai fushin ne har yanzu? Be kamata ace abu irin wannan ya bata maka rai ba, yara hakuri ake dasu."

 

Daga mata hannu yayi

 

"Bana son maganar nan, idan har ba zaki iya tankwara yarki ba, kuma ba zaki nuna mata dai-dai ba, shikenan, abinda kuke so kuka zaba zanyi muku."

 

"Allah ya huci zuciyar ka, da anyi auren ma.in sha Allah zaka sauko, musamman idan kaga zaman nasu lafiya lou."

 

"Allah ya taimaka." Yace yana kokarin mikewa

 

"Dama magana nazo muyi, gida zanje."

 

"Allah ya tsare hanya, ya kiyaya" yace kawai cikjn halin ko in kula

 

"Kwana uku zuwa sati nake son yi."

 

"Duk yadda kika ga yayi miki." Ya karasa ficewa. Kwafa tayi ta mike tana jin haushin sa. Ko me zaiyi ba zata hana Zeenat abinda take so ba, an wuce zamanin auren dole. Zai gaji dan kansa ya sakko.

1/12/22, 08:56 - Buhainat: Halin Girma

    12

 

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

 

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb

 

***Kai tsaye ya wuce zuwa chan gaban Bubun, fadawa na aika masa da kikari, kirarin da yake jin sa har cikin kansa, sai dai baya taba bari yayi tasiri a gareshi, hasalima yi yake tamkar be san me suke cewa ba. Dukawa yayi kamar yadda yake a al'adah ya gaida Bubun, ya amsa masa da ka ba tare da yace komai ba, a irin wannan zaman Bubun baya magana sai ta kama, sanin haka ne yasa Muhammad din ya koma daga bangaren dama ya zauna kafin sauran yan fadar su shiga kawo masa gaisuwa. Amsawa yayi duk a jimlace, ya hakimce a gefe yana sauraron  zaman yake wakana. Kasancewar zaman na gab da tashi ne yazo, shiyasa yayi tunanin ba za'a wani ja lokaci ba, sai yaga an dauki lokaci ana maimaita abinda aka fad'a a baya, ya sani sarai hakan tsarin bubu ne, kila kafin ya iso ya shirya hakan saboda shi, murmushi yayi yana satar kallon Bubun da shi din ma shi yake kallo. A karon farko yaji tausayin mahaifin nasa ya kamashi, yadda yake kokarin ganin ya damka mulkin a hannun sa bayan shi kuma bashi da ra'ayin hakan, amma kuma be tursasa masa ba, ya cigaba da bin sa a hankali zuwa lokacin da yake ganin ya dace.

   Be san ta yaya zai fahimtar dashi ba, amma yana da dalilin sa babba da ya saka shi tsayawa akan bakan sa, akwai babban kalubale a gabansa idan har ya amince da muradin Bubun , amma ta yaya zai iya gujewa hakan? Bayan babu wanda yasan dalilin sa?

   Yana jin sanda zaman ya kare, ya sauke ajiyar zuciya me nauyi ya daga idon sa sama yana kallon tsaruwar fad'ar, komai na ciki me tsada ne da kawa, haka duk wani abu da yake ciki me muhimmanci ne ga masarautar.

  Tunanin Bashir ne ya fado masa, da ganin da yayi masa da fitsararriyar yarinyar nan, Bashir yana direbobin Masarautar Kano wanda ya sanshi sosai saboda kaudin sa da hayaniyar sa, kafin ya auri wata mata wadda ake kyautata zaton auren jari yayi, tun daga lokacin kuma ya bar masarautar sai jefi jefi yakan je ya gaida Fulani idan ta kama. Yayi mamakin ganin sa da zabgegiyar mota amma da ya bincika ya gane komai, sai yaji hakan yayi matukar yi masa dadi, yayi Kuma daidai da tsarin da yake son dora su akai.

   Dawowa yayi daga tunanin jin kamar an taba shi, ya kalli wanda ya taba shin sai ya fad'ad'a fara'ar fuskar sa,

 

"Aji!"

 

"Tunanin me kake haka Muhammad?"

 

" Babu komai, mun same ku lafiya?"

 

" Lafiya lou, ya aikin? Amma kazo kenan ko? Zaka dade?"

 

" In Sha Allah!"

 

" Sannu da zuwa." Yace yana mikewa

 

" Zuwan ka dana ji ne ya sakani zuwa , Ina fatan idan ka huta zaka shigo, akwai batutuwan da nake so mu tattauna."

 

" Muje na taka maka, dama nima akwai maganar da nake so muyi."

 

" Toh toh madallah."

 

" Muhammad."

 

Bubu ya kira sunan sa yana daga zaune

 

" Na'am Bubu!"

 

" Naji dadin ganin ka da shiga irin wacce ta dace da kai, Ina fatan dorewar hakan."

 

" In Sha Allah Bubu, zan kokarta."

 

" Madallah da kai."

 

" Allah ya kara girma."

 

Tashi yayi suka fice tare da Aji, hannun su cikin na juna, Maimartaba ya jinjina kansa yana mamakin tarin kaunar da suke wa juna, har suka bacewa ganin sa sannan ya sauke ajiyar zuciya yana tafiya tunanin abubuwan da aka tattauna don cigaban al'umma. Sai dai yana fara tunanin, tunanin ta ya shigo ya katse masa duk hanzarin sa, ya rasa dalilin da ya saka a duk sanda ya tuna da maganar yake jin duk wata walwalar sa da farin cikin sa ya ragu, musamman a dan tsaikon nan, sai yake jin tamkar ana dakatar dashi da yin wani yunkuri. Shi din mutum ne me riko da addini matukar gaske, baya taba bawa maganganun da za'a zo a fad'a masa muhimmanci ko kad'an, sai dai a duk abinda ya shafi Muhammad baya wasa, yana ji a ransa kar fa abinda tsohuwar matar ta sanar masa ya zama gaskiya, tsoron hakan ya hanashi gabatar da komai cikin sauri yake bin komai a hankali, ba kuma wai dan ya gasgata maganar ta dari bisa dari ba, sai dan yana ji da tsoron sharrin masu sharri, be san me suke shirya wa dan nasa ba, sai dai be gaza ba, babu dare babu rana kullum cikin nema masa kariya yake a wajen ALLAH, ko ma menene tabbas zai zo masa da sauki.

 

 ***A falon Ajin ya same shi yana zaune fuskar sa kamar gonar auduga, da kansa zai je amma sai Bubun yace ya bari yazo kawai ya huta. Bayan ya zauna ne fadawan suka fice suka jawo musu kofar.

 

"Na matsu na sanar da kai wannan albishir din, abinda muka dade muna jira ne, Muhammad dai yazo da magana, har yana neman aje ayi masa tambaya!"

 

Fuskar Bubu ta fad'ad'a,farin ciki ya mamaye shi

 

" Masha ALLAH! A kanon ne kamar yadda Takawa yace?"

 

" Eh har binciken da mukayi, nan din ne in Sha Allah."

 

" Sai a sanar wa Takawa babu jira, in Sha Allah gobe duk abinda ya kamata ayi sai ayi, jibi sai aje musu da magana, da tsayayyiyar rana domin Takawa ya bukaci ayi komai a cikin kankanin lokaci."

 

" Madallah...Hakan yayi."

 

Tattaunawa suka shiga yi har dare yayi sosai,kafin ya koma bangaren sa cikin jin dadin labarin auren Muhammad din.

 

***Jifa tayi da kofin hannun ta, ya fashe a wajen gaba daya kwalbar ta wawwatsu a dakin, wani irin bakin ciki take a duk lokacin da taji wani abu da ya danganci Muhammad din. Yau Itace a turakar Bubu amma tasan ba zata taba samun kansa ba, idan ma ta zafafa zai iya cewa ta bar masa dakin shiyasa ta yanke wa kanta hukuncin ko da yadawo daga wajen Aji ba zata je ba zatayi zaman ta tayi tunanin menene mafita a gareta.

 

"Ranki ya dade, Yarima Muhammad yana waje yana neman iso."

 

" Uban me zai min!!"

 

Ta daka mata tsawa tana huci, sai kuma ta hau kokarin daidaita kanta

 

" A shigo dashi babban falo gani nan."

 

Da sauri baiwar ta fice tana mamakin uwar dakin nata.

 

Zaman sa yayi yana karewa falon kallo, an sabunta komai ba kamar zuwan sa na karshe ba. Murmushi ne a fuskar sa, yana da yakinin bata da bukatar ganin shi, ko da gilmawar sa ne balle har ya kai ga zama a falon nata, yana sane yazo domin ya kara tabbatar da abinda ya sani tun tuni.

  A yadda ta fito, da yadda ta zauna kadai ya isheshi amsar abinda yazo nema, yana kallon yadda take satar kallon sa cikin kallon da yasan na tsantsar tsana ne tun da ya riga da ya dade da sanin bata kaunar sa ko daidai da minti daya ne

 

" Barka da gida, mun sameku lafiya?"

 

 

Ya fad'a da yanayin da yasan zai sake tunzura ta.

 

" lafiya, ya aikin naku?"

 

"Babu dadi, na gudo ma na dawo gida cikin yan uwa!"

 

"Ka kyautawa kanka." Tace a gajarce

 

Mikewa yayi yana zuba hannayen sa cikin aljihun sa, ya yi mata kallon cikin ido tace

 

"Bari na koma."

 

"Baka Sha ko ruwa ba." Tace tana daga zaune

 

"Na yafe, bani da bukata."

 

 Ya dage gira yana juyawa, da kallon bakin ciki tabi bayansa har ya fice daga falon, ta yarfe hannunta tana jin kamar ta kamo shi ta tayi ta jibgar shi har sai taga ya daina motsi.

 

"Ciwon Ido, zanyi maganin ka!" Ta furta tana tashi ta koma ciki

 

 

***Daga nan bangaren Ammin sa ya wuce, yana jin kansa kamar sabon ango, farin ciki yake ciki shiyasa ma be wani damu da abinda ya faru ba. Dama yasan kafin ya isa ta samu labarin ko ta wajne Hajja ko Bubu, aikuwa yana shiga ta tare shi da murnar ta, ya zauna ya tankwashe kafarsa a gabanta tana jin yadda take lissafo masa abubuwan da za'a bukata na zuwa gidan su Fatiman.  A farkon farko be so wani abu na sarauta ya shigo ba, amma kuma da ya tabbatar hakan ba zai yiwu ba, shiyasa yayi amfani da damar nan wajen hadawa Mama gadar zare, dalilin tafiyar ta da shine ya assasa bayan ya kira Khalil a waya ya karanta masa yadda duk yake so ayi, babu musu ya amsa kuma ya tabbatar masa da zai yi komai daidai. Dazu Kuma ya kira shi ya tabbatar masa da Maman ta iso tun wayewar gari. Da wannan ya yi gaba wajen aiwatar da saura shirin sa da ya tabbata zasu yi matukar girgiza kowa ba Maman kawai ba.

  Har dare sosaii yana shashen Ammin, ta hada komai abubuwan da ya tabbata zasu dace da tsarin fatimar sa, shi din ma akwai tanadin da yayi mata amma ba yanzu ba, sai ranar da dubban mutane suka shaida, ya zama ita ta zama shi, a ranar zai nunawa duniya kalar gatan da take dashi a wajen sa.

  Da sassarfa ya karasa part dinsa, Kai kace wani uban aiki yayi saboda yadda yake jin sa a gajiya. Kwanciya kawai yayi bayan ya aika mata da cool night text message ya kashe wayar sai bacci, baccin da yake yi a duk lokacin da ya samu kansa a dakin sa na cikin gidan.

  Zai iya cewa ya jima beyi bacci me dadin na ranar ba, ko dan abinda ya faru a ranar ne? Ko Kuma dai dan ance gida daban yake, dama bahaushe na cewa kowa ya bar gida... wanka ya soma yi, ya fito domin ya karya dan yasan komai na kammale a ajiye yana jiran sa. Zaman karyawa yayi, yayi dialing number dinta yana kallon plate din da ake zuba masa abinci, da hannu yayi masa alamar ya isa, ya karba ya soma ci jin bata daga ba, a yar mu'amular da yayi da ita, ya lura tana da bawa kowanne abu muhimmanci idan har shi ta saka a gaba, misali idan tana aiki takan ajiye wayar ta waje daban ta kammala aikin, haka idan tana wani muhimmi abun bata hada shi da komai har sai ta gama. Tunanin sa ne ya katse lokacin da kiranta ta ya shigo nasa. Murmushi yayi yana jan tissue ya goge bakin sa, yayi rejecting kiran sannan ya bi bayan yana kishingid'a a jikin lallausan tumtum din dake kusa dashi.

  Da sallamar ta, ta daga kamar ko wanne lokaci, ya amsa mata shima kafin ta dora da gaisuwa

 

"Ina kwana?"

 

"Lafiya lou, kin tashi lafiya?"

 

"Lafiya lou, yasu Ammi? Ka same su lafiya?"

 

"Kalou kowa, ya sister Maryam da jiki?"

 

"Gata ta samu sauki, inaga ma na tafi gida tunda naga ta warke sosai. "

 

" A ah kiyi zaman ki! " Yace da sauri

 

" Me yasa? "

 

" Amm kin gane, kinga tana bukatar ki, ki dan kara mata ko da kwana biyu ko uku ne, zata ji dadi. "

 

" Owk tam. "

 

" Yawwa. "

 

" Ina kika shiga dazu na kira no answer, kitchen? Ko shara? "

 

" Ya ka sani? Ina kitchen. "

 

" Na sanki ai, nasan bakya wuce wuraren nan biyu. "

 

" Lallai, kasan abubuwa da yawa akaina, amma ni bansan komai ba. "

 

" Zaki sani, karki damu zaki sani fiye da sanin da kowa ma yayi min. ".

 

 Ya karashe maganar cikin sigar tsokana, bata ce komai ba, yasan kuma ba zata ce din ba, shima ba dan tace wani abu yayi maganar ba

 

"Zan zauna takanas, kiyi min duk tambayoyin da zaki yi min, zan amsa, amma kafin lokacin ina so ki san, nifa soja ne!"

 

"Soja!" Tace gabanta na faduwa sosai, bata son aikin soja ko miskala zarratin, bata kuma taba tunanin auren soja ba, dan tasan yadda suke very busy da aikin su

 

"Eh ni soja ne, amma fa irin kurtun nan."

 

"Soja dai ai duk soja ne, sunan daya ne."

 

"Amma rank din daban daban ba."

 

"Uhummm. " Ta ja ajiyar zuciya, ya sammace ta, kenan dai zaman kadaici be rabu da ita ba, dan sojoji basu da lokacin kansu balle na matan su, yanzu ita kenan...

 

" Karki damu, ba zan dinga nisa ba kinji? Zan zama ko yaushe kika bukace ni Ina kusa, nayi miki alkawari."

 

"Allah yasa, dan da gaske bana son aikin soja wallahi."

 

"Saboda me? Aikin taimakawa kasa ne fa, aikin lada ne idan har ka yi yadda ya dace."

 

"Na sani, ni kawai bana so ne, basu da time din kansu ballanta na ..."

 

"Na matan su? Haka ko yaushe aka cewa dama, toh ni dai Ina da time dina Ina kuma da na matata, har sai kin gaji kin koreni daga gidan ma wataran."

 

"Shikenan."

 

"Zaki gani ai, ki zuba ido."

 

Shigowar Ya Maryam ya sakata yin shiru

 

"Ki fito falo ya tafi wallahi, ni kadai kamar mayya." Tace mata tana rik'e kofar, tun dazu tace tazo falo taki sboda maigidan yana nan, shiyasa Maryam din tazo kiranta da ya tafi, ko yar hira sa yi

 

"Kice ina gaishe ta, ya jikin nata."

 

"Da sauki." Tace tana janye wayar daga kunnenta.

 

"Ashe waya kike shine kika yi luf, toh ki gaishe shi, in kin gama Ina jiran ki."

 

Ta fita ta ja mata kofar

 

"Bari na barki kuyi hirar ku, zan sake kira anjima."

 

Kamar ta tambaye shi maganar zuwa gidan amma ba zata taba iyawa ba, sallama tayi masa ta ajiye wayar ta fita wajen Maryam.

 

 

Yana sane sarai yake ce mata komai, baya so tasan komai sai anyi komai ya kammala, ba zai ma gaya mata zuwan nasu ba, Abba kawai zai wa text ya sanar masa, idan yaso sai ya turo Musaddik ya sameshi ya sake fad'a masa Incase ko be ga message din ba. Haka kuwa akayi, yana masa text din ya gani, yayi saurin kiran kowa ya sanar dasu zuwan bakin, anan suka fara tunanin abinda ya kamata suyi, baki daga irin wannan babban gidan dole ne ayi abinda za'a fita kunya. Sun dade suna shawarwarin su kafin su tsaida matsaya, nan da nan suka shiga shirin tarbar su cikin tsarin da suka san ba zai zama wani iri ba.

 

Abba na zaune kiran Mama ya shigo wayar sa, shi kadai ne a gidan sai Habib ta tafi da Zeenat da Marwan, shiru gidan babu kowa kallon tv yake a zahiri amma a badini tunanin masu zuwa neman auren Iman yake a gobe, yaso ya sanar wa mahaifiyar ta zuwan nasu da komai akan maganar sai dai baya samun ta a waya wajen kwana uku kenan, yasan tana business sosai kamar ma tana fita kasashe saro kayayyaki shiyasa yayi tunanin ko kila bata k'asar ne.

   Kallon wayar tasa yayi, har lokacin haushin Maman yake ji musamman abubuwan da ya gano akan irin rikon da tayiwa Fatiman tsawon lokaci be gane komai ba, har Marwan ya titse ya tambaya ya kuma gaya masa komai abinda ya sake daga masa hankali sosai kenan. Kiran ne ya sake shigowa ya daga ba dan yaso ba, dan dai kawai be san ko wani abu bane emergency ya taso, sallama tayi ya amsa ciki ciki. Dama tasan za'a rina shiyasa kawai ta tafi kai tsaye akan dalilin kiran

 

"Dama Zeenat ce ta ce na sanar da kai iyayen Bashir zasu zo gobe idan Allah ya kaimu."

 

"Su bari jibi gobe Yaya yana da abinda zai yi."

 

Yace mata kai tsaye

 

"Amma da ka barsu sunzo goben ba dole sai wajen Yayan ba ai."

 

"Haka tsarin mu yake tun farko, babu Kuma dalilin da zai saka na chanja yanzu dan anzo auren nawa yayan, idan har ba zasu iya bari sai jibin ba sai ki nema musu wanda zasu gani a goben."

 

"Abin be kai haka ba ai, Allah ya kaimu jibin."

 

"Amin."

 

 Yace ya katse kiran yana Jan tsaki, wato duk dadewar ka da mace ba zaka taba sanin wasu daga cikin halayen ta ba har sai abu ya faru, lallai.  Shi kadai yake ta wannan tunanin har lokacin da zai kwanta yayi, ya kwanta da addu'ar Allah yasa komai ya tafi dai-dai goben.

 

***Duk cikin su babu wanda ya makara, suka tashi aka hau gaggayara gidan harabar da lungu da sako su Habib suka taimaka aka tsaftace ko ina, dama dai a gyara yake saboda takanas aka dauki me aikin kula da wajen amma duk da haka idan suka tuna bakin da zasu zo sai suga ya kamata a sake gyara ko ina.

   Wajajen sha biyu cikin jagorancin Musaddik suka iso, cikin manya manyan motocin alfarma da aka rubuta Emir Kano 1 guda biyu sai guda biyu dauke da tambarin Adamawa Palace.

  Cikin kankanin lokaci unguwa ta dauka, mutane suka dinga lekowa daga gidajen su dan tabbatar da abinda yaran su suka je suka fad'a musu, kowa ya leko sai ya rik'e baki cikin tunanin abinda ya kawo irin mutanen gidan.

   Cikin matuakr girmamawa Abba suka karbe su, sai dai sunyi tunanin zasu gansu a matsayin mutanne da basu kai ba ko kuma level dinsu ba daya ba, amma sai suka ga akasin haka, cikin girmamawa, karamcin da dattako suka zo musu, suka nuna Halin Girma, halin babban gida babu fariya ko nuna su din wasu ne, cikin tattautasa harshe da girmamawa suka nemarwa dan su kuma jikansu Muhammad auren Fatima. A take Abba yace an bashi. Su kuma nan take suka gabatar da ranar da suke so a saka, babu musu nan ma Abba ya amince suka tsaida wata daya kachal, shi din ma saboda Muhammad din ne ya bukaci haka, amma idan sune toh sati biyu zasu saka.

  Babu wani bata lokaci abinka da manyan mutane, masu Halin Girma, suka yi komai cikin sauki sannan da zasu tafi suka gabatar da kyaututtuka daga iyaye da kakannin Muhammad din da yake cikin al'adarsu idan za'a zo neman auren. Tarin kayan da suka kasance mota guda sai da suka bawa su Abba mamaki, a gefen Abba aka ajiye mukullin motar nufin su har da motar da duk abinda yake ciki kyauta ce ga sirikar Sarki Ahmad Santuraki, da iyalan gidan sa kafin zuwan ta, sannan suka yi musu sallama suka tafi.

 

 

#HafsatRano

#ZafafaBiyar2021

Not edited

Ignore typos

 

 

 

 

Masu sharing sannun ku da kokari kunji? Allah ya shirye ku idan masu shiryuwa ne, idan kuma ba masu shiryuwa bane toh... Kun san sauran dai😀

1/12/22, 21:41 - Buhainat: Halin Girma

    13

 

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

 

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb

 

 

***Sai da suka ga tafiyar su sannan suka dawo ciki, kowa da abinda yake cin sa a zuciya. Tabbas sun amsa sunan babban gida, haka sun nuna Halin Girma da dattako na irin manyan mutane da suka san mutunci da yakana.

   Fadar irin tarin kayan da suka zo dashi ba abu bane me sauki, hakan ya dan tarsa tsoro a zuciyar Abba, yake jin tamkar siyar da Iman din zai yi, wannan uban dukiya a matsayin tambaya, ina ga idan aka zo auren? Basu da talaucin da arziki zai tsorata su, sai dai dole ne suyi mamaki ganin uban dukiyar da aka lafto da sunan na Iman din ne, tun daga kan sutura zuwa kayan kawa na mata, da kyautata gwala-gwalai tamkar ba'a san darajar su ba.

   Haduwa suka yi suka tattauna yadda zasu adana komai saboda yadda rayuwar yanzu ta zama ta rashin tssro, shawarar farko shine su bar maganar tsakanin su domin mata akwai sakin baki musamamn idan abun da ya sha musu tunani ne, yanzu zasu yi ta kwazozotan sa har wasu dake waje su samu damar aiwatar da mummunan kuduri akan su.

  Tabbas shawarar tayi dan da gaske komai na iya faruwa idan maganar ta fantsama shiyasa kawai a take aka fita da motar da duk abinda yake ciki daga gidan zuwa in da zai fi zama safe kafin bikin yazo kusa sosai sai ayi abinda ya dace dasu, ko bata kayanta ta tafi dasu tunda dama su chan babu wani tsoron rashin tsaro ta ko ina zagaye suke da Jami'an tsaro. Karshen magana kuma ma shi Muhammad din kansa, su ne tsaron ma baki daya. Da wannan shawarar suka tashi bayan Abba ya sanar musu da zuwan iyayen Bashir a gobe kamar yadda Mama ta shaida masa.

  

Sake gwada kiran Maman Iman din yayi bayan ya koma gida, cikin sa'a kuwa kiran ya shiga, bata wani jima tana ringing ba ta dauka a nutse cikin sallamar ta da muryar da yake jin ta kullum a bakin Iman din, maganar da sak ta mahaifiyar ta, hatta nutsuwar ta irin ta uwarta ce shiyasa yake jin ba zai iya mantawa da ita ba ko da shekaru sun ja, duk da yanzu babu batun soyayya a tsakanin su tun da be riga yasan matsayar da take a yanzun ba ko da aure ko babu, a dai kwanakin baya ya samu labarin tayi aure har da albarka Yaya a tsakanin su.

 

"Ina wuni Abban Iman?" Ta gaishe shi jin yayi shiru bayan amsa sallamar ta

 

"Lafiya Lou Maimunatu, ya gida ya kowa da kowa?"

 

"Kowa lafiya Alhamdulillah, Iman fa?"

 

"Tana nan lafiya."

 

Shiru sukayi baki daya, kowa da kalar tunanin sa a ransa, shine ya katse shirun ta hanyar cewa

 

" Inaso zan kawo miki ita kamar yadda nayi miki alkawari idan auren ta ya tashi, ta samu miji har an tsaida rana wata daya, in sha Allah a tsawon wata dayan nan zata zauna a wajenki, a matsayin ki na mahaifiyar ta sai kiyi duk abinda ya dace, kiyi hakuri da Kaddara, kiyi hakuri!"

 

Wani irin yar taji har cikin kanta, Iman dinta har ta girman da zata yi aure, rayuwa na gudu sosai, tana tuna lokacin da ta dawo masa da ita, da irin tashin hankalin da ta shiga a rashin ta wanda bata taba tunanin zata dawo daidai ta cigaba da rayuwa ba, a lokacin tunani take rayuwarta ta kare gaba daya, amma kuma sai gashi ta cigaba da rayuwa duk da babu ranar da zata fito ta fadi bata tuna yar tata ba, amma ya zatayi? Mutane na fifita al'ada akan addini. Ta sani sarai uwa ce taka da ikon rik'e yarta har zuwa aurenta, tare da sharadin kula da duk wata bukatar ta daga mahaifin ta, sai dai idan anji tsoron tarbiyyar da zata samu a wajen uwar, toh amma a lokacin wa take dashi da zai tsaya mata? Bayan iyayenta da take ganin su a matsayin gatan ta sun kekashe kasa sun ki amincewar da rikon nata a wajenta? A lokacin da akwai karancin shekaru a tare da ita, amma da ace yanzu ne, babu me raba ta da yarta kuwa, duk yadda zatayi zatayi ta tabbatar da ta rik'e ta a wajen ta. Ta bata kulawa da dukkan gatan da take bukata.

 

"Allah ya sanya alkhairi, ya nuna mana lokacin."

 

Kawai tace dan bata kuma san me zata ce masa ba, taji dadi da ma ya cika alkawarin sa, zatayi kokari a dan zaman nan ta koya wa yarta kaunar ta da sabawa da ita da yan uwanta, sannan ta nusar da ita rayuwa da yadda zata kula da auren ta. Sallama sukayi da alkawarin ana gobe zai kawo ta, zai kira ya sanar mata. Godiya tayi masa dan har gobe tana ganin kima da mutuncin sa, mutum ne shi na gari, me kirki da son iyalin sa.

 

  Bayan gama wayar da sukayi ne zuciyar sa ta gwada masa kiran Zeenat ya sake gwada tankwarata, idan Allah ya taimake shi ta hakura sai yafi kowa murna, dan yanzu bashi da babban tashin hankali kamar auren zeenatun da yake da yakinin zai iya zamar mata wani Babban tashin hankali a gaba.

  Kiran nata yayi, tana dagawa yace ta matsa daga wajen kowa zai yi magana da ita, da ido ta kalli Mama dake zaune ana maida maganar auren Zeenat din da Hajiya ta fice zuwa tsakar gidan.

 

"Abba na fito."

 

"Yawwa zeenatu, magana nake so muyi a matsayi na, na mahaifin ki, kin san dai ba zan taba zabar miki abinda zai cutar dake ba, ba kuma zan ga cigaba a gareki na dakushe ki ba, ina neman alfarma, kiyi hakuri da Bashir  ki kawo wani ba shi ba,nayi miki alkawarin tsaya miki kinji?"

 

Gabanta ne ya fadi, a tunanin ta an gama wannan babin, sai gashi Abban ya dawo da shi yana kuma kokarin daure ta da jijiyoyin jikinta.

 

" Kina jina zeenatu?" Ya sake fad'a cikin yanayi me wahalar fassarawa

Shashekar kuka yaji, ta fashe da kuka cikin muryar kukan tace

 

" Dan Allah Abba kayi hakuri?"

 

"Ai ba laifi kikayi min ba Zeenatu, alfarma kawai nake nema a matsayi na, na mahaifin ki."

 

"Abba dan Allah kayi hakuri, wallahi ba zan iya hakura da Bashir ba."

 

Kamar saukar aradu haka Abba yaji, ya dafe kansa ya shiga karanto innalillah wa inna ilaihi rajiun, babu babbar jarrabawa irin yayanka suyi rashin sa'ar miji, duk abinda yaje ya dawo dole kana ciki, kamar ka saida akuyar ka ne tazo tana ci maka danga, baya fatan hakan ta faru ga ita, shiyasa tun farko ya hakurkurtar da zuciyar sa be ga laifin ta ba sai na Mama, amma yanzu ya tabbata abinda Zeenat din take so shi Maman take goyan ba, dama mafiya yawan lokuta uwa na tafiya ne da ra'ayin yarta.

 

"Shikenan zeenatu, duk abinda yaje ya dawo karki kuka da kowa, ki kuka da kanki."

 

"Abba dan..." Kafin ta kai karshe ya katse kiran, Jan kafarta tayi ta koma ciki tana jin a ranta tayi abinda ya dace, a kalla ta yi kokarin kare soyayyar ta ko ba komai idan akayi auren Abban zai hakura ya sakko.

 

"Lafiya?" Mama tace tana kallon ta.

 

"Ya kukayi da Baban naki? Maganar dai ce ko?"

 

Da kai ta amsa mata da eh, tsaki Maman taja

 

"Shine kike kuka ko me? Ni wai Zeenat asiri Bashir yayi miki ne? Da bakya ganin kowa da komai sai shi?"

 

Kanwar Maman Atika ta fad'a cikin bacin rai

 

" Ni banga wani abun naci a Bashir din nan ba, tunda mahaifin yarinyar nan baya so toh a hakura mana? Iyaye maza sun fi mu tunani da hangen nesa."

 

"Toh Atika ya za'a yi? Shi ma fa duk zuga ce wallahi, ai da be san da hakan ba sai bayan yaga mijin da yar lelen tasa ta samu, shikenan kuma sai kananan maganganu bansan daga ina ba, amma ina kyautata zaton daga wajen Gaji ne, dan ita kadai ce take sauya musu tunani da raayi dukkan su, ita kuma na tabbata munafurcin Iman ne dan ko yaushe tana wajen ta."

 

"Duk wannan ta tunani ne Yaya Hajara, bamu da tabbas din hakan, kinga dai yadda Dr ya dage ya kamata ace kin bashi dama kinji ta bakin sa akai."

 

"Kyale shi kawai, zai sakko ne."

 

"Me yace miki?" Ta tambayi Zeenat din tamkar abin be dameta ba.

 

"Cewa yayi nayi masa alfarma na hakura da Bashir."

 

"Ehen kinji? Har ya saukar da kansa a matsayin sa na mahaifi yace yana neman alfarma kema Yaya Hajara kinsan da matsala."

 

" Me kika ce masa ke kuma?" Taki amsa atikar ta tambayi Zeenat din.

 

" Hakuri na bashi." Tace tana rakubewa a gefen Hajiya da tunda aka fara maganar bata saka musu baki ba sai lokacin

 

" Gaskiya da kun hakura kun bi zabin Ibrahim, a kalla shi namiji ne yafi mu dukka tunani da hangen nesa."

 

" Hajiya toh ya za'a yi? Lokaci ya riga ya wuce bata kula kowa sai shi, yaushe zata fara daga farko kafin ma ta samu saurayin su fuskanci juna a zo maganar aure."

 

" Duk wannan me sauki ne akan ka dauki dan ka, ka kaishi inda zai Sha wahala."

 

" It's better to marry late than to marry wrong." Atika tace tana girgiza kafarta

 

" Khair in sha Allah, babu abinda zai faru."

 

Maman tace a kasan zuciyar ta tana jin tsoron abinda zai je ya dawo, ita kanta ta fara tsoron yadda Abban ya kafe ta tabbata akwai babban dalili, amma kuma ta Ina Zeenat din zata fara? Hasalima bata da farin jinin samarin duk asalin su Iman suke so sai ita maman tayi amfani da wannan a juya mata kansu zuwa Zeenat din dan ba zata iya gani Iman din tayi aure musamman auren babban gida ita kuma Zeenat din na zaune a gida.

 

 

***Da sauri ya karasa part dinsa yana jin kayan na masa nauyi sosai, yau tun safe Bubu ya Aiko masa da kaya sannan ya bukaci ganin sa a kofar part dinsa dan shiga tawagar sa zuwa Fada, haka ya tashi ya shirya ba dan yaso ba ya fita. Tun lokacin sai yanzu ya samu dawowa part din sa, yana shiga ya hau cire kayan yayi wurgi da rawanin yana jin shi sakayau. Allah Allah yake ya samu feedbacks din aikin da ya saka Musaddik sai gashi kuwa ya kirashi adaidai lokacin, dagawa yayi yana rage daga shi sai singlet da boxer kasancewar zafi ya fara hurawa kadan kadan ba kamar kwanakin baya da ake sanyi sosai ba.

 

"Gani fa ga mutumin ka." Musaddik yace yana dagawa

 

"Da gaske? Sharp sharp haka? Ok bari na kiraka Video Call."

 

Ya katse sannan ya kira video call, a daidai saitin fuskar Bashir Musaddik ya saka wayar yadda yana dagawa Moh zai fara ganin sa. Yana durkushe tamkar me neman gafara, wata dariya ce ta zowa Moh, yayi murmushi kawai yace

 

"Oga Bashir barka da warhaka."

 

"Dan girman Allah ranka ya dade kayi hakuri, wallahi bansan gidan da kaje Neman aure bane nima naje, wallahi kuskure ne kawai amma kayi hakuri."

 

"Ai ba laifi kayi ba Bash, ni hakan yayi min dadi sosai, kuma ina tayaka murna, kaga ni da kai mun zama yan uwa tunda zamu auri yan uwa."

 

"Tuba nake ranka ya dade!" Yace yana kasa da kansa

 

"Dago kanka bash, bafa wani laifi kayi ba, aiki nake so na baka, bana son kuskure ko kadan a ciki, idan har kayi min yadda ya dace akwai babban tukuiwaci."

 

"Hakan shi yafi komai sauki a wajena ranka ya dade, fadi ko menene ."

 

"Yaushe za'a je tambyar maka auren?"

 

"Gobe ne ranka ya dade, amma idan kace a fasa na fasa wallahi."

 

Girgiza kai yayi

 

" Ba za'a fasa ba, Ina so idan sun je su nemi a saka musu wata daya!"

 

" Wata daya!" Ya zaro ido

 

" Wata biyar nace ko shekara, ban shirya ba wallahi,dan dai bana son na rasata ne."

 

" Ba zaka taba rasata ba, ni zan maka komai na auren tun daga lefe har gidan zama zan baka, ni dai kawai kayi duk abinda nace kayi."

 

Dukawa yayi jiki na rawa

 

" Nagode nagode Allah ya kara girma, zanyi duk abinda kace, ba zan yi komai ba sai da sanin ka."

 

" Good, yanzu aikin me kake?"

 

" Buga buga kawai, sai kuma aiken Hajjaju idan ya tashi."

 

Dariya sosai Moh yayi, ya hangi tsantsar mutuwar zuciya da son zuciyar a tattare da Bashir din, mikar da yan yatsun sa yayi baya, ya dawo dasu gaba suka bada sauti kafin ya katse dariyar yana zama so serious.

 

" Abinda nake so kayi min, zaka ji daga bakin Musaddik, bana son kuskure ko kadan, komai Ina so ya tafi cikin tsari , Ina so gobe ka dauki hanyar Katsina, zan aiko maka da sako ka kaiwa Gimbiya Zeenatu, hakan zai sake goge shakku ko wani tunani akanka."

 

" Nagode ranka ya dade, nagode nagode."

 

" Karka damu, kai dai kayi abinda nace, bana son kuskure ko kadan!"

 

" Da yardar Allah zaka same ni da bin duk umarnin ka. "

 

Daga masa kai Moh yayi sannan yace

 

" Guy!"

 

" Yeah Captain!" Musaddik yace yana matsawa daga wajen da Bashir din yake

 

"Ka kula dashi sosai dan dan iskan kansa ne, duk da be isa ba, amma dai bana so a samu matsala har zuwa ranar daurin auren, watch him and report anything da be maka ba."

 

"Karka damu, babu ma abinda zai faru. "

 

" Yau nayi zaman fad'a, kamar nayi kuka wallahi, wannan yazo ya fadi yayi gaisuwa, wanna yazo ya ce makwafcin sa kaza, wannan suzo maganar aure, wannan ta kawo karar mijinta wannan ya kawo karar matar sa, maganar gado, kai abubuwan da mugun yawa, kamar na gudo nake ji, nasan iya zaman da zan Bubu ba zai raga min ba wallahi, har na fara ramewa. "

 

" Haka zaka hakura kayi abinda yake so, iyaye dole a bisu ayi musu yadda suke so. "

 

" Haka ne dama, shiyasa na matsu nayi auren nan nima na zama me yancin kaina, kasan aure fa yanci yake siyo ma da martaba ba komai Bubu zai dinga matsa min ba da zarar yaga nima na zama dan gari a harkar. "

 

" A harkar me? "

 

" Harkar auren mana, ina fita daga novice zai yanta ni, kwana kad'an kaji nima ana Daddy, Daddy! Wayyo I can't wait. "

 

" Kaifa yanzu baka da magana sai ta aure ko? Wannan sanyin ne ba komai ba. "

 

" Sanyi ai ya wuce kuma, ba zan kara yarda na sake wani sanyin a gauro ba wallahi, haba Malam ai an ji jiki kawai. "

 

" Dan air. " Musaddik yace yana dariya

 

" Yan air dai, Wa ma ya kaika ne? Gwara ni wallahi kowa yasan uztaz. "

 

" Nima haka ai. "

 

" Fadawa wanda be sani ba toh. "

 

" Toh ai idan har Moh uztaz ne toh tabbas ni sai da shehin malami, kai din? Ina dai tausayin yar mutane da zata shigo hannun tuzuru irin ka wallahi. "

 

" Naji karka bata min tunani, jeka zan neme ka anjima bacci zan."

 

" Hahaha, shikenan sai na jiki, angon Fatiti. "

 

" Musaddik.!!! " Ya furta da karfi

 

" Sorry sir, angon Fatima. "

 

" Zaka shigo hannu ne wallahi, sai na saka an samin kai frog jump. "

 

" Idan wannan ne ai na gaji da yi, a chanja wani punishment din dai Captain. "

 

Kashe kiran Moh yayi, yasan ya biye Musaddik sai su cinye lokacin suna abu daya, wurgi yayi da wayar gefe ya kwanta dan rama baccin da Bubu ya katse masa.

1/18/22, 19:54 - Buhainat: Halin Girma

     15

 

_*Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾*

 

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾*

 

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

 

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

 

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

_________________________

 

•••••••••�

 

Kasa fitowa tayi, tana taraddadin yadda zasu karbe ta, ji tayi an bud'e kofar bangarenta, taji muryoyinsu a lokaci daya suna mata sannu da zuwa

 

"Yau ga Fatima,sannu da zuwa dota, sannu da zuwa."

 

Wata farar mata da a kalla zatayi sa'ar Mama ta fad'a tana riko hannun ta. Da wani irin yanayi take kallonsu su dukka, kowannen su kokari yake ya nuna mata kansa, mutum daya dage gefe tsaye ta harde hannayen ta a kirjin ta ta daga kai ta kalla, tun isowar su wajen ita kadai ce bata yi magana ba. Wani irin shock taji ta furta Mommy a tsakanin lips dinta, gyada mata kai matar tayi da sauri ta isa gareta ta rungume ta tana sakin kuka, bata chanja ba ko kad'an daga yadda take a hoton ta da take dashi tun na zamanin yan matantaka, duk da ganin ta da ita a zahiri kadan ne amma ko yaushe zuciyar ta na manne da hoton mahaifiyar ta.

   Tafi sukaji an saka daga bayan su, duk Kuma sai suka saka dariya har Iman din da kunya ta kamata ta sake shigewa jikin mahaifiyar ta tana jin wani irin son ta da kaunar ta.

 

"Muje ciki ko?" Babban namijin ya fad'a yana nuna musu hanya da hannun sa. Sakin Mom din tayi, matar farkon nan ta kama hannun ta zuwa ciki hanyar da ta ga sun fito dazun.

   A falo suka yada zango, kowa a cikin su kokari yake yaga ya nuna mata soyyayyar sa, da kallo kawai take binsu cikin mamakin dalilin da ya saka basa neman ta tsawon lokaci haka duk kuwa da soyayyar ta da ta hanga a tattare da family din. Tana da bukatar amsa saboda tasan yadda kowacce uwa take kulafucin danta musamman ita da aka dauke ta da karancin shekarun ta, tabbas a farko farko ta kan zo ta ganta tare da wani babban namiji duk kuwa da karancin shekaru basa barin ta tuna komai amma tabbas ta san anyi haka kuma Abba da kansa ya kara sanar da ita a wani lokaci da ta tambaye shi.

   Kamar an jeho su suka shigo su biyu, suka yo kanta da gudu macen ta rungume ta tana sakin ihu, namijin kuma ya durkusa a kusa da su yana dariyar farin ciki

 

"Welcome sister!" Yace bayan macen ta saketa ta zauna tana maida numfashi

 

"Welcome sis!"

 

Tayi saurin fad'a itama tana hararar sa

 

"Sannun ku."

 

Tace tana murmushi tana mamakin su,

 

"na riga shi ganin ki, na rigashi yi miki magana dan Allah ni kadai zaki so kinji? Dama kullum ina jin haushin bani da big sister sai wannan coconut head din , sai gashi na samu yanzu, I'm so happy wallahi, da k'yar na bari aka gama islamiyya yau wallahi."

 

"Amaani kin cika surutu wallahi, ai sai ki barta ta huta ko?"

 

" Tell her Mamma, wallahi kamar na bugeta yau din nan ta bani haushi."

 

" Kaifa ya sunan ka?" Ta tambaye shi

 

" Amaan." Amani tayi charaf ta rigashi fad'a sannan ta dora

 

"Nice hassana, shine husaini, na girme shi so nice babba."

  

Murmushi Iman tayi, so adorable yaran,

 

"Oya ku wuce kowa ya cire uniform dinsa kuzo muyi dinner, nasan Iman ta gama gajiya tana so ta huta"

 

Mamma tace tana mikewa

 

" Zayd, Ya Mubarak dinner na table."

 

" Ni sai nace gida gaskiya, I'm full."

 

Ya Mubarak yace yana gyara zama sosai. Kama hannun Iman Mamma tayi, suka wuce dining din tare da Zayd yana mata tambayoyi. Mommy na jinsu bata saka baki ba, dama kuma ita haka take da kara sosai, komai nasu Itace akai amma bata taba nuna musu iyaka akan nata, shiyasa suma duk wani abu da ya shafe ta toh sune a gaba gaba, sai ta koma gefe ta zama yar kallo. Bata da hayaniya kamar dai Iman koman ta a nutse takeyi musamman kuma abun da ya hadu da arziki sannan ga ilimi both boko da islamiyya. Kujera taja gefen Iman din da suka bar mata ta zauna daidai lokacin Amaan da Amaani suka dawo kowa ya sauya kayan sa zuwa na zaman gida. Amaani na kokarin fara surutun ta suka hada ido da Mommy, kallon da tayi mata kadai yasa taja bakin ta tayi shiru har suka gama babu wanda yayi magana.

   Falon suka dawo, a lokacin Ya Mubarak da Zayd suka yi musu sallama akan zasu dawo gobe kowa da family dinsa, har bakin mota Mommy ta rakasu ta dawo sai kawai ta wuce dakin ta, ta bar Mamma da yaran suna hira, ta lura da yadda Iman din ke jin kunya da rashin sabo amma kuma tasan wace Mamma ba zata taba barin ta ba har sai ta tabbata ta sake dasu, balle uwa uba iyayen magana su Amaani su kadai ma sun isheta.

   Kwanciya Mommy tayi farin cikin zuwan yarta na ratsa ta, wayar ta ta dauka ta kira number Abba, lokacin ya gama cin abinci kenan yana kokarin duba wasu papers dinsa a computer yaga kiran nata, tsaywa yayi da abinda yake yi ya daga.

 

"Nagode sosai IB, naga Iman fiye da yadda nayi tunanin ganin ta, hankali na ya kwanta dan na tabbatar da tarbiyyar ta, kayi ma maman tasu godiya dan Allah. "

 

" 'yaya amana ce a garemu da dole mu kula dasu da tarbiyyar su, domin dole ne Allah ya tambaye mu a ranar gobe kiyama, banyi komai ba face abinda ya zama wajibi na."

 

Ya fad'a yana jin chan kasa zuciyar sa da zata samu labarin abinda ya faru a zaman Iman din da Maman daku tabbas za'a iya samun matsala, abu daya ya hanata yin wani katabus akan maganar Iman din, tabbatar mata da yayi akan bata da matsalar komai, kuma tana hannu na gari.

    Sallama sukayi ta runtse idon ta, hasashen irin shirye shiryen bikin da zatayi kawai take, ba zata bari ta koma ba har sai tayi mata nata kalar gatan da zata tabbatar da ita din yar gata ce.

   Turo kofar akayi, ta daga kai ta kalli Iman din cikin rakiyar Mamma.

 

" Sai ki gudo ki bar mu? Gamu toh mun biyo ki."

 

" Na zata wajen Hajiya kuka yi ai."

 

" Munje chan din ma."

 

" Ok." Tace tana mikewa zaune.

 

" Bari na duba yaran chan, ina ga daga haka zan kwanta, sai da safe Iman."

 

Murmushi Iman tayi ta amsa sannan mummy tace

 

"Sai da safe Yaya."

 

Fita tayi ta ja musu kofa cike da farin cikin kwanan da ya da uwar zasuyi yau.

 

"Dawo kusa dani."

 

Dawowa tayi ta zauna daf da Mummy din, ta jawota ta dora kanta a saman cinyar ta, cikin tattausan lafazi tace

 

"Kin girma sosai Iman, nayi mamakin yadda kika kara chanjawa akan last da Dr. Ya tura min hoton ki, amma kuma naga baki da walwala sosai, ko rashin sabo ne? Ko kuma hakan halitta ne?"

 

Murmushi tayi me sauti, nutsuwa ta saukar mata, taji da gaske she's safe fiye da yadda ta taba ji a rayuwa ta, a hankali ta furta

 

"Babu komai Mummy."

 

"Shikenan, ki kwanta idan kika huta duk maganar da zamuyi sai muyi kinji?"

 

Ta shafa kanta tana murmushin. Daga kan ta tayi ta ajiye a saman gadon ta fita daga dakin. Wajen kayan ta, ta nufa ta ciro wayar ta, tasan ya mata magana a WhatsApp bata samu sukunin dubawa ba. Misscalls ta gani ta whatspp call sai messages dinsa da ya turo mata. Sakon ta fara dubawa ta,tabi kowanne tayi reply ta bar daya da yake tambayar ta size din undies dinta kunya na kamata. Godiyar kudin da ya bata tayi masa hade da addu'a tana turawa sai gashi yazo online, maimakon ya amsa sai taga yana kiranta, kasa dagawa tayi kunyar tambayar da yayi mata na dawo mata

 

_" Baby menene size din B da P?"_

 

Haka ya rubuto mata fa, kin dagawa tayi har ta katse ya sake kira ta kara bari ta katse,

 

_" Please dan Allah ki daga, kwana nawa banji muryarki ba? Sam na manta zan iya kiran ki ta whatspp call sai daxu, please ki taimaka ki daga inaso naji muryar ki wallahi."_

 

_" Ni dai muyi chatting."_

 

_" Ni dai ki daga, zan sake kira. "_

 

Kafin tayi reply sai ga kiran sa, ta daga da k'yar tanayin nesa da wayar. Ajiyar zuciya ya sauke da karfi

 

" Kin iya rigima wallahi, haka kawai sai anyi punishing dina ko? "

 

" Um um. "

 

"Toh naji, ya hanya? Ya me ya faru?"

 

Cikin zumudi tace

 

" Ina cikin farin ciki yau, komai ya tafi yadda ya kamata, kowa so na yake kamar zai goya ni. "

 

"Mum fa? "

 

" She's just like me, kamar ni take har I don't care attitude dinta, amma deep down she's super happy, na gani a idon ta. "

 

Dariya ya saka

 

" Alhamdulillah, nayi miki murna sosai sosai, Alhamdulillah. "

 

" Nagode sosai. "

 

" Yau kwana zakuyi nasan da Mum kuna magana. "

 

" Anya? Kila ko sai an kwana biyu. "

 

" Bari ki gani dai. "

 

" Uhum tohm shikenan. "

 

" Baki min replying dayan chat din ba, abinda na tambaye ki. "

 

Dauke wuta tayi gaba daya kamar bata ji ba, ya sake maimaitawa yana rik'e dariyar sa, ya gano kunya taji tunda taki daga wayar sa, bata san halin sa ba lallai, rage murya yayi sosai yace

 

" Dan Allah ki fad'a min Aunty zata yi min fad'a gobe idan nace ban tambaye ki ba, dan Allah. " Shiru tayi masa

 

" Please ki fad'a min, ko da yake ma zan iya chanka ai, bari muga... zasu kai size..."

 

" Innalillahi. " Tace tana zare wayar gaba daya ta kashe ta. Tuntsurewa yayi da dariya kamar zai fado daga gado, yayi saurin komawa chat din ya hau rubuta mata

 

"Sorry matar Muhammad, daga wasa sai ki yanke min waya? Toh ai ban gama jin muryar ki ba wallahi."

 

Tick daya ya gani alamar ta ma kashe datan gaba daya, gwada kiran ta yayi aikuwa yaji switch off.

 

Tsaki taja ta wurgar da wayar , ta rasa me yasa me maxa sam basu da ta ido, zata dade kuwa bata yi waya dashi ba. Samun kanta tayi da yin murmushi sai kuma ta hade fuska ta sake jan tsaki. Ya ma bata haushi gaba daya.

 

Har ta gama shiryawa ta jona wayar a charge amma bata kunna ba har lokacin Mum din bata shigo ba, gefen gadon ta kwanta cikin lallausan zanin gadon da yake kamshi sak irin kamshin da mummy din take, tana rufe idon ta, ta shigo rik'e da cup a hannun ta.

 

" Iman, kinyi bacci?"

 

" A ah." Tace tana mikewa zaune

 

" Yawwa ungo karbi kisha, fresh milk ce nayi miki warming dinta."

 

Karba tayi, tayi godiya ta kafa kai ta shanye tas, ta tashi da cup din rik'e a hannun ta

 

" Ajiye shi anan zan kira azo a fita dashi."

 

A saman fridge din jikin kofar ta ajiye ta dawo ta zauna tana so abinda tasha ya dan yi settling a cikin ta.

 

"Zo ki tayani duba wannan kayan."

 

Tayi maganar tana bud'e profile dinsu a cikin system din, gefenta Iman ta zauna suka hau duba wasu jewelries, duk wanda Iman din tace yayi kyau sai tayi starring dinsu, sai da suka gama tsaf sannan suka dawo kan wanda akayi starring din suka sake fidda guda biyar masu kyau sosai, biyu gold biyu azurfa sai daya fashion ne daga wani babban company, a take mummy tayi payment din da komai sannan tace Iman din taje ta kwanta zata karasa wani aiki.  

    Tana kwanciya bacci ya dauke ta  dama ta gama kurewa sosai tana lura da Mummy din bata so ta matsa daga kusa da ita ne. Cikin bacci tayi juyi ta jita a bayan ta, daga nan bata sake farkawa ba sai da aka kira sallah.

 

***Gaba yayo ya bar su a chan su karasa siyayyar abinda zasu siya dan yaga abin nasu bana kare bane, a Kano ya dira domin su karasa abinda zasu karasa da Bashir saboda yadda lokacin yazo sosai. A gidan sa ya same shi, suka jira Musaddik ya karaso suka fita zuwa wata unguwa da tafi kama da a kirata da unguwar talakawa kai tsaye, tunda suka shigo layin Moh ya tabbatar da zai samu yadda yake so, lallai Musaddik mugu ne na gaske, idan ba haka ba ya rasa unguwar da zai samo ya siya gida sai irin wannan unguwar. A daidai wani kofar gida karamin gaske suka tsaya, suka fito a tare wanda zasu gani yana tsaye yana jiran su, yana ganin su ya karaso bakin sa cike da murna ya gaishe su, sannan ya bud'e musu gidan yace su shigo.

   Siminti ne gaba daya tsakar gidan sabo yana ta kamshi, bashi da girma tsakar gidan sosai dan be fi yaci tabarma days da rabi ba, a gefe yar karamar rijiya ce saboda rashin ruwan unguwar.

   Dakunan guda biyu da suka kasance falle-falle ya bud'e musu suka shiga nan ma ko ina an masa fenti yana ta kamshi, babu abinda ba'a saka ba hatta karamin gado da kujeru an saka,da yar karamar tv babu batun fridge ko cooker gas balle azo maganar su AC da sauran kayan more rayuwa, kitchen din babu komai dama sunyi da nufin daga gida sai a kawo mata kayan kitchen suyi amfani dashi. Kitchen din karamin gaske ne dan mutum biyu ba zasu iya aiki a ciki ba saboda kankantar sa, balle a samu sukunin cika shi da kaya.

   Fitowa sukayi ya rufe gidan yana sake washe baki

 

"Ranka ya dade gidan yayi ko?"

 

"Yayi sosai yadda nake so, sai ka sanar musu ba sai an kawo kayan gida ba ,iya kitchen ya isa shima karsu matsawa kansu duk abinda babu zaka saka musu."

 

"An gama ranka ya dade, sai maganar lefe."

 

"Ana gobe daurin aure za'a kai, an gama hada komai ina tunani."

 

" Nagode Allah ya kara arziki."

 

Be amsa ba, yayi gaba ya fad'a motar yana kallon tsarin gidan, murmushi ne ya kwace masa, ya girgiza kansa yana ayyana yadda zuciyar Mama zata buga ko kuma ta kusan bugawa,yayi alkawarin shayar da ita mamaki irin wanda bata taba tunani ko hasashe ba.

 

  Kai tsaye wajen gym suka wuce, ya kwana biyu be motsa jikin sa ba, yana bukatar hakan saboda tafiyar da sukayi be samu lokaci ba. Dariyar shakiyanci Musaddik ya dinga yi masa, ya tsaya daga abinda yake yana hararar sa

 

"wai dariyar menene haka? Uhum?"

 

" Naga yadda ka dage kake ta faman daga karafu nan nan ne wallahi, kar dai ka illata musu yarinya wallahi, kasan dai kai din tsohon tuzuru ne da yaki auruwa. "

 

Robar ruwan da ya gama sha ya jefe shi dashi, ya goce ta fadi kasa yana sake tuntsurewa

 

" Ka kiyaye ni wallahi. "

 

" Anki din, daga fadar gaskiya?"

 

" Zan kamaka ne, naga kafarka a gida na wallahi. "

 

" Gidanmu dai. "

 

Towel ya ja ya goge gumin fuskar sa, ya biye wa Musaddik zai dauke hankalin sa ne ga abinda yake shirin yi. Wayar sa ya dauka akan dan table din wajen yayi dialing number ta, sai da ta kusan katsewa sannan ta daga.

 

 

"Huh!" Ya furzar da iska yana jan numfashin

 

"Ranki ya dade an gama jamin ajin ne?"

 

"Ina wuni?" Ta kautar da maganar ta hanyar gaishe shi

 

"Lafiya lou, ya gida ya kowa da kowa?"

 

"Alhamdulillah."

 

"Masha ALLAH, yaushe Abba yace zaki dawo?"

 

"Be fad'a ba, amma naji Mummy tace ba zan dawo ba sai ranar."

 

"Ranar? Yaushe kenan?"

 

" Ka cika tsokana wallahi, nima ban sani ba."

 

"Ke kuma kin cika kunya ba, sai kici sai ranar auren mu kawai."

 

" Allah zan kashe wayar." Ta fad'a tana turo baki, dariya yayi yace da sauri

 

" Allah ya baki hakuri Matata."

 

Shiru tayi tana wasa da album din hotunan da Mamma ta bata bayan ta mata bayanin kowa da yake jiki.

 

"In sha Allah ana gobe za'a kai lefe, kinsan sha'anin rayuwar, Allah yasa be makara ba."

 

" Be makara ba, Allah ya saka musu albarka."

 

"Amin Matata, nagode sosai da bani dama da kikayi, in sha Allah ba zaki yi Dana sani ba."

 

"Kullum godiya? Ni me nayi?"

 

"Ai wai kinga dai yanayin yadda abubuwan suke."

 

"Babu komai Allah ya tabbatar mana da alkhairi."

 

"Amin Amin amarya ta."

 

Yar karamar dariya tayi, shima ya tayata kafin suyi sallama. Mamma ce ta shigo dakin rik'e da jaka babba, sai me aikin gidan dake biye da ita da wasu kayan suma da yawa, ajiye su sukayi a gefe me aikin ta fita kafin ta sake dawowa ciki dauke da tray da aka doro chicken pepper soup da wani cup shima cike da abu kamar kunu, sai wani da akayi ma hadin fruits aka saka madara. Dora shi tayi a saman drawer ta fita ta barsu.

    Da hannu Mamma tayi mata alamar ta taso, ta taso ta zauna a k'asa in da Mamma din ta nuna mata, tray din ta sakko mata dashi tace maza ta cinye naman tas, idan ta gama akwai bakuwar da zata shigo wajenta, Itace me jakar chan. Tun zuwan ta gidan take faman shan abubuwa, a dan lokacin tayi masifar chanjawa, tayi kara fari da kiba jikinta ya sake murjewa sosai. Ita kanta tana jin da gaske ta kai mace, tana jin zata iya karawa da ko ma wace amma a dah, bata da wannan confidence din.

   Bata kyuwar cin duk abinda aka bata dan da bata samu wanda zai dubeta ba balle har ya bata abinda yasan zai amfane ta. Shiyasa ta bada himma take yin duk abinda za'a sata.

 

***A bangaren gidan su Iman kuwa, bayan dawowar Abba sai da suka sake wani rikicin da Mama, wanda ya saka kowa ji har aka dinga ganin baiken Maman, amma kishi ya rufe mata ido matar Abba Musa na zugata tayi masa tijara son ranta, be kula ta ba don a yanzu baya sakata cikin jerin masu hankali, yana mata uzurin kishi ne ya sakata yin wasu abubuwan. Bayan kamar kwana biyu da dawowar sa ta same shi har daki ta bashi hakuri abinda ya bashi mamaki sosai, hakura yayi ya sakko amma ba wai don ya hakura da maganar Iman ba, yana nan sai ya yi mata hukunci daida abinda ta aikatawa yar sa.

   Shirye shirye ya kankama sosai, mama babu zama kullum tana hanyar kasuwa tun da ta samu labarin cewa Bashir yace iya kitchen kawai zasuyi, hakan yayi mata dadi shine ta maida hankalinta sosai wajen kawata kitchen din dan ta tabbata gidan ba karamin gida bane, dole ne su fita kunya ta hanyar hada mata kitchen din yayi sosai.

   Duk abinda ta tambaya Abba bata yake dan baya son wata doguwar magana, hankalin sa gaba daya yana kan maganar auren Iman, da yadda daurin auren zai kasance domin yasan za'a yi taro ne irin wanda ba'a taba yi ba, manyan mutane zasu halarta da yan siyasa da manyan sarakunan k'asar nan da ma na ketare. Duk abin nan Mama bata san komai akai ba, bata taba tambayar shi game da Iman din ba ko yadda nata tsarin yake, shiyasa kawai shima ya rufe ta ruf ya barta da abinda take yi.

   A yadda tsarin bikin yake, alhamis za'a yi kamu, juma'a a daura aure sai asabar dinner kamar yadda Zeenat din suka zauna suka tsara ita da Bashir bayan ya sanarwa Moh da tsarin ya kuma bashi go ahead.

  Tsarin bikin da su kuma chan masarauta suke shirya wa biki ne gagarumi za'a yi a Kano da Adamawa, kowanne kuma kwanaki za'a dauka anayi tun daga asabar din washegarin bikin, na Kano za'a fara kafin a koma adamawa in da za'a kai amarya.

   Kamar yadda yake a tsari, ranar alhamis za'a karbi lefe, lefen Zeenat da Iman, wanda Mama tayi gayya, gayya irin ta ban mamaki, tana Kuma sanarwa mutane suzo suga lfen Zeenat dan ta tabbatar za'a ga kayan da baa taba gani ba.

  Yan uwa da abokkan arzikin Mama su suka cika gidan, aka shirya kaya na mamaki, aka gyara gidan. Wata sister Mama ce tazo ta sameta tana zaune cikin kawayenta ana shewa, ta jata gefe hankali a tashe tace

 

"Yaya, wani labari naji fa, dangin mijinki na hirar basu san Ina wajen ba, naji suna cewa Iman tayi goshi ta samo jinin sarauta, ana ma tunanin dan sarki ne duk da Basu tabbatar ba ana boye zancen ne amma kamar hakan ne."

 

Wata irin dariya Maman ta saka, har da hawaye

 

" Kinji ki Fatima da wani zance, su fa basu san kan zancen ba, maganar Zeenat ake ba Iman ba, na ji wannan zancen tun bayan zu ba ai, kawai na kyale mutane ne yadda abun zai kada su, ba dai anjima kadan zasu iso ba? Zamu gani ai."

 

" Allah yaya? Kin Kuma tabbatar da hakan ne?"

 

" Zaki gani ai."

 

Tayi gaba tana murmushin mugunta, ba karamar kunya tasan za'a sha ba a lefen Iman din ba.

 

 

Hmmm

 

 

 

 

 

 

***Assalamu alaikum sisters fatan alkhairi ga kowa da kowa. In Sha Allah hutun mu zai kama asabar da lahadi, domin kowa ya samu damar aiwatar da wani abu me muhimmanci a rayuwar sa, sannan mu kula da gidajen mu da iyalan mu dukka, mu bawa yaranmu da mazajenmu lokacin da suke bukata daga garemu. In Sha Allah Monday to Friday za'a samu posting in sha Allah, sai dai wani uzurin ya gifta. Sannan masu korafin ba'a basu page biyu ko uku a rana, wani page dayan yayi wasu pages din guda biyu, so idan hakan ne gwara dayan me tsawo mu tafi a hankali har Allah ya bamu ikon kammalawa.

  Zafafa biyar na godiya da zabin su da kuke a kowanne lokaci, dan Allah mu cigaba da yi ma juna uzuri kuma mu kyautata lafazi a tsakanin mu domin magana me kyau ma sadaka ce.

 

 

Masu sharing novels group group una weldone kunji? Dan Allah ku daina babu kyau, ka sowa dan uwan ka abinda kake sowa kanka hakan na cikin cikar imanin mumini.

 

Rano

1/18/22, 19:58 - Buhainat: Halin Girma

    14

 

 

_*Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

 

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾*

 

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

 

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾*

 

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

 

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

 

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

 

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

 

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

 

_________________________

 

*_MACE SAI DA GYARA_*💃🏻💃🏻

_GYARAN MA NA KAMFANIN TURAREN:_

    *YERWA INCENSE AND MORE*

 

*Ƴar uwa ta hanyar gyara ne kawai zaki cigaba da amsa sunanki mace hamshaƙiya a wajen miji ba tare da ya ga kin tsufa masa ba.*

 

_Maza garzayo ki gyara jikinki da kayan ƙawatattu kuma nagartattu irin namu na gida da suka sami haɗi na musamman da babu cutarwa a ciki. hadin bornu/chadian na kamfanin turaren YERWA INCENSE AND MORE_

 

*_Muna da haÉ—in_*

 

_Turaren wuta kala kala na gidah_

_khumrahs_

_Kullaccham_

_Turaren wanka_

_Turaren Kaya_

_Turaren wanki_

_turaren mopping_

_Dukkanil al’ajab (Turaren tsugunno na Matan aure kad’ai)_

_khumratul al’ajab (khumrah ta jiki ta matan aure_

 

_Muna Gyaran jiki_

_Na amare_

_Da masu jego_

_Da sabulai masu gyara fata_

_Turaren tsugunno_

_zumar goran tula_

_Scented hair cream and spray (man kamshin gashi da gyara gashi_

 

_Akwaisu kujeran tsugunno

_Dilke and halwa set_

_Burners da igniters da tong_

_turaren fesawa dana ruwa._

_wardrobe balls_

_scented pebbles_

_cotton wooly oudi incense_

_kabbasas_

 

_Da sauran kayayyaki da yawa da bamu ambata ba_

 

_Akwai ragi na musanman ga yan zafafa fans❤️_

 

_Muna bada sari, Ko sayi ‘dai ‘dai akan farashi mai sauƙi da rahusa. Ga mai buƙata sai ya nememu tanan 👇🏼_*

 

_EMAIL:yerwaincenseandmore@gmail.com ko INSTAGRAM PAGE d’inmu:yerwaincense_and_more dama nambR mu:08095215215_

 

_MUNA TURAWA KAYAN MU KO’INA A FADIN NIJERIYA DAMA KASASHEN KETARE.

100% TESTED AND TRUSTED_

 

•••••••••�

 

 

 

*****

Azahar sosai ya tashi, ya mike yana salati, daga curtains din dakin yayi yana mamakin tsawon lokacin da ya dauka yana baccin, wayar sa dake saman gadon ya dawo ya dauka ya bud'e ta, misscalls ya gani ya duba sannan ya ajiye ya fito zuwa falo in da yatar da abincin sa a jere cikin manyan warmers sai kuma wani dan basket da aka rufe shi da jan kyalle me kyau dake dauke da hoton heart, matsawa yayi gabansa yana kallo,

 

"Menene wannan?" Yayi maganar yana rik'e kugun sa da sauri wani bafade ya shigo, ya rissina yace

 

"Sako ne daga shashen Kilishi, inji gimbiya Laila."

 

"Laila?" Ya furta cike da mamaki

 

"Yaushe ta zo?"

 

"Tun da safe, lokacin baka nan."

 

"Dauke shi a kai sashen Ammi, ace ta ajiye."

 

Sake dukawa yayi cikin girmamawa yace

 

"An gama ranka ya dade."

 

Juyawa yayi ya koma ciki, yayi wanka sannan ya shirya yana tunanin dawowar Laila a irin wannan lokacin da yasan suna tsakiyar karatu ne. Fitowa yayi ya tsattsakuri abincin ya fita wajen ammi dan be samu ganin ta da safe ba.

 

A gabanta ya tarar da sakon nasa, ta bishi da kallo sannan ta kalli kwandon da yake na Kaba. Sai da ya zauna ya gaishe ta sannan ya saka aka miko masa basket din

 

"Ammi kinga ko? Menene ma'anar haka?"

 

"Ni kaina nayi mamaki, amma kuma kasan dama hakan zata faru idan har ta samu labarin auren ka."

 

" Bana son wata matsala gaskiya, zan aika da sako wajen Kilishin dan ba zan dauki rainin hankali ba."

 

" Ka rabu dasu, karka yarda su bata maka rai har kayi tunanin biye musu, ka cigaba da addu'a nima kuma ina tayaka mahaifin ka ma,.ba zasu taba samun nasarar abinda suke so ba."

 

" Shikenan Ammi, dan Allah aje a kona basket din nan dan bana son ko ganin sa."

 

" Shikenan, ka cigaba da walwalar ka karka yarda makiyinka ya gane weakness dinka."

 

" In Sha Allah Ammi."

 

" Allah yayi maka albarka."

 

" Amin." Ya amsa yana jin tamkar dawowar Laila akwai wani babban dalili

 

" Yawwa na kira Fatima akan lefen ka, zata hada komai in sha Allah, idan yaso sai su tafi ita da kai da wata dai cikin su, Takawa ma yace shi zaiyi komai, amma duk da haka Fulani tace yayi nasa itama zatayi nata mu ma nan sai muyi namu."

 

"Wayyo ni dan gata." Yace yana murmushi

 

"Ammi gatan kar yayi min yawa ai."

 

"Ba zai ba, Allah yasa ayi damu kawai, amma dole sirikata taga gata."

 

"Uhm.. Allah sa idan tazo karta kwace min wajena."

 

" Dole ne ai, kasan dai yadda nake son ya mace ko?"

 

" Shikenan sunana sorry wallahi."

 

Dariya Ammi ta saka

 

" Aikam ka shirya tun yanzu."

 

" Shikenan, Muhammad kana ji? Kayi hakuri da duk abinda zaka gani."

 

Ya fad'a cikin yanayin kalar tausayi, dariya sosai ya bawa Ammi tayi sosai, kallon ta ya dinga yi cikin tsantsar son ta, yana son Ammi da duk wasu halayenta, babu abinda yake so irin yaga tana farin ciki sosai, hakan yake sashi jin zai iya komai dan ganin ya faranta mata, ya dawwamar da farin ciki a kan fsukar ta, hakan kuma ba zai yiwu ba sai dole yaki karbar muradin Bubu, dole ya hakura da mulkin ko da yana so, saboda farin cikin Ammin Sa!

 

***Satin Mama daya cif a Katsina, ranar da zasu dawo ranar Bashir ya iske su a chan da dalleliyar mota da sha tara ta arziki, murna wajen Mama da Zeenat ba'a magana aka dinga turashi gida gida na dangi dan aga irin mijin da zeenatun ta samo, aikuwa nan da nan magana ta karade ko ina cikin family din Maman, anan wasu da yawa suka samu labarin bikin Zeenat din wanda aka saka wata daya kachal bayan Bashir din ya tabbatar musu da zaiyi komai basa bukatar komai hatta da kayan gida duk shi zai zuba, hakan ya sake fasawa Mama kai ta dinga hura hanci a lallai zeenatun ta ta dallo miji na kere sa'a, tausayi da farin cikin halin da ta tabbata Iman zata shiga idan har ta auri fakirin nan take, gashi dai su kam Allah yayi musu gam da katar dan yadda aka dinga maganar Bashir din a dangi kadai ya ishi Mama tutiya da alfahari.

   A motar ya kwaso su Zeenat na gaba gida na tashi cikin taken soyayya Mama da Marwan na baya har Kano, Zeenat ji take kamar tafi kowa sa'a a duniya dan da gaske take jin wani irin son Bashir din na ratsa ta.

   Sanda suka isa gida magriba tayi saboda basu taho da wuri ba yana faman zaga dangi, alwala aka kawo masa ruwa yayi, ya zauna Zeenat din ta shiga ta fito suka dasa sabuwar hira irin ta yaushe rabo. Cikin hirar ne yake fad'a mata lefe in sha Allah za'a kawo cikin upper week, zai sanar mata da ranar sai ta fadawa Mama, hakan yayi mata dadi har tana hasashen uban kayan da za'a kawo mata dan taga Bashir din me bajin ta ne sosai.

  Ranta fes ta koma ciki bayan ya tafi, ta labartawa Maman lokacin Matar Abba Musa ta shigo wajen Maman yi mata sannu da zuwa.

 

"Haba ni nayi mamakin da aka ce manyan mutane ne suka zo neman aure gidan nan na tabbata dama wajen Zeenat ne, yarinya kakarki ta yanke saka wallahi."

 

Tace tana dariya, murmushi mama tayi

 

" Kice manyan mutane ne suka zo? Bani labari Binta."

 

" Ai Maman Habib baki gani ba, wallahi manyan mutane ne kamar ma daga wata babbar masarauta, yadda naga mazan gidan nan sun rikice kadai zaka gane ba kananun mutane bane, na zata ma na Iman ne ashe na Zeenatu ne, Baban Walid be min bayanin da zan gane ba kinsan wajen lokaci daya suka zo dukka."

 

" Aikuwa sune, kai kice dai manyan mutane ne, masarauta fa? Kai masha ALLAH abu yayi kyau wallahi."

 

" Ai Maman Habib ba karamin dace Zeenat tayi ba wallahi, Allah dai ya kaimu bikin nasan za'a ga lefe na ban mamaki."

 

" Bari kawaii, sai muzo mu tanadi kyautar girma da zamu fita kunya, na gode da kika sanar dani dan Dr ba lallai ya fad'a min ba muna yar tsama dashi."

 

" Ai haka suke, basa fadar cikin su wallahi, itama kuma Gajin ba zaka ji daga bakin ta ba tunda komai suna fad'a mata ai."

 

Tabe baki Mama tayi

 

" Ai ni baki sani ba, so akayi a yi min bakin ciki."

 

Sai ta rage murya

 

" So akayi fa a hana Zeenat auren Bashir din nan, kuma ina kyautata zaton akwai saka hannun Gajin a ciki, toh in ba haka ba yadda Dr ya rikice akan maganar lokaci daya zaki gane zugashi akayi."

 

Kama baki Matar Abba Musa tayi

 

" Allah? Tab ashe an so yi miki tsakiyar da ba ruwa."

 

" Ke dai bari, shiyasa na tsaya kai da fata, kinsan mutane basa son ka cigaba ko aga danka ya cigaba ko zai huta."

 

" Zahiri, toh Allah ya kyauta, ban yi zaton hakan daga gareta ba."

 

" Ai ba laifin ta bane, itama yadda aka dora ta haka zata tafi akai."

 

" Eh kuma gaskiya, tunda kinga ai bata cika saka ido akan al'amuran mu ba."

 

" Shine, koma waye kansa yayi wa, aure kam babu fashi."

 

" Assalamu alaikum."

 

 Iman tayi sallama ta shigo, gimtse fuska Maman tayi,ta gaishe su matar Abba musa ta amsa a sake tana tsokanar ta da amarya amarya, murmushin yake kawai tayi tana satar kallon yanayin fsukar Maman, zuwa tayi ta fad'a mata anjima zata tafi wajen dangin Mamanta amma ganin Matar Abba Musa ya saka ta fasa ta wuce kawai daki ta karasa hade koman ta waje daya.

  Bayan tafiyar Matar Abba Musa ne ta fito ta samu Maman a kitchen tana rarrabe kayan da tazo dasu dangin su kuka kubewa da daddawa waje daya

 

"Mama dama yau zan tafi gidan su Mamana."

 

Tsayawa da abinda tayi, tayi ta kalle ta a mamakance tace

 

"Yau? Yaushe aka yanke  maganar tafiyar taki ban sani?"

 

"Dama tun ranar da na dawo daga gidan Ya Maryam Abba yayi min maganar."

 

"Toh! Shi zai kaiki kenan? Ko turowa za'a yi kije? Ko da yake mutanen da basu damu dake ba yaushe zasu turo? Wannan din ma nasan dan Dr yayi magana ne."

 

"A ah tare da Abban zamu je."

 

"Kutmar Uba!" Da sauri Iman din ta ja baya dan yadda ta ga Maman ta birkice lokaci daya

 

" Ni za'a yiwa munafurci? Wato yace zai ganki saboda yaga tsohuwar matar sa ko? Dan an raina min wayo an maida ni wata sakarai. "

 

" Dama... "

 

" Dallah rufe min baki, wato gani shashasha an dauko raino an bani shine yanzu za'a nuna min bariki ko? Toh wallahi ba zata sabu ba wallahi kinji na rantse, ko ya barki ki tafi ke kadai ko ya hada ki da wani cikin yan uwansa ko Hafiz ne ma. "

 

Shiru Iman tayi kamar ruwa ya cinye ta, tana jin sababin da Maman take kanta na kasa ita dai bata ce komai ba,me zata ce ma?

 

" Bari yazo naji abinda yasa zai munafurce ni wallahi, bayan duk kokaarin da nayi wajen rik'e ki amma sam yanzu baya gani, dan kawai yar matsala ta ratsa tsakanin mu shikenan sai ya rufe ni. "

 

" Uwata zo ki wuce, kije waje kina da bako. " Abba da yazo a lokacin yace yana kallon Maman, sum sum Iman ta fice kafin Abban ya dubi Maman cikin bacin rai yace

 

" Kin bani mamaki Hajara, ban zaci haka daga gareki ba."

 

" Dama ai haka ne, duk abinda mutum yayi ba gani za'a yi ba musamman aka ce da ba naka bane, amma ai Allah ya gani. "

 

" Bakya tsoron Allah kuwa in dai haka ne, har kece zaki ce Allah yana gani? Kina tsoron haduwar ku kuwa? Bayan wahalar da kika bawa yarinyar nan har kina da bakin magana? "

 

" Wahala? Ita tace maka na bata wahala kenan ? Oh shine ka shirya zaka kaita wajen uwarta kenan bayan na gama cin wahalar ta, duk abinda nayi baka gani ba. "

 

" Kiki tsoron Allah, na gano duk irin rikon da kika yi wa Ummi, kinci amanata kin ha'ince ni, Ashe ke din fuska biyu ce dake ban taba sani ba."

 

" Da yake yanzu hankalin ka ya koma wajen tsohuwar matar ko, ko nace tsohuwar karu... "

 

 A wani irin bacin rai ya daga hannu zai Kai mata mari, fasawa yayi yaji kamar an rik'e  hannun zuciyar sa na tafasa, ba ya cikin mazan da zasu daki matar su,baya kuma fatan hakan duk da irin yadda Maman ta bata mishi rai.

 

"Dukana zakayi Ibrahim? Dukana? Akan na fadi gaskiya, waya san auren da kukayi na gaske ne ko kuwa? Tunda mu dai babu wanda ya shaida, shine zaka dauki hannu ka dake ni akanta ko?"

 

Ji yayi kansa yana sarawa, be taba tunanin tashin hankalin mAman ya kai haka ba, juyawa yayi da nufin barin kitchen din amma sai yaji ta rik'e masa riga ta baya

 

"Wallahi ba zaka je wajen ta ba, wallahi ba zan yarda ba."

 

Tsoro ne ya kamashi jin ta daga murya sosai, da sauri ya fizge rigar sa ya daga kafarsa wajen ficewa daga gidan ma gaba daya, ba zai biye mata ba, har a jisu a gidan abinda zai zamar masa abun kunya a wajen yan uwan sa .

  Shashen Gaji ya wuce da ya hango Iman tsaye da Musaddik a chan wajen gate din. Sako ya kawo mata daga Muhammad ya juya ita kuma ta koma cikin gidan.

  Tana shiga Mama dake tsaye a falo tana huci ta fisgota, saura kad'an ta fadi amma ta tsaya akan kafarta, kallon Maman take a tsorace dan bata dauka abin nata ya kai haka ba

 

"Zan ga uban da ya isa ya fita daga gidan nan wallahi, wato kece munafukar kina so ki hada uwarki da ubanki ko? Toh wallahi baki isa ba na gama cin wahalar ki."

 

Matsawa baya tayi ganin kamar dukanta Maman zatayi, kamar daga sama sai ga Habib kaamr an jeho shi, yayi saurin shiga tsakani yana wa Maman magana,

 

" Lafiya Mama? Me tayi?"

 

Bata jira amsar Maman ba ta yi saurin ficewa.

   Abinda Abba ya guda sai da ya faru, magana har gaban gaji, mama ta dage ba zai tafi ba shi kuma yace bata isa ta hana shi ba, haka sukayi ta kai ruwa rana karshe ya je da kansa ya dauko kayan Iman din ya bawa Habib ya saka masa a mota sannan suka tafi tana kallo ta cigaba da haukanta.

 

 

 

***Jingina tayi ta rufe idonta a lokacin da suka shiga jirgin, karon ta na farko kenan shiyasa take jin tsoro tsoro amma ta dake dan da wuya kaga abinda zai sa kaga weakness dinta, rashin tsaron da ake fama dashi a k'asar ya saka Affan yi musu booking flight kawai zuwa Abujan dan ba zai yi risking tafiya da Iman din a hanya irin wannan ba. Lokacin ma da Moh yaji labarin tafiyar tata sai da yaji tsoro Allah yasa ba a mota zasu ba, dan har ya gama shirya yadda zai siya musu ticket din kawai ya aikawa abba amma kuma baya so a san shine sai kuma tace masa a jirgin zasu, hakan ya saka shi samun relief. Tafiyar su Dubai ya saka basa waya sai dai chatting dan kar tayi saurin gano shi. Da zata tafi ya saka Musaddik kai mata dubu biyar a cikin envelope, sai da ya jinjina kudin kafin ya aika, kyautar sa ta farko kenan amma sai yake jin kunyar kai mata, tana bukatar manya manyan abubuwa a wajen sa amma akwai sauran lokaci.

   Tunawa da tayi da envelope din ya sakata cirota a cikin handbag dinta ta bud'e, murmushi tayi ganin kudi ne sai wani dan karamin note an rubuta I love you da shape din heart a k'asa. Sosai taji dadin kyautar tayi ta kallon note din tana jin dadi sosai.

   Cigaba da rikewa tayi a hannun ta har zuwa sanda zasu sauka sannan ta maida cikin handbag dinta tana jin wani irin feeling, she's nervous bata san wanne irin tarba zata samu ba. Tana ganin sanda Abba ya dauko waya bayan sun sauka yayi kira.

 

"Mun sauka." Taji yace sai kuma yave

 

"Owk tura min number shi."

 

Suna tsaye ya sake duba wayar, number aka turo ta text message ya ciro ta ya kira ya fad'a masa yadda zai gane su kafin ya kashe yana cewa

 

"Ummi muje gashi chan ma."

 

Matse jakar hannun ta tayi, taja akwatin ta zuwa wajen wanda yake nufo su.

 

"Welcome Sir."

 

 Yace cikin girmamawa, ba bahaushe bane jikin sa sanye da wasu uniform navy blue an saka number 5 a daidai aljihun.

 

"Thank you."

 

Karbar kayan su yayi ya zuba a booth sannan ya budewa Abba gaban motar ya zauna ita kuma Iman ya bud'e mata baya sannan ya jasu suka fita daga airport din.  A daidai wani hotel suka tsaya Abba ya juyo bayan ya kalli Iman yace

 

"Zanzo da safe in sha Allah, ki gaishe su, idan kina bukatar wani abu ki kirani."

 

"In Sha Allah Abba, Nagode sai da safe."

 

"Allah ya kaimu." Ya fice ya rufo kofar ya tsaya daga gefe yana kallo suka bar wajen.

 

   Ta cikin dark tinted glass din motar Iman take karewa garin kallo tana admiring ko ina musamman da dama magriba ta kawo kai dan wasu masallatan suna kokarin fara kiran sallah.

    A wani babban gida cikin jerin gidajen Babbar unguwar nan ta Maitama yayi horn, a hankali gate din ya shiga zugewa har ya karasa budewa gaba daya. A gefe daya yayi parking kafin ya gama daidaitawa wasu mata su uku da wasu maza biyu suka fito ta wata kofa suka nufo su dukkansu fuskar su dauke da farin ciki mara misaltuwa.

1 comment for "HALIN GIRMA 11-15"

  1. As a result, it's played by superior gamers or these with extra bankrolls. These bonuses permit you to play free of charge with out risking your own cash. With these bonuses, have the ability to|you probably can} play free of charge with out risking your own cash. It is crucial to read the casino’s phrases and conditions fastidiously for a specific 1xbet korean bonus to grasp the wagering requirement. They are typically divided into two distinct sorts; Free Spins or a free sum of money. For every spin, the dual reels can broaden to turn into three, 4 or even five-doubled reels.

    ReplyDelete