Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

AZIZA DA AZIMA 31-40

 


*PAID.*

🅿️==3️⃣1️⃣↪️3️⃣2️⃣

Sarki Chubaɗo cikin fushi ya kalli mutanen da suke wajan ya ce.

"Amma wallahi kun bani mamaki! Kuma kunji kunya! Yanzu akwai masifar da zata samu Magaji wanda har zai sa ku juya masa baya? Idan har ku wa inda ku ka zo bayan shekara ashirin baku san gwagwarmayen da Magaji ya yi ba, to ku wa inda ku ka zo kafin bayan shekara ashirin zaku ce kun manta da wannan halaccin ne? Dayawanku a nan wasunku basu da dangi kaff Banju ya kashesu!

dabadin Magaji ba babu ko da ƙwaro da zai rage a wannan yankin!!" Sarki Chubado ya karasa da tsawa idonsa jajur dan ransa ya b'aci matuka

"A ce ina sarkin fulanin yankin kwana amma Jauro ya ja ku ba tare da sanina ba ku zo yiwa Magaji rashin mutunci da dibar albarka! Jauro ne sarkinku!! Na ce Jauroo neee sarkinkuuu!!!?" shuru jama'a suka yi masu zare ido da masu tsilli-tsilli da ido suna yi, Mai Unguwar yankin kwana bayan Sarkin fulanin kwana Chubaɗo ya dasa ayar tasa shima ya karbe da cewa

"Jauro dai mai maganin yankin kwana ne kamar yadda ku ka sani, amma a da kun san waye GARKUWAN YANKIN KWANA KAFIN A ƊORA GARKUWA NA YANZU!! TO GA SHI NAN SHINE DAI! *MAGAJI BAWA!!* kafin ya sauke duk wata baiwa tasa ya binne bayan yasha wahalan kama aljanu da mayu ya kullesu!! Ya sauka ne a kan matsayinsa da yake da shi bayan ya kashe Banju! Amma har kwanan gobe! kai ba ma kwanan gobe kawai ba! HAR GABAN ABADA BABU WANI GARKUWAN FULANIN YANKIN KWANA SAMA DA MAGAJI! SANNAN BABU WANI MAI MAGANI SAMA DA MAGAJI! Har ta Garkuwan fulanin yankin kwana na yanzu da Magaji yake tunkaho"



    Garkuwan fulanin kwana na yanzu ya fito ya ce

"Tabbas hakane, da taimakon Magaji Bawa na zama Garkuwan fulanin kwana shi ya maidani mutum, gaskiya baku kyauta ba" wasu ne jikinsu ya fara sanyi ganin haka yasa Jauro ƙara tattaro sauran munafurcinsa dan shi baya so ace mutane su banzartar da maganarsa idan ba haka ba ba zai cika burinsa ba,baya so yaji sunan Magaji na daukaka! yafi so duk yankuna yadda ake kiran sunan Magaji Bawa! Magaji Bawa! ya kasance shi Jauro Mai Maganin yankin kwana shi ake kira ba wani Magaji Bawa ba, ace shine shahararsa ta kai inda yake so kuma yake bukata, saurin cewa ya yi

"Babu wani borin kunyar da za ayiwa mutane an dai cutar dasu! Wa inda aka kashe musu yara su ce mai? Sannan tunda daɗewa Magaji yasan yaransa Macizai ne amma ya boyewa mutane bai gaya musu dan yanzu yana da mugun nufi a ransa!"


 

       "Magaji baya da masaniya a kan cewa *AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE* taya idan ya sani har zai barsu su yi kisan kai!? Da kake maganar su na kisa Aziza bata taba kisa ba,akasari ma ita dabi'un Magaji ne tattare da ita, ku a tsammaninku da Azima ce har kwa fara yi mata abunda ku ka yiwa Aziza? Inaaa! Da kafin mu iso wlh sai dai gawawwakinku!" cewar Baffa Mandi, jauro ya ce

"Owoohh! Kenan da saninku ma kamar yadda na faɗa! Jama'a kuna dai ji ko? An zalinceku an munafurceku an kashe muku! Kuma ta yadda zaku gane Magaji ya san yaransa Macizai ne shine basu zuwa bikin gargajiya ta al'adun fulani wanda ake gabatarwa duk shekara, sabida sun san a lokacin ana amfanin da magungunan macizai! Sannan......"



       "Ya isheka haka Jauro!!" Baffa ya katse Jauro jikinsa na rawa, ya tako ya zo gabansa ya ce

"Da ace da sanina yarana macizai ne da tuni na dauki mataki wani zancan 7ake yi yanzu ba wannan ba, a da nace maka muddun ka gano yarana macizai ne nina maka lamuni ka kashesu! Amma tunda na gano cewa ku ɗin ba mutane bane dabbobi ne wanda shanu ma sun fiku hankali ko da Azima da Aziza sun dawo yankin kwana duk wanda ya yi gigin taba min yara a lokacin zan basu umarni su kashe min koma waye!! Sannan ka zuba ido ka gani, zan maida yarana mutane ko da kuwa hakan zaiyi sanadiyar mutuwata, a yau kuna zaginsu macizai kuna ci min mutunci, amma ku sani ko nace kai jauro ko sani, MAGAJI BAWA KAFIN ALLAH NE BA KAFIN MUTUM BA! KO DA ACE MISALI BANA RAYE! AZIMA DA AZIZA SAI SUNANSU YA BUGA TAMBARI A YANKUNA BA MA IYAKAR YANKIN KWANA BA! KAMAR YADDA NA MAHAIFINSU NI MAGAJI BAWA NAYI! NA MAKA WANNAN ALKAWARI! BAIWA DA FARIN JININMU DAGA ALLAH NE KA ZUBA IDO KA GANI JAURO!!!" Baffa na gama faɗi ya bar wajan tare da daukar Hajja suka yi gida yana tunanin tashin hankalin da Hajja zata farka da shi, da fari yara macizai yanzu kuma babu su ma kwata-kwata, amma ya zata yi dole su rungumi kaddara.




         Bayan Baffa ya bar wajan Sarki Chubaɗo ya kalli Jauro ya ce

"Ka dai ji kunya wlh! Da ace nima tsoron kar nayi abun kunya ba wlh da yau a yanzu na koreka daga yankin kwana, ku kuma idan dai Jauro ne gaku ga shi,in dai ba a mutu ba to ba shakka ba a daina kallo ba, ba fata nake muku ba amma na tabbata akwai jarabawa,sannan Allah ba azzalumin bawansa bane, duk wani abunda ya sameku karku sake kuce zakuje wajan Magaji ya taimaka muku! kuje wajan Jauro ya taimaka muku, wannan umarnina ne a matsayina na sarkin wannan yankin!! Idan kuma na ga akasin abunda nace mutum zai fuskanci mugun hukunci!" Chubaɗo na gama faɗi ya yi gaba ya bar su a tsaye a wajan, wasu jikinsu yayi sanyi inda nadama ta kamasu wasu kuwa zuciyarsu kamar busashshen itace!.



      🍃🐍🍃🐍🍃🐍


Azima kwananta biyu tana tafiya kafin ta fito bakin titi, tana fitowa wani guɗa ta yi da dogon harshenta, duniya sabuwa! Tana nan tsaye a kan titi da lullubi tana tunanin hanyar da zata fara dosa, nan ta yanke shawara kawai ta bi dogon titi ta ga iyakar karewarsa, haka ta hau tafiya a tsakiyar titi tana murmushi, kamar daga sama sai ga wani mota ta yanko da gudu amma sai ganin yarinya ya yi tana tafiya akan titi sai horn yake danna mata amma a banza! Azima kuwa tunda farkon fitowarta kenan ba fahimta tayi ba, da kyar mutumin ya taka burki ya fito a motar gami da daka mata tsawa "keeeeeeee!!" wani tsayuwa Azima tayi tare da ware blue eye dinta, babu wanda ya taba mata irin wannan ihun, a hankali ta kara jan mayafinta ta rufe fuska sannan ta juya a hankali kanta a duke, mutumin kallon sama da kasa ya mata yana yatsine fuska dan ya ganta da shigar fulani ba mamaki irin kidahuman nan ne na jeji dan haka cikin izgilanci ya hau ta da zagi.

"Ke wace iriyar bagidajiya ce da ana miki horn amma da shike kin fito a cikin jeji baki ganewa kwakwalwarki a toshe yake kina tafiya a kan titi banza ballagaza daƙiƙiya ƙidahuma tunkiya!!" hakika zagin ya soki zuciyar Azima, zaro ido ta yi tare da yaye mayafinta rai b'ace cikin hausar da babu sosai a kan harshenta ta ce

"Ba dai tunkiya ba, sai dai *MACIJIYA!🐍**" ta faɗi tare da komawa macijiya ba ta jira ya gama firgita ba ta kai masa sara a wuya nan ya fadi kasa yana shure-shure,komawa mutum ta yi tana dariya ta ce

"Kaina mutum na farko da na fara kashewa daga fitowata,hakan na nufin cewa zan sha jini da yawa kenan sabida mutanen cikin gari basu da ɗa'a,ni kuwa AZIMA MACIJIYA bana daukar wargi!" ta faɗi tana murmushin gefen baki ta leƙa cikin motar ta wargaza ta ga kuɗi ta kwashe duk da bata san amfanin me zasu mata ba, ta ci gaba da tafiya, ta yi tafiya sosai inda ta iske tasha wanda yake cike yake da jama'a a hankali ta ƙutsa kanta cikinsu tana ji ana ambatar sunayen garurruka, garin da taji ya mata masauki a kunneta shine *KANO TUMBIN GIWA KO DA MAI KA ZO AN FIKA!* murmushi ta yi ta kara nanata KANO  ranta, sannan ta afka mota ta nemi can baya ta zauna tana murmushi yau burinta ya cika ta bar yankin kwana.



        Kuɗi aka fara karba aka zo kanta, ana cewa kawo kuɗinki nan kuwa ta cire ta miƙa ba tare da tayi magana ba ko tasan nawa ta bayar ba,duk da zuciyarta na raya mata da sun isa kanon da zasuje zata  kashe mutanen da suke motar!.



       Bayan yan wani lokaci ƙalilan mota ta tashi daga tasha ta hau tafiya, inda Azima ta ji ta gaji dan gani take yi motar bata mata sauri,amma ance biyan bukata yafi dogon buri dan haka ta kara rungume hakuri.



      Basu da isa kano ba kuwa sai magriba, ganin tsananin girma da faɗi da cikowa irin na garin kano yasa taji ma ta fasa kashe mutanen da tayi niyyar kashesu, ta shagala da kalle-kalle ta ji ana mata magana ta bayanta

"Barka dai 'yar fulani"


    🍃🍃🍃🍃🍃🍃



😭😭😭😭


Yau baƙin ciki ne a raina sau biyu ina cin uban typing yana gogewa, Allah dabadin bana son nayi missing update ba da ɗiff zaku jini😭



*PAID.*

🅿️==3️⃣5️⃣↪️3️⃣6️⃣

Cikin gari ya nufa inda ya kaita asibiti mafi kusa, yana shiga ya ce a bata taimakon gaggawa,inda wasu nurses suka hau masa iskanci a kan ba zasu karbeta ba, hannu yasa a aljinun wandonsa ya ciro wallet dinsa ya bude ya ciro ID Card dinsa ya nuna musu, suna gani suka hade gefe suna sorry sir, ya ce

"Baku da tausayi ko kaɗan! haka ku ke yiwa jama'a da haka idan yazo da ƙaran kwana sai marar lafiya ya mutu amma kune sanadi! An san likitoci da tausayi dan haka ku gyara,ina mai wannan asibitin ina son magana da shi idan har yana kusa" jiki na rawa suka ce bari su nuna masa office din, har bakin kofar office ɗin suka kaisa, ya kallesu su biyu ya ce

"Ku fara duba yarinyar nan kar ta mutu ina zuwa bari nayi magana da shi zan zo nayi mata dressing da kaina"

"Ok sir" suka fadi shi kuwa ya shiga ciki da sallama.



          Amsawa wanda aka yiwa sallama ya yi, ya kalli wanda ya masa sallamar ya ce

"Bismillah ƙaraso ga waje zauna mana" ƙarasowa ya yi cike da jin kansa ya zauna,sannan ya miƙawa Dr din hannu suka gaisawa, Dr din ya ce

"Amma ban gane ka ba daga ina? sannan baka yi kama da marar lafiya ba"  murmushi ya ɗan yi na gefen baki, sannan ya miƙa masa ID dinsa,yana dubawa ya kallesa ya ce

"Doctor?" ya yi murmushi yana gya ɗa kai, tashi ya yi da sauri yana fadin


"Allah dai yasa sa'a ce ta sameni har office zaka fara aiki a hospital dina" shi ma tashi ya yi tsayen ya ce

"A'a ko ɗaya wlh,ai ni ba a nan yola nake da zama ba,ina zama a kd ne akwai aikin da ya kawoni ne,tun jiya ma ya kamata ace na bar yola to ashe tsautsayi ne ya tsayar dani dan na buge wata yarinya ne da mota shine na kawota asibitin,inaso nayi treatment dinta sai mu wuce dan bana so na ƙara kwana a garin nan" 

"Ya Subhanallah! tana ina yarinyar? muje sai ka dubata ai ba komai"  ba tare da ya sake magana ba ya bi bayan Dr har izuwa dakin da aka kwantar da Aziza, suna shiga ya hau dubata ya ga bata mutu ba, kayan aiki yace a ba shi ya fadi abubuwan da za a ba sa aka kawo masa sannan ya hau dubata,ya mata su allurai ya sakawa kanta bandage ya mata komai sannan ya ɗora mata ruwa, ya duba agogon dake daure a hannunsa ya ga sha ɗaya, ya kalli Dr ya ce

"Tnk u so much Dr on my way" ya faɗi tare da kokarin daukar Aziza, Dr ya ce

"Haba Doctor ka bari mana ko zuwa gobe sai ka wuce idan ta farka,ga shi kace baka santa ba,duk yadda akayi inaji irin fulanin rugan nan ne, yanzu idan ka wuce da ita kd alhali ba yar kd ɗin ba ce fa?" shuru ya yi yana nazarin maganarsa kuma gaskiya ne tunda a nan ya sameta miye hujjarsa na tafiya da ita? Kawai ya barta idan ta farka taji sauki sai su sallameta ta koma inda ta fito, da wannan tunanin ya ce Dr ɗin ya ba shi acct number ya masa transfer'n kuɗi ya kula da ita idan ta warke sai su sallameta,haka kuwa aka yi bayan ya masa transfer ɗin nan ya fito da sauri ya shiga mota ya tayar yaja ya bar asibitin, har ya fara tafiya ya ɗan yi nisa sai yaji hankalinsa bai kwanta ya tafi ya barta ba,ko ba komai shi ya bugeta sannan bata farfaɗo ba ya tafi ya barta anya ya kyauta kuwa? Saurin juya kan motar ya yi ya koma asibitin, yana zuwa ya ce a ba shi ita kawai, Dr ya ce

"Haba Doctor baka yarda damu bane?"

"No ba haka bane ba wai ban yarda daku bane,kawai ban yarda da shawaran da zuciyata ta bani bane na in tafi in barta alhali ban san a wani condition zata farka ba that's why, amma yanzu zan tafi da ita,idan ta farka lafiya taji sauki zan sa a maidata gidansu" da haka yasa hannu ya dauketa tare da drip ɗin da ya ɗora mata, har yanzu tana bacci, ya gyara bayan motarsa ya kwantar da ita ya ajiye drip ɗin a gefenta yana duba agogo tare da auna tym din da ruwan zai ƙare" da sauri yaja motar yanayi yana duba tym.




      🐍🐍🐍🐍



Horn ta yi a wani madaidaicin gate da sauri gateman ya zo ya buɗe yana zuba mata kirari, hannu ta daga masa sannan ta danna hancin motar cikin gidan,tana parking ta fito tana fitowa ita kam ma ta manta da ta saka mutum a bayan both cikin gida ta wuce tun kafin ta shiga take kwalawa Lantana kira, da gudu wata 'yar dattijuwar mata ta fito ta zube a gabanta ta ce "gani *Hajiya Zubaida*" 


"Oh dan iskanci dama kinaji ina ta faman kwala miki kira amma ba zaki iya amsawa ba sai dai ki wani fito da mugun gudu sai kace ana gasan tsaren karnuka, ki fa kiyayeni kiyi hankali!, ina Hajiya?"

"Tana ciki" 

"Hajiya! Hajiya! Hajiya!" ta hau kwalawa Hajiyan kira.




        An ɗau kusan mintuna uku kafin Hajiyar ta fito tana hamma tana matsa ido alamun bacci take yi kiran Zubaida ne ya tayar da ita

"Zuby me ya faru?"

Zama ta yi tana fadin

"Wlh Hajiya sai na ci uban baban mai aikin nan, kin san wai har da kai karar mu police station wai mun yi 'yarsa duka a bi masa kadi"

"To yanzu ya aka kare?" Hajiya tana tambaya tana zama kusa da inda Zubaidan ta zauna,ta ce

"Na basu kudi nayi gaba abina,kee! Lantana kawo min ruwa mai sanyi" tashi tayi da sauri tana fadin to, sannan Zubaidan itama ta tashi ta shige wani daki wanda yake nuni da nata ne, kaya ta shiga canzawa ta ga ko gyara mata dakin ba a yi ba, da sauri ta cire na jikinta ta watsar dan haka dabi'unta yake, ta saka wani riga iyakarsa guiwarta sannan ta fito tana masifa tana zama

"Haba Hajiya ashe ba a gyara min bedroom dina ba?"

"To Zuby wa zai gyara? Masu aikin duk sun gudu sai Lantana ce kawai ita kuma aiki ya mata yawa" tsaki ta ja tana shirin faɗin yanzu wa zai gyara mata daki sai ta tuno da ta sa mutum a bayan mota, tashi tayi da ɗan sauri tana fadin

"Wayyo na manta da wan can bagidajiyar bafulatanan" a haka ta fita riga iya guiwa kai babu ɗan kwali sai uban attachment, Azima kuwa tana kwance a both a macijiya hankalinta kwance tana bacci, jin kara ne ya sakata buɗe ido tayi saurin komawa mutum,tana zama mutum tana bude both din ta kalleta a wulakance ta ce

"Fito" a hankali Azima ta fito tana gyara mayafinta tana tafiya tana lankwasa kamar yadda take tafiya a yankin kwana.


     Shiga parlourn sukayi, Zuby ta ce

"Hajiya naji dama kina neman mai aiki to gata nan, a hanya na tsinceta, sai ta ɗora da aikin da Kuluwa ke yi" Hajiya ta kalleta tana toshe hanci ta ce

"Ya sunanki?" 

"AZIMAA!" ta faɗa da kaushin murya dan duk tana kula da yatsine fuska da toshe hancin da Hajiya ke yi.

"To dubu biyar zamu dinga baki a duk wata, zaki dinga share-share da goge-goge,inada yara guda uku, ga Zuby nan akwai Yayarta mai suna Baby sai kuma Babban ɗana namiji yayansu kenan, sunansa Munir dik basu nan sun fita idan suka dawo zaki gansu, ke ce zaki dinga gyara musu bedroom dinsu!" Azima dake duƙe ta ce

"Hajiya miye shi badorom din?" Zuby ta ce

"Hajiya ƙidahuma ce daga jeji take taya zaki mata turanci,keee Bagidajiya ana nufin daki,nasan bukka ku ke kira a can jejinku" cije baki Azima ta sake yi, jin yadda zuciyarta ke tafasa idan bata tashi ba komai zai iya faruwa,hannunta ta kalla ta ga ya fara sab'ulewa yana zama blue saurin ajiyar zuciya ta koma yi dan zuciyarta ta yi sanyi, Zuby ce ta sake kwalawa Lantana kira ta amsa da ta zo tace mata ta tafi da Azima ta nuna mata yadda zata yi wanka ta bata wasu kaya da turare dan Azima na wari,sannan idan ta nuna mata ta taho ta saka musu turaren wuta, Lantana ta amsa tana kamo Hannun Azima suka shige daki, suna shiga Hajiya ta ce

"To ita haka zata dinga rufewa mutane fuska a gida?"

"Hajiya manta da wannan kin san bata taba shigowa birni ba,dan haka bata waye ba"

"Kuma hakane fa" cewar Hajiya, Zuby ta ce

"Wai ina Munir da Baby suka je ne?"

"Wa ya san musu" share zan can suka yi suka kamo wata hirar,    da Lantana suka shiga daki ta kalli Azima ta ce

"Baiwar Allah zauna ki jirani kinji bari naje na saka musu tiraren na dawo" ta fita da sauri, buɗe ido Azima tayi tana fadin

"Babu wanda ya isa ya zageni ya tafi a banza ba tare da nayi masa hukunci ba! Babu shi!" ta faɗa tana lankwasa yatsun hannunta, an dauki mintuna sha biyar kafin Lantana ta shigo, ta ce

"Azima ko?" Azima ta sunkuyar da kai tana fadin

"E" a sanyaye kaman wata ta kwarai, Lantana ta kama hannunta suka shiga bayi,ta haɗa mata ruwan wanka ta dauko soso da sabulu da shampoo dan ta ga tana da ga shi mai tsayi, ta ce

"Na wanke miki kan naki naga gashin naki da tsayi sosai" Azima ta gyaɗa kai, Lantana ta bata fallan zani ta ce ta cire na jikinta ta ɗora, ba musu Azima ta cire kayanta ta ɗora fallan zani lantana ta jiƙa mata kayan a ruwa tace zata wanke mata su, sannan ta bata kujera ta zauna, Lantana na fara kwashe gashin Azima tayi saurin lumshe ido dan bata son Lantana ta ga kwayar idonta.


 


     Shampoo sosai Lantana ta zuba a kan Azima amma ta ga idan har ta juye ba isa wanke mata kai zaiyi ba, haka yasa ta dauke ledar omo sai da ta zuba ya kai kwankwani ɗaya da rabi kafin ta fara dirzan kai Azima wanda yake fitar da datti, sun kai mintuna talatin tana wanke mata kai kafin gashin ya fito baƙi da shi ga tsamtsi yayi fess!    Lantana ta yi murmushi ta ce

"To kiyi wanka,bari na baki waje" har Lantana ta kai bakin kofa sai ji tayi Azima na faɗin

"Miyatti Inna" karo na farko da ta fara yima wani ɗan adam godiya a rayuwarta, murmushi Lantana ta yi ta fice, sai a lokacin tunanin 'yan yankin kwana ya faɗowa Azima a rai,dariya ta hau yi tana fadin

"Ko ina Macijiya Aziza sarkin tausayi oho! Watakila sakaran tana can an kasheta a jeji! Ko da yake ba zasu iya kasheta ba! Amma nasan shanuwar tana can suna jibgarta" ta karasa maganar tana haɗe rai, wanka ta yi sosai ta dirje jikinta ta fito, sai da jikinta ya bushe ta kuma saukowa da gashin kanta kafin ta fito ta samu Lantana ta ajiye mata fallan zani da t-shart da su mai da turare, kayan ta saka, sannan ta dauki kum ta sharce gashin kanta ta zubo da wanda yake rufe masu gefen fuska sabida kar ana ganin kwayar idonsu, gashin ya sauko har ƙirjinta, kallon kanta ta yi a madubi ta ga ta yi kyau,murmushi ta yi, sai ga Lantana ta shigo

"Wa Subhanallahi bi'ahsanul Khaliƙin!" cewar Lantana Azima ta sunkuyar da kai, Lantana ta ce

"Zo muje na nuna miki ayyukanki" Azima ba ta kuma magana ba ta bi Lantana a baya, nunnuna mata komai Lantana ta yi har da dakin Baby da dakin Munir, Azima ta ce ta gane, sannan Lantana ta ce

"Yanzu ki fara gyara dakin Munir dan bai da mutunci ko kaɗan duk wulakanci Baby da Zuby suna bin bayan Munir ne, idan ya dawo ba a gyara masa daki ba ya ganki ba  zaiyi la'akari da cewa ke sabuwar zuwa bace ya yi ta kwallo dake" 

"DA KUWA KO ƘASHINSA BA ZAN RAGE BA!" Lantana ta ce

"Iyeeee!!?" sauri saita kanta Azima ta yi ta ce

"Inna je ki kawai zan gyara yanzu" fita Lantana ta yi,Lantana na fita Azima ta bi lafiyar gado ta kwanta dan tayi wanka mai dadin da bata bata yi ba taji bacci takeji.




       🍃🍃🍃🍃



Karfe sha daya saura ya shigo kd bai wuce gida ba ya wuce asibitinsa da ita, har yanzu kuma bata farka ba,bai damu ba tunda ya mata alluran bacci mai karfi ne, bayan ya mata komai ya ba wasu nurse mutum biyu kula da ita wanda zasu yi nyt duty, kafin ya wuce gida.



      A wani katafaren gate yayi horn da sauri aka zo aka buɗe masa, ya shiga ya yi parking din motarsa, da fari ji ya yi kamar ya shige part dinsa dan ya gaji,amma kuma gwanda ya shiga ya yiwa Mom sai da safe, da wannan tunani ya yi babbar parlon nasu da sallama,kanwarsa Sultana tana zaune wacce ba zata wuce 18 ba tana kallon wani horror seris film tana jin sallama ta miƙe da gudu tana fadin

"Oyoyoo *BROS NAWAZZ!"*



      🍃🍃🍃🍃


MOMYN AHLAN✍🏻

[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃


    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨

    (🐍 _Macizai ne_🐍)


    MALLAKAR.


*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*


SAHIBAR KAINUWA.


Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.


Sanarwa.

Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association


*____________________________________*


*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_


_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_


   🍃🍃🍃🍃🍃


*INA GAISHEKU KYAUTA YAN PAID GRP MASOYAN........BAN DAI KARESA BA KU KARASA DA KANKU*




*PAID.*

🅿️==3️⃣3️⃣↪️3️⃣4️⃣





Saurin juyowa Azima ta yi ba tare da ta dago ba

Ya yi murmushi ya CE

"Yan mata magana nakeyi fa" da sauri  ta matsa gefe ta hau tafiya tana sake rufe fuskarta, shi kuwa binta ya hauyi yana kan yi mata magana,da ya ga ba zata tsaya ba ya sha gabanta, cije baki  Azima ta yi tana hade rai,babu abunda ta tsana kamar a sha gabanta,Cikin murya da yake nuna taji haushin takura mata da yayi tace

"Malam wai lafiya?"   

Dariya ya hau yi jin yadda kalar Hausar  ta ta ke fita, a ransa yake fadin "wow! Wannan daga ganinta bagidajiya ce daga jeji take,bari nayi mata wayo, ko Allah zai sa na shana da ita daga dawowata!" 

"Amm yi hakuri ba nufina na ɓata miki rai ba,naga yadda kika ta kalle-kalle ne kamar baki san kowa ba, shine nake so na taimaka miki" ya karasa maganarsa yana murmushi, itama Azima murmushin ta yi ta ce

"To taimakona da me? ko nazo nace da kai inada bukatar taimako ne iyee!!? Na ce maka ina da bukatar taimako ne?"

"Allah ya huci zuciyarki sarauniyar kyawawa, Kano gari ce mai girman gaske da faɗi kuma ke naga alama kamar baƙuwa ce, dan haka ki yarda na taimaka miki naga ke mace ce,ki zo muje gidanmu" mutuwa da mamaki Azima ta yi ko me ta tuna ta yi murmushi ta ce

"Na gode da taimako muje"

"Ina kayan ki?"

"Wala!"

Ta ba shi amsa hankalinta yana can wajan kalle-kalle, jakarsa da ledarsa ya dauka ya ce

"Muje" ya yi gaba ta bisa a baya, kekenapep ya tare musu suka shiga, wani farin ciki ne ke mamaye zuciyar Azima sai magana yake mata amma ina hankalinta ya yi ƙololuwa wajan ganin girma da faɗi da cikowa irin na NA DABO TUMBIN GIWA, ana cikin tafiya sai ji ta yi kekenapep din ya tsaya sai a lokacin ta maido da dubanta ga wani ƙazamin gida wanda ko bukkarsu na yankin kwana ya fi sa kyawun gani, bata damu ba, yayinda ya ce mata ta fito a keken, ba musu kuwa ta fito tana kallon mutanen da suke zaune a kofar gidan masu caca da masu shan wiwi da sigari har ma da masu shan giya, jin yadda ta hadiyi hayakin sigari da wiwi yasa ta hau tari kadan-kaɗan tana yamutse fuska, mai kekenapep ya biya sannan ya kalleta ya ce

"Mu shiga ciki ko?" ya yi gaba ta bisa a baya mutane sai kallonsu suke yi har suka shiga,suna shigewa a cikin wa inda suke zaune a kofar gidan wata mace tayi shigar riga da wando,duk da babu mai kayan mutunci a cikinsu, tab'o dayar dake kusa da ita ta yi ta ce

"Kee Bariki Dadi, baki ga Hoge ya wuce da wata bafulatana ba?" wacce aka kira da sunan Bariki dadi tana riƙe da sigari a hannunta tana zuga suna buga caca ta ce

"Hoge dai? Yaushe ya dawo?"

"Ba mamaki dawowarsa kenan dan na gansa da kayansa" miƙewa tayi da sauri ta ƙudundumo wani ashar sannan ta yi cikin gidan da sauri wa inda suke zaune a tare suka hau zugata suna fadin "idan kinje kici uwarta da ubanta! Bariki dadi! Baki da kyau baki da dadi!" suna fadi suna ihu,ita kuwa fuuuu tayi ciki,a lokacin Hoge har ya buɗe a kulkin dakinsa ya kalli Azima ya ce

"Shigo mana yar fullo" a hankali Azima ta sa kafa ta shiga, a wani jagalgalalliyar katifa ta zauna tana saƙa abubuwa dayawa a ranta, tana zama sai ga Bariki dadi ta banko kofar kamar zata b'alla shi, Azima bata dago ba illa Hoge dake fadin

"Wannan wani irin iskanci ne haka?" 

"Ga ka nan kuwa babban dan iskaci baƙin munafuki! Ka hanani kula ko wani bunsuru, sannan ka dauko wata banziya daga dawowarka ka huce da ita a gabana! To wallahi sai naci Uwarta! Ke kuma munafuka zo nan! Sai wani rufe fuska kikeyi sai kace wata ta Allah kina sunkuyar da kai, to idan baki sani ba ki sani! Kina sa kafarki a nan gidan dukkan wata mutuncinki ya zube kuma saina koya miki hankali!" murmushi Azima ke yi a ranta ta ce

"Inason mutane irin haka! Wa inda basu shiga gonata ba ina kau dasu balle wa inda suka shiga" bata gama maganar zucinta ba Bariki dadi ta shaƙo wuyarta, tashi tsaye Azima tayi,tana tunanin dame zata kasheta! ta sareta ne ko ta watsa mata dafi? Hoge ne ya fizgi Bariki Dadi ya koɗa mata mari sannan ya ingizata waje ya juyo yana ba wa Azima hakuri, bata ce masa ci kanka ba,illa da ya gama rawar bakinsa ya fice wai zai kawo mata abinci, bai jima ba kuwa ya shigo da bakar leda ya ajiye mata, budewa Azima ta yi nan tayi arba da kayan dadi murmushi tayi dan bata taba ganin kalar abincin ba, da sauri ta buɗe ta hau ci tana lumshe ido tana gya ɗa kai, shi kuwa yana zaune a gefe yana kallon gashin kanta da ya rufe mata fuska aransa ya ce

"Hummm! dama ana ganin irin wa innan matan a gaske? Dole na shana wlh,daga ganin wannan ɗanya ce jaƙab, zatayi ruwa zata kai yadda ake so, idan tayi daga nan zata zama cikata!" sai sambatu yakeyi a zuciyarsa yana hadiye yawu,Azima kuwa fess ta cinye abubuwan da ya kawo mata, ta kwankwaɗe maltina har tana lashe baki, tana gamawa ta koma ta jinginu da banko tana sauke ajiyar zuciya ta lumshe ido,jin saukar numfashi ta yi a wuyarta, saurin buɗe ido ta yi ta gansa ya matsota sosai, sai wani washe baki yake yi, bata gama karantarsa ba taji yana fadin

"Meyasa kike rufe baiwar kyawun da Allah ya miki da wannan dogon gashin naki? Duk da ba a ganin fuskarki da kyau amma da an ganki an ga kyakkyawa ajin karshe, dan Allah ki buɗe idanunki na ganki,sannan ina so ki bani hadin kai nayi miki alkawari zan baki duk abunda kikeso zan miki komai" cije baki Azima ta yi jin yadda wani baƙin ciki ya mamaye zuciyarta,daurewa ta yi tasa yatsarta babba manuniya a kan goshinsa, ta ture kansa daga wajan saitin wuyarta sannan ta ce

"Kasan daga ina nake? Sannan ni fuskata kallo daya ake mata,idan har ka gani babu fuskar da zaka kara kalla a rayuwarka"

"E na yarda ni dai ki bude fuskarki na gani, sannan zan baki abun dadi" ya fadi yana shirin kai hannunsa kirjinta,da sauri Azima ta ja da baya tana fadin

"Owohh kenan kai ɗan iska ne! Zan koya maka hankali, ka taba ganin maciji?" 

"E amma a zahiri sau daya na taba gani kuma ƙarami ne ma,amma ina gani a fina-finai"

"To yau zaka ga Babban a zahiri ido da ido!" ta faɗi tana dariya yayinda ta kwashe gashinta ta maida su baya,blue eye dinta ya bayyana, a gigice hoge ya ja da baya, yayinda ta hau rikiɗewa,tun kafin Azima ta taba Hoge numfashinsa ya fara barazanar daukewa, yana ganin zureren Maciji har na sheƙi a gabansa nan ya fadi sumamme, Azima ta sa baki ta saresa a gabansa, sannan ta koma mutum ta fice, ta zo fita kenan suna karo da Bariki dadi,shaƙeta bariki dadi tayi,Azima tace

"Dama kafin na tafi ina nemanki!" tana gami fadi ta zaro harshenta ta watsa mata dafi sannan ta bar gidan.




        🍃🍃🍃🍃🍃



Kuka Hajja keyi yayinda Inna Wuro da Yawuro suke ta aikin bata hakuri suna rarrashinta,amma pinaa Hajja kamar ba da ita ake yi ba, idonta ya kumba ya yi him sabida kuka fuskarta ya yi jaa! Baffa ne ya duka a gabanta ya ce

"Jumala? Kiyi hakuri,In sha Allah idan anyi duniya DAN MANZON ALLAH S,A,W, Azima da Aziza zasu dawo garemu In sha Allah,kuma yaranki zasu dawo mutane ko da kuwa zan rasa raina na miki alkawari!" ita dai Hajja bata ce komai ba, tun daga wannan rana Hajja bata um bata um-um, idan ta zauna idonta na kan bakin kofa,ta ajiye idanunta har izuwa ranar da yaranta zasu dawo gareta.




       🍃🍃🍃🍃


Fitan Azima yawatawa ta ci gaba da yi,dama ita ba sallah take yi ba balle ya dameta, idan kuma wani mai kararren kwana tsautsayi tasa ya shiga hidimarta ta kashesa ta yi gaba, yau kwananta uku da shigowa garin kano bata damuwa da wajan kwana idan dare ya yi duk babbar bishiyar da ya mata zata zama macijiya ta hau ta kwanta tayi bacci ko ta huta, yau ta fito tana cikin tafiya taji ƙaran mota ƙiiiiiii! da sauri ta juyo ta ga wata matashiyar budurwa ce wacce zata kai shekara ashirin da biyar,fitowa tayi tana zazzagawa Azima zagi, yayinda take binta da ƙaramin kallo

"Ban da hauka taya zaki rufe fuska ki dinga tafiya a kan titi! Sakarya kawai bagidajiya!!" cije baki Azima tayi meyasa ake son ce mata bagidajiya? duk da bata san ma'anar kalman ba amma taji ta tsani kalman, lankwabe murya ta yi ta ce

"Dan Allah ki taimaka mini, ni yar gudun hijira ce an kashe dukkan yan uwana a rigarmu ni daya ce kawai na rage,ban san kowa ba ban san inda zanje ba, dan Allah ko aiki ne a gidanku ki nema mini zan dinga yi" yatsine fuska ta yi tana fadin

"Kuma fa kamar naji Hajiya na neman mai aiki,to amma gaskiya sai dai na sakaki a cikin both dina dan ba zaki shiga mini mota ba"

"Ina ne shi hakan bat din?" 

"Banza jahila both nace, nan kenan zo ki shiga" ta fada tana mata nuni da both tana budewa,Azima ta shige tana murmushi tare da fadin

"Matakin farko!" tana rufe murfin both din Azima ta koma Macijiya, shiga motar tayi ta ja tana tsaki.



      A kwana ukun nan Aziza ta fito daga bakin titi ita ma,tana fitowa ta zube a kan titi tana sakin kuka tana kiran sunan Hajjanta da Baffanta, Inno Fandi ce ta taimaka mata ta fiddota bakin titi sannan ita ta koma, kuka sosai Aziza ta yi kafin ta tashi ta hau tafiya, tana ganin kamar ta shigo wani sabuwar duniya ne, bata ma san a inda take tafiya ba, shi kuwa da sauri yake jan mota,yana driving yana duba tym, wayarsa ce ta yi kara yana dubawa ya ga Friend 4 Life, dagawa ya yi, ya ɗan yi shuru tukunna kafin ya ce

"Hey Dude bazan maka karya ba,wlh bazan je na dubasa ba,guy din nan ya raina min hankali, jiya banyi niyyar kwana a garin yola ba amma ya sakani kwana, yanzu haka ma nikam gani a hanya ko kwana zanyi sai dai na kwana amma yau din nan sai na kasance a cikin garin Kd in sha Allahu!" yana magana a waya ransa a b'ace sai ji ya yi, ya yi sama da mutum, wani mahaukacin burki yaja ya fito da gudu, yana isowa gareta tana lumshe ido, duk da bai ga fuskarta da kyau ba gashi ya rufe amma daga ganinta a jeji ta fito, kallon gabas ya yi,ya kalli kudu,ya kalli arewa,ya kalli yamma bai ga wani ɗan adam ba, shi a tunaninsa sun fito kiwo ne yan uwanta suka tafi suka barta, to amma idan haka ne shi ya zaiyi da ita? Ga kanta ya fashe yana zubda jini, "No dogon tunani ba nawa bane i need to save her lyf first" ya faɗa yasa hannu yana shirin daukarta, wani mummunar faduwar gaba ce ta riskesa inda yaji dukkan wata gab'a ta gangar jikinsa ya sake, saurin kauda abun a ransa ya yi ya dauketa ya sakata a mota ganin bata motsa, yana addua Allah yasa dai bata mutu ba.


      🍃🍃🍃🍃🍃




MOMYN AHLAN✍🏻

[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃


    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨

    (🐍 _Macizai ne_🐍)


    MALLAKAR.


*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*


SAHIBAR KAINUWA.


Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.


Sanarwa.

Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association


*____________________________________*


*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_


_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_


   🍃🍃🍃🍃🍃



*PAID.*

🅿️==3️⃣7️⃣↪️3️⃣8️⃣




Murmushi ya mata ta zo ta rungumesa tana yi masa sannu da hanya, ya amsa da "yawwa sannunki,ina Mom kar dai har tayi bacci?"

"Kai anya kuwa, da muna zaune da ita a nan bata jima da tashi ta hau sama ba"

"Okay bari na dubata" ya faɗa yana maida dubansa ga tv'n ya ce

"Ke da kallon horror ko, sai kin fara ganinsu a gaske zaki sani" murmushi Sultana ta yi ta koma tana zama shi kuwa ya hau sama,dakin Mom ya shiga da sallama tana zaune tana waya, zama ya yi kusa da kafarta har sai da ta gama wayar ta ajiye kafin ta kallesa cikin kulawa ta ce

"Nawaz sai yanzu? Ya hanya an dawo lafiya?"

"E wlh Mom, Alhamdulillah! ina wuni? Ya gida? na sameku lafiya?"

"Alhamdulillahi Doctor, fatan dai lafiya ko? Ko dai gajiya ce dan fuskarka ta tuna,yanzu haka ma da Amminka muka gama waya wai ta kiraka wayar bata shiga nace ba mamaki hanya ce ba netwrk"

"E hakane zan kirata gobe yanzu dare yayi zan shiga part dina,kunyi waya da Son dinki ne Mom?"

"E dazu ya kirani dan albarka"

"Mom muna cikin waya da shi dazu tsautsayi tasa na buge bafulatanan yarinyar mutane"

"Subhanallahi!" Mom ta faɗa tana zabura

"Kwantar da hankalinki Mom tana hospital dina" nan ya bata labarin yadda hatsarin ya kasance har izuwa shawaran da ya yanke na tahowa da ita kaduna idan taji sauki sai a maidata gida, Mom ta sauke ajiyar zuciya ta ce

"Shawaran da ka yanke mai kyau ne Nawaz, Allah ya bata lafiya, ma je mu dubata gobe idan Allah ya kaimu ni da Sultana"

"Allah ya kaimu Mom" ya faɗa yana duba agogon hannunsa

"Dare yayi Mom zanje na kwanta na huta akwai gajiya a tare dani"

"To Allah ya tashemu lafiya a huta gajiya,Allah ya yi albarka" Nawaz ya amsa da amin yana tashi ya fice a dakin, yana saukowa ya kalli Sultana ya ce

"Idan baki kashe tv'n nan kinje ki kwanta ba Allah sai na zaneki" da sauri Sultana ta miƙe ta kashe tv'n kasancewar tasan halin Yayan nata, sai da ya ga ta hau sama kafin ya fice ya nufi part dinsa, wanka ya yi ya gabatar da salloli har da nafila ya jima yana addua kafin ya tashi ya koma gado ya kwanta,har ya lumshe ido ya buɗe ya dauki wayarsa ya kira Amininsa suka hau ɗan taba hira inda yake ba shi labari ya buge bafulatana, Allah ya kiyaye gaba ya masa,sannan ya ce

"Yaushe zaka dawo america?" Nawaz ya sauke ajiyar zuciya ya ce

"Nan da 2wks In sha Allahu,but idan nazo ina shekarar karshe zamuyi mu dawo gida gabadaya?,dan gaskiya na gaji da zaman outside"

Daga can bangaren ya ce

"In sha Allahu, duk da ni bana son zaman nigeria gaskiya"

"To ya zaka yi dole ka dawo,duk lalacewa kasarka kasarka ne, sannan karka damu da abinda Momma take maka, ka ci gaba da yi mata biyayya a matsayin uwa,wata rana zata gane In sha Allah" ajiyar zuciya ya sauke, nan Nawaz ya gane damuwar dake damunsa dan haka ya kau da hiran ya jawo musu wata, sun kai biyun dare kafin suka yiwa junansu sallama, yana ajiye wayar bai jima ba bacci ya kwashesa,yana cikin bacci ya hau mafarkin yarinyar da ya buge da mota, suna cikin wani ƙasurgumin jeji sai faman ihun take zabgawa tana fadin ya taimaketa ya taimaki rayuwarta, tana ihu tana gudu yana binta a baya, da haka har suka je jikin wata babbar bishiya taja ta tsaya kanta a sunkuye tana sanye da kayan fulaninta,ta ƙanƙame jikinta tana ihu, shi kuwa yana riƙe da fitila a hannunsa yana haskawa sabida tsananin duhun jejin, yana shirin matsowa gareta ya ga mummunar tashin hankali dan kuwa gani ya yi ta koma wata zabgegiyar macijiya🐍 fara sol sai ƙyalli take yi,tana ci gaba da ihun ya taimaketa.



     A mugun gigice Nawaz ya farka yana fadin

"INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN!!³" hannu ya miƙa ya kunna wutar dakin ya rike kansa da karfi dan ji yakeyi kamar kan na shi zai faɗo kasa, gabadaya jikinsa ya jiƙe da gumi, yayinda ko wani kofar gashi ta gangar jikinsa ya buɗe sun miƙe tsaye, jijiyoyin wuyansa duk sunyi waje, jikinsa sai b'ari yake yi har yana jin wani zazzabi, da kyar ya jawo wayarsa ya duba tym ya ga karfe biyar, tashi yayi ya shiga bathroom ya dauro alwala ya tada sallah, yana nan zaune yana addua har aka kira sallah, sai da yayi raka'atul fajir sannan ya miƙe da kyar ya fita zuwa masallacin da yake wajen gate ɗin gidansu, bayan an idar da sallah ya shiga ya gaida Mom bai wani zauna ba yace mata kansa na ciwo zai sha magani ya kwanta dan bai samu bacci daren jiya ba, Allah ya kara sauki Mom ta masa ya koma part dinsa ya kwanta, ba jimawa bacci ya sake kwasansa amma still mafarkin daren jiya shine ya kara tayar da shi, cikin kiɗima ya zauna a bakin gado yana tunani barkatai.

"To miye haɗina da wannan yarinyar? daga haɗuwa da ita jiya shikenan sai na kasa bacci? ni da ko fuskarta ban gani da kyau ba gashin kanta ya rufe! sannan me hakan yake nufi nake ganinta a macijiya!? ko dai ba mutum ba ce? kai inaa a'a ko dai wani abu ya sameta ne a asibitin?" sauri tashi ya yi ya dauki jallabiyarsa yana kiran nurse's din da ya basu kula da ita,amma babu wacce ta daga a cikin su biyun, tym ya duba ya ga 7:30 da sauri ya zare car'key dinsa ya fice ya bar gidan ya nufi asibitinsa mai suna *ALWAZ HOSPITAL KADUNA.*




          Yana isa ko parking bai gama ba ya shiga ciki da sauri,yana shiga reception ya samu nurses ɗin suna bacci, a tsawance ya tayar dasu nan ya hau su da faɗa a kan basu san aikinsu ba, hakuri suka hau ba shi amma bai tsaya ya sauraresu ba illa dakin da Aziza ke kwance,kamar yadda ya barta jiya haka ya sameta tana bacci gashinta ya rufe mata fuska,yana ganin lafiyarta ya saki ajiyar zuciya wanda bai san dalilin hakan ba bai ma san lokacin da ya saki ba, dubata ya sake yi ya ga zata iya farkawa ko da wani lokaci, hannu yasa da niyyar kwashe gashin fuskarta a fili ya ce

"Wai meke damuna ne kam? Mtsww!" ya ɗan ja gajerar tsaki yana fita a dakin, gida ya koma dan kansa ke masa ciwo sosai,magani ya sha cikin ikon Allah bacci ya kwashesa bai farka ba sai daya saura,yana tashi ana kiran sallar azahar, bai tsaya bata lokaci ba ya yi alwala ya tafi masallaci bayan ya dawo babban parlour ya wuce ya samu Mom da Sultana suna zaune suna hira, gaishe da Mom ya sake yi ta amsa Sultana ta gaishesa ya amsa yana haɗe rai da fadin

"Keee me ya hanaki zuwa skull?"

"Brother yau bani da komai shiyasa ban je ba"

"Kin san dai bana son wasa da karatu ko?" 

"E Brother bana wasa da karatu ko Mom?" ta fada a shagwabe tana kallon Mom,Mom ta yi murmushi ta ce

"Ai kai ma kasan yadda Sultana ke son karatu,ya gajiyar hanyan da kuma jikin?" 

"Alhamdulillah Mom na warware"

"To Ma sha Allah haka ake so, dama mun gama shiryawa kai muke jira idan ka farka sai mu gaya maka zamu je asibitin duba yarinyar"

"Okay Mom bari nayi wanka sai na kai ku,nima akwai marasa lafiyan da nake son dubawa, gobe kuma zanje abuja akwai aikin da nake da shi"

"Kuma?" cewar Mom,ya ce

"E wlh Mom,ai idan har mun samu sauki sai dai idan mun dawo kasarmu gabadaya,tunda ko kaɗan zuwan nan wan can guy din dan ya raina min wayo ba zuwa yakeyi ba,ya maqale a kasar wasu" murmushi Mom tayi ta ce

"Ka kyalesa mana Nawaz,kasan fa ba jin dadin zama yakeyi dasu Hajiya  Lawiza da Hajiya Luba ba, kai mutanan duniya sai Allah wlh,ace kuna zaune karkashin mutum kuna cin albarkacinsa kuna rayuwa da dukiyarsa amma kun tsanesa kuna cin dunduniyarsa,kai Allah shi kyauta" Nawaz ya amsa da amin yana fadin

"Ba ri na shirya nazo na kaiku nima na samu nayi aikin dake gabana a hospital din" 

"To a fito lafiya" cewar Mom.



 

      Mintuna sha biyar ya daukesa ya gama shirinsa ya shiga ya yiwa su Mom magana suka fito suka nufi asibiti,ko da sukaje kwatanta musu room din ya yi shi bai shiga ba ya tafi dan akwai cs din da zai yi, su Mom ne suka shiga suka zauna da ita,Sultana tasa hannu ta kwashe mata gashin fuskarta ta ce

"Woww! Allahu Akbar! Ma sha Allah!" 

"Menene Sultana?"

"Wlh Mom kyakkyawa da ita, ki ga gashi, wayyo Allah na ni,wlh Mom kamar ba yar nigeria ba" Mom tayi murmushi ta ce

"Baki rabuwa da shiririta Sultana ba bafulatana ba ce"

"Ai wlh Mom ko a fulanin ba kowa ke da kyau ba"

"To anji ki rufe min baki, karki cika marar lafiya da surutu Yayanki ya shigo ya sameki kina zuba zaneki zaiyi kema kin sani" zare ido ta yi tana riƙe bakinta dan tasan sarai zai zanetan sai dai idan bata cika masa ciki ba dan akwai sa da saurin zuciya abu kaɗan ke tunzura shi ransa ya b'aci.



     Su na zaune a asibitin sai wajan uku da rabi kafin Aziza ta fara farkawa, farkawartata yazo mata da mugun mafarki Azima ta biyo Baffa da wani zabgegen takwabi tana shirin kashe Baffa bayan sun gama dambatuwa In da Baffa karfinsa ya ƙare ya hau kwalawa Aziza kira ta kawo masa dauki Banju zai kashesa! Ga Hajja a sume a kasa, wani ihu Aziza ta yi dai-dai da lokacin da Nawaz ya sako kafarsa dakin ya zo dubasu ya iske ihunta tana fadin

"BAFFAAAANAAAAA!!! HAJJAAAAA!! KEEEEE!!! AZIMAAAAAA!! KARKI KASHE BAFFAAAA!!" sauri yin kanta suka yi Nawaz ya tallabota kirjinsa ya kalli Sultana yace "maza je ki kirawo min wasu nurses ko Dr duk wanda kika samu su zo yanzu" da gudu Sultana ta fice suka dawo da nurse mutum hudu, nan yace su ba shi allurai, bayan sun miƙa masa ne tana ta faman buge-buge, Mom tana tsaye daga saman kanta tana mata tofi, yana mata alluran ta koma ta yi lamo a kirjinsa tana kan ambatar sunan Baffanta da Hajjanta, kamar da minti biyar abun ya lafa,Mom ta ce

"Nawaz ya dai?"

"Ba komai Mom,nan da 30mins zata farka zata dawo dai-dai In sha Allah" Mom ta ce

"Ka gani ko Nawaz? Gwara da Allah yasa baka barta ba ka taho da ita, Allah ya bata lafiya ya tashi kafaɗunta" ya amsa da amin yana me leƙa fuskarta ya ga gashi ya rufe,kwantar da ita ya yi ya fice, Sultana ta zauna kusa da ita tana kamo hannunta.



     Kamar yadda Nawaz ya fada haka kuwa ya kasance 30mins ta farka, tana buɗe ido ta hau bin inda take da kallo, ba dai har ta mutu bane yanzu haka tana lahira? Take tambayar kanta,kallon hannunta ta yi ta ga wata budurwa zaune kusa da ita, ga wata dattijuwar mata zaune hannunta dauke da carbi tana lazimi, budurwar kuma hannunta da waya tana dannawa,saurin janye hannunta Aziza ta yi ta matsa baya, tana dafe kanta da kafarta da ta ga an daure mata shi,nan abunda ya faru ya dawo mata kai, Sultana ta ce

"Sannu kinji! Ya jikin naki?" 

"Sultana kira yayanki mana" cewar Mom

"To Mom" Sultana ta faɗa tana ficewa.



       Tare suka dawo da shi, a lokacin Aziza na maqale can jikin gado tana wani irin kuka kanta a sunkuye tayi mayafi da gashin kanta, jin magana yasata dagowa kaɗan ganin mutum na matsota ya sakata fashewa da sabon kuka tana fadin

"Aradu karka matso kusa dani" a yadda take magana zaka san babu hausa a harshenta,banza da ita Nawaz ya yi yasa hannu zai tabata ta saki ihu tana kiran sunan Baffa, haushi ne ya kama Nawaz ya daka mata tsawa

"Keeeee!!! Bana son hauka!! Ki natsu!!" Mom tace

"Haba Nawaz!? Miye haka? Ka mata a hankali mana" wani tsoro ne ya kama Aziza,ganin haka yasa Mom matsowa kusa da ita ta ce

"Ɗana ne! Ba zai cutar dake ba, wancan kanwarsa ce, shi kuma likita ne, ya bugeki ne bisa tsautsayi sannan wannan asibitinsa ne yana kula dake,alhamdulillah kin farka, yanzu haka kina garin kaduna ne,munji kina ambatar sunan Baffanki, da kinji sauki zamu maidaki gida kinji ko? Karkiji tsoronsa zai duba ki ne uhum?" Mom ta faɗa tana bubbuga Aziza, dubata Nawaz ya yi ya fice cikin haushi.




      🐍🐍🐍🐍🐍




Tun shigan Azima dakin munir da niyyar gyarawa ba a sake ganin mai kama da ita ba, har dare, kuma cikin wani ikon Allah babu wanda ya nemeta,dan sun manta da ita,tunda sun san mai aikinsu ta gudu sun manta sun dauki sabuwa, sai wajan karfe tara Munir ya dawo shi da Baby, bayan sun yi magana da Zuby da Hajiya Baby ta wuce dakinta,Munir ma ya wuce nasa,yana shiga ya yi turuss yana ganin ikon Rabba, Azima ta yi ɗaya-ɗaya a kan gado ta bararraje an samu gado mai laushi bana kara ba, sai kwasar baccinta take cikin salama hankali kwance, gashinta da ya sha wanki sai kyalli yake yi duk ya baje ya rufe mata fuska, wani yawu muqut Munir ya hadiye yana fadin

"Kai daga ina wannan balarabiyan?" ya fada yana yin kanta ba tare da yayi dogon tunani ba shin aljana ce ko mutum.



       

       🍃🍃🍃🍃🍃



MOMYN AHLAN✍🏻

[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃


    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨

    (🐍 _Macizai ne_🐍)


    MALLAKAR.


*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*


SAHIBAR KAINUWA.


Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.


Sanarwa.

Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻


https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association


*____________________________________*


*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_


_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_


   🍃🍃🍃🍃🍃



*PAID.*

🅿️==3️⃣9️⃣↪️4️⃣0️⃣




Hannu yasa jikinsa na rawa yana lashe baki yana kwashe gashin da ya rufe mata fuska cikin bacci Azima ta ji mutum a kanta, bata gama tabbatarwa ba sai da taji saitin hannun mutum a wajan dukiyar fulaninta, nan da nan ta farga da abunda ke wakana a kanta, idonta ne ya sauya,    da tafin hannunta ta tokari kirjin Munir kamar kiftawar ido da bismillah sai ga Munir ya yi sama ya bugu timm da kasa!! Saurin tashi Azima ta yi,ta dauki mayafinta ta yi lullubi sannan ta yi kan Munir,tana zuwa ta shaƙosa da hannu daya ta haɗasa da bango,nan idon Munir ya yi waje yana so ya yi ihu amma baya so kannansa suji su rainasa, lallai yau ba shakka ya yi gamo da aljana a garin ɗan banzan son matan tsiya tun bai tsaya ya ga wacece ba ya afka mata ga shi tana neman kashesa,  lokuta da yawa Munir ya sha yiwa yaran aikinsu fyaɗe,da anyi kara kuwa uwarsu zata zuba kuɗi ta karbo ɗanta tace an masa sharri.



     Cikin zafin zuciya Azima ta kamo hannun Munir wanda ya taba mata kirji da shi, matse hannun tayi jikake ƙashi na haɗewa yana bada ƙaƙassƙasssƙass!! Ihu Munir ya sake na azaba, Hajiya da Zuby dake parlour suka ji ihun Munir da gudu sukayi dakinsa, a lokacin da ya yi ihu Azima ta sakesa ta koma gefe jin kafar mutane da gudu, kafin su shigo Azima ta duƙa kasa a gaban Munir, Hajiya da Zuby suna shigowa Munir ya yi saurin maida hannuwansa baya, Hajiya tace

"Munir ihun me kakeyi haka?"

"Ha...ji....ya...wa..ce..ce...wan...nan...yarinyar.." sai a lokacin suka maida kallonsu ga Azima da take duƙe tana murmushin mugunta ta cikin mayafi, tsaki Zuby tayi tace

"Mtswww Munir amma dai wlh kaji kunya,duk iya shegenka amma wannan yarinyar kake yiwa ihu? Sabuwar mai aikin da hajiya ta dauka ne fa, wlh nikam har na manta da ita a gidan,ke dan uwarki miye kikeyi a dakin nan tun rana har yanzu?" matse hannu Azima tayi tana cije baki, da kyar ta ce

"Da na shigo na manta abubuwan da Inna Lantana ta gaya mini nayi ne,kuma da nazo fita ban san ta inda zan fita bane shiyasa na zauna, shi kuma da ya shigo ya ganni sai ya tsorata" Hajiya ta ce

"Ba dole ba!, fuska a rufe kina dukar da kai, banza kawai maza ki tashi ki gyara masa dakin yanzun nan idan kin gama kije ki gyarawa Baby da Zuby nasu, sannan ni kuma kije ki wanke min toilet, ohh ina nufin bayi ko kewaye ku ke cewa oho,dalla tashi!!" Hajiya ta faɗa da tsawa suna ficewa a dakin ita da Zuby, Munir ya ce

"Kee dan ubanki! Dama ke mai aiki ce shine kika shaƙeni! Kin san waye ni kuwa?" waigowa Azima ta yi ta ce

"Kamar yadda kaima baka san wacece ni ba! Ka kiyaye! Bana gargaɗi sai dai zartar da hukunci!" tana gama fadi harta juya zata fita ya ɗan sake ihu yana maqale hannunsa, juyowa Azima ta yi ta dawo ta cafke hannu yayinda ta sake matsewa ta ware hannun ya sake sakin kara, hannun nasa ya dawo dai-dai ta ce

"Ban taba lalata abu na gyara ba! Sai dai idan aka gyara na b'ata!" tana gama fadi ta fice, wajan Lantana a kitchen taje Lantana tana ganinta ta ce

"Ahh Azima tun rana ina kika shiga haka?" abunda ta gayawa su Hajiya shi ta kara nanatawa Lantana daga nan ta hau tayata aiki suna girkin Azima taji tana bukatar watsa dafi a cikin abincin,amma kasancewar tasan Lantana zata ci yasa ta hakura da watsa dafin,bata taba jin bata son kisa ba sai a kan Lantana ko meyasa hakan oho,  bayan sun gama kowa yaci abinci suka gyara kitchen har sun kwanta Hajiya ta kwalawa Azima kira, cike da takaici da haushi Azima ta dauki mayafinta ta fice tayi dakin Hajiya, ko sallama ba tayi ba ta shiga Hajiya na zaune a gefen gado,tana ganin shigowar Azima kamar an bankota yasa Hajiya miƙewa da masifa

"Ke wace iriyar jahilace! Ƙidahuma bagidajiya! 'yar can cikin jeji kawai! ban gaya miki ki zo ki wanke mini bayi ba?" Azima na shirin magana Munir na kwala mata kira, Hajiya tace

"Maza je kiji me yake da bukata ki gama masa ki zo ki wanke min toilet dina yau din nan, ai babu ke babu bacci" fita Azima ta yi ta nufi dakin munir yana tsaye daga shi sai gajeran wando,kallonsa tayi ko gizau bata yi ba balle taji dari-dari dan ta gansa a haka

"Keee!! Banza 'yar jeji, gyara min gadona"

"Kaiiii!! Banza shanu ɗan iska ban gyarawa!" ta juya zata fita Munir yasa hannu ya fizgota ya ɗaura mata sannan ya tureta gado ya bita ya danne, wani gurnani Azima ta yi tare da rikiɗewa rabinta mutum rabinta macijiya! A haukace Munir ya tashi a saman kanta ya yi baya-baya ya faɗi a gado jikinsa na rawa, gashinta ta kwashe blue eye dinta ya bayyana ya ƙare rinewa

"Ban ce maka ka kiyayeni ba! Baka san wacece ni ba ko!?" 

Cikin shiɗewar numfashi sabida tsananin tsoro da firgici Munir ya ce

"Dama ke ba mutum ba ce!!?"

Murmushi Azima ta yi ta ce

" *RUWA BIYU!* Mutum Macijiya!"

"Dan Allah kiyi hakuri karki kasheni!"



    "Duk wanda ya ga kwayar idon Azima baya sake ganin wani!" tana fadin haka ta koma macijiya ta saresa a bayan wuya nan munir ya faɗi ya hau murkususu yana birgima har ya dai na! rai ya yi halinsa, sai da Azima ta ga ya mutu kafin ta zama mutum ta fice a dakin taja ta rufe shi, ta koma dakin Hajiya da take ta sababi, Azima ta ce Hajiya

"Ki ɗan jira a parlour na gama gyara miki dakin"

"Saura kuma karki gama da wuri ki ga yadda zanyi dake a cikin daren nan 'yar can cikin jeji kawai!" Hajiya ta faɗi tana ficewa, Hajiya na fita Azima ta kulle kofa ta hau gadon Hajiya ba daɗewa bacci ya kwasheta, Hajiya kuwa tana parlour tana jiran Azima ta gama gyara da fito yau ne gobe ne shuru,har bacci ya fara kwasar Hajiya, ta farka taje ta tura kofar ta jita a gangame! Bugawa Hajiya ta hau yi amma a banza har ta gaji, tana bugawa tana aunawa Azima zagi, dakin Zuby taje ta buɗe mata Zuby tace ita ba zata tashi ba ta riga da ta kwanta,haka ma Baby ita kam har da yiwa Maman tsawa ta tayar da ita a bacci, haka Hajiya ta dawo parlour ta kwanta a kujera nan ta kwana.




       Azima bata farka ba sai bakwai na safe tana tashi ta wargaza dakin Hajiya ta kwashi kudin dake dakin kafin ta buɗe dakin ta fito,nan ta ga Hajiya na bacci wani murmushi ta yi na gefen baki, dakin Lantana ta nufa taje ta sameta zaune tana karatun al'kur'ani mai girma, wani wawan jiri ne ya ɗibi Azima,Lantana ganin haka yasata rufewa ta tashi da sauri ta kamo Azima tana tambayarta lafiya? Azima ta ce

"Lafiya lau! Ga wannan kudi ke da mai jiran ƙyauren gidan nan(gateman) ku bar gidan nan ku koma garinku,ke yar wace gari ce?" 

"Ni 'yar can cikin kauyen kano ne, amma meyasa zamu tafi?'' cikin tsawa Azima tace

"Bana son tambaya zaku tafin nan ne ko zaku shiga sahun wa inda za a binne?" jin haka yasa Lantana karban kudi jikinta na rawa dan bata taba jin murya nai amo da firgici irin wannan ba harta kayanta tace ta yafesu dama tsumokara ne, ta ce "ki yafeni Hajiya Azima idan na bata miki sai wata rana" bata jira amsar Azima ba ta fice, ta  kai wa Mai gadi yana tambayarta miye tace masa kawai ya yi ta kansa, sai da Azima ta tabbatar da sun bar gidan kafin ta ja kofa ta koma, shiganta parlour ya yi dai-dai da farkawar Hajiya, bata yi wata-wata ba tasa hannu ta fizgi Azima ta gaura mata mari dai-dai sadda Baby da Zuby suke buɗo kofa dan lokacin haɗa musu tea ya yi, Zuby ce ta ce

"Hajiya me ya faru haka?" cikin kumfar baki Hajiya ta ce

"Wannan 'yar jeji ni zata bari na kwana a parlour?"

"A parlour kuma?" cewar Baby tana bin Azima da kallo da kanta babu dankwali sai gashinta da ya rufe mata fuska

"Ke ba magana ake miki bane?" cewar Zuby tana hararan Azima dake tsare jikinta na tsuma, hannu Baby tasa taja gashin Azima yana kwashe na fuskarta nan Azima ta ware kwayar idanunta a kan Baby,wani ihu Baby ta saki tana ja da baya, Zuby tasa hannu zata juyo da Azima dan ta ga me Baby take yiwa ihu kafin ta juyo da Azima, Azima ta juyo ta hura mata baƙin hayaki a fuskarta, kafin su farka tuni Azima ta yi juyi ta zama rabi mutum rabi macijiya, fadin yadda su Hajiya suka shiga firgici ba zai misaltu ba, ihu suke yi suna kiran Munir,dariya Azima ta kyalkyale da shi ta ce

"Ya ri  ga ku mutuwa! Yanzu a cikinku wa zai bisa na biyu? Bari na kawo muku shi ku gan shi" Azima ta faɗa tana shiga dakin ta naɗo munir da jelarta ta zo ta jefar da shi a gabansu a tsakiyar parlour, wani kuka su zuby suka saka ita da baby hajiya kuwa jiki na kyarma ta takure jikinta gefe daya.




        A tsawace Azima tace

"NA CE A CIKINKU WA ZAI BISA NA BIYU!!?" cikin kuka da tashin hankali suka hau fadin tayi hakuri karta kashesu basu so su mutu, Azima tace

"Akwai abu daya da zan muku, ruwa zaku sha? Ko abubuwan da kuke sha a robobi zaku sha?" cikin kuka da majina da zufa suka ce ruwa, Azima tasa hannu ta janyo ruwa ta zuba a kofi uku ta ce

"Duk wanda baya son mutuwa ya sha wannan ruwan!" jikinsu na rawa suka dauka suka kafa baki suka kwankwaɗe suna kan bata hakuri, kamar da minti biyu tsakani Hajiya ta hau tari tana rike wuya, da sauri Zuby ta tashi tana fadin Hajiya meya sameki,nan ita ma ta hau riƙe wuya tana tari, Baby ma haka, tari sosai suke yi jini na fita baki da hanci, Azima ta miƙe ta ce

"BANA MANTUWA! BANA YAFIYA! NA RIGA DA NA ZUBA DAFI TA YATSAR HANNUNA!" tana gama fadi ta shiga ta dauki kayanta na fulani da Lantana ta wanke mata ta saka ta fice ta bar gidan.




         🍃🍃🍃🍃



Kwanan Aziza biyu a asibiti jikin nata alhamdulillah duk da da ace taso zata iya warkar da kanta amma bata so ta sakawa su Mom da Sultana shakku a ransu su fara zarginta, sannan yanzu idan tace zata gudu bata san duniyar da Azima take ba kuma tana ji a jikinta duk inda Azima take bata shuka alkairi, abu biyu ne ya haɗe mata waje guda ya jagula mata lissafi, bata san taya zata fara neman Azima ba tunda basu al'karya daya, sannan bata san wani hali iyayenta suke ciki ba,duk da tana da yaƙini a kan Baffa zai kula da Hajja sosai shima zai kula da kansa, tana zaune tana tunani, wani dabara ne ya faɗo mata, wannan dabara kuwa shine ta fara yawon bin garurruka! duk garin da suka haɗe da Azima idan ta lumshe ido zata iya hangota ta cikin tauraronsu, da wannan tunani ta samu karfin guiwa,lumshe ido tayi ta shafi tafin hannunta amma bata ga Azima ba, a fili ta ce

"Hakan na nufin bamu gari daya kenan, wannan hajiyar (Mom kenan) ta kira sunan wannan yankin da kaduna ko? Ina gani gwara na tambayi wannan yarinyar tata sunayen yankuna sabida naje na dudduba Azima, amma kuma kafin na tafi dole ina bukatar kudi, hakan yana nufin dole na yi musu aiki dan na tara kudin neman Azima? Idan kuwa haka ne Banju ya cuci rayuwarmu,ga shi wahalar a kaina da Baffa yake karewa" ta karasa maganar da sakin kukan tausayi, tana sakin kukan su Mom da Sultana suna shigowa.



     Ganin tana kuka yasa suka karaso wajanta da sauri suna tambayarta ko akwai inda yake mata ciwo ne? ta girgiza musu kai alaman a'a, Mom ta ce

"Yarinya? Kiyi hakuri kodayaushe kina cikin kuka, ina yan uwanki suke? A wani ruga kuke a garin yola idan yaso gobe sai a maidaki" jin haka yasa Aziza kara sakin sabon kuka,inaa ai ba zata so ta koma ba tare da burin Baffa na su dawo tare da Azima ba, mafita daya ne shine kawai ta yi karya,cikin kuka ta ce

"Yan fashi ne suka fada rugarmu suka kashe mana kowa, nima da kyar na sha,dan Allah Hajiya ki taimaka mini na dinga yi miki aiki kina biyana,yanzu idan na barku ban san inda zan hadu da mutane nagari kamar ku ba dan Allah Hajiya!" Aziza ta fada tana kuka sosai,jikin Mom ne ya yi sanyi sosai, Sultana ma kwalla ya cika a idonta ta kalli Mom ta ce

"Mom mu dauketa kawai,tunda dama kinga Haule ta yi aure,ita wannan ma zata jima " Mom ta ce

"To shikenan kira mana wani Dr ya zo ya rubuta mana sallama,dan munyi waya da Nawaz yace sai gobe ko jibi zai dawo,kuma yace idan har jikin nata da sauki mu koma gida, to gwanda gidan dai zaman asibiti ba dadi garesa ba"

"To Mom" Sultana ta fice bata jima ba suka dawo da wani likita ya rubuta musu sallama suka yi gida, dakin masu aiki dake kasa wajan cikin parlour bayan step dakin mai aikinsu na da Haule wacce tayi aure,bama iyakar Haule ba duk masu aikinsu nan ne dakin da suke zama,babban daki ne dasu babban gado da wardrope da toilet da komai da komai, Sultana ce ta nuna mata yadda zata yi amfani da komai,bayan ta nuna mata Aziza ta kalleta ta ce

"Na gode Anty Sultana" Sultana ta yi murmushi ta ce

"Ba komai mai kyau, amma meyasa kike son rufe fuskarki? Har yanzu baki saba damu bane?"

Cikin in-ina Aziza ta ce

"Inada matsalar ido ne, tun ina yarinya bana son haske, sannan bana iya kallon mutane da idona shiyasa mahaifiyata ta bani wannan mayafin ina lullubi da shi, gashi na kuma na fiddo da shi dan ya rufe min daya idon da zan dinga ganin hanya"

"Ayya Subhanallah! Idan Brother ya dawo zan gaya masa sai ya duba miki idon, watakila idan aka dace sai ya miki magani"

Da sauri Aziza ta ce

"A'a Anty Sultana karki gaya masa halittatace a haka aka haifeni" 

"To shikenan,bari na bar ki ki huta sai na shigo anjima,idan kika warke sosai akwai abunda zan dinga koya miki,ina sonki da ƙawa! kinga bana da ƙawa bana shiga hidimar mutane amma ke kin shiga raina" murmushi kawai Aziza ta yi dan ita kadai tasan yaƙin da yake gabanta, tashi Sultana ta yi tana fadin

"Bari naje na kawo miki wasu kayana ki saka yanzu kiyi wanka duk da nasan kayan zasu miki yawa, amma ki canza na jikinkin nan" Aziza ta amsa da to na gode sosai, Sultana tana fita Aziza tayi shuru tana saƙa da warwara, zuwa can ta mike zata shiga bayi har ta manta da ciwon kafarta sai ji ta yi ta takesa, zafi taji ta saki kara sannan ta koma ta zauna tana fadin

"Ba zan iya jurewa ba" hannu tasa ta shafe wajan nan kafarta ya dawo dai-dai sannan ta shiga ta yi wanka kamar yadda Sultana ta nuna mata amma bata wanke kanta ba,tana fitowa Sultana na shigowa ta kalleta ta ce

"Ba ki wanke kanki ba? To ki bari karki wanke,idan kikaji sauki sosai sai muje a wanke miki, wannan gashin naki ai sai wajan masu salon, yanzu ga wa innan kayan ki fara lallabawa da shi Mom ta ce zata siyo miki wasu" godiya sosai Aziza tayi,ta dauki wani dogon abaya ta saka ya mata kyau duk da ya mata yawa tasa ta dau hijabi ta tada sallah,ta jima tana addua Allah ya bata mafita a kan wannan babban lamari nasu, kafin sultana ta shigo ta kirata ta fito taci abinci.




        🐍🐍🐍🐍



*KUNTAU.*



wani hamshakin gate Azima ta tsaya tana kallon gate din, ganin tsaruwarsa da haduwarsa zuciyarta ne ya raya mata wannan gida taji gidan ya kwanta mata a rai,kuma dole uwar naki sai ta zauna a wannan gida ko ana ha maza ha mata, da wannan tunani ta yi gate din ta hau kwankwasawa.



       🍃🍃🍃🍃


Post a Comment for "AZIZA DA AZIMA 31-40"