AZIZA DA AZIMA 11-20
FREE..*
🅿️==1️⃣1️⃣↪️1️⃣2️⃣
Da washe gari asubanci yankin jimo suka yi, takwas na safe su na yankin kwana,a maƙabarta jikin ƙabarin Jarman macizai, kuka sosai sarki Haruna yake yi shi da jama'ar yankinsa wa inda suka zo, an sha musu mutuwa amma farat ɗaya na Jarman macizai wanda yake jarumi a yankinsu ya gigita
tunaninsu, haka suka ƙarashi koke-kokensu suka gama dan ba dawowa zai yi ba, haka jamar'ar kwana suka taru ƙwansu da ƙwarƙwatansu suka sake yiwa yankin jimo ta'aziyya tare da ban hakuri, daga fuskarsu kawai zaka kalla ka gane su na cikin mugun damuwa da tashin hankali, babu yadda yankin jimo suka iya dole suka hakura tunda dai Jarman Macizai ba dawowa zaiyi ba ya tafi kenan, sai dai fatan Allah ya yafe masa.@@@@@
Bayan kwana biyu an gama ƙuri'u, inda aka samu sab'anin ra'ayi, jama'ar da suka fi rinjaye shine wa inda suka ce aje yankin ja'i neman taimako kar aje yankin tudu a fara zuwa yankin ja'i, dan ba za a zauna da matsala ba tare da an bukaci taimakon Allah da wa inda zasu shawo kan matsalar ba, shi dai Baffa shuru ya yi bai ce kanzil ba, haka aka sa mai rubuta wasika ya rubuta aka yiwa yankin ja'i aike da shi.
🍃🍃🍃🍃🍃
Sarkin fulanin yankin ja'i na zaune Maga Isar da Sakon yankin ya zo ya zube a gabansa yana fadin
"Allah ya taimakeka! Hakika a yau nasara tamu ce" wazirin fulani ya ce
"Maga Isar da Sako meke tafe da kai ne?" murmushi Maga Isar da sako ya yi ya ce
"Hakika yau muke da nasara, sako ce ta isko mu daga yankin kwana! su na cikin bala'i shine suke bukatar taimako daga yankinmu, yanzu haka ga takwabi sarkin kwana wato Chubaɗo ya aiko mana da shi alaman sun sakar mana igiyar, munyi nasara su sun faɗi, wannan takwabi da Chubaɗo ya aiko mana da shi alama ce na sun duƙawa wannan yanki tamu"
Sarkin fulanin yankin ja'i ya ce
"Maga Isar da sako, zai fi kyautuwa da kayi mana bayani dalla-dalla, ko kuma ka buɗe wasikar da suka aiko da shi ka karantawa dukkan wanda yake zaune a wannan fada dan jin meke tafe da sakon"
Ƙara russunawa Maga Isar da sako ya yi ya buɗe wasikar ya fara karantawa kamar haka.
" _ASSALAMU ALAIKUM, SAKO CE DAGA YANKIN KWANA IZUWA YANKIN JA'I, MUNA FATAN WANNAN SAƘO TA ISA GAREKA SARKIN FULANIN JA'I WATO SARKI JAWO TARE DA MAI UNGUWAR YANKIN JA'I WATO MAI UNGUWA SODANGI, A YAU MU YANKIN KWANA MUN WAYI GARI CIKIN RUƊU DA RUƊANIN TASHIN HANKALI DA RASHIN ZAMAN LAFIYA, WA HAKA NE MUKA RUBUTO SAƘO DAN YA YI TATTAKI ZUWA GA YANKIN JAMA'AR DA SUKE JA'I GABAƊAYA, AMADADIN NI SARKIN FULANIN YANKIN KWANA CHUBAƊO DA MAI UNGUWAR YANKIN KWANA ORI, DA ARƊO DA TSOHON SARKIN FULANI MANDI, DA MAGAJI BAWA DA DUK WANI WANDA YAKE YANKIN KWANA MUNA NEMAN TAIMAKONKU! MUN GAMU DA IFTILA'IN MACIZAI WANDA SUKE KASHE MANA MUTANE! AN KASHE DUK WASU MASU KAMA MACIZAI NA YANKINMU! MUN NEMI TAIMAKON YANKIN JIMO INDA SUKA TAIMAKA MUKA ROƘI ALFARMA DA JARMAN MACIZAI YA KAWO MANA DAUKI WANDA SHI MA AKA KASHESA KWANA BIYU DA YA WUCE, GA WANNAN TAKWABIN DA MUKA AIKO YANA NUNI NE DA MUN ZUBAR DA MAKAMAN YAƘIN GABAR DAKE TSAKANINMU NA TSAWON LOKACI MUN DUƘAWA YANKINKU, MUN YARDA KUNYI GALABA A KANMU! BA DAN KOMAI BA, SAI DAN MUNA NEMAN ALFARMA DA A TAIMAKA MANA DA TAIMAKON *INNU MACIJI* MUN SAN SHI KA ƊAI NE KAWAI ZAI IYA, TUNDA HAR TA ALJANUN MACIZAI DA MAYU DA ALJANU DUK YANA FAƊA DASU, DAN ALLAH SARKI JAWO DA MAI UNGUWA SODANGI A TAIMAKA MANA, KANMU A ƘASA! A YAU MUN YARDA YANKINKU YANA SAMAN TAMU, SAƘO DAGA YANKIN KWANA, SAI MUNJI DAGA GAREKU, MUN GODE_"
Wani murmushi sarkin fulanin ja'i ya yi yana mai kallon Maga Isar da Sako,yayinda jama'ar ja'i suka hau murmushin nasara, dan sun jima suna neman cin galaba a kan yankin kwana amma sun kasa, hakan ya samu asali ne da nasabar da Baffa yake da shi,amma wai yau sai ga shi su da kansu suke cewa sun zubar da makaman yaƙinsu? Wannan ai nasara ce babba a garesu, wakilin yankin ja'i ya ce
"Allah ya taimakeka! Ai mu nasara ce ta tako da kafarta tazo mana har gida, wai shanu daga sama gasheshshe!"
Wazirin ja'i ya ce
"Ai ranka ya daɗe abunda muka jima muna nema ne, shine suka sakar mana shi yanzu,tun yaushe muke neman nasara a kan yankin kwana amma mun kasa samu sabida Magaji Bawa" wazirin fulanin ja'i ya karasa maganarsa yana murmushi, wakilin fulanin ja'i ya kuma cewa
"Ranka ya daɗe kar mu b'ata lokaci kawai mu amsa da cewa e mun amince da bukatarsu" girgiza kai garkuwan fulanin ja'i ya hau yi ya ce
"Shekara da shekaru ake ɗibi ba daɗi tsakanin yankinmu da yankin kwana, rana daya tak su aiko mana da sako su ce sun janye anya babu lauje cikin naɗi? A gaskiya ni ban yarda da yankin kwana ba, sai dai wani shirin kawai suke yi ta yadda zasu shafemu!" garkuwan fulanin ja'i ya karasa maganarsa yana haɗa rai sosai, sarki Jawo ya ce
"Bana tunanin haka! Idan ma kuma hakane karka manta muna da fidda kunyar gasa a yankin nan wato *INNU MACIJI* wanda a halin yanzu shi suke bukatar taimakonsa,Innu Maciji dai duk faɗin yankuna sun san shahararsa! Tunda shi ya lashe kambu na daya a gasar fidda gwajin macizai! Innu Maciji bai ci sunansa a banza ba! Tunda har aljanun maciji da mayu yana yaƙi dasu kuma ya ci nasara, dan haka idan muka tura Innu Maciji dan zuwa taimakawa yankin kwana kamar yadda suka bukata yaje ya dawo ya kake tunanin martaban da yankin ja'i zai samu tare da karramawa daga sauran yankuna?"
Ajiyar zuciya Garkuwan fulanin ja'i ya sauke tare da kallon Sarki Jawo ya ce
"Ranka ya daɗe bana so mu manta da abu daya, a lokacin da aka raba kambu Magaji Bawa ya jima da sauke duk wata gab'ob'in baiwa da yake da shi, na san idan har zaka manta da tarihin Magaji Bawa da Tsohon sarkin ja'i ya baka ba zaka manta da sunansa da ya shahara a sauran yankuna ba, *GWARZON DAFIN MACIZAI!!* ka tuna?" Garkuwan fulanin ja'i na furta wannan kalma sai da mutanen da suke wajan suka firgita, Wakilin Fulanin Ja'i ya ce
"A gaskiya na so na yarda da maganarka Garkuwan ja'i! Me yasa Magaji ba zai yi wani abu a kai ba da zasu dinga bukatar taimakon yankuna! A da shi Magaji a ina ne bai yi taimako ba, gaskiya maganarka abun dubawa ce" Maga Isar da sako ya ce
"Amma shekaru ashirin Magaji Bawa ya ce ya daina duk wani abu na yaƙe-yaƙe da yake yi, bayan ya sauka ne shine aka naɗa Firi jarumin yankin kwana ko ba haka bane? Ni a tunanina da ace Magaji Bawa zai iya wani abu a kai da ba za a zo neman taimakon Innu Maciji ba har su russunawa yankin nan"
"Amma dai kun san da cewa duk wata shahara da Innu Maciji zai yi ba zai taba kamo ko da tsilen takalmin Magaji Bawa ba ko?"
Maga Isar da sako ya ce
"Ni dai bana tunanin haka gaskiya, da ace zai iya da ba zasu zo nan ba" Sarki Jawo ya ce "tabbas haka ne maganarka Maga Isar da sako, yanzu abunda za ayi,aje a cewa mai unguwa Sodangi akwai magana ta gaggawa, a biya a kira Innu Maciji, a rubutawa yankin kwana da cewa su tsumayemu zuwa gobe idan muka gama shawara da tattaunawa zamu tura musu da sako idan ma mun amince ko akasin haka" Sarkin fulanin Ja'i yana gama magana ya miƙe tsaye ya bar wajan.
🍃🍃🍃🍃
*YANKIN KWANA*
Maga Isar da sakon yankin kwana ne ya gama karanta wasikar da yankin ja'i suka aiko musu da shi, sarki chubaɗo ya ce
"Ba komai yau da gobe duk daya ne a wajan Allah, Allah ya nuna mana" mai Unguwa Ori ya ce
"Amma Allah ya kara maka yawan rai, anya yankin ja'i zasu yarda su taimakemu kuwa? Gani nake kamar su na neman hanyar da zasu wofantar da bukatarmu ne, tunda mun sanar dasu yankin jimo sun rasa jarman macizai, da mun sani da bamu rubuta musu da cewa an kashe jarman macizai ba" Arɗo ya girgiza kai ya ce
"Maganar duniya bata b'uya, gwanda dai da muka gaya musu gaskiya zai fi, balle kuma abu babba irin haka ya faru ace manyan yankuna basu sani bane? Ai hakan ma ba mai yuwa ba ce, dan naji ance yankin gangare da yankin jauro da yankin ulela da yankin nasare duk sunje yiwa yankin jimo ta'aziyyar jarman macizai"
Sarki Chubaɗo ya ce
"Mu jira har zuwa goben muji sakamakon abinda zasu ce" Arɗo ya yi murmushin karfin hali ya ce
"Bana tunanin yankin ja'i zasu wofantar da bukatarmu! Abunda muka jima da sanina suna neman yankin kwana ta duƙa musu, sai ga shi laluri tasa duk taurin kan da fulani ke da shi mun russuna musu da muka ji uwar bari, dan muna da bukatar mu san waye ba mutum ba a yankin nan! WAYE MACIJI! a yankin nan! Dole azo ayi gwaji dan a fidda zargin juna a zukata, gwanda a nuna mana inda matsalar take mu kuma mu san ta inda zamu shawota"
Aka amsa da haka ne,nan dai suka gama tattaunawa suka ajiye maganar tasu akan su saurari yankin ja'i.
Bayan an watse a fadar Sarki Chubaɗo Arɗo da Baffa ne suke tafiya a hankali su na magana kasa-kasa,Arɗo ya ce
"Magaji, fatan kana sa a ido sosai a kan su AZIMA DA AZIZA?"
"E Arɗo ina iyakar bakin kokarina wajan saka musu ido, ita Azima baka iya gane gabanta,gwanda Aziza, gasu dai a tare aka haifesu amma halayyarsu ta sha bamban, a kwana biyun nan basu kula juna, Jumala sai korafi take yi a kan nayi musu magana ko me ya haɗa su, amma ban dauki hakan da mahimmanci ba sabida ba shi ya kamata na kula ba, kare rayukan yankin nan shine abu mafi mahimmanci" Arɗo ya gya ɗa kai ya ce
"Tabbas hakane, ba mamaki sun ɗan yi faɗa ne tinda ana samun irin haka" Baffa yace
"Eh nima haka nake tunani Azima bata da dadi ko kadan, Arɗo barin wuce gida"
"To a gaida Jumala da Azima da Aziza"
"Zasu ji" Baffa ya fada tare da yiwa Arɗo sallama.
🍃🍃🍃🍃
Tun safe Aziza ke rafin jimulo tana wanke kayan Hajja da na Baffa, Azima kuwa dan Aziza na rafin jimulo yasa ita bata je ba tana gida, abinci Hajja ta ɗora amma Azima ta hana abincin dahuwa, har la'asar tana zaune a kan tabarma kaba tana saƙe wani igiyoyi, Hajja ta kalleta ta ce
"Wai ni kam Azima wannan saƙe-saƙen da kikeyi na miye ne? Tun safe kike zaune a wajan ba sallar azahar bare la'asar ki tashi kiyi sallah" ba tare da ta dago ta kalli Hajja ba ta ce
"BANA SALLAH!" 😏
Baki sake Hajja ta kalli Azima ta ce
"Kina fashin sallah ne?" kafin Azima ta bada amsa Aziza ta yi sallama da kaya a hannunta ta shige bukkan Hajja ta ajjiyesu sannan ta fito ta duƙa ta ce
"Sannu da gida Hajja"
"Yawwa sannu Azizatuna, kin dawo?"
"E Hajja na dawo"
"Ayya Aziza maimakon idan kin wanke kayan ki dawo gida idan ya bushe anjima a kwaso shine kika zauna har yamma a rafi ba tare da kin dawo gida ba? Ga shi haka kika fita ba ki ci komai ba" murmushi Aziza ta yi a ranta ta ce
"Idan na so zan iya wanke kayan nan na busar da shi a lokaci guda sabida karfin dafin da nake da shi,amma bana son hakan nafi son na samu ladar iyayena" a fili kuma ta ce
"Wlh ba komai Hajja bana jin yunwa ai"
"Allah ya miki albarka Aziza ke da yar uwarki, kinyi sallah ne?"
"Amin, E Hajja nayi sallolina a rafin jimulo ban bari lokaci ya shige ba" Hajja ta kalli Azima ta ce
"Azima kince baki sallah kina fashi ne?" da blus eyes dinta ta dago ta kalli Hajja ta ce
"Ni sallah ne kwata-kwata bana yinsa a rayuwata!" dam!dam!dam! Ƙirjin Hajja ya bada ta b'ata shuru tana bin Azima da kallo, da kyar ta buɗe baki zata yi magana amma Azima bata jira hakan ta faru ba dan kamar ƙiftawar ido ta tashi tare da tattare dogon igiyar da ta saƙa ta shige bukka, Aziza ganin yadda hankalin Hajja ya tashi da maganar da Azima ta faɗa ya sakata faɗin
"Karya take yi Hajja, kin san halinta bata damuwa da maganar da zata faɗi zai yi maka dadi ko akasin haka faɗi kawai take yi" sai a lokafin Hajja ta sauke ajiyar zuciya, Aziza ta ƙwaƙulo murmushi dan sallah kam Azima baya yi, ta ce
"Hajja ba a gama abinci ba?"
"Wollah Aziza ban san wani irin abinci yau nake dafawa ba, tin rana na ɗora kafin ayi azahar amma har yanzu ta ƙi nuna" shuru Aziza ta yi tana kallon tukunyar kasan na wani sakanni kafin ta ce
"To Hajja je ki ciki ki huta yanzu zan karasa"
"A'a Aziza yanzu fa kika dawo daga...."
"Ohh dan Allah Hajja ki je ki huta" murmushi Hajja tayi tana shigewa bukka, Aziza ta buɗe abinci ta ga rashin dahuwarsa yana da nasaba da sa hannu da Azima ta yi, rintse ido ta yi ta buɗe nan idonta ya koma fari sosai ta zaro harshenta ta hura wani hayaki a cikin tukunyan, nan kalar abincin ya canza alaman ya dahu, sannan ta rufe tana miƙewa tsaye ya yi dai-dai da shigowar Baffa da kuma fitowar Hajja daga bukka, sannu da dawowa suka masa, Baffa ya amsa yana zama a inda Azima ta tashi, kallon baƙin igiyar da Azima ta yi saƙa da shi ya gani guntun, dauka ya yi a fili ya ce
"Zaran saƙar dana? me yake yi a gidan nan? Wa ya kawo?"
🍃🍃🍃🍃
COMMENTS AND SHARE
BY MOMYN AHLAN
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
*NA GAISHEKI SIS NA🥰 SURRY BABY, ALLAH YA BAR MIN KE.*
*AZIMA DA AZIZA GRP NA GAISHEKU😂 MASU MAFARKAI DA TSORATA NA JINJINA MUKU, A CI GABA DA CHAPTAWA.*🤙🏻
*FREE..*
🅿️==1️⃣3️⃣↪️1️⃣4️⃣
"Zaran saƙar dana kuma?" Hajja ta faɗa tana kallon hannun Baffa da ya riƙe zaren yana kalla, Aziza ce ta matso kusa da Baffa ta duƙa ta ce
"Baffa me zaran ya ƙunsa?" shuru Baffa ya yi na wasu lukota kafin ya ce
"Ba ƙaramin hatsari wannan zaren yake da shi ba, ana amfani da shi wajan yaƙi! Ko kuma a ɗaure takwabi da shi, duk wanda aka sara ko aka yanka da takwabin da aka d'aure da shi to sunansa gawa! Walau mutum ko aljan! " a firgice Aziza ta ce
"Kenan mutum mutuwa zai yi?"
"E Aziza, wa ya kawo zaran nan gidan nan? Sannan ta ya aka samo shi? Dan nasan ba a samunsa nan kusa sai an je can cikin jejin lore, wanda wannan jeji tun kafuwarsa shekaru aru-aru babu wani ɗan adam din da ya taba zuwa idan ba ni ba" Hajja ta ce
"Ai kuwa dai Azima ce na ganta da shi dan tun safe take zaune a inda ka tashin nan take saƙa shi,bayan ta gama ta shige ciki, bata jima da shiga ba ka shigo" da sauri Baffa ya miƙe tsaye ya ce
"Azima! Azima! Azima!?" ya kwala kiran sunanta da karfi, Aziza ta ce
"Bari na kirata Baffa" cikin faɗa Baffa ya ce
"Nan da bukka ta ce bata jin kiran da na mata?" Hajja ta ce
"Ayye Baffan yan biyu ka bi a hankali mana, watakila bacci ne ya kwasheta Aziza kirawota" Baffa ya ce
"Ke da kika ce ina shigowa bata jima da shiga ciki ba shine har bacci zai kwasheta?"
"Ai Azima bata da wuyan bacci" cewar Hajja, shi dai Baffa shuru ya yi tare da gyara tsayuwarsa ya maida hannunsa baya yana jiran fitowar Azima.
Tana kwance a gadon kara, rabin jikinta macijiya sai juyi take yi kanta a hargitse, Aziza ta shigo da sallama ko amsawa Azima bata yi ba, Aziza ta ce
"Ba ki jin Baffa na kiranki ne?"
"Mtswwwww! Na ji mana, tunda dai ni ba kurma ba ce! Je ki ce ba zan zo ba!" a fusace Aziza ta sa hannnu ta janyo wuyar Azima ta ce
"Wallahi! Wallahi! Wallahi! Kinji na rantse miki ko? To sai kinje, kuma dole ki ba wa Baffa amsar tambayoyin da zai miki, za ki tashi ne ko sai na b'ace dake a dakin nan na wujijjigaki!?" Aziza ta karasa maganar idonta da fatar jikinta suna canza kala, ganin haka yasa Azima miƙewa fuuuu ta fice, rufe ido Aziza ta yi ta dawo dai-dai sannan ta bi bayan Azima, a tsaye ta sameta Baffa na tuhumarta inda ta samo zaren sakar dana, cike da rashin tsoro da rashin kunya ta ce
"A inda ake samu na samo!"
"AZIMA!!!" Aziza ta faɗa a tsawance ta yi kanta dan ta kai mata mari, da sauri Hajja ta ja hannun Aziza sannan ta fashe da kuka, murguɗa baki Azima ta yi ta fice a gidan ma gabadaya, Baffa kuwa suman tsaye ya yi, Aziza kuma tana lallashin Hajja dake kuka.
Cikin kuka Hajja ta ce
"Wai ni meke shirin faruwa dani ne kam? Me yasa Azima ta zama haka? Kwata-kwata yanzu bata shakkar gaya mana magana! Aziza dame ku ke so naji? Idan ba ki taimakawa yar uwarki ki gyara mata halinta wa zai iya yin hakan?" Hajja ta ci gaba da kuka, Baffa kuma bukka ya shige ya zube a bakin gadon kara jikinsa na rawa, hakika jejin lore ɗan adam baya shiganta ya fito lafiya, duk ɗan adam din da ya shiga jejin lore to sunansa gawa! Shi ma sanadiyyar shigarsa jejin lore ya yanko zaren saƙar dana sadda zasu gwabza da Banju ne, rass! rass! rass! gaban Baffa ya bada nan zufa ta shiga tsatstsafo masa ta ko wace kusurwar gashi dake gangar jikinsa, a fili ya ce
"AZIMA BA MUTUM BA CE! TAYA ZAN GWADATA NA GANE HAKAN DAN NA WARKARWA ZUCIYATA TANTAMA DA ZARGI!? INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN! YA ALLAH KASA KAR ABUN DA NAKE KWANA NAKE TASHI DA SHI YA ZAMA GASKIYA!" Baffa ya karasa maganarsa hannunsa a sama hawaye na gangarowa.
Da kyar Aziza ta ɗaga Hajja ta shigar da ita bukkarta tana lallashinta amma ina Hajja ta kasa tsaida hawayenta, kasa juran kukan nata Aziza ta yi ta miƙe a hankali ta fita zuwa randar kasar dake tsakar gidansu ta ɗibo ruwa a kwarya ta bude bakinta ta zuba abu a ciki sannan ta koma ta ba wa Hajja, ƙin karba Hajja ta yi ta ci gaba da kuka, Aziza ta ce
"Dan Allah Hajja kiyi shuru ki daina kuka, kin ga gidan nan bamu da sauran ganyen magunguna balle na haɗa miki ki sha idan kanki ya fara ciwo, zan yiwa Azima magana ga ruwan nan ki sha zuciyarki ta yi sanyi" da kyar Hajja tasa hannu ta karbi ruwan ta sha, tana shan ruwa ko minti uku bata yi ba, ta zube a jikin Aziza, hawaye ne masu zafi sosai suka zubowa Aziza a fuskarta a fili ta ce
"Kiyi hakuri Hajja ki yafe min ba zan iya ci gaba da kallon kukanki ba, baccinki shine mafi alkhairi, tun a yau da ba ki san su waye mu ba kina irin wannan kukan ran da kika sani za ki hadiyi zuciya ne Hajja? Ina ba zan bari hakan ta faru ba! Ba zan iya rasaki ke da Baffana ba! Zan ci gaba da boyewa tare da dakatar da yar uwata, ko da kuwa zamu kashe juna" Aziza ta karasa maganarta tana sake rungume Hajja, ta sha kuka sosai kafin ta gyarawa Hajja kwanciya ta fita.
sallama ta yi a bukkan Baffa, da sauri Baffa ya share hawayensa ya ce
"Shigo Aziza" cikin natsuwa ta shigo,zama ta yi kusa da kafarsa ta ce
"Baffa kuka kake yi?" girgiza kai Baffa ya yi ya ce
"A'a ba kuka nake yi ba Aziza" shuru Aziza ta ɗan yi kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Baffa
ina so na san meke ƙunshe da wannan zaren da Azima ta saƙa"
"Me kuma kike so ki sani bayan wanda na gaya miki Aziza? Hatsarin da ke cikin wannan zaren ba zai faɗu a baki ba tsananin yawanta, da ace za a dauki kwaya ɗaya tak! A jefata a cikin rafin jimulo, ina mai tabbatar miki duk wanda ya sha ruwan wannan rafi zai mutu!" dam! dam! dam! gaban Aziza ya bada nan ta shiga saƙe-saƙe a ranta tare da tunane-tunane, shin wa Azima take son kashewa da wannan zaren? *"BAFFA"* wata zuciyar ta bata amsa da sauri ta miƙe tsaye a firgice tana zare ido tare girgiza kai gami da fadin
"A'a karya ne! Ba zai yu ba! Ba zan bari hakan ta faru ba!" ganin yadda ta ruɗe lokaci ɗaya ne yasa Baffa tashi da sassarfa ya kama hannunta ya zaunar da ita ya ce
"Aziza natsu mana! Tsaya...kina ji? Menene? Gaya mini? Miye ba za ki bari ya faru ba?" kuka Aziza ta fashe da shi mai tsanani tana kwanciya a jikin Baffa, sosai hankalin Baffa ya tashi yana tambayar Aziza meke faruwa!.
Cikin kuka Aziza ke faɗin
"Me yasa! Me yasa! Me yasa!" da kyar Baffa ya shawo kan Aziza ta yi shuru ta daina kuka, Baffa ya ce
"Aziza meke faruwa ki gaya min gaskiya karki boye min komai, ni mahaifinki ne" saita natsuwarta Aziza ta yi ta ce
"Baffa, haihuwarmu ta yi muku rana?"
"Subhanallahi! Wannan wace irin magana ce kike faɗi Aziza?"
"Baffa kukan da Hajja ta yi a kan Azima dazu bazan sake bari hakan ta faru ba, ba zan sake bari ba!" ajiyar zuciya Baffa ya sauke,ita kuwa Aziza ta yi hakane dan kawar da shakku a zuciyar Baffa, shuru na ɗan wani lokaci ne ya ratsa wajan kafin Aziza ta ce
"Amm Baffa? Taya za a lalata zaren saƙar danar da yake hannu Azima?"
"Wannan ba shi bane abunda nake tunani Aziza, yadda aka yi Azima ta samu zaren nake tunani"
"Amm amma Baffa ta ce inda ake samu ta samu! Ya matsayin hatsarin jejin lore yake?"
"Aziza faɗin hatsarin jejin lore ba zai yu ba, dan yafi karfin ki fasalta shi da komai, taya har Azima zata shiga wannan ƙasurgumin jejin ta fito tana yar adam? Wannan shine tambayar da nake yiwa zuciyata amma na kasa samun amsa, ban san meke shirin faruwa da mahaifana ba"
"Baffa ka rabu da maganar Azima, kasan wani lokaci ba hankali gareta ba, yawwa kuma Baffa na mance ne ban gaya maka ba, Azima kamar tana da aljanu! Dan cikin dare sai na dinga ji kamar tana ta buge-buge da sambatu ita dayanta, Baffa na tabbata su ne suke saka ta rashin kunya,kuma ba mamaki karya take yi ba ita taje jejin lore ba, sai dai idan aljanun ne suka je suka kawo mata, ka yarda dani Baffa gaskiya nake gaya maka" Aziza ta karasa maganarta tana riƙo hannun Baffa, jinjina kai Baffa ya yi ya ce
"Kenan wani irin aljanu Azima ke da shi? Wanda har zasu iya kawo mata zaren saƙar dana? Me zata yi da shi? Kuma har tasan yadda ake saƙata?" zare ido Aziza ta yi ta hau rawar murya tare da in'ina
"Amm....eh.....umm....ohh...Baff....Baffa ....kar...ka...da..mu...da...Azima...ni nan zanji da ita, zan mata hayaƙin aljanu zata warke da yardan Allah na san ka yarda dani ko Baffa?" murmushi Baffa ya yi yana jin kaunar Aziza a cikin ransa, hakika ba zai ce baya son Azima ba tunda ita ma ƴarsa ce, amma aka ce mai kyautata maka shi ne wanda yake rayuwa a cikin zuciyarka,
"Na Yarda da ke Aziza, Allah ya miki albarka" murmushi Aziza ta yi ta miƙe tsaya tare da fadin "Amin Baffana" fita ta zo yi a bukkan har ta duƙa sai kuma ta ɗago tare da juyowa ta ce
"Amm Baffa? Baka faɗa mini abunda zai iya lalata zaren saƙar dana ba?"
"Aziza sanin wannan ba sauki garesa ba, har sai an koma jejin lore, jejin da mutane ba su shiga"
"To amma Baffa kai a garin yaya ka shiga ka fito?"
"Tsoron tarihi ne Aziza, kun dai sannin a matsayin mahaifinku! Amma har kwanan gobe baku da tarihin mahaifinku, na sha miki alƙawari zan baki tahirin jarumtar mahaifinki! Abunda yasa bana son faɗi yanzu sabida jarumtar bata jawo min komai ba sai babban kuskure"
Da sauri Aziza ta dawo ta zauna ta ce
"Baffa kamar ya? Dan Allah ka gaya min"
"A'a Aziza dama kin tashi kin tafi ne da ya fi miki alkairi, dan ba zaki ji komai ba a yanzu" ganin yadda Baffa ya yi maganar yasa Aziza miƙewa a hankali ta fice, tana fita ta koma bukkansu tana tsaye tana ta saƙa da warwara, a fili ta ce
"Kenan domin dakatar da Azima nima sai naje jejin lore? Idan kuwa hakane! *yau din nan zanje domin dakatar dake, amma kafin nan sai kin gaya min wanda kike hari da zaren sakar Azima!" Aziza ta faɗa tana harɗe hannuwanta.
🍃🍃🍃🍃🍃
Zaune suke a fadar sarki Chubaɗo, da sauri Maga Isar da saƙon kwana ya zo ya zube a gaban sarki ya ce
"Ranka ya daɗe! Sako ce daga yankin ja'i" da sauri wa inda suke zaune a wajan suka mai do da kallonsu kan Maga Isar da Sako, wazirin kwana ya ce
"Maga Isar da sako, buɗe ka karanto mana abunda yankin ja'i suka rubuta" jiki na rawa Maga Isar da saƙo ya zo zai buɗe sakon sarki Chubaɗo ya dakatar da shi da cewa
"Dakata! Maga Isar da Saƙo, wannan saƙo ba na iyakar mu na nan kawai za a karanta ma wa ba, a'a yanzu maza kuyi aike a tara mutane,kuje ku sanar da Mai unguwa Ori, ku kira Arɗo tare da Baffa Mandi, da Magaji Bawa duk a hallara yanzu" Maga Isar da sako ya amsa da to, sannan ya mike da sauri dan isar da saƙon sarki chubaɗo.
A cikin yan mintuna ƙalilan kowa ya hallara a fadar sarki Chubaɗo , kowa yana fargaban kar yankin ja'i ace sun rubuta ba zasu taimake su ba.
Bayan kowa ya bada hankalinsa sarki Chubaɗo ya ce
"Maga Isar da sako karanto mana abunda yankin ja'i suka rubuto" Maga Isar da sako ya amsa da to, sannan ya buɗe wasikar yankin ja'i ya fara karantowa kowa naji.
" _Wa'alaikumussalam, da fatan yankin kwana su na lafiya? Ya kuma fargaban iftila'in da ku ke ciki? Kashh! Ayya! Allah Sarki! Wasikarku ta iso garemu na neman taimako! Tunda har yankinku ya duƙawa tamu yankin,mun yarda zamu taimaka muku da Innu Maciji! Zai zo gobe, amma abun mamaki ace kuna da mutum a yankinku kamar Magaji Bawa har sai kunzo yankinmu neman taimako? Koma miye daukakarmu ce, tunda yankuna yanzu zasu shaida kun watsar da makamanku wa yankinmu, saƙo daga yankin ja'i, mun karb'i ƙudirinku!_"
Maga Isar da sako yana gama karantawa Baffa ya miƙe cikin fushi ya ce
"Sadda muka tura wasika yankin jimo dan su taimaka mana da jarman macizai magana mai dadi suka mana sannan suka jajanta mana suka amince da bukatarmu, amma yanzu wannan wasika na yankin ja'i har da izgilanci a ciki" Arɗo ya mike shi ma ransa a b'ace ya ce
"Duk abunda aka gaya mana laifin waye Magaji? Na ce laifin waye!?" tsohon Sarkin fulanin kwana Baffa Mandi ya ce
"Yanzu ba lokacin nuna fushi bane sabida halin da muke ciki, tunda sun amince zasu taimaka mana shikena!" Garkuwan fulanin kwana ya ce
"Amma abunda Arɗo ya faɗa gaskiya ne, Magaji da ace ka yi wani abu a kai da yanzu wannan bala'in an gama shi, me yasa ba zaka dawo yadda kake da ba? Idan ka manta da takenka sai a tuna maka....!"
"Ya isa haka Garkuwa!" Baffa ya dakatar da shi idonsa jajur, Ori ya ce
"Garkuwa yana da gaskiya Magaji, da ace kayi wani abu a kai da yanzu yankin ja'i basu gaya mana magana ba" Wazirin kwana ya ce
"Tabbas hakane Magaji, da ace kayi wani abu a kai da har yaushe zamu duƙawa yankin ja'i balle su mana izgili kamar mu muka ɗorawa kanmu masifar!" haka kowa yasa Baffa a gaba ana cewa duk abunda yankin ja'i suka faɗi har da laifinsa, jikin Baffa ne ya hau rawa ya daka tsawa da faɗin
"NA CE YA ISAAAAA!!" ya juyo yana kallon mutanen da suke wajan ya ce
"Wai ku baku duba gagarumin bala'in da nake hangowa ne? Na koma na haƙo kayayyakina da na binne tamkar haƙo maƙabarta ne wa yankin nan! Dan karku manta da aljanun da mayun da na rufe! Duk abuna ban cika kisa ba sai inta kama dolen- dole! Tunda na kashe Banju nayi sallama da kwanciyar hankali, wanda a yau duk faɗin yankin kwana babu yaran da ake zargi kamar yarana AZIMA DA AZIZA! duk da ba zan hanaku zarginsu ba, amma ko da sau daya ne zaku min uzuri! na rayu ne wa yankina inda nayi aikin tuƙuru da jinina da lafiyata! naje na haƙo abunda na binne duk aljanu da mayun da na ɗaure tass zasu kunce, me ku ke tunani zai faru da iyalin da nake da shi a halin yanzu?" Baffa ya faɗi yana fashewa da kuka yana dukawa, jikinsu ne ya yi sanyi sosai, yayinda Arɗo ya dago Baffa yana rarrashinsa inda sarki Chubaɗo da mai unguwa Ori suka hau ba shi hakuri tare da nadaman ganin laifinsa, Arɗo ya ce
"Kayi hakuri Magaji, yanzu abunda za ayi a rufe wannan maganar, Allah ya kaimu gobe Innu Maciji ya zo ya warware mana wannan sarƙaƙiyar" Sarki Chubaɗo ya ce
"Kowa zai iya kama gabansa"
Da kaɗan-kaɗan aka fara watse wa, Arɗo da Baffa Mandi da Baffa ne suka fara tafiya, Baffa Mandi ya ce
"Amma na rasa me yasa Magaji kake yawan maganar Banju" Baffa ya ce
"Sabida ni kaɗai nake ganin abunda nake gani a gidana" yana gama faɗin haka bai jira amsarsu ba ya yi gaba, Arɗo ya sauke ajiyar zuciya ya ce
"Mandi, akwai abunda yake damun Magaji" Baffa Mandi ya ce
"Nima haka nake gani, amma anya baya da nasaba da yaransa da ake yawo dasu ake zarginsu kuwa? A gaskiya Magaji ya yiwa yankin kwana hidima bai kamata a dinga masa haka ba"
"Gaskiya kam hakane" tafiya sukeyi a hankali suna tattaunawa, Baffa kuma hanyar gida ya ɗauka.
🍃🍃🍃🍃
Zaune ta sameta a rafin jimulo, ita ma zama ta yi kusa da ita ta ce
"Azima tambayarki na zo yi"
"Wai ni Aziza me yasa kika rainani ne? Ba nice gaba da ke ba?" murmushi Aziza ta yi ta ce
"Au haba dai da gaske? Rainin babu dadi ne? To haka iyayenmu suke ji a ransu idan kika musu, balle ni da ba ki bani ko da kwana daya bane, kawai iskar duniya kika rigani shaƙa" Azima ta kyalkyale da dariya ta ce
"Macijiya Aziza me ya kawo ki wajena?"
Kallonta Aziza ta yi ta ce
" ZAREN SAƘAR DANA! WA ZA KI KASHE DA SHI!?" sake kyalkyalewa da dariya Azima ta yi ta ce
"Idan naki faɗi fa me zakiyi?"
"Sai na gwada ta wata hanyar!" Aziza ta faɗa tana mikewa tsaye, da sauri Azima ta mike ta ce
"Muje zuwa" tana gama faɗi ta hau ajijiya, Aziza na tsaye tana kallonta.
🍃🍃🍃🍃
COMMENT AND SHARE
BY
MOMYN AHLAN
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*IDAN AKA CE ƘAWANCE ANA NUFIN AMINTAKA! WANDA WANNAN AMINTAKAR WATA DANƘO CE MAI MANNUWA,ANA SAMUNSA NE IDAN AKA SAMU YARDA DA AMANA! IDAN NA KIRAKI DA SUNAN ƘAWATA BAI KAI INDA ZAN NUNA YADDA NAKE YINKI A CIKIN RAINA BA, HAKIKA MU DIN BA IYAKAR KAWANCE BANE,INAJINKI TAMKAR WACCE MUKA FITO CIKI DAYA,INA MIKI SON SO SABIDA ALLAH! ALLAH YA BAR MINKE ƘAWALLITA _RASHEEDAT USMAN UMMU NASMA&NASREEN_ ALLAH YA ALBARKACI ZURI'ARMU ALLAHUMMA AMIN, INA KU KE MAKARANTA? UWAR NASMA TA YUNƘURO FA A BOOK DINTA MAI SUNA _GELLE 'BINGEL_ WANDA ZAKU SAME SHI CIKIN FARASHI MAI SAUKI, KU NE ME NI TA LAMBATA DAN ISA GA FASIHIYAR MARUBUCIYAR KAI TSAYE, KARKU BARI A BAKU LABARI, SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*👐🏻
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
*FREE..*
🅿️==1️⃣5️⃣↪️1️⃣6️⃣
Bata motsa ba, har Azima ta gama hajijiyarta, ta girgije ta zama macijiya daga ƙasanta, ta ce
"Mu gwada mana Aziza, yau inaji da abunda ba ki ji" murmushi Aziza ta yi ta ce
"Dan kin saƙa zaren dana shine kike tunanin zaki iya dani? Kawai cewa nayi ki faɗa min wanda za ki kashe da shi, idan ba haka ba na gwada ta wata hanyar" sosai Azima ta haɗe rai fuskarta ya fara komawa blue ta ce
"Idan zakiyi kawai kiyi! Bana son magana a baki sai dai a aikace!" Azima na gama faɗi ta daga hannunta ta huro wuta, Aziza na tsaye na kallonta, sai da Azima ta gama hura wutar ya yi jajur sannan ta yi wani gurnani ta hurawa Aziza, Aziza na ganin yadda wutar ya nufota ta yi tsalle ta haɗa wani farin hayaki ta maidawa Azima abunta nan ya sameta patttt! A ƙirji! Zubewa ƙasa ta yi tare da komawa mutum, a hankali Aziza ta zo gabanta ta ɗurkusa tana shirin yi mata magana taji yankan wuƙa a kafadarta ya shige, kafin ta farga Azima ta yi mata kafa ta nausheta a ciki nan ta faɗi kasa numfashinta nayin sama, Azima kuma ta miƙe tana dariyar mugunta gami da cewa.
"Gaskiya bana da burin kasheki yar uwata, amma ya zama dole ko dan na kammala aikina a kan lokaci! dan zaman wannan dajin ya isheni ina da bukatar shiga gari, to amma idan kina raye taya burina zai cika? Ba ki san ta yadda akai na samu zaren saƙar dana ba taya kuwa zan gaya miki wanda zan kashe da shi!? To ba zan faɗa ba! Yanzu kuma idan na kasheki bani da wata sauran damuwa a rayuwata ko abunda zai dinga kawo min cikas da burina!"
Duk maganar da Azima ke yi Aziza na jinta yayinda hannunta daya tana riƙe da kafadarta da yake zubar da jini dayan kuma yana kan cikinta da Azima ta yi mata naushi da kafarta, tsoronta daya shine Allah yasa wuƙar da Azima ta yanketa da shi babu zaren saƙar dana a jiki, idan hakane yana nufin Azima zata yi b'arna? Idan ta kasheta zata kashe sauran mutane sannan ta shiga cikin gari ta tarwatsasu? Inaaa! Hakan ba zai yu ba, dole na dakatar dake ko ta wace hanya! To amma me zanyi yanzu? Aziza take tambayar kanta mafita, Azima kuwa na tsaye ta juyawa Aziza baya tana ta zuba kamar indararo, wata zuciyar ta cewa Aziza
"Kin manta ba zaku iya kashe juna ba? Amma ke zaki iya kashe Azima! Duba Taurarinku dake haɗe ke kaɗai aka yarjema wa dan ki gani da mai zaki dakatar da Azima" a hankali Aziza ta miƙe ta kama bishiya ta ɗan jinginu, ta lumshe ido, nan ta hau gane-gane, tabbas ba zasu iya kashe juna ba amma zata iya karyawa Azima kwarin guiwa, sannan wukar da ta yanketa da shi babu zaren sakar dana a jiki, Aziza na ganin haka tasa hannu ta shafe inda Azima ta yanketa nan wajan ya koma kamar ba a taba saka ma shi wuƙa ba, sannan a ranta ta ce
"Inno Fandi! Yau inaso ki bani abunda kika sha miƙa min ina ƙin karba,ko ta wace hanya ce ina so na dakatar da Azima,ina so na san wa zata kashe da zaren saƙar dana dan na basa kariya,duk da zuciyata tana zargin Baffa Azima take son kashewa! Amma ita baka iya tunanin abunda zatayi dan komai ma zata iya yi! Inno Fandi yau ina so ki bani" Aziza a ranta take magana idonta a lumshe, wata farar tsohuwa ce fara sosai tsohuwa tukuff ta bayyanawa Aziza tana murmushi ta ce
"Wani lokaci domin tsaida zubda jini! Muma sai mun wanke hannayenmu da jini! Magaji Bawa ya ajiye baiwarsa yayinda ya binnesa, na zabi shiga jikinki dan taimaka miki ke da mahaifinki a lokacin da na hango bala'in da zai faru a rayiwarku bayan an haifeku, Magaji ya yi tunanin binne baiwarsa zai ce wannan yanki ta yi sanyi, amma kashe Banju shine babbar bala'i ma wannan al'karya dan yace zai dawo, ba zaki iya jin komai a bakina ba Aziza dan alƙawarin da muka yiwa Magaji cewa daga bakinmu wani nasa ba zai ji tahirinsa ba sai dai idan shine ya bayar, sabida alkhairin da Magaji ya mana ba zan manta da shi ba, hakika Magaji Bawa jarumi ne, Aziza wannan abunda zakiyi ba ƙaramin yaƙi bane wanda ke daya ba zaki iya yi ba,ni kuwa bazan iya tayaki ba, amma ga wannan ki ɗora shi a ɗamtsen hannunki zai taimaka miki sosai,sannan karki taba rabuwa da shi dan wani sirhitaccen karfi ne, duk sadda kike bukatar taimakona ki kirani zan zo!" tana shirin b'acewa da sauri Aziza ta ce
"Inno Fandi! Jejin lore! Ina so naje" zaro ido Inno Fandi ta yi ba tare da ta yiwa Aziza magana ba ta b'ace, a hankali Aziza ta buɗe ido ta kalli Azima wacce har yanzu take tsaye take magana a kan zata kashe Aziza.
Ɗora zaren da Inno Fandi ta bata ta yi a damtsen hannunta sannan ta juya baya ta rintse ido nan fatar jikinta ya hau sab'ulewa alama ce na zata koma macijiya, nan ta zama wata katuwar macijiya🐍fiye da yadda take zama a da, fara sol sai kyalli take yi, Azima dake ta zuba tin dazu bata san abunda ke faruwa a bayanta ba, sai bayan da ta gama maganarta na karshe da fadin
"Sai fa hakuri! Amma yau za ki mutu! Ni haka nake! Muguwa ce ni! Ban san sani ba! Ban san sabo ba!" tana gama faɗi ta juyo dan cakawa Aziza wuka nan ta ga babu Aziza, ɗaga kan da zata yi ta hangi kanta a can sama, Aziza ta zama katuwar macijiya mai cike da tsoro da firgici, da mugun tsoro Azima ta ja da baya tana fadin
"Ya haka?" bata ankare ba ta ji anyi sama da ita an yi kasa da ita, kafin ta girgije ta ji an dauketa ana zagaye iska da ita, sai da aka wujijjigata sosai sannan aka yi wulli da ita, faɗuwa ta yi ta bugu.
Buɗe baki Aziza tayi a tana macijiyar🐍ta hau yiwa Azima ruwan macizai🐍 su na fita suna saren Azima, sai da ta cikata da macizai sannan ta koma mutum tana tsaye tana kallon Azima wanda macizai ke sara, Azima ta kasa tabuka komai, da taji jiki taji tabbas zata iya mutuwa ita kuwa ba zata yarda ta mutu ba tare da ta dauki fansa ba yasa ta ce
"DAN ALLAH AZIZA! KI KWASHE MACIZANKI! ZAN GAYA MIKI WANDA ZAN KASHE!" jin haka yasa Aziza ware hannu ta janyo macizan sannan ta b'acer dasu, tana janyesu Azima ta zube kasa a galabaice, Aziza ta ce
"Gaya min! Wa za ki kashe da zaren saƙar dana?"
" *BAFFA*" Azima ta faɗa cikin muryan galabaita, saurin ja da baya Aziza ta yi ta ce
"Baffa?"
Da jan ido a tsawance Azima ta ɗago idonta ta watsasu a cikin na Aziza ta ce
"Eh Baffa zan kashe da zaren saƙar dana! Ban san wani irin kalar baiwa Baffa yake da shi ba, amma abunda na sani shine duk wata hanyar guba da nabi dan son kashesa duk basu aiki! Tun ina gwada kashesa a boye har na fara bayyanawa kika sani! Bincikena ya nuna min cewa zaren saƙar dana ne zai kashe Baffa wanda da shine ya......." maganar da Azima bata karasa ba kenan Aziza ta wanketa da mari, za ta kara Azima ta riƙe hannun Aziza ta ce
"Karki kuskura idan ba haka ba a yau din nan wannan al'karya zata koma toka, kodayaushe kina nuna min karfin dafi da baiwar da kike da shi, ga taken kalmata ta karshe wanda kika sani Aziza, *IDAN KIN ISA KI DAKATAR DANI!*"
miƙewa tsaye Aziza ta yi ta ce
"Na yarda da maganarki Inno! Domin tsaida zubda jini! Dole ne muma sai mun wanke hannuwanmu da jini! Ke dodon mutan yankin nan ne da Baffa ko Azima? To ki sa a ranki ni nice dodonki, dakatar dake kamar na yi na gama" dariya Azima ta kyalkyale da shi ta ce
"Muje zuwa, ai ba a buga komai a wasan ba! " ba tare da Aziza ta sake magana ba ta bar wajan, a hankali Azima ta miƙe ta b'alli gashin kanta tsili ɗaya ta hura wani hayaki a jiki sannan ta haɗiye nan inda macizan Aziza suka sareta wajan ya koma ya yi fess sannan ta dauki hanyar gida, Aziza kuwa ba gida ta yi ba, dan bata ga ta zaman gida ba,dole ne taje jejin lore dan lalata zaren sakar dana in ba haka ba kuwa Baffa da sauran jama'a zasu mutu.
🍃🍃🍃🍃
A tunzure ta zo shiga gidan, amma jin maganar da Baffa da Hajja ke yi ya sakata maqalewa a jikin zana tana sauraronsu, Hajja ke faɗin
"Innu maciji kam ina da sa rai a kansa sosai, zai iya kawo mana karshen wannan matsalar da yardan Allah, tunda yana gwagwarmaya da aljanu, a goben zai zo?"
"In sha Allahu! Haka suka ce zai zo a gobe, amma a gaskiya da a so samuna ne da bamu nemi taimakon yankin ja'i ba sam wollah, karki so ki ga izgilancin da suka mana a cikin wasikarsu kafin su amince da bukatar yankin nan"
Ajiyar zuciya Hajja ta sauke ta ce
"Koma miye tunda sun amince shikenan Allah ya shiga mana gaba! Idan kuma tsohon gaba ne yanzu kuma ta kau ai, tunda yankin kwana ta duƙa musu" girgiza kai Baffa ya yi ya ce
"Jumala! Ba shi bane abunda nake hange! Idan wani abu ya samu Innu Maciji ko da ƙwarzani ne to fa! Sabon yaƙin da ba ayi ba kwanakin baya shi za ayi yanzu! Duk inda ake neman rashin hakuri masu jiran sammacin yaƙi idan aka samu yankin ja'i to an kai karshen magana, mutanen da jira suke a tab'osu ko kaɗan ne su yiwa mutane cin mutunci, meyasa gabanmu dasu yafi tsanani? Ina sabida yankin kwana taƙi daukar cin mutunci ne, amma al'ummar yankina sun kasa fahimtar abunda nake gaya musu, idonsu ya rufe da neman mafitar wannan bala'i shiyasa duk shawaran da zan basu, ba su gani inda a karshe ma laifi ne suke gani, suna ganin kamar zan iya wani abu a kai amma naki, duka so suke naje na haƙo kayana da na binne wanda haƙo wannan kaya sabon bala'i ne da barazana wa rayuwar su Azima da Aziza har ma dake! Balle kuma ace ni da ake neman fansa a kaina! Su tsaya su saurareni na gaya musu yadda za ayi amma sam!" Baffa ya faɗa yana riƙe kansa dake sara masa, shuru Hajja ta yi ta ce
"Komai ya yi zafi maganinsa Allah Baffan yan biyu, mu dage da addua Allah na nan!"
"Haka ne Jumala, Allah ya shige mana gaba"
"Amin" Hajja ta fada tana miƙewa da fadin
"Ko inasu Azima da Aziza suke? Kai wannan yara yanzu haka suna can rafin jimulo" Baffa dai bai kuma cewa uffan ba.
Wani murmushi Azima ta yi da saurin komawa baya, ta ce
"Kai ashe dai ina da babbar mugun ƙulli! Gobe Innu Maciji zai zo, ayya Innu Maciji ashe kwana ya kare! Ajali ya yi kiranka gobe, wayyo dadi zan so na ci gaba da ganin tashin hankalin wannan yanki, hakika Innu Maciji gobe asalin Macijiya Azima zata kasheka! Wayyo farin ciki! Zanyi tsumayen jiran zuwanka yankin kwana!" ta faɗi tana dariya tare da gyara mayafinta, sannan ta shiga gidan da sallama wanda rabonta da sallama harta manta,tana yin sallamar taji har wani ɗaci wuyarta ke mata, da mamaki Hajja ta amsa ita da Baffa dake zaune, kusa da Baffa Azima ta zauna tana murmushi sai kuma ta koma tayi fuskar tausayi tana kallon Baffa ta ce
"Baffa kayi hakuri da abunda nayi dazu ban san nayi ba, amma Aziza ta fahimtar dani, ka yafe min Baffa ba zan sake ba, ban san lokacin da nake yi ba dan Allah Baffa👏🏻" shuru Baffa ya yi yana kallon Azima a ransa ya ce
"Kenan da gaskiyar Aziza, Azima aljanu gareta?" a fili kuma Baffa ya ce
"Shikenan ya wuce Azima,Allah ya miki albarka, amma ki gaya mini gaskiya ina kika samu zaren saƙar dana?"
Turo baki ta yi ta ce
"Baffa ganinsa kawai nayi a hannuna! Yanzu kuma ya b'ace, ban gansa ba"
Baffa ya sauke ajiyar zuciya har yana hamdala, Azima ta miƙe taje ta rungume Hajja wacce rabon da ta rab'eta ba zata iya tunawa ba ta ce
"Hajja ke ma kiyi hakuri" murmushi Hajja ta yi har kwalla na taruwa a idonta tana shafa fuskar Azima, yatsine fuska Azima ta yi a ranta tana kallon Hajja ta ce
"Ni dai bana jin shaukin komai a tare daku, ko da ba zan ji a kan Baffa ba a matsayinki ta mahaifiyata ya kamata ace naji shaukin uwa da 'yarta, amma bana ji saboda ni ba mutum ba ce! muguwar macijiya ce, shiyasa ma babu amfanin na dinga rab'anku, abunda nake so shine....." maganarta ce ya tsaya jin Hajja ta jijjigata tana mata magana, dan tun dazu Hajja ke mata magana amma hankalinta ya yi nisa da tunani
"Na'am Hajja me kika ce?"
"Tunanin me kike yi Azima?"
" kawai Hajja babu komai mai kika ce?"
"Ina Aziza?" tsaki Azima ta yi a boye da tana shirin tace bata sani din ba, sai kuma ta tuno da abunda take son yi ta ce
"Na barota a rafi, Hajja bari na tayaki aikin gida yau" tana gama faɗi ta hau gyara kara a murhu,Hajja har can kasar zuciyarta take jin farin ciki, Baffa ya miƙe yana fadin
"Ba ri naje na gaida Inna Wuro (matar Arɗo) kwana biyu ma tace ba kuje kun gaisheta ba, wai dama Aziza ce yar albarka yar dakinta, ke kam ma Azima ko meyasa jininku bai zo daya ba oho!"
"Ai ni babu wanda jinina ya zo daya da na shi!" Azima ta faɗa tana murmushin gefen baki mai ciki da ma'anoni, Hajja ta ce
"Kinyi magana ne?"
"A'a Hajja ban ce komai ba, bari naje na ɗibo ruwa" ta faɗa tare da daukar tulu ta yi waje.
🍃🍃🍃
Tsaye take a wani jeji suna magana da Inno Fandi, Inno Fandi ta ce
"Aziza jejin lore ba kamar sauran jejin yankin kwana bane! Jeji ne da bai tara komai ba fa ce sai manyan aljanu masu mugun sihiri, babu abunda babu a jejin lore,kina tunanin zaki iya zuwa?"
"Inno Fandi Azima ma taje ta dawo balle ni? Ba ma Azima ba, Baffa da yake mutum ma yaje" murmushin manya Inno Fandi ta yi na yaro-yaro ne ta ce
"Aziza tabbas Baffanku mutum ne amma ba kamar kowa ba"
"Eh ni dai Inno Fandi ko ma miye zanje"
"To shikenan Aziza, dokar tafiya jejin lore, ba a yinta da rana, sai dai ki bari da magriba ki tafi, sannan ki tabbata kafin garin Allah ya waye kin baro jejin! Za ki ta gane-ganen abubuwa amma karki tsorata, dan tsoronki barazana ce ga rayuwarki!"
"To amma Inno Fandi ina ga hakan ai babu amfani tunda ni ba mutum ba ce macijiya ce" sake murmushi Inno Fandi ta yi ta ce
"Sanin kasancewarki ba mutum ba shiyasa nake gaya miki hakan, da ace mutum dan adam ne da ya kama hanyar sunansa gawa! Tun kafin ma ya kai ga shiga" Aziza ta jinjina kai, nan Inno Fandi ta gama gaya mata matakin da zata bi taje jejin ta dawo, godiya sosai Aziza ta mata daga nan Inno Fandi ta b'ace, Aziza ta kamo hanyar gida, tana cikin tafiya har ta kusa isa gida ta haɗu da wasu yan matan yankinsu wanda za a kamasu nan da sati daya wato amare kenan, wanda dukkansu babu wacce ta haura sama da shekara shaɗaya, su hudu suka sha gaban Aziza, dayar mai suna Lantai ta ce
"Ke wacece Azima ce ko Aziza!?" Aziza ta ƙara gyara lullubinta tana rufe gefen idonta da gashinta da ya sauko mata har kirji ta kara dukar da kanta kasa ta ce
"AZIZA" wata mai suna Huwe ta ce
"Yau kwayar idonki muke son gani, da asalin fuskarki!" gaban Aziza ne ya faɗi ta ɗan dago a hankali ta ga rana ya faɗi ga shi dole taje gida ta yi shiri, dan haka ta ce
"Kun ga bana son kalen rigima da jan faɗa ku barni naje gida ni ba sa'arku ba ce!" dariya suka kwashe da shi inda suka hau tureta tana ja da baya, har suna faɗin wai gandamemiya marasa farin jini sun ƙi aure, babu mai sonsu! Gajiya Aziza ta yi inda ta daka musu tsawa sai da suka dare, hannu tasa ta kwashe gashinta na gefen fuskarta farin eyes dinta na mage suka bayyana, da mugun gudu wannan ta yi gabas,daya ta yi kudu,daya arewa,daya kuma ta yi yamma, Aziza ta ce
"Alhamdulillahi! Ni ku ka samu, da ace Azima ce sai dai a aurar da wasu amma ba ku ba" tana gama fadi ta wuce da sauri tana sake rufe gefen fuskarta.
🍃🍃🍃🍃
"Assalamu alaikum" Aziza ta yi sallama Hajja dake kwashe kaya ta amsa ta ce
"Aziza sai yanzu? Tun dazu nake tambayar Azima tace min kina rafi, sawunta yau biyar tana ɗibo ruwa"
"AZIMAR!?" Aziza ta tambaya a mamakince, Hajja ta ce
"Eh wollah, yana ganki haka Aziza ba ki da lafiya ne?"
"E Hajja kaina ke ciwo sosai, shiyasa ma na zabi na zauna a rafin yau, ammm Hajja ga wannan ki sha"
"Inji waye?" Hajja ta tambayi Aziza
"Ba kowa nina haɗa miki sabida ciwon bayan da kike fama da shi"
"Ayye Aziza ai naji sauki tun wanda kika bani kwanakin can"
"E duk da haka ma ki sha wannan Hajja" ba tare da Hajja ta sake magana ba tasha, tana gama sha Aziza zata yi magana taji ana shelan kiran sallar magriba, hakan ne yasa kawai ta rungume Hajja wacce taji komai na kanta ya dauke, sun ɗau lokaci a haka kafin Aziza ta saki Hajja ta yi alwala ta gabatar da sallar magriba ta jima tana addua kafin ta tashi ta canza kaya ta ɗauki abubuwan da zata dauka ta kara da wa inda Inno Fandi ta bata ta fito ta fice a gidan kafin Baffa ya dawo, tana zuwa bayan zanar gidansu ta rufe ido nan ta b'ace b'atttt!!.
🍃🍃🍃🍃
Ko da Azima ta dawo gida ita ma shiri gwabzawa ta yi da Innu Maciji,dan ta lashi takwabin kashesa!.
Hajja kuwa bata tambayi inda Aziza take ba.
Tun tsawon dare Azima ta zama macijiya ta sulale a hankali ta fice a gidan, bata zarce ko ina ba sai tsakanin shigowa yankin kwana da yankin ja'i.
🍃🍃🍃🍃
HAHAH NA HADA MUKU DA PG DIN JIYA DA NA YAU, MUN RABU LAFIYA🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️
COMMENTS AND SHARE by
*FREE..*
🅿️==1️⃣7️⃣↪️1️⃣8️⃣
A wani ƙasurgumin jeji Aziza ta tsinci kanta, jeji mai cike da wani mugun duhu da abubuwan tsoro tare da wasu mugayen halittu marasa kyawun gani da ban tsoro, haƙiƙa ganin wa innan abubuwa sun tsorata Aziza, amma tunowa da maganar Inno Fandi da cewa kar ta tsorata yasa ta takure tare da tattaro jarumta, ta hau tafiya, tare da furta kalman "makarin zaren saƙar dana!" wani sowa ne taji na tashi ta tsakiyar kanta da wani irin mugun jijjiga nan wasu halittu suka yi sama da ita, saura qiris Aziza ta saki ihu amma kuma ta daure tana karanto dukkan adduar da ya zo zuciyarta, nan halittu suka dauketa suka kara yin sama da ita suka hau tafiya da ita a cikin duhu,amma duk wannan duhu ba shi ya hanata ganin mugayen halittu marasa kyau da ban tsoro ba.
Wa inda suka dauketa basu ajiyeta a ko ina ba sai a gaban wani katon halitta wanda bata san dame zata fasalta halittarsa ba sabida tsananin muni da girmarsa, ana ajiyeta muryar wannan katon abun ya ce
"Keeeee! Me ya kawoki jejin lore!!!" a yadda muryarsa take ɗan adam idan ya jita ya ci ace ya mutu tsananin amo marar daɗi da kaifi, cikin dakiya Aziza ta ce
"Makarin zaren saƙar dana, shi nake so" shewa wannan halittar ya yi,sannan ya ce
"Ya matsayinki yake a halittu!?"
" *NI MACIJIYA CE!*" Aziza ta bada amsa, wannan halittar ya ce
"Ke ba iyakar macijiya ba ce, akwai wani sirri a tattare dake, dan haka ko ba mu baki makarin zaren saƙar dana ba,kaifin gubar dake jikinki zai iya ƙonasa! Amma kasancewar sau daya tak! Muke bada alfarma zamu baki taimako guda daya, zamu ƙara miki karfi, da kinje ki hurawa zaren wuta ta idon ki zai ƙone ƙurmuss! Ga wannan" ya faɗa yana daukar wata kyakkyawar dutse mai cike da hasken gaske ya hura mata shi ya shige ta goshinta, abun na shiga jikin Aziza sai da ta girgiza ta yi kamar zata faɗi amma ta yi iyakar iyawarta bata faɗi ba,dama tana tsaye ne ita ba a sama ba ita ba a kasa ba, abun na shiga jikin Aziza nan ta kalli fatar jikinta ta ga yana sab'ulewa har yana komawa wata fari-fari, kafin ta gama dawowa hayyacinta tuni ta fara rikiɗewa tana komawa macijiya, nan ta zama wata shirgiɗeɗiyar macijiya mai cike da abun tsoro, nan aka hau guɗa wanda yasa duk jejin lore ya dauka, kafin wannan katon halittan ya ce a maidata gida lafiya, nan suka fizgi Aziza,wacce tunda suka fizgeta bata kara sanin ina kanta yake ba, sanyin asuba ne ya farkar da ita,tana buɗe ido ta ganta a kofar gida, saurin tashi ta yi tana karkaɗe jikinta, nan abunda ya faru a daren jiya ya hau dawo mata, lallai kam jejin lore ba jejin mutane bane, da kyar ta saita kanta jin yadda jikinta ke mata ciwo, da sanɗa ta shiga cikin gida, tana shiga Baffa na fitowa daga kewaye ya yi alwala zai je masallaci, ya ce
"Aziza har kin farka? To shiga ki tada Hajjarku sannan ki tashi Azima su yi sallah"
"To Baffa" Aziza ta faɗa ta shiga ta tada Hajja sannan ta fito ta shige bukkarsu, ko da ta shiga bata gan Azima ba, a ranta ta ce ko ina taje oho mata, kayanta ta ajiye sannan ta fito ta yi alwala ta yi sallah ta jima tana addua sannan ta tashi.
Abu na gaba da zata yi shine daukar zaren saƙar dana taje ta kona shi, to amma abun tambayar a nan shine a ina Azima ta ajiyesa? "zaki iya dubawa ki gani ta tafin hannunki ai an baki karfi a daren jiya a jejin lore" wata zuciyar ta bata amsa da haka, da sauri ta buɗe tafin hannunta na dama tasa hannun hagunta tana shafe tafin hannun daman tare da lumshe ido, nan ta ga ashe ma a cikin kayanta Azima ta ajiye zaren saƙar danar, tasan tabbas Aziza sai ta binciko,kuma duk bincikenta ba zata duba kayanta ba tunda ba zata yi tunanin zata saka a ciki ba, da sauri Aziza ta buɗe ido tana fadin "lallai Azima ke shaiɗaniya ce! A cikin kayana kika ma ajiye?" da sauri ta wargaza kayanta ta dauki zaren wanda Azima ta saƙa shi ya yi tsayi, lullubi ta yi ta boyesa a cikin mayafinta ta fito a hankali dan gari ya yi haske, har ta kai bakin kofa zata fita ta ji Hajja na kwala mata kira da gudu ta fice dan bata son ta rasa wannan damar, jejin kwana taje ta ajiye zaren bayan ta duba babu kowa a wajan, da ido ta kalli zaren yayinda idon nata ya koma jajur kamar garwashin wuta,nan wani jar wuta ya fito daga idonta ya kama zaren,nan zaren ya kama da wuta har yana wani irin ƙara passpasspass! Da sauri Aziza ta ja da baya, nan zaren ya ƙone ƙurmuss! tokar Aziza tasa hannu ta shafe shi ya b'ace nan ta sauke ajiyar zuciya mai karfin gaske tare da fashewa da kuka tana zubewa a kan guiwowinta tasa goshinta a kasa ta yi sujjadar shukur, ta yi tsammanin ta kashe wannan bala'in bata san wanda yake shirin ci ba.
🍃🍃🍃🍃
*AZIMA.*
tun fitarta a gida tana kwance a kan bishiya a macijiya tana jiran isowar Innu maciji, sai bayan da garin Allah ya fara wayewa ta ga wasu yan matasan samari biyu sun zo sun tsaya a jikin bishiyar da take kwance, dayan ya ce
"To ma ban da abun Mai Unguwa taya zamu iya kare Innu Maciji da za a wani turo mu dan mu tarbesa"
"Nima dai abun da na gani kenan" saurin zare ido Azima ta yi ta kallesu da kyau sannan ta yi murmushi
"Ohhho kenan yan fadar mai unguwa ne! Aiko su ya yi, shin na bar ma su bada labari ne? Idan kuma suka tona min asiri fa?" nan ta haɗe rai tare da sulalowa daga bishiyar ta zama mutum, hannu ta miƙa sama sai ga kwaryan nono, murmushi ta yi ta buɗe kwaryan wanda yake cike da nono kindirmo fari sol abun sha'awa ta watsa dafi a ciki sannan ta gyara mayafinta tayi lullubi ta rufe fuskarta ta nufi inda suke, cikin karairaya ta musu sallama, su kuwa sun ga ƴar budurwa har rige-rigen amsawa suke yi,cikin harshen fulatanci suke magana ta ce musu
"Ga fa nono, daga ina ku ke da sassafen nan haka ku ka zo ku ka zaune a tsakanin yanki?".
"Wlh mai unguwa ne ya aiko mu, kin san ai masifar da ake fama da shi a yankin nan na macizai, to yau Innu Maciji zai zo wanda yake yankin ja'i shine mai unguwa ya aiko mu dan mu tarbesa,kin san kwanaki da Jarman macizai ya zo gawarsa kawai muka gani, kai duk wannan macijin da yake kisan nan ko take kisan nan ko humm idan Innu Maciji ya zo zan ce ya bani dama na kashesa da hannuna" cije baki Azima ta yi ta ce "da gaske?"
"Aradun Allah kuwa! Sanda zan sha na dinga roɗewa macijin kai har sai ya koma ga Allah" damƙe hannu Azima ta yi jin yadda ranta ya b'aci zuciyarta na tafasa amma ta daure tare ta k'wak'ulo murmushin mugunta ta ce
"Ai kuwa nima ina da wasu sirrika a kan macizai, kafin na gaya muku ga wannan nonon ku sha" ta fada tana tura musu kwaryan, dayan ya ce
"Allah sarki! Ashe kin san yau da yunwa muka tashi, ga shi kafin mu karya karin kumallo aka turomu yanki" murmushi kawai Azima ta yi ba tare da ta sake magana ba, nan suka buɗe nonon nan suka hau sha, sai da suka shanye tass har suna mata godiya, Azima ta kyalkyale da dariya tare da yaye mayafin fuskarta nan blue eyes dinta ya bayyana, tare da rikiɗewa ta hau komawa macijiya, tsananin tsoro da firgici yasa suka kasa motsi illa junansu da suka rungume gagam!, bayan Azima ta zama macijiya sannan ta koma ta zama mutum ta matso kusa dasu ta duka ta ce
"NI CE AZIMA MACIJIYA! WACCE DUK KASHE-KASHEN DA AKE YI NI NA KE YI! NI! NI! NI CEEEE! SANNAN KU TAKU TA KARE DAN DAGA NAN BABU WANDA ZAI MOTSA A CIKINKU, DAN KUN SHA GUBANA" tana gama faɗi kuwa suka hau aman jini, su na riƙe wuyarsu tsananin azaba, jini na fita ta baki da hanci, suna birgiman fitar rai Azima na ta sheƙa dariya, da haka har suka daina motsi, bayan sun mutu ta kwashesu ta maida su gefe ta ajiye sannan ta ci gaba da tsumayin jiran isowar Innu Maciji, ba jimawa sai ga shi nan kuwa ya yanko a kan dokinsa, daka gansa ka ga basamudan bafulatani mai ji da kansa, wuyarsa rataye da maciji, Azima na ganinsa ta hau murmushi tare da gyara lullubinta ta zo ta tsaya a kan hanya, (ga Azima ga Innu Maciji, ya zata kaya?).
Kamar yadda ta yiwa jarman macizai haka ta yiwa Innu Maciji, shi ma kalar tambayar da jarman macizai ya mata shi ya mata
"Mutum ko aljan?" murmushi ta yi tare da fadin
" *RUWA BIYU!*" sannan ta juyo gami da yaye mayafinta, Innu Maciji na ganin kwayar idonta nan ya sauƙo da sauri tare da zare takwabinsa yana fadin
"Keeeee!" haɗe rai ta yi ta ce
"Ajali ya kiraka!"
Gyara tsayuwarsa ya yi ya ce
"Kina tunanin zan mutu a hannunki ne?"
"Ashe dai baka cika ba! Tunda har ba zaka iya bambance wacece ni ba, amma ina so ka sani ba zaka shiga yankin nan ba,kamar yadda ba zaka koma yankinku ba" tana gama fadi ta yi kansa tare da komawa macijiya,ganin haka yasa Innu Maciji saurin b'acewa dan ya ga da karfinta ta nufosa, Azima gani ta yi Innu Maciji ya b'ace yasa ta koma mutum tana ta kalle-kalle,ji tayi an tokareta ta baya nan ta fadi kasa ta bugu tukunna Innu Maciji ya bayyana yana dariya yana kallonta ya ce
"Ba mamaki baki da labarin waye Innu Maciji ko? Humm ni ne nan mai fada da aljanu da mayu, sabida shaharata yasa sadda aka raba kambun girmamawa ni ne nan nayi na daya, dan haka sai na baki wahala! Na galabaitar dake sannan na daukeki na kaiki wajan mutanen yankinku na nuna musu ke!" yana gama fadin haka ya zaro wani dogon igiya ya naɗe Azima da shi, ya hau bugunta tare da watsa mata wani ruwan magani wanda da ya watsa mata zata kurma ihu, fatar jikinta ya koma blue sabida karfin dafinta ne ke raguwa, haka Innu ya ci gaba da ganawa Azima azaba wanda izuwa yanzu fadin halin da take ciki b'ata lokaci ne, sai da ya ga bata iya motsin kirki sannan ya kyaleta yana shirin daukarta ya ɗorata a dokinsa yaje ya nunawa jama'ar yankin kwana, har ya dauketa Azima ta buɗe ido a galabai ce, a ranta ta ce
"Yanzu idan aka kaini Baffa da kansa na san zai kasheni! To ina kuma daukar fansata!? Inaaa ba zan bari hakan ta faru ba! Ba zan bar yankin nan ba, ba tare da burina na son maida yankin kwana maƙabarta ba, sannan ba zan bari na mutu ba tare da na shiga cikin gari ba" tana gama fadi ta yanki gashin kanta ta haɗiye ta rintse ido ta mamayi Innu Maciji wanda ya sab'ata a wuya yana shirin ɗorata a kan doki, nan ta zama macijiya tasa jelarta ta shaƙe wuyar Innu Maciji, shaƙa bana wasa ba, sannan tasa hannu ta b'abb'alle guru da layoyin dake jikinsa ta zubar, sannan tasa ihu ta koma macijiya gaba dayarta ta hau sarensa,duk yadda Innu Maciji ya so kwacewa ina hakan bai samu ba, Azima sai da ta ga Innu Macijiya ya zube kasa babu rai a tattare da shi sannan ta sulale gefe ta koma mutum tana sauke ajiyar zuciya idanunta jajur, kallon Innu Maciji take yi na wasu lokuta sannan ta ja samari biyun da ta kashe ta haɗa da innu maciji sannan ta bar wajan.
🍃🍃🍃🍃
Bayan Aziza ta koma gida aikin gabanta ta ci gaba da yi, ko kaɗan bata tambayi ina Azima take ba, nan ta yiwa Hajja shara da girki sannan ta hau ɗibar ruwa, sai da ta cika babbar randar kasarsu sannan Hajja ta ce
"Ayye Aziza ba za ki huta ba?" murmushi ta yi ta ce
"Hajja hutuna shine naga Allah ya rabani dake lafiya" Hajja ta yi murmushi jin dadi tare da sa mata albarka,nan suka zaune hira suka shantake sai zuwa anjima Hajja ta ce
"Wai ni ina Azima ne kam?"
"Wa ya san mata" cewar Aziza,
"Bata rafin jimulo ne?"
"Ni dai wlh Hajja har na gama jido ruwa ban ganta ba, da ace tana can dana ganta"
"Ikon Allah!" Hajja ta fada, Aziza ta ce
"Hajja miye amfanin damuwa a kan Azima ita da ba jaririya ba,duk inda taje zata dawo ai" Hajja ta ce
"Hakane" suka ci gaba da hirarsu, sai zuwa can Aziza ta ce
"Hajja wai ina Baffa? Tun fitarsa sallar asuba fa bai dawo ba ga shi yanzu ana neman lokacin azahar" Hajja ta ce
"Oh! Kinga na mance ban gaya miki ba, ai suna can fadar sarkin fulani, Chubaɗo"
"Wani abun ake yi ne?" Aziza ta tambaya cikin rashin sani tana kallon Hajja, Hajja ta ce
"E lafiyar kenan, kin san ai an yiwa yankin ja'i aiken wasikar taimako, har Innu Maciji ma ya ce zai zo yau, to jiran Baffan naku nake yi idan Innun ya iso zai zo ya gaya mana muje can fadar sarkin fulani"
Wani firgita Aziza ta yi ta miƙe tsaye ta ce
"Hajja yaushe aka yi aike yankin ja'i har Innu Maciji yace zai zo?" ita ma Hajjar miƙewa ta yi ta ce
"Aziza lafiya kuwa?"
Kama hannunta Aziza ta yi ta ce
"Hajja tun yaushe ne Azima bata gida?" Hajja ta ce
"Ban sani ba Aziza, dan ni tun wayewar garin yau ban ga Azima da idona ba, ba shine nake tambayarki ko kin ganta rafi ba"
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!" Aziza ta faɗa tana jan mayafinta zata fita Hajja na tambayarta ina zata je, har ta kai bakin kofar zanar gidansu bata kai ga fita ba suka yi mugun karo da Baffa wanda ya shigo a fijajan hankalinsa a tafin hannunsa, da sauri Hajja da Aziza suka tare Baffa,ganin yanayin da Baffa yake ciki yasa Aziza fara addua a ranta Allah yasa dai Azima ba Innu Maciji ta kashe ba,idan kuwa ta kashesa tabbas ta b'allowa yankin kwana yaqi.
Da sauri Aziza ta ɗibawa Baffa ruwa ta kawo ta ba wa Hajja, Hajja ta karba ta ba wa Baffa wanda da kyar ya yi kurbi daya wanda ya taho masa da kuka,ganin haka yasa ita ma Aziza ta fashe da kuka, Hajja na ganin Aziza ta fashe da kuka ita ma tasa kuka,nan aka rasa mai rarrashin wani,da kyar cikin kuka Aziza ta kama hannun Baffa tana faɗin
"Dan Allah Baffa ka gaya mana meke faruwa!"
" *AZIZA? JUMALA! AN KASHE INNU MACIJI!! DA MASU TARBAN BAƘIN SHIGOWA YANKIN KWANA SU BIYU!*"
BAFFA na fadin haka Aziza ta sake hannunsa tare da yin zaman yan bori!
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! mai Azima take son zama?" kasa motsin kirki Aziza ta yi illa komawa da ta yi tana bin Baffa da Hajja da suke kuka da ido, sai zuwa can Hajja ta ce
"Ya aka yi da gawar har an binne su ne?" Baffa ya girgiza kai ya ce
"Ba zamu iya hakan ba, ana ganin gawar ba shiri Arɗo da Chubaɗo da Ori suka ce garkuwan fulani da Galadima da Liman da mutum biyar a fada su tafi yankin ja'i da gawan, yanzu Allah ne kadai yasan me zai faru an kashewa yankin ja'i Innu Maciji, taya zasu fara fuskantarmu su fahimce mu? Innalillahi wa inna ilaihirrajun!" nan suka ci gaba da jajinta lamarin inda a karshe Hajja da Baffa zasu fita Hajja ta ce
"Aziza zo muje" murya can kasa wanda take ji da kyar ma take maganar ta ce
"Hajja kuje zan zo"
"To amma kiyi lullubi kafin ki fito anani ko?" Aziza ta gya ɗa kai, kanta a sunkuye, Hajja da Baffa suka fice,dan Aziza tana ji ba zata iya tafiya ba jin kamar kafafunta basu gangar jikinta.
Bayan fitar su Hajja da Baffa kamar da rabin awa sai ga Azima ta shigo babu sallama kamar an wurgota ko kallon Aziza ba ta yi ba, da ido Aziza ta bi Azima tana ji kamar ta haɗa musu guba su sha su mutu ko duniya zata zauna lafiya.
Azima na shiga bukka ta hau dariya kasa-kasa gami da faɗin
"Innu Maciji na kashesa! Yau kuma *MAGAJI BAWA* zaka mutu! Sauran mutanen yankin nan za a kashesu ne idan tarzoma ta tashi, dan nasan yankin ja'i ba zasu hakura ba, ta fada tana murmushi tare da zura hannu dan ta dauko zaren sakar dana da ta saka a kayan Aziza amma ta ji wayam,ido buɗe take warware kayan Aziza amma bata gani ba,kamar mahaukaciya haka Azima ta fito ta zo ta tsaya a kan Aziza
"Ke Aziza Magaji! Nayi ajiya a kayanki amma ban gani ba" dago kai Aziza ta yi ta kalli Azima sannan tasa hannu ta share hawayenta ta miƙe a hankali cikin sanyin murya ta ce
"Me kika ajiye a kayana?"
"Mtswww! Bana son rainin hankali Aziza! Ki bamu abuna!?"
"Wani abunki?"
"Zaren sakar dana da na ajiye a kayanki" Aziza ta jinjina kai ta ce
"Owoohhh zaren dana? Na ƙonasa!!" wani zabura Azima ta yi tasa hannu ta shaqi wuyar Aziza ta ce
"Kin ƙona fa kika ce!? Ke meyasa baki son mu dauki fansa ne kam!? Me yasa ba zaki bari na rama mana abunda aka mana ba! Kin ƙonasa!? Aziza ke mahaukaciyar wace al'karya ce? Na ce ke....." ture hannunta Aziza ta yi daga wuyarta sannan ta kwalfa mata mari ta ce
"Kin kashe Innu Maciji da samarin fada mutum biyu! Akan me!"
Ɗagowa Azima ta yi ta wanke Aziza da mari ita ma, ta kuma shaƙe mata wuya
"Kin min asara! Shin kin san da cewa jejin lore sau daya tak suke ba wa mutum abu? Kuma dole da zaren sakar dana zan iya kashe Baffa me yasa! Aziza na ce me yasa! To wlh kin jawowa kowa, yau kisan da zanyi ban ga mai dakatar dani ba!" tana gama faɗi ta zama macijiya ta sulale ta fice, ganin haka yasa Aziza ita ma ficewa da gudu.
🍃🍃🍃🍃🍃
COMMENT AND SHARE
BY MOMYN AHLAN BAIWAR ALLAH MASOYIYAR ANNABI MUHAMMADU S,A,W,🙌🏻🥰
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah'0_
🍃🍃🍃🍃🍃
🤦🏻♀️🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*KASSH! WLH ALLAH TAMBAYAR NAN TA ISHENI! TUN BAN SO NAYI MAGANA BA AMMA INAJI DOLE NAYI YAU DA MANYAN HARUFA! FISABILILLAHI MUTUM NA GANIN ABU DA IDONSA AMMA A ISHENI DA TAMBAYA MARAR AMFANI! (BOOK DIN NA KUƊI NE? SANNAN NAWA?KO KUMA AU DAMA NA KUDI NE?) HABA DAN ALLAH! TUN A FARKON SAMAN PAGE NA RUBUTA NA KUƊI NE NAIRA ƊARI KACAL DAN MASOYANA, KI DUBI ALLAH IDAN KIN SAN BA ƊARIN ZA KI BIYA BA KI DAINA KIRANA KO TURO MIN SAƘON CEWA KINA BUKATA BA DAN NI BA DAN ALLAH,👏🏻 MAZA KUMA MASU DAUKAR LAMBATA KU MIN MAGANA MAY BE TA FACEBOOK NE,KU MA KU DUBI ALLAH KU DAINA KARKU JAZA MIN MAGANA, GRP DINA BABU MAZA👏🏻*
*MASU CEWA CMPLT SUKE SO, ABUNDA KO SATI INAJI BAN KAI DA FARA SAKIN BOOK DIN BA, YANZU NAKE TYPING DINSA.*
*SANARWA*
_WA INDA BASU BIYA KUƊIN KARATUNSU BA, SU KOKARTA SU BIYA NAN DA KWANA UKU, SABIDA NA BUƊE PAID GRP YAU, SANNAN FREE PAGE ZAI IYA YANKEWA NAN DA KWANA UKUN IN SHA ALLAHU, DAGA NAN ZAMU ƊORA NE DAGA PAID GRP, BANA SO AYI WANNAN CAKWAKIYAR BABU KU DAN CAKWAKIYA BA A MA YI KOMAI BA😊 KU DAI KU BIYONI DA NAIRA ƊARINKU DAN KUJI YADDA ZATA KAYA A CIKIN LITTAFIN AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE, NGD MASOYANA MASU NUNA MIN ƘAUNA_😊🤙🏻
*STILL FREE..*
🅿️==1️⃣9️⃣↪️2️⃣0️⃣
Amma bata ga inda Azima ta yi ba, rafin jimulo ta je amma ba Azima bare mai kama da ita, hankali tashe Aziza ta hau neman Azima amma bata ganta ba, jejin kwana ta nufa ta hau dubata amma bata ganta ba, riƙe kai Aziza ta yi tare da furta "YA ALLAH! dabadin ace kisan kai haramun bane babu abun da zai hanani ban kashe kanmu a yau ba kowa ya huta, wannan wani irin bala'i ne haka? Ya Allah ka yaye mana, Allah ka bani mafita ka nuna min haske, Ya Allah ka nuna min hanya! Ya Allah ni dai bana da masaniya a kan fansar da Azima take dauka, dan a iya sanina banga wanda ya mana laifin komai ba, Ya Allah idan ita haka halinta yake Allah kai kasan yadda zakayi da ita, Allah ka taimake Baffana da Hajjata da jama'ar mahaifata! Ya Allah ka karesu daga dukkan sharri!" Aziza ta karasa adduar hawaye masu zafi suna wanke mata fuska tare da jinginuwa a jikin bishiya, wani nishi taji na tashi a bayanta da sauri ta buɗe idonta da ta lumshe tana waige daga ina nishin ke fitowa, taji ashe ta bayan bishiyar ne,saurin leƙawa ta yi nan ta iske wata budurwa kwance bakinta sai jini ke bulluƙowa, cike da tashin hankali Aziza ta karasa ta ɗagota, tana dudduba meyasa meta,goshinta ta kalla ta ga bakin maciji wanda yake sara ne na Azima, ihu Aziza ta yi tana ajiye kan budurwar a kasa ta tashi da sauri tana ja da baya ta kuma sakin wani mahaukacin ihu tana furta "AZIIIMAAAAAAA!!!?" da gudu ta bar wajen dan babu taimakon da zata iya yiwa budurwar dan kuwa gubar ya shige mata jiki sosai dan harta idonta da tafin hannunta sun koma blue.
Duk inda Aziza take tunanin zata ga Azima amma da ta je sai dai ta iske gawa, hakiƙa fadin yadda hankalin Aziza ya tashi b'ata lokaci ne, ga shi ta rasa yadda zata yi, bata kara shiga ruɗu ba sai da ta yi gamo da gawar mutum takwas wanda Azima ta kashe, daga karshe Aziza ta koma tayi zaman yan bori.
🍃🍃🍃🍃
*YANKIN JA'I.*
a lokacin da garkuwan fulanin yakin kwana suka isa yankin ja'i da gawar Innu Maciji hakika sun ga tashin hankali, sun ga masifa da bala'i a wajan jama'ar yankin ja'i, ko kaɗan sarkin fulanin yankin ja'i wato Jawo da kuma mai unguwa Sodangi da sauran duk wanda yake yankin ja'i basu tsaya sun saurari su Garkuwan fulanin kwana ba, suna isa da gawar fadar sarki Jawo nan yankin ya ɗauka daga tafiyar Innu Maciji yau yankin kwana sun kashesa, nan jama'ar yankin ja'i suka janyo wuƙaƙe da adduna da sanda kokara,suka yi kan su garkuwan fulanin kwana tare da fadin su ma ba za a barsu a raye ba, Galadima da Liman suka ce yadda suka tunzura gwanda kawai su gudu, garkuwan fulanin kwana ya ce bai kamata su gudu ba tare da sun musu bayanin abunda ya faru ba" Galadiman fulanin kwana ya ce
"Baka da hankali ne garkuwa? Ka ga yadda suka haukace suna ihu ka ce mu tsaya musu bayani taya zasu sauraremu? Ka zo kawai mu gudu dan ceton ranmu daga baya idan suka yi sanyi sai mu dawo! Amma kaga yanzu suna abu kamar wa inda mahaukacin zaki ya cije su" Garkuwa ya ce
"A gaskiya ba zamu tafi ba tare da munyi musu bayani ba,tunda duk abunda ya faru mu muka ja wa kanmu! Da ace mun bi shawaran Magaji da ba haka ba"
"Amma dai garkuwa kasan rashin hakuri irin na yankin ja'i da haukarsu ko? Ka zo mu gudu idan ba haka ba zasu iya kashe m...." maganar da Liman bai karasa ba kenan yaji saukar dutse a goshinsa,nan ya riƙe goshin yana faɗin "Ya Rabbi!" kafin su Garkuwa su dago nan suka ji ihu, inda gaba daya ahalin yankin ja'i mata da mazansu kowa ka gani da makami nan suka yo rututu suna shirin kai wa su Garkuwa farmaki,nan suka hau musu ruwan manyan duwatsu kafin su isosu,ganin haka yasa Galadiman fulanin kwana da Limamin fulanin kwana suka kwasa a guje dan tseratar da ransu, sauran mutum biyar na fada mutum uku su ma suka arce da gudu aka bar Garkuwan fulanin kwana da mutum biyu na fada su uku kenan, kafin Garkuwan fulani ya yi kokarin faɗin wani abu tuni, an rufesu da duka da sanda, yayinda ƙanin Innu Maciji yasa adda ya sare daya daga cikin ɗan fada a wuya yana sare san nan ko minti daya bai yi ba yace ga garinku, ganin haka yasa garkuwan fulanin kwana yace shi da dayan ɗan fada su gudu, da kyar suka kwace suka hau dokinsu ba shiri suka sab'i hanya jikinsu jina-jina da jini, dan garkuwa ma kam an saresa a hannu.
Har mutanen yankin ja'i zasu bi su garkuwa, Sarki Jawo ya ce su dawo ai sun b'allowa kansu yaƙin da basu san wanda zai tare musu ba, za ayi wasika a tura musu su shirya tarban yaƙi,kuma suna da yaƙinin zasuyi nasara ta hanyar shafe al'karyan kwana tunda Magaji Bawa ya yi murabus!.
@@@@@@
*YANKIN KWANA.*
haqiqa yau yankin kwana tana cikin ruɗu da ruɗani,yayinda suka jera gawawwaki har na mutum sha ɗaya wanda saren maciji ne a jikinsu.
Yau da safe mutum biyu sun sha dafin maciji sun mutu, Innu maciji saran maciji ya mutu,yanzu kuma ga gawawwakin mutum sha daya, tsananin tashin hankali yasa suka kasa yiwa gawawwakin jana'iza ga magriba ya gabato, ganin haka yasa sarki Chubaɗo bada umarnin a musu sutura a binnesu kar su yi kwanan keso, da kyar suka yi musu jana'iza suka binnesu, bayan sun fito daga maƙabarta sai ga isowarsu Galadiman kwana shi da Liman a fujajan, da sauri mutanen yankin kwana suka tarbesu suna tambayarsu me ya faru? Baffa ya kalli goshin Galadima dake zubar da jini an fasa masa goshi,Baffa ya ce
"Daga ganin goshin Galadima ba sai an tambaya ba! Mun taro yaƙi ko? Ina su Garkuwa!?"
🍃🍃🍃🍃
😔😔😔 1readmore
Post a Comment for "AZIZA DA AZIMA 11-20"