AZIZA DA AZIMA 1-10
AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL
بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _ZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
🍃🍃🍃🍃🍃
*FREE..*
🅿️==1️⃣↪️2️⃣
"Subhanallahi! Wannan bala'i ya yi yawa, a ce a kwana uku an kashe mutane goma? Masu kama macizai mutum takwas, wannan wani irin masifa ce ta macizai da ya fara addabar mu haka a gari? abu sai tsamari yake yi, tun ana samun sara kaɗan-kaɗan, ga shi saran macizai din bakinsu da girma! Me yake shirin faruwa ne haka a cikin wannan alƙarya na da mutanen yanki na?" cewar mai garin yankin kauyen kwana dake jihar yola da yake can cikin dajin fulani wanda ya cika da albarkatun korayen shuke-shuke, a wannan sassanin fulani ne suke rayuwa a wannan yanki, kuma su na da yawa dan sun hayayyafa, basu fita cikin gari kuma ba a shigo musu.
Jama'ar da suke tsaye a wajen ne cike da jimami da fargaba su na alhini, wani dattijon tsoho cikin harshen fullanci ya ce
"Gaskiya muna cikin hatsari a wannan alƙarya, ga shi yanzu an fara samu kisan macizai da yawa, ya kamata mu san abun yi" sai tattaunawa suke yi ta yadda zasu shawo kan wannan babbar matsalar da suke ciki, wata kyakkyawar budurwa ce a tsaye a can gefe fara sol, tana da idanun mage, sanye take da kayan fulani ta naɗa farin mayafi a saman kanta, ta rufe gefen fuskarta da shi, rabin gashinta ya sauko ya rufe mata rabin fuska wanda ya sake hana asalin kyawun nata fitowa sosai a gani,kafarta babu takalmi, a hankali ta bi mai kama macizai wanda aka kashe da kallo, ranta a b'ace ta juya a hankali tana tafiya dukkan sassan jikinta yana lankwasawa, a yadda take taka kasa da ka ganta kasan bata yi maka kama da cikakkiyar mutum ba, daji ta yanka ta shiga cikin korayen bishiyoyi inda zata samu yar uwarta kawai take hari, can kusa da wani rafi mai sanyi da dadin kallo ruwan fari k'al da shi abun sha'awa taja ta tsaya, bata ankara ba taji saukan wani zureriyar wutsiyar maciji🐍, ko kaɗan hakan bai tsoratata ba, tunda ita ma macijiyar ce, d'aga idonta ta yi saman bishiyar da wutsiyar macijin ya sauko mata, ta kalli yar uwarta wanda dukkanta macijiya ce,a hasale ta ce
" *AZIMA!!?* me yasa kika son kashe mutane kwanan nan ne kam?" macijiyar da aka kira da Azima a hankali ta sulalo daga saman bishiya ta kanannaɗe yar uwarta tana lasarta da harshe, hannu dayar tasa ta ture kanta a macijiyar, sannan ta ce
"Azima tambayarki fa nake yi?" gefe ta koma ya yinda ta saki wani huci ta girgije nan ta zama rabi mutum rabi macijiya, daga ƙugunta abun da ya yi sama mutum ce, daga kugunta abun da ya yi ƙasa macijiya ce.
Dariya ta sheƙe da shi cikin wata murya mai amo da rashin dadin sauraro, sai jijjiga take yi tana naɗe jelar macijinta ta ce
" *AZIZA!* bana mantuwa kuma bana yafiya!! Duk wanda ya shiga gonata sai na hallaka shi, sai na ga bayansa ko ma waye! Duk wanda nake kashewa sun tab'oni ne! Dan haka bana bukata ki din ga tuhumata akan abun da kike da masaniya a kai"
"Amma Azima kisan ya yi yawa! Da an miki laifi kaɗan sai kisa? So kike yi sai an gano mu ba mutane bane macizai ne mu a kore mu a gari?"
Rintse blue eyes dinta Azima ta yi sannan ta buɗe tana zaro harshenta suffan na macizai sak ta ce
"Ina so na bar wannan alk'aryan, ina so na shiga cikin gari wanda yake da al'umma da yawa ta yadda zan tarwatsa su!" girgiza kai Aziza ta yi ta ce
"Ke nan za ki iya tafiya ki bar su Baffa da Hajja?"
"Me zai hana Aziza!? Ina da burin shiga cikin jama'a masu yawa duk da na san ni din ba mutum ba ce!"
"Shigarki jama'a ba alkhairi bane Azima, dan haka ki bar wannan maganar ki zo mu tafi gida kar mu koma mu samu Baffa ya dawo ya titsiye mu da tambaya daga ina muke, amma dan Allah ki koma mutum tun daga nan" Aziza ta faɗa tana yin gaba, dariya Azima ta yi a madadin ta zama mutum kamar yadda aka ce mata sai ta rikiɗe ta zama katuwar macijiya mai sheƙi da ban tsoro, ko da Aziza ta juya ta ganta a haka girgiza kai ta yi, ba tare da ta ce mata uffan ba.
Sai da suka kusan isowa gida kafin ta girgije ta zama mutum, yadda yar uwarta Aziza ke tafiya haka ita ma take tafiya, mayafinta da ta ajiye ne kusa da gida ta dauka ta yi irin lullub'in da yar uwarta ta yi, su na yin wannan lullub'i ne saboda idanunsu da yake abun tsoro barin ma kwayar idon Azima blue, ita kuma Aziza idon mage mai fari-fari, ko kaɗan basu da baƙin ido,shi yasa Hajja mahaifiyarsu ta basu su din ga lullubi, shi yasa idan sun yi lullubin suke saukowa da dogon gashinsu ta gefe ya rufe musu gefen fuska, ga shi dai alk'aryan duk fulani ne kuma kyawawa, amma duk fadin yankin kwana babu mace ko namijin da ya kai su *AZIMA DA AZIZA* kyau.
Ko sallama basu yi ba suka shiga gidan suka iske mahaifiyarsu Hajja a jikin murhu tana aikin hura kara, Aziza ta ce
"Sannu da aiki Hajja" dagowa ta yi ta kalli kyawawan yan biyun nata ta ce
"Yauwa sannu Aziza, daga ina ku ke haka? Tun safe fa ku ka fice a gidan nan"
"Amm Hajja muna rafin jimulo" murmushi Hajja ta yi ta kalli Azima wanda idonta yake kan garin Mahaifiyarta, haka kawai take ji ta watsawa garin dafi, Aziza ta ce
"Hajja karan ya ƙi kamawa ne?"
"Eh Aziza ya ƙi kamawa wallahi ga idona ya yi ja yana min zafi"
"Ayya sannu Hajja bari na hura miki!"
"Yauwa yar albarka hura min, Azima lafiya kuwa kika ƙurawa garin da zamu yi tuwo ido?" murmushi ta yi ta ce
"Lafiya lau Hajja" girgiza kai Hajja ta yi ta duƙa ta shige bukka, ita kuma Aziza Hajja na shiga bukka ta rufe idonta ta rintse nan idon ya dawo ja, bakinta ta buɗe ta fiddo da turirin ta hura a murhu nan kuwa ya kama da wuta, Azima kuwa wajan garin ta je ta bude bakin tana shirin zuba dafi sai ga sallamar Baffa, da sauri ta mai da harshenta, amsa sallamar Baffan suka yi tare yi masa sannu da dawowa ya amsa, fitowa Hajja ta yi,ita ma ta ma sa sannu da dawowa tare da shinfiɗa masa tabarman kaba, ya zauna, Aziza ta ɗiba masa ruwa ta kawo masa, sannan suka zauna dukkansu.
Sai da Baffa ya sha ruwan sannan ya saki ajiyar zuciya, cikin fulatanci Hajja ta ce
"Baffan Azima da Aziza lafiya kuwa?"
"Ina kuwa lafiya, wannan alk'arya ya kafu tsawon shekaru sama da hamsin, anyi gwagwarmaya da aljanu da mayu, amma a yanzu bala'in da yake tunkaro wannan alk'arya ya yi yawa, ina wannan shahararren mai kama macizai din nan, Ilu Mai Macizai?" Hajja ta ce
"Eh na ganesa,waye bai san Ilu mai Macizai ba"
"To shi ma an kashesa yau" salati Hajja ta sa tana tafa hannu ta ce
"Hande in bone ni Jamila, yanzu shi ma Ilu mai macizai an kashesa?"
"Eh har ma anyi masa jana'iza an binnesa, ga shi duk macizan da ake kamawa babu wanda bakinsa ya yi dai-dai da saran da ake samu, ga shi yanzu har zargi ya fara shiga tsakanin mutane da mutane, yanzu haka mai gari ya yiwa Jarman Macizai aike da wasiƙa,kin ganesa?"
Hajja ta riƙe hab'a alaman tunani ta ce
"Jarman Macizai ba wannan na yankin al'karyan jimo ba?"
Baffa ya ce
"Eh shi dai, ya ma amsa da gobe zai zo, zai taho da ruwan wani magani wanda za a ba wa kowa ya sha wanda hakan ne zai bayyana waye ba mutum ba a cikin al'umman yankin kwana, kin san titsiyeni aka yi a kan su Azima da Aziza, wai yarana basu abu irin na mutane, shi ne za ayi wannan gwajin" wani firgita Azima har ma da Azizan suka yi, suka kalli juna, ba tare da iyayensu sun san halin da suke ciki ba,tuni idon Azima ya kara komawa blue sosai, nan ta kalli fatar jikinta ta ga ta fara zama blue da sauri ta miƙe ta shige bukka, ita ma Azizan tashi ta yi, Hajja ta ce
"Dan kawai yara basu mu'amala da kowa, sannan idonsu ba baƙi ba shikenan sai a saka mun yara a gaba?" Baffa ya ce
"Amma kin san dai har da maganar aurar dasu, bisa al'ada ta wannan yanki namu yara da sun shekara 11 ake aurar dasu, yanzu kuma su Azima da Aziza su na da shekara 15 kin ga kuwa dole a saka musu ido mun ƙi aurar dasu, ga shi kullum Arɗo sai ya min magana" tabe baki Hajja ta yi ta ce
"Allah ya kyauta amma ai aure lokaci ne" ta miƙe taje duba ruwan tuwonta.
A bukka kuwa sadda Azima ta shiga nan kasanta ya koma macijiya har sai da ta cika bukka din, kalar fatarta ta koma blue, Aziza ce ta biyo bayanta ta ce
"Azima ki koma dai-dai kar Hajja ta shigo ta ganki haka fa?"
A hautsine Azima ta ce
"Dole na kashe Jarman Macizai! Nayi alkawari sai na ga bayan wanda yake shirin ya san su waye mu na asali!."
🍃🍃🍃🍃🍃
*HANZARTA BIYAN NAIRA ƊARINKI KACAL🤗 DAN JIN CAKWAKIYAR DAKE CIKIN WANNAN LITTAFI, MOMYN AHLAN TANA KAUNAR MASOYANTA*🤗
COMMENTS
AND SHARE
BY MOMYN AHLAN🥰🤗
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
🍃🍃🍃🍃🍃
*FREE..*
🅿️==3️⃣↪️4️⃣
"Ba ki da hankali ne Azima? Jarman macizai za ki kuma kashewa? To bari kiji! Kin ga wannan kashe-kashen shi zai sa a gane su waye mu, dan Allah Azima karki kashesa, bana son kisan da kikeyin nan" Aziza ta faɗa tana bin Azima da kallo, cikin huci Azima ta ce
"To tsammaninki me zai faru? Idan har jarman macizai ya kawo maganin gwaji dan a tabbatar da su waye ba mutane ba? Ke a tunaninki mutanen yankinmu zasu barmu a raye ne? Ina kashemu zasu yi, dan haka kafin hakan ta kasance ni nan zan kashe Jarman Macizai kuma ba ki isa ki hanani ba" Azima ta fada tana komawa mutum tare da ficewa a bukkan, tana fitowa hanyar waje ta nufa Hajja ta ce
"Azima ina kuma zaki je bayan baku jima da shigowa gidan ba?" kafin Azima ta yi magana Baffa ya fito daga kewaye yana fadin
"Ban hanaku fita sakakan ba Azima? Ina za kije?" cikin in-ina da kame-kame ta ce
"Zan duba abu na ne a nan waje" Baffa ya ce
"Ba za ki duba ba koma ciki" haɗe rai sosai Azima ta yi tare da yiwa Baffa wani irin kallo ta koma fuuu, da kallo Baffa da Hajja suka bi Azima, jiki a sanyaye Baffa ya koma ya zauna, tunanin abunda ya faru shekara ashirin shike dawo masa kwakwalwa, kar dai ace fansar da *Banju ya ce zai dawo ya daukar wa kanwarsa Bahula da kansa shine ya dawo dauka kan yaransa!?* Haqiqa shima zuciyarsa ta fara yi masa saqe-saqe a kan yaransa ba cikakkun mutane bane amma baya so zarginsa ya tabbata, rintse ido ya yi yana karanto kalmar "Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!" kallonsa Hajja ta yi ta ce
"Lafiya kuwa Baffan Azima da Aziza?"
"Haqiqa Jumala ina jin tsoro!"
"Tsoron me fa Baffan yan biyu?"
"Inajin tsoron furucin Banju lokacin da zan kashesa maganarsa ta karshe, ko kin manta da kalman da ya ce...." Baffa bai karasa ba Hajja ta dakatar da shi
"A'a Baffan Azima da Aziza! Karka yiwa yarana baki! Taya wa inda suka mutu shekara ashiri a ce sun dawo? Azima da Aziza dai ni na haifi yarana! Kuma ni mutane na haifa, kwata-kwata wannan maganar bai kamata ace ya fito daga bakinka ba, kai da kanka ka fara zargin yaranka to ba dole jama'ar gari ma su fara zarginsu!" Hajja ta faɗa cikin sosuwar rai, girgiza kai Baffa ya yi ya ce
"Ba haka bane Jumala, amma dai jikina ya yi sanyi! Allah ya kaimu gobe jarman macizai zai zo ya warware komai" ita dai Hajja ba ta sake cewa kala ba, illa aikinta da ta ci gaba da yi, Azima kuwa tana saman bukka a macijiya tana jin maganganun Baffa, a ranta take ayyana yadda zata kawar da Baffa!.
🍃🍃🍃🍃🍃
Washe gari tun kafin garin Allah ya waye Azima ta sulale ta fice, hanyar yankin Jimo dai-dai kan layin shigowa yankin kwana a kan wata babbar bishiya ta kwanta ta nannaɗe idonta sun kara komawa blue, tana jiran isowar jarman macizai, awanta kusan uku kafin ta hangosa, wani murmushi ta yi mai tattare da zallar mugunta kafin ta sauko ta koma mutum, tsayuwa ta yi bayan ya gama shigowa yankin kwana.
Yana kan tafiya akan dokinsa a hankali ya hangi budurwa tsaye a hanyarsa,magana ya hau mata amma shuru, tana tsaye da lullubi, saukowa ya yi a kan dokin ya tunkaro inda take tsaye, sai da ya zo kusa da ita kafin ya ce
" *MUTUM KO ALJAN!?"*
Murmushi ta yi tana lankwasa harshe ta ce
" *RUWA BIYU!"* sannan ta juyo ta yaye mayafin da ta lullube jikinta ta jefar, jarman macizai na ganin idonta ya yi saurin ja da baya, dariya Azima ta sheqe da shi ta ce
"Na ga bai kamata ace kasha wahala ba wajan zuwa gwajin wanene wanda ba mutum ba a wannan yankin! Gani na zo da kaina dan dakatar da kai! Ba zaka shige ba sannan ba zaka koma ba!" da sauri jarman macizai ya yi baya dan dauko kayan aikinsa tsalle daya Azima ta yi ta zama macijiya ta cakume jarman macizai nan suka hau kokawa, duk yadda yaso kwace kansa daga hannun Azima ya kasa, daga karshe ta rufesa da sara, sosai ta yi masa jina-jina sai da ta ga ya daina mutsu-mutsu sannan ta sakesa ta sulale ta yi hanyar rafin jimulo, tana isa rafin ta hau kyalkyala dariya nan ta zube kusa da rafin.
🍃🍃🍃🍃🍃
A cikin unguwa kuwa ana nan ana jiran isowar jarman macizai, tun ana sa ran ganinsa takwas har goma, inda a karshen mai unguwa ya ce aje a duba ko lafiya a binciki hanya aka tura mutum uku.
Ai kuwa can suka gano gawar jarman macizai a yashe cikin jini, cikin tashin hankali suka juya da mugun gudu suka koma suka sanar da jama'ar gari an kashe jarman macizai.
Fadin tashin hankalin da mai unguwa da jama'ar gari suka shiga b'ata lokaci ne.
🍃🍃🍃🍃
Fitowa Aziza ta yi daga bukka dan tun sadda taji motsin yar uwarta jikin dare kafin garin Allah ya waye jikinta ya bata ta tafi kashe jarman macizai, abunda yasa bata yi yunkurin bin bayanta ta dakatar da ita ba sabida tasan dole Hajja da Baffa su leƙo duba lafiyarsu, tana fitowa dauke da murmushi a fuskarta Hajja ta ce
"Aziza ke kin tashi? Azima ta farka ta yi sallah kuwa?" tsilli-tsilli da ido Aziza ta fara kafin ta ce
"Eh Hajja ta tashi ta yi har ma ta fita wai ta je rafin jimulo" Aziza ta karasa maganar da in-ina sabida da asuba da Hajja ta shigo tada su kara Aziza ta jera kusa da ita ta yadda zata ga kamar Azima ce ke bacci, dan lokacin da Azima ta fita Aziza ta ji motsinta tsoron kar su fita duka a gane yasa Aziza hakura ta kwanta, dan Baffa kunnuwansa akwai saurin jiyo abu.
Kallon Aziza da kyau Hajja ta yi kafin ta ce
"Me ku ke zuwa yi kullum ne a rafin jimulo?"
"Ba komai Hajja kawai rafin akwai dadi ne, ga iska mai dadi, Hajja kin manta sadda kike kai mu muyi wasa?" murmushi Hajja ta yi ta ce
"Eh na tuna, yanzu dai je ki kirawo Azima ku zo kuci abinci"
"To Hajja, Baffa ya fita ne?" Aziza ta tambayi Hajja kamar bata san Baffan ya fita ba, Hajja ta ce
"Eh ya fita kin san ai jiya yace yau Jarman macizai zai zo, yace min idan yazo zai zo ya kiramu muje gabadaya ayi gwaji" Aziza ta jinjina kai tana fadin "to Hajja bari naje na kira Azima kafin Baffa ya dawo"
"To a dawo lafiya,ki tabbatar kinyi lullube da kyau fa"
"To Hajja" Aziza ta fada tana ficewa jiki a sanyaye, tana fita da gudu ta yanki rafi inda tasan Azima ba zata wuce can ba.
Tana zuwa ta sameta kwance a kusa da rafi.
Hannnu tasa ta janyota ta ce
"Kin kashesa ko Azima? Na ce kin kashesa ko!?" dariya ta kyalkyala cikin amo marar dadin sauraro ta ce
"Ai na gaya miki Aziza sai na kashesa!"
Rike kai Aziza ta yi ta ce
"Me kika so ki zama ne kam Azima?"
"Bana son ganin zaman lafiya a wannan yankin! Na fi so ayi ta b'arin jini! Ina so na haɗa maƙotan yankunan nan faɗa, duk wani mai kama macizai wanda za a yi masa aike ya zo yankin nan sai na kashesa! Kin ga daga nan za a fara yaƙi tsakanin yankuna da yankuna, sannan dama akwai y'ar tsama tsakanin yankin kwana da yankin tudu da kuma yankin Ja'i nasan kuma dole mai unguwa zai bukaci taimakonsu, duk wanda aka turo ni kuma zan kashesa! Na tabbata daga lokacin zaman lafiya ya kare, Baffa shine jarumi na farko a wannan yankin wanda da shi aka yi gwagwarmaya kinga kuwa ba mamaki a wajan yaƙin a kashesa!"
🍃🍃🍃🍃
*DAN ALLAH JIYA NA FARA LITTAFIN NAN, BAN BUƊE PAID GRP BA, SABIDA BAN GAMA FREE PAGES BA,KUYIWA ALLAH IDAN BA KU GA UPDATE DINA A RANA BA KARKU CE ZAKUYI KORAFI, NA SANI DOLE NE TUNDA NA FARA ZAN KARASA DA IZININ ALLAH, SABIDA HAKA KU MIN UZURI RANAR DA BAKU GA UPDATE BA TUNDA BAN GAMA FREE PGS BA, IDAN ZAKI BIYA DARINKI YANZU FYN, IDAN KUMA SAI AN GAMA FREE PG NE DUK DAYA AMMA DAN ALLAH BAN DA KORAFI, MATAR GIDA CE NI MAI IYALAI, UWA UBA KUMA DALIBAR MAKARANTA, FATAN ZAKU FAHIMCENI,INA GODIYA GA MASOYANA MASU GANIN SUN BIYAN KUDIN KARATUNSU, NA GODE DA BIBIYATA DA KUKEYI, ALLAH YA BAR KAUNA, 1 LUV*
COMMENTS AN SHARE
BY
MOMYN AHLAN.
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: https://chat.whatsapp.com/BXDHlYEJdRi65a26Qt5OSe
🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
🍃🍃🍃🍃🍃
🥁🥁🥁🥁🥁🥁
💃🏻💃🏻💃🏻😍😍😍
*YAU TAMBARINA NA MASOYA NE,INA GODIYA DA SAKONNINKU,KIRAN WAYA, KAI MA SHA ALLAH, ALLAH DAI YA BAR KAUNA,INA ALFAHARI DAKU A DUK INDA KU KE MASOYANA, ALKAIRIN ALLAH YA KAI MUKU HAR KUJERAR ZAMANKU😍*
*FREE..*
🅿️==5️⃣↪️6️⃣
Zaro ido Aziza ta yi tana kallon Azima kafin ta ce
"Na rasa dalilinki na son ganin bayan Baffa! A yadda na fahimceki, ke ba ki ƙi kowa ya mutu ke ki rayu ba, idan kika samu dama na tabbata za ki kashe Baffa" dariya Azima ta kyalkyale da shi tana kewaye wajan kafin ta koma ta haɗe rai sosai ta ce
" *AI BA YAU BANE KAWAI NA SHA GWADA HAKAN!* ko a yanzu na samu sarari sai na kashe Baffa! Ko kin manta na sha yunkurin kashesa!? Lokuta da yawa ke ce kika katse min burikana! Ga shi ke ban san ya zanyi dake ba! Ke ta biyu na ce! Ba zan iya kasheki ba! Sabida duk muguntar gubana naki yafi nawa! Kuma ina sonki yar uwata! Da ace nike da karfin dafin da kike da shi da na jima da shafe wannan yankin kakaf dinta!" Azima ta fada tana daga hannuwanta sama.
Aziza ta girgiza kai ta zauna a kasa tare da fashewa da kuka ta ce
"Azima ba zan taba bari ki cutar da Baffa ba,ko da kuwa zaki iya,ni dai a gaskiya inaji a jikina kamar ni da mutum ce! Ban san a garin yaya muka zama macizai ba, miye dalilinki na son kashe Baffa Azima!?" Aziza ta faɗa tana haɗa kai da guiwa tana ci gaba da kuka,duk sadda ta kalli jikinta ta ganta a macijiya tana jin zafi a zuciyarta, ta yi nisa sosai a kuka ta ji wani irin murya na namiji wanda yake abun tsoro an bata amsar maganarta.
" *ZUNUBIN DA BAFFANKU YA AIKATA NE YAKE BIBIYARKU!, TARE DA GOYA MASA BAYAN DA JAMA'AR YANKIN NAN SUKA YI!*" da sauri a matukar firgice Aziza ta dago tana waige ta ga daga ina ne maganar ya fito? Amma bata ga kowa ba illa Azima dake wasa a cikin rafi kana ganinta zaka san tana cikin nishaɗi, ta zama macijiya ta koma ta zama mutum.
Sauri tashi tsaye Aziza ta yi tana waige a fili ta kara furta kalman da ta ji "Zunubin da Baffanmu ya aikata? Me Baffanmu ya yi kuma?" tambayoyi ne maqil a ranta amma babu mai bata amsa, ko dai zata je ta tambayi Baffa ne? Kai amma kuma idan ta yi haka za a gane su ɗin ba mutane bane, riƙe wuyanta ta yi jin kamar zuciyarta yana shirin fitowa bakinta, kallon Azima ta yi ta ce
"Azima ki zo muje gida"
"Tare muka zo dake ne?"
"Idan ma ba tare muka zo ba Hajja ta ce mu dawo tare yanzu, kar Baffa ya dawo...." Aziza ba ta karasa ba Azima ta fito tana fadin
"Ke komai ki ce Baffa?"
"To idan ban kira sunan Baffana ba sunanki zan kira?" murmushi Azima ta yi ta ce
"Yau bana jin yin faɗa dake, dan yau ina cikin farin ciki, nasan idan sako ta iske sarkin yankin jimo an kashe masa Jarman Macizai me kike tunani zai faru Aziza?"
"Ban sani ba!" Aziza ta faɗa a ƙufule ta yi gaba, ita ma Azima a macijiya ta hau bin bayan Aziza, yau tsananin takaici ya hana Aziza ta cewa Azima ta koma mutum, Azima kuwa da gangan take wani abun dan Aziza ta mata magana.
A macijiya ta shiga gidan Allah ya so Hajja na bandaki, zama Aziza ta yi ta buga tagumi, Azima kuwa bukka ta shige, bayan Hajja ta fito ta ga Aziza da tagumi ta ce
"Ah Aziza kun dawo?" shuru Hajja taji dan Aziza ta yi nisa cikin tunani, sai da Hajja ta tabota tukunna ta dawo hayyacinta ta ce
"Na'am Hajja magana kike yi ne?"
"Tunanin me kike yi haka Aziza?" murmushi Aziza ta k'wak'ulo ta ce
"Abunda yake faruwa a mahaifana shine yake tayar min da hankali Hajja"
"Karki ce zaki saka hakan a ranki,addua ita ce mafita,duk abunda ya yi tsanani maganinsa Allah" kuka Aziza ta fashe da shi ta rungume Hajja ta ce
"Dole ne na saka a raina Hajja! Idan mun san abunda ya faru yau ba bamu san me zai faru gobe ba Hajja!" sosai Aziza ke kuka yayinda hankalin Hajja ya tashi, Azima ce ta fito daga bukka dauke da abinci a hannunta zama ta yi ba tare da ta kalli Hajja ko Aziza da ke kuka ba,abincinta ta hau ci hankalinta kwance, Hajja ta kalli Azima wacce ta jima da gane ita damuwar wani bai dameta ba, ta ce
"Azima meke faruwa da yar uwarki!?"
Cikin halin ko in kula ta ce
"Oho mata! Tana son ɗorawa kanta damuwar da bata da mafita a kansa, ta ga zata iya ne, Hajja ki daina damun kanki a kanta!" Hajja zata yi magana sai ga Baffa a fujajan ya shigo ko sallama babu, da sauri hankalin Hajja da Aziza ya koma kan Baffa akasin Azima da ta yi kamar bata san da shigowarsa.
"Baffan yan biyu lafiya kuwa na ganka a cikin wannan yanayin?"
Sharce zufa Baffa ya yi ya ce
"Jumala ina kuwa lafiya! Ku zo muje gaban gari ana neman dukka mutanen yanki, kin san an kashe Jarman Macizai kuwa?" hannu Hajja ta zuba a kirji tare da fadin
"Ma'asabumin Musibati qalu Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! An kashe jarman macizai to waye kashesa!?"
" *MACIJI! SARAN MACIJI NE A JIKIN JARMAN MACIZAI!*" Baffa ya faɗa yana sauke idonsa a kan Azima wanda hankalinta sam baya kansu, Hajja ta ce
"Ba ri na dauko mayafina mu tafi gaban gari din" Hajja ta karasa maganar tana shigewa bukka, Aziza kuma tana gyara mayafin kanta hankalinta a tashe! Baffa ya ce
"Ke Azima? Ana gaya miki mahaifarki babu lafiya amma kina zaune hankalinki kwance ba tare da kin nuna damuwarki ko a fuska ba kina cin abinci! Za ki tashi ne ko sai na saka sanda na roɗe miki shingen kafafunki nan masu kama da fuffuken sauro!" Baffa ya faɗa yana yin kan Azima da sauri ta tashi tana huci tare da juya baya, hanyar randar kasan dake tsakiyar gidan taje ta ɗibo ruwa a kwarya tare da fakan idon Aziza ta watsa dafi a ciki, sannan ta juyo tana kallon Baffa a ranta take fadin
"Ba zan taba samun salama ba idan har ban kasheka ba!" tunkaro Baffa ta yi har ta zo gabansa tana tura baki ta ce
"Baffa na ga alama kan ka ya dau zafi kaɗan sha ruwa zuciyarka ta huce! Baffa ita fa damuwar duniya bata karewa barin ma idan mutum yasa hannu ko nace mutane suka sa hannu suka jawo bala'i wa kansu, sannan dole akwai abunda ku ka aikata ma wasu yake bibiyarku! Dan haka Baffa a koma a yi tunani da kyau, ga ruwan ka sha" ta mika masa tana sunkuyar da kai kasa sai kace wata ta Allah, shuru Baffa ya yi yana son yayi tunani a kan maganar da ta fada amma tashin hankalin da suke ciki ya ƙi basa damar haka, hannu yasa ya karbi ruwan caraf idon Aziza ya sauka a kan ruwa ta hangi dafi, cikin azama ta ce
"Baffa wani ruwa kuma zaka sha? Ka manta Azima ita bata damuwa da damuwar wani? Kawo ruwan nan Baffa" Aziza ta karba, wani kallo ne Azima ta bi Aziza da shi jikinta har na tafasa tsananin takaicin abunda Aziza ta yi, Aziza na karban ruwan da gangan ta yi tuntube ruwan ya b'are kwaryar kuma ta riɗata da dutse ta fashe, cije baki Azima ta yi, idonta ya kara rinewa tana shirin tunkaro Aziza wacce itama ke kallonta ko gizau bata yi ba, Hajja ce ta kara katse mata hanzari ta fito tana fadin
"Yi hakuri Baffan yan biyu! Na zubar da wake ne na tsaya kwashewa shiyasa ban fito da wuri ba,muje" gaba Baffa ya yi Aziza ta bisa a baya, Azima ta zo fita Hajja ta ce
"Ina mayafinki?"
"Ba zan saka ba! bana jin saka wa Hajja! Raina a b'ace yake karki min maganar wani mayafi!" daskarewa Hajja ta yi jin amsar da Azima ta bata,ita ma Azima bata san lokacin da ta faɗi ba dan bata taba yiwa Hajja magana haka ba,ganin Hajja ta tsaya tana kallonta ne yasa ta cewa "yi hakuri Hajja bara naje na dauko,kuyi gaba zan zo a baya" Hajja dai bata iya cewa komai ba illa bayan su Baffa da Aziza da ta bi wanda sun yi gaba abunsu.
Su na kan tafiya Aziza ta ce
"Baffa?"
"Na'am Aziza yaya ne?"
"Baffa baka taba bani labarin kafuwar mahaifata ba, kullum kana cewa an sha gwagwarmaya da aljanu da mayu, amma baka taba bani labarin kalar gwagwarmayen da ku ka sha dasu ba"
"Yo to banda abunki Aziza ana cikin wannan tashin hankali kina maganar labari? Abunda ya kafu sama da shekaru hamsin? Ki bari Allah ya bamu ikon dakatar da wannan ambaliyar wutar masifan dake tunkaro wannan yankin" shuru Aziza ta yi ba tare da ta sake magana ba, da haka har suka karasa gaban gari inda cincirindon fulani suke tsaye kowa ka gari hankalinsa a tashe, har anyiwa jarman macizai jana'iza an binnesa.
Ana ta shawaran yadda za a rubutawa sarkin fulanin yankin jimo sakon cewa an kashe jarman macizai wanda yankuna sun san shi jarumi ne, idan ka cire yankin ja'i da yankin tudu za a iya cewa babu wani jarumi wanda ya shahara a kama macizai sama da jarman macizai, amma a yankin Ja'i akwai wanda har aljanun macizai yana kamawa tsananin shahararsa wanda har laƙabi ake masa da INNU MACIJI, daga shi kuma sai na yankin tudu wanda shike takawa Innu Maciji baya wato IRO MAGANIN MACIZAI daga shi sai wanda aka kashe na yankin jimo wato JARMAN MACIZAI, lokacin da aka raba kambun girma na wa inda suka shahara a kama macizai aka ba wa INNU MACIJI lamba daya, aka ba wa IRO MAGANIN MACIZAI lamba ta biyu sai kuma JARMAN MACIZAI lamba ta uku, har ta Ilu mai Macizai da Azima ta kashe na yankin kwana shine aka ba wa lamba ta shidda, sannan aka rabawa na ƙasa dasu, tashin hankalin da yankin kwana ke ciki shine rashin jituwar da basu da shi da yankin tudu da yankin ja'i, barin ma yankin ja'i tsatstsauran gaba ce daɗaɗɗiya, dan kuwa an sha gasan kisa a tsakani, yankin tudu kuwa dan sarkin yankin ne ya zo yankin kwana ya yiwa yar yankin fyaɗe bai kyaleta ba har sai da ya kasheta! Hakan ce tasa ARƊO ya bada umarnin a kashesa shi ma,aka gille masa kai aka turawa mahaifinsa da shi daga nan gabar ta soma, yanzu taya zasu fara neman taimakon Yankin Tudu ko kuma yankin ja'i? Yanzu dai ba shi bane tashin hankalin, tashin hankalinn shine yadda zasu fara tunkaran yankin jimo da sakon an kashe jarman macizai.
@@@@@@@
Su Baffa sun iso ana kan shawara ba a tsaida mafita ba, sai da Baffa ya karaso aka sake yin shawara a kan a rubuta sako a tura mutum huɗu da suje yiwa yankin jimo ta'aziyya tare da rigan Jarman Macizai wanda yake jina-jina da jini, sannan ayi musu bayanin abunda ya faru bai kai ga yin aikin da yazo yi ba aka iske gawarsa, tare da sakon ban hakuri iri da kala daga wajan mai unguwan yankin kwana da kuma sarkin fulanin yanki kwana tare da Arɗo, hakan ce ta kasance aka tura mutum huɗu izuwa yankin jimo, tare da kayan Jarman Macizai da kuma dokinsa da takwabinsa.
Aziza na tsaye a gefe da lullubi hawaye ne cike a idonta,ba dan komai ba illa su na zuwa wajan aka fara darewa ana matsawa babu wanda ya tsaya kusa da ita.
Azima kuwa za ta zo yau ne gobe ne shuru, har aka gama tattaunawar da za ayi Azima bata zo ba.
Bayan an fara watsewa Arɗo ya kira Baffa gefe ya ce
"Magaji? A gaskiya ba zan boye maka ba, ka binciki yaranka! Barin ma wannan yarinyar taka Azima,jiya an kawo min wani magana a kanta, bana son na tsawaita zargi dan babu kyau, sannan jikokinane kasan dai ba zan so abunda zai cutar dasu ba, amma ya kamata mu san abunyi,kasa ido sosai a kansu, bana so na kirawo Jumala dan duk abinda za a gaya mata ba yarda zatayi ba, sannan bayan sallar isha'i za a zauna ayi tattauna a faɗar mai unguwa, zamu je neman alfarma a yankin tudu" da sauri Baffa ya ce
"Arɗo yankin tudu kuma?"
"E Magaji, yankin tudu bamu da wani mafita wanda ya wuce hakan"
"To amma Arɗo kana ganin anya Sarkin Tudu zai sauraremu? Ko ka manta abunda ya shiga tsakanin yankinmu da nasu ne? Ɗansa yazo ya yi laifi a yankin nan an masa hukunci hakan ne ta haifar da gaba mai tsauri a tsakani, bana tunanin Sarkin yankin tudu zai yarda Iro Mai maganin macizai zai zo taimakonmu, kana gani duk wasu masu kama macizai da muke dasu a yankin nan sun mutu, a gaskiya inajin tsoron abunda zaije ya dawo, kar bamu gama da wani yaƙin ba mu sake kunna wani, a gaskiya bana so duk shawaran da za ayi ace za a bukaci taimakon yankin tudu da yankin ja'i"
Nauyayyiyar ajiyar zuciya Arɗo ya sauke ya ce
"To Magaji mai zai hana kai ka maida hannun agogo baya?"
"Bangane ba Arɗo?"
"Ina nufin ka dawo yadda kake a da dan mu taimaki yankinmu, Kayan aikinka da kaje ka binne kaje ka hakosu saboda......" girgiza kai Baffa ya hau yi yana ja da baya, ya ce
"A'a Arɗo na riga da nayi alkawari ba zan sake ba, har kwanan gobe ban manta da kuskuren da na aikata bisa tsautsayi a baya ba, abun shekara ashiri amma a yanzu gani nake yi yanzu abun ya faru, Arɗo ba a son raina na kashe *BANJU* ba, na kashesa ne sabida shafe mutanen yankin nan da ya fara, sannan idan baka manta ba yace zai dawo daukar fansa a kaina da mutanen yankin nan! tunda na kashe Banju nayi alkawari na dai na! duk wani abu wanda na gada daga gareka da kakanni! Dan Allah Arɗo a bar wannan maganar"
🍃🍃🍃🍃🍃
WLH IDAN NAYI POSTING A GRP BAN CIKA BI TA CIKIN GRP DIN BA,AKWAI WASU GRP DIN MA BANA BUDEWA INDAI BA GOGE SAKONNI ZANYI BA, IDAN KINA SON BIYAN KUDIN BOOK DIN NAN KI TUNTUBENI TA LAMBAR WAYATA TA SAMA, IDAN TA ACCT NE KO KATI.
AND PLS&PLS 4 ALLAH'S SAKE, IDAN KIN SAN BA BIYA ZAKIYI BA KARKI KIRANI KI GAYA MIN MAGANAR DA BA HAKA BA, A BOOK DIN NAN DAI BAN CE DARI BIYAR KO DARI UKU BA,HAR TA DARI BIYU MA BANCE BA, DARI NE NACE DAN MASOYANA,BAN SAKA TA INDA BA ZAKI IYA BIYA BA, SO PLSS A DINGA FAHIMTA,DAN WATA MAGANA JIYA BAI MIN DADI BA SAM.👏🏻
MASU KIRA NA DAN KARA MIN ƘWARIN GUIWA NA GODE,NA SAN ZAKU GANI DIK DA BAN SANKU BA AMMA KUNA RAINA🌹🤝🏻
COMMENTS AN SHARE
BY MOMYN AHLAN
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
*JINJINA GAREKI UWA BA DA MAMA, ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA, SHUGABA DAYA TAMKAR DA DUBU,(GWAGGOTA TA KAINA ALLAH YA IYA MIKI.*
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
🍃🍃🍃🍃🍃
*JINJINA GAREKI HAJIYA MAMAN YUSUF MAI KAYAN MATA😍 SAFIYAR YAU KECE KIKA FARA SAKANI DARIYA😂 DAN HAKA GA KYAUTAR PAGE HAJIYA JIRGIN DANƘARO*😂
*MAMIE'S CLUB HAKIKA SHARHINKU YA TAFI DA RUHINA, A KODAYAUSHE KUNA NUNA MIN E KU ƊIN YAN AMANA NE NA GASKEN-GASKE, AZIMA DA AZIZA FANS GRP, WLH KARKU YARDA A ZO GARINKU A FI KU RAWA AHA TO😜, DAN ARADU YAN MAMIE'S SUN CE BA ZAKU KAMO SU A SHARHI BA,KUMA NA YABA🌹🥰, A KAFTA*🤾🏻♀️
*ALHAMDULILLAH! ALLAH NA GODE MAKA, YA ALLAH KA KARAWA SHUGABA JA GABA ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM DARAJA! DA IYALAN GIDANSA DA SAHABBANSA DA MAGOYA BAYA HAR IZUWA RANAR SAKAMAKO! HAKIKA AZIMA DA AZIZA YA YI FARIN JINI FIYE DA TUNANINA! ALHAMDULILLAH! MASOYA A CI GABA DA NUNA MIN ƘAUNA TA HANYAR SIYAN BOOK DIN NAN CIKIN FARASHI MAI RAHUSA, ƊARI KACAL*👌🏻
FREE..*
🅿️==7️⃣↪️8️⃣
Shuru Arɗo ya yi yana kallon Baffa na wasu lokuta kafin ya ce
"Shike nan Magaji, ba zan takura maka ba, amma ban yi tsammanin zaka tsorata da maganar Banju haka ba"
"Ba tsorata nayi da maganar Banju ba a lokacin da ya faɗi, amma a halin yanzu ina cikin zullumi na maganar Banju, dan idan baka manta ba ya ce zamu gani ko ba jima ko ba daɗe sannan kuma zai dawo daukar fansa a kaina da mutanen yankin nan, abunda yake faruwa a halin yanzu abun a duba ne, sannan bamu san wani martani sarkin fulanin yankin jimo zai maidowa mutanen da suka je ban hakuri garesu ba, ba kowa bane zai lamunci hakan, munyi aiken neman taimako anzo dan a taimaka mana amma kuma sai a mai da musu da kaya ace an kashesa! Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!" Baffa ya faɗa fuskarsa dauke da zallar damuwar da yake ciki, Arɗo yaja ajiyar zuciya ya ce
"Ko ma miye ne idan suka dawo ma ji, yanzu dai ka je amma ka tabbatar bayan sallan isha'i ka halacci fadar mai unguwa"
"In sha Allahu zan zo" daga haka suka yi sallama, Baffa ba hanyar gida ya yi ba dan ba gidan zai koma ba illa cewa da ya yi su Hajja da Aziza su koma gida, ina Azima bata zo ba? Aziza ta ce
"Eh Baffa bata zo ba" girgiza kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, Hajja da Aziza suka dauki hanyar komawa gida, su na tafiya su na hira, Hajja ta ce
"Ohh Allah ni Jumala, ko me ya hana Azima zuwa? Ita kullum ta fi so ku ta zama a bakin zargi"
"Ai ko basu zauna a bakin zargi ba, ba lallai bane yaranki su kasance mutane ne!" da sauri Hajja da Aziza suka juya su na kallon Mairo da Hadi wanda suka riƙe ƙugu sai kace zasu dake su, Hajja ta ce
"Mairo me kike nufi?"
"Oho miki kuma! Kin fi kowa sanin abunda nake nufi, yara ko ma dai nace iyayen yara! Ace kamar su Azima da Aziza a wannan yankin gote-gote dasu amma babu aure! Sannan suna tafiya jiki na lankwasa! Daga mai idon mage (wato Aziza kenan) sai mai ido ruwan ganye(Azima kenan) taya kuwa zasu zama mutane, ga shegen kyau! Duk da lokacin da muka yi yan matanci dake duk yankin nan babu mai kyawunki sannan babu jarumi sama da Magaji, ba wai hakan yana nufin zaku haifi yara masu kama da mutanen wani duniya daban bane ehe! Ko ki so ko karki so Azima da Aziza dai ba mutane bane!"
Idon Hajja ne ya kawo ruwa ta ma kasa magana, da kyar ta ce
"Mairo idan ke kike aurar wa sai ki zo ki aurar dasu, sannan kuma idan kina canza halitta ki zo ki canza musu" caraf Hadi ta cab'e zancan da cewa
"Wa ye bai sani ba, ba mamaki duk wannan kisan da ake yi a yankin nan Azima da Aziza suke yi, kuma da saninki ke kike daure musu....."
"YAAAA ISAAAAAAAA!!!" Aziza ta faɗa da kakkausar murya, ganin yadda fuskar Mahaifiyarta ya jiƙu da ruwan hawaye, gaban mahaifiyarta ta tsaya yayinda idonta suka kara rinewa zuwa fari-fari ,yatsarta manuniya ta ɗaga tana nuna Mairo da Hadi cikin gargaɗi ta ce
"Zan iya jure komai! Zan iya shanye komai! Amma kar na ga hawaye a idon MAHAIFIYATA SANYIN IDANIYATA! ku fita tsabgarmu! Mu mutane ne, maganar da kika fada yanzu kuma Inna Hadi ki bar shi a iya nan kawai kar yaje gaba!" Aziza na gama fadi ta kamo hannun Hajja suka bar su Mairo da Hadi jiki na rawa, Hadi ta ce
"Mai....Mai...Mairoo....ban....gaya...miki....da...da..da cewa ba mutane...bane...wollah inaji ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba...kalli ki ga lokaci daya yadda idonta ya canza...anya ma ni kuwa ba su bane....." saurin dakatar da ita Mairo ta yi ta ce
"Hadi ki bar maganar nan a nan dan ban shiryawa mutuwa ba, zo mu tafi" Mairo ta fizgi hannun Hadi.
@@@@@@
Sun ɗan yi tafiya Hajja ta tsaya, Aziza tasa hannu tana sharewa Hajja hawaye tare da fadin
"Kiyi hakuri Hajja, dan kuka mai ja wa uwa jifa ko Hajja!?" Aziza ta faɗa tana fashewa da kuka, Hajja ta ce
"A'a Aziza, har ga Allah ni har zuciyata ban taba zargin yarana ba, na san ni dai mutane na haifa"
"To me yasa kike kuka Hajja?"
"Saboda dukkan uwa ta gari ba zata so a dinga sokin yaranta ba! Har raina nake jin zafi" Hajja ta fada tana mai kamo hannun Aziza, wani tausayin mahaifiyarsu ne ya ɗarsu a zuciyar Aziza, duk yadda take tausayawa kanta da yar uwarta tafi tausayin Hajja, ranar da zata gane cewa su din ba mutane bane MACIZAI NE ranar da zata san duk kisan da ake yi Azima ke yi, shin ya dace ta ci gaba da boyewa Hajja cewa su ba mutane bane? Ko dai ta fito ta gayawa Hajja da Baffa gaskiya? Kai amma kuwa gunduwa-gunduwa za ayi dasu, sannan Azima ta ce ko da ta faɗi ba shi zai hanata cika burinta ba! Girgiza kai Aziza ta yi ta sake rungume Hajja tana kuka, Hajja zata yi magana suka ji nishi na tashi ta gefensu wanda yake ciyawa ne kore shar a wajan, saurin maida hankalinsu suka yi, Aziza ta ce
"Hajja kamar fa nishi nake ji?"
"E nima naji Aziza, kamar ta nan yake fitowa zo mu duba mu gani" suka yanki gefen ciyawar, wani yaro suka gani kwance fuskarsa ta koma blue bakinsa sai fitar da farin kumfa yake yi tare da jini, salati Hajja ta saka, da sauri Aziza ta dagosa tana kallonsa tare da jinjigasa, gefen wuyarsa ta kalla ta ga saran maciji, wanda bata raba dayan biyun *AZIMA* ce, girgiza kai ta hau yi cikin tashin hankali, ta buɗe baki, Hajja ta ce
"Aziza me ya faru da shi?"
"Hajja maciji ne ya saresa, bari na gwada yi masa magani" kasancewar lokuta da dama Aziza na gwada wa Hajja kamar tana magani wanda Hajja ke danganta hakan da nasaban Baffa, bata jira Hajja ta yi magana ba ta hura iska a bakinta ta rufe ido gam na wasu daqiqu sannan ta buɗe, yayinda idon ya koma fari sol, hannu tasa a bakinta ta dibo farin yawu ta gogawa yaron a wuyarsa dai-dai shatin saran, sannan ta koma kallonsa, duk fuskarsa ta yi blue, tana saka masa ya hau gurnani yana murkususu sannan ya koma ya yi ɗifff! Hajja ce ta daga hannunsa ta ga ya koma, da sauri ta janye Aziza ta ce
"Aziza zo mu bar nan wajan"
Kallon Hajja Aziza ta yi cikin damuwa ta ce
"Hajja taya zamu barsa bayan yana buqatar taimako,ki bari na taimaka masa Hajja kar ya mutu"
"Ai ya riga da ya mutu Aziza! Ki zo muje kar ace kece kika masa wani abun"
Suman tsaye Aziza tayi tun sadda Hajja tace ai ya riga da ya mutu, kallon yaron kawai take yi, hannu Hajja tasa ta ja Aziza da sauri suka bar wajan basu tsaya ko ina ba sai gida, suna shiga gida Aziza ta shige bukkansu bata ga Azima ba, duk yadda akayi tana rafin jimulo, hannu tasa ta goge hawayenta tare da daukar mayafinta, Hajja ta juyo zata bata ruwa ta ga ta fice a gidan da sauri Hajja ta bi bayanta tana fadin
"Aziza! Ke Aziza!? Azi..." Hajja bata karasa ba sakamakon dakatar da ita da Aziza ta yi, ta rufe mata ido ta hura mata iska, haka kawai Hajja ta tsinci kanta da komawa gida, Aziza kuma hanya ta yanka ta yi rafin jimulo, a yadda take tafiya zaka gane cewa ba mutum ba ce, haqiqa yau Azima ta kai ta karshe! Me wannan karamin yaron ya mata da zata kashesa!.
Tana isa rafin ta kwala kiran sunan Azima.
"AZIMAAAAA!" sulalowa Azima ta yi hannunta dauke da mangoro fuskarta wasai, ganin fuskar Aziza ya sakata sakin baki dan bata taba ganin fuskarta a haka ba
"MACIJIYA AZIZA LAFIYA!" Azima ta fada cikin halin ko in kula.
"AZIMA ME YARON DA KIKA KASHE YA MIKI!?"
kyalkyalewa da dariya ta yi ta ce
"Sabida ya cancanci ya mutun ne, saboda ya ganoni, kuma yace sai ya faɗa kin ga kuwa dole na kashe sa tunda...." dauketa da mari Aziza ta yi, tana dagowa ta sake kai mata wani marin, ran Azima ya tunbatsa nan ta riƙiɗe ta koma macijiya,in da ita ma Aziza yau ta rikiɗe ta zama macijiya fara sol, nan dambe ya kaceme.
🍃🍃🍃🍃
WAI YAU MACIZAI NA FAƊA,NAYI NAN🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️
A lallaba chaji wala🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️
COMMENTS AN SHARE
*FREE..*
🅿️==9️⃣↪️🔟
Dambe suke yi sosai a tsakaninsu ba ji ba gani, yayinda Azima ta yanki Aziza a gefen wuya,nan ta koma mutun ta faɗi kasa, ita ma Azimar rabi mutum rabi Macijiya ta zama tana kallon Aziza ranta a haɗe idonta ya kara rinewa zuwa blue, a hankali Aziza ta miƙe tsaye tasa hannu ta karkaɗe jikinta ta juya baya,ta sa hannu a gefen wuyanta inda yake zubar da jini ta lumshe ido, kamar ƙiftawar ido da bismillah ta shafe wajan, sannan ta daga hannunta sama ta haɗa wani guguwa mai karfin gaske ta turawa Azima, Azima bata ankara ba taji anyi sama-sama da ita, sai da taje can sama kafin ta faɗo timm! Da kasa nan ta koma mutum, a hankali Aziza ta juyo tana kallonta yau fuskarta babu fara'a, haqiqa dan faɗa su na faɗa amma basu taba dambe ba, bar su a cacan baki.
Saurin tashi Azima ta yi ta sake komawa macijiya ta yi hajijiya ta tada ƙura ta yi kan Aziza, da sauri Aziza ita ma ta sake zama macijiya suka haɗe aka hau dambe, da jelarta na maciji ta nannaɗe wuyar Azima ta shaƙeta sosai, murkususu Azima ta hau yi tana son kwacewa daga hannun Aziza amma ta kasa, inda karfinta ya fara karewa dan duk muguntarta bata kai Aziza karfin dafi ba.
Nan numfashinta ya fara yin sama inda a karshen jikinta ya sub'ale ta koma mutum sumammiya, ganin haka yasa Aziza sakinta ta wullata kusa da rafin ita ma ta koma mutum sannan tasa hannu ta dibo ruwa ta watsa mata a fuska, wani wawan ajiyar zuciya Azima ta sauke alaman ta sha wuya, da tari ta farka tana yunkurin tashi ta ce
"Duk abun da zakiyi Aziza kema kin sani ba zaki iya kasheni ba!"
Kafadarta Aziza ta kama hawaye cike a idonta ta ce
"Nima bana fatar kasheki! Har na bar duniya bana fata na kashe ko da tururuwa! Azima kisan ya yi yawa! Azima me kikeson zama ne! Ga shi yau kin sani na aikata abunda bana son aikatawa wanda ban ma taba aikatawa ba! meyasa Azima! Me yasa! Me yasa!" Aziza ta karasa tana sakin kuka mai cike da ruɗani.
Zufa Azima ta goge tana ture hannun Aziza daga kafadarta ta ce
"Kullum ba zan gaji da faɗin cewa da ni ce da karfin gubarki da na shafe jama'ar yankin nan an wuce wajan! Duk wanda nake kashewa sun tab'oni ne! Bana mantuwa bana yafiya!"
A fusace Aziza ta sa hannu ta dago Azima tsaye tare da fadin
"Da anyi magana za ki ce ba ki mantuwa ba ki yafiya! Ni a iya sanina ban ga abun da aka miki ba kike wannan kisar! Shin zaki iya gayamin laifi daya tak ƙwaƙƙwara wanda aka miki kike kisa? Mutum ko da ya miki kallon bai miki ba shikenan ya cancanci kisa!? Kina fakewa da cewa dan kar a tona mana asiri da cewa mu ba mutane bane macizai ne, a da ina yarda amma a kwana biyun nan na daina yarda dake! A da kin san da cewa ke macijiya ce amma ba kya kisa kamar na kwanan nan me yasa Azima!? Me yasa!?"
Idonta ne ya sake rikiɗewa zuwa blue sosai, fatar jikinta har na caccanza kala ta ce
"Fansa! Fansa! Fansa! Fansa nake ɗauka Aziza!"
"To fansar me Azima gaya min?"
"Abun da mutanen yankin nan suka min shekarun baya"
Da mugun mamaki Aziza take kallon Azima dan ba ta taba furta wannan kalman ba sai yau, ta ce
"Shekarun baya fa kika ce!? Duka-duka yaushe aka haifeki da zaki dinga lissafin shekarun baya?"
Murmushin mugunta Azima ta yi ta ce.
"Koma yaushe aka haifeni! Ba damuwarki ba ce! Amma ina so ki sani ki kara sani! Sai na kashe BAFFA! sai na kashe ARƊO! sai na kashe TSOHON SARKIN FULANI KWANA! da kuma wanda suka sauka a bayansa! sai na kashe MAI UNGUWA! kee sai na shafe dukkan mutanen yankin nan! Sannan na shiga birni cikin inda yake da jama'a da yawa na tarwatsasu! Zan bar wannan alƙaryan!"
Gabanta Aziza ta tsaya ta ce
"NI KUMA AZIZA MAGAJI ARƊO! ZANYI YAƘI DAKE NA DAKATAR DAKE! ZAN TAIMAKI MUTANEN YANKIN NAN KO DA KUWA ZASU GANE CEWA NI MACIJIYA CE SU KASHENI! ZAN TSAYA A GABAN BAFFA NA KARESA BA KI ISA KIYI MASA KOMAI BA!".
Murmushi Azima tayi ta ce
"Idan kin isa ki dakatar dani Aziza! Na fi ki mugunta! Kin fini karfin dafi! Muje zuwa Allah ya ba wa mai rabo sa'a!" Aziza ta yi murmushi ta ce
"Amin!" nan Azima da Aziza suka rabe ko wacce tayi hanyarta daban.
🍃🍃🍃🍃
Hankali tashe Maga Isar da sakon sarkin fulanin yankin jimo ya faɗo fadar sarki Haruna ya ce
"Allah ya taimakeka! Mummunar labari! Mai cike da tashin hankali, hakika yau munyi asara! Munyi babbar rashi!" daga nan kuma ya fashe da kuka! Nan hankalin jama'ar wajan ya tashi yayinda Sarki Haruna ya miƙe tsaye ya ce
"Maga Isar da sako, me ya faru!?"
"Haqiqa mun shiga ruɗu da ruɗani! Munyi sallama lafiya-lafiya da jarman macizai, amma yanzu haka sako ne daga yankin kwana a kan cewa an kashe jarman macizai! Yanzu haka gasu can sun dawo da kayansa da dokinsa! rigarsa duk jini!" ba iyakar sarkin fulanin jimo ba harta jama'ar da suke zaune a wajan sai da suka miƙe tsaye.
Waziri ne ya yi karfin halin faɗin
"Ce dasu su karaso su mana cikakken bayani dan bamu fahimci maganarka ba Maga Isar da Sako!" da sauri Maga Isar da Sako ya tashi yaje ya ce dasu su karaso, jiki a sanyaye babu kwari suka karaso suka zube a gaban sarkin fulanin yankin jimo, daga kallon da ake musu yasa suka sha jinin jikinsu, da kyar garkuwan fulanin yankin kwana ya ce
"Allah ya taimaki Sarki Haruna, da fari kafin muce komai zamu fara da ban hakuri da neman afuwa da gafarar duk wani wanda yake wannan yanki a kan rashin jarman macizai! Haqiqa munji kunya! Mun yarda munji kunya! Amma ba laifinmu bane, mai afkuwa ce ta afku, amadadin Sarkin fulanin yankin kwana da Arɗo, da mai unguwar yankin kwana wato Ori, dani Garkuwan fulanin yankin kwana da Magaji Bawa da duk jama'ar da suke yankin kwana muna mai neman yafiyarku a kan abunda ya faru na rashin jarman Macizai! Haqiqa ya cika jarumi kuma ya amsa sunansa, ba zamu manta da halaccin wannan yanki ba har izuwa karshen rayuwarmu! Mun gode da yunkurin taimakonmu! Haqiqa mu abun tausayi ne, kuyi hakuri ku yafe mana! Bai kai ga aiwatar da aikinsa ba muka iske gawarsa da saran maciji, ba zamu iya kawo muku tashin hankali goma da ashirin bane, shi yasa muka sallacesa muka binnesa muka yi masa sutura, zaku iya zuwa ganinsa tare damu gobe idan Allah ya kaimu sai muje ku ga ƙabarinsa!" Garkuwan fulani ya karasa maganar a sanyaye yana mai duƙar da kai.
Tabbas jama'ar yankin jimo sunji mutuwar jarman macizai har can kasar zuciyarsu yayinda suka ji tsanar yankin kwana duk da hakika sun tausaya musu matuƙa, amma zafin mutuwar jarman macizai ya hanasu ce uffan wasu Garkuwan fulanin yankin kwana, ba a wani musu tarba mai kyau ba dan kuwa su na cikin ƙunci da jimanin mutuwar jarman macizai, inda suka sa da washe gari da safe zasu yi asubanci su tafi yankin kwana.
@@@@@
*YANKIN KWANA.*
Ko da su Aziza da Azima suka koma gida ba su shiga hidimar juna ba, harta abinci da Hajja ta haɗa musu ga mamakinta sai gani ta yi sun raba kwano, sosai abun ya damu Hajja ta yi musu tambayar duniya me ya hadasu, Aziza ce dai ta iya cewa babu komai fa Hajja, amma Azima kam ko kallon Hajja bata yi ba.
@@@@@@
Bayan anyi sallar isha'i dukkansu suka hallara a fadar mai unguwa, kowa da kalar shawarar da yake badawa, shi dai Baffa duk sauraronsu yake yi ya gaza cewa kanzil, inda a karshe Arɗo ya ce
"Magaji in ce dai lafiya ko? Na ga kowa na ta magana amma kai baka ce komai ba" ajiyar zuciya Baffa ya sauke ya ce
"Hankalina yana can wajansu Garkuwan fulani, ko ya Haruna zai dauki lamarin? Abun fa sai wanda ya ɗaure" Ardo ya ce
"Tabbas haka ne Magaji, to ya zamu yi? Mu ma ba yin kanmu bane, Allah yasa su fahimce mu" aka amsa da amin, tsohon sarkin fulani ya ce
"Yanzu abun duba a nan shine taya zamu shawo kan wannan matsalar? Abun kara yawa yake yi fa? Jarman macizai da safe! Yaro dazu! Ba zamu zauna mu naɗe hannu a kirji mu zuba ido a shafe mu ba, mai zai hana mu aika da kokon barar mu neman taimako yankin tudu?" wani zabura Baffa ya yi yana girgiza kai ya ce
"A'a Baffa Mandi, kar mu kara wannan kuskuren! Munyi kuskure na farko an rasa jarman macizai, yanzu kuma sai mu sake aikata wani ta hanyar yin aike yankin tudu! Mu nemi taimakon IRO MAGANIN MACIZAI? Duk shawaran da za ayi a sauran yankuna amma banda yanki biyu, ban da yankin tudu ko yankin ja'i, kar mu taro wani yaƙin ba tare da mun dakatar da wani ba, kun san tsananin gabar da ke tsakanin yankin tudu da yankin ja'i da yankinmu, har kwanan gobe ana samun kisan kai a tsakanin yankin nan da yankin ja'i, har kwanan gobe yankin tudu su na riƙe da abunda ya faru sun kasa mantawa kiris suke jira su fasa abunda yake zuciyarsu, dan Allah ku fahimceni!"
Shuru wajan ya dauka kowa da abunda yake tunani,
Sai zuwa can anjima Mai Unguwa Ori ya ce
"To shikenan, za ayi ƙuri'a duk bangaren da ya fi rinjaye shi za a zaba, idan bangaren kar aje neman taimako yankin tudu ko yankin ja'i sunfi yawa to ba za aje ba,idan kuma bangaren wa inda suka ce aje sunfi yawa to za a je" shi dai Baffa shuru ne ya yi yana hango musu gagarumar balbalin gobarar yaƙin da zai tashi amma sun kasa ganewa.
🍃🍃🍃🍃
COMMENTS AN SHARE
BY
MOMYN AHLAN.
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃
💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨
(🐍 _Macizai ne_🐍)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA'YA KASHE ZAHRA'U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_
🍃🍃🍃🍃🍃
*JINJINA GAREKI SIRKATA MAMAN NOOR, 😍 SANNU DA COMMENT,INAYINKI OVER.*
*
Post a Comment for "AZIZA DA AZIMA 1-10"