Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

HALIN GIRMA 13


 Halin Girma

    13


*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 


I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb



***Sai da suka ga tafiyar su sannan suka dawo ciki, kowa da abinda yake cin sa a zuciya. Tabbas sun amsa sunan babban gida, haka sun nuna Halin Girma da dattako na irin manyan mutane da suka san mutunci da yakana.

   Fadar irin tarin kayan da suka zo dashi ba abu bane me sauki, hakan ya dan tarsa tsoro a zuciyar Abba, yake jin tamkar siyar da Iman din zai yi, wannan uban dukiya a matsayin tambaya, ina ga idan aka zo auren? Basu da talaucin da arziki zai tsorata su, sai dai dole ne suyi mamaki ganin uban dukiyar da aka lafto da sunan na Iman din ne, tun daga kan sutura zuwa kayan kawa na mata, da kyautata gwala-gwalai tamkar ba'a san darajar su ba. 

   Haduwa suka yi suka tattauna yadda zasu adana komai saboda yadda rayuwar yanzu ta zama ta rashin tssro, shawarar farko shine su bar maganar tsakanin su domin mata akwai sakin baki musamamn idan abun da ya sha musu tunani ne, yanzu zasu yi ta kwazozotan sa har wasu dake waje su samu damar aiwatar da mummunan kuduri akan su.

  Tabbas shawarar tayi dan da gaske komai na iya faruwa idan maganar ta fantsama shiyasa kawai a take aka fita da motar da duk abinda yake ciki daga gidan zuwa in da zai fi zama safe kafin bikin yazo kusa sosai sai ayi abinda ya dace dasu, ko bata kayanta ta tafi dasu tunda dama su chan babu wani tsoron rashin tsaro ta ko ina zagaye suke da Jami'an tsaro. Karshen magana kuma ma shi Muhammad din kansa, su ne tsaron ma baki daya. Da wannan shawarar suka tashi bayan Abba ya sanar musu da zuwan iyayen Bashir a gobe kamar yadda Mama ta shaida masa.

   

Sake gwada kiran Maman Iman din yayi bayan ya koma gida, cikin sa'a kuwa kiran ya shiga, bata wani jima tana ringing ba ta dauka a nutse cikin sallamar ta da muryar da yake jin ta kullum a bakin Iman din, maganar da sak ta mahaifiyar ta, hatta nutsuwar ta irin ta uwarta ce shiyasa yake jin ba zai iya mantawa da ita ba ko da shekaru sun ja, duk da yanzu babu batun soyayya a tsakanin su tun da be riga yasan matsayar da take a yanzun ba ko da aure ko babu, a dai kwanakin baya ya samu labarin tayi aure har da albarka Yaya a tsakanin su.


"Ina wuni Abban Iman?" Ta gaishe shi jin yayi shiru bayan amsa sallamar ta


"Lafiya Lou Maimunatu, ya gida ya kowa da kowa?"


"Kowa lafiya Alhamdulillah, Iman fa?"


"Tana nan lafiya."


Shiru sukayi baki daya, kowa da kalar tunanin sa a ransa, shine ya katse shirun ta hanyar cewa


" Inaso zan kawo miki ita kamar yadda nayi miki alkawari idan auren ta ya tashi, ta samu miji har an tsaida rana wata daya, in sha Allah a tsawon wata dayan nan zata zauna a wajenki, a matsayin ki na mahaifiyar ta sai kiyi duk abinda ya dace, kiyi hakuri da Kaddara, kiyi hakuri!"


Wani irin yar taji har cikin kanta, Iman dinta har ta girman da zata yi aure, rayuwa na gudu sosai, tana tuna lokacin da ta dawo masa da ita, da irin tashin hankalin da ta shiga a rashin ta wanda bata taba tunanin zata dawo daidai ta cigaba da rayuwa ba, a lokacin tunani take rayuwarta ta kare gaba daya, amma kuma sai gashi ta cigaba da rayuwa duk da babu ranar da zata fito ta fadi bata tuna yar tata ba, amma ya zatayi? Mutane na fifita al'ada akan addini. Ta sani sarai uwa ce taka da ikon rik'e yarta har zuwa aurenta, tare da sharadin kula da duk wata bukatar ta daga mahaifin ta, sai dai idan anji tsoron tarbiyyar da zata samu a wajen uwar, toh amma a lokacin wa take dashi da zai tsaya mata? Bayan iyayenta da take ganin su a matsayin gatan ta sun kekashe kasa sun ki amincewar da rikon nata a wajenta? A lokacin da akwai karancin shekaru a tare da ita, amma da ace yanzu ne, babu me raba ta da yarta kuwa, duk yadda zatayi zatayi ta tabbatar da ta rik'e ta a wajen ta. Ta bata kulawa da dukkan gatan da take bukata.


"Allah ya sanya alkhairi, ya nuna mana lokacin."


Kawai tace dan bata kuma san me zata ce masa ba, taji dadi da ma ya cika alkawarin sa, zatayi kokari a dan zaman nan ta koya wa yarta kaunar ta da sabawa da ita da yan uwanta, sannan ta nusar da ita rayuwa da yadda zata kula da auren ta. Sallama sukayi da alkawarin ana gobe zai kawo ta, zai kira ya sanar mata. Godiya tayi masa dan har gobe tana ganin kima da mutuncin sa, mutum ne shi na gari, me kirki da son iyalin sa.


  Bayan gama wayar da sukayi ne zuciyar sa ta gwada masa kiran Zeenat ya sake gwada tankwarata, idan Allah ya taimake shi ta hakura sai yafi kowa murna, dan yanzu bashi da babban tashin hankali kamar auren zeenatun da yake da yakinin zai iya zamar mata wani Babban tashin hankali a gaba.

  Kiran nata yayi, tana dagawa yace ta matsa daga wajen kowa zai yi magana da ita, da ido ta kalli Mama dake zaune ana maida maganar auren Zeenat din da Hajiya ta fice zuwa tsakar gidan.


"Abba na fito."


"Yawwa zeenatu, magana nake so muyi a matsayi na, na mahaifin ki, kin san dai ba zan taba zabar miki abinda zai cutar dake ba, ba kuma zan ga cigaba a gareki na dakushe ki ba, ina neman alfarma, kiyi hakuri da Bashir  ki kawo wani ba shi ba,nayi miki alkawarin tsaya miki kinji?"


Gabanta ne ya fadi, a tunanin ta an gama wannan babin, sai gashi Abban ya dawo da shi yana kuma kokarin daure ta da jijiyoyin jikinta.


" Kina jina zeenatu?" Ya sake fad'a cikin yanayi me wahalar fassarawa

Shashekar kuka yaji, ta fashe da kuka cikin muryar kukan tace


" Dan Allah Abba kayi hakuri?"


"Ai ba laifi kikayi min ba Zeenatu, alfarma kawai nake nema a matsayi na, na mahaifin ki."


"Abba dan Allah kayi hakuri, wallahi ba zan iya hakura da Bashir ba."


Kamar saukar aradu haka Abba yaji, ya dafe kansa ya shiga karanto innalillah wa inna ilaihi rajiun, babu babbar jarrabawa irin yayanka suyi rashin sa'ar miji, duk abinda yaje ya dawo dole kana ciki, kamar ka saida akuyar ka ne tazo tana ci maka danga, baya fatan hakan ta faru ga ita, shiyasa tun farko ya hakurkurtar da zuciyar sa be ga laifin ta ba sai na Mama, amma yanzu ya tabbata abinda Zeenat din take so shi Maman take goyan ba, dama mafiya yawan lokuta uwa na tafiya ne da ra'ayin yarta.


"Shikenan zeenatu, duk abinda yaje ya dawo karki kuka da kowa, ki kuka da kanki."


"Abba dan..." Kafin ta kai karshe ya katse kiran, Jan kafarta tayi ta koma ciki tana jin a ranta tayi abinda ya dace, a kalla ta yi kokarin kare soyayyar ta ko ba komai idan akayi auren Abban zai hakura ya sakko.


"Lafiya?" Mama tace tana kallon ta.


"Ya kukayi da Baban naki? Maganar dai ce ko?"


Da kai ta amsa mata da eh, tsaki Maman taja


"Shine kike kuka ko me? Ni wai Zeenat asiri Bashir yayi miki ne? Da bakya ganin kowa da komai sai shi?" 


Kanwar Maman Atika ta fad'a cikin bacin rai


" Ni banga wani abun naci a Bashir din nan ba, tunda mahaifin yarinyar nan baya so toh a hakura mana? Iyaye maza sun fi mu tunani da hangen nesa."


"Toh Atika ya za'a yi? Shi ma fa duk zuga ce wallahi, ai da be san da hakan ba sai bayan yaga mijin da yar lelen tasa ta samu, shikenan kuma sai kananan maganganu bansan daga ina ba, amma ina kyautata zaton daga wajen Gaji ne, dan ita kadai ce take sauya musu tunani da raayi dukkan su, ita kuma na tabbata munafurcin Iman ne dan ko yaushe tana wajen ta."


"Duk wannan ta tunani ne Yaya Hajara, bamu da tabbas din hakan, kinga dai yadda Dr ya dage ya kamata ace kin bashi dama kinji ta bakin sa akai."


"Kyale shi kawai, zai sakko ne."


"Me yace miki?" Ta tambayi Zeenat din tamkar abin be dameta ba.


"Cewa yayi nayi masa alfarma na hakura da Bashir."


"Ehen kinji? Har ya saukar da kansa a matsayin sa na mahaifi yace yana neman alfarma kema Yaya Hajara kinsan da matsala."


" Me kika ce masa ke kuma?" Taki amsa atikar ta tambayi Zeenat din.


" Hakuri na bashi." Tace tana rakubewa a gefen Hajiya da tunda aka fara maganar bata saka musu baki ba sai lokacin


" Gaskiya da kun hakura kun bi zabin Ibrahim, a kalla shi namiji ne yafi mu dukka tunani da hangen nesa."


" Hajiya toh ya za'a yi? Lokaci ya riga ya wuce bata kula kowa sai shi, yaushe zata fara daga farko kafin ma ta samu saurayin su fuskanci juna a zo maganar aure."


" Duk wannan me sauki ne akan ka dauki dan ka, ka kaishi inda zai Sha wahala."


" It's better to marry late than to marry wrong." Atika tace tana girgiza kafarta


" Khair in sha Allah, babu abinda zai faru."


Maman tace a kasan zuciyar ta tana jin tsoron abinda zai je ya dawo, ita kanta ta fara tsoron yadda Abban ya kafe ta tabbata akwai babban dalili, amma kuma ta Ina Zeenat din zata fara? Hasalima bata da farin jinin samarin duk asalin su Iman suke so sai ita maman tayi amfani da wannan a juya mata kansu zuwa Zeenat din dan ba zata iya gani Iman din tayi aure musamman auren babban gida ita kuma Zeenat din na zaune a gida. 



***Da sauri ya karasa part dinsa yana jin kayan na masa nauyi sosai, yau tun safe Bubu ya Aiko masa da kaya sannan ya bukaci ganin sa a kofar part dinsa dan shiga tawagar sa zuwa Fada, haka ya tashi ya shirya ba dan yaso ba ya fita. Tun lokacin sai yanzu ya samu dawowa part din sa, yana shiga ya hau cire kayan yayi wurgi da rawanin yana jin shi sakayau. Allah Allah yake ya samu feedbacks din aikin da ya saka Musaddik sai gashi kuwa ya kirashi adaidai lokacin, dagawa yayi yana rage daga shi sai singlet da boxer kasancewar zafi ya fara hurawa kadan kadan ba kamar kwanakin baya da ake sanyi sosai ba.


"Gani fa ga mutumin ka." Musaddik yace yana dagawa


"Da gaske? Sharp sharp haka? Ok bari na kiraka Video Call."


Ya katse sannan ya kira video call, a daidai saitin fuskar Bashir Musaddik ya saka wayar yadda yana dagawa Moh zai fara ganin sa. Yana durkushe tamkar me neman gafara, wata dariya ce ta zowa Moh, yayi murmushi kawai yace


"Oga Bashir barka da warhaka."


"Dan girman Allah ranka ya dade kayi hakuri, wallahi bansan gidan da kaje Neman aure bane nima naje, wallahi kuskure ne kawai amma kayi hakuri."


"Ai ba laifi kayi ba Bash, ni hakan yayi min dadi sosai, kuma ina tayaka murna, kaga ni da kai mun zama yan uwa tunda zamu auri yan uwa."


"Tuba nake ranka ya dade!" Yace yana kasa da kansa


"Dago kanka bash, bafa wani laifi kayi ba, aiki nake so na baka, bana son kuskure ko kadan a ciki, idan har kayi min yadda ya dace akwai babban tukuiwaci."


"Hakan shi yafi komai sauki a wajena ranka ya dade, fadi ko menene ."


"Yaushe za'a je tambyar maka auren?"


"Gobe ne ranka ya dade, amma idan kace a fasa na fasa wallahi."


Girgiza kai yayi


" Ba za'a fasa ba, Ina so idan sun je su nemi a saka musu wata daya!"


" Wata daya!" Ya zaro ido


" Wata biyar nace ko shekara, ban shirya ba wallahi,dan dai bana son na rasata ne."


" Ba zaka taba rasata ba, ni zan maka komai na auren tun daga lefe har gidan zama zan baka, ni dai kawai kayi duk abinda nace kayi."


Dukawa yayi jiki na rawa


" Nagode nagode Allah ya kara girma, zanyi duk abinda kace, ba zan yi komai ba sai da sanin ka."


" Good, yanzu aikin me kake?"


" Buga buga kawai, sai kuma aiken Hajjaju idan ya tashi."


Dariya sosai Moh yayi, ya hangi tsantsar mutuwar zuciya da son zuciyar a tattare da Bashir din, mikar da yan yatsun sa yayi baya, ya dawo dasu gaba suka bada sauti kafin ya katse dariyar yana zama so serious.


" Abinda nake so kayi min, zaka ji daga bakin Musaddik, bana son kuskure ko kadan, komai Ina so ya tafi cikin tsari , Ina so gobe ka dauki hanyar Katsina, zan aiko maka da sako ka kaiwa Gimbiya Zeenatu, hakan zai sake goge shakku ko wani tunani akanka."


" Nagode ranka ya dade, nagode nagode."


" Karka damu, kai dai kayi abinda nace, bana son kuskure ko kadan!"


" Da yardar Allah zaka same ni da bin duk umarnin ka. "


Daga masa kai Moh yayi sannan yace


" Guy!" 


" Yeah Captain!" Musaddik yace yana matsawa daga wajen da Bashir din yake


"Ka kula dashi sosai dan dan iskan kansa ne, duk da be isa ba, amma dai bana so a samu matsala har zuwa ranar daurin auren, watch him and report anything da be maka ba."


"Karka damu, babu ma abinda zai faru. "


" Yau nayi zaman fad'a, kamar nayi kuka wallahi, wannan yazo ya fadi yayi gaisuwa, wanna yazo ya ce makwafcin sa kaza, wannan suzo maganar aure, wannan ta kawo karar mijinta wannan ya kawo karar matar sa, maganar gado, kai abubuwan da mugun yawa, kamar na gudo nake ji, nasan iya zaman da zan Bubu ba zai raga min ba wallahi, har na fara ramewa. "


" Haka zaka hakura kayi abinda yake so, iyaye dole a bisu ayi musu yadda suke so. "


" Haka ne dama, shiyasa na matsu nayi auren nan nima na zama me yancin kaina, kasan aure fa yanci yake siyo ma da martaba ba komai Bubu zai dinga matsa min ba da zarar yaga nima na zama dan gari a harkar. "


" A harkar me? "


" Harkar auren mana, ina fita daga novice zai yanta ni, kwana kad'an kaji nima ana Daddy, Daddy! Wayyo I can't wait. "


" Kaifa yanzu baka da magana sai ta aure ko? Wannan sanyin ne ba komai ba. "


" Sanyi ai ya wuce kuma, ba zan kara yarda na sake wani sanyin a gauro ba wallahi, haba Malam ai an ji jiki kawai. "


" Dan air. " Musaddik yace yana dariya


" Yan air dai, Wa ma ya kaika ne? Gwara ni wallahi kowa yasan uztaz. "


" Nima haka ai. "


" Fadawa wanda be sani ba toh. "


" Toh ai idan har Moh uztaz ne toh tabbas ni sai da shehin malami, kai din? Ina dai tausayin yar mutane da zata shigo hannun tuzuru irin ka wallahi. "


" Naji karka bata min tunani, jeka zan neme ka anjima bacci zan."


" Hahaha, shikenan sai na jiki, angon Fatiti. "


" Musaddik.!!! " Ya furta da karfi


" Sorry sir, angon Fatima. "


" Zaka shigo hannu ne wallahi, sai na saka an samin kai frog jump. "


" Idan wannan ne ai na gaji da yi, a chanja wani punishment din dai Captain. "


Kashe kiran Moh yayi, yasan ya biye Musaddik sai su cinye lokacin suna abu daya, wurgi yayi da wayar gefe ya kwanta dan rama baccin da Bubu ya katse masa.

Post a Comment for "HALIN GIRMA 13"