THE GOVERNOR'S WIFE 18
*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....
*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat
Bismillahir Rahmanir Rahim
Book one
18
Asiya ce ta fara shiga falon. Ta samu Gwamna yana zaune yayi tagumi. Ya mata tsufa, idonsa ya faɗa, ƙasan idonsa ya yi baƙi, ga furfura kaɗan-kaɗan a jikin gemunsa. Asiya ta zuba masa ido ba tareda tace komai ba.
Minti uku sai ga Bilkisu ta shigo ɗankwali a hannu.
"Saifuddeen koma wanene ya rubuta labarin nan sai na sa an nemoshi an hukunta shi. In fact sai nayi kaca-kaca da jaridar Climax"
"Nana tana zama a gidan nan tareda ke amma baki san tana shaye-shaye ba"
"Kar ka kawo min wannan Saifuddeen, ka san ina ƙoƙari akan yarana, especially Nana. Zunnairah ce ta koya mata. Na riga na turata wajen uwarta kafin ta ɓata min 'ya"
Ta zauna gefensa kafin ta cigaba da magana
"Saifuddeen kai ne Gwamna, ya kamata ka ƙwace lasisin gidan jaridar Climax. Ta ya za su ce Nana zata zama 'yar lesbian"
"Saboda da gaske ne" Gwamna ya furta a hankali
Bilkisu ta zaro ido.
"Da gaske kuma? Mi kake nufi?"
"Nana ta faɗa min komai. Ita da Zunnairah suna aikata maɗigo a gidan nan kuma babu wanda ya sani cikinmu, saboda mun gaza, mun gaza Bilkisu. Ba jaridar Climax zamu bincika ba, kanmu za mu bincika a matsayinmu na iyaye"
Jikin Bilkisu yai sanyi, ta fara yin fifita da ɗankwalin hannunta duk da kuwa sanyin AC ya ratsa falon.
Kaman wanda aka tsikari Bilkisu haka ta tashi ta fice daga falon.
"Tsanar da kika min har ta kai haka"
Asiya ta zaro ido dan a tunaninta ya gano cewa ita ta rubuta labarin ne, sai kuma ta ji ya ƙara da cewa.
"Na karɓi wayan Nana, na ga irin saƙonni data dinga tura miki. Lokacin da tace tana sonki miyasa baki faɗa min ba? A matsayina na Uba ba kya ganin ya dace na san 'yata tana yiwa wata mace 'yaruwarta kallon da bai dace ba"
In dai ya ga chats ɗinsu to babu halin ta masa ƙarya dan a ƙasan wajen da Nana ta ce mata "I love you" tambayarta tayi wani irin so, Nana ta amsa da cewa " ina son lips ɗinki, ƙirjinki, bayanki, kai komai na halittar ki"
"Ko a tunaninki yarinyar shekara shabiyar ya kamata ta dinga faɗin irin wannan maganganu?"
Idan ya cigaba da bin diddigi zai iya alaƙantata da jaridar Climax kuma ba yanzu take so ya sani ba. Ta yi saurin cewa " ni ban ɗauki wannan komai ba tunda na ga kamar tarbiyyan gidan kenan. Kana gani 'ya'yanka na yin shiga da bai dace ba a cikin gidan nan bayan akwai ma'aikata maza, baka taɓa musu magana ba, ban taɓa gani suna karatun addini ba, bana ma tunanin suna zuwa Islamiyya. Rayuwar da kuka ɗaurasu irin ta turawa ce, sannan a wajen mahaifiyarsu ni jikar maiƙusumbi ce, a wajenka kuma ni hajar Kamfen ce. Taya zan ƙalubalanci abinda 'yarka ke faɗa mini, ƙila ba matsala bane a wajenku"
Tun kafin ta gama bayanin Gwamna ke kokawa da numfashinsa, yana ƙoƙarin ciro inhaler a aljihunsa inhaler ta faɗi ƙasa.
Asiya ta yi saurin ɗauko inhaler ta matsa kusa da shi ta jijjiga sannan ta miƙa masa, ya haɗa da hannunta ya matsa inhaler ɗin a bakinsa.
Kallonsa ta ke yi yadda lokaci guda ya rikiɗe har jijiyoyinsa sun taso saboda wahala. Matsayinsa ba komai bane a hannun wannan lalura.
"Nagode" ya faɗa bayan numfashinsa ya daidaita.
Asiya ta girgiza kai sannan ta fita daga falon zuciyarta fal. Ta ji daɗin ganinsa cikin halin tashin hankali, itama haka mahaifiyarta ta shiga damuwa lokacin da aka ɓata mata suna a media.
"Yadda Umma ta zubda hawaye saboda abinda kuka min haka kaima sai ka zubda hawaye saboda 'yarka. Ita kuma waccar kucakar matar taka rananda aka koreku a gidan nan zata san cewa ba a dawwama a matsayin Matar Gwamna"
Da wannan tunanin Asiya ta shige ɗakinta tana jiran yadda za su ji wata sati idan aka kai masa impeachment notice.
Daren ranan Gwamna ya je ya samu Alhaji Sani akan yana son ajiye aikinsa.
"Kanada hankali kuwa, Saifu mi kake nufi za ka yi resigning. Saboda abinda wata jaridar ƙarya ta rubuta akan 'yarka. Miye ne a ciki idan duniya ta san Nana na shaye-shaye, kai ne kaɗai Gwamnan da yake da yara masu shaye-shaye. Ban yarda da wannan maganar ba, ta mutu a nan"
"Baba ko da ban yi resigning ba, ba zan nemi takarar zaɓen bana ba"
"Ba za ka ɓata min shiri ba Saifu, shekara takwas ɗin nan sai kayi Gwamna a jahar nan. Ban yafe ba idan ka yi resigning"
"Baba..."
"Idan kuma zaka nuna min cewa ba nina haifeka ba to, Bismillah"
Gwamna yai shiru bai iya cewa komai ba.
Kafin ya bar gidan sai daya leƙa sashen Dadda. Ya samu Mahira tana karatun ƙur'ani a falon Dadda. Zuciyarsa yai sanyi, da zai maida hannun agogo baya da duka yaransa biyun zai ajiyewa Dadda, ƙila da Nana itama halin Mahirah za ta tashi da shi
"Ina 'yaruwar ki?"
Ya tambaya bayan ta gaisheshi.
"Tana bacci"
"Dadda fa?"
"Tana sashen GrandMa"
"Mahirah"
"Yes Daddy" ta amsa tana rufe ƙur'anin da ke hannunta
"Akwai abinda kike buƙata, ina nufin baki da matsala, ba abinda ke damunki?"
Mahirah ta girgiza kai tausayin mahaifinta ya kamata. Yana ƙoƙari sosai a kansu, shi dai kawai sanyinsa ne da yai yawa yasa a mafiya lokuta yake biyewa mahaifiyarsu.
"Ehm Daddy, Dan Allah kar a kai Nana ƙasar waje, idan aka barta a nan ma zata warke, zata dena duk abinda take yi"
"Allah ya miki Albarka" Mahirah ta amsa da Amin.
Shima tunanin da ya zo masa kenan da Alhaji Sani ya ce bai amince ya ajiye muƙaminsa ba. Dama da ya amince ɗin yai niyyar zai tattare iyalinsa ne su koma ƙasar waje, a nan kuma zai kai Nana rehabilitation centre har sinadarin ƙwayoyin da tai ta sha ya bar jininta. Sannan a cire mata sha'awar mata.
***
Labarin 'yar Gwamna ya zamo abin hira a kowanne lungu da saƙo na Jahar. Kowa sai tofa albarkacin bakinsa yake. Wasu na zagin Gwamna wajen rashin bawa 'yarsa tarbiyya wasu kuma na ganin cewa laifin first lady ce saboda ai mace aka sani da tarbiyya domin itace ke tare da 'ya'ya koda yaushe.
Mai bawa firstlady shawara ya fito ya ƙaryata maganar maɗigo da jaridar Climax ta soki 'yar Gwamna da shi sannan sun rantse cewa Nana Kachallah bata shaye-shaye, a wajen party ƙawayenta suka tursasata ta sha shisha. Kuma za su shigar da jaridar Climax ƙara.
Ko kaɗan Asiya ba ta ji ɗar ba da wannan magana koba komai ta samu abinda take so, yadda aka yi ta yawo da ita a yanar gizo ana gulmanta haka nan itama Nana za ayi ta gulmanta har zuwa wani lokaci, kuma hakan zai ƙona ran Gwamna ita kuma duk abinda zai ɓata masa rai sai ta yi.
Yanzu jira kawai take ta rubuta labarin da zai wargaza Gwamnatin Saifuddeen Kachallah.
***
Ranan Litinin ƙarfe tara na safe aka kawowa Gwamna notice na impeachment trial. Bai yi mamaki ba saboda tun lokacin daya rage kuɗin allowance da ake bawa members na state house of assembly suka fara nuna ɓacin ransu gareshi. Ba abinda zasu iya tuhumarsa da shi. Record ɗinsa is clean. Sai dai dama tunda yana son ajiye aiki ƙila yanzu Alhaji Sani zai bari yai resigning kafin a fara trial ɗin.
Ya kira Alhaji Sani ya sanar da shi gameda takardar da aka kawo, tun a wayan ya bircike yana faɗin ba zai yiwu ba, babu wanda ya isa ya tsige Saifuddeen matuƙar yana raye.
Yana gama waya ya kira Mr Paul yana masa kashedi akan indai shine ya haɗa hannu da Umaru Kwom dan a tsige Saifuddeen to ya sani ba su isa ba. Ba a taɓa tsige Gwamna a jahar Congo ba kuma baza a fara akan ɗansa ba.
Mr Paul ya saka dariya yana faɗin miye abin tsoro idan har ya san Saifuddeen bashida abin aibu. Ai trial za a fara idan ya kare kansa bisa duk zargin da za ai masa ai shikenan.
Alhaji Sani ya kashe wayar ya kira Yallaɓai, nan ma nunawa yai duk wanda yasa aka tsige Saifuddeen sai ya ga bayansa a jihar. Yallaɓai ya kwantar masa da hankali akan indai ya yarda da Saifuddeen to ai babu mai tsige shi a kujerarsa.
Da wuri Gwamna ya isa gida yau, ƙarfe huɗu da rabi yana falonsa. Bilkisu ya kira yace ta sameshi a falonsa. Yana zaune ya miƙe ƙafafuwansa akan table wayarsa ta fara ƙara, yana ganin sunan Attaruhu yai murmushi sannan ya ɗauka.
"Your Excellency Ummata ba ta da lafiya, na taho gida tun ɗazu. Idan ba matsala ina so na kwana a gidanmu"
"Ba matsala"
Ƙiit ta kashe wayar.
Ba dan Abba da yace bai yadda ta kwana ba ai ba abinda zai sa ta kira Gwamna ta nemi izininsa. Ta kusa ta daina amsa sunan matarsa balle ace komai za tayi sai ta tambayeshi.
Minti ishirin yai yana jiran Bilkisu saboda bata gida lokacin da ya kirata.
Tana shigowa gidan, Hansa'u da ke kallo a falo ta karɓi jaka da gyalenta ta wuce mata da shi ɗaki. Bilkisu ta ƙarisa sashen Gwamna.
Ta riga ta samu tabbaci akan babu wanda ya isa ya tsige mijinta shiyasa ta shigo gidan hankali kwance.
"Na san kin ji labarin Impeachment notice da aka kawo"
"Wahala kawai za su bawa kansu, ba wanda ya isa ya tsige ka"
"Ki fara tattara kayanmu, zamu koma asalin gidanmu"
"Wasa kake ko?"
"Zan yi resigning Bilkisu. Kin sani tun farko ba wai ina son harkan nan bane, ina yin komai ne saboda Baba. Munada komai Bilkisu kafin wannan matsayin babu abinda muka rasa na rayuwa. Bayan komai ya lafa dukkanmu zamu bar ƙasar nan. Nana, Mahirah, Junior duk zasu samu kulawar mu"
Bilkisu ta fara kallon gefe da gefenta sannan tace "akwai abinda ka sha ne kafin na shigo?"
"Bilkisu siyasa ba a jinina yake ba, i'm failing the people, i'm failing my family. Ki duba yadda Nana ta lalace a ƙarƙashinmu because we are busy doing other things"
"Ba ka hau kujerar nan dan na zamo matar Gwamnan wata shida ba. Shekara takwas zan yi a matsayin nan kuma babu wanda ya isa ya ja da hakan"
"Bilkisu"
"Idan ka yi resigning gawata za ka zo ka tarar a gidan nan, ba inda zan je, siyasa kuwa yanzu ka fara dan wanda kayi a baya sharar fage ne"
Gwamna ya zubawa matarsa ido yana kallon yadda ta ke magana da izza kaman ta san gaibu.
"Suma masu son tsigekan muna nan jira muga da wani ƙaryar za su tuhumeka"
***
Umma tayi-tayi Asiya ta tafi gidanta ta ƙi. Kunyar 'yarta take ji wai sun je Asibiti tare ance musu ciki gareta. Bata san ciki gareta ba da ba za ta bari su je Asibiti tare ba. Yawan amai da zazzaɓi da take ji ta ɗauka malaria ce, ta ma siyi maganin malaria ta sha na kwana uku amma sauƙin sai a hankali. Ali daya shigo da rana ya samu tana sheƙa amai sai ya ji tsoro ya kira Asiya ya sanar da ita saboda Abba baya nan Inna Yaha ma ta fita.
Asiya kam ko ajikinta sai murna take yi za a haifa musu ƙani ko ƙanwa. Ta shiga kitchen ta haɗawa mahaifiyarta dambun couscous da ya ji kayan lambu da hanta.
Lokacin da ta kawo tare suka zauna, suna ci tana bata labarin wasu 'yan ƙauye da suka zo kwanakin baya wai su dangin Matar Gwamna ne. Suka zo su kusan takwas da tsummokaransu har da zabi da suka riƙo wai za su bawa Gwamna, da aka hanasu shiga suka ƙi tafiya suka tsaya a bakin gate, ƙarshe aka nemo Yaya Bello ya zo ya gansu yace bai taɓa ganinsu ba. Asiya tace abinda ya fi bata dariya wai su da Yafendon Tabawa uwa ɗaya uba ɗaya suke.
Umma ma sai da tayi murmushi. Asiya ta cigaba da gaya mata cewa kusan kullum sai an kirata ana ƙaryar dangi da ita. Akwai wadda tace ƙanwar Ale Faruƙ ce Asiya tace mata Ale ba shi da ƙanwa mace.
Bayan Isha Ya Ubayd ya zo gaida Umma. Sama-sama suka gaisa da Asiya kowa da abinda yake ji a zuciyarsa.
"Asiya we have to talk" ya faɗa yana nufin ta yiwa Umma bayani.
Umma dai ta yiwa Asiya kashedi akan ta sani ita ɗin matar wani ne dan haka ta kama kanta.
A ɗakin suka yi maganan nasu wanda ko Umma da bata jin abinda suke faɗa zai da ta zargi akwai matsala. Da ta tambayi Asiya mi suke faɗa Asiya ta mata ƙaryar magana suke akan bikin Faty da za ayi, tace sai anyi Kamu shi kuma yace ba za ayi ba. Umma tace mata ta bari yai abinda ya dace domin ya fita kusa da Faty.
Ubayd dai fita yai a ɗakin ransa ba daɗi.
Post a Comment for "THE GOVERNOR'S WIFE 18"