THE GOVERNOR'S WIFE 16
*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....
*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat
Bismillahir Rahmanir Rahim
Book one
16
Asiya da Sumayya na cin abincin dare Sha'awanatu Bacchi ta kirata. Jinjina ta mata kan abinda ya faru a wajen taro, ta bata shawaran kada ta taɓa bari Bilkisu Kachallah ta taka ta sannan idan tana son samun matsayi sama da Bilkisu dole ne ta koma gidan Gwamnati. Asiya ta mata godiya ta ajiye wayar tana murmushi.
"Anty Ale ya kira wayarki ɗazu da kika shiga banɗaki"
"Kin ɗauka?"
"A'a"
"Good"
"Anty, har yanzu fishi kike da shi?"
Asiya ta ajiye cokalin hannunta tace "taya ba zan yi fushi ba Sumy. Bayan kuɗin da Mutumin nan yake da shi, bayan kuɗin daya karɓa a wajen 'yanuwan Gwamna, kwanana huɗu da aure ya kirani yana cewa na nema masa kwangila a wajen Gwamna. Wani uban ƙwarai zai yiwa 'yarsa haka. Dan ba a chanja Uba ne da tuni na chanja shi"
Sumayya ta sa dariya.
Basu gama cin abincin ba Nana ta kira Asiya. Ko a ina ta samu numbarta oho.
"Antyna ina gayyatarki birthday na da za'ayi ranan Friday. Dan Allah ki zo"
"Wai ni yarinyar nan mi kika ɗaukeni ne?"
"Please Sweet Anty"
Asiya ta yi shiru na 'yan sakanni kafin ta ce "zan zo"
Tana ajiye wayar tace "inaga Gwamna mahaukata ya ajiye a gidansa"
Sumayya ta kwashe da dariya ta ce "Anty ai harda ke"
"Zan saɓa miki Sumy. Ni sa'ar ki ce"
"Anty ke fa kika faɗa da bakinki"
"Da matarsa da 'yarsa duk basu da kai, ranan da ta zo nan kinga yadda take girgiza kai kaman notinan kanta sun kunce, ni cewa ma nayi kan roba gareta"
"Kai! Anty"
Asiya ta sa dariya.
***
"Babu birthday wannan karan. In fact har na bar kujeran nan babu birthday, babu anniversary, babu wani celebration da za ayi sai dai biki ko suna"
"Wasa kake Saifuddeen. Mun yiwa Junior nashi farkon shekara ita kuna Nana sai kace ba za a mata ba. Ina ruwana da abinda mutane za su faɗa. Mu fa ba matsiyata bane, babu abinda muka rasa kafin ka hau kujeran nan dan haka dole ne mu kashe kuɗi wajen taya first born ɗinmu murnan cika shekara shabiyar a duniya"
" lokacin da Mahira tace ba ta son birthday ta gudu wajen Dadda, wani abu ya sameta da ranan ya zo ya wuce ba tareda anyi komai ba"
"Darling Mahira daban Nana daban"
"Dukkansu 'ya'yana ne Bilkisu. Kuma yadda ba ayi na Mahira wannan shekaran ba, ba za ayi na Nana ba"
Bilkisu ta matso kusa da shi, ta riƙe hannunsa tana murzawa a hankali, ta sassauta murya tace " na san baka son abinda zai jawo maka magana a gari, nima bana son haka. Ka yi haƙuri muyi mata small get together birthday party, acikin gidan nan, daga ƙawayenta sai 'yanuwa. I promise babu, 'yan jarida da za su zo. Na yarda Mahira ba ai mata birthday ba wannan shekaran, amma kasan itace tace bata so, Nana kuma tana so. Ba kuɗin Gwamnati zamu yi amfani da shi ba ka sani. Na maka alkawarin ni zan ɗau nauyin komai daga aljihuna"
"Still dai..."
Shhhh ta faɗa tana rufe masa baki da yatsunta biyu. Ta sani an gama kenan, Saifuddeen mijinta bai iya dogon jayayya ba...
Ranan Alhamis Gwamna Saifuddeen Kachallah ya wuce Birnin tarayya wani taro da za su yi na Gwamnonin Arewa.
Ranan Jummu'a kuwa Bilkisu Kachallah ta shiryawa 'yarta bikin birthday.
Babu taro sosai saboda taron strictly na wanda aka gayyata ne.
Ana tsakiyar taro Asiya ta zo, Nana na ganinta lokacin za ta yanka cake ta je da gudu ta rungumeta. Bilkisu Kachallah ta hangame baki tana mamakin 'yarta.
Asiya ta karɓi ɗan ƙaramin akwatin gift da ke hannun Sumayya ta miƙawa Nana ta ce "Happy birthday"
Nana ta sake rungumeta tana faɗin "thank you, thank you"
An ci, an sha, an bada kuma an karɓi kyaututtuka. Ana daf da za a rufe taro Asiya ta tafi.
Da Asiya ta dawo gida, dare ta bi tana tsara labari a laptop ɗinta, da ta gama ta turawa Mr Bassey tareda hotunan data ɗauka.
Washegari jaridar Climax ta fito da labarin birthday ɗin 'yar Gwamna. Hoton Nana sanye da wata matsatstsiyar doguwar riga kanta babu ɗankwali shine a shafin farko na jaridar, an rubuta *Gwamna Saifuddeen Kachallah ya zubar da miliyoyi wajen yiwa 'yarsa birthday*
A ƙasan labarin kuwa irin ɓarnar kuɗi da akayi aka lissafo, tun daga decoration, abinci, cake, souvenirs dama kayan da Nana da Bilkisu Kachallah suka dinga chanjawa a wajen, duk an bayyana. Daga ƙarshe aka ƙiyasta jimillar kuɗin da aka kashe zasu kai miliyan arba'in.
Lokacin da Bilkisu Kachallah ta ga jaridar Climax cilli tayi da wig ɗin kanta tana faɗin koma waye yai rubutun nan sai ta sa an ɗaure shi. Ta kira wani numba tana faɗin a nemo mata wanene ke da jaridar Climax, sannan tana son sannanin ɗan jaridar daya yai rubutun nan.
Duk wanda suka zo bikin sai da aka karɓi wayoyinsu saboda ba a son ɗaukan hoto. Mai hoto ɗaya ne ta yadda ya ɗau hotuna a wajen, cousin ɗin Nana ne ɗan Anty Rufaidah, babu yadda za ayi ya siyar da hotunan Nana wa 'yan jarida. Koma waye ya fitar da hotunan nan sai ta sa an hukunta shi.
Gwamna Saifuddeen na ɗakin hotel da suka sauka Chief of Staff ya nuna masa jaridar Climax a wayarsa.
Gwamna ya haɗiyi yawu da ƙyar. Ba abinda aka rubuta ne ya dameshi ba sai ganin duk cikin hotunan Nana da aka ɗaura babu wanda tayi shiga na mutunci aciki. Ya cizi leɓensa na ƙasa yana inama Nana a wajen Dadda ta taso kamar yadda Mahira ta taso a wajenta, ƙila da duk wannan ba zai faru ba. Da farko Bilkisu ya ɗaurawa laifi daga baya kuma ya gane cewa shine silar komai, ya barwa Bilkisu ragaman tarbiyyan 'ya'yansa bayan ya san irin tarbiyar da itama ta taso a kai.
"Wa ye keda jaridar Climax?"
Ya tambayi COS bayan wasu mintoci daya ɗauka bai yi magana ba.
"Da dai wani ne Mr Emmanuel Bassey amma na ji ance wani ɗan siyasa ya siyi jaridar watanni biyu da suka wuce"
"Ka bincika min waya siya"
"An gama excellency"
***
Asiya kuwa tsaf ta shirya dan fara aiki da investigative reporter mai suna Fou'ad Salisu. Shekaransa uku da fara aiki amma ya fitar da manya-manyan report guda biyu da ya ɗaukaka shi a ƙasar da ma duniya baki ɗaya.
Fou'ad ya yiwa Asiya alƙawarin binciko mata abin da take nema cikin ƙanƙanin lokaci...
Asiya na zaune akan kujera ta harɗe ƙafafuwanta, hannunta ɗaya riƙe da waya tana karatu, ɗayan kuma soyayyiyar gyaɗa take ci da shi. Lokaci lokaci ta kan yi dariya. Wannan karan da ta fara dariya harda tunkuɗe kwanon gyaɗa da ke gefenta.
Sumayya da ke rubutu a kan carpet ta ɗago ido ta kalli 'yaruwarta tana tambayarta ko lafiya. Sai da Asiya ta yi dariya ta isheta kafin ta ce "wani waƙar KaSaSa nake karantawa wai Attaruhu, kin ji abin dariya. Kai matar nan Allah ya bata baiwar tsara waƙa. Bari ki ji na karanta miki..."
Sallamar Uwani ya katseta. "Ranki shi daɗe kinada baƙi a falo"
"Su waye?"
"Yaya Bello ne da wani tsoho"
Asiya ta kalli Sumayya, Sumayya ta kalli Asiya, dukkansu suka haɗa baki wajen faɗin "Ale".
Asiya ta sako hijabi ta fito yayinda Sumayya tace fir bazata fito ba. Ale na zaune yana kora lemu Asiya ta shigo falon.
"Matar Gwamna" Ale ya faɗa da ƙarfi kaman wani Yaro.
Asiya ta haɗe rai ta zauna nesa da su tace "Baba lafiya?"
"Haba Asiya Shahidan Baba. Babu gaisuwa sai tambaya"
"To ai ni ban taɓa jin inda aka yi aure sati biyu Baban Amarya ya fara bibiyar 'yarsa ba, sai dai idan babu lafiya ne"
"Lafiya ƙalau muke, su Baffanki ma sun ce na gaisheki"
Yaya Bello ya miƙe yace "barin barku ku tattauna"
Asiya ta harareshi dan ta san shine zai yiwa Ale kwatancen gidanta. Sai kuma ta tuna Ale da Yaya Bello basa shiri.
"Tunda na miki maganar kwangila kika dena ɗaukan kirana. Haka ake yi, ko kin shigo daula kin manta da iyayenki ne"
"Ban manta da iyayen da tunda nayi aure suke aiko mani da addu'a ba. Amma na manta da Uban da ke maula a wajen mijin 'yarsa"
"Asiya!" Ale ya faɗa yana miƙewa a fusace.
Basu ji shigowar Gwamna falon ba sai da yai sallama.
Asiya ta kalleshi ta kauda kai yayinda Ale ya shiga gaishe shi jiki na rawa.
"Asya" ya kira a hankali. Ta ɗago ido ta kalleshi
"Follow me"
A tsakiyar falonsa ya tsaya, ya juyo ya kalleta. Yana tattare da fushin Bilkisu da Nana abinda ma ya hana ya fara wucewa chan gidan kenan, ya biyo nan ne saboda ya ɗan huce kafin ya je gida, kada garin fushi zuciyarsa ta sa shi aikata abinda bai dace ba. To gashi ya zo nan ma itama wannan Attaruhun tana yiwa mahaifinta rashin kunya.
"Disrespecting your father Asya. Kin san darajan Uba kuwa, kin san mutane nawa ne a duniya ke kukan rashin Uba. Ba zan lamunci wannan ba, ki je ki bawa mahaifinki haƙuri"
"Ba abinda zan yi. Ba a chanja Uba amma ni na chanja ranan da ya sayar maka ni. Idan ba zaka lamunta ba ka sake ni mana, ai kasan yadda nake sarai amma ka nace sai da ka aureni saboda zalin....ci"
Numfashinta sai da ya kusa ɗaukewa saboda matsowa da Gwamna yai daf da ita. Kallo ɗaya ta yiwa ƙwayar idonsa ta san babu wasa tattare da shi.
"Na gaya miki iya zaman da za mu yi tare dole ne ki riƙe matsayin Matar Gwamna da kyau, which means duk wani rashin kunya, shirme da shiririta za ki ajiye su gefe. Ki je ki bawa mahaifinki haƙuri kafin raina ya ɓaci"
Ai da sauri Asiya ta bar falon. Bata manta kashedinsa ba, daren farko da aka kawota gidan. Ya riga ya san abu ɗaya take tsoro, kuma da shi ne kawai zai iya maganinta.
Ale na zaune yana jujjuya maganganun Asiya a ransa, Asiya ta shigo falon.
"Kayi haƙuri Baba" Asiya ta faɗa ba tareda maganar ya kai zuciyarta ba. Ta tsani halin mahaifinta fiye da soyayyar da take mishi.
"Ya zan yi da 'ya'yan zamani. Allah ne ya baki wannan matsayi Asiya, ni ba sayar da ke nayi ba.
"Na ji daɗi da kika kawo Bello kusa da ke, ina fata za ki nutsar da shi ya dena shaye-shaye, yai ƙoƙarin ajiye Iyali. Na barki lafiya"
"Baba" Asiya ta kira da muryar kuka.
Ale ya juyo ya kalleta jikinsa a sanyaye.
"Ka yafe min dan Allah"
"Na yafe miki, nima ki yafeni in Allah ya so ya yarda ba zan sake yi miki maula ba"
"Haba Ale Faruƙu na gidan Tabawa da Gwani Lukman. Ni fa ban ce kana maula ba, inaga dai daga TV ka ji wannan maganar"
Ta yi maganar tana kamo hannunsa ta zaunar da shi a kujera. Wani abu ta gani a idonsa lokacin da yai maganarsa ta ƙarshe. Bata taɓa tunanin Ale zai ji kunya ko yai danasanin wani abu ba, amma yau ta ga kunya a idonsa, ya yi danasanin neman alfarma da ya zo yi.
"Baba barin shiga kitchen da kaina na maka girki"
Ale yai dariya yace "Ina Sumayye? ko ta je makaranta"
"Barin kira maka ita".
Asiya ta shiga kitchen ta zage ta yiwa Ale girki. Tuwon shinkafa miyar kuka da ya ji naman kaza ta yi, ta haɗa masa da tacaccen juice ɗin Kankana da Abarba.
Ale ya ci abincin sosai ya kuma sa albarka. Da zai tafi ya ce ta gaishe masa da Gwamna ya ajiye mata kyautar da ya kawo wa Gwamna na tacacciyar Zuma a cikin jarka 5 liter.
Ga mamakin Asiya lokacin da ta shiga falon Gwamna sai ta sameshi a dining table yana cin abincin da ta girka.
Ta san dai ta ɗebi abincin Ale sannan ta barwa Sumayya ta kwashe sauran. Yaushe Sumayya ta haura sama ta kawo masa abinci bata sani ba?. Tukunnama dama tuntuni bai fita bane. Ita ba sanin ranakun ta yi ba balle ta gane yau kwananta ne ko ba nata bane. Bata taɓa masa girki ba, idan ya zo gidanta bata san ya yake cin abinci ba, bata ma san su waye ke gyara masa sashensa ba.
Gaskiyar Sha'awanatu Bacchi ne da tace dole ta koma gidan Gwamnati. Idan suka cigaba da zama irin haka ba zata rinƙa samun bayanai akansa ba.
"Babana ya wuce, ya bayar da wannan a baka"
Ta ajiye jarkar kusa da ƙafarsa. Bata san ya akayi ta tsaya kallon ƙafarsa ba, babu takalmi a ƙafarsa, jallabiya ya saka hakan ya sa zaman da yai ya bayyana silangarinsa da ƙafafuwansa. Ta kan ce Ya Ubayd na da marteten ƙafa, mai kauri, mai faɗi. Har tana tsokalarsa idan suka yi aure sai dai ya dinga saka safa saboda ƙafarsa ba ta da kyau.
Ta zubawa doguwar ƙafarsa ido, ƙafar a mulmule take da gani zai yi laushi, yanada dogin yatsu cike da baƙin gashi zara-zara da suka ƙarawa ƙafar kyau.
"Ƙafar ne yai miki kyau ko neman wajen da zaki ɗaura min jarkar kike?"
"Allah sawwaƙa, mi zan yi da baƙin ƙafa kamar na Burgu"
Murmushi yai har saida haƙwaransa suka fito. Asiya ta yi saurin ajiye jakar ta juya.
"Ki shiga min da shi ɗaki, Please"
"Ban san wanne ne ɗakin ka ba"
"Kin taɓa tambaya ba a nuna miki ba?"
"Zan nema da kaina"
Ɗakin farko da ta duba a kulle yake, na biyu ma haka, na ukun da ta shiga ta ajiye masa jarkar kusa da gadonsa. Ɗakin ya mata kyau sosai, tun daga design zuwa furnitures da aka saka.
Ta buɗe ƙofa kenan tayi kiciɓis da Gwamna zai shigo.
"Har kin gama ganin ɗakin?"
"Babu abun kallo ai"
"Na ɗauka za ki tsaya muyi wanka tare ai"
Yai maganar yana kanne mata ido. Ƙirjinta ya shiga lugude. Iya zaman da za ta yi da shi ba abinda zai shiga tsakaninsu, jikinta da ruhinta duk na Ubayd ne.
Ta tsane shi, daga nesa zata gama cika baki akansa amma yana zuwa kusa da ita ƙwaƙwalwarta sai ya juya ya fara kawo mata wasu tunani daban.
Matsawa yai ta fice daga ɗakin ba tare da ta iya furta komai ba.
***
Umaru Kwom na zaune a guest house ɗinsa tareda wasu mutane guda biyu. Ɗaya member ne na House of Assembly, ɗayan kuma mai bashi shawara ne.
"Idan har aka tsige Saifuddeen Kachallah banida matsala da Alhaji Yamai, saboda tamkar na lashe zaɓe ne an gama"
"Kana ga za a tsige Saifuddeen Kachallah? Mutumin nan fa ba shida wani aibu, he's totally clean"
"Senator Bashari kenan. Ai idan Saifuddeen Kachallah bashida wani datti, mu zamu yaɓa masa dattin, burinmu ai duniya ta ganshi da datti ne"
"Da kamar wuya Alhaji Umaru" Senator Bashari ya faɗa. Ya cigaba bayan ya kurɓi giya "Alhaji Sani Kachallah ba zai taɓa bari a tsige ɗansa ba"
"Ko ba a tsige Saifuddeen Kachallah ba, na yi alkawarin shi da kansa sai ya yi resigning"
Mai bashi shawara yace " ban ƙi taka ba Excellency, amma koma mi zamu yi ya kamata muyi da sauri tunda sati uku masu zuwa za a yi primary election daga nan kuma ba wani lokaci garemu ba, Kamfen za a fara gadan-gadan"
"Kar ku damu komai zai zo cikin sauƙi, an riga an fara aiki akai"
Post a Comment for "THE GOVERNOR'S WIFE 16"