Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

THE GOVERNOR'S WIFE 15

 


*THE GOVERNOR'S WIFE*

...... MATAR  GWAMNA....



 *©Azizat Hamza*

 wattpad Azi_zat 



Bismillahir Rahmanir Rahim




Book one



15



Washegari da Asiya tayi sallar Asuba komawa bacci ta yi sai ƙarfe goma aka fara buga mata ƙofa. Jiya bayan Gwamna ya fita daga ɗakin kullewa tayi dan bata yarda da shi ba.

Lokacin da ta buɗe ƙofa wata mata ta gani sanye da uniform riga da wando da ƙaramin hijabi kalar ruwan ƙasa.


"Ranki shi daɗe fatan kin tashi lafiya. Na zo tambaya ne shin abin karinki a kawo shi falonki ne ko a barshi a dinning room?"


"Ki kawo min ɗaki"


"Shikenan, barin kawo"


Bayan ta karya kiran Faty da Sumayya ta yi ta musu ban gajiyar biki. Da ta kira Queen Bee tsiya ta dinga mata wai ƙila an samu ɗan Gwamna jiya da dare. Asiya tace Allah ya sawwaƙa.

Duk da ta yiwa Ummanta text da Asuba sai da ta sake yi mata wani text ɗin tana tambayarta ko 'yan biki sun gama tafiya.


Ƙarfe shaɗaya da rabi,  Uwani matar data kawo wa Asiya abinci ɗazu ta zo ta sanar da ita cewa tayi baƙi. Asiya ta zura hijabi ta fito babban falo inda baƙin ke jiranta.

Wasu mata ne guda huɗu dukkansu babu wanda ta sani a ciki. Jagorarsu ta mata bayanin ko su ɗin su waye, sannan suka faɗi abinda ya kawosu wai sun zo gaisheda Amarya.


Women leader ce ta jam'iyya da kuma shugaban ƙungiyan Mata 'yan kasuwa da Sakatarorinsu.

saura kaɗan Asiya ta ce musu ko uban mi zuwansu zai ƙara mata sai kuma ta dakatar da harshenta.

Ta musu godiya bayan sun ajiye mata kyauta, ta haɗa da cewa da basu yi wahalar kawo komai ba.


Asiya ba tayi minti shabiyar da shiga ɗaki ba aka sake zuwa kiranta wai tana da baƙi. Wannan karan su Hajiya Batula  ne da wasu 'yanuwan Gwamna suka zo mata sallama dan zasu wuce garuruwansu.

Haka baƙi suka dinga zuwa mata gaisuwa har dare. Ƙarfe bakwai na yamma ta ce da Uwani duk wanda ya sake zuwa ace ya dawo gobe.

Bayan ta bada umurnin sai kuma chan ƙasan ranta ta fara tunanin tun yanzu har ta fara bada umurni, ita ɗin fa ba kowa bace.



***



"Mommy zan je gidan mu, akwai wasu kayana da na ke son ɗebowa"


"Nana duk kayan da suke nan basu isheki ba"


"Kai Mommyyy, kin san dai ba komai muka ɗauko ba da zamu dawo nan"


"Naji, je ki amma ki dawo da wuri, sannan ba ruwanki da jikar maiƙusumbi"


"Yes Mom"


Daurewa kawai take amma tun safe take neman hanyar da zata zo ta ga Asiya. Airah data kasa ta tsare ne ta hanata zuwa.


Asiya na sallah Nana ta faɗo mata ɗaki babu ko sallama. Sai da Asiya ta sallame ta juya ta ga Nana zaune a kujera tana murmushi.


Ta ganeta saboda kamannin Gwamna gareta har dimple ɗinsa.


"Lafiya za ki shigo min ɗaki babu sallama?"


"Haba Amaryarmu, nan ma fa gidanmu ne"


"Idan gidan ku ne, ai ba ɗakin ki bane. Tashi ki fita "


"Haba Anty nah" ta faɗa tana bubbuga ƙafa tana tura baki


Lallai yarinyar nan sangartacciya ce. Asiya ta faɗa a ranta.


"Anty dan na zo gaishe ki shine zaki kore ni"


"Ya sunan ki ma?"


"Nana Khadijah"


"Fita min daga ɗaki Khadija. Nagode da gaisuwa"


Nana ta miƙa mata hannu tace " please be my friend"


"Kin san Allah idan baki fita ba zan wanka miki mari"


"Ok, goodnight Sweet Anty"


Asiya ta bi bayanta da kallo tana taɓe baki...




Washegari ƙarfe tara na dare Gwamna ya shigo gida. Asiya na jin shigowarsa ta fito da sauri tabi bayansa suka haura sama tare. Da safe ya bata key ɗin mota wai kyauta daga Alhaji Sani Kachallah sannan yace duk lokacin da zata fita akwai Dreba da zai fita da ita


Zai buɗe ƙofar falonsa tace " inada magana"


Bai amsa mata ba ya kutsa kai ciki.

Sai da ya zauna ya ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya sannan yace " ina ji"


"Ina so ƙanwata ta zo ta tayani zama. Sannan ina son kawo Driver nawa na kaina"


"Mi ya samu Dreban da aka baki?"


Yai maganar yana tsareta da idanu.


"Na fi son wanda zan yarda dashi ɗari bisa ɗari"


"I see.  Ki submitting CV ɗinsa a duba"


" Yayana ne, Ubanmu ɗaya, akwai wani CV daya wuce wannan?"


"Ta ya zan yarda cewa wanda ki ka faɗa shi ɗin za ki kawo?"


Ta ji zafin maganansa amma ta dake tace " ka iya sawa a mana DNA test da ni da shi" 


Yai murmushin gefen baki yace " abu ne mai sauƙi ai"


"Sannan abu na gaba. Bana son kuɗin jini, kuɗin talakawa. Kasan yadda za ka yi ka cire kuɗin da ka zuba a account ɗina yau da rana, bana buƙatarsu"


Miƙewa yai yace " gudummawa ce da Ahalin Kachallah suka miki, idan ba kya buƙata ki tuntuɓi Hajiya Umma ki mata bayani"


"Zan iya kawo Sumayyan? ko itama sai da DNA test"


"Zasu iya zuwa" ya furta sannan ya wuce wani hanya wanda take ganin a nan ɗakunan sashen suke.



Tana shiga ɗaki ta kira numbar Yaya Bello. Yana nan teburin mai shayi ana rikici da shi akan kuɗi ta kira.


Daga wajen da yake yana ɗaukan kira ya fara cewa "gashi nan ai ƙanwata Matar Gwamna ke kira"


"Yaya Bello"


"Hello Asiya, Hello esselenci. Esselenci kina jina" 


"Ina ji Yaya, ya kuke"


"Lafiya lau muke. Ya Gwamna?"


Asiya ta katse zancen da cewa "Yaya inada aiki da zan baka, idan babu matsala"


"Wallahi zan yi"



Lokacin data faɗa masa direbanta take so ya zama wani tsalle ya daka yana ihu. Yaya Bello ya girmeta da kusan shekaru shahuɗu amma bai damu da cewa ƙanwar bayansa zai dinga tuƙawa ba.


Shine babban ɗa namiji acikin 'ya'yan Ale Faruƙ amma kuma shine marar aikin yi walaƙantacce. Shaye-shaye ya lalata masa rayuwa. Lokacinda yake yaro shekara goma shabiyu zuwa shabiyar haka, ya taɓa halin ɓera, da abin ya ishi Ale sai ya kaishi wajen Gwani. Gwani ya dinga masa addu'a yana bashi ruwan rubutu har ya zo ya rabu da abun. 

Daga baya daya bi wasu abokai suka tafi chan kudu leburanci shikenan ya lalace da shaye-shaye. Baya bin mata, dan akoda yaushe addu'ar Gwani Allah ya raba shi da sata da kuma zina.


A shekarar da Gwani ya rasu a shekaran ya dawo gida. Bai dawo da komai ba saboda komai ya tafi a shan abubuwan maye.

Ale ya masa aure ya buɗe masa shago ko zai nitsu amma inaa. Kafin wata shida komai ya ƙare a shagon, ita kuwa Amarya shekara ɗaya tayi da 'yan kwanaki iyayenta suka sa ya saketa saboda tunda aka kawota ko hannunta bai taɓa riƙewa ba.

Ale ya kaishi wajen wani abokinsa mai maganin gargajiya a duba shi ko bashida lafiya ne,  amma akace lafiyarsa lau.


Ƙannensa maza biyu sun yi aure harda 'ya'ya,  sannan suma kasuwancinsu ya fara bunƙasa tun lokacin da Ale ya yaye su daga kasuwancinsa, amma Yaya Bello kam sai zaman daba...



***


Asiya na aiki a laptop ɗinta Sumayya ta shigo ɗakin da sallama.

"Kai Anty na gaji" ta ajiye jaka ta faɗa kan gado


"Tun yanzu? Shekara huɗu zaki yi, idan kuma aka shiga yajin aiki ƙila kiyi biyar ko shida"


"Kai! Allah ya sawwaƙa"


"Welcome to the game sister, haka muma muka yita cika bakin nan, daga ƙarshe sai da muka ƙara wata biyar akan shekaru huɗun daya kamata muyi"



"Anty kin san me, wata a ajinmu tace tana son ƙawance dani, ta nuna min hoton da mukayi a wajen dinner ashe nima na zama celebrity"


"Ban yadda ba"


"Iye?"


"Ban yadda da ƙawancen nan ba. Duk wacce za ta shiga jikinki saboda ke ƙanwar Matar Gwamna ce ba ƙawa ce da zata ɗore ba. Sannan ina so ki sani cewa matsayina na Matar Gwamna na lokaci kaɗan ne"


Sumayya tayi saurin miƙewa zaune.


"Anty dan Allah kada kice min za ki bar gidan nan. Kwana biyu dana yi a gidan nan ban taɓa gani kin shiga sashen Gwamna ba, idan ya dawo ko..."


"Bana son gulma. Kada ki bari wani matsayi ya ruɗe ki dan ba mai ɗorewa bane"



Sumayya ta riƙe baƙi tana kallon Asiya da hankalinta ke kan abinda take ta rubutawa a laptop ɗinta.


Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin aka yi, Sumayya ta je ta buɗe.

Da ta dawo ta miƙawa Asiya wani envelop tace Uwani ce ta kawo.


Asiya ta karɓi envelop ɗin ta yaga ta fito da wasiƙar ciki.


"Shegiyar mata wai office of the first lady, ko uban wa ya bata office oho"


"Anty minene?"


"Bilkisu Kachallah ke gayyatata taron gajiyayyu da naƙasassu da za ayi gobe Asabat a foundation ɗinta"


"Anty zaki je?"


"Idan ban je ba ai ta ci nasara a kaina"...


Tunda aka kawota bata taɓa fita ba, a ranan da ta yiwa Yaya Bello maganan zama Direbanta washegari ya niƙo garinsa ya taho.


Kiran Yaya Bello tayi a waya tace masa gobe za su fita za ta aiko Sumayya da key ɗin mota ya duba lafiyar motar.



Washegari kuwa ƙarfe shaɗaya Asiya da Sumayya suka wuce wajen taro.

Lokacin da suka je an tanada mata waje na musamman kusa da Bilkisu Kachallah. Tana zama Bilkisu tace "ƙarfe goma aka fara taro, nan gaba ki duba agogonki da kyau"


"Ohh sorry! Kin san yau Excellency zai bar gidana, dole na kimtsa shi kafin na fito. Kin san ai yana jimawa a banɗaki idan zai yi wanka, da muka shiga tare kuwa na yi ƙoƙarin na dirzashi da kyau amma dana taɓa shi sai jikinsa ya ɗau mazari..."


"Shut up!" Bilkisu ta faɗa a fusace, bata san ma maganar ta fito da ƙarfi ba sai da ta ga wanda suke kusa da su na kallonta. Sai ta bige da kama hannun Asiya tana dariya kamar irin wasan nan take. Asiya ta yi murmushin nasara, yau duk ta inda Bilkisu Kachallah za ta fito tana nan dai dai da ita.


Kiran Bilkisu Kachallah da aka yi ta zo tayi bayani nan take naƙasassun wajen suka fara tafi suna kiran sunanta.


Ko da za su shigo hall ɗin abin daya fara ba wa Asiya haushi shine UWAR MARAYU da aka rubuta a saman hoton Bilkisu Kachallah. Bilkisu ba ta yi kama da macen da za ta so talaka ba balle maraya amma da sannu za ta karya mata fiffiken da take furkawa da shi.


Maganan minti shabiyar tayi sannan ta ce zata kira 'yaruwa, ƙanwa, kuma abokiyar zamanta ta zo ta faɗi abu ɗaya ko biyu a wajen duba da cewa ita ɗin ma ta fito daga tsatson naƙasassu.

Asiya ta cizi leɓenta lokacin da Bilkisu Kachallah ta kirata da 'yar Kurma jikar maiƙusumbi. 


" Hajiya Asiya Kachallah"  MC ɗin wata mata wacce bleaching ya gama koɗar mata da fiska ta sake kiran Asiya a karo na biyu bayan Bilkisu ta koma ta zauna.


Dai dai zata tashi taji Bilkisu tace "maza aje a gaya musu yadda ake kula da naƙasassu"



Sallama Asiya tayi lokacin data karɓi mic a hannun MC. Jin an amsa ƙasa-ƙasa ya sa ta ƙara maimaita sallamar da muryarta mai kaifi, wannan karan suka amsa da ƙarfinsu.


"Barin baku wasu labarai masu daaaaɗiiiii" ta ja ƙarshen maganar tana juya hannunta. Nan da nan aka saka dariya 

"Akwai wani yaro da aka haifeshi da ƙusumbi shekaru tamanin da biyar da suka wuce. Aka damƙa shi wajen wani malami dan yai karatu tun yana shekara shida haka. Wannan yaro yai karatu sosai a wajen Malaminsa dama wasu Malaman daban. Yai aure Allah ya azurta shi da 'ya'ya uku Maza. Wannan yaro mai ƙusumbi ɗinkin hula yake yana ciyar da iyalinsa da gumin hannunsa har Allah ya ɗau ransa. Sai dai kun san me? Kafin ya rasu yayi  karatun ƙur'ani, ya ji haddan Ƙur'ani har mutane su ka rinƙa kiransa da Gwani. Wasu daga cikin ɗalibansa sun ce kafin Gwani ya rasu ya rubuta ƙur'ani daga farko har ƙarshe da ka sau ashirin da ɗaya wasu ma su kance sau talatin ne.  Lokacin da Gwani ke ciwon ajali kafin a bashi abinci ya ci sai ya yi ƙoƙari ya rubuta ayoyin ƙur'ani a Allonsa kafin ya ɗanɗani abincin. Har ya koma ga Allah bai taɓa roƙo ba, bai taɓa zuwa maula wajen Attajirai ba.


"Akwai wata mace dana sani  da aka haifa da lalurar kurmanta, aka mata aure, suka rabu da mijinta da 'ya ɗaya tsakaninsu. Wannan mata ta sake aure mijinta ya taimaka mata ta fara karatun yaƙi da jahilci. Ta koyi sana'ar ɗinki da saƙa, yanzu haka matar nan Allah ya rufa mata asiri tana ɗinki tana kuma saida kayan sanyi irinsu, Zoɓo, kunun Aya da sauransu.


"Akwai wani gurgu a ƙasan layinmu kullum idan zan wuce Islamiyya yana zaune a ƙofar gidansa yana gyaran takalmi , da Allah ya yassara masa har takalma ya saro na maza da mata yana saidawa, duka a ƙofar gidansa.


"Lokacin da nake bautar ƙasa a wani gidan talabijin akwai wata mata makauniya wacce ke gabatar da shiri na musamman dan wayae da kan al'umma akan mahimmancin ilimi wa naƙasassu.  Inaga za ku tuna da Dr Hajiya Laraba Bakatsine wacce ta rasu farkon shekaran nan, ga wanda basu sani ba degree uku ta yi kuma duka da lalurar makanta.


"Abu na ƙarshe da zan faɗa shine, naƙasa ba lasisi bane na yin barace-barace ko maula. Ina so ku sani Naƙasassu na da damar yin kasuwanci ko sana'a, sannan su nemi ilimi kamar kowa. Ina fata Gwamnati za ta bawa naƙasassu damar yin kasuwanci d neman ilimi kamar kowa. Mu tashi lafiya"


Kafin ta kai kujerarta wani gurgu ya turo kekensa ya sha gabanta, idonsa fal da hawaye ya haɗe hannunsa biyu ya fara mata godiya,  kan kace me, naƙasassu  sun yanyameta suna mata godiya.  Maganganunta sun taɓa naƙasassu da dama a wajen, wanda zuciyarsu ta kafe kuwa, sun sawa ransu cewa bara sana'a ce kuma ko me za a musu sai sun je Kudu sun yi sana'ar su.


Yadda ka san sassaƙa Bilkisu akayi haka ta daskare akan kujera ta kasa motsawa. Ba ta hango wannan ba, ba haka ta shirya ba. Da ƙyar ta iya tashi lokacin da aka kirata ta zo ta rufe taro da addu'a. Asiya ta yi murmushi lokacin da taji Bilkisu tace ayi salati wa Annabi amma ba ta buɗe baki anji salatin ba, sai ta rufe ido tana muimui da baki kaman Akuya na cin ciyawa... 


***

A wani ƙaramin ɗaki kuma wata mace ce sanye da riga da zani da ɗankwali dukkansu daban-daban. Kallo ɗaya zaka mata ka kirata 'yar ƙauye, sai dai yanzu da take gaban wata na'ura tana magana da harshen faransanci dole ka kirata gogaggiyar 'yar boko, yadda take magana da harshen ka ce a birnin Paris aka haife ta.


Cikin bayaninta take bayyana cewa har yanzu bata samu ƙwaƙwƙwaran hujjar da take nema ba, amma kuma tanada yaƙinin za ta samu nan bada jimawa ba. Babu tantama matar da take bincike akanta tana  kasuwancin miyagun ƙwayoyi, amma saboda matsayinta ba za a kamata ba sai da hujja mai ƙarfi. Hujjar take nema sama da shekara ɗaya da take aiki da ita.


"Ba matsalata Bilkisu Kachallah ba, matsalata Madam Bintu ce ka sani. Dan haka ba ruwana da matar da Gwamna ya aura, that's his business"


Mutumin da take magana da shi yace "akwai jami'ar DEA da zata zo daga America kan batun safarar miyagun ƙwayoyi, idan ta iso zan haɗaki da ita. Agent Dahlia tanada interest sosai akan case ɗin nan, kuma na san za ta taimaka sosai"


"Yes Sir"  daga haka ta rufe na'urar  ta ɓoye shi a ma'ajiyarsa...



"Hansa'u...Hansa'u...Hansa'u"



Masu aiki uku ne a gaban Bilkisu Kachallah amma ba su take nema ba. Hansa'u ta iso da gudu tana faɗin "Hajjaju nah ki gafarceni, sallah nake"

Bilkisu ta ce " Sallan Uwarki, matso nan" Hansa'u ta matsa kusa da ita kafin ta gama matsawa ma Bilkisu ta ɗauketa da mari tana faɗin " dan Ubanki kashe min ɗa zaki yi? "


"Hajiya wane Ubana" Hansa'u tayi maganar tana sosa kumatu


"Uban me ya hana ki sawa junior inhaler a aljihunsa?"


Ta sani lokacin data shirya Junior  ta saka masa inhaler a aljihun wandonsa sai dai in cirewa yai, amma a yadda Bilkisu Kachallah ke tiriri ba zata saurari bayaninta ba sai dai kawai ta bada haƙuri.


"Tuba nake Hajjaju, mantawa nayi"


Bilkisu ta sake kai mata duka tana faɗin "idan haka ya sake faruwa sai na yanka ki a gidan nan"


Abu biyu ne ya haɗuwa Bilkisu, na farko ta ƙumso baƙin ciƙin Asiya, na biyu kuma ta shigo falo ta samu ɗanta na kokawa da numfashi babu kowa kusa da shi. Saboda mijinta da ɗanta na da lalurar Asthma ba a rasa inhaler a jakarta. Hakan ya sa ta ciro ta jakarta ta matsa masa a baki.


Hansa'un dai aka saka ta goyi Junior ta wuce da shi ɗaki.



Da dare da Gwamna ya dawo gidan Gwamnati saboda kwanan Bilkisu ne. Bilkisu ta same shi ta fara sauke masa fushinta.


"Saifuddeen sati ɗaya da zuwanta amma har ka fara nuna banbanci. Ta ya zaka siya mata sabon mota bayan akwai mota a gidan da za ta yi amfani da shi.

I thought you said you married her for political reason, miyasa kake wanka tare da ita? Have you slept with her?"


Gwamna ya fara rage kayan jikinsa ya manta da ita a ɗakin. A gajiye yake baya son abinda zai ɗaga masa hankali.


"Saifuddeen ka gaya min gaskiya, ka..."


"Wanda suka kawo miki gulmar za ki tambaya bani ba"


"Ita da bakinta ta faɗa min yau kun yi wanka tare"


Har ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya fasa yai murmushi ya wuce banɗaki. Kafin ya kulle ƙofa Bilkisu ta faɗo ciki tana faɗin da ita zai yi wanka.


Lokacin da Sakatare ya nuna masa video na abinda ya faru a wajen taron da Bilkisu ta shirya ya jinjinawa Asiya saboda tarko Bilkisu ta ɗana mata lokacin da ta kirata da 'yar Kurma jikar maiƙusumbi. Ya sani ta so Asiya ta harzuƙa ne ta faɗi baƙaƙen maganganu a wajen  ko ma ta zagi Bilkisun da wani abu, sai kuma Asiya ta nuna mata cewa ita ɗin 'yar jarida ce.

Post a Comment for "THE GOVERNOR'S WIFE 15"