THE GOVERNOR'S WIFE 14
*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....
*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat
Bismillahir Rahmanir Rahim
Book one
14
***
Tunda su Asiya suka ci abinci suka koma sashen Dadda. Daga safe zuwa yammaci baƙi ne ke ta shigowa ganin Amarya. Matan manya da kuma manyan manyan Mata da su kayi suna a ƙasar. Wasu kallon ƙwaƙwaf ne ya kawosu saboda a samu latest gist da za a tattauna idan an haɗe a wajen shaƙatawa, wasu kuwa sun zo ganin Asiya Shahidan da ake kururutawa ne saboda ba su santa a Talabijin ba. Wasu kuma sun zo ne domin samun gindi a wajen Asiya dan basa shiri da Bilkisu Kachallah.
Asiya bata bada fiskar da zai sa a gane tana cikin matsala ba. Ko Faty da Queen Bee sun yi mamakin yadda ta sake tana dariya cikin mutane kamar auren soyayya akayi.
Kusan ƙarfe biyar da rabi na yamma Anty Saudah ƙanwar Bilkisu ta kawo musu wata jaka tace kayan da Amarya zata saka ne a wajen dinner. Basu waiwayi kayan ba saboda suna cikin jama'a.
Ƙarfe bakwai da minti Arba'in bayan Asiya ta idar da sallar Isha ta shiga banɗaki ta watsa ruwa. Suna ɓangaren da suka kwana jiya, su huɗu ne a ɗakin a chan falo kuma ƙawayen Asiya na makaranta ne da abokanan aikinta da suka samu pass ake wa kwalliya. Queen Bee ce ta karɓo pass ɗin dan haka Asiya bata san iya mutanenta da zasu zo wajen dinner ba.
Tunda Queen Bee ta fito da kaya Asiya ke girgiza kai, amma bata ƙi ta su Faty ba da suka ce ta dai gwada ta gani. Abu ɗaya ta sa aranta shine ko ta sha giyan wake ba za ta sa wannan kayan ta fita waje ba. Gown ɗin yayi ba ƙarya, ya amshi jikinta, duk wani tudu na jikinta ya fito sosai, sai dai rigar offshoulder ce rabin ƙirjinta a waje yake sai net da aka rufe wajen da shi wanda ko makaho ya shafa ya san ba abinda net ɗin ya tare. Cikinta ma net ɗin aka saka saboda an fafe lace ɗin wajen ne aka saka net. Ɗinkin yayi kamar bra ta saka da skirt sai aka rufe sauran wajen da ke bayyane da net.
"Inaga za mu nemi shawl da zai je da kayan kawai sai..."
"Baki da hankali Bahijja" ta kira sunan Queen Bee na asali.
"Gaskiya dai wannan kayan sai a hankali" Faty ta faɗa tana girgiza kai, sai yanzu da Asiya ta sa kayan ta gano akwai matsala.
"Bilkisu Kachallah ta riga ta rubuta headline da zai fito gobe a labarai idan na sa kayan nan. Beside, ni ba mahaukaciya bace na san darajan gidan dana fito"
"Anty dan Allah barin ɗauke ki a hoto, wallahi kin yi kyau" Sumayya ce da wannan maganar.
"Ban yadda ba... ki bari" sai kawai ta haƙura ta tsaya saboda Sumayyan ta riga ta fara ɗaukanta hoto.
Ɗaya kayan dake cikin jakar ma babu kanta, atampa ce da aka yiwa fitanniyar ɗinki. Ko gwadawa batayi ba ta tura gefe.
Ba abinda ya rage sai dai su saka abinda suke da shi.
"Ko na yiwa Hajiya Umma magana ne? tunda dama tace za a kawo mana kaya na ce an riga an kawo" Queen Bee ta faɗa tana kallon Asiya da ke zaune a gefen gado daga ita sai zani.
"Akwai wani gown a jakar da nace ki tahomin da shi Sumy, ɗauko min"
Tayi maganar kaman mai shirin yin kuka. Malaysian gown ne data gani a Amazon watanni kaɗan da suka wuce. Simple gown ce ruwan madara da aka yiwa design da duwatsu ruwan gwal. Model ɗin data saka kayan ta yi rolling da gyalen kayan ta saka crown a kanta kamar sarauniya. Asiya alokacin data ga kayan hango kanta ta yi sanye da irin kayan tana zaune kusa da Ubayd a ranan da za ayi kamunsu.
Su Queen Bee sun yaba da gown ɗin, sai dai kamar yai kaɗan ace Matar Gwamna guda ta sanya gown irin wannan da kuɗinsa ba zai wuce dubu hamsin ba. Kuɗin shipping dana kayan duka-duka dubu arba'in da huɗu Asiya ta siya a kuɗin Nigeria.
Lokacin da Queen Bee ke mata rolling gyale wasu mata suka shigo wai suyi sauri motoci sun fara isowa, Gwamna ya kusa ƙarisowa.
Asiya tace ba make up, amma duk da haka sai da Queen Bee ta shafa mata powder, ta sa mata mascara ya ƙara fito da dogon gashin idonta, sai kwalli da man leɓe, shikenan.
Ɗankunne da sarƙan diamond da aka haɗo a cikin kayan duk ba wanda Asiya ta saka. Hannunta dai zoben Azurfa ne da Ubayd ya siya mata sai kuma awarwaro na Azurfa shima da Maama ta bata da jimawa.
Takalmi flat ta saka ruwan gwal sai Queen Bee ta bata wani purse ruwan gwal shima. Ba su yi amfani da ko ɗaya daga cikin kayan da Bilkisu Kachallah ta aiko musu ba.
Hajiya Umma ce da kanta ta shigo yanzu dan duba shirin na su tunda Gwamna yace mata zasu iso nan da minti uku zuwa biyar.
Asiya tayi kyau sai dai ga wanda ya gaji arziƙi zai ga kamar shigar bata dace da irin wannan taro ba.
"Hajiya kayan da aka kawo bai d..."
"Kar ki damu, Bilkisu ai da gayya ta aiko miki kaya. Kinyi kyau sosai, ni dai roƙona kar ki bata dama akan ki domin yau ranan ki ne"
Asiya tayi murmushi. Ba wai dan taji daɗin abinda Hajiya Umman ta faɗa ba sai dan kawai dama abinda tayi niyyar yi kenan. Yau zata fara haɗuwa da Bilkisu Kachallah kuma sai ta nuna mata cewa ita ɗin ba hajar Kamfen ba ce. Tana cike da ita da abinda ta fitar na cin zarafi data mata, iyayenta da kuma Ubayd. Da sannu zata bata kashinta a hannu.
***
Gwamna ne da matarsa Bilkisu zaune a bayan lemosine wanda motar Alhaji Sani Kachallah ce aka fito da ita takanas saboda tafiyarsu wajen dinner.
Gwamna bai shirya yin hidima ba bayan reception da aka yi jiya suna dawowa daga wajen ɗaurin aure. Akwai abubuwa dayawa a ƙasa da suka fi hidiman bikinsa mahimmanci. Bilkisu ta riga ta shirya komai ba tareda ta tuntuɓeshi ba, abokinsa kuma ɗanuwansa Abdullahi ya takura masa akan sai yaje dinner ɗin sannan a ƙarshe kuma Alhaji Sani ya kirashi ya faɗa masa manyan mutanen da zasu halarci dinner ɗin.
Ya sani sarai Bilkisu neman suna take da abinda ta shirya, fatansa kawai ayi taro a watse lafiya.
A dai dai sashen Alhaji Sani Kachallah motarsu ta tsaya.
"Here's the plan, zaka zo tareda ita, ni kuma zan tareku a bakin ƙofa daga nan sai mu wuce wajen zamanmu. And, ka gayawa 'yar kurma ta yi murmushi saboda hotunan da za a ɗauka"
Bai amsa mata ba sai kawai ya shiga kiran numban Hajiya Umma.
Ana buɗewa Bilkisu Kachallah mota ta fita tana murmushi ta wuce inda jerin wasu motoci ke jiranta, Saudah Kachallah na bakin wata mota tana zuba mata murmushi na jinjina.
Hajiya Umma da Queen Bee ne suka fito da Asiya daga cikin gida, dake daga ɓangaren da suke zuwa inda motar Gwamna ke jiransu akwai tazara ko ina suka wuce sai guɗa da kirari ake mata ana taka musu baya. Sanda aka kai wajen motan Gwamna mutanen da suka rako Asiya sunyi Ishirin. Wani security ya buɗewa Asiya mota Hajiya Umma ta yi kane-kane a wajen saboda masu ribibin son ganin Gwamna. Sai da ta tabbatar Asiya ta zauna da kyau kafin ta rufe ƙofar tun ma kafin security ɗin yayi.
Kallo ɗaya ta masa ta kauda kai gefe. Yana sanye da farin babbar riga. Fari na ƙarawa baƙinsa haske, yana ƙara fito da kyaunsa. A kallo ɗaya data masa wanda hankalinsa ma na kan waya sai taga ya mata kwarjini, duk wani haushinsa da take ji sai taji wani nitsuwa ya sauka mata.
Ba ta san dalilin da ya sa ta ɗago dan sake dubansa ba, sai dai rashin sa'a lokaci ɗaya suka kalli juna. Ƙirjinta ya shiga lugude musamman da zuciyarta ya ankarar da ita cewa ita ɗin matarsa ce.
"Ina fata babu ruwan zafi a purse ɗinki?" Yai maganar yana nuna purse ɗin data riƙe.
Bakinta ya kafe na wasu sakanni, ta kasa bashi amsa har sai da ya sake cewa "Abubuwa sun faru a ƙurarren lokaci Asya. Amma a hankali zaki fahimci banyi komai dan na cutar da ke ba"
Maganar da ya faɗa ya tunzurata. Tace
"Mai girma Gwamna, a sannu zaka fahimci cewa bana barin sai ta kwana"
Daga haka ba wanda ya ƙara furta komai.
Suna isa hotel ɗin da aka shirya taron kafin a buɗe ƙofa Gwamna ya kalli Asiya yace "banda rawa" kafin Asiya ta bashi amsa aka buɗe masa ƙofa.
Tana jira a buɗe sashinta ta fita sai taga Gwamna ya ɗan rankwafa ya miƙa mata hannunsa.
Ta so ta buge hannun amma ta sani idon mutane akansu yake, duk abinda za tayi dole tayi takatsantsan. Ba mamaki akwai 'yan jaridar ƙwaƙwaf da ke ankare da samun hoto mai jan hankali.
Bata sani ba ko tunaninta ne, ko kuma dai gaske ne amma taji wani shock ya ratsa ilahirin jikinta sanda tafin hannunta ya shiga cikin nashi. Ko kaɗan hannunsa babu taushi da aka sani da hannun maza. To ina zai yi taushi kullum cikin AC.
Lokacin da ta fito maimakon ya sake hannun sai ya ƙara damƙe shi da kyau, a haka suka shige cikin hotel ɗin, Securities sun saka su a tsakiya suna basu kariya.
*to yanzu dai zamu dakonci shigowar Mai girma Gwamna Alhaji Professor Saifuddeen Kachallah da Amaryar sa Hajiya Asiya Kachallah. Dan haka kowa ya tashi tsaye a nuna musu soyayya*
MC kenan da wannan magana.
Daga inda suke tsaye suna jira a buɗe ƙofa Asiya ta ja tsaki jin sunan da MC ya kirata, kwana ɗaya da ɗaura aure amma har an fara laƙa mata Asiya Kachallah.
Daga bakin hall ɗin 'yan mata da maza ne masu ji da kansu suna tsaye daura da juna kowa ɗauke da ƙaramin kwando na alfarma da aka cika da flowers.
Security biyu da suke gabansu Asiya suka juyo garesu suka sara musu sannan suka koma gefe dan basu waje.
Bismillah Asiya ta furta a bayyane hakan ya sa Gwamna ya juyo ya kalleta kan kace me an musu hoto yayi goma.
Hannunsu sarƙe cikin na juna Suka fara takawa a hankali. Waƙa na tashi yayinda 'yan mata da samarin nan ke barbaɗa musu flowers a duk inda zasu taka.
Daga inda Bilkisu Kachallah ke zaune wani abu mai tsini ta ji ya soki zuciyarta. Abu biyu ne ya zo mata lokacin da ta kalli Asiya da Saifuddeen suna takowa fiskarsu ɗauke da murmushi.
Na farko dacewa na ban mamaki da suka yi wanda tamkar an halicci Asiya dan Saifuddeen ne dama. Shi baƙi dogo, ita fara doguwa. Ita ga ushirya daya ƙara hasko da kyaunta, shi kuma dimple ɗinsa daya bawa fiskarsa kyau da kwarjini na ban mamaki. Asiya bata saka kayan data aika mata ba, hakan na nufin babu abin yaɗawa gobe kenan, asalima kayan da ta saka da kuma kwalliyar da ba ta yi ba zai ja a yabeta a kafafen yaɗa labarai.
Na biyu kalaman malamin taurari Tsu Zhang ne ya sake dawo mata. *akwai wani tauraro daya fito a gefen tauraron mijinki. Yadda tauraronki ke haskawa tareda ta mijinki, haka wannan tauraro zai dinga haskawa tareda shi har sai tauraron mijinki ya haskaka fiye da tunaninki. Idan kikayi ƙoƙarin disashe wannan tauraro babu makawa da taki tauraron data mijinki haskensu zai dinga disashewa. Ki sani taurari uku a waje ɗaya suna bada haske na ban mamaki*
Murmushin yaƙe tayi a ranta ta furta "in dai ni Bilkisu Kachallah ina raye sai na juya ƙaddararki, tauraronki ba zai taɓa haskawaba. Saifuddeen nawa ne ni kaɗai, idan na gama dake har Saifuddeen ya shige cikin ƙasa babu macen da zata sake karambanin shiga rayuwarsa"
Kamar wacce aka tsikara sai ta miƙe da sauri tana faɗaɗa murshinta kamar bakinta zai taɓa kunnenta. Tana isa gabansu Asiya ta buɗe hannu ta rungumesu duka biyu nan da nan mutane aka sa tafi, hasken camera ta ko'ina sai wawal-wawal kake gani a hall ɗin.
Lokacin da ta sake su ta kama hannun Gwamna, ɗaya hannun kuma ta sa yatsa tana ƙoƙarin taro ƙwalla.
"Ikon Allah" Asiya ta faɗa a zuciyarta.
Dukkansu uku sai da suka zauna a mazaunin da aka tanada musu sannan mutane suka zazzauna banda ɗaiɗaikun manyan mutane irinsu Alhaji Sani, Umaru Kwom da Yallaɓai da basu tashi ba tun farko.
Kujerar Gwamna ce a tsakiya, gefensa na dama ta Bilkisu, gefensa na hagu kuma Asiya. Bilkisu Kachallah ta kalmashe ƙafa sai wani bushashatul wajahi take yi kamar itace Amaryar.
MC ya shiga yabon Bilkisu na yadda ta ajiye kishi gefe ta rungumi Amaryar mijinta. MC da azarɓaɓi harda cewa Bilkisu Kachallah tana koyi ne da matan Manzon Allah wanda suke kishi da ilimi. Asiya da jin haka ta ja tsaki.
Babu wanda zai ce Amarya bata fito ba. Babu kwalliya na hauka, babu takalmi mai tsini, babu sarƙa na Gwal ko Diamond, babu babu babu. Amma duk da haka Asiya Shahidah Faruƙ Baba ta burge kowa, shigarta mai sanyi ne daya fito da sahiihin kyaunta, babu ƙyalƙyalin shirme.
Queen Bee ce ta bada tarihin Asiya yayinda Alhaji Abdullahi babban abokin Gwamna ya bada tarihin Gwamna.
Lokacin da aka zo yanka cake su duka ukun suka haɗa hannu suka yanka. Gwamna ya fara bawa Bilkisu cake ɗin a baki, zai kuma yankawa ta karɓi wuƙan ta yanka ta kai cake ɗin saitin bakin Asiya tana murmushi...
Asiya bata yi mamakin ganin 'yan adawa a wajen ba saboda dama haka siyasa ta gada. Umaru Kwom sai washe haƙora yakeyi kace bikin ɗansa ko 'yarsa ake. Haka yazo yai musabaha da Gwamna aka ɗau hoto.
Da aka fara ɗaukan hotuna har sai da Asiya ta fara jin hajijiya, sai lokacin ta ankara ma ashe tun karyawar safe bata sake saka komai a bakinta ba.
Hoto za'a ɗauka tareda 'ya'yan Gwamna, Asiya tayi baya kamar zata faɗi sai jinta tayi jikin mutum, idonta na rufe dan haka bata san ƙirjin wa ta faɗa ba.
Ba ta ma san duk abinda ke faruwa ɗaukansu kawai ake a hoto ba. Bata ma samu kanta ba sai da mutumin da take ƙirjinsa ya jata ya zaunar da ita a kujera mafi kusa da su. Ya miƙa mata ruwa a baki, ta kafa kai ta shanye ruwan tas.
Dai dai kunnenta ya furta "are you alright?"
Sai lokacin ta ankara da mutumin da take tare da shi shine mutumin data fi tsana a duniya.
Gwamna ya murza hannunta yace "kar ki damu hoton ya isa haka"
Bai ƙarisa maganar ba Bilkisu ta iso wajen ta saka hannunta a kafaɗar Asiya ta raɗa mata magana a kunne.
"What's the meaning of this, na san ba zaki so gobe a rubuta ciki gareki ba ko"
"Idan an rubuta, zan faɗa musu cewa cikin Gwamna ne"
Babu wanda ya san mi suke faɗa. Ko Gwamna da ke wajen bai ji mi suka faɗa ba. Mutanen da ke wajen sun ɗauka Asiya na yiwa Bilkisu bayanin abinda ke damunta ne.
Dinner yayi kyau kowa ya samu abun gulma idan anje gida. 'Yan jarida kuma gobe zasuyi rububin bada bayanin abubuwan da suka faru a wajen taron dinner.
Bilkisu ce ta yiwa mutane bayanin cewa Amarya na tare da gajiya dan haka za'a ƙarƙare taron da wuri.
Ƙarfe goma da kwata na dare Hajiya Umma da Hajiya Batula suka wuce da Asiya Kachallah house inda aka sa tayi wanka ta shirya cikin wani haɗaɗɗen lifaya kalar baby pink mai zanen flowers ja, fari, purple da kuma yellow.
Dake daga wajen dinner kowa gida zai wuce shiyasa babu ko ɗaya cikin 'yanuwan Asiya lokacin da aka kaita ɗakin mijinta. Hajiya Umma da Hajiya Batula kawai ta sani cikin waɗanda suka rakota amma akwai wasu matan kusan su shida da bata taɓa ganinsu ba.
Addu'a suka mata da 'yar nasiha sannan suka mata sai da safe.
Bayan kowa ya tafi Asiya ta ɗau wayarta ta turawa Umma text. Allah Sarki UWA ko minti biyu bai cika ba Umma ta turo reply tana yiwa Asiya addu'ar Allah ya bata zaman lafiya sannan ta kwantar da hankalinta ta yiwa mijinta biyayya.
Asiya na gama karanta saƙon ta fashe da kuka. Kukan taka umurnin Umma da zata yi, kukan hukuncin data yankewa kanta ta ke, wanda shi kaɗai take ganin zai kawo mata kwanciyar hankali a rayuwarta.
Bayan ta sha kuka ta ƙoshi ta kwanta akan gadon tana tunanin inama inama. Inama wannan dare tasu ce ita da Ubayd...
***
"Mutumina irin wannan soyayya haka. Ka ganka a wajen nan kuwa, kaman wani super man tamkar ƙyaftawar ido har ka tarota jikinka, ni na ɗauka ma ɗaukarta zaka yi sai na tuna akwai sauran burbuɗin kunya a tattare da kai"
Gwamna ya harareshi yace "ban san yaushe zaka girma ba" Alhaji Abdullahi ya sa dariya.
Bayan sunyi sallama da Abdullahi Gwamna ya haura sama yana takawa a hankali kamar mai tsoron wani abu a saman. Cire kayansa yai ya watsa ruwa sannan ya fito ya shirya cikin riga da wandon bacci masu tsantsi kalar navy blue.
A hankali ya sauko ƙasa ya shige sashen da aka gyarawa Asiya. Falo da ɗakuna biyu. A da wajen an ginashi ne saboda Juniour idan ya kai kaman shekaru shabiyar sai ya koma wajen amma yanzu wajen ya zama ɓangaren amaryarsa.
Saifuddeen Kachallah bai taɓa tunanin ƙara aure ba tunda ya auri Bilkisu. Bayan ya rasa Misturah bai taɓa sawa ransa zai auri mata biyu ba.
Asiya ta zo gareshi ne saboda akwai ƙaddararta a cikin rayuwarsa. Sai dai yayi alƙawarin idan har aka gama ribibin zaɓe komai ya lafa zai sawwaƙa mata ta je ta auri wanda take so, alokacin babu wanda zai yi farautar Kamfen da ita. Bai faɗawa kowa hakan ba amma shawaran daya yanke a zuciyarsa kenan, kuma ya sani hakan ne daidai...
Da sallama ya shiga ɗakin Asiya. Tana kwance a tsakiyar gado tana sheshsheƙar kuka. Tausayinta ya ji ya shigeshi. Shi mutum ne da bayaso ya takurawa kowa balle kuma mace.
Bata ankara da shigowarsa ba sai da taji ya ɗan taɓa hannunta. Ta yi saurin tashi zaune tana faɗin "lafiya?"
Lifayarta da ya saɓule ya bashi damar ganin dogon baƙin gashinta mai tsantsi.
Ya ƙurawa gashin ido yana tantamar gashinta ne ko kuma wig.
"Na ce lafiya?"
"Ahm. Na zo ne na..." lura yai da hannunta na rawa alamar ta tsorata da shi hakan ya sa shi matsawa gefe, sannan ya cigaba.
"Kin sani daga jiya matsayinki ya tashi daga Asya 'yar jarida a jihar nan. Hakan na nufin akwai nauyi a kanki. Play your part a matsayinki na Matar Gwamna ni kuma zan sawwaƙa miki a lokacin da komai ya lafa"
"Lallai kam, to barin gaya maka idan ma wani abun kake nema ba zaka samu a wajena ba. Gangar jikina, zuciyata, ruhi na duka mallakin Ya Ubayd ne"
Magananta na ƙarshe ya shigeshi fiye da zato
"Ki faɗi koma minene, hakan ba zai chanja cewa daga yau gangar jikin, zuciyar da ruhin duka Allah ya mallaka min ba"
"Babu wanda na tsana irin ka, babu wanda na ke Allah wadarai da rayuwar sa irin ka, sannan ba ni da maƙiyi a duniya da ya wuce ka Your Excellency Governor Saifuddeen Sa'ad Kachallah. Ba za ka taɓa maye gurbin Ya Ubayd ba ko mi zaka yi kuwa" Ta ƙare maganar tana huci. Ta ɗauka zai fusata, ta ɗauka zai nemeta ta ƙarfi amma sai gani tayi ya tashi ya fice daga ɗakin ba tareda ya furta komai ba.
Post a Comment for "THE GOVERNOR'S WIFE 14"