THE GOVERNOR'S WIFE 12
*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....
*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat
Bismillahir Rahmanir Rahim
Book one
12
*GUZURIN TAFIYA*
"Asiya....Asiya"
Juyowa tayi ta kalli Mama ba tareda ta amsa mata ba.
"Ba za ki je ki gaida Baban naki ba. Sau biyu yana aikowa wai kije"
"Mama zan je gobe, na gaji"
"Ba abinda kika yi tunda kika zo gidan nan sai kuka. An gaya miki kuka na maganin matsala ne. Tashi maza ki shirya ki je ki gaishe shi kafin Magariba ta ƙariso"
"Mama ba zan iya fita yanzu ba. Dan Allah ki bari sai gobe"
"To ki kirashi ki gaya masa zaki je goben"
Hannu data ɗaga zata jawo jakarta sai data rintse ido saboda yadda zuciyarta ke sukan ƙirjinta. Missed calls ta gani dayawa a wayar wanda na Ubayd ne yafi yawa. Tun isowarta ta turawa Umma text ta sa wayar a silent ta jefata cikin jaka.
Numbar Ale ta kira taji shi a kashe, hakan ya mata daidai dan ba son magana da shi take ba.
"Numbarsa a kashe take" ta faɗa da muryar da yafi kama da raɗa.
"Ki tashi kiyi wanka kizo ki ci abinci. Haka kawai ki hana kanki sakewa saboda a kanki aka fara yaɗa jita-jita"
"Tashi maza kin ji. Barin cewa Ladi ta ɗeba miki ruwan zafi"
"Toh"
***
"Sumayye, Sumayye"
"Na'am Baba"
"Uban me kike a ɗakin ne. Ki fito mu tafi ko na barki a nan"
"Gani zuwa Baba"
Minti ɗaya sai ga Sumayya ta fito daga ɗaki sanye da hijabi ruwan toka wanda saboda akwai duhu zaka ɗauka baƙi ne. Babu wuta shiyasa gidan ya ɗau duhu, wata da taurari kuma a daren kaman sunyi ƙaura.
Wayar latsawa ce a hannunsa amma yana dannata da ƙarfi kaman wanda idan bai yi hakan ba ba za tayi aiki ba.
"Baba gani"
Ya ɗan yi murmushi saboda bazawararsa da suke chatting tace tana jiransa ya zo ya ga kwalliya.
"Baba gani fa"
"To fasa mun kunne Sumayye."
Sumayya ta fara tura baki wanda ba dan dare bane kuma hankalin Ale na kan bazawararsa da ya gani.
"Kin ɗauko kazar?"
"Na ɗauka"
Ficewa sukayi daga gidan dan yana sauri daga wajen Asiya zai wuce wajen masoyiyarsa Lubabatu.
Cikin motarsa ƙirar peugeot 406 fara wacce aƙalla ta bawa shekaru shatakwas baya ya ɗau Sumayya suka wuce gidan Gwani wanda yanzu ƙannensa da iyalensu ke zaune a ciki.
Masallaci ya fara tsayawa ya gaisa da Baffa Malam wanda ke koyarda ɗalibai karatu sannan ya wuce cikin gida ɗakin Mama.
"Gashinan Anty Asiya Ale yace a kawo miki Kaza. Ni na soyata da kaina"
"Ki ajiyeta Summy ba zan iya ci ba"
"Dan Allah ki tashi ki ci"
"Salamu Alaikum"
"Amin Alaikas Salam. Bismillah"
"Ina wuninku dai"
"Lafiya, Sannu da zuwa Ale Faruƙ"
Mama ta miƙe daga kujera ta koma bakin gado gefen Sumayya.
Bayan sun gaisa da Mama sannan ya maida dubansa ga Asiya ya tambayeta ya hanya.
Daga inda Asiya ke kwance ta amsa masa da lafiya.
"Mama bata da lafiya ne? Ko za a kira Malam ya mata rubutu ko Asibiti zamu wuce?" yai maganar ba tareda ya tsaya ya ja numfashi ba.
"Taƙi cin abinci ne fa tunda ta iso"
"Wai haka Asiyata? Ke Sumayye baki bata kazarta bane?"
"Baba gashi nan ita tace ba zata ci yanzu ba"
"Ki daure dai ki ci kinji Asiya"
Kaman gaisuwar ce kawai ta kawoshi sai kuma bayan shirun minti biyu ya fitar da abinda ke ransa.
"Ke Sumayye ki bamu waje"
Bayan Sumayya ta fita daga ɗakin, Mama ta fara ƙoƙarin miƙewa Ale yace ta zauna.
"Asiyata ya jikin dai" bai jira amsarta ba ya cigaba.
"Wai asalin kuɗin da akace 'yan adawan sun baki nawa ne? Tun da safe Malam Yusha'u da Alhaji Ɗansabo suke musu akan kuɗin nan, ni dai nace duk kuɗin Umaru Kwom ai ba zai baki ƙasa da Miliyan biyar ba ko?"
Kaman wanda aka tsikara haka Asiya ta miƙe zaune tana yiwa mahaifinta kallon ƙurilla kamar yau ta fara ganinsa.
"Ba sai kowa ya san asalin kuɗin ba Asiya. Kinga bikin ki ya kusa idan kika bani miliyan biyu ko uku a ciki zan juya miki shi kafin lokacin biki"
Magana take son yi amma kukane ya ƙwace mata. Abin nata ya kai har mahaifinta ya tsaya musu da wasu akan kuɗin da ba ta san da su ba. Ba ma wannan ba, ashe har sunanta ya ɓaci a garin da take iƙirarin cewa nan ne asalinta.
"Lah! Daga tambaya sai kuka. To kiyi haƙuri"
"Ale Faruƙ inaga dai gara ka barta ta huta zuwa gobe sai kuyi maganar"
Bai musawa Mama ba ya miƙe ya musu sai da safe ya fice daga ɗakin. Sumayya dake zaune a balbalin Baaba Ladi matar Baffa Malam tana ganin Ale ya fito daga ɗakin Mama tayi saurin miƙewa ta wuce ɗakin da sauri.
Lokacin da ta shiga ɗakin kuka ta samu Asiya ke yi. Tayi saurin ƙarisawa wajenta ta shiga jijjigata tana bata haƙuri.
***
"Shi Malam Nuhu mijin uwarta ne, shi kuma Ale Faruƙ Uban daya haifeta kenan. Inaga dai chan garin nasu kawai zamu je saboda ayi komai daga tushe"
"Kana jina kuwa Saifu?"
"Baba, Bilkisu..." Gwamna ya faɗa cikeda damuwa
"Idan ta dawo ka turo min ita, za muyi magana"
Daga haka bai sake cewa komai ba. Shima Gwamnan ajiyar zuciya ya sauke ya cigaba da taraddadin abinda zai faru idan Bilkisu ta dawo taji maganar auren daya ke shirin yi...
A daren ranan Gwamna ya wuce gidan Abba. Tunda ya fara yiwa Abba bayani Abban bai ce uffan ba, kansa na ƙasa ya kasa ɗaga ido ya kalli Gwamna. Magana ne yayi a taƙaice amma nauyinta zai iya kaiwa nauyin treloli goma.
Ba wai bai yarda da maganar Gwamna bane daya ce zai auri Asiya ne saboda ya kare rayuwarta. Girmansa ya wuce ya zo har gida ya masa ƙarya. Gaskiyarsa ya faɗa sai dai gaskiyar nauyi gareta. Idan har zai yi tunanin cewa auren Asiya shi zai sama mata lafiya to kuwa tabbas abinda ke bibiyan Asiya abune mai girma.
Asiya 'yarsa ce kuma lafiyarta shine abu na farko da zai fara dubawa sama da komai. Ƙila ƙaddarar Asiya kenan, ƙila tsakaninta da Ubaydullahi sai dai alaƙar Ya da ƙanwa.
Ya kai minti biyu bai iya cewa komai ba. Ya sani, indai su Alhaji Sani Kachallah suka je gaban Ale Faruƙ gobe to an riga an gama dan maganar aurenta da Ubayd ta tashi kenan. Ya ji daɗi da Gwamna ya girmama shi bai manta cewa Ubaydullahi shine saurayin da zai auri Asiya ba.
"Ba a kai sadaki ba. Mun tambaya ne kuma an bamu kuma har an saka lokaci. Shi Ubayd akwai kuɗin sadakinta daya ajiye a wajena zuwa idan lokaci ya ƙarato sai na baiwa magabatanta, amma tunda Allah ya rubuta ba matarsa bace zan maida masa kuɗin gobe da safe idan Allah ya kaimu"
"Malam Nuhu..."
"Your Excellency nagode daka karramani, ka bani girma har kazo da kanka ka sanar dani komai. Ina addu'ar Allah yasa wannan haɗi ya zamo alkhairi a rayuwar Asiya"
Gwamna ya so yai wata maganar amma bashi da bakin yi. Duk abinda zai faɗa ba zai chanja abinda Abba zaiyi tunani akansa ba.
***
Kwanaki biyar kenan da zuwan Asiya gida. Kwana biyun farko zazzaɓi mai zafi ya sata a gaba. A kwana na uku ne ta samu ta fara warwarewa saboda ta rage tunani da kuka. Umma ta kan turo mata saƙo na ƙarfafa gwiwa kullum sannan Mama ma kullum tana cikin yi mata nasiha akan haƙuri da kuma yarda da ƙaddara. A wannan lokaci ta so ace Gwani na da rai. Yadda duk lokacin data shiga damuwa yake karanto mata tarihin Nana Asiya dan ya nuna mata mai sunanta jaruma ce da bata taɓa karaya ba.
*"Kina tunanin Allah ba zai jarrabce ki bane?"*
Kalamansa kenan ranan da tazo ta sameshi tana kuka saboda Ale Faruƙ ya gaya mata cewa ya karɓi kuɗin aurenta a hannun Alhaji Talba. Tana shekaru shabiyar alokacin, Alhaji Talba kuma zai iya kaiwa shekaru hamsin da biyu zuwa da biyar. Da kuka wiwi ta iso zauren Gwani inda yake koyarda wasu manyan Almajirai dama wasu ɗalibai magidanta dake ɗaukan karatu a wajensa.
Bayan sun keɓe ta fara bayani
"Shi Baba komai kuɗi komai kuɗi. Ni gaskiya ba zan yarda ya sayar dani ba, ai bance masa aure nake so ba. Ni gaskiya karatu zan yi" tayi maganar cikin kuka.
"Ishiru Uwata, faɗa mini mi aka miki?"
Asiya ta goge hawaye ta zayyane masa duk abinda ya faru kan cewa Ale ne da safe ya gayawa Iyani da Fulani cewa su shirya karɓan baƙi gobe za a kawo kayan gaisuwar Asiya.
Ta haɗa da cewa " shi Baba rayuwarsa ta ƙare a kuɗi da mata. Abin kunya kwanakin baya daya saki Delu ina Bibalo ya auro. Bibalo fa, yarinyar da tun tana ƙarama take fama da taɓin hankali. Tsofai tsofai da shi ya ɓata mata rayuwa gashi Aljanunta sun hanata zama a gidansa"
Jin irin maganganun nan na fitowa daga bakin jikarsa zuciyarsa ta shiga ƙunci. Yai saurin karanto Isti'aza a zuciyarsa sannan ya riƙo hannun Asiya yace
*"Kina tunanin Allah ba zai jarrabce ki bane?"*
Tayi shiru tana kallonsa. Ya cigaba da yi mata nasiha tareda cewa ba abinda zata iya yiwa Ale sai dai ta rinƙa masa addu'ar Allah ya shirya shi, domin shi ɗin Uba ne gareta hakan kuma ba zai chanja ba har abada.
Bayan wannan abinda ya faru Gwani ya kira Ale Faruƙ ya masa faɗa yace bai hanashi aurar da 'yarsa ba idan ya ga hakane mafi alkhairi amma matuƙar yana raye ba zai taɓa bari ya mata auren dole ba kuma ko yayi bai yafe masa ba.
Saboda fasa auren da akayi Alhaji Talba ba ƙaramin rigima sukayi da Ale ba dan sai da suka yi kaca-kaca da shi.
Wannan dalilin ne kuma yasa Asiya ta dawo gidan Gwani da zama permanently har lokacin data samu admission a Congo University ta koma gidan Ummanta da zama.
Ale Faruƙ na kasuwa aka zo aka sameshi da zancen daya saka shi shiga mota ba takalmi dan har sai daya fita daga motar ya tunkari motocin Alhaji Sani Kachallah daya taka wani ƙaramin kara mai tsini ya lura cewa ashe babu takalmi a ƙafarsa. Wannan bai karya masa gwiwa ba yai saurin cire karan a ƙafarsa sannan ya ƙarisa motar daya ke tsakiya wacce yake tunanin a nan babban baƙonsa yake.
Samun buɗi ya sa Ale Faruƙ ya gyara ƙofar gidansa dama sashensa, wanda yanzu falo biyu gareshi ta farko ta karɓan baƙi ta biyu kuma wanda yake kallo ya ci abinci sannan anan yake zama da 'yan uwansa da abokansa na kusa lokaci zuwa lokaci.
Lokacin da Alhaji Sani ya fito daga mota har ƙasa Ale ya durƙusa yana kwasan gaisuwa fiskarsa washe kaman an masa albishir da Aljannah. Jiki na rawa ya masa jagora da tawagarsa ta mutum uku zuwa falonsa. Sai da suka zazzauna ya sake risinawa ya gaida su. Alhaji Sani da wani tsoho da yake tunanin zai kai shekaru casa'in sun girmeshi sosai amma sauran biyun ɗaga cikinsu zai kai sa'an Bellonsa sai ɗayan kuma dai zaiyi sa'an ƙaninsa Zakari.
Ƙokarin fita ya nemo musu ruwa yai amma Alhaji Sani ya dakatar da shi yace idan akwai wanda zai kira ya kira domin sun zo neman auren 'yarsa ce.
Ale Faruƙ ya ɗau waya ya fara kiran Baffa Malam yace ya zo maza-maza akwai manyan baƙi na jiransa. Bai san wacce cikin 'ya'yansa ake so ba amma cikin 'ya'yan dake gabansa mata da suka kai aure ba suyi aure ba, su biyar ne. Asiya data haura ishirin, Nafisatu da Ɗayyiba da suke shatakwas sai Sumayya data ke shabakwai sannan Baraka dake shashida. Koma waccece a cikinsu Alhaji Sani na nunawa to ya bashi ita ne kawai, babu mahalukin daya isa ya hana. Gwani ne ya isa ya dakatar da shi akan lamurran 'ya'yansa kuma Allah ya jiƙan rai ya jima acikin ƙasa.
Malam Audu maƙocin Ale ne ya fara isowa kafin Baffa Malam da Baffa Zakari wanda dama jiran baƙin suke dan tun jiya da dare Abba ya kira Baffa Malam ya sanar dashi abinda Gwamna yace da kuma matakin da shi ya ɗauka na janye neman da ɗansa ke yiwa Asiya. Baffa Malam da Baffa Zakari sun tattauna tsakaninsu kuma sun zuba ido ne tun jiyan suga yadda komai zai wakana tunda magana irin wannan Ale ne zai yanke hukunci ba su ba.
Minti bakwai da zuwan Malam Audu suma suka iso, dake kujerun sunyi kaɗan A ƙasa suka zauna tunda uban gayyarma a ƙasa suka sameshi. Duk da Alhaji Mustafah Kachallah Baffa a wajen Alhaji Sani ya nemi su Baffa Malam su zauna a kujera, Baffa Malam da Malam Audu ne kawai suka zauna a kujera.
"Na bayar" Ale Faruƙ ya faɗa tun kan Alhaji Mustafah ya ƙarisa bayaninsa.
"Idan hakane zamu ajiye sadakin yarinyar da kuɗin mun gani muna so idan yaso a hankali sai a kawo sauran abubuwan. Sannan kuma idan babu matsala muna so nan da sati biyu ko uku a ɗaura auren"
"Wallahi ko yanzun nan kuka ce a ɗaura mun shirya"
Baffa Malam ya bi Ale da ido. Kuɗi ai ba hauka bane. Tunda ya shigo falon ya lura da yadda Yayan nasa ke yi kaman wani wawa a gaban waɗannan mutane. Ya yarda suna da kuɗi sunada matsayi, suna da daraja a idon al'umma. Amma ba wannan bane zai sa kuma su basu wuƙa da nama a lamarin auren 'yar su. Sunada 'yanci ai. Ya dai yi shiru ne kawai saboda sanin halin Yayansa da yai, abune mai sauƙi a wajensa idan yai magana ya fara masa gori cewa ai shine Uban Asiya.
Miliyan ɗaya cash aka ajiye musu. Sadaki dubu ɗari biyar sauran dubu ɗari biyar kuma kuɗin na gani ina so kamar yadda suka faɗa.
Su Baffa Malam ne suka raka baƙin waje yayinda Ale ya shige ƙuryar ɗakinsa yana neman wajen yiwa kuɗin mafaka.
Sanda ya fito zai bisu ya ci karo da kayan da aka jibge a ƙofar falon, tarkacen kayan gaisuwane su buhun gishiri, buhun suga, kwalin sabulai, kwalin minti da cingam, damin goro kusan kashi goma da kuma ƙwaryan Zuma guda uku.
Ya haɗiyi yawu ya yi waje da sauri lokacin har motocin baƙin sun riga sun juya...
***
"Ba zaku maidani mahaukaciya ba Baffa. Ta ina za'a karɓi kuɗin aurena bayan akwai maganar aurena da Ya Ubayd. Baffa kaima ka koma son abin duniya ne kaman Baba?"
"Zauna Asiya"
"Noo Baffa. Ka gayamin gaskiya, kuɗi da mulki sun fara tsole muku ido kuma?"
"Ki zauna aka ce miki ko" Baffa Zakari ya daka mata tsawa.
"Wannan abin yafi ƙarfinmu. Amma duk abinda kika gani ya faru da bawa to rubutacce ne daga Allah. Ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddara. Insha Allah zamu cigaba da yi miki addu'a Allah ya tabbatar da alkhairi a rayuwarki"
"Shikenan dan kunga Gwani baya raye sai ku yanke hukunci bisa son zuciya. Baffa wannan son zuciya ne, da ku da Baba duk dukiya ce ta tsole muku ido. Ba zan auri kowa ba sai Ya Ubayd"
Daga haka ta bar musu ɗakin da gudu.
Ranan ƙarfe bakwai na yamma a gidan Abba ya mata. Tayi ta kiran nambobin Ubayd amma duka a kashe su ke. Hankalinta ba zai iya ɗaukan wannan abin ba. Ta yarda da ƙaddarar data faɗa mata na abubuwan da suka faru da ita cikin kwanakin nan. Yanzu ma maganarta ya ja baya a duniyar yanar gizo an koma gulmar wani ɗan film da aka ce yana luwaɗi.
Umma ma kamar kowacce Uwa ta damu da halin da 'yarta ta shiga musamman data ganta a fige kamar kazar sadaka.
Ta yi iya baƙin ƙoƙarinta wajen nuna mata cewa hukuncin da aka yanke mata ana mata zaton alkhairi ne ba sharri ba.
" Addu'a shine abinda ya rage miki yanzu Asiya ba kuka ba"
Maganar Mama kenan lokacin da ta riƙe mata ƙafa tana kuka akan ta tayata roƙon Baba da Baffaninta.
Itama Umman sunan addu'a take kira mata. Addu'a, Addu'a, Addu'a. Ta fa gaji da jin wannan suna.
Lokacin da tace zata fita, Umma cewa tayi sai dai dole su tafi da Gwani ko Aliyu. Dake Aliyun ne ke kusa shine ya rakata gidan su Umma Hussaina.
Rabonta da gidan ma zai iya kaiwa shekara.
Ta tsammanci samun Ubayd a gidan amma aka ce mata yayi tafiya.
Ta jima tana zaune a ɗakin Umma Hussainan kafin daga baya ta haƙura ta miƙe ta tafi ko sallama bata yiwa Umma Hussaina ba.
Damuwa kan chanja tunanin mutum matuƙa. Wasu lokutan Asiya sai ta shirya zata gudu sai ta fasa, wani lokaci kuma tayi tunanin ta kashe kanta ma kawai ta huta. A wasu lokutan kuma tayi tunanin samun bindiga ta je ofishin Gwamna ta bindige shege kowa ma ya huta. Wani lokacin kuma tayi tunanin ta haukace kawai saboda a dakatar da komai. Wasu lokutan ma zuciyarta na riya mata cewa ƙila ba Ale Faruƙ bane ubanta. Abin da ya fi riƙe mata rai ma bai fi yadda Ubayd ya ɓace mata ba, ga numbarsa da har yanzu bata shiga.
Ta fara tunanin ƙila Gwamna ne ya sa aka ɗauke shi, an ƙi faɗa mata ne kawai.
Sati ɗaya tayi a gidan bata san inda kanta yake ba. Abba da Umma kullum suna nuna mata ta saki ranta komai zai zo ya wuce amma zuciyarta bai shirya ma yarda da zancensu ba balle har ya amince da shi. Ubaydullah shine masoyinta na farko kuma na ƙarshe, ita tunda ta taso ma bata taɓa son wani ba, ko crush na primary ko secondary school bata taɓa ba. Ubayd ta fara so tun lokacin da ya ɗauka mata tsumman abunta, tun lokacin bata san so ba.
Saboda Ubayd bata taɓa bawa wani damar shiga rayuwarta ba. Ko lokacin da take Jami'a da tayi tashe, samari ke mata chaa babu wanda ta taɓa buɗewa ƙofa. It has always being Ubayd and will always be.
Yayinda Asiya ke fama da damuwa, a chan gida kuwa Ale Faruƙ ya kasa ya tsare wajen ganin wannan biki ya tafi yadda ya kamata. Sati ukun nan gani yake kaman ba za su iso ba. Tun yanzu ya fara kiran kansa sirikin Gwamna har tambayar siriki yai da turanci aka ce masa Inlaw amma idan shi ya faɗa sai kaji kamar 'yanlo yace.
Yi masa kirari da sirikin Gwamna kaga ya ɗau kyautan dubu ya baka mutumin da ɗarinsa idan ba a mace ba baya iya bayarwa.
Tuni yasa aka yiwa gidansa sabon fenti. Matansa da sauran yaransa duk ya musu ɗinkin biki kala biyar biyar hatta yayyen Asiya da ke gidajen mazajensu ya aika musu da nasu kayan. Wannan kashe kuɗi ko a sallah albarka. Shi dai yanada abu ɗaya gidansa ana cima mai kyau amma wani siyan kayan sawa ko na ado to ko a sallah sai anyi da gaske, yawanci ma iyayen 'ya'yan ke musu. Haka batun makarantar boko idan ka wuce sakandare sai fa ka tallafawa kanka. Mace ɗaya ce tayi karatu a 'ya'yansa mata bayan Asiya, itama kuma a gidan mijinta tayi. Adda Hadiza kenan da ta karanci ɓangaren midwifery.
***
"It was for political reasons Bilkisu"
"Shine sai dai naji a bakin Babana"
"Sanda kika dawo bana gari kuma wannan magana bata waya bace"
"Saifuddeen ka rasa wacce zaka aura sai 'yar Kurma jikar maiƙusumbi" ta tintsire da dariya. "I'm sure ba wai zaka nemi haihuwa da ita bane ko? dan ba zan juri ganin 'ya'yan guragu, kutare da makafi a gidan nan ba"
Gwamna yai seƙeƙe yana kallonta. Ita ce dai da take zuwa gidan marayu tana ɗaukan hotuna da naƙasassun yara.
"Na ɗauka baka ƙyamar nakasassu Bilkisu"
"Oh please Saifuddeen. Ka sani sarai campaign nake yi"
Ido ya zuba mata ya rasa ma mi zai ce. She never seizes to amaze him.
"And Darling, ka sani zan haƙura ne kawai saboda lokacin campaign ya kusa, bana son abinda zai ɓata maka ƙuri'u. Abu na ƙarshe kuma shine ka nema mata wani gidan dan a nan" ta juya yatsarta manuniya "ni kaɗaice Matar Gwamna"...
Post a Comment for "THE GOVERNOR'S WIFE 12"