ZAN FASA KWAI 40
.....Alh uba Dan yaro yazo har gida ya samu eng AK Akan Dan wurin shi badamasi yaga yarshi Yana so har ma suna rokon iri don hada ZURIA
Eng yayi shiru don har ga Allah baya son yiwa ummita auren da ba itace ta kawo Wanda take so ba Kuma hasalima Yana da tarihin Rayuwar badamasi da yadda yake son sheke Aya da Matan bariki shi da kanshi ba zai yarda da auren badamasi ba don haka Bai boyewa Alh uba Dan yaro ba.
"To alh na gode da kauna don me son hada ZURIA da Kai ya gama maka Dukkan kauna sai dai gaskiya alh bana son matsa Mata akan aure don yaran yanzu kana so ina so ma ya aka Kare bare anyi basa so?
"Zan sanar da ita zancen badamasi ka Kuma turoshi yau ko gobe don su gana idan yayi Mata shikenan idan kuwa baiyi Mata alh sai yaro yayi hakuri......
"Kar ka damu abdulkarim koni ba zanso kayiwa yarka Dole a aure ba don wannan zamanin ba irin Wanda ake Dole a zauna lafiya bane Ina fatan alkhairi agaresu idan Kuma baiyi Mata ba sai ya nema agaba da haka sukayi sallama inda ya dire mishi kudi masu kauri akan Wai ya bawa Yar shi ta siyi kayan kwalliya sukayi sallama ya tafi
Bai boyewa lubabatu ba dake ta Shan sharafinta da daukewa ak Kai ya zayyane Mata yadda sukayi da alh uba Dan yaro Amma ke da ke can in kin tanka ta tanka mishi don tana ganin awannan halin za ayiwa ummita aure cikin halin Babu?
Bai bi ta kanta ba ya kira ummita dakin shi ya sanar da ita abinda ke faruwa na game da badamasi da ubanshi ya Zo neman aurenta ya Kuma nemi Jin Ra ayin ta
Ta sunkuyar da kanta kasa tanajin kunya tana Kuma nazari...............
"Kar ki kwari kanki ummita ba Zan taba yi Miki AUREN Dole ba Wanda kike so shi Zan Baki don haka idan kinji ranki Bai dauka ba Babu kunya tsakanina dake Zan Baki damar ki.
"Abba na baka zabi wallahi zanyi maka biyayya muddin ka hango cancanta da dacewa akan shi zanyi maraba in Kuma roki Allah ya zaba min abinda yafi ALHERI
Ya sauke ajiyar zuciya Yana godewa Allah da ya bashi ya me biyayya
"Allah yayi Miki albarka ummita na gode da karrama Ni da kikayi Amma ki Bari zuwa yau ko gobe badamasi zaizo ku gana yadda Kika ganshi ko kikaji shi aranki kar ki boye min ta haka ne Zan yanke hukunci na adalci amatsayina na mahaifin ki
Ta amsa ta fito
Washe gari kuwa sai ga badamasi ya iso cikin shiga ta Alfarma da son ya siyo zuciyar ummita Amma Rashin sa ar da yayi kallo daya tayi mishi taji yayi Mata Kama da Yan duniya ita Kam Bata muradin auren irin su don wayewar su tayi yawa
Sukayi fira ta Yan Mintoci duk yadda yaso ya yaudari zuciyar ta hakan Bata yuwu ba haka sukayi sallama Yana Bata kudi Amma Taki karba tayi godiya inda yake Jin lallai irinta yake so wace macece ke kin kudi a wannan duniyar? Sai yaji ta Kara burgeshi da haka ya taho Yana santin aurenta
"Yaya Kika ga badamasi ummita? Shin yayi miki Koko akwai matsala? Tayi shiru kafin ta dubi abban nata
"Kayi hakuri Abba ka gafarce Ni gaskiya Bai yi min ba wayewar shi tayi min yawa............
"Nima da kin zabi badamasi ummita to da Zan fada Miki aibin auren shi don Nima tarbiyar shi batayi min ba Amma tunda Ra ayin mu yazo Daya shikenan sai abashi hakuri dama ban rufeshi ba ke Kuma Ubangiji ya Baki miji na gari ta amsa ta fito
Haka kuwa akayi ya iske alh uba Dan yaro ya sanar dashi yadda sukayi da yarinya ya Basu hakuri ya dawo gida
Kwana biyu Wilson na kwance Babu lafiya abinda ya tabbatar ciwon son ummita ne ya kayar dashi inda ya hadiyi magani da allurai Amma duk abanza Babu wani sauki sai radadin zuciya
Tamkar Wanda ya amsa umarni ya zaro key din mota ya fice zuwa kuki inda yayi nasarar ganin shigarta ya zauna zaman jiran fitowar ta
Sai yamma ta fito inda ya shigo mota ya karaso inda take tafe akasa ya danno Mata horn
Ta juyo Inda idonta ya hasko Mata shi sai tayi maza ta daure fuska yayin da shi Kuma yajefota da wani murmushi ya fito Yana fadin
"Kice yau da kafar dama Kika fito gashi mun hade don hanyar gidan naku zanbi
Ta sassauta fuskar ta
"Ayya yau Kuma inajin Kaine baka fito da kafar damar ba don yau ba inda kasani zani ba.........
"Sa ar takice take da yawa har nayi nufin kaiki duk inda zakije
Ta dubeshi
"Na taba fada maka duhu da haske basa tarayya a wuri Daya me kake nufi da SHIGA cikin Rayuwata?
Ya shafi sumar kanshi Yana murmushi
"Nagode da wannan damar da Kika bani manufata itace muyi musayar zuciya.......
"A hakan zamuyi musayar zuciya kana a duhu?
"Kasancewar mu mutane jinsi Daya shine kawai alakar mu ta kasanwa mutane Amma akwai banbanci me yawa tamkar nisan sama da kasa don haka kar ka Kuma bibiyata don abinda kazo dashi Kai da kanka kasan ba Mai yuwa bane na gode da taimakon da kataba yi min sai anjima
Ta wuce ta barshi inda yake biye da ita Yana nacin ta shigo motar shi ya kaita gida Amma Bata saurare shi ba haka shima Bai fasa binta ba har ta karaso gida shi Kuma yayi zaman awa kusan biyar Yana son ganin fitowar ta Amma shiru har dai ya gaji ya dawo gida sai dai me?
Yayiwa ummita tsaye arai bacci ma da ta kwanta mafarkin shi tayi tayi da ta farka ma Babu abinda take bege face ta saka idonta cikin nashi inda Kuma kwana biyu shi Kuma baije kuki ba ta damu matuka gaya har ta soma zubar hawaye ta dafe gurbin zuciyar ta
"Kar ki yaudare Ni Mana zuciya? Ta Yaya Zaki sakani son abinda Bai dace Dani ba? Ko kusa haka Kuma ko alama ita kanta lamarin Bai burgeta ba to bare Kuma iyayenta suji Dole ta watsar da wannan gurbatacciyar dake nuna Mata mafarkin ido biyu ......................
Post a Comment for "ZAN FASA KWAI 40"