ZAN FASA KWAI 39
......."A a dady wallahi bana son sa don ya gama saka min kiyayyar sa idan kuma kace Dole sai na aure shi to wallahi Zan bar gida ne kawai in SHIGA duniya........
"A a ba za ayi hakan ba cewar izzatu tunda dai Baki so an Bari.
"To hakan dai yafi momy....
Ta fada tana hayewa saman bene
inda Kuma Kabir yace
"Ba fa Zan janye hadata aure da Anwar ba don auren su shine tabbata ta Akan aikina don auren ta zai zamo min tsani..........
"Nima ba zanso fasuwar auren ba Kabir na dai fada ne don kar ta gudu Amma ai gata can gidan Anwar din da haka suke rufe zancen
Koda Anwar ya koma gida Mr President ya tambayeshi "ya ka ganta ne Anwar? Ya shafa sumar kanshi
'dady batayi min ba wallahi Bata da tarbiya.........
"In Dan tarbiya ai me sauki ne Anwar sai ka dorata Kan irin taka tarbiyar munyi magana ne tuni da ubanta Kai ai Dan gata ne Mata biyu lokaci Daya? Tashi kaje zamuyi magana dashi Kabir din Kai dai ka zamo me adalci agare su Allah yayi jagora
Ya tashi ya fito yanajin shi Kam baiyi sa ar aure ba don kaf Matan da ake Shirin bashi Babu wacce yake so Amma yanajin zaiyi biyayya tunda duka iyayen shi ALHERI suke nufin shi dashi don haka ya zari key din mota ya fice wurin abokin shi badamasi Wanda ya zamo Dan gidan Alh uba Dan yaro don ya sanar dashi irin auren da ake Shirin yi mishi
Yana tafe kamar Wanda akacewa kalli can sai kawai idon shi ya hango mishi ummita wadda ke tafiya akasa zuwa kuki
Gabanshi ya amsa inda ya kusa buga motar Amma Allah ya tsare ya dawo Kan doka da oda inda Kuma ya nemeta sama ko kasa ya rasa
Haka ya Isa gidan su badamasi ya sameshi suka kashe inda badamasin ke fada mishi yanzu yake Shirin zuwa ya Kai mishi albishir din ya samo mata..........
"Kai Amma nayi maka murna don gara kayi aure da dai barikin da kake Kai ba mutumin banza ba Amma ka biyewa Matan banza nima dama nazo ne in fada maka yadda ake Shirin aura min Mata biyu Kuma duk cikin su Babu wadda nace inaso daya daga haj daya daga dady Amma yanzu tahowar Nan da nayi Allah da ikon shi nayi tsuntuwar soyayya Amma Wai kafin na kyafta ido har ta bace wa ganina Amma nayi alkawarin duk duniyar da tashiga sai na nemota nayi ta uku da ita.........
Badamasi ya kyalkyale da dariya
"Kai Amma wallahi su Dad sunyi min daidai Mata biyu lokaci Daya in ba irinku Yan gata ba
Ya Mike da Shirin tafiya
"Na lura ban baka tausayi ba badamasi Bari kawai in wuce tun baka sa zuciya ta bugawa ba..........
"A a malam Bari nazo na nuna maka yarinyar da nake fada maka na samu don ka ganta sai dai fa ban taba yi Mata magana ba saboda kwarjini da tayi min na dai binciko ance min Yar gidan eng AK ce na Kuma San baba ya sanshi shine kawai na fada mishi ina sonta yace in Bari zaiyi mishi magana Amma har yanzu na kasa yi Mata magana sai dai kawai na Zo inda Zan hango ta na kalleta na more.......
"Amma dai ka kusa bada maza badamasi duk barikin ka ace tsoron mace kake?
Ko dayake wata Kil kamila ce shiyasa kake shayinta kaga banbancin matar kwarai da ta banza inda abariki ne Babu wani kwarjinin da Matan bariki kewa Yan bariki tara ce ke dukan goma...........
'ban Yi maka gardama ba abokina muje in nuna maka ita...
Haka suka fito har zuwa kuki cafee inda Kuma cikin sa a ta fito ta soma takawa domin komawa gida inda Kuma agefe guda Wilson shima yake lafe yana Kare Mata kallo inda Kuma gaban Anwar ya buga da karfi yarinyar da ta saci zuciyar shi itace masoyiyar badamasi?
Lallai akwai hayaniya a gaba duk surutun da badamasi keyi domin Koda ummita Anwar baya cikin hayyacin shi da haka sukayi sallama ya taho Kai tsaye ya tunkari Mr President cewar yanzu ne ya samu matar aure idan zasu yarda ya auri Mata uku to ahada mishi da ita idan kuwa ba zasu yarda ba to abar auren duka
Mr President yayi murmushi
"Yar gidan waye ita wannan din ?
Yar gidan eng AK ce ya bashi amsa
"To kaje zanyi mishi magana ko ta hudu ka Kara hangowa kayi magana Zan cike maka su hudu dai dai ai Kai din Dan gata ne,
Anwar ya tashi Yana murmushi yayiwa Mr President sallama ya wuce abinshi..................
Post a Comment for "ZAN FASA KWAI 39"