Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

ZAN FASA KWAI 38

.......Anwar ya fito sukayi kicibus da mahaifin shi ya zube Yana rattaba mishi abinda hajiya sabuwa ta fada mishi akan Wai ta yi mishi Mata da kudusiyya wadda shi atsarin shi kudusiyya batayi mishi ba. Mr President yayi murmushi


"In Banda abinka Anwar meye na damuwa don ta zabo maka matar girma ? Nima fa nayi nufin Yi maka gata kanaji? 

"Eh inaji dady.

Yauwa ai kasan gidan Alh Kabir mashi ko? Eh gaskiya kamar na sani Amma dai akwatanta min . Yayi mishi kwatance ya Kuma Gane inda ya bashi rafar dubu hamsin hamsin guda biyu ta dubu dari yace idan sun gama magana ya bada amatsayin kyauta

Ya dubi uban cikin Rashin Gane abinda yake nufi har dai ya tambaya


"Dady wa za a ba wannan kudin shi alh Kabir mashi din?


"A a kaje Zan kirashi zamuyi magana bashi zaka bawa ba ita wadda zaku yi maganar da ita zaka bawa amatsayin kyautar ka.

Ba don ya Gane ba ya taho don har ga Allah shi Bai kawo komai aranshi ba yayi nasarar Gane gidan ya Kuma tura me gadin yayi mishi sallama da alh Kabir 

Atare suka iso inda Kabir kewa Anwar sannu da zuwa ya sauke shi a wurin da yake karbar Baki suka gaisa inda Anwar din yake sanar dashi dady ne ya turo shi


"Eh ai ya kirani bayan ka taho Bari in turo maka ita. Ya Mike ya bar Anwar sake da Baki Yana maimaita kalmar Bari  in turo maka ita, to itawa za a turo mishi? Sai ya zuba ido kowacece itan


Fulani na zaune cikin ado da kwalliya tamkar me shiri fita party ta zubawa TV ido tana kallon India Wanda take son sanar da dadyn ta tana izuwa  India don garin na burgeta sai Kuma gashi ya shigo Yana kiranta 


Ta dago da sauri "gani dady

Yauwa dama bakone gareki Yana can masaukin Baki kije ku gaisa..........

"Bako Kuma dady? Ni yace maka yake nema?

Gaskiya dady bani yake nema ba sai dai in wrong address ya samu don Ni ban ba kowa address Dina ba.......


"Eh shi wannan din ma ba cewa ke Kika bashi ba Ni nace mishi yazo ku daidaita ke dai jeki idan kin dawo zamuyi magana.

Ta motse fuska don Sam acewar ta Bata ga mijin Aure a yanzu ba sai gashi Kuma ana son shigs Rayuwar ta


Tasa me aikin su talatu ta biyota da ruwa da lemu inda ta yi gaba don zuwa duba wannan marar kunyar da aka jajubo Mata


Ta taho tamkar tana Jin tausayin kasar fuskar ta murtuk Wai don kar yaga hakoranta  ta shigo Babu ko sallama inda idanun su suka hadu su duka tamkar wuta taja su suka ji bugun zuciya Atare inda ta zauna tana auno mishi harara tamkar idanunta zasu fado inda talatun ta shigo dauke da tire Wanda ta jero ruwa da lemu tana Shirin ajewa humaira ta doko Mata tsawa.....


"Koma da ruwan Nan talatu wannan ba bako bane abokin Adawa ne.....


Talatu tayi dabar dabar don Bata fahimta ba inda kuma humaira ta Kuma daka Mata tsawar

"Nace ki koma dashi ko bakiji ba?

Da sauri talatu ta dauki tiren ta koma ciki inda ta fusknce shi shima Yana mamaki abinda suke nufi da turoshi inda atake ya gano gatan da dadyn yace yayi nufin yi mishi har yayi murmushi don yasan ba zasu taba daidaita wa da wannan marar mutuncin ba


Murmushin shi ya Bata haushi. "Au harma na Zama abin dariya agareka ?

"Uban me kazo yi agidan mu? Ko Nan ma kazo ne don ka sake bawa Yan sanda damar su kulle Ni ? Ta fada tana Kada kafa alamar masifa na Shirin tashi


Ya Kuma yin murmushi Wanda ke kuleta da haushi da takaici

"Kiyi hakuri Ranki ya dade............  

"Kai bari fa in gaya maka dama inajiran Allah yasake hadamu don in Rama abinda kayi min

To Ni nan da kake gani wallahi uban kuturu ma ya Yi kadan bare na makaho da ba gani yake ba duk uban da ya daure maka.....


Ya gaji da Jin zagin da take mishi don Babu abinda ya tsana a Rayuwar shi irin zagi don haka ya cire hannu ya tsinke ta da Mari Marin da sai da taga giccin koriyar wuta


"Nafi karfin zagi agareki ko Zan zagu ba dai ga irin ki ba jahila marar tsinkaye  wallahi ba Irina Mata ke zagi ba nafi zagi ga irinki dabba dake Kuma in har kece ake Shirin abinda aka shirya zanyi maraba da hakan ko don in koya Miki tarbiyar da uwarki Bata koya Miki ba 

Ya Mike afusace ya watso Mata kudin da dadyn ya bashi ya Bata 

"Gasu Nan ki kaiwa Kabir mashi don saboda su yayi tallar ki inda ya San zai samesu Ashe ke da uban naki duk nema kuke akarkashi na to ku biyo Ni Zan baku na cin abinci


Tana dafe da inda ya zabga Mata Mari har ya fice ta kasa cewa komai Akan cin fuskar da yayi mata

Me yake sanar da ita? Da gaskene tallarta dadyn yayi? Eh ai in Bata manta ba dadyn ya fada Mata shi ya turo shi don haka ta tabbata sai dai tanajin ba abune me yuwa ba matukar Kuma akace hakan sai ya yuwu to za ahaife da marar ido


Ta kwashe kudin ta nufi cikin gidan inda take ganin karfin halin shi na zuwa har cikin gidan su ya zabga Mata Mari


Kabir ya tareta

"Yaya Yar dady Yaya Kika ganshi ? Yayi Miki? 

"Wai dady baka San shine yayi min wulakanci har sau uku ba?

"To dady bana son shi don  fansa ma Zan dauka akanshi ba Kuma Zan kyale ba don bashi da mutunci to nima Zan gwada mishi bani da mutunci.....


"A a karkiyi haka Anwar Yana da kirki Baki fahimce shi bane don haka dama fada Miki ne bamuyi Anwar shine mijin da aka tsayar Miki Nan da lokaci kadan za ayi biki.....................

Post a Comment for "ZAN FASA KWAI 38"