ZAN FASA KWAI 37
*ZAN FASA KWAI*
...........Arude yake kallon malam Ali Jin yace Wai Babar tashi ta bace an nemeta sama da kasa Babu ita Babu labarin ta.............
"Malam Ali ba asan inda take ba kenan?
"Abinda yake daurewa mutane Kai kenan don faruwar lamarin tamkar kiftawar ido Wai an nemi dungo Babu ita Babu dalilin ta
"Shin wani ne ya sace ta Koko guduwa tayi???..........
"Allah shine mafi sani abinda kawai na kawowa Raina shine dungo tana ganin Bata da kowa sai kanta idan ta faku idanun Al umma batayi laifi ba shiyasa don nafi zargin guduwa tayi don bakin ciki Babu abinda baya sawa...........
"Bakin cikin me malam Ali?........
"Bakin cikin ka kabiru me yuwa dungo tana kallon kanta a wadda batayi SA AR haihuwa ba don ban taba ganin Dan halak yayi irin abinda kayiwa mahaifiyar ka ba Kabir
Abu Daya Zan fada maka shine ka saurari zuwan musiba don kuwa kajawo Allah fada....
Arikice kabiru ya Mike Yana duban malam Ali da ya fada mishi gaskiya Amma ya kasa abinda zaiyi don ya yarda ya amince lallai ya jawo Allah fada
Malam Ali ya Mike Yana fadin
"Ni na koma sai Allah ya kaddaro saduwar mu idan kazo inda nake ma gaisa idan kuwa ta Kama mun hadu shima ma gaisa don ba Zan yaudari kaina cewa zaka zo gidana sada zumunci ba Toni a wa?
Da haka malam Ali ya fice ya bar Kabir da hada hudu da ukun da zasu bashi takwas
Izzatu da taji batun itama taji Babu Dadi Amma sai tace addua kawai zasuyi itace mafita
Yayinda humaira fulani taji ya kakar tata ta Bata kuka take tamkar dai izzatu ce ta Bata abinda ya Bata ran izzatu ta shiga zazzaga Mata masifa
Kwana biyu Kabir ya watsar da batun dungo inda yace duk ma inda ta SHIGA zata fito idan Kuma tayi haka ne don ta tada mishi hankali to ta tada mishi
Bai samu zarafin duba kunshin da takardar ba ya kwashe su ya watsa ciki kabit din ajiyar takardun shi
Kwana biyu ummita na zuwa kuki cafee kasa saboda Babu kudin da zatayi transport din zuwa gashi saura wata biyu ta Ida ta karbi sakamakon
Tana tafe anatse inda kamar daga sama Wilson ya hangota zata ketare titin da zai sadata da kuki cafee inda ya zuba Mata ido a yau ji yake tamkar idan baiyi Mata magana ba zaiyi Rashi na zuciyar shi sai dai kafin ya faka motar ya fito har ta shige
Ya kasa tsaye da zaune zuciyar shi na kawo mishi shawarwari akan kawai ya jira ta fito in yaso ko mayar da its gidane sai yayi Aiko ya dasa zaman jira har uku na maraice ta fito ta soma tafiya inda ya kula tamkar Bata da lafiya
Ta gota shi kadan ya ga ta dafe bishiya ta rike kanta Wanda alamu suka nuna ciwo yake Mata inda dabara ta fado mishi ya tashi motar ya karaso gareta Yana fitowa
Ya tunkaro ta ta zuba mishi ido kallo daya ta Gane shine Wanda ya tsura Mata idon Nan a country mall
Yayi Mata sallama cikin hausar shi da Bata fita Bata amsa ba ta dai dubeshi
"Sannu fa Naga kamar kina neman taimako na?......
Tayi saurin Kada mishi kanta
"No nagode zaka iya tafiya.
"Kiyi hakuri nasan inda zakije akwai nisa kizo na kaiki Naga kamar kina headache ne ......
"Nagode sosai Zan iya komawa ba damuwa...........
"Kiyi min alfarma ko ta kaiki gida ne tunda har Baki da lafiya..........
"Idan aka ganni a motarka nace me? "Ka ganka kuwa ? "Taimako wani abune da addinin mu ya koyar damu ga mabiyan sa shin kana daga mabiyan ne da zaka taimakeni?
"To duhu da haske basa tarayya a wuri Daya Dole daya ke bawa Daya wuri idan haske ya bayyana to duhu yayewa yake don haka na gode da taimakon ka gareni
"Na sani amma haka Nan naji Ina son taimakon ki tunda muma namu addinin ya koyar damu taimakon Kuma Bai saka kiyayya ga sauran addinan ba indai ba naku adfinin ya saka muku kiyayyar sauran addinan ba. Kiyi hakuri ki shigo na saukeki nayi Miki alkawarin Babu cuta tsakanin mu haka kawai nake son taimakon ki
Azahiri ita kanta tana bukatar taimakon don Jin kanta take tamkar zai tarwatse Dole ma ta nemi abinda zai kaita gida don Bata sababa ga kuma yunwa da takeji wadda idan akasa tace zata tafi to ko shakka Babu sai dai akwashe ta amika gidan don haka ta sallama ta shiga motar yaja suka iso gida ya sauketa ya Miko Mata fakitin maganin ciwon Kai me tsadar gaske ta karba tana godiya
Tun daga wannan Rana Bai Kara shiga cikin lamarin ta ba sai dai zai labe ya kalleta ya more ya koma gida inda kusan kullum sai yazo kuki internet cafee ya ganta batare da ya Bari ta ganshi ba
Hajiya sabuwa first lady matar Mr President take sanar da Mr President din maganar da ta taba fada mishi ta samowa Anwar auren diyar kawarta matar soja wato kudusiyya ta taso don haka atura mutane su nema mishi auren
Ya dubeta Yana murmushi
"Kice auren gata za ayiwa Anwar ba na fada Miki Yar gidan Kabir mashi Nima na nema mishi ba? Ta kwabe Baki da zaka yarda sai ince ka bar maganar Yar gidan Kabir mashi kudusiyya macece daya tamkar da goma.........
"Ba zanyi magana biyu ba tunda dai kema kin samo mishi wata sai ahada mishi biyu don haka itama Yar gidan Kabir mashi din sai muyi magana kawai
Wannan abin ya Bata ran haj sabuwa don tasan idan matar soja taji haka ba zata yarda ba Amma kome kenan zasu San yadda sukayi suka lalata Shirin Yar gidan Kabir din don kudusiyya kawai suke son tayi Rayuwa a gidan Anwar din baza ta tabs Zama da kishiya ba bare har ta Zama Bora
Sai dai da Anwar din ya shigo hajiya sabuwa ke mishi maganar kudusiyya da zaba mishi ita da tayi a matsayyin matar aure yayi saurin tareta.....
"Bana son ta hajiya ku barni na zabo matar da Nike so da kaina tunda Kuma zabar kanku kukayi ke da dady ba hada ku akayi ba.......
"Kayi karya ka bani kunya Wallahi Anwar Dole ne ka auri kudusiyya.....
'to shikenan haj duk abinda ya samu Yar mutane kar kiyi kuka da kowa......
Ya fice ya barta sake da Baki...............
Post a Comment for "ZAN FASA KWAI 37"