Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

ZAN FASA KWAI 36

 *ZAN FASA KWAI*


               *Page 36*

.......... Lubabatu tamkar wadda aka zuge dare Daya ta sauya sauyi kuwa me yawa abinda ya bawa AK mamaki Amma duk da haka yayi Mata uzuri don aganin shi Dole taji Babu Dadi musamman yadda ta Saba Rayuwa cikin iko da wadata yau Kuma lamarin sai sannu


Bata fito fili ta fada mishi ba Amma ya lura da ita da take taken ta

Amma duk da haka yayi Mata hanzari don abinda ya nuna mishi kamar tagaji shine kullum cikin bacin Rai take abu kadan Kuma sai ya fusata ta Koda ko ita da yarane sai kaji tana ta antaka musu zagi abinda ta San bayaso bare duka sai ya zamo yanzu duk ta hada tanayiwa yaran sai dai ya kalla ya kauda kanshi


Idan Kuma ta hadosu shi da ita zata rufe idonta ta gurza Rashin mutunci son ranta Amma duk da hakan baya biyewa don ya San mafarin lamarin har dai wata Rana ya zaunar da ita Yana mata nasiha


"Kiyi hakuri lubabatu komai Kika gani aduniya Yana da farko da Kuma karshe. Kar wannan canjin yasa kiji aranki ko Rahamar ta Kare ko babu sauran wani Jin Dadi Nan gaba . A a yanzu ne ma lamarin zai Fara duk bawan da Kika ga an jarrabeshi matukar ya cinye jarrabawar shi to matakin nasara ne ya hau . Hska Kuma Babu Wanda zaiyi hakuri Bai cimma rabar hakurin shi ba don haka don Allah da manzon sa kiyi hakuri babun da muke ciki in Sha Allah zamu samu kanmu cikin wadata wata Rana matukar dai munyi hakuri domin Allah. Na sani ba kowane zai jurewa Rashi ba to Amma ai bawan da yayi imani yasan Dole ajarabeshi sai mu godewa Allah da ya bamu wannan jarabtar me sauki kiyi hakuri ki Kuma jure ki koma hango baya yadda kika samu Kai sai ki godewa Allah shi Kuma sai ya dubeki ke da lamarin ki.


Ta matse hawaye ba tare da tankawa nasihar sa ba inda yaji tausayin ta ya Kara kamashi


Da hakan dai ake ta gurgurawa da Dadi ba Dadi kamar dai ta dauka ko ta hakura inda ake cikin Rufin Asirin Allah wani abun mamaki Kuma ba a Kara kiranshi Kan abinda ya shafi harkar kwangila ba shima kuma Bai nemi cusa kanshi ba ya tsaya matsayin shi Yana ta laluben hanyar da Asiri zai rufu inda Allah cikin ikon shi masu zanen taswirar gidaje Kan bashi aikin zanen kasancewar shi eng Wanda ya hada har da sanin makamar zanen inda Kuma kudi ke Dan shigowa Amma ba kamar yadda aka sababa 


Inda agefe Daya Kuma Kabir yayi wata irin shahara da tunbatsa akan harkar gwangila saboda ayanzu shine ke Kan kadamin shi aiki Kuma Babu nagarta haka za ayi shi agama kafin lokaci kadan ya lalace saboda an saka manuba da ha inci


Malam Ali yayi ta Kiran wayar shi Amma kememe yaki dagawa saboda ya San maganar dungo za ayi mishi inda a yau malam Ali ya bugo hanya ya iso garin Abuja duk da Bai San gidan Kabir din ba Amma akace matambayi baya Bata kasancewar shi shahararre Bai Sha wuya wurin gano gidan ba inda ya tsaya Yana karewa gidan kallo Wai gidan dan dungo ne wannan Amma ta Rayu a wani gida da bashi da maraba da kufai saboda ruwan damuna da ya kayar dashi Anna Bata samu arzikin tadawa ba Amma dubi gidan da yazo garin Abuja ya Gina tamkar yayi wurin Zama aduniya


Bama wannan ne abin ji ba irin yadda aka kirashi yazo ya samu mahaifiyar shi cikin halin ciwo da neman agaji Amma bawan Allah Nan tunda ya ufa ya tafi  Bai Kara waiwayo ta ba bare yayi tunanin duba yadda ta karaji da jiki bare ya kawo Mata dauki ko agaji 

Yau tsayin watanni shida Babu dungo Babu labarin ta Amma ko dai dai da Rana guda Daya Tak Bai tunawa da uwar shi na cikin neman taimako da agaji bare Kuma ya ruko wani Abu irin na jinkai da ya'yan kwarai masu neman albarka kewa tsaffin su Kai wannan wace irin SHIGA UKU da asara ce? Ubangiji ka shiryi bayinka masu Bata kasa yaran musulmi su zamowa iyayen su sanyi idaniya irin su kabiru Kam da haihuwar su wallahi gara barin su don haihuwar su batayiwa Wanda yayita Rana ba


Malam Ali ya share hawayen tausayin dungo yayiwa me gadin magana akan asanar da me gidan yayi bako 

Aiko sai gashi ya fito cikin shiga ta Wanda ya samu wurin Zama a duniya Kaya masu tsada Wanda kallo daya zakayi mishi ka bashi matsayin minister ko Dan majalissa


Ganin malam Ali yasa ya ji wani Abu marar Dadi ya sauki she da ruwa da lemu inda yake tambayar shi 


"Kabiru baka tambayi me jiki ba bare ka Kira kaji ya ta Kare ji?

"To ai lafiya ita ke fakuwa na San dai taji sauki..............

"Amma ko taji sauki ai tana bukatar kulawa mussamman Kai da kake dolen ta 


"Kabir kayi sannu da kidan da duniya ke maka kana taka rawa Wallahi Babu komai acikin wannan Rayuwar sai rudani 

Duk nasarar mutum a Rayuwa ya samota ne daga addu ar iyaye don su ke da mabudin kowace irin nasara...


"Bama abinda ya kawo Ni wurinka kenan ba don kowa ya gyara ya sani banzo don nayi maka wa azi ba sakone dungo taba Ni ta Kuma ce in isar gareka gashi Kuma Allah ya Taya min na kawo maka sai dai abin tashin hankali da saka zuciya rawa shine mun nemi dungo sama ko kasa mun rasa.....................

Post a Comment for "ZAN FASA KWAI 36"