ZAN FASA KWAI 35
......Kukan da hajiya Mama keyi ne yaba wani Jami I tausayi inda yake girmama girman kaunar uwa ga danta lallai duk Wanda Bai kyautatawa iyayen shi ba shine asararre duniya da lahra
Don haka sai ya ce abude musu su shiga aikuwa hajiya Mama tayi ta saka mishi albarka Inda yace ai albarkar ku muke nema mama duniya da lahira
Suka shigs inda suka samu AK lafiya kalau sai dai zaman wuri Daya kawai ne damuwar
Ummita ta makale shi tana kuka lubabatu da hajiya ma kuka suke inda yake ta Basu hakuri akan yadda kaddara ke saukowa bawa babu zato bare tsammani Kuma da anyi hakuri sai komai ya wuce .
Mubarak da Ahmed da Fatima ma rungume shi sukayi inda hajiya ke tambayar yadda abin ya faro ya Kuma sanar da ita kaf abinda ya faru.
"Ubangiji ya fidda ka kunya abdulkarim yau duniya wani baya so ko silifas ka sauya bare Kuma Ubangiji ya daukaka ka shikenan sai ashiga hassada da bin mutum ta karkashin kasa Amma Babu komai inda ADDU A ta zatayi tasiri akanka to Babu Ranar da zaka tozarta Kuma da ikon Allah kayi gaba gaban da ba za a iya cimma ka ba.............
Wani Jami I ya shigo yake sanar dasu Wai lokacin da aka Basu ya wuce sai dai suyi hakuri sai wani lokacin na gaba
Haka suka taho suna addu a da neman mafiita sai dai duk yadda suka dauki lamarin ya wuce Nan don kusan tsayin wata biyu Amma Babu bayanin komai Wai bincike ake duk yadda yan uwa da dangi ke shiga da fita Kan lamarin Dole aka saurara aka barwa Allah ikon shi
Agefe guda Kuma Kabir mashi kashe arna fakuwar eng AK ya dawo da martabar shi dominko yanzu Dole tasa ake bashi aikin kwangila ya Kuma yi yadda yake so don da gaske son Rai yafi yawa cikin aikin shi Wanda yake zaftare kaso arba in cikin dari sittin shine za ayi aiki dashi ko Babu nagarta inda Kuma izzatu da fulani suke warwasawa yadda suke so don yanzu duniyar dasu take damawa kudi suna ta shigowa asusun izzatu ya cika ya tumbatsa yayin da fulani Bata da sauran damuwa komai ta nema tana samu don haka suke Jin Basu da sauran matsala
Tsayin watanni shida Wai ana bincike inda daga karshe aka Mika batun gaban kotu don Alkali ya yanke hukunci
Zuwa kotun ma Bai zo da sauki ba domin ko wasu Bakin fuskoki ne suka zo suka bada shidar zur akan eng AK Wai dama Yan unguwa suna jitajita akan shi game da lamarin shi inda wasu ke ganin Yana da hannu a kungiyar matsafa don an Sha gano yaran da suka Bata agidan shi don haka kotu ta yanke mishi humunci irin Wanda yake yankewa yaran jama a
Sharri dai kala kala inda daga karshe Ubangiji ya kawo mishi dauki ta hanyar binciken da akayo gidanshi ba a samu wata shaida da zata nuna shi amatsayin me hannu a kungiyar matsafa ba haka Kuma duk tsayin lokacin ba akama shi da abinda zai alamta tabbatar zargin ba
Abinda dai akayi mishi an karbe duk abinda ya mallaka don biyan diyyar ran da ya kashe na Wanda aka samo kafa da hannu har da kokkon Kai
Haka aka sallamo shi ya dawo gida Inda murnar iyalai da Yan uwa ta kasa boyuwa acewar hajiya mama ita dukiya dama bakuwa ce Kuma raba bawa da arziki sai mutuwa inda take mishi nasiha da kar ya damu da abinda aka karbe mishi yanzu ne ma yake da damar sake samun wani arzikin fiye da Wanda yayi don ita hassada takin arzikice (Allah kajikan haj Saliha Zaria ita ke fada min hassada takin arzikice me hassada kuwa Yana cewa Allah Bai iya ba to Wanda yace Allah Bai iya ba ya kake zaton zai Kare?)
Bai damu ba ya Kuma amsawa hajiyar da cewa komai ya samu bawa da sanin Allah Kuma bawa Bai Isa kaucewa kaddarorin shi ba ko da kuwa zai shige akasa ne don haka ya riki hajiya da tayi mishi ADDU A Allah yasa ya cinye jarrabawar shi
Haka Yan uwa da abokan arziki ke ta zuwa yi mishi jaje kasancewar shi mutum me ALHERI kowa nashi ne inda Kuma yake matukar Jin kunyar mutane akan sharrin da aka kala mishi amma Allah shi zai wanke shi
Rayuwa tayi wata irin sauyawa agidan shi Babu abinda ya tsira dashi sai gida hatta da motoci an karbe sai Yan kudin da sukayi saura abanki
Kallon lamarin yake tamkar mafarki Wai yau shine a wannan bigiren Amma babu komai ya godewa Allah da ba imanin shi ya rasa ba sai ya karbi kowace irin Rayuwa da ta Zo inda ajalin shi ya riska Dole ya mutu Kuma Dole ayi hakuri
Sauyin da Rayuwa tazo dashi har ta Kai an cire su Mubarak daga makarantar kudi zuwa ta gwamnati don ba za a iya biya musu kudin ba inda takai abincin da za akai baka ma na neman gagara sai dai dayake lubabatu macece me kokari itake Kara karfafa mishi gwiwa akan yayi hakuri dai kar yayiwa Allah butulci da sannu bawa ke cimma Rabo da arziki
Haka Kuma da sannu kunkuru zaije inda jirgin sama yaje
Hajiya da Yan uwa da abokan arziki wadan da Basu zamo kaza me ci ta goge Baki ba suke ta hidimta mishi don Suma ya hidimta musu lokacin tasu bukatar Amma fa da yawan su Wanda suka ci moriyar tashi suna Nan suna juya kudi Amma dayake Dan Adam ne me yin Abu don yabo ko ganin ido sun ma manta da tsiruwar shi zumuncin zamani kawai mutane suka Rika Amma duk da haka shi Bai rike su ba duk inda Rabon yake zai fito shiyasa ya ke zaune lafiya inda Kuma hajiya ke taimaka mishi har ta Fara siyar da kaddarorin ta tana bashi kudin don ita Kam ranta ma zata iya bawa abdulkarim don yayi Mata Hidima tana Kuma addu a Allah ya kawo mishi mafita ya Kuma bude mishi kofofin arziki
Dare daya lubabatu ta soma kosawa da wannan Rayuwar ta talauci tun Bai Gane ba har aiyukan ta suka soma nuna mishi....................
Post a Comment for "ZAN FASA KWAI 35"