Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

ZAN FASA KWAI 33

             *Page 33*

........Sannu ahankali akazo Kan eng AK Wanda ke kallon yadda ake binciken motocin mutane har akazo gareshi

"Ranka ya Dade muna son duba cikin motarka idan Babu damuwa.......

"A a Babu komai yallabai Bismillah ya fito Yana daga musu cikin motar suka bincike ba su samu komai ba sukace ya bude musu but

Ya kewayo ya soma kokarin bude but din Amma wani abun mamaki tamkar an sakawa but din kwado yayi yayi ya bude Amma yaki buduwa yayi iyakar kokarin shi Amma but ya ki buduwa ya dubi Dan sandan Yana sharce zufa
"Ranka ya Dade wallahi yaki buduwa karfen nasara kenan ban fa Dade da budeshi ba Amma yanzu da yake so ake ya bude yaki da zaku yarda sai ince muku babu komai aciki.............

"A a ranka ya Dade a dai bude don Rana tsaka aka tashe mu aikin Nan ..............
Ya Miko mishi key din motar

"Karbi to ka gwada kagani Ni dai na gaji gaskiya,
Dan sandan ya karbi key din ya soma kokarin gwada tashi sa ar inda ya turza sosai kafin yayi nasarar bude but din cikin sa a Kuma ya hango wani Abu me kama da jini na bin wani tsumma dake kudun dune yajawo shi ya warware inda yaga wani Abu me kama da hannun mutum inda kafar mutum ta fado  Kuma wani Abu ya fado me kama da kokon Kan mutum

Eng AK ya zaro idanu Yana mamakin yadda wannan alamarin ke Shirin faruwa ta Yaya akayi wannan abin ya shigo motar shi

Inda Dan sandan yake kallon eng abdukarim da mamakin wannan abinda da ya samu acikin motar inda daga can baya Kuma cikin masu jiran go slow Kabir masi ya fito daga tashi motar ya karaso wurin inda shima yaga abinda ake mamakin gani amotar abdulkarim

"Wai abdulkarim Kaine da part din mutum a mota? Eh lallai da gaske kake har da tsafi kake hadawa shiyasa ka shiga gabana to Allah ya shirye ka ya fada Yana murmushi ya koma motar shi Yana kallo aka fidda motar eng abdukarim aka saka Mata key aka kulle shi Kuma aka wuce dashi sashen da zai bincike shi yayin da Yan sandan suka ci gaba da bincike motocin mutane 

Da wata irin dariya Kabir ya SHIGA gida inda izzatu ta tarbeshi tana tambayar dariyar Nan ta lafiya ce?

"Ki tayani dariya don ya akan idona Dan banzan can AK ya shiga hannu shigar da ba zai taba fita a yanzu ba. Kai lallai na yabawa gambo mafiyas akan wannan aikin nashi Dole ne in mishi biya me kyau,

Izzatu ta kyalkyale da dariya tana fadin nasan gambo mafiyas ya fi da haka Amma ya akayi har hakan ta faru?

"Nima ban San yadda gambon ya shirya wannan makircin ba ya dai kirani ya fada min abinda Zan sanar da Jami an tsaro na Kuma fada musu sai gashi akan idona aka damke Dan banza da kafafun mutane har da hannu da kokon Kai 
Amma Bari in Kira gambo mafiyas din yazo ya karbi kudin shi kuma inji yadda ya shirya wannan makircin
Ya dauko wayar shi ya Kira gambo ya ce yazo yanzu
Ai kuwa ba a rufe awa guda ba sai ga gambo mafiyas

Kabir ya daga mishi hannu alamar jinjina  inda gambon ke murmushi
"Me gida kaga aiki ne Hala?
"Naga aiki gambo don akan idona aka damke Dan banza da kafafun mutane har da hannu da kokon Kai ya akayi ka shirya mishi hakan?

"Ai me gida na Dade ina binshi sannu ahankali har na samu sa ar ya bude but din na fakaici idon shi na saka mishi hannu da kafar shiyasa nace ka sanar da hukuma don ta fara binciken motocin ta yadda Za a kamashi kaga idan aka samu wannan abin a motar shi Dole za a shiga bincike kaga daga Nan sai sunan shi ya baci har ya Kai Babu me kallon shi bare sunan shi ya motsa 

Izzatu da Kabir suka tafawa gambo mafiyas akan makircin shi  Kabir kuwa ya bashi kudi masu yawa ya Kuma ce zai neme shi matukar wani zai yi mishi shigar sauri irin na ak to yanzu ne zai Kira shi don yayi mishi maganin shi da haka sukayi sallama gambo ya wuce Yana murna izzatu da Kabir ma suka wuni farin ciki sun jefa Rayuwar bawan Allah cikin garari....................

Post a Comment for "ZAN FASA KWAI 33"