ZAN FASA KWAI 10
*ZAN FASA KWAI*
*page 10*
....... Doctor Usman ya tarbeta cikin mutunci don Bai zaci sun rabu da AK ba bayan sun gaisa yake Mata fatan alkhairi akan auren AK din
"Ashe eng ya angwa ce madam ? To Allah ya baku zaman hakuri da haka Mata ke goyawa mazajen su baya ai da ko Ni Nan na karo wata to Amma abin ne ba duka Kai ba sunan wata hula
Izzatu ta kwabe Baki kafin tace
"Shi dai Kam ai aikin banza ne yake Wai jefa agwagwa ruwa Wanda Bai ko Kai ga harara cikin duhu ba .Doctor Usman yayi murmushi"To madam na Gane karatun sai ayi ta hakuri dama shi zaman haka ya gada Amma da anyi hakuri sai komai ya zamo ba komai ba duniyar ma guda nawa ce?
"Likita bama tare fa da AK ahalin yanzu don Allah ya sani ba Zan jure zaman asara agidan shi ba shekaru goma Sha biyu Babu haihuwa haka Zan Kare saboda Allah? Yanzu ma zuwa nayi ka fasa min wancen KWAN na gwajin da kayi Mana don har yanzu Bai fuskance Ni da sakamakon gwajin ba Wanda Ni da kaina na gano matsala daga gareshi don yadda dangin shi ke son saka min ciwon Kai da nice da matsala da tuni sun mishi aure shine kawai na zabi ya sauwake min auren shi in Kara gaba don kasar Allah me yalwa ce in kaji matsatsi ka Kara gaba shine nake son sanin sakamakon don in har da bukatar Nima adora Ni Kam magani ko ya sakar min wata cutar sai na Tara kusa.
Doctor Usman ya zuba Mata ido Yana Mata kallon kinyi wauta.
Ya tambayeta
"Yanzu shi eng yasan Zaki zo Nan wuri na?
"Eh yasani ta bashi amsa Amma duk da haka sai da ya Kira wayar shi don sunyi dashi shima zai Taya shi rufe sirrin
Kara biyu ya daga bayan sun gaisa yake sanar dashi madam ce tazo da wata magana wadda muka Dade da haka Rami muka binne na Kuma yi maka alkawarin sai dai ta fito ta bakin ka ba dai Baki na ba.
"Kar ka damu Usman baba tare da ita a yanzu ta nemi saki ne gareni don tana ganin nine me matsala bayan ta gama cinye fuskar hajiya ta tas inda na sauwake Mata Kuma tunda tazo gareka na yarda ka fada Mata gaskiyar magana don ta Gane kalmar tausayin ta da nake yawan nanata Mata Amma Bata taba daga kalmar tayi Mata duban fahimta ba
So kar ka damu na yarda na amince ba ita ba duk wani ma me min kallon da take min ka sanar dashi na gode ya fada Yana tsinke wayar shi
Radam tajiyo maganar da AK yayi inda taji wani ruwa na bin jikinta inda ta Gane zufa ce don ko Usman Bai fada Mata ba ta gano bakin zaren.
Usman ya soma da yi Mata tambayoyi akan Shan kwayar Hana daukar ciki
Kai tsaye ta amsa mishi da eh kwarai ta yi su.
Inda shi Kuma ya Dora yi Mata bayani
"Wadan Nan magunguna da Kika Sha sune sukayiwa mahaifar ki muguwar illah wadda ta kassara ta har kikaji babu batun ciki ko haihuwa
Ranar da kukazo gwaji eng ya nemi sanin dalilin matsalar ku inda ta bangaren shi ba a samu matsala ba sai ta bangaren ki inda bincike ya gano illar da maganin yayi Miki
Dalilin da yasa na ce ki bamu wuri kenan don ban San ya me gidanki zai fahimci zancen ba inda nayi mishi bayanin komai Amma ga mamaki na sai Naga ya tausaya Miki har ma yace mu haka mu binne Ni da shi baya son kowa yaji shine dalilin da Bai fuskance ki da maganar ba ya dai karba Miki magunguna Wanda ya sanar Dani Wai kinki amfani dasu wannan shine dalilin da kikji Bai sanar dake komai ba
Amma banji Dadin abinda Kika sanar Dani ba gaskiya Kuma kin tafka kuskure ba karami ba
Ta dafe kanta hawaye na zuba inda take Jin wani Abu me kama da nadama duk da Bata taba yin nadamar wani Abu da tayi a Rayuwar ta ba sai yau da taji inda ake halacci ba tare da an duba Kai waye Wanda akewa halaccin ba
Bata cewa Usman komai ba ta taso ta taho Kai tsaye ta zarce gidan abdulkarim duk da ita Kanta Bata San me zai kaita gidan ba bare abinda zata yo.............
This comment has been removed by a blog administrator.
ReplyDelete