HEEDAYAH 6
⚡ _Heedayah_ ⚡
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
Da asuba bayan an idar da sllh a masallaci da kusan minti sha biyar Shuraim ya mike ganin Abbansa xai fita masallacin don dama shi yake jira, sai da suka fita masallacin ya isa gun Abban nasa, ya d'an risina yace "Barka da asuba Abba" Abba ya kallesa ba tare da ya tsaya ba yana ci gaba da tafiya yace "Yauwa...." Shuraim na biye da shi yace "Abba dama i
na son baka hakuri ne kan abubuwan dake faruwa...." Abba ya katse sa yace "A'a kaje dai ka ba babarka hakuri, ita ta fi daukan abun da xafi, sannan kuma dama a bayanta kake as always" Ya girgixa kai yace "A'a Abba, ba wai ina bayanta bane, just that muna tsoron abinda xai je ya dawo ne a kan lamarin...." Abba yyi murmushi yace "Ehh gaskiya ne Ali, barin ma da ya kasance cewar duk abinda yaro ya hango ba lallai babba ya hango ba" Shuraim yace "A'a ba haka bne" Abba yace "No haka ne" Shiru Shuraim yyi yana dai biye da Abban nasa, can yace "Toh Abba tana ina yarinyar ynxu?" Abba ya tsaya ya juya yana kallonsa yace "Do you have any problem with that?" Bai iya yace komai ba, Abba ya watsa masa wani kallo ya ci gaba da tafiyarsa, Har suka shiga gida babu abinda Shuraim ya sake ce masa. Reaction din Abban nasa bai hanasa bin sa har cikin parlonsa ba, Abba ya xauna saman kujera ya dau remote xai powering TV, Shuraim ya xauna kasa daga gefensa, a hankali yace "Kayi hakuri Abba, ni ban ga aibun abinda kayi ba haka ma ban ga aibun abinda Mumy tayi ba, she's right in many ways" kallonsa kawai Mahaifin nasa yake, can ya girgixa kai yace "Baxa ka ta6a yin alkibla ba dama, look... Ur mother like it or not dole gidan nan Heedayah xata xauna har sai naga she's back to her parent, idan ku ka ga Heedayah bata dawo gidan nan ba to iyayenta ne Allah ya bayyanar, amma I mean it, bbu abinda xae hana hakan, kuma tare xata dawo gidan nan da matar da xan aura ta kula da ita, ur mother can do whatever she want bbu wanda ya isa canxa ra'ayina" Shuraim dake kallonsa da wani expression yace "Abba aure?? I'm sorry to say... you want to spoil ur home because of a mere little girl da baka san ma me ya rabata da iyayenta ba, baka san daga inda ta fito ba, think about it plss Abba, this is wrong" Abba yyi wani murmushi yace "It's my home not urs, ko da wasa ai baxa ka gaya ma uwarka irin wannan maganar da kake gaya min ba yanxu, ni kuma ga abokin rainin ka, check out pls my frnd" Mikewa Shuraim yyi kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Kayi hakuri" daga haka ya fice daga parlon, lkci daya ya hade rai bayan ya fita ya nufi dakinsa, who the hell is this forsaken girl that's trying to cause confusion in their home.... Muryar Mumy yaji tace "Ya aka yi Shuraim? What's wrong?" Tsayawa yyi ya juyo bbu walwala yace "Ina kwana Mumy" tace "Lafiya lau, ya naga ranka a bace haka?" Yyi kasa da kai yace "Nothing mum, xan shirya ne yanxu" daga haka ya juya ya shige dakinsa, sarai tasan daga parlon Abbansa ya fito, ta d'an yi jim kamar me naxari sannan tayi murmushi ta juya ta nufi dakinta a ranta tace Idan barrister ya san wata bai san wata ba ai.... Karfe sha biyu saura na safiyar ranan barrister ya isa gidan Yayansa Dr Umar, yana shiga main parlor bangaren Mahaifiyarsu ya nufa, ya bude kofar parlon tare da sallama, a guje kaka ke kokarin boye bowl din gabanta tana cewa "Naga fitina waye kuma wannan" d'an murmushi yyi ya karasa cikin parlon, tace "Au ashe Amadu ne, wllh na xata yaran nan ne masu halayyar bera, to idan na ajiye d'an nama na da cin cin sai su bi dare su yashe...." Abba yace "Ina yini Baaba?" Kaka tace "Lfya lau Amadu, ya aikin" yace "Alhmdllh, ke daya ce gidan kenan" Da sauri tace "To da fa?? Ai Kullum a haka suke bari na, kar fa kayi xaton basu gidan, duk suna nan wllh, dama wannan yaro Aliyu ne me shigo min, shi ma kuma na koresa gaskiya, don raini ya shiga tsakanin mu" Abba yace "Daga gun aiki nake nace bari in xo mu gaisa" Kaka tace "To ae ka kyauta, Allah yyi maka albarka, Wai ya maganar da kayi ranan na cewa xaka kara aure ne naji shiru" yace "Ehh dama xan gaya maki maganan na nan in sha Allah..." Kaka na washe baki tace "Toh Alhmdllh, yar ina ce?" Yace "Nan kaduna" kaka tace "Abu me sauki, to ni dai Allah ya sa ta kirki ce, don Maryam ta gasa mana Aya a hannu gaskiya, to ta amince xata rike yar makauniyar??" Abba yace "Ehh ba matsala" kaka tace "Atoh ita da ke tsoron Allah kenan, Maryam ae shaidaniya ce sanye da kaya irin na mutane" Abba ya mike yace "Bari in je kaka sai na shigo ko gobe" Kaka tace "Toh, ni dai haka nn nake sae bin yara nake ina rokon hamsin, dari, suna xagina suna ba ni" Abba ya juya yana kallonta da sauri, ta tsuke fuska tace "A'a kai ba ubana bne da xaka min kallon tuhuma Amadu, idan gantalalliyar dubu ashirin din ka ce ta shekaranjiya to ta kare tun jiya wllh" Bai ce komai ba ya nufi kofa ya bude yace "Sae anjima" Daga haka ya fita. Hajiya Rahinah ce xaune tare da Barrister kan kujerun dake karkashin inuwar bishiyar tsakar gidanta, barrister ya ajiye wayar hannunsa yace "Sae kuma kika yi shiru" Sae a sannan ta kallesa tace "Ehh shirun naga xai fi, barrister in dae har sbda wannan yarinyar kke son aurena, ina nufin indan sbda in riketa ne to kar ka damu ni me iya rike little girl din ne har bayyanar iyayenta idan Allah ya yrda, ina hada ka da Allah ka rabani da xancen auren ka, bbu aure a tsarin rayuwata ynxu...." Shiru yyi yana kallonta, sannan ya d'an yi murmushi yace "Sae dai fa kiyi hakuri Rahinah, you can't stop me from marrying you, Heedayah kuma gidana nake son ta xauna ba wani waje daban ba" Mami ta tabe baki sae dai bata ce komai ba, Budewar gate ya sa duk suka juya, Junaid ne ya shigo compound din hannunsa rike da Makullin mota, har ya isa inda suke ya fara gaida Abba sannan ya gaida Maminsa, Abba yace "Kana aiki ne Junaid?" Yace "Ehh ina aiki tare da Uncle dina a hospital dinsa" Abba yace "To that's good ya fi ka xauna, Allah ya taimaka" Yace "Ameen" daga haka ya wuce ciki, Abba ya kalli Mami yace "Ya kusa gama masters din nasa ne?" Mami tace "Ehh months suka rage masa idan Allah ya yrda" Abba yace "Allah ya taimaka" Junaid na shiga parlor ya ga Heedayah ce kadai parlon kwance saman kujera tana bacci, ya dauke idonsa ya wuce sama xuwa bedroom dinsa. Sae kusan la'asar Abba ya bar gidan har sannan kuma bai yi convincing Hajiya Rahinah ba dake kan bakanta na cewa bbu aure a gabanta. Yau dai har sha daya saura na dare Hajiya Maryam na xaune parlor tana jiran ganin lkcn da barrister dake compound yana ta waya xai shigo, yau kwana biyu kenan da ta lura da hakan duk da kasancewar ta mai bacci da wuri yau kam coffee me kauri ta sha tayi xamanta a parlor tana jiran ganin ikon Allah, lkci lkci take tashi ta leka waje ta dawo, lekawar da tayi na karshe ne taga ya gama wayar xai shigo ciki, da sauri ta shige kitchen ta kulle don ma kar ya san idonta biyu, sae da taji ya wuce part dinsa sannan ta fito ta dinga xaga parlor tana jiran ya kwanta sanin bashi da wuyar bacci, a haka Shuraim ya sakko downstairs ya sameta, ganinta da mamaki yace "Mum baki kwanta ba" Tace "Ehh yanxu dai xan je in kwanta na gama kallon wani film ne" Bai ce komai ba ta wuce sama shi kuma ya shiga kitchen, sae da taji Shuraim ya shiga dakinsa ta fito ta nufi part din mai gidan nata, a hankali ta bude kofar parlonsa ganin wuta a kashe ta gane ya kwanta, ta lallaba ta nufi daki tana tafiya a hankali, tana shiga duk da wutan a kashe yake tasan yyi bacci ta tafi inda tasan yana ajiye wayarsa ta dauka ta fita daga dakin, bangarenta ta koma ta bude wayar ta shiga call log dinsa, Number da aka yi saving da Great barrister taga last call dinsa, nan ta duba taga yana yawan kiran number, msg ta shiga tayi scrolling har xuwa farko, hankalin ta ya fara kwanciya ganin kawai text ne da ya shafi aiki, a hankali ta fara gwalo ido bayan tayi nisa ganin salon message din ya fara sauyawa har ta kai karshe, xufa ne ya karyo mata ta ajiye wayar ta rasa tunanin da xata yi, can ta dau wayarta ta kwashe number tas sannan tayi dialing, sae da ya kusa katsewa aka daga, daga daya bangaren Mami tayi sallama, shiru Hajiya Maryam tayi xuciyar ta na bugawa jin muryar mace, kawai ta katse ji tayi kamar ta daura hannu a ka tayi ta ihu, ta xauna gefen gado tana furta innalillahi, kallon wayarta tayi, sae kuma ta shiga call log tayi dialing wani lamba, yana fara ring aka dauka, Ta hadiye abu da kyar tace "Sadiya wllh da gaske Barrister neman aure yake, Ashe da gaske yake wllh, gashi ynxu na bincike wayarsa kaff har na samu lambar warce yake nema da aure, na shiga ukuna Sadiya, da yarinta ta ba a min kishiya ba sai yanxu a kan wata shegiyar yar tsintuwa makauniya...." Ta fashe da matsanancin kuka tace "In dai Alhaji yyi auren nan ai tawa ta kare, dariya xa ayi min a gari ki bani shawara don Allah kawata, wllh dariya makiyana xa su min" Hajiya Sadiya dake saurarenta baki bude tace "Aure fa kika ce Maryam?? Ke sai ki yrda ki barsa yyi auren? Toh ynxu dai ae sai ki wanke kafarki mu tafi inda kike ikirarin bbu abinda xai kai ki" Hajiya Maryam tace "Ina???" Hajiya Sadiya ta kyalkyale da dariya tace "Wa enda kike raina taimakonsu mana...." A fusace Hajiya Maryam tace "Allah shi kiyaye, tun da can da kuruciyata ban ta6a xuwa ba sai ynxu a kan yar yarinyar da na haifa?? Yar cikina? Ni nan da kike gani na ishi kowa wllh, Kuma muna nan dake auren nan baxae ta6a yiwuwa ba ni nasan me xan yi, ke dai kawai ki xo gobe don Allah, sae da safe" daga haka ta katse wayar, ta kusa awa daya xaune kafin ta iya tashi ta mayar masa da wayarsa ta dawo dakinta, daren ranan bata yi baccin kirki ba, Wai ita barrister xai ma kishiya sbda taki rike makauniya??? Tayi kwafa ta juya tana jiran dai gari ya waye. Mami na xaune tana ma Heedayah gyaran dogon gashinta dake ta kyalli, yau ma dai bata je aikin ba don har lkcn bata samu wanda xai kulan mata da Heedayah ba, Farida kuwa na boko daga safe har 6, wayarta ne ya fara ring ta dauka ta kai kunne, sallama aka yi mata daga daya bangaren ta amsa, Hajiya Maryam dake xaune dakinta da Hajiya Sadiya da wata kawarsu Hajiya kyauta tace "Don Allah da barrister nake magana" Mami tace "Yes, wacece ke magana?" Hajiya Maryam ta gyara xama tace "Toh Barrister wata yar matsala ce wllh ta taso mana muna neman lawyer, shine wani abokin aikina ya bani lambar ki, yyi assuring dina you can help..." Mami tace "Allah sarki sai dai na dau hutu baxan yi aiki ba cikin satin nan gaba daya" Hajiya Maryam ta gwalo ido tace "Don Allah ki taimaka barrister, ya gaya min irin kirkin ki da taimakon ki, ke kadai xaki iya rufa mana asiri kan lamarin nan, don Allah barrister ki dubi girman Allah ki sauraremu, wllh muna cikin tashin hankali sosai" Mami tace "Kar ki damu malama xan hada ki da wani barrister, he is also good xama ki ji dadin nasa aikin fiye da nawa, I can send you his number now" da sauri Hajiya Sadiya tayi ma Hajiya Maryam alamar tace mata to ta turo... Hajiya Maryam tace "Toh ngd Barrister, Allah ya saka, ina jiran lambar" Mami tace "Kar ki damu, let me send you" daga hka ta katse wayar, cikin few seconds ta tura ma Hajiya Maryam number Barrister Ahmad, Hajiya Maryam da ta ji kmr xuciyarta ya fashe cikin tashin hankali tace "Na shiga uku, kun ga lambar mijina ta turo min dai koh???" Hajiya Sadiya tace "Toh sake kiranta" hannu na rawa ta sake kira, Hajiya Sadiya ta amshe wayar tace "Ki dubi girman Allah Barrister ki bamu lkcn ki ki saurari matsalar mu, an ce mana ke ce maganin kukan mu, wllh ko nawa kika bukata xa mu biyaki domin Allah ki taimake mu..." Da mamaki Mami tace "Wnn barristern da na tura maki numbersa ya ma fini iya aiki, xae saurare ku fiye da ynda ni xan saurare ku" da kyar da kyar suka shawo kan Mami kan ta amshi case dinsu, Mami ta girgixa kai tace "Gaskiya baxan fita gidana ba ynxu, sae dai ko ke ki xo ki sameni" Hajiya Maryam tace "Wnn ae ba matsala bane, bari in taho ynxu ma, Allah ya kara girma da daukaka Barrister, ki turo min address din plss" Mami tace "Ameen, xan tura maki ynxu" daga hka ta katse wayar, ta tura address din nata, Hajiya Maryam tayi wani murmushi ta mike ta dau mayafi da Makullin mota jikinta har wani 6ari yake tace "Ku mu je" fita duk suka yi suka bar gidan a motarta. Gane gidan Hajiya Rahinah bai masu wahala ba, suka yi parking a waje bayan sun sanar ma Mai gadi Hajiya Rahinah suke nema kuma ta san da xuwansu ya bar su suka shiga cikin gidan. Har entrance din shiga gidan suka nufa suka tsaya, Hajiya Sadiya ta danna bell, Mami da ta saka Heedayah gaba tana mata tambayoyin ynda aka yi har ta fito gida.... exactly labarin da Heedayah ta bada a station ta sake ba Mami, ta kare da cewa sai taji ana tafiya da ita a bicycle kawai sai ya wuce ya bar ta bai kai ta gun Amminta ba kuma, tana fadin haka ta fara hawaye, Mami dake ta naxarin d'an labarin ta gane daga all indication kidnapping yarinyar aka yi sai kuma Allah ya kubutar da ita, mikewa tayi jin an sake danna bell for the third time ta nufi kofa ta bude tana kallonsu Hajiya Maryam, Hajiya Maryam ta kirkiro murmushi tace "Sannu fatan ke ce barristern?" Mami tace "Oh, okay ga kujeru can bari in fito yanxu, ku jirani a can" Hajiya Maryam ta saka kai ta raba ta gefenta ta shiga ciki, tace "A'a xai fi daga cikin dai barrister, tonon asiri ai ba dadi" sauran ma duk suka shige ta gefenta, kallonsu Mami tayi da d'an mamaki, Hajiya Maryam ta isa tsakiyar parlon tana kallon Heedayah da wani expression, sauran kawayenta ma duk suka tsaya kusa da ita suna kallon Heedayar, Kasancewar Mami lawyerr yasa lkci daya ta gane abinda ya kawo matan nn gidanta ba abinda suka ce bane, Hajiya Maryam tace "Toh kinyi tsaye bakin kofa ae sai ki karaso ki ji case din mu koh barrister?" Heedayah dake xaune saman kujera da apple a hannunta ta mike da sauri don in dai ta ta6a jin murya to baya ta6a bacewa a sense of hearing dinta, ko da kuwa an dau lkci sosai sai ta gane muryar duk inda taji, Mami ta karaso parlon tace "Bana bukatar jin case din ku, domin bana hulda da Yan tasha, ku kai case din ku wani wurin, and ku fitar min a gida immediately now...." Hajiya Maryam tayi wani dariyar rainin hankali tace "Koh?? To sai ki fitar da mu ta karfi Mai gida, bari ki ji..... ba barrister ba, ko judge ce ke na xo ne in yankar maki lafiyayyen wani ki fita hanyar mijina Barrister Ahmad, shi ba gantalalle bane irin ki, kin gama xaga duniya kinyi yawon karuwancinki shine xaki wani makale masa ya aure ki sbda baki da tunani ko? To wllh kin yi kadan, mijina ba sa'an auren ki bane, Ashe ke ya kawo wa shegiyar yarinyar nan kika karba kika rike tunda dama kina sonsa da aure, to don kaza kazan ki nace baki isa ba, mijina ni kadai ne shi din, baxan hada shi da karuwa ba yar boko da ke yawon duniya don ma kiji, don haka tun wuri ki san inda dare yyi maki" Tunda ta fara Mami ke kallonta, duk da maganganun sun ma Heedayah girma ba duka xata iya ganewa ba hakan bai hanata dinga kuka ba tana kiran Mami, Mami ta nufi gun wayarta ta dauka cikin few seconds tayi dialing number Abba, yana fara ringing kuwa ya daga ta sa hands free tace "Ahmad kana ji na?" Yace "Yeah ina ji my barrister, ya gidan?" Tace "Alhmdllh, dama nace ne you can come forward with ur pride price to my elders ko gobe, na karbi tayin auren ka idan Allah ya yrda" Yace "Da gaske kike barrister, pls don't joke with me" farin ciki ne sosai tare da words dinsa, Mami tace "I'm not joking barrister, na baka go ahead, we will talk later in sha Allah" daga haka ta katse wayar, Hajiya Maryam da wani xaxxafan xufa ya keto mata ta dinga kallon Mami so speechless, Mami ta isa gabanta ta tsaya tace "xa mu shigo gidan barrister Ahmad tare da wannan yar yarinyar nan da sati daya, sai dai ciwon xuciya ya kashe ki a banxa, sannan wnn yarinyar da kike gani ita xata xamar maki nightmares dinki kafin ni.... Lastly kin ci sa'ar mijinki na da k'ima da daraja a idona sannan ga soyayyar da nake masa, wllh da yau bbu abinda xai hana ke da mahaukatan kawayen ki kwanan cell kuma in ga uban da xai bada bail dinki, amma soyayyar mijin ki baxai bar ni inyi hakan ba..." Tana fadin haka ta ja hannun Heedayah suka fita xuwa gun mai gadi tace "Salisu ka tattaro abokanan ka masu gadi ka fitar min da wasu mashaya da suka shigo min gida, and from henceforth duk wanda ya xo ka fara sanar min kafin ya shigo" da sauri ya fita yin yanda tace.Start patronizing Heedayah lovely fans.... last free update later at night in sha Allah😍
07087865788.....
Post a Comment for "HEEDAYAH 6"