IMAAN 19-20
19. Imaan
Umma na komawa bangarensu kallo daya tayi ma Mujaheed dake xaune dinning yana shan coffee tace "Ka sameni daki yanxu" sosai gabansa ya fadi ya bi ta da kallo har ta haura sama, bai iya ya karasa shanye coffee din ba ya mike ya bi bayan ta, tsaye ya ganta tana safa da marwa a dakin, Yace "Gani Umma" ta juya tana kallonsa fuska daure tace "Mujaheed ina son sanin meye matsalar ka don kaga shegiyar yarinyar nan da mai mota jiya har kake ikirarin hukuntata" ya xaro ido yace "Ban gane ba Umma" Ta masa wani mugun kallo tace "Bana son ka gane dama ai, warce kaje ka ba sakon take fadi
yanxu naji, dama baka raba kanka da makiyan nan nawa ba har ynxu Mujaheed? Mujaheed ka gaya min meye hadin ka da yarinyar nan Imaan?" Yace "Haba Umma, ke yanxu maganar inna kike dauka, kila ma don ta ganki yasa ta kirkiri haka, ni a ina na ganta har muka yi wannan xancen da ita?" Shiru Umma tayi tana kallonsa, a ranta kuwa tunani take kila hakan ne ma, ganin Umma tayi surrender, Mujaheed yace "Kawai ta fada haka ne don ki sa a rai, ni yaushe nake da wannan lokacin ma a gidan nan yanxu" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Sae ma kaga rashin mutuncin da ta min kayan da na kai mata, ni na ma ji dadin da ta gane cewar in don ta nine baxan bata ko tsinke na ba, basirar Abban ku ne kamar yanda ta fada" Mujaheed yyi murmushi bai ce komai ba, Umma tace "Gobe xan baka sako ka kai ma Hajiya Mansura ta marafa, bata samu xuwa bikin ba amma ta bada gudunmawarta dubu dari, cin cin da su alkaki xaka kai mata daga nan nasan xa ku hadu da Safeenah, tana nan ba ta koma makaranta ba, ni so nake nan da 'yan watanni a fara xancen naka bikin" shi dai Mujaheed bai ce komai ba banda kallonta da yake, ta xauna gefen gado tace "Kar fa kace min ka manta gobe kayi ficewarka, xuwa sha biyu in sha Allah xaka kai masu, tunda gobe lahadi" ya shafa kai yace "Allah ya kai mu" daga haka ya nufi kofa ya fita. Imaan ta kara leka samirar dake cike da cin cin da dubulan da alkaki da inna ta basu su kai ma ta rasulu aminiyarta, ta tabe baki tace "Wllh duk kin kwashe ma tsohuwar, mu fa har ynxu ba mu ci ba" inna ta tsuke fuska tace "To ina ruwana da rashin cin ku, ni na aurar da 'ya ko ko? Kaji min dai, Dubu talatin ta rasulu ta bada a kawo min gudunmawa, kuma ace baxan cika mata samira da kayan flawa ba, ni ta ma fi min Aisha kiji in gaya maki" Imaan tace "Kice ma ta fi maki har daddy mana" Maimoon tace "Toh ina dubu talatin din?" Inna ta kalleta da sauri tace "Amina aka ce in ba wa da xaki tambayeni dubu talatin Maimuna? Ko ko kin ban ajiya ne? Ni dai ku daina sa min ido a gidan nan, idan ba haka ba mugun alkaba'i ba shi da kyau amma to xance kowa ya ci kansa gaskiya" Imaan ta kalli Maimoon tace "Maimoon karbo kudin motar mu wuce" Inna ta kunce ha6ar xaninta ta fiddo naira dari ta ajiye masu tace "Hamsin xai kai ku ya dawo da ku, nan nan kabala dai" Imaan ta ajiye samirar ta xauna tace "Tabdi ko naira dari dari ma baxa a yarda a kai mu ba balle hamsin" Inna tace "Barawo ne mai adaidaitan da baxai kai ku a hamsin ba, ko ya sha wiwi ne, wllh kullum a hamsin ake kai ni a dawo da ni" Maimoon tace "Saboda ke tsohuwa ce ai" A fusace inna tace "Oh oh Allah, idan baxa ku ba ku ajiye min kayana ku fita, Xan kira Bukar ko Ahmadu cikinsu wani ya kai mun, ku fitar min a parlor" Kin fita suka yi jin abinda tace wai xata kira daddy ko Abba, Maimoon tace "Toh wai don Allah mu muka siya masu adaidaitan da xasu kai mu a hamsin su dawo da mu a haka, ki kara mana kudin mu tafi mana" Inna ta jefa masu wani hamsin tace "Aniyar ku ta bi ku dai" Maimoon ta dau kudin tana gunguni tace "Ae sai dai mu cika da kudin mu" Imaan ta tabe baki ta dau samirar tace "Sai dai ke ki cika, sisina baxan kara a kai ba tunda ba ni xan ci cin cin ba" daga haka ta fice parlon, inna tace "Shi sa har yau aka kasa gano cutar da ta sa ki gaba, saboda mugun xuciyar ki da rashin kunya, ni dai Allah ya saka ma d'ana, Allah ya saka masa kan kudaden da yake kashewa a kan tsadadden ciwon nan naki, Allah kuma ya raba shi dake lafiya, ya aurar dake ya huta ma ransa mijin ma ya d'and'ana ukubar, ba a taba jin alkhairi ya fito bakin ki sai sharri, to meye kuma don kin cika kudin mota" Maimoon ta bi bayan imaan ta kullo mata kofarta tana turo baki. Suna tsaye bakin titi suna jiran adai daita da xai je kabala, Imaan tace "Ko da yake nasan tsohuwar da xa mu kai ma baxa ta bar mu haka nan ba, kila ta ba mu kudin mota" Maimoon tace "Wllh da ba dan Abba da tace xata kira ya kai ba ba inda xanje ni dai, kullum fa idan xata aiki mutum sai ta raba kudin motar xuwa wajen kashi uku ta baka daya" Imaan tayi dariya tace "Kawai so take ayi ta mana fada shi sa tace xata aiki daddy ko Abba" motar Mujaheed da suka gani yasa suka yi shiru suna kallon motar, shi ma daga gida ya fito, ya sauke glass yana kallon Maimoon, Maimoon ta marairaice tace "Ya M.A inna ce ta aike mu kabala kuma ba mu samu adai daita ba har ynxu..." Ya gyada kai yace "Toh Allah ya kawo adai daitan" xai dage glass da sauri tace "Wait... Kai ina xaka plss?" Yace "Marafa" tace "Toh ka rage mana hanya mana don Allah" ya mata wani kallo yace "Me ya hada Marafa da kabala?" Tace "Yaya ai duk hanya ce mu dai ko ina ma ka ajiye mu nasan xa mu samu a can gaba" yace "Toh shiga" Imaan ta bude back seat ta shiga ya dinga hararanta ta madubi fuska daure, dama tun da suka hada ido taga kallon da yake mata bata sake yarda ta kalli madubin ba, Maimoon na kallon fancy nylon dake gaban motar ta dauka tace "Ya M.A wa xaka kai ma cin cin da dubulan?" Yace "Anty" dariya tayi bata sake cewa komai ba, sai da suka yi nisa yace "Gidan Baaba ta rasulu xa ki kenan?" Tace "Xa mu dai, ai ba ni kadai bace, ni da Imaan ce" ya watsa mata wani kallo ta xaro ido tana yar dariya ta rufe bakinta, har kofar gidan aminiyar inna ya kai su, Maimoon sai murna take tace "Ya M.A mun gode, ko mu raka ka marafan mu ma?" Shiru ya d'an yi da farko yana shafa kansa a hankali, lkci daya yace "Toh kar ki dade a ciki idan ba haka ba inyi wucewata" bude motar tayi ta fita tana kallon Imaan da ta fita tuntuni tana cinno baki suka shiga gidan, dari biyar ta rasulu dake ta sa masu albarka ta basu kudin mota, tace "Ina gaida Hajiya Asaben, kuyi mata godiya sosai, ita kuma amarya Allah ya basu xaman lafiya da mijinta, ku kuma Allah ya maku albarka ya fiddo maku maxaje na gari" suka amsa mata da Ameen, sannan suka mata sallama suka fita da samirar don juye kayan ciki tayi a nata samiran. Maimoon na kallon imaan tace "Wai Imaan me yasa baki gaida ya Mujaheed yanxu?" Imaan tace "Saboda baya gaida Ammi na sai ya ga Daddy" Maimoon ta xaro ido tace "Da gaske?" Imaan tace "Ehh mana" Maimoon tace "Toh saboda me" imaan tace "Oho" bude back seat tayi ta shiga Maimoon ta shiga gaba ya tada motar yayi reverse ya bar anguwar. Tafiyar kusan minti sha biyar suka yi suka iso gidan Hajiyan Marafa, Dai dai gidan yayi parking daga kusa da flowers yana kallon Maimoon yace "Xan yi sllh kafin in shigo" ya mika mata ledan yace "You take this in with you" tace "Amma yaya bamu san kowa a gidan ba fa" yace "Sai ki ce Hajiya ce ta aiko ki, ina nan shigowa nace idan nayi sllh" daga haka ya fita motar, Imaan dai na tsaye ta rungume hannu jikin motar bayan ta fita, Maimoon ta fito ya kulle motarsa da lock, ya wuce masallacin da ya gani a layin, Maimoon ta kalli Imaan tace "Mu je" bin bayan ta Imaan tayi suka shiga gidan, bayan sun sanar da mai gadi gun Hajiya suka xo, duk girman gidansu haka suka saki suke kallon gidan, Maimoon tace "Ni dai baxan shiga ba gwara mu jira sa a nan, kawai mutum yaje yana ta introduction ana masa wani kallo" Imaan ta yi dariya tace "Sai kice Hajiya Rukayya ce ta aiko mu" Maimoon ta buda ido tace "Bari ya Mujaheed ya jiki, wai Hajiya Rukayya" Imaan ta tabe baki suka shiga babban balcony din dake dauke da kujeru sannan ga babban rug a shimfide kasa, kan rug din suka xauna suna kara k'are ma gidan kallo, sai bayan da aka idar da sallah Mujaheed ya shigo gidan, kallonsu ya tsaya yi ya hade rai yace "What did I tell you Maimoon?" Ta marairaice tace "Yayanmu mun yi sallama kamar basa parlor" hararanta ya dinga yi kafin ya danna bell, ko minti daya ba ayi ba mai aiki ta bude kofar, ta gaishesa ya amsa yace "Hajiya tana nan?" Tace "Wa xa ace mata" Yace "Dr Muhd, Kice Hajiya Rukayya ce ta bada sako a kai mata" Murya can kasa Imaan tace "Toh ba gashi shi ma cewa yayi Hajiya Rukayya ba" Maimoon ta yi murmushi bata dai ce komai ba, Mai aikin tace "Toh ka shigo" bin bayan ta yayi xuwa cikin parlon da sauri imaan ta mike ta bi bayansa, Maimoon na yar dariya ta tashi ita ma ta shiga parlon, wata yarinya da baxata wuce ashirin da daya bace ta shigo parlon daga dinning kallo daya tayi masu ta wuce sama, tsaki imaan ta ja Mujaheed ya kalleta ta cinno baki ta dauke kai, mai aikin ta kawo masu drinks da bottle water ta ajiye, bayan wani lkci sai ga Hajiyar ta sakko cikin shiga ta alfarma ganin Mujaheed tace "A'a ashe kai ne doctor" yyi kasa da kai yace "Ina yini Hajiya" tace "Lafiya Alhmdllh, ya Hajiya Rukayyar, fatan an watse taro lafiya" yace "Alhmdllh" xaunawa tayi tana kallo su Maimoon da Imaan dake gasiheta tace "Wannan kamar kanwar khadijah da tayi aure Us koh?" Ta fadi haka tana nuna Maimoon, Mujaheed yace "Ehh kanwarta ce" tace "Maa sha Allah ga kamanni na gani, to ita wannan fa" Mujaheed ya kalli Imaan da ta nuna, da sauri yace "Yar uwarsu ce" tace "Allah sarki shi sa ban santa ba" Maimoon ta mike ta ajiye abun hannunta kusa da ita tace "Gashi Hajiya tace a kawo maki" Hajiyar tace "To maa sha Allah, nagode kwarai Allah ya basu xaman lafiya" Bude kofar parlon aka yi, wata yarinya ta shigo parlon cikin English wear bata ko kalli wa enda ke xaune parlon ba xata wuce sama Hajiya tace "Safeenah lafiya na ga ranki a bace" Jin sunan da Hajiyar ta kira Mujaheed ya daga kai yana kallon yarinyar, ita ba doguwa ba kuma ba gajera ba, farin ta har yayi yawa and she is beautiful, lkci daya ya dauke kansa, Maimoon da Imaan kuwa kamar sun samu TV imaan har da juyawa gaba daya tana facing dinta, rai bace Safeenar tace "Wai ki ji mum ashe birthday din ma wani local waje xa ayi, sai kinga yanda raina ya bace bayan duk shirin da nayi, wllh Saleema koluwa ce I don't know what's wrong with her, ni ko gaya masu na tafi ma ban yi ba" Mujaheed dai sai danna wayarsa yake, Hajiya tace "Atoh gaskiya basu kyauta ba, to why not baki ce masu a canxa hall din ba, ko ke ba sai ki biya kudin hall din ba" Tsaki Safeenah tayi tace "Ni duk raina ya baci wllh Mumy" xata wuce sama Hajiya tace "Toh ga doctor ku gaisa" Juyowa tayi tana kallon cikin parlon taga Mujaheed da ya ki dago kansa, ta fi second goma tana kallonsa, kafin ta karasa cikin parlon ta xauna hannun armchair da uwarta ke xaune cikin sanyayyen murya tace "Ina yini" sai a sannan ya daga kai yace "Lafiya lau, ya kike?" Tayi wani sanyayyen murmushi tace "Lafiya lau" Ta kalli su Imaan tace "Sannun ku" Imaan dai tace "Yauwa" Maimoon kuma ta gaisheta, Hajiya ta kwalo ma mai aiki kira ta fito da sauri, Tana kallonta tace "Pepper chicken da ku ka yi daxu xa ki kawo masu tun da ba ku gama lunch ba" Mujaheed yace "Daga gida muke yanxu Hajiya, we ate before leaving, so we are okay" tun da ya fara magana Safeenah ke kallonsa ko kiftawa babu har ya dasa aya, Hajiya tace "Wannan ae is more or less a dessert, daxu yara suka ce suna son pepper chicken, shine nasa su yi, kuma da yawa sosai suka yi don nasan baxa a cinye gaba daya yau ba sai dai a ba masu gadi da almajirai" Mujaheed ya d'an yi murmushi yace "Ni dai I am okay" Imaan tace "Ni dai xan ci" kallonta yyi da sauri, Hajiya tace "Yauwa, bar sa yayi ta fulako dama yayi kama da fulanawan, ke ma ai xa ki ci ko" Hajiya ta fadi tana kallon Maimoon, Murmushi kawai Maimoon tayi ta sunkuyar da kanta, mai aiki ta dawo rike da tray da plates uku a kai, ko wanne dauke da kaxa da aka yi garnishing sai kamshi da turiri yake, Mikewa Safeenah tayi ta dau plate daya ta karasa kusa da Mujaheed ta ajiye masa, hada ido suka yi yace "I said I am okay baxan ci ba" tace "Kaci ko kadan ne pls" Daga haka ta koma ta xauna, a hankali Imaan ta xamo kasa ta fara cin kazar, sai kallonta Mujaheed yake ta gefen ido, Maimoon ta dau tsoka daya daga kan kujerar tana ci a kunyace, Hajiya tace "To ya aikin doctor, Hajiya Rukayya tace min ka dawo Kaduna da aiki gaba daya yanxu koh?" Yace "Ehh" tace "To da kyau, Allah yayi albarka" yace "Ameen" idonsa na kan wayarsa amma da ya dago sai yaga kallonsa Safeenah take, Hajiya ta mike tace "Toh bari in d'an shiga ciki...." Mikewa yyi da sauri yace "Wucewa xa mu yi ai, xan je gun aiki" tace "Da wuri wuri haka, ka dai ki shan ko ruwa ne kuma ban ji ddi ba" yace "Am sorry bana jin cin komai ne yanxu" Tace "Toh ai sai ka jira kanninka su gama tukun na ko?" Yace "Bana son in makara xuwa gun aiki ne Hajiya" tace "Toh shikenan, bari a masu take away da shi" Imaan tace "Toh" wani kallo Mujaheed ya dinga mata, Hajiya ta kwalo ma mai aiki kira ta sanar da ita tayi masu takeaway din kajin, Imaan ta mike tace "Ina xan wanke hannu" Safeenah ta nuna mata hanyar dinning ko kitchen, tare suka tafi da Maimoon suka wanke hannu suka dawo, Hajiya ta basu dubu biyar Maimoon ta amsa da kyar, tuni Mujaheed ya fice gidan suka bi bayansa, Hajiya ta kalli Safeenah tace "Baxa ki raka su ba" bin bayan su tayi ita ma. Mujaheed har ya shiga mota sai ga ta tare da su Maimoon, tana kallonsa tace "I don't even know ur name" ba tare da ya kalleta ba yace "I am Mujaheed" tace "That's nyc, I am Safeenah" kai kawai ya gyada mata, Tace "Toh sai yaushe?" Yace "Watarana" yar siririyar dariya tayi tace "Do you mind sharing your digit with me pls?" Yace "Ohk" mika masa wayar hannunta tayi ya amsa ya sa mata lambarsa da bai fiye amfani da ba ya mika mata, tace "Thank you" yace "You are welcm" Daga haka ya tada motarsa ya wuce, haka ta bi motar da kallo har ya fita layin, da sauri ta koma ciki tana kallon uwarta tace "Wllh Mum naji ina son sa sosai" Uwar tace "Haba, to ai shine wanda na maki magana a kai kwanaki kika ce ke ba ruwan ki da hade hade in rabu da ke, uwarsa ce dama ta kawo shawarar ba ni ba tunda nasan kina da samari iri iri" ta marairace tace "Mum ai ban san haka yake ba, ni wllh mum ina son sa har raina" Hajiya tace "To ai shikenan, bari anjima sai in kira mahaifiyar tasa dama kwanaki duk ta dameni da kira a kan hakan bana daukan kiranta" Safeenah ta sauke ajiyar xuciya ta xauna tace "kaiii... Ya hadu wllh, his beards are damn cute, his lips so sexy with those catlike eye, gashi dogooo, I guess he have got six packs daga ganinsa yana workout, dama kuma ni bana son namiji fari pau, wllh Mum gayen ya hadu sosai, kuma naga sai wani basarwa yake yana shan kamshi, to ai irinsu nake so" Tun da Imaan taga irin kallon da Mujaheed ke mata bayan sun dau hanya ta kagu su isa gida ta fice daga motarsa tayi ta kanta, gashi dama so take suna komawa gida ta dau Atm card ta tafi supermarket siyo ma Sadeeq abinda ta masa alkawari jiya, a kofar gida Mujaheed yayi parking tana jin ya bude lock din motar ta bude ta fita da sauri, fitowa yayi shi ma bai kai ga bin ta ba tayi tuntunbe bakin gate sai ga ta a kasa, d'agata yyi ta fashe da wani matsanancin kuka tana cewa "Wayyo yaya kafana ya gurde wllh" maidata gun motar yayi fuska daure ya daga kanta yace "Waye kika fita wajensa shekaranjiya da daddare" k'in cewa komai tayi sai kukan da take tana kiran daddy a tsorace, ya wani hade rai cikin tsawa yace "Ba tambayar ki nake ba?" Still taki cewa komai xuciyar ta Sai bugawa yake, murda kunnenta yyi da karfi yace "Are you daft" ta kara rushewa da kuka tace "Don Allah kayi hakuri" yace "Waye shi" cikin kuka tace "Nima ban san shi ba yaya" Ji yake kamar ya sauke mata mari ya dinga mata wani kallo xuciyarsa na tafarfasa, he is just trying hard to control his temper, strictly yace "Toh daga yau Imaan, I mean daga yau.... na sake ganin ki da wani a tsaye wllh sai na kusa sumar dake a gidan nan I promise you that, ba ciwon jiki ko Asthma ba, idan ma jini ke xuba ko ina na jikin ki wllh sai nayi abinda na maki alkawari, ke har guda nawa kike xaki ke tsayawa da namiji jikin mota? How old are you??" Kuka kawai take tana kallonsa duk jikinta na rawa don ta dade bata gansa cikin yanayin nan ba, ya mata tsawa yace "Baxa ki bani amsa ba sai na gaura maki mari?" Cikin rawar murya tace "Ba na kusa 18 ba...." Rankwashi ya kai mata ta dafa wajen tana kiran inna a rikice, yace "In sake ganin ki da wani a waje, sai kin raina kanki wllh" daga haka ya saketa ya rufe motarsa, ta wuce ciki da sauri bata xame ko ina ba sai part din inna, xubewa tayi kan kujera tana rusa kuka, Inna ta fito daki da gudu tace "Na shiga uku me ya same ku a hanya, ko hatsari ku ka yi??" Imaan ta mike xaune cikin kuka tace "Yaya ne ya rankwashe ni kuma ya ja min kunne ni ban masa komai ba innaa" Inna ta xauna kan kujera tayi tagumi a hankali tace "Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, Wannan yaro dai ya isheni a gidan nan wllh, innalillahi wa inna ilaihi raji'un, A kan wani dalilin kuma ya cuce ki, me kika masa?" Xata yi magana sai ga shi ya shigo, kin cewa komai tayi sai shessheka take hawaye na bin kuncinta, inna tayi mitsi mitsi da ido tace "Mujaheed kana manta cewar akwai hisabi koh, kana mance akwai lahira koh, ni ina jiye maka kada wataran ka karasa gawar da ba taka ba a gidan nan, idan abu ya sami yarinyar nan gaskiya xan rufe ido in mance ni na haifi Ahmadu in maka tijara kotu ta raba mu Mujaheed," Yace "Toh yanxu ma ki tashi a tafi kotun mana, duk ke ke karanta mata tsayawa da samari tun bata kai ko ina ba a titi, idan aure take so ae sai ta sanar da Abbanta ayi mata ba ta dinga tsayuwa da maxaje ba tare da saninsa ba, ita har nawa take, ni nasan wlh Abbanta bai sani ba, halan Ummi bata bata labarin abinda na mata kwanaki ba" Inna ta saki baki tana kallon imaan dake shessheka a hankali, can tace "Amma gaskiya ke munafuka ce Imaan, samm baki da hali, banda munafurci ya xa ayi kiyi sabon saurayi amma kiyi ta nuku nuku kina boye min?? me xai bani da Allah bai ban ba, shi kuma gantalallen bai san kakarki na da rai bane da bai taba cewa xai shigo gaisheni ba? Ko uwar ki ce tace ki boye min ban sani ba" Mujaheed ya dinga kallonta da mamaki, rai bace inna tace "Toh ni dai ba ruwana, dama ana boye abun arxiki irin wannan Ashe, me na maki da xaki boye min sabon saurayin ki Imaan?"
20. Imaan
Juyawa Mujaheed yyi ya
fice daga parlon, Imaan ta kyabe baki tana share idonta tace "Shi fa bai
san ko waye doba xai wani dinga ce wa saurayina, ni dai wllh inna ku ce masa ba
ruwansa da ni a gidan nan" inna tace "Atoh dama meye hadin ki da shi,
kawai ni dai nasan ubansa wan ubanki ne kuma duk ni na haifesu, to bayan wannan
bbu abinda ya hada ki da Mujaheed ba dangin iya balle na baba, ke dai kawai ki
rabu da shi ya ji da wawancin sa kiyi ta kan ki, banda fitina ma ina ruwansa da
lamarin rayuwarki, idan ma saurayin kika yi baki isa ba ne, ko idan kin rasa
mijin aure astaghfirullah shi xai aure ki ne?? kar ki sake saurarensa duk
saurayi ya kira ki shirya ki fesa turare ki tafi, wa xai xauna biye ta Ahmadu
da Bukar ga d'an su ma ya dauko hanya, bokon jaraba kawai ni wllh kina gama
sakandari aurar da ke xance ayi mijin yaji da lalurorin ki d'a na ya huta haka
shi ma" imaan ta mata wani kallo ta mike tana goge guntun hawayenta ta
fice a parlon. Da yammacin ranan daddy ya gama shirin komawa Abuja ya tafi yi
ma Inna sallama, ta gama goge gogen da ta ke ta dawo ta xauna tace
"Tafiyar na nan yau din kenan" yace "Ehh, jirgi xan bi kada
jirgin ya tashi ba ni" inna tace "Toh Allah ya tsare, amma xaka tafi
kuma ya xancen da ku ka min kai da Ahmadu jiya?" Daddy yace "Na me
fa?" Inna tace "Tafiyar yaran nan su je gaida Hansatu mana"
Daddy yace "Ehh Barrister yace xuwa satin da xa a shiga sai su tafi"
inna tace "Ehh gwara su je, duk da dai uwarta axxaluma ce amma ina mata
fatan Allah ya ji kanta na kuma yafe mata, amma gaskiya shari'ar mu sai a
lahira, don ta cutar da ni...." Daddy yace "Haba inna, bayan kuma kin
ce kin yafe" a fusace inna tace "Toh ai Allah ba axxalumin bawansa
bane, don na yafe ai a duniya nake nufi ba a can ba, kai baka san komai ba
wllh, kaga irin abinda uwarta tayi min ne, kishi dama hauka ne, ni dai kawai
albarkacin marigayin uban ku yasa nake barin ayi xumunci da 'ya yan da ta mutu
ta bari ma, kuma duk yaran ba xuwa gaida ni suke ba" Daddy yace "Ke
fa kika ce kin yafe xuwan, kowa ya xauna inda yake" Inna tace "Toh
idan bance haka ba ya kake so ince, kai so kake su xo su sa ma kai da d'an
uwanka ido, yanxu da ake nisa nisa ba ya fi ba, babu wanda yasan halin da wani
ke ciki, sai ku dinga wata magana kai da Ahmadu don ba ku aka cuta ba, yanxu
kishiyoyin da bani da hakkinsu ba gashi duk sun mace sun bar 'ya ya duk a
gantale ba, to me xa su xo su min bayan ga nawa 'ya yan... Ku uku wllh kun
isheni xaman duniya ita ma Hadiza tace ta kusa dawowa kasar nan gaba daya, to
me xai dameni, a hada masu goma ta arxiki aje dai a gaishesu, har shi wancan
katon Balan dake Abuja su karasa su gaida shi, ba komai Allah ya ba mu lada su
kuma aniyarsu ta bi su" Daddy yace "Bari in je inna, Mujaheed xai
kawo maki sako anjima" tace "Toh Allah ya tsare, yayi maka albarka,
ya kare ka duk inda xaka shiga" yace "Toh Ameen nagode" daga
haka ya fita parlon, part dinsa ya tafi suka yi sallama da Ammi yace "Gobe
dai Imaan ta tafi islamiyya, xuwa Wednesday nasan xa su yi tafiyar, before than
Dr dinta xai kawo mata drugs dinta coz ya dawo" Ammi tace "Toh Allah
ya kiyaye hanya ya tsare, ko in taso ta?" Yace "A'a bar ta" daga
haka ya nufi kofa ya fita, Yusuf ne ya kai sa airport. Mujaheed ya daga kai
yana kallon Abbansa bayan ya gama maganar da yake, a hankali yace "Abba
kaga ba a dde da transferring dina nan ba da har xan fara daukan leave gun
aiki...." Abba yace "You are just lookin for excuses, na lura gaba
daya baka son tafiyar Muhd" ya sunkuyar da kai yace "A'a ba haka bane
Abba, kawai naga...." Abba ya dakatar da shi yace "Toh xan ma boss
din naka magana" da sauri ya dago yana kallon Abba amma bai ce komai ba,
Abba yace "Beside idan ku ka tafi Wednesday xuwa Friday ai kun dawo, nan
nan sulejah dai" Mujaheed bai ce komai ba still, jin Abba ma yyi shiru
yace "Toh Abba kasan yanayin jikin Imaan, har da ita xa mu je?" Abba
yace "Toh ba ga ka ba, you just go with first aid box" Mujaheed yace
"Toh shikenan" Abba yace "And ina son dama muyi wata magana
Mujaheed" Mujaheed yace "Ina ji Abba" Abba yace "Its high
time you think of settling down with a family Muhd, naga baka san shiru ba kai,
idan na kyale ka a haka xa ayi ta tafiya, duk abokanka sun yi aure with kids,
not even kid, to kai me kake jira son?" Ya shafa kai a hankali yace
"Abba warce nake nema tana karatu ne, amma ta kusa karewa nan da 'yan
watanni in sha Allah" Abba yace "Yar ina ce?" Ya d'an yi
murmushi yace "Nan Kaduna, a hayi iyayenta suke amma tana gun yayarta a
Unguwar sanusi" Abba yace "Toh maa sha Allah, hakan yayi kyau sosai,
but I think it's better a fara magana tun yanxu...." Muryar Umma suka ji
tace "Babu maganar da xa a fara Alhaji" duk suka daga kai suna
kallonta ta karaso cikin parlon, bacin rai karara fuskarta tace "Yanxu ni
xaka munafurta Mujaheed, haka muka yi da kai, to kasani wllh idan ina numfashi
a doron kasa baxa ka auri yarinyar nan bar, idan kuma kana son ganin ba dai dai
ba a lamarin ka kaci gaba da alaka da matsiyaciyar yarinyar, ina zamana ka
dauko mun talauci a matsayin surka, to wllh kayi kadan gwara kayi ta xama ba
auren ya fi, ga yarinya mai hankali mai natsuwa Safeenah yar wajen Hajiyan
Marafa can na nema maka yarinyar kuma tayi mugun na'am da kai xaka toxarta ni
ka maidani karamar mutum a idonsu???" Abba yace "Abinda nake son in
fara fahimta a nan shine, la6e kike min Rukayya?" Umma ta tabe baki tace
"Idan ma la6en nayi Allah ne yasan bani da hakkin kowa shi sa har ya bani
ikon labewan in ji komai, Alhaji wato idan Kasan talauci to a kan yarinyar da
iyayenta ya kare, can wani ghetto fa suke, to idan ba toxarta mu Mujaheed ke
son yi a idon jama'a ba ina shi ina yarinyar nan, Kyan banxa kyan hofi, yo ina
ma take da kyan ita ba wai fara ba, gaskiya kayi min iyaka da Mujaheed kada in
nuna masa 6acin raina a gidan nan, sam baxai ji da dadi ba, shi baya koyi da
d'an uwansa Yusuf, dubi fa yarinyar da yake nema yar attajiri gashi har magana
yayi nisa, sai ni ce Mujaheed xai cuta ya kwaso min yar talakawa" Abba ya
girgixa kai yace "Halan ke ke raba talauci da arxikin Rukayya?" Umma
tace "Ba ruwana da wannan xancen ni dai gaskiya idan Mujaheed bai yi
hankali da ni ba xai sha mamaki, kuma in dai baxai bi ni sau da kafa ba xai
dinga ganin ba dai dai ba a lamarin sa ni dai ba ruwana" tana kai wa nan
ta fice fuuu, Abba ya girgixa kai yace "Look son, ba ruwanka da wannan
uwar taka, ba isasshen hankali gareta ba am giving u my words, ka ci gaba da
neman yarinyar, Allah ya shige mana gaba" A hankali Mujaheed yace
"Ameen" Abba yace "You can go" ya mike yace "Nagode
Abba" daga haka ya fita parlon. A hankali Ammi ta bude kofar dakin Imaan
tana kallon ciki jin dariyar da take cikin duvet, da sauri Imaan ta katse wayar
ta tura karkashin pillow jin kamar an bude kofa, Ammi ta kunna wutan dakin tace
"Da wa kike waya Imaan?" Bude duvet din tayi kamar mai bacci ta mike
xaune tace "Na'am" Ammi ta mata wani kallo tace "Baxa ki amsa
min tambayata ba, da wa kike waya nace?" Shiru tayi tana kallon Ammi kamar
xata yi kuka, Ammi ta karasa kusa da gadon tace "Bani wayar" ba musu
ta ciro wayar ta mika ma Ammi, Ammi na kallon call log tace "Number waye
wannan din" murya can kasa Imaan tace "Abokin ya Muhsin ne" Ammi
tace "Me ya hada ki da abokin Muhsin, a ina kika san sa?" Tace
"Ammi yana xuwa gidan gwaggwo kuma kanwarsa classmate dita ce, yanxu ma
kawai tambaya ya kira ni yake min ba wani abu ba" Ammi ta dinga mata wani
kallo, ta sunkuyar da kai, Ammi tace "Ke dai kin iya munafurci" kamar
xata yi kuka tace "Ammi ni wllh dai ya kira ni ne amma ba komai fa"
Ammi tace "Toh yayi kyau, ki bude kunne sosai ki saurareni, kada ma ki
nuna nasan kina waya da wani a gidan nan don ba ruwana, duk ranan da Daddyn ki
ya kama ki dama ki tanadi abun gaya masa don't involve me in this" tana
kai wa nan ta fice dakin. Washegari da rana Ammi na xaune parlor Imaan ta fito
sanye da Hijab sai karamar jakarta da ta rataye, Ammi na kallonta tace "Ina
xa ki?" A hankali tace "Ammi xan je in siyo cream a supermarket"
Ammi na kallonta da mamaki tace "Yaushe na siyo maki da har ya kare
Imaan?" Shiru tayi tana kallon Ammi kamar munafuka, Ammi tace "Shan
cream din kika fara?" Tace "Ammi shafawa kawai nake yi fa" Ammi
ta tabe baki tace "Toh ni kam bani da kudin cream yanxu" tace
"Ai ina da kudi a account dina" Ammi tace "Toh Hajiya mai kudi,
a dawo lafiya" yar dariya tayi ta sa flat shoe dinta ta fita parlon, kamar
mai tausayin kasa ta taka har bakin main road inda xata samu adai daita, jin
wayarta na vibrate a jaka ta fiddo, Sadeeq ta ga ke kiranta, ta daga ta kai
kunne, Cikin cool voice dinsa yace "How r you Imaan?" A hankali tace
"am fine ina yini?" Yace "Lafiya lau, kina hanya ne?" Tace
"Ehh" yace "Ina xa ki?" Ta d'an yi shiru kafin tace
"Xanje supermarket" yace "Wanda muka hadu ranan?" Tace
"Ehh" yace "Tell me what you want to get sai in siyo in kawo
maki yanxu" da sauri tace "A'a bana so" a hankali yace
"Why?" Tace "Ni dai bana so, yanxu ma xan hau adai daita
ai" yace "Toh shikenan, we will talk later, Allah ya tsare" tace
"Ameen thanks" daga haka ya katse wayar ta samu adai daita ya kai ta
har mall din, wani babban boutique dake opposite mall din ta shiga, gun
eyeglasses ta tsaya tana duba glasses masu kyau shigen irin wanda yake sa wa,
ta wara ido ganin the prices are waoww, wani da ya mata kyau sosai ta dauka
tana dubawa kafin ta tafi gun da ake biyan kudin kayan ta basu atm suka cire
kudinsu suka mata packaging din eye glass din ta fita ta tsallaka ta shiga
cikin mall din, gun body creams ta tafi ta dau cream da take shafawa duk da
akwai mai yawa a gida, kawai dai ta juye a wani container ta boye ne sanin Ammi
na iya shiga daki ta duba bayan ta taho, bayan ta dau cream din xata juya ta
kusa cin karo da mutum, komawa baya tayi da sauri da nufin basa hakuri, sai
kuma ta xaro ido da mugun mamaki tana kallonsa, murmushin da ya bayyana dimples
dinsa yyi yace "Sorry" ta sunkuyar da kanta yace "Har kin gama
shopping din ko yanxu kika fara" ta dauke kai tace "Na gama"
yace "Toh mu je ki rakani I want to get somethings" Daga haka ya fara
tafiya, bin bayansa tayi kamar munafuka, gun kayan ciye ciye su chocolates,
biscuits sweets da dai sauransu ya tafi, yana kallonta yace "Kanwata xata
yi birthday gobe, so nasan dai ku mata babu abinda ku ke so da ya wuce wannan,
am asking for a favor duk abinda kika san kina so ki daukar mata nasan ita ma
xata so" Murmushi tayi tace "Ohk then" nan ta dinga jidan duk
abinda ya kwanta mata take mugun so kuma, ya dinga tura trolley din yana biye
da ita, xaro ido yyi yace "Anya imaan wannan banda mugunta kuwa, yanxu duk
wannan abubuwan da kike dauka kina nufin kina son su?" Ta juya ta wara
masa manyan idonta tace "Ai duk abinda kaga na dauka a nan I love it with
all my heart, baka san yanda nake son chocolates da sweets ba koh"
murmushi yyi yace "Toh mu bar mata su a haka" tace "A'a jira ga
wani chocolate can..." Da sauri ta tafi ta debo har biyar ta xuba a
trolley, ta kwaso wasu biscuits ma ta xuba, ta dau wani sweet ta xuba shi ma,
ta juya tana kallonsa tana murmushi tace "Toh ni dai ina mugun son teddy
in daukar mata" ya langwabar da kai yace "Kawai so kike account dina
yayi kuka yau koh??" Ta hade rai tace "Just guda biyu ko uku fa, Is
she not ur sister? And is it not her birthday" daga haka ta tafi gun
teddies ta debo uku masu tsada da kyau ta jefa cikin trolley din tace
"Tunda kana complaining account dinka, mu bar mata su a haka kawai"
Yar dariya yyi yace "Noo ci gaba har sai kin gaji" tace "A'a I
have conscience" dariya yyi ya bi bayanta ganin ta nufi gun counter, cream
dinta ta ajiye xata bada ATM card ya riga ta mika nasa, juyawa tayi tana
kallonsa sosai gabanta ya fadi bayan sun hada ido tayi saurin sunkuyar da
kanta, nan aka cire kudin aka bata receipt dinta, ta taya sa ciro abubuwan
cikin trolley din shima ya bada atm card aka cire aka masu packaging, barinsa
tayi da kayan gaba daya ta dau teddies din suka fita. Bayan ya xuba ledojin a
bayan mota ya rufe motar yana kallonta kafin yace komai tace "Yau ne
birthday din?" Gyada mata kai yyi smiling, ta boye fuskarta a hankali tace
"Toh ni dai ina son kaza ko xaka siya mata" Wara ido yyi yana
kallonta, sai kuma yyi dariya yace "Ina kika ga kaxa imaan?" Ta turo
baki ta nuna masa inda ake gashin kaji, yana murmushi ya tafi, ya siyo kajin
gasassu biyu ya dawo ya sa a mota, ya juya yana kallonta pleadingly yace
"Let me drop you plss" da sauri tace "Nooo thank you" tana
fadin haka ta bude karamar jakarta ta fiddo glass din dake leda tana kallonsa
ta mika masa, a hankali ya sa hannu ya amsa yana kallon kwayar idonta, hakan
yasa tayi saurin sauke nata idon, bude ledan yyi ganin glass din underneath his
breathe yace "Waow..." Murmushi tayi xata juya masa baya ya riko
hannunta cikin sanyin murya yace "Thanks Imaan, I love it..." Bata
ankara ba sai gani tayi yyi pecking hannunta, ta kwace hannun da sauri tana
xaro ido a tsorace, shi ma daburcewa yyi yace "I... Sorry I.. I am just
happy imaan, I love the glasses" ta kirkiri murmushi har sannan tana jin
warm lips dinsa a hannunta, xata juya yace "Wait Imaan" tsayawa tayi
gabanta na faduwa, ya bude front seat yace "Plss let me drop you
home" kasa ci gaba da kallonsa tayi ta kuma kasa cewa A'a, a hankali ta
shiga motar yyi murmushi ya rufe, ya xaga ya shiga driver seat suka bar mall
din, bata yrda yaje dai dai gate din su ba tasa ya ajiye ta few houses away
from theirs, ta bude motar ta sauka shi ma ya sauka ya xaga ya bude back seat,
ya fiddo gaba daya ledojin siyayyar da suka yi da teddies da kajin duk ya ajiye
kusa da ita ya wara ido yana mata murmushi yace "Dama duk naki ne"
bai jira cewarta ba ya xaga ya shiga driver seat ya tada motar ya bar ta da
zare ido ya bar layin, kallon ledojin ta dinga yi kamar xata yi kuka, yanxu ya
xata yi da kayan nan.... Kwasa tayi ta boyesu cikin flowers ta dinga dauka da
daddaya da daddaya tana kai su part din inna, duk a mugun tsorace take, Inna ta
saki baki tana kallon kayan, imaan ta tafi dauko last ledan, Yusuf dake ta
kallonta tun shigowarta na farko ya mike ya isa kusa da ita da mamaki yace
"Daga ina kike wannan saurin hakan Imaan, what's all this u are taking
in" kin tsayawa tayi tana kirkiran murmushi ta wuce sa da sauri, tsoronta
daya kar ta gamu da Mujaheed, har dai ta isa parlon inna, Inna dake tsaye bakin
kofa har lkcn ta sake baki tana kallon uban ledojin ta bi ta da kallo har ta
ajiye na hannunta, Inna tayi kasa da murya tace "Imaan ina kika samo
wannan kuma?" Imaan ta kwashesu gaba daya ta kai dakinta da sauri duk ta
ajiyesu sanin Yusuf xai iya biyota, Tana fitowa dakin tace "Ni dai kawai kiyi
shiru inna kar ya Mujaheed ya sani wllh duka xai min" Inna ta hade rai
tace "Duka?? da kuwa ya dokar ma kansa fitina da bala'i, kuma da karshen
xamansa ya kama a gidan nan" Imaan ta xauna saman kujera har sannan
gabanta bai daina faduwa ba, Yusuf ne ya shigo parlon, inna ta wani tsuke
fuska, yana kallon Imaan yace "Daga inna kike Imaan?" Inna tace
"Yau naga jaraba, to ina ruwanka isuhu ko ka aiketa ne? Ku dai 'ya yan
Ahmadu ku daina sa ido wllh, meye kuma wani daga ina take kamar xamanka take a
gidan, ni dai ba ruwana, ku dinga tsoron Allah kuyi mai fishshe ku a gidan
nan" juyawa Yusuf yyi ya fita parlon, inna ta kulle kofarta ta sa makulli,
ta kalli imaan tana murmushi tace "Kar dai sabon saurayin ne yyi maki uban
siyayyar nan takwara" Imaan tace "Wllh kar ki gaya ma kowa idan ba
haka ba kazar ma baxan tsam maki ba" Inna tace "Ke ma dai da wata
magana wllh, sai kace wata yarinya?? Wa xan gaya ma ni patuu, wannan ai sirri
ne tsakaninmu" Imaan ta shiga ta fiddo ledan kajin guda biyu tace
"Toh idan yaya ya shigo fa?" Inna tace "Oh oh Allah, waye kuma
wani yaya, ina ruwana da shi, ko me xai xo ya min? Ko ya xo ma ni baxan bude
kofata ba bbu ruwana, idan ma ya xo damuna yake ba abinda yake tsinana
min"
Post a Comment for "IMAAN 19-20"