Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

IMAAN 17-18

 

17....

Imaan dai na tsaye har ya gama wankin bedsheet din tana rike da kayan da ta cire, ya saka xanin gadon a bucket ya fito, a hankali tace "Yaya to wankin bayin fa?" Wani mugun kallo ya watsa mata ya dau wayarsa da makullin mota da ya ajiye kan gado zai fita ta xaro ido tace "Yaya don Allah ka tsaya, baxan iya shanya bedsheet din ni kadai ba ai" ko juyowa bai yi ba balle ya tanka ta, a bakin kofar parlor ya hadu da Inna, Inna ta gwalo ido tace "Har an wanke min bayin?" Yace "A'a xan fita in amso Hypo ne" yana magana ne yana kokarin fita, inna ta cakumosa tace "Sai dai ka raina ma Bukar ko

Ahmadu hankali, ce maka nayi bani da hypon?" tana fadin haka ta ja sa xuwa bedroom din fuskarta daure, yace "Toh ki sakeni mana" ko saurarensa bata yi ba har suka shiga dakin, Imaan dake labe bayan kofar dakin tana jin sun shigo dama ta fito da sauri ta fice a dakin, Har bandakin Inna ta turasa ta dauko Hypo biyu ta jefa masa, yace "Biyar fa kika ce Inna" a fusace tace "Toh ai ni ba asararriya bace Mujaheed, Ko sisin Bukar da Ahmadu babu a Hypon, Isuhu ne na roka ya siyo min" tana fadin haka ta dau ledan omo babba ta jefa masa tace "Har jikin tiles ni dai a gurje min ba ruwana, kuma daga yau gaskiya idan Imaan ta sake shigo min daki xa a ga bala'i, wato kawai fasa bomb din bala'i xanyi a gidan nan, naje yanxu uwar bata nan, da sai in ji ko ita ta turo min ita ta cuce ni ta xuba min al'adarta, banda ma kazanta irin na yaran ynxu duk sai sun bari kowa ya san suna al'ada, gantalalliyar duk ta tashi ta kazance min kan gado da bandaki, to hirrr dinta kada ko da wasa ta sake leko min daki ta tsaya iya falo, idan kuwa dama bata da tsarki kar ta yo min nan xan koreta don parlona na tsarkakakku ne" Mujaheed dai bai tanka ta ba ya nade sleeve din shirt dinsa ya fara wanke bayin bayan ya kada kumfa da hypo, inna tace "A'a bana son aikin al'gus malam, ka kara barbade bandakin da omo lungu da sako sai ka juye dayan hypon" ya jefa mata wani kallo yace "Toh wai ni na bata maki bandakin daga taimako kawai" Inna tace "A'a ba ruwana saboda kai na bude, in don ta wancan matar ce ai sai dai ta tafi bangarensu jage jage da jini don wllh baxan bude ba, haka kawai" ko kallonta bai yi ba ya ci gaba da wankin bayin da babu abinda ya samesa, haka inna ta dinga basa wahala tana tsaye daga bakin kofa tace can tace nan, har daga karshe aka gama wanke bayin, ya wanke hannunsa ya fito fuska daure, tace "Toh don Allah ni dai kar in kwana cikin k'arni yau ka taimakeni ka fidda min katifar can ka ajiye dai dai idon rana" yace "Wannan kuma sai dai ki kira Yusuf baxan iya ba gaskiya" Tace "Toh wllh baxa ka fita dakin nan ba sai tare da katifar nan, haka kawai in kwana cikin najasa, kafar ka kafar katifan" tana fadin haka ta sa makulli a dakin ta tsaya bakin kofa, kallonta ya dinga yi fuska daure, inna tace "Oho dai duk kanwarka ta ja maka, ita yanxu ba gashi ta gudu ta bar ka da aikin jini ba, yarinya sai mugunta fal cikinta" Babu yanda ya iya haka ya cire katifar ta bude masa kofa tace "Saitin rana xaka ajiye duk ya kona abinda ya xuba kai" fita yyi da katifar ya ajiye inda tace, ya dawo dakin don daukan wayarsa da makulli, ganin babu su a inda ya ajiye ya kalli inna dake tsaye tana kallonsa kyarr, bucket din xanin gadon ta nuna masa tace "Idan ka shanya wnn sai ka dawo ka amshi wayar ka da makulli ba ruwana, yarinya dai ta cuce ka kawai, sae dai sakayyar Allah" tana fadin haka ta koma parlor, Mujaheed ya fi minti uku a tsaye, yasan ko me xai ce mata baxata basa ba, hakan ya sa ya ja tsaki ya dau bucket din fuska daure ya fice dakin, yana gama shanyawa a nan parlorn ya ajiye mata Bucket din yace "Bani wayana in wuce" ta jefa masa makullin siff dinta tace "Ka bude ka dauka ka rufe min kayana" daukan makullin yyi ya koma daki ya bude yana daukan wayarsa da car key ya bar mata siff din a wangale ya fice kamar xai tashi sama, inna tace "Oho dai....." Dab da Magrib Ammi ta shiga tada Imaan dake ta bacci tun bayan da ta kara shan magani, Ammi tace "Ya jikin?" A hankali tace "Da sauki, Ammi Daddy ya dawo?" Ammi tace "Ehh ya dawo" wara ido tayi ta sakko kan gado ta sa Hijab har ta isa kofa ta tsaya ta juyo tace "Ammi hope bak'in duk sun tafi?" Ammi tace "Ina kuwa xa su gobe biki?" Imaan tace "Toh daddy yana bedroom dinsa ne?" Ammi tace "Aa ina jin suna can tare da Abba" Imaan na sa takalminta bakin kofa aka bude kofar parlon, d'aga kai tayi taga Inna ce, Inna tace "Ya jikin, na ji shiru tun daxu baki leko ba shine nace bari in lallabo in xo in duba ki, kun je asibitin ne?" Imaan da ta hade rai ta ki kallonta tace "Ni na ji sauki" inna ta amsa gaisuwar masu gaisheta a parlon sannan ta kalli Imaan tace "Tohhh, Allah dai ya sauwake, amma wannan wahala ba gwara Bukar ya aurar da ke ba kowa ma ya huta kema ki huta" Ammi dake tsaye tana jin su ita ma ta gaida inna, inna tace "Lafiya lau Aisha, in ji mai gidan ya dawo lafiya?" Ammi tace "Alhmdllh" Inna tace "Toh da kyau, duk da dai ni ko tsinke ba a kawo min a tsarabar da yake yowa, sai dai ke da yar ki ku cinye, to duk ba wannan ba don bai dameni ba wanda Ahmadu ma ke bani Allah ya amfana, yanxu dai xuwa nayi in duba jikin Imaan, ta xo daxu tana ciwon mara ban kai ga jik'a mata ararra6i ba na nemeta na rasa" Ammi tace "Ta ji sauki yanxu, sai dai ko ta bi ki ta amsa ta sha a can" inna ta gwalo ido da sauri tace "Ta bi ni ina? A'a ta xauna xan lallaba in koma in jiko mata in kawo yanxu, ta bi ni kuma ana xaune kalau? Taje ta min me kuma ban da abun ki Aisha yarinya na fama da kanta, Aa bari inje in dawo yanxu, dama na bar sauran tsoffin da basu tafi ba kada a min barna" daga haka ta juya ta bar bakin kofa murya can kasa tace "Haka kawai ta sake koma min ta min wani aika aikan da kazantar ta a gida ta cuce ni, wa gareni da xai bi min hakkina ban da Allah" Imaan ta turo baki ta fita parlorn ko da wasa bata fadi ma Ammi abinda ya faru daxu ba, part din su Maimoon ta nufa, kasa shiga parlon tayi ganin mutane a ciki, ta fi minti biyar tsaye bakin kofar taji muryar Yusuf yace "Me kike yi nan Imaan" kallonsa tayi tace "Toh akwai mutane a parlon ta ya xan shiga" tana magana tana kallon Mujaheed da ya wani hade rai don tare da Yusuf suke, dauke kai tayi bata son tayi dariya, can ta turo baki ta bar bakin kofar ya shiga ciki, Yusuf yace "Toh ko in maki jagora?" Dariya tayi tace "Daddy na yana parlon Abba?" Yusuf yace "Eh mana" tace "Toh oya ka shiga gaba sai in bi ka a baya" a haka suka shiga parlon tana boyewa a bayansa wanda hakan yasa few kawayen Umma dake parlon suka dinga kallonta har suka shiga parlon Abba. Da gudu ta tafi ta rungume daddy tace "Daddy sannu da dawowa" Daddy yace "Baki gaida Abba ba" kallon Abba dake kallonta tayi, ta boye fuskarta tace "Ina yini abba" yyi murmushi yace "Lafiya lau daughter" Daddy yace "Toh baki gaida yayanki ba shi ma" ta kalli Mujaheed dake parlon tace "Ai mun hadu a waje" Daddy yace "Toh maa sha Allah" Tace "Daddy baxan je gombe Hutu ba tunda mun yi holiday?" Abba yace "Wajen wa a gombe" murmushi Daddy yayi yace "Kanwar mamarta" Abba yace "Ohk If I recalled well last holiday ma can kika je ko" Kai ta gyada masa, Abba yace "Kuma babu canji, ga gwaggon ku Suleja ma ba sai ki je can ba ko da su Maimoon, dama bata da lafiya" Daddy yace "Gaskiya ne ya kamata" Imaan ta xaro ido tace "Kauye?" Abba yace "Of course, you will have more experience.... Shi kauyen ba wuri bane" Ta dauke kai bata ce komai ba ta cinno baki gaba, Abba yace "Nasan inna xata ji dadi idan taji xa ku je, kinga sae Mujaheed ya kai ku a mota tunda ya sha xuwa tare da mu" Da sauri Mujaheed ya kallesa yace "Abba... ai ba lalle xan gane wajen ba fa" Abba ya kallesa yace "Last time ma ba kai ka kai mu a mota ba" da kyar yace "Abba kusan shekara daya fa" mikewa Imaan tayi ba tare da ta kallesu ba tace "Xan je ina taya Ammi aiki" bata jira cewarsa ba ta fice, Abba yayi dariya yace "On a serious note dole su je riga suyi hutu bari dai a gama bikin nan lafiya" mikewa Mujaheed yyi yace "Xan je ana kirana can waje" daga haka ya fice a parlon, Daddy ya gyada kai yana murmushi yace "Su masu wayo wai, gaskiya ne ya kamata su kai ma Hansatu ziyara tunda gashi bata samu xuwa biki ba ba lafiya" Abba yace "In sha Allah I will see to that on Tuesday if everything is settled"  Daddy yace "Alhmdllh, Allah ya kai mu lafiya" Washegari Friday bayan an sakko juma'ah aka daura auren Seeyama da angonta Abdul, throughout shagalgulan da ake a gidan imaan na dakinta tana bacci ko ankon bikin bata sa ba, Ammi bata takurata ta shiga jama'a ba sanin cewar bata wani jin dadi, kuma dama bata son tayi stressing kanta ta jogana masu wani ciwon, sai dab da xa a tafi da Amarya Ammi ta tasheta don tun daxu Inna ke cigiyarta, sai a sannan imaan ta shiga bayi tayi wanka ta wanke baki ta fito ta shirya cikin daya daga ankon da suka yi, ta d'an shafa powder tasa eye pencil da chappette, sannan ta dau farin hijab har kasa ta saka ta dau wayarta, ganin missed call ta tsaya ta duba, Sadeeq ne ya kirata, komawa tayi ta xauna tayi dialing, katsewa yyi ya kirata, bayan sun gaisa yace "Ina kika shiga yau" tayi murmushi tace "Bacci" yace "Uhm baki da damuwa, ya su mama?" Tace "Alhmdllh" yace "Daxu Mariya tace min kuna biki gidanku" tace "Ehh haka ne" yace "Shine ba gayyata?" Tace "Uhmm" yace "Toh kin kyauta" a hankali tace "Kayi hakuri, next time" yace "Toh waye next din auren? Ko ke?" Ta xaro ido sai kuma tayi dariya tace "Ni kuma, yar yarinya da ni" yace "Haba?" Tace "Ehh mana" yace "How old are you?" Ta langwabar da kai tace "Na kusa 19 soon" dariya yayi yace "Ehh gaskiya ne, ke yarinya ce sosai ma" tace "Toh kaga" yace "Ko aure aka maki yanxu ma baxa ki haihu ba ai" ta xaro ido sai dai bata ce komai ba tayi murmushi, yace "Yeahh" tace "Xa mu je raka Aunt dina dakinta yanxu" yace "Wani anguwa ne?" Tace "Ban sani ba dai" yace "Toh idan kun je gidan ki kirani" tace "Toh in sha Allah" sallama yayi mata ya katse wayar. Inna ce tsaye tsakar gida ta cakare cikin atamfa England an mata dinkin su irin na tsoffi, ga katon gyalenta ta yafa, ga mutane duk ana ta shirin xa a wuce da seeyama gidanta, motocin dake compound din sun fi shidda duk na daukan yan kai amarya, tun daga nisa Imaan ke jiyo Inna ta tana cewa "Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, duk an wani yi cirko cirko a gaban motoci ku ja baya mana kar ku gurje masu dukiya in shiga uku, ni wllh saboda bala'in mata ma duk xafi ya isheni abu kamar maita dai, ke Maimuna ba ca nayi ki dubo min Imaan ba ko har yanxu jinin bai dauke ba ne, duk yau ban ganta cikin jama'ah ba ko bakin ciki take ma yar uwartata ban sani ba" Imaan ta turo baki bayan sun hada ido da Innar, inna ta ja tsaki tace "Kai ni dai ko limamin babban masallacin Habuja ne Bukar yau dai baxai hanaki sa gyale ba, duk yan uwanki ga su fess cikin gyale ke ko kin maka hijabi uwa xamu je xaman makoki ba amarya xa mu kai ba haba imaan, ni dai na gaji da maganar ki a gidan nan" Imaan ta dauke kai har ta iso gun motar, wata kawar Umma ce ta xo tayi announcing wai Umma tace wasu su fara tafiya kafin a fito da amarya, nan aka fara kokarin shiga motoci, inna ta bude baki ta gwalo ido ganin wata katuwa cikin shiga ta alfarma da gwalagwalai na kokarin shiga daya daga motocin, cikin daga murya tace "Wayyo meye wannan kuma... Kee don Allah ki bar sirara su shiga, banda neman magana da tsokanar fada ina xa a dake a haka, kisa kike son yi cikin motar fisabillahi, wannan ai sai dai idan ke kadai xa aje a ajiye a dawo to ina kuma hakan xai yiwu tunda motar ba taki bace, fito don Allah mutane su shiga" Imaan ta boye fuskarta da Hijab kar tayi dariya, mutanen wajen wasu sai dariya suke kasa kasa, matar ta fito kamar warce ruwa ya cinye kanta a kasa, inna ta karasa kusa da ita tana kallonta tace "Haba baiwar Allah... ke ba kya tsoron Allah ne wannan abu haka kinyi wani bake bake bayan motar mutane, ina kike son a xuba sauran jama'a, ko ke baki ga irin ki bane" Wata mata ta karaso kusa da Inna tayi kasa da murya tace "Hajiya babban kawar uwar amaryar ce fa" inna ta bude baki tace "Babban kawar uwar amarya kuma sai a sa mata ido ta latse hanjin 'ya yan mutane a bayan mota, dama kisan kai ya kawota ba biki ba, wannan abu kamar giwa kice ta shiga mota, amma bakya tsoron Allah wllh" sum sum matar ta bar wajen, Inna ta ja tsaki tace "Kai sirara su shiga a wuce, ba ruwana a aje a tatse hanjin mutane daga kai amarya ace bikin jikata ga abinda ya faru, to banda gwalagwalan ma duk karya ne ya xa ayi kamar ta ace bata da mota, ke kuma imaan ga motar da xa mu shiga can da Seeyama nace ban son tukin kowa sai na Mujaheed haka kawai mahaukatan abokan angon su ja mu su watsar da mu a rami" Bude motar Imaan tayi ta shiga back seat tana murmushi, Maimoon xata shiga inna tace "Toh ina kuma wancan figaggiyar xata shiga ni patuu, ba ga motoci can ba" Maimoon ta sauka da sauri, Imaan ta dinga dariya har da kyakyatawa, Kamar yanda inna tace Mujaheed ne ya ja su, ita, Seeyama da kawayenta biyu sai Imaan, suna hawa main road inna tace "Toh yau dai Seeyama gashi xa mu kai ki dakin ki, duk da dai mijin naki wani ga6o ga6o ne kiyi masa biyayya iya yanda xa ki iya, ni baxan ce kiyi hakuri yaje ya kashe mana ke ba gaskiya, bbu xancen xaman hakuri, mu dai da aka cuta da hakan aje a haka, amma duk kika ga abinda baxa ki iya dauka ba yafa gyalenki ki dawo gida, ko ki tafi sashin ubanki ko ki tafi sashin kaninsa ko kuma ki yo sashina sai iya Inda karfin mu ya kare na kwatar maki hakkin ki, ni fa tun daga lefen da ya hada maki dama na raina masa aji...." Mujaheed da takaici ya ishesa yace "Haba inna yanxu fada kike mata ko hudubar tsiya?" Inna ta hade rai tace "Ka ji min yaro da aka haifa ina tsaye bakin kofar asibiti daga safe har dare, kai xaka koya min xaman duniya Mujaheed, ko ance maka ban san abinda nake bane, to bari kaji ko kai yau aka daura ma aure iyakar abinda xan gaya ma matar kenan don ni yar gaskiya ce, akan me xa ayi ta wani ce ma mace tayi hakuri gidan miji ana cutarta ana musguna mata, Allah kadai yasan me yasa ya halitto ni a mutan da ba na yanxu ba, kuma ai bance kada tayi masa biyayya ba kawai idan taga xai takata ta gudo gida, ina laifin wannan shawara tawa??" Kawayen Seeyama dai sai kallon inna suke k'asa k'asa, inna ta ja tsaki tace "Tun da shaidan duk na makale gefen xuciyar ku ba dole kaji haushin abinda na fada ba, maxa dai sun xama masifa yanxu, duk halinku daya dama, yo banda halinku daya ya wuce idan yace xai walakanta maka kanwa ka matse gantalalle ka nakada masa duka tunda ga irin sa kamar tsinken sakace, wllh xaka iya dukansa" Seeyama dake hawaye cikin gyalenta ta fashe da dariya, imaan na taya ta, shi dai Mujaheed bai ce komai ba yana mamakin warce Allah ya basu matsayin kaka.....

 

 

*The book Imaan is not free, you read for free ur cup of coffee wllh*🤷🏻‍♀️

 

It's 300 via Fcmb 3276052019

Hauwa Bello Jiddah

 

Then u show ur evidence of payment via my WhatsApp digit 07087865788 to be included in the payment group.

 

18....

 

Suna isa gidan bakin inna ya mutu murus sai 'yan idanuwa ganin gida ne ba na wasa ba, ni ko nace dama Umma ce xata yarda 'yar ta ta auri mai rufin asiri kawai?? Inna ta fito cikin motar tana cewa "Fito da kafar ki ta dama in sha Allah gidan xama ne, yi nayi bari na bari, aure kuma da kike gani d'an xaman hakuri ne duk shi muka yi muka kawo yanxu da rai da lafiya, Allah ya maki albarka yasa gidan ki ne ke kadai don na xauna da kishiyoyi ban ji da dadi ba, kishiya masifa ce" Wani kallo Mujaheed ya dinga mata, inna na washe hakora tana kara kallon katon gidan tace "Toh kai Mujaheed baka da abinda xaka ce mata ne ka tsaya wani sandandan kana kallonmu, wannan ai ya ma fi gidanka girma wllh" Yace "Kece baki mata nasihar tun a gida ba amma ni nayi tun a can" Kuka kawai Seeyama take, inna ta hade rau tace "Ji shashanci don Allah, to ki bude ido ki ga gidan mana idan ba sae kin daina shegen kukan nan ba" Mujaheed ya karasa kusa da ita yana kallonta yace "Be the best wife you can be lil sis, wishing you a peaceful married life" rungumesa tayi tana kuka, shi ko ya dinga kallon imaan da ta ja can gefe tana 6a66aka dariya har da rike ciki, ganin kallon da yake mata ta shige cikin gidan da sauri bata kuma fasa dariyar ba, cike da damuwa Inna tace "Ni dai wllh wannan 'ya ta Bukar gani nake kamar ciwace ciwacen ta ya shafi kwakwalwarta, to banda haka taya xa a kawo yar uwarki dakinta tana kuka, ke baki bata hakuri ba kina dariyar mugunta, to Allah dai ya kai mu naki kiga iskanci wllh" tana fadin haka ta janye seeyama tace "Mu shiga ciki kiyi kukan a tsanake kin ji jikalle, kai kuma Mujaheed bayan isha ka xo ka daukeni, idan kuma ya kama a nan xan kwana to shikenan" daga haka suka wuce ciki shi kuma ya fita compound din da motarsa yana girgixa kai. Bayan Magrib da rashin arxiki inna ta sallami duk kawayen Umma yan kawo amarya, Aunty da Ammi dama basu dade ba suka bar gidan, tsaye inna tayi bakin kofa rai bace tana cewa "Wannan ai ba yi bane, sai kace baku da maxaje baku da mafada, amarya dai ga ta an kawota lafiya har ta hakura ta daina kuka, to ai kuma sai kowa ya kama hanyar gidansa sai kuma wata shekarar idan ta haihu, amma duk kun wani ja6e ba niyyar tafiya, a dai dinga jin tsoron, ni ma nan da ku ka ga ban tafi ba kakar ta ce, ni na haifi ubanta Ahmadu, bai baci ba ko da cewa nayi xan kwana, amma mutane karere kawai ku cika gidan yarinya kun ki tafiya, ko ita Rukayyar ce tace ku kwana tare da su bani da labari? To ni dai ba ruwana" Wa enda suka fita iskanci yi suka yi kamar basu ji abinda take cewa ba, wasu kuma haushi yasa duk suka bar gidan, a fusace inna tace "Mata wasu katangala kawai rai ba ga ta sun xaune ma yarinya a gida, ni ban taba ganin haka ba tunda uwata ta haifeni, ku barta daga ita sai kawayenta su ma a xo a sallamesu su kama gabansu mana" Inna na kallon imaan dake kokarin fita ta gefenta tace "Ke kuma ina xaki sanyi ya kare maki ki cuci d'a na da kashe kudi?" Imaan ta turo baki tace "Ina xuwa ni dai" inna tace "Toh kar dai kiyi nisa don Mujaheed ya kusa xuwa yanxu, ba ruwana in kwana su Ahmadu su min fada" imaan bata ce komai ba ta fita, tana ganin motarsa ta gane don layin tamkar rana saboda hasken fitilu, ta karasa gun motar ya bude ya fito yana kallonta, Ta sunkuyar da kai tace "Ina yini" yace "Lafiya lau Imaan, nan ne gidan sistern naki?" Kai ta gyada masa, yace "Maa sha Allah, Allah ya basu zaman lafiya" tace "Ameen" yace "Amma ba nan xaki kwana ba dai koh?" Ta xaro ido tace "In kwana kuma?" Murmushi yyi ya rungume hannu sa yace "Shi na gani ai, Idan kika kwana ai xaki yi inconveniencing amarya da angon" turo baki tayi tace "Toh ni dama ta ya xan kwana" yar dariya yayi yace "Gaskiya ne, yaushe xa ku koma gida?" Tace "Muna jiran yaya ne, xai maida ni da Maimoon da Grandma dinmu" yace "Ohk yayanku kenan" ta gyada masa kai, yace "Idan bai taho ba let me drop you people mana" ta xaro ido tace "Bayan ma yana hanya yanxu, ai shi ya kawo mu" Yace "Ohk then...." Bata kuma cewa komai ba, shi kam yyi shiru yana kallonta, a hankali yace "Kin yi kyau" Dauke kai tayi tana murmushi, shi dai bai fasa kallonta ba, murya can ciki tace "Kai kuma baka sa glasses dinka yau ba" wara ido yyi yace "Ya 6ata.... sai dai ki siya min wani" ta kallesa tace "Da gaske?" Yana murmushin sa mai kyau yace "Yea" Sunkuyar da kanta tayi, yace "Ko baxa ki siya min ba" Ta d'an kallesa tace "Xan siya" yace "Toh yaushe xan xo amsa?" Tace "Idan na siya" yace "Toh gobe nake so, I can't do without it" da sauri ta kallesa sai kuma ta dauke kai tana murmushi tace "Toh Allah ya kai mu" yace "Ameen... Da yamma xan xo amsa" ta girgixa kai tace "A'a kawai ka bar shi next tomorrow" Shiru yyi yana kallon bayanta.... Can yace "Or wancan ne yayan naku?" Imaan ta juya da sauri taga motar Mujaheed yayi parking, ta gyada masa kai a hankali, tunda Mujaheed yyi parking d'an nesa da su dama yake kallonsu, Sadeeq yace "Tunda ya gan mu bari in je mu gaisa" shiru tayi da farko, ganin yanda yake kallonta a hankali tace "Is it necessary?" Yayi murmushi yace "Baki son yan gidanku su san ni kenan?" D'an bude ido tayi tace "Toh kaje ku gaisa ni xan shiga ciki in kira su Maimoon" yace "Ohk" gate ta nufa tana satan kallon Mujaheed da ya bi ta da kallo gabanta na faduwa, Sadeeq kuma ya nufesa, sauke glass Mujaheed yyi ya bude motar ganin sadeeq, ya fito yana kallonsa directly cikin ido, sadeeq ya masa sallama hade da mika masa hannu, sai bayan kusan seconds biyar Mujaheed ya mika masa nasa yana d'an murmushi wanda iyakarsa lips, nan suka gaisa... Cikin cool voice Sadeeq yace "I am Dr Abubakar Ahmad" Mujaheed ya gyada masa kai kamar baxae ce komai ba, sai kuma yace "Muhammad Ahmad" Sadeeq yace "Maa sha Allah it's nice meeting you" Mujaheed yace "Same" Sadeeq yace "Alryt xan koma, sae da safe" Mujaheed yace "Ohk... kun yi sallama ne" Sadeeq yace "Sure" daga haka ya nufi motarsa ya shiga ya wuce. Inna bata fito parlon Seeyama ba sai da ta kada kan sauran mutanen dake parlorn, har Mujaheed ya gaji da jira cikin mota, Inna ta fito gate tare da Maimoon da Imaan ta shiga bayan mota tana cewa "Mujaheed kaga Gantalallu kila da so suka yi su kwana a gidan, don da ban masu jan ido ba baxa su tafi ba, ni dai ba ruwana" Maimoon ta bude front seat ta shiga, imaan ta shiga back seat gun inna, Mujaheed dai bai kulata ba yyi reverse, Inna tace "Ni bikin Imaan da na Maimoon ma gaskiya sae na xabi wa enda xa su raka su daki, iyaka kawai in xauna bayan mota ni da su don ina fatan ya xamo rana daya, Mujaheed ya ja mu in kai su dakunan su ya maida ni gida idan Allah ya yarda, ba katuwar da xata bi mu" Mujaheed dai driving yake har ya bar layin ya hau saman titi, lkci lkci ta madubi yana kallon imaan da ta ki yarda ta kalli gaban motar, inna tace "Mujaheed kaga kawayen uwar ka kamar mayu kuwa, wllh da kyar na kora su, duk sun ban wahala, ita ina ta samo su haka wasu lafta laftan mata ba kyan gani kamar aladu? kaii Rukayya dai shahararriyar mahaukaciya ce wllh" taka brake Mujaheed yyi bayan ya tabbatar bbu motar dake bayansa ya gangara gefen titi, inna ta saki salati tace "Lafiya Mujaheed, me ya sami motar" ya bude motar ya fita ya bude side dinta yana kallonta yace "Ita uwar tawa ce mahaukaciya?" inna ta bude baki tana kallonsa, sai kuma ta kalli Imaan tace "Ga reshen bishiya can, sauka ki karyo ki kawo masa...." Imaan ta hade kai da kafarta tana dariya kasa kasa, a fusace inna ta kunduma masa xagi tace "Na ce mata mahaukaciyar sharri na mata, da hankalinta ina ita ina gunduma gunduman matan da ta ajiye matsayin kawaye, wasun su idan suka xaune kanta shegiya nake idan bata suma ba bayan sun latse ta" yace "Ku saukar min a mota ku samu wanda xai kai ku gida Hajiya" kamar jira Inna take ta sauka da sauri tana kallon Imaan tace "In dai kin san motar ba ta Bukar bace ki sakko ki bar masa tsiyar sa" Imaan ta hade rai tace "Inna bai ce har da mu ba fa" Irin kallon da Mujaheed yyi mata yasa ta sauka da sauri don ya dade bai mata irin kallon ba, Inna ta kalli Maimoon tace "Ke kuma idan ba ta Amina bace motar ki sakko kema" Maimoon ta bude front seat ta sakko, inna ta fara matsar kwalla tace "Ku sama min Adaidaita sahu" ko kallonta Mujaheed bai yi ba ya rufe back seat dinsa ya shige motarsa ya kara gaba, inna ta bi motar da kallo tace "Allah dai ya isa, kuma sai Ahmadu ya min iyaka da Mujaheed yau, ni xai toxarta ya walakanta a bakin titi a kan Rukayya" Imaan ta tsayar da adaidaita ta fada masa inda xai kai su, Mai adaidaita yace "Ba can xan yi ba" bai gama rufe baki ba inna ta shige adaidaitan ta xauna, Imaan da Maimoon suka saki baki suna kallonta, Mai napep din ya juya yana kallonta yace "Baaba nace ba can nayi ba" a fusace tace "Dalla can mu je d'an nan, ko baka ganin dare yyi ne xaka ce min ba can kayi ba, jika na ne fa ya watsar da mu a titi yanxun nan yyi wucewarsa daga nayi ma katuwar uwarsa gyara, banda haka yaushe xaka gan ni bakin titi tsaye da gata na, motocin 'ya yana sun fi biyar wllh, ko da yake in mun je gidan ma xaka gane abinda nake nufi, ko kai so kake inyi ta tsayuwa kamar yar iska bakin titi?" Shiru yyi bai ce komai ba, Inna ta kalli su Imaan sannan ta kallesa tace "Yaro idan baxa su shiga ba ja ni ka kai ni gida, su kuma Allah ya kawo masu mafita, mu je ni dai" murmushi mai napep din yyi, Imaan ta turo baki ta shiga Maimoon ma ta shiga, inna tace "Atoh da kun tsaya jiran d'an sahun da xai je ku kwana a wajen" suna isa gida dama inna ta sauka napep din ta nufi gate tana gyara yafin mayafinta, Maimoon ta kalli Imaan dake dariya ta ja tsaki ta bude jakarta ta fiddo dubu daya ta basa ya bata canji ta wuce ciki, can suka ga inna har ta shige parlon su Maimoon, Imaan ta nufi part din su Maimoon ta bi bayan Inna, babu kowa parlon Abba hakan yasa inna ta dawo main parlor tana kallon mutanen da ta wuce da farko tace "Ahmadu baya nan ne" Daga kitchen Aunty ta leko tace "Bai shigo ba inna, kun dawo lafiya?" inna bata tanka ta ba ta fice parlon, bata tsaya ko ina ba sai part din su Imaan, ba kowa parlon sai kamshi dake ta tashi, cikin daga murya inna tace "Salama alaikum" Imaan ta bude kofar bedroom dinta tana lekowa, Inna tace "Ina Bukar din?" Daddy ya fito daga daki yace "Har kun dawo inna" karasawa cikin parlon tayi ko takalmanta bata cire ba ta xauna saman kujera tana share guntun hawayen idonta, Ammi dama na jin irin sallamar da inna tayi tasan ba lafiya don haka bata fito ba, duk xaton ta k'aran imaan ta kawo, Imaan da har ta cire kayanta ta sa Hijab kawai ta fito da sauri, Daddy na kallon inna a hankali yace "In ji dai lafiya inna" a fusace tace "Ina fa lafiya Bukar, shegen d'an ku ya watsar da ni tsakiyar titi gefen jaji yayi wucewarsa, daga nayi ma Rukayya gyara" Shiru Daddy yyi yana kallonta da mamaki, ta fashe da kuka tace "Gaskiya Bukar idan ba a bi min hakkina ba yau duk a station xa mu kwana gwara in kai karar can a bi min hakkina, da girmana da matsayina da martabata Mujaheed xai juye ni tsakar titi yyi wucewarsa?? Ae wannan babban magana ce wllh" Daddy ya sauke ajiyar xuciya yace "Subhanallah me ke damun Mujaheed haka" Inna ta tsaida kukan da take tace "Toh ai ba ni xaka ma tambayar ba, waya xaka dauka yanxu ka kirasa, kada ma ka nuna masa ina nan, kawai ce masa xaka yi ya xo xaka aikesa yanxun nan, daga nan sai kaji me ke damunsa ko wiwi ya fara sha bamu sani ba" Daddy ya kara sauke ajiyar xuciya, inna tace "Sae wani sauke sauken ajiyar xuciya kake Bukar, ko tsoron sa kake ne inyi ta kai na?" Yar dariya kawai daddy yayi ya dau wayarsa, inna ta tsuke fuska tace "Wllh yanda ya min tijara a kan uwarsa kai ma haka xaka masa tijara akan taka uwar, kuma idan baka ce masa aikensa xaka yi ba wllh baxai xo ba nan kuma xa mu kwasa mu tafi police station " Daddy dai bai ce komai ba yayi dialing number Mujaheed ba a dau lkci yana ringing ba ya daga, Daddy yace "Muhammad kana kusa ne?" Daga daya bangaren Mujaheed yace "Eh Abba" daddy yace "Toh ka xo parlor na yanxu" Mujaheed ya d'an yi shiru, kafin yace "Toh Abba" Daddy yace "Don't keep me waiting fa naji kayi shiru ko baka kusa ne?" Yace "Ina nan" Daddy yace "To ina xaune ina jiranka yanxu" Mujaheed yace "Toh" daga haka daddy ya katse wayar, inna tace "Kai xaka kwana a ciki wllh idan yaron nan bai xo ba Bukar" Daddy dai bai ce komai ba, Mujaheed ba don yanda yake jin kunyar daddy ba da fa ba xai je ba don yasan sarai inna na can, kuma da Abbansa ne ma ya kirasa ba lallai yaje ba, jallabiyarsa kawai ya xura ya fita dakinsa, banda girgixa kafa babu abinda inna take, da sallama ya shiga parlon, ba tare da ya kalli Daddy ko ita ba ya tafi ya xauna kasan lallausan carpet din parlon yace "Barka da dare Abba" Daddy yace "What happened between you and ur grandma yanxu?" Mujaheed ya daga kai yana kallonta yaga yanda ta wani tsuke fuska tana kallon sa, ya maida kansa kasa, inna na nuna Imaan dake kwance kan kujera tana kallonsu tace "Idan sharri na masa ga 'yar ka kwance kusa da kai ka tambayeta ka ji ko ba tsakiyar titi ya juye mu ba" Daddy ya juya ya kalli Imaan, a fusace Inna tace "Ke tashi xaune ki basa labarin abinda ya faru, ba tsakiyar titi Mujaheed ya sauke mu ba, naga kamar tantama Bukar yake" Imaan ta mike xaune tace "A'a ba fa tsakiyar titi bane inna, gefen hanya ne....." Rai bace Inna tace "Amma wannan anyi shegiyar 'ya... Dama akwai bambanci tsakanin gefen titi da tsakar titi, ke dai munafuka ce wllh" Imaan ta harareta ta gefen ido tana turo baki ta koma ta kwanta, Inna tace "Wllh Bukar gefen hanya yayi watsi damu, kuma kafin ya sauke ni don Allah mai yace min Imaan" da sauri Imaan ta daga hannu tace "A'a ba ruwana nima ban sani ba" Bude baki inna tayi tana kallonta, daddy yace "Yanxu dai ki tashi ki tafi ki bar ni da shi inna" inna tace "In tashi in tafi ka basa hakuri shima ya tafi xaka ce min" Tana fadin haka ta mike tace "Tun farko ma ban san me ya kawo ni gun Bukar ba, duk inda Ubansa ya tafi ai ya ci ace ya dawo yanxu" daga haka ta fice parlon fuska daure. Daddy ya hade rai yana kallon Mujaheed yace "Saboda baka da kirki xaka ajiye su bakin hanya Muhammad?" Mujaheed yyi kasa da kai bai ce komai ba, Daddy yace "Yanxu ka kyauta kenan, idan Hajiyar ka ce ko min abinda tayi maka xaka mata haka?" Yace "Kayi hakuri Abba" Daddy yace "Haba Muhammad, I am highly disappointed at you, this is very rude and stupid of you, she is our mother fa, no matter how she behaves baxa mu canxa ta ba" Mujaheed bai iya cewa komai ba, daddy yace "Ka tashi ka bi ta ka bata hakuri yanxu" yace "Toh, ayi hakuri Abba" Daddy ya kalli imaan yace "Ke kuma I've warned you times without number ki daina fada mata magana anyhow amma baki ji ko, xan fara sa6a maki soon wllh idan baxa ki canxa naughty attitude din nan ba, will you dare talk to ur mother  that way?" mikewa xaune tayi kamar xata yi kuka, Mujaheed ya tashi yace "Xan je in sameta yanxu Abba" daga haka ya fita parlon. Washegari da safe da kyar imaan ta tashi tayi wanka tayi breakfast da Ammi ta ajiye mata a dinning, Ammi tace "Idan kin gama ki dau magungunanki ki sha kada in tuna maki, kuma da Ac kika kwana ko?" Ta xaro ido tace "Ammi wllh A'a" Ammi tace "Toh ga mura nan na shirin kama ki" Ta langwabar da kai tace "Jiya fa da daddare a napep muka dawo, kin ji sanyi kamar xanyi freeze a hanya"  Ammi ta fiddo kindirmo a fridge yayi sanyi sosai ta ajiye mata a dinning din tace "Gashi ki kai ma inna inji daddyn ki, you make sure kin goge min dinning table idan yayi stain" Ta marairaice tace "Ammi my legs are aching me fa" Ammi ta harareta ta wuce dakin ta, Imaan na gama breakfast ta tashi ta dau kindirmon ta tafi kai ma inna, Tana shiga parlon bayan ta ajiye tana kallon inna dake ta kukkula dubulan da cin cin a leda sai ga Umma ta shigo parlon da sallama, Inna ta kalleta ta ci gaba da abinda take ta amsa sallaman ba yabo ba fallasa, Umma ta dafa kujera tace "Ina kwana inna" inna tace "Lafiya lau" Umma tace "Ya gajiyan taro" inna tace "Bana tare da gajiya duk ya bi lafiyar gado" Umma tace "Toh Alhmdllh Allah ya saka da alkhairi yaji k'an mahaifa" inna tace "Ameen" karasawa tayi kusa da inna ta ajiye ledan hannunta tace "Ga wannan dai ba yawa" inna na kallon ledan tace "Meye wannan din? Ke imaan xo ki bude" imaan dake xaune ta mike ta karasa kusa da Inna, Umma ta bi ta da kallon gefen ido, durkusawa tayi ta bude ledan ta ciro atamfa da pack din sabulu guda biyu da turare mai tsada" Inna ta bude atamfar tana kallo da kyau, tace "Holland ce wannan din?" Umma tace "Ehh" inna ta tabe baki tace "Toh, da dai basirar ki ce hakan da sai ince Allah yyi albarka, amma wannan ko kaffara baxan yi ba Ahmadu ya sa ki, Allah ya masa albarka ya kare min shi duk inda xai shiga, Allah ya ci gaba da hada kansu da d'an uwansa Bukar ya raya mai 'ya yansa yayi masu albarka, ita kuma wannan da ya aurar Allah xaunar da ita da mijinta lfya, ke kuma nagode da isar da sako" Umma ta dinga kallonta ko kiftawa babu, Imaan sai danne dariyarta take, Inna ta ci gaba da kulla dubulan dinta a leda, Umma tace "Sai anjima" inna tace "Mu jima da yawa" daga haka ta nufi kofa, inna na kallon Imaan tace "To ke sai kiyi ta kanki, don wllh jiya Mujaheed ce min yyi xai kakkarya ki ya xane ki, wai ya ganki da wani mai mota a tsaye a kofar gidan seeyama, imaan ina kuma kika samo mai mota kike ta boye min ban sani ba ni Asabe??" Umma ta d'an dakata bakin kofa jin abinda inna ke cewa, Imaan ta turo baki tace "Shi sa ma xan tashi in tafi yanxu kar ya xo nan, to har kun shirya ne inna?" Inna tace "Haba dai sai kace wata yarinya, to me yyi min da baxa mu shirya ba, wai na ce ma Rukayya mahaukaciya, ke ki ji fa? to me ta min xan xageta banda abunsa ma dai, kawai daga ina mata gyara? Ni fa na yarje ma Ahmadu ya aureta wllh, baki ganta ba a lkcn yar siririya yanda kika ganki, kamar iska xai hure 'yar banxa ta fadi, gashi iyayenta basu da komai basu kuma ba wani ajiya ba, wani d'an akurkin gida fa gare ubanta a lkcn, to ni ban masu bakin ciki ba don xuciya ta fess mai kyau ne na yarda Ahmadu ya auro mana ita a haka, ke kinga wahalar da nayi da ita kuwa? Wllh kare baxai ci ba, gashi ba abinda ta iya a lkcn, har girki ni ke sa ta kan hanya ina koya mata, kishiyoyina su yi ta jin haushi yanda nake ji da ita bana son ko k'uda ya ta6ata har dai ta samu cikin wannan yaro Mujaheed, sai kin ga wahalar da nayi mata sbda laulayin da ta dinga yi ba kakkautawa, to ni duk ba wannan ba don nasan sakayya ta dai na gun Allah, to don kuma yanxu Rukayya ta xama abinda ta xama sai me xai dameni ni patuu? ga dai Amina na bina sau da kafa ga Aisha, ni dai abinda na sani shine Mujaheed ai xai yi auren, to nan xata d'an dana ko da dadi ko babu, abinda duk abinda ka shuka shi xa ka girba, tsaf xan karance ma yarinyar xaman da xata yi da ita, muna nan da ku sai an dinga xuwa daukata shari'a a mota...." Imaan har wani kwanciya tayi kan kujera tana dariya amma ba mai sauti ba, Umma da ta makale jikin kofa ta fita ta sa takalmanta, inna ta tabe baki tace "Wllh Mujaheed da gwiwowinsa bibbiyu ya durkusa ya dinga ban hakuri tun ban kai ga gaya ma ubansa ba, to tunda naga yyi nadama kawai sai na yafe masa don ba halinsa bane gaskiya bai taba juye ni a tsakiyar titi ba tunda mu ke" Imaan ta fashe da dariya tace "Jiya dai ya juye ki ai"

Post a Comment for "IMAAN 17-18"